Hukumar Hisbah a jihar Kano ta umarci wasu matasa biyu da yin sallar nafila raka’a 100 biyo bayan furucin ɗaya daga ciki na ƙin yin salla kwata-kwata.
Bayan wani faifan bidiyo da ke yawo wanda aka hango wani matashi na yin iƙirarin daina sallah, hukumar Hisbah a Kano ta umarcesu da yin sallah raka’a 100.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar ta ce iyayen matasan ne su ka kai yaran domin a ja kunnen su.
Shugaban hukumar Ustaz Haroon Ibn Sina ya ja kunnen matasan tare da yi musu nasiha don neman gafarar Allah.
Hukumar ta ce bayan kammala nasihar ne ta umarci matasan da yin sallah raka a 100 nan take.
Guda cikin matasan wanda ya yi suna a kafar sadarwar zamani mai suna Muhammad Ikbal ya gamsu tare da bin umarnin hukumar.
Al’amarin ya samo asali ne bayan wata hukuma ta yi wa matashin kwaryar molo wanda hakan ya fusata shi ya yi furucin daina sallah kwata-kwata har sai gashin kan sa ya fito.