Jingine jikin gini ta tadda shi ya dafe goshinsa da hannu yayin da hanunsa ke cikin aljihu,sallama ta masa cikin dashashshiyar muryarta da baya fita,ba tare daya waiwayo ba ya amsa. "Ko ina na shiga bazan manta alkhaurin daka min ba,kada kaji haushin iyayenka don sunada gaskiya." kuɗi ya ciro kimanin dubu goma ya sa a hanun Yasmin. "Banso hakan ba Khadija sai dai babu yanda na iya,ko ba dan Mama na ba Fatima nada darajar da ƙima wajena wanda bazan taɓa yin abinda zai ɓata mata rai ba saboda halacci irin ta Fatima ta aureni alhalin tasan bazan taɓa haihuwa ba,kada kice tana so na,ko ƙaɗan sai dai tayi hakanne saboda biyayya ga iyayenmu,Fatima amana ce wurina iyayenta sun rasu tun tana yarinya batada wani gata sai mu wannan dalili ne yasa zan jajirce wajen faranta mata ta ko wace hanya matukar bai saɓawa shari'a ba." "Allah sarki rayuwa,Annabi yayi gaskiya daya ce Allah ya la'anci wanda ya la'anci iyayensa,gashi nan tun kan naje can na fara gani." inji Azeezat cikin rai,zahiri kuwa shiru tayi sai hawaye dake ambaliya a fuskarta. Musa ne yazo akan machine,parking yayi dai-dai inda suke tsaye baki a buɗe yana mamakin meya haɗa Yayansa da Azeezat. "Yaya me ya haɗa ka da wannan kuma? Subhanallah." inji Musa yana ƙokarin sauka. "Kai ma ka santa ne?" inji Isma'il. Sauƙar da idonta tayi kansa,tana ganin shi tasan tata ta ƙare asiri ya taunu. "Hmm Yaya inaga idan baka daina yarda da mutane da wuri ba zaka jefa kanka cikin bala'i." Isma'il kansa a ƙulle ya ce "Kasan wani abu game da ita ne?" gyara parking yayi ya ɗauko labarin Azeezat tun daga farko ya basa,cikin ɓacin rai ya wanke ta da zafafan mari. "Dama ke ba mutuniyar Allah bace,maƙaryaciya ta Allah ma taki ba,tunda kika saka iyayenki zubda hawaye sai ke ma kinyi,indai kuka ne yanzu kika fara yi,rayuwar ƙunci kuwa sai ta ishe ki Allah ya wadaran hauhuwa irin taki." fizge ƙuɗin daya basu yayi ya kureta cikin layin ma gaba ɗaya. Shigarsa yake faɗawa su Mama sunyi farin ciki sosai da aka gane ta tun wuri.
Goya ƴarta tayi ta so ma tafiya ba tare da sanin inda ta nufa ba,tsananin yunwa ta sa ƙafarta harɗewa da ƙyar take ganin gabanta,jiri ne ke neman ɗaukarta ta yi gaggawar kunce Yasmin ta zauna ƙarkashin bishiya,ruwa aka fara kasancewar garin da hadari,rungume ƴarta tayi sanyi na shiga jikin duka su biyun,gartin maza ne kusan biyar suka hangosu yayin wucewa cikin muryar maye ɗaya ya ce "Ya Baba ga nama fa kawai muje mu kwashi ga ra." Azeezat najin haka ta mike a guje suka fara binta,gudu take sosai ba tare da waiwaye ba,ganin saura ƙiris su cin mata ta faɗa wani ɗan ƙaramin gida da akayi tsa'a a buɗe yake. Matashiyar mata wanda take sanye da kananun kaya riga da wando,wanka take cikin ruwan sama,saƙarwa Azeezat murmushi tayi lokacin da sukayi ido biyu "Shigo mana mata kuma kya tsaya a bakin ƙofa." takowa tayi a hankali ta isa inda wannan matar ke tsaye. "Na kula sanyi kuke ji,shigo daga ciki." ba musu ta bita direct ɗaki ta kaita ta basu sabon kaya itada Yasmin,shayi da bread ta kawo masu dama ta haɗa masu tea mai ƙauri. Bayan sun kammala Hajiya Rabi ta dube ta ta ce "Hala daga unguwa kike ruwa ya riske ku,yaya sunarki." "Sunana Azeezat." "Na shiga uku karde kece Azeezat ɗin Abdul da ake faɗa?" cike da kaurin murya take faɗa. Hawaye kawai take batada ta ce wa shikenan kowa yaji labarin abinda ta aikata,lallai na zalunci kaina amma Allah na gani nayi nadama kuma na tuba. "Allah bazai taɓa ƙarɓan tubarki ba tunda Mahaifinki ya mutu ba tare da ya yafe miki ba,maza ki bar min gida kafin na miki shegen duka." "Ba sai kin koreni ba zan bar miki gida,amma ki sani yafiya a hanun Allah take kuma har gobe ina kyautata zaton Ubangiji ya ƙarɓi tubana." hanun ƴarta ta ja suka fice daga gidan Allah yasa ruwan ya ɗan tsagaita. Gara-ramba kawai suke a titi babu mafaka,tana tsaye bakin kwalta baƙar mota ƙirar Marcidi ya tsaya dai-dai inda take,sauke glass ɗin motar yayi,ganinshi sai daya sa ƴaƴan cikinta kaɗawa "Alhaji dama baka mutu ba?" abinda ya fara fitowa a bakinta kenan. "Ban mutu ba,amma na kawo miki albushir ɗin mutuwarki,da farko dai bari na datse alakar dake tsakanin mu,ni Alhaji Mamu na sake ki saki ɗaya,biyu,uku." murmushi tayi hakan ya mata daɗi sosai "Da baka zo ba ma da kaina zanje na sameka kuma dole ka sake ni,tafi nono fari wallahi amma ina so ka sani sakin da kamin ba zai taɓa datse alakarmu ba don ko ba komai Yasmin jikarga je yar gidan ɗanka,ko ince agola a wurinka matsayi har biyu ai ba wasa bane." murmushi yayi mai ɗauke da fassarori,yana mata kallon sha-sha-sha,mika mata takardar yayi "Karanta abin jikin paper nan nada muhimmanci ga rayuwarki yakamata ki sani." sauke glass ɗinsa yayi ya figi motarsa a guje. Zuciyarta ce ta fara harbawa don babu shakka tasan ba alkhairi ne zai kawo Alhaji Mamu ba,ware takardar take a hankali harta gama abinda idonta ya fara sauka a kai ne ya matuƙar razana ta a tsorace ta ce "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,Astagfirullah wa atubu ilaihi." hawaye ta fara sosai tana sheƙar kuka.
[9/21, 4:35 PM] Kawallie Hafsah💖💋🌹: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*
_Labarin *AZEEZAT* mai cike da kunci haɗe da nadamar rayuwa_
Story/Written
By
Hafsat Ibrahim Khalil
Cute HapCyyy
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[Karamci tushen mu'amula ta gari]_
Visit to Like our Page-https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatspp
Wattpad
https://my.w.tt/zKU4d0JvE8
Youtube
https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ
```Dedicated to my life Allah ya maka rahama tare da salihan bayi Abbanah```
*When you fail you learn from the mistakes you made and it motivates you to work even harder.*
Page 45~46
____________📲Jingine jikin gini ta tadda shi ya dafe goshinsa da hannu ɗaya yayin da ɗayar hanunsa na cikin aljihu,sallama ta masa cikin dashashshiyar muryarta da baya fita,ba tare daya waiwayo ba ya amsa.
"Ko ina na shiga bazan manta alkhairin daka min ba,kada kaji haushin iyayenka don suna da gaskiya duniya cike take da mugayen mutane musamman ma ni da baka da wata masaniya a kai na." kuɗi ya ciro kimanin dubu goma ya sa a hanun Yasmin.
"Banso hakan ba Khadija sai dai babu yanda na iya,ko ba dan Mama na ba Fatima nada daraja da ƙima wajena wanda bazan taɓa yin abinda zai ɓata mata rai ba saboda halacci irin ta Fatima ta aureni alhalin tasan bazan taɓa haihuwa ba,kada kice tana so na,ko ƙaɗan sai dai tayi hakanne saboda biyayya ga iyayenmu,Fatima amana ce wurina iyayenta sun rasu tun tana yarinya batada wani gata sai mu wannan dalili ne yasa zan jajirce wajen faranta mata ta ko wace hanya matukar bai saɓawa shari'a ba." "Allah sarki rayuwa,dama biyayya ga iyaye na kai mutum irin wannan matsayi da Fatima ta samu,lallai nayi watsi da dukkanin dama ta akan banza Abdul,Allah ya isa na. Annabi yayi gaskiya daya ce Allah ya la'anci wanda ya la'anci iyayensa,gashi nan tun kan naje can na fara gani." inji Azeezat cikin rai,zahiri kuwa shiru tayi sai hawaye dake ambaliya a fuskarta.Suna cikin wannan zullumin Musa yazo akan machine,parking yayi dai-dai inda suke tsaye baki a buɗe yana mamakin meya haɗa Yayansa da Azeezat.
"Yaya me ya haɗa ka da wannan kuma? Subhanallah." inji Musa yana ƙokarin sauka. "Kai ma ka santa ne?" inji Isma'il. Sauƙar da idonta tayi kansa,tana ganin shi tasan tata ta ƙare asiri ya taunu. "Hmm Yaya inaga idan baka daina yarda da mutane da wuri ba zaka jefa kanka cikin bala'i." Isma'il kansa a ƙulle ya ce "Kasan wani abu game da ita ne?" gyara parking yayi ya ɗauko labarin Azeezat tun daga farko ya basa,cikin ɓacin rai ya wanke ta da zafafan mari. "Dama ke ba mutuniyar Allah bace,maƙaryaciya ta Allah ba taki ba,tunda kika saka iyayenki zubda hawaye sai ke ma kinyi,indai kuka ne yanzu kika fara yi,rayuwar ƙunci kuwa sai ta ishe ki Allah ya wadaran haihuwa irin taki." fizge ƙuɗin daya basu yayi ya koreta cikin layin ma gaba ɗaya. Shigarsa yake faɗawa su Mama sunyi farin ciki sosai da aka gane ta tun wuri.
Dandazon Yara ta gani ana raba masu sadaka itama taje ta shiga layin,nan ma bata tsira ba sai da mutumin ya mammake ta,yara suka watsa mata ƙasa da duwasu,da waka,jefa haka aka rakata bakin hanya.
Goya ƴarta tayi duk ta galabaita tana azabtuwa matuka, tafiya take ba tare da sanin inda ta nufa ba,tsananin yunwa ta sa ƙafarta harɗewa da ƙyar take ganin gabanta,jiri ne ke neman ɗaukarta ta yi gaggawar kunce Yasmin ta zauna ƙarkashin bishiya tana sauke numfashi sama-sama,ruwa aka fara kasancewar garin da hadari,rungume ƴarta tayi sanyi na shiga jikin duka su biyun,kartin maza ne kusan biyar suka hangosu yayin wucewa cikin muryar maye ɗaya ya ce "Ya Baba ga nama fa kawai muje mu kwashi ga ra." Azeezat najin haka ta mike a guje suka fara binta,gudu take sosai ba tare da waiwaye ba,ganin saura ƙiris su cin mata ta faɗa wani ɗan ƙaramin gida da akayi tsa'a a buɗe yake.
Matashiyar mata wanda take sanye da kananun kaya riga da wando,wanka take cikin ruwan sama,saƙarwa Azeezat murmushi tayi lokacin da sukayi ido biyu "Shigo mana mata kuma kya tsaya daga bakin ƙofa." takowa tayi a hankali ta isa inda wannan matar ke tsaye. "Na kula sanyi kuke ji,shigo daga ciki." ba musu ta bita direct ɗaki ta kaita ta basu sabon kaya itada Yasmin,shayi da bread ta kawo masu dama ta haɗa masu tea mai ƙauri. Bayan sun kammala Hajiya Rabi ta dube ta ta ce "Hala daga unguwa kike ruwa ya riske ku,yaya sunarki." "Sunana Azeezat." "Na shiga uku karde kece Azeezat ɗin Abdul da ake faɗa?" cike da kaurin murya take faɗa. Hawaye kawai take batada ta ce wa shikenan kowa ya san da labarinta,"lallai na zalunci kaina amma Allah na gani nayi nadama kuma na tuba." "Allah bazai taɓa ƙarɓan tubarki ba tunda Mahaifinki ya mutu ba tare da ya yafe miki ba,maza ki bar min gida kafin na miki shegen duka." "Ba sai kin koreni ba zan bar miki gida,amma ki sani yafiya a hanun Allah take kuma har gobe ina kyautata zaton Ubangiji ya ƙarɓi tubana." hanun ƴarta ta ja suka fice daga gidan Allah yasa ruwan ya ɗan tsagaita. Gara-ramba kawai suke a titi babu mafaka,tana tsaye bakin kwalta baƙar mota ƙirar Marcidi ya tsaya dai-dai inda take,sauke glass ɗin motar yayi,ganinshi sai daya sa ƴaƴan cikinta kaɗawa "Alhaji dama baka mutu ba?" abinda ya fara fitowa a bakinta kenan. "Ban mutu ba,amma na kawo miki albishir ɗin taki mutuwarki,da farko dai bari na fara datse alakar dake tsakanin mu,ni Alhaji Mamu na sake ki saki ɗaya,biyu,uku." murmushi tayi hakan ya mata daɗi sosai "Da baka zo ba ma da kaina zanje na sameka kuma dole ka sake ni,tafi nono fari wallahi amma ina so ka sani sakin da kamin ba zai taɓa datse alakarmu ba don ko ba komai Yasmin jikarka ce yar gidan ɗanka,ko ince agola a wurinka matsayi har biyu ai ba wasa bane." murmushi yayi mai ɗauke da fassarori,yana mata kallon sha-sha-sha,mika mata takardar yayi "Karanta abin jikin paper nan nada muhimmanci ga rayuwarki yakamata ki sani." sauke glass ɗinsa yayi ya figi motarsa a guje.
Zuciyarta ce ta fara harbawa don babu shakka tasan ba alkhairi ne zai kawo Alhaji Mamu ba,ware takardar take a hankali harta gama abinda idonta ya fara sauka a kai ne ya matuƙar razana ta a tsorace ta ce "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,Astagfirullah wa atubu ilaihi." hawaye ta fara sosai tana sheƙar kuka.
"Yanzu shikenan inada cuta mai karya garkuwar jiki? Ya Rabbil izzati! Tabbas duk wanda baiji bari ba zai ji jiki ya Allah na roƙe ka kada ka ƙarɓi raina face sai na haɗu da iyayena sun yafe min,ya Ubangijin sammai da ƙassai,ya mai gafara da ƴantarwa,ya mai maida dare yini,kai ne kace mu roƙe ka zaka amsa mana sannan kace kana son masu nemar yafiya,kai ka ƙira kanka afuwun gafur,Allah na tuba taubatan nasuhan,Ya Allah ya yafemin,ko a yanzu naga ishara na ɗauki lessons,na lalata rayuwata Abdul ka cuce ni haɗuwa da kai ƙalubale ne wanda bashida ranar ƙarewa."
Tafiya ta ƙara so mawa kanta na sara mata sosai,wannan labarin ya matuƙar ɗaga mata hankali gani take kawai kamar yanzu zata mutu,sign both ta gani gaba da ita kaɗan ta tsaya karantawa, *KHALIL'S DELIOUS BEKERY* ta gani jiki,share fuskarta tayi ta shiga direct wurin cike yake da ƴan mata wanda shekarunsu bazasu ɗare na ta ba kowanne da aikin daya ke,sallama ta masu ta bukaci a nuna mata mai wurin,babu wanda ya kulata cikin ƴan matan sai ma kallon raini da suke mata. Hajiya ladi ce ta zo inda Azeezat ke tsayi cikin gadara ta ce "Ke mahaukaciya meya shigo dake nan,oya out i don't want rubbish." kafin ta bude baki ta sake faɗin "Security! Security! Come and let her out abeg" cikin hanzari suka zo suna janta kamar tsunma har waje kafin suka barta. "Munin abin da na aikata har ya kai jama'a su dinga kyamatata kamar haka." kwanciya tayi a wurin tare da ɗaura kan ƴarta a jikinta ta fara hawaye.
Comment
Like
Share and vote
[9/21, 4:36 PM] Kawallie Hafsah💖💋🌹: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*
_Labarin *AZEEZAT* mai cike da kunci haɗe da nadamar rayuwa_
Story/Written
By
Hafsat Ibrahim Khalil
Cute HapCyyy
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[Karamci tushen mu'amula ta gari]_
Visit to Like our Page-https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatspp
Wattpad
https://my.w.tt/zKU4d0JvE8
Youtube
https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ
```Dedicated to my life Allah ya maka rahama tare da salihan bayi Abbanah```
_*Il y a des gens qu'on reconnaît immédiatement comme des amis. Vous vous sentez à l'aise avec eux parce que vous savez que vous ne serez jamais,jamais en danger*_
_Special greetings for U my motivators! Hrt you all_
Page 47~48
______________📲Masu sharan kwalta (BOSEPA) ne ke sanitation nan ma suka ta da ita maza ta bar wurin dan wurin kwanciya bane inji ɗaya daga cikin ma'aikatan. Magiya ta masa kan ya taimaka mata da ƙyar da zage-zage ya wurga mata naira hamsin,bata raina ba tayi godiya da sa albarka,Napep ta hau ta ce ya kaita Tudun wada,tafiya suke har aka ƙira Magrib,tun tana gane wurin har ta daina. "Mai Napep ina zaka kaini ne?" ta tambaya dan abin ya fara bata tsoro,bai ce kala ba,ya juya ya fesa masu powder,bacci ne ya ɗauketa take bata ƙara sanin inda take ba.
Buɗe ido tayi ta ganta a wani wuri daban ɗaki ne mai shegen tarkace gashi baƙi ƙirin,jikinta yayi tsami sosai dukan data sha ba ƙarami bane nishi kawai take ta kasa faɗar komai. "Ogo ta tashi." wani ya faɗa hakanne kuma ya bata tabbacin ba ita kaɗai bace a ɗakin.
"Bawan Allah me na maku kuka kawo ni nan,ku barni da abinda nake ji ma ya ishe ni ku sake ni dan Allah." cewar Azeezat cikin kuka.
"Ke ki mana shiru nan ba wurin kuka bane kuma kar kiyi tsammanin fita daga nan." Inji wannan gayen. Bataliyar ƴan ta'addan suka rako ogansu ɗakin dukkanin su babu mai kyan gani,kujera aka ɗauko masa ya zauna kusa da Azeezat,shin-shina ta ya fara tamkar maye, janyewa take tana baya-baya don a tsorace take. "Azeezat Abdul! Lallai soyayyarki ga abdul ta kai akirata *MAKAUNIYAR SOYAYYA* ya akayi kika makance,kika ƙasa fahimtar komai,kika zaɓi katon banza akan mahaifanki? Anya kodai kinada taɓin hankali ne.?" "Ko wanne ɗan adam ajizine yakan iya aikata kuskure,sannan kuma babu laifi idan ya gyara tabbas Ubangiji zai yafe masa." "Dan adam ajizi ne tabbas amma ke ba ajizanci kikayi ba ganganci ne,sannan kuma ba kuskure kika aikata ba,babbar laifi ne wanda bazai taɓa gogewa ba." "Ko ma me zaka faɗa ka faɗa,abinda na sani kawai shine nayi nadamar rayuwa ta ta baya kuma na shirya tsaf domin na gyara gaba na." "Kar ki ɓata lokacinki,Allah bazai saurareki ba." "Tony!" "Na'am Zeezan Abdul." "Da farko dai ka daina haɗa sunana da na Abdul,na biyu kuma ka kunce ni na tafi." "Zan kunce ki bayan na faɗa miki abinda yasa na ɗauƙo ki." "Inajinka sai ka faɗa da sauri." "Kina burgeni Azeezat saboda rashin tsoronki,hakan ne yasa nake so mu fara aiki tare tunda babu Abdul,ko ba komai nasan zaki inganta rayuwarki da wannan gara-ramba da kike a titi." "Mtw amma Tony ka raina min wayo,kana tinanin zan sake komawa rijiyar da Allah ya tsamo ni daga ciki ne? Ko yau na mutu zanyi farin ciki domin Allah ya ganar dani gaskiya kaima ina maka fatan shiriya kuma kada ka manta da sannu kaima zaƙaje inda Abdul yaje indai cutar wa ne aikin ku." dariya yayi sosai kafin ya ce "Very soon Abdul zai fito mu cigaba da harka tare waya gaya miki ana hukuncin gaskiya a wannan ƙasar tamu." "What! Kana nufin za a sake shi?" ta faɗa a tsorace. "Ina kyautata zaton hakan,dan haka gwara ma ki zo a ɗaura daga inda aka tsaya." "Bazanyi ba,bana bukata." okay ya faɗa tare da bada umarnin a sake ta ta tafi,a bisa umarnin Tony aka fidda ita daga wurin,bayannan ya ce "Olu,na baku nan da 24hours ku tabbatar kunyi sanadin da Azeezat zata nemi kuɗaɗe masu yawa,idan ta rasa zata amshi tayi na."
Wane ne Tony?
Tony kasurgumin ɗan ta'adda wanda yayi suna wajen safaran cocaine,coiden,da dai sauran miyagun kwayoyi,yana da ƙarfi wajen gwamnati hakan ne yasa har yau an kasa kamasa sai dai a kame yaransa,lokacin da su Ammar suka kore Abdul ya shiga halin ƙunci na rashin madafa,bashida komai hatta wurin kwana babu balle batun abinci ga kuma Azeezat da Yasmin da suka maƙale masa yayi-yayi ya yageta amma a lokacin haka ta rintse ido tace ta ji kuma ta gani zata zauna dashi a kowane irin yanayi,ƙyaleta yayi ba dan yana ƙaunar haɗa inuwa da ita ba, a faɗarsa idan taji wuya zata nemi barinsa,suna cikin wannan yanayi suka haɗu da Tony a bakin kogi daga nan abota ta kullu,ahaka har ya jashi suka fara tsaida ƙwayar tare,haka Azeezat ma ta fake ta tallan goro amma ba goron shi kaɗai bane zallar drugs ne kuma tanayin hakanne dan ta kasance da Abdul har zuwa lokacin da aka kame sa. Ƙaɗan daga cikin labarin Tony kenan.
A wannan tsuhuwar daren ta fita goye da ƴarta,da kyar take iya jefa kafarta tsantsar gajiya ne ke damunta ga bala'in yunwa da take ji,haushin kare ta fara ji kuma da alama a kusa da ita ne,dunkulewa tayi waje ɗaya jikinta na ɓari.
"Waye anan." taji muryar mace,sai da aka ƙara mai-maita tambayar before ta ce "Sace ni akayi aka kawoni nan dan Allah kada ki cutar dani." haska ta da touch tayi ta ƙare mata kallo. "Taso ki biyo ni." inji wannan matar. Da ƙyar ta iya mikewa,sunyi tafiya sosai kafin suka isa bukkar matar.Yanayin cikin ɗakin kamar babu rai dake rayuwa a cikin yana wari sosai,toshe hanci Azeezat tayi matar na lura da hakan, ta gara ta da bango har sai da kanta ya fara jini,dafe wurin tayi ta ce "Ashh." "Duk wanda na kama kashe sa nake kafin na kawo gawarsa ɗakina,kinci sa'a Allah ya saka min tausayinki a rai na ba dan haka ba tuni na kashe ki,shine kike toshe hanci? Wato ɗakina na wari ko." cewar matar cikin murya mara daɗi,"K...kiyi hakuri dan Allah." "Da ban hakura ba kashe ki zanyi,ni bana dogon zance da mutane tsari na shine kar a shiga tsabgata idan ban kasa da mutum ba,na tsani rashin gaskiya bana son ƙarya idan kin amince zaki zauna dani to dole ki kiyaye kuma duk abinda na saka ki zakiyi." "Namiki alkawari bazaki same ni da saɓa miki ba." "Idan kika saɓa,ki tabbatar ranar ki ce ta zo ƙarshe bana so ki ƙara ce wa komai." shiru tayi a ranta tana ce wa wacce irin mata ce wannan,fitila ta kunna ya haske ɗakin,ƙashi da rai na mutane ne dayawa sosai Azeezat ta tsorata,gefe guda kuma gwala-gwale ne da azurfa masu ɗauke ido,tana so tayi tambaya sai dai kuma sharaɗin matar ba a magana idan ba ita ta nema ba,haka nan ta kame bakinta tayi shiru amma a rai tana kyautata zaton ƴar damfara ce matar.
Tabarma ta shimfiɗa masu kusa da wani skulls ba tare da ta ce komai ba,har ta buɗe baki zatayi magana ta tuna da sharaɗin matar tayi shiru,ƙwanciya tayi tana mai zayyanu abubuwa daban-daban a ranta,kawo yanzu ta salwantar da komai,tasan rayuwarta ba zata taɓa gyaruwa ba da wannan tinanin bacci ɓarawo ya sace ta.
Har wurin yaran Tony suka zo dama kullum suna kallon matar amma sun rasa meya ajiyeta a daji tana mace,komawa sukayi suka faɗa wa Tony daga nan yace su tabbatar sunyi shirin tinkarar wannan matar,sai da suka tabbatar ta fita farauta sukaje gwal da azurfa kawai suka kwashe masu yawa lokacin Azeezat ɗin ma ta zagaya baya.
Da yammaci matar da dawo babu dayawa daga cikin gwala-gwalen,ranta ya ɓaci sosai da duba ko ina babu Azeezat,ihun matar taji lokacin tana bayan gidan. "Tabbas an taɓo wannan matar." "Ina kike yau sai na kashe ki dama na faɗa miki bana ƙaunar maha'inci." ta faɗa cikin kaushin murya. Juyawa gefe tayi ta ci karo da yaran Tony,zuciyarta ta ƙara harbawa. "Dan Allah karku kashe ni." "Waya gaya miki kashe ki zamuyi,matar nan ma kaɗai ta ishe ki tunda kika sata mata kaya." "Wallahi ba ni na sace mata ba ku taimaka ku fahimtar da ita." "Hmm kinga tafiyar mu dan idan ta riske mu anan kwanan mu ya ƙare." ji take kamar ta bisu dan a rikece take,har sun fara tafiya ta ce "Ku jirani dan Allah." "Tab babu inda zaki bimu,Tony da kansa jiya ya miki tayin ki zauna amma kika nuna masa bakya bukata,yanzu gashi ai." "Dan Allah ku taimaka min bana so na mutu ban haɗu da iyayena ba." "Bazaki bimu ba sai kin amince zaki fara aiki tare da mu." shiru tayi tana nazari can ta ce "Na amince,amma dan Allah ku tsaya naje na ɗauko Yasmin." "Yasmin an kashe ta a gabanmu,bamuda lokaci kizo muje." "An kashe Yasmin! Na shiga uku na wayyo Yasmin." kuka ta fara sosai,taɓe baki sukayi tare da fara tafiya babu yanda ta iya haka ta bisu ranta na sosa.
Yana ganinta ya so ma dariya da ƙarfin gaske irin dai na marasa tausayi,sai da yayi mai isarsa ya ce "Kada ki damu dan an kashe yarinya ƴar karama wanda take ɗauke da HIV,taimaka mata ma akayi domin kuwa bazata rayu ba dama,abinda nake so da ke shine ki manta da kowa da komai kamar yanda mutane ke ƙyamatar ki ki ƙyamace su,kada ki tausaya wa kowa dan ke ma ba a tausaya miki ba,babu wanda ya taimaka miki lokacin da kika bukaci taimako daga ciki harda iyayenki,dan haka ki manta da kowa da komai tubarki batada wata amfani." "Na naimi yafiya an gaza yimin,dan haka na shigo harka dumu-dumu a dama dani." cewar Azeezat cike da ƙwarin guiwa. Sosai Tony yaji daɗi fuskarsa shimfiɗe da murmushi ya ce "Good girl."
_Ƙalubale gareku jama'a,a duk lokacin da mai laifi ya tuba ya fara neman taimako,kuka tabbatar yayi taubatan nasuha,ƙarɓarsa hannu biyu shine zai ƙara ingantashi ba ƙyamatarsa ba,idan aka guje masa zuciyarsa zata ke ƙase ta sake komawa gidan jiya da wannan nke faɗakar da al'umma da su gyara dan Allah mu dinga kai zuciya nesa musamman iyaye._
_INA ALFAHARI DA MASOYANA A DUK INDA KUKE_
[9/21, 4:36 PM] Kawallie Hafsah💖💋🌹: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*
_Labarin *AZEEZAT* mai cike da kunci haɗe da nadamar rayuwa_
Story/Written
By
Hafsat Ibrahim Khalil
Cute HapCyyy
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[Karamci tushen mu'amula ta gari]_
Visit to Like our Page-https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatspp
Wattpad
https://my.w.tt/zKU4d0JvE8
Youtube
https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ
```Dedicated to my life Allah ya maka rahama tare da salihan bayi Abbanah```
_*The only way to permanently change the temperature in the room is to reset the thermostat. In the same way, the only way to change your level of financial success 'permanently' is to reset your financial thermostat. But it is your choice whether you choose to change.*_
Page 49~50
____________📲Ko ina ta duba babu Azeezat babu dalilinta,tayi mamaki da ganin ƴarta gashi sai kuka take,murmushi tayi ta share guntun hawayen dake sauki mata a ranta tana tunu abubuwa dayawa wanda sune silar ruguje mata rayuwa, durkusawa tayi ta ɗauketa tana jin ƙaunar ƴar a ranta.
Karan hancinta taja ta ce "Zaki cigaba da zama tare dani,zan koya miki yanda ake ɗaukar fansa da dukkanin abinda ya dace ki koya kuma dole ne mu bar wannan wurin mu koma inda baza a taɓa samun wani halitta ba bare muyi kokarin haɗa rayuwarmu da tasu." Yasmin ko sai gwaranci take tana wangale baki ga hawaye caɓa-caɓa a fuskarta.
Ɓangaren Azeezat kuwa,sabon rayuwa ta so ma ta manta da komai da kowa,sai dai wata zuciyar na tuna mata da alhakin iyayenta dake kanta ga kuma fargaban HIV da take ɗauke dashi duk da ta fara ɗauƙar magunguna.
Tana zaune kan kujera tayi nisa wajen tinanin yanda rayuwarta ke tafiya,tana matuƙar jin bakin cikin kasancewa mara sa'a da tayi,ji tayi an taɓa ta ta baya firgit ta dawo hayyacinta. Ajiyar zuciya ta sauke yayin da idonta suka sauka kan Tony,murmushi ya sakar mata tare da faɗin "Big girl kina jin daɗinki fa." gyara zama tayi ta ce "Idan har kana so naji daɗi ka mayar dani gidanmu tunda na kawo maka cigaba sosai a rayuwarka." "Kin riga kin cika min burina tunda na samu dollars yanzu zan iya kaiki gidanku,amma da so samu ne muje a ɗaura mana aure idan yaso sai mucigaba da chilling tare." "Really!" ta faɗa tana murmushi,murmushin ya mayar mata. "Amma dai kasan ina ɗauke da cutar Hiv ko?" "Hhhhm to menene a ciki ai nima ina dashi." bushewa tayi da dariya,tana jin daɗi ta samu mijin aure. "Sai dai da sauran rina a kaba." inji Tony "Akwai matsala ne?" inji Azeezat. "Daina safaran Cocaine bazai taɓa yiwa ba,idan har ka shiga harkar to ba a fita sai dai mutuwa." "To me kake nufi." cewar Azeezat cikin rashin fahimta. "Tambaya mai kyau. Burinki iyayenki su yafe miki ko?" da sauri ta kaɗa masa kai. "Fine,na amince muje kamar yarda na faɗa,amma da sharaɗi." "Menene sharaɗin?" "Sharaɗin shine ki nuna masu kin tuba da aikata laifuka gaba ɗaya,idan sun yafe miki sai ki fidda ni a matsayin mijin da zaki aura kinga daga nan shikenan sai mu wuce ƙasar waje mu cigaba daga inda aka tsaya." smilling tayi ta ce "Tony you are so smart! I like you."
A take ta tashi ta shirya suka ɗau hanyar Damaturu,awa biyu ne ya ɗaukesu zuwa cikin garin,tsuhuwar gidansu Abba ta kaisu dake batada labarin sun canza gidan,makota ta shiga Allah yasa akwai waɗanda suka san inda suka koma da zama.
Abba,sunyi mamakin ganin Azeezat matuka dan babu wanda yayi tsammanin dawowarta. Ƙasa shigowa tayi ta tsaya da ga bakin kofa tana kuka sosai,Umma ce taje da gudu ta rungumeta tana kuka. "Khadija ashe zaki dawo gida,ke nake gani ko idona ne ke min gizo,Alhamdulillah tsarki ya tabbata ga Allah." cin karfinta kukan yayi tayi shiru da maganar.
"Me kika dawo kiyi,ki fice mana da gani na miki iyaka da mu har abada,bana sonki bana ƙaunarki na sadaukar wa duniya ke duk da na tabbata ko ita duniyar sai dai tayi Allah wa dai da ke,kin azabtar dani Azeezat kin sani kuka ba dare ba rana,kin azabtar da zuciyoyinmu,ke ce silar rushewar farin cikinmu,kinyi silar mutuwar Abi har aka binne shi baki zo kin nemi yafiyarsa ba,kina tinanin waɗannan munanan abubuwan abin mantawa ne?"
"Ummi na tuba,duniya ta shiryar dani dan Allah kuyi hakuri ku yafe min nasan na kasance mara hankali da tinani a baya,na azabtar da ku,amma ku sani tun wannan lokacin ban taɓa jin daɗin rayuwata ba har zuwa yanzu da na zo nemar afuwarku, na tabbata rashin sa'a ta nada nasaba da fushi da kuke dani,Abba na roke ku dan Allah ku yafemin nayi nadamar abinda na maku a baya." "Yi shiru Azeezat komai ya wuce inji Abba,zuciyarsa ta karaya Ummi kawai yake tausaya wa yanda tai wani abin tausayi.
"Ina babu abinda ya wuce." inji Ummmi still tana kuka. Mamakin furucinta sukayi karde ace haryanzu bata yafe mata ba. "Karkiyi haka Habiba,yarinyar da muke fata ta dawo gida Allah ya kawota kamata yayi muji daɗi ba ƙara tunzura ba,idan kika daɗa korarta ina zata faɗa? Gidan jiya ne fa,to menene amfaninsa." inji Abba cikin tattausar murya. "Ƙwarai zancen Malam gaskiya ne kiyi hakuri ki yafe mata Habiba." da kyar suka lallashi Ummi tace ta yafe mata,babu ɓata lokaci aka kira su Kudrat aka faɗa masu gaba ɗaya suka dawo gida taya murna.
Bayan kwana biyu still Aliyu ya nuna yana buƙatar ya aureta sai dai taki amince masa,dama kuma bai fara kai maganar gaban iyaye ba haka dai suka watsar da zancen tsakaninsu.
Tony ta fidda matsayin mijin aure da farko basu amince ba duba da bashi da kamala ta mutanen kirki,daga bisani kawai suka aura ma Tony don ta nace akan lallai sai shi.
Bayan ɗaurin aure Tony ya masu VZn fita ƙasar waje,kamar yarda ya alƙarwarta mata,sai yau Allah ya kawo ranar kwanciyar hankalin Azeezat,iyayenta sun yafe mata tayi aure.
Niko nace menene amfanin tuba ba dan Allah ba Azeezat." taɓe baki tayi ta ce "O ke dai HapCy akwai ki da shishigi yanzu har london ɗin sai da kika biyo ni." Murmushi kawai nayi,nayi wucewata.
Zuwarsu London bata haifar da ɗa mai ido ba don Tony ya ƙara jefa ta a harkar fashi,Kidnapping,safarar ƙwaya da sauransu.
Numfashi ta sauke tare da faɗin "Wannan shine tarihin rayuwar Azeezat,Mahaifiyarki kenan." hawaye kaca-kaca a fuskarta sai shan majina take,ranta yayi baƙi irin,idonta ya dishashe,kunnuwarta basu taɓa jin tarihi mafi muni kamar wannan ba, "Lallai rayuwata bata samu kyakywar asali ba,zan iya ce wa nafi kowanne halitta rashin sa'a a duran ƙasa,wannan wacce iriyar rayuwa ce,Azeezat kin gama da rayuwata,meyasa kika kasance uwa a gareni,banga amfanin rayuwata ba dama kashe kaina nayi na huta da wannan takaicin rayuwar." kasa cigaba tayi,don kukan ne ya kufce mata mai tsuma rai,kanta na sara wa sosai bata taɓa shiga ƙunci irin na yau ba. "Ba kuka zakiyi ba Yasmin,zage dantse zakiyi ki shirya don ɗaukar fansa,ki naimu inda Mahaifiyarki da Mahaifinki suke ki gana masu azaba don haryanzu suna nan suna zaluntar bayin Allah." "Yanzu kina nufin haryanzu suna raye?" "Tabbas suna raye cikin jin daɗi ma kuwa." "Idan kuwa hakane nayi alƙawari sai na kashe su na gasa gawarsu na bawa karnuka su ci,bayan na kwashe dukiyar su da duk wani abinda suka tara na rabawa marasa ƙarfi." "Zan baki duk wata gudun muwa da kike bukata,zan tayaki ganin cinma burinki." "Ba Buri bane uwar ɗakina,muradi ne."
Murmushi tayi suka rungume juna.
_Alhamdulillah_ _Alhamdulillah_ _Alhamdulillah_
_Ina godiya ga subhanahu wata'ala daya bani damar kammala book one na wannan littafin naku mai farin jini wato MAKAUNIYAR SOYAYYA, I ask Allah to forgive all my mistakes nd bad did, fatana shine ayi amfani ya kyawawan abubuwa da suke ciki tare da watsi da marasa amfani_
_Kunyi yawan da bazan iya lissafo ku ba, sai dai idan nace masoyana tabbas daku nake Allah ya bar kauna🥰_
_Sai mun hadu a Book 2 wanda zai zo maku da suna DAREN JIYA, labarin YASMIN wanda ta tashi a hanun 'yar ta'adda, wanda batasan komai ba sai kashewa, ta ƙunsa mata rashin tausayi da imani,bata san gata ba bare jin daɗi,karde na cika ku da surutu amma ya kuke tinanin YASMIN zata zama? Shin bakin tukunya ce zata haifar da farar tuwo ku a'a? Ku biyoni don samun cikakkiyar bayani, littafin zai zo maku ne kan farashi mai sauki wato SHARHI 😍😅 sai dai bata tinanin zan fara typing ɗinsa nan kusa saboda dalilai nawa masu ƙarfi,_
*ƁANGAREN RAYUWAR AZEEZAT YA FARU NE DA GASKE,TRUE LIFE STORY SAI DAI MAFI YAWANCIN ABUBUWAN CIKIN NOVEL ƊIN WANDA BAI SHAFI AZEEZAT BA NE FINCTIONS,KUMA NAYI HAKANNE DAN ƘARAWA MASU KARATU ARMASHI*
~KUNDIN TSAFI~
~DARA TACI GIDA~
_Suna nan tafe da yardar Ubangiji🥰_
_Thanks for enjoying! Urs Lovely💃🏼_
_REAL HAFSAT IBK_
08130035170