.
An watse taro Lafiya yan Uwa sun koma gidajensu lafiya lau sai addu'an zaman lafiya da aka bi maauratan dashi. Ɓangaren Agaysha kuwa kawayenta na nuna mata gara da tayi hakan kafin wata ukun ya wuce za'a tura mata warin jaɓa da ɓallewan jini. Haka dai sukayi ta shawara har dare ya tsaga. Washe gari ma haka sukai ta bata shawaran da suke ganin zai fishe su, kafin suka watse aka barta da kunan zuciya. Mafarkin ido biyu ta yini tana yi, idonta na hasko mata Abdoul ɗinta da Halima. Tayi kuka kashi kashi, ta yini tana tsine ma bokayen da sukayi mata aiki, barinma wanda ta ba jikinta. Kamar an muntsile ta, wayarta ta ɗauko ta kira shi don ta ci masa mutunci. Ringing biyu ya ɗaga. "mace mai garɗi Uwargidan Abdoul kina lafiya" Ya faɗa yana kasa da murya, hakan bai hana ta jin kaurin muryar kamar saukar aradu. "kasan kuwa an ɗaura auren" abinda bakinta ya iya furtawa kenan. "Kinsa kokwanto, baki bada gaskiya akan zan iya hana auren ba. Aiki da kokonto ai ba zai taɓa karɓa ba." Ya faɗi daga chan ɓarayin. "Kokwanto kuma?" Ta tambaya tana zare idanu kamar yana ganin ta. "Eh! Ai da kin mika gaskiya, kin amince zan iya yin komi duk da ba haka ba. Amma bai yi latti ba, ki samu ki zo sai a tura mata cuta wanda zai kar da ita har lahira." jin hakan ya saukar mata da wani farin ciki da bata san daga ina ya fito ba. Haka dai yai shawo kanta da zantuka na karfin gwiwa da tabbatar mata da Halima mai karan kwana ce.
.
Tunani da kukan da ta yini tana yi ya saukar mata da zazzaɓi, wasa wasa tana zata ji sauki ta samu ta leqa maraɗi amma ina sai da tayi sati kwance. Kullum Abdoul kan kira su sau biyu ko uku a rana don ya ji lafiyansu, amma tana ɗauka zata mika ma su Ummu Abeyha wayar su yi masa magana. Auren na da sati biyu ya samu zuwa duba su, nan ya iske duk ta rame tayi baki, da ya tambayi dalili ne yaji ta yi ciwo, bai tambayi dalilin ta na kin sanar da shi ba. Dare na yi ta wuce ɗakin Yaransu ta kwanta abin ya ɓata masa rai har ya tunkare ta da zancen, buɗan bakinta kuwa sai cewa tayi "Ni fa sai munje anyi maka gwaji zan kara amincewa da kai, ba zaka auro min raguwan sida sannan in amince maka ba" tana faɗin haka ta juya baya. Bakin cikinsa ya ninku amma sai bai nuna ba. A daddafe ya karaci kwanakin da ya ɗiba zai yi on yazo yayi ya kara gaba. *** A Ɓangaren amarya da ango kuwa soyayya suke gudanarwa mai tsafta.
.
Tun da ya amfana da sadakinsa ya kara jinjina ma Halima, ya san ba karamin jihadi tayi ba na tsare mutuncin ta. Ace mace yar shekara ashirin da shida ai dole tana da sha'awa, zata bukaci abokin ɗebe kewa tunda dai mutum ce ba dutse ba. Amma yana da ga cikin jihadi (jihadul nafs) wanda yafi kowane nau'i na jihadi daraja fin karfin zuciya. Yayinda mutum yai hakuri, ya danne sha'awarsa har zuwa lokacin da ba ma sha'awa hakkinsa zai kai ka ga aljanna ne ba wuta ba shima babban nau'i ne na jihadi mai babban daraja (ni safiyyah Ummu Abdoul nace Allah ya kare mu da zuriarmu daga aikata zina da sauran Alkaba'ir, Aameen ya rabbi ). Tun lokacin yake bata wani daraja na musamman don ta karyata masu bahagon tunanin duk yar da ta je jami'a har ta kammala to lallai ta siyar da yan matancinta. Wasu ma har kauɗin kiransu karuwai suke yi, su kan manta babu tsattsauran sheda a musulunci kamar shedan zina. "banga kaddarar da zai kaini ga auren yar jami'a ba, balle a ce ta gama har tana aiki, ai duk ba budurwa cikinsu sai dai budur-budur" faɗin wani abokin aikinsa. Tsakin da ya ja ne ya dawo da hankalin Halima wajen shi. "Sweetyna! Lafiya kake tsaki" Ta tambaya fuskanta cike da damuwa.
.
Kallon cikin idonta yake zuciyarsa na ayyana masa tsarkin da ke tattare da dukkan lamuran ta,chan dai ya ce "Ina mamaki ne, yanda wasu mazajen musamman namu na Hausa Fulani ke jifan matan da suka yi karatun boko da rashin tsarki... " nan dai ya bata labarin yanda sukayi da abokin aikinsa mai wancan tunanin. "ka ji ka dai sweetyna, wai me yasa mazan hausa fulanin kuma suke ganin nasu kalar tsarkin a matsayin ado. Amma fa laifin matan ne, sakarkaru, su bari ko wani gardi ya taso sai ya ba gaɓɓai huɗu wahala, kuma su garadan ganin kansu suke a tsarkaka yayin da matan najasa. Duk namijin da kaji yana kiran matan jami'a ko wa'inda suka Gama a Yan iska toh Allah sweetyna ya san inda yake haɗuwa da su. Sai ka ga namiji ya gama sheke ayarsa wai shi a dole zai ma Allah wayau se ya koma ma auren karamar yarinya. Hukuncin mace da namiji a fagen shari'a dai ɗaya ne, duk namijin da yayi saɓon Allah toh saɓo ne dai dai da na mace, hukuncin su ɗaya sweetyna" Ta karasa tana sakar masa wasu sakonni mai gamsar da mai amsa. "Allah ya bar min ke Amaryar Abdoul" Ya faɗi yana sumbatarta a goshi.
***
June 2016 Raywarsu na tafiya gunin ban sha'awa, Abdoul yayi kiba sosai, haskensa ya fito sosai. Da gani hankalinsa a kwance ne. Duk sati biyu yana zuwa zindar yayi kwana biyar, matukar yana kasan.
.
Agaysha dai kiri kiri ta ki amincewa da shi, akan sai an masa gwajin sida, yayinda sai chushe chushe takeyi a jikinta da birne birne duk don Halima ta mutu. Sau biyu yaranta na zuwa hutu wajen Halima, duk suka dawo takan lura da chanjin da take gani tattare da su, nan ta fara rigimar baya adalci Halima daɗi ta ke ci. "Halima aiki takeyi ba ta jira sai na ɓata kafin ta yi" Ya iya ce mata ya barta nan.
.
Kwatsam! Wata rana ta je fitsari sai ta ga kyankyaso a cikin masan, kasancewar ta matsoraciyar kyankyaso yasa ta tsuguna tayi a kasa, ta tsorata ainun ganin kalar Fitsarin kamar jini ga wasu fararen ababenan a ciki wanda da ta kalla da kyau sai ta ga ashe tsutsotsi ne. Ta firgita ainun, kasancewa ya fi sati take jin azaba yayin fitsari, kuma bata taɓa tunanin in tayi ta duba ba, tana tsarki take matsa wajen da zai flushing. "kar dai Halima ce ta turo mata" wani sashi na zuciyarta ya faɗa mata. "ko kuma naki ne dawo miki ba" ɗayan sa shin mai faɗin ya ce hakan. Shiru tayi duk a tsorace. Wa za ta kira, gashi ana azumi balle ta je wajen boka.
.
Wasa wasa ciwo ya cin magani, tsutsotsin har fitowa suke, tunda aka je asibiti likita ya ce sanadiyyar chushe chushe ne ko kuma jima'i da mai ciwon ko duka ya jawo hakan Abdoul ya sa ma ransa chushe chushe ne, ya haɗa kan yaransa sai Niamey, sai de ya turo mata kuɗin magani in ya samu sarari ya leqo ta don cewa yake "kinga ranar zuwa wajen boka" Sai da su Halima suka je Zindar da sallah sannan ta iske laluran Agaysha, kwarai ta tausaya mata nan ta ɗauki alwashin taimaka mata. Bata yi shawara da kowa ba ta shirya komawa har da Agaysha kasancewa Abdoul ya riga su komawa. Da fari taki yarda su tafi tare sai da ta tambayi kawayenta nan suka zuga ta akan taje sai ta haɗa mata tuggun da zai fitar da ita. Ko da Abdoul ya gansu bai ce uffan ba, don yana shirin zuwa wani course a Spain. Ba zai dawo ba sai Satumba. Nan Halima tayi ta haɗa ta da likitocin mata gwanaye masana makamin aiki, sannan ita ce har sako tayi aka haɗa mata magunguna daga Egypt duk ta haɗe ma Agaysha. Basa ko zaman hira, iyakansu gaisuwa sai bayani akan magani in an kawo. Duk bidirin nan daga aljihun Halima ne hakan ya kara mata daraja a idon Abdoul. September 2016....
.
Fari da kyawun Agaysha ya fito sosai, lafiya ya samu tana son ta nemi gafaran Halima amma sam bata ba ta fuska ba, don ko aikin gida bata yarda ta sa mata hannu ba. Ranar da Abdoul zai dawo ta ga abin mamaki don shirin da tayi don tarbansa ko ita da ya yi shekara a France bata yi masa ba a lokacin. Da ya shigo gidan kuwa taga abin mamaki, ita da yara suka tarbo shi tun daga gate, Agaysha na kallon su ta window, yaran nan fa ba na Halima ba amma bata yi son kan raba su da uban su ba. Nan tayi mamakin kyawun hali irin na Halima.
.
Sai da ya kintsa ya zauna cin abinci sannan ta fito tayi masa sannu da dawowa. Ya amsa a hankali ya dago ya kalle ta, ya girgiza da kyan da tayi. Sai ka ce kafin suyi aure. Fitowan Halima ya kalle ta yace "me kike ba my dear da ta chanza haka" dariya Halima tayi ta ce "kace kawai na fita iya kula, ai se Ka biya kawai" "Ai gidanki na nan a Aljanna mai babban daraja" inji Agaysha. Duk sunyi mamaki don Halima bata taɓa mata abu don ta ce ta gode ba ma. Nan ta dage ta roke su gafara, inda ta ke faɗin ta ga illar boka da bokanci, ta ga illar zalunci da mugunta. Nan duk suka yafe mata tare da kara mata nasiha akan tsoron Allah, wuta gaskiya ce haka Aljanna ma gaskiya ce.
.
8th October, 2016
Tun a hanyarsu na dawowa asibiti Halima ke tsokanar su "Ya kamata ku je honeymoon fa, wata 9 kenan fa rabonku da juna, tab ni dai na yafe har sai na haihu nayi arba'in" Ta faɗi tana kallon Abdoul da ke harararta.
.
Asibiti suka je aka tabbatar da lafiyan Agaysha. "wai ido kika sa mana ne haka, mu de tsofai tsofai damu ina zamu kai honeymoon" Ya faɗi yana kashe ma Agaysha ido. "meye na kashe mata ido " Halima ta faɗi tana dariya. "Halima ba fa rayuwar Abdoul kawai kika haska ba, har na wa da yaranki. Allah ya sauke ki lfy ya kara mana kaunar juna" "Aaameeeen!" suka faɗi su duka... And they live happily ever after.... Et il vécurent heureux pour l'éternité.... Godiya ta musamman ga Haj. Mas'ouda Moulaye.
.
Thank you all for sticking around, MAFARKIN ABDOUL is neva complete without u. I Luv u all fisabillillahi.