Tana b'acewa b'at bata sauka a ko'ina ba sai a can bayan gari cikin d'an daji,,, tana bayyana a cikin dajin tayita yawonta da shawagi tana d'ebo wasu itacen da zata had'a tayi wani maganin sihiri,,, bayan ta kamalla d'iban duk abinda takeso daga cikin dajin,,, saita juyo ta fara tafiya domin komawa gidanta,,, tayi tafiya mai nisa harta kusa shiga cikin gari kwatsam! Babu zato babu tsammani taga Ummaru d'an Sala mafarauci agabanta kamar an jefosa,,, ta murza idanunta domin tabbatarwa idan ba mafarki takeyi ba,,, gabanta ya buga da k'arfi rassssss! Hankalinta yayi k'ololuwar tashi sosai amma ko a fuskarta bata nuna masa ba,,, tayi tsaye tana jiran taga irin abinda zai faru atsakaninsu. Ummaru ya dubeta yayi murmushin mugunta da jin dad'i,,, sannan yayi mata walak'antaccen kallo yace "kin gama b'oye b'oyenki da guje gujenki Gwamma mayya,,, dama na gaya miki idan kere yana yawo zabo ma yana yawo wata rana dole su had'u,,, saboda haka yanzu nan zan gana miki azaba sannan in shiga dake cikin gari kowa ya ganki a walak'ance! Sannan in kasheki kamar yadda kike kashe wasu ".Iya Gwamma ta bushe da mahaukaciyar dariya sosai sannan tace "Ummaru kenan ka d'auka kasheni abu ne mai sauk'i awurinka,,,ko ubanka Sala mafarauci na kashesa cikin sauk'i bale kai! Saboda haka k'aryarka tasha k'arya ka kaini a walak'ance cikin mutane,,, saina gana maka azabar da baka tab'a shanta ba a rayuwarka! "."yimin shiru bak'ar annoba dangin tsiya,,,, idan kin saba kashe mutane acikin sauk'i,, toni naci dubu sai ceto ba zaki iya jadani ba Gwamma azzaluma macuciya mai cin naman mutane da aljannu! ".Cewar Ummaru d'an Sala mafarauci cikeda matuk'ar hasala,,, Iya Gwamma ta dubesa da idanunta jawur kamar barkono,, jijiyoyin kanta suka tashi tsaye rud'u rud'u akan b'acin rai k'arara tace "hak'ik'a ka tafka babban kuskure daka tunkareni gaba da gaba,, yau zan shayar dakai d'acin mutuwa ayau sai dai uwarka ta haifi wani amma ba kai ba! ".Ummaru ya harareta yace "sai an gwada akan san na k'warai,, saboda haka yau zan gabatar dake durk'ushe agaban mutane domin kowa yasan Gwamma mayya,, shahararra azzaluma mara imani azuciyarta ".Kai! Ya isheka ayau zakasan ka zageni saikabi ubanka acan lahira! In yaso ka iskosa acan barzahu! "Cewar Iya Gwamma cikeda hasala da jin haushi,,, Ummaru yace "karki kuskura ki gayamin maganar banza shegiyar karuwa! Annobar gari k'are dangi,,, wadda tayi abin kunya acikin gari ".
"yanzu kuwa zan nuna maka ainahin wa ce ce Gwamma ".Ta rufe bakinta ta afka masa suka rungutsume da azababban fad'a mai cikeda tashin hankali da bala'i! Naushin juna da bugun juna kawai sukeyi cikeda matuk'ar dauriya da zafin nama,,, Ummaru yana amfani da takobinsa domin ya kare kansa yayinda Gwamma ke jifarsa da ababen tsafi irinsu wuk'a,, mashi,, wuta,, kibiyoyi da dai sauran abubuwan mugunta iri iri daban daban,,, da bala'i yayi bala'i ta dinga feso masa wuta jawur yana kaucewa,, ta k'ara karanta d'alamisai na tsafi wata irin bak'ar guguwa ta bayyana,, ta d'auki Ummaru tana hajijiya dashi asama yasha wuya sosai sannan yayi wata addu'a,,, guguwar ta b'ace b'at kamar k'iftawa da bismillah,, ganin haka ne yasa ta k'ara yin wani sihirin k'aton rami da macizai ya bayyana a tsakiyarsu! Yana bayyana igiyar tsafi ta fito daga cikin ramin ta d'aure k'afafun Ummaru tana jansa da k'arfi,, yasha bak'ar wuya sosai sannan yayi wata addu'ar ramin ya b'ace b'at kamar bai tab'a wanzuwa ba! Iya Gwamma ganin ya tsira ne yasa ta k'ara harzuk'a da hasala ta feso masa ruwa tafasasshi suka zuba ajikinsa! Ummaru yayi kuwwa da kururuwar da k'arfi akan zafi da rad'ad'in ciwon ruwan zafi,, fatarsa jikinsa ta fara kwayewa akan masifa ganin ya fad'i d'immmmm ak'asa yasa Iya Gwamma ta bushe da mahaukaciyar dariya sosai tace "bazaka iya ja dani ba Ummaru,,, ubanka ma baisha d'a dad'i ba a wajena! ".Tana gama yin magana ya taso cikeda matuk'ar zafin nama ya naushi fuskar Iya Gwamma cikin shammata,, ai kuwa ta fasa gigitacciyar k'ara da kuwwa da k'arfi! Bakinta ya fashe da jini tasa hannunta ta lakato jinin dake zuba daga cikin bakinta,, tana ganin abinda ya faru da ita rayuwarta ta k'ara b'aci idanunta suka k'ara ja ta girgiza sannan ta rikid'a ta koma gwaggon biri,,, ta sake afkawa Ummaru suka sake rungutsumewa da wani rikitaccen fad'a cike da bak'in rai da mugun nufi! Dajin gaba d'aya ya kama girgiza da rawa tanbal tanbal kamar zai kife acikin k'asa,, masifa tayi masifa bala'i yayi bala'i dajin gaba d'ayansa ya kama da wuta yana k'onewa,,,tsuntsaye da dabbobi sai hijira sukeyi suna barin dajin baki d'ayansa.
Haka dai suka cigaba da azababben fad'a cikeda tashin hankali! Ummaru ganin wankin hulla zai kaishi dare yasa ya k'ara k'aimi,, tareda tattaro dauriya da zafin namansa ya chanza salon fad'ansa nan da nan ya rikita hankalin Iya Gwamma,, ya samu ya yanketa a cinyar k'afar dama ihu da kururuwar Gwamma kawai kakeji ta fad'i k'asa cikeda matuk'ar zafi da rad'ad'in ciwo! Ummaru yayi hanzari da sauri yasa igiya ya d'aure Gwamma,,,, ya d'auketa ya azata saman kafad'unsa ya nufi hanyar zuwa cikin gari fadar maigari Garba.
********************
Alhaji Suleiman da Mama Sa'ima sunje gaisuwar rasuwar Fadila cikeda jimamin mutuwa da sanyin jiki,, anan ne suke k'ara jajantawa juna hak'ik'a Mama Nafisa tayi matuk'ar basu tausayi sosai,,, saboda duk ta fita acikin hayyacinta kallo d'aya zaka yi mata kasan tana cikin rad'ad'in zafin mutuwar Fadila,, anan ne Alhaji Suleiman yake sanarda baba Nura akwai Malam Usama da zaizo gidansa yayiwa su Fatima magani,,, baba Nura ya nuna babu matsala ya umurci Fadil daya d'auki Fatima ya sanyata cikin motar Alhaji Suleiman,, Fadil ya d'auki fatima ya sanyata cikin motar baban Maryam,, shima ya zauna bayan motar rungume da Fatima Alhaji Suleiman yaja motarsa suka wuce direct zuwa gida.
Ya parker motarsa a waje sannan suka fito daga cikin motar gaba d'ayansu,, Fadil ya d'auko Fatima daga cikin motar suka nufi cikin gidan suna shiga suka iske Malam Usama zaune,, Alhaji Suleiman yayi murmushi tareda bayyanar da farin cikinsa da fara'arsa,, yaje wurin Malam Usama sukayi musabaha da sallama da juna,, Mama Sa'ima ta shige cikin d'akinta.
Malam Usama ya aje casbaharsa da qur'ani agefe,,, ya kalli Alhaji Suleiman yace "akawomin ruwa masu tsabta yanzun nan ".
Alhaji Suleiman yace" to Malam Fadil jeka ka kira Maman Maryam sannan kace tazo da ruwa masu k'yau".
Fadil yace "to baba ".Tareda mik'ewa tsaye ya nufi hanyar zuwa d'akin Mama Sa'ima,, babu jimawa sosai saiga Mama Sa'ima ta fito tareda Fadil d'auke da jug d'in ruwa a hannunta,, suna isowa ta aje ruwan agaban Malam Usama ta koma gefe ta zauna.
Malam Usama ya d'auki ruwan ya fara karatun qur'ani da addu'o'i na tsari da sihiri,, ya jima sosai yana yin addu'ar sannan daga baya ya tsaya ya d'auko gagarin maganin ya zuba acikin ruwan yana jijjigewa da sauri,,, yana gama jijjigar ruwan maganin ya watsasu ajikin Maryam da Fatima ,,,ai kuwa batare da b'ata lokaci ba sukayi wani irin gigitacciyar k'ara da kuwwa da k'arfi! Suka kama zabure zabure da shure shuren zafin magani,,, Malam Usama ya cigaba da yi musu karatun qur'ani da addu'o'i kala kala,,, kuwwa da kururuwarsu Maryam kawai ke tashi acikin parlourn su Mama Sa'ima jikinsu sai rawar tsoro yakeyi itada Fadil cikeda matuk'ar firgita da fargaba! Ya dad'e sosai yana yi musu karatu sannan daga baya kowacessu tayi atishawa da k'arfi sau uku nan da nan barci ya d'aukesu batare da b'ata lokaci ba.
Malam Usama yayi murmushi sannan yace "Alhmdlilah yaran sun samu lafiya Alhaji Suleiman dama mayya ce ta kamasu,,, sannan ta had'asu da miyagun aljanu domin kada suyi saurin samun waraka,, yanzu dai godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikkai wanda ya bani ikon k'ona aljannu da yardar Allah,,,, shikenan da sun tashi daga barci sun warke har abada,,, zan basu wani turare da garin maganin da zasu cigaba da shafawa garin kuma wanka akeyi dashi ".Yasa hannun cikin leda ya d'auko turare kwalba biyu garin magani leda biyu,,, kowacce su d'ai d'aya.
Tsananin farin ciki da murna ne suka bayyana a fuskokinsu k'arara mara misaltuwa,, Mama Sa'ima hawayen dad'i ne suka cigaba da kwaranya daga cikin idanunta,, Fadil ma sai kwallar murna yake fitarwa,, Mubarak daya shigo ayanzu cikin parlour amma yaji abinda Malam ya fad'a bakinsa yak'i rufawa akan murna da farin ciki sosai,, ya samu wuri kusa ga Fadil ya zauna fuskarsa d'auke da farin ciki da nishad'i sosai.
Alhaji Suleiman akan farin cikin dake d'auke afuskarsa har rungume Malam Usama yayi yanata zuba masa godiya,,, tareda da kwararo masa addu'o'i na gamawa lafiya. Can ya bud'i baki yace "hak'ik'a godiya ta tabbata ga Allah ubangijin sammai da k'assai wanda yake sanya ciwo alokacin da yaso,, sannan ya warkar da bawa aduk lokacin da yaga dama,, Malam Usama mun gode sosai Allah ubangiji ya saka maka da mafificin alkhairi yasa ka gama da duniya lafiya ".
Gaba d'ayansu yan parlourn sukace "amin amin ".Fuskokinsu d'auke da farin ciki da nishad'i sosai k'arara,, daga gani babu tambaya kasan suna cikin jin dad'i da farin ciki sosai.
"wannan ba wani abu bane Alhaji ai an zama d'aya,, Allah ubangiji dai ya tsare gaba ni yanzu zan wuce zuwa gida ".Ya aje ledar maganin ya tashi tsaye ya nufi hanyar fita daga cikin parlorn,, Alhaji Suleiman ne ya bisa a baya domin yayi masa rakiya,, bayan sunje waje ne Alhaji Suleiman ya bashi kud'i masu yawa wanda shi kansa baisan ko nawa bane,, dak'yar Malam Usama ya amsa sannan sukayi sallama da juna ya shige cikin motarsa,, Alhaji Suleiman shi ko ya juya zuwa cikin gidansa fuskarsa d'auke da farin ciki da annashuwa mara misaltuwa.
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
Ummaru d'an Sala mafarauci d'auke da Iya Gwamma akafad'arsa,, ya kawota ya ajeta saman k'asa agarkar maigari Garba cikin halin somewa,, jini sai zuba yakeyi daga cinyarta yana ajeta saman k'asa,, ya shiga cikin gidan maigari ya jima sosai sannan suka fito tareda da maigari da dogarawansa,, nan da nan maigari yasa akayi sanarwa acikin gari kowa da kowa ya taru mata da maza,,, yara da manya da tsofaffi,, bayan mutane gaba d'aya sun gama taruwa wani dogari ya ciko bokiti da ruwa aka juyesu ajikin Iya Gwamma mayya,,, batare da b'ata lokaci ba ta farfad'o daga suman da tayi jikinta d'aure da igiya,, kallon mutane kawai takeyi d'aya bayan d'aya,,,Maigari ne yayi gyaran murya sannan yace "muna godiya ga Allah daya bama Ummaru nasarar kama wannan k'usurgumar mayya wadda ta addabi rayuwar mutanen gari shekara da shekaru,, ta dad'e tana cin amana da zaluntar mutane da dama ta kashe mana iyaye,,mata,,,,'yan uwa,,, yara da abokan arzik'i,,,, dama duk abinda kakeyi wata rana sai dubunka ya cika komai yayi farko k'arshensa yana nan zuwa,,, mai hak'uri mawadaci ne saboda haka gashi yanxu Allah ya tona asirin Gwamma an kamata !Dama na gaya muku duk wadda /wanda aka kama yana yin maita hukuncin kisa shine ya kamacesa,,, saboda haka yanzu nan za'a yankewa Gwamma hukunci dai dai da abinda ta aikata,, ina dogari Tukur ne yake? ".
Tukur ya matso da sauri kusa ga maigari ya durk'usa yace "gani rankashi dad'e ".
"kaje cikin gida ka d'auko fetur da tayar mota yanzun nan ka kawomin ".Inji maigari. Tukur yace "angama ranka ya dad'e ".Ya mike zubur da saurinsa ya shige cikin gidan maigari Garba.
.
Maigari ne ya bada umurnin a d'auki Iya Gwamma amatsa da ita kusaga icce a d'aureta,, nan da nan aka cika umurnin maigari tareda daureta tamau ga icce,, Iya Gwamma sai kuwwa da kururuwa takeyi tana cewa "ku sakeni ku sakeni wallahi idan na kwance kaina duk saina kasheku,, saina kasheku ! Nayi alk'awarin bazan bar ko d'aya daga cikinku ya rayu yaji dad'i ba,, Garba tsohon munafiki dakai zan fara kaida shegen yaron nan Ummaru! ".Haka dai suka d'auketa d'aureta ga iccen,, bada jimawa ba saiga Tukur ya fito da tayar mota da fetur yana kawowa Ummaru ya amshi tayar da fetur,,, ya sanyawa Gwamma taya a wuya sannan ya dubeta yana murmushin mugunta yace"dama na gaya maki duk daren dad'ewa saina kamaki da hannuna,, shiyasa akeson mutum ya kasance mai aikata alkhairi akodayaushe akowane lokaci baki tab'a jin ance gaskiyarka ta k'are ba,, sai dai ace k'aryarka ta k'are saboda haka yanzu nan zan aikaki can inda kika saba aika mutane da dama ".Gwamma ta kama kuwwa da k'arfi tana kuka tana cewa "wallahi baka isa ba nice zan kasheka da hannuna,, saina kashe duka mutanen garin nan saboda su suka duka munafukan......... ".Bata k'arasa maganar ba ya kyasta ashana tareda zuba mata fetur ajiki,,, Iya Gwamma ta saki wani irin gigitaccen kuka tana cewa "kada ku kasheni wallahi duk sainaga bayanku,,, saina zare muku rai daga cikin gangar jikinku wayyo Allah ni Gwamma na shiga uku na lalace! ".....haka dai wuta ya cigaba da cin jikinta bal bal bal sosai sai kuwwa da kururuwar neman agajin gaggawa takeyi,, mutane sai kuwwace-kuwwace sukeyi na tsananin farin ciki da murna sosai,, kowanensu ka kalli fuskarsa farin ciki da murna ne bayyane afuskokinsu saboda ganin k'arshen Iya Gwamma,, Hassan ne na hango wani wuri zaune.......
[7/12, 1:46 PM] Mugiratmusa66: 🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*MAYYA CE*
🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍🏻
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*Ina godiya sosai matuk'a da soyayyarku da kuma k'aunarku gareni,, hak'ik'a ina matuk'ar farin ciki da kasancewarku acikin group d'ina saboda kuna sanyani cikin nishad'i da farin ciki mara misaltuwa.*
*Maman Haneef*
*Suwaiba Danabu*
*Maman twince*
*Ummu Shaheeda*
*Maman Hanifa*
*Ummu Usman*
*Maman baffa*
*Aishat Salisu*
*Ummeen Amatullah*
*His priceless jewel*
*Mom Hauwee*
*Khadijat Lookman*
*Hajja Saki*
*Ayshat*
*Firdausi Muhammad da duk sauran wad'anda ban ambata ba ina godiya sosai matuk'a sister's.*
*LAST PAGE*
*PAGE 32*
Hassan ne na tsinkayo yayi zaune yana tagumi,,, hawayen bak'in ciki da k'uncin rayuwa sai shatata yakeyi daga cikin fuskarsa,,, jijiyoyin kansa sun tashi rud'u rud'u idanunsa sunyi jawur kamar barkono,,, baba Labbo ma kwallar takaici da bak'in cikin rayuwa ne ke zuba daga cikin idanunsa,,, tausayin Iya Gwamma ne da takaici ya mamaye zuciyarsa ga wani abu ya tokare masa acikin k'irjinsa,, Suhaila tana ganin irin kisan gillah da walak'ancin da akayiwa mahaifiyarta ta fasa gigitacciyar k'ara da razananniyar kururuwa da kuwwa da k'arfi! Wani irin kukan bak'in ciki da k'uncin rayuwa takeyi da k'arfi nan da nan ta kama fisge fisge kamar mahaukaciya sabon kamu,, 'yan uwanta mata sukazo zasu rik'eta cak numfashinta ya d'auke ta fad'i k'asa d'immmmm ta some,,,, ina lillahi wa inna ilaihirraji'un!!! Kawai mutanen wurin suke fad'a tana fad'uwa mata 'yan uwanta suka d'auketa sukayi gidan mijinta da ita!..
Tokar gawar tana gama k'onewa,, wata irin mahaukaciyar guguwa da razananniyar tsawa suka bayyana k'arara atare,,, mutane da suketa kuwwace-kuwwace da yin farin ciki da murna akan mutuwar Gwamma mayya,,, guguwar ta fara d'iban mutane tana yassuwa k'asa rikcham da majinjiwa dasu,,, mutane suna ganin irin abinda ke faruwa kowa yace k'afa mi naci ban baki ba suka ranci na kare dimm dimm dimm,,, kawai ke tashi k'arar gudunsu!. Guguwar ta daina bin mutane ta tashi sama ta lulluk'a a cikin sararin samaniya ta nufi hanyar zuwa gidan boka LOK'ORO da saurinta!.
Boka LOK'ORO yana zaune kwatsam tokar gawar Iya Gwamma,,,tazo ta shige cikin jikinsa da sauri boka ya buga wata irin gigitacciyar k'ara da mahaukaciyar kuwwa! Yana cewa "ni boka LOK'ORO na shiga uku na lalace! Banyi kaina adalci ba saboda arayuwata ban aikata alkhairi ba,,, gashin tokar shegiyar nan Gwamma mayya tazo xata kasheni,, domin Ummaru ya k'oneta da ranta wayyo Allah wayyo Allah na tuba kiyimin rai! Baxan sake aikata mummunan dabi'a da kashe mutane ba,, yau ni boka LOK'ORO naga takaina yau nayi mugun gan..... ".Bai k'arasa maganar ba jini da mugun tari ne ya sark'esa ya fad'i kwance k'asa yana shure shuren mutuwa da kakarin fitar rai! Sai da jini gunduwa gunduwa ya zuba sosai acikin bakinsa sannan ya fad'i k'asa d'immmmm ya mutu,,, aikuwa nan da nan batare da b'ata lokaci ba gawarsa ta kama wuta bal bal bal tana ci! Sai da wutar ta k'onesa k'urumumus ya zama toka,,, acikin tokar kana hango macijizai da kunamai suna yawo wurin ya gameda wani irin mahaukacin wari da d'oyin masifa da bala'i!.
Wa iyazubillah ina lillillahi wa inna ilaihirraji'un!!! Allah ubangiji ya rabamu da aikata shirka ya kuma sa muyi k'yakk'yawan k'arshe.
********************
Bayan wani lokaci ne su Maryam da Fatima sun warke garau kamar basu tab'a yin irin wannan ciwo ba,,, suka cigaba da zuwa makaranta da kuma rage yawon banza,,, da sukaji cewa Fadila ta mutu ta barsu suka kama yin kuka babu mai kama wani,,, aranar sunyi kuka fiye da tunanin mai tunani idanunsu sukayi jawur akan bak'in ciki da rashin Fadila,, iyayensu ne suke lallashinsu tareda basu kalamai masu dad'i har suka dangana suka barwa Allah komai.
Mama Nafisa da baba Nazifi,, Fadil sun hak'ura da dangana akan rashin Fadila saboda sunsan Allah da yabasu ita yafisu sonta ya amshi ran abarsa,,, saboda haka ne suka cigaba da binta da addu'o'i da yawan karatun qur'ani domin ta samu rahamar ubangiji Allah..
Bayan mutuwar Iya Gwamma mutane suka cigaba da gudanar da rayuwarsu cikeda matuk'ar farin ciki da kwanciyar hankali,,, komai zasuyi cikin natsuwa sukeyinsa saboda sunsan an riga an kashe Gwamma mayya wadda ta addabi rayuwar mutane da aljannu! Sai godiya da addu'a sukayiwa Ummaru d'an Sala mafarauci akan irin k'ok'arin da yayi wurin kamata da hannunsa da kuma nuna matuk'ar jarumta,,, garin ya dawo dai dai farin ciki,, annashuwa,, jin dad'i,, walwala,, nishad'i,, da dai sauransu duk sun dawo cikin garin Gumi..
*ALHAMDULILLAHI.*
Duka anan ne na kawo k'arshen wannan littafi nawa mai suna *MAYYA CE*,,, da fatar mutane zasu d'auki darasin dake cikinsa su watsar da abinda nayi kuskure,,, sannan alal hak'ik'a maganar mayyu gaskiya ce bawai k'age ne nayi ba,, naman mutane sukeci dana aljannu babu k'arya.
Ina rok'on Allah ubangiji ya yafe mini kurakurren da nayi acikin wannan littafi,,, abinda nayi dai dai Allah ubangiji ya bani sakamako mai k'yau.
Godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki wanda ya bani ikon gama wannan littafi lafiya,, ina mai numfashi da cikakkiyar lafiya sannan ina godiya ga dukkan masoyana masu bibiyar labarina da k'aunar wannan novel nawa.
*Ina godiya sosai da mik'a dubun gaisuwa ta ga wannan k'ungiya tamu mai tarin albarka,, INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION kungiya d'aya tamkar dubu wadda ta tara shahararrun marubuta masu matuk'ar ilmi,, hazak'a,, fasaha da kuma iya tsara labari mai fad'akarwa da nishad'antarwa,, ilimantarwa Allah ubangiji ya k'ara d'aukakaku yasa kufi haka shahara da d'aukaka har k'arshen rayuwarku,, ya kareku daga sharrin mahassada da mak'iya..*
_Ni Mugirat ina muku fatar alkhairi a rayuwa masoyana,,, sai kun jini asabon novel d'ina mai suna *SOYAYYAR GASKIYA* nan ba dad'ewa ba...._