Lokacin da Umar Faruk ya je asibitin MEEMA na barci bata tashi ba
Sai Zabba'u wacce ta kwana da ita, tana zaune a kan sallaya tana lazimin safe ya shigo. Suka gaisa
Sannan ya tambaye ta me jiki?
A nan take faɗa masa, "da sauƙi jikin ta ga ta nan ma tana ta barci bata tashi ba."
Idanuwan sa na a kan kyakykyawar fuskar ta wanda take a rame sosai. Ta sake fayau da ita tayi haske sosai. Ƙure ta da ido kawai yayi yayinda hannayen sa na a ciki aljihu
Ganin ya tsaya ɗin ne sai Zabba'u tace, "baka zauna ba Umaru? Tsayuwar ai sai ya ishe ka."
Murmushi yayi ba tare da musu ba ya ja kujeran Robber ya zauna a gefen gadon. Hakan ya ba shi damar ci gaba da kallon cuty face ɗin ta yayinda ya juya wa Zabba'u baya
Itama tunda ta ga ya zauna ɗin sai ta mayar da hankalin ta kan lazimin ta
Tsawon mintuna ashirin ya ɗauka a zaune a wajen ko ƙyafta idanun sa ba ya yi a kanta. Tun daga saman kanta da ke ɗauke da hulan sanyi har izuwa ƙafafuwan ta yake bi da kallo, tana sanye da doguwar riga ne baƙa me ɗan sakayau ɗin nauyi, tana da tsantsi rigan kuma bata da kwalliya, sai kuma blanket da ta rufa da shi wanda iyakan sa saman ƙirjin ta
A lokacin ne ta soma motsi alamun ta tashi daga barcin. Tana buɗe idanu kuwa a kansa suka soma sauka. Sai da ta rufe idon ta sake buɗe wa a kan nasa, sai dai ta kasa ɗauke wa daga kallon shi yayinda lokaci ɗaya ta dakata daga motsa jikinta
While Shima kallon ta yake yi ido cikin ido
Sun fi mintuna uku a haka kafin ita ta janye idanun nata ta sake rufe su ruf tana jin gaban ta na matsanancin faɗuwa, bugun da ƙirjin ta yake yi har shi yana iya gani. Sai da ta saka hannu ta janyo blanket ɗin ta rufa da shi har zuwa kanta ta juya kwanciya ta ba shi baya
A nan take ya lumshe idanun sa yana matse bakin sa. Sai kuma ya buɗe a hankali ya sake kai duban sa gare ta. In cool voice ɗin sa yace, "Are you all right? How your body?"
Tana jin sa sai dai ta kasa amsawa illa sake mayar da idanun ta da tayi ta rufe tana jin wani abu na tokare mata maƙoshi sakamakon tunawa da auren sa da tayi
Zabba'u wacce itama ta ji maganar nasa sai ta juyo tana kallon su, sai kuma tace, "ta tashi ne?"
"Eh Baaba." Ya amsa mata yana tashi kana yace, "zan tafi."
"To Umaru ka gaishe da su Momyn taka, Allah ya bada Sa'ar aiki, Ubangiji ya dafa maka."
"Amin." Ya furta but ya ƙi tafiya. Yana son sake kallon fuskar MEEMA amma ina ta shigar da fuskar nata a cikin blanket
"MEEMA open your face and say goodbye. He greets you without answering." Cewar Zabba'u wacce ta kula da halin da yake ciki
Sai dai ko kulata ta ƙi yi, tamkar ma ba ta jin su
Dole ya sake yin ma Zabba'un sallama ya fice
Yana fita ta buɗe fuskar ta, ko kaɗan babu wani walwala a tattare da ita ta sauka a kan gadon ta shige Toilet
Itama Zabba'u ganin yanda take shan ƙamshi yasa ta ƙyale ta, sai dai a ranta murmushi tayi da cewa, "ƴar nema, wannan yarinya rigimammiya ce, kya yi kya gama ai".
Sai ƙarfe tara su Hajiya suka iso asibitin. Sai dai Uncle Hashim be jima ba ya tafi kasancewar zai je asibitin da aka kwantar da Sajjad ya ga halin da yake ciki daga nan ya wuce Police station, don ya saka an tsare Kawu Ali kuma ya hana a ba da Belin sa. Bare zancen Umar Faruk ya shiga ciki shiyasa su ma ƴan sandan suka riƙe shi gam. Koda ya je har a lokacin be farfaɗo ba domin sukan wuƙan da tayi masa ya shige sa sosai, ko numfashi ba ya yi sai da oxygen
Su Umma duk suna asibitin suna ta kuka but an hana su ganin shi
Kawu Zubairu ne ma ke ta sintiri wajen ganin an saki Kawu Alin amma an hana, shi ke ta shige da fice a asibitin da can station ɗin
Sai da Uncle Hashim ya tabbatar ya kai maganar kotu kafin hankalin sa ya kwanta. Domin so yake yi a hukunta Sajjad a kan abinda ya yiwa MEEMA har da ma iyayen nasa domin gani yake yi da ɗaurin gindin su, daga can kuma a raba auren nasu, da farko shi cewa ma yayi, "auren be ɗauru ba tunda dole yayi mata, babu wani zancen ayi ta jiran saki."
Sai da Hajiya ta kwantar masa da hankali a kan, "a amsa takardan kawai a bar shi a auren ya yiwu, don bazai yiwu ace duk zaman nan da suka yi da mayar da ita matar sa da yayi ya zama zina ba, aure ba wasa bane tunda har an tabbatar da cewan ya tara jama'a ya aure ta to ya ɗauru."
Domin a lokacin tuni ƴan sanda sun cafke Mutumin da ya siyar mishi da gidan, ta hannun sa suka ci galabar samo Mutanen da suka zo suka ɗauki MEEMA, tunda da su aka ɗaura auren su kuma sun tabbatar da hakan, har wajen Malamin da ya ɗaura auren sai da aka je, shima ya shiga koman ƴan sanda daga taimako
Yanda Uncle Hashim ya ɗau zancen ba da wasa bane; don shi ya saka a kama duk wanda yake da hannu koda ba shi da laifi. So yayi ma a ba shi su ya kai su barikin sojoji wanda ya tabbatar muddin ya tafi da su wlh sai dai uwayen su su haifi wani, don sai ya ɗanɗana musu azaban da tunda suka fito duniya basu taɓa jin sa ba. Yana jira ne yanzu ma Sajjad ya farfaɗo a shiga kotu ya ji hukuncin Alƙali, idan be masa ba da kansa yayi ninyan ɗaukan mataki zai mayar da maganar ne wajen aikin su, ko tausayin Sajjad ɗin ba ya ji duk da ya ga halin da yake ciki, da za'a bar shi ma a haka ya hukunta shi da tuni ya hukunta shi ɗin.
Kwana uku MEEMA tayi a asibitin aka sallame ta tunda jikin ta yayi sauƙi, ga shi tana samun kulawa ta ɓangarori da dama na Mutanen gidan su, har Ummee kamar ta goya ta tsaban kulawa, shiyasa komi ba ta ce mata domin itama tana son kulawar uwa, tana kewar mahaifiyar ta shiyasa a ranta take jin kamar ta yafe mata, sai dai takan koka idan ta tuna tun farko ita ce ta ja mata, da bata aikata hakan ba da tuni babu ita a Nigeria. Wani lokacin kuma ta kan ga kamar rashin yarda da ƙaddara ce irin nata, idan ta yarda da ƙaddara baza ta taɓa ɗaurawa mahaifiyar ta laifi ba, komi da ke faruwa a rayuwar ta Allah ne ya ƙaddara, mutuwar Abee ɗin ta da silan dawowar ta Nigeria; hakan ke saka wa take jin sanyi daga tsanar da tayi mata.
A wajen Umar Faruk kullum yana a asibitin, idan be zo sau uku a rana ba zai zo sau biyu
Yanda yake nuna damuwar sa a kanta sam-sam ita hakan be mata ba, shiyasa ko kallon sa ba tayi bare ta tanka shi. Tun Hajiya da Zabba'u suna mata faɗa har sun gaji sun zira mata idanu
Koda aka sallame ta ma a ranan lokacin yana Office ne. Yana koma wa gida ya ci wanka ya fito da zummar zuwa gidan, har ya fita kuma ya dawo ya saka Luwaira ta shirya su Hafsah domin ya tafi da su
Kasancewar yanzu yana bata kulawa, duk kuma yana ƙoƙarin ya ga ya sauke haƙƙin ta, suna zaune lafiya babu wani abu kuma tunda Umar Faruk Mutum ne me tausayi da son kyautatawa na kusa da shi, ya riƙe Luwaira hannu bibbiyu yana faranta mata duk abin da take so tana samu, sai dai har yanzu ba ya jin ta a zuciyar sa
Ita kuma a ganin ta ya soma ƙaunar ta ne sakamakon shawarwari da Abida take bata wajen ta ga tabi wasu hanyoyi ta mallaki zuciyar sa. Haka kuma tana jan yaran sa a jiki sosai wanda shawaran Abida ne domin a ganin ta hakan zai saka ta sake samun zuciyar sa, tana basu kulawa sosai.
Koda ta gama shirya su ɗin ɗaukan su yayi ya fice ba tare da ya sanar da ita inda zasu je ba
Itama bata damu da sai ta tambaye shi ba illa adawo lafiya da tayi masu ta shige ɗaki abun ta
Kai tsaye shi kuma supper market ya wuce ya yo wa MEEMA siyayyan kayan dubiya abubuwa da yawa, har waya sai da ya siyo mata don dai kawai ya faranta mata. Yana son su riƙa kasancewa a koda yaushe shiyasa ya ga ya dace shi ya fara mallaka mata wayan ko don hakan zai rage masa wahalan kasancewar su tare.
✳️✳️✳️✳️✳️
MEEMA na zaune a ɗaki a lokacin sai ga Zabba'u ta zo kiran ta Umar Farouk na jiran ta. Jim tayi tana kallon ta bata amsa ta ba. Bata san kuma me zai ce mata ba, tunda yanzu yayi auren sa me zai nema a wajen ta? Mene ne dalilin zuwan sa wajen ta? Idan ma sabida soyayyar da yake mata ne ba ta jin zata iya zama da shi da wata, taya ma zata iya zama da kishiya alhalin ta tsani kishiya? baza ta iya ba sam, duk da zuciyar ta ba ta mata daɗi tana cikin ƙunci da jin zancen auren sa, amma ta ji daɗi da bata amince masa da soyayyar sa ba, ko ba komi bata amince ba bare yayi tunanin tana son sa ne, dole kuma zata faɗa mishi gaskiyar abin da ke ranta domin baza ta iya jure sintirin shi a wajen ta ba, zuciyar ta zata iya bugawa idan ta ci gaba da damuwa da shi. That's why ta tashi ta fito daga ɗakin tayi Parlour, daga ita sai doguwar rigan atamfa me ruwan ƙwai, sai aka yi design ɗin sa da ja da fari, hakan yasa ya sake haska ta sosai kayan, ɗinkin yayi mata kyau sosai tunda akwai kwalliya da aka yi a gaban rigan da ƙyallen atamfar, sai gashin kanta da ta tufke a tsakiya ta ɗaura baƙin siririn gyale a kan ba tare da ta ɗaura ba
Daga shi sai yaran sa ne a parlour'n tunda duk sun gaisa da su Hajiya sun wuce ɗaki. Fitowar ta yasa suka haɗa idanu wanda ya bi ta da kallo kamar wacce yau ne ya soma ganin ta, be taɓa ganin ta da kayan hausawa ba sai yau shiyasa ba ƙaramin mugun kyau tayi masa ba, ji yake yi tamkar yau ya saba ganin ta, yayinda yake jin ƙaunar ta da begen ta na ƙara huda can cikin zuciyar sa
Ita kuwa tuni ta kawar da nata idanun daga kallon sa ta samu waje a ɗaya daga cikin kujerun falon ta zauna. Sosai take jin kaifafan idanun sa a kanta suna yawo wanda suke sake sagar mata da jiki tare da ƙara mata bugawar zuciya da rashin natsuwa, ko kaɗan ba ta ƙaunar kallon sa sabida yanda yake mata kwarjini shiyasa a yanzu ɗin ma bata sake ɗago kai ba bare ta kalle sa
Shi kuma yayi shiru ya kasa cewa komi. Sai kuma daga baya ya kalli yaran nasa waɗanda su ma sun mayar da hankali wajen MEEMA suna ta kallon ta kamar sun samu t.v. ce musu yayi, "su gaishe ta."
Hakan yasa suka haɗa baki wajen furta, "ina wuni."
Ita kuma a sa'ilin ne ta ɗaga kai tayi duba gare su. Guntun murmushi ta saki tare da amsa su da, "lafiya." A cikin gurɓataccen Hausan ta, kasancewar yanzu zaman ta a cikin hausawan yasa ta soma iya guntayen words waɗanda basu da wahala kuma tana fahimtar su. Miƙa hannun ta tayi kuma alamun, "su zo wajen ta."
Hakan yasa Yusra ta taso da sauri ta isa wajen ta
Hafsah kuwa ƙin zuwa tayi. Sai da shi yace mata da kanshi, "ta je." Sannan ne ta nufe ta
Hannayen su ta riƙe yayinda har yanzu bata gusar da murmushin da ke fuskar ta ba ta soma tambayar su, "ya suke?" Da school ɗin su
Yusra ce kaɗai take amsa mata while Hafsah tuni ta samu waje ta zauna abun ta tana wani ɗaɗɗaure fuska. Dama ita ba ƙaunar Mutane take yi ba musamman waɗanda taga suna mu'amala da mahaifin ta, Yusra ce kawai idan ta je waje take iya sakin jikin ta tamkar ta sanka
Hakan yasa MEEMAN ta ɗauke ta ta azata a jikin ta
Yanda Umar Faruk ya ga ta nuna wa yaran sa kulawa sai ya saka shi farin ciki tsantsa, domin shi Mutum ne me son ya ga ana ƙaunar yaran sa. Sai kallon su yake yi da murmushi a face ɗin sa
Ita ce da ta ji shirun nasa yayi yawa sai tayi ƙarfin halin ɗago kai tana kallon sa, a hankali ta furta, "What are you going to do in my place?"
Shiru ya ɗan yi shima yana kallon ta, kana kuma ya buɗe baki yace, "I came to greet you in your body. I hope you are well?"
"Na'am." Tafaɗa a takaice tana ɗauke kai
Hakan yasa suka sake yin shiru gaba ɗayan su
Can kuma da ya gaji don kansa ya buɗe baki yace, "I brought the phone to you so we can greet each other." Sai ya kira sunan Yusra yace mata, "ta zo ta miƙa mata."
Tasowa tayi da gudun ta ta amsa ta kai mata
Ba da son ranta ba sai don ganin idon yaran yasa ta amshi wayan tare da ce mishi, "shukran."
Murmushi yayi kawai yana kallon ta. Ya rasa abun cewa dole yayi shiru, sauran kayan ma da ya zo dasu su Ummee ya ba. Wai, "na dubiya," wayan ce kawai yayi ninyan miƙa mata da kansa
Ita MEEMA ta gaji da zaman su a haka shiyasa ta tashi tace mishi, "She'll go inside." Da haka ta shige abun ta ba tare da ta jira cewar sa ko wayan bata ɗauka ba, domin haushin kanta take ji a yanda ta kasa buɗe baki tayi masa magana, takan rasa meyasaka ba ta ƙaunar yin magana a gaban shi koda kuwa tana son furta wani abu a cikin ranta?
Shi kuwa kwata-kwata ransa babu daɗi da yanda ta nuna masa, musamman ƙin ɗaukar wayan da tayi ta wuce da shi hakan ke nuni da cewa bata yi farin ciki ba. Ɓoye damuwarsa kawai yayi ya saka Hafsah ta je ta faɗa wa mutanen gidan, "za su tafi". Bayan yayi musu sallama suka fice tare da niƙi-niƙin kaya da su ma su Hafsan suka samu daga wajen su Hajiya da Ummee.
Kai tsaye suna zuwa gida ɗakin sa ya shige ya bar su a falon ƙasa. A kan gado ya zube komi be iya cirewa ba illa takalman kafafun sa, lumshe idanun sa yayi yana mayar da ajiyan zuciya. Ya jima a haka kafin ya tashi tsaye jiki a mace ya wuce Toilet don ɗauro alwalan sallan asar.
Luwaira sai da ta tambayi yaran inda suka je
Da sauri Hafsah ta faɗa mata, "ai wajen budurwan Dady suka je wai ya je duba lafiyan ta." Ta ƙare maganar tana tura baki gaba
Yayinda Yusra kuma cikin murna tace, "Aunty wlh ga ta kyakykyawa, Dady ma yace mu ce mata Aunty, kuma ƴan gidan su ne suka bamu Waɗannan kayan."
Yanda maganar nasu ta bigi zuciyar Luwaira hakan yasa ta kasa cewa komi illa kallon su da take yi. Kenan dai wajen yarinyar da yake so ɗin ya je? Har yanzu be rabu da ita ba? Wani irin ƙunci ne ya tabaibaye mata zuciya, tsam ta tashi zata wuce ɗaki ba tare da ta sake bi ta kansu ba
A lokacin ne Umar Faruk ya sauko daga saman yana saukar da hannayen rigan sa da ya naɗe wajen alwala, fuskar sa duk ruwa har saka hannu yayi ya sake sharce wa, idanun sa a kan Luwaira wacce ta tsaya ta kasa shigewa ɗaki tana sunkuyar da kanta ƙasa, sai da ya sauka Steps ɗin kafin yace, "ki tasa yaran nan mana kiyi musu alwala suyi Sallah, and ki dafa min ruwan lipton ina buƙata ki saka min na'a-na'an nan a ciki."
"To." Ta amsa mishi tana kallon sa a yanzu ɗin
Shi kuwa tuni ya wuce wajen su Hafsah yana cewa, "to ƴan mata na a tashi aje ayi sallah, ku bi Auntyn ku ɗaki tayi muku alwala."
Amsa masa suka yi suna tashi da gudu suka yi ɗakin Luwairan
Ita kuwa tuni dama ta shige ta sanƙami wayan ta ta soma kiran layin Abida, don yanda take ji baza ta iya jira ba sai ta kwashe komi ta faɗa mata. Suna shigowa ɗakin kallon su tayi da ce ma Hafsah, "ke Hafsah ba kin iya alwalan ba?"
"Eh Aunty na iya."
"To ku shiga Toilet ɗin kuyi ina zuwa, but ban ce kuyi min ɓarnar ruwa ba don na san halin ku musamman ma ke Yusra, ban son rashin ji."
Duk gyaɗa mata kai suka yi suka wuce cikin Toilet ɗin nata
Ita kuma ta mayar da hankalin ta kan wayan ta.
✳️✳️✳️✳️✳️
Tunda MEEMA ta shige ɗaki kuka kawai ta saka saboda yanda take jin ƙunci da wani abu ya tokare mata a wuya, duk yanda ta so ta jure ta kasa. Ta rasa me ke damun ta domin har yanzu ta kasa gane kishi ne ke ɗawainiya da ita. Har yanzu fargaba da tsoron abun da Sajjad yayi mata yana tare da ita, shiyasa hakan ke tasirantan zuciyarta take jin babu wani namiji da zata iya yarda da shi a halin yanzu, tana cikin tsoro sosai, but sai dai Umar Farouk ya tsaya mata a rai matuƙa. A ranan haka ta saka su Hajiya gaba da rigiman ta wai, "dole sai sun mayar da ita Riyadh, baza ta iya zama a nan ba zata iya mutuwa, ta tsani Nigeria ba ta son zama." Haka take ta musu kuka duk ta rikita su, sun kasa gane me ke damun ta don da farko sun yi tunanin wani abun ne Umar Faruk yayi mata, sai ce musu tayi, "ita a'a ba ta son Zama a nan ne kawai."
Ƙarshe dai sai da Uncle Hashim ya dawo ya rarrashe ta kafin ta samu tayi shiru, shima sai da yayi mata alƙawarin, "zai komar da ita."
Hajiya tace, "me zai hana idan zaka koma Abuja kawai ka wuce da ita can, na san can zai fi mata nan tunda ƙila abubuwan da Sajjad ya yi mata ne har yanzu yake ɗaga mata hankali, ya kamata ta koma can da zama hakan zai fi mata."
Uncle Hashim yace, "to Hajiya, amma sai mun gama da case ɗin nan don ba na son idan na tafi na sake dawowa, daƙyar aka bani hutun sati biyun nan da na ɗauka shima daƙyar sai da na basu ƙwararan hujjoji".
Daga haka suka bar zancen a kan MEEMA zata bi Uncle Hashim can Abuja
Itama ta amince domin dama ba ta son zaman ta a nan ne ba don komi ba sai don Umar Faruk, tana jin idan har ta ci gaba da saka shi a idanun ta ƙarshe zuciyarta ce zata buga, baza ta iya jura ba, baza ta iya juran halin da take ji a zuciyar ta a game da shi ba.
Bayan kwana biyu da faruwar abun wanda yayi dai-dai da saura kwana huɗu a shiga kotu, sai dai labari suka ji Sajjad ya mutu
Tashin hankali da ba'a saka mishi rana, rikici fa ya ɓarke a tsakanin su Uncle Hashim da su Kawu Ali
Domin shi Kawu Ali ya hau ya dira yace, "wlh bazai yarda ba shima sai ya maka su a kotu domin MEEMA ita ta kashe mishi Yaro, bazai taɓa yarda ba sai ya bi kadin ɗan sa."
Rigima aka yi ta yi daga ƙarshe ya maka su shima a kotun. A kwana huɗun da ya rage yanzu za'a shiga kotu
Su Umma sun sha kuka har sun gode wa Allah, ɗan su ɗaya tal ya mutu a kan wata, babu zagin da MEEMA bata sha ba a wajen dangin su, tuni labari ya bazu kowa ya san MEEMA ƴar wajen Faruk ita ce ta kashe Sajjad, wasu suna, "Allah wadai da ita." Wasu kuma suna cewa, "su ma Allah ya ƙara da suka amshe ta har suka ajiye ta a gidan su, ga shi nan ta zame musu ƙarfen ƙafa ta kashe musu yaro be ji ba be gani ba." Yayinda wasu kuma suke faɗin, "ai baza su yarda ba dole sai an kashe ta itama." Shiyasa suka ji daɗin shiga kotun da za'a yi domin a hukunta ta, ko kaɗan ba sa ganin laifin da shi ya aikata mata.
💎💎💎
*MEEMA FAROUK*
💎💎💎
*NA_NAFISA ISMA'IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏻
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._
*TARIHIN FARILTA SALLAH*
```An farilta sallolin nan biyar ne gabanin ƙaura, watau hijira, da shekara ɗaya da rabi. Sallah ce kaɗai ibadar da aka farilta ta a sama a daren Isra'e, kamar dai yadda aka ruwaito a hadisin nan na Anas. Da farko an umurce shi da Sallah guda hamsin ne; da sannu aka dinga rage su har suka zama biyar a bisa roƙon da shi Manzon ya yi wa Ubangijin sa. Da suka zama biyar, sai Allah ya ce masa su biyar ɗin nan, dai-dai suke da hamsin.
Malamai da yawa sun yi bayanin yadda sallar ma'aikin Allah, mai tsira da aminci, take gabanin Isra'en.
Wasu malaman sun ce, "Gabanin Isra'e, babu wata sallah wadda aka farilta sai sallar dare (Ƙiyamul lail) wadda aka umurci ma'aiki da yin ta ba da iyakataccen lokaci ko adadi ba, kamar yadda yake a suratul Muzzammil, ayoyi huɗu na farko:
"Ya wanda ya lulluɓe! Ka tsayu domin yin Sallah a cikin dare (duka) face kaɗan, rabin sa, ko ka rage abu kaɗan daga gare shi, ko ka ƙara kansa... Ma'aikin Allah ya kasance yana yin sallar a kashi biyu cikin uku na dare ko a rabin sa ko kuma sulusin sa. Musulmi suka dinga yi tare da shi kamar shekara guda har suka gaji; daga nan sai Allah ya shafe ta don jin ƙan su.
An ruwaito cewa sallar da Musulmi suke yi gabanin tafiyar dare suna yin ta ne kafin faɗuwar rana da kafin ketowarta kamar yadda yake a sallah littafin Almanhalil Azb. Gabanin ƙaurar Annabi zuwa Madina raka'o'in sallah bibbiyu ne, bayan ƙaura ne suka zama hurhuɗu, illa magriba da ta kasance raka'a uku, ita kuma sallar subahi ta tsaya a kan biyu saboda dogon karatun da ake yi cikin ta. Buhari da Ahmad sun ruwaito daga Nana A'ishah cewa, "an farilta sallah raka'a bibbiyu, bayan ƙaura ne aka mai da ita raka'a hurhuɗu, amma an bar sallar tafiya a kan raka'a ne bibbiyu, sai sallar magriba ita ko da ma raka'a uku-uku ce."
Allah ya sa mu dace.```
*NO_38*
A ranar da aka shiga kotu abun da aka soma tuhumar Sajjad da shi; laifin kidnapping, sannan auren dole da ya yiwa MEEMA ba tare da amincewar ta ba; ya zamar da ita Matar sa ta ƙarfi da ya ji, laifin drugs abused, yayi amfani da ƙarfin sa wajen ɗura mata magunguna waɗanda suka gusar mata da hankali har hakan ya kusa sanadiyar taɓa mata ƙwaƙwalwa, sannan kuma ya yi mata abortion wanda hakan yasa ba don tana da rai kusa ba da tuni an rasa ta. Waɗannan laifukan da aka lissafo a kan Sajjad su ne yasa Alƙali ya yanke hukunci nan take ya wanke MEEMA da laifin ita ce ta kashe shi, tayi hakan ne kawai domin ƙwatan kanta wanda ko waye ma a madadin ta hakan ne ya kamata yayi, don haka bata da laifi ko kaɗan tunda shi ne ya cutar da ita, azumi ne zata yi wanda kuma wannan tsakanin ta da Ubangiji ne
Sanda Alƙali ya buga guduma ya tashi ya fice sosai zuciyoyin su Kawu Ali ke tafarfasa, ba haka suka so ba amma basu da yanda za suyi, suna ji suna gani an kasa hukunta MEEMA a bisa kashe musu ɗa da tayi
Yayinda Mutane su ma suke ganin laifin Sajjad ɗin da irin ta'addancin da yayi, sun yi tur da Allah wadai da shi duk da babu shi a raye, haka yake ta shan zagi nan da nan labarin ya bazu a ko ina, kama tun daga gidajen talabijin da gidajen rediyo da jaridu duk labarin ya bazu, ko wani kafa ka kunna zancen kawai ake yi ana tur da Maza irin su.
To farin ciki dai a wajen su Uncle Hashim ba a magana tunda komi yanzu ya kau sai murna, sun koma gida cike da farin ciki inda kowa hankalin sa ya kwanta har ita MEEMAN wacce ta ɗaga hankalin ta gaba ɗaya sai kuka take yi, a tunanin ta ko za'a kama ta da laifin kisan kai ne
Yanzu haka kuma shirye-shiryen wuce wa Abuja suke yi ita da Uncle Hashim
Sanda ya sanar wa da Umar Faruk hankalin sa yayi ƙololuwar tashi, be shirya yin nesa da ita ba sabida ƙaunar da yake mata, yana ganin kamar idan tayi nesa da shi zai rasa ta. Duk ya tashi hankalin sa har yana cewa Uncle Hashim ɗin, "Dude yanzu shikenan bazan aure ta ba why zaka tafi da ita bayan ka san ina son ta? Idan tayi nesa da ni hakan zai saka na rasa ta gaba ɗaya?"
Murmushi Uncle Hashim ɗin yayi zuciyar sa cike da mamakin abokin nasa, sosai yake mamakin yanda yake kasa ɓoye soyayyar MEEMA har hakan ke son cutar da shi, hakan yasa yace mishi, "ka kwantar da hankalin ka idan har muna raye MEEMA Matar ka ce, ba wai tafiyar da zamu yi shi ne ka rasa ta ba, idan Allah ya yarda kai ne Mijin ta domin zan fi kowa farin ciki da hakan, ace yau daughter ta aure wanda ke matuƙar son ta ai Ni abin murna ne a wajena, Please be a man mutumi na ban son ka nuna ragwanta daga ƙarshe kuma ka ja ta raina mu, sai kace wani yaro?"
Murmushin da be shirya ba ya saki yayinda yake kallon sa, cike da sanyin murya irin nasa yace, "baza ka gane bane Dude, amma zancen raini kuma ai ya kau tunda har nake ƙaunar daughtern ka."
"Haka ne. To dai ka zama na Mijin kai ma ka ja ajin ka, itama daughter tana son ka fa ba Wai kai kaɗai ne kake kiɗan ka kake rawanka ba, ka bata lokaci na san komi zai wuce da yardan Allah."
Cike da fara'a a fuskar sa yace,
"Are you really or kidding me? Are you sure she loves me?"
"Yes she loves you."
Lumshe idanuwan sa yayi cike da farin ciki ya kasa cewa komi
Sai Uncle Hashim ya dagi kafaɗun sa yana dariya da cewa, "ka zurma da yawa Mutumi na, Allah ya baka daughter na zaku dace sosai."
"Ameen Ameen." Yafaɗa yana shafa kansa, sai kuma yace, "when are you going?"
"Tomorrow insha Allah."
"Ok Allah ya kai mu, zan zo muyi sallama."
Da haka suka rabu kasancewar dama Uncle Hashim ɗin ne ya je ya same shi a Office ɗin sa.
Koda goben tayi a lokacin da zasu tafi sai ga Umar Faruk ya zo gidan. Shi ne ma ya ɗauke su ya kai su airport kasancewar ta jirgi zasu bi. Duk yanda ya so suyi magana da MEEMA hakan ya faskara
Domin ita ko kallon sa ba ta son yi, tunda ya zo gidan sai ta ɗauke walwalan ta take ta faman fushi, ko magana ta ƙi yi har suka wuce. Haka ma a cikin motan tunda ta shiga baya ta mayar da hankalin ta a kan wayan da ya siyan mata tunda yanzu da shi take using sakamakon nata tun sanda Sajjad ya amsa ba'a san inda yake ba ma, bata sake ɗago kai ba har suka kai
Shi kuma suna ta hira da Uncle Hashim kasancewar shi ke tuƙa motan, Uncle Hashim kuma na gefen sa, but hankalin sa na a kanta yana ta kallonta ta mirror ko zata ɗago kai, sai dai hakan ya gagara
Koda suka kai shi Uncle Hashim ɗin tuni ya fice yana amsa call
Hakan ya ba shi damar saka luck koda ta zo buɗe wa sai ta kasa
Dalilin da yasa ta ɗaga manyan idanuwan ta ta sauke a kanshi kenan tana kallon sa fuska babu fara'a. Yanda suka haɗa idanu ta cikin mirror ɗin ne sai tayi saurin ɗauke kai saboda wani irin faɗuwa da gaban ta yayi, yayinda ta ji wani abu ya tsarga mata tun daga tafin ƙafafuwan ta har a cikin kwanyan ta, dole ta lumshe idanuwan tana wani ƙanƙame jiki sakamakon tashi da tsigan jikin ta tayi
Shima lumshe idanun yayi kafin kuma ya juyo sosai yana fuskantar ta, tsawon soconni biyu ya ɗauka befor ya buɗe baki ya kira sunan ta, "ZULAIHA."
take a nan ta ɗaga kai ta sake duban sa saboda yanda ta ji sunan ya shige ta sosai. Ido cikin ido suka kalli juna sai ta sake ɗauke kai saboda ta kasa jurewa da abubuwan da take ji na sauyi daga jikin ta
"Why are you going to leave me?"
Tambayar ta zo mata a bazata shiyasa ta sake ɗaga kai ta ɗan tsira masa ido kaɗan before ta sake ɗauke kai, hannayenta ta haɗe waje ɗaya tana jin zuciyar ta na sake gudu, sosai a yanzu ɗin ta soma rasa nutsuwar ta kasancewar su waje ɗaya
Numfashi shi kuma ya ja yana ci gaba da kallon ta ko ƙyafta idanu ba ya yi, a duk second soyayyar ta na ƙara huda magudanan jinin sa yana sake linƙaya; ta yanda yake jin tamkar yayi ta kurma ihu sabida azaban son ta, yana jin kuma kamar ya jawo ta ya mayar da ita cikin sa ta zama mallakin sa na har abada daga yanzu ɗin, sai dai babu hali. Sake jan wani ajiyan zuciyar yayi tamkar dai ya dawo daga duniyar tunanin da ya afka, ya sake kafe ta da ido cikin cool voice ɗin sa yace, "I will miss you when you leave, I love you and I love you so much! I hope you continue to remember Me when you leave?"
Shiru ne ya biyo bayan zancen nasa, sai dai ita tuni ta sake kai kanta ƙasa tana sake haɗe hannayen ta waje ɗaya waɗanda suka soma tsatstsafo da gumi, ta soma gajiya da yanayin da take ji a tare da ita shiyasa ba tare da ta kalle sa ba tace, "I'm leaving... Open the door for me."
Yanda sassanyan muryan nata ya daki kunnen sa ne yasa shi mayar da idanun sa ya rufe. Take kuma ya buɗe yana kallon ta be ce komi ba, sai can kuma ya danna luck ɗin ya buɗe mata yana me sake gyara zaman sa sosai
Ita kuma tuni ta buɗe ƙofan ta fice har tana rawan jiki, daƙyar ta aro jarumta wajen daidaita tafiyan nata wanda hakan ya sake mayar da ita tamkar tana yanga ko ba ta son taka ƙasan
Shima tuni ya fito ya harɗe hananyen sa a ƙirji yana bin ta da kallo. Har ta ƙarisa wajen Uncle Hashim be ɗauke ido a kanta ba
Sai daga baya da Uncle Hashim ɗin ya gama wayan ne ya taho wajen sa daga nan suka sake sallama. Sai suka wuce tare shi da MEEMAN kasancewar har an fara shiga jirgi, tana jan akwatin ta shima tare da nashi a hannu suka tafi
Umar Farouk sai da ya ga tafiyan nasu kafin ya hau mota ya tafi shima, zuciyar sa duk babu daɗi don shi gani yake yi tamkar ba ta son shi, and kuma Hashim yana faɗa masa, "tana son shi". a haka ya koma gida cike da tunani kala-kala a ransa da kuma yanda zai jawo hankalin ta a wajensa, gaskiya bazai iya haƙura da ita ba dole ne ya san abun yi.
✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️
Sun isa Abuja By three. Drever'n Uncle Hashim shi ya zo ya ɗauke su zuwa barikin sojoji
Bayan sun isa gida Jalila da Habeeb suka fito tarban su
Da gudu Habeeb ya je ya rungumi MEEMA yana faɗin, "Aunty Oyoyo."
Murmushi tayi cike da farin ciki a fuskar ta ta sake ƙanƙame shi
Jalila wacce ta amshi Trollyn mijin ta tana murmushi ta kalli MEEMAN da cewa, "Today you are at our house. Welcome."
"Thanks Aunty." Tafaɗa itama still tana murmushin
Cikin gidan suka wuce, inda gaba ɗayan su suka zube a saman sofa. Daga baya kuma Jalila ta tashi ta kawo musu drinks duk ta zuba ta basu. Bayan sun huta sai ta raka MEEMA ɗakin da zata zauna
Wanka ta soma shiga tayi kasancewar ta kwaso gajiya, sai ta ɗaura alwala tunda four ta kusa. Sallah tayi ta saka doguwar riga me sauƙin nauyi green color kafin ta fita Parlour. Jalila kaɗai ta tarar tunda su sun fita masjid
Nan Jalilan tace mata, "ga abinci nan a saman dainning."
Zuwa tayi ta zauna tayi serving kanta ta soma ci kasancewar da yunwa dama a tattare da ita
Ita kuma Jalilan kichen ta wuce ta ci gaba da aikin ta
Babu jimawa su Uncle Hashim suka dawo daga masallacin. Shima kan dainning ɗin ya nufa ya zauna. Suna cin abincin suna taɓa hira, daga ƙarshe bayan sun gama suka koma Parlour
A nan ne Jalila itama ta fito ta zauna aka ci gaba da yi da ita
Daga baya kuma Uncle Hashim ɗin ya tashi ya fice a gidan; su kuma suka ci gaba da hira tare.
Zuwa dare bayan sun ci abinci ne MEEMA ta koma ɗaki, tayi wanka har ta saka kayan barcin ta riga da guntun wando baƙaƙe masu tsantsi, tana tufke gashin kanta wayan ta tayi kar'ar shigowar text message, sai da ta gama abin da take yi kafin ta taso a gaban mirror ɗin ta zauna a saman gadon tana ɗaukan wayan nata. Duba wa tayi ta ga text ne daga Umar Faruk, kasancewar dama ya saba mata a koda yaushe, tunda ya bata wayan ya soma kiran ta but bata taɓa ɗauka sun yi waya ba, tun sanda ta ɗauka ta ji muryan sa shikenan kuma ta dena ɗauka, shiyasa a koda yaushe yake mata text babu dare babu rana, sai dai ta buɗe ta duba but bata taɓa mishi reply ba. Yanzun ma koda ta gani karanta wa tayi ta mayar da wayan ta ajiye, sai ta kwanta tana aza kanta a saman pilow tare da matse wa, lumshe idanun ta tayi tayi shiru bata sake motsa wa ba, sosai ta faɗa duniyar tunani sai da wayan ta soma ring before ta buɗe idanun ta a kasalance. Sai da ta ɗauki two seconds before ta ɗauki wayan tana duba screen ɗin, ganin Numban Umar Faruk sai ta tsaya kawai tana kallon wayan, daga ƙarshe har ta katse bata ɗauka ba, baza ta iya ɗauka bane shiyasa koda ya sake kira bata yi peacking ba, tana ji har wayan ta gaji da ring ta dena, sai kuma wani sabon message ɗin ya shigo. Dole ta ɗauka jiki na rawa ta soma duba wa. Murmushi kaɗai ta saki tana ajiye wayan ta koma ta kwanta. Shiru tayi kawai tana sauraron bugun zuciyar ta, ta jima a wannan yanayin wanda ita kanta ta kasa gane abun da ke damun ta, daga ƙarshe kuma sai tayi addu'a ta gyara kwanciyar ta. Babu jimawa barci ya sure ta cike da mafarkai kala-kala.
Zuwan ta Abuja yasa ta samu sauƙi daga abun da ke damun ta, sosai zaman gidan yake mata daɗi kasancewar yanda Uncle Hashim ke kula da ita matuƙa, kuma da yanda suke gudanar da al'amuran su shi da Jalila komi birge ta yake yi
Jalila yanzu da kanta take jan MEEMAN suke fita yawo ko kuma wajen aikin ta, komi Idan zata yi sai tace, "MEEMA ta zo suyi tare." Har ta girki tare suke shiga kichen
Duk da ita MEEMAN ba ƙaunar cooking take yi ba but ba ta mata musu haka take shiga suyi tare tana koya mata wasu abubuwan. Shiyasa da sannu da sannu komi ya soma bata sha'awa har idan Jalilan ba ta nan ita zata shiga tayi ta jagwalgwala girkin, ko ta girka abin da take so ta ci, idan be yi daɗi ba kuma ta zubar.
Zuwa yanzu Uncle Hashim ya sama mata wani aikin but a wani Company ne na jaridu, shiyasa itama yanzu bata da lokacin kanta ko yaushe tana wajen aiki, ita da kanta take tuƙa mota ɗaya daga cikin motocin Uncle Hashim ɗin, tunda shi ba ya hawa any time yana wajen aikin sa
Har yanzu kuma Umar Faruk yana bibiyan ta but bata taɓa ɗaukan wayan sa ba. Sai dai a ko yaushe idan yayi mata text tana buɗe wa ta karanta, har idan be mata ba tana jin babu daɗi, ta saba yanzu da kalaman sa shiyasa duk sanda bata ga text ɗin ba a ranan kuwa tana rasa sukunin ta ne, ta kasa gane kanta a game da shi tunda ta kasa yarda son shi take yi, wani ɓangare na zuciyar ta tana burin ace a koda yaushe ta kasance da shi but bata san meyasa ta kasa amincewa da soyayyar sa ba, shiyasa duk sanda tayi kamar zata amsa Calls ɗin sa ko kuma ta mayar masa da reply sai ta tuna yana da aure, hakan ke sawa take jin wani irin tuƙuƙi da baƙin ciki wanda har sai ta ji tamkar ta kira sa tayi masa gargaɗin, "ya rabu da ita." But ba ta iyawa.
Time ɗin da suka yi Seven weeks da zuwan su ne sai ga shi ya dira a gidan. A lokacin ita tana wajen aikinta sai dawowa tayi ta ganshi kwatsam.
💎💎💎
*MEEMA FAROUK*
💎💎💎
*NA_NAFISA ISMA'IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏻
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._
*NO_39*
Shigowar MEEMA falon babu inda idanun ta suka faɗa face cikin na Umar Farouk, hakan yasa ta kasa ci gaba da takowa illa kallon sa da take yi ta kasa ko ƙyafta idanu, mamakin ganin sa ne ya bayyana a kan fuskar ta
Yanda shima ya tsare ta da ido ya gaza ko kaudawa. Yana riƙe da Glass cup a hannun sa wanda Jalila ta zuba masa Holandia yana sha. Sanye yake da fararen kaya kamar yanda ya zame masa ɗabi'a, gezna ce me tsananin tsada wanda kana kallo zaka san ba ƙaramin kuɗi ne da ita ba, kansa ya murza hula wanda yayi dai-dai da kalan aikin kayan nasa, sai farin eyeglasses medical da ya saka wanda ya ƙara fito da ainihin kamalan sa da kwarjinin sa tare da haiban sa, kana kallon sa ka ga mutum me tsananin kamala, har wani ƙiba ya sake yi ya yi kumatu
Abin da MEEMA kenan ta hango daga gare shi
Yayinda shima ya hango sauyi sosai a wajen ta, duk da bata yi ƙiba ba but ta sake murmurewa sosai, sai haske da ta sake yi yayinda kyakykyawar fuskarta ta sake fayau da ita
A hankali ta taka ta soma tahowa cikin falon saboda gajiya da tayi da tsayuwar, tuni ta ɗauke kanta daga kallon shi zuciyar ta na sake bugawa da sauri-sauri a kuma wani yanayi
Kasancewar gidan babu kowa sai Jalilan, domin shi Uncle Hashim ɗin yana wajen aiki, while Habeeb kuma yana school be dawo ba
Fitowar Jalila daga kichen da hango MEEMAN yasa ta saki fara'a tana cewa, "MEEMA are you back?"
Kallon ta tayi sai ta gyaɗa mata kai
"Ok. Your guest has come. He's been waiting for you to come." Tafaɗa da fara'a
Ita kuma ta kasa yin magana illa sauke kai da tayi ƙasa
While shi kuma yana kallon ta har yanzu sai dai be ce komi ba
Ganin haka yasa Jalilan tace mata, "She went to the bathroom and got ready and came out to greeting."
Hakan yasa ta wuce da sassarfa ta shige ɗakin ta
Sai a lokacin ya lumshe idanun sa yana buɗe wa tare da ajiye ɓoyayyen ajiyan zuciya
Inda ita kuma Jalila zama tayi a wajen suna taɓa hira. Daga ƙarshe sai ta tashi ta wuce kichen tunda girki ta ɗaura saboda shi, dawowar ta kenan daga aiki ya zo ga shi babu komi a gidan, dole ta tashi da sauri ta ɗaura girki.
MEEMA wacce ta shige ɗaki ta kasa aiwatar da komi illa zama da tayi ta tsirawa waje ɗaya idanu, duk ta rasa sukunin ta jikin ta gaba ɗaya babu ƙwari, sai da ta ɗau lokaci a haka kafin ta tashi ta soma rage kayan jikin ta, Toilet ta shiga tayi wanka ta shirya cikin riga da wando, pink color ɗin wando burgujeje daga sama har ƙasa, sai farar riga Robber me dogon hannu wanda tayi talking ta cikin wandon, kasancewar wandon Robber ne ya kama mata ƙugu ɓam, bata saka komi ba a fuskar ta ba illa veil da ta sanya tayi Rolling a kanta light pink
Jalila ce ta shigo ɗakin saboda jin ta shiru da tayi bata fito ba, don a lokacin har ta gama girki ta zuba mishi yana ci. Shigowar ta yasa tace mata, "She came out and left him waiting for her."
Ɓata fuska ita kuma tayi da cewa, "So what's going on from me? I think there is no connection between us."
"Don't say that MEEMA, this man loves you so much, he came from somewhere to you why would you do that to him?" Cewar Jalila da ta riƙe mata hannu
"Aunty he didn't come for me, he come to Uncle." Tafaɗa tana tura baki
"No, he didn't tell me that, he came to you, but please accept him with open arms. Let's go." Ta ja ta suka fice. Har kujeran kusa da shi ta kai MEEMAN ta zaunar da ita sannan ta kalli Umar Faruk ɗin tana murmushi tace, "Ni bari in shiga ciki."
"Ok." Yafaɗa shima yana yalwata fuskar sa da murmushin. A lokacin har ya tsakura abincin ma ya gama
Tafiya tayi ta bar su ta shiga ɗaki
Shi kuma sai ya mayar da kallon sa kan MEEMA wacce ta haɗe hannayen ta waje ɗaya ta ɗaura su a saman gwiwowin ƙafafuwan ta, fuskar ta na kallon gefe ta wani haɗe rai tare da turɓune fuska. Sosai tayi masa kyau a shigan nata wanda har ya kasa ɗauke kai a kanta, tasbihi kawai yake yi a cikin ransa. Ya ɗau seconni yana kallon ta kafin ya ja numfashi da faɗin, "You Are not happy for my coming?"
Ɗago manyan idanun ta tayi ta zuba su a kansa, sai dai bata ce komi ba ta sake ɗauke kai
Sai yace, "Did I offend you MEEMA? Tell me what I did to you, I followed you to let me know what I did to you, why don't you pick up my phone when I call?"
Shiru tayi tana mirza yatsun ta
"Zulaiha."
Jin yanda ya kira sunan ta ne yasa ta sake ɗaga kai a karo na biyu ta kalle sa. A wannan lokacin bata iya kawar da kanta ba domin tayi ƙoƙarin ganin ta kalle sa sosai kamar yanda ta arawa kanta jarumta, shiyasa take bin shi da kallo ba tare da walwala a fuskar ta ba
Hakan yasa shi kuma jikin sa yayi sanyi, sai yace, "You don't like me? Tell me please why don't you love me?"
Lumshe idanu tayi ta buɗe, abun da take ji a zuciyar ta yana sake ƙuntata mata zuciya hakan yasa ta kasa yin magana, kuma ba ta jin zata iya yin magana ɗin, shiyasa ta ɗauke kai kawai, sosai zuciyar ta ke shiga ƙunci duk sa'ilin da ta tuna yana da wata mata, ta kan ji kamar ta amshi soyayyar shi sai dai hakan ke hana ta ba shi amsa, baza ta iya cewa ba ta ƙaunar sa ba sannan baza ta iya cewa ta amince da shi ba
Umar Faruk wanda ya gaji da shirun nata wanda har ya ji zuciyar sa tayi masa zafi. Shiyasa ya kalle ta yace, "You can go."
Jin abun da yace sai ta sake kallon sa. Yanda ya kawar da kansa yasa ta ɗan tsira mishi ido, bata ce komi ba kuma ta tashi ta wuce ɗaki
Shi kuma da kallo ya bi ta har ta shige, sai ya ja numfashi yana jin zuciyar sa na sake zafi, hannun sa yasa a fuskar sa yana mayar da ajiyan zuciya a hankali, shi mutum ne mara son damuwa abu kaɗan ke ɗaga masa hankali. Daƙyar ya iya daurewa ya ɓoye halin da yake ciki. Koda Jalila ta fito sai yayi mata sallama a kan, "zai wuce, zai wuce ta wajen Uncle Hashim sai su gaisa daga can".
Ita kanta MEEMA ta san bata kyauta mishi ba, but bata san meyasa ba ta ƙaunar buɗe baki a gaban sa tayi magana ba, duk dai tana kishi ne saboda auren shi shiyasa ta gummaci tayi banza da shi, amma kuma zuwan da yayi har ya tafi da yanda ta nuna masa ya tsaya mata a rai, shiyasa ta kasa sukuni, walwalan ta gaba ɗaya ta rasa a ranan. Har dare yayi tana jiran text ɗin sa but babu, shiyasa can tsakar dare da zuciyarta ta kasa sukuni haka ta tashi ta ɗauki wayan ta, ta jima tana tunanin abin da zata aiwatar daga ƙarshe kawai ta bi umarnin zuciyar ta. Text message ta tura masa na gaisuwa da kuma komawar sa gida lafiya. Daga ƙarshe sai ta kashe wayan ta kwanta tana ƙanƙame pilow, daƙyar barci ya sure ta a wannan daren saboda a halin da take ciki.
✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️
*AFTER SIX MONTHS*
Abubuwa da dama sun faru a cikin waɗannan watannin, ciki kuwa har da nasaran da Umar Faruk yayi a kan MEEMA, a yanzu haka ta amshi soyayyar sa inda suke gudanar da ƙaunar junan su kamar zasu cinye juna
Da taimakon Uncle Hashim da ya jajirce wajen nuna mata dacewar su da yanda yake nuna mata muhimmancin Umar Faruk a rayuwar ta, hakan yasa har yayi galaba a kanta
Yanzu ta rigada ta sallama zuciyar ta a kanshi, tana ganin shi ne zai zamo Abokin rayuwar ta, shi ta zaɓa ya zame mata farin cikin rayuwa, tana matuƙar son shi yanzu wanda ko kwatankwacin sa bata yiwa Ishaq ba, don tuni yanzu ta haƙura da Ishaq tunda Uncle Hashim ya sanar mata, "bazai taɓa biyo ta nan ba".
Yanzu haka Ummee ta samu mijin aure har an tsayar da rana. Wani hamshaƙin me kuɗi ta samu a nan Kaduna, sai dai yana aiki a can Zaria ne shiyasa a can zasu zauna da ita, but uwar ƴaƴan shi kuma tana Kaduna ne
Yanzu haka saura kwana uku bikin shiyasa MEEMA da Jalila da Habeeb suka shirya suka wuce Kaduna
Kasancewar shi Uncle Hashim yana Legos a halin yanzu wajen aiki, kusan two weeks yayi a can sai ranar ɗaurin auren zai leƙo.
Sun isa Kaduna da magriba, su Hajiya sun yi murna da ganin su musamman ma MEEMA wacce dama tunda ta tafi bata taɓa zuwa ba sai yau.
Washe gari sai ga Laɗifa ta zo gidan. Lokacin ma MEEMA na barci sai ita ne ta tashe ta, suka rungume juna cike da farin ciki a fuskar su
Laɗifa tace, "I'm glad to meet you again. I'm missing you. You left us."
Murmushi ita kuma tayi tace, "No, I'm not leaving you. You're in my heart, and we're making a phone call."
"But I want you to come back and live here. I'd rather enjoy that."
"Ok zan dawo idan kina so." Tayi maganar a cikin gwarancin Hausan ta wanda har yanzu ya kasa kama bakin ta
Waro ido Laɗifa tayi cike da farin ciki tace, "oh my MEEMA kin iya Hausa? Wow I'm happy wlh."
Dariya ita kuma tayi wanda ba kasafai take yin shi ba, sosai kuwa ya yiwa fuskar ta kyau matuƙa, hannayen ta ta riƙe tana kallon ta tace, "I am learning with my Aunt, but Hausa akwai wahala." Ta ƙare maganar tana ɓata fuska
Laɗifa dake dariya tace, "kuma tayi miki kyau wlh, but zamu sha dariya fa, wannan Hausa sai kace kina larabci, bari in kira Idris muji Idan Yana Kira."
Murmushi tayi kawai don ba wai duka maganar nata ta gama gane wa ba, har yanzu hausa wahala yake bata sosai, idan ta iya wani abun kuma sai tazo koyan wani sai ta manta wancan, shiyasa a kullum ƙorafin ta wajen Jalila, "Hausa da wahala."
Bayan Laɗifan ta gama wayan ta kalle ta tace, "Should we go to their house because it's there."
Shiru tayi sai kuma ta ɗaga kafaɗan ta da faɗin, "why not."
Daga nan sai ta tashi ta shiga wanka ta fito ta shirya
Ita kuma Laɗifan tuni ta fice Parlour wajen su Hajiya
Bayan ta gama shiryawa cikin bak'ar material ɗinkin riga da skert, an yi zanen flowers da Orange color, ya ɗauki skin ɗin ta sosai kayan ya sake mata kyau ainun, bata saka ɗan kwali ba sai ta tufke gashin ta a ƙeya, sannan sai ta saka siririn farin gyale me kwalliyan Stones ɗan ƙarami, iyakan kanta ya rufe mata ya sauka a kafaɗan ta, flet shoes ta saka fari da agogon hannun ta ma fari, sai ta ɗauki wayan ta ta fito. A falo ta tarar da su. wajen Hajiya ta nufa ta rungume ta tana sakar mata peak a kumatu, kana tace, "good morning my grandma."
Sai da ta shafo fuskar ta kafin ta amsa ta cike da fara'a
Daga nan suka gaisa da Zabba'u wacce dama su biyu ne a parlour'n sai Laɗifa da ke zaune
"Grandma we will go to their house Idris."
"But you didn't do Breakfast?"
Shafa cikin ta tayi da faɗin, "I'm not hungry."
"No, you can't go out without breakfast. Go and do whatever."
Hakan yasa ta wuce kan dainning ɗin ba tare da ta sake cewa uffan ba
Zabba'u tace, "ke ma Laɗifa kin ƙi cin komi haka ake yi?"
Murmushi tayi da faɗin, "Baaba ba na jin yunwa wlh, sai da na cika ciki na kafin na fito".
Daga nan hiran su suka ci gaba da yi inda ita Laɗifan ta tashi ta wuce wajen MEEMA da ke kan dainning
Bayan ta gama suka fita tare suka yi gidan su Idris. A can suka wuni har da Idris ɗin tunda yana gida, daga ƙarshe ma sai suka fice gaba ɗayan su wai zasu je zaga gari. Idris ne me tuƙin. Bayan sun gama yawon sai suka dira kuma a gidan su Laɗifa
Suna can ne Umar Faruk ya kira MEEMA yana tambayar ta, "inda take zai zo wajen ta?"
Shi ne tayi masa kwatancen inda take
Yace, "ga shi nan".
✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️
A fannin Luwaira har yanzu bata san yana tare da MEEMA ba, duk a tunanin ta yanzu ba sa tare, ta kwantar da hankalin ta yanzu gaba ɗaya ta cire wata MEEMA a rai tunda tana samun kulawa ɗari bisa ɗari a wajen sa, ba ta rasa komi abun da take buƙata. Umar Farouk mutum ne shi wanda ya iya soyayya ko kaɗan ba ya tauye mata haƙƙin ta a matsayin ta na matar sa, dai-dai gwargwado yana bata farin ciki da ƙarfin iyawan sa, shima yana jin daɗin zama da ita tunda tana ƙaunar sa sannan tana nunawa yaran sa ƙauna, abun da ya fi so kenan ya ga an damu da yaran sa
Har Momy itama tayi tunanin ya rabu da zancen MEEMA tunda be sake tayar da maganar ba. Abun da ke damun ta yanzu shi ne rashin samun cikin Luwaira har yanzu shiru ko ɓatan wata bata taɓa yi ba
Bata san cewa ita Luwairan magani take sha ba don hana ɗaukan ciki, a bisa shawaran Abida wacce ta sanar mata da komi kasancewar yanzu babu ɓoye-ɓoye a tsakanin su, ita ta bata shawaran, "kar ta sake tace zata ɗauki ciki, muddin ta ɗauka kuwa su Momy zasu cika burin su a kan Umar Faruk, zata rasa shi a nan gaba, sabida idan ta haifu su kuma a nan ne zasu aiwatar da ƙudirin su a kansa, idan kuma bata haihu ba zasu yi ta jelan jira har sanda zata samu ciki ta haihu kafin su kashe sa."
Ita kuma Luwaira ba ta son a raba ta da mijin ta, ƙaunar da take mishi baza ta bari tana ji tana gani Mahaifiyarta ta aiwatar da abun da take so ba, shiyasa taga ya dace ta bi wannan hanyar. A halin yanzu har ta gama karatun ta kasancewar dama suna zangon ƙarshe ne. Ta mayar da hankalin ta yanzu kan mijin ta tana kyautata mishi da iyawan ta domin kawai ta ga ta sake shiga zuciyar sa ainun.
Inda shi kuma Umar Faruk ɗin ya jingirta da auren MEEMA ne ba don komi ba sai don ganin auren su da Luwaira be wani daɗe ba, idan har yace zai taso da maganar auren su da wani idon zai kalli Momy? Ace yana auren ɗiyar ta sannan ko shekara bata rufa ba yazo musu da zancen sake aure, shiyasa ya bari zuwa nan da kamar sun yi shekara ɗaya sai ya taso zancen
Duk da Uncle Hashim yana ta faɗa masa, "gwara ayi a huta hakan zai fi."
But yanzu sun yanke shawaran nan da one month zai tura a nema masa auren ta, tunda zancen auren Ummee ya taso shiyasa suka ce a bari zuwa an yi nata ya wuce
Itama MEEMAN ta amince tunda ta ƙosa ta aure shi, a yanda take ji yanzu ba ta ƙaunar ko sati ne ta ƙara a gida, ƙaunar da take mishi ya rigada ya tabaibaye ta wanda tana jin baza ta iya rayuwa babu shi ba, shi kaɗai yanzu take kallo a zuciyar ta. Babu wani saurayi ko namjin da ke burge ta sama da shi. Soyayya me tsafta sosai suke gudanar wa wanda burin ko wannen su yaga ya mallaki ɗan uwan sa.
_Mu je zuwa. Yanzu za'a fara._
💎💎💎
*MEEMA FAROUK*
💎💎💎
*NA_NAFISA ISMA'IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏻
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._
*NO_40*
A tsanake yake shirin sa duk da yana sauri ne, ya shirya a cikin shadda gezna maroon color me tsada sosai, sai yayi using da Black shoes and wrist watch, ya saka ƙuben hula da ya dace da aikin kayan sa, yanda ya kofa hulan ne yasa ake iya hango kwantaccen baƙin gashin kansa daga ƙeya, ta zauna masa hulan ɗass ta sake fito da ainihin kamalan sa da tsantsan kwarjinin da Allah ya ba shi, sai ya saka eyeglasses medical sannan ya feshe jikin sa da turarukan sa masu shegen ƙamshi da saka zuciya natsuwa. Ya kalli kansa a madubi sai ya saki murmushin sa me kyau yana sake shafa kyakykyawar fuskar sa. Wayoyin sa ya kwasa ya zuba a cikin aljihun rigan sa kana ya ɗauki keeys ɗin mota ya fice
Luwaira wacce ke zaune a katafaren parlour'n ƙasa ita da su Yusra suna kallo, ta ci kwalliya a cikin ƙananan kaya fuskar nan ta sha kwalliya tana ta faman taunan chewing gum, jefi-jefi take sauraron Yusra wacce take mata surutu gaba ɗaya ta ishe ta; tana sauraron ta ne kawai ba don tana so ba. Tunda Umar Faruk ya doso Steps ɗin ƙamshin turaren sa yayi mata maraba a cikin hanci, shiyasa ta lumshe idanuwanta tana ƙara zuƙo shi sosai tare da buɗa hancin. A take ta buɗe idanun nata ta sauke a kansa
A lokacin ya rigada ya sauko daga Steps ɗin idanun sa shima a kanta, yayinda fuskar nan tasa me kamala take fitar da annuri kamar yadda ta saba. "My babies." Yafaɗa sanda ya isa wajen idanun sa a yanzu a kan yaran nasa
Da gudu Yusra ta soma tashi ta nufe sa tana kiran sunan sa
Itama sai Hafsan ta tashi ta nufe sa duk ya rungume su
Luwaira wacce ta kasa motsi sai a lokacin ne ta miƙe zuciyar ta cike da bege gami da ƙaunar sa itama ta ƙarisa wajen sa. Cikin murmushi tace, "ranka ya daɗe sai ina kuma?"
Murmushi yayi mata yace, "zan fita ne akwai inda zan je. But har yanzu lessing teacher ɗin su be zo bane?"
"Eh be zo ba. Amma na san maybe zai zo tunda yanzu 4 tayi."
Numfashi ya ja kana ya kalli yaran yace, "ok babies ku sake Ni zan tafi, me kuke so in siyo muku?"
Nan ko waccen su ta soma sanar mishi da abin da take so
Shi kuma murmushi yayi yana shafa kansu, sai kuma ya mayar da idanun sa a kan Luwaira wacce itama fuskar ta yalwace take da murmushin. yace, "ke fa baki faɗa min abin da kike so ba? Ko kar in siyo miki komi?"
Still murmushi tayi tana ɗan kawar da kai, cikin kunya tace, "nima ka siyo min abin da suke so saboda bani da zaɓi".
"To shikenan. Take care, bari in wuce." Daga haka ya bi yaran ya sakar musu peak a kumatu su ma suka yi masa. Har ya juya zai tafi kuma sai ya jiyo ga Luwairan yana kallon ta
Yanda ya zuba mata fararen idanunsa ne yasa ta ɗauke nata idanun
"Ke baza kiyi min naki kiss ɗin bane?" Yayi maganar a hankali
Murmushi tayi tana kallon su Yusra waɗanda suka zuba musu idanu
"Oya Common." Yayi maganar yana riƙe mata hannun ta tare da jawo ta jikinsa suka haɗe
Hakan yasa ta ɗago kai cike da kunya tayi mishi kiss ɗin a kumatu
Shafa wajen yayi kawai ya sakar mata smile sannan yayi mata nashi a goshi ya sake ta ya juya ya fice coz a ƙage yake ya fice
Ita kuma tabi bayan sa da kallo cike da zallan farin ciki da ƙaunar sa. Sai da ta gama tsayuwar ta a wajen kafin ta juya zuwa ɗakin ta
Su kuwa su Yusra tuni sun wuce kan kujera sun zauna sun mayar da hankalin su a kan kallon su.
*********
Fitan Umar Faruk Part ɗin Momy ya je ya gaishe ta sannan ya wuce compound ɗin gidan. Koda securities ɗin sa suka nemi bin sa dakatar da su yayi, ya shiga ɗaya daga cikin motan nasa wanda ta kasance fara ce ya bar gidan. Sai da ya tsaya a masjid ɗin kan layin yayi Sallah. Kai tsaye sai ya wuce address ɗin gidan su Laɗifa. Yana zuwa bakin ƙofan gidan su bayan yayi parcking sai ya ɗauki wayan sa ya kira Numban MEEMA
Kamar mintuna goma da tsayuwar sa sai gasu sun fito ita da Laɗifan, kasancewar shi Idris tuni ya tafi tunda MEEMAN ta faɗa masa, "za'a zo a ɗauke ta." Sai da ya gama mata tsiya da tsokanar ta kafin ya wuce a cewar sa, "yana da wurin zuwa dama".
Umar Faruk wanda ke cikin mota idanun sa ƙyar a kan MEEMA, har suka iso wajen yana kallon ta, sai da ya lumshe idanun sa ya ya wani ja gauron numfashi kafin ya saka hannu ya buɗe ƙofar motan ya fito still idanun sa a kan MEEMA yayinda fuskar sa ke fitar da annuri
Laɗifa ita ta fara gaishe shi cikin girmamawa
Ya amsa ta yana murmushi da cewa, "kina lafiya?"
"Lfy kalau Sir."
Still murmushi yayi da cewa, "baza ki fasa kira na da Sir ɗin nan ba? Da alamu kina so muyi faɗa ko? Heartbeat you are listening her?" Ya ƙare maganar yana mayar da idanun sa kan MEEMA tare da sakar mata wani irin kallo wanda yasa ta kawar da kanta tana kaɗa manyan idanuwan ta
Dariya ita kuma Laɗifa tayi ba tare da tace komi ba
"Ok tunda baza tayi magana ba, mu zamu tafi. Ki gaishe min da mutanen gidan idan kin shiga." Sai ya saka hannu cikin aljihun rigan sa, ya ɗan laluba kuma sai ya buɗe motan da cewa, "wait kar ki tafi." Yayi maganar saboda ganin Laɗifan tana yiwa MEEMA sallama zata wuce. Motan ya koma ya ɗauko bandir ɗin ƴan dubu-dubu da shi kansa be san nawa bane, ya miƙa mata yana cewa, "ga shi ko sai ki siya kayan kwalliya."
Hannu ta saka ta amsa tana masa godiya
Yace, "a'a babu godiya tsakanin mu Laɗifa. Kuyi sallama ina mota." Sannan ya shige cikin motan
Laɗifa hannun MEEMA ta kama tana kallon ta da murmushi tace, "Ni bari in shiga ciki in barki da masoyin ki, until we make a phone call."
Gyaɗa mata kai tayi ba tare da ta furta komi ba. Sannan suka zaga tare Laɗifan ta buɗe mata ƙofan ta shiga ta rufe mata tana ɗaga musu hannu. Sai da motan ta tafi kafin itama ta shige cikin gidan su
Umar Farouk wanda ke murza motan a hankali ya juyo yana kallon ta da cewa, "heartbeat are you quiet or is something bothering you?"
Girgiza kanta tayi sai kuma ta juyo tana kallon sa itama. Murmushi ta sakar masa da cewa, "Nothing's bothering me."
"Ok now. Where are we going?"
Ɗan kawar da idanun ta tayi tana juya su da turo baki gaba, "We are going home."
"No, there's a place for me to go. I'm waiting for that day."
"Where are we going?" She said looked at him
Murmushi yayi mata yace, "ki bari idan mun je zaki gani, I'm going to surprise you."
Kanta kawai ta ajiye a jikin kujeran ba tare da ta furta komi ba
Sai ya kira sunan ta da cewa, "heartbeat ko ba kya so?"
Idanunta ta zuba mishi, sai ta sakar mishi murmushin ta me kyau tana kaɗa manyan idanun ta tace, "whatever you want I want, or I say let's go and follow you."
Lumshe idanun shi yayi yana buɗe wa tare da sake tamke sitiyarin motan. Cikin amon muryan sa me sanyi yace, "If you look at me like that, you're making me lose my temper heartbeat."
Dariya tayi wanda yasa dumples ɗin ta suka bayyana
"I love You! I love You so Much my heartbeat!" Yayi maganar yana sake kallon cikin idanun ta cikin narkewar soyayyarta
Ita kuma ta kasa jure kallon nasa shiyasa ta ɗauke kai zuwa kan titi tana zuba murmushi wanda ke bayyana tsantsan farin cikin da take ciki
Shi kuma numfashi ya ja kawai yana ci gaba da tuƙin sa, inda idanun sa shima ke kan titi, but jefi-jefi yake waigo da idanun sa gare ta yana sakar mata murmushi. Can kuma sai yace, "heartbeat I long to get married, buri na a yanzu kawai in mallake ki in huta da zuciyata."
Ɗan kallon sa tayi kafin ta ɗauke kai tace, "I don't understand. What happened to your heart?"
"Oh you don't know?" Yayi maganar still yana ware idanu a kanta
Tura baki tayi da faɗin, "Yes I don't know."
"Ok soyayyar ki take wahalar da Ni a zuciya ta." Sai ya kama setting zuciyar sa da cewa, "I feel like I'm going to die because of your love, MEEMA I'm not tired of expressing to you how much I love you, i love You with all my heart!"
Cike da farin ciki take kallon sa. Cikin so da ƙauna ta langaɓe kanta tana sake narke idanu tace, "me too love! I love you so much in my heart, I love you so much and so much!"
"Kar ki saka in Yi hatsari Heartbeat ki rage min irin Wannan kallon."
Kasancewar bata fahimci inda ya dosa ba sai ta ware idanunta sosai a kansa da cewa, "whattt..?"
"I mean the look on your face will make me take an accident, stop kinga I'm driving."
Murmushi tayi kawai tana sauke kai gefe.
Wani wajen shaƙatawa ya wuce da su inda masoya da ƴaƴan masu kuɗi suke zuwa wajen, wajen na manyan Mutane ne sosai don ba a samun ƙananun talakawa a wajen. Parcking yayi a haraban wajen kafin ya ɗauki wayan sa ya soma dealing number
MEEMA wacce take kallon sa lumshe idanuwan ta kawai tayi tana sake realising a kan kujeran da take
Shima kallon ta yake yi but a lokacin ya ɗaura waya a kunnen sa yana magana. Zuwa can kuma ya cire wayan yana tsare ta da idanu, cikin murmushin sa da ke masa kyau matuƙa ya kirayi sunan ta
Hakan yasa ta buɗe manyan idanun ta a kanshi, sai itama ta sakar masa murmushi tana sake ɗauke kai saboda yanda take ji a jikin ta da kallon nasa
"Don't get tired. Give me some time. There's someone I'm waiting for."
Kanta ta jinjina kawai tana ɗan sakin numfashi
Shi kuma sai ya saka hannu ya buɗe motan ya zura ƙafafuwan sa a waje, wayan sa a hannu yana duba wa sai kuma ya fice hango wani receptionist ya taho wurin
Koda ya ƙariso cikin girmamawa ya soma gaishe shi domin alamu ya nuna sun san juna
Dayake shi Umar Faruk yana yawan ziyartan wajen domin wajen zuwan sa ne, musamman idan yana buƙatar keɓewa. Bayan sun gaisa magana suka yi kafin shi ya juya shi kuma ya shiga cikin motan. Sai yace, "heartbeat."
"Uhm." Tafaɗa tana buɗe idanu tare da zuba masa su
"Are you tired?"
Murmushi tayi kafin ta girgiza masa kai, sai kuma tace, "But what are we going to do here?"
"Surprised. I'll let you know." Yayi maganar yana mata murmushi. Sai kuma wayan sa ta soma Ring, hakan yasa ya ɗauka yana karawa a kunne, "ok". Kaɗai ya furta kana ya cire wayan yana kallon ta. "Let's go."
Murmushi tayi kana ta saka hannu ta buɗe motan ta fita
Shima fitan yayi yana gyarawa eyeglasses ɗin sa zama, sai ya rufe motan kana suka taka a tare zuwa ciki. Kai tsaye wani rumfa suka nufa inda babu kowa a wajen don sun wuce Mutanen da ke can haraban wajen tsilli-tsilli
Yanda suke tafiya zaka san cewa tabbas lover's couple ne, domin ba ƙaramin dacewa suka yi da juna ba, a hankali suke takawa har sanda suka isa rumfar, inda wajen an ƙawata shi da fitilu masu haske kala-kala, yayinda table ɗaya kuma aka fi ƙawata shi da flowers, ga kuma expensive drinks duk an cika table ɗin
"Bismillah." Yafaɗa yana mata wani kallo me shiga rai fuskar sa yalwace da fara'a
Ita kuwa tsaban farin cikin ganin wajen yanda ya burge ta har buɗe baki take yi, kallon sa take yi ba tare da ta furta komai ba
Sai ya gyaɗa mata kai yana sake nuna mata da hannayen sa yace, "sit Please."
Zama tayi tana mayar da idanun ta a kan table ɗin
Sai shima ya zauna idanun sa a kanta yace, "Are you happy to see the place? I hope you are enjoying?"
Kanta ta gyaɗa masa sai tace, "na'am, I'm happy Love, But why did you prepare this for me?"
"I'm telling you it's because you're happy. I want to be alone in such a place. I'm impressed."
"Me too." Tafaɗa cikin farin ciki
Kallon ta kawai yake yi yana murmushi, kana kuma ya saka hannu ya ɗauki Cup ɗaya da ke kife a cikin ƙaramin Glass plate tare da ɗaukan ɗaya daga cikin drinks ɗin wanda ke a cikin wani irin dogon kwalba, ya tsiyaya a Cup ɗin kafin ya sake ɗaukar wani ya zuba, sai ya miƙa mata yana kashe mata idanu tare da murmushi yace, "take."
Farin hannun ta ta saka a hankali ta amsa tana kallon sa itama
Shima ɗaukan nashi yayi kana ya matso dashi kusa da nata ya ɗan buga kaɗan before suka kai bakin su a tare. A taren kuma suka cire suna sakar wa juna murmushi, sai da ya ajiye nashi kafin ya gyara zaman sa yana kallon ta da cewa, "heartbeat I have a gift for you."
Ɗan waro ido waje tayi still har yanzu fuskar ta yalwace da fara'a, sai kuma ta ɗan saki murmushi tana tokare haɓan ta da hannayen ta biyu da ta dunƙule, ta zuba masa idanu tana wani narke su cike da ƙaunar sa tace, "Will you give me a gift?"
"Yes, but close your eyes."
"Ok." Tafaɗa tana murmushi, sai kuma ta rufe idanuwan ba tare da ta cire hannayen ta daga haɓar nata ba
"Ok open." Yafaɗa sanda ya gama zaro wani ɗan ƙaramin kit na Ring ya ciro shi
Ware idanun ta tayi a kansa sai kuma tabi Ring ɗin da kallo, ta kasa yin magana illa kallon sa da take yi
Sai ya sakar mata murmushi tare da cewa, "Bring your hand and I will put it on you."
Hannun damar ta ta miƙa masa. Sai ya zira mata farin zoben wanda ya kasance na gold ne, a ɗan ƙaramin yatsanta ya zira mata kasancewar ɗan siriri ne me kwalliya a saman, sai ka kula sosai zaka hangi haruffan sunan su a jiki an saka *U&Z*
Janye hannun ta tayi ta kai dai-dai fuskar ta tana ƙarewa zoben kallo, a nan ne itama ta kula da harufan da ke cikin zoben, shiyasa ta furta, "woww!" Tana washe ƙananun haƙoran ta wanda dumples ɗin ta suka samu damar fito wa sosai da sosai suka sake ƙawata kyakykyawar fuskar nata
Shi kuwa murmushi kaɗai yake zuba wa yana sake tsare ta da idanu domin ba ƙaramin kyau ta sake masa ba a yanzu ɗin, soyayyar ta ne ke ƙara huda jinin jikin sa tana yawo a duk gaɓoɓin sa da ke aiki. "I hope he impresses you and does it for you?" He speaks still smiling
Kasa magana tayi illa kallon sa da take yi, sai kuma ta langaɓe kai kamar zata yi kuka tana sake narke murya da cewa, "I'm so happy with this gift of yours for Me. I can't tell you how I feel in my heart! I love the Ring so much, thank you Love."
Yanda idanun ta ke ƙyalli hakan ya gane hawaye ne a cikin idanun ta. Sai ya lumshe idanu yana sake buɗe wa a kanta yace, "Are you going to cry?"
Ware ido tayi sai ga hawayen sun soma ɗiga a kuncin ta, "I'm very happy! I can't describe to you how I feel Love, I love you so much!"
"Let's have some drinks and go. Don't let Hajiya hear you shut up." Yayi maganar sabida ya ɗauke mata hankali don ba ya son ganin hawayen nata, yanzu ba lokacin su bane lokacin farin ciki ne
Hakan yasa ta ɗauki Cup ɗin tana kaiwa bakin ta, sai dai idanun ta a kansa suke ta kasa ɗauke wa
Yanda suke sakar wa junan su kallo me ma'anoni daban-daban wanda su kaɗai ne suke iya fahimtar a halin da zuciyoyinsu suke ciki.
Sai da suka gama sha sannan suka tashi suka bar wajen. Kai tsaye gida ya mayar da ita, sai da suka ɓata lokaci a waje suna sake soyewa kafin suka rabu, ta shiga gida shi ya ja motan nasa ya bar wajen
Koda ta shiga gidan akwai baƙi sosai, don yawanci ƙawayen Ummee suka zo
Shiyasa tana shigowa Ummee ta soma nuna musu, "ita ce ɗiyar ta."
Hakan yasa suka gaisa suna ta yaba kyawun MEEMAN, sai janta da hira suke yi kowa na haba-haba da ita
Ita dai murmushi kaɗai take musu tana zaune a cikin su don sun hana ta tafiya. Sai daga baya ta samu ta silale ɗaki, a lokacin ne taji shigowar message wanda Umar Faruk ya tura mata na kalaman soyayya, murmushi kaɗai take zubawa tana karantawa, sai da ta gama sai ta mayar da idanunta a kan zoben hannun nata tana kallo still fuskarta ɗauke da murmushi, hannun ta kai bakinta ta sakar wa zoben kiss tana wani lumshe idanuwa, sai kuma ta kwanta tana ƙanƙame pilow still idanuwan ta a rufe, shauƙi da bege gami da soyayya ne ke tsumata wanda har ta kasa taɓuka komi tana nan kwance a wajen, sai kuma daga baya ta tashi zaune ta ɗauki wayan nata ta tura masa message ɗin itama kana ta tashi ta soma rage kayan jikin ta, saka towul tayi ta shiga Toilet tayi wanka ta fito ta sanya doguwar riga na atamfa me ruwan zuma da ratsin baƙi-baƙi da ja, ta yafa siririn gyale a kanta sannan ta fice Parlour tunda akwai sauran time ɗin sallan magriba.
**********
Ranan juma'a dubban jama'a suka shaida ɗaurin auren Ummee ita da mijin ta Alh. Shu'aibu Khabeer. A ranan aka wuce da ita Zaria, daga ƙawayen ta sai Zabba'u suka tafi, su ma a ranan zasu dawo tunda ba kwana zasu yi ba
Hajiya ta so MEEMA taje but ita taƙi, duk da har yanzu ba wai ta saki jikin ta da Ummeen bane amma dai ta sauka daga fushin da take mata sosai, tunda Uncle Hashim yana zaunar da ita yayi ta mata nasiha yana gaya mata girman uwa, ko me Uwa ta aikata wa ƴaƴan ta ba a fushi da ita. Kuma ta gane sosai yanzu sai dai rashin sakin jikin ta da ba ta yi da ita ne.
Koda aka gama bikin MEEMA bata koma Abuja ba sai da tayi sati ɗaya curr a garin, Jalila ce suka koma ita da Uncle Hashim a washe garin bikin. Ranan da zata koma Umar Faruk ya kai ta har can Abujan, sai da yayi kwana biyu a can don dama akwai aikin da ya kai shi
Bayan ya dawo ne ya je wa Momy da zancen auren sa da yake son ƙarawa, duk da be so ya taso da maganar a yanzu ba duba da rashin daɗewar auren sa da Luwaira, to amma ya kasa jurewa ne, fatan sa a yanzu kawai ya mallaki MEEMA ta zama tashi ta har abada, hakan zai saka hankalin sa ya kwanta shiyasa ya kasa jurewa ya sanar mata da zancen
Ita kuma sanda taji maganar hankalin ta ya tashi tunda bata san har yanzu yana da burin auren MEEMA ba. Sai dai ta kasa nuna hakan a fili illa nuna farin cikin ta da jin zancen da tayi a fuskar ta
Shi kansa har kunya ne ta kama shi saboda ganin yanda ta nuna farin cikin ta, sai ya ga tamkar be kyauta mata ba ace yana auren ɗiyar ta ko rufa wata takwas da aure basu yi ba ya kawo wani zancen, amma ya ya iya? Bazai haƙura da auren MEEMA ba, ita ce jinin jikin sa, ita ce farin cikin sa a yanzu, be da buri a yanzu sama da ya mallake ta, da ita yake kwana a koda yaushe, farin cikin sa da walwalan sa yana da nasaba da ita, ita ce cikamakon rayuwar sa a yanzu, be da wani abun bege sama da ita, ita kaɗai ce zata zamo cikon rayuwar sa kuma cikon farin cikin sa. Ya ji daɗin yanda Momy ta nuna damuwa da farin ciki da abinda yake so, shiyasa ya ji a zuciyar sa be da wata Uwa bayan ita, ya ƙara ganin girmanta sosai a zuciya, musamman da ta sanar masa, "a hanzarta a kai gaisuwa gidan su MEEMAN sabida a tsayar da ranan aure". Wannan zancen ya fi komi saka shi farin ciki. Shiyasa koda ya tashi daga wajen ta sai ya wuce Part ɗin sa. Kasancewar yaran sa suna school a lokacin sai Luwaira kaɗai ya gani a parlour, bayan tayi masa sannu da zuwa ya amsa ta cike da fara'a yana zama a gefen ta tare da zame hulan kansa
Ita kuma ta tashi ta kawo mishi ruwa ta zuba masa a glass Cup
Sai kallon ta yake yi a zuciyar sa yana tunanin yanda zata ji idan ya sanar mata zancen ƙara auren sa, shiyasa ya yanke shawaran barin zancen gwara Momy ta sanar mata domin bazai iya ganin damuwa a kan fuskar ta ba. Da ya sha ruwan ɗaukan hulan sa yayi yana miƙe wa tare da cewa, "muje ki haɗa min ruwan ka."
"To." Ta amsa mishi tana bin bayan sa har zuwa ɗakin sa. Ta shiga Toilet ɗin domin haɗa masa ruwan
Shi kuma ya zauna a gefen gado ya ajiye hulan yana zare agogon hannun sa, bayan ya gama ya miƙe ya soma ƙoƙarin cire rigan nasa. Sanda ya gama daga shi sai Singlet da dogon wandon jikin sa
A lokacin ne Luwaira ta fito daga Toilet ɗin ta gama haɗa masa ruwan. Zuwa tayi wajen sa tana kallon sa da cewa, "ranka ya daɗe ko zan taimaka maka?"
Murmushi yayi mata yana ɗan hura iska daga bakin sa, sai ya ɗan gyaɗa mata kai tare da kama hannun ta ɗaya da cewa, "kin dai ƙi sauya min sunan nan ko? Ba na son kina ce min ranka ya daɗe ɗin nan saboda ina jin wani iri. Ki samo suna me daɗi na soyayya ki riƙa faɗa min zan fi jin daɗin hakan."
Murmushi tayi tana ɗan ɗauke idanun ta daga kallon cikin nasa idanun, domin ba ta son kallon cikin idanun nasa saboda yanda suke da matuƙar kwarjini da tada hankalin duk wani me ji da kanshi gami da ƙara saka Mutum shauƙi da tsananin begen shi. Hannun ta ta kai jikin sa tana shirin ɗaga Singlet ɗin nasa da cewa, "to na maida maka Yayana, hakan yayi?"
Shima hannun yasa yana taimaka mata da cewa, "no ban yarda ba, sunan baya ne ba na so, ki sake wani." Yayi maganar a hankali a cikin wani irin yanayi idanun sa na yawo a kan fuskar ta
Bata kalle sa ba duk da ta san itan yake kallo, sai da ta gama cire masa Singlet ɗin tare da ɗaura sa a dantsen hannun ta tana shirin juyawa tace, "to zan canza maka, amma kafin nan ka shiga wankan idan ka fito sai in faɗa maka time ɗin nayi tunani nima."
Hannun ta ya kamo ya dawo da ita gaban shi, yanda ya narke fuska kamar zai haɗiye ta don kallo ya matso da ita sosai ta yanda ta jingina da jikin sa, kana ya mayar da hannun sa ɗaya a ƙugunta yace, "tare zamu shiga, ke zaki yi min wankan ma."
Waro ido tayi tana kallon sa a yanzu ɗin, sai dai bata yi magana ba illa murmushi me cike da kunya da ta saki
"Oya muje kiyi min wankan". Ya sake rungumo ta a jikin sa ta yanda gaba ɗayan ta ta gama manne masa
Bata iya masa musu ba illa bin sa da tayi ganin ya nufi hanyar Toilet ɗin.
Sai da suka yi wankan tare kafin suka fito. Be bar ta ta fice ba sai da ta shirya sa tayi masa komi, a lokacin wayan sa ta fara Ring, sai ya kalle ta yana faman taje suman kanshi yace, "miƙo min waya ta".
Ajiye lotion ɗin dake hannun ta tana ƙoƙarin mutstsika masa a kai tayi, sai ta wuce gaban gadon tana sake gyara towul ɗin da ke ɗaure a jikin ta daga saman ƙirjin ta zuwa ƙasan gwiwowin ta, ɗaukan wayan tayi nan idanun ta suka faɗa kan sunan da ke kan screen ɗin wayan, inda taga an rubuta Heartbeat ɓaro-ɓaro, take a nan kuwa zuciyar ta tayi wani irin sarawa wanda ƙiris ya rage ta yar da wayan, sai kuma ta sake tallabowa tana jin komi na jikin ta ya dena aiki, can kuma sai ta soma rawan hannu sai dai bata yi wata-wata ba ta juya ta nufi inda yake da wayan ta miƙa masa jikin ta a matuƙar sanyaye, yayinda zuciyar ta ke luguden bugawa tana son hana bayyanuwar firgita gami da halin da take ciki
Shi kuwa da ya juya amsar wayan, yana amsa ya kalli screen ɗin wayan, ganin wacce ke kiran ne yasa ya mayar da idanun sa kan Luwaira, sai dai ta kasa bari su haɗa idanu amma hakan be sa ya kasa fahimtar a halin da take ciki ba, barin ma yanda ya ga fuskarta ta nuna, hakan yasa ya dakata daga ɗaukan wayan yayinda wayan ma ta tsinke a time ɗin. Sai wata kiran ta sake shigowa, kallon Luwairan yayi kamar zai yi magana, sai kuma ya tashi a wurin ya nufi gaban gadon sa, sai da ya zauna ya kalle ta daga inda take tsaye ko motsin kirki ta gaza yi kuma ta ƙi kallon sa, "ki je ki shirya na hutashshe ki." Yayi maganar a cikin matuƙar sanyin muryan sa me daɗi
Ɗago kai tayi ta kalle shi zuciyar ta na ƙuna, sai dai a dole tayi ƙoƙarin danne abun da take ji illa gyaɗa masa kai da tayi ta juya ta fice
Sai da ya ga ta datse ƙofan kafin ya saki numfashi da ƙarfi yana yin peacking call ɗin.
Ita kuma kanta tsaye ɗakinta ta ruga aguje tana sakin kuka, bata tsaya a ko ina ba sai a kan gadonta ta faɗa tana ci gaba da kukan sosai, zuciyarta ne ke tafarfasa sabida tuna sunan da ta gani, "to wace ce?" Tambayar da ke kai kawo a ranta kenan wadda ya hana ta sukuni yayinda kishi ke ƙara nunkuwa a zuciyarta. Babu shakka yarinyar da yake so ce ita ce har yanzu take bibiyan rayuwar sa, har yanzu suna tare basu rabu ba wanda ta ɗauka a tunanin ta sun daɗe da rabuwa ne, idan kuwa haka ne bata san inda zata saka ranta ba, muddin aka yi auren nan baza ta iya jurewa ba saboda tsantsan kishin da take ji a ranta, zata iya haukacewa, ada soyayyar da take mishi be kai yanda take ji a yanzu ba, zata iya yin komi domin ta raba shi da koma waye ne, baza ta iya barin shi ya auri Wata ba, hakan na nufin zata ci baya idan har ya auri wacce yake ƙauna? Ita kenan ba ƙaunarta yake yi ba har yanzu? kawai taimakon ta yayi. Yanda zuciyarta take kawo mata wannan hasashen ji take yi kamar zata mutu, har wani kama maƙogwaron ta take yi sabida zafin da take ji. Take kuma ta tashi tana share hawayen nata yayinda wasu suke gudun tseren fitowa daga cikin idanun, inda suka kaɗa suka yi jazur har wani kumbura suka soma yi, "Heartbeat." Tafaɗa a maƙoshi tana jin kamar zata mutu, majina ta ja tana wurga idanunta a cikin ɗakin domin neman wayan ta, can ta hango shi a gaban dressing mirror ɗin ta sai ta tashi da azama ta ɗauko ta dawo ta zauna, wayan ta soma latsawa tana neman Numban Abida, baza ta iya jurewa ba gwara ta kira ta ta sanar mata a halin da take ciki, hakan shi ne kawai maslaha da abinda take ji, ta san ita zata bata shawarar abun da ya dace tayi, domin baza ta taɓa bari Wata ta shigo mata gida ba, Umar Faruk nata ne ita kaɗan ta, babu Wata mahalukiyar da ta isa ta mallake shi bayan ita, baza ta bar hakan ta kasance ba har abada.
_Enjoy your weekend FAN'S._