biyu ai”. Guntun murmushi nayi kawai batare dana motsa ɗinba. Mannani da yay da jikinsa ya sakamu sauke ajiyar zuciya a tare, ya busomin numfashi a saman wuyana zuwa kunne yana sake ƙanƙameni. “Kin fasa jin labarin kenan?”. Da sauri na girgiza kai, “Naga kamar ka gaji ne shiyyasa nai shiru, amma cike dake da zaƙuwa wlhy”. Murmushi ya saki mai sanyi yana matsa yatsun hannuna daya riƙe, “To aike miskilancinki bai bari asan kinason abu”. Sosai maganarsa taso bani dariya, amma saina dake nai murmushi kawai, wai ni yake kira miskila, ai shinema ya dace da wannan sunan bawai niba. Yanzunma bance komaiba ina dai saurarensa, saida ya gama jan ajinsa da shan ƙamshi sannan ya juyo dani muna fuskantar juna, idanunsa a kaina yace, “Idan kuma na fara kikace zakimin barci saina ƙarya ƙasusuwanki”. A zuciyata nace, ‘Ai tun daren jiya ka kakkarya ƙasusuwan nawa da sauyamin kamanni Alhaji’. Dariyarsa da naji ciki-ciki ya sakani fahimtar maganar zuci ce ta fito fili. Baya nai zan juya yay saurin riƙoni ya maidoni, dole na haƙura tunda dai nariga nayi katoɓarar.
Yaɗanja hancina kaɗan, “Wato tun daren jiya na sauya miki kamanni da karya ƙasusuwan ki? To a yafeni bazan sakeba Zinaraina”.
Bance masa komaiba dan naji kunya. Ya fara shafa bayana a hakali da gyara kwanciya, “Jawaad Abdul-Azez Yuseef ɗane da ga. zuri'ar Alhaji Yuseef Tafida. Alhaji Yusif talaka ne mai rufin asirin ALLAH, domin kuwa manomine kuma makiyayi, duk dai a birni yake rayuwarsa da iyalansa to dukkan wani sabgoginsa na ƙauyensu, acan yake nomansa da kiwo, hakan yasa hankalinsa rabuwa biyu, harma zamansa a ƙauyensu ya so ya rinjayi zaman birnin. Matan Alhaji Yusif uku ne cif, kuma kowacce a cikinsu ALLAH ya azurtata da haihuwa, matarsa ta farko hajiya Atika yaranta shida huɗu duk maza biyu mata, sai ta biyu badiyya yaranta huɗu itama, mata uku namiji ɗaya, sai amarya Rahina ke da uku maza biyu mace ɗaya...............
Tunda ya fara nake hawaye, sanda ya dire ƙarshe tuni kuka yaci ƙarfina har ina shashasha, ya jani jikinsa ya rungume yana lallashi, “To kuka ya isa haka mana uhmyim, haka rayuwa take, ganin wani a cikin ni'imar rayuwa bashine yake nufi ya samu komai ba, kowacce irin rayuwa zaki samu akwai rauni da jarawa a cikinta, da yawan dariyar da mutane keyi idanda zaki zauna dasu kiji suwayesu zaki fahimci iyakarta haƙori ne kawai, Haƙuri rahamane, duk wanda yay haƙuri baya yin asara, idan kayi haƙuri kaga babu riba a cikinsa to ɗan kaɗan kayi, sannan ka binciki kanka maybe kana zaluntar waninka ne, dan bakowacce jarabawa bace ga ɗan adam take zama daga ƙaddararsa, wasu mutanen sune da kansu suke shuka sharri sai kiga suna ta naɗar sakamakonsa da sharrika suma. Duk sanda na samu wani bakin zare na binciken mahaifiyata koxan dace da samunta sai kaina ya kulle Miemaa, kiga hankalina ma da tunanina sun gushe daga wajen, bansan miyasa hakanba?”.
“Al'amarinta kamar akwai sihiri a ciki boss”.
Saurin ɗagoni yay daga jikinsa, yace, “Miyasa kikace haka?”. Hawayena na share ina ɗan jan hanci kaɗan, “Duk musulmin ƙwarai ya yarda akwai ƙaddarar mutuwa, kuma wajibice ga kowa babu fashi, a ganina rasuwar Abba bazata gusarma Mamah hankali ba, koda zata shiga ruɗani bazai yuwu ace na gushewar hankaliba har akai gayin haukan da za'a bar gida ma gaba ɗaya. Matar dana zauna da ita a saudia bansan asalin sunanta ba, amma haka kawai tun ganina da ita na farko naji ƙaunarta mai tsanani ta shigeni har nakanyi mamaki, itace mahaifiyar Anum da Anuwar, aɗan zamana da ita na fahimci abubuwa da yawa daga gareta waɗanda suka sakani a ruɗani, bazan yanke hukunci akan gaibu ba, dan ALLAH shi kaɗaine masanin gaibu, saidai ga shawara”.
“Wace irin shawara?”. “Mizai hana muje Saudia a zuwan kamar na kai mata kai ku gaisa, dan dama ta roƙeni akan wataran na kai mata kai, haka kawai a ranta takejin son ganin mij.......”
“Ƙarasa mana to”.
Fuskata na ɓoye cikin ƙirjinsa ina murmushi. Murmushin shima na jiyo yanayi, ya tura hannunsa cikin sumata yana yamutsawa kamar maimin susu. Tsawon lokaci muka ɗauka a haka babu wanda ya sake magana, daɗin yan
Page 45
..................Ganin ya nata juya spoon a abincin ya kasa kai ko lauma ɗaya yasa tausayinsa kamani. nasan yana cikin yanayin ruɗani da shikaɗai yasan yanda yakeji, sai dai jarumtar ƴan mazan ta ɓoye komai daga fuskarsa harma da kuzarinsa. naɗan rumtse idanuna ina tariyo kalamun Umm-Anum. ‘Anya zan iya kuwa?’ na ayyana a cikin raina, daga can gefen zuciyata tace zaki iya ki daure, ruɗanin da yake ciki yana buƙatar kulawarki, hakan zai bashi nutsuwa. Kaina naɗan jinjina ina danne fargabata da matsananciyar kunyar da nakeyi na ɗaura hannuna akan nasa dake riƙe da cokalin.
Ɗago lumsassun idanunsa yay yana kallona batare da yace komaiba. daƙyar na iya danne zuciyata nabar idanuna cikin nashi daya tsareni dasu, na langaɓe kaina cikin tsananin nuna kulawa nace, “Dan ALLAH ka kwantar da hankalinka kaci abincin karya huce, kagafa harka rame, kanaso Ummah tace bana kula mata da kai duk farfesun da take sawa kullum Nabeelah tana kawowa”.
Lallausan murmushi na musamman ya saki har dimples ɗinsa guda biyu na loɓawa, haƙwaransa suka fito kaɗan, yaɗan lumshe idanu ya buɗe a kaina yana faɗin, “Yarinyarnan na kula wayo kawai kikeson min dan karna fita”. Ya ƙare maganar a hankali yana wani kashemin ido ɗaya da ɗage gira sama.
Hannu na saka na rufe fuskata ina murmushi, ba ƙaramin kasheni murmushinsa yayiba, dan nikam zan iya rantsewa ban taɓa ganin kalarsa daga garesaba sai yau, fuskata a rufe cikin tafukan hannuna nace, “Ni ƴar ƙaramarnan da nice zan maka wayo?”.
“Ba gashi ba kinamin”. Yay maganar da kamo hannuna ya miƙar dani tare da zagayo dani inda yake ya ɗaurani saman cinyarsa, ya zagayo hanayensa duka biyu kan cikina, kansa kuma na bisa kafaɗata. Jinai kamar na nutse dan kunya amma na daure kaina a ƙasa nace, “karfa kasa wani yaji ya ɗauka da gaske ne, ina ni ina yima boss wayo, bayan kai ɗin wayon ne da kansa”.
Kansa ya ɗaura saman wuyana yana huramin iskar numfashinsa, hakanne ya saka tsigar jikina tashi lokaci guda, naɗan ƙanƙame jikina ina haɗiye yawu daƙyar. Dai-dai saitin kunnena ya ɗora bakinsa yana magana a hankali kamar mai tsoron a jisa, “Ni ina naga wani wayo tunda gashi kinamin kuwa, a wajene Jay yake boss, amma a gaban Zinaran bawane, kece boss ɗin. buɗe idonki kiga wani abu”. Sosai maganarsa ta nema fasan kai, ashe mutumnan haka yake yana magana raɗam abinsa, amma yayta mana mazurai a office. Janye hanayen nawa nayi daga kan fuska a hankali harna kaisu ƙasa sannan na buɗe idanuna dake rufe. Ina buɗewa yana ɗaura laɓɓansa akan nawa. Na zaro idanu sosai dan ba haka na zataba. Shima idanun nasa dake cikin nawa yaɗan zaro yana cigaba da abinda yakeyi.
Nasan banida ƙarfin dazan ƙwace, kuma ma nayi alƙawarin insha ALLAH bazan taɓa zama mai bijirewa a garesaba a komai da zaizo min dashi inhar bai taka dokar ALLAH ba. Ballantana a yanzu da nake hango tsagwaron damuwa akan fuskarsa, dannewa kawai yake dankar na fahimta. Mun kwashi tsahon mintuna biyar ahaka kafin ya barni, ya rungumeni muna sauke ajiyar zuciya a tare, ya sumbaci kuncina da wuyana, acan ƙasan maƙoshi yace, “Idan nace tadaban ina nufin keɗin tadabance har ƙasan ruhina Miemaa, a kwana biyu kacal da mukai dake na fahimci ƙyawawan abubuwa masu yawa daga gareki, inason mace mai juriya da biyayya akan abu koda bai mata ba, inason mace mai tsafta da ƙamshi, inason mace mai kawaici, kunyarki tana a farkon abinda ke ƙara miki daraja da girma, inason mace mai aji, mai addini, mai kamun kai, na tsani ballagazar mace mai rawar kai, da ace ƴammata da yawa zasu zama irinki da sun zama masu darajar daraja bisa daraja a wajen maza......” ya ɗagoni daga ƙirjinsa, muna haɗa idanun nai azamar maida kaina a ƙirjin nasa.
“Ka daina huramin kai da yawa irin haka, yanda kake lissafin nan bankai haka ba, ni macece mai rauni, maison kulawa, waɗanan makaman suna saurin sakani bama mutum yarda, ada kallon bahagon mutum nima nake maka, wanda ba damu da damuwar kowaba sai abinda ya shafesa, amma a tsakanin jiya da yau na kula kai adaline mai sauƙi ga iyalanka, ka yafemin akan gurɓataccen tunanina, idan nace k
ai na dabanne ko a cikin mazan ina nufin nadaban a cikin miliyoyi, ba dan kafi sauran maza bane dan dukiya, ba dan kafi sauran maza bane dan ƙyau, ba dan kafi sauran maza bane dan darajar da ALLAH ya baka, kafi sauran mazan dan kai ɗin mai ƙyaƙyƙyawar ZUCIYA ne”. Na ƙare maganar da ɗora yatsana akan saitin zuciyarsa ina hawaye”.
Bilkisu ko duniya zatace ƙarya nake saina faɗa, keɗin tadabance ko acikin nadaban ɗin kinzo da banbanci mai tazarar nisa.
“Karfa kasa mata sumin bugun kayan wanki”. Ɗagoni ya sakeyi yana murmushi, “Su sun isa ko kallon banza ga matar Jay ma”. Dariya muka ƙyalƙyale da ita a tare saboda yanda yay da fuska kicin-kicin kamar mai shirin shiga filin daga. Na yunƙura zan sauka daga jikinsa ya sake riƙeni. Naɗan marairaice masa batare da nabari mun haɗa idanu ba, “Yanzufa za'a kira sallar isha'i, ga abincin zai huce kuma”. Siririyar ajiyar zuciya ya sauke yana sakina, “Idan bakiso na fita akwai sharaɗi”. Kallonsa nai alamar ina sauratensa. tattausan hannunsa ya ɗaura akan haɓata ya matso da fuskata gab da tashi. “Idan har bakiso na fita sai dai ki ciyar dani da hannun nan naki, inba hakaba bazanci abincin nanba, kuma saina fita, kuma yunwa nakeji, kuma nagaji barci nakeji”. Ƙoƙarin juyar da fuskata nayi dan kunya da dariyar dake tahomin dan a narke yay maganar, amma ya hanani damar hakan, saima wani sake narke fuska da yayi irin na (Aji tausayina ɗinnan😔).
Da sauri na jinjina masa kai danya barni na tashi nidai, zuciyata sai wani zallo take cikin ƙirjina tamkar zata fito, ga kunya kamar ƙasa ta buɗe na shige ciki, dan kusani ALLAH ba ƙaramar dauriya nakeyiba yasin.
Ɗauke hannunsa yay ya gyara zamansa, hakan ya bani damar tashi tsaye, kujerar kusa da shi ya zaunar dani da juya kujerar yanda zanyi facing ɗinsa sosai. Ya zanyi, nina taroma kaina match ɗinan ai. Abincin na fara basa idanuna a ƙasa ban yarda na kallesa ba, amma shi inajin yanda idanunsa kemin yawo a zahiri da baɗini na, koda naɗan saci kallonsa sai muka haɗa idanu. Saurin maidasu nai ƙasa, daga haka ban sake ɗagowarba harna tabbatar ya ƙoshi. Ina murnar an gama zan tashi ya riƙe hannuna, kallonsa nai ya ɗagan gira, “Malama saura ke dan baza'amin ɗuraba ni kaɗai”. Dukda da gaske yunwar nakeji saina ɗan ɓata fuska nace, “Nifa na ƙoshi”. “Idan na yarda kenan”. Yay maganar yana ɗebo abincin ya kai bakina. Dole nima na haƙura na karɓa, yana bani yana addabata da kallo, hakan yasa duk naji na takura matuƙa. Sai da ya tabbatar na ƙoshi sannan ya barni.
Naɗan kallesa ina tattare kayan ganin bai tashiba, kuma salla akeyi. Nace “Sallafa akeyi”. “Kin karyamin alwalata ai?”. Yanda yay maganarne ya sakani barin wajen da sauri na nufi kitchen. Bayan na kammala ɗauraye kayan na fito, ban iskesaba ya tashi, ɗakina na nufa nima domin gabatar da sallar isha'i.
Sai da nai wanka na saka doguwar riga mara nauyi sannan na fito falon dan banji motsinsa ba, zaune na iskesa cikin kujera yana waya, ga takardu ya baza saman centre table. ‘Agogo sarkin aiki kenan’ na faɗa a zuciyata ina ƙarasawa. Kitchen na wuce domin ɗakko masa ko ruwa ne. Inaji a jikina kallona yake amma ban juyaba. Harna dawo ɗauke da ruwa da lemo bai gama wayarba, naja ƙaramin copy table na ajiye tiren sannan na ɗago na kallesa, ganin ni yake kallo na ɗauke kaina, “Wanne zan zuba?”. Maimakon ya bani amsa sai ya amshi kofin ya ajiye ya kamo hannuna, zaunar dani yayi a gefensa tare da kwantar da kaina a kafaɗarsa ya cigaba da wayarsa.
Bai jimaba sukai sallama ya ajiye yana ɗan guntun tsaki, ɗago kaina nayi na kallesa, kafinma na tambayesa yacemin, “Inaga yarinyarnan zan taka mata birki, iskancinta sake gawurta yakeyi, aikin nan kusan sati ɗaya kenan na batashi amma sai yawo takemin da hankali”. Tsaf na fahimci da Rose yake, dan naji muryarta ta cikin wayar, amma sai nai kamar ban fahimtaba nace, “Wacece?”. Tsakin ya kuma ja da ɗaukar wata takarda yana dubawa, harma na fidda rai da samun amsa sannan yace, “Rose” a taƙaice. Ƙin cewa komai nayi dan naga kamar ya hau sama. Sai da ya gama shan ƙamshinsa niko nai kamarma na manta da sh
da yakemin a cikin kai ya sakani fara lumshe idanun barci, cikin mintuna ƙalilan kuwa barcin yay gaba dani.
Tunda Bilkisu tai barci sai idanun Jawaad suka sake bushewa, kalamanta kawai yakema fashin baƙi dalla-dalla, daga ƙarshema zameta yay daga jikinsa a hankali ya kwantar, bayi ya shiga ya ɗauro alwala yazo yayta nafilfili, ya jima yana miƙama ALLAH kukansa cikin ƙanƙan da kai da ƙasƙantarwa, harda hawayensa shaɓe-shaɓe, fatansa ALLAH ya buɗa masa haske akan al'amarin nan ya fahimci sirrin dake ɓoye, duhun dake lulluɓe da shi da matarsa ALLAH ya yaye musu shi ya zama haske. Bai kwantaba sai kusan ƙarfe uku. Yana kwanciya barcin yay gaba dashi dan idanunsa dama har zafi suke saboda barcin.
Kiran sallar asuba da aka ƙwalane ya sakashi farkawa a ɗan firgice hannunsa dafe da kansa, sai da ya jero addu'ar tashi barci kafin ya iya furta Aunty Mah-mah, yau kam ya sake mafarkinsa daya saba na ƙaddarar jini a cikin jini, sai dai yau ya farka bai manta fuskar matar dake masa kalaminba, Gwaggonsa ce Rahma wadda suke kira da Aunty Mah-mah. Juyawa yay ya kalli Bilkisu data cure waje guda cikin bargo ta rufe har rabin fuskarta. Yaɗan lumshe idanu ya buɗe yana sauke ajiyar zuciya, tsahon lokaci yana kallon Bilkisun da nazarin abubuwa masu yawa har aka fara kiraye-kirayen sallar shiga masallaci. Nannauyan numfashi ya sauke sannan ya sauka a kan gadon da ƙyar dan jikinsa ko ina ciwo yake masa alamar barcin bai ishasa ba.
Alwala yayo, ya fito a gaggauce ya tada Bilkisu sannan ya fice masallaci.
Sukuku na tashi da ƙyar nai alwala, raina cike da wasuwasi akan mafarkin da nayi maiban mamaki da al'ajabi, gashi komai dalla-dalla a zuciyata ban manceba kamar azahiri komai ya farumin ba'a mafarkiba. Bayan na idan da sallar ina cikin yin azkar ya dawo, baimin maganaba ya cire jallabiyar jikinsa kawai ya haye gadon ya kwanta daga shi sai boxer. Kallo kawai na iya binsa dashi haryaja bargo ya lulluɓa sannan ya miƙomin hannu alamar nazo. Janye idanuna nai daga garesa ina faɗin, “Ban kammala azkar ba fa”. Baice komaiba ya maida hannunsa a bargon ya lumshe idanu.
Lokacin dana kammala azkar haryay barci, dan saukar numfashinsa kawai nake jiyowa a hankali. Lallaɓawa nai na fice daga ɗakin danni idanun nawama sun bushe banajin barcin kuma. Ɗakinsa na nufa na fara gyarowa dukda babu wani datti tunda bawai zama akeba, kuma yau ba'a nan muka kwanaba, daga nan na dawo falonsa sai babban falo kuma har zuwa nawa falon tunda dama ƙananane su, turaren wuta da air fresheners na baza ko ina, nan take gidan ya ɗau ƙamshi. Jina nai tiɓis da gajiya, nifa dama can na tsani mopping yasin, babu abinda nake kallo mai wahala a aikin gida irin mopping da wanke-wanke, na tsani wanke-wanke fiye da zato, to amma yaya na iya haka zankeyi dole, idan wahalarce dama mun riga mun saba da ita ai tun ƙuruciya, to yanzukam data kasance dole kuma mai muhimmanci a gareni ai dole na zage nayi, sai dai harna fara tausayin kaina idan na koma aiki, lallai zanci ƙaniyata da ayyuka.
Agogo na kalla ƙarfe tara harda wasu mintuna, cikin jan jiki na nufi kitchen, ina tsaye da tunanin miya dace nayi mai sauƙi da bazan sake jigata kainaba naji ana knocking ƙofar falo. Fita nai kasancewar jikina da hijjab, na buɗe ƙofar. Drivern gidan Ummah ne ɗauke da kwando. Ya gaisheni sannan ya miƙamin basket ɗin, amsa nai da masa godiya, nakumace ya miƙa mana godiyarmu ga Ummah kafin muyi kiranta.
Sauƙi dana samu bazanyi girkiba kenan, sai kawai na shirya komai a D/table ɗin. Nagama zubama maigadi abinci a kularsa ya fito. Ɗagowa nai na kalli sashen da nakejin motsi, yana daga tsaye jikin glass ɗin daya raba falona da babban falon hannayensa duka a harɗe saman ƙirji. “Barka da tashi”. Na faɗa kaina a ƙasa ina ɗan murmushi.
Baice dani komaiba ya tako zuwa Dining ɗin yana wani yamutse fuska na alamun bai jima a tashi barci ba. Hannuna da nake rufe kulan ya kamo cikin nashi, cikin yanayin muryan wanda ya tsashi a barci yace, “Haka ake gaida miji dama hajjaju?”. Ɗagowa nai naɗan kallesa na ɗauke idanuna, “Nifa idan aka cigaba da takalata faɗa zan
i a falon sannan ya juyo ya fara sakani wani aikin muka cigaba dayi tare, sai kusan goma da rabi sannan muka kammala, munayi yanamin bayani akan abinda suka tattauna yau da yaje office, da yanda suka tsara yanda abubuwan zasu kasance, tsarin yayimin, nakuma ƙara da shawarata dana fuskanci yaji daɗinta sosai.
____________________________
Su Abdul-raheem kuwa suna isa masarauta clinic aka wuce da Anuwar, likitan da yay aiki da rana ma har yana shirin tashine na dare kuma zaizo ƙarfe tara, dole ya dakata, taimakon gaggawa ya shiga bashi, cikin amincin ALLAH ba'a wani ɗauki lokaci ba numfashinsa ya dawo dai-dai. Hannun Abdur-raham dake kusa dashi ya riƙe yana hawaye, “Abdull kamarmu ɗaya fa da shi, komaifa iri ɗayane, Wlhy ina cikin ruɗani Abdull, ko ku baƙwa irin wannan mugun kamar dasu Abdul-Raheem ai, inason ku maidani wajensa naji wanene shi? Idan kuma kun sani ku faɗamin Please, karkuce na rasa hankalina wlhy a rikice nake, jinake zuciyata na wani irin tsitstsinkewar da bantaɓa jin tayi ba.....”
Abdur-raham bai samu damar bama Anuwar amsaba aka sanar da zuwan gimbiya. Kanta tsaye kan Anuwar tayi, tashi Abdur-raham yayi ya bata wajen zama, ta zauna tanama Anuwar sannu. Hawaye na shatata a kumatunsa yace, “Ummu yau naga mai kama dani kama mai ban al'ajabi da saka zukata ruɗani”. Murmushi Ummu tai masa cikin sigar lallashi tace, “Nasan da hakan Anuwar....” “Kin sani? Kenan kema kinsan shi? Kuma kinsan muna kama Ummu?”. Kanta ta jinjina masa tana sake faɗaɗa murmushinta, “Anuwar muma kamanninku ba ƙaramin sakamu a ruɗani sukai ba alokacin da muka gansa, hakanne ya saka muka tura Bilkisu wajenku, muka kuma ƙirƙiri hanyar da zakuzo ƙasarnan danmu sake tabbatarwa...”. “Ummu kin sake sakani a duhu wlhy”. “Zaka fita insha ALLAH Anuwar, amma lokacin hakan baiyi ba. abinda dai nakeso shine ka kwantarmin da hankalinka kaji, komai zai warware fiyema da abinda muke hasashe”. “To Ummu, amma inason na sake ganinsa dan ALLAH”. “Eh to banƙi ta takaban ba, amma ina ganin mubarshi basai ka koma ba, hakan zai saka ya sake zaƙuwa da ganinka kaima, dan inason ku wuce saudia goben idan ALLAH ya kaimu, lokacin da zai biyo sawunku nan ku kuma kun wuce, hakan zaisa yaso zuwa saudia ɗin, mukuma dama wannan damar muke buƙata ai”. Kansa kawai ya iya ɗaga mata danshi ta sake dulmiyasa a ruɗani, amma sai yay shiru bai sake tambayar komaiba. A take ma Doctor ya shigo ya bashi sallama suka tafi sashensu Abdul-Raheem.
A wannan dare inhar Anuwar yayi barci to ragaggene, gashi Ummu ta gargaɗesa karya kira Umm-Anum balle sukai ga tunanin sanar mata wani abun, kuma koda komawa sukai karsu sanar mata komai har sai Jay yaje saudia da kansa.
Washe gari jirgin safe suka bi shi da Anum cike da tsarabar biki daga Ummu, daka kallesu kasan basa son tafiyar dan ransu duk a cinkushe yake musamman ma Anuwar, har jiyake kamar ya zauna yayta kuka, sam bayason tafiya bai sake ganin Jawaad ba, baiji wani abu daga garesaba kuma.
_____________________________
Ɓangaren Shahudah kam an sallamota itama sun dawo gida, taji sauƙi amma dukta rame ta ƙara wani irin haske maiban tsoro kamar wadda bata da jini a jiki, gashi yanzu ko yawan magana batayi sai dai ka ganta tayi zugum kamar wadda abin duniya ya dama. Koda yake ya dametan, dan Shahudah tanama Jay so mai tsananin gaske, sai dai tanaji a ranta bazata taɓa iya shearing ɗinsa da kowacce maceba ballema Bilkisu ƙasƙantacciya da tazo ƙarƙashin inuwarsu cin arziƙi. Har yanzu zatonsu na akan bilkisu asiri taima Jay ya aureta wai.
Shi Dad harya bar ƙasar ma yau kwana biyu kenan, dan wani business ne na gaggawa yace ya taso masa, ko sallama saita waya yayma Momy ma, da yake ta rigada ta saba da irin wannan halin nasan sam sai bata damuba bakuma ta kawo komai a ranta ba.
_________________________
Koda na kammala shirin barcina ban nema inda ya keba nai kwanciyata a ɗakina, har barci ya fara figata naji shigowarsa ɗakin, banko motsaba balle yay tunanin idanuna biyuma, gadon ya hawo yana faɗin “Wannan amaryar dai matsoraciya ce, nasan idanunki
kaninmu muyi haƙuri da juna mu daure wajen yima juna uzuri da ƙyaƙyƙyawan zato, bance dake niɗin na daban bane, bankuma miki alƙawarin zama na daban ba, sai dai insha ALLAH zan kasance miki mai sauƙi da rangwame kamar yanda nake fata daga gareki, randa kuma zan ƙara aure ki kwantarmin da hankalinki kamar kinyi baƙo ya mutu”. Harara na zuba masa batare da nayi zatoba ina mai zumɓura baki da juya masa baya. Ya ƙyalƙyale da dariya yana rungumoni jikinsa, “Oh gulmammiyar matata ashe tana sona take basarwa, garama ki shirya yarinya mata huɗu zanyi gangariya”. Ƙin tanka masa nayi, dan jinai zuciyata ta kumbura, har nai mamaki dan bansan dalilin hakanba.
Bai fasa tsokanata ba har Sadiq ya kawo cefanen muka shiga yin aikin girkin ni da shi, yanda yake komai a nutse ya sani fahimtar ya iya girki shima, ban tambayesa ba dai har muka kammala komai, sai dai lokaci-lokaci yakan fita Dining ya amsa wayarsa daya bari a can sai ya dawo................✍
😵kuttt addu'arkufa ta cini da yawa words 4412😫🤒
Barka da juma'a😍😍😘😘.
ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.
SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.
HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO
MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.
MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.
BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....
abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.
Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899
sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.
Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300
Sai kunzo😍😍😍😘.
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
maida murtani”. Yay maganar da ɗora bakinsa saman goshina ya sumbata sannan ya ɗago haɓata ya haɗe ba....🙄😏
Da ƙyar na samu ya barni mukai zaman yin breakfast, a hakanma ba tsira naiba dan kallonsa kawai ya isheni. Muna tsaka dacin abincin kira ya shigo wayarsa, ɗauka yayi, yanda naji yana amsawa da girmamawa ya sakani fahimtar da Umman su Nabeelah yake. Har muka kammala cin abincin basu kammalaba, na fahimci maganar tasu duk akan Anuwar ne, Nabeelah takai bayani kenan, nidai kwashe kayan nai na nufi kitchen domin wankewa, shi kuma ya ɗauka abincin maigadi ya fita.
Na kammala wanke-wanken na nufi ɗakina zanyi wanka, ina gama cire kaya na ɗaura towel sai gashi ya shigo tsulum babu zato. Kunya naji kamar in nutse, shiko ya wani fuske abinsa saima jallabiyar sa shima ya cire, sama kawai naji anyi dani, hakan ya sakani tsorata nai saurin zagaye hannayena a wuyansa. Ƙaramar dariya yayi da ranƙwafowa ya sumbaci gashina yana faɗin, “Ki rage tsoro yarinyarnan wlhy”.
Ban iya bashi amsaba muka shige bathroom. tunda na fahimci yana nufin muyi wanka tare na shiga zare idanu, ‘kutt inani ina wanka da sangamemen ƙaton nan’. Cikin marairaicewa na shiga roƙonsa akan ya barni na fita idan ya gama sai nayi nima.
Towel ɗin jikina ya sunce yana faɗin, “Barma wahal da kanki Zinaran”. Saurin juya masa baya nai ina rumtse idanu da ƙarfi, sai kawai jinsa nai ya sakani jikinsa da saukar ruwa a kanmu lokaci guda. Sassanyar ajiyar zuciya na saki.
Duk wani noƙe-noƙena akan wankan nan dole na sake mukai wankan nan tare yanda ya keso, dan hanyoyin da ya ringabi dani bazasu yuwu na iya cigaba da bijirewanba. duk yanda zan fassara muku dodon nan nawa da wahala ku yarda dani, dan haka bara kawai nai zipping🤐 bakina kamar zaifi sauƙi.
Man ma tare muka shafa, yaymin drying kaina da yake wuta ta kwana har yanzu akwai, tsaf ya gyaramin shi tamkar wani mai'aikacin gidan saloon. Kayan sawama shine ya zaɓamin zani da riga na wani lass mara nauyi, sai dai ya haɗu harma ya gaji da haɗuwar, zaunar dani yay wai zai ɗauran ɗan kwali, nikam yau naga idi an maidani kamar wata doll. Tunda aka fara ɗaura ɗan kwalin nake gumtse dariya, sai kace irin yadikkon nan na cikin ruga, kasa jurewa nai na ƙyalƙyale da dariya, ya dunguremin kai shima yanayi da faɗin, “Ai dai nayi ƙoƙari”.
Nace, “To dama waye zaice bakayiba ya kwana a call”. “Ashe kin gane karatun ta wajena, muje a ramawa kura aniyarta nima a shiryani yanda Ummah zatazo ta tabbatar ɗanta ya gama dacewa a duniya sai fatan lahira”.
Murmushi nayi ina rufe fuska. sai kuma na buɗe da tambayarsa zuwa zasuyi?. Kansa ya ɗagamin, “Nabeelah takai gulma ta kasa haƙuri sai tazo taji bayani, dama kuma akwai wani abun a ƙasa, zasuzo itada Ummah ƙarama”. Daɗi naji ya sake kamani dan ƙaunarsu nake bayin ALLAHn nan, yaja hannuna muka tafi ɗakinsa, tsareni yay na zaɓo masa kayan shima, ya kuma rantse nice zan shiryashi babu ɗaga ƙafa. Jama'a yau nasha kunya fiye da hasashe, shi dai wannan boss ɗin ku gansa kawai ku barsa inda yake, sanin wanene shi saini matarsa😉 (karfa aimin snatching ƴammatan Bilyn Abdull😝. Lol😂).
Tsaf na shirya abuna ina ƙuƙƙumshe fuska na feshesa da kalolin turarensa masu daɗin ƙamshi, kiransa da akai a wayane ya bani damar gudowa nawa ɗakin na gyara nai zaman ɗaura ɗan kwali, sai da na tabbatar nayi dai-dai buƙatar mai kallo sannan na ƙara turare na fito ina tunanin abinda zan girkama baƙina da rana.
Na shiga kitchen ɗin ina nazari da duba abinda muke dashi ya shigo. “Ki rubuta abinda zaki buƙata ga Sadiq nan yazo zaiyo cefane”. Kaina na jinjina masa.
Ina gama rubuta abinda zan buƙata na dawo kitchen ɗin na fara ɗaura abinda ke a hannu, a mamakina sai gani nai shima ya shigo, riga ya ɗauka ya miƙamin wai na ɗaura masa. Na ɗan waro idanu waje da faɗin, “Namiji da girki?”. Ido ɗaya ya kannemin da faɗin, “Bakiso nai koyi da ƙyawawan halayen MANZON ALLAH (S.A.W)? Miemaa insha ALLAH zaki sami mijinki a cikin gidanki fiye da yanda kike zato, zan riritaki na shagwaɓaki na gatantaki, idan saɓani ya shigo a tsa