Around 9:30pm Aliyu ya kira Fadwa,saeda yyi ringing sau biyu ta d'aga,suka gaisa suka d'anyi hira, though Fadwa bata wani sake dashi ba amma be damuba dan yana tunanin ko bata gama haqura bane amma yasha alwashin saeta zo ta haqura gabaki d'aya sun koma yadda suke harma sufi da d'in,daga qarshe sukayi sallama dan ce mishi tayi zatayi bacci..
Washegari Abba da wani abokinsa sukayi tafiya zuwa birnin tarayya wato Abuja,inda suka jesu kan maganar auren Aliyu da Fadwa,sunsha tarba sosae,anyi musu kalolin abun ciye*2 dana shaye*2 dan musanman Anty Rauda ta gayyato wata qawarta me suna Haj.Bilki dan ta tayata yin ayyukan dama tun safe Baffa ya sanarda ita cewa Abban ya kirashi a waya ya sanardashi zuwansu.Bayan sun d'an tab'a abubuwanda aka kai musu sae suka dawo palour suka zazzauna,lokacin Anty Rauda ta shigo suka gaisa saeta fita,su kuma suka fara maganan abunda ya kawosu,daga qarshe dae suka tsaeda ranar auren nanda 1month kacal,a take Abba ya bada sadaki naira 50,000 sannan sukayi sallahn azahar kafinnan sukayi sallama suka tafi..
漏Hama G Muh'd
[10:27am, 12/2/2016] Eesha Bebe: 馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯 *KOMAI RINTSI PART 3*馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯
This page is dedicated to u my besty *(Eesha bebe馃槝)* luv u buhu buhu鉂�
庐EHW
*_Written by鉁嶐煆� Hamerh gee Muh'd馃尫_*
Page1鈨�3鈨�5鈨�
Bayan tafiyarsu Anty Rauda ta kira Momy take sanarda ita yadda akayi,Alhmdllh Momy ta ambata,Anty Rauda tace "inaso zuwa next week ki turo mun Fadwa da Allah zamuje Dubai da ita dan siyayya kuma akwae gyare*2 daya kamata ayi mata",Momy tace "ba komai insha Allah zatazo",Anty Rauda tace "ameen,amma wa zae kawota?",Momy tace "ko Aliyun ba",Anty Rauda tace "ina fa ace Aliyu ya kaita har wani gari,karkiyi wannan d'anyen aiki Amina,karki manta fa ba'a d'aura auren bafa tukunna sannan in ya zamana sun keb'ance su kad'ae komai fa zai iya faruwa dukda mun san halayyarsu duka amma kin san shaid'an",Momy ta nisa sannan tace "wannan gskiya ceh wllh,wani lokaci mu iyaye mumuke janyo sanadiyyar lalacewar yaranmu kinga kaman wannan za'a ae ba komai bane amma tabbas zae iya zama komai d'in,nagode qwarai da wannan tunasarwa taki Allah ya shiryar mana da zuri'a",Anty Rauda tace "Ameen ya Allah,yanxu dae ki bar maganar zan turo Muhammad yazo ya kawo mun ita insha Allah,zuwa next week Wednesday saeta shirya zaizo dan tafiyar tamu will b Thursday insha Allah",Momy tace "Allah ya kaimu nagode sosae",Anty Rauda tace "ba komai yiwa kaine ae",sukayi sallama..
Momy ta sanarda Fadwa cewa Muhammad zaezo su tafi Abuja on wednesday amma bata fad'a mata komai akan zuwan nata ba itama kuma bata damu da tambayar dalilin zuwan nata ba kwae dae tasan cewa Anty Rauda ceh tace hakan..
Bayan su Abba sun dawo abokinsa yyi mai sallama Abba ya mai godiya sannan ya tafi gida,waya ya d'aga ya kira num Momi lokacin tana main palour tana jin wa'azi,yace tazo ta sameshi a d'akinshi,ta ansa sannan ta miqe ta nufi d'akin,kan rug na d'akin ta sameshi tayi sallama ya ansa saita shiga ta nemi guri ta zauna,ya dubeta yace "mun gama maganar auren yaran nan yau harma an bada sadaki,nanda 1month in Allah ya kaimu",Momi tace "Allah ya kaimu da rai da lfya",Abba yace ameen sannan yace...
漏Hama G Muh'd
[10:33pm, 12/5/2016] Hamagee馃尫: [10:27am, 12/2/2016] Eesha Bebe: 馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯 *KOMAI RINTSI PART 3*馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯
*Dedicated to Mom Sudaes*馃槝
庐EHW
*_Written by鉁嶐煆� Hamerh gee Muh'd馃尫_*
Page 1鈨�3鈨�6鈨�
"Yanxu abunda nake so kiyi estimate na kud'in da kke ganin zai isa na kayan lefe kafin daga baya sai ayi sauran",Momi tace "ba komai innayi zan maka magana zuwa ajima,kaga ko jibi sae muje Umrah daga nan sae'a sayi wasu daganan kuma mu dawo ta Dubai dan gaskiya nan yafi kaya,in mun dawo gida kuma sae a siya wasu a Kano kafin mu komo",Abba yace "good idea,Allah ya kaimu",Momi tace Ameen,yace "inaganin wannan gidan nawa na State lowcust yyi musu ae ko dan last month ma aka sake gyara shi anjima zamuje ki gani",Momi tace "yyi sosae ma Allah ya kaimu anjima d'in"Abba yace "ameen".Around 5:30 su Abba sukaje duba gidan,hmmm gida ya had'u fa馃槏..Babban flat neh a tsakiya gefen anyi shuke*2 na flowers da fruits,a wani side kuma wajen parking motoci neh,wanda a qalla zaayi parking motoci hud'u a iya wajen banda filin gidan,kusada gate kuma d'akine qarami na megadi,cikin gidan ya wuce nayi muku bayanin sa a wanga littafi iyakaci zan iya ceh muku gidan ya had'u,ba gidan kad'ae ba har anguwar abun burgewa ceh dan tayi mugun burgeni kasancewar batada hayaniya shirune ta ko'ina,Momi tace "masha Allah gida yyi"..Four bedrooms neh a gidan,biyu na kallon juna sae dogon corridor a tsakiya,kowannen su da babban toilet a ciki,d'akunan Fadwa kenan,sae in aka zo palour za'a ga wata qofa can wacce take kallon qofar da zae kaika side na Fadwa,nan kuma d'aki d'aya neh a cikin wani palour madaidaici,side d'in Aliyu kenan,shikuma idan ka fito same palourn can gefe zaka hangi dining area,gefenshi kuwa kitchen neh babba,har an sassaka kitchen cabinets,gida dai masha Allah,bayan sun gama kallo sai suka fito suka tafi..
Da daddare Abba ya bata kud'in bayan tayi estimating,1.5m ya bata,tayi godiya sannan ta sanarda Aliyu da Saeema abunda ake ciki,sannan ta cema Saeema ta sanarda Suraj idan bbu damuwa sae suje tareda ita,hakan kuwa akayi..
漏Hama G Muh'd
[10:27am, 12/2/2016] Eesha Bebe: 馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯 *KOMAI RINTSI PART 3*馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯
*Dedicated to Mom Sudaes*馃槝
庐EHW
*_Written by鉁嶐煆� Hamerh gee Muh'd馃尫_*
Page1鈨�3鈨�7鈨�
Bayan kwana biyu Saeema tazo gida dan Suraj ya amince,Momi kuwa ta gama komai na visa dama tafya kwae ya rage,Aliyu neh ya kaisu airport suka tafi,saeda sukayi 1week a Saudiyya kafin nan suka dawo Dubai nanma sukayi sayayya sae suka dawo Kano inda suka qarasa wasu sayayyan sannan suka dawo gida,da daddare Suraj yazo yyi ma Momi sannu da dawowa daga nan ya tafi da matarshi dan yyi missing nata sosae..
Fadwa kuwa ranan Wednesday d'in Muhammad yazo ya kaita Abujan inda washegari suka jesu Dubai da Anty Rauda,siyayya sukayi na gani na fad'a,daga kan kayan d'akuna,palour,kitchen har kayan da zata sanya a duk events na bikin a can suka sayo,Anty Rauda bata gaji da kashe mata kud'i dan haka saeda ta tabbatar sun gama sayen komai kafinnan suka juyo gida ranan Asabar..
Shirye*2 akeyi a gidaje ukunnan bbu tsayawa,gidansu Aliyu,gidan Anty Rauda da gidan Momy,Ummah ma ba'a barta a baya ba dasu Tasleem,Jaleel da Yaya Faruk,kowa sae hidima yake,yau saura 2days bikin Fadwa da Aliyu..
漏Hama G Muh'd
[10:27am, 12/2/2016] Eesha Bebe: 馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯 *KOMAI RINTSI PART 3*馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯
*Dedicated to Mom Sudaes*馃槝
庐E.H.W
*_Written by鉁嶐煆� Hamerh gee Muh'd馃尫_*
Page1鈨�3鈨�8鈨�
Anty Rauda da kanta take gyara Fadwa,Fadwa tasha gyara tayi kyau ta d'an qara haske ga wani kanshin da take zubawa.Ana gobe za'ayi Momy da hajiya suka zo Abuja,Momin Saeema,Saeema da Suraj,Aliyu,Umma Tasleem da Jaleel duk sunzo,gidan a cike yake danma babban gida neh,Jaleel da Tasleem tareda Umma a gidan Yaya Faruq suka sauqa..
Yau ya kasance ranar Thursday neh,kuma yau za'ayi kamun Fadwa,an qawata waje sosae yyi kyau da flowers colourn kayan amarya wato red and blue,colour of d day kuma blue colour neh,outfit na kowa kenan,bayan an shirya amarya kowa ya shirya,y'an uwa da abokan arziqi kowa ya hallara,kuda kanku kun san cewa komai yyi excellent ba saena ce muku komai ba,aka sha hidima aka watse,washegari akayi walima shima yyi kyau sosae..
Yau Saturday 28th February sannan kuma ranar auren Aliyu da Fadwa,anyi d'aurin aure lfya inda ango yyi ta murna y'an uwa na taya shi,aurensu yyi jama'a sosae,dan ba qaramin taruwa akayi ba,bayan an gama hidimar d'aurin auren ne Ango da abokansa suka nufi wajen reception da abokan suka shirya mai shi bema sani ba,Suraj neh kan gaba wajen shiyawar...
Washegari ranar wuni that's on Sunday,y'an uwa suka tattari amarya suka koma Yola da ita,Fadwa tayi kuka kamar ba gobe haka aka sata a motar tana riqeda hannun Anty Rauda da qyar ta saketa,saeda tasa Anty Rauda yin qwalla,su Momy da Momyn Saeema da haj kuwa tun jiya suka dawo saboda yin jeren gidan,sun gyara gidan komai ya zauna yyi daedae..
漏Hama G Muh'd
[10:27am, 12/2/2016] Eesha Bebe: 馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯 *KOMAI RINTSI PART 3*馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯
*Dedicated to Mom Sudaes*馃槝
漏E.H.W
*_Written by鉁嶐煆� Hamerh gee Muh'd馃尫_*
Page1鈨�3鈨�9鈨�
Koda su Fadwa suka iso ba gidanta aka kaita straight ba,gidansu Saeema kowa ya sauqa though akwae wasu way'anda suka sauqa gidan Momy amma basuda yawa.Anan suka qarasa wunin,sae bayan sallahn isha'i around 8:00pm akaje dinner,Fadwa and Aliyu look so lurvely sun matuqar yin kyau gashi shigansu yyi match,wani hadd'ad'en french less tasaka jikinsa Army green da gold neh,yyi mugun haskawa saeta sa head,purse,takalmi da jewelries army green kasancewa yafi kad'an ajikin kayan kuma ya haska sosae,Aliyu kuma yasa wata bugaggiyar shadda me tsada army green sae d'an ratsin aikin jikin shaddar akasa light brown zare,takalmi da hula light brown,wayyo sunyi kyau馃槏,ga decoration na gun ma yyi sosae,ansha hidima an gama har mutane sun fara watsewa dan lokacin dare ya d'anyi,past 10 neh,koda aka dau amarya gidan Momynta aka kaita aukayi mata nasiha sosae kafinnan aka kai amarya d'akin,Fadwa tayi kuka kaman bazata daena ba..
漏Hama G Muh'd
[10:27am, 12/2/2016] Eesha Bebe: 馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯 *KOMAI RINTSI PART 3*馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯
*Dedicated to Mom Sudaes*馃槝
庐E.H.W
*_Written by鉁嶐煆� Hamerh gee Muh'd馃尫_*
Page1鈨�4鈨�0鈨�
Bayan,frnds sun gama nasihun su kowa ya tafi abunsa,Suraj da Saeema tare suka tafi gida suma duk sun gaji,Aliyu kuwa na dawowa yyi wanka tareda yin alwala yazo yace da Fadwa tayo alwala,daba din sallah bace data qiyi,but wat could she do? Noting dan haka ta miqe ta shiga toilet d'in fuskanta duk hawaye danma ansata ta wanke makeup na fuskanta lokacinda taje gidan Momy,Anty Raida ceh tasa ta sannan bayan tayi wanka ta bata wani turare me shegen dad'in kamshi tayi wanka dashi dan gabad'aya jikinta ta shafa shi sannan tasata ta canza kaya..
Bayan tayi alwala ta fito ta samu Aliyu na kan jiranta suyi sallahn,walldrop ta bude dan dubo himar,walldrop d'in cike yake da kayan Aliyu aranta tace this is his room kenan,ta rasa yadda zatayi,duk abun da take yinnan Aliyu na kallonta ya taso ya nufa inda take cikeda murmushi a fuskarshi yace mata "hijabi kke nema?"bata ko kalleshi ba tace "eh",yace "jirani ina zuwa",fita yyi ya koma d'akinta ya dauko ya dawo ya bata,ta saka sukayi sallan,suna idarwa tayi adduo'in ta sannan ta miqe,bata son fita dan kar yaga rashin kunyarta ace daga zuwan amarya harta ware zata je wani gun dan haka ta kwanta a qasa dan bacci takeji,Aliyu yyi yyi da ita kan ta koma kan gadon amma ina qitayi,naman daya kawo da drinks ma bata ko kallesu ba tace mai a qoshe take,be sake neman wani abu a wajenta ba ya dawo gadon ya kwanta,ita kuwa har tayi baccin ta,ranan Aliyu da missing nata yyi bacci.
漏Hama G Muh'd
[11:16am, 12/8/2016] Hamagee馃尫: 馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯 *KOMAI RINTSI PART 3*馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯
*Dedicated to Mom Sudaes*馃槝
庐E.H.W
*_Written by鉁嶐煆� Hamerh gee Muh'd馃尫_*
Page1鈨�4鈨�1鈨�
Washegari da asuba Aliyu ya tashi ya shiga toilet yyi alwala sannan yazo ya tashi Fadwa,fitowa yyi dan neman masallaci,be wani sha wuya ba kuwa ya samu,Fadwa kuwa tashi tayi tayi alwala saeta fito ta nemi inda d'akinta yake ,anan tayi sallahn,bayan ta idar ta tashi ta hau gado ta kwanta tana jin shigowarshi..
Koda Aliyu ya shigo bega Fadwa ba be wani damuba dan yasan ta tafi d'akinta neh dan haka ya koma ya kwanta.Da safe Momi ta aiko musu da breakfast,koda yaje d'akinta kiranta saeya ji qofan a rufe kuma batada niyyar bud'ewa,ya kira wayanta yaji ko bacci takeyi amma shiru bata ansa ba kuma tana jin shi,qarshe dae ya haqura yaje yyi breakfast dinshi ya bar mata nata saeya koma d'akin yyi wanka ya shirya zuwa office dan yau Monday neh.Bayan ya fito ya sake trying ko Fadwa zata bud'e qofan amma sam kaman bbu mutum agun shidae yasan tana d'akin dan d'azu yaji motsinta,message yyi mata kamar haka:
*_Hlw dear,na tafi office saena dawo,kuma dan Allah kada ki zauna da yunwa kici abinci kinji,miss u saena dawo!_* sae yyi sending sannan ya fito ya tafi..
漏Hama G Muh'd
[11:16am, 12/8/2016] Hamagee馃尫: [10:10am, 12/5/2016] Hamagee馃尫: [8:20am, 12/5/2016] Hamagee馃尫: 馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯 *KOMAI RINTSI PART 3*馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯
*Dedicated to Mom Sudaes*馃槝
庐E.H.W
*_Written by鉁嶐煆� Hamerh gee Muh'd馃尫_*
Page1鈨�4鈨�2鈨�
Koda Fadwa ta karanta text d'in dariya tayi a ranta tace ae yunwa ba uwar kowa bace,bayan ta gama dariyanta saeta tashi ta bud'e qofan ta fito dama already tayi wankan ta tasa kaya gashi tayi kyau,tazo ta d'au plate ta d'ebi paper-soup sannan ta had'a tea sae bread,bata son yam ball d'in shiyasa bata ciba,a hankali take cin abunta harta gama sannan ta tashi ta tattara shirgin,ta juye na juyewa saiya wanka kwanukan ta kikkifa su,bayan ta gama tazo ta gyara kan dinning table d'in sannan ta koma palour ta zauna tana kallo,can around 12:30pm Momi ta aiko musu da lunch,taje ta bud'e qofar ta karb'i abincin sannan ta d'ebo na safen ta bada a mayar tayi godiya sannan ta dawo ta rufe qofar,setting table tayi saeta kashe kallon data kunna ta koma d'aki dan tasan Aliyu ya kusa dawowa kuma bata so su had'u,ta rufe qofar sannan tayo alwala tayi sallah,tvn d'akin ta kunna sannan ta koma gado tana kallo,can taji shigowan Aliyu bata ko matsa daga inda take ba ta cigaba da kallonta..
Aliyu neh ya shigo a gajiye,side d'insa straight ya wuce ya canza kaya ya fito dan ba kad'an ba yunwa yake ni,yazo palourn gurin dinng ya duba yaga flasks na abinci ga plate,spoon,cup an ajiye,yaji wani dd'i dan a tunanin shi Fadwa ta sauko dan haka yace bari yaje gunta sae kuma ya fasa yace bari ya fara cin abinci dan gaskiya in yaje ma bazata gane mishi ba dan yunwa yake ji ssae,ya zauna ya d'iba abincin shi yaci yasha ruwa sannan ya tashi ya nufi d'akinta,knocking ya shiga ya amma shiru bata anda ba balle tayi attemptng bud'e qofar...
漏Hama G Muh'd
[8:47am, 12/5/2016] Hamagee馃尫: 馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯 *KOMAI RINTSI PART 3*馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯
*Dedicated to Mom Sudeas*馃槝
庐E.H.W
*_Written by鉁嶐煆� hamerh gee Muh'd馃尫_*
Page1鈨�4鈨�3鈨�
Daya gaji da knocking d'inne yayi tafiyarshi zuwa d'akinshi,ya nemi gu ya zauna,ya jima a gurin yana tunanin irin zaman sunnan kafin ya tashi yaje ya kwanta,can barci ya d'ibeshi..
Fadwa ma baccin take ji dan haka ta miqe ta kashe kallon ta dawo ta kwanta,har bacci ya fara d'ibanta wayanta ta shiga ringing,kamar a mafarki taji ta tashi wayar na gefenta dan haka ta d'auko taga me kiran,Saeema ceh dan haka tayi saurin d'agawa,"Hello saeema ya kke",cikin muryan bacci take magana,Saeema tace "lfya ta qlou,ya kke da angon kin dan nasan kuna tare yanxu",cikin zolaya ta fad'a,Fadwa tace "kedae baki gajiya da zolaya to yyi barci nima yanxu daga baccin na tashi",(ta b'oye mata halinda suke ciki),Saeema tace "y'an hutu,ni ba wannan ba ina son in tuna miki cewa next Monday me zuwa in Allah ya kaimu zamu koma scul karki saki jiki ki dd'in amarci yasa ki mance",driya Fadwa tayi kafin tace "ai inaga nafi ki riqe date d'innan wayace miki zan manta",Saeema tace "ohoo dae,nidae na tuna miki dan nasan for sure kin sakankance kin mance",Fadwa tace "yanxu haka fa kema kiranki akayi aka miki tuni kkazo kina mun kumfar baki anan",Saeema tace "koma miye dae karki shagala next Mon back to scul".Haka sukayi ta zolayar junansu daga qarshe sukayi sallama kowa tace ma y'ar ta gaida mijinta..
Bacci neh me nauyi yyi gaba da Fadwa,ba ita ta tashi ba sai past 4,tana tashi ta shiga tayi alwala ta fito tayi la'asar d'inta,bata ma san tym ba lokacin saeda ta duba wayarta,ta tashi ta bud'e qofa dan cin abincin rana,tana bud'ewa sukayi ido biyu da Aliyu,yan zaune a palour kan kujeran dake facing side nata,dawowarshi daga sallah neh ya zauna a gurin yana kallon ball,Fadwa ta tsaya cak tama rasa wacce hanya zata bi,ta koma d'akinta neh koko tayi fitowar ta tayi abunda zatayi ta koma?ta rasa nayi,Aliyu kuwa kallonta yake bbu ko kyafta ido,ya tashi ya nufa inda take tsaye..
漏Hama G Muh'd
[9:35am, 12/5/2016] Hamagee馃尫: [9:11am, 12/5/2016] Hamagee馃尫: 馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯 *KOMAI RINTSI PART 3*馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯
*Dedicated to Mom Sudaes*馃槝
庐E.H.W
*_Written by鉁嶐煆� Hamerh gee Muh'd馃尫_*
Page1鈨�4鈨�4鈨�
Tafiya yake idonshi na kan nata,itama shi d'in take kallo,yana qarasowa ta fara jaa da baya,yazo zae riqo hannunta tayi saurin shigewa d'aki tasa lock,yyi yyi da ita kan ta bud'e ta saurari abunda zaice amma ina,qi tayi ta bud'e,daya gaji neh ya bar gurin ya koma ya zauna,ya jin dd'in irin rayuwarda sukeyi amma yana iya qoqarinsa ya jure saboda yana sama ransa cewa komai laifinsa neh,saedae ya d'aukar ma kanshi alqawarin mantarda ita abunda ya faru,ta koma Fadwar shi ta asali dan yanxu bata asali bace kuma shiya maidata hakan dan haka shi zae dawo da ita..
[9:34am, 12/5/2016] Hamagee馃尫: Koda Fadwa ta rufe d'akin,kuka ta fara yi wanda bata san dalilin yinsa ba,ita dae all she knows is that tana son Aliyu but meyasa ta kasa haqura da abunda yyi mata after all ta haqura da kowa but y not him?ma kanta take yima wannan tambayar,nima dae hakan na gani馃檨ku faa??..
Ta jima a gurin kafin ta tashi ta koma kan gado ta zauna,tana nin fitar Aliyu da kaman 5mins haka ta tashi ta fito ta nemi abunda zata ci,tana gamawa ta kwashe taje ta wanke sannan ta dawo d'akinta tayi alwala tayi sallahn magrib.
Da gangan Aliyu ya fita,saboda ta samu taci abinci,koda ya fita bbu inda zaeje amma dae yaqi dawowa saboda ita,bayan yyi sallahr magrib da isha ya shigo gidan,bayan an kawo musu dinner yaci nashi ya koma d'aki ya zauna yana kallo..
漏Hama G Muh'd
[10:09am, 12/5/2016] Hamagee馃尫: 馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯 *KOMAI RINTSI PART 3*馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯
*Dedicated to Mom Sudaes*馃槝
庐E.H.W
*_Written by鉁嶐煆� Hamerh gee Muh'd馃尫_*
Page1鈨�4鈨�5鈨�
Washegari da wuri ya shirya yazo qofan d'akinta as usual yyi knocking ko zata bud'e amma bata bud'e ba,daga ji ma bacci takeyi,yyi mata text na cewa ya tafi office saeya dawo sannan yyi maza-maza ya tafi beko karya ba.Sae wajen 9:00am Fadwa ta tashi tayi brush tayi wanka sannan ta fito tasa kaya,tayi matuqar yin kyau,ta d'au wayanta dan duba time saeta ga new message dan haka ta shiga ta gani,murmushi tayi da ta gama karantawa,ta ajiye wayan ta fito palour,ji tayi kamar motsin mutum a waje dan haka ta leqa ta windown wajen qofan,wanda yake kawo musu abinci ta gani tsaye da gani har ya gaji da knocking,tayi saurin komawa d'akinta ta d'auko gyale ta yafa kafinnan ta bud'e qofar,bayan sun gaisa take cewa "yi haquri ka jima anan ko?",yace "eh,bbu komai karki damu,ni zan tafi",tace "to mungode ka gaida Haj",yace "zata ji" sannan ya tafi ita kuma ta shigo ciki,breakfast ta zauna tayi abunta..
鈽呪槄鈽呪槄鈽呪槄鈽呪槄鈽呪槄鈽呪槄
A kwana a tashi bbu wuya yau satin su Fadwa uku kenan da aure,kullum idan Aliyu zae fita saeya ajiye mata kudin zuwa makarantar ta a kan dinning,idan tazo fita saeta dauka,abinci kuma koda yaushe tana yi,duk abunda ya dace ta mishi tana yi,saedae magana har yau bata had'asu,kamar koda yaushe tana wanke toilet d'inshi dan sae 2:00 noon za takeda makaranta yau,kuma kullum ta saba idan Aliyu ya fita sae 3:00pm yake dawowa shiyasa ma basa ko had'uwa.
Aliyu na isowa office ya tuna be d'auko wasu files ba kuma yanaso yyi submiting neh dan haka ko shiga beyi ba ya koma motar ya juya zuwa gida,gudu-gudu yake tafiya harya iso,me gadi neh ya taso zae bud'e mishi qofa yace aa ya bari ba shiga zaiyi ba abu kwae yazo d'auko,me gadin ya koma ya zauna bayan Aliyu ya shigo.Key ya nema ya bud'e qofar sannan ya shiga,be tsaya wata-wata ba kai tsaye ya nufa dakinsa,yana shiga lokacin kuma Fadwa na fitowa daga toilet ta gama wankewa kenan,Aliyu harya manta abunda ya dawo dashi dan duk gaggawar dayake yi bbu shi a yanzunnan.Fadwa na tsaye a inda take tana mishi kallon mamaki dan bata tab'a jin ya dawo at this very time ba..
漏Hama G Muh'd
[10:34am, 12/5/2016] Hamagee馃尫: 馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯 *KOMAI RINTSI PART 3*馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯
*Dedicated to Mom Sudaes*馃槝
庐E.H.W
*_Written by鉁嶐煆� Hamerh gee Muh'd馃尫_*
Page1鈨�4鈨�6鈨�
Aliyu ya qaraso inda take ga mamakinsa bata qara step ko d'aya ba,dan haka ya fara mata magana "sannu da aiki",tace "yauwa",ta zata wuce ta gefenshi ya riqe hannunta gamm,ya juyo itama juyowan tayi yace "y can't we live like every couple do?",bata ce mishi komai ba sae kallon shi kwae da takeyi,ya cigaba "mun yi 3weeks da yin aure amma befi sau biyu na ganki ba sae kuma meyasa ba zaki bar abunda ya wuce ba Fadwa,meyasa bazaki bani chance nayi prooving miki yanda nakr sonki ba?meyasa kka zab'i kullum ki barni cikin kad'aeci,meyasa kke haka",qwalla fal a idonsa,yyi mugun bata tausayai amma bata san me zata ceh mishi ba dan haka tayi shiru sae hawayen da suka fara zuba mata,Aliyu yace "am talking to u just tell me d reason pls,nasan na miki laifi amma ba na nemi afuwanki ba meyasa bazaki haqura ba? Ba komai zan cigaba da haquri har lokacinda zaki haqura dani amma ki sani u'r really hurting me"ya sake mata hannu ya juya zai duba files d'in,qwallan idon shi ya goge,ya d'auka file d'in zae fita kwae yaji ta rungume shi ta baya,kuka sosae takeyi ba tsayawa,har cikin qwaqwalwan shi yake jin kukan ko kad'an baya son ganin damuwarta balle kuka,ranan da ta fad'o jikinshi a gidansun nan ya tuno,yaune rana ta biyu da suka tab'a jiki,wani abune ya soma mishi yawo a kai ya rasa inda zaiyi saedae har yanxu bata ce dashi komai ba,sae kukan da takeyi..
漏Hama G Muh'd
[11:16am, 12/8/2016] Hamagee馃尫: [10:34am, 12/6/2016] Hamagee馃尫: 馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯 *KOMAI RINTSI PART 3*馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯
*Dedicated to Mom Sudaes*馃槝
庐E.H.W
*_Written by鉁嶐煆� Hamerh gee Muh'd馃尫_*
Page1鈨�4鈨�7鈨�
Aliyu neh ya juyo ta gaba saeya jaa ta zuwa kan gado ya zaunar da ita shima ya zauna a gefenta yana share mata hawaya yyi hugging nata yana d'an buga bayanta irin yadda ake ma yara idan rikicin su ya tashin nan,sun kai good 10mins a haka kafin kukan ya tsaya,itace ta fara magana "Yaya Aliyuu!!" Wani irin sanyi neh ya ziyarci zuciyar Aliyu dan rabon daya ji Fadwa ta kira sunan shi harya manta gashi kamar a bakinta aka halicci sunan dan ji yake kamar tafi kowa iya kiran 'Aliyuu' nan.
Ya ansa da "princess",saeta cigaba "am so sorry for all that happened,pls forgive me bazan sake ba" Aliyu yyi saurin d'agota ya d'aura mabiyin yatsar shi ta tsakiya kan libs d'ina yace "shshshshhh,don't take any blame on wat happened,becoz I was the one to be blamed not u,also u don't have to appolozise bcoz it's all my falt,had it been I stood for u,show u care and concern,this should haven't happened between us",Fadwa tace "na sani but still kayi haquri ae kai mijina neh kuma na kasa baka kulawar ka am so sorry for that",Aliyu yace "bbu komai ya wuce even though I didn't consider it to be blamed,al I want now is only ur forgivenss",Fadwa tace "na yafe maka duniya da lahira muma Allah ya yafe mana namu kurakuren",Aliyu yace "ameen godiya nke",Fadwa ta marairaice "toh ni baka ce ka yafe munba kuma na riga ka neman gafarar",Aliyu yace "ae na jima da yafe miki",dukansu sukayi dariya,sun d'an tab'a hira kafin Aliyu ya koma office zuciyar shi fall da farin ciki,megadi ma saeda yaji mamakin sa yau yadda yaga yake walwala ba kamar shigowar shi ta d'azu ba,gashi daga shiga d'aukan yafi 1hour a ciki..
漏Hama G Muh'd
[10:55am, 12/6/2016] Hamagee馃尫: 馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯 *KOMAI RINTSI PART 3*馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯
*Dedicated to Mom Sudaes*馃槝
庐E.H.W
*_Written by鉁嶐煆� Hamerh gee Muh'd馃尫_*
Page1鈨�4鈨�8鈨�
Bayan Fadwa ta gama gyaran gidn tayi abinci saeta tafi scul,sae 5:00pm ta dawo gida,horn tayi megadi ya bud'e mata gate d'in,tana shiga taga motar Aliyu shima ya dawo saetayi wani murmushi sannan tayi parking ta fito ta shiga cikin gidan..
Bayan fitar Aliyu kai tsaye ya wuce office hankalin shi duk yana gida,be tab'a experiencing irin wannan yanayin ba tunda yake,tunanin shi d'aya *Fadwa*,alla*2 yake ya dawo gida ya ganta ji yake kamar yau aka d'aura musu aure,yana ji kamar bbu wata rana a iya tsawon rayuwar shi da yyi farin ciki acikin kamar yau,da haka har ya taso.Bayan ya baro office d'in saeda ya tsaya ya sayi kaji guda 2,da wasu drinks though sunada drinks kala*2 a gida amma saeda ya siya sannan ya nufa gida,lokacin da ya dawo already 3 ta wuce dan haka be tsaya komai ba ya cire kaya yyi alwala sannan yazo yasa jallabiyar shi ya nufa masallaci,ya d'an jima yana adduoi bayan yyi nafila raka'a 2 kafin aka shiga sallahn la'asar,bayan an idar ya dawo gida yana jiran dawowan Fadwa,harya d'an fara gyangyad'i a inda yake zaune saeya ji dawowarta,tashi yyi ya bud'e mata qofa kafin ta iso..
Tana isowa taga Aliyu tsaye a bakin qofar yana jiran isowarta,murmushi ta sakar mishi yace "sannuda dawowa",tace "kaima sannun ka",tsak yazo ya d'auketa ya shigada ita har d'akinta kafinnan ya ajiye yace "fresh up and meet me at my room",tace "as u wish dear",Aliyu ya juya ya koma d'akinsa yana jiran Fadwa yau ko abincin rana beci ba,ita kuma wanka ta shiga tayi dan tayi sallahn ta a scul,bayan ta gama ta fito tazo tasa kaya marasa nauyi dan lokacin nazafi neh,tayi kyau abunta,tasa turare kamar yadda ta saba sannan ta fito ta nufi side d'insa,ta samu shima ya fito daga wankan kenan,bayan yasa kaya saeya ce ta zauna suci dan yunwa yake ji,sunaci suna d'an hirarsu har suka gama..
漏Hama G Muh'd
[11:32am, 12/6/2016] Hamagee馃尫: 馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯 *KOMAI RINTSI PART 3*馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯
鈽呪槄 *_SECOND TO LAST PAGE_*鈽呪槄
*Dedicated to Mom Sudaes*馃槝
庐E.H.W
*_Written by鉁嶐煆� Hamerh gee Muh'd馃尫_*
Page1鈨�4鈨�9鈨�
Fadwa ta tattara shirgin zuwa kitchen lokacin har an fara kiraye-kirayen sallahr magrib,dan haka ta koma d'akinta tayi alwala,shima Aliyun alwala yyi ya tafi masallaci,saeda ya jira har isha kafin ya dawo gida.
Bayan Fadwa ta idar itama bata bar kan sallayar ba saeda tayi isha'i sannan ta tashi,tana jin shigowar Aliyu ma dan haka tayi sauri ta shige toilet,Aliyu na shigowa kuwa ya duba kitchen bata nan ya duba d'akinta bata nan kuma yasan bata d'akinshi,kwae sae ya koma kitchen ya d'auko wajenda suke sa abincin megadi ya dawo palour gun dinng ya zuba mishi yadda zae isheshi sannan ya miqa mishi,bayan ya shigo saeya kulle qofar gidan ya kashe abubuwan da suke kashewa idan zasuyi bacci sannan ya dawo d'akin Fadwa,har yanxu bata fito a toilet d'inba,kai tsaye ya shiga dan bata kulle qofar ba,a zaune ya ganta,ita kuma tana ganinshi tayi sauri ta miqe tana dariya,yace "wato wayo kke mun ko",shima dariyar yake,haka ya jaata har d'akinsa bayan ya kashe wutan d'akin,bayan sun shigo ya kulle qofar d'akin,yace mata tayo alwala tazo,tace mai yanxu ta idar da sallah so tana da alwalarta,sallah raka'a biyu ya umarceta da suyi,bayan sun idar da sallahn sun gama adduoi saeya matso kusada ita ya d'aura hannun shi na dama a kanta ya soma karanto addua kamar haka:
" _Allahumma innii asaluka khairahaa wa khairamaa jabaltamaa alaihi wa auzhu bikamin sharrahaa washarramaa jabaltahaa alaihi_"
(Wannan addu'a anayinta neh idan mutum yyi sabon aure ko baiwa me hidima ko kuma raqumi,amma a yanxu bamu wannan zamanin,yawanci idan anyi aure neh ko kuma an sayi raqumi,y'an uwa a kiyaye wayannan adduoin sunada matuqar tasiri ga rayuwar aure,rashi adduoin nan shi yakan jefa futintunu a rayuwar aure so dan Allah mu gyara馃檹馃従)...
鈽呪槄鈽呪槄鈽呪槄鈽呪槄鈽呪槄鈽呪槄
Bayan ya idar ya d'aga hannun shi a kanta saeya kalleta itama kallon shin take,yace "toh muje mu kwanta kou",dayaga batada niyyar tashi saeya miqe ya d'auketa cak ya ajiye ta kan gadon,jallabiyar jikinsa ya cire shima ya kwanta,Fadwa duk ta kasa sakewa kasancewar bata tab'a kwanciya waje d'aya dashi ba,Aliyu ya fahimceta,dan haka ya kira sunanta "Fadwaa",ta ansa "naam",yace "ya kamata ki sake saboda nii mijinki neh kinji",kai kwae ta d'aga mishi,ya jawota jikin shi yana mata wasu maganganu a kunne harta d'an sake,(ganin abunda ke shirin wakana na tattara littafi da biro nah na fito a guje na rufo qofar ina musu saeda safe馃弮馃徎鈥嶁檧dan naga hararar da Aliyu keh mun馃槜)..
漏Hama G Muh'd
[11:16am, 12/8/2016] Hamagee馃尫: *_THE END鉁嶐煆絖*
馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁 *KOMAI RINTSI PART 3*馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯
*Dedicated to Mom Sudaes*馃槝
庐E.H.W
*_Written by鉁嶐煆� Hamerh gee Muh'd馃尫_*
Page1鈨�5鈨�0鈨�
Washegari da wuri Aliyu ya tafi asibiti kamar yadda ya saba,Fadwa kuwa batada scul yau dan haka ta samu isheshen tym ta gyara musu gidan kamar yadda ta saba,bayan ta gama gyaran tayi girki sannan tazo tayi wanka tayi sallah ta gode ma Allah tareda roqonshi ya basu zaman lfya me d'orewa ya qara musu qaunar junansu,bayan ta idar ta tashi ta d'anyi kwalliya daedae na misali sannan tasa kayanta,tayi kyau sosae,palour ta koma tana kallo,bada jimawa ba Aliyu ya dawo gida,wani tarban da be tab'a tunanin Fadwa zatae mishi ba tayi mai,bayan ta raka shi ya canza kaya suka dawo palour tare sukayi lunch cikeda soyayya,love d'insu ya zama abun sha'awa ga kowanne me kallon su...
Haka rayuwarsu ta kasance akoda yaushe,su kanje gaida Momyn Fadwa,wataran Momin Saeema,harta waje Ummahn Jaleel suna zuwa,yanxu Momy da Ummahn Jaleel sun zamo d'aya bbu wani munafinci ko tada hankali,Anty Rauda kuwa Fadwa bata yin good 2days basuyi waya ba.Rayuwarsu ta zamo abun alfahari ga alumma,tabbas *mahaqurci mawadaci*neh,kuma *KOMAI RINTSI*haquri yanada ranarshi,sannan kishin jahilci ba da neman raba jini d'aya ba abunyi bane..
鈽呪槄鈽呪槄鈽呪槄鈽呪槄鈽呪槄鈽�
*Two years ltr*..
Fadwa neh da Aliyu a palour,Aliyu na riqe da Baby Afreen,yarinyace y'ar kimanin shekara 1 tak a duniya,Aliyu da fadwa suna ji da babynsu sosae,gata bbu irin wanda basu nuna mata,yanxuma wasa sukeda ita tana ta dariya abunta,wat a cute Baby馃槝( I like children Allah馃槏)...Yanxu Fadwa da saeema suna final year d'insu anan Apti,Saeema ma da Babynta,ta riga Fadwa haihuwa,ita kuma sunan d'anta Sudaes,suna zolayar zunansu da Fadwa wae,Saeema tayi ma Sudaes kamun Afreen.That's how their lives continue..
Anan na kawo qarshen littafinnan me taken suna *KOMAI RINTSI*,ina roqon Allah yasa mun amfana koda kuwa da abu daya zuwa biyu neh a ciki馃檹馃従 Allah ya had'amu a littafaina na gaba wanda nan bada jimawa ba zaki jisu insha Allah masu suna *UNIVERSITY GIRLS*wanda littafi neh daya qunshi both English and hausa saboda yanayin abunda nake son fad'akarwa ya qunshi both,sae kuma *MAFARKIN HAMAGEE* wanda base on mafarkin da nayi neh kuma nake son ku ji ko zaku amfana.
Ina gaisuwa gareku
*MIEMIE BEE NOVELS
*K-SQUARE'S CHAMBER
*EXCELLENT WRITERS
*WISDOM OFFICIAL WRITERS
*FATY AFREEN NOVELS
*PRECIOUS WRITERS FORUM
*PHARTY B-B NOVELS
*ZARAH'S NOVELS
With lots more..
Godiya da nuna kulawarku a gareni,nima ina son forever and ever
*HAMAGEE NOVELS
*HOME OV HAUSA NOVELS, I love u all mhuaa馃拫馃槝
Ban san irin godiyar da zan muku ba馃槍 kun nunan tsantsar so da kulawa,nima kusani ina sonku all
*MY FACEBUK GROUP MEMBERS,TOGETHER WIT ALL MY FACEBUK FANS,luv u pple buhu buhu馃槏馃...
Ban manta ki ba my sweet,unforgetful dirling sister *Maman Sudaes*,u r really amazing and different馃槏u alwaiz stand for me
May Allah continue to protect u against ur bad wishers,and may u continue to excell,lurv u lot wit mah sweet lurving kids
Sudaes
Ilham and
Lil Saif, Allah ya raya mana su musha biki馃懐馃拑馃徑...
Ina sane dake Easha Bebe ta馃拫words can't express mah gratitude upon u馃..U r such a sweethrt,tnks alot for ur help dear,luv u daro-daro馃槂
Never I forget u pple with d luv,care and support u showed me mah Habeebtis馃槏
*Leemcy dear鉂�
*Preety queen鉂�
*Faty Afreen鉂�
*Khausar Lurv鉂�
*Billylosh鉂�
*Billy Tobacco鉂�
*Khairat up鉂�
*Faxyfashion鉂�
*Jamila AG鉂�
*Zeenaseer鉂�
*Laure (馃悞)鉂�
*Jidda鉂�
*Ummijafar鉂�
*Ummikhaleel鉂�
*Miemie bee鉂�
*Ummi Hambali鉂�
*Cute zarah鉂�
*Ummu Adnan鉂�
*Fausat鉂�
*Ayusha Ilyasu鉂�
*Aisha Gana鉂�
*Anty Deeqa鉂�
*Anty sad鉂�
*Anty Ruky鉂�
*Zubaida (my facebuk fan)鉂�
*Amal (also a facbuk fan)鉂�
*Zarah (a facebuk fan)鉂� wit more of u that I could'nt mention here鉂ne love for u all馃檶馃徑
Da wannan ni Hamagee nake ce muku bissalam