Se da suka kara introducing kan su ma junan su, a yanda Janan ta lura da Annabelle tana da sakin fuska! Hira jefi jefi suke dan yi tunda ba wani sabawa suka yi balle su saki jiki sosai, Janan tace "Wani course zaki karanta?
Annabelle tace ''ai ni returning student ce ina karanta Pharmacy'' ke fa?
Janan tace ''ni sabuwar daliba ce amma through Direct Entry yanzu haka zan karanta Gynecology ne!
''Wow kice ke babba ce, gaskiya nayi sa'an roommate, congratulations Dear!
Murmushi me sanyi Janan tayi mata tana fadin thanks!
******
Haka zaman su ya kasance gwanin ban sha'awa inda Annabelle ta dinga nunawa Janan koina na makarantan! Tare suke fita lectures dan kusan komai iri daya ake musu se dan abunda ba za a rasa ba!
Kusan kullum se sun yi waya da su Ummiey, dan ba karamin kewan ta suke yi ba, ga kuma kudi da dukkan su suke turo mata harda su Yaya Khaleel wai na handouts da Assignment, kwata kwata Annabelle bata bari tayi komai da kudin ta ita take musu wani lokacin ma Janan bata san an bada abu ba tunda bata shige-shige se dai taga Annabelle tayi mata, har girki basa yi se dai Annabelle tayi musu takeaway!
Yau ma kamar kullum Janan sanye da dogon Hijjab har kasa da socks sun fito daga lectures a gajiye suna tafe suna maganan lectures din da aka musu yau, Annabelle tace ''mitchwwwww ni ban san me ya sa ba ban son mutumin nan, lectures din shi is boring ni bana ma gane komai idan na shiga class din!
Janan tace ''ni kuma gaskiya ina ganewa duk da baya da method of teaching amma yana kokari!
Annabelle zata kara magana wayan ta ya fara ringing! Babyn Momma ne ke kiran ta, murmushi tayi sannan ta dauka tana fadin "Babyn Momma nayi fushi da kai, tunda na zo sch din nan sau 2 kawai ka kira ni kaman baka missing dina!
Daga daya bangaren yace ''No Lil Sis ba haka bane ke ma kin san dole in yi missing din ki kwana biyu ban san meke damuna ba ne kawai ina jin kamar wani abu da na rasa yana kokarin dawo min kuma ban se mene ne wannan ba!
Babyn Momma ka dena sa damuwa a cikin ranka kar ka ja ma kanka ciwo pls!
''Thanks Lil Sys shiyasa nake kara son ki!
Hira suka dinga yi harda shirme ma!
Can tace Babyn Momma ga Bestie na da nake baka lbr ku gaisa!
Ki bari wani lokacin yanzu zan dan yi wani abu ne!
Jin tayi shiru alaman ta ji haushi yasa shi fadin "ki ce ina gaida ta kafin in kira mu gaisa da ita!
Yawwa Babyn Momma I love u! Bye! Tayi dropping call din!
Sorry Bestie, na barki ina ta waya, Babyn Momma ne yace in gaishe ki!
Bata san dalili ba taji gaban ta ya fadi, daurewa tayi tace ina amsawa!
Wajen siyan abinci suka je nan sukayo takeaway Janan na mamakin tsadan abincin , ita bata ma yi zaton kudin da Annabelle take kashe musu wajen siyan abinci ya kai har haka ba!
Tafiya suke za su koma hostel se ga wani course mate din Annabelle ya zo wucewa shida yan grp din su yace '' Hi Anny!
Tace hello Sam!
Janan dake gefe taga alaman yana son tsayawa yasa ta matsa can nesa dasu tana jiran Annabelle!
Suma yan group din Sam suka koma gefe!
Sam yace ''wassap Babe, ykk ne?
Tace ''am fyn!
Wai waccan kawar taki me take nufi ne?
Wani harara ta balla mishi tace kamar ya? Ta san halin Sam akwai san matan tsiya irin marasa jin 'ya' yan masu kudin nan ne!
Yace haba ki gane mana ita kullum fuska a daure ga wani abu da take sawa tana yawo a ciki ko irin dan gayun nan ba tayi balle agane ko tana da figure 8 ko.... Be karasa maganan shi ba Annabelle ta dakatar da shi da fadin
''excuse me! Kada ma ka kuskura ka zage ta ko ka fadi wani mugun magana a kanta! Ina ruwan ka da dressing din ta? Ina ruwan ka da shape din ta? Ka ga ka kama kanka ka natsu ita ba irin wawayen emmatan da suke biye maka bane!
Ganin ta dau zafi yasa shi fadin "calm down Babe ba wai na fadi haka bane dan in bata miki rai ba, kawai dai tana burge ni ne'' ya karasa maganan yana shafa kai!
Mitchwwwww taja tsaki sannan tace "whatever! Ni kaga tafiya ta! Har tayi taku biyu se ta juyo tana fadin '' Ehen! Mind u! Daga yau se yau kar ka kara tsayar da ni kana fadin min shirme cuz lokaci na yana da anfani a waje na in kai ba shida anfani a wajen ka! Tayi wucewar ta
Yaji haushin abunda tayi mishi amma Dan dai kawai yana shakkatar ta ne da se ya koya mata hankali!
Wajen abokan tafiyar sa ya koma suka wuce, suna ta tambayan shi abunda ya faru amma ya share dan ba zai iya fada musu wannan abun kunyan ba!
Tana komawa wajen Janan tace "muje!
Duk da taga yanayi Annabelle din ya nuna tana cikin bacin rai bata tambaye ta dalili ba dan ita ba ta san shiga abunda ba a sata ba! Suna shiga daki suka ajiye kayan su da books din su, Janan ta wuce bayi dan yin alwala sbd lokacin sallah yana wucewa sakamakon rike su da Lecturer din su yayi ita kuma Annabelle plate ta dakko ta juye musu abincin tun daga tsaye ta fara ci dai dai lokacin da Janan ta fito daga bayi tana goge ruwan dake fuskan ta! Da sauri Annabelle ta ajiye cokalin tana rufe baki, daria Janan tayi tace ''na riga na kamaki kina cin abinci a tsaye, ai na san ba zaki dena ba kuma na fada miki ba kyau!
Sorry Bestie na dena, na kasa jurewa ne cuz yunwan nan kamar zata kashe ni!
"Aiko se dai ta kashe ki cuz se na idar da Sallah za mu ci punishment din ki kenan!
"Pls kiyi hakuri ba zan kara ba, idan kika ce se kin idar ai se dai ki ganni a sume dan kin iya dogon Sallah kuma in kika idar se kin dade kina Addu'a ni kam ba zan jure jiran ki ba!
"Toh ki fara ci kafin in idar kin ga time ya wuce sosai! Ta janyo Hijjab din ta ta shimfida darduma ta tada sallah!
Babu yanda Annabelle ta iya dole se ta jira Janan din cuz ta saba cin abinci tare da ita yanzu ba zata iya ci ita kadai ba!
Bata ja dogayen surori ba sbd bata so ta shiga hakkin Annabelle!
**
Seda suka koshi sannan Janan tace ''Sis! Gaskiya lokaci yayi da zamu dena siyan abinci a waje muna da komai fa, tunda muka zo sch din nan bamu taba girki ba se dai mu siya haka zamu bar food stuffs din mu su lalace? Kinga almubazzaranci ba kyau sbd wasu na neman ko da kwatan abincin da muke da shi su dinga dafawa!
"Naji kuma na yarda da shawaran ki amma ai akwai kudi sosai kuma duk Friday Babyn Momma ke turo min kudi banda wanda Momma da Dad suke turo min ai ze ishe mu har muyi hutu dan ni gaskiya ban iya girki ba kuma bana yi ko a gida"!
"Ni zan dinga yi kuma zaki iya In Shaa Allah in muna tare!
Thanks Bestie!
Suka yi murmushi a tare!
***
Tun daga ranan suka rage siyan abinci se dai snacks ko abun marmari sbd Janan tana kokarin dafa musu abinci masu dadi!
**
Kowa ya san Janan da Annabelle da kuma yanda suke tafiyar da rayuwar su a sch, yan gulma da sun gansu se su tsaya suna kallon su suna mamakin su! Wasu ma har wajen Annabelle suke zuwa su ta sukan Janan amma da tsiya suke rabuwa dan ita bata yarda a zagi Janan a gaban ta ba!
鈾�
Karatu suke yi sosai dan Jarabawa ta karato, duk abunda Annabelle bata gane ba Janan ke kara mata haske a kai haka duk abunda Janan bata gane ba Annabelle din ne ke kara mata haske akai!
Haka suka yi Jarabawa suka gama cike da jin dadi!
Dad da Momma suka zo daukan Annabelle dan Dr.Godwin baya jin dadi shiyasa be biyo su ba suma din jirgi za su bi! Exchanging address suka yi da alkawarin ziyara, sun so Janan ta bisu su tafi tunda garin su daya amma taki tace ita ma za a zo daukan ta! Babu yanda suka iya haka suka tafi suka barta!
Can ba da jimawa ba se ga Yaya Khaleel da Yaya Saleem sun zo daukan ta! Taji dadi sosai,, suma sun ji dadin ganin ta su suka taya ta kwasan kayanta suka sa a bayan boot suka tafi....
_Rukkybae_馃槒馃槒馃槒
[12/17/2017, 11:11 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [12/17, 7:05 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂も潱: 鉂ゐ煐も櫏鈾b櫊鈾モ櫍鈾犫櫍鈾モ櫍鈾犫櫍鈾b櫏鈾モ櫍鈾犫櫊鈾b櫏鈾b櫊鈾犫櫏鈾モ潳鈾p煐も潳鈾モ櫊馃枻鉂も櫍馃枻鈾モ櫊鈾b潳馃枻 *MATAR DOCTOR* 鈾モ櫍馃枻鉂も潳馃枻鈾b櫊鈾モ櫍馃枻馃枻鉂も櫍馃枻鉂も櫏鈾犫櫏馃枻鉂ゐ煐も櫍鈾モ櫊鈾p煐も櫏鈾狆煐�
_Rukkybae_馃槒馃槒馃槒
馃寪 *HAJOW* 馃寪
*_Hakuri Da Juriya Online Writers_* 鉁嶐煆烩湇馃徎鉁嶐煆�
_Your birthday was on the 14th and page 114 is urs Safiyya Zubairu Aliyu (Sophie Luv) WOW! What a coincidence..... Happy Birthday to u, wish u Allah's Noor and Khair Always! Em sorry 4 d late birthday wishes but is better than none! I love u so much Habibty! Allah ya kawo miji na gari! AMEEN!_馃槝馃槝馃槝
1鈨�1鈨�4鈨�
Sun ji dadin hutun da aka basu kuma hakan yana su daman waya a kai a kai!
Wata ranan Laraba suna waya Annabelle tace ''Bestie gobe ina nan zuwa gidan ku zan tambayi Momma anjima na san ba zata hana ni zuwa but idan na zo kema se kin zo idan mu!
Janan dake tsaye ta dan yi tsalle tare da ihun murna tana fadin ''naji dadi sosai dama ina ta missing din ki nima muna gama waya zan fada ma Ummiey zaki zo kuma nima In Shaa Allah zan zo! Sun taba hira sannan suka ajiye wayan!
Annabelle na fitowa daga dakin ta ta wuce dakin Momma, a gado ta same ta kwance tana duba wani magazine, jin an shigo ya sata dagowa, Annabelle ta gani ta shigo tare da fadin ''Hi Momma!
Tace "Hello Princess!
Gefen kafafun ta ta zauna tana dan danna mata su kafin ta fara fadin "Momma gobe ina so in je gidan su Bestie dazu mu kayi waya da ita na fadi mata zan zo shine nace bari in sanar dake''
"naga alama kina ji da wannan kawar taki!
"Momma, nima kaina na san ina son ta, tana da kirki, tsafta, kamun kai, kyauta ga kokari, bata da yawan surutu kuma it's hardly tayi fushi shiyasa take burge ni kuma nake kara jin ta har raina!
Tunda ta fara magana Momma ta tsaya tana kallon ta se da ta gama sannan tace "lallai Princess wannan irin zuzuta ta haka! Kinyi saan kawa dama ni tunda nake dake ban taba ji yau kin ce ga frnd dinki ba balle har ki zauna kina yabon ta har haka!
"Momma Janan is different, duk yanda zan miki bayani ba zaki gane ba se kin zauna da ita zaki gane haka!
Murmushi Momma tayi sannan tace "goben se ki shirya driver ya kaiki!
Cike da jin dadi ta rungume ta tana fadin ''Thank u Momma, U r d bst! Ta fice daga dakin!
****
Da Yamma Dr. Godwin ya dawo gida yana shaida musu ze tafi Makarfi sannan ga letter nan daga Teaching Hospital Abuja sun turo mishi akan suna so ya fara aiki da su! Sun yi murna sosai tare da mishi Addu'a!
Annabelle tace "Babyn Momma me zaka je yi a Makarfi?
"Kiyi min fatan alkhairi kawai ba se kin sani ba" Ya tashi ya bar parlon!
Kallon juna suka yi ita da Momma tare suka hada baki wajen fadin miskilancin ya motsa!
***
Janan ta sanar da Ummiey zuwan Annabelle, murmushi tayi tace ''Allah ya kawo ta lfya, ashe gobe muna da babbar bakuwa!
Tace ''aikam dai Ummiey, bari in duba abinci karya kone!
馃枻
Washe gari Annabelle sanye da riga da skirt na lashi orange nd black, simple makeup tayi ta taje kanta, dan gutun tsaki tayi tace "Ba abun in je haka ba yanzu Bestie zata fara min korafi bana son rufe kai" dankwalin ta ta jawo tare da zama tayi dauri me kyan gaske sannan ta sa flat shoes baki ta dauka bakin jakarta ta fito! A parlor ta tarar da Momma zaune, kamshin turaren ta ne yasa Momma kallon ta tana fadin "wow! Kin yi kyau sosai Princess''
Annabelle tace "like seriously Mum!
Gira Momma ta daga mata!
That's My Momma" ta fada tare da daga mata hannu ta fita!
Har ta dan yi nisa Momma ta daga murya tana fadin "Ki gaida min ita, kuma ki dawo da wuri, hope kin tafi mata da tsaraba!
"zan fadi mata, zan tsaya a hanya mu siya mata chocolates!
A hanya ta tsaya ta siyo mata packs na chocolate me yawa sannan suka wuce! Suna hanya Janan ta dinga kiranta tana dauka tace "huh! Gani nan zuwa ko in fasa zuwan ne?
"Aa karki fasa pls! Se kin karaso! Ta kashe wayan..
Basu wani sha wahalan gane gidan ba sbd driver din dan gari ne kuma gidan yana da saukin ganewa! Har kofan gidan ya kaita yace "Maam zan jira ki fito se mu tafi bari in yi parking a inuwa!
Cike da tausayi ta kalle shi tace "no karka jira ni, naji dazu kana waya akwai ina da zaka je watakila abun is important kaje kar in tsayar da kai cuz I don't think zan fito nan kusa idan na gama zan kira ka"
Godiya sosai yayi mata yana jinjina kirkin ta, seda yaga shiganta gidan sannan ya juya ya tafi!
A harabar gidan ta tarar da Janan tsaye tana jiran ta, da gudu suka karaso tare da rungume juna cike da farin ciki sannan suka rabu, ta kalli Janan tace "Bestie me kike ci haka ne kika yi wani fresh da 'kiba?
Janan tayi daria tace "Ba wani nan ke baki ga kanki ba se ni? Suka kwashe da daria sannan suka shiga parlorn!
Har kasa ta duka tana gaida Ummiey!
Ummiey tace yau dai at long last kinzo kullum Hulwaty bata da hira se naki, sannu da zuwa, ga wuri ki zauna, ya mutan gidan naku?
Cike da jin kunya ta zauna sannan ta amsa mata!
Ganin ta kasa sakewa yasa Ummiey ce ma Janan "Ki kaita dakin ki, anan se ta huta taci abinci koh!
Annabelle taji dadin haka kuwa, suna shiga Janan ta wuce kitchen ta kawo mata abinci a cikin cooler tare da Kunun aya me sanyi cikin jug, ba wani abinci iyayi tayi ba dambun couscous tayi wanda ta sa nikakken nama, zogale, se karas, albasa da green pepper se kamshin abincin yake yi, Annabelle taci sosai tana ta santi suna hira tana shan kunun aya can se wayan Janan ta fara ringing da sauri ta dauka tana fadin ''Ayi min hakuri kawar amana, Eeesher ce ta kira take mata tsiya wai ta share su, bata da bakin magana se dai hakurin da ta bata, sun dan dade suna waya sannan suka ajiye! Annabelle cikin damuwa tace wacece haka?
Kafin ta kai ga bata amsa Wani kiran ya shigo tace ina zuwa pls, ta daga wayan tana fadin "kawar rai da rai hada baki kuka yi ne? Zee ce! ita ma dai tsiyan tayi mata daga karshe suka 'bige da hira! Se can suka ajiye wayan!
Annabelle ta cika fam! Idon ta sun ciko da kwalla, Janan tace lfya?
Cikin murya me rauni tace su waye?
Janan tace Aisha da Zainab kawaye na da na baki labarin su"
"Kin fi son su ko? Sbd ni ba Musulma bace shiyasa kika fi son su a a kaina ko?
Janan tayi shiru jiki a sanyaye dan maganan Annabelle ya taba ta, can ta daure tace "Ba haka bane!
Hmmm! Cikin mu wa kika fi so toh?
"Dukkan ku ina son ku sosai, but ke matsayin ki ya wuce frndship kin koma yar uwata baki ji Sis nake kiran ki ba ma?
Haka yadan sa taji sanyi a ranta tana fadin in dai kika fi son wata a kaina gaskiya ba zan ji dadi ba sbd ni bani da wacce nake so kamar ki!
Ina son komai naki Bestie, ta ruko hannun ta duka biyu tana fadin "ina jin matsayin ki na daban a zuciya ta, pls ki rike ni da amana kar ki juya min baya sbd ni christian ce!
Zuciyar Janan ta yi rauni ita kanta ta san Annabelle na son ta sosai dan haka ta dinga mata kalamai masu dadi har ta samu ta saki jiki!
Bata bari Yamma tayi sosai ba ta kira Driver, dama yana kan hanya dan haka bada dadewa ba ya karaso!
Ledan chocolate din ta mika Janan tace gashi nan a sha lfya in an gama asha maganin ciwon ciki da bisir" suka yi daria Janan tayi mata godia!
Wani agogo da zoben azurfa me kyau ta bata Ummiey kuma ta bata Arabian perfumes guda biyu masu tsada, har bakin mota Janan ta raka ta tare da alkawarin ita ma tana nan zuwa! Haka suka rabu cike da kewan juna.....!!!!
Cikin ranta tana jinjina tsafta da karamcin su Janan!!!!
_Rukkybae_馃槒馃槒馃槒
[12/22/2017, 9:56 AM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [12/21, 6:17 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: 鉂も櫏鈾b櫊鈾b潳鈾モ櫍鈾犫櫏鈾b潳鈾犫櫍鈾モ櫍鉂も櫊鈾b櫏鉂も櫍鈾犫櫏鈾b櫏鈾b櫏鈾犫櫍鈾モ潳鈾b櫊鈾モ櫍 *MATAR DOCTOR* 鈾b櫏鈾b潳鈾モ潳鈾モ櫊鈾b櫏鈾b潳鈾モ櫊鈾モ潳鈾モ櫍鈾犫潳鈾犫櫏鈾犫櫍
_Rukkybae_馃槒馃槒馃槒
馃寪 *HAJOW* 馃寪
*_HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS_*鉁嶐煆烩湇馃徎鉁嶐煆�
_This page is 4 u Bilkisu Muh'd Hassan, Alhaji Khaleefa and CO. Thank y'all for the support, Allah ya saka da alkhairi_鉂b潱鉂�
1鈨�1鈨�5鈨�
******
Sati na zagayowa Janan ta shirya ta tafi gidan su Annabelle, sosai Momma taji dadin zuwanta dan haka kawai taji tana kaunar Janan, tarba na musamman aka mata ga abinci da drinks din kwali kala kala aka ajiye mata Ta dan ci abinci dai dai dama ita ba wani ci gare ta ba! Nan suka fara hira Momma na kallon su cike da sha'awa, tun tana iya biye musu ayi da ita har ta gaji dan da alama hiran su ba me karewa bace daga karshe dai tashi tayi ta koma dakin ta suma tashi suka yi suka shige dakin Annabelle suka cigaba da hiran su.. Annabelle tace "Nifa kin san duk yawan lecturers din mu babu wanda ke burge ni kuma nake gane lectures din shi kaman me mana Biochem akwai daukan wanka ga sakin fuska gaskiya bashi da matsala"
Tsaki Janan taja tana fadin "wallahi ni baya burge ni, ke dan kina son course din ne shiyasa kike fadan haka''
"No ba sbd haka bane ke ma dai kin san abunda na fada gaskiya ne"
"Ba wani gaskiya, in banda iyayi da kallon matan tsiya daya sa a gaba"
"Kai Bestie wannan mutumin kike ce ma haka? Ba ruwan shi very silent abun shi"
"Nifa ban gane irin wannan yabon da kike mishi ba"
"Ba abunda zaki gane tunda abun haka ne"
Musu suka dinga yi!
Dr. Godwin dake kwance a dakin shi yana bacci hayaniyar su ya tashe shi, tsaki yaja tare da janyo pillow ya cusa kan shi a ciki ko ze dena jin hayaniyar amma kamar kara zuga su ake yi, yama fi jin muryan Annabelle duk da baya fahimtan abun da suke fada, ignoring din shirmen su yayi ya juya dan ya cigaba da baccin amma wani ihu da suka yi seda ya tashe zaune nan take kanshi ya sara!
"Ohhhh My God! Na dawo daga tafi ina son in samu bacci amma wannan shirmen ya hanani ya kara jan tsaki!
Cike da jin haushi ya tashi ya canza kaya, makulli da wayar shi ya dauka dan baya jin ze iya zaman gidan nan sbd hayaniyar su tayi yawa!
Parlor'n ya shiga bega kowa ba In banda muryan Annabelle dake tashi daga dakin ta, "wato Momma itama hayaniyar ta hanata zaman parlor! kalan ta kalar kawarta shiyasa suke ta zuba shirme, har yanzu basu girma ba, yarinta yana damun su"
Dakin Momma ya nufa yana daga labule ya ganta tana bacci, dakin ya shiga har gaban gado ya durkusa yana kallon fuskan ta, peck ya mata a kumatu sannan ya bar dakin!
hanyar dakin Annabelle ya nufa, dai dai an fara kiraye kirayen sallah, Janan tayi wuf! Ta mike tana fadin "Anny! Musun ya isa haka ana kiran sallah"
Sannin halin Janan yasa tayi shiru dan ta san ko wani magana ake yi ba zata amsa ba In dai ana kiran sallah!
Bayi ta shiga dan tayi alwala tana rufe kofan bayin Dr. Godwin ya daga labulen dakin, wani kallo yake ma Annabelle sannan yace ''sannu da aiki, duk kun bi kun ishe mu da ihu da surutu kaman parrots, bakin ku ko ciwo ba ya muku, toh hankalin ku ya kwanta kun tashe ni daga bacci"
Kallon mamaki take mishi dan bata san ya dawo ba, tasowa tayi ta karaso har bakin kofan tana fadin "Babyn Momma yaushe ka dawo?
"Ba wannan nake son ji ba, ai kin ji na fada miki kin tashe ni bacci gashi nan kaina yana ciwo"
Kunnuwan ta duka biyu ta kama sannan tace "sorry Dr. Babyn Momma"
Abun yaso bashi daria se kawai ya dan yi murmushi, ya juya yana son barin dakin da sauri tace "Babyn Momma ka dan tsaya ku gaisa da Bestie na tana alwala a toilet"
A ranshi yace "bana son haduwa da kawar Lil Sis din nan kafin ma taga kaman ni na damu mu hadu haka nan ta raina ni! A fili kuma yace "OK bari in bata mintuna 2 in bata fito ba zan tafi cuz ina sauri ne akwai inda zanje"
"toh lemme tell her tayi sauri kana jiran ta ku gaisa"
"No ki barta mana, kin san wasu basa son rushing in suna abu balle kuma kin ce alwala take yi"
Kwata kwata be son haduwa da kawar Annabelle din nan Dan ba karamin faduwa gaban shi ke yi ba In tana maganan ta toh ina ga sun hadu? Maybe zuciyar ta fito daga kirjin shi sbd faduwa!
Hira ta dinga jan shi da shi dan ta dauke mishi hankali!
Mintuna 2 na cika kamar hadin baki wayar shi ta fara ringing yaji dadin haka, da sauri yace "Lil Sis ki gaida ta an fara kira na kuma gashi bata fito ba In ta fito ina gaida ta" ya juya da sauri ya bar dakin!
Yana wuce wa sega Janan ta fito tana gyara hannun rigar ta!
Annabelle tace "yanzu Babyn Momma ya wuce se jiran ki yake yi ku gaisa kin wani yi zaman ki a bayi! Bari in ga in beyi nisa ba In ce kin fito"
Kafin Janan tayi magana har ta fita kiran shi!
Mai gadi har ya bude mishi gate yana shirin fita ta karaso tana fadin Babyn Momma pls ta fito!
"Kin cika rigima Princess, Dad ne kadai ke iyawa dake, kinga yanzu bazan iya fitowa ba bt zan dawo da wuri se mu gaisa haka yayi miki?
Ba dan taso ba tace "Eh! Ta juya ciki abunta!
Sallah ta tarar Janan nayi ta zauna tana jiran ta ta idar!
Tana idarwa taga bata gan shi ba, taji dadin haka Annabelle tace "Ana jiran shi ne bt na san ba zai dade ba ze dawo in ya so se mu maida ki gida ni da shi!
Kai kawai ta daga amma a ranta tana ta Addu'a kar ya dawo ya same ta a gidan nan!
Har La'asar be dawo ba Janan kam abun ya mata dadi dan haka tace ita yanzu zata wuce kar tayi dare bari ta kira Yaya Khaleel in ya gama yazo ya dauke ta!
"Kar ki kira shi bari mu kai ki nida driver", jiki a sanyaye ta tashi taje dakin Momma ta tarar ta tashi daga baccin, ta fada mata Janan zata wuce! Takalma flats guda biyu da loafers guda daya ta sa a leda suka fito tare, Annabelle kuma kayan kwalliya ta hada mata godia ta dinga ma Momma kamar zata ari baki! driver'n gidan su tare da Annabelle din suka kaita har kofan gida amma bata shiga ba se dai tace a gaida Ummiey!
Se can dare Dr. Godwin ya dawo,, ko inda yake Annabelle bata kalla ba sbd tana fushi, ya san dama haka ze faru amma shi yaji dadi daya dawo bata nan!
Har inda take yaje ya dinga janta da magana da tsokana har seda ta hakura!
Suka dan taba hira!
_Rukkybae_馃槒馃槒馃槒
[12/24/2017, 8:27 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [12/23, 11:15 AM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: 鈾モ潱鉂も櫍鈾モ櫊鈾b櫏鈾b櫊鈾モ櫏鈾犫櫍鈾モ櫍鈾b櫏鈾犫櫊鈾モ櫍鉂b櫊鈾モ潱鈾b櫏鉂も潱鈾b櫊鈾モ櫊鈾� *MATAR DOCTOR* 鈾b櫏鉂b櫍鉂も櫊鈾モ櫊鉂も櫊鉂も櫊鈾モ櫊鉂も櫍鈾モ潱鉂も櫊鈾モ櫊鉂も潱
_Rukkybae_馃槒馃槒馃槒
馃寪 *HAJOW*馃寪
_*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*_鉁嶐煆烩湇馃徎鉁嶐煆�
_Wannan shafin naki ne *Lubnerh Sufyan!* Baki sanni ba nima ban sanki bt posts dinki da novels dinki su suka sa nake son ki kuma kike burge ni, kina kokari wajen kare mutuncin mata tare da fadakar da alummah!! Allah ya kara miki Ilimi, hazaka da basira!_鉂b櫏 _Rukkybae_馃槒 loves u so much!!! 馃槝馃槝
1鈨�1鈨�6鈨�
Hutun su Janan ya kare suka koma makaranta! Dawowa nan yasa Janan ta canza salo, ta kan shiga cikin mutane a dan yi hira, sakin fuskan ta da farin jinin ta yasa kowa ke son suyi mutunci da ita, ta lura Musulman sch din addini be dame su ba kwata kwata, se taga wata wai Muslma amma ko gyale babu a jikin ta!
Dan zaman da suke yi kafin a shiga lectures yasa ta fara jan hankalin su cikin taushin harshe akan irin dressing din da suke yi!
Da alama nasihan ta ya fara tasiri a cikin zukatan su, dan haka a yan kwanakin nan da yawa sun fara sa gyale duk da kanana ne amma ta ji dadi dan da alama akwai nasara! Ganin irin raunin addinin Musulunci a makarantan yasa ta rubuta Letter ta kai Department din su a kan a kirkiro Kungiyar MSS (Muslim Students Society) a sch din dan a kara daukaka Darajan Addinin Musulunci! Yafi kusan sati biyu tana bi amma anki approving mata, wani Letter ta kara rubutawa ta kai ma Dean na Faculty of Sciences shima shiru..... Dabara ce ta fado mata dan haka ta sake rubuta wani Letter din ta nufi office din V.C (Vice Chancellor)! Kwanaki Uku ta jera tana zuwa amma bata samu daman ganin shi ba se a rana na hudu, da kyar ta samu securities din wajen suka barta ta shiga wajen shi! Cikin faduwar gaba tayi knocking ya bata izinin shiga, Babban Mutum ne me kwarjini, wurin zama ya nuna mata ta zauna kafin yace
"ina so in san me ya kawo ki kuma me kike bukata!
Addu'a ta jero a zuciyar ta sannan tayi mishi bayanin komai da duk hanyoyin data bi dan isar da sakon amma be zo wajen shi ba!
Mamaki ne ya cika shi yanda karamar yarinya kamarta tayi wannan tunanin duk da shi ba Musulmi bane amma ta burge shi kuma ya yaba da jajircewan ta tare da yanda ta nuna kishin Addinin ta a fili!
"kar ki damu nan bada dadewa zaki ji feedback daga gare ni" yace mata
Numban wayan ta ta rubuta a wani takadda cike da murna ta dinga mishi godia!
Sauri sauri ta koma dakin su harda sallama tana shiga ta tarar da Annabelle kwance a gado tana karanta Kitabbuttauhid me fassaran turanci! Kallon ta kawai Janan take yi dan da alama Annabelle din ma bata san ta shigo ba!
Tace "Sis Anny Em Back!
Wani irin firgita Annabelle tayi tare da tura takardan a karkashin pillow din ta!
Inda inda ta fara yi tana fadin "Bestie yaushe kika shigo ban sani ba?
"tun dazu na shigo har Sallama seda nayi amma naji ki shiru"
"Am.. am..am I was so carried away ne shiyasa ban ji ki ba"
Gefen ta Janan ta zauna tare da dafa mata kafada tana fadin "tell me! Ina so in sani, ya akayi kika samu book din nan kuma yaushe kika fara karantawa?
Shiru tayi kanta a kasa ta kasa magana
Janan ta kara cewa "kin san bama boye ma juna komai koh? And kece kika kawo wannan shawarar akan mu dena boye ma juna komai, so tell me"
"it's been long Bestie, na dade ina so in gane mene ne a ciki amma se naga naki na larabci ne shine na dauka naje kasuwa na siyo me fassara!
"Sis! Kina so ki shiga Addinin Musulunci ne?
"Bestie ina so, na dade ina kallon duk wani dabi'un ki da komai naki, yanda kike tafiyar da Addinin ki shi yafi komai daukan hankali na, nasha mafarke mafarke akan ki da kuma hasken dake tattare dake, duk wani littafin addini da kike da shi nima ina da shi kuma ina karantawa, tsam ta tashi ta dakko wani jakarta ta dinga fito ma da Janan Islamic Books su Seerah, Fiqhu, Hadeeth harda littafin Kaba'ir!
Wani irin runguma Janan ta mata tana zubda hawayen farin ciki, ita ma Annabelle hawayen ke zuba daga idon ta, janye jikin ta tayi daga rungumar da Janan tayi mata ta fara share mata hawaye tana fadin "Bestie ki dena zubda hawayen ki, na sani haduwar mu alkhairi ne"
Janan tace "hawayen farin ciki ne ke zuba daga ido na ba na komai ba! Ta kara fashewa da kuka!
Da kyar suka tsagaita da kukan sannan Janan tace zan fada miki kalmar shiga Addinin Musulunci kema se ki maimaita amma ki tsarkake zuciyar ki akan zaki shiga addinin Musulunci ba tare da tursasawa ba ko dan wani abu se Don Allah!
Kai Annabelle ta daga sannan Janan ta fara fadin
"Ashhadu Alla ilaha illallah, Annabelle ta fada kamar yanda Janan din ta fada kafin Janan ta kai ga karasawa Annabelle tace "wa Ashhadu anna Muhammadan abduhu warasuluhu!
"ya akayi kike iya? Janan ta tambaya
Murmushi tayi tace "na gani a cikin littafin tauhid kuma na dade da haddacewa!
Janan ta rasa inda zata sa kanta sbd farin ciki! Ta ce "duk wani zunubi da kika aikata lokacin kina cikin addinin ki na baya yanzu Allah ya yafe miki kin koma tamkar jaririyar da aka haifa yau, baki da zunubi ko daya, zan koya miki wankan tsarki wanda shine mataki na biyu da zaki dauka bayan amsan kalmar shahada, wannan wankan ana yin shi sbd tsarkaka sannan ana yin shi a bisa dalilai daban daban kuma duk iri daya ne se dai banbancin niyya! Kuma ya wajabta akan Baligi namiji da baliga Ta mace!
Ana yin shi idan janaba ya samu mutum,
ana yin shi bayan daukewar jinin al'ada ga mace,
Mace na yin shi lokacin daukewar jinin Biki wato Jinin haihuwa
Ana yin shi lokacin shiga addinin Musulunci bayan karban kalman shahada
Sannan ana yi ma duk mutumin daya mutu cikin Musulunci
Sannan yana da kyau duk wani Musulmi yayi wannan wankan duk Juma'a domin Allah Mai tsarki ne, ya wajabta tsarki akan mu kuma yana son masu tsarki!
Dalla dalla tayi mata bayanin wankan tsarki!
Bayi ta shiga tayi kamar yanda Janan din ta koya mata! Tana fitowa ta gyara jikin ta ta sa wani dogon riga, ita kanta yau taji wani iska me ni'ima yana shiga jikin ta sannan ga wani Kwanciyar hankali na daban, har zuciyar ta kara tabbatar da Addinin Musulunci addini ne na gaskiya!
Janan dake zaune gefen gado ta kalle ta dauke da murmushi a fuskan ta sannan tace "wlcm to the world of Islam! (Barka da zuwa duniyar Musulunci) Annabelle ta zauna cike da jin dadi sannan tace "Bestie na zaba sunan Fadimatuzzarah! Sbd na dade ina son sunan!
"Alhamdulillah kin zabi suna me kyau kuma me daraja domin sunan 'Yar Annabi Muhammad SAW ce kuma duk yafi son ta a cikin 'ya'yan domin ita kadai ce tayi rayuwa me tsawo da shi dan duk sauran suna kanana suka rasu!
Tace "Dan Allah kada ki fada ma kowa cewa na Musulunta sbd iyaye ne manyan mutane ne kuma an san su sosai domin Dad din shine Babban Pastor a Church din mu, ina tsoro a fada musu nafi so in fada musu da kaina amma ba yanzu ba se na samu enough Ilimi da Hujjan da zanyi challenging din su!
Janan ta jinjina kai! Sannan ta bata lbrn yanda suka yi da V.C !
Tun daga ranan Janan ta zama Malamar Zarah (Annabelle) ta dauki alwashin koya mata karatu tun daga *Alif*!! Sannan ta koya mata karatun Alqurani daga *Quhuwallahu zuwa Ammah* sannan ta fara koya mata sallah! Alhamdulillah ta fara daukan abunda ake koya mata dama tana da saurin fahimtan abu!
鉂�
A yau sako ya iso zuwa ga Janan kan an yarje mata ta yada addinin Musulunci amma akwai sharrudan da aka gindaya mata kuma ta dauka! Ciki harda kare mutuncin waenda ba addini su daya ba!
Mutane kadan suka fara aiki tare da ita a haka suka dinga jurewa suna Da'awah cikin Hikima da Mutuntawa!
An samu bunkasar mutane a cikin Kungiyar wanda ya hada da Malaman su da basu cika nuna addinin su a fili ba, an hada Seminar inda mutane dayawa suka zo harda daliban wasu makarantu, abun ya kayatar inda Janan ta tashi tayi bayani akan *Mutuwa DA KWANCIYAR KABARI* cike da kwarewa cikin harshen turanci!
Sosai Jawabin ta ya taba Zukatan masu sauraro!! Bayan kammala taron aka nadata a matsayin *Ameerah* ta Kungiyar!!
Abubuwa sun ma Janan yawa sbd Jarabarwar su ta matso ga kuma Da'awah da suke yi!! Cikin Hukunci Ubangiji suka kammala Jarabawan su, wannan karon Dad din Zarah (Annabelle) ya turo musu da kudi suka biyo jirgi suka dawo Abuja, driver'n su Zarah ne ya dauko su daga Airport, seda aka kai Janan sannan suka wuce!!!!
_Rukkybae_馃槒馃槒馃槒
[12/28/2017, 8:52 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: RukkyBae馃槒 馃槒馃槒鉂b潱: 鉂ゐ煐も櫍鈾モ櫊鈾b櫏鈾b櫊鈾b櫏鈾b櫍鈾モ櫍鈾犫櫏鈾モ櫍鈾犫櫏鈾モ櫍鈾犫櫍鈾モ櫏鈾b櫏鈾モ櫊鈾モ櫏鈾b櫏 *MATAR DOCTOR* 鉂も櫊鈾b潳鈾モ櫊馃枻鈾b櫏鉂も櫍鉂も櫏鈾p煐も潳鈾p煐も櫊馃枻鉂も櫍鈾ヰ煐も櫊鈾ヰ煐も櫍鈾狆煐も櫍鈾モ櫏鈾b櫊鈾�
_RukkyBae_馃槒馃槒馃槒
馃寪 *HAJOW*馃寪
鉁嶐煆烩湇馃徎 *_Hakuri Da Juriya Online Writers_*鉁嶐煆烩湇馃徎鉁嶐煆�
_Sallah na da haske me girma, tana haskaka zukatan masu yinta, idan ka tashi dan yin sallah, seka kakkabe zuciyar ka daga duniya da abunda ke cikinta kuma ka shagaltu da ganawa da Ubangijin ka! Kada ka bari shedan yayi wasa da zuciyar ka...!!_
1鈨�1鈨�7鈨�
Gaba daya yanzu Dr. Godwin ba shida lokaci sbd ayyuka sun mishi yawa har baya samun time din kanshi sbd duba marasa lafiya, kullum se dare yake dawowa gida.... Tun Momma na damuwa har ta dena dan ta fara sabawa da hakan!
Da zaran lokacin sallah yayi Annabelle (Zarah) zata sulale jiki ta faki idon su Dad ta shige dakin ta ta rufe da makulli sannan tayi sallan ta!
Yau kusan kwanaki 3 kenan bata samun lamban Janan, ta damu sosai dama Janan din ce ke yawan tashin ta sallan asuba sbd karta makara.. Parlor ta fita tana zuwa ta tarar da Momma da Dad sunyi ankon kaya ta kalle su tace "Morning Momma, morning Dad bata jira sun amsa mata ba tace ina zaku je?
Kallon ta kawai suke yi tunda ta fito cike da mamaki ganin ta da kayan bacci sannan kuma tana tambayan su inda zasu je!
Dad yace "Princess kar dai kice min kin manta yau Sunday, dan naga ko alaman shirin zuwa Church ba kiyi ba''
Kai ta dafe tana fadin ''na manta yau Sunday fa!
Momma tace "toh kije ki shirya da sauri se mu tafi ko kuma driver ya kawo ki dan zaki iya bata mana lokaci"
Gaban ta ne ya fadi tace "Momma yau ba zan iya bin ku ba cuz bana jin zuwa Church yau, em nt in a good mood, sbd yau kusan 3 days kenan ba muyi waya da Bestie ba kuma ina ji a jiki na ba lafiya so se kun dawo ni se driver ya kaini gidan su inna gama"
Tunda Annabelle ta dawo hutun nan suka kasa gane kanta kwata kwata bata san zuwa Church duk sanda za a je tana da excuse din da zata bada!
Ki bari in mun dawo se muje gidan su Bestie din taki, mu ga iyayen ta kuma mu san ko tana lfya cuz yanda kika damu da wannan frnd din taki abun yanada daure kai!
Duka su biyun ta hada ta rungume tana jin wani irin son su na ratsa ta, tace "I love u Both, se kun dawo"
Ta ruga dakin ta da gudu su kuma suka wuce abun su, ko ta kan Godwin basu bi ba dan sun san halin shi baya zuwa Church!!
Bacci ta koma, se can da aka idar da sallan Azahar ta iya tashi, agogon dake manne a dakin ta kalla cikin hanzari ta mike tana fadin "Subhannallah"
Bayi ta shiga tayi wanka sannan ta dauro alwala, wardrobe din ta ta bude ta fito da kayan ta masu kyau ta saka tare da fesa turaren ta me kamshi, Darduma ta shimfida ta dakko dogon Hijjab da socks ta saka sannan ta tayar da sallah tana me farin ciki, zuciyar ta cike da nishadi!
Tana raka'an karshe taji alaman an shigo dakin dan yau bata kulle ba tunda su Momma basa gida, gaban ta ne ya dinga faduwa amma haka ta kara maida hankali kan sallan ta, tana idarwa ta waiga dan taga waye! Dr. Godwin ta gani tsaye ya harde hannuwan shi a kirji yana kallon ta, ido ta zaro waje tare da dafe kirjin ta, bakin ta na rawa tana shirin mishi magana suka jiyo muryan su Momma alaman sun dawo, da sauri ta cire Hijjab din tare da tura shi cikin drawer tana waigowa taga Momma a tsaye a kofan dakin tana musu kallo me nuna alaman lafiya?
Da kafa Annabelle (Zarah) ta dinga jan darduman har seda ta tura karkashin gado! Wayancewa tayi da fadin "Momma sannun ku da zuwa ina Dad?
A haka ta samu ta janye ta zuwa parlor Dr. Godwin na biye da su!
Abincin rana suke ci amma duk ta tsargu dan data dago za su hada ido da Dr. Godwin, gani take yi kamar ze fadawa su Momma! Ya gane abun da take nufi dan haka suna sake hada ido yayi mata murmushi tare da girgiza kai! Se a sannan hankalin ta yadan kwanta!
Suna gamawa suka dan taba hira, nan ta kara musu tuni akan zuwa gidan su Janan!! Dr. Godwin yaji yau yana son ganin kawar Lil Sis din shi dan haka ya dau aniyar bin su!
Se da aka yi sallan Isha'i sannan suka shiraya tafiya, Godwin wasu carton brown half kaftan ya saka, yayi kyau sosai, Zarah tayi mamakin jin Yayan ta ze bisu!
A tare suka fito, motar shi yace suyi anfanin da ita, Momma da Zarah suka shiga baya, Dad ya zauna a gaba, Dr. Godwin ya ja motan suka tafi!!!
Kwatance Zarah ta dinga yi mishi har suka kai bakin kofan gidan, parking suka yi tare da gaisawa da Mai gadi, yana ganin Annabelle (Zarah) ya gane ta da sauri yace su shigo, kin shiga suka yi Dad yace "Princess je ki fadawa mutanen gidan tare muke dan kar mu shigan musu gida ba tare da izinin su ba"
Tace ''OK Dad" sannan tayi shigewar ta!
A parlor ta tarar dasu Ummiey da wasu dattijai 2 amma Janan bata parlor'n, har kasa ta duka ta gaida su tare da fada musu dasu Dad suke, Nan Abbiey yace "aa, ya suka tsaya a waje? Je ki shigo da su! Da sauri ta fita tace musu su shigo!
Gaban Dr. Godwin se faduwa yake amma ya rasa dalilin hakan!
A tare suka shiga parlor'n, dai dai Janan ta fito daga dakin ta!
Wani irin abune ya gilma musu kamar walkiya, Dr. Godwin yace *JANAN!!* tare da nuna ta, Be gama Mamaki ba yaji ance *SHRUIEM!!* yana juyawa yaga daya daga cikin dattijan ke mishi magana, Dr. Godwin yace *BABA LIMAN!!*
Abbiey ya kalli Dad tare da fadin *MR. AHMAD!!*
Dad yace *BARRISTER PHAROUK MAKARFI!!*
Ummiey ta kalli MOMMA tace *HAJIA HALEEMAH!!!*
Momma kuma tace *HAJIA NANA!!*
_RukkyBae_馃槒馃槒馃槒
[12/31/2017, 12:17 AM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [12/28, 8:54 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: 鉂ゐ煐も櫍鈾モ櫊鈾b櫏鈾b櫊鈾b櫏鈾b櫍鈾モ櫍鈾犫櫏鈾モ櫍鈾犫櫏鈾モ櫍鈾犫櫍鈾モ櫏鈾b櫏鈾モ櫊鈾モ櫏鈾b櫏 *MATAR DOCTOR* 鉂も櫊鈾b潳鈾モ櫊馃枻鈾b櫏鉂も櫍鉂も櫏鈾p煐も潳鈾p煐も櫊馃枻鉂も櫍鈾ヰ煐も櫊鈾ヰ煐も櫍鈾狆煐も櫍鈾モ櫏鈾b櫊鈾�
_RukkyBae_馃槒馃槒馃槒
馃寪 *HAJOW*馃寪
鉁嶐煆烩湇馃徎 *_Hakuri Da Juriya Online Writers_*鉁嶐煆烩湇馃徎
_Wannan Shafin naku ne gabaki dayan ku Makaranta kuma Masoya littafin MATAR DOCTOR!! Ina godia da kulawar ku da soyayyar ku a gare ni!! Ina gaishe ku tare da muku fatan alkhairi a duk in da kuke!! Allah ya kara mana son juna!!...._
1鈨�1鈨�8鈨�
Gaba dayan su sun zama confused se kallon kallo suke yi a tsakanin su! Abbiey ne yayi karfin halin samun kujera ya zauna, su Momma suma suka zauna, Dr. Godwin da Janan kuma suna tsaye kamar an dasa su!!
Shiru ya ratsa dakin se T.V kadai ke aiki, fuskan Dad aka nuno a alon TV yana preaching a Church! Tambaya da mamaki ne a fuskan Abbiey, Ummiey da Baba Liman! Se yanzu suka lura Momma ko Dankwali babu akan ta!
Abbiey yace "Mr&Mrs Ahmad??
Dad ya gane Abbiey na neman karin bayani ne!
Shiru ya dan yi se ga hawaye suna fita daga idon shi, ganin haka yasa su Janan suka zauna dan abun da mamaki Babban Mutum kamar Dad yana zubda hawaye!
Dai dai lokacin Yaya Khaleel da Yaya Saleem suka shigo!
Abbiey ya musu nuni da su zauna!
Godwin, Annabelle yau zaku san abunda baku sani ba, gara kai Godwin zaka iya tuno wasu abubuwan!! Dad yace
*TUSHEN LABARI!!*
Asalin su Dad yan garin Sokoto ne, sunan Mahaifin su Malam Shureim, su biyu kadai iyayen su suka haifa Dad (Ahmad) da Yayan shi Hamza! Sun yi karatun primary da secondary duk a nan Sokoto, mahaifin su ya rasu da shekara daya da rabi Mahaifiyar su itama ta rasu, sun yi kuka har suka dangana, lokacin Dad yana Ss2, shi kuma Yayan shi ya fara zuwa Jami'ar Dan Fodio, yau dadi gobe ba dadi a haka Dad ya fara aikin kanikanci, da haka ya samu ya biya kudin WAEC da NECO harda Jamb, cikin sa'a ya samu ya ci komai inda ya tafi Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria ya karanta Geography, kwata kwata Yayan shi be cika damuwa da shi ba, da kyar da wahala ya samu yake karatun nan, ana haka kudin Baban su na Pension ya fito
Da yake lokacin kudi na da daraja se suka dan samu da tsoka, ya kira Dad ya fada mishi kudin Baban su ya fito, yaji dadi dan ya san ko ba komai ze huta da wahala, ba abunda ya sauya daga rashin kulan da Yayan shi ke mishi, haka ya samu ya kammala karatun shi cike da nasara, a lokacin Yayan shi ya yi aure suka zauna a gidan su da Baban ya bar musu, tun lokacin Dad yace a raba gado aba kowa nashi sbd yana so ya fara kasuwan ci amma Yayan shi ya ki yarda, babu yanda Dad ya iya haka ya kyale shi, wani dan mokocin su dake zuwa Lagos saro kaya ya fara bi suna siyo kayan tare ana bashi lada...
Kudin ya dinga tarawa har shima ya fara saida takalma, cikin hukuncin Allah ya hadu da Haleema (Momma) lokacin yaje Kano saro takalma, sun shaku da juna har suka yi aure, bayan da kyar Yayan shi ya yarda!
Tun bayan auren su da Momma yake samun budi amma basu samu haihuwa ba, cinikin takalma ya habbaka da haka ya koma Lagos, ganin yana ciniki kuma Alhamdulillah yana da rufin asiri yasa shi be nema aiki ba, lokacin daya zo Sokoto dan duba Yayan shi se yake ce mishi "Ahmad yanzu baka son zuwa garin nan kuma ka san bani da kowa se kai amma ka kyale ni a nan, me yasa nima ba zaka samamin wuri a can ba in dawo kusa da kai!
Ba haka Dad yaso ba amma daya fadawa Momma ta dinga murna tace ai ba komai gara su zauna kusa da shi!
Bayan ya dawo ya neman mishi wani gida ba nisa tsakanin su, tunda ya dawo Dad ke dawainiya dashi!
Wani abokin kasuwancin shi yace "Malam Ahmad me yasa ba zaka sa kudin a hannun jari ba? Ana samun riba sosai da sosai fa!
Maganan abokin kasuwan cin shi ya tsaya mishi a rai dan haka ya fada wa Momma komai ita kuma ta bashi shawara ya fada wa Yayan shi Hamza!
Bayan ya fada mishi komai da irin riban da zasu samu se yace "toh ai wannan cigaba ne a gare mu baki daya ka bari kudin gadon mu se in sa mana a ciki ko ya ka gani?
Ba tare da wani tunani ba ya yarda da shawaran Yayan nashi!
Duk wani shige da ficen kudin ta hannun Yaya Hamza yake fita, a haka har abun ya bunkasa ya gina haddaden gida!
Duk Dad be ce komai sbd hakuri da kawaici, a haka kasuwancin shi ya fara kasa ga Momma da tsohon ciki haihuwa ko yau ko gobe, duk ya fita hayyacin shi tun yana daurewa har ya fara sarewa, wajen Yayan shi yaje akan ya bashi rance a kudin su amma ya rufe ido yayi mishi kacakaca! Jiki a sanyaye ya dawo gida, Momma ta lura mijin ta baya cikin kwanciyar hankali ga nakuda ta fara, a haka ta dinga kokarin kwantar mishi da hankali! Washe gari yana shirin tafiya kasuwa yaga tana cije cije, tambayan ta yayi ko lfya amma tace ba komai, haka ya shirya ya fita ko nisa be yiba faya ta fashe, mantuwa yayi dan haka da sauri ya dawo gida, yana shigowa ya ganta a wannan halin ga wani ruwa dake bin kafafun ta, cikin hanzari ya fita ya nemo me taxi ya kwashe ta se asibiti! Labor room aka wuce da ita, bada dadewa Nurse ta fito tana tambayan kayan haihuwa dan ta kusa sauka, shi gaba daya ma ya rude ya manta da wani abu wai kayan haihuwa dan haka da sauri ya koma ya kwaso dan tun cikin be yi kwari ba yake siyo kayan haihuwa!
Bayan mintuna 30 aka mishi albishir da ta haifi dan ta namiji! Yayi farin ciki sosai, da Baby da Maman duk suna cikin koshin lfya! Kwanaki 2 bayan haka aka sallame su, nan ya sa ma yaro sunan Baban shi marigayi (Shureim) suna kiran shi da Baba!
Haihuwan Baba ya sa sun samu alkhairi dayawa daga wajen mutane ta fanni daban daban! A haka suka cigaba da manajin rayuwa har Baba ya fara zuwa makaranta, kuma Momma bata kara haihuwa ba!!
Ganin alamura sun kara kasa yasa Dad komawa wajen Yayan shi kan kudin gadon shi, wannan karan ma rashin mutunci ya sake mishi dan haka Dad yace "ba zan yarda ka danne min hakki na ba shekara da shekaru dan haka kotu ce zata raba mu! Fuu ya fita daga gidan, abunka da wanda be iya fushi ba, da barin gidan Yayan shi kotu ya tafi ya kai kara nan aka hada shi da Barrister Pharouk Makarfi (Abbiey)! Be boye mishi komai ba tun daga tasowan su har zuwa yanzu!
Daya koma gida ya ba Momma lbr bata ji dadin haka amma ta mishi fatan alkhairi!
Sammaci aka aikawa Yaya Hamza, abun yazo mishi a ba zata dan haka ya dinga bala'i daga karshe shima ya nemo lawyer!
Bayan zama da hujjoji masu yawa su Abbiey suka cinye shari'a kuma a take a kotu Alkali yasa aka raba kudin kowa aka bashi!
Dad yayi farin ciki tare da godia ga Allah, bayan barin su kotu ya ciro kudi masu yawa ya ba Abbiey amma yace shi ba zai karba, Dan Allah ya taimake shi!
Tun daga lokacin suka kulla alaka suka zama tamkar yan uwa!
Haka Momma (Haleema) da Ummiey (Nana Khadeeja) suka zama kawaye! Har hutu Shrueim na zuwa yi a gidan da yake sa'anni suke da Saleem!
Tamfatsetsen gida Dad ya gina suka koma ciki, ya hada walima dan godema Allah! Har gidan Yayan shi ya zo yace "kada ka kuskura ka nuna ni a matsayin dan uwanka kuma duk abunda ya same ka kada ka sake kazo inda nake, bani ba kai! Ya fice daga gidan!
Abun ya dade yana damun Dad tare da mamakin hali irin na Yayan shi!!
Hannun jari ya cigaba da zubawa kafin ya samu sana'an yi!
Ya dade yana tunanin abunda ze yi ya saka ma Abbiey amma ya rasa dan haka ya biya ma dukkan su kudin aikin Hajji, Ummiey da Abbiey sun yi farin ciki dan haka aka kai su Shrueim, Khaleel da Saleem Makarfi kafin su dawo!!
鈾�
Bayan dawowan su da wata 3 aka ma Abbiey canjin wajen aiki! Harda su Dad suka je suka ga sabon gidan da su Abbiey suka koma! Lokaci zuwa Lokaci suna ziyartan junan su!
Bayan Shekaru 9 Momma ta samu ciki, sun yi murna sosai!
Dad ganin yayi karfi a cikin hannun jari yasa shi janyewa, gaba daya kudaden shi ya kwaso dan yana so ya fara business a Dubai, a daren ranan yan fashi suka duro gidan tare da kwashe duka kudin sannan suka cinnawa gidan wuta, Allah yayi da sauran rayuwa a tare da su Dad suka fito a guje, Shureim yana hannun Dad!
Wani kongo suka samu suka rakube dan basu san inda suka dosa ba! A haka suka kwana su tashi a cikin kongon nan, ba suda abinci se gari, haka Dad ze fita nemo musu abunda za su ci amma baya samu, Haka Shureim shima ze fita yana dako duk da kankancin shekarun shi!
Wani dare hadari ya hadu a take aka fara ruwa! A nan nakuda ya turnuke Momma duk inda suka je a taimaka musu babu wanda ke kallon su, a haka ya samu ya nemo me mota suka kaita asibiti (labarin baya da Dr. Godwin ya ba Janan a ranan birthday din su kan dalilin da yasa ya tsani kalman taimako)
Tana labour Dad ya fito haraban asibitin nan aka bashi lbrn an tafi da dan shi police station! Ya shiga rudu ya ma rasa ta ina ze fara, kongon da suke kwana ya koma ya hada kai da gwiwa yana kuka! Horn din mota ya dinga ji amma be damu daya dago ba, ji yayi an dafa shi da sauri ya dago fuska yana kallon su, wasu mutane ne guda 2 sanye da coat, daya yace "da gani kana cikin matsala, toh kada ka damu mu zamu taimake ke amma idan muka taimake ka zaka mana duk abunda muke so"
Cikin muryan kuka yace '' wani abu kuke so in muku?
"zamu fada maka amma yanzu kai ka fara fada mana damuwar ka mu nan masu taimako ne!
"gida na ya kone, matata tana asibiti tana nakuda, ba nida kudin da zan biya asibiti, 'Dana yana police station wajen en sanda, ta ina zaku fara taimaka min?
Kallon juna suka yi tare da murmushi, motar suka koma suka ce ya biyo su! Babu musu ya bi su! Wani gida me kyau suka kai shi tare da fadin "ga sabon gida nan mun baka, wani brief case suka miko mishi, wannan kudi ne ka je ka yi settling bills dinka na asibiti kuma ka yi bailing yaron ka, nan da sati daya zamu dawo kuma lokacin zamu fada maka abunda muke so"
Dad ya dinga godia yana kuka! A haka suka wuce suka barshi!
Se da yayi bailing Shureim sannan suka biya komai na asibiti tare da dawowa sabon gidan su! Momma tayi mamaki kan sauyin da suka samu dan haka ta dinga tambayan shi yanda aka yi, be boye mata komai ba ya fada mata! Ita dai jikin ta be yarda da mutanen ba amma haka tayi shiru!
Kamar yanda suka fada sati na zagayowa suka zo gidan! A parlor suka zauna bayan sun huta suka ce "Mr. Ahmad kamar yanda muka yi da kai yau zaka cika mana alkawarin mu!
Dad da Momma suka kalli juna! Dad yace "ina jin ku, ku fadi abunda kuke so!
'' So muke ka bar addinin ka ka koma addinin mu na Christian!!
Wani irin mikewa Dad da Momma suka yi lokaci guda suna fadin ''What!!
Suka ce "Calm down, ai deal muka hada dan haka babu ja da baya!
Zuciyar Dad na tafarfasa ya ce "ba zan taba barin addini na ba, duk abunda kuka bani zan dawo muku dashi nan da sati daya nima!
Murmushi suka yi sannan suka tashi tsaye " OK nan da sati daya idan muka dawo baka biya mu komai namu ba baka da wani option illa ka dawo addinin mu! Da haka suka bar gidan!
Momma tayi kuka kamar ranta ze fita, haka ma Dad ya shiga tashin hankalin da be taba shiga ba!
Duk inda ya san ze samu kudi yabi amma be samu ba gashi saura kwana 2 sati daya ta cika dan haka ya yanke shawara ya tafi garin da aka maida Abbiey dan tun kafin suyi gobara yaje shida su Momma! Yana zuwa yaji labarin an canza ma Abbiey wajen aiki kuma suma basu san inda ya koma ba!
Tun a hanya yake kuka da dana sani har ya iso gida!
Tunda ya fadawa Momma be samu su Abbiey take ta faman kuka! Kullum ba suda aiki se kuka! A haka har satin ya zagayo, mutanen suka dawo, su Dad ba suda mafita face suka koma addinin kiristanci! Inda Momma daga *Haleema* ta koma *Lidia*
Dad daga *Ahmad* ya koma *Williams*
*Shuruiem* ya koma *Godwin*
Ita kuma jaririya aka sa mata *Annabelle*!!
Sosai suke daukan dawainiyar mu ga kudi da ake sake mana, a haka har muka fara zuwa Church nan aka yanke shawaran a bani Babban Pastor a Cocin sbd kar ma in samu hanyar barin addinin!!!!.....
Dad ya karasa labarin yana gunjin kuka!!!
Kowa a dakin kuka yake sbd labarin akwai tausayi da daga hankali! Abbiey cikin kuka yace "nima nazo Lagos yafi so a kirga ina neman ka amma na kasa samun ka ashe abunda ya faru kenan" ya karasa maganan yana kuka!
Nan Dr.Godwin yace nima ina da labarin da zan bada!!!
_RukkyBae_馃槒馃槒馃槒
[1/2, 10:06 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [1/2, 5:57 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: 鉂ゐ煐も櫏鈾b櫊鈾モ櫍鈾犫櫏鈾モ櫍鈾犫櫍鈾モ櫍鈾犫櫏鈾b櫊鈾b櫏鈾b櫊鈾b櫏鈾b櫊鈾b櫏鈾b櫏鈾犫櫍鈾モ櫍 *MATAR DOCTOR* 鈾犫櫏馃枻鈾b櫏鈾ヰ煐も櫍鈾犫櫏鈾モ櫍鈾犫櫏馃枻鈾モ櫏鈾モ櫏鈾p煐ゐ煐も櫏鈾�
_RukkyBae_馃槒馃槒馃槒
馃寪 *HAJOW*
鉁嶐煆烩湇馃徎 _Hakuri Da Juriya Online Writers_鉁嶐煆烩湇馃徎鉁嶐煆�
_Musulunci shine mika wuya ga Allah da kadai tashi tare da yi Mishi biyayya da bauta Mishi!_
1鈨�1鈨�9鈨�
Dr.Godwin ya fara magana "tun lokacin da naji Dad ya canza min suna na tsani sunan, lokacin shekaru na ba suda yawa amma ina da wayau sosai, tun lokacin na lura mun dena zuwa masallaci se Church, kafin a cire ni a islamiya Malamin mu yana mana waazi tare nuna mana addinin Musulunci shine addinin gaskiya sannan babu inda yafi dacewa ayi ibada se masallaci, wannan dalilin yasa bana bin su Momma Church!
A haka har na gama karatuna na samu aiki a Kaduna, anan na hadu da Janan, ita ta fara nuna min tare da koya min sannin darajan Mutum, dabi'un ta da yanayin rayuwar ta yasa na fara kwadayin nima in kama addini guda daya, lokacin da muka je Seminar da aka bude Babban asibiti a Makarfi, a nan na hadu da Baba Liman, muna da wajen kwana amma yace me ze hana in sauka a gidan shi!
Tunda na zauna a gidan suke girmama ni da darajta ni, so da dama idan yana ma mutane karatu tare da fada musu hukunce hukunce a Musulunci na kan saurara, na lura akwai rikon addini a gidan Baba Liman kuma ba sa nuna kyama ga wanda ba Musulmi ba!
A haka na fara tuno maganganun Janan, ji nayi ina son nima in koma Musulunci!
Ana saura kwanaki 2 mu gama Seminar din mu naje na samu Baba Liman na fada mishi ina so in koma Musulunci, yayi farin ciki da jin haka! Ni nace a maida min sunan na farko wato SHUREIM!!
Tunda na shiga Musulunci nake karo da abubuwan alkhairi tare da cin nasara a duk abunda nasa agaba, kuma a lokacin ne nayiwa Yar Mataimakin Gwamna Plastic Surgery!
Ko san da na bar aiki na dawo gida naga su Momma still suna cikin addinin dana barsu ciki, nayi bakin ciki na so in fada musu na canza addini amma na san hankalin su ze tashi shiyasa ban sanar da su ba se dai na cigaba da musu addua'a Allah ya ganar dasu gaskiya !!!
Maganar shi ta kashe musu jiki sosai! Janan murna da farin ciki take yi sosai tare da godia ga Allah!
Zarah ita ma ta basu labarin komai da yanda ta Musulunta!
Dad yace "a yau zamu bar wannan addinin 'bata, kuma duk abunda na samu a cikin addinin zan barsu domin in yi kyakyawan tuba! Kuma ina rokon Allah ya yafe min duk zunubai na, Lallai munyi babban asara! Ya karasa maganan cikin kuka!
Dad da Momma kuka suke yi kamar za su shide, kowa na wajen jikin shi ya mutu ga tausayin su Dad na halin da suka shiga!
Baba Liman yayi gyran murya sannan ya fara da fadin "Yabo da godiya sun tabbata ga Allah, abubuwa sun faru wanda dama kaddara ce kuma yana nan a rubuce a cikin littafin kowannen mu, bamu isa mu canza abunda Allah ya tsara ba! Saboda haka mu gode mishi da har yasa baku mutu a cikin wannan addinin ba!
Nan suka karbi kalman shahada!
Kabbara kawai ke tashi a parlor'n! Se da suka ci abinci suka koshi sannan suka tafi cike da farin ciki mara misaltuwa!
Suna komawa gida suka yi wankan shiga addinin Musulunci! Se a lokacin suka samu natsuwa da kwaniyar hankalin da suka rasa na shekaru masu yawa!
鈾�
Dr. Shureim sun kara fahimtan juna shi da Janan din shi, ga wani zumunci me karfi daya kara shiga tsakanin gidaje biyun!
Ya tambaye ta dalilin da yasa aka fasa auren ta da Imran! Bata boye ba ta fada mishi komai!
Wani irin soyayya ta ban mamaki ya kara shiga tsakanin su, magana tayi karfi dan har iyayen su sun san komai!
A haka hutun su ya kare suka koma sch inda a yanzu suke 300 lvl! Sosai Dr. Na kula da ita dan duk karshen sati se ya je sch din su ziyara!
*******
Tunda suke hanya za su dawo daki daga lectures Zarah take waya har se da suka shiga daki sannan ta ajiye wayan, Janan tace "Sis wai ke dawa kike waya tun dazu ne?
Zarah tace "Ni da Bro Saleem ne mana!
Janan tace "uhum! Ni fa ban gane tsakanin ku da Yaya Saleem ba, naga kuna wani mannewa ne kaman chewing gum!
"Bestie sa ido fa ba kyau! Me kike tunani toh!
"A! Ni ba ruwa na, nawa ido ne! In tayi wari ma ji!
Suka yi daria!
Duk wani abu da Dad yasan ta hanyan haram ya same su ya fitar ya maida musu Church harda takardun gidajen daya siya tare da tabbatar mu su ya bar addinin su ya koma Musulunci!
Sun yi bakin ciki tare da cewa za su bashi ninkin kudin da ya dawo da shi!
Dad yace "ni yanzu ba wannan bane a Gaba na, ina so in gyara kurakuran da nayi kuma in ma addini na hidima! Ya fice daga cocin!
Gidan su Ummiey ya je ya samu Momma, nan yake fada musu yanda suka yi, bayan Ummiey ta tashi yace ma Momma "Yanzu ina kike ganin zamu koma? Ba ni da komai daga mu se rigunan jikin mu!
Kusa dashi ta koma tare da kamo hannun shi tace "kada ka damu, Allah zai ba mu yanda za muyi!
Can yamma Dr. Shureim ya shigo gidan su Ummiey, bayan sun gaisa yace "Ummiey, Momma, Abbiey da Dad, ina so in roki alfarma a wajen ku, zamu je wani waje ne Gaba dayan mu!
Basu musa ba suka shiraya, a motan shi suka fita!
Kofan wani hadadden gida suka tsaya, gaba dayan suka fito yace su shiga! Komai yaji a gidan dan an tsara shi seda suka gama duba ko ina suka dawo parlor suka zauna!
Gaban su Momma da Dad yaje ya durkusa tare da ruko hannun su! Makulli ya sa musu a cikin hannun tare da fadin "wannan shine gidan ku, ina fatan zaku so shi kuma yayi muku!
A tare suka rungume shi suna sa mishi albarka!
Dadi ya dinga ji saboda ya faranta musu rai! Nan su Ummiey suka mishi godia!
鈾�
Haduwa akayi bayan dogon nazari da lura aka sa auren Janan da Shureim, Saleem da Zarah, Khaleel da Hameeda sister'n Imran! Shi kuma Imran aka hada zumunci da Zee inda se da akayi da gaske ta yarda wai kar Janan tayi tunani zata ci amanarta!
Anyi hidima sosai tare da komai cikin tsari, duk da suna da kudi hakan be sa sun yi almubazzaranci ba!
Daurin auren su ya tara jama'a masu yawa inda aka daura auren Janan da Shureim, Saleem da Zarah akan sadaki mafi karanci dan auren yayi albarka! Angwaye sun sha akon cikin manyan fararen kaya!
Ana gama daurawa aka tafi Kaduna aka daura na Khaleel da Hameeda! Shi kuma Imran da Zainab!
Walima, Kamu da Dinner kadai akayi! Amare suka tare a gidajen su!!!
_RukkyBae_馃槒馃槒馃槒
[1/11, 10:50 AM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [1/8, 10:29 AM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: 鈾モ潳鉂ゐ煐も櫍鈾犫櫏鈾b櫍鈾モ櫏鈾犫櫍鈾モ櫊鈾モ櫍鈾犫櫏鈾b櫊鈾b櫏鈾モ櫍鈾b櫊鈾モ櫏鈾モ櫍鈾b櫊鈾b櫏鈾b櫊鈾モ櫍鈾犫櫏鈾� *MATAR DOCTOR* 鈾犫櫍鈾b櫊鈾b櫍鈾b櫍鈾犫櫍鈾モ櫏鈾b櫏鈾b櫊鈾モ櫍鈾犫櫍鈾モ櫏鈾b櫊
_RukkyBae_馃槒馃槒馃槒
馃寪 *HAJOW* 馃寪
鉁嶐煆烩湇馃徎 *_Hakuri Da Juriya Online Writers_* 鉁嶐煆烩湇馃徎鉁嶐煆�
_Alhamdulillah!_
鈾�
_Alhamdulillah!!_
馃枻
_Alhamdulillah!!!_
鈾�
鈾� *_LAST PAGE_* 馃枻
1鈨�2鈨�0鈨�
Da sallama Dr. Shureim ya shigo dakin Amaryar sa, zaune ya tadda ita a kan gado an nade jikin ta da Lapaya, a hankali ya karasa tare da ajiye ledojin hannun shi!
Gadon ya hau tare da bude mata fuska! Ido ta runtse sbd kunyar da take ji! Murmushi yayi yana fadin "Alhamdulillah! Nagode da Allah ya nuna min wannan rana wacce ba zan taba mantawa da ita ba, yau babban buri na ya cika, ina rokon Allah ya bani ikon kula dake tare da kare miki dukkan hakkin ki dake kaina, sannan ina neman alfarmar ki da kiyi hakuri da duk wani laifi da zan miki cikin sani ko akasin haka domin shi Dan Adam ajizi ne! Allah ya bamu hakurin zama da juna cikin so, kauna, rikon amana, gaskiya da kuma juriya!
Tun da ya fara maganan bata ce komai ba kuma bata dago ta kalle shi, ji tayi wani irin son mijin ta na ratsa dukkan sassan jikin ta ga kuma girman shi da a yau taji ya kara nunkuwa a zuciyar ta!
Ganin bata yi magana ba yasa shi tashi tare da cire malum_malum din shi sannan ya mika mata hannu alaman tazo! Cike da jin kunya ta rarrafo a hankali sannan ta mika mishi hannu, mikar da ita tsaye yayi sannan ya riko ta ta gefe suka wuce toilet! Alwala suka yi sannan suka fito! Da sauri Janan ta nufi akwatunan ta dake gefe ta ciro darduma guda 2 se dagon Hijjab da socks! Daya ta shimfida mishi sannan itama ta shimfida nata a baya, seda ya jira ta saka socks din sannan ya tada sallan!
A nutse tare da kaskantar da kai yake jan su sallan! Rakao'i biyu suka yi sannan ya sallame! Juyowa yayi yana kallon ta dai dai ta dago ido ya sakar mata murmushi, itama murmushin tayi, har gaban ta ya matsa sannan ya mika hannu ya daura a saman kanta, adduo'i ya dinga jerowa sannan yayi mata tambayoyi akan addinin ta, duk da ya san tana da ilimin amma yana so ya kara tunatar da ita, bayan ta amsa mishi ya umurce ta itama ta tambaye shi!
Tayi mamakin yanda ya dinga bata amsa ba tare da kuskure ba! Shi da kanshi ya dakko plate da cups ya zuba musu Holandia da gasasshiyar kaza! Da kyar ta iya ci sbd kunya danma shi ya dinga bata har suka koshi, tare suka nufa kitchen ta wanke kayan shi kuma ya dauraye ya maida su in da suka sannan suka koma daki, toilet suka shiga suka yi brush!. Gado suka hau tare da yin addua'a! Sun bautawa Allah tare da raya sunan Manzo Allah SAW a daren!
Haka zaman su ya dinga tafiya cike da so da kaunan juna gashi dama Dr. An bashi hutun, babu inda yake zuwa suna tare kullum se dai in ya tafi masallaci sallah!
Tare suke wanka, gyaran daki, shara, wanke_wanke da girki, komai tare suke yi hatta wanki da guga su suke yi da kan su!
Yau ta kama Weekend, bayan Dr. Shureim ya dawo daga sallan azahar suka shiraya suka nufi gidan su Momma, a nan suka tadda Abbiey da Ummiey, Janan taji dadi sosai dan tun bayan bikin su bata kara ganin su ba se dai suyi waya! Dr. Shureim ya duka har kasa ya gaida su sannan ya gaida su Momma!
Momma da kanta ta tashi ta debo musu dambun nama da juice, su na ta hiran su, Janan da Dr. Shureim kuwa suna ta faman kallon juna suna murmushi, ana haka Zarah da Yaya Saleem suka shigo!
Wani irin ihu Zarah tayi tare da fadowa kan Janan se gasu sun zube a kasa Dr. Shureim yace "ke miye haka? Kada ki karya ta mana! Ya tashi daga inda yake ya dago Janan yana fadin sorry Darling" gaba daya ya manta da su Ummiey a wajen ita ko Janan tayi kasa kasa da murya tace "ga fa su Momma a zauna kar suce ba muda kunya"
Kai ya dan sosa sannan ya mika hannu suka gaisa da Yaya Saleem!
Gefe Zarah taja Janan suka dinga hiran su, Mai Gadi yayi sallama daga waje, suka amsa Dr. Shureim ya tashi yaje yace "Ya dai?
Ina wuni Likita bokan turai? Be jira ya amsa ba ya cigaba da fadin, wasu Mutane ne su biyu suka zo wai suna neman Alhaji, dayan ma a keken guragu aka turo shi, shine suka ce in musu iso''
Kace su shigo! Watakila suna neman taimako ne!
(Tun bayan abunda ya faru da Dad yayi alkawarin taimaka wa duk wanda ba shida karfi! Gaba daya Dr. Shureim ya dauke nauyi su kuma duk wata yana turo musu kudi)
Dr. Shureim ya koma ciki ya fadawa Dad, sannan ya zauna!
Sallama aka yi tare da daga labulen! Zunbur Dad ya mike yana kallon su haka ma Momma, a hankali aka dinga turo wheel chair din har gaban Dad sannan suka tsaya!
Kallon su kawai Dad yake yi amma ya kasa magana dan ya rasa abunda ze ce be gane na tsayen ba amma ya gane na kan kujeran guragun!
Momma tayi karfin halin fadin "Yaya Hamza? Kaine? Kaine a haka? Kuka ya subuce mata ta koma ta zauna a kujera!
Dad da idon shi suka yi ja yace "me yasa ka neme ni? Me yasa ka tuno kana da wani dan Uwa a duniyar nan?
Yaya Hamza yace "Kayi hakuri Kanina, ka yafe min na san ban kyauta maka kuma ban yi maka adalci ba, na cutar da rayuwar ka, ni ne na turo yan fashi suka kwashe kudin ka sannan suka kona maka gida sbd ina so ka shiga wani hali.. Bayan na biya su an kwana biyu nima suka zo suka kwashe komai harda takardun gidaje na sannan suka min duka tare da karya min kafafu sanadin haka na zama gurgu! Kuka yaci karfin shi!
Salati kawai Dad yake yi sbd yanda jikin shi ke rawa... Duk wanda ke parlor'n se da ya dauke wuta sbd jin abunda Yaya Hamza ya fada! Momma, Ummiey, Janan da Zarah kuka kawai suke yi!
Dr. Shureim dake zaune ya tako har inda yake, da ganin shi yana cikin bacin rai da bakin ciki.. Dai dai setin kafafun shi ya durkusa yace "mun gode da abunda kayi mana kuma mun ji bayanin ka saboda haka ku tafi! Ya mike tsaye dan ya san in ya cigaba da magana ze iya fadan abunda be dace ba!
Kwata kwata Dad ya kasa magana se kallo kawai yake bin Yayan nashi da shi yana jin wani irin daci a zuciyar shi wai yau ace Dan Uwanka Uwa daya Uba daya ke maka wannan hassadar tare da son ganin bayan ka? Me ya tsare mishi? Daga ya karbi hakkin shi shikenan! Oh Duniya ina zaki damu ne?
Cikin dauriya da karfin hali ya bude baki yana fadin ''Lallai kaci amanan iyayen mu, ka ci amanar zumunci, ka cuce ni ka cuci kan ka, ka zama silan fadawa ta halaka ni da iyali na, saboda haka ni bani da dan Uwa illa wannan bawan Allahn da ka gani zaune ya nuna Abbiey, kuma ba zan taba yafe maka ba sannan daga karshe ina baka shawaran ka fice min daga gida kafin in sa a maka koran wulakanci kuma in kira yan sanda! Sannan baka ga komai ba ma in dai alhaki ne yanzu ya fara binka! Tari ya sarke shi a nan ya fadi kasa, gabaki daya suka yo kanshi, jijjiga shi Momma ta dinga yi amma kamar ba shida rai!
Da gudu Dr. Shureim ya nufi motan shi ya dakko kayan aiki, yana zuwa ya fara dudduba shi nan ya gano jinin shi ne ya hau sosai! Ruwan sanyi ya sa Zarah ta dakko a fridge ya dinga shafa mishi, can Dad yayi ajiyar zuciya alamar ya farfado kenan! Waigawa yayi ya ga Yayan shi yana nan be tafi ba, sake runtse ido yayi yana son yin magana! Ganin haka yasa Abbiey tashi yaje har gaban Yayan yace "kayi hakuri muje waje"
Jiki a sanyaye Yaron shi ya ja keken suka fita Abbiey na bin su a baya! A tsakar gidan suka tsaya Abbiey ya karaso yace "kayi hakuri da duk abunda ka gani, ka san dole abun ze mishi ciwo kuma ba zai iya furta ya yafe maka ba a cikin halin da yake ciki ba! Tas Abbiey ya kwashe duk abunda ya faru dasu Dad ya fadawa Yaya Hamza!
Hankalin Yaya Hamza ya tashi sosai da sosai, wani irin nadama da dana sani suka saukar mishi! Wasu hawaye masu zafin gaske suke ta zubo mishi, Lallai ya san cewa yayi babban kuskuren da baya fatan sake maimaitawa! Jiki a sanyaye suka bar gidan!
Gaba daya abunda ya faru ya dagula wa Dad lissafi, ya kasa mantawa, a haka Abbiey ya dinga mishi Nasiha yana fada mishi ladan da zai samu idan ya yafe ma Dan Uwan shi!
Se da akayi sati sannan Dad ya hakura, tare da Abbiey suka je gidan da Yaya Hamza ke haya wanda gidan kamar na almajirai saboda lalacewa!
Nan Dad ya tabbatar mishi da ya yafe mishi, suka rungume juna! Suna kukan farin ciki! Washe gari ya sama mishi gida yace su dawo shida yaran shi, ya jibge musu kayan abinci, harda masu aiki guda biyu!
In an samu hutu dukkan su suke tafiya Kano wajen Dangin Momma haka ma suna zuwa Sokoto wajen abokan arziki! Sosai Dad yake musu alkhairi!
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, duk bayan sati 2 sukan je gidan su Momma ko gidan su Ummiey! Hakanan suna zuwa gidan su Zarah ko kuma su su zo! Har gidan su Yaya Khaleel suna zuwa!
Akwai randa suka shirya suka je gidan su Imran, sun ko ci saa yana gida, sosai yayi farin ciki da zuwan su! dr. Shureim da Dr. Imran suna ta hira ita kuma Zee da Janan suka shige daki suna nasu hiran! Se da yamma suka tafi cike da jin dadi!
Tunda Da Dr. Shureim ya koma wajen aiki Janan ta zama tamkar marainiya, duk da idan ya samu sararin aiki suna waya sosai!
Cikin haka har hutun su ya kare suka fara shirin komawa sch, dauriya kawai Doctor ke yi amma gaba daya ya rasa me ke mishi dadi!
Tare suka tafi da Yaya Saleem da Zarah! Ya Saleem ke tukin Zarah na zaune a gefen shi! Dr. Shureim su kuma suna zaune a baya shida Janan! Tana kwance a cinyan shi yana ta fama shafa kanta! Seda suka tsaya suka siya abinci, snacks da drinks sannan suka cigaba da tafiya! Suna zuwa sch din suka ce su jira su a mota, su suka musu duka reg din su! Dama Dr. Shureim yasa an kama musu wani 2 bedroom flat dan yace ba za su koma hostel ba, can suka nufa seda suka yi sallah sannan suka cinye sauran abincin! Dare nayi su Zarah suka dau daki daya su Janan ma suka dau Daya! Washe gari da safe suka shiga kasuwa suka siyo abubuwan da za su bukata! Se da yamma sannan su Dr. Suka shirya tafiya! Janan ta sha kuka kamar ranta ze fita haka ya dinga jin kukan har zuciyar shi ji yake kamar ya bude kirjin shi ya sata a ciki, da kyar ya samu tayi shiru da alkawarin duk sanda ya samu time ze dinga zuwa dubata! Zarah ma ta sha kuka amma ba kamar Janan ba! Har bakin mota suka raka su, wannan karon Dr. Shureim ne ze tuka! Sun tafi cike da kewan Matan su! Suma haka suka dinga kewan mazajen su!
鈾�
Shekaru sun ja sosai dan a yau ake yaye su Janan daga makaranta a matsayin Cikakkun Likitoci! Farin ciki kawai suke yi tare da godia ga Allah! An bata kyauta a matsayin wacce ta kafa tarihi a makarantan dan har kawo lokacin ba a dena MSS ba!
Zarah na nan da Babyn ta haka ma Zee da Hameeda Matar Yaya Khaleel! Janan kam har yanzu Allah be bata ba! Cikin yan tsakanin nan aka yi Bikin Eeesher da saurayin ta Pharouk, Fatima da saurayin ta Dawud! Janan ta je musu duk da bata kwana ba amma an kai amare da ita!
Babban asibiti Dr. Shureim ya gina inda ya dauki kwararrun Likitoci da Nurses har da Pharmacists! A cikin asibitin ya ginawa Zarah Pharmacy (dakin shan magani) dan be manta alkawarin daya mata tun tana karama! Karshen shekara yake so su fara aiki, an samu tsaiko ne wajen isowar kayan da yayi ordering daga India! Se kuma Dan gyare gyare da baya a rasa ba!
A lokacin Janan ta samu ciki, laulayi take yi sosai gashi bata iya cin komai, gaba daya hankalin Dr. Shureim na kanta! Seda cikin ya shiga wata uku sannan ta rage laulayin se dai bata cin komai se Buredi da yaji se kuma tasha Bobo!
Dawowan shi kenan daga duba asibitin shi ya ganta zaune akan kujera tana cin Buredi da yaji, har inda take ya karaso ya jingina da fuskan ta yace " kina nan kina cin abincin ki kenan! ya Baby na? Baki ta turo tace "tun kafin a haifi Baby har ka fara nuna son kai ko?
Kunnuwan shi biyu ya kama yana fadin "a yi Hakuri, ai se da na fara sanin Maman Baby kafin in san Babyn afterall ma Babyn is still unborn sbd haka ki kwantar da hankalin ki babu batun son kai!
Har dining ta kaishi yaci abinci seda ya gama sannan suka fara hira yana bata labarin yanda aikin asibitin ke tafiya! Sosai taji dadi tare da fatan alkhairi!!
Cikin ikon Allah asibitin ya samu karbuwa dan ba sa cika kudi kuma suna iya bakin kokarin su wajen taimakon marasa karfi! A kusa da office din shi ya ginawa Janan nata office din dan har akwai ma kofa ta ciki da zai iya sada su da juna!
Yau ta samu marasa lfya sosai amma haka be sa ta gaji ba, wata ce ta shigo ta zauna! Dr. Janan na duba result din ta! Ji tayi an rufe mata ido da tafin hannu ta baya, murmushi tayi tare da fadin wanene?
Yace "chewing gum din ki ne! Haka take ce mishi idan tana son tsokanan shi!
Hannu ya zura ya shafo cikin ta da ya fara girma yace "I missed u Both!
Kafin Janan tayi magana suka ji an ce "Godwin? Cike da mamaki suka dago suna kallon me magana! Precious ce tsohuwar budurwar shi , kallon ta kawai Janan ke yi dan ba zata taba manta fuskarta ba se dai yanzu tayi baki ta rame!
Se da ya kalli fuska Janan yaga ba bacin rai a tare da ita sannan ya kalli Precious yace "yanzu ba sunana Godwin ba sunan Shureim nd here is my Wifey! Ya ruko hannun Janan yana murzawa!
Kuka kawai take yi se yanzu take da na sanin abunda ta dinga aikatawa ga shi yanzu tana dauke da chronic infection wanda watakila se an mata aiki ga kuma cancer'n mahaifa!
Tace "kayi hakuri, naso in cutar da kai amma ban yi nasara ba sbd kai baka zina, garin biyebiye na yanzu gashi ina dauke da cuta! Ta cigaba da kukan ta!
Wani irin sanyi Janan taji a ranta da yau Precious ta kara wanke mijin ta kuma a yau ta kara tabbatar da shi kamilin Namiji ne! Shiru yayi se can yace "kin ga illan abunda nake fada miki ko? Yanzu wa gari ya waya? Mece ce ribar ki in banda zubar da mutuncin ki da kika yi daga karshe kuma kika kwaso cuta? Kina da sauran lokacin barin wannan shirmen tun kafin ki hadu da cutar Kanjamau!
Ita dai ta kasa magana se kuka, a haka Dr. Janan ta duba ta tare da rubuta mata magunguna! Jiki a sanyaye ta bar asibitin tana dana sani mara anfani!
Janan ta rungume shi tace "I love u so much my chewing gum! Kara rungume ta yayi se ko Baby ya fara motsi, a tare suka kai hannu kan cikin tare da tuntsurewa da dariya suna fadin "we love u our unborn!
Wata tara cif Janan ta haifi Babyn ta namiji me kama da Dr. Shureim! An yi shagalin suna inda Yaro yaci sunan Dad wato Ahmad amma suna kiran shi da Imam!
Bayan Shekaru masu yawa! Janan ce kwance gefen ta Dr. Shureim ne suna ta bacci, kiran sallan farko tare da bugawan alarm ya tada su, tare suka yo alwala suka fito! Nafilfili suka gabatar sannan suka yi raka'atanil Fijir! Dakin su Imam ya nufa ya tada su dan su wuce sallah shida kanin shi me sunan Abbiey wato Pharouk amma suna kiran shi Mahbub! Masallaci suka wuce dan tun basu kai haka ba yake zuwa dasu masallaci dan ya sa musu son ibadan! ita kuma Janan ta nufi dakin yammatan ta ta tada su, Khadeeja me sunan Ummiey suna kiran ta Iman, Haleema me sunan Momma suna kiran ta Baby se Little Janan suna kiranta Little! Suma suka yi alwala suka yi sallah! Bayan dawowan su daga masallaci kowa ya biya karatun shi na Qur'ani Baban su ya musu kari haka suma Matan suka biya nasu Maman su tayi musu kari! Da yake ranar ta Jumma'a ce gashi ana public holiday dan haka basu koma bacci ba seda gari yayi haske Sannan suka koma! 10 dai dai Janan ta farka ta shiga kitchen dan hada musu abun kari tun kafin ta fara aikin dukkan su suka shigo suna gaida ta, sannan suka ce "Mum! Mun tashi ki bamu namu aikin da zamu taya ki da shi! Nan ta kasa musu kowa da abunda yake yi! Tana cikin fere dankali Baban su ya shigo suka gaida shi ya amsa yana kallon Janan yace "Mum em late kuma baki tashe ni ba, ki bani nawa aikin! Dariya suka yi sannan tace "saboda kayi latti kai zaka soya dankali, plantain harda kwai!
Fuska ya bata yace shikenan duk ni kadai zan yi wannan aikin?
Tace "of course yes!
Cikin lokaci kankani suka gama kammala abun break din sannan suka ci!
Daya bayan daya suka yi wanka, dukka yan mazan suka shirya cikin farin shadda me malum-malum harda Baban su, su kuma matan suka sa jallabiya iri daya da Maman su!
Bayan su Dr. Sun dawo daga sallan Jumma'a dukkan suka tafi kaima su Momma Ziyara daga nan suka je gidan su Ummiey, Yaya Khaleel, da Yaya Saleem ! Se can dare suka dawo bayan sun biya ta Mr. Bigs sun yo takeaway!
Tunanin zaman su take yi ita da Dr. Shureim duk da akwai soyayya a tsakanin su amma yau da gobe se Allah wata rana ayi fada wata rana a shirya! Ta lura cewa ba kasafai ake fadin kalman ayi *HAKURI* ba se dan rayuwar aure dole se da hakuri dan ba zaka samu komai dari bisa dari ba!
Jin alaman motan ya tsaya yasa ta dawo daga Tunanin da take yi!
Bayan sun ci abinci kowa yayi brush tare da yin alwala suka yi shafa'i da Wutri sannan suka wuce dakin su! Kayan bacci suka sa suka hau gado sannan suka yi addua'an bacci, Maman su da Baban suka shigo suma suka sake musu addua'a tare da manna ma kowannen su peck a goshi suka rufe su da bargo tare da kashe musu wuta!!!!!
*_Tammat Bi hamdulillah! Alhamdulillah! Allah na gode maka da ka bani iko na kammala wannan littafin lafiya! Kuskuren da nayi Allah ya yafe min abunda na fada masu kyau Allah ya bamu ikon anfani da su!!__*
_RukkyBae_馃槒馃槒馃槒