Daddy ya d'anyi shiru,da alama yana nazarin maganar.
Zahra ta sake cewa "daddy kada ka zarce hukuncin da bazamu ji dad'i ba,kamar yadda yaya Arish ya kawo waccan" ta nuna ilham da hannu,sannan ta cigaba da fad'in "kuma Ashaq ma ya kawo Ayrah ka aura masa yaya Aryaan mai babban laifi ma ai ya kawo mace ka kuma aura masa,daddy shima Asrar ya kawo tashi yana jiran ka zartar.........................."
wani wawan mari taji ya sauka a kuncinta,wanda har sai da ta saki k'ara ta dafe gurin.
Ta d'ago kai ta kalleshi,
"menayi maka?"
Ya d'an ja da baya cikin zafin rai yace "idan kika k'ara jifana da munanan kalami sai ranki yayi mummunan b'aci"
Bilkisu tayi saurin cewa "ai gaskiya ta fad'a babu k'arya a maganart..............."
"rufamin baki sakarai kawai" ta tab'e baki ta kauda kai.
Ya juyo kan zahra ya cigaba da fad'in "ko dan kinga ina k'yaleki akan duk abinda kike,ina sane da abinda kukewa ilham duk k'yaleku nake keda Asrar"
"wallahi dole na fad'i gaskiya"
ya k'ara saka hannu ya dake ta,magana d'aya idan tayi sai ya daketa,haj karima kuwa tayi2, tayi shiru amma taurin kai ya hanata daina maganar.
Da sauri Sumayya ta ajje khalid ta k'araso gurin ta kare Zahra,
"ki matsa ko in had'a har ke"
"dan Allah kayi hak'uri ka k'yaleta"
"ki matsa ki barshi ya kasheni,wallahi yau dole gaskiya tayi halinta,tayaya za'a d'auki tsana a d'aura wa Sumayya,ai an zalunce ta Allah zai saka mata"
Aikuwa ya Fuzgota daga bayan Sumayya yayi ta duka,amma aka rasa wanda zai hana shi,hatta daddy dake zaune ya kasa cewa komai.
Asiya ce ta rugo da gudu ta rungume Zahra "kuna gani zai kasheta,zai kashe min 'yar uwa"
Zahra ta zame jikinta hancinta na fidda jini,yayinda hawaye ke kwarara a idonta,ta mik'e tsaye tace "a yanxu na gwammace ya kasheni Alhamdulillah akan gaskiyata nake,kuma wallahi bazan daina fad'a ba"
Ta dafe kanta dake mata azabar rad'ad'i sannan ta d'ago ta kalli Aryaan dake tsaye kamar bijimin sa tace "na fad'i ka kasheni dan Allah,na fad'a nace ita Sum.............."
bata k'arasa ba ya kai mata naushin da sai da ta fad'i k'asa wanwar...
Asiya ta durk'usa ta rungumeta tana fad'in "babu wanda zai hana shi dukanta a cikinku"
"baza'a hana ba tunda ita bata da kunya gobe ma zata sake in bata da hankali" haj karima ta fad'a rai a b'ace.
A hankali Asrar yake matsowa yana tafa hannu yana fad'in "gaskiya tayi k'aranci a duniya"
Ya kalli daddy yace "daddy duk abinda Zahra ta fad'a gaskiya ne,idan kukayi la'akari da cewar Sumayya bata san waye mijinta ba a lokacin"
Aryaan ya taho gadan2 zai daki Asrar,
Sai a lokacin momma tace "idan ka sake dukan wani a cikinsu Allah ya isa ban yafe maka ba"
"amma kina jin abinda suke fad'a ko?"
"eh ai gaskiya suke fad'a ko ban fad'a maka ba,tun daga ranar da aka kawota gidannan kullum idan kazo sai nace kaji tsoron Allah ka tsare mutuncinta"
Asrar yayi murmushi ya kalli Arish dake tsaye ya dafe kai,yace "kaga kuwa yaya Arish bai kamata ka ga laifin sumayya ba,saboda dalilai kamar haka:-
1-bata san wa aka aura mata ba,kawai an kawota kuma an nuna Aryaan a matsayin mijinta.
2-Kamata yayi lokacin da aka kawota gidannan ace mata ba Aryaan bane mijinta amma karta bari kowa ya sani,tunda saboda daddy aka b'oye abin ba dan komai ba,amma aka b'oye mata wanda kamata yayi ace ta san mijinta.
3-hatta iyayen Sumayya fa,ce masu akayi Aryaan ne mijinta ba Arish ba,dan bata ma san waye Arish ba a lokacin.
4-Shi Aryaan daya sani kamata yayi ace ya jajirce amma shi ya rik'a rinjayarta akan idan bata amince masa ba so take yaje ya nemo matan banza a waje bayan gata matarshi,koda a lokacin ta amince masa wallahi bata da laifi saboda bata sani ba,amma ta kare mutuncinta lokacin data gane kaine mijinta yaya Arish"
Ya goge hawayen idonsa ya cigaba da fad'in "shin bazaku ga laifin d'an uwanku ba sai ita?gaskiya ba'a yi mata adalci ba,zan aure ta kuma zan rik'e ta fiya da yadda kuke zato"
Ya koma gaban daddy yace "daddy ka amsa dan Allah ka amsa ka yarda in aure ta"
Ya d'ago ido ya kalleshi cikin b'acin rai yace "ai ina jiran ku gama hayaniyar da fad'a da doke2 sannan in muku magana,wato dan yanzu ina zama cikinku shiyasa kuka samu damar yin fad'a har a gabana,lokacin daya kamata ace muna farin ciki,amare har biyu aka kawo gidannan amma tun yanzu kun fara nuna halinku"
Fad'a sosai ya rik'ayi ta inda yake shiga bata nan yake fita ba.
Hak'uri sukayi ta bashi,Zahra kuwa bata ce komai ba ita da Arish,dan ita hannunta na rik'e da tissue tana goge hab'on da Aryaan yayi mata.
Sai da suka tabbatar daddy ya huce sannan Asrar ya sake tambayarshi.
"na yarda ka aure ta,Allah tayamu rik'onsu ya baku ikon yin adalci"
"La haula wala quwwata illa billah" abinda Arish ya fad'a kenan tare da zubewa k'asa,A rud'e dukansu suka k'arasa gabanshi,ilham ta tallabo kanshi tana kuka.
Momma ta jijjaga shi sosai taji babu alamar motsi a tare dashi "Alhaji na shiga uku baya motsi fa"
daddy yayi saurin rik'e tsintsiyar hannunshi sannan yayi ajiyar zuciya yace ?"yana da rai"
Aryaan ne yayi saurin kiran family doctor d'insu dan yazo.
_1h later_
Dukkaninsu suna part d'in Arish,idan ka d'auke momma,daddy da Asrar.
Yana kwance an saka masa drip ,idonsa a rufe yana bacci.
Zahra dake jingine da bango ta kafeshi da ido a zuciyarta tana fad'in
_Yaya Arish Allah ya baka lafiya amma na san halin da Sumayya ke ciki yafi naka muni domin ka wulak'antata wulak'anci mafi muni,zamu karb'ar mata 'yancinta koda bazaku cigaba da zama tare ba_...
Ita kuwa sarkin hawaye hannunta na rik'e da nashi sai kuka take,Aryaan kuwa sai zirga2 yake kamar wanda yayi wa sarki laifi.
_gaskiya dole inyi maganin yarinyar nan dan bazata haddasa min tashin hankali ba daga warkewarshi zata sake b'arko mana rigima lallai dole inyi maganin komai_
Ilham ta ayyana a ranta.
Shi kuma Aryaan da sauri ya fita,yayinta Zahra tayi saurin bin bayan shi ba tare daya sani ba.
A k'ofar flat d'in suka ci karo ta Asrar,kallon kallo suka tsaya sunayi da juna kafin Aryaan yace
"babu aure tsakaninku da Sumayya dan kasan babu inda aka tab'ayin *Aure kan Aure*"
Zahra dake lab'e a bayan k'ofa gabanta yayi mummunan fad'uwa,tasa hannu ta rufe bakinta.
Asrar yace "Ashe ka san da haka kai kuma kake son kayi zina da matar aure?"
Murmushi Aryaan yayi sannan yace "kadai je kayi tunani saboda kasan tana da aure"
"tunanin ne ya saka ni yin hakan saboda baka da niyyar fad'in gaskiya"
"oh ashe kana sane kake k'ok'arin jefa kanka a jahannama"
dariya sosai Asrar yayi sannan yace "kai kuma fa?a ina za'a saka ka?kai da kasan gaskiya amma kak'i fad'a"
bai sake cewa komai ba ya wuce.
Zahra ta fito ta kalli Asrar tace "meye abinyi yaya?"
"yana da taurin kai Zahra"
"wannan karin kuwa zai ajje,dan maganar aure za'a fara gadan2"
"okay Allah yasa mu dace"
"Amin yaya".
_3h Later_
Kusan minti biyar yana zaune yana hawaye,ya kasa cewa komai,itama ilham kuka take.
Ya kalli Asiya yace "kirawo min daddy da momma"
Da sauri ta tashi ta fita,tare suka shigo dasu daddy,momma ta kalli ilham tace "ki daina kukan kinji ya isa haka"
Suka zauna gefen gadon "ya akayi Arish"
"momma ina zanga Sumayya?ina son in rok'eta gafara"
Dukkansu kallonshi suke cike da mamaki.
"momma banaso ace sai aure ya kawota gidannan sannan zan nemi gafararta,zata ga kamar dan ta dawo cikin family ne zan bata hak'uri"
Sun kasa cewa komai,ya d'aura kanshi a kafad'ar daddy yana kuka yana fad'in maganganu wanda suka d'aukeshi a matsayin sumbatu.
Ranar haka ya yini,ya suma ,ya farfad'o.
******* ******* *******
*_06:27:09am_*
Da sauri doctor isma'il ya turo k'ofar ya shigo,Fu'ad na tsaye a kanta sai juya kai take gaba d'aya ta fita hayyacinta.
"lafiya fu'ad?"
Hankalinshi a tashe ya kalli doctor "wallahi doctor bamu runtsa ba,ciwon ya tashi sosai,da tun a cikin daren zan kiraka naga kamar bai dace ba"
"Doctor daya ke on duty bai zo ba?"
"gaskiya ban ganshi ba sai nurses kawai,amma sunce min jininta ya k'ara hawa 220/95"
"Subhannallah,bara ina zuwa" ya fita da sauri.
Fu'ad ya matso gabanta yace "Sumayya dan Allah karki mutu ban san me zan cewa su malam ba,karki mutu lokacin da muke buk'atarki a raye"
bata ma san inda hankalinta yake ba,bare ta samu damar bashi amsa.
Tare da wata mata ya shigo, da nurses guda uku da alama matar consultant ce,da sauri ya fice dan ya basu damar yin aikinsu.
Yana tsaye a k'ofar d'akin yayi tagumi,kallo d'aya zaka yi masa ka tabbatar da yana cikin tsananin tashin hankali da fargaba.
Minti Asharin yana tsaye a gurin sai ga doctor isma'il ya fito jikinshi a sanyaye...
"Doctor lafiya?"
Kallon Fu'ad yake cikin tausayi ya kasa ce masa komai.
"Doctor please ka fad'amin halin da Sumayya ke ciki"
Dafashi yayi sannan ya janyo hannushi zuwa office.
"ka janyo ni nan bayan baka fad'an meke faruwa ba"
"Ka kwantar da hankalinka fu'ad,ka yarda kuma da k'addara dan babu wanda yake kaucewa k'addarar Allah"
Mik'ewa yayi tsaye sannan yace "ka barshi iya nan doctor,kawai ka ce min ta mutu"
Da sauri ya fita zuwa d'akin da take,yana turawa yaga an lullub'e mata jikinta duka.
"inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" ya furta lokacin daya bud'e fuskarta ya kalleta,kamar ka kirata ta amsa.
"Meyesa zakiyi min haka meyasa zaki mutu lokacin da muke son rayuwarki,da wane ido da wane bakin zan fad'awa su malam mutuwarki,na shiga uku,meyasa zaki sa nayi musu k'arya?meyasa ban gaya musu gaskiya ba,ki taimaka ki tashi Sumayya"
kuka sosai yake,doctor isma'il ya turo k'ofa ya shigo.
"kayi hak'uri Fu'ad ka zamo mai tawakkali"
Bai samu damar bashi amsa ba saboda kukan daya ci k'arfinsa.
*muje zuwa✍🏼*
*Hannu biyu*🤝
_Sadeey_
_&_
_Nafsal_
[10/5, 3:21 PM] Little ngel👄: *🍁MENE AIBUNA🍁*
🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁
_by_
*_SaNaz deeyah_*
_&_
_*Nafisa S Adamu*_
```Dedicated to beebahluv & Munay```
*_😂😂😂page 83&84 is ol about masu Zagina,har ta pc,menayi muku? mene aibuna da kuke zagina?meye a cikin littafina wanda bai dace ba kokuma mara kyau,i dont have tym to hate u guyx,infact na sadaukar muku da wannan page d'in dan so ne yasa kuke zagin SaNaz,babu damuwa kuci gaba da zagina kunji🤣🤣🤣babu komai k'auna ce ta jawo hakan,ILYSM😘_*
_Rasheedah karki damu mun tsara novel d'in tun kafin mu fara,so gaskiya idan muka canza salo zai b'aci,ki cigaba da karatu zaki ji dad'inshi vry sn_...
_*SANAZ NOVELLA@my group members kuma naji k'orafin ku,kuma nagode da k'arfin gwiwar da kuke bani ILYSM😘😍*_
_Like I said,I dedicate this page to masu zagina😂😂😂 83&84 is ol about u guyx! sai ku d'ora daga inda kuka tsaya😂😂😂 englishiyya🤣🤣🤣🤣lol💃_
*_Am always wit u my readers,ILYSM once again...._*
*_#ANA TARE😍❣#_*
8⃣3⃣↗8⃣4⃣
"be a man Fu'ad,ka sanyaya zuciyarka mana,kai fa namiji ne"
Ya d'ago idanunshi da suka gama rinewa sukayi jajir yace "Ban san me zan cema iyayenta ba,ban san a me zasu d'aukeni ba"
Ya sake kallon gawar Sumayya yace "wai dagaske kin mutu?shikenan kin mutu da bak'in ciki Sumayya?haka kika koma ga Allah ba tare da an dad'ad'a miki a rayuwa ba,Allah yasa mutuwa ta zamo hutu a gareki"
Doctor isma'il da kanshi ya karb'i wayar ya sanarwa su malam.
Lokacin da umma taji labarin mutuwar Sumayya kuwa Sumewa tayi,dan haka malam bai samu damar tahowa da kowa ba,daga shi sai abokinshi malam habu.
Haka ya baro gidan suna ta koke koke,Fatima kuwa ta fita da gudu dan ta sanarwa Nasiba.
Sai da malam ya d'akko hanya sannan ya bugawa mahaifinta ya sanar dashi tare da bashi address d'in asibitin.
Fu'ad kuwa motarshi ya hau ya sake komawa unguwar rimi dan ya sanarma Arish yazo ya gani burin shi ya cika,wayarshi na ta ringing amma yana tsoron ya d'aga saboda number ce,kuma a tunaninshi malam ne...
Sai da aka kira kusan sau hud'u sannan ya d'auka.
muryarshi a sanyaye yace
"hello"
"hello da gaskene 'yata Sumayya ta rasu ko kuma plan ne?"
Jikinsa gaba d'aya karkarwa yake ya rasa ta yadda zaiyi magana dan ya tabbatar mahaifinta ne...
"kayi shiru ka fad'a min gaskiya"
"baba da gaske Allah yayi mata rasuwa" k'itttt yaji an katse wayar,idonsa ya cigaba da zubda hawaye.
Horn yayi maigadi ya bud'e gate,da gudu ya shiga da motar.
Yana yin parking ya d'an tsaya yana tunanin wane part ne suka shiga lokacin da suka zo,bai gama tunanin ba sai ga Ashaz ya fito hannunsa rik'e da key d'in mota.
Da sauri ya k'arasa gurin Fu'ad tare da fad'in "lafiya meya dawo da kai gidan nan?"
Muryarshi a dashe yace "ka shaidani kenan?"
"eh na gane ka"
"Arish nazo nema dan Allah kayi min jagora"
"duk 'yan gidan ma suna falo muje mana,Arish ma baya da lafiya yau kwananshi biyu yana jinya"
Fu'ad baice komai ba suka nufi main part d'in gidan.
Arish na duk'e gaban daddy yana rok'an shi akan karya ce zai aura ma Asrar Sumayya dan zamanta a gidan zai tuna masa abubuwa da dama,kawai sai tsinkayar sallamar Ashaz da Fu'ad sukayi.
Aryaan Arish,Ashaq,Asrar dukkansu suka mik'e tsaye....
"me kuma ya dawo da kai gidannan?haba kun ishemu da jaraba muna zaman lafiya kuna neman d'aga mana hankali"
"Banzo dan na d'aga maku hankali ba,nazo ne in sanar da Arish cewa wadda ya tsana ya kuma tsangwama ta bar masa duniya,sai yayi farin ciki ya kuma kwashi tsiyar da ake samu a duniya"
A tsorace Arish ya k'araso gabanshi yace "ban gane ba me kake nufi"
Hawaye na zuba a fuskar Fu'ad yace "ina nufin Sumayya Allah yayi mata rasuwa yau d'innan a Asibitin Nasmir,burinka ya cika Arish"
Kaf wanda suke d'akin sai da suka tashi tsaye,tsananin fargaba da rashin gaskata maganar Fu'ad ta cika musu zuciya.
Wuyan Fu'ad Arish ya. shak'o tare da fad'in "ban yarda ba ban yarda da cewar Sumayya bata numfashi ba"
Fincike hannun yayi sannan ya cigaba fad'in "tabbas sumayya ta rasu kuma kaine sanadi Arish"
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Shine abinda kowa ke nana tawa.
Da gudu Zahra ta sakko daga upstairs ta k'araso gabanshi cikin kuka mai fidda sauti "dagaske Aunty ta rasu?shikenan bazan sake ganinta ba".
Asrar ya kalleshi yace "ka fad'a mana gaskiya dan Allah"
Fu'ad na hawaye ya kalli Asrar yace "ba sai kun yarda da hakan ba,nazo na sanarwa mijinta ne dan shine ya cuce ta"
Yana kaiwa nan ya fice.
Aryaan ya dafe kai yana ganin abin kamar a mafarki.
Tangal tangal Arish yake kamar zai fad'i,ilham tayi saurin tashi ta rik'eshi,ya tureta ta fad'i k'asa,kawai ya fuzgi key d'in hannun Ashaz ya fita da gudu.
Da sauri daddy ya d'auki key suka rufa masa baya.
Yana shiga motar ya figeta da gudu,shima daddy yayi saurin bud'e motar,momma ta rik'eshi.
"karku barmu cikin jimamin dan Allah"
"ki kwantar da hankalinki habiba,kalli yadda yaron nan ke gudu fa dole mu bishi ai, kiyi hkri yanxu zamu dawo"
Suka shiga Ashaq ne ya jasu.
Zahra kam anan ta zube tana dirzar kuka(Allah sarki sun shak'u sosai tana sonta).
***********
Yana tura k'ofar ya tadda manyan mutane a tsaye su uku,d'aya daga cikinsu yana tsaye kan gawar yana ta tofa addu'a da alama dai mahaifinta ne.
Jikinshi a sanyaye ya k'arasa wajen har lokacin idonshi bai daina zubda hawaye ba.
Sai da mutumin ya gama mata addu'oin sannan ya juyo ya kali sauran mutanen,idonshi babu hawaye amma sunyi jajir da alama yayi kuka ya gama ko kuma kukan zuciya yake yi.
"'yata ce wadda ta jajirce akan sai na sosu,hakanne yasa har ta fara yi min rashin kunya saboda ni kawai na tsani 'ya'ya mata inaso na samu magaji,nayi aure na kuwa tura mamanta gidansu amma dai bance na saketa ba,haka Sumayya ta rik'a yiwa matar da na aura rashin kunya,saboda bata wani basu kulawa abinci ma ba kullum ba,kullum ta kance baba mu 'ya'ya mata meke garemu na tsana,muma muna da rana,danaga dai bazata daina fad'a ina fad'a ba saina aurar da ita kawai na huta,ban san mijinta ba ban tab'a ganin shi ba,na turo ta aure nan cikin garin kaduna,ta tab'a zuwa gida sau d'aya a lokacin da matata hadiza zata haihu,Sumayya na zuwa hadiza ta haihu 'ya mace kuma babu rai,dukan mutuwa nayiwa sumayya nace ita ta kashe min d'a tayi musanya da mace,tun lokacin ban k'ara ganinta ba sai yanzu dana ga gawarta"
ya saka handkerchief ya goge hawaye sannan ya cigaba da fad'in "na cucesu Allah ya yafe min,gashi dai har yau hadiza bata sake haihuwa ba wannan ma ya isheni *ISHARA* Zan rok'i matata ta koma d'akinta zan rungumi 'ya'yana hannu biyu,zan nuna masu soyayyar da basu samu ba"
Ya sake kallon gawar yace "Allah ya miki rahma Sumayya,yasa mutuwa ta zamo hutu a gareki"
Fu'ad dake bayanshi kuka ya cigaba dayi,musamman daya ji tarihinta a yanzu,kenan bata tab'a samun soyayya a duniya ba,haka tayi rayuwa cikin bak'in ciki har ta mutu wannan shi ake kira da *HUZNUL HAYAT* gashi ta mutu bajin dad'in rayuwa.
Sai a lokacin baba ya kula da shi "kaine mijin nata?"
bai bada amsaba aka hankad'o k'ofar da k'arfi....
Arish ne ya shigo,da sauri ya k'arasa gaban gawar,
"kin mutu da gaske Sumayya?inna lillahi wa inna ilaihi raji'un,dan Allah ki tashi ban gaskata haka ba"
Su baba suka rik'eshi sai kuka yake yana sambatu(ashe dama kana sonta ka wulak'anta ta ko😂😭).
Daddy,Aryaan,Ashaz,Ashaq,Asrar,suka shigo d'akin,Asrar ya rik'oshi shima yana kukan yana fad'in "ya isa haka yaya Addu'a zaka yi mata kaima fa baka da cikakkiyar lafiya"
Baba kuwa babu wanda ya sani a cikin su dan haka bai san matsayinsu ba a gurinta.
A hankali Aryaan ya yaye zanen ya kalli fuskarta,yayi saurin rufewa,bai san sanda ya durk'usa k'asa yana kuka ya fara fad'in "meyasa baki fad'a min zaki mutu a kurkusa haka ba?taya zan samu damar neman gafararki?na cuceki na zalumceki,sharrin aboki,abokine yayi min had'u ba,Sumayya ki tashi na nemi gafararki dan na zalumceki na tauye miki hak'k'i"
Daddy ya k'arasa gabanshi ya tallaboshi yace "haukata ni kuke son yi Aryaan?wa zan lallasa a cikinku?"
Jin an ambaci Aryaan ne yasa baba k'arasowa gabanshi dan ya tabbatar Aryaan ne wanda aka d'aura wa aure da Sumayya.
"kayi hak'uri addu'arku kawai take buk'ata" baba yayi maganar.
Ya kallesu hawaye na fita a idonshi yace "a'a ni abinda nayi mata yafi k'arfin wasa,ban san taya zata yafe min ba,najiwa kaina rauni na goga a bedsheet sannan na nunawa 'yan gidanmu a matsayin na san Sumayya a 'ya mace,bayan ba gaskiya bane,bata tab'a kusantata ba,na dai so hakan amma Allah ya tonu asirina a ranar da zanyi amfani da ita,tayi kukan tayi rok'an amma nak'i fad'in gaskiya,rashin lafiya d'an uwana yayi har tsohon shekara had'u amma duk ban fallasa ba,saboda ina bak'in cikin in ganta da wani a matsayin miji ba ni ba,na barta da aurenshi a kanta bayan nasan babu abinda ya tab'a shiga tsakaninmu duk wata hanyar danasan za'a bi asan gaskiya na tosheta,Asrar da Zahra ne kad'ai suka san gaskiya amma babu wani abu da zai zamar musu shaida,daddy taya kake tunanin Allah zai yafe min abinda na aikata"
Mik'ewa tsaye daddy yayi cikin b'acin rai,Arish ya k'araso gabanshi yace "Dagaske ne ko mafarki nake?"
shiru Aryaan yayi yana hawaye.
Arish ya mik'e tsaye yana kuka jikinshi na karkarwa ya nuna Aryaan da hannu yace "kai d'an uwane wanda nake so na kuma aminta dashi,ka cuceni ka cuci Sumayya,baka tausayina kamar yadda nake tausayinka Aryaan na tsaneka,nima mutuwa zanyi,kayimin abinda bazan tab'a iyayiwa koda mak'iyi na ba"
Kai kawai ya girgiza ya cigaba da ja da baya,kafin ya kai k'ofa kuwa ya zube a k'asa ko motsawa bai sake yi ba.
*Muje zuwa*📝
Hannu biyu🤝
Sadeey
&
Nafsal
[10/5, 3:21 PM] Little ngel👄: *🍁MENE AIBUNA🍁*
🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁
_by_
*_SaNaz deeyah_*
_&_
_*Nafisa S Adamu*_
```Dedicated to beebahluv & Munay```
_And dis latest page goes to ol *mene Aibuna Fans* I dedicate dis page 2 u guyx_........
*_oyaaaa Lts enjoy d page😊_*
#Ana tare fa#😆❤😍😘
8⃣5⃣↗8⃣6⃣➡EDITING✔
Dukkansu suka nufo kanshi,daddy ya rik'eshi yana jijjagashi,da sauri Aryaan ya k'araso gurin,wani mugun kallo daddy yayi masa tare da fad'in "ban yafe maka ba Aryaan ka cutar damu".
Babu shiri aka bawa Arish gado tare da bashi taimakon gaggawa.
Babu jimawa malam ya k'araso asibitin,da sauri ya k'arasa jikin gadon ya bud'e fuskarta "Allah ya miki rahma sumayya" ya rufe fuskarsa ya tsaya kanta yana ta kwararo addu'oi,bayan ya gama ne ya tashi zai fita aka turo k'ofar.
Baba ne ya shigo,cikin girmamawa ya durk'usa ya gaida malam....
Hannu malam ya d'aga masa yace "dakata,bana son jin komai,Allah ya jik'anta da rahma,bara na fad'awa likita azo a sallamemu dan ayi jana'iza da wuri an bar gawa haka ai ta gaji gashi bata son jinkiri" Cikin damuwa ya fita....
Fu'ad na lab'e yana hangoshi,tsoro da kunya duk sun mamaye shi bai san me zai cewa malam ba,yana hango malam lokacin daya shiga office d'in doctor isma'il.
*_2m later_*
Yana zaune a harabar asibitin fuskarshi cike da damuwa,idanunshi sunyi jajir ga wani hawayen ya mak'ale yana shirin zubowa.
Kamar daga sama yaji ance "gashi nan"
da sauri ya mik'e tsaya,karaf suka had'a ido da malam.
Duk ya bi ya rud'e ya diririce,malam ya k'araso gabanshi yace "Fu'adu ko kaima kayi cutane naga ka koma haka?"
Sunkuyar da kai yayi k'asa hawayen da suka mak'ale a idonshi sune suka samu damar zubowa.
"ka kwantar da hankalinka Fu'adu,,doctor yayi min bayanin komai,Allah ya fimu sonta kuma dama ruk'o ya bamu lokaci yayi ya kuma amshe kayansa,fatan dai Allah zai gafarta mata,kuskure d'aya kukayi daka biye mata taje gidansu Arish,sannan kuma kuka k'i gaya min gaskiya amma duk da haka dai Allah ya k'addara bazamu gana ba,addu'a take buk'ata ba kuka ba"
Haka malam yayi ta rarrashin Fu'ad,
Cikin mintuna k'alilan aka shirya gawar Sumayya suka tafi Gombe,dan malam cewa yayi kar a fad'awa su daddy.
Baba kuwa waya yayi wa abokanshi na kano da 'yan unguwa wanda Allah ya bawa damar halartar zana'iza sai ya halarta.
Koda daddy da Asrar suka koma d'akin suka tarar wayam babu su fu'ad,katifar ma an fitar da ita,ran daddy ya b'aci sosai lokacin da doctor isma'il ya shaida musu cewar sun tafi,shima kuwa yace a sallamesu su koma gida.
Haka aka sallamesu ba tare da Arish ya farfad'o ba,Suka saka shi a mota suka yi gida,Aryaan kuwa tuni ya bar asibitin dan baiga fuskar zama ba.
Ko da suka koma gida ma baya nan,daddy ya bada labarin abinda ya faru a gaban kowa,gaba d'aya aka hau salati,momma kuwa kuka take sosai dan ta san tabbas Aryaan ya zulumci Sumayya da Arish,gashi abin takaicinma sai da ta mutu sannan gaskiya ta bayyana.
Ilham kuwa cikin tashin hankali ta tashi ta nufi bedroom d'in da Arish yake kwance.
"still dai ni kad'ai zan zauna dakai my man,na tsani kishiya,I hate rival,dan Allah ka tashi mu gina soyayyarmu cikin aminci da yardar juna ka manta da komai dan Allah"
A falo kuwa haj karima ce ke tambayar daddy shin yaushe zasuje gombe "Sai Arish ya warware ko ranar sadakar bakwai sai muje"
"to Allah ya kaimu"
duka suka amsa da "Amin"
Zahra kuwa an nufi bedroom anata aikin kuka,haka dai family d'in suka zauna suma suna ta'aziyya a cikin gida.
_3h Later_
_Yana zaune yana wasa da tsummukaranshi,ta k'araso gurin da sauri a gigice ta zube k'asa tana nishi,kallonta yake cike da mamaki yace,meya sameki ne na ganki a gigice?_
_gentle rabamu ake son yi,gentle ka taimakeni zasu rabani da kai,wani abu mai haske ne ya fara janta,tana kuka tana mik'a masa hannu tana fad'in zasu rabamu da kai gentle ka ceceni_.
"bazasu tab'a iya rabani dake ba Sumayya" ya fad'a yana mik'a hannu.
Ilham ta kalli momma cike da mamaki,momma tayi saurin rik'e hannunshi tare da yayyafa masa ruwa a fuska,a hankali ya bud'e ido.
Ganin inda yake ne yasa shi saurin tashi zaune,ya kalli momma yace "momma mafarki nayi"
"na sani Arish,addua zaka mata"
"dagaske Sumayya ta mutu momma?"
"mutuwa gaskiya ce Arish"
"na kasa gaskata hakan,momma Aryaan ya cuceni,bana son k'ara ganishi a rayuwata,shine ya kasheta momma wallahi shine sanadi"
"cool your mind Arish kaga baka da cikakkiyar lafiya fa"
"shike nan yanzu ya rabani da ita bazan sake ganinta ba"(ashe kana sonta😜cewar Nafsal)
momma na rarrashinsa amma sai sumbatu yake,hakanne yasa aka kira doctor yayi masa allurar bacci.
Ilham kuwa ta k'ulu iya k'uluwa.
******
A b'angaren Su malam kuwa,bayan sun isa gombe,haka akayi ta fama da umma ta suma ta farfad'o(kunsan d'a mara ji akwai shiga rai,musamma ita sumayya da ta taso cikin tsiwa amma daga baya duk tayi sanyi).
Su Nasiba kuwa kuka suke tayi,har aka yi mata wanka aka shiryata suna kuka.
An zo za'a tafi da gawar Nasiba tayi saurin rik'ewa ta zube a k'asa,aikuwa ta k'walla k'ara saboda wani azabben ciwon da takeji,tuni jini ya fara biyo k'afafunta.
"subhanallahi tayi b'ari ai ku d'auke ta daga gurin"
da sauri wasu mata suka shigar da ita band'aki.(just imagine!🤦♀kaiiiii abin tausayi).
Su farida sai kuka suke da k'yar aka janyesu aka fita da gawar(gaskiya family d'in sun bani tausayi matuk'a🤦♀😭).
Ana fitowa da gawar Fu'ad ya k'arasa gurin yayi mata addu'a sosai,malam da baba ma sunje sunyi addu'o'insu,Fu'ad kuwa yak'i daina kuka kawai rayuwarsu a London yake tunawa yanzu haka zai koma cikin kad'aici.
Haka suka tashi aka had'a sahu dan gabatar da sallar gawa.
Idonshi ne ya kai gurin yaga kamar k'afarta ya motsa,ya murza idonshi dan yaga ko gizo ne,aikuwa yaga ba motsawa take ba.
An tada sallar ya kasa jurewa ya kalli gawar a karo na biyu yaga k'afarta ta motsa...
"la haula wala quwwata illah billah" ya fad'a tare da k'arasawa da gudu gaban gawar.
Malam yayi saurin sallama yazo gare shi...
"malam bata mutu ba,ni dama ban gaskata ba,wallahi sau biyu k'afarta na motsawa dan Allah ku bud'e ta shak'i numfashi.
Kallon k'afar yayi ya tabbatar da hakan,da sauri kuwa ya saka aka shigar da ita gidan dan mata su bud'eta......
mutane kuwa aka hau surutu cike da al'ajabi.
_*Wash Allah nah,bara na barku iya nan na huta,amma zan d'an tofa albarkacin bakina nima*_.
_Readers masu zagin SaNaz bawai dan ku nak'i kasheta ba,saboda a haka muka tsara novel d'in,kundai yi gajen hak'uri kun subirbid'o min zagi🤦♀😡,dan *HUZNUL HAYAT* ma haka kukayi ta zagina dana kashe Rabi'atu kuma daga k'arshe kunga yayi dad'i novel d'in,ba dole sai star ta rayu ba,a'a kawai ana duba yadda littafin zaiyi mana'a ne,kamar yadda na fad'a a HUZNUL HAYAT ba kowane yakeyin happy ending a rayuwa ba,kawai dai kowa ya kan so ace yayi happy ending a rayuwanshi_.
_*Nima SaNaz zan iya cewa rabon asirin Aryaan ya tonu ne yasa Sumayya tayi doguwar Suma*_
_*Ku biyomu*_✍🏼
Hannu biyu🤝
Sadeey
&
Nafsal
[10/7, 1:40 PM] Little ngel👄: *🍁MENE AIBUNA🍁*
🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁
_by_
*_SaNaz deeyah_*
_&_
_*Nafisa S Adamu*_
```Dedicated to beebahluv & Munay```
8⃣7⃣↗8⃣8⃣
Bayan an gama shiryata aka yiwa malam iso ya shigo tare da Fu'ad da baba...
Tana zaune a d'akin an zura mata hijabi a jikinta,duk kansu suka zauna sannan malam ya fara magana,
"Sumayya sannu ko"
tayi shiru bata ce komai illa binsu da ido da takeyi kawai.
Fu'ad kuwa sai hamdala yake a cikin zuciyar shi,malam ya sake cewa "yanzu ya kike jin jikin naki?" a karo na biyu ma bata ce uffan ba sai ido da take binsu dashi.
"A kawo min ruwa a kwano,sannan ya kamata mutane su ragu dan bazata so hayaniya ba" malam ya fad'a yana kallon umma,ita kuma ta mik'e ta fita,fuskarta duk ta kumbura..
Da ruwa ta shigo d'akin ta mik'a masa yayi addu'a ya bata tasha.
Kwanciya tayi a gurin ta rufe fuskarta da hijabi.
Malam ya bada umarnin a barta ta huta kada a cikata da surutu.
Nasiba kuwa ciki ya zube tana can tana baccin wahala bata ma san meke faruwa ba.
Zo kuga murna wajen Farida da Fatima,kamar zasu had'iye Sumayya sunje sun zauna kusa da ita sun kafe ta da ido.
Allah sarki Fu'ad hotel ya kama ya zauna,dan gani yake ko zaria ba zai iya komawa ba idan bai ga Sumayya ta warware sosai ba.
Kwananta biyu sannan ta fara magana.
Duk kansu suna zaune akan tabarma a tsakar gida,malam da baba suma suna zaune a wata tabarmar.
Ta cigaba da basu labari "ina biye da mutanen dukkansu sunsha fararen kaya munata tafiya,kawai saina ci karo da malam iliya marigayi mak'ocinmu, ya kalleni ya b'ata rai tare da fad'in in koma ba yanzu zanzo nan ba,na juya har na d'anyi nisa da tafiya kawai juyawar da zanyi naga mutanen sun biyoni da gudu suna cewa sai mun tafi,haka nima na ruga da gudu ina kuka a cikin gurin nan wanda yayi kama da sahara dan babu komai sai rairaye,ina cikin gudun na hango gentle a sigar mahauciya kamar da,yana zaune gaban tsummukaronshi,na k'arasa ina fad'in ya ceceni yana tambayata meya faru ne?kawai wani farin haske kamar iska ya fara jana,nayi saurin mik'a hannu na rik'e Gentle ina kuka sai najini a takure a guri guda,iya abinda na sani kenan"
Malam yayi ajiyar zuciya yace "Alhamdulillahi doguwar suma ne,wanda kika gani kuma duk matattu ne idan kika d'auke shi Arish d'in,Allah ya k'ara tsare mu"
"amin" duk suka amsa.
Addu'oi ya k'ara bata.
Da yamma Fu'ad yazo gidan,still suna tsakar gida amma ita tana d'aki tana tunanin data saba.
"umma ina Sumayya"ya tambaya
"tana cikin d'aki sai kace matar da aka yiwa kulle"
"Ayya umma ku daina barinta tana zama ita kad'ai shine sanadin ciwon nan nata"
"to ya zamuyi"
Tashi yayi ya nufi d'akin,tana zaune kuwa tayi uban tagumi,ya k'arasa d'akin ya tafa mata hannu,da sauri ta d'ago kai ta kalleshi...
"gawa tak'i rami tunanin me akeyi?"
Murmushi tayi tace "oh nice gawa tak'i rami ko?"
"a'a bance ba"
"ki rage tunani please Sumayya ko so kike a koma gidan jiya?"
"a'a,kai ma kuma ka daina yawaita damuwa ko so kake ka kamu da cuta?"
Murmushi sosai yake ba tare da hak'oranshi sun fito ba.
"yawwa yaya Fu'ad muje ka zab'a,ga Fatima ga Farida,amma kace fatima ko"
"no a'a muje dai na zab'a,idan fatima na zab'a zance T idan kuma farida zance R,sannan kuma kada ki fad'awa su malam a gabana ki bari sai na tafi"
"to shikenan muje"
suka fita aka zauna anata hira,tuni a zuciyarshi ya zab'i wadda yake so,dan yaga suna kama da Sumayya sosai,dan dai ita fara ce Sumayya kuma bak'a.
A hankali yake satar kallonta yana son yaji an ambata ya fad'awa sumayya.
Baba ne yayi gyaran murya ya fara magana "ada kam tabbas nayi kuskure,domin a tunanina 'ya'ya mata ba wata tsiya bane,amma a yanzu kam na gane kuskurena Allah ya nuna min ishara gashi har yanzu ban k'ara samun wasu 'ya'yan ba tun bayan haihuwar ihsan"
Ya kalli malam sannan ya duk'a gwiwoyinshi k'asa yace "na tuba malam dan Allah ku yafe min na gane kuskurena,zan rungumi matata da 'yay'ana cikin amince da so da kuma k'auna,gashi yanxu har farida da Fatima sun gama secondary skul Sumayya na shirin kammala degree,tabbas tsufa ya zo,dole in tattali 'ya'yana"
Malam yayi ajiyar zuciya yace "to Alhamdulillahi,mungodewa Allah,dama ni tuntuni wannan ranar nake jira,kuma gashi Allah ya kawota ka gane gaskiya masha Allahu"
Umma kuwa ta sunkuyar da kanta k'asa ba tare da tace komai ba(Allah sarki umma akwai kawaici).
Goggo ce tace "yanzu sai su tattara duk su wuce kanon tare tunda gobe yace zai koma"
"eh haka za'ayi"
Nasiba tayi saurin cewa "ni kuma fa?"
"tambayata kike?" goggo tayi maganar.
"auren naki wa zaki barwa in kin tafi kano?" malam yayi maganar.
Shiru tayi ba tare da ta sake cewa komai ba,Fatima ce ta kalleta tayi mata gwalo,ta had'e rai tace "baba kaga Fatima nayi min gwalo ko"
Da sauri Fu'ad ya kallesu dan ya gane wacece Fatima,aikuwa tace "baba bani bace fa ni ko kallonta ma banyi ba"
"zaki aikata fatima na san halinki"
Dariya take ta tashi ta shiga d'aki dan tayi mai isarta.
Kasa fad'i yayi dan haka ya tashi kawai da niyyar komawa hotel shima dan ya had'a kayanshi.
A bakin motar Sumayya ta tsaya tace "baka fad'a min ba"
Ya d'an sosa kai yace "mai kama dake"
"wace mai kama dani?"
"Farida"
"wow ka zab'i salihar mace kuwa,bara naje na fad'a masu"
"a'a please"
ta d'an harareshi tace "kaga tafiya ta"
da sauri ta shige gidan,shima ya shiga mota yaja.
Suna tsakar gidan inda ta barsu,Fatima ta dawo ta zauna.
Cikin murna Sumayya ta fad'awa malam abinda ya faru tun daga alk'awarin da tayi masa.
Malam kuwa yayi Farin ciki sosai,Baba kuwa yace indai har da gaske yake to ya turo iyaye ayi magana zai yanke bikin sati uku masu zuwa.
Farida kuwa kunya tasa ta tashi ta shige d'aki,a zuciyarta tana fad'in kamar ya karanceni tun da yazo naji ya burgeni dan dai ni macece bazan yi rashin kunya na furta masa ba,farin ciki sosai ya baibayeta.
Fatima kuwa sai tsokanarta take,Sumayya tace "kina zaune zasu tafi England kinga sai ta cigaba da karatu acan"
"cab ni kuma sai inje hutu koda banyi karatun ba" cewar fatima.
"k'atuwa dake kije masu gida" inji Nasiba
"na ajje girman na bawa Farida" ta fad'a tana dariya.
Koda Fu'ad yazo da daddare Farida kasa fitowa tsakar gida tayi,malam ya k'ara yi masa bayani,shi kuma yace zai turo amma yana so a saka bikin sati biyu saboda yana son komawa da ita can london ga aiki yayi kusan 2wks baije ba,baya son ayi mata komai shi zaiyi.
_wani hanin ga Allah baiwa ne_....
baba ya fad'a a ranshi.
Sumayya kuwa tace "Tare zamu koma saboda nima nayi missing lectures yaya"
"eh harma da Fatima itama sai a sama mata admission acan"
tsalle Fati ta daka,wai yau ita zata taka k'afar jirgi zuwa England,cabb za'aga gayu.
"a'a Fatima tana nan zan sama mata admission a b.u.k,abin zaiyi yawa Fu'ad" baba ya fad'a,Fatima kuwa rai ta had'e.....
"a'a baiyi yawa ba baba ai duk yiwa kaine".
Haka sukayi ta hira Farida na jiyo su a d'aki kunya ta hanata fitowa,ita duka 'yan gidanma kunyarsu takeji wai ita ce za'ama aure,haka take ta fad'a.
Sumayya kam babu wanda ya sanar mata cewar Asirin Aryaan ya tonu.
Sai da har ya shiga mota sannan aka kira Farida taje ta tsaya a jikin motar suka gaisa ta dawo gida.
***** ****** *****
Yana zaune acan k'arshen gado yayi shiru yana tuna irin rayuwarshi shida Sumayya tun farkon zuwanshi kano....
_tabbas Sumayya bata cancanci wulak'anci a gurina ba,tana kula dani tun kafin ta san ni mai hankali ne,sannan tazo ta tsare mutuncin aurenta tun kafin ta san gentle d'inta ne Arish,tabbas nayi mata *Rashin Halacci*,tare da gudunmawar Aryaan_...
Cikin sallama ta shigo ta zauna.
"tunani kuma my man?"
ya d'ago kai ya kalleta sannan ya kawar da kanshi gefe.
"gaskiya ana shiga hak'k'ina wallahi,tun da nazo gidannan babu abinda ya tab'a shiga tsakanina dakai wai a sunan kai mijina ne,baka bani hak'k'ina sannan yanzu ka daina kulani ka daina cin abinci na"
ta mik'e tsaye ta cigaba da fad'in "wallahi zan kai k'ararka gurin momma,kaiiii"
ta dafe goshinta da hannu,sannan ta kalleshi cikin b'acin rai "na fara kishi da gawa Arish"
yayi saurin d'ago kai ya kalleta...
"yes!wallahi na fara kishi da Sumayya duk da bata raye,nifa na gaji dole in samu mafita ehe"
A fusace ta fita ta bar d'akin shi kuma ya bita da kallo.
A b'angaren su Sumayya kuwa a washe gari suka bar gombe tun k'arfe tara na safe,Fu'ad ne ya d'aukesu sai da ya kaisu har k'ofar gida sannan ya wuce Zaria.
Nasiba kam tasha kukan rabuwa da umma da 'yan k'annenta.
Shi kuwa Fu'ad yana zuwa Zaria ya sanarwa da mahaifinsa abinda ke faruwa,babu abinda daddy yace sai Allah sanya alkhairi sannan ya tambayeshi ko son aurene ya ramar dashi haka,cikin kunya yace a'a rashin lafiya yayi.
Daddynsa kuwa a washe garin ranar ya tafi tare da yayanshi da k'aninshi nemarwa d'ansu auren Farida,sunyi murna ganin gidan malamai ne kuma masu karamci,sai baba idris(k'anin mahaifinsa) ya kushesu kasancewarsu talakawa,daddy da baba yahya(yayan baban Fu'ad) sukayi ta masa fad'a tare da nuna masa illar abinda ya fad'a dan da talauci da arzik'i duk na Allah ne.
Shi dai daddynsa murna yake dan da Alama tilon d'an nashi yayi dace da mata.
A b'angaren Arish kuwa yau sadakar bakwai na Sumayya,sun shirya tun k'arfe bakwai zasu tafi,Ilham kuwa da bazata je bs sai da Arish ya matsa mata.
(baku tambayeni Aryaan ba?,ai tuni yayi visa ya koma Australia ya kuma ce bilkisu ta bishi,tak'i yarda ta bishi,daddy ma ya bada goyon bayan karta je idan ya gaji zai dawo da kanshi dan sai ya d'auki babban mataki a kanshi).
Suna zaune a babban falo,duk kansu cikin shiri,Ayrah na gefen 'yar uwarta suna hira kad'an2.
Sumayya ce ta fito rik'e da hannun khalil,d'ayan hannunta kuma trolley'n kayansu ce.
"lafiya na ganki da trolley?"
Arish ya tambaya...
"zan koma orphanage" ta fad'a cikin sanyin murya...
Yayi saurin k'arasawa gurinsu,ya rik'e khalid ya kalleta yace "ko wani abu ake miki?"
ta girgiza kai alamar a'a
"to idan babu komai meyasa kike son tafiya?"
"ina tsoron kar wata rana azo ayimin gori dan naga fad'ace2 yayi yawa"
Daddy ne yayi ta mata fad'a,akan meyasa har yanxu bata d'aukeshi uba ba,ya saka Zahra ta mayar da trolley cikin d'aki.
Har zasu tafi momma tace "kamata yayi ayi musu waya akan zamuzo muna kan hanya saboda babu dad'i su gammu kwatsam"
"hakane bara na kirawo malam tunda ina da numbershi"
Yayi dialing har ta katse ba'a d'aga ba,ya sake kira sannan aka d'auka shima sai da ta kusa katsewa,bayan sun gaisa ne daddy ya fad'a masa cewar ga sunan zasu taho gaisuwa,malam kuwa ya basu labarin abinda ya faru har ya shaida musu ta koma kano ma gidan mahaifinta....
"to Alhamdulillahi lallai Allah mai hikima ne,to shikenan maje can d'in nagode a gaida iyali" shine abinda suka ji daddy yace,Allah Allah suke ya katse ya gaya musu abinda ke Faruwa.
Cikin farin ciki yace "bata mutu ba doguwar suma tayi"(kuyi tunanin irin farin cikin da zasuyi😃 ni kuma zan gaya muku yadda Zahra,ilham da Arish zasuyi nasu farin cikin).
"daddy da gaske ne ko mafarki nake?" ya fad'a yana hawayen murna.
"dagaske ne Arish bata mutu ba tana raye ta koma kano"
"daddy na san gidan please kuzo muje in ganta" ya fad'a cikin murna da zumud'i ya rasa wane irin farin ciki yake....
Ita kuwa Zahra tsalle tayi ta dire tace "ashe da rabon zamu k'ara rayuwa dake a cikin gidannan Aunty,gaskiya bazan iya kwana ban ganki ba" da murna ta fad'a kan kujera ta rungume pillow.
_Na shiga uku_ maganar da ilma tayi a zuciya ce ta fito fili.
"kin shiga uku kuma kamar ya ya?ana farin ciki kina cewa kin shiga uku" Asiya tayi maganar.
Da gudu ilham ta fita tana kuka.
_*KU BIYOMU A NEXT PAGE WANDA SHINE LAST PAGE*_📝
Hannu biyu🤝
Sadeey
&
Nafsal
[10/7, 1:40 PM] Little ngel👄: *🍁MENE AIBUNA🍁*
🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁
_by_
*_SaNaz deeyah_*
_&_
_*Nafisa S Adamu*_
```Dedicated to beebahluv & Munay```
8⃣9⃣↗9⃣0⃣
Kowa yayi jigum cike da mamakin abinda ilham tayi.
Ayrah ce tayi saurin fita ta bita,daddy ya kalli Arish yace "kaje ka rarrashi matarka"
har zaiyi magana daddy yayi saurin katseshi da fad'in "kabi umarnina Arish"
Fita yayi ya nufi part d'in nasu,shi kam hankalinsa ya gama kwanciya tunda zai rayu da Sumayyar shi.
A bedroom ya tarar da ita tana had'a kaya tana kuka,Ayrah ma na zaune gefen gadon tana kuka.
Tsayawa yayi a gabanta bata ko kalleshi ba ta cigaba ta zuba kaya a trolley.
"wai ina zaki ne?"
ta d'ago idonta cike da hawaye tace "gidan mu"
ajiyar zuciya yayi sannan yace "to ni dai har ga Allah ban san mena yi miki ba da kike ta faman kuka kina had'a kaya"
Wani sabon kuka ya kubce mata tayi ta gama bai ce komai ba....
ta zuge trolley ta kalleshi tace "ya lafiyar kura bare tayi hauka,ai indai sumayya ta dawo gidannan na san farin cikina ya k'are"
"okay saboda ance bata mutu ba shine kika ce kin shiga uku?"
"k'warai ma kuwa Arish dan tun kafin asan bata mutu ba kake kyarata,baka kusantana baka cin abinci na baka zaunawa muyi hirar arzik'i dakai indai muka zauna maganar d'aya ce *SUMAYYA*,haba gaskiya bazan iya ba"
"Ilham duk yadda zan kwatanta miki irin yadda sumayya ke sona bazaki tab'a yarda ba tunda kishi kike da ita,amma ni dai na sani kuma Allah ya sani ina sonta so mara misaltuwa"
"ai a hakan ne naga ka wulak'anta ta"
"hmm bazaki fahimta bane kamar yadda na fad'a"
"tunda haka ne kuwa kaga sai ince asha soyayya lafiya,ni kuma gidanmu zan tafi"
tab'e baki yayi yace "as you wish,kiyi yadda kikaga dama" ficewarshi yayi ya bar mata d'akin..
Rungume Ayrah tayi tana kuka tana fad'in "Ayrah dan yaga ina sonshi ne,dan yaga bazan iya rabuwa dashi ba shiyasa yake wulak'anta ni"
lallashinta Ayrah tai tayi tana kukan itama.
*KANO*
'Karfe 12:00pm daddy,Arish,Asrar Suka isa garin kano.
Arish ne yayi masu jagora har gidansu Sumayya dan shine kad'ai ya sani.
An karb'e su hannu bibbiyu,sannan suka yiwa baba barka tare da fad'a masa abinda ya kawo su,dan su bawa Sumayya da iyayenta hak'uri akan abinda ya faru musamman ma Umma.
Umma kam koda aka kirata haka tace babu komai k'addarace kuma jarabawace ta rayuwa dan haka komai ya wuce,Sumayya kuwa kuka ta saka tana fad'in ita kam baxata koma wannan gidan ba dan haka kawai ya bata takardar saki.
Baima kula da daddy da iyayen matarshi ba yace "dan Allah ki ceci rayuwata Sumayya,kiyi hak'uri ki yafemin wallahi bani da laifi,dan Allah ki manta komai kizo muci gaba da rayuwa"
Instead of ta tausaya masa ta hak'ura kawai sai ta fashe da kuka,ta tashi da gudu tayi d'aki....
Haka suka koma kaduna babu k'arfin gwiwa duk da dai baba ya tabbatar masu da cewar zata koma...
A gida ma haka ilham ta saka shi gaba tana kuka,ranshi duk a cunkushe yake.
Tun zuwan su Arish kuwa Sumayya bata da aiki sai kuka,baba yayi tayi mata fad'a yana fad'in dama ta san tana sonshi amma tak'i yin hak'uri akan duk abinda ya faru.
Hadiza kuwa tuni ta bar gidan dan baba ya sawwak'e mata tun ranar daya gane makircin ta.
Asrar da Ashaz basu gajiya wajen zaryar zuwa kano bikon Sumayya,da k'yar suka shawo kanta ta hak'ura,ai kuwa Arish ya samu gurin zuwa kullum yana kano tun safe sai dare yake dawowa,ilham ta shiga tashin hankali sosai,babu abinda ke shiga tsakaninta dashi.
Sumayya kuwa tace ita bazata dawo ba sai anyi bikin Farida da yaya Fu'ad.....
_A TAK'AICE_
Shagali sosai akayi bikin Farida da Fu'ad,haka shima Arish ya dage sai anyi masu sabon biki da Sumayya.
Party kala hud'u akayi biki na d'an gata Fu'ad d'a d'aya tilo a gurin daddynshi....
Washe garin d'aurin aure kuwa da magrib jirginsu ya d'aga zuwa london,Farida tasha kuka kamar zata mutu,gashi ba'a samu visa fatima ba,sai dai dole ta biyosu daga baya,Sumayya ma taso tafiya amma baba
yace Fu'ad yaje skul d'in yayi complain...
itama kuwa washe garin tafiyar su Farida k'arfe biyar na yamma a kaduna tayi mata...
flat d'in Arish aka kaita, ko wane flat bedrooms uku ne,da falo 2,dan haka dama tuni ya raba musu ko wacce falo d'aya bedroom d'aya.
Hmmmmm Su Arish kam an angonce,dan ko falo bai lek'o ba sai k'arfe d'aya da rabi ya fito,yaje yaga lafiyar ilham duk da dai cikin damuwa take amma shi kam bai damu da hakan ba tunda farin cikinsa ta dawo.
Yau kwanan Sumayya uku da dawo wa,gidan amma Arish kulum sai bayan Azhar yake fitowa daga d'akinta,sallah ma jam'i yake masu shida ita,da yamma Zahra da takwararta sukanzo su taya ta hira.
*****************
A falo ta tarar da Ayrah tana karatun novel,ta fad'a jikinta tana kuka tana fad'in "bani da wani 'yanci Ayrah,zaman gidan Arish ya isheni,baya da abin cewa sai Sumayya baya kulani baya shigowa d'akina idan kin ganshi a gurina to zuwa yayi yace min ya nike shikenan fa"
labari ta bawa Ayrah akan duk abinda yake mata,a fusace Ayrah ta tashi ta yafa gyale tayi part d'insu.
Falon sumayya ta dosa,tana kwance kan doguwar kujera kunnenta mak'ale da waya kawai ganinsu tayi a gabanta....
"ina zuwa Farida"
ta fad'a tare da katse wayar...
"ke munafuka ce,wallahi idan ma asiri kikayi mu bazai cimu ba,kurwarmu kur" Ayrah tayi maganar cikin fad'a.
"ban gane ba lafiya?"
"kiji tsoron Allah ki barmin mijina nima ya ririta ni,kamar yadda kike ji dashi kike sonshi,haka nima" Ilham ta fad'a tana kuka...
Cikin fad'a Ayrah ta cigaba da fad'in "ke kika tsaya kina bata hak'uri yaya,shin ita wacece,ai wannan cin mutuncine da shiga hak'k'i,kink'i bari mijinta ya rab'eta tunda aka kawota gidannan haka take,ai ita ba hoto bace,amma dubi a kwana uku yadda kika zama,saboda kin kanannad'eshi ko?kewai kinsan dad'in miji,kin saka 'yar uwata a k'unci kullum Arish yana lik'e dake kamar chewing gum"
"wallahi ban san komai ba,ban san anyi haka ba,kiyi hak'uri ilham"
"k'arya ne,ke kuwa kika san komai makira" sai da ta k'are mata tass sannan taja ilham suka fice.
*11:03:02pm*
Tayi alwallah ta fito ta hangoshi ya kwanta har ya rufe rabin jikinshi da blanket,tayi murmushi ta k'arasa gurin tare da janye bargon...
Juyowa yayi ya kalleta ta sakar masa murmushi sannan tace "magana zamuyi gentle"
"oh my god,bacci nake ji please ki bari sai gobe in Allah ya kaimu"
"Arish babu kyau shiga hak'k'in wani"
Zubur ya mik'e tare da kafeta da idanu "ban fahimta ba?"
"Ina nufin ilham ya kamata ace yau ka kwana a d'akinta"
kwanciya yayi yace "tunda surutun bai isheki ba sai kiyi tayi"
"Arish ita ba dutse bace kaji tsoron Allah"
Tashi yayi ya zauna sosai yace "ya kike son ayi kenan?"
"inason itama ka bata hak'k'inta ka kwana a d'akinta yau,Gentle ka kamanta adalci a tsakaninmu"
"Allah ya sani bani da burin auren mata fiye da d'aya,wlh ji nake kamar na saketa amma idan na tuno itace sanadin samun lafiyata sai na kasa,Sumayya bani da kamarki ba macen da zan had'a sonki da nata,naso ace koda da yaushe ke nake gani"
"k'addara gentle,k'addararmu ce haka,ka tashi kawai na maka jagora"
Babu yadda ya iya tunda ta takura masa,dan haka kawai ya tashi ya bita...
Suna tura k'ofar suka jita a bud'e,a kwance kan gado suka ganta,tayi kuwa saurin tashi tana binsu da ido...
"ashe bakiyi barci ba?"
"wallahi kuwa,ina ta son yi amma yak'i zuwa"
"Allah sarki"
Suka d'anyi shiru sannan sumayya ta tashi tace "to sai da safenku"
ta fice ta ja masu k'ofa..
Tana shiga d'akinta ta kulle ta hau kuka,tabbas sai yau ta san zafin kishi,amma dai babu yadda ta iya da k'addararta,kwana tayi tana kuka da zulumi,haka tayi ta jero nafilfili tana rok'on Allah ya basu zaman lafiya.
Tun da Asuba ya shigo d'akinta,ta sake korashi d'akin Ilham,da safe kuwa tare sukayi breakfast su uku,haka tayi ta bawa Arish shawara akan ya danne zuciyarshi,ilham kuwa tabbas ta yarda Arish baya ganin hasken kowa sai sumayya,dan haka ta cigaba da addu'oi Allah ya sa ya dawo gareta.
Satin Sumayya d'aya da dawowa gidan miji,Arish ya nemar mata visa ita da Fatima,sai sumayya daya nema mata admission a Oxford itama,dan haka su uku suka had'u suka tafi,rik'on Khalid ya dawo hannun ilham.....
_1yr later_
Jirginsu ya sauka a babban airport d'in Kaduna,Ilham ce da kanta taje ta tarota tare da twins d'inta mace da namiji da ta haifa a can london _Haashir da hajar_,itama ilham tana nan da tsohon cikinta.
A asibitinsu doctor isma'il ta samu aiki,haka ilham ma,dama course iri d'aya sukayi, nan da nan suka fara aiki tare,sannan Sumayya ta kanje AKTH sau d'aya a sati,ta zama babbar likita,doctor isma'il kuwa kullum cikin tsokanarta yake yana ce mata gawa tak'i rami,haka Fu'ad ma.
Arish kuwa tuni ya saka ana gina masu babban asibiti a cikin gidan.
_5yrs later_
Tuni an saka bikin 'yammatan da suka kammala degree d'insu,Fatima English ta karanta,Sumayya kuwa Architecture duk kansu suka zama cikakkun lecturers,ita Fatima a B.U.K ita kuma Sumayya a K.A.S.U,aka saka bikinsu rana d'aya..
Fatima da Asrar,Sumayya da Ashaz,Zahra da Asiya ma duk sun fiddo miji tare za'ayi bikin,shagaline za'ayi bana wasa ba,daddy zai aurar da biyar uku mata biyu maza,baba kuma d'aya...
A dai dai gab'ar nan kuwa Ilham nada 'ya'ya uku Sumayya kuwa biyu tun haihuwar twins bata sake yin wasu ba,sai yanxu da ake tunanin cikin da ke jikinta triple ne,Farida ma 'yarta d'aya sunan Sumayya Fu'ad ya saka mata suna kiranta da Shahina(princess),Ayrah yaranta biyu duk maza.
Hafsat kuwa ta nutsu sosai,dan tunda taga Fu'ad yayi aure ta saduda,dan haka tana gama karatun itama tayi aure sannan ta cigaba da masters a cairo.
_ARYAAN_
a gurguje,Aryaan kam gaba d'aya kowa ya d'auke masa k'afa dan daya dawo daddy korar kare yayi masa,bilkisu kuwa da k'yar ta bishi,kullum cikin kyararshi take....
in tak'aice muku dai kwata kwata babu k'wan haihuwa a jikinshi haka likitoci suka sanar dashi,Arish kuwa cewa yayi alhakinsune,ya godewa Allah daya nuna masa iyakarshi tun a duniya,Sumayya kuwa tace ta yafe masa...
Amma gaba d'aya komai ya tsaya masa,bilkisu kuwa ta sa dole ya saketa,ya dawo tamkar almajiri,abinci ma gagararshi yake,gashi daddy yace duk wanda ya bari ya shigo masa gida Allah ya isa....
Shekararshi d'aya baya garin bama asan inda yake ba,kwatsam abokin daddy ya zo masa da labarin Aryaan yana wani k'auye kusa da kaduna ya haukace,hauka tuburan.
Allah sarki tsakanin d'a da mahaifi sai Allah,daddy da kanshi ya d'akkoshi ya dawo dashi gidan...
Sumayya kuwa ta saka akayi ordering magunguna,ita ta rik'a treating d'inshi wata uku ya warke yayi nadama sosai,halinshi ya canza,ya zama ustazu.
_KOMAI YAYI FARKO TABBAS YANA DA K'ARSHE_
_Readers sai ku shirya mu tafi musha shagalin gagarumin bikin da za'ayi_
ALHAMDULILLAH
KOMAI NADA LOKACI MAI HAK'URI KEDA RIBA.......💃👯👯♂
Anan muka kawo k'arshen wannan littafin,fad'akarwar dake ciki Allah ya bamu ikon yin amfani da ita,kuskuren dake ciki,Allah ya yafe mana cox shi d'an Adam Ajizi ne....