Tabbas wannan zance haka yake , Allah ya bawa Dikko lafiya ya ƙara soyayya a tsakaninku ya kuma ƙaro irinsu Papi hada Junior Dikko muzo musha suna , murmushi Sultana tayi amma batayi magana ba , saukowa nayi daga saman gadon ina ɗan gyarawa cewa ni zan wuce zan tara ƙarshen labarin a takardar labarin rayuwarki , godiya tayi min sosai mukayi sallama cikin mutunci da mutuntawa , itama Inna munyi sallama cikin mutuntawa na barsu lafiya nima zan tara muga ƙarshen labarin tare daku masoyan Sultana & Dikko ,
Bayan Jamila ta tafi wanka na farayi tare da ɗoro alwallah dan magrib ya gabato , ina fitowa kayana na saka na shafa mai sama² da powder naci gaba da tattara kayan da Inna keyin parking zatayi tafiya zuwa Abuja ita da mijinta.
Inna ce ta shigo ɗakin tana cewa wai ga wani Abbakar can yana miki sallama a waje , ba tare dana kalleta ba nace wane Abbakar kuma ? Abokin ɗan iskan yaron nan mana , murmushin jin daɗi nayi a zuciyata a fili kuma na ɗan basar cewa Hajiya Inna kenan waye ɗan iskan yaro kuma ? Dikko , Inna wai me yasa kikejin zafin Dikko da yawa ? Bana san yaron ne kwata² gaba ɗaya ya siremin kamar tusar safe....
Saura kaɗan na fita na zageshi dan dai kar ace na haukace , ai bana nan ma dan ni bazanje ba , aiko sai kinje kodan ya ganki baki lalace ba ci gaba aka samu ba ci baya ba yaje ya bawa Dikko labari , nidai Inna gaskiya bazan wani je ba , aiko sai kinje kuma kin barbaɗa masa rashin mutunci yadda Dikko da uwarshi suka tozartaki kema sai kin tozartasu kuma sai ya baki sakinki tunda basu da mutunci....
Inna kenan na faɗa a raina , a zahiri kuma na bita da kallo , kin wani tasani kina kallo kamar niɗin baƙuwarki ce ki wuce kije ki dawo , banyi magana ba na ɗauki hijabi na fice , a harabar gidan naga wata irin lutsetsiyar mota ɓaka sai sheƙin sabinta take tunda na taho nake ganin kaina a jikinta bana iya ganin na cikin motar shima a gilashin kaina nake gani saboda yana da duhu , jikina ya bani ba Dikko bane a ciki amma ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba duk inda wannan motar ta fito tashi ce kuma ban taɓa ganinta a cikin motocinshi ba ,
A jikin motar na tsaya na ciki ya sauke gilashin motar tare da cewa sannu , yawwa na faɗa rai a ɗan haɗe , ya gida ? Lfy , kin gane ni ? Ey a Bakori daka kawo katifa a motar ka ko ? Murmushi yayi tare da cewa ashe baki da mantuwa , ya akayi ne ? Gefenshi ya kalla ya ɗauko wata "yar leda bansan ko miye a ciki ba ya miƙomin ba tare dana ansa ba nace meye a ciki ne ? Ki ansa koma miye zaki gani , hannuna ɗaya a ƙugu ɗayan nake nunashi amma bada ɗan yasa ba kawai ka faɗa danni bazan karɓa ba , ki ansa An mata , ban sake magana ba na juya na wuce dan kar in ɓata lokaci Inna ta biyoni ta yabamin , sallah na samu Inna tanayi nima abin sallah na shimfiɗa na kabbara sallah.
Kai Ashiru ɗauki yaron nan ka maidashi gida fita zanyi , riƙe Dikko yaron yayi yana kuka cikin gwaranci yace bajan je ba tare da maƙale ƙafaɗarshi , Ashiru yace mai gida bazai zo ba , kai da Allah ɗaukarshi basai zaije ba ku tafi zanzo nima , ƙara riƙe Dikko Papi yayi yana kuka , kafin Dikko ya sake magana Abbakar ya shigo inda Dikko yake tsaye yayi parking tare da sauke glass yace DK bata ansa ba , ko tace maka wani abu ne ? Yadda sukayi da Sultana ya faɗa masa , babu damuwa An mata tana da matsala , ni bansa abinda ya faru ba tunda bana nan bazan iya ƙarda komai ba , kawai anje an kwaɓa abu duk sun jagwalgwale min komai , taya kai tsaye zan tunkari inda take bayan Momy taje ta ɗauko yaro ta taho dashi dole kowa zaiji babu daɗi , Momy Dady duk su ba'ayi musu dai² ba , itama Mamar kanta yayi zafi , kallon Ashiru yayi tare da cewa kiramin Umar yazo yanzu²n nan ya ƙarasa maganar yana kallon Papi daya duƙunƙune shi , isowarshi kenan su Nabeela suka zo dashi yi ma Dikko sannu da hanya da kuma dubashi da jiki , shi kuma sai wani bin Dikko yakeyi kamar yasanshi dan ko su Nabeela gajiya sukayi suka tafi suka barshi yaƙi binsu , iyakarshi gidanshi baije gidansu ba ,
Kai ka sanni ne ? Ya tambayi Papi fuska a haɗe , yadda yayi abun yasa Papi yayi dariya danshi a tunaninshi Dikko wasa yakeyi mishi , kai kasanni ne nace ? Ƙara ƙyalƙyalewa da dariya yayi yana kallon Dikko , tsoki yayi tare da buɗe mota ya sakashi a baya ya rufe yace ma Ashiru idan Umar yazo kace masa nace yaje wurin An mata haka kawai zakace masa , Ashiru yace to , zagayawa yayi ya shiga gaba suka fita da Abbakar ,
A palon Momy ya samu Jiddah tasha wanka na ɗaukar hankali da firgita tunani , Dikko ne a gaba Abbakar yana ɗauke da Papi da yayi bacci , suna shiga Momy ta ansheshi tana cewa Nabeela taje ta kwantar dashi , ansar shi tayi ta shiga ciki dashi su kuma suka samu wuri suka zauna , Yaya DK sannu da zuwa ya ƙarfin jiki ? Ko inda take bai kalla ba bare ta sa ran zaice yawwa , gaishe da Abbakar tayi shidai ya ansa saida ta rufe bakinta sannan Dikko ya gaishe da Momy , ta ansa cikin jin daɗi tana nuna yanayin farin ciki ɗanta ya dawo lafiya kana kallonta dai kasan tanajin daɗi ne a daren nan , labari marar ma'ana taita bashi akan Papi shidai shiru yayi baiyi magana ba kuma ko murmushi baiyi ba hankalinshi da kaf tunaninshi yana can wurin tunanin yadda zai taro matsalar da suka haifa da kansu , amma An mata ta bashi mamaki yayi tunanin ko bashi ne da ita suka haifi Papi ba zata iya riƙe mishi ɗanshi ko bayan baya nunfashi amma shine ta bada yaro da baiji bai gani ba da yana da ƙarar kwana daya mutu shikenan ya sake tashi a zero.....
Momy ce ta dawo dashi daga tunanin da yakeyi taci gaba da fanfo da ƙaga abinda bai faru ba kuma ba'ayi ba akan Sultana tayi mata rashin kunya ita da uwarta , yadda ta faɗawa Dady haka ta faɗawa Dikko ta kuma ƙara da cewa tuntuni suke aiken rashin mutunci akan ka sakar mata "yar ta , hankalin Dikko akan waya yace wa suka aiko ? Wata maƙociyarsu ce can Barhim , sai kuma kai tsaye aka barta ta shigo saboda an aikota daga gidansu An mata ? Ya ƙarasa maganar yana tsare Momy da ido , tou ƙarya nake Dikko , ah yi haƙuri ba nufi na kenan ba , daga haka bai sake magana ba sai ita taci gaba da farfaɗo maganganu marasa daɗi da ɓatanci , a ranshi kuma yace da na saki yarinyar nan gara na dawo da ita muci gaba da cakuɗawa daga inda aka tsaya har tayi hankali danshi kullum kallon Yarinya yake ma Sultana bai san ta ƙara girma ba , saida Momy ta tsiyaye mai isar ta tana faɗa tana kunnuwa ta tata rashin mutunci iyakar iyawarta , har tayi ta gama Dikko bai sake magana ba , ita ta gaji da kanta tace ya tashi ya bata wuri sakaran da baisan inda duniya ta nufa ba , miƙewa yayi ya fice Abbakar ya biyo bayanshi amma Jiddah Momy tana fara faɗa ta tashi....
Bai fita ba saida ya haɗu da sauran "yan uwanshi suka gaisa suna mishi sannu da addu'ar Allah ya tsare gaba ya bashi lafiya mai ɗorewa , suma dai sunyi mishi labarin Papi wai ya tambayi Papi ina Mamanshi yaji me yake cewa , murmushi kaɗan Dikko yayi wanda iyakarshi kawai a saman fuskarshi ya tsaya baizo baki ba , bai wani daɗe ba ya wuce saboda Dady baya nan ,
Abinda yasa ya tura Abbakar wurin Sultana waya ce ya bada yakai mata zasuyi magana dan tabar wayarta a goruba road ta gudu tou yaso ta ansa wayar suyi magana yaji ita kuma Mama ko tayi fushi ? Wai me yasa wasu iyayen miji suke tsanantawa akan matan "ya "yansu ne ? Suke nuna ƙiyayya tsana da kuma hantara ne ?
Matar ɗa abun so ce kuma itama ɗiyarki ce inda mutunci , abin tausayi ce ta wuce wulaƙanci , baki san yadda take zaune da ɗanki ba , tanajin daɗin sa ne ? Ko kuwa wahalarshi take sha ? Idan kinsan ɗanki yana da kyawawan hali kila ita matarshi munana yake mata , idan ke yana da haƙuri a wurinki kila ita rashin haƙuri yake mata Koma dai wane irin baƙin hali ɗanki yake da tadai yi haƙuri ta zauna dashi , waye yasan ni ina dukan An mata ne ? Duk wanda ya ganta idan dai mai hankali ne da ilimin karantar rayuwar ɗan adam yasan An mata bata da kwanciyar hankali , na doketa na zageta mari rashin haƙuri akanta gashi kuma sam² baya mata uzuri akan komai ƙanƙantar laifi idan tayi mishi , gaskiya iyayen miji ku daina tsanantawa wa matan "ya "yanku a gidan aure dan baku san yadda su matan suke haƙuri da "ya "yan naku ba ,
An mata tayi haƙuri da halinshi tuni ba tun yau ba kuma a hakan dai tana sonshi bata daina ba , ko a yaddar mishi ko kar a yaddar mishi , ko aji daɗi ko kishirya hakan shidai ba yaro bane yasan abinda yake shine yake auren matarshi dalilin wani bazaisa ya sake aurenshi ba , dan haka babu wani abinda ya dameshi dasai an yadda ya dawo da ita kawai zaije ya taho da matarshi ,
Umar ne zaune a palon Inna yaci abinci yasha lemu ya wani mimmiƙe yana kallo , dan ita Inna bata san Umar ko daga ta ina ya fito ba kawai dai tana gani na dashi data tambayeni waye shi nace mata a can gidan Babana lokacin bata nan ne yake min mutunci tou shine take cewa ya shigo idan yazo ,
A zahiri kallo yakeyi amma a baɗinance wallahi rahotanni kawai yake iba , danshi Allah yasa mishi bakinshi bashi da saiti akan magana duk abinda ya gani ko yaji kamar mai aljanun surutu saiya faɗa , ya daɗe sosai daya tashi tafiya Inna ta bashi kuɗi wai yasha mai ,
Ƙarfe 8:21pm yabar gidanmu misalin 8:41pm Dikko ya bayyana a gidan , kuma kai tsaye ya shigo har palo ba tare daya bari an bashi izinin ya shigo ba , da sallama ya shigo daga ni har Inna muna ciki ina tayata tattara kayanta , jin muryar Dikko yasa na sauko daga saman gado da gudu Inna tana cewa ina zakije ne ? Banyi mata magana ba na bayyana a cikin palon a dai² lokacin da itama Inna ta fito , gefe na koma ina maida numfashi Inna da Dikko suna fuskantar juna kan Dikko a ƙasa ni kuma duk su nake kallo saina kalli wannan na kalli wancan ,
Mama barka da yi..... Fizgoni Inna tayi muka koma ciki gefen gado ta zaunar dani ta durƙusa gabana ta riƙe hannayena , cikin lallashi tace karki manta da yadda kikayi kuka Dikko ya turo aka ɓanɓare miki yaro daga aihuwarshi yace a anso mishi ɗanshi baya so yasha nonon karuwa , kinaji kina kallo suka anshe ɗan suka tafi dashi , a gaban idonki nayi ta kiranshi a waya yaƙi ya ɗauka daga baya ma ya rufe wayoyinshi gaba ɗaya kuma har zuwa yau bai kirani ba , wannan shine ya dace ya zama siriki na ? Mijin da bashi mutunta mahaifiyarki ? Mijin da baya so ɗan sa yasha nononki yace miki karuwa ? Kar ɗansa yasha nononki shima ya zama karuwi ? Wannan shine mijin daya dace ya zama siriki a gareni ? A , a , tou sakinki zai baki maza nawa kika sani suna jiranki ? Me zakiyi da Dikko daya fara tsofewa ? Nan zai tsofe ya barki ki shiga tararrabin rayuwa , sakinki kawai nake so ki anso zakiga mijin da zaki aura yafi Dikko duk abinda kike tunani kiyi ƙoƙari ki more rayuwarki tun kafin duniyarki ta ƙare.
Inna waye zan aura ? Wayarta ta ɗauko ta nunomin hoton wasu matasa har 4 wai idan bana san wannan ga wannan kuma duk shekarunsu kamar na Dikko ne , bayan na gama gani nace umm umm suma dai duk sun tsofen tunda naga zasu kai shekarun Dikko , amma aisu basu ciccika fuska da gashi ba , gemu take nufi da ƙasimba , taci gaba da cewa ya sakeki ki auri zaɓina ko kuma dani dake kowa yaja tashi da'irar danni gaskiya bana san Dikko a matsayin siriki , me yasa Inna ? Saboda yaron baida kunya ko kaɗan , to me yasa kika yaddarmin na aure shi tun farin fari ne ? Wancan karon ra'ayi ne yanzu kuma muradi ne shin Dikko kika ɗauka ko ni.............???
Haba harma sai an tambaya ? Ai ke na zaɓa Inna , idan ni kika zaɓa ta faɗa tana bani biro da takarda a hannuna anan ciki zaki dawomin da ansar , ansa nayi na fito jiki a sanyaye ban samu Dikko a palo ba , dan haka na fito harabar gidan , a mota na sameshi zaune yana waya , tsayuwa nayi ina jira ya gama , buɗe murfin motar yayi ya fito da duka ƙafafuwanshi waje sannan ya kirani da hannunshi ɗaya wanda bai riƙe waya dashi ba , matsawa nayi ya riƙeni jikinshi ni kuma na dafa kafaɗarshi ina wasa da gemunshi da ɗayan hannuna , murmushi yayi ya kalleni amma bai daina magana a waya ba ni kuma baiyi min magana ba yadai tsareni da ido yana kallona.
Ɗauke idona nayi gefe ɗaya na janye hannuna daga gemunshi , kamo hannun yayi ya maidashi a dai² lokacin daya ajiye waya , riƙo ƙuguna yayi da duka hannayenshi ya jinjina shi tare da ɗan girgiza jikina sannan ya ansa biron hannuna da takaddar ya ajiye a gefe , jawoni yayi jikinshi yace me ne ne zakiyi da ? Ya nuna inda ya ajiye , Inna tace ka sakeni , wane irin saki haka babu daɗin ji ? Shiru nayi banyi magana ba , yana nan dai da halinshi na faɗa , yace ina miki magana kinmin shiru kuma kinaji , yanzun ma banyi magana ba , turani yayi baya daga jikinshi yana cewa wuce ki bani wuri , da sauri na sake komawa , dakamin tsawa yayi karki sake ki taɓani ya ƙarasa maganar yana gyara zamanshi zai rufe mota ,
Ƙara matsawa nayi da sauri na riƙe murfin motar cikin rawar murya nace yi haƙuri na bari , cikin fushi yace ni duk abinda kika min banji fushi a kanki ba saike mai Mama zaki wani cemin wai tace miki na sakeki ? Me nayi miki ? Ƙiyayyar harya kai fagen saki ? To me yayi zafi haka ne ? Ke ko kunya ma bakij.... Nima irin abinda ya taɓayi min can² baya nayi mishi nima na kulle bakunan mu wuri ɗaya , da sauri ya sauke ajiyar zuciya ya riƙeni jikinshi sosai yanayin lunfashi da yanayin gajiya , riƙe fuskarshi nayi da duka hannayena gefe da gefen fuskarshi na lumshe idanuwa na nima inayin irin yadda yakeyi idan yana kwance dani , murmushi yayi mai sauti amma bai raba bakunanmu ba kuma ba magana yayi ba yana dai ci gaba da fitar da numfashin kamar wanda yakeyin mura , miƙa yayi a kasalance da niyar ƙara jawoni jikinshi najiyo muryar Inna tana ta kwararamin kira cikin ɓacin rai , ƙoƙarin raba jikina da nashi na farayi amma ya wani riƙeni sosai , ƙyarma jikina ya farayi har yanzu bai saki bakina ba , nace Dikko Inna ke kirana kar tayi faɗa fa , fita yayi daga bakina yace shigo , Inna kuma ƙara kira takeyi Sultana........
Ƙoƙarin kwace hannuna na farayi daga riƙon da yayi min dan tafiya wurin Inna , shi kuma yacemin shigo , Inna fa ke kirana , Innar , shigo nace , ah ni gaskiya bazan shiga ba , shigo nace , haba Dikko wai meye haka ne ? Nima bansan koma miye ba , Sultana.......... Na rantse da Allah idan nazo wurin nan saina zaneki , Inna ta ƙara² faɗa , cikin kwantacciyar murya yace karki tafi ki barni , ko kina so inyi rashin lafiya ne ? Ya ƙarasa maganar yana yimin yaudararren kallonshi fuskarshi ɗauke da kyakkyawan murmushin shi mai ɗaukar hankali , girgiza kaina nayi alamar a , a , tou zo muje kinji jarumata yayi maganar cikin sigar lallashi , ita kuma Inna zuwa wannan lokacin ta ƙufule ta daina kirana , ni kuma Dikko ya ɗaukeni a mota muka bar gidan....... Shin Inna laɓewa tayi ta gani abinda mukeyi ? Me yasa ta kirani , Allah kaɗai ya sani.
Saida muka fita daga barhim na matsa na riƙe Dikko , murmushi yayi cikin izza sannan ya riƙeni da ɗayan hannunshi ɗayan kuma ya riƙe sitiyari amma baiyi magana ba , kwantar da kaina nayi a jikinshi fuskata tana kallon kyakkyawar fuskarshi saida naja gemunshi nace ina kaje ne ? Ba da fuskarshi ya kalleni ba da idonshi ya kalloni kaɗan sannan yace nima bansan ina naje ba , ba kin gudu kin barni ba ? Baki san ɗana ko An mata ? Hmmm ba komai ni ina sanki a haka ,
Sauka nayi daga jikinshi cikin hayaniya nace bana san² , ai basai kin faɗa da yanayin fushi ba nasan yadda abun yake , ai nima na sani , karki min rashin kunya ƙaramar yarinya , Dikko nayi , ai baki da lissafi mai gotacciyar kwalwa dake kuma saina ƙara aure tunda har yanzu baki da lissafi , kaje ka ƙara mana ba kaji abinda Inna tace ba , shiru yayi bai sake magana ba saini nayi ta rattafa ɗimi kamar wacce ta lashi wuta , kafin muje G R A harna ratto mishi yadda Momy tazo ta ƙwacemin ɗa , har yanzu bai sake magana ba , bayan yayi parking bai fita ba kashe motar yayi ya ɗauki wayarshi yana latse² , ni kuma har zuwa wannan lokacin abin faɗawa Dikko bai ƙare a wurina ba , saida na gaji na ɗauke da kaina , cire makullin motar yayi tare da cewa muje yayi maganar ne a dai² lokacin daya fita daga motar , nima fita nayi nabi bayanshi ina cewa kuma ai ni banajin tsoron kishiyar ko an faɗa maka ni ɗin lusarar mace ce mai ma auren miji kuka , jinjina kai yayi cikin ɓacin rai , saida muka raba palon 2 ya juyo yace nidai kika raina ko ? Yadda yayi maganar cikin ɗaure fuska yasa na koma baya ina kallonshi , jinjina kai yayi cewa muje yayi gaba nabi bayanshi har ɗakinshi....
Yau da kanshi ya rufe ƙofa , kuma bai wani bani wannan maganin nashi da yake bani idan zai kwanta dani ba , na yau wani iri ne daban saida nasha akaje wasa , kamar dai na daren farkonmu yauma saida ya tabbatar ya gama gigitani yace tunda na raina shi saida in tashi in tafi gida , kamar sakara haka naita kuka ina bashi haƙuri amma sam Dikko ya kifa kanshi wai bayajin yaren da nake mishi magana dashi , nayi kuka kamar raina zai fita ina cewa bana san hakan wai kai me yasa mugu ne da Allah ? Ba kin rainani ba ? Tou yi haƙuri , cewa zakiyi kin bari bazaki ƙara ba , na bari bazan ƙara ba , ɗan gajeren tsoki yayi cewa kawai kije idan kinyi hankali sai kizo inyi wasan danbe , riƙeshi nayi ina kuka yace min na fita jikinshi karya kasheni , ƙin fita nayi naci gaba da kuka ina kallonshi , dariyar mugunta yayi min sosai yana min video , kuma ban daina mishi magiya ba , haka yaita gwalgwala ni , yana dariya wai saina faɗa yadda ake cewa wasan danbe da indianci idan ba haka ba shi bayaji da hausa , cikin ɓacin rai nace ban iya ba buɗemin ƙofar na tafi , anƙi a buɗe ba makullin a hannuna yake ba ? Idan kece kika kulle ai sai kinga dama kike buɗewa , sai kin faɗa , kuma ko kin faɗa sai Dikko yaga dama zai danbace ƙaramar yarinya ya ƙarasa yanamin gwalo , da nazo nayi shiru sai inji bana iyawa , kamar wata zararra haka ya haukatani a ɗaki naita hauka yana min dariya , saida ya gaji da ranfa ni sannan ya kwanta dani da wani irin baƙon salo , daga farko naji daɗin yadda yayi min daga ƙarshe saida yayi ɗabi'ar tashi dan idan baiyi mugunta ba ji yake bai haɗu ba , da naji azaba nayi magana sai ya nunamin vidion yace kefa kika roƙa , saida ya tabbatar ya wahalar dani sosai sannan yace gobe ma ki sake raina ni kindai ga amfani na...
Tare mukayi wanka , kuma kayan da nazo dasu sune na maida , saida na gode masa kamar yadda ya koyamin , shine da kanshi ya maidani gida , bayan yayi parking yace kin yafemin ? Saida nayi shashshekar kuka nace na yafe maka , rumgumeni yayi a jikinshi yace Allah yayi miki albarka , nace amin , kuma wasa nakeyi miki bazanyi wani aure ba , ai babu mai iya haƙuri da halina saike , ina sanki sosai "yar matana Allah ya ƙara miki haƙuri da halina , banyi magana ba ina kallonshi dai , murmushi yayi tare da sumbatar saman bakina , yace yi haƙuri don Allah , banyi magana ba har yanzu , da , da ne nake masa wannan kallon daya zazzaromin ido yace daina kallo , kinyi haƙuri ko ? Ey , tou jeki , kuma ki huta gajiya ngode , yawwa nima ngode na faɗa a dai² lokacin dana fita na rufe ƙofar bam ,
Ajiyar zuciya ya sauke bayan Sultana ta shige , vidion da yayi mata ya kalla sannan ya ƙyalƙyale da dariya yace baiwar Allah An mata , cike da tausayin Sultana da soyayyarta mai girma ya ɗaga mota yabar gidan.
Har yanzu Inna batayi bacci ba , a palo na sameta zaune tayi takurarren zama , Inna har yanzu bakiyi bacci ba ? Na tambayeta , ummmm ta bani amsa ba tare data kalleni ba , kuma cikin yanayin jin kunya dai ta bani ansar , zan wuce ciki ta kirani har yanzu bani take kallo ba ta kasa haɗa ido dani kwata² , ɗazu bakiji ina kiranki ba ? Yi haƙuri Inna banji ba , dama taya zakiji tunda kina so kibi Dikko , shiru nayi ban sake magana ba , tou tsaya kiji ina tsaye wurin ganin na nemo miki mutuncin ki da martabarki harni zan kiraki kiyi kunnen uwar shegu dani kibi namiji a gaban idona ke mara kunya ko ? Yanzun ma shiru nayi mata , idan wani abu ya faru ke kin isa kice Dikko ne ? Munafikin Allah ya saɗaɗo ya biyo dare ya ɗaukeki to ina kukaje ? Kaina na kallon ƙasa nace kiyi haƙuri don Allah ,
Wallahi bazanyi haƙuri ba saidai ki tattara kayanki ki koma wurin Dikko danni babu mai jamin dogon zance da karkata kai ina wallahi² , tunda kina san Dikko kawai kije ki koma amma ki sani idan har shi yayi miki wani abu ko "yan uwanshi karma ki sake kizo min gida na faɗa miki , tunda kika zaɓi Dikko wallahi na bar mishi ke duka , dama ai nace miki idan kika zaɓi Dikko a kaina saidai dani dake kowa yaja tashi da'irar , kin bishi kuma kin dawomin babu takaddar sakin ki , zanyi magana ta dakatar dani ta hanyar dakamin tsawa tana ci gaba da cewa jaka ya ɗaukeki sakarar banza da baki da kyakkyawan tunani , tunda kin bari ya rainaki ya ɗauke matattara sauke buƙatunshi , yazo yayi miki daɗin baki kin kwashi jiki kin bishi amfaninki kawai ya samu natsuwa dake ya samu kuma ya maidoki hoto kawai dake , to sai kije idan wahala ta kasheki kece kika huta idan sun barki kin zauna ɗangin nashi kiyi ta haihuwa suna ɓanɓare "ya "yan ta ƙarfi da yaji , shi kenan kin zama jaka saidai kullum kisha wahalar ɗaukan ciki ki haihu a barki da shan ruwan zafi , In , ki rufemin baki ko inci mutuncinki a daren nan , kuma sai kin barmin gida tunda kin zaɓi Dikko akaina , I , ki rufemin baki wallahi kika sake kamo suna na saina wulaƙantaki , simi² na wuce ciki ita kuma tana cewa ki tattara kayanki yazo ya tafi dake , tunda kinƙi ya sakeki ki aure wanda nake so a cikin maza 4n dana nuna miki.........
Da safe Inna haka ta barbaɗomin kayana a tsakar gida ta rufe ɗakunanta , duk haƙurin dana bata² saurareni ba bayan ta cemin kar na sake naje inda duk wani ɗan uwanta yake , duk saboda ta kirani Dikko yace nazo muje akan me zan bishi ? Kuma itama ai tasan kiran wanda yake gaba tsakanin miji da uwa , kawai dai tana so ta kashe min aure ta auranmin wanda ranta yake so , a cikin mazan da tace na zaɓa su tana da tabbacin daga su har iyayen nasu dashi kanshi wanda zan aurar bazasu wulaƙantani ba ?
Dikko baice baya so na ba , bai wulaƙanta ni ba , tou wai me ma yayi min ne ? Ko sai in kashe auren nawa inzo in zama na Jiddah nima in tashi biyu babu , idan kuma nabi irin nata ra'ayin ita Inna kenan itama ba wannan mijin aka ce ta aura tun farkon farko taƙi aurensa taje ta auri Babana , saini zance Dikko ya sakeni inje inma kashe auren Allah ya jarabeni da fitinar duniya , zawarci ai shima ɗaure yake da ƙugunshi ,
Saida nayi musu rakiya har wurin mota duk addu'ar sauka lafiya da nayi mijinta kaɗai ya ansa ita kuma ko kallona batayi ba , addu'a ta dai su sauka lafiya kuma su dawo lafiya.
Haka na yini a filin gidan Inna har kicin inta ta rufe abinta , ina zaune a ƙofar ɗakinta data rufe kamar asara duk abinda zanyi a bayin tsakar gida nake huɗɗoɗina amma har dare babu abinda naci saboda banda ko si² a hannuna. A ranar yau Dikko bai zo ba , kuma a maƙotan gidan Inna na kwana ganin zan kwana da mai gadi , a gidan ne suka bani abinci naci ,
Washe garin tafiyar Inna ma Dikko baizo ba , kuma ranar ma a maƙota na kwana , saida akayi sati biyu da tafiyar Inna Dikko yazo , ina maƙota mai gadin gidan Inna ya kirani , yauma babu driver ba ɗan rakiya a mota na sameshi zaune daga shi sai wani ɗan kyakkyawan yaro anci mishi gayu cikin wata irin zuƙeƙiyar shadda { getzner } hutu ya zauna a jikinshi sosai , kallo ɗaya zakayi ma yaron kasan gidan kuɗi ya fito daga shiyar manyan mata gogaggi wanda suka san darajar wanka da gayu sai kuka yakeyi , Yaya mu cafi jida ya cire hular da aka ɗora mishi a kai ya riƙe a hannu sam ya hana Dikko yayi min magana ,
Kai ni bazan tafi ba waye yace ka biyoni ? Ni a nan zan kwana , ƙara fashewa yayi da kuka yana ta maimaita suje jida , kashe motar yayi yana cewa muje ciki , taya zan iya faɗa masa Inna ta kulle ko ina ne ? Ah kawai mu zauna a mota shi kuma harya fito da yaron daya zo dashi yasa na ɗaukeshi sai yagushin fuskata yakeyi yana kuka baya co , ƙafarshi ɗaya a waje ɗayar a ciki yake miƙomin wayoyinshi da hular da yaron ya jefar , daka mishi tsawa Dikko yayi yana cewa kai bana san iskanci kaji , shiru yayi yana kallon Dikko yana kuka kaɗan² , saukeshi ya tafi da ƙafafuwanshi , da sauri na sauke shi nima ina kallon Dikko kamar yadda yaron keyi tare da cewa wurin fa a rufe yake....
Tou kije ki buɗe yayi maganar hankalinshi nakan wata leda da yake dubawa , shiru nayi na rasa abin cewa , da faɗa ya juyo kunzo kunmin tsaye nace kuje ciki zanzo , babu makulli a hannuna , sai a hannuna nake da ? A , a ina nufin bana nan Inna ta fita bata dawo ba , daga Abujar ? Kai tsaye nace masa Ey , da ɗan yanayin damuwa yace shikenan ku shigo mu tafi ba tare daya kalleni ba yayi maganar yana gyara zamanshi ya rufe ,
Zagayawa nayi zan shiga motar yaron nan ya fara kuka bana shiga musu mota , Dikko yace kai zan zaneka wallahi , fashewa yayi da kuka yana turani baya , juyawa Dikko yayi bayanshi ya ɗauko dorina yace masa gafara daga nan , cikin kuka yace bata ciga ya matsa baya ya riƙemin hijabi wai basu zuwa dani , da bulalar ya kawo duka yaron ya matsa yana kuka bai sameshi ba sai cewa yakeyi bacu zuwa dani , Dikko yace An mata shigo muje mu barshi a nan , ɗaukarshi nayi na sakashi ciki nima na shiga na rufe , tunda muka ibi hanya Dikko yake faɗamin Mama ta kirashi ta tozartashi iyakar iyawarta , abun bai mishi daɗi ba dan saida tasashi ya sameta har Abuja ta wulaƙantashi hmmmm , cika idonshi yayi da hawaye yace ta faɗi maganganu masu muni a kaina marasa daɗin ji , nayi mata uzirin ɓacin rai nasan duk fushin abinda ya faru ne ta tattara ta sauke a kaina da bansan abinda ya faru ba , ina can ina jinya banma san ina nake ba , ina nan zan barki kizo ki zauna gida har banzo ba ? Da nasan inda kaina yake ko a waya ai zan kiraki tunda gashi ranar dana dawo ai ranar nazo wurinki , kuma ita Mamar da tace ta kirani ban ɗauka ba idan naga kiranta zan basar ne ? Haka nan ma nake kiranta na gaisheta babu ranar da bana kiranta na gaisheta tunda na aureki , tou idan baki saki ba ranar da kika kulleni a ɗaki kika gudu kinsan yadda na kasance a wannan ranar ?
Ba abinda ya dameni da yadda ka kasance har ni kake cema kayi ma Inna uziri idan bakayi uzirin ba me zakayi ? Ko itama haukar zakayi mata ne ? Cikin ɓacin rai yace aike yarinya ce uzirin ne hauka ? Ni nasan darajar duk wanda ya haifi ɗiya ya bani , bawai rashin kunya ko rashin ɗa'a yasa nace nayi mata uziri ba , ina nufin nasan taji fushi da ɓacin rai akan abinda akayi miki na ɗauke Papi ya nuna yaron yana ci gaba da cewa shi yasa kirkina dubu wannan dalilin ya gogeshi na dawo mara mutunci a idonta , to kici gaba da kiran hauka zamu haɗu anjima , shiru nayi ban sake magana ba har muka iso G R A , haka na taho ba abinda na ɗauko daga gidan Inna , kuma bansa yadda sukayi ita da Dikko ba amma tabbas nasan zai faɗamin yadda sukayi da ita har yaje ya taho dani , da yadda ya kasance bayan na kulleshi na gudu , da yadda suka ƙare da Yazeed da Aunty Suwaiba Al ' Ameen da kuma labarin Mardiyya.
Saida Parpy yayi bacci Dikko yasa Ashiru ya maidashi , kuma yau da ya bani maganinshi ban ma yadda nasha ba dan abinda na fahimta ta cikin maganin nan yake haukatamin lissafi , yayi lallashi nace bafa zansha ba , haba An matana dan Allah kisha , Allah bazan sha ba , kar Allah yasa kisha "yar rainin hankali , oho maka dai......
A ranar wasan ba magani akayi shi , kuma ran Dikko ya ɓaci , tunda naƙishan maganin banzarshi , har gari ya waye bai min magana ba sai fushi yakeyi , daya tashi fita ma nayi masa a dawo lafiya bai ansa ba , daya dawo ma sannu da zuwa na ma bai karɓa ba.
Haka dai mukaci gaba da dafa rayuwar , Momy tayi ruwan wulaƙanci da taji labarin na dawo kuma tazo ta zabgaga rashin mutuncin ta iya ƙarfinta , kuma Dikko yaji babu daɗi sosai ya bani haƙuri kuma nayi , Dady kuwa Dikko ya zauna ya warware masa komai kuma Dady yayi ma Momy faɗa yace bataji dai daɗin halinta ba , ɗiyar ɗanta da girmanta ta zauna tana mata ƙarya bata kyauta ba , kuma ya ƙara maimaita mata batayi hali mai kyau ba data raba uwa da ɗanta ta guji ranar da sakayya ta waiwayota , shi dama bai wani ɗauki zafi da Sultana ba Momy ce takaishi ta baroshi kuma yanzu ya gane gaskiya dan haka ya dawo daga rakiyarta.
Gaba ɗaya Dikko ya tsameni daga sabgar "yan uwanshi , biki suna jaje ko mutuwa bana zuwa , yace tunda basa so na kawai inyi rayuwata na manta da sabgar duk wanda baya sabga na , hankalina kwance banda wata damuwa dan Dikko ya hana duk wannan gayyar "yan gidansu zuwa gidanshi , kuma makaranta ɗaya muke da sauran ƙannenshi amma ba wanda suke ɗaki ɗaya ba , ban koma SS a tsohuwar makarantar da Inna ta kaini ba , Ashiru ke kaini yana ɗaukoni , idan kuma Dikko yana gari shine yake kaini yana dawo dani ,
Muna cikin haka ne babbar ɗiyar Rabiya ta kwanta ta mutu , kuma banje gaisuwa ba , mutuwar ta tashi rankatakaf hankalin ahalinsu Dikko , saboda babu wata jinya da tayi lafiyarta lumi tana cin abinci maka'ikan mutuwa ya zare ranta , koda akaje asibiti likitoci sunce tuni ta mutu saima a wurin wankan gawa aka kwakwale sauran abincin daya maƙale a bakinta.
Rashin shigata cikinsu yana musu ciwo Dikko kuwa ya zuƙeni daga cikinsu kwata² , tou rashin zuwa gaisuwar ne ya ƙara basu mamaki , abin ya damesu , koda Momy tace ma Dikko meya hana matar ka zuwa gidan gaisuwa ? Cewa yayi shine ya hanani , dalili Momy ta tambaya.........
Kuyi haƙuri wallahi wayar lumshewa takeyi bata doguwar tafiya yau dasai na ƙarƙare labarin nan amma ku bari mu ƙara ko feji biyu ne ,
18/12/2019 👇🏻
*JAMILA MUSA...* 💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 89
*_YAHANASU YUSUF A Y RAƊƊA , {{ Mrs TANIMU MUSA QERAU }} yau gaisuwar taki ce ke ɗaya matar Yayana , ina miƙo saƙon dubun gaisuwa ta zuwa gareki tare da addu'ar fatan alkairi , kiyi farin ciki , cikin farin ciki kuma kyakkyawa..._*
Shiru Dikko yayi ya gagara cewa ummm ummm idonshi yana kallon ƙasa ya kwantar da gefen kanshi a gefen kujera kusa da inda Momy take zaune , ita tana sama kenan shi yana zaune a ƙasa , cikin sigar lallashi tace Dikko mace ta fini mutunci a idon ka ko ? Yanzun ma shiru yayi babu amsa , idona biyu ban mutu ba kenan , idan kuma na mutu ka gama da "yan uwanka har abadan duniya haka kayimin adalci kenan ? Yanzun ma a ɗauke yake baiyi magana ba , me yasa daga kai har matarka bakuje wurin zaman ta'aziyya ba...... ???
Ba tare daya ɗago ba yace ai ni naje , sau ɗaya tak kaje fa , ko kana tunanin ban sani ba ko bana ganewa iye..... ? Duk yaran gidan nan tunda akayi rasuwar nan suna gidan Rabiya suna tayata jimamin rashin ɗiyarta , duk wacce ke aure kuma mazansu duk dasu ake zaman ta'aziyya , sai kai zaka kawomin wata sabuwar aƙida a cikin zuri'ata ka warwaremin zaman lafiya ka jefa ƙiyayya a cikin kai da kuma "yan uwanka ? In banda kake ɗan iska yarinyarta ta kwanta ta mutu ba ciwon kai bare na jiki , kuma ba yarinya ba budurwa Dikko kace kaine ka hana matarka zuwa gidan ta'aziyya kuna cikin "yan uban suna nan suna kallonku kuma suna karantarku idan har kuka kuskusara suka ga wata ɓaraka ta fita a cikinku sai sun hanaku zaman lafiya ,
Zaiyi magana ta daka mishi tsawa tace rufemin baki mara kunya , baka san dama ƙufule nake dakai ba ? Ni bana san "yar iskar yarinyar nan bana santa ׳ ko zan mutu bazan so yarinyar nan ba , ƙaton banza ƙaramar yarinya ta maida kai susutancen namiji , har nawa take da zata juyaka sakaran banza marar tunani , tou ita ɗin da kake gani kana iya rabuwa damu saboda ita muɗin dai daka ɗauka ba'a bakin komai ba mune na gaskiyar , ita kana iya rabuwa da ita kuma wata zaka auro , mace ana canja ita amma ni da "yan uwanka baka iya canja mu har abadan duniya , ka saki gaibu ka kama zahiri idan ba haka ba sai kayi dana sani wata rana , da sauri ya ɗago ya kalli Momy cikin damuwa yace kar kiyi min baki Momy , ba baki nayi maka ba , gaskiya na faɗa maka , bani na faɗa ba kaima ka sani kuma kowa ya sani , karuwa har amana ne da ita ?
Karuwa bata zaman aure , sai ka gama gina rayuwarta zata zazzage ka tayi gaba abunta , badai yarinya ka auro ba ? Yarinyar ma karuwa , karuwar ma da bata fito daga tsatson mutunci ba ko ? Hmm addu'a ɗaya ma zakayi karta kashe ka , dan wannan yarinya daga ganin idonta babu Allah a lamarinta kana can ana barbaɗa maka kana tanɗewa , Allah kaɗai yasan iya ƙazantar da take baka kake ci a abinci , layu kuma baka san ta ina kake takasu ba , ka kwanta akansu ka tashi akansu gaba ɗaya ta ɗimauta ka , ka dawo wani sakarai , banajin daɗin ganin wannan ranar Dikko ka cuci rayuwata daka auri karuwa , ka rusa gidanka ka rusa rayuwarka da bayanka , dama mutuwa nayi banga zuwan wannan ranar ba , ta ƙarasa maganar kamar zatayi kuka.
Parpy dake tsaye bayan Momy saman kujera yana wasa da makullin motar Dikko yace , Culcana , shi Dikko ba wai duka yaren Papi yake ganewa ba dan hausarshi bata fita yana tsamin baki , Momy taci gaba da cewa , ina gudar maka irin abinda ya faru da mijin Safiya Ya'u ne , haka mijinta yaje ya auro karuwa , Papi ya juyo ya anshi labarin yana zaro ido cikin tsoro cine Culcana ta yankaci , ya ƙarasa maganar duk idonshi a waje yana nuna yankawa da hannunshi dai² wuyanshi , maimakon Momy tayi ma Papi faɗa tunda ita tana gane abinda yake cewa sai tace Ey mana haka zata yanke Yaya ya mutu shima , dariya Papi yayi yana kallon Dikko , ita kuma taci gaba da cewa hankalinta da natsuwarta bazata zauna lafiya ba harsai taga ya saki yarinyar nan , zata natsu.
Jiddah ce ta shigo palon da sallama gaba ɗaya palon ya disashe duk wani ƙamshin turare da wani turaren wuta gaba ɗaya turarenta ne kaɗai ke tasiri , tafa wanku yadda hankali baya iya hasasowa dan Jiddah "yar gayu ce sosai , murmushi tayi tare da taɓo Perpy tana cewa dan Yaya yazo baza kamin Oyoyo ba ? Da sauri yayi baya yana goge inda ta taɓa mishi fuska , Momy ji abinda Perpy yakemin , Momy tace ai kun saba , Perpy kuma cewa yayi kuma baciyi cau ba , Jiddah tace kam lallai ma yaron nan aiko na haɗu kuma nayi kyau ka tambayi Yaya kaji , daga bayan Momy ya leƙo Dikko yace Yaya aije batayi cau ba , shiru Dikko yayi bai kalli Perpy ba kuma bai ɗago daga yadda yayi zamanshin tun farko ba , a yangance Jiddah tace Yaya barka da yini , yawwa ya faɗa tare da fiddo wayarshi daga aljihu yace Momy zan tafi , da sauri Papi ya sauko yayi gaba kar Dikko ya tafi ya barshi , Jiddah kuma ciki ta wuce tana wata irin tafiya mai ɗaukar hankali , da wutsiyar ido Dikko yabi bayanta da kallo , a ranshi yace hmm mata kenan..........
Momy kuwa taci gaba da cewa , ashe karuwar nan badan Allah ta auri mijin Safiya ba kuɗi aka bata akan ta kaso shi , shi yasa gabana yake faɗuwa kar haka ta kasance dakai , shima kamar kaine dai , da iyayenshi sun hanashi aurenta amma yayi kunnen uwar shegu dasu yaje ya aurota , ashe bai sani ba ajalinshi ya ɗauko , daya aureta dangi suka taso ta gaba saiya tsameta daga cikinsu dama tunda taje gidan bata ma wani yadda tayi ciki ba tunda tasan aiki ne ya kaita , Dikko ni nake faɗa maka wannan labarin dare tabi ta yankeshi ya mutu har lahira , da wuƙa nake faɗa maka , Allah ya jiƙanshi , saida Momy ta ƙara zage Dikko sosai tana farfaɗa mishi manyan illoli game da auren karuwa da kuma haɗarinta , sannan tace ya tashi ya bata wuri sakaran banza da mace ta gama dashi ,
Jiki a sanyaye tattare da damuwa Dikko ya fito daga palon , makullinshi ya ansa a hannun Papi ya faffalla mishi mari yace ya wuce ya bashi wuri idan ya sake biyoshi saiya ci ubanshi , riƙe Dikko yayi ya fashe da wani irin kuka mai tada hankali , danshi Dikko idan dai ranshi ya ɓaci tou saiya rarrabashi kowa ya samu , cikin hayaniya yace sakeni yayi maganar yana zazzaro mishi ido , kallon Dikko yakeyi kuma bai daina kukan ba yaƙi sakinshi , jin ihun Papi ne yasa Momy fitowa tace me yayi maka ne ? Ni babu inda zanje dashi , Momy tace sai kaje dashi , cikin ɓacin rai yace haka zan ɗauki yaro inta yawo dashi a gari kamar wani sakarai , ai sakaranne , shima ya san kai sakarai ne shi yasa yake ganin ka kamar wani abokinshi.
Ni gaskiya babu inda zanje dashi , Momy tace wallahi sai ka tafi dashi , Papi kallon Momy yayi yana shashshekar kuka bai saki Dikko ba , Momy tace sai yaje dakai daina kuka kaji ko.....? Har yanzu ita yake kallo sai kuma ya kalli Dikko bayan wani lokaci , Dikko baiyi magana ba ya buɗe mota ya shigar dashi suka tafi....
Momy kuwa palo ta koma cike da ɓacin rai , irin wannan ranar ce take gudun zuwanta kuma gata nan tazo , wannan dalilin yasa taso Yaya tayi haƙuri karta kashe auren Jiddah , gashi tun ba'ayi nisa ba Dikko ya hana kowa zuwa mishi gida , ya tsame matarshi tsam daga cikinsu bare in tazo su riƙa muzanta mata , gaba ɗaya Dikko ya canja hali kuma ya rage masifa ya zama wani ruwan sanyi saboda mace , ita dai Allah ya sani bata san Sultana kuma idan dai tana rayuwa saita raba Dikko da yarinyar nan , dan ta faɗawa wata ƙawarta abinda yake faruwa kuma tana nema ma Dikko auren "yarta amma tace matarshi ta katantane ko ina ta hana wata shiga , ɗiyar Yayarta ma da yake aure itace tayi mata asiri ta tashi hankali saida dai akayi saki Jiddah ta samu natsuwa , kuma saki 3 ne babu damar a koma , ita bata iya wannan ɓatar ba ta neman asiri amma idan zata iya ta fitsare ƙafafuwanta ta fitar da Sultana ita kuma zata sa Dikko ya auri ɗiyarta.
Da ɓacin rai ya dawo gidan , tunda naga yanayinshi banma shiga sabgar shi ba daga sannu da zuwa ban sake mishi magana ba , kuma bai ansa ba , tunda ya shiga ɗaki bai sake fitowa ba , da Papi yayi bacci text ya turomin inje in ɗaukoshi daga ɗakinshi , ko da naje ɗaukarshi faɗa yayi tamin wanda shi kanshi baisan dalilin faɗan ba , waishi yafi ƙarfin mace ta raina shi , haka kuma babu wata banzar macen da zata iya juyashi ko wacece ita , nidai ban masa magana ba na ɗauki Papi zan fita yace idan naje na kaishi inzo , a ɗan tsorace nace ina zan kaishi ne ? Saman kaina zaki kaishi ,
Allah ya baka haƙuri , na ɗauka zan kaishi wurin Ashiru ne ya maidashi , duk yadda kike so haka zakiyi , yadda dai kake so Dikko , to da kinsan wurin Ashirun zaki kaishi zaki tsaya kina tambayata saboda raini......? Tou ki sani jiya ba yau bane ba idan kuma kika ce zaki min yarinta yanzu zakiga yadda zan ruɗa miki rayuwa.
Ajiye mishi ɗanshi nayi zan fita , An mata zo nan , yi nayi kamar banajin shi , wallahi idan kika fita saina zaneki , zo nace , tsayawa nayi ban dawo ba , karki bari na sake miki magana , ɗaure fuska nayi na koma wurin shi , cikin ɓacin rai yace ke har kin isa ni zaki ma baƙin rai ? Wace ce ke ? Ɗaukarshi , ban sake magana ba na ɗauke shi na fita ,
Ina kaishi na dawo , ci gaba yayi da faɗa yana rufe idanuwanshi cikin rashin mutunci , waishi ya gaji da cin zarafin da ake masa akaina , ko aure kanshi farau saidai insan inda zanje danshi ya gaji , da wane rayuwa zaiji da Allah , gani nima mara kunya na raina shi harna faɗa masa , tou ya gaji wallahi saidai in tafi gidanmu , ƙyarma jikina ya farayi gaban ya faɗi , a raina nace na shiga3 Inna ta koreni kaima ka koreni ? Abinda Inna tace tunda na zaɓi Dikko ko zai kasheni karna zo mata gida ta yafe mishi ni duniya da lahaira , cikin rawar murya nace Dikko me kuma nayi maka yanzu....... ? Ba abinda ya dameni ki barmin gidana ni na gaji bana iyawa , kayi haƙuri idan nayi maka wani abu insha Allah bazan sake ba , cikin ɓacin rai ya juyo tare da nunani yace ke............ Ki barmin gida nace ,
Fashewa nayi da kuka nace kayi haƙuri don Allah , bazanyi ba.......... Sai kin tafi daga gidan nan , yau akanki zagi nawa Momy tayi min ? Tacemin sakarai har take cemin Perpy ma yasan ni sakarai ne , ance kin shanyeni tou yau sai kin barmin gidana dan kowa yasan ni ba shanyeyyen namiji bane ba , ya ƙarasa maganar yana ciro bero daga gaban aljihun rigarshi....
Cikin kuka nace haba Dikko me kakeyi haka don Allah ? Ke ni ba mahaukaci bane ba nasan abinda nakeyi ya nuna saman ƙoƙon kanshi , ita Mamar taki kinsan me tacemin akanki ? Ta muzantani ta tozartani me nayi mata ne ? Kayi haƙuri Dikko , naƙi inyi haƙuri tunda kika shigo rayuwata farin ciki yayi bankwana da zuciyata , matsalar yau daban ta gobe daban in fita waje a ɓatamin rai in dawo gida dan na samu natsuwa kimin rashin kunya , ba tattalin miji kwata² baki san darajata ba , kina ƙasa na amma kina nuna ke wata isashshiya ce , wace ce ke ? Wanda kinsan ko a gado nine a samanki duk ta inda aka juya , na bari , hararata yayi cikin fushi yaci gaba da cewa , wane fi'ili zakimin duk wani feleƙenki a tafin hannu a yake , me ma kika iya ? Me kika sani akan namijin....... ?
Shiru nayi ina kallon ƙasa , yaci gaba , kullum ɗaurin zanin ki iri ɗaya ne , tafiyar ma tun wacce na sani , kullum kina nan dunkume ba ranar da zaki buɗe idonki kisan wace irin rayuwa akeyi , babu ilimin zama da miji sai rashin kunya shi kaɗai kika iya mutum ya taɓaki ki ɓare baki kiyi ta wani kukan munafinci , { idan yana kwanciya dani } me kika nema kika rasa ne ? Ni wallahi bana san kidahumar mace , bana san jakar mace bana san ƙazamar mace , idan na faɗa miki yadda nake so kiyi rayuwa dani sai kicemin ina miki cin fuska , me Jiddah tafi ki ne ? Babu abinda takai ki a cikin mata dubu baki kasuwa ba'a fini mata ba amma an fiki sanin zamani , cikin ɓacin rai nace niba kidahuma bace ba , kuma kai kanka kasan ni ba ƙazamiya bace ba , dan kaga ina baka haƙuri kake ganin kamar inajin tsoron rabuwa dakai ne ? Banda ilimin zaman mijin kuma bazan koya ba , idan ka rabani da kanka zan mutu ne ?
Ai saika rubutu abinda zaka rubuta ga biron nan a hannunka , ni ba abinda zan rubuta da biro ajiyeta zanyi saidai in zaneki kikaimin rashin kunya , murus zan kasheki babu wanda yaji babu wanda ya gani , amma yau sai kin tafi gidanku na faɗa miki , bazan tafi gidanmun ba , wallahi babu inda zanje , cire kayanshi yayi ya nufi toilet yana cewa shi yasa duk namijin da yasan abinda yakeyi wallahi bai auren yarinya , kullum kaida mace faɗa cikin gida , ai kasan inda ake auro manyan mata kaje ka auro mana , shigewa yayi bai sake magana ba , ni kuma naci gaba , banyi shiru ba har yayi wanka ya fito.
Yana fitowa yaci gaba , ina ma amfanin mace ba soyayya , kije cikin matan gidanmu su koya miki yadda ake tattalin miji , ki koyo yadda ake rainon miji , a koya miki kissa su koya miki wanka da saka sutura tunda ni kin raina ni , Nabeela zata koya miki yadda ake tafiya a gaban miji je kiga yadda suka wayar da Jiddah suka buɗe mata ido baki ajiye komai ba sai girman kai , da raina miji , kin ɗauki miji kamar wani sa'arki ina magana kina ɗaga min murya sama sai kace kece kike aure na.
A daren yau saida ya tabbatar ya ɓatamin rai harsai da nayi kuka ya jagulamin lissafi tas , sannan yayi shirinshi yana gama shiryawa ya wurgamin kuɗi a saman gado shi ya tafi Abuja kuma kar in sake zuwa makaranta saiya dawo , binshi nayi ina kuka , kila tausayi na bashi ya tsaya ya rungumeni yace An mata bakijin magana wallahi , cikin kuka nace Dikko dan Allah na bari , na faɗa ina kallon idonshi , riƙeni yayi sosai a jikinshi , a hankali ya duƙo saitin fuskata cikin magana mai saukar da kasala yace yi shiru , ya ƙarasa maganar yana tsareni da kyawawan idanuwanshi , rufe bakina nayi ina kallonshi , buɗe bakinshi yayi , yayi wani iri da harshenshi kaɗan yana wasa dashi sannan ya kirani da harshen nashi ,
Saida na sauke ajiyar zuciya cikin shashshekar kuka na riƙe jikinshi tare da shiga bakinshi da nawa , kullum idan zaimin wani abu yakan canja min sabon salo ne , nayau daban , na gobe ma zaizo da baƙon salo , ya ɗauki wasu "yan ƙalilan mintuna sannan ya sakeni daga jikinshi , ƙara riƙeshi nayi ina kuka nace dan Allah karka tafi , ba tare daya kalleni ba yace ki bari sai kin iyo riƙe namiji a gida sai ki riƙeni in zauna , inaji ina gani yayi tafiyarshi....
Ɗakinshi na koma na faɗa saman gado ina kuka , nidai Allah ya sani banda wannan idon tsakiyar kai irin na gogaggin mata , ko a can baya dana riƙa iskancin nan ba'a hayaccina nayi ba , ina naje ina aka sanni ne ? Wa na gani waya ganni ? Ban taɓa haura Katsina ba daga Daura sai Katsina iyakata nan , kenan tunda akayi min sauka aka sauke duk wani sheɗanci dake saman kaina , tou me Jiddah tayi wanda yasa Dikko yake faɗamin ita a magana harso 2 ? Duk yadda akayi kila yaga Jiddah ta burgeshi ne , shidai Dikko yana san gogaggiyar mace , mai tafiya da zamani , wacce ta waye sosai idonta ya buɗe da duniyanci amma a gidan aure , ƙwanƙwasashshiyar mace a fagen tarairayar miji , "yar duniya da tasan logon maza , wacce ta shahara ta kuma ƙware a wurin iya wasan danbe ,
Tou ba Dikko kaɗai ba duk mazan zamani mata haka suke , gadai Jiddah an saketa amma tunda tasan yadda yake san mace ta kasance ta kasa sanya , kullum a riƙe take , irin su Jiddah ne matan da idan namiji ya sakesu zasu kashe shi da bariki shi kuma yaci gaba da zagayawa kina gida kwance kamar asara ana can ana hidimar duniya babu ke , yanzu zamanin nan duk inda kika nufa mazan sun zama iri ɗaya ko wane baya san afi matarshi kuma basasan baƙauya ko ƙazamiya , wallahi duk kyanki duk tsarinki duk iya haɗuwarki duk irin sigarki da nagarta da kike da , idan dai baki da gayu baki da wayewa baki iya girki ba tsafta da ilimin zaman aure ke hoto ce , hoton ma elajiment da zaran an liƙaki a bango an gama dake , tou haka macen da bata san damarta ba take wurin mazan zamani , baki da wani amfani saidai ki share gida kici abinci , idan kuma kikayi sa'a da ɗan duniyan namiji kina nan sake da baki kina ta rashin wayanki yana can shi kuma yana miƙa kuɗinshi ana sashi a ɗaki , duk hidimar da miji yake miki zata ragu tunda masu ci sun ƙaru , gaki ke matar gida ga matan bariki , yake "yar uwata me akafi ? Wane duhun kai kika tsaya ? Tou rayuwa ta canja , zamani ya juya keda mijinki kina ji kina kallo makwaɗaitan matan bariki zasu ɓanɓare miki miji ta ƙarfi da yaji ,
Dan wallahi wasu mazan basu iya ba koya musu akeyi , wasu kuma dama can jarabar a jininsu take , wasu abokai ne suke kaisu su barosu , wasu kuma matan nasu ne da kansu suke yanka musu tikitin shiga bariki, idan kikayi masa magana ya daina kwanciya dake in kinci sa'a ya faɗa miki illolinki idan kina da rabo saiki gyara , idan kuma kin samu namiji mai zafi ya buɗe miki ita tsaye yace ake ƙazamiya ce ba wanka ba gayu ba shafa turare haka zai dosoki kina ƙarnin hayaƙi ko zufa ko zarni fitsarin yara , ke kuma sai kiji haushi an faɗa miki gaskiya ki masa rashin kunya , idan akaci sa'a da irinsu Dikko su zaneki a barki da kunburaren jiki , ke kuma fuuu kinyi yaji daga nan matsala ta samu hanyar shigowa , mata mace ƙwalisa ce ita , fulawa ce bata rayuwa saida gyara , zamanin ga ya lalace idan kuma kika kwanta tou fa lallai kinji a salansa , bawai ina nufin ki tashi ki nemi asiri ba , a , a ki tashi ki gyara domin zamanin yazo da sabon salo.
Tunda Dikko suka ibi hanya saidai yayi tsoki , Sultana fa ga mace har mace komai yaji , ga kyau , ga siga , nagartacciyar mace gata tayi dai ko ta ina baka isa ka kusheta ba inba hassada ba , ga ƙugu An mata , ƙaramar yarinya da ita amma Allah yayi mata zubin bodi irin na manya mata , saidai ɗanyen kai ya hanata ta fuskanci damuwarshi , wace ce Jiddah ? Wace ce ita idan An mata tana nan ? Gaskiya An mata kyakkyawa ce , mace ce ta tsara , fitacciyar mace mai kyakkyawar halitta , bakinta mai kyau , tana da tsarin haƙora masu burgewa kuma tsaftatacci , tayi sosai gaskiya saidai matsalarta yarinta , zuciyarshi ce ta bashi haƙuri cewa shekarun Jiddah da Sultana ba ɗaya ba , inda Jiddah taje Sultana bata je ba , ƙawayen da Jiddah keda su ba irinsu An mata take da , ba wani , yaran ƙauye ai basu kai An mata ba ake musu aure kuma lumi suka riƙe miji babu mai ji , saishi ko kwanciya zaiyi da ita saida "yan dabaru , zuciyarshi dai haƙuri take ta bashi akan cewa idan Sultana ta goge wallahi shi kanshi saiya zama swry ya kwantar da hankalinshi da sannu za,azo wurin......
Wayarshi ya ɗauka tare da tura mata text , taje makaranta , sai kuma adireshin { address } in gidan Rabiya taje mata ta'aziyya , sai izinin hawa mota da inda zata ɗauki makullin saboda Ashiru bashi nan , hada lambar { number } Momy ta kirata tayi mata gaisuwa , kuma daga makaranta gidan Rabiya karta je ko ina......
Saida safe naga saƙon Dikko bayan nayi sallah asubahi zan koma bacci na gani dana ɗauki wayar , ban ce masa na gani ba kuma ban kirashi ba nima na basar da lamarinshi , da ya tafi saida yayi wata ɗaya da sati biyu kuma har yaje ya dawo banyi waya dashi ba , koya kirani ma bana ɗauka kuma banje gaisuwar ba , kuma kuɗinshi a inda ya wurgasu a gado ban taɓasu ba banma ko kalli inda suke ba , yadda yabar ɗakin haka ya dawo ya sameshi , ya cancara ruwan rashin mutunci a daren nan saida yasa ni na gyara ɗakin na goge ko ina da ina yace kuma tunda banda wayau kar in sake zuwa mishi ɗaki , ni kuma abinda ya ɓatamin rai dashi da yace wai me Jiddah tafi ni ne ? Ashe ma kallonta yakeyi , sai kuma abun ci baya waini zanje Nabeela ta koyamin yadda ake tafiya a gaban miji , inje inga yadda suka wayar da Jiddah suka buɗe mata ido , wato ni ban iya komai ba ? Shine abinda ya ƙonamin rai nake zuciya tunda ya tafi har ya dawo kuma ban huce ba.
Fita nayi daga ɗakin ya biyoni yana cewa ko zaki mutu saina faɗa miki gaskiya duk duniya baki da wanda ya isa ya faɗa miki iskan nan mai kaɗawa saini , ko yayi miki daɗi ko yai miki zafi saina faɗa , ke ni har zaki nunamin fushi ? In banda iskanci ni zaki barma ɗaki har inje in dawo yadda na barshi haka zanzo in sameshi , nace kije ma Rabiya gaisuwa shine baki je ba kuma bazaki ba inyi duk abinda zanyi , zama nayi a gefen gadona nidai na rasa abinda yakemin daɗin duk an jagulamin lissafi , wayata na ɗauka ya fizge wayar ya bugata a bango duk ta tarwatse yace ina miki magana zaki latsa waya , nace kije ki koyo zamantakewar aure idan kinji fushi ki koyo saiki zauna lafiya.
Ke in kina da hankali ma har ni zakiyi gaba dani ? Nine nake aurenki ko kece ? Ni zan kiraki a waya ke a dole kinyi fushi , tou ƙarya na faɗa ne ? Ba komai cikin wannan sakaran kan sai wauta da yarinta , idan kinga dama ki shirya zamu fita , yana faɗin haka ya fita abunshi.
Goge hawaye nayi cikin ɓacin rai , duk duniya babu wanda ya cuceni sai Inna , ko waya na kirata ta daina ɗauka , gata a raye Dikko yake iƙirari shine kaɗai zai faɗamin gaskiya , tabbas shine zai faɗamin , zanji fushin na iya zamantakewar zama dashi dan mu zauna lafiyar.....
Ya daɗe sosai sannan ya dawo ɗakina , yasha gayu cikin sigarsu ta "yan gayu , nima nayi wanka na shirya amma daya shigo saida ya gyaramin diresin , yana cewa saura in munje ki saki baki kita surutu ko yawan murmushi , daga ina yini Allah ya jiƙanta kika sake ko kallon wani muka dawo zan kulleki a ɗaki.
Shine a gaba ni nake bayanshi bayan ya gyaramin tafiyata muka fita , 9:32pm a palon Rabiya tayi mana , kafin ta fito saida tasa aka fara tara mana "yan abubuwan taɓawa , Dikko ya nunamin ko ruwa nasha muka koma gida saiya ɓatamin rai , yana tsaye wurin ganin ya siyomin mutunci amma ni bahaguwar kwanya gareni ,
Bayan wani lokaci ta dosa , ƙarar takalminta kakeji a saman tayils ƙwas׳ , ƙamshi yayo gaba ta bayyana a palon sai isa takeyi mijinta na biye da ita , saman kujera mai zaman mutu 3 { 3sieter } suka zauna , mu kuma muna saman 2sieter , gaisawa aka farayi nima na gaisheta tare dayi mata ta'aziyya , ta amsa dai cikin sakin fuska , daga haka ban sake magana ba , sukaci gaba da firarsu , bamu wani daɗe ba muka tafi , kuma Rabiya tace ko ruwa musha Dikko yace an gode , tace tana zuwa kila wani abu zata bayar yace ai zamu dawo ,
A mota ne yake cewa kaje wuri ana marmarinka ka tafi kafin ka fita ran mutane , kin gani dai ko ? Dare ne muka je amma kallarta shirye , tsakanin palo da bedroom sai an saka takalmi masu kyau , kana doso miji yasan ka taho , amma ke duk babu wannan takalmin ma "yan maraɗi kike yawo dasu babu wani notice saidai kawai mutum ya ganki , har muka isa gidan gwamnati Dikko faɗa yakemin , kuma saura idan munje canma inyi surutu ko inci wani abu Jiddah tana nan idan ta barbaɗeni ba abinda ya dameshi ,
Daga gidan Rabiya har gidansu babu abinda na kalla kar yacemin na cika ƙauyanci , a kame nake dan nima ba sakara bace ba , amma a raina inajin daɗi , tunda Dikko yayi parking su Nabeela suka yo waje har Papi shima baiyi bacci , duk sannu sukayi mana , Papi kuma ya tafi wurin Dikko yana oyoyo , hannunshi ya kama sukayi gaba Papi yana bashi labari shidai baya gane yarenshi.
Wata irin mummunar faɗuwar gaba naji lokacin da idona ya sauka akan Momy , kai uwar Dikko "yar gayu ce , ta haɗu ׳ , Allah yayi mata kyau sai kuma ya haɗu da hutu uwa uba kuma gayu , kamar yadda Dikko yayi nima a ƙasa na zauna jiki a sanyaye sai mulki Momy ke zubawa , kai Momy tayi wallahi ta haɗu "yar gaye ce first class kuma ko a ajin ma itace ta gaban benci , bayan sun gama gaisawa da Dikko nima na gaisheta , saida ta mula tasha iska bayan ta gama kalleni tas sannan tace lafiya qalau , ƙannenshi suka shigo wanda muke karatu dasu makaranta ɗaya , wai me yasa kwana biyu banje sch ba ? Saida na kalli Dikko sannan nace musu ba komai , su jina suke kamar wata ƙawarsu dan haka sukace inzo muje ɗakinsu suma ,
Momy tace bazata je ku koya mata kilbibi ba , Dikko yace Momy ki barta suje , kasan yaran gidan nan munafukai ne basu aje komai ba sai kilbibi da gulma idan suka ɓata maka mata da tsigudidi ka huta , Nabeela tace matar Yaya zo kiji , ta leƙo daga ciki tana kirana , kallon Dikko nayi , da girarshi ya nunamin inje wurin Nabeela , tare da sauran masu cewa naje ɗakinsu duk muka runguɗa ciki , muna shiga suka ciremin kallabi suna ganin gashina , Nabeela ta ɗauko abin taje kai ta fara tsigarmin kai , wai ince ma Yaya zan kwana , nidai banyi magana ba , sune sukayi ta surutu nima ina so ince wani abu amma Dikko ya hanani magana dole nayi shiru , Jiddah kuwa yanzu ta shigo ta fara masifa wai anzo ana ciccira musu datti a gado , ganin babu wanda yabi ta kanta ta koma palo ta faɗawa Momy amma sai Momy tace idan mun gama an gyara ,
Nan Dikko ya barni yace zaije ya dawo , Momy ma ciki ta dawo bayan fitar Dikko , kuma bata wani ji ƙanƙamina ba , ganin Dikko ya tafi yasa ta kora duk wanda ba itace ta haifesu ba , tana satar kallona lokaci² irin kallon nan na gefen ido , itace ma tayi ma Nabeela faɗa ta rufemin kaina saboda dare , shine Nabeelar tace muje ɗakinta , Momy tace bazanje ba ,
Har 11:46pm Dikko bai dawo ba , ni kuma na gaji ni bana san irin kallon da Momy kemin kila kuma karatu na takeyi , kallon Nabeela nayi tare da riƙe hannunta nace nidai muje ɗakinki , Momy tace muyi zamanmu , sai kuma take tambayata bayan gidan Rabiya sai ina Dikko ya kaini , nace sai nan , zai kaini gidan Yayarshi wacce yake bi itama inje in mata ta'aziyya nace to , wai kuma duk abinda akayi in riƙa zuwa idan ba haka ba babu wanda zai sanni nace tou ,
Sai 1 saura Dikko ya dawo kuma Nabeela tace masa in kwana yace a , a , itace ta anshi Papi ni kuma muka wuce gida , tun daga wannan ranar ina zuwa gidansu Dikko amma tare dashi , idan kuma anyi wani abu biki ko suna Nabeela take zuwa ta tafi dani ko Dikko baya gari , basa dai min wani gani² ko habaici , amma Jiddah idan muka haɗu sai tacemin ga irin asiri wai na mallake dangi miji , bana tanka mata tunda dai Dikko ya gargaɗeni da baya san inje in zama ɗaya dasu na riƙa kama kaina banda yawan surutu banda yawan dariya , ba ruwana da sabgar kowa , kuma kar in kuskura na riƙa shiga sabgar Jiddah.
Shigata cikin familynsu Dikko yasa na gane banbanci tsakanin "yan geto area da boti sayit , na gane matsayin wanka kuma na gane shima kanshi wankan iri² ne , na gane matsayin gayu kuma nasan nawa gayun an daina yayin irinshi , na zubar da gayun rayuwar baya dan na ɗauki sabon darasin wanka a wurin wayayyin mata , lokaci guda kaina ya fara hayaƙi nima na fara fizge² , idona ya fara wayewa , akwai banbanci tsakanin wayewar talauci arziƙi da kuma rayuwar lingu , ko a karuwanci ashe iri² ne nawa da nayi a baya wahalallen karuwanci ne , Nabeela tana taimako na tana shiga dani wuraren da tunda nake ma bansan akwai su a cikin garin Katsina ba sai su masu kuɗi , kai talaka ya rayuwar haƙuri ? Talaka bawa alere dangin jakki ka mutu gobe a sake sabo , da nasan zanzo irin wannan rayuwa da ban ɓatawa kaina lokaci ba wurin shirmen da nayi a baya , wanda bai haifa min komai ba sai ɓacin suna , karuwancin wahala ya bugamin tambari mara goguwa , kai kuɗi na inda suke gayu wayewa da buɗewar ido na gidan gwamnati , idan taƙamarki wanka sai kin gama wankuwa har kin gaji , idan kika tunkari ahalin Dikko sai kin raina kanki ,
Nidai ban sani ba , shin Dikko yayi magana da "yan gidansu dan su ɗago rayuwata ko kuwa sune suka ga ya kamata su wayar dani oho musu , nidai dama can gaskiya bawai wata kidahuma bace ba saidai kunsan wayewar kuɗi da talauci ba iri ɗaya bane ba , kawai dai ciwona rashin ganewa a boko shine ciwo na tou yanzu ina ganewa kuma na iya , rabon da muyi faɗa da Dikko harna manta , shidai burinshi ya samu natsuwa cikin kulawa da soyayya kuma kullum nazo masa da baƙon salo , na jiya ba irin na yau ba , na yanzu daban na anjima ma yazo a baƙo , kuma karna gajiya da sauri shine dalilin yasa yake bani magunguna dan na ɗauki buƙatarshi har ya samu gamsuwa ba tare dana gaji ba , na zama jajirtacciya mai juriya a fagen tsakiyar filin wasan danbe , sai kuma biyayya shi mutum ne mai san ka bashi girma , yana san girma sosai kuma yana so ka girmamashi , saboda san girmanshi yasa Rabiya ke zaulayarshi cewa saida tayi aure ma yazo duniya , kuma shi mutum ne mai san godiya , yana san godiya akan duk abinda yayi maka , sannu da zuwa idan ya dawo cikin soyayya rakiya idan zai fita da addu'ar Allah ya dafa mishi akan duk abinda yasa gaba na alkairi , yawan damuwa da rayuwarshi ta hanyar yi masa waya idan baya nan , sai kuma idan yana gari bana zuwa ko ina sai makaranta shikenan matsalarshi.
Inna kuwa har yanzu babu ruwanta dani , ko gidanta mukaje dani da Dikko haka zata watsar damu sai mun gaji da zama mu tafi , dan dama Dikko shi komai rayuwarshi na dare ne yakeyi kamar mara gaskiya , shi yasa ko gidan Innar sai dare muke zuwa.
Ita dai yanzu Momy bata da sauran ja tunda tayi karatu na kuma ta fahimci rayuwata , kawai dai tayi ma Dikko addu'ar mu zauna lafiya , ɗiyar ƙawarta kuma da taso ta aurawa Dikko ashe itace karuwar bata sani ba , can wata ƙawarta ta faɗa mata yarinyar nan da take nemawa Dikko fa batajin magana har ciki aka zubar mata kwanan nan , sai ta zauna tayi karatun ta natsu tare dayi ma Dikko addu'ar su zauna lafiya da Sultana , sai kuma tayi hangen idan Sultana ta tafi bata san wace surukar zatayi ba , shine suke lallaɓa Sultana a jone , a taƙaice dai kawai ta gane idan bata share masallaci ba aradu kasuwa zata share hada mofin ,
Amma duk da haka nan dai yana nunamin nesa² dai , danshi yasan "yan gidansu yanzu sukeyin ka anjima su sauke ka ƙasa , Dikko dai yana tsaye kullum yana ta kwatanci yana ɗorani hanya , idan yaga na lauye nan zai ɗagoni ba faɗa ba ɗaga murya , zaice wannan da kikayi ba haka akeyi ba , haka zakiyi , zama dai nayau da gobe idan kuma yayi min wani abu nayi fushi , zaicemin ba'ayin fushi da miji kuma ko nayi miki abu ya ɓata miki rai ki riƙa haƙuri ba komai ne zakiyi fushi akanshi ba , rayuwa juyawa takeyi ba kullum akeyin farin ciki ba , kuma shima kanshi ba kullum zan sameshi yanajin haƙuri ba idan na hawoshi yana ɓacin rai ba abinda ya dameshi kawai zai zaneni ne kuma inyi masa godiya idan ya gama , wannan shine ake cema yau da gobe...
Ina shiga ahalin Inna sosai , duk abinda akayi ina zuwa , idan Dikko yana nan Ashiru ke kaini , idan basa nan ni zanje da kaina , idan yana Katsina da abokinshi Abbakar suke fita ni kuma a barni da Ashiru , idan kuma zai bar gari tare suke tafiya gaba ɗayansu , masu gadi da sauran masu hidimar gida ake bari , dan yanzu Dikko baida lokacin kaini wani wuri kuma ko yana gari nima kaina wahalar gani yakemin suna can wurin siyasarsu zaɓe yazo sunƙi haƙura su fita wasu su shiga , itama Momy bata zama suna can basa nan basa can hada Jiddah ake zuwa , niko banma ga fuska ba bare ince ko so ɗaya naje naga yadda akeyi , hmmmm Dikko ? ׳ halinshi saishi.
Gidan Sultan ma duk abinda akayi ina zuwa , amma ni Dikko baya bari na zama wuri , mintuna 15 shine nawa idan na fita , idan yaji dani 25 ne , makaranta kaɗai nake zuwa na daɗe , nidai bansan dalilinshi na wannan tsarin ba , ko gidan Inna idan naje shima haka ne , ni idan tana gari ina zuwa dan wallahi shi yanzu ya daina zuwa gidan kwata² , haka zamuje yaita gaisheta tanaji tana kallonmu tai mana banza , shi kuma tsakani da Allah ya bita² harya gaji idan kuma zamu tafi taita zagin Dikko tana aibatashi , shi yasa ya daina zuwa , tun kana da mutunci a idon siriki yana jin nauhinka har kazo kayi abinda zaka fita ranshi haba ina ma amfani da Allah..............?
Sati biyu rabon da nasashi idona sai yau a asibiti , yazo ganin Kaka nima Ashiru ya kawoni muka haɗe , kuma shine ya iskeni , yana shigowa nasa takalmina nayi gaba ina jirashi waje , koda ya gama abinda yakeyi bansan ta ina aka ɗaukeshi ba kawai ya ɓacemin saida na ga an hau motoci babu shi , na koma ko an barshi ban ganshi ba , nima sallama nayi musu na wuce gida raina ɓace , kuma shi ba waya yakeyi ba saida ya turo text.
Duk yadda na kasa na tsare a ranar ban ganshi a gida ba , washe garin ranar ma baya nan , wata washe garin sai naji shi kawai ya halba Abuja bansan abinda yajeyi ba , kwanashi biyu ya dawo , ina makaranta ya dawo kafin in dawo harya bar gidan , naji babu daɗi dan haka na zauna na zuƙa mishi zuƙeƙen text nace kana can kana yawon kamfen ka manta da yankin iyalinka , waini waye ya faɗamin shi yawon kamfen yakeyi ? To nidai koma me kakeyi ina san ganinka , gani nan zuwa......... !
22/12/2019 👇🏻
*JAMILA MUSA...* 💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 90
Bayan na gama dubawa ajiye wayar nayi na nufi madafar abinci dan samawa cikina abinda zan bashi , ko uniform ina ban cire ba yunwa nakeji sosai kamar zan faɗi , Dikko kuwa bai wani daɗe ba yazo , kicin ya sameni wai gashi yazo ta ina zai fara kamfen in a yankin iyalin tashi , yayi maganar yana murmushi , dariya nayi sannan nace kaima sai kawai ka kama kayi wani tafiyar ka abunka , gaba ɗaya ka wani manta dani na ƙarasa maganar ina shiga jikinshi ,
Dariya yayi cikin izza ya riƙe ƙuguna yace yi haƙuri An mata , naƙi inyi haƙurin , nine zahiri bakiyi ba tunda har kin faɗamin magana , wai na manta da yankin iyalina banyi kamfen ba , dariya kika bani nace tou ? 🤔 bari in rugo kar aƙi bani ƙuri'a ranar zaɓe , wannan "yar yarinya har tayi ƙorafi gaskiya Dikko bai kyauta ba. Ey mana inata jin babu daɗi na zama kamar wata marainiya dubeni da Allah duk na wani zama abin tausayi , na ƙarasa maganar a shagwaɓe ina kallon idonshi da yanayin kallon da yake so , murmushi yayi tare da lumshe idanuwanshi yace An mata......... Ya ƙarasa maganar yana sumbatar bakina.
Fita nayi daga jikinshi na juya da niyar tafiya inda na ɗora girki , riƙo ƙuguna yayi ta baya yana jawoni jikinshi , ai ƙarya kikeyi bayan nazo kamfen , da Allah ka ƙyaleni yunwa nakeji , taɓe baki yayi tare da ɗaga gira yace , tou ? Ya faɗa cikin yanayin mamaki sannan yace , idan nayi tafiyata karki sake kirana kice inzo kamfen , tou ka tafi mana sai me.... ? Juyawa yayi yaɗanyi tafiya , inajin ƙarar takalmin shi , na juyo a dabarance naga shin da gaske tafiyar zaiyi , ina juyowa muka haɗa ido , dariya yayi tare da cewa yes 💪🏻 , da baki juyo ba dana tsaya amma kinga tafiyata , da za'aimin yanga a wani latsani sai Allah ya kamaki nima saina rama , yana faɗin haka ya fita daga kicin in da sauri , kashe gas in nayi na bishi nima da sauri , ɗakinshi ya wuce yana dariyar mugunta.
Lokacin dana shiga harya cire agogon hannunshi , da farin ciki ya rumgumeni wai oyoyo An mata , ya faɗa yana tsuke bakinshi tare da lumshe idanuwanshi yana ɗan kaɗa kanshi cikin yanayin shauƙin so , ya riƙeni sosai a jikinshi , murmushi yayi mai sauti ya sake maimaita wai kana can kana yawon kamfen ka manta da yankin iyalinka , kai An mata , tou ya akeyin kamfen a yankin iyali ya ƙarasa maganar yana haɗa idanuwanmu wuri ɗaya kowa yana kallon kowa , bayan wani lokaci yace caf aiko lallai nan ne ya kamata inyi kamfen muje a gama abincin inci nima in ƙara tsatsubo ƙarfina.
Bayan mun koma ya zauna a saman matakalar da zaka shiga kicin yana yanka albarsa , da yaji azabar yaji yace kai ban iyawa anshi harna yanke , kawo dai in miki wani abun wannan wahala ji naji ciwo yana nunamin inda ya yanke tare da goge idonshi yace wai wahala , nidai albasar zaka yankamin , ke ban iyawa kinji , nima ban iyawa saidai a dafa abincin ba albarsa , ai yama fi daɗi yi sauri ki gama.
Ciki ya shiga yana wanke hannunshi wayashi ta fara ringing , ni yasa na ciro mishi ita daga aljihu , dana faɗa masa Momy ce da sauri ya anshi wayar tare dayin sallama , bansan abinda Momy tace masa ba saidai yanayin idonshi ya canza zuwa launin ja , ya tsareni da kallo har naji tsoro ya kamani , gani nan zuwa ya faɗa tare da fita daga kicin in cikin tsananin ɓacin rai , ajiyar zuciya na sauke tare da cewa Allah ya tsare hanya , bai ansa ba ni kuma naci gaba da abinda ya shafeni.
Hankalin kaf "yan ɗakinsu Dikko idan yayi dubu ya tashi har Momy gaba ɗayansu sun hallara a bedroom inta sai koke² sukeyi , wai Jiddah ta bawa Perpy fiya² a lemu , Dikko yayi tashin hankali shi ba kanshi yakeji ba An mata yake tausayi , yasan zata shiga damuwa duk da tana nuna kawaici da kara akan yaron amma ai tana san ɗanta kodan bata fito ta faɗa ba ? Yarinya mai kunya da kawaici waye ma zaiyi irin haƙurin da An mata tayi ? Idan da wata mara kunya ce aka ɗauki ɗanta ba uwar miji ba ko uwar waye sai anyi tashin hankali , Allah kaɗai yasan ciwon da takeji akan rashin Papi baya kusa da ita , amma bata taɓa faɗa ba bata kuma taɓa nunawa ba , koshi bata taɓa nuna mishi ba daɗi ba akan rashin Papi , ta daiyi haƙuri tabar ma ranta , kuma babu wanda yasan ina ma Jiddahr tayi , Dikko kuwa cewa yayi shi baiga ma duk dalilin wannan fitinar da tashin hankalin da yasa aka ɗauko Papi ba , mema yasa tun farko aka ɗauko yaron daga wurin An mata , shi ina zaisa ranshi ? Wane hali rayuwar Sultana zata shiga ? Gaskiya fa ba'ayi ma rayuwarta adalci ba , me yasa ׳.............. ? Wallahi idan har Papi ya mutu saiya kashe Jiddah , sannan shima ya kashe kanshi dan wallahi yana jin kunyar An mata.
Shima Dady cikin tashin hankali ya iso , ganin Dikko yana kuka yasa Dady shiga wani irin mawuyanci hali , yace Babana yi haƙuri ka daina kuka , a shagwaɓe Dikko yace kuka Dady ? Ai yanzu ma na fara , yi haƙuri Babana zai samu sauƙi bazai mutu ba , ya faɗa yana kallon idon Dikko cikin yanayin shi Dikko ya tausaya mishi , Dikko yace haba Dady misali nine a irin wannan yanayi nayi imani kai da suma zakayi , yadda kakejin ni nine zuciyarka ya nuna kanshi , sannan yaci gaba da cewa nima uwarshi itace zuciyata , idan har yaron nan ya mutu , An mata ɗan ƙaramin hauka zatayi , wane irin hali kake tunanin zan shiga idan ta shiga wani hali ? Idan na shiga wani hali kaima shiga zakayi , kana shiga Momy ta shiga , Momy na shiga kaf "ya "yanta sun shiga , na rantse da girman Allah idan yaron nan ya mutu tou tabbas nima mutuwa zanyi dan bazan yadda inga tashin hankalin da An mata zata shiga ba , saina hau saman bene zanyo ƙundubala kuma nima saina sha fiya²n in faɗo matacce........ Yana faɗin haka ya fita yabar ɗakin.
Cikin damuwa Dady yake kiran Dikko , Babana² , amma Dikko yai tafiyarshi , hankalinshi kuma ya tafi wurin Sultana da tace masa yana can yana yawon kamfen ya manta da yankin iyalinshi , dole yaje ya bata natsuwa duk haƙurin ta saida ta cire kunyarta ta nemi haƙƙinta wurinshi , itama Jiddah sai yaci uwarta idan ya riƙeta babu wanda ya isa ya tashi hankalin An mata idan dai yana numfashi , ƙaramar yarinya mai haƙuri , ai haƙurin An mata yayi haƙuri ko sai an kasheta ne wai............?
Cikin wani irin ɓacin rai mai tsananin ɓaci ya dawo , ni bana san ganinshi a yanayin fushi tsoro yake bani wallahi , tunda na gama abincin banci ba naje nayi wanka ina zaune ina zaman jiran dawowarshi , sannu da zuwa nayi mishi bai amsa ba , saida yazo dai² inda nake zaune yaja hannu na har zuwa ɗakinshi kuma baiyi magana ba.
Dakel ya rufe ƙofa sannan yazo inda nake tsaye ya fara cire kayan jikina , kallonshi nayi cikin damuwa nace baka da lafiya ne ? Baimin magana ba yaci gaba , saida ya saukeni duka sannan ya jani zuwa bakin gado , da hannu ya turani na faɗa sama ina kallonshi , bargo na ɗauka na rufe jikina tare da saukowa ina matsawa inda kayana suke nace masa ka barshi kawai ngode , yaye bargon yayi tare da maidani saman gadon , ban sake saukowa ba , a damuwance shima ya hau gadon , har yayi abinda zaiyi ya gama baiyi magana ba kuma bai wani nuna yanajin shauƙi ko farin cikin kasancewa dani ba , kuma duk fushin da yakeyi bai hanashi maidai nushi ba , ya maida duka sosai , saida ya tabbatar na samu natsuwa kuma ya bani natsuwar da farin ciki da ƙoƙari ba wani lalaci , saida ya tabbatar nakai sosai sannan ya barni , ya rigani yin wanka , yana fitowa ya shirya , godiya nayi masa tare da masa addu'ar Allah ya ƙara mishi lafiya kuma ya bashi wata lafiyar a fagen wasan danbe , yayi nisan kwana mai albarka , baiyi magana ba ya shirya ya fita daga ɗakin amma duk wayoyinshi a nan ya barsu kila ba fita zaiyi ba.
Bayan ya fita nima na gyara jikina na fito , palon ɗakinshi na sameshi zaune saman kujera ya kwantar da kanshi saman hannun kujera , ina fitowa ya fara faɗa wai ba ya hanani wannan ƙazantar ba ? Kodai in rabo kayana ɗakinshi da nawa , yana nufin in ibo wasu in ajiye a ɗakinshi , ko kuma duk lokacin da zanzo in riƙa tahowa da wasu kayan , daga yau bazai sake min magana akan idan na cire kaya na daina maidasu ba saidai zai zanemin jiki tunda kunnen ƙashi nake da , murmushi nayi ba tare da nace masa komai ba , nasan kila wani ya ɓata mishi rai yana neman hanyar da zai dakeni ne danya huce shi yasa yake nemen ya tsakuloni faɗa tunda banda haƙuri in masa rashin kunya ya zaneni yai tafiyarshi , dole kimin dariya tunda kin raina ni , haba niɗin banza ? Ni na isa in raina ka tunda nasan amfaninka ina faɗin haka nayi waje.....
Cike da tausayi yabi bayan Sultana da kallo , wata zuciyar tace masa kodai ya faɗawa An mata abinda ya faru , yayin da wata zuciyar ta gargaɗeshi akan ya barta kawai tayi farin ciki , idan kuwa ba haka ba yau bata iya bacci kuka zatai tayi mishi kuma yace zai daketa , ya ƙyaleta Allah dai ya bawa Papi lafiya kawai ya ɗauko mata ɗanta , ashe shi yana ta hasashen Jiddah zata barbaɗe An mata ashe tunaninta ya karkata ne akan ɗanta , hmmm Allah ya kauda ɓacin rana , dan ya ɗaukar ma kanshi idan har Perpy ya mutu wallahi saiya kashe Jiddah ,
Dady kuwa ya kira Dikko baisan adadi ba amma Dikko yayi fushi bai ɗauki wayar ba , Momy ma ta kirashi itama har ta gode Allah amma sam Dikko yanaji kuma yana gani amma ya basar da kiransu , Dady kuwa yayi ma Momy fata² yace bata da lissafi kwata² in banda hauka da rashin tunani irin na mata , yace yarinyar da uwarta ta kashe auren "yarta da ɗanta akan wani dalili banza can nasu na mata , kuma "yar ta fita da ciki taje ta zubar da cikin kuma ta kirata ta faɗa mata dan taga iyakarta , duk abinda sukayi hakan baisa ta gane inda duniya ta nufa ba taje ta sake jajibo Jiddah ta kawo cikin zuri'arta , dama ita Momyn Jiddah ta zubawa fiya²r ta mutu kowa ya huta , ya ƙara da cewa kuma idan har Papi wani abu ya sameshi ba abinda ya dameshi da yadda zuminchin su yake saiya ɗaure Jiddah daga ita har uwarta. Momy zatayi magana Dady yace ta rufe mishi baki , ba abinda zata faɗa mishi , batayi ma Mom Papi adalci ba , ko albarkacin yadda Babanshi ya jefo yarinyar mutane daga sama kuma ta dawo daga duniyar ƙanwar mutuwa a hakan bata rabu da Babanshi ba ta haƙura ta zauna dashi , idan bata sani ba Babanshi dukan yarinyar nan yakeyi wahalarshi takesha kamar tashin hankali amma ahakan tayi haƙuri ta zauna dashi bata taɓa guduwa ta barshi ba ,
Cike da nadama Momy tace taya zai daketa ne ? Dady yace da kanshi ya faɗamin ko nasan sunyi ne ? Yaje ya ɗauko amanar yarinyar mutane yazo ya kulle yarinya a gida yana ta gana mata azaba , nayi imani da Jiddahr ce tuni saita faɗa kuma sai anyi tashin hankali , ita kuwa ya doketa ya zageta duk haukarshi idan ya tasoshi akanta yake sauke masifarshi , ko wani ya ɓata mishi rai saiya je ya juye akanta ko ita jakace ne ? Ita iyayenta basa santa ? Ko ita ba haifarta akayi ba ? Amma duk wannan baiyi ba da masifa saida sukaje suka fitar mata da ciki tun farko ya nuna Rabiya , yace duk da haka tayi haƙuri kullum tana liƙe dashi haba baki da adalci , da kece akayi ma wani daga cikin "ya "yan naki ko aka taɓoki a gidan nan haka zaki ƙurmusashi a ɗaki ki haukatoshi ya fita yaita hauka yana saiya kashe² , baƙin halinki yasa aka birkita miki tunanin ɗa , baya auren karuwa , ita karuwa ce ki kiyayi kanki da duniya , da hannunshi ya nuna yace duk sirrin dake rufe ki kiyayi buɗeshi idan kuwa ba haka ba wata rana sai kunya ya hanaki fita , mtswww ya fita daga ɗakin.....
Dikko nidai banajin daɗi , ba tare daya kalleni ba yace An mata me ya sameki ne ? Ya tambaya a sakatance , kallonshi nayi tare da cewa cikina ne ke ciwo na faɗa ina kwanciya jikinshi , yana burgeni idan yayi magana da shagwaɓe ko sakata irin nasu na "ya "yan "yan gayu , sannan yayi murmushi dakel yace to ko sai na ƙara kamfen in ne ? Yayi maganar yana riƙeni da riƙon da nake so , ƙara lafewa nayi sosai a jikinshi , gyara kwanciyarshi yayi tare da ɗagoni daga saman gadon ya ɗora rabin jikina a jikinshi yace ta ina kikejin ciwon ne ? Ya ƙarasa maganar yana laluba cikina da lallausan hannunshi , agogo ya kalla da sauri ya saukeni daga jikinshi yace Dady yayi maganar yana sauka daga saman gadon jikinshi yana ƙyarma , lafiya yazo gidan nan ? Yayi maganar cikin tashin hankali , a zuciyarshi yace na shiga3 kardai Papi ya mutu Dady ya taho , da sauri yasa talkaminshi ya fita ,
Sauka nayi daga saman gadon na fita palonshi ta jikin window na tsaya tare da yaye labulaye , a dai² lokacin da naga Dikko ya isa wurin Dady da gudu ya riƙeshi yana magana , wurin da nisa sosai banajin abinda yake ce masa , amma shi Dikko yanayin maganar da yanayin fushi yana nuna kanshi sai kuma ya nuno bayanshi , da hannu Dadyn ya nuna mishi yayi haƙuri yana shafa kanshi , girgije hannun Dady yayi daga saman kanshin da yake taɓawa ya juyo cikin fushi , riƙoshi Dady yayi ya rumgumeshi yana magana cikin yanayin lallashi , shima Dikkon riƙe Dady yayi ya rufe idanuwanshi yana ci gaba da magana , bansan yadda akayi ba naga Dikko da Dady sun shiga mota sun fita daga gidan , Ashiru da Abbakar kuma sun fita a motar Dikko sunbi bayansu , tsoki nayi tare da cewa wannan siyasar banza Allah ya raba Dikko da ita......
Yau bai kwana gida ba , kuma washe gari bai dawo ba sai 11:30 na dare , ko makaranta yau ni naje da kaina ba Ashiru ya kaini ba , kuma daya dawo gidan baifi mintuna 5 ba ya fita , dan naji shigowarshi amma kafin in fito harya fita ban samu haɗuwa dashi ba , saida yayi kwana biyar baya gida kuma yana Katsina , ranar daya dawo , dashi da Papi dasu Nabeela suka sauka gidan , palo na samesu su dukansu "yan uwanshi manyansu da yaransu , Papi sai kuka yakeyi yana kiran Momy , Dikko kuma yana kwance saman kujera 3siater da yanayin damuwa , Rabiya tana zaune saman hannun kujera sai cewa takeyi yayi haƙuri , kai gaskiya bazan gaji da faɗa ba , "yan uwan Dikko wayayyin matana ne , "yan gayun billahillazi , ibar ƙarshen ƙarni , gogaggi masu ilimi da buɗewar ido , duk iya gogewarki idan kika tun karesu wallahi sai kin kama kanki dakarun mata ne da zamani kebinsu , sannu nayi musu nima na samu wuri kusa da Nabeela na zauna ina kallon Dikko , kaɗan ya buɗe bakinshi yaja iska ta ciki da yanayin da idan muna cikin wani yanayi dani dashi , murmushi nayi tare da sauke kaina ƙasa , shima murmushin yayi tare da cewa An mata ga ɗakinki nan yana kiranki , da gudu Papi yayi wurin Rabiya yana ci gaba da kiran Momy ya maƙale ƙafaɗarshi ya riƙeta ya juyo yana kallona.
Jawoshi Dikko yayi gabanshi yace kai sa idonka nan , kallonshi Papi yayi yana kuka , nan ne gidanku ɗan ƙwaƙwar tsiya kana can kana ƙwaƙwa za'a kashe ka bari inji ka sakemin kuka kaga yadda zanci maka , dariya akayi gaba ɗaya , duk suna kallon Dikko da Papi , ƙara ɓata fuska da baki Papi yayi saida yayi ajiyar zuciya yace Momy , Dikko yace ga Momy can ya nunoni tare da cewa kai fashin iyaye kakeyi ne ? Ajiyar zuciya ya sake saukewa a karo na biyu yana kallon Dikko , murmushi Dikko yayi cewa zaka hau doki ? Ya ƙarasa tambayar da girarshi , kai ya ɗaga alamar zai hau , waya Dikko ya ɗauka ya fara kiran Umar , bayan ya ɗauka yace a kawo doki Papi ya dawo gida , yana faɗin haka ya tsinke kiran yace je ka wurin Momy itace zata ɗoraka a doki , wurina ya taho yana ajiyar zuciya , amma da yazo saiya tsaya wurin Nabeela yana kallona ,
Dikko yace kace mata ka daina kuka zaka hau doki , cikin shaƙaƙƙiyar murya ya faɗa yana kallon cikin idanuwana , dan kauda kaina nayi cikin yanayin jin kunya , dariya Dikko yayi tare da cewa Papi riƙeta idan baka riƙeta ba bazata ɗoraka ba tace , da sauri na tashi , dariya Dikko yayi sosai yace ku kalli fulani da kawaici , yau ni ga ɗan farko gaban An mata , kam aiko yau saina ɓanɓare miki kunya tashi yayi ya ɗauki Papi suka biyoni ɗaki ,
A kona ya sani ya sauke Papi ya riƙe hannunshi yana daga ta bayanshi , cikin kwantacciyar murya yace riƙeni ya faɗa yana min kallon ƙauna , riƙeshi nayi cike da soyayya , yace sumbaceni ya nunamin saman bakinshi da ɗan yatsa kuma bai daina kallona ba , matsawa nayi na sumbaci bakinshi , da hannun ya riƙo ƙeyata ya haɗe bakuna wuri ɗaya yana sauke ajiyar zuciya cikin ƙaramin sauti mai tada hankali , bakinshi a cikin bakina yace ke Papin ne baki ɗauka ? Ni bana san wannan kunyar gaskiya so kikeyi yazo bai saba dake ba kullum yana kiran Momy ? Haba An mata nidai bamu iya irin wannan abun ba kinji ? Kija ɗakin a jiki idan Umar yazo da doki ki ɗorashi da kanki , yana san doki sosai , kuma zan bar muku doki ɗaya anan zaki ga ya liƙema gidan nan bazai wani sake tunanin gidanmu ba , kiyi wasa da ɗanki kija shi jikinki idan kina wannan kunyar haka zasuyi ta ibe miki "ya "ya suna tafiya dasu su kuma zasu saba da can ke kuma ko oho , idan kika bar "ya "yanki sake haka za'ayita labbatarki ana kakkashe miki su , ki koya ma "ya "yanki tsoron mutane , banda Allah yasa Papi yana da sauran rayuwa yanzu da an kashe miki ɗa , kuma ai nasan zakiyi kuka ko ? Ya ƙarasa maganar yana ci gaba da tsotsar bakina cikin wani irin bahaggon yanayi , mutsurniya na fara ya girgaza kanshi alamar in bari , kuma in bashi harshe na , riƙe harshen yayi tare dayin murmushi mai sauti yana kallon idona cike da tsantsar ƙauna , gaba ɗaya jikina mutuwa yayi na kasa wani ƙwaƙwƙwaran motsi , da ɗayan hannunshi ya kamo hannuna ya ɗoramin inda yake so na riƙe mishi kanshi , nice na ajiye ɗayan da irin yadda yake so ya kasance , dan nima zuwa wannan lokacin na fara zama "yar hannu , ina riƙeshi kukan Papi ya fara fitowa , sakeni yayi tare da jana ya kwantar dani gefen gado dan yasan bazan iya tsayuwa ba , dan cewa yayi wai da an taɓani sai kawai in wani mutu murus , shi wannan abun yana mishi baƙin ciki ragguwa da ni , fita yayi daga ɗakin dashi da Papi.....
Har dare duk basu tafi ba , nima ban sake fita ba , koda Umar yazo da doki shine ya ɗora Papi , abinci ma Momy ce ta bada aka kawo musu , bayan abinci yazo Nabeela tazo ta kirani muci abinci , gaba ɗayansu sun hallara a saman tebirin cin abinci nima kujera naja na zauna , mai bin Rabiya take ba Dikko labarin yadda suka ƙare da mijinta da zaiyi aure , bansan farkon labarin ba , amma tunda naga Dikko yana gaggaɓa dariya nasan cuta akayi , jakarta ta buɗe ta fiddo irin maganin da Dikko ke bani , ƙara ƙyalƙalewa yayi dariya yace nafa yadda basai na gani ba , mata ? Mata ? Hmmm , Rabiya tace ai raina ta ma yayi ni tayama namiji zai fara hasashen ƙara aure bare ya fara tunkarar matan , dariya Dikko yayi tare da riƙe kanshi da hannun haggunshi yaci gaba da cin abinci kanshi yana kallon filet in da yake cin abinci , Nabeela tace ai wallahi ba wanda ya isa ya auramin tsoho tayi maganar tana fashewa da kuka , Rabiya tace banza karki ma kanki baƙin baki wannan jakar matar tashi ba a bakin komai take ba wurinshi , koma komai ce ke a wurinki mayinos ce , cikin kuka tace ni sai kace nice kaɗai ɗiya a gidan ? Dikko yace tou auren tsoho miye kuma ? Yayi maganar yana ɗaure fuska , yace ko dan anyi magana a gabanki zaki mana rashin kunya , cikin kuka tace Yaya amma waye aka haɗa da tsoho ? Saini ? Rabiya tace ai tsohon yafi saukin shigarwar lungu , ga matarshi wata tutar ƙasa ce , ke har akwai macen da zata tayar miki da hankali ? Dikko yace ƙyale sakara , Nabeela tace nifa banajin matarshi kawai dai yamin tsufa ne , Dikko yace to zani ne shi da zaki ce ya miki tsufa wurin ɗaurashi ? Ko zani ne shi ai abun iyawa ne ma , idan ya miki tsufa ai kinsan irin wanka ke da zaki ɗauka iya wankuwarki iya adadin yadda tsufan zai ɓoye a jikin tsuhuwar sitirar da kika saka , kinga tunda ya haɗu dake basai ki rage mishi tsufan ba ? Nuna Rabiya yayi tare da cewa ai kamar Hajjaju ce da atamfar data ɗaura tun ina rakiyar zance take da atamfar nan har yanzu kullum kyau take mata duk tsufarta , dariya akayi gaba ɗaya amma banda ni , Rabiya tace lallai Baban Dady amma wallahi ka rainani da yawa , kai lokacin da nayi zance ma ina kazo duniya ? Ɗaure fuska yayi , gaba ɗaya suka sake ɗaukar dariya , maibin Rabiya tace bar ɗan iska saboda yaga ya ajiye wannan gemun yake raina mutane sai munbi dare mu askeshi , dariya yayi tare da cewa da kuwa kun asko masifa , mai bin Nabeela ta canja firar da cewa mukam dai sai baba gomna muma muna bayan Dady , Nabeela tace idan ya faɗi zaɓen fa ? Kike wani kiran gwamna , mai bin Rabiya tace bama zai faɗi ba sai yaje insha Allah , ah munga su Nabeela as matar gwamna , kwarkwasa kenan ,
Dikko kuwa cewa yayi oh , An mata kin daiji ko ? Wai ita matar ta gidan itace tutar ƙasa , bata miƙe ba kenan tana kwance , jinjina kanshi yayi tare da cewa lallai matan ciki sai sun dage , ai ya kama ace idan mijinki zaiyi aure ita wacce zata shigo ya zamana gabanta na halbawa saboda shakkunki da tsoron kishi dake , amma sai ya zama ita mai shigowar wai itace zata halba zuciyar ta ciki , kina aikin me mace ? Haba mata ? Idan ke tutar ƙasarce kamar yadda kuka faɗar saita shigo gidan dake da mijinki da "ya "yanki tazo ta gigita miki miji , kina can kina haukar banza zakiji karatun yasha banban , idan kuma mara adalci ne saidai ya yarfeki tunda shi ya samu lallausar rayuwa , nidai idan zan ƙara aure nasan amaryar sai taji tsoron An mata , Rabiya tace ƙwarai kuwa ita bama zata yadda ta fara shigowa ba ko Sultana ? Tayi maganar tana kallona , Dikko kuwa cewa yayi ai zanyi auren da wuri ne ,
Gyara zamanshi yayi tare da cewa bara in baku labari , a london na haɗu da wata "yar tasha , tunda ta shigo jirgi kawai tayo wurina ta zauna kusa dani , ɗan yamutsa fuska yayi tare da nuna yadda mata keyi , da irin maganar mata , yaci gaba da cewa aka wani cemin sannu ko ? Ya nuna yadda tayi maganar da yadda ta zauna , yadda yayi abun ne ya ba kowa dariya gaba ɗaya harni saida nayi dariya ina kallon Dikko , wallahi Dikko baijin magana ko kaɗan , shi kuma baiyi dariya ba yaci gaba da cewa da wutsiyar idona na kalli sakarai a zuciyata nace suna can na baro gidanmu , nidai ban mata magana ba , riƙe take yarinya tana da aji sosai gaskiya "yar gayu ce kuma ta iya wanka tana fama da wani irin girman kai , amma duk girman kanta da tazo wurina saida ta saukeshi , nidai banyi mata magana ba kuma ban kalli inda take ba , can bayan wani lokaci sai ga Abbakar yazo , yana zuwa yace DK ya haka kuma ? Shima Abbakar ya kwaikwayi maganarshi , yaci gaba cewa keda ke Katsina idan kin gansu ko kinji maganarsu tou Dikko yasan suna nan daga ita har Abbakar in , Abbakar yace malama da Allah tashi , batayi ma Abbakar magana ba ta juyo wurina tace suna na Yusra , haka nan naji zuciyata ta tashi kamar zanyi amai wallahi , da sauri naci cingom ,
Abbakar kuwa yaci gaba da cewa bara ki tashi a wurin ba ? Wurin zamanta ta nuna mishi da hannu tare da cewa ni ba'amin magana a saman kai , danni maza basa burgeni , saboda hauka irin na Abbakar ƙiƙi² ya kamata da kokowa , yana bara ki tashi a wurin ba ? Naso in musu dariya amma sai nace ya barta , bayan ya saketa ni saina tashi nace shi ya zauna , ina tashi ta taso da yanga sai ƙwarƙwasa take tana yauƙi tafiya cikin tsari da ɗaukar hankali irin tafiyarki Hajjaju ya nuna Rabiya , yace cikin kissa tace haba Yayana ya nuna da salo mai burgewa yana ci gaba da cewa tace yi haƙuri idan na ɓata maka rai , tana maganar tana wani kakkafe ido , ya nuna yadda takeyi , gaba ɗaya aka sakeyin dariya amma yanzu banda ni , Dikko yayi wata irin dariya , yace kamar wani sakarai haka na kalleta , kallona yayi tare da cewa tafa burge , kunga kenan ya ɓadda labarin akan yadda ya ɗaukoshi , ai farkon labarin cewa yayi duk girman kanta da tazo wurinshi saida ta sauke , kuma yace data faɗi sunanta yaji zuciyarshi ta tashi , amma da yaga naji kishi saiya juya labarin kunga kenan ya fasa faɗar yadda labarin yake kenan , bai ci gaba da labarin ba , duk yadda akayi kila Yusra ƙawar Sadiyya matarshi data mutu , irin tafiyar Rabiya da ya faɗa kenan yana so ni na koya kenan.
Cikin fushi na tashi , amma kafin in miƙe ya zaunar dani da ƙarfarshi yana kallona , Rabiya kuma tace , tou ya kukayi ? An mata najin kishi mubar maganar , Rabiya tace haba Sultana ai laifin kine ma fuska kika bashi har yazo gabanki ya samu ikon maganar mace , Dikko yace ai ban shanyu ba shi yasa zanyi ma Perpy wata Momyn.
Canza labarinsu sukayi akan kishiryar Nabeela wai ƙazama ce ba gogewar rayuwa , bata iya komai ba saidai taci ta jibge a wurin , Dikko dai bai sake magana ba ni yake kallo , yanajin yadda ake ta aibata sakarkarin mata , sai ƙara yi ma Nabeela ɗamara ake ana ƙara ɗorata a hanya , bayan wani lokaci kuma sai suka koma labarin kayan mata , tashi Dikko yayi dan har yanzu Umar bai dawo da Papi ba ,
Nima tashi nayi na barsu , ina shiga ɗaki wanka na shiga , lokacin dana fito har sun tafi , sai Nabeela da Papi kaɗai , ina fitowa suka shiga danyi mishi wanka , kafin ta fito na ɗauki kayana nayi ɗakin Dikko , sannu da zuwa yayi min tare da ansar kayan cikin ladabi , yace Allah ya taimakeni kenan ? Ai ina nan nace tou kai Dikko me ya kaika ? Ila marin mace da mangariba , 🤔 ai na ɗauka yau dahuwar kan rago zakimin ? Nayi tunani kila a saman wuta zan kwana dan nayi wannan maganar , nace Dikko yau zakaci ubanka An mata tayi fushi kuma ga Nabeela , Allah dai ya rufamin asiri ashe ina da rabon zanyi farin ciki a daren nan yayi maganar yana zaunar dani gefen gado , yaci gaba da cewa ai ban sani ba "Yar matan nawa ta girma ba.
Kusa dani ya zauna ya rungumoni , sannan ya shiga rattaɓamin kaf abinda ya faru da Papi , naji babu daɗi sosai amma shi saina nuna mishi ai ba komai , yace munafuka ce Jiddar nan , yace lokacin da nayi rashin lafiya , wanda na tafi na barshi kenan , yace tazo ta zauna tayi ta haɗa masifa , kuma itace ta kai Momy ta barota suka ɗauko Papi kila tun lokacin take so ta kashe shi....
Bayan kin tafi kin barni...........
Kai.................... Saina kashe kaina , wallahi saina mutu tunda baki so na mutuwa zanyi , Yazeed kike so ko ? To ni zan mutu in bar mishi ke , buɗe ƙofa nayi na fito , na biyo bayanki amma ban ganki ba , komawa nayi ina ihu , na ɗauki wayar wuta da aka sauke ƙasa na koma ciki , ina shiga na hau sama ina ihu saina kashe kaina , mai gadi ya fara kiransu Ashiru , nasan na ɗaura waya a wuyana bayan na ɗaure ƙarshen a jikin ƙarfen bene nayo ƙasa ,
Daga haka ban sake sanin abinda ya faru ba , Ashiru yacemin da mai gadi yai mishi waya gaba ɗayansu suka zo , hankalin kowa ya tashi gani na zube a ƙasa , kila wayar bai ɗauru ba , ko kuma nayi ma ɗaurin nauhi shi yasa ban tsaya a saman iska na mutu ba , a haka suka sameni , da suka tambayi mai gadi abinda ya faru , yace bai sani ba amma ya ganki kin fita da gudu ni kuma ina kiran Yazeed , Dady suka kira kai tsaye suka sanar dashi cewa Mai gida ya mutu , Dady yana jin haka ya maƙale wurin ya daina aiki kwata² , sune suka sanar da kowa Dikko ya mutu , Dady kuwa daya dawo saidai yace Babana , haka yaita ɗaukewa kamar "yan nepa suna wasa da wuta , tafiyar ƙarshe ce da yayi saida aka kaini government house Dady ya dawo , yayi kuka wanda bana san ina faɗa , saida aka taru Dikko ya mutu , An mata da anyi gaggawa rufeni da an binneni da raina.
Bayan an tabbatar ban mutu ba wanda shima Dady ne ya kafe ban mutu ba , irin sabbatun nan na wanda zafin rashi ya ɗimauta , haka Dady yasa akaita kirayen² likitoci , a ido ni na mutu amma a baɗinance Dikko yana nan , murmushi yayi tare da cewa wai aljannu sun shanye numfashi na , haka aka fita dani waje akayi ta magani daban ciwo daban , jinyar nan da Dady akayita bawan Allah....
Abinda yasa dana samu sauƙi ban wani ji damuwa akanki ba , nasan ina da fushi sosai kuma haka nike da riƙo kuma ina da halin ko oho , duk abinda na bashi baya na gama dashi har abadan duniya wallahi , bansan abinda yasa ni bana iya fushi dake ba , ko nace zanyi zuciya dake bana iyawa , tunda nake a rayuwata ban taɓa gardama wa iyayena saida kika zo rayuwata ,
Labarin mafarkin da kikeyi kaf abinda kika faɗamin saida Mustapa ya faɗawa Ashiru , kuma shine yace wai anyi ma Al ' Ameen lamba su duba kanshi zasu ga aski da lambar mutuwarshi , ni bansan Al ' Ameen yana tsafi ba kwata² , tou tayama zan fara mishi wannan mummunan zaton bayan rayuwar kowa a rufe take , babu wanda yasan sirrin wani sai wanda ya faɗa , Mustapha yasa aka fitar da Al ' Ameen yace wallahi mutuwa zaiyi kuma idan ya mutu hannuna zan tabbata matsafin kamar yadda mutane duniya ke kallona.
Naso naga Al ' Ameen dan naso zanyi magana dashi amma hakan bai yuwu ba , shi Mustaphan yayi ma Ashiru jagoranci zuwa inda sukayi tsafe²nsu , komai Ashiru yayi saida suka gama komai lumfashi na ya dawo , tunda nake ban tabajin irin wannan tashin hankali ba wai an shanyemin nufashi kiji wani masifa , hmmmm , Yazeed kuwa Ashiru yaci ubanshi kuma shine ya maido Abbakar company duk bansan anyi ba ,
Waye shiɗin ? Kawai abokina ne amma abotar ba wani can² ba ya faɗa yana yatsina fuska , tou shi me yasa Ashiru ya ɗaukoshi ne ? Munyi maganar shi da Ashiru anyi ma wata "yar uwarshi fyaɗe harta mutu , da na shiga cikin lamarin Ashiru ya fitar dani , amma ni Mustapha yacemin wai matan Babanku dasa hannunsu a damuwarka , kwanciya yayi tare da kwanto dani jikinshi yace can damuwarsu duk abinda mutum yayi kanshi , idan nayi maganarta nayi imani Dady saiya saketa ni kuma bazanji daɗin haka ba , saboda duk Momy za'a ɗorawa laifi , familyn su Dady haushinta sukeji sosai danma suna shakkun su Rabiya ai da yanzu sunyi waje da ita , ya faɗa yana nunawa da hannunshi , yaci gaba da cewa "yan uwan Dady basujin magana yadda baki tunani amma zaki gani tunda zaki shiga cikinsu , suma dai wayayyi ne amma Momy ta raina ma wayewarsu shi yasa "ya "yanta suka fita daban , tsarinsu ya fita daban idan kun shiga zakiga yadda su Rabiya ke bada haske a taro , gasu da rainin wayau , idan su Rabiya suka raina miki ƙura tom hmmm ya jinjina kanshi , amma duk wani banzar wayewar familyn Dady idan "ya "yan Momy sunzo to kin zama "yar kallo da koyon gyara inda aka tsere miki a wanka , zamani yazo anan zaki gani ki koya ki kuma yi gyara , ni dama bana wani shiga sabgar kowa , tunda bana binsu biki ko suna , iyakata dasu gida , idan basa nan zanji babu daɗi gidan yamin ba daɗi kuma Momy bata da magana , ni kuma faɗan da mukeyi dasu ne nakejin kewarsu idan basa nan , ko wuri zasu zasuce munafiki yau idan muka tafi bazamu dawo da wuri ba , kuma kowa baya rayuwa da "yan wasu ɗakin sai "yan ɗakinsu , haka zan gaji da zama in fita cikin gida bana nan bana can kamar wani maraya tunda ni bana fita waje iyakata gida Dady baya bari naje wani wuri saidai in saci hanya idan baya nan , idan suka dawo zanyi farin ciki , kuma zasu bani labarin duk abinda ya faru idan sunje wuri sun dawo , ni ba abinda ya dameni da rayuwar wani tawa nakeyi , sai "yan uwana mata sune kaɗai abokaina muyi faɗa mu shirya , suma "yan uwan Dady ni babu wani ruwana dasu dan Momy ta koyamin tsoronsu tun ina ƙarami , su kuma suna so na saboda yadda Dady yake ƙaunata dan soyayyar Dady a kaina bai ɓoye ba , amma iyakata da mutum sannu daga nan kawai zan zama kurma , kenan bayaji bare ya bada amsa , idan kuma ba'aci sa'a ba ko kayimin magana sai in maka shiru bazan ma ce maka sannun ba sai in tsare ka da ido ya faɗa yana murmushi , yace sai kiga simi² mutum ya kama gabanshi , kuma ba ƙarya ya faɗa ba , ashe yana sane da duk iskancin da yakeyi , dan aradu idan Dikko ya riƙeka da ido sai kaji babu daɗi har ka kama kanka , tou gashi baida yawan murmushi kuma shi dariya ma sam² da bayayi sai yaji mugunta zakiji shi ƙa׳ yana dariya , kuma dariya ba ƙaramin kyau take mishi ba , Allah sarki mai uwa baya san laifinta , amma gaskiya Momy gaba ɗayanta batayi ba bata da mutunci ko kaɗan , gata da raini , rankatakaf ta ɓata "ya "yanta da baƙin hali basu san mutunci kowa ba saina mazajensu shi yasa mazan nasu kamar sun masu asiri biye mazajensu suke dasu , kuma ita bata iya neman asiri ba saidai bariki da duniyanci wurin iya nannaɗe zuciyar namiji , shi yasa Momy ta share kowa a wurin Dady dan yanaji da ita sosai , amma basa san ace Momynsu tana da miyagun halaye , kai , amma gaskiya "yan uwan Dikko da suke ɗaki ɗaya zamani ne su , makaranta ce mai zaman kanta , sunyi׳ , sun haɗu׳ wayayyi ajin farko , kuma sunfi "yan ko wane ɗaki yawa a gidan , ga kuma Mai gida DK nasu.....
Satin Papi 3 a wurina amma har yanzu bai daina kukan Momy ba , kuma Nabeela tana nan ta dawo gidan kwata² da zama , ga Dikko baya zama , ni kuma banda lafiya , dana ce masa ko akai Papi wurin Momy cewa yayi kar a sake akai mishi ɗa wani wuri yaje yaita kukan idan ya gaji zai daina , Nabeela kuwa ta faɗawa Momy Papi yana ta kuka shidai Momy , tazo da kanta itama dai tayi kewar Papi , cike da soyayya Papi ya riƙe Momy su tafi wurin Dady , har ranar da suka dawo dasu Rabiya saida yaba Momy labari amma wasu ya manta sai ya tambayi Nabeela , murmushi Momy tayi irin na ƙasaitaccin mata da irin yanayin kallon Dikko , dai² gani sukeyin kallon amma idan kasa ido sosai zakaga kallon nasu yanayin ƙasa kuma basa motsa idon , baka ganin lokacin da idon yake tafiya idan suna rageshi , idan kuma suka gyara kallon nasu sai kallon ya bada wani iri mai burgewa , da irin kallon ta tsare Papi tana cewa ni duk naga ka zama wani baƙauye ta faɗa tana murmushi da gefen bakinta tana ci gaba da cewa Nabeela anya zanyi auren nan ? Kafin Nabeela tayi magana Papi yace ni nayi cau ya faɗa yana harar Momy.
Dariya tayi tare da cewa ni bakaimin wani kyau ba , iyayenka basu iya raino ba kuma bazanje dakai ba , kuka ya farayi yace ina juwa , dama da yawo ta kama Papi , duk wankan da akayi Papi saida Momy tasa Nabeela ta sake wankeshi aka gayeshi tace Nabeela taje anjima ta dawo dashi , gaba ɗayanmu mukayi mata rakiya ta tafi.
Dikko kuwa ya kirani yayi faɗa sosai yace an ce masa wai anga Papi gidansu , meya faɗa min ne ? Zanyi magana yace in mishi shiru ni dama na raina mutane , ya ƙara da cewa ya rantse da Allah idan wani abu ya sameshi ni idan nayi mishi kuka saiya zaneni , itama Nabeela zai haɗu da ita shima Papin zaici ubanshi bari ya dawo , yana faɗin aka ya tsinke wayarshi.
Ashiru ya bashi haƙuri , Dikko yace shi bawai yana hana Papi zama wurin Momy ba , fiya² fa aka bashi sai kace wani ƙwaro , idan suka kashe mata ɗa ni ba abinda ya dameni kuka ne dai bata isa tayi min ba , gidan nan munafinki gida ne kuma na faɗa mata , mu kanmu "yan gidan ya muka ƙare bare kuma wani jika , kadai san halin Momy haka take zama ta tisa Papi taita habaice² , tana irin wannan maganganun nasu na mata. Haƙuri Ashiru yai ta bashi ƙarshe dai Dikko yayi shiru ya ƙyale Ashiru.
Nabeela kuwa kila shi ya kirata yaci mata mutunci , bansan yadda akayi ba taje ta taho da Papi , yana ta kuka , ta waya Dikko ya zageshi yace kuma bari yaji ance masa ya sake kiran Momy saiya turo Jiddah ta kashe shi aje can a jefar dashi , bazai sake ganin Momy ba kuma bazai sake cin abinci ba ,
Na faɗawa Inna banda lafiya , kuma na faɗa mata ciki nake da , na ɗauka zatayi farin ciki ta kirani tunda saƙo na tura mata , cewa tayi can ni ya dama , kuma bata faɗamin duk abinda ya shafeni da Dikko kar na sake faɗa mata ba ? Dole na haƙura naci gaba da rayuwata daga ni sai Dikko da "yan uwanshi mata.
Rabona da Inna kenan , saida ta kirani ta faɗamin rasuwar ɗan uwanta baban Sultan , yayi haɗarin mota , a nan gidan Kaka ake zaman ta'aziyya , za'ayi jana'izarshi da bayan azahar , dani da Nabeela da Papi muka tafi , kuma kaf "yan uwan Dikko sunje min a ranar da akayi rasuwar suna nan akayi jana'iza bayan an dawo sukayi gaisuwa wa Inna Kaka da matan mamacin sukayi tafiyarsu , amma muna tare da Nabeela , Dikko kuwa bai zo ba dama baya gari , yadai turomin text in tafi gida haka nan bawai nan zanje in jibge ba harsai an raina ni ba , dana nuna masa ya bari zuwa anjima cemin yayi ya gama magana , dana faɗa ma Inna zan tafi taji damuwa tace in bari sai anjima nace mata shi yace in tafi , taji ba daɗi dan kowa da "ya "yanshi a kusa dashi haka na tafi tanaji kuma tana gani bataji daɗi ba , gashi ba dama ta kira Dikko.
Tun daga ranar ban sake zuwa ba sai ranar addu'ar 3 , Momy ma taje min a ranar kuma su Inna anji daɗi matar gwamna tazo , haka taita tattaro mutane tana cewa ga surukar Sultana suje tayi musu ta'aziyya Momy kuwa riƙenta take tana wannan rainin nata , da ta tashi tafiya ta bada kuɗi masu yawan gaske sadaka , shima Dikko ranar addu'ar 3 yazo , kuma yana zuwa yayi gaisuwa yai tafiyarshi bayan shima ya haukatasu da kuɗi sadaka , ranar mu kuma sai dare muka koma gida dani da Nabeela bayan nima na bada tawa sadakar dan nima yanzu inaji na dai² nake da duk wani mai jin shi yana da hatimin nasarar shi , dan duk wata damuwa ko takaici Dikko ya shanyemin shi , baya bari inyi tagumi shi yasa ya sakarmin ragamar girman kuɗi , buɗa min fili kawai yakeyi ina yadda naga dama da rayuwata....
Yana nan bazai sake tafiya ba sai an gama zaɓe , itama Nabeela bayan zaɓe za'asa ranar aurenta , addu'arta Allah ya maida Dady a mulki sai kuma wanda zata aura shima ya haye , shima Dikko addu'arshi kenan Dady ya koma mulki , nima ina mishi fatan komawa bana so su faɗi.......
24/12/2019 👇🏻
*JAMILA MUSA...* 💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 91
_Alhamdulillah_
_Alhamdulillah_
_Alhamdulillah_
*_Assalamu Alaikum masoyana , suna na Jamila Musa wacce kuka fi sani da Meelat Musa , ina muku fatan alkairi maudu'in rayuwata 😊 , zanyi matuƙar kewarku sosai , inajin wani iri a raina , jiki yai sanyi , idona shima zaiyi kewarku , yana muku bankwana da hawaye 😭 , gaskiya ina matuƙar sanku yadda bazaku iya ganewa ba , hmmm , tou ina dai muku fatan alkairi a duk inda kuke a faɗin duniyar nan alfaharina , zan tafi׳ , sai kuma Allah ya sake haɗamu idan muna rabon sake haɗuwa a cikin sabon littafina mai taken ƁOYAYYAR SOYAYYA , KWARATA yazo , kuma zai tafi , Dikko da An mata suna muku fatan alkairi , ni kuma Jamila nake neman yafiyar duk wanda na mishi babu daɗi , wani ban ganshi ba , amma rubutu na yaje gareku , ina alfahari daku , kuma ina muku fatan alkairi , ina matuƙar ƙaunarku sosai da sosai , masoyana da mukeyin waya daku , wasu kuma cht da wanda Allah yasa na gansu ido² duk ta dalilin Dikko da An mata ina matuƙar ƙaunarku , Allah ya sadamu da alkairi gaba ɗayanmu , ngode ׳ da yadda kuka nunamin ƙauna , na barku lafiya......_* 👏🏻
Yaya janje , a , a , da gudu Papi yabi bayan Dikko yana kuka , kai nifa babu inda zanje dakai , ƙara faɗar janje yayi yana bin bayan Dikko da sauri dan taƙaita gudun saboda ya isko shi , a , a Dikko ya sake maimaitawa , bin bayan shi Papi yakeyi yana ci gaba da kuka , dariya Dikko yayi sosai yace tou zo muje , yayi maganar yana kama hannun shi , juyowa Papi yayi tare dayi ma Nabeela gwalo da tace Allah yasa kar a tafi dashi , murmushi Dikko yayi ba tare daya sake magana ba suka fita , yayi kyau sosai a cikin ƙananan kaya , riga jinin kare baƙin wando rufaffun takalmi suma baƙi sai baƙin agogo , Papi kuma manyan kaya ne jikinshi.....
Dariya nayi tare da kallon Nabeela nace zakisha mamaki , tunda yayi waccan dariya lallai sai yayi ma Papi wani abu na mugunta , kuma zaki sha al'ajabi bara su dawo , dariya Nabeela tayi tare da cewa kuma nima in rama gwalon da yayi min da zai fita.....
Gaban mota Dikko yasa Papi yana cewa ai dai zakaje ko ? Ya ƙara tambayar Papi , goge hawayen shi yayi tare da cewa Janje Yaya , yayi maganar yana kallon idon Dikko , tou zauna , zama yayi a dai² lokacin daya tashi mota ya fara tafiya , Ashiru dake tsaye daga gefe yace Mai gida ai ban san fita zakayi ba , ba tare da Dikko ya tsaya ba yace ai ba nisa zanyi ba , ya ƙarasa maganar yana ɗage gilashin gefenshi da ya sauke danyin magana da Ashiru ya fice daga gidan da gudu.....
Suna fita muma muka zagaya can bayan gida ina taya Nabeela aiki zatayi baƙi , gidan ne gaba ɗaya aka firgita , yasa ana ta rosheshi , nidai a ganina asara ce kawai dan wallahi gidan ya haɗu iyakar haɗewa , kuma banga abinda yayi ba , duk komai na gidan da aka fitar tsohon namu kenan , yaranshi ne suka kwashe su , ni ɗakinshi ma nafi tausayi dan Allah ya sani an daddaƙe ma kuɗi rai a ɗakin Dikko , anyi masa haɗuwa ta haɗaɗɗin haɗewar masu haɗuwa , can baya ma da akayi gidan anyi surutunshi sosai kuma har yanzu ba'a gama surutun ba , yanzu kuma wane irin gini za'ayi...... ? Aikin baizo wurinmu ba shi yasa bamu tashi ba , amma dai duk an fitar da komai na gidan su Ashiru sun kwashewa "yan uwansu , ba komai a gidan muma goruba road zamu tafi a daren yau sai an gama aiki zamu dawo , aikin da nake taya Nabeela baida wani yawa , amma kunsan yadda jiki yake , shi jiki sabo ne dashi , idan an horashi da wahala da ita zai horu kuma idan harma bakayi abun wahalar ba bakajin daɗi , idan ya saba da hutu tabbas baya iya ɗaukar wahala , shi yasa "yan gayu ashe muke ganinsu kamar sun raina mana hankali , to ba haka abun yake ba , saida na shiga fagen na gane haka , nima dai yanzu bana iya sakin jiki inyi aikin nan kamar jakkar ci rani , idan kuwa nayi aiki mai yawa sai nayi jinyar gajiya.....
Bare dama akwai masu aiki maza da mata , kuma duk wani ma'aikaci , daga direbobi , masu shara , masu girkin abincin da ma'aikatan gidan ke ci , masu gadi , masu ban ruwa wa fulawowi har masuyi musu aski su gyarasu idan sun zame daga tsarin da ake sansu , gaba ɗaya a gidan suke zaune , suna da wurinsu daban , kuma a gidan ake basu abinci kuma albashi ake basu duk ƙarshen wata , amma shi Dikko bayacin abincin gandu , namu mukeyi daban ina da mai aiki ta daban amma baya san abinci masu aiki sai ni zanyi idan yana gari , kuma masu aiki basa gyara masa ɗaki , ko yanzu da bana lafiya shi yake gyarawa ya goge komai fes kamar mace , ya iya gyaran gado idan har yayi miki gyaran gado zakisha mamaki , baya san ƙazanta ko kaɗan , da nace masa Nabeela cewa yayi a , a , dan iyakarta palonshi bata taɓa shiga bedroom inshi ba , nidai da nazo amma ban sani ba ko a zamanin Jiddah tana shiga ba , saida muka gama abinda mukeyi Nabeela tasa aka kwashe komai aka kai a motar ta , sannan muka taho dan komawa ciki.
Da gudu ya shigo gidan a dai² lokacin da mu kuma muka bayyana gaban fuskar gidan , tun kafin motar ta ida tsayawa cak ya kashe motar ya fito , tunda nake da Dikko ni ban taɓa jin waƙa a motarshi ba sai yau , ya wani ƙuro volume , buɗe hannuwan shi yayi ya nufo inda muke tahowa yana wata "yar munafukar rawa , daga ni har Nabeela dariya mukayi , rumgumeni yayi tare da ƙyalƙyalewa da dariya ya raɗamin wai Papi ya girma , cikin rashin fahimta na leƙa ta gefenshi naga Papi ya fito daga mota yana cewa ban nuna muku , dariya Dikko ya sakeyi sannan ya sakeni yana cewa yanzu zai cire wando ya fara kuka , ya faɗa yana nuna ma Papi yayi rawa , tsalle Papi ya farayi yanayin yadda Dikko keyi , murmushi Dikko yayi tare da kallon Papi ayyo ah² wayyo yana murmushi , sakin jiki Papi yayi yana ta rawa , saida Dikko yaga ya shagala yana rawa , ya koma mota yai tafiyarshi.
Nidai ban gane girman da Papi yayi ba , kuma ni kwata² raina bai kawomin kaciya Dikko yayo ma Papi ba , saida muka shiga ciki yaci gaba da cewa ban nuna muku abinda Yaya yayi min , ya faɗa yana rumgumer bango , duk babu wanda yayi ma Papi magana , bayan Nabeela ta fito wanka yace mata , yayinya joki in nuna miki , cire wando Papi yayi , Nabeela tana zuwa , yayi dariya tare da maida wandonshi yace baci gani ya faɗa yana mata gwalo , kowa fita harkarshi yayi muka ci gaba da abinda ya shafemu , shi kuma sai murna yakeyi , saida ya fara shan azaba ya cire wando , muma bamu sake shiga sabgar shi ba kuma bamu sake kallonshi ba , allura tana fita Papi ya fara ihu....
Yana taɓa kaciya , Nabeela ta fara dariya tana ɗaukarshi a waya , tana cewa da nace karka je ba sai da kaje ba ? Yanzun nan zan tura Momy ta gani , nima abun dariya ya bani sosai , iskancin Dikko saishi , kullum abunshi gaba yakeyi babu alamar sauƙi , Nabeela daina video tayi ganin Papi yana halbe² a ƙasa yana cewa nama ɓata da Yayan nan , rumgume Papi tayi suka ci gaba da kuka tare ,
Duk daɗewar da Dikko yayi waje harya dawo daga Papi har Nabeela basu daina kuka ba , da nace masa me yasa yayi haka baiga Papi ƙarami bane ba ? Kallon Papi yayi tare da cewa gobe ma idan ka biyoni ƙaro maka zanyi , cikin kuka Papi yace kuma na fata dakai , ai nine na ɓata dakai shi yasa naje na kaika akayi maka , miƙa hannunshi yayi tare da cewa zo muje , maƙale kafaɗa Papi yayi yana harararshi cewa kuma saiya faɗawa Dady , murmushi Dikko yayi tare da cewa tou jeka fa faɗa masa , yayi maganar yana fito da wayarshi yace bara kaji ma in kira Dadyn ya ƙarasa maganar yana kara wayar a kunnenshi.
Bayan wani lokaci ya fara magana a waya , Dady ga Papi zai kawo ƙarata yayi maganar yana ba Papi waya , cikin disashshiyar murya Papi yake faɗawa Dady abinda Dikko yayi mishi , bansan abinda Dadyn yace masa ba , ajiyar zuciya Papi ya sauke sannan yace to , shiru yayi , bayan wani lokaci Papi ya sake sauke ajiyar zuciya yace to , ajiyar zuciya ya ƙara saukewa ya faɗi Nabeela , ɓata fuska yayi ya taɓe baki yana ajiyar zuciya , bayan wani lokaci kuma yaba Nabeela waya , bayan ta gama tabani waya nima na gaishe shi , yamin sannu da mai jiki , bayan mun gama gaisawa nima nayi masa addu'a kamar yadda naji Nabeela tayi , sannan nabawa Dikko waya , fita yayi daga ɗakin yana magana a waya.
A gaggauce muka shirya muka bar gidan , saida muka biya ta wurin Momy , tayi faɗa sosai da abinda Dikko yakai Papi akayi mishi , ta kuma yi addu'a Allah yasa a fita lafiya , anjima zata aiko Ashiru wurin Papi , bamu wani daɗe ba muka wuce goruba mu dukanmu , shi gidan an gama aikinshi , kuma babu abinda ba'a saka ba , komai na gidan sabo ne katakal , har kicin ma anyi mishi tsari mai kyau babu abinda babu. Abundai , sai Allah sabunanni......
Satinmu biyu a goruba road , gaba ɗayanmu bamu da wata damuwa , rayuwar mukeyi cikin farin ciki , amma tunda wannan satin ya kama Nabeela da Papi basa tare dani saboda asabar ta gaba ake zaɓe suna can gidansu , mijin da zata aura kuma an tsayar da ranar aurensu ne idan yaci zaɓe za'a haɗa da murnar cin mulki da kuma shagalin ɗaurin aure , idan akayi rantsuwa kuma amarya zata tare a gidan gwamnati kenan......
Ni yanzu gaba ɗaya na daina gane kan Dikko , ya burke bansan abinda yake damunshi ba , saidai idan na buƙaci ganinshi zaizo ne ya bani haƙƙina da zaran kuma ya gama zai kama gabanshi , da nace masa wai ina yake zuwa yanzu sai yacemin shi bazai zauna gida ba tunda ba mace bane shi ,
Abun ya dameni sosai , dan haka na kira Rabiya na faɗa mata kai tsaye , haƙuri ta bani tare da cemin in bari idan aka gama zaɓe zata zo , Inna dana kirata nace mata shawara na kirata muyi cemin tayi idan dai ya shafi Dikko karma na fara faɗa mata.
Har akayi zaɓe aka gama ni bansa Dikko a ido ba , kuma Allah ya basu sa'a sun sake ɗagewa sama , wanda Nabeela zata aura shima yaci , duk shagalin da akayi banje ba Dikko ya hanani zuwa , Nabeela bataji daɗi ba kwata² , Momy ma taji babu daɗi da tace azo a taho dani cewa yayi idan dai shine yake aurena ya hanani zuwa idan kuma aurena ba a hannunshi yake ba tou inje , Momy da kanta ta haɗani da Dady a waya nayi mishi murna ,
Shagalin sake komawa a mulki banje ba , amma na ranar da aka ɗaura auren Nabeela naje , kuma tun safiyar ranar ina wurin Momy , kayan da zan saka Momy ce da kanta tayi minsu , duk abinda ya kamata itace tasa akayimin nima dai na fito kamar sahun "ya "yanta tunda ina da kyau na mai burgewa da baka gajiya da kallona , kuma banda irin wannan duhun kan na ƙauyanci , suna ta nunamin ƙauna da soyayya daga ni har Papi ,
Hmmmm , anyi wani irin shagali daya zo ma al'ummar jahar Katsina baƙo , ɗiyar gwamna ta auri gwamna , manyan mutane daga jahohi da dama sun samu damar halattar wannan gagurumin ɗaurin aure , wanda aka tara dubun² mutane , ni ina nan zaune a bedroom in Momy saman gado zaune kusa da Rabiya , abun duniya duk ya dameni , dan yanzu ko wayata Dikko ya daina ɗauka idan na kirashi saidai ya turo min text , wai idan wani abu nake so daga gareshi in mishi a rubuce basai na wani dameshi kira ba , kenan idan bani na buƙaceshi ba shi baya buƙatata ? Me hakan yake nufi tou......?
Lokacin da za'a tafi wurin shagalin party , yanzun ma Momy ce ta bani kayan da zan saka da mai kwalliya ta kuma tsaida Rabiya wurina dan ita tana fama da jama'a , idan dai mutum ya gitto wurin ya gani zaice masha Allah , wasu daga ahalinsu Dikko basu sanni ba , idan akace wacece Rabiya zatace matar Dikko ce , ko abokan wasa daa suka fara jana da wasa Rabiya cemin tayi kar in koya musu , basu da mutunci. Duk yadda dangin miji zasu soki idan dai baki da power wurin miji kin zama katin ɗaurin aure ,
Jiddah tana cikin tawagar "yan gidansu , kuma hada Mardiyya Hafsa da Mom inta suna tare da Asma'u amma banga Amisty ba , nidai duk jina nake a takure , Papi kuwa yana liƙe da Nabeela tana fama da hidima amma yaƙi tafiya wurin kowa sai wurinta , duk yadda Momy taso su Ashiru su fita dashi Dikko cewa kar wanda ya ɗauko shi wai su barmin ɗa na can , nidai bansan abinda ya faru ba tsakanin ni da kuma Dikko , amma kuma na fahimci kamar Momy da Dikko akwai abinda yake faruwa.
*_Uhum baya da ƙura kenan_*
Anyi shagali na wuce ni na rubutashi , kowa ta ƙiyasta yadda hankalinta da tunaninta zai iya ɗauka , ɗiyar gwamna ta auri gwamna , ga gidansu amarya da kuɗi ko ba mulki su dama attajirai ne wanda kullum kuɗin nasu kamar aiko musu su akeyi , caf lallai , neman suna ba banza ba , ga wani ya tafi nema amma ya rasa ranshi bai samo ba , su Dikko tun ba a waye da sanin amfanin a sanka ba sukayi suna kuma aka sansu , sun nemi kuɗi kuma sun samu tun ba'asan amfanin kuɗi ba , rabon da naga Dikko harna manta sai yau a wurin party , yayi wani irin wanka na tashin hankali , yasa wata irin sheɗaniyar shadda akayi mata ɗinki "yar ciki wando da babbar riga , gemun nan yasha gyara sai ɗaukar hankali yake , yana tauna cingom a hankali cikin salo mai ɗaukar hankalin duk wanda ya kalleshi , yayi׳ , ya haɗu iya haɗewa , ya burge , yayi kyau harya gode Allah , wallahi an tara duk irin mutanen da baku tunani wurin shagalin nan , amma na rantse muku da girman Allah babu kamar Dikko a wurin , ya haɗu iya haɗuwa yaci taro , yaba maza azaba kuma yaƙi barinsu su huta , duk wani mai kucakin gayu a wurin ya kama kanshi , yana gaba su Ashiru na biye a bayanshi , yana tafe yana jin kanshi kamar zai tashi duniya.... Su Ashiru na biye dashi ɗauke da wasu irin ƙattin jakukkuna biyu , tunda ya doso wurin yake ɓata rai , mutane sukaci gaba da darewa suna buɗe mishi hanya yana wucewa , daya wuce sai abi bayanshi da kallo.
Rabiya dake tsaye kusa dani tajani muka tunkaro hanyar fitowa , wai dan kar in gani , hmmmm , hankalin kowa ya koma wurin Dikko tunda ya shiga inda ake rawa , ya kafe kanshi yaci gaba da ɓara mata kuɗi , makaɗa suka ruɗe , duk wani mawaƙi da aka tara wurin nan ya daina waƙa sunan Dikko kawai yake kira ana mishi kirari , da kuɗin hannunshi ya ƙare sai a miƙa mishi , DK kawai suke kira , dakel aka fiddoshi daga wurin dan bashi da hankali akan ɓarar da kuɗi , idan zai kwana a haka baya gaji kuma bazai daina ba , zaiyi ta zubawa ne baya gajiyawa , haka kuma idan zai bayar yake kyauta maisa ɗimuwa. Wace ce ita.....................???
Nace muku banda labarin Bello ko Dady ko ? Babu ruwansu dani , dan tunda Dikko ya gwagwaɗa musu layi akaina , yace musu ko ciwon kai nayi ko naji an kira sunansu bacci a bacci yayi musu rantsu kashe su zaiyi , tou wannan dalili yasa suka fita sabgata....
Mardiyya
Jiddah
Amisty
Hafsa
Saude
A ` e
Tawagar gidanmu , su tuni na siya musu gida kuma har yanzu basu daina harkar bariki ba , danbe da duk wata harkar iskanci.....
Ummu Affan , ita mijinta a saketa , Abbu Afsar wato { Alaji } wanda da Dikko ya tafi dani Babana ya ƙafe ? Wanda ya siya min rigar birthday ? Ya kula da Baba ? Tou har yau ni banda labarinshi , kuma ba abinda ya dameni da sanin halin da yake ciki.
Yazeed
Wace ce Dikko yayi ma liƙe a wurin party...... ?
Mu koma baya......
Gyara zamanshi yayi tare da cewa bara na baku labari , a london na haɗu da wata "yar tasha , tunda ta shigo jirgi kawai tayo wurina ta zauna......
Dikko yace ai ban shanyu ba shi yasa zanyi ma Perpy wata Momyn ,
Ashe ni ina tunanin Yusra ƙawar Sadiya matarshi data rasu ne , abinda yasa tace ita maza basa burgeta bata samu irin tsarin da take so ba , shi kuma yace kamar wani sakarai haka ya kalleta ,
Ya ɓoye labarin , haukata ya hana na barshi naji yadda labarin yake na tsaya wani kishin banza da wofi , duk yadda Dikko yake tsaye akaina ? Kuma "yar uwarshi ke tsaye kaina , soyayyar mu da Dikko zakuyi tunanin akwai wata bayan An mata........?
Wane sakaci nayi ne ? Me na rageshi dashi ? Meye yarinyar daya kakkaɓe idonshi ya mata liƙe take masa , Dikko baya zina ya akayi wata macen ke riƙeshi waje har yakai 3 dare bai dawomin gida ba ?
Jamila Musa gareki.......
Jama'a duk wanda ya kalli labarin nan yasan tuni na yankeshi , naso kuyi haƙuri kubi labarin yadda yazo min , ba labarin zamu kalla ba darasin ciki zamu ɗauka , amma sai kuka firgitani , idan kunyi nazari shi labarin rayuwarka yasha banban da labarin shaka tafi , ba ƙirƙira bane ba da zan rubuta muku yadda kuke so ba , kowa da yadda Allah ya rubuto mishi jarabtarshi , kuma babu wanda ya isa ya goge ƙaddar rayuwarshi a yadda tazo ,
Maganar lalurarshi , yace Ashiru yaji da komai , kuma duk Dady baisan anayi ba , bai faɗa masa ba saboda baya so Dady ya saki matarshi dan kar Momy tayi baƙin jini , meya faru bayan Mustapha yakai Ashiru wurin daya ce nan ne asirin yake ? Ya aka ƙare ne ? Ina Al ' Ameen ? Ya mutu ko yana raye ne ? An dai buga mishi lamba haka Dikko ya faɗa tunda bashi nan baisan abinda ya faru ba , Al ' Ameen daya fita daga inda Dikko ya tsareshi ina ya tafi ? Me yayi bayan ya fita ? Meya faru ? Koma dai miye idan ta amince zakuji ya warke ko yana tare da matsalar ne.............?
Duk mai imani yasan akwai jarabta , ni naso na rubuta muku yadda duk zamu ƙaru gaba ɗayanmu , naso kuji yadda Sultana tayi rayuwarta a gidan Dikko dole ta nan zamu warwaro matsalolinmu , mu fahimta inda muke da gyara kuma mu gyara , amma sai kuke cewa bana san Sultana ina bata wahala , bayan bani bace na ɗora mata ba , wasu kuma sai suke zagin Dikko , wasu Sultana , wasu kuma niɗin suke zagi babu gyara babu dalili , daga gyara kayanka ai bai zama sauke mu raba.....?
Nidai ina san insan yadda kissa da kisisina da kuma kwarkwasa take , tafiya magana kallo da dai sauransu , mi ke kawo yawan mace²n aure ? Tou idan mai labarin ta yadda zaku jini , salon labarin zai dawo muku da wannan tambarin..... 👇🏻
*KWARATA RETURN...*
_{Ƙalu bale gareku matan aure....}_
*SAINA AURI DK*
Labarin zaizo muku a kyauta ne kamar dai yadda wannan yazo , bana siyarwa bane ba ,
Ga dai .
*JIDDAH*
*MARDIYYA*
*HAFSA*
*YUSRA*
Kowa a cikinsu saita auri Dikko , su suna waje An mata a cikin gida , gadai Yusra tana riƙe Dikko yana kai 3 na dare yana waje , shi baya zina tou dame take riƙeshi wanda har yake tafiya wurinta yabar matarshi ? Me ta iya wanda Sultana ta raga mishi ? Sultana zata yadda kuwa wata ta shigo ? Koma dai miye idan ta amince zaizo a cikin sabon labari mai taken.
*KWARATA RETURN*
Alhamdulillah jama'a , Jamila tana godiya sosai , sai Allah ya haɗamu a sabon littafina in Allah ya yadda 👇🏻
*ƁOYAYYAR SOYAYYA...*
Gasuwa ta musamman gareka *IBRAHIM MUSA QERAU* { Alhajeje } ngode sosai da ƙoƙarin da kayi mana , muna godiya sosai daga kai har mutuminka Mai gida DK , ngode׳ sosai.
Godiya gareku "yan uwana , ngode sosai da irin taimakon da kukemin , wurin ganin kun tayani yaɗa wannan labari , ngode sosai da ƙauna Allah ya daɗa zuminci. 👇🏻
*SA'ADATU* {{ AUNTY MUSA }}
*HAWWA MUSA* {{ F JIDDAH }}
*RABI MUSA* {{ MRS USMAN }}}
BISSALAM.
MASOYANA 😊 na barku lafiya , ina matuƙar kewarku cike da maraicinku.......
*RUƘAYYA MATAWALLE* , ina godiya da kyautar rake...... 😘
26/12/2019 👇🏻
Daga alƙalamin
*JAMILA MUSA QERAU...* ngode ׳ Allah ya sake haɗamu da alkairi.