Tunda Yarima yace ma Bily beauty cikin satin nan zan diro,amma ba zance miki ga rana ba,ta kasa zaune ta kasa tsaye, harma su Umma sukai ta mata dariya.yau ta shirya wannan tayi wancan da kanta take shiga kitchen amma shiru sai kiga har dare babu labari,yau kam tasha alwashin ba zatayi komai ba,tana falon Umma bayan sallar la鈥榓sar, Umma tana zaune kan kujera yayinda ta dora kafafuwanta kan tuf-tuf.yallabai wato jaririnsu Bily yana kan cinyarta,Bily tana zaune kasa kusa da kafafun Umma tana shafa mata maganin ciwon kafa,tare da dan mammatsa mata kafar Umma tace,鈥榶ata yau baza鈥榓yi wa ubannawa girkin ba?Cike da tsokana tayi maganar,Bily tace,na gaji Umma,babankin nan ja min rai kurum yakeyi bawani zuwan da zaiyi.Umma tace,muma kinga ai munci girki kwana biyu, dama haka kika iya girki?Kafin Bily tace wani abu sai sukaji sallamar Yarima da wannan muryar tasa ta kasaita. Zaraf Bily ta mike tsaye tare da cewa, dama kana hanya? Shiko kallonsu yakeyi ransa yayi fari kar yanda ya samesu yaji dadi,Bily ji tayi tamkar ta rungumesa,shiko ita ya nufo sai tayi maza ta zauna ya kalli Umma yana dariya,sannan yasa hannu ya dauki dansa yana cewa, Umma son yayi girma fa,kuma ya kara kyau, gaskiya beauty ta iya haihuwa.Umma tayi dariya sannan tace, shirmen kan nan yana nan dai babana?To kaki sanar damu ranar dawowarka, kullum sai Bily tayi maka shiri na musamman in baka dawo ba mu da 鈥榶an gida kakarmu ta yanke saka sai mu kwashi gara, yace Allah sarki beauty yau dai gani ta dan harare sa cikin wasa tace,yau kam sai dai aci na gida nan ya gaida Umma sannan ya nufi sasansu Bily ta zauna zata cigaba da shafa ma Umma kafa tace a鈥榓-a鈥榓 na yafe jeki gurin mijinki,haka ta bishi. Ai suna shiga falon farko ya ajiye(son)kan kujera ya jawota zuwa kirjinsa,wata irin ajiyar zuciya ya saki, jinsa yake tamkar an masa gafara,yace I miss you beauty,sannan ya lalubi bakinta.sun jima sannan suka dauki dansu zuwa sasansu. Nan ma da suka shiga ya kara jawo ta jikinshi ya tura hannuwan shi cikin rigar ta yana wani sansanar kamshin ta ta dan ture shi abban son kaki bari nayi maka sannu da zuwa ma ya dan tsotsi bakin ta toh ai beauty wannan ita ce sannu da zuwan ko? Ko akwai wanda yafi wannan ya kara shige mata dole ta hakura saida ya ja ta suka lula duniyar da suka kwana biyu basu je ba sannan suka yi wanka ta kawo mashi abinci yana ci yana kallonta yana jin nishadi da farin cikin dawowarsa wurin kyawawan iyalansa.
Da dare sun gama shirin kwanciya tana jikin Yarima son na gefen su sai kawai wayar Yarima ta fara ringing kuma tafi kusa da ita sai ta dauko Wayan kan screen din taga an rubuta T.girl ta mika masa sai ya kasa dauka tun a nan ta gane bashi da gaskiya sai ga call din ya kara shigowa sai ya dake dan kar ta zaci wani abu ya dauka duk da haka tana kwance jikinshi kuma tana jiyo muryar ta kadan kadan tana lura da a darare Yarima ke amsa mata har ya kashe tace kai da wa kake waya ya dake yace abokiyar karatun sa ce tace iya matsayin ta ke nan? Yarima yace ban gane ba tace kasan abunda nake nufi ai ko ita ce wadda ka maye gurbi na da ita da ka tafi sai ya hau fada shi baya son zargi kaza kaza ba dama yayi wata hulda da mace sai kice ina neman ta sai kawai ta tsura mashi ido kawai har ya gama tace masa Yarima da duk abun da kake ba wani damuna yake ba amma yanzu kasan wannan ta canza kuma da baka boye gaskiyarka amma yanzu ka koyi karya ta tashi ta dauki dan ta ta bar masa dakin ya bita da kallo tamkar ya bita sai kuma ya fasa,ransa ya sosu, yace tayi ta tafiyarta mana don taga na damu da ita shiyasa take yi min abinda take so,ya koma yayi kwanciyarsa,duk da bawai yaji dadin kwanciyar tasa bane, kuma yana zargin kansa da cewa shine bai mata adalci ba,ita kuma data kwanta sai ta soma tunanin cewa fushinta ba mafita bane,shin dama fushin tane ya dawo mata dashi kanta?Lallai fa ba fushinta bane,hakurinta ne da kuma addu鈥榓 dole ne taci gaba da hakuri tare da addu鈥榓,amma bari ta barsa sai da safe ta koma gurinsa. Da safe tayi wankanta tana sanye da riga da siket na blue jeans kanta babu dan kwali ta tufke gashinta da ribbon blue,tana zaune tsakiyar gado tana yiwa son shafa, tafi son ta shirya yaronta da kanta. Yarima ya rasa sukuni dole ya nufo dakin beauty ya iske ta tana kici-kicin saka masa pampers. tsayawa yayi ya harde hannu daga bakin kofa yana kallonsu, cikin tsananin sha鈥榓wa, ajikinta taji da akwai mutum a bakin kofa,da sauri ta juyo tana kallonsa,murmushi ta sake tare da cewa, abban son muna sauri muzo mu kwashi gaisuwa shine ka rigamu zuwa?Ya shigo cikin jin dadin yadda ta tarbe shi,shima gadon ya hau ya zauna kallonta yakeyi sannan yace,ni da kuke fushi dani?Ta dora masa son akan cinya, kafafunsa kuma suna kan gado tana kokarin sa masa wando,tace haba nawa, wazai fushi da aljannarsa?Yasa hannu ya shafi kumatunta,dama matan duniya suyi koyi da kyawawan halayanki na hakuri da saurin yafiya,ga mazajansu,saboda ladabin da kike min yanzun ina jin kunya ki kamani da wani laifi tace ni dama ina jin kishinka bana son ka dinga rabar mata abin yana soya raina,ta zuba masa idanu gami da tagumi ya jawota zuwa jikinsa,insha Allah ba zan kuma ba,kinji?Tace to ka yafe min jiya na barka kai daya amma kasan banyi wani bacci ba,yace na yafe miki beautyna, inda kana gurin kai ko baka san so ba zaka fahimci wadannan suna cikin mayen so amma su basu gane ba.
Ranar da Yarima zai fara halartar asibiti don fara aiki a matsayin babban likitan mata,duk hankalin Bily ya dagu,gani takeyi matan zasu kwace mata miji,ya gama shirinsa tsaf cikin suit,takwas saura kwata ya kalli beauty yace duk wannan damuwar ta mecece?Tace to doctor ba ka fa karya ba zaka fita,ya tura mata kofi zuba min lipton kinsan bazan iya karyawa 8:00 ba,tace to in ten din tayi in kawo maka office?Ya girgiza kai,bance ki fita ba,tace to ni don Allah kada fa ka kalli mata,cikin sigar shagwaba tayi maganar, yace cikin dariya kema kinsan dole na kallesu tunda sana鈥榓ta ce kallon nasu,ina nufin aiki nane duba lafiyarsu, in ta kama ma har taba jikinsu zanyi,t tace daina gaya min abin haushi,ya dubi agogo beauty barni in tafi,kinsan cikin tsarina babu African time 8 nayi alkawarin halattar office kinga saura mintuna,ta dauki jakar muje in raka ka Umma tayi maka addu鈥榓.yace ta min tun asubahi zan dai musu sallama a tsaitsaye, suka fita tare.goma daidai ta kirasa cikin hanzari ya daga wayar tace yaya aiki nawa?Ya lumshe idanu ya bude,aiki kam gashi nan inayi,kamar ni aikin ke jira,dama kinsan Allah beauty?Yacigaba tunda na zauna kan wannan kujerar marasa lafia suke shigowa ga kuma katunan wasu nan jibge,so ki tayani da addu鈥榓,tace zanyi amma break fa?Yace babu time tace haba don Allah shikenan nima bazanci komai ba,yace no,no kada kiyi min haka, me son zai sha yau?Tace duk mu hakura har dashi yace,a鈥榓 zanci to nan da sha biyu kinji beautyna. tace zan kira sha biyun dai,ta kashe wayar.
**************************
Haka suke rayuwa mai ban sha鈥榓wa,sai dai a boye Yarima yana amfani da wani cream lokacin saduwarsu wanda a lokacin tarayyarsa da Tina yasan wannan in ya shafa shi yana tsinka spam ba zaiyi da ba sam bata sani ba ta dai gaya daina mata zancan tsarin iyali.
[8:41AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 86馃彽
Duk wannan satin Bily rigima takeyi ita tana son taje Zaria,ta jima tana naci yana cewa son bai saba da iska ba,baya so a debo masa sanyi,ta hakura amma yau ta tada daru. kallonta kawai yakeyi duk taki cin abinci yanzun ma da zasu kwanta sai ta saka kanta gurin kafafunsa komai tayi sai yaji birgesa takeyi,ya tashi zaune yanzu beauty ba zaki ci abinci ba?Ta tashi zaune tana shasshekar kuka,don Allah yaya zanyi in iya cin abinci?Ni dai in kana son inci ne sai dai inka yarda inje inga mahaifana. sun jima suna son ganina kuma su suna min kara ne irin na 鈥榶ar fari bazasu iya zuwa gidana ba,sai yaji tausayinta yace to naji zakije,amma shine kika juya min baya,alhalin kin san na tsani hakan ko?Ta fada jikinsa to yi hakuri yaushe zan je?Yace jibi amma kwana nawa zakiyi?Tace sati ya zaro idanu,to wallahi a fasa tafiyar,ta kankamesa sorry,to kwana nawa zanyi?Yace zan daure kiyi daya,tace haba dai yaushe muka gaisa?Ta turbune fuska ta ja baya,indai daya ne na hakura,yace to naji biyu,tace ina laifin uku don Allah,shima a maneji, yace to naji amma gida nawa zaki bana sonki yawaita fita ana kallonki, tace to ina zanje ma daga fa gidanmu sai gidansu Umman Mansu,sai ko makota sai gidan Mansu din,ya zaro idanu Kaduna?Tace eh,ya girgiza kai ina hauka nike in barki kije Kaduna mutanan da aka ce suna kwace matan aure?Yanayin yanda yayi maganar sai data yi dariya, tace duk ba gaske bane fa ni dai iyakata gidan Mansu,sai kasuw... ya katseta da cewa kasuwa? Tabdijam, ki fasa zuwan ke nan salon kije maza suyi ta kallonki bazan iya ba,tace to shikenan na fasa zuwa kasuwan kaji?Amma fa gobe zanje gidan Umma muyi sallama da kuma Modibbo,yace goben sai da daddare na kaiki.ta shirgi tsaraba ga kudi da Yarima ya jibge mata, sirikanta ma sun hada mata tasu. su Mama sunyi murna da zuwanta, wannan karon ranar data zo tasa babansu ya kira masu aikin gini sukayi mata lissafin kudin da gidan nasu zai ci,fulastan bangon tsakar gida da kuma yin barandar waje tare da siminte bangon waje,Nan ta cire kudin ta bada ga abinci lodi-lodi sannan tabawa Umman Mansu kudi in an gama gyaran ta siyawa Mama kayan daki.itama ta bata nata.su Ladiyo duk sun zama ababen tausayi, suma ta basu kudi dama kowace bashi yayi mata kanta,nan sukayi ta godiya,da dare tana kwance Umma tana shafa鈥榠 da wuturi,Yarima ya kirata yace waton yau an sami Mama an manta dani ko?Ta dan dubi gefen Mama,sannan ahankali tace,haba nawa komai na keyi kana raina,ban manta da kai ba,shine kaima kaki ka kirani yace ina sane na zata zaki kirani ne,tace to ya aiki? Yace lafia ina son dina?Tace gashi nan kusa dani yana bacci yace Mama fa?Tace gata can tana sallah,yace a鈥榓 kice ba hira to bari muyi text to tace ina jira.sai ga Yarima yana kwance ya dage yana rubuto ma beauty maganganu masu dadi da nuna kulawa akan mutum, itama tana bashi amsa.Mama ta idar sai Bily ta ari bakin Yarima tace Mama ya kira ku gaisa kina sallah,yace yana gaisheki,tace ina amsawa haka sukayi ta text har nisan dare.kafin suka hakura.dangi da makota sun san Bily tazo,dan kuwa sun sha tsaraba,washegari kuma Kaduna ta diba zuwan bazata ta yiwa Mansu,sai da suka zo kofar gidan ta kira wayar Mansu tace Mansu kina gida?Tace ina zani Bily,menene?To ki fito kisa abude mana gate. Mansu tace bana son wasa fa,na taba maki wannan wasan?Inji Bily,ta fito da gudu tana kiran baba maigadi,har ya tsorata tace leka ka gani muna da baki Yana bude kofa sai ga zungureriyar Jeep din Yrm wadda ya bada aka kawosu ciki suna shigowa ana tsayawa ta fito da murna suka rungume juna.Asabe ta fito dauke da son yayinda Atika ta fito da jaka da kuma wayoyi,Bily kenan an zama manyan mata,daga kin ganta kinsan matar manya ce, tayi 鈥榶ar kiba tajin dadi,ga wata gogewa da fatarta tayi, ita kanta tasan tayi. Nan suka shige ciki,hira ta balle labarin daddadan zaman da su Bily sukeyi ne take labarta wa aminiyarta,nan Mansu ta shiga tsokanarta da cewa,da ko kin raina masa wayo ke ya miki yaro,Bily ta rufe mata baki da cewa,yi shiru an daina wannan zancan tuntuni tunda na gane halittarmu ba daya bace. Namiji komai kankantarsa indai ya balaga to namiji yake, suka sa dariya,tace bare nawa gara kowa dashi baya gajiya nan suka koma hirar kayan gyara jiki dana kwalliya.kwana dayan da Bily tayo gidan Mansu tayo guzurin tsarabarta mai yawa tare da shawarwari,itama kuma dama ta cika Mansu da tsaraba da kuma kudi har Mansu taso taji haushi.Bily tace,nasan ba don baki dashi bane na baki don kawai kullum burina in kyautata miki,suka dawo Zaria washegari suka dauki hanyar Bauchi. bayan ta cika iyayanta da kudi. shiko Yarima duk bayan mintuna sai ya kira waya ya kosa yaji tace sun iso gida,tazo da tsarabar su doya ne, dankalin turawa da dai sauransu,tasa aka gyare musu gida ta turare shi da turaren kamshi tayi gayu cikin riga da wando shigar da bata taba yi ba duk da Yarima na son haka, Mansu ce tasa ta lallai ta ringa yi tunda yana so,kuma yanzun babu kalolin matan da ba zai gani ba masu kuma kalolin dressing dama ta gyara kanta ta shiga kitchen ta shirya girki masu dadi koda Yarima ya shigo sasan nasu sai kalolin kamshi suka masa sallama,kan kujera ya ajiye jakarsa ya nufi dakin beauty kwana ukun nan a daddafe yayi su baya son ya dawo idanunsa basu ganta ba,amma me?Yana shiga bata ciki,sai gashi yana ta nemanta,kitchen ne toilet ne ya nufi sasan sa basa can,ya sauko falonsa na kasa ransa ya sosu ya ciro waya yana neman layinta,sai kawai ji yayi an rungume shi ta baya,tace oyoyo nawa!Yayi ajiyar zuciya sannan ya birkitota gabansa tsayawa yayi yana kallonta sannan ya jawota da karfi ya matseta a kirjinsa,kinyi beautyna I love....da sauri ta dago tana kallon bakinsa,shi kansa bai san lokacin daya soma furta kalmar ba,tace da gaske kakeyi? Ya lumshe idanu tare da jan numfashi yace ban sani ba beauty ta kwantar da kanta laf cikin kirjinsa sannan tace don Allah ka soni kaji? Shine kawai abinda na rasa a rayuwata. ya dago fuskarta yana kallo tace,tana kallon kwayar idanunsa zuciyata zata so ka,don ta aminta dakai tana girmamaka tana darajaka,kila ma tana tsananin sonka.Ya manneta har sai da ta kasa numfashi,sannan ya nemi bakinta,kukan son ne ya dawo dasu cikin hayyacinsu,ya fadi daga kan kujera inda yake zaune,babansa ne yayi zafin naman cafko sa ya daga shi sama
Haka suke gudanar da rayuwarsu kowa yana kaf-kaf da dan uwansa tare da gudun bata ma dan uwansa Yarima yana zaune cikin office dinsa marasa lafia suna ta shiga da fita kowace mace tafi son ganin doctor Yrm,a cewarsu yasan aikinsa,da yawa sunce in sun gansa kuma ya rubuta musu magani ko yace aiki ne in anyi suna samun salama, wasu 鈥榶anmatan kuwa son ganinsa ke sa suyi ta ziyarar asibitin,nurses har ma da wasu daga cikin likitocin mata su kan so ko da hira ne ya dinga yi dasu,amma shi sam baya sakin fuska,ko tiyata ce ya shiga yana gamawa yake kame kansa,shiyasa suke shakkar shi tare da ganin girmansa.wata nurse ta shigo da kati ahannunta tace,likita ga Emergency an kawoma doctor Salihu yace akawo maka,ya dago ya dubeta idanunsa cikin farin glass shi me ya hanasa dubata?Tace yace ka fishi sanin wannan matsalar,ya dan taba baki gami da daga kafadu shigo da ita na gani,bai san lokacin daya mike tsaye tare da cewa,oh my God!Ganin yanda fuskar yarinyar yayi caba-caba duk ta lalace da ruwan batir,ya dubi nurse din ita da matar dake tare da mara lafiyar yace,kuje gurin doctor Salihu kuce nace yayi mata abinda ya dace ya bata gado zan dubata inna tashi,kuje dai zan kira phone dinsa.鈥榶ar wani hamshakin dan siyasa ne aka batawa fuska kuma 鈥榶arsa daya ce shi baya nan ma yana saudi anyi masa waya dai kuma yace zuwa gobe yana kan hanya.kafin Yarima ya shige gida sai daya dubata,tana bukatar aiki ne sai dai akwai karancin kayan aikin a nan kasar,shi yana dasu amma ko fara amfani dasu baiyi ba,domin asibitinsa ya shigo dasu.hankalin mahaifin yarinyar yayi mugun tashi da yaga 鈥榶ar tashi.doctor Salihu ya samu a office yana cewa don Allah ataimaka masa ko nawa ne zai bada ya sani anyi haka ne don kawai abata masa rai a daga masa hankali,Dr. Salihu ya dauke su zuwa office din Dr. Yarima .
[8:42AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 87 馃彽
Nan Yarima ya yiwa mahaifin bayanin cewa matsalar ta kayan aiki ne,cewa yayi shi zai bada kudin kayan aikin ko nawa ne. Yarima cikin satin yayi aike kayan suka iso, ya bukaci hoton yarinyar lokacin da take lafia,Allah cikin ikonsa sai gashi aiki ya kammalu zuwa wasu kwanaki ya bude aikin,an sha mamaki ganin fuskar yarinyar ta samu,shi kansa sam bai zaci aikin zaiyi kyau haka ba,sai dai kamanninta sun dan canza kadan,sai tafi da kyau ma,wannan aikin ya jawo daukakar sunan Yarima a fadin kasar nan inda asibitoci masu zaman kansu dana gwamnati suka yi ta gayyatar Yarima ire-iren wadannan aikin har ya kasance baya samun isasshen lokacin zama a gida,wani lokacin kuma cikin dare ne zaki ga anyo masa waya ana nemansa Emergency. Tiyata da makamantansu,abin yana cin ran Bily,domin aikinsa yanzu yasa bata samun kulawa sosai zata tsaya tayi gayun da kananan kaya ne da shaddodin ne zuwa lesuka,atamfofi amma wani lokacin ma har ta cire tasa kayan bacci bai dawo ba,yana dawowa kuma duk a gajiye da yayi wanka shikenan zai kwanta sai bacci.yau ma kusan kwana tara kenan haka na faruwa,domin wannan karon har asibitin Ibadan yaje yayi kwana biyu.yau tana sa ran sati ne da Lahadi dole yana gida,tunda yayi sallar asubahi ya koma ya kwanta,tara daidai ta tashi ta shi ta koma dakinsa ta zauna kusa da fuskarsa tace,abban son bazakayi wanka ba?Yayi mika barni inyi bacci beauty jiya nayi aiki sosai,mutum shidda na fede,tace shikenan mu kuma yanzu aiki yafi mu, ya tashi zaune yana kallonta,kamar yaya?Ta dubesa to yanzun fa bakada lokacinmu,yau kana aiki nan gobe kana aiki can.ya matso kusa da ita ya jawota jikinsa wannan aikin fa in kinyi tunani beauty dalilinsa ne na bata shekaru ina karatu,kuma an samu Allah ya taimakeni inda zaki lura aikin taimako ne,kin sani na fiki son hutu tunda kika ga sai mu kwanta mu tashi ban lalubeki ba kin san wani aikin yasha gaban wani Amma kiyi hakuri ko wane dan adam yanacin zamaninsa ne,yanzun lkcina ne akan aikina wata rana sai kiga an sami wanda ya doke ni,to ba kya ganin gara nayi amfani da damata da lokacina in samu aljannata, nasan dama ke ba makawa in dai miji ke daga kafa a shiga tawa dama a dage take shikenan sai ki jagoranci sauran matana na gidan aljanna,tayi driya to kwanta ka huta,yace a鈥榓 na fasa yanzun 鈥榶ar hira zamuyi irin wadda muka kwana biyu bamuyi ba, tace yau ai kana gida harda irin wadda bamu taba yi ba duk zamuyi. Yanzun dai kwnta kurum kayi baccinka,kuma matseta yayi sai sukaji kiran waya,ya kalleta fuskarta daure ya dauki wayar yana yi mata dariya,bataji kome aka ce masa ba ta daiji yace zanzo to nan da 10.ya fada tare da kallon agogo,ta mike zata fita yace zo nan gimbiya bana fushi bane maigadon zinari,marasa lafia na zan duba ance biyu daga cikin wadanda nayiwa fida basu farfado ba,amma ina ganin ba wata matsala bace,kafin goma zasu farka,tace um ai kai nasan in kaje sai kuma na ganka,yace shirya muje tare ta dubesa da gaske? Yace na taba cewa ki shirya muje?Tace a鈥榓 ta fita ta zuwa dakinta cikin doguwar rigar shadda ta fito aslin soly ja,takalmi da jaka da gyale farare,hatta abin hannunta fari ne, shi ko farin yadi ne mai shara-shara wnda kana gani kaga yadin manya,salon daurin dankwalin Bily ya burgesa yace kai beauty dafa naso inyiwa kaina asara tayi fari tareda cewa ko?Yace ina son? Dashi zamu dakkosa in kina cigaba da min wannan farin tafiyar tamu zata iya fasuwa,tace yana hannun Asabe,yace amsosa mukadai zamu baki so muyi 鈥榶ar hira irinta sirri?Tace to muje in amshesa sai muyi ma Umma sallama.Son yayi kyau cikin wandon jeans,pink da fara kar din shirt, takalminsa pink da 鈥榶ar safa fara,shine ya dauki son din suka yiwa Umma sallama da cewa sunje asibiti,hakan yayi matukar birge Umma,suka nufi katuwar jeep dinsa tace tunda nazo gidannan yau ne rana ta farko da na shiga unguwar nan da rana kamar yanzun,ya dubeta yanzun ma shahada nayi don fa ni bana son ana kallemin ke,tace um wata rana inna kallemu sai inga tamkar masoya? Ya dubeta yaya ake gane mutum ya kamu da so?Tace kaine fa doctor nawa, zaka fini sani yayi murmushi ni ba likitan zuciya bane,kuma ban karanci so ba,kuma bai taba kamani ba,don haka ban san shi ba,tayi shiru yace kin taba so?Ko kuma sanin yanda yake?Tace ban taba so ba,sai dai ina sha鈥榓war aso ni,ina so in sanshi inyishi,da sauri ya dubeta kiyi ma wa? Tace kai mana nawan. Ta cigaba na taba karantawa wani littafi, marubuciyar cewa tayi shi so wani halitta ne wanda da zaran mutum yaga abinda yake so zai shige shi nan take,da zaran ka kamu da son wata baka da sauran nutsuwa,zaka kasance cikin tunanin abin sonka tare da kasancewa da abin son naka duk rintsi duk wuya,Yarima yayi dariya tare da cewa,malamar so kice kinsan so kenan?Tace a鈥榓 naji dai labarinsa amma banyi saba ban kuma sansa ba.suna isowa asibitin shine ya dauki son suka jero duk da cewa Asabar ne asibitin yana cike da mutane,sai kallonsu akeyi ballantana nurse din da suke nan sai kallon Bily sukeyi,a cikin zukatansu suna cewa lallai dole ne Dr. Yrm ya dinga yiwa mata kallon baku yi ba,daf da zasu shiga office dinsa wata Dr. Jamila ta iso tana cewa a鈥榓 Dr. kai da madam ne?Ta amshi son suka shiga office din ta bisu,tamkar ba asibiti ba office din domin ya tsaru(AC)ma kusan guda uku ne tace dama shi dan sanyi ne,gadon dake gefe ne irin wanda marasa lafia kan kwanta kawai zai nuna maka cewa nan office din likita ne.kujerar da aka tanada domin likitan itace ya nuna Bily tare da cewa beauty please sit down,ta zauna tana kallonsa tare da cewa,yau nima nazama doctor. Dr. Jamila ta dubi Bily yaya gajiya madam ya kike? Lafia,inji Bily fuskarta ba walwala tace Dr. Familyn ka masu kyau,yace na gode me kika zoyi asibiti yau Sunday?Tace ina da mara lafia,maman kawata ce ba lafia,yanzun sukayi min waya wai jikinta din ya tashi shine nazo in duba,Allah ya sauwake.
Yace zaki zauna anan ne in dawo?Ta mike muje nima na samu ladan gaishe da marasa lafia.yasa hannu ya dauki jakarta mu gani kina da kudin da zaki basu sadaka ko,tace duba ka gani ni na jima rabon da nasa jakar nan kila kuma asamu koba yawa,ya dago daga kallon cikin jakar da dan murmushi,yace Haj. Bily ai jakar taki tam take,ai na sani ke din babba ce,indai kudi ne,tace oh zagina zakayi,me nake saidawa?Yace au bakya sai da komai fa shine kike da kudi haka? Cikin tsokana yake mata maganar,ta warce jakarta nidai muje,Jamila itama dariya takeyi a xuciyarta tana mamkin dama ashe Dr. Yarima yana wasa haka?Ya mika hannu zai amshi son tace muje in rakaku. Bily ko yanda Jamila keta iyayi da salo shine yake bata haushi,kodai mijinta yana kula ta?Suna shiga dakin da marasa lafiar suke sai da ya fara shiga inda nurse din dake kula dasu suke zaune daga ganinsa duk suka tashi, Bily ma suka shigo suka gaida Bily tare da cewa madam din Dr. ce,Bily tayi murmushi suka amshi son suna cewa fine boy dayar tace Dr. dukansu sun farfado yace Alhamdulillah, bari mu duba su suka tafi dukansu,daga kansu Bily ta soma rabon kudin sannan tabi sauran marasa lafian,suna godia,nan taga da sauran kudin tasa sister guda daya ta rakata sauran dakuna don basu taimakon dubu daddayan,sannan taxo taba wadannan nurses din guda biyu ta samu ya gama rubuta ma mara lafian maganin daza a siyo,sannan suka fito har gurin mota sukayi musu rakiya harda Dr. Jamila ya amshi son yana cewa,to mun gode,sai Monday suka ce Allah ya kaimu,ta zauna agurin zamanta shi kuma ya shiga gurin tuki,ta kai hannu tare da cewa,zo nan son baba yayi driving ko?Ya rike baban gam, Yarima yace bazai zo ba,da kin iya da kin ja mu,tace to ka koya min yace sai kin gama fushin,tace fushin me?Yayi dan murmushi sannan yace haba beauty ni yanzun ko ido kika kifta nasan me hakan yake nufi bare fushinki,tace to wai fushin me zanyi ne? Yace kin fini sani kila ganin Jamila ne, tace umh wannan sarkin shisshigin nifa batayi min ba sai wani kaudi takeyi maka, yace to banda ke beauty kema mace bata miki ba bare ni?
[8:42AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 88馃彽
Ni dake da kamarki sanin kanki ne kaf kasar nan ke daya ce kike burgeni,tace um ai so bashi a muni, haka sha鈥榓wa yace wai wanene so din nan ne?Ban fa sanshi ba, sha鈥榓wata kuwa bata zuwa irin nan guraren,don haka kibar damun kanki ni naki ne ke daya,tace to yaya batun koyan motar mu fara yau mana?Yace, ok bari muje ko dana minti talatin ne.an kammala gina katafaren asibitin na Yarima,asibitin katon gaske ne mai dauke da fannoni na kalolin cututtuka,ga na鈥榰rori na aiki irin wanda ake cewa sai an fita kasashen turawa ake samu,ga gefe na musamman saboda tada komada wato gyara fata da sauran abinda yayi course akansu an tsaida ranar bude asibitin,nan Yrm ya shiga yo gayyar jama鈥榓 musamman abokan karatunsa wadanda ke kasashe daban- daban.da kuma abokan course dinsa ciki harda Tina.yaso da zai yiwu daya dauki Tina aiki a asibitinsa,saboda ya samu abokiyar aiki fannin fata domin itama ta kware,amma zaya gwada ya gani indai ta amsa gayyatarsa tun ana jibi bikin bude asibitin baki suke sauka,鈥榶an Zaria ma sunzo gida da masaukin baki tam da jama鈥榓 banda otal-otal da aka kama cikin katon filin asibitin akayi taron inda manyan likitoci,kwamishinonin lafia,zuwa ministocin lafia,ga kuma 鈥榶an uwa da abokan arziki. Su Tina an duro domin tana ganin sakon sai taji tamkar yayewar matsalarta ce,don haka bata yi kasa a gwiwa ba,ta amsa gayyatar, domin tana azabar son Yarima.taro yayi taro,bayan yin duk abinda yakamata aka bude asibiti inda mai martaba ya wakilta sarkin musulmi ya bude asibitin mai suna(Dr. Yarima Hospital)an dunguma cikin asibitin don ganin cikinsa,hatta bakin kasashen wajen sun jinjina dukiyar dake cikin asibitin,wato kayan aiki zuwa kayan kawata asibitin kafin sati daya tuni asibitin ya kama aiki gadan-gadan.gashi dama ya tanadi likitoci da kuma nurses kwararru.Tina ma ta yarda da gayyatar da Yrm yayi mata,amma sai taje ta dawo. Al鈥榓mura sunci gaba da tafia yanda yakamata,beauty kam yanzun ta gama yarda Yarima nata ne,yanzun ne ta gane cewa halayan Yrm masu kyau ne in ta cire neman matansa wanda ayanzun take tunanin ya daina yana da kyauta ga sadaka yana da kulawa gami da ibada.girman kan da ada take ganin yana dashi yanzu ta gane shi mutum ne mai matukar saukin kai da kuma tsokana duk da bai cika dariya ba,zaya tsokaneka yayi fuska tamkar bashi yayi maganar ba,tuni ya soma ginin gidansa babu nisa sosai da asibitinsa, son ma tuni ya soma takawa shiko Yarima kudi sun kara zaunawa dama dogo ne ga kuma 鈥榶ar kiba irin ta hutu, azumi yana gabatowa tuni Bily ta cire son daga nono,yana gurin Umma tana son zuwa zaria kafin azumi,amma Yarima yace a鈥榓. Auta Asma鈥榰 tunda ta gama karatu tana gidan gurin Bily duk dangin Bily daga Asma鈥榰 sai su Sakina, Yarima ya sani sai dai yana musu aike ko yanzu da take hankoron zuwa zaria kafin azumi,tana son ne takai musu kayan azumi,bata san tuni Yarima ya tura musu dashi ba,sai gashi babansu yayo waya yana cewa tayi musu godiya gurin Yarima ,azumi yana ishirin suka nufi saudi, wayewar garin sallah suka dawo.rayuwar Bily abin sha鈥榓wa,yanzun ta manta da komai da duk matsalolinta na baya kuma ta yarda da batun Mansu cewa suna son juna koda Yarima baya sonta ita dai tayi imanin tana matukar sonsa, shiyasa kishinsa yanzun yayi yawa azuciyarta, harma bata iya boyewa, duk da bata da masaniya game da Tina sai dai tana zargin kamar yana neman wata,in tayi magana ya kalallame ta da baki kan cewa shifa nata ne ita daya Ranar wata litinin tana kwance a falonta, asma鈥榰 ta miko mata waya cewa ana kira,tana dubawa sunan Umma ta gani tana dagawa ta shaida mata ta fito suje gidan Modibbo zasu dubashi yanzun nan akayi mata waya kan cewa jikinsa yayi tsanani,ta mike da sauri ta nemo mayafi ta soma kiran layin Yarima ,yanayin muryarsa yasa ta wani zargi tace lafia naji muryarka wata iri?Yace na gaji ne kawai tace to zamuje duba jikin Modibbo inji Umma,sai taji yace umh humh sai kuma taji an kashe wayar.yanayin sautin muryar yafi kama da wanda yake tare da mace, don kada Umma suyi ta jiranta sai ta nufi gurinsu Umman,suna mota ta kuma kiran wayar a kashe, sauran layikan kuma suna ta ringing ba鈥榓 daga ba. zuciyarta tamkar ta fashe don bakin ciki,amma dole tayi hakuri ta shanye.suna isa gidan suka shiga gurin nasa Umma ta tallaboshi lokacin ya dubeta duk sukayi masa sannu yana tayi musu godiya,sauran kishiyoyin Umma sun dawo sun barsu acan ita da Bily,ya dan samu bacci suka shiga cikin gidan, kamar minti goma Kawu ya shigo hankali tashe yana ce musu Modibbo dama ashe baccin nan tafiar kenan?Hawaye ne suka soma zirya akan kumatun Bily,ta sani in zata tuna da tarihin rayuwarta to zata tuna da Modibbo,Allah ya jikansa ba zata gushe ba gurin yi masa addu鈥榓 duk sallah.ta soma neman layin Yarima taci sa鈥榓 an kunna a zuciyarta tace an gama kenan,wani irin takaici ne yasa taji sabon hawaye ya zubo mata ya daga wayar da cewa,hello beauty.wani tukuki taji, itace banza ya raina mata hankali cikin shasshekar kuka tace inka gama ne sai kazo nan gidan Modibbo Allah yayi masa cikawa,ta kashe wayar ta shiga neman 鈥榶an zaria. Yarima yaji rasuwar sosai,dole yayi wanka kafin ya nufi gidan,don haka sai da yaje gida saboda a cikin gidan Tina dake nan asibitin ya tara da ita kuma bazai iya yin wanka a gidan ba. bayan dawowa daga makabarta su Yarima suka shigo cikin gidan,Bily kam ko son ganin Yarima batayi,tana zaune da carbi kanta na kasa,Yarima ya zauna kusa da Umma yana mata gaisuwa,ya dubi Bily,beauty yaya muka ji da hakuri?Banda Umma dake gurin da sauran mutane da bazata amsa ba Amma duk da haka bata dubesa tace mun gode Allah,Umma tace Bily ta kasa daina kuka shi Modibbo yanzun ai sai addu鈥榓, a ranta kuwa cewa tayi yaya ma zata iya daina kuka alhalin mai tayata addu鈥榓 akan Yarima yanzun babu,sai yanzun ne data kamu da son Yarima shine zai koma bin matansa,ita kam ta gaji da hakuri bazata iya ba.har ranar da akayi uku Yrm ya kasa gane kan Bily,sam ta fita harkarsa galarin gabanta kawai takeyi ko tana dariya ne data gansa sai kawai ta daure fuska. washegari bazasu je gidan rasuwar ba domin an riga ya anyi sadakar uku,har ya fita sai kuma gashi ya dawo kusan misalin karfe sha daya tana kwance cikin dakinta ya shigo,Asma鈥榰 ya fara gani a falo yace mata ina antynki?Tace tana ciki.ya shiga tayi rigingine fuskarta tana kallon sama tunani takeyi koda iyayanta suka zo gaisuwa Yarima bai ma zo sun gaisa ba har suka tafi,duk da yayi ta kiran waya yana cewa gashi nan zuwa wai yana duba wanine sai bayan sun tafi sannan yazo.ya zauna gefen gadon beauty tashi muyi magana,ta tashi zaune ba tare data kallesa ba,tace ina jinka yace a haka zamuyi maganar kina kallon wani guri ta juyo ta kallesa sai dai ranta a daure yace wai ni shin menene ya faru ne kika saka ni cikin damuwa?Me yasa kika saba min da kanki da hirarki da dumin jikinki kinsan ba zaki dore ba?Shin ko rasuwar nan ce duk tasa kika koma haka?In ma rasuwar ce niya kamata infi jinta, domin duk yanda zaki damu ni zaki yiwa kara.ta dubesa rai bace, in kana zaton kara nayi ma donna damu da rasuwar Modibbo kayi kuskure, domin duk wanda yayi kukan mutuwa kansa ya yiwa,kuma da zaka ce na saba dayi maka kaza da kaza ina ce yanzun ka samu madadina ce?Ya dubeta ban gane ba?Tace ai bazaka gane ba,bari kaji nifa yanda na juri huldarka da mata da yanzun bazan iya ba,Allah sai in kama gabana. A haka kowa ya ganni zai zata ina jin dadi ana min kallon sha鈥榓wa da hutu amma zuciyata ba hutu?Ya daga mata hannu saurara min,me kike nufi da zuciyarki ba hutu,me na miki? In kana so dole sai na sanarda kai zan iya domin kayi ne dama don inji kana kwance da mace na kira,ai sai kaki daga wayar amma don ka cuzguna min sai ka daga, kana ce min wai ka gaji,saboda ka raina min hankali,ya mike don yin abin nan da hausawa suke cewa tabarmar kunya da hauka ake nade ta.ke ki shiga taitayinki,kin tabbata ina tare da wata ne?Kin yarda Allah ya tsaida ke ranar shaida?Tayi shiru ya cigaba da cewa,shikenan tunda da ina neman mata yanzun bani da damar nayi wani dan kuskure sai ace ina tare da mace,to duk yanda zakiyi kiyi,tace haka kace?Shikenan ya dubeta ko da sanda nake yima baki daga min hanakali irin haka ba sai yanzun? Tace gara da lokacin baka gabana kuma kaima baka damu dani ba,ballantana kasan kona damu ko ban damu ba,sannan ko banza lokacin baka boye gaskiyarka, amma yanzun fa?Shikenan kawai tunda kace duk yanda zanyi inyi ni kuma zan nema ma kaina mafita,ta mike ta shige toilet.ya rike kansa tare da yin ajiyar zuciya sannan ya fita.wasa-wasa rigima taki karewa ranar ya ritsata da cewa wallahi shi bazai iya ba,yaya yana matsayin mijinta zata barshi yana walagigi shi in ta ci gaba da wannan halin zai hadata da Umma, tace zanfi son haka domin sai tasan me kakeyi,kila in tayi maka fada kaji nata,ta cigaba da shafa manta,yace to yanzun naji na amshi laifina shikenan me kike so inyi miki ki huce?Ta dubesa alkawari zaka dauka tsakaninka da Allah cewar bazaka sake bin mata ba,yace naji zanyi amma kinsan mutum yace zai dauki alkawari tsakaninsa da Ubangiji ba karamin abu bane,nasan muhimmancin alkawari nidai ina bukatar addu鈥榓rki kuma zanyi kokarin kiyayewa, kenan ka yarda kanayi?Yace a鈥榓 bawai na yarda bane,don dai ranki yayi fari ki daina fushi shiyasa nace miki na yarda,don Allah kinji? Ta tsura masa idanu,yazo ya rungumeta,don Allah beauty in na sake ki mini duk hukuncin da kikeso, tace shikenan ya wuce, duk da haka tana masa komai amma ta kasa sakewa dashi kamar da, yanda take wasa ajikinsa suyi ta wasa ta bashi abinci abaki amma yanzun batayi.
[8:43AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 89馃彽
Ya kuma samunta da complain shifa bawai tamai abinci yaci ya kwanta da ita ne farin cikinsa ba,yanzun farin cikinsa bai wuce ta saki jikinta ta koma normal ba,data zauna tayi tunani da tayi banzan nan dashi in yayi gaba can zai tare inda kadangarun bariki suke sai yaga dama bacci zai kawosa amma shi yana ta faman binta sai ta kara rikosa tare da jansa jikinta saboda ta samu ta rabashi da kowace,cikin kwanakin suka koma daidai da sharadin cewa inya kara duk hukuncin data ga dama ta masa shi yaja. yaita kokarin ganin bai kuma barin wata baraka da zatasa beauty ta gane yana tare da wata ba.Hankalinta kwance yanzu,damuwarta bata wuce son samun ciki ba,wanda in tayi magana sai yace ta daina damun kanta,kwata-kwata shekarun son nawa da za鈥榓ce sai anyi masa kani?Sannu a hankali ta soma zargin cream din da yake shafawa in zasu kwanta, domin ta kula inya kare komai matsuwar da yayi da ita yakan hakura,don haka sai ta dauko salon cewa ita dai tana jin zafi maimakon ce matan da yayi cream din zai sa su jin dadi,ta tubure tace ita sam bata so ga zatonta zai bari sai taga yayi matukar daukan zafi da ita harma ya fita harkarta, gami da kaurace mata, ita ma ta yarda da hakan suka share juna na kimanin sati uku,su duka sunji jiki domin shima duk da yana da Tina ya gane bawai biyan bukata ne kawai amfanin beauty ba tana da wani matsayi wanda mata da yawa basu takashi ba a cikin zuciyarsa.ita kuma babu abinda yafi kona mata rai yanda ya daina cin abinci agida wani sa鈥榠n ma sai tayi kwana biyu bata sashi a idanunta ba,kuma zuciyarta ta dinga raya mata cewa yana can tare da matan banza.Ganin bazata iya cigaba da wannan zaman ba yasa ta samesa, sai ce mata yayi indai bazata yarda suci gaba da amfani da wannan cream din ba sai dai su zauna a haka Ga Allah ta koma ta cigaba da gaya masa kafin wani tsawon lokaci sai gashi ya soma sakkowa,tana zaune yazo ya sameta yace tayi masa tuwon semo,bata tsaya jan aji ba ta shirya masa tuwo miyar danyan kubewa,sannan tayi kwalliya irin wacce bata taba yi ba,lokacin da yazo cin tuwon sai ta bayyana donta zuba masa tun yana satar kallonta harma daga karshe ya zage da kallon nata ita kuma tayi amfani da wannan damar ta saki jikinta tamkar wani abu bai taba faruwa ba.ganin haka shima yabar cin abincin suka koma wani fanni,sai da suka tausaya ma junansu,aranar lallai sun fahimci sunyi missing din juna daga nan suka ci gaba da harkokinsu. amma kuma sai me?Data samu ciki wata daya biyu sai ya zube kuma ya dubata acewarsa ba wata matsala anyi haka har kashi hudu,inda abin ya soma damun Umma,su anty Saliha kuwa cewa sukayi ita ke cirewa shi kuma tsabar son mace ya hanasa ya gane hakan, tsana suka kuma saka mata tare da zuga Umma akan Yarima ya kara aure, umma cewa tayi babu ruwansu amma anty Salma sai data kirasa tace, lallai ne ya sake aure,sannan sukayi kungiya suka samu Bily suka ce inma tana cire ciki ne don tayi sisi to su karuwa suke so kuma Umma tace dole ne ma ya sake aure.hankalin Bily yayi matukar tashi,jin cewa harda Umma cikin lamarin.da sauri ta kira Mansu ta shaida mata halin da take ciki,Mansu tace mijinki ya canza miki?Tace,a鈥榓 shi yana boye min maganar nema bai san sunzo har gida sun gaya min ba,tace to ko da wasa kada ki canza masa kinji ko?Tace to sannan kadaki yarda ki sanar dashi duk abinda 鈥榶an uwansa suke miki tace shikenan Mansu tace shawara daya itace ki dage da addu鈥榦鈥榠,nafilfilu kiyita gayama Allah,tace to cikin kwanakin shi kansa Yarima ya fahimci tana da damuwa,haka nan inya farka sai ya ganta tana nafilfili,wannan karon data samu ciki bata bari ya sani ba,don tana tunanin da sa hannunsa yawan barin ta tunda bai taba nuna damuwarsa kan cikin ba don ya fita,sai dai ya damu da lafiarta,ita kanta tana son ta sake haihuwa ballantana ga bala鈥榠n danginsa duk da nuku-nukun data ke har cikin yakai wata uku. Nan fa ya farga ya tambayeta kan cewa ciki ne da ita ko?Tace me ka gani?Yace, alamu da dama,tace shine don Allah ka tayani addu鈥榓 wannan karon Allah ya bar min,yace to yanda yake amsa zancan tasan bai kai zuci ba,sai dai zatayi taka tsantsa da duk wani magani da zai bata.har aka kwana biyu bai bata komai ba kuma bai canza mata ba,yana ma taji da ita ne,ashe yana amfani da wani mai ne in yayo wanka sai ya shafashi cikin toilet din a gabansa da zaran ya kwanta da ita sai cikin ya fita wannan karon ma haka yayi bayan ya fita,zuwa asibiti misalin sha biyu sai taje fitsari nan taga jini,da sauri ta fito taje ta shirya ta nufi gurin Dr. Aisha,bayan gama bincikenta ta gano cewa Yrm yana amfani da wani sinadari ne dan fitar mata da ciki,sannan tace wannan cikin ma fita zaiyi.Bily bakin ciki ya isheta,Dr. Aisha tayi mata allura tace taje gida.har zata gida sai kuma taga ba zata iya daurewa ba sai taje asibitin ta tabbatar masa ta gano komai kuma zata shaida ma Umma komai,tana zuwa baya office nan nurse din dake kula da marasa lafian dake shiga gurinsa ma鈥榓na mai kai masa katuna tace yanzun nan ya fita gama marasa lafia suna jiransa zai dubasu da yake sun san ita matarsa ce,tace ina to yaje nurse tace,kila suna wani aiki ne a cikin gidan Tina,har zata shiga office din ta zauna sai kuma tace am nurse ina ne gidan?Tace gashi can bari in nuna miki suka fita ta kaita har bakin gate din gidan kai tsaye ta shiga ta ratsa dan tsakar gidan mai kyau da furanni ta isa kofar da take zaton ta falo ce,ta tura sai taci sa鈥榓 abude ne ta tura ta shiga ta shiga falon mai kyau ta waiga ko鈥榠na babu alamun mutum sai dai taga kofofi guda uku.ta juyo da nufin ta fito sai taji maganar TV cikin wani daki ta nufi gurin har zata kwankwasa sai dai ta fasa ta kama murfin kofar ta murda sai taga kofar ta bude,duk da gargadin da zuciyarta ta rika mata kan cewa ta fa yi gangancin shigo ma mutane gida,hakan bai hanata leka dakin ba,TV ta hango sai ta cusa kai,take numfashinta ya soma zarya da kyar ta iya furta Inna lillahi wa鈥榠nna ilaihi raji鈥榰n da karfi. Wanda hakan yayi sanadiyar jawo hankalin Yarima da wanda kamu ta masa irin wanda ake cewa turmi da tabarya, da kyar ta lalubi hanya ta fita,tana mai data sanin wannan zuwan da tayi. data jirasa ya koma gida ta zauna acikin mota ji tayi jinin yatsunko mata gaba daya da sauri ta ciro wayarta ta kira direbansu tace dan Allah ya hau mashin ya sameta asibitin Yarima tazo ne bazata iya dawowa ba,babu jimawa sai gashi ya jata zuwa gida,dakyar takaicin gidan yasa ta isa dakinta ganin halin da take ciki ne direban ya shiga gurinsu Umma ya shaida musu.lokacin da jakadiya ta iso ciwon baya da mara sun tirnike ta,nan take jakadiya taje tana ya mutsa baki tana cewa Umma wannan mata ta Yarima bata da dabi鈥榓 to gata can ta kuma yo allurar zubar da cikin tana ta murkususu jini yana zuba,Umma ma haushi ne ya kama ta, amma duk da haka sai tace jeki kula da ita jakadiya,ba laifinta bane laifin mijin ta ne da tun farko ya nuna mata bacin ransa daga na daya ai bazata kuma ba,bari in kirasa yazo ya dubata su dai suka sani,ni menene nawa Allah na tuba jika wane iri ne ban gani ba.lokacin da Umma tayi masa waya ya zaci ko tazo ta fada ne a tsorace ya daga wayar,tace masa sai kazo ga matarka nan kila barin zata kuma yi ta kashe wayarta,lokacin daya iso tama sume bata san wanda ke kanta ba a firgice ya dauke ta zuwa mota Asabe ce kurum ta bisu suna isa asibitin a gigice ya sureta zuwa Emergency su uku ne kanta shi ya kasa yi mata komai ma,cikin ya fita sukayi mata wankin mara sannan suka kaita daki na musamman ta farka ne ta ganta a dakin asibiti. kwananta biyu duk babu wanda yazo dubata kaf dangin Yarima ance sai Umma lokacin tana bacci su Salma cewa sukayi bazasu zo duba taba tunda tana sani.Yrm ne ko yaushe yana dakin sai dai ya kasa ce mata komai kamar yanda ko ganinsa bata son yi shi dai bashi da tacewa ne, sannan ga carin da 鈥榶an gidansu suka rutsa sa suna masa yayyinsa ne suka tsara shi a gaban Umma sunce matarsa tana zuwa tana cire ciki yakasa yin komai akai saboda ta mallakesa, don haka zasu nema masa aure, Nan take anty Saliha tace 鈥榶ar mijinta Nafisa ta jima tana son Yarim kuma Nafisa tana da hankali sosai,shidai jinsu kawai yakeyi shi damuwarsa daya mummunan kamun da matar tasa tayi masa, yanzun bai san yaya zasu kwashe ba in ta warke, gashi shi ne silan wannan wahalar da tasha duk da yana zaton bata san shi ne sila ba inda ma yake jin da dan sauki kenan.da yamma su Magaji suka zo dubata tace haba Magaji maimakon kabar Sumayya ga tsohon cikin nan?Yace to nace ta zauna tace ita dai zata zo Bily tace shikenan na gode, duk surutun da akeyi cikin gida Magaji yaji sai dai bai yarda wani Bily ce ke cire cikin ba sai dai ko Yrm so yake ta fito daga asibitin yaji komai kuma yasha alwashin sai su Umma sunji. washegari ta fito daga asibiti,Yarima yazo yace an sallameta tazo ya kaita gida,bata musa ba dama kala bata ce masa ba ta shiga mota suka nufo gida. nan shima ya dan zauna shiru sannan ya fita jim kadan su anty Salma suka zo sukayi mata ta tas,har da cewa dama dan talaka bai iya samun guri ba,anty Fulera tace zaki ga tsiya aike baki ma iya abun ba inma cin dukiyar kike so dakin haifa kin tara dakin samu,yanzun kuma zamu kawo wadda zamu karu da ita 鈥榶ar masu dashi, suna fita ta tashi zaune ta ma rasa meke mata dadi duniya,nan ta dauko jakarta ta dibi 鈥榶an kayanda basu fi biyar ba sai dai kudi ta dauka ta zari makullin mota ta fita.sai data hau titi tama rasa ina zata?Kai tsaye ta dauki hanyar Kaduna, gidansu Mansu taje ita kanta tasha mamakin tukin da tayi domin bata taba fita cikin Bauchi da mota ba,Mansu bata Kaduna suna zaria kuma daga nan zasu wuce Gombe saboda hutun karshen shekara da Faruk ya samu,maigadin ne yace mata basa nan tace ta sani itama wani aiki zata yi a Kaduna ta shiga ta aje kayanta cikin dakin Mansu,sannan ta zauna ta rubuta ma Yrm text kamar haka.
[8:43AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 90馃彽
Na baka guri ka shakata sannan kasani bazan iya zama dakai ba, ka kasa tsaya wa akan halalin ka alhalin ban rage ka duk wani jin dadi ba. Baka sona baka son karuwa dani, burinka in mutu gurin cire min ciki ta hanyar da kai ka sani ni bansani ba, amma naje gurin likita ta min bayanin komai dama ance duk mutumin da baya kaunarka zai iya yi maka komai ciki harda neman rayuwarka. Da fatan daka samu sakona zaka rubuto min sakina koda ta waya ne sai 鈥榶an uwanka su aura maka wadda suke so 鈥榶ar masu kudi kuma wadda zata tara musu 鈥榶aya kamar yarda suka ce,tana turawa ta kashe wayar gaba daya.shiko Yarima yana ganin sako ya shigo ya duba ai a rikice ya nufi gida, ta tabbata nan kuma babu motarta yaje yace ma Umma ina Bily? Umma tace ni ban sani ba bata nan ne?Yace a'a na zaci tazo ne ya fita,gidan Umma ya nufa yana tafe yana neman layinta amma a kashe,bayan sun gaisa sai yace shin ko Bily ta iso?Umma tace ta nufo nan ne?Yace dana ce tazo ne ina zuwa kila tana gida ya fita duk inda yasan Bily tasansu sai da yaje har magariba ta shigo ya dawo gida ta gurinsu Umma ya shigo tana sallah son ma yana ta binta sallar.ya fita ya nufi sasansu,ya daure ya watsa ruwa sannan yayi sallah ya ci gaba da neman layinta shiru sannan ya kira Magaji bai boye ma Magaji komai ba,Magaji yace shikenan gaskiyarta ne tunda ta tafi ba sai ka huta ba? Haushi ya kama sa yace haba Magaji na kiraka ne fa don ka taimaka min yanda zan bulloma al鈥榓marin ka kuma dauko wata caftar, Magaji yace to in ba haka ba me zance?Yarima yayi shiru can yace da zan iya dana ce tayi tafiyarta amma na kasa ba zan iya ba, cewa fa tayi wai in sake ta? Magaji yace ka saketan mana to yaja tsaki,sannan ya nuna ma Magaji kofar fita,fita baka da amfani,Magaji ya mike ya fita Yarima yabi shi da kallo. Bacci ranar sai dai barawo amma kasa bacci Yarima yayi,baya son su Umma susani amma dole ne suji,sai dai zai ce musu taje gaida iyayenta ne,to kuma zasu ce babu ko sallama?Haka yayi tayi ya saka ya kwance,har gari ya waye.Magaji daya koma gida sai ya kira layinta yaji sa akashe, washegari ya fito ya shiga gidan sasan Yarima ya shiga lokacin Yarima shima ya gama tunanin cewa dole ya koma gurin Magaji,domin shine yasan zaria, kai shi abin kunyar nasa ma yana da yawa shekara nawa shida matarsa bai san kowa nata ba sai wanda ya kawo kansa yanzu gashi zai je dalilin yana bukatar ta dawo?Magaji ne ya katse sa da cewa abokina yaya ne? Yarima ya dubesa mun tashi lafia?Lafia lau inji Magaji sukayi shiru can Yrm yace ko can gidan iyayanta zamuje? Magaji yace to sai muje,kaga kaima tunda yanzun tayi dalili sun san kai Yarima yace to sarkin sheri naji yanzun yaushe zamu tafi?Magaji yace ko yaushe,Yarima ya mike yace jeka shirya mu tafi.sun iso zaria misalin karfe biyun rana,unguwar suka shiga kai tsaye, kallon unguwar yakeyi yana mamakin dama beauty a irin wannan unguwar take?Duk da an ce iyayanta talakawa ne da za鈥榓barsa inya iso(G.R.A)zai nufa nemanta,bai kara tsinkewa ba sai da suka tsaya akofar gidan,yace Magaji don Allah nan ne gidan iyayan beauty?Magaji yace tabbas Yarima yace,amma baka kyauta min ba da ka kasa sanar dani kamar ni ace surukaina suna cikin wannan gidan, ai samuna yazama na banza.Magaji yace lokacin gyaran ne baiyi ba shiyasa Allah bai horeni da sanar dakai ba amma yanzu ai kaga lokacin yayi tunda ance gani ya kori ji.suna fitowa daga mota Asma鈥榰 tana fitowa daga gida,tace a鈥榓 yaya Yrm sannunku da zuwa,Yrm cikin zumudi yace Asma鈥榰 beauty tana ciki ko?Asma鈥榰 tace wace antynmu?Yace eh,tace bata zo ba.Magaji yace babanku yana nan?Tace yana ciki,yace to shaida masa ga baki. Da sauri ta koma tace Mama ga yaya Yrm mijin anty,ta mike da sauri tace,to ina malam kirasa dakin Salame ta sanar dashi da sauri ya fito sai daya canza 鈥榶ar riga mai haske sannan ya fita wajen yayinda Umma ta shiga gyara gurin. malam ya shigo dasu Asma鈥榰 ta fita siyo musu lemu mai sanyi.Yrm cikin tausayi yake kallon gidan hakama dakin,bayan sun gaisa Asma鈥榰 ta kawo musu swan water mai sanyi da lemu,Yrm dai ruwan kawai yasha.Magaji ne ya gabatar da Yrm, sannan yace sun zo ne su duba ko Bily tazo gida,s saboda wata 鈥榶ar matsala da suka samu.Mama ta kalli malam shima ya kalleta sannan yace ikon Allah,amma ko daya ban zaci haka daga gurin Bily ba,domin yarinya ce mai hakuri,amma kunga bata zo nan ba,tun yaushe ne?Magaji yace jiya ne. Yarima ya cire hula saboda wata zufa data feso masa,a hankali ya furzar da wani huci mai zafi.sannan yace,ni babbar damuwata bata da isasshiyar lafia,to amma baba ba kuji anan din akwai inda zata?Malam yace kun duba cikin gidan Umman Bauchin kakarta?Magaji yace duk bata can,Mama ta nisa tace kun tuntubi Mansura?Duk da dai Mansu ma tana nan zaria,kila gidan Mansu taje.tunda kunce jiya ne ni kuma shekaranjiya Mansu tazo nan,nan aka hada su da Asma鈥榰 zuwa gidan Mansu,sun samesu har Faruk dinma yasha mamakin ganin Yarima a gidansa.Mansu ta musu kyakkyawar tarba sai dai Yrm ya kasa cin komai domin baiga beautynsa a gidan ba,sannan bai tsaya kwauron baki ba ya shaida ma Faruk dalilin zuwansu.cikin mamaki Mansu tace,Bily tabar gidanka?Yace wallahi tun jiya babu inda banje ba,Mansu tace shiyasa na dinga neman layinta shiru?To ina Bily zata?Wai ma meya faru haka da zafi ne har ta saka kafa ta fita?Yrm yace gaskia laifina ne,na sani kedai kawai abar zancan sai in Allah yasa anganta.wasa-wasa har kwana uku,su Yarima sun koma gida,Magaji shine ya sanarda Umma komai, amma ya boye kama shi da wata da Bily tayi, ya dai ce Yarima ne ke cire mata ciki shine ta gaji ta gudu gashi kuma su anty Salma suna ganin laifinta. Hankalin Umma ya tashi ta shiga cewa dama nayi tunanin yarinyar nan bazata aikata wannan aikin ba.
[8:43AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 91馃彽
Hankula sun tashi ana ta nemanta,ita ko tana can tana zamanta gidan Mansu na Kaduna,ta kashe wayarta,bata bukatar ji daga kowa kuma ba wanda hankalin sa yaje gurin.mai martaba daya samu labari ranar Yarima yaga bacin rai irin wanda bai taba gani ba,sannan mai martaba ya bashi kwana uku rak mazamaza ya nemo inda Bily ta shiga inko ba haka ba zaisa a tsare sa har sai an ganta.al鈥榓marin ya wuce duk yanda Yrm ya zata,domin wai don ma basu ji dayan ba.Waziri da Magaji sune suka roki mai martaba kan batun tsare Yarima,amma fa yayi fushi dashi sosai daidai da magana ta daina hadasu, ko Yrm ya gaisheshi baya amsawa.ranar data cika kwana goma cikin dare ta kunna wayarta,sakwanni tayi ta gani suna shigowa na Yrm ne,tayi ta delete bata karanta ba,amma nasu Mansu,Magaji,su Sakina da Maryam harda auta,kowa dai rokonta yakeyi ta dawo,hankula sun tashi Magaji har abinda mai martaba da Umma suke ma Yrm sai daya shaida mata sai taji dan sanyi cikin ranta damuwarta iyayanta,don haka sai ta tura ma Mansu text cewa tace suma su kwantar da hankalinsu tana nan lafia,sai dai bata Kaduna in lokaci yayi wato in Yrm ya saketa zata dawo ta tura sannan ta tura ma Yrm cewa,tana fa jiran sakon sakinta,tana tura masa ta kashe wayar. Lokacin da sakon ya shigo yana zaune kan sallaya ya idar da nafilfilun da suka zamar masa a madadin bacci yanzu,yana ta addu鈥榦鈥榠 gani yake tunda iyayansa suna fushi dashi bama zai ganta ba,shi dama zasu barshi da zafi gami da radadin rashin ganinta domin yanzun da baya ganinta dinnan yafi kowa tashin hankali,ya yarda sonta ne ya kamashi tuntuni bai gane ba sai yanzun.ganin sako ya shigo da sauri ya dauki wayar yana dubawa,jiki na bari ya soma kiran layin a kashe.haka yayi ta kira har ya gaji,yanzun yama daina zuwa asibiti,kuma sai yanzun yayi kukan rashin Modibbo,yasan da yana nan da iyayansa ba zasuyi fushi dashi ba,yaji da batan masoyiyar tasa. Mansu sun wuce Gombe bayan Bily ta shaida mata cewa tana nan lafia lau,sai dai bazata sanarda ita inda take ba,wasa-wasa shiru har sai da aka kai dasa rokon Allah ko ta wane gefen,gurinsu Umma ne gurinsu Mamanmu ne Allah ya bayyanata,su Umma yanzun sun sassauta ma Yrm saboda ganin halin da yake ciki,duk ya sukurkuce jin cewa su Mansu sunzo Gombe ya nufi Gombe ko zai samu wani labari.Yrm da kansa ya zauna gaban Mansu yana shaida mata cewa alhakin Bily ne yake binsa,Allah ya jarabce sa da sonta,yace kalleni kiga yanda na dawo shin baki sami wani labari daga beauty ba? Tausayinsa ya cika Mansu,tace tayi min text cewa tana nan lafia,yace to ni dazan san inda take wallahi ko ina ne zanje kome zata min indai zata huce zan yarda,tana da hakuri,Mansu tace,ai tasha a nonon hakuri ne haka mahaifiyarta take ya gyara zama don Allah bani labarin beauty mana? Nan ko Mansu ta zauna ta zayyane masa komai,sai kawai taga hawaye yana bin kumatunsa,dama cikin mafarki Bily ta soma saninsa?Lallai aurensu hadin Allah ne,dama tasha wuya agidansu?Yanzunne ya gane taki zuwa gida ne saboda kada kishiyoyin Mamanta suyi mata dariya.lallai bai dace ya wulakanta Bily ba tun farko lallai ya mata laifi dayawa.Mansu tasha mamakin ganin Yrm yana kuka,mai saka mata kuka yau gashi yanayin kuka don mace lallai gara da Bily ta tafi gashi sanadin haka ansamu cigaba, domin su anty Salma ma mai martaba ya saba musu yace dasa hannunsu Bily ta bace,kuma yana fushi dasu bazai gushe ba sai sun roketa gafara.Faruk yazo kuma sun lallashi Yrm, daya dawo hankalinsa yace yana so ya taimaki iyayan Bily amma kada suce sai da 鈥榶arsu ta bata,Mansu tace bazasu ce ba,shida Faruk da Magaji suka je zaria inda suka samu shahararren mai gini ya tsara musu yanda za鈥榓 maida kafdin gidan kirar zamani ba tare da an shiga hakkin kowa ba,nan ya yarda da aikin yace kuma yana bukata cikin gaggawa Abu indai da kudi yanzun ne sai gashi cikin sati biyu an tsara guri,matan gida kuma duk sai kowa ta koma neman shiga gurin Mama,gefen su Mama yafi kyau ga kayan alatu daya zuba musu,ya saiwa malam wanda yanzun ya koma Alhaji Mamman tun shekarar da suka je makkah,katon shago yasa akayi daga waje ya cika masa da kayan masarufi na saidawa,sito kuma cike da abinci,lokacin Yrm gani yake koda zai karar da dukiyarsa bazaiji komai ba.su Ladiyo anga babu sarki sai Allah an hakura, domin dai nagaba yayi gaba wadda suka tsana yanzun arzikinta suke ci.hassadar da sukeyi baya suke ci ba gaba ba.Yau watansu Mansu guda da kwana goma tuni sun soma shirin komawa gida,don ma sun tsaya ne sunsha sunan Sumayya,ta haifi 鈥榶arta mace,inda Yrm ya rada mata Bilkisu.sai da suka bita zaria sannan suka wuce,abinda Mansu ta rinka tunawa tana dariya a mota,lokacin da suka je yiwa Mama sallama,sai ta samu su Goggo amarya(kakarsu Bily)zaune a falon Mamanmu suna kallon TV.Ladiyo kuma an leko cikin falon tana cewa yaya gashi na fere miki doyar ai Goggo kuna kallo ne?Nima bari inzo in kallata. shima Faruk sai daya dara da Mansu ke bashi labari.abin al鈥榓jabi suna shiga farfajiyar gidansu sai taga motar Bily ta fito da sauri tana cewa abban dady ko dai nan gidan Bily tazo?San da suka shiga tana bacci kan kujera, gabanta kwalbar maltina ce da plate din farfesun kaji.duka Mansu ta dada mata tare da cewa,鈥榶ar iskar nan dama kina nan?Bily ta tashi tana dariya tace,kash!Da nasan yau zaku dawo dana cigaba kafin kuzo,Mansu tace wannan 鈥榶ar duniya ce dama nan kike?Kin shammace mu kina nan kici goma ki tsoma biyar,lallai 鈥榶ar duniya kin wahalar da Yarima kuma sai Allah ya saka masa.ta daure fuska wane abu ne kuma Yarima ?Don Allah kadaki sani nayi amai, Faruk kuwa mamaki ne ya hanasa magana,sai dai kallon Bily yakeyi,Mansu tace dole ka rasa bakin magana.Mansu tana shiga daki ta kira Yrm tace yazo ga Bily agidansu, sannan ta sanar dasu Mama.yarima jin abin yayi tamkar mafarki,a gurguje ya nufi toilet yayo wanka yana fitowa ya kira Magaji awaya cewa ya shirya suje Kaduna anga Bily,suna mota ne Magaji ke cewa da munje kayi aski gami da gyaran fuska,yace muje zanyi acan.cikin dare suka iso,Mansu lokacin ta soma bacci,Bily kuma tuni tayi baccinta,suna shiga Mansu ta nufi kiran Bily,tace wallahi bazata fito ba dole aka kyaleta Faruk yakaisu masauki.b bacci ranar Yarima baiyi ba gani yake inya kwanta zai farka yaga cewa cikin mafarki ne.babu yanda Mansu batayi ba ta fito su hada abin karyawa takai musu,tace Allah ya tsareta. Koda Mansu ta gabatar musu da kari,sai Yarima ya debe tsammanin ganin Bily,harma yace Mansu ban taba zaton zaki tsokane niba,zolayata kikeyi ashe.tace kai dai kugama tana zuwa,sam ko sha鈥榓war karyawar baiyi ba,ya koma ya zauna can kuma harda kuka Bily wai ita bata ko son ganin Yrm.Faruk shida kansa ya shigo yace dan Allah tazo,tana kuka tace kayi hakuri baban dady bazan iya kaffara ba kan cewa bazanje ba.ya mike ya fita kai tsaye gefen bakin ya nufa yace suzo ta hada kai da gwiwa suka shigo da tasan zasu shigo data shige toilet,Yrm yana yin arba da ita da sauri ya nufi gurinta kusa da ita ya zauna tare da cewa, beauty!Da sauri ta dago idanu jajir ta zabga masa harara.yayi murmushi tare da yin ajiyar zuciya, sannan ya mike ya kalli gabas ya tsugunna yayi sujjada,yana daga zaune agabanta yana kallonta shi duk tausayinta yake ji tunda yaji tarihinta agurin Mansu.yace beauty ki min duk abinda kike so nidai bukatata ki yafeni bazan kara ba,na dauki alkawari tsakanina da Allah.ta dubesa kabani takardata cikin mutunci kafin mukaiga kotu,yace kin manta ne beauty aure gidanmu ba鈥榓 saki,har sai mace tazo da alfasha, keko saliha ce.ya dubi Magaji sa baki abokina, Magaji yayi gyaran murya sannan yace kiyi hakuri Bily kiyafe masa komai ya wuce,tace Magaji ina ganin mutuncinka kayi shiru kawai cikin wannan maganar,yace to nayi shiru Allah ya huci zuciyarki.
[8:43AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 92馃彽
Ya tashi ya fita Yrm ko sai gashi y zube gwiwa biyu gaban mace,macen ma 鈥榶ar Nigeria 鈥榶ar Arewa wadanda ada yake kira kauyawa.yana cewa ta yafe masa ki yarda dani wallahi ina sonki da sauri ta dubesa gami da bude idanuwanta sosai,ina tsananin sonki beauty ban farga da tsananin sonki daya kamani ba sai da baki tare dani,na azabtu na wahalu,kalli yanda sonki ya maidani.hawaye ya soma gangaro mata tace yaya ka gane cewa kana sona?Ban yarda ba zaka yaudareni ne zaka cuceni ne,ya matso ya rungumeta duk da ta game jikinta guri guda, yana cewa I love you my beauty,I love u so much,I miss u a lot.turesa tayi tare da cewa ni bana sonka don Allah kabarni a takaice duk yanda suka zaci shawo kan Bily cikin sauki sai abin ya faskara, har Umman Mansu ta shigo ciki amma Bily ta kekashe nan ta tasa ta suka nufi zaria tace da Yarima yaje yayi hakuri zasu kawo ta ya dubi Umma yace don Allah kada ku mata fada laifina ne.bari in sanar dake laifukan dana mata.Bily ta dubesa da sauri an tambayeka ne?Yace a鈥榓 zan dai fada musu ne don kada suyi miki fada suga laifinki bada hakkinki ba,tace suma kasheni ina ruwanka ba鈥榓ce dai kafada ba,harma abin yaba Umma dariya tace to kai tunda bata son aji laifin naka ba sai ka barsa ba?Ku koma zamu maida ta insha Allah. A zaria idanu Bily ta zare tana kallon yanda aka fitar da titi cikin layinsu ga kwalbati layin yayi kyau bata gama tsinkewa ba sai data ga gidansu taga gefen mahaifyarta nan tayi sororo,Umma tace duk aikin Yrm ne,kuma yace shi don Allah yayi bawai saboda yana aurenki ba,ni kaina mota ya sai min wai in dinga zuwa aiki,baki kurum Bily ta taba ita abin bai burgeta ba.washegari sai gasu anty Saliha dasu Salma mai martaba yace suje su bada hakuri harda son suka zo yayi lakur jikin mamansa suka ce ta yafesu,tace insha Allah ya wuce.amma ita sai jibi zata dawo,Yrm yana samun labari sai yahau gyaran gidan aka sake fenti ya kwashe komai ya zuba sababbi don da tuni ya kammala nasu to hankalinsa ba kwance ba. Kafin ta dawo sai da Mansu tazo sukaje aka yimata gyaran gashi da lalle sai kace sabuwar amarya,ga kuma ainahin gyaran duk anyi suka nufi Bauchi.hutawa kawai Umma da Goggon sasa suka yi mata nasiha suka tafi.tana kwance kan sabon gadonta tana kallon kudin da Yarima ya kashe acikin dakin kawai sai kace baza鈥榓 mutu ba,son yana bacci a gefenta,Yrm ya shigo cikin kayan bacci,zo muje mu kwanta beauty ko nan zamu kwana?Tayi masa shiru,ya matsa jikin gadon daidai fuskarta ya tsugunna cikin kunnenta yace baki huce bane?Tace,subhanallah don girman Allah ka barni nace ya mike na barki sai da safe.komawa Bily tayi tamkar bakuwa agidan, kowa na gidan tana dari-dari dashi har Umma sai datayi mata magana tace wai shin 鈥榶ar nan kin kasa sakewa kodai baki yafe bane? Tace,a鈥榓 Umma aini dama ban riki kowa cikin zuciyata ba,ko Yrm da yayi sanadin komai tun kafin ya ganni ma na yafe masa,Umma tace Allah sarki,ai haka ake son bawa na kwarai,me saurin yafiya.Ubangiji yana yafe ma mai yafe laifin dan uwansa,Allah ka yafe mana zunubanmu wanda muka sani da kuma wanda bamu sani ba.Bily sai da ta dan kara gyara Yrm na sati daya sannan ta dauri aniyar karbarsa ranar juma鈥榓 ta shiga cikin kitchen ta tsara girki sai ranar ta shiga gefensa tunda ta dawo,yanda ya tsara gurin ya burgeta sosai ta jere masa abinci,sannan taje tayo gayunta cikin riga da wando na yan ubansun gurin Umma ta tura son ita kanta data dubi madubi tasan tayi ne.Yrm suka shigo da Dr. Salihu duk da yana dar-dar din kada ta bada shi ga mamakin Yarima sai ya ganta cikin gayun da yaji dama bai shigo da Dr. Salihu ba,domin zai kalle masa ado.tace abinci yana samansa,ai fa Yrm sai doki nan suka hau ta zuba musu,Dr. Salihu yace yana son abincin gargajiya ita matarsa tafi son na nasara,zai kawota su saba ta koya don ta rika masa,Bily tace sai sunzo.Yrm ya rakasa ya dawo. Ya zauna yana dubanta gaskia kinyi kyau,ta dubesa da fara鈥榓 ko?Yace sosai ma,har fa sai naji haushin shigowa da Salihu,tayi 鈥榶ar dariya ka kara abincin naga kamar baka koshi ba,yace ai kallonki ya kosar dani beauty,dan dawo kusa dani in dan ji kamshinki,da dan dumin jikinki.ba musu ta dawo,wayyo yau Yarima jinsa yake tamkar yau ne ya cire beauty dinsa daga leda,surkulle dai kala- kala ta jisa har sai daya bata tausayi kalaman so kuwa har sai da tayi hawaye don dadi ashe za鈥榓 gaya mata wannan kalmar a rayuwarta? Fahimtar da Yarima yayi beauty tana son a so ta sai ya shiga nuna mata so a baki a aikace,fili a boye a waya,nan fa ya tsumata itama ta shiga fiddo masa da nata son filla-filla.tuni Yarima ya sallami Tina duk da sai da yayi mata jan ido ta tafi.zama suke na tsantsan so babu algus a cikinsa suna kaf-kaf da juna,in yana gida suna like da juna in ko yana office suna nane da waya,wai wayaga sabon shiga?Abin zallar sha鈥榓wa ko aiki yake cikin laptop zaki samesa ya tada kai ne da cinyarta ita kuma tayi wasa da sumar kansa,wanka tare cin abinci tare,in yana gida zatayi musu abinci shima sai ya shige kitchen din.tafia suke cikin mota zasuje ganin sabon gidansu shida ita suna gaba abayan kuma son ne da Bilkisu 鈥榶ar gidan Magaji,ta kwanto kanta akan kafadarsa yayi dan murmushi tare da sa hannunsa ya shafi cikinta.yarona yana damunki ko?Tace yaya zanyi cikin shagwaba,yayi fakin gefen titi bari na gani sauran kwana nawa yazo ne ma?Cike da shagwaba tace,in Dr. acikin mota?ya kwantar da kujerar sannan ya kwantar da ita ya daga rigar yana aunawa,son yana dariya yace lah!Dady kana duba bebyn ne?Yace eh yayi kusa yazo son yace dady kullum sai kace ya kusa yazo ni nafi so in gansa.Bily tace don Allah nidai daga min kujera in tashi kun cika zumudi kaida yaronka,nina fiku kosawa in haihu in huta. Makeken gidane tsarin ginin abin sha鈥榓wa,an gama komai anata fenti.Bily tace nawan wannan gida sai kace mai mata hudu?Gaskia yayi mana girma,yace to shikenan zan sake aure,sai mu zau.....ta banko masa harara yace,ai subutar baki ne,tace yanda kayi subutar baki kace kai nawa ne ni kadai haka zaka hakura,ya kalli inda yaransu suna ta guje-guje cikin dakuna,ya jawota jikinsa ya tsotsi lebenta na kasa,yace ke dayace matata nan duniyar baki da kishiya,ta kalli idanunsa cikin ido tace inna mutu fa?Ya rumtse idanu ya kara matseta jikinsa,insha Allah bazaki rigani mutuwa ba,domin inkin mutu beauty nizan lalace ne na sani zan koma useless rayuwata zata daina amfani ko yaushe ina addu鈥榓 ki rayu ki rike min yarana ni kuma in mutuwar tazo ta daukeni,Bily tace baka min adalci ba nawa inka mutu nima binka zanyi,yace to yaran fa?Tace ga su Umma,yace su Umma sun tsufa,tace bazamu mutu bama yanzun duka-duka shekarunmu nawa ne?Yace beauty bata nan ake daukar jariri ma? Tace to ya isa muje gida.Yrm yanzun ne yake tashensa,shekarunsa talatin da hudu in bakin sani ba baki cewa yana da aure,duk inda ya shiga mata suna kallonsa,sai dai duk wata mace gani yake ta biyo bayan beauty.arziki yanata bunkasa yanzun ya gina asibitin(surgery)daban sunan Yrm ya zagaya ko鈥榠na cikin kasa,ko鈥榠na kaji ana kwararren likitan mata Dr. Yrm,jaridu,gidan talabishan,da kuma radio,sunsha hira dashi maza da mata Yrm birgesu yakeyi,ga kyau ga kudi ga kuma aji.Bily ta fara nakuda misalin karfe daya na rana lokacin Yrm yana asibiti amma bini-bini zakiga ya bugo waya,dama yana sa ran haihuwar tata gobe ne,ko kuma cikin dare ita kuma taki sanar dashi cewa tana nakuda,yana cikin duba marasa lafia sai kuma ya sake kiranta,matar dake zaune gabansa ya dubata yace yi hakuri madam,ya daga wayar da kyar yace beauty are you ok?Muryarta na rawa tace eh,yace ke ban yarda ba,meke damunki?Sai kawai yaji tace Innalillahi wa鈥榠nna ilaihir raji鈥榰n da sauri ya mike ya dubi matar don Allah ki jirani ya fita da matsiyacin gudu ya figi mota
[8:44AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 93馃彽
Yana isa cikin gida ya fita zuwa sasansu yana shiga dakinta beby yana fadowa,da sauri ya riketa beauty me yasa kika min haka?Nan ya kira Umma ta waya sannan ya dauko zaninta ya nade bebyn ciki.duk yanda zan baku labarin suna ya wuce nan,domin anyi sunan ne acikin sabon gidansu wanda suka tare ana jibi suna,washegarin sunan ne,Yrm ya shigo ya wuce Faisal babban dan anty Fatima suna hira da Asma鈥榰 auta,ya samu Bily tana bawa Al鈥榓min nono wato Yarima karami kenan,Bily ce ta zaba masa sunan,ya kalleta tana murmushi tace sannu da zuwa,ya zauna kusa da ita yasa hannu ya rungumota ya kai hannun ya matsa nonon,ta dubesa zakasa ya kware fa?Yace wai me ke tsakanin auta da Faisal ne?Bily tayi dariya tare da cewa, oho.adai cikin 鈥榶an kwanakin nan kullum suna tare,ina zaton har free call sukayi shekaranjiya dana cemata meke tsakaninku sai tace min wai yana koya mata karatu ne,nace shine karatun har cikin dare?Sai kuma tayi shiru.Yrm yace,Faisal yana da hankali kuma ya gama karatunsa yana aiki wannan ba matsala bane,da zaran sun sasanta sai ayi magana. Bily tace,Allah yasa mu dace.yayi dan murmushi,鈥榶an suna sun watse azo a san yanda za鈥榓yi dani fa,tace Allah basu tafi ba su Sakina suna can baya suna soya nama.Mansu ma tana nan,yace don Allah kaima Mansu beby kizo ki duba wani bebyn,tace kasan kuwa kai ne asalin bebyn nawa kayi kokari kwana takwas bari nazo inma irin hikimomina kaji nawa?Bily tasan kalar mijinta wurin bukata,dole ne ta kula dashi ta samu da rokon Allah da rigima ya daina neman mata bata fatan ya koma ruwa.kai radadin da tasha na neman matan da mijinta yayi bata fata ko makiyiyarta mijinta ya nemi mata,shiyasa bata barin sa cikin sha鈥榓wa ko wane lokaci yazo mata takan jure ko tana so ko bata so,in lokacin tana al鈥榓da ne zatayi amfani da hikimominta har sai ya gamsu ba tare da sun keta haddin musulunci ba,ciki ko laulayi basa hanata sauke nauyin daya rataya a wuyanta. Yarima kansa yana tausaya mata domin ya sani tana kokari, don haka sai ya koma tamkar bawanta, duk abinda take so cikin sauri zai mata,gashi yana dawainiya da duk wani mai hulda da ita bama danginta ba,amintakarsu da Mansura kuwa babu wanda ya kaisu murna da farin ciki,haka lokacin da suka ji cewa Faisal na son auta murna suka yi domin sun san duk halinsu daya da Bilkisu.haka rayuwa ta ci gaba da tafiya cikin sha鈥榓wa,鈥榶a鈥榶a maza Bilkisu tayi ta tarawa abinda mai martaba yaso yanzun gashi Allah ya bashi 鈥榶a鈥榶a biyar maza,t tuni suka amshe uku.Son da Al鈥榓min,da kuma Abba (wato mai sunan malam mamman)suka barsu da Saddik da Usman,ga kuma ciki mace? Namiji? Sai dai an haifa.
Tammat Bihamdullah!