***Yi tayi kamar bata gansu ba ta wuce dining area taje ta bude fridge ta dauki kwalin lemon abarba guda daya sannan takoma sama tuni lokacin maamy ta shige dakinta shi kuma Khalil yawuce part dinsa zuciyarsa cike da abubuwa guda biyu wato damuwa da kuma farin ciki,bangare daya na zuciyarshi yana farin ciki zai samu abokiyar rayuwa sannan daya bangaren kuma yana bakin cikin tunawa da mosoyiyarshi Ramlat wacce ta tafi ta barshi cikin shauki da kewarta,
Zama yayi a falonshi ya cire p cap din dake kansa ya ajiye sannan yafara kunce igiyoyin dake jikin takalmin combos din dake kafarshi daidai lokacin Hanan ta turo kofa ta shigo tana mai yimasa sallama,
Daga kansa yayi ya kalleta sannan ya amsa mata sallamar yana zare takalman daga kafarshi,
"Masha Allah...." Ta fada acikin ranta saboda yanda yayi kyau ya sake ja cikin kayan jikinsa,zama tayi dan can nesa dashi cikin sanyin murya mai cikeda tsantsar ladabi gamida biyayya tace,
"Sannu da zuwa uncle...."
"Yawwa" ya fada atakaice domin zuciyarshi ce ke wani irin hautsinawa tana yimasa kuna,yarasa meyasa aduk lokacin da yaso yin maganar da ta shafi aure yake samun kansa cikin wannan mummunan halin,
Bata yi kasa agwiwa ba ta sake kwantar da murya tace,
"Ga abinci can saman table,ko akawo nan...?"
Girgiza mata kai yayi sannan ya kwantar da kansa jikin kujera ya lumshe idanuwansa,shi kadai yasan abinda yake ji kuma yasan abinda yake damunsa shiyasa kadaici kadai yake bukata daidai wannan lokaci,
Ganin yaki kulata yayi shiru baya ko motsi yasata fahimtar cewa yau fa yan miskilancinne akusa wannan dalilinne yasa ta tashi tafita ta nufi sashenta tana zuwa tayi shirin bacci tayi kwanciyarta,sai sake sake take yi a cikin zuciyarta tana ta tambayar kanta to yaushe Khalil suka fita da maamy? Ina sukaje? Tambayoyin da ta rinka jujjuyawa kenan cikin ranta amma bata da amsarsu shiyasa zuciyarta ta cika da kunci da bacin rai,da damuwa aranta ta samu nasarar yin baccin ranar.
Washe gari kamar jiya yauma tunda ta tashi da asubah bata sake komawa bacci ba kitchen ta shiga bayan ta kammala taje ta shirya Aryan shirin makaranta,suna falon kasa tana bashi breakfast yana ci lokacin ba afi 7:30 ba anty maamy tafito zata hau sama, Hanan tasan bazai wuce wurin Khalil ba shiyasa ta gaggauta karasa bashi breakfast din taja hannunsa zuwa sama tana cewa,
"Zo muje kayiwa Papa sallama sai kazo akaika school"
Khalil na zaune afalo sanye da farar t shirt da bakin trouser wanda yawuce gwiwarsa da kadan da laptop gefenshi yana duba wani sako ta email dinsa maamy ta bude kofa ta shiga,
"Ranka yadade har antashi?"
"Ba dole na ba maamy.... Mai girma deputy president da kansa yaturo min sako ai dole intashi"
"Haka kam.... To yakake?" Ta fada tana kokarin zama gefen kujerar dake kusa dashi,
"Alhamdulillah,kefa?"
"Lafiya lau wallahi Khalil"
"Any problem?" Ya bukata idanuwanshi na kan system dinshi,
"Ehh to.... Dan Allah idan zaka fita zaku yi dropping dina wurin saloon ina so zanyi kitso...."
Daidai lokacin su Hanan suka shigo kuma kunnuwan Hanan sun samu nasarar jin kalaman maamy,sam Hanan bata nuna tajiba suka gama abinda zasuyi taja hannun Aryan suka fita,
Bata sake komawa part din Khalil ba sai bayan da tayi wankanta ta shirya ta saka wata pink and blue colour din atamfa riga da skirt sannan ta nufi wurin Khalil tana rike da kayan breakfast dinshi,baya cikin falon lokacin da ta shiga sai dai ga system dinshi nan da wayoyinshi zube saman kujera,fita tayi tai maza taje ta ci nata breakfast din cikin sauri sannan ta dawo tana shigowa yana fitowa sanye cikin farin yadi tissue,bai san ko yaushe Hanan ta koyi wannan abun arzikin ba ko da yake ai kullum mutum girma yake yi hankali na kara shigarshi,
Kan dining din ya karasa ya zauna tana biye dashi abaya,dumamen tuwon daren jiya tayi masa da kunun gyada sai yan soye soyenta da tayi,ga mamakinta sai taga ya wanke hannu ya zuba dumamen tuwon yana ci,wai dan Allah Khalil wanne irin mutum ne shi mai saukin kai haka? A wannan level din nasa da wanine ai ko kallon tuwo bazai yiba bare har yaci,
Shiru ne ya mamaye wurin sai shi dake ta faman cin dumamen sa,dan ajiyar numfashi tayi sannan tace,
"Uncle zan bika.... Ina so zanje gyaran gashi da k'unshi dan Allah sai ku saukeni......"
Shiru yayi bai amsa mata ba dan yi yayi ma kamar bai jita ba,ita maamy tace zata bishi itama wannan yanzu tazo tace wai zata bishi to wa zai dauka acikinsu? Tunda shi dai bazai taba hadasu gaba daya su fita tare ba,kuma idan yatafi da Hanan yabar maamy bai kyauta ba haka idan yatafi da maamy yabar Hanan to yayi ganganci ko kuma yaso kansa dayawa saboda ko babu komai Hanan matarsa ce kuma dole akirata da wannan sunan,
"Kaji uncle......" Muryarta ta katse masa tunaninsa,
"Ba yau ba..." Shine amsar da yabata yana wanke hannunshi cikin sink,bata kai ga kara magana ba anty maamy ta shigo taci wata bubu na wani dan ubansun leshi baki mai adon pink sai kyalli yake ta dan yafa mayafi akanta da alama dai tafi son shiga irin wannan,
"Khalil ka gama ne muje?"
Shiru yayi na wasu mintuna sannan yace,
"Maamy kiyi hakuri bazai yuyu mu fita tare ba saboda inada urgent meeting yanzun nan,but zan turo miki driver idan hakan yayi miki....."
"No kabarshi kawai babu matsala bari sai infita da kaina kawai"
"Ok"
Juyawa tayi tafita ita kuma Hanan tafita fuuuu itama alamun wai tayi fushi,bai bi ta kanta ba yawuce yafita shima.
***
Tun bayan dawowar sumayya daga katsina abubuwa suka fara canjawa tsakaninta da mujahid,sai yayita janta yana tsokanarta koda kuwa bata kulashi ba,haka makaranta shine yake kaita ya koma ya daukota,gashi babu dama yaganta da saurayi sai ya koreshi duk wanda yazo wurinta sai ya koreshi,sosai abin yake bata mamaki duk da ta dan fahimci inda yasa gaba amma bata yi saurin bada kai ba,
Yau daga makaranta dan ajinsu ya rage mata hanya domin sun gama lectures daya lecture din ance malamin bazai zo ba,suna zuwa kofar gida tana shirin fitowa mujahid na fitowa daga ciki, parking yayi yaje wurinsu yace tafito, tambayar ta yafara yi wai wanene wannan? Meye hadinta dashi da har zai kawota gida a mota?
"Course mate dinane fa ya mujahid.... Rage min hanya yayi"
Zura kansa yayi cikin motar yace,
"Barka dai.... Dan Allah daga yau karka kara rage mata hanya,koda kuwa itace ta bukaci hakan,kana iya tafiya"
Fuskantarta yayi wacce ke tsaye baki bude saboda tsabar mamaki,
"Daga yau sai yau kar na kara ganinki acikin motar wani da sunan wai yarage miki hanya.... Kina jina?"
"Haba dan Allah ni wai meyasa kake takura minne? Menene dan anrage min hanya? Ni wallahi....."
"Zaki wuce kishiga ciki ko sai na baki mari...."
Wucewa tayi tana kunkuni sai bubbuga kafa takeyi,har yashiga motarsa zai fita ya kashe yafito yabita cikin gidan can dinma sakata yayi agaba da dokoki wai babu ita babu kula kowanne namiji ta inda yake shiga ba tana yake fita ba da ya isheta da fada mikewa tayi tsaye cikin fada tace,
"Wai menene naka idan na kula wani namiji? Ina ruwanka dani?"
Kallonta yayi idanuwanshi cikin nata sannan ya dan sassauta muryarshi,
"Saboda ke tawace..... Ke tawace ni daya sumayya,bazan iya jure ganinki tare da wani da namiji wanda ba niba"
Ai rasa abinda zatace tayi,ta ma rasa wanne irin farin ciki zatayi gaba daya, kwalla ce ta ji ta ciko mata idanuwanta saboda tsabar farin ciki,dama tajima tana mafarkin jin wadannan kalaman daga bakinsa amma bata tsammaci jinsu kwana kusa ba,bata zaci zata jisu a daidai wannan lokacin ba,rufe bakinta tayi da dukkanin hannayenta guda biyu.
***
Ta jima akwance tana kuka tun bayan fitowarta daga part din Khalil ta kwanta tana kuka,haba wannan cin fuska da tozarci har ina? Dan kawai anty maamy tana matsayin kanwarsa sai yarinka fifitata akanta? Duk yanda akayi ba a iya yan uwantaka al'amarin nasu ya tsaya ba sai dai idan akwai wata akasa,ita tana nan tanata wahalar dawainiya da soyayyar shi bai tsaya ya kulata ba a matsayinta na matar aurenshi amma yaje yana kula da wata mace dan kawai yana takamar jininshi ce,
Sam Hanan bata iya samun abu ba shiyasa wuni tayi tana kuka kuma har lokacin bata jin zuciyarta ta huce daga bacin ran dake makale dankare acikinta, Aryan tunda yadawo daga makaranta yake son ta tashi suje garden su hau lilo kuma ta koya masa karatun hisnul ad'fal amma taki tana nan dai kwance kamar ruwa kan gadonta duk idanuwanta akode,
Duk da bawai azumi take yiba amma wuni tayi bata ci komai ba bata saniba yaturo andauki anty maamy din ko bai turoba oho musu,bayan tayi sallar magriba wanka tayi ta saka riga da wando na English wears jeans da t shirt ta dan yafa mayafi ta fita ai karuwancin kowama ya iya kunya ce da kara ke sawa ake nuna kamar ba a iya ba,azo har gidanta anemi takura mata? Wallahi bazai yuyu ba ai tunda anty maamy tasata kuka wallahi itama sai ta sakata kukan kuma shima Khalil din zai gane shayi ruwane dan sai yagane kurensa,umma kadai ta samu a falon kasa sai Aryan dake kan kekenshi yana ta faman zagaye harabar falon,zama tayi suka gaisa da umma anan umman ke tambayar ta wai ko lafiya kuwa kodai jikinne? Murmushi kawai tayi aranta tana tunanin wai har sai yaushe su umma zasu farga su gane cewa babu juna biyu a tattare da ita? Tashi tayi zuwa dining area ta hado golden moon cup biyu ita da Aryan domin shima gwaninshi ne yana son golden moon haka zata yita hada musu suna sha kamar wasu yan boarding,suna nan falon suna taya Aryan kallon cartoon anty maamy ta shigo tabe baki Hanan tayi ta kawar da kanta gefe acikin zuciyarta tana cewa ashe ma bata nan ko ina taje kuma oho? Itama Anty maamyn umma kadai ta kula sai Aryan tawuce bedroom daga nan bata sake fitowa ba,har 10 suna falon kasa da umma suna hira ganin karfe 10 ya dan gota kuma batayi sallar ishah ba yasata hawa sama dan tayi,tana tashi Khalil na shigowa,ai tun ahanya Aryan yasoma tsegunta masa wai mommy tanata kuka tun da yadawo daga school yau ko karatu bata koya masa ba blah blah,
Bayan sun shiga falonshi text massage ya tura mata wai tazo, shareshi tayi ta sake gyara zamanta saman kujerar da take zaune tana kallon tashar zee world,har yayi wanka yafito bata zo ba ga Aryan nan yayi bacci kasa kan rug acikin falonsa,da kanshi yafita ya nufi sashenta, knocking yafara yi sannan yabude yashiga duk zatonta Aryan ne shiyasa bata ma ko dago ba daga kwancen da take da pillow akirjinta ta rungume,
Kamshin turaren sa tafara ji sai kuma tajiyo muryar shi,
"Baki ga kiran da nayi miki bane nace kizo?"
Bata rai tayi sannan ta tashi zaune tana sake babbata fuska,
"Zo...."
Daga haka yajuya yafita ta tashi tabi bayansa tana gwada tafiyarsa harda wani dan sakin doro take yi,shi dai baima san tanayi ba,suna shiga part dinsa bedroom yawuce zai dauko system dinshi ita kuma ko zama batayi ba ta hango anty maamy rikeda karamin flask tana tahowa tashi tayi taje ta sakawa kofar lock,ta dawo ta zauna, knocking anty maamy tafara yi amma Hanan taki budewa zuwa can dai ta tashi taje ta bude amma tayi bake bake akofar ta yadda mammy bazata iya wucewa ba,
"Lafiya?" Hanan ta fada tana kallon gefe,
"Matsa inwuce..."
"Ki wuce ina? Haba anty dare ne fa,ai wannan lokacin na ma'aurata ne,muna cikin tsaka da raya sunna kinzo kin katse mana jin dadi......."
Daga haka ta mayar da kofar ta rufe ta sake danna lock ta wuce ciki tabar anty maamy tsaye baki abude.........................鉁嶐煆?
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:14 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*
43***Tana iya hango anty maamy daga zaunen da take wacce takaici ya hanata ko motsi daga inda take tsaye kawai mamakin maganganun da yarinyar nan ta fada mata take yi,ta dan jima atsaye sannan taja kafafunta wadanda suka yimata nauyi ta kara gaba zuciyarta cike famm da takaicin furucin da hanan tayi mata,
Hanan sake gyara zamanta tayi tana hango lokacin da maamy ta juya ta koma inda tafito dama allah allah takeyi ta tafi kafin Khalil yafito yaganta yaje da kansa yabude mata kofar,ai kuwa tana tafiya sai gashi yafito yana yin waya da alama ma wayarce ta tsayar dashi cikin dakin dan har yanzu bai gama ba,zama yayi a kujerar da yafi zama wacce ke kallon kofa,jin ya ambaci barrister muhsin yasata fahimtar cewa da lawyer dinsa yake yin waya,
Aryan ta dauka ta fita zata kaishi dakinshi ta kwantar dashi kafin Khalil yagama wayar da yake yi,saida ta zauna tayi zaman canjawa Aryan kaya sannan ta fita,part din Khalil ta sake komawa sai kunkumbura baki take yi ita kadai,
Ayanda ta tafi ta barshi haka ta dawo ta sameshi sai dai yanzu ba waya yake yiba laptop dinshi yake dubawa,a kasa ta zauna tana wani turo baki,
"D'anki yace yau ma kinyi kuka,meya faru?" Yafada idanuwanshi na kan system dinshi kyarr,
Jin abinda yace yasata sake turo baki amma batayi magana ba,ai yafi dan dako sanin tasha,yafi kowa sanin abinda yasata kuka tunda shine sila,
"Uhmmmm....?" Ya sake fada batare da ya kalleta ba,
"Da safe ne na tambayi zuwa saloon aka hanani....."
Murmushi yayi jin abinda tace, lallai yarinyar nan yar yice,
"Shine kika zauna kina kuka?"
"Uhmm"
Shiru yayi yaci gaba da abinda yake yi tsawon mintuna biyu taji yace,
"Jeki ki hado min coffee ki kawo min"
Tashi tayi tafita aranta tana mitar dama dan dai yasata aikine kawai yaje ya tasota, kitchen dinta ta shiga,tana cikin hadawa taga diff an dauke wuta akaro nafarko tun bayan zuwanta gidan bata taba ganin an dauke wutaba sai yau, wayarta ta kunna da ita tayi amfani ta karasa ta dauka ta fita wato da ita maamy kawo mishi tayi kenan to sai dai taje tasha kayanta yau bazai sha ba.
Daga shi sai gajeren wando ta sameshi lokacin da ta koma amma jin motsinta yasa shi lulluba t shirt dinsa a kirjinsa,sai tsaki yake yana kiran wani awaya wanda bata san ko waye ba,shi kwata kwata baya shiri da zafi duk da ba wani jikin azo agani gareshi ba amma jin zafine dashi to sai Allah yarufa masa asiri ya iyoshi agidan hutu kullum yana cikin AC,
"Wai meke faruwa da Gen dinne?........ Ok tom"
Daga haka taga ya katse wayar yamike daga kan kujera yashiga bedroom dinsa,ruwa yaje ya watsa ya fito yana fitowa wuta tazo dama wai Gen din aka yiwa juye, jallabiya yasa yafita har lokacin tana zaune tana jiransa,
"Gobe za akaiki saloon din...."
Kamar tace ta fasa sai ta amsa masa,cewa yayi ta tashi taje ta kwanta,tashi tayi ta fita sai faman cika take tana batsewa kamar zata fashe, bai san har lokacin akule take dashi ba shiyasa ma ai yau ko girkin bata yimasa ba ita maamy din da ta fita awurinsa ba sai tayi masa ba.
Juyi ta fara yi lokacin da ta kwanta domin yin bacci sai dai sam baccin yaki zuwa maimakon ma taji alamunsa sai tunanine taji yana bijiro mata adaidai wannan lokaci,bata taba ganin namijin dake burgeta yana jan hankalin ta ba kamar Khalil tsawon rayuwarta, musamman ma yau da ta ganshi cikin yanayin da bata taba ganinsa ba koda yake bama shiba bata taba ganin babban namiji baligi ahaka ba dan ko yaya shamsu zata iya bugar kirji tace bata ganinsa yana zama haka,
Wani irin bege da shaukine ke fusgarta agame dashi,jin zuciyarta takeyi tana wani irin harbawa da karfi, runtse idanuwanta tayi tana fatan bacci ya dauketa ko wai zata samu ta huta da wannan tunane tunanen amma hakan bai samuba har wurin k'arfe 1:30 dakyar da addu'a tasamu tayi bacci a wannan dare,
Washe gari bayan ta shirya Aryan yatafi makaranta itama shiryawa tayi cikin wata jar atamfa mai zanen camera ajiki,sashen Khalil ta wuce dauke da kayan breakfast a hannunta,tana shiga ta wuce kan dining ta soma shirya masa tana gamawa ta koma ta rufe kofa b'am ta dawo ta zauna tasan yanzu haka anty maamy tana kan hanyar zuwa sai kace wata matarsa kullum tana manne dashi,wani dogon tsaki taja saboda kishin da ke ciciyar zuciyarta wanda ita bata ma gane ba kawai dai tasan tana masifar jin haushin anty maamy sannan tana jin haushin yanda take shisshigewa Khalil duk da yar uwarsa ce,
"Keda wa?"
Juyawa tayi sakamakon jin muryarshi da tayi abayanta yana tsaye ya dafa kujerar da take kai shirye yake tsaf cikin shirin fita office yau kam yafi koda yaushe yimata kyau saboda abaturensa yafito sak domin suit yasaka bakake amma farar t shirt mai dogon hannu wacce keda kwala yasa aciki,
"Tsarki ya tabbata ga mahaliccin wannan kyakkyawar halitta.... Masha Allah" Ta furta can kasan makoshinta,kasa dauke idanuwanta tayi daga kansa ahaka suka gaisa ya nufi dining tabishi,dan wake da yaji da man gyada da vegetables ta zuba masa harda dafaffen kwai sai kunun farar shinkafa mai dauke da gyada da madara,kai masha Allah shima hakan yaketa nanatawa cikin ranshi saboda tsabar dadin da abincin yayi masa,yana masifar son irin girke girken nan amma baya samu sai idan yaje gombe,
Kiran Khalid ne yashigo cikin wayarshi saboda tun daren jiya yatura Khalid din text massage yana yimasa maganar daidaita kansu da sukayi da maamy yanzu wani abu kadai yake jira sai yasanar da gida,yasan Khalid zaiyi farin ciki saboda dama maamy kanwarsa ce shikuma amininsa ne,
"Kai baban yan uku ya akayi?" Khalil yafada cikin raha,
"Lafiya lau babban mutum,ya aiki? Ya Aryan?"
"Yatafi school...... Kaga sakona ko?"
"Ehh naga abin farin ciki,wai ya akayi hakan ta kasance? Kodai kun tuna tsohuwar soyayya ne?"
Kamar tv haka Hanan ta sakashi gaba tana kallonsa, Kai wannan mutum da kyau yake,ga nutsuwa ga kuma aji,shagala tayi da kallonsa shiyasa ma bata samu damar ganin tahowar anty maamy ba kawai sai knocking dinta taji,da hannu Khalil yayi mata alama wai taje ta bude,mikewa tayi cike da bacin rai ta nufi kofar tana harare harare ita daya,tana zuwa ta tsaya bakin kofar kamar yadda tayi jiya,anty maamy tasha kwalliya cikin doguwar riga ta shadda hadaddiya peach,
"Anty maamy gaskiya bazan boye miki ba kina shiga hakkinmu..... Wai meye tsakaninki da mijina da har zaki rinka shigowa part dinsa kullum? Nidai agaskiya kina takura min sannan kuma nagaji...."
Murmushin takaici anty maamy tayi,
"Bani wuri inwuce ni ba gunki nazo ba gurin mijinki nazo"
"Toh ai duk daya..... Koba wurina kika zoba tunda kika zo wurin mijina ai baki nemi zaman lafiya ba,nifa kina shigar min hakkina kuma bazan lamunta ba..... Nayi kara nayi kara har nagaji"
"To yanzu zaki bani hanya inwuce ne ko yaya?"
"Gaskiya sai dai ki koma inda kika fito dan wallahi bazaki shiga ba,haba ya wai nida gidana nida mijina amma ahanani sakewa?"
Turata anty maamy tayi zata wuce nan kuwa ta dage karfinta ta dawo da ita baya tana kokarin mayar da ita waje abu sai yakoma fada fada kokawa kokawa,wayar da yake yi ya katse yamike domin kamar hayaniyar su yake jiyowa,mamakine karara ya bayyana akan fuskarshi lokacin da ya iskesu suna kai ruwa rana ita Hanan ta daddage tayi bake bake abakin kofa tana hana maamy shiga ita kuma maamyn itama ta dage tana kokarin ita alallai dolen dole sai ta shiga,
"Maamy..... Menene haka?" Yafada idanuwanshi akansu su duka biyun,
"Wai daga nazo inaso zan shiga wurinka shikenan yarinyar nan ta daddage ta hana wai bazan shiga ba...."
"Meya faru?" Ya maida kallonsa kan Hanan gaba daya wacce ta bata fuska ta hade rai tana ta faman gurmude gurmuden baki sai karkada jiki takeyi alamar masifa da bala'i karara,jin tambayar da yayi mata yasata kallonshi sannan ta kawar da kanta gefe tana hararar anty maamy,
"Abinda ta fada maka shi akayi,ba ita kafara tambaya ba....?"
Bashiba ita kanta maamy saida kalaman Hanan suka bata mutukar mamaki kuma suka daure mata kai mutuka gaya,yanzu yarinyar nan ce ke fadawa Khalil haka agabansa bawai abayan idonsa ba? Shi kuwa dama yasan hali yasaba da rashin kunyarta sai dai ma yabawa wani labari shiyasa abin bai wani dameshi ba sannan shi mutum ne mai hakurin gaske sau tari sai dai mutum ya cuceshi amma shi yakan jima kafin ya nunawa mutum rashin hakurinsa,
"Ehh ai ta fada min kuma naji nata yanzu naki nake son ji shiyasa na tambayeki....."
"Takura min take yi duk lokacin da ta shigo min b'angaren mijina,jiya cikin dare tazo nace bazata shiga ba yauma ta sake dawowa to menene ma'anar hakan? Wannan safa da marwa din ya isa haka...."
"To yanzu me kikeso ayi? Yar uwata ce fa"
"Duk da yar uwarka ce ai bai kamata ta rinka shigo mana ba anyhow,ya za ayi ace ni banda sirri? Shikenan kuma har turakar mijina sai wata mace tagani? Ni karta kara shigowa sashenka idan gaisawa ne tajira duk lokacin da ka sauka k'asa sai ku gaisa...."
Shi gaba daya ma mamaki Hanan take bashi saboda yanda ta fututtuke ta hakikice tana tada jijiyar wuya wai harda cewa maamy karta kara shigar mata turakar miji,
"Yanzu ke idan akayi hakan kin kyauta kenan? Fada da bakuwa? Kwana nawane zata taf...."
"A'a wannan yanzu ba bakuwa bace ai tajima da zama yar gida....yau kwananta nawa agidan?"
"To yanzu dai kar na kara ganin kinyi mata irin wannan babu ruwanki da ita,ba wurinki take zuwa ba wurina take zuwa...."
"To wallahi ni bazan zauna da ita ba agidan nan,zanje intafi gidanmu inyaso ita taci gaba da zama tare daku......."
Fuuuuhhh tayi waje tabarsu awurin tawuce sashenta hawaye na karakainar zubowa daga cikin idanuwanta,tana zuwa ta janyo babban akwati daga cikin na lefenta tasoma kwaso kayanta na sawa tana zubawa aciki wanda kawai cakuda su take tana hautsinawa aciki babu wani jerawa ko shiryawa,
Jiki asanyaye maamy tajuya tabar Khalil tsaye ta sauka kasa zuciyarta duk babu dadi, Kai tashin hankali baiyi ba arayuwa me za ayi da bacin rai,
Shi kuwa Khalil ciki yakoma ya dauko wayoyinsa yasaka bakin takalmi sau ciki yafito yasauka kasa,a babban falon kasa yasamu Hanan da umma barira wacce keta faman riketa tana bata hakuri akan ta janye maganar tafiya gidan da ta dage sai tayi amma taki sai jan uban akwati take yi,
"Wai meya faru ne? Mu'azzam meke faruwa?" Umma barira ta tambaya tana kai dubanta gareshi,
"Umma ni bazan zauna tare da anty maamy ba,sai dai azabi daya ya zauna tsakanin nida ita acikin gidan nan.... Wallahi tafiya zanyi"
Lamarin Hanan gaba daya mamaki yake bashi wai yarinya duk tabi ta burkice tace ita lallai lallai sai maamy tabar gidan,to wai menene azuciyar yarinyar nan? Kafin yayi magana fuuhhh yaga taja akwati ta nufi kofa ita kuma umma ta tsaya cak tana kallonsu tama rasa me zata tsara balle tasamu ta cewa,bin bayanta yayi tana ta kokarin yafa jan mayafin dake hannunta cak numfashinta yanemi daukewa sakamakon rikon da taji yayi mata wanda har saida yayi sanadiyyar haduwar jikinsu wuri daya...............................鉁嶐煆?
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:14 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*
*44*
***Fuskarta ya tallafe da dukkan hannayensa guda biyu masu tsananin taushi hakan yasa ta lumshe idanuwanta wanda yayi sanadiyyar zubowar wasu tagwayen hawaye ajere,
"Meyasa bakya jin magana ne? Kina musu dani ko? Ga gardamar tsiya kamar sabon angon jaki...... Kina son infadawa abbanki?"
Girgiza kai tayi tana cigaba da b'arin hawaye afuskarta,
"To yanzu da kika debi wadannan uba uban kayan cikin akwati ina zakije? Kin gaji da zama da mune?"
Kai ta sake girgiza masa har lokacin idanuwanta a rufe suke sai hawaye dake ta faman malala,
"Kar ki tafi ki daure ki zauna ko dan d'anki Aryan.... Yanzu idan yazo ya iske bakya nan wanne irin hali kike tsammanin zai shiga? Kar ki tafi kibar d'anki idan kuma kin dage sai kin tafi to kibari yadawo sai ki hada masa nasa kayan kutafi duk inda zakije tunda ni kin gaji da zama tare dani...."
Sai lokacin ta bude idonta ta kalleshi shima ita yake kallo ko kiftawa bayayi ita dai tasan kawai yafada ne amma ya za ayi yabata Aryan yace wai sutafi duk inda zataje ai ko giyar wake yakesha bata jin zata yi masa tasiri anan,
Kai ya jijjiga mata alamar tabbacin abinda yafada,daga haka ya saketa daga rikon da yayi mata yawuce yafita yana kokarin gyara necktie dinshi,
Tafi minti biyar tsaye wurin ta kasa koda kwakkwaran motsi har umma barira ta karaso tazo tana mai sake bata hakuri akan karta tafi tunda bada mijinta sukayi fada ba to babu amfanin tabar gidan wai da sunan yaji,
Juyawa tayi ta ja akwatinta ta nufi ciki dakyar ma take jan akwatin saboda kayan da ta loda ba kadan bane sai kace wacce idan ta tafi zatayi shekara agidan,har bedroom dinta umma ta rakata tana sake bata baki tana cemata kowa kagani agidansa hakuri yake yi amma akwai matsalar da take tare dashi,
Bayan fitar umma Data ta kunna awayarta ta hau online saboda tana son ta dan debewa kanta kewa amma acan kasan ranta ta kuduri aniyar itafa bazata cigaba da zama da anty maamy ba sai dai ayi wacce za ayi.
Har Khalil yaje office bai daina mamakin abinda Hanan tayi ba,to wai me zai kira wannan lamarin nata dashi? Kishi ko kuruciya? Gaba daya yarinya ta dage sai ta kori maamy daga gidan,yana shiga office kiran maamy yashigo masa, dauka yayi muryarshi asanyaye kamar kullum,
"Ibrahim ni nagama shirya kayana zan wuce gombe......"
Dan jimm yayi sannan yace,
"Ban gane zaki wuce gombe ba..."
"Ehh zan koma gidan ubana mana,inbanda matarka ta samu dama wai har ni zata yiwa gorin gida? Taje ta tambaya waye ubana,kai kanka kasan ubana yanada gidajen da bazasu lissafu ba,ni kaina inada gidaje sunfi goma mallakina amma wai ni ake yiwa gori akan gida nida gidan mijina akasar turai yake amma wai yau saboda nazo gidanka karamar yarinyar da bata fi sa'ar autar gidanmu ba take kokarin wulakanta ni..... Nagode"
Kitt ta katse wayar,rabuwa yayi da ita bai kara kiranta ba saboda yasan yanzu ranta abace yake ko daga kalaman da take yi yasan akule take maamy kuma badai zuciya ba,rabuwa yayi da ita har zuwa yamma lokacin da zai tashi daga office inyaso sai yabita can gomben ya wanke kansa.
Misalin karfe 6 yatashi daga office kuma direct hanyar gombe suka kama wanda basu suka isa ba sai bayan sallar magriba,salla yafara yi sannan ya karasa gidan Alhaji Idris kanwa mahaifin maamy,bai samu abban agida ba kasancewar baya gari, Jawad yatura yace yayi masa sallama da momyn su nan Jawad din ya ruga da gudu ya nufi can cikin gida,
Maamy tana gaban mirror tana tsala kwalliya tamkar wata budurwa dan ko da wasa bata daukar kanta a matsayin wata babba ta azo agani duk da tana da samarin yaya da budurwar 'ya,
"Mommy kizo inji uncle Khalil...."
"Yana ina?"
"Yana falon abba na kasa"
"Ina zuwa to"
Fita jawad yayi ita kuma ta tashi ta karasa shiryawa cikin doguwar riga ja tasha turare sannan ta dauki dan siririn mayafinta ta fita tana takunta mai cike da nutsuwa da daukar hankali,
Zaune ta sameshi ya dora kafarshi daya akan daya yana duba wayarshi,zama tayi gefenshi bayan tayi masa sallama,
"Haba amarya irin wannan fushi haka kuma? Sai kace dani akayi fadan....."
Wani kallo tayi masa kafin ta rausayar da kanta gefe,
"Ai wannan matar taka sai Kai..... Kasan wani abu? Wallahi bazan zauna gida daya da ita ba, tun wuri ma ni ka sama min gida amma banda wannan..... Ban son rashin kunya"
Murmushi Khalil yayi ya shafi sajensa,
"Kinji tsoro kenan?"
"Ba maganar tsoro anan fa Ibrahim gaskiya ce"
"To Allah dai yabaki hakuri,dan Allah ki dauki abinda yafaru yau amatsayin ba komai ba saboda kinga ita yarinya ce,yanzu ne ma take sanin yaya rayuwar take......"
"Nifa banda case da ita,kawai nidai bukatata awurinka shine karka hadamu gida daya dan bazamu zauna lafiya ba...."
"Baki da matsala a wannan bangaren Maryam,insha Allah zanyi yanda kike so......., Yanzu ina son zan karasa wurin hajiya mu gaisa sai inkoma Abuja,dan nan nafara zuwa"
"Ayya babu matsala,ka gaida min da ita"
"Zata ji insha Allah, shikenan intafi an sallameni?"
Murmushi tayi ta dan fara idanuwanta alamun shagwaba,
"Da ance maka kai mai laifine?"
"Ehh mana ranki yadade..... Za dai muyi waya insha Allah"
"To babu matsala yallabai,muje in taka maka"
Har inda motocinsa ke ajiye ta rakashi aka bude masa yashiga sannan tajuya tawuce cikin gida,shikuma suka nufi gidan hajiya can dinma bai wani zauna ba dan ana kiran sallar ishah yafito bayan sun gabatar da salla suka juya abuja zai koma ya tarar da yar rigama Hanan,karo na farko da yayi tunanin abinda ya shafeta har yayi dariya shi daya,gaskiya yarinyar nan case ce,wai,wayarshi ya ciro ya soma kiran layin Aryan.
Ita kuwa Hanan bayan tafasa tafiya ta mayar da kayanta ciki sai da ta zauna ta sha kukanta sannan tayi shiru wannan dinma zuwan umma ne wacce ta tisata agaba tana ta faman bata hakuri tana cemata shi dama zaman aure gaba dayansa hakurine yafi yawa acikinsa kai bama iya zaman aure ba ita kanta rayuwar gaba dayanta hakuri ce dan haka ta dauki wannan abun da yafaru amatsayin ba komai ba kuma taci gaba da yiwa mijinta biyayya,
Tsamm tayi ta tsaida hankalinta da tunaninta wuri guda tana mai cigaba da jujjuya maganganun umma acikin ranta duk da cewa umman adunkule ta bata maganar bawai zama tayi tai mata ita dalla dalla ba amma akwai alamar tana bukatar tayi wa dukka maganganun duba na tsanaki domin umma cemata tayi taci gaba da kyautatawa mijinta saboda zuciya ahar kullum tana son mai kyautata mata sannan ta guji fushi da bacin ransa,to tayaya zata guji wadannan abubuwan? Dole tana bukatar daura damarar kulla abota da hakuri da gujewa duk wani abu da ka iya bata ransa sannan umma tace duk runtsi duk tsanani karta karaya daga fafutukar yakin neman cikar burinta taci gaba da fadawa Allah dukkan bukatunta haka kuma ta jajurce ta tsaya tsayin daka har sai hakarta ta cimma ruwa,
Murmushi tayi aranta tana tambayar kanta to kodai umma ta fahimce cewa tana son Khalil? Ko umma ta gano sirrin da taketa boyeshi acikin zuciyarta ita kadai wanda bata fatan wani mahaluki ya fahimta baya gashi wanda take yi dominsa? Cigaba tayi da aikinta acikin tamfatsetsen kitchen dinta mai dauke da komai da komai na bukata wurin girke girke,dama tasan bazai dawo da wuriba shiyasa itama bata tarki aikin da wuriba har sai da tabari la'asar tayi liss sannan tafara,tuwon semovita ta dora saboda Aryan yanata damunta da tambayar wai "mommy tuwo zaki dafa mana?" Wannan dalilinne yasata dora tuwon semovita miyar shuwaka, farfesun zabbi da kuma kunun shinkafa. A kitchen magriba tayi mata,agurguje ta karasa aikace aikacenta sannan ta kwashi na umma ta kai mata can ta isketa tana ta drama da mutumin nata Aryan ita dai da yake bata yi salla ba komawa sama tayi taje tayi wanka sannan tayi salla bayan ta idar ta koma k'asa dauke da tuwon da zata bawa Aryan,
Anan umma ke sanar da ita tafiyar anty maamy wadda sam ita Hanan bama tasan cewa ta tafi ba sai yanzu da umma ke bata labari,
"Allah yaraka taki gona......" Shine abinda Hanan ta fada acikin zuciyarta,afili kuwa sai kawai tayi murmushi tana sauraren umma,
Yau sun jima sosai da umma wacce keta yiwa Aryan tatsoniya har saida yayi bacci,daukarshi Hanan tayi a kafadarta ta nufi dakinsa dashi ta kaishi ta kwantar,daga can kuma part dinta ta wuce tana kallon agogon dake kan wayarta karfe 11 na dare harda wasu mintuna,shirin bacci tafara yi itama bayan tagama ta saka dogon hijab ta fita,kanta tsaye sashen oga ta nufa wanda dawowarsa kenan dan ko minti biyar baiyi ba da shigowa cikin gidan,wani abun mamaki kuma wai sai yanzu ne taji tana jin kunyar abunda yafaru da safe sai yanzu take jin kunyar rufe idanuwanta da tayi ta zazzaga masa rashin ta ido,
Tana shiga falon yana fitowa jikinsa sanye da rigar wanka fara, hannunshi rike da charger da alama wayar shi zai saka ajikin chaji, sunkuyar da kanta kasa tayi tana yimasa sannu da zuwa daga bisani ta mike tafita domin kawo masa abinci kamar kuwa tasan dama yunwa yake ji saboda rabonsa da abinci tun wanda yaci da safe. Yana zaune yayi nisa kadan aduniyar tunanin da ya tafi tabbas yana son maamy bawai so irin can mai zurfin nanba amma kuma wani lokacin sai yaji kamar yafasa auren nan domin shi yanzu gaba daya mace bata gabansa bawai dan baya bukatarta ba a'a saboda kawai ruhinsa da tunaninsa gaba daya kacokan suna ga Ramlat,iya gangar jikinsa ce kadai anan ita kanta wannan yarinyar Hanan kawai yana zaune da itane saboda Aryan,amma har gobe Ramlat ce abirnin zuciyarsa, shigowar Hanan bayan tayi masa magana shine yayi sanadiyyar dawowarshi daga tunanin da ya zurfafa acikinsa,
Cikin sanyin jiki da na murya yace ta zubo masa tuwon guda daya,zubo masa tayi sannan ta zuba masa kunu cikin cup da farfesun da tayi agefe takai masa gabansa,samun wuri tayi ta zauna duk da ta dan fara jin bacci sama sama domin 12 ta kusa,lura da gyangyadin da yaga tana yi yasashi fadin,
"Je ki kwanta sai da safe,nagode......"
Tashi tayi tana lullumshe ido ta fita,tana zuwa daki ta fada kan gado tana zare hijabin dake jikinta babu jimawa bacci ya dauketa,
Shi kuwa Khalil yana can yana sakawa da kwancewa yarasa meyasa aduk lokacin da maganar aure ta fara shiga tsakaninsa da wata mace sai yasamu kansa cikin mugun hali sai yaji gaba daya kunci da damuwa sun rufeshi koda yake yasan hakan bai rasa nasaba da tsananin kaunar da yake yiwa Ramlat,lumshe idanuwansa yayi yana mai barwa Allah zabi,idan har aurensa da yar uwarsa maamy alkhairi ne to Allah ya tabbatar idan kuma babu alkhairi Allah ya canja musu da mafi alkhairi.
3:30 AM
Daidai wannan lokaci Hanan ta farka daga nannauyan baccin da take yi,yanda taga yanayin d'akin nata sai ta dan tsorata domin kamar anshigo mata dan ga kofar dakin nan abude alhalin kuma ita ta rufe sai dai bata saka mukulli ba,wuta ta kunna ta sad'ad'a taje ta rufe da key sannan ta wuce bathroom tayi abinda zatayi ta gama tazo ta sake kwanciya tana dauko wayarta daga karkashin pillow dan ganin time, text massage taga anturo mata da kamar ba zata budeba sai kuma ta bude nan taga abunda yayi nutukar razanata kuma yasata cikin tunani sakamakon ba sanin wanda yaturo sakon tayi ba...................................鉁嶐煆?
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:14 AM - Ummi Tandama: 45
***Gabanta ne yasoma faduwa saboda sako aka turo mata mai cike da kalaman soyayya tsantsa wanda kuma ba sanin number din tayi ba,kasa komawa bacci tayi tanata faman sak'awa da warwarewa,to ko waye wannan kuma? Innalillahi,shine abinda take ta faman nanatawa acikin zuciyarta,shiru tayi tana tunanin abinda yadace tayi daga karshe dai ta tattara sakon da mai turo sakon ta watsar da tunaninsu tayi kwanciyarta tana fatan sake komawa wani baccin,
Daidai wannan lokacin shikuma Khalil ya idar da sallolinsa na dare kamar yanda yasaba yahaye saman gado ya kwanta yana son ya huta, tunani kwaya daya shine keta faman kaiwa da kawowa cikin kwakwalwarshi wato tunanin auren maamy,yanzu shikenan ta tabbata yaci amanar Ramlat? Yanzu shikenan ya saba alkawarin da yajima yana yiwa Ramlat akan bazai taba auren wata 'ya mace ba bayan ita? Shi yanzu abinda yafi damunsa kenan dama ita Hanan ba a ta ita domin yanada hujja da dalilin aurenta,har yayi bacci tunanin dake cikin ransa kenan.
Washe gari karar shigowar text massage ne ya tada Hanan daga bacci,bata budeba tawuce toilet kai tsaye domin ta so ta makara,cikin sauri sauri ta ke gabatar da komai har ta kammala sannan ta shirya Aryan,sai da yahau sama yaje wurin abbanshi sannan yazo yawuce makaranta,ita kuma daki ta koma tayi wanka tafito sai lokacin ta bude sakon da aka turo mata tun dazu, number din jiyace kuma yanzun ma sakone na barka da safiya mai dauke da kalaman soyayya,lumshe idanuwanta tayi aranta tana fatan inama inama.... Inama ace wanda zuciyarta take bege take mutukar kauna shine ke turo mata wadannan kalaman ai da tayi tsalle akan kaya saboda tsabar farin ciki.
***
Rayuwa haka taci gaba da tafiyarwa Hanan cikin gidan Khalil duk da babu wani sauyi a zamansu amma idan tace bata jin dadin zaman gidan tayi karya,har ila yau Anty hasinah naci gaba da bata shawarwari da kwarin gwiwar hanyoyin da yakamata tabi domin mallaka da siye zuciyar mijinta wanda amafi yawan lokuta tafi kwatanta shi da bahago,miskili kuma murdadde domin kamar bai san wadannan abubuwan da take yimasa ba shiyasa duk tabi ta kare ta sake bushewa saboda tsananin damuwa domin ita tana sonshi kullum ta Allah da sabuwar soyayyar shi take wayar gari amma kamar shi baya ganewa, sannan wani abun karin takaicin shine wasu zafafan massages da ake turo mata kullum safe da rana da dare wanda takasa gane ko waye sai dai tanata addu'ar Allah yasa muradin ranta ne.
Abinda Hanan bata saniba shine shikam Khalil tuni shirye shiryen bikinsa da anty maamy yayi nisa domin har sun kai maganar gaban iyaye bayan sun gama shirya yanda suke son abunsu ya kasance,duk da wani lokacin idan ya kadaice kansa ya zauna sai yayita tambayar kansa Wai meyasa zaiyi auren nan ne? Wani bangare na zuciyarsa na son yayi auren yayinda wani bangaren kuma ke adawa da hakan,
Daurewa dai kawai yakeyi akan maganar auren nan tunda har anyanke lokaci bayan babbar salla da sati uku kamar yadda ita amarya maamy ta bukata,shima uban gayyar hakan yayi masa shiyasa ya sanar da Abban London wanda shine zai nema masa auren kuma gaba daya family kowa yayi farin ciki da murnar wannan al'amari dake shirin kulluwa nan wasu cikin dangi ke fadin ai dama tun suna yara budurwar shi ce ashe da rabon aure,ita Hanan koda wasa bata san abinda ke faruwa ba saboda dama can shi zuwa gombe bata yimasa wahala shiyasa yanzun ma idan yace yatafi gombe bata jin komai aranta,
Yau kam tun kafin ta kwanta bacci ta gama shirya kayanta saboda Khalil yace mata ta shirya gobe zasu tafi gombe saboda acan zasuyi salla shi dama agida yake salla karama da babba,
Washe gari tare da Aryan suka je school dinsu ta rakashi saboda ranar za abasu hutu,taji dadin zuwan da tayi sosai domin daliban makarantar sun shirya wasanni kala kala dan nishadantar da iyayen yara wadanda suka samu damar halattar bikin rufe makarantar,
K'arfe 2 saura suka dawo gida nan suka fara zaman jiran Khalil saboda sai yataso daga office zasu tafi ai kuwa kamar yadda Hanan ta tsammata sai dab da magriba yazo nan suka tattara suka tafi,umma barira da Aryan motarsu daya shikuma oga da Hanan suma mota daya suka shiga dukkansu sun kame agidan baya,zaman kurame yau dinma sukeyi kamar koda yaushe,ajiyar zuciya Hanan ta dan ajiye sannan ta saci kallon sa tace,
"Abban Aryan nidai da son samune inyi salla a kano....."
Idonshi na kan jaridar daily trust dake hannunsa yabata amsa da,
"Saboda wanne dalili?"
"Nafa jima rabona da gida....." Ta fada cikin shagwaba,
"Shine kadai dalilin?"
"Dan Allah....."
Shiru taji yayi hakan ya tilastata itama yin shirun tana zunburo baki duk da tasan ba ganinta yake yiba. Bayan sallar ishah suka shiga cikin gombe kai tsaye cikin gida suka wuce tun daga lokacin basu kara ganin Khalil ba dan ko shiga gidanma baiyi ba lokacin, wannan karonma sun samu tarba ta girma da karamtawa daga daukacin jama'ar dake rayuwa agidan lokacin salla saura kwana biyu kacal,
Tun bayan zuwansu rabonta da Khalil dan ko da safe lokacin da takai masa breakfast baya nan har yafita sai ajiye masa tayi afalo tadawo,suna tare dasu Sarah da Rufaida hajiya ta dauko musu mai k'unshi tana ta yalyala musu text massage din Khalil yashigo wayarta gashi lokacin kunshin kafarta bai busheba bakin amma jan yayi dan harma ancire,
_Zo ina part dina._
Abinda taga yarubuto kenan,babu yanda zatayi haka dole ta tashi da kwayayyen zani tabi ta baya saboda mutane ta nufi sashen nasa,yana baje falo yana cin kilishi cikin wata babbar takarda da waya a kunnenshi,wuri ta samu ta zauna tana kallonsa kallo na kurulla aranta tana gulmarsa ita daya wai har yanzu bai fara furfura ba domin babu ko kwaya agashin kansa,
"Idan kin gama gulmar ga kayanku nan keda Aryan....."
Jin abinda yafada yasata saurin dauke idonta daga kan sumarshi,
"Gulma kuma uncle?"
Bai bata amsa ba maimakon haka ma sai taji yace,
"Wannan menene aka mammanna miki?"
"Lalle ne fa...."
Jijjiga mata kai yayi, nannade kilishin da yake ci yayi yasaka mata cikin leda sannan ya mika mata,karba tayi ta tattara kayan da yakira da nasu ita da Aryan tafita.
Bata kara sakashi a idonta ba sai ranar salla yasha manyan kaya farare tas andawo daga masallaci dama ita bataje ba saboda ta tashi tana fashin salla,gidan gaba daya cike yake da baki daga wurare daban daban sai rabon kudi da danyen nama yake yi domin ya yanka shanu da raguna sun kai talatin duk wanda yazo maroka da mabukata sai ancika masa leda Viva da nama,sai bayan da yayi sallar la'asar sannan yafita. Wannan karonma kamar karamar salla sun yi ziyarce ziyarcen gidajen dangi da yan uwa,washe garin salla suka tafi katsina gidan yayarshi saudat wannan shine karon Hanan nafarko da taje gidan anty saudat kuma ta karbeta hannu bibbiyu basu wani jima sosai ba suka tafi nan kuma kano suka wuce direct gidansu Hanan ai tun acikin mota hanan ke murna kamar zatayi tsalle,
Ta samu gidansu cikin wadata da walwala domin suma saniya suka yanka da raguna guda biyu kuma duk Khalil ne yakawo banda kayan salla da ya aiko dasu wadanda za arabawa dangi,wuni guda yabarta tayi agida dan har gidan anty salaha suka je a tsattsaye daga nan suka juya gombe,yauma Hanan harda kukanta wanda bai san ko kukan me zai kirashi ba shin kukan shagwaba zai kirashi ko kukan sakarci?
"Ke Wai bakya girma da kuka?" Taji yace da ita lokacin da take share hawaye da gefen mayafinta,dole yafadi haka mana tunda shi yana zuwa gida yana ganin kowa nashi aduk lokacin da yaso ta ayyana hakan acikin ranta.
Washe garin salla da kwana uku suka koma Abuja inda akaje aka cigaba da zama irin na da,gashi kullum mai turo mata sakon nan bai daina ba yi yake ita kuma bata ko bi takai dan bata san waye ba,
Bikin maamy da Khalil kam kullum kara karatowa yake yi domin saura sati daya da yan wasu kwanaki angama komai sadakine kadai yarage Khalil bai bada ba amma har gidan da maamy zata zauna da komai da komai yagama shiryashi.
K'arfe 11 saura minti shida agogon bangon dake cikin falonsa yanuna,zaune yake akan sofa yana sanye da farar t shirt mai tambarin Nike ajiki da farin dogon wando mai santsi yana tura wasu bayanai ta laptop dinshi, Hanan yake ta jira ta kawo masa coffee din da yaturata ta hado masa amma shiru kamar wacce aka aiki bawa garinsu,
Bai kai ga gama tunaninsa ba ta turo kofa tashigo,sanye take cikin kayan bacci riga da wando marassa nauyi shiyasa ta dora dogon farin hijabi akai,gabansa takai ta ajiye kan center table sannan ta nemi wuri ta zauna,
"Gashi...."
Kai ya daga mata sannan cikin taushin murya yace,
"Thank you"
Shiru tayi kawai ta dan yi murmushi tana mai cigaba da satar kallonsa,zuwa can ta mike saboda bacci take ji,
"Saida safe...."
"Ok Allah yakaimu"
Ya furta yana binta da manyan idanuwansa masu haske, yarinyar tana dan bashi tausayi kadan saboda yanda take dawainiya da Aryan da kuma shi kansa wani lokacin domin kullum cikin fama take da girkin abincin da zai ci da gyaran sashensa kamar wata house girl,watsar da tunanin yayi yaci gaba da aikinsa yanayi yana kurbar coffee din da ta ajiye masa wanda bashi yagama ba sai misalin karfe 1 na dare,
Tattare komai yayi zai wuce bedroom dinshi nan yaji k'arar wayar Hanan wacce ta manta,idonsa ne yakai kai bayan tagama kara alamar shigowar sako,komawa yayi ya dauki wayar zuciyarshi na tambayar shi to waye yaturowa yarinyar nan sako adaidai wannan lokaci? Tambayar da yaketa yiwa kansa kenan saboda ko babu komai ai a karkashin ikonsa da kulawarsa take dan haka wajibine yasan dukkan motsinta da kuma mu'amularta da kowa, ajiye wayar yayi tare da sauran wayoyinsa akan gado yawuce bathroom yaje ya dauro alwala yafito,fitowarsa tayi daidai da shigowar wani sakon cikin wayar Hanan,zama yayi gefen gadon ya dauki wayar tata luckily babu wani lock ajiki nan yabude sakonnin yasoma karantawa idanuwanshi aware bakinsa abude alamar mamaki..............................鉁嶐煆?
_Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din._
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:14 AM - Ummi Tandama: 46
***Idanuwansa aware bakinsa abude alamun mamaki yasoma bude sakonnin yana karantawa daya bayan daya wadanda ke dauke da kalamai na soyayya,
Kasancewar abun yayi mutukar bashi mamaki shiyasa bai tsaya wuri daya ba dan koda yagama karanta wanda aka turo yanzu cigaba yayi da bude sauran sakonnin dake cikin inbox din nata yana dubawa,shi kansa bai san dalili ba amma dai bai ji dadin wannan al'amari ba sam baiji dadin ganin sakonnin da yagani ba saboda har da na mujahid duk yagani,to Hanan wacce irin yarinya ce? Koda yake dama yajima da fahimtar cewa akwai wanda take so wanda ta mallakawa zuciyarta shikuma yazo yayi musu karfa karfa ya aureta,
Gaba daya ji yayi kansa ya kulle yarasa ma wanne irin mataki yadace ya dauka akanta,ya za ayi tana gidansa karkashin ikonsa a matsayin matarsa amma wani gardin banza acan waje yana turo mata sakonni makamantan wadannan?
Raba dare yayi yana binciken dashi kansa baiga alfanunsa ba acikin wayar tata ko ina saida yaduba hatta nata sakonnin da ta tuttura saida yabude yagani bayan ya gama ya kashe wayar ya ajiye cikin bedside drawer sannan ya kwanta zuciyarshi cunkushe da fushin da bai san hujjarsa ba.
Hanan bata da masaniyar abinda ke faruwa shiyasa bayan tayi sallar asubah ta wuce kitchen kamar yadda ta saba ta dorawa oga breakfast,tana ta tunanin to a ina ta ajiye wayarta saboda ta duba bata ganta ba babu inda bata duba ba daga karshe ta tuno cewa ai a sashen Khalil ta barta jiya da daddare,cike da kwarin gwiwa ta kammala komai kamar yadda ta saba taje ta shirya Aryan yatafi makaranta sannan itama ta shirya ta nufi bangaren Khalil. Ta jima zaune kadan a falon nashi tana dakon jiran fitowarshi,misalin karfe 8 taji alamun fitowarshi,duk da dama can shi ba ma'abocin dariya satataa bane amma yau kam kallo daya tayiwa fuskarshi ta gane akwai matsala saboda irin yanda yatsare gida ya hade bangon gabas da yamma ya daure fuskarshi tamau,
Cikin sanyin jiki da tsoro bayyananne ta gaidashi,
"Uncle ina kwana?"
Sai da ya dan ja lokaci kafin ya amsa mata da, "lafiya"
Daga haka yawuce yayi waje yana kara waya a kunnenshi ko kallon inda ta ajiye masa abincinsa baiyi ba saboda amugun kule yake da ita,ita mahaukaciyar inace da bata san darajar aure ba har zata rinka musayar kalamai da wani katon banza awaje? Shiyasa ya zama dole agareshi ya dauki matakin da yadace,
Hanan abun duniya ne taji yataru yayi mata yawa domin sam bata da masaniyar abinda ke wakana,ita dai kawai abunda ta sani shine yanzu Khalil ya canja completely yana yin wasu abubuwa fushi fushi,zafi zafi dan ko abincinta yadaina ci tsawon kwana uku kenan sannan ko gaisheshi tayi asama yake amsawa kamar zai mareta to wai me yake faruwa? Ita ba abinda yafi tayar mata da hankalima kamar yajin cin abincinta da yayi domin haka zata zage ta bata lokacinta ta shiga kitchen ta shirya masa abincin da ta san zaiyi farin ciki dashi amma yanda ta ajiye masa haka zata samu abinta ta dauko bai ko taba ba, gashi wayarta tana son tambayarsa amma tana tsoro domin wani irin kwarjini gareshi na innanaha. Khalil kuwa ya zabi ya hanata wayar ne har zuwa lokacin da zai gama fahimtar komai saboda bazai yuyu ya zuba ido tayita aikata son ranta ba,
Maganar aurenshi da maamy kuwa ankammala komai sai daurin aure kawai da yarage sadakinta ma yayi order dinsa dubai tun kwanaki biyu da suka wuce aka kawo masa dan haka yau bayan yatashi daga office yawuce gombe domin kaiwa maamy zoben,
Bayan sallar magrib yashiga gidansu maamy din yana shiga ya isketa zaune tare da abbansu jawad wato tsohon mijinta, kamar zasu mari juna suka gaisa abban su jawad yatashi yafita,da alamar tuhuma akan fuskarshi yake kallon maamy kafin ya furta,
"Wannan fa?"
"Ibrahim kenan.... Abbansu jawad ne fa....,Yazo ganin yaranshi"
"Ehh nasani,but da nashigo ban ganshi tare da yaranshi ba da ke naganshi"
"Su dinma da suna tare damu basu jima da fita ba saboda zamu tattauna akan makomarsu wato inda yadace su zauna a hannunsa ko a hannuna....."
"To yanzun a ina kuka yanke hukunci zasu zauna?"
"Nidai idan son samuna ne shine su zauna anan wurin iyayena shikuma yaki yarda wai ala dole lallai lallai sai nabashi yaranshi ya kaiwa mom dinshi wacce nasan gallaza musu kawai zatayi"
"To ke meyasa ba zaki rikesu ba?"
Dan Damm tayi sannan ta saki murmushi,
"Ibrahim kenan,taya zan rikesu alhali ubansu na raye? Da dai ace baya raye ne shine zan iya daukarsu intafi dasu gidan aure na"
"Kar ki damu indai dan tani ne,maamy nima fa mai rike yaranki ne koda kuwa babu aure tsakaninmu....... Babu matsala kina iya rikesu"
"Allah sarki Khalil..... Can't wait lokacin da zamu zama ma'aurata"
Murmushi yayi ya kalleta,
"Wanne albishir za ayi min?"
"Farin ciki kawai...."
Murmushi yayi baice komai ba,har suka gama hirar yatafi bai nuna mata zoben ba ko yamanta ne ko kuma meyasa oho shi dai yasan dalili.
Karfe 11 yashiga gidansa a abuja, Hanan na zaune taji shigowar shi yau kam ta daura damarar sai taji daga gareshi, mintuna 30 tabashi yagama kintsawa sannan sai taje gareshi taji abinda ke faruwa da har yadauki fushi da ita,
Tana ganin mintuna 30 sun cika ta tashi ta fita tana sanye cikin kayan bacci ta dora hijab akai,falon nashi ta shiga wanda ya wadatu da kamshinsa mai sanyaya zuciya da tsayawa arai,bata fi mintuna biyu da zama ba taji fitowarsa yana magana awaya cikin sanyin murya,
"Khalid maganar aure na da maamy ne...... Dazu naje na sameta tare da baban yaran nan nata,ni banda problem akan yara zan rike mata amma inda problem din yake shine....."
Ai bata jira taji karshen bayanin nasa ba ta tashi jiri na d'aukarta kamar zata fadi tafita daga sashen nasa gaba daya. Wani irin kuka ne yaci karfinta kuma tun kafin ta shiga bedroom dinta ya subuce mata,haba ashe da walakin,ashe dama can akwai wata akasa shiyasa anty maamy tazo gidanta ta tare tun kafin adaura musu aure da Khalil,ashe sun jima suna cin amanarta bata saniba,
Kukan rashin sanin mafita tayita faman yi gashi babu waya a hannunta bare ta bukaci shawarwarin yan uwa da abokan arziki,kusan kwana tayi tana kuka sai da asubah ta iya samun bacci. Haka ta wayi gari kamar wata marar lafiya gashi sam babu farin ciki atare da ita danma dai kafin ta tashi umma tuni ta shirya Aryan yatafi makaranta,kasa cin abinci tayi sai ruwan tea kadai da ta iya kurba,tsawon kwanaki biyu tana fama da rashin cin abinci da kuma rashin bacci wanda yayi sanadiyyar haddasa mata ciwon kirji da zazzabi,
Da farko zazzabin baiyi zafiba amma magriba nayi sai ya tsananta jikinta kamar ana kada mata mazari saboda tsananin rawar sanyin da take yi,waya umma tayiwa Khalil ta sanar masa akan ya turo musu Dr,babu jimawa sai ga Dr Al'amin din yazo nan ya dubata yayi duk abunda yadace yatafi,
Wani bacci ne mai dadi ya kwasheta bayan tafiyar Dr nan umma taja hannun Aryan suka fita suka barta dan ta samu bacci,shi kuwa Khalil lokacin da umma ta kirashi awaya tana fada masa rashin lafiyar Hanan yana can gombe tare da maamy wacce gyaran jikin da aka fara yimata na dilke da halawa yasa ta sake fitowa dauu kamar wata balarabiya ga wani azababben kamshi da ke tashi daga jikinta kamar masana'antar sarrafa turare,
K'arfe 12 yasamu shigawo gida domin bai baro gombe da wuri ba,wanka yafara yi yasaka k'ananan kaya na bacci sannan yafita zuwa part din Hanan domin ganin yanda jikin nata yake tunda lokacin da umma ta kirashi awaya tace masa jikin Hanan din ya dan tsananta,
Kamar koda yaushe wani sanyayyen kamshi ne yafara yimasa maraba lokacin da yashiga falon nata,kai tsaye bedroom dinta yabude yashiga,tashinta kenan tana zaune tsakiyar gado ta jingina tana tunanin ta yanda zata sauka domin ta hado tea saboda yunwa kuma take ji,
Kamar wanda baya so haka ya karasa gaban gadon fuskarshi babu yabo babu fallasa, sunkuyar da kanta kasa tayi saboda tsoro da kwarjinin shi take gani,
"Ya jikin?" Taji ya fada yana tsaye yakama kugunshi ya rike,
"Da sauki..." Ta fada muryarta adashe sakamakon yawan kukan da tayi,
"Me yafaru naganki a zaune kuma?"
"Yanzu natashi tea nake son zan sha...."
Dan shiru yayi sannan ya kalleta,
"Zaki iya zuwa ki hado ne?"
Kai ta girgiza masa batare da ta kalleshi ba,
Juyawa yayi yafita ya sauka k'asa,tea din ya tsiyaya cikin cup ya hada mata yaji madara da milo sosai dan ba karamin kauri yayi ba sannan ya daukar mata snacks yakoma sama,har lokacin ta zaune kamar yadda take dazu,
Mika mata yayi ya nemi wuri ya zauna gefen gadon domin sai yaga ta rame sosai,to ko dama tajima tana zazzabin ne bai saniba? Harga Allah bata son tea dinnan da ya hado mata saboda yasaka madara ita kuma saboda zazzabin da take yi bata ko kaunar taji karnin madarar gashi yazuba da yawa da ace itace zata hada to da ruwan bunu zata hada tasha shi bak'i,daurewa tayi kawai tafara sha ahakan tana rintse idanu,tasha yakai rabi ta yunkura zata ajiye ya kalleta,
"Wa kika ragewa wannan din? Shanyeshi"
Jin abinda yace yasata fasa ajiye cup din taci gaba da sha tana jin zuciyarta tana tashi amai yana taso mata, yunkurin amai ne ya addabeta har bata san lokacin da ta rikeshi ba saboda babu tazara sosai tsakaninsu,tare ta wankesu da aman wanda yaki karewa domin gaba daya tea din da ta sha sai da ta amayar dashi, lokacin da tagama aman jikinta duk ya saki babu karfi ko kadan,lagwaff ta sakeshi ta kwanta tana jin wani sabon zazzabi na shigarta,mikewa yayi yafita, bedroom dinshi yaje ya wanke jikinsa ya sauya kaya sannan yadawo tana nan kwance kamar yadda yatafi yabarta,
Baida zabin da yawuce ya gyara ta ya tsaftace wurin da ta bata, tunanin ta inda yadace yafara yayi nan yafara da kan gadon sannan ya dagata itama,tana son tayi masa gardama amma kuma tana tsoro domin yau akwai wani kwarjini na musamman akan fuskarshi,yar doguwar rigar jikinta ya cire ya goggoge mata jikinta sannan ya bude drawer dinta yaciro mata wata,tun dazu ya lura da ita sai faman kakkare kirjinta take yi tanata bobboyewa ko ta manta da yataba ganinta ahakane oho? Amma wanne dare ne wanda jemage bai ganiba ya furta hakan acikin ransa,yana gama saka mata rigar ta tukunkune taja bargo ta rufe jikinta tana rawar dari,
Sai da yagama tsaftace duk wurin da ta bata da aman sannan yafita zuwa sashensa, kwanciya yayi amma ba bacci yake ba,bayan kamar mintuna 30 yasake tashi yafita yaje ya dubata,bacci ya samu tanayi dan haka yakoma sashensa shima ya kwanta zuciyarshi cunkushe da tunani iri iri................................鉁嶐煆?
_Wannan littafin na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din._
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:15 AM - Ummi Tandama: 47
***Haka yaci gaba da jinyarta amma koda yaushe fuskarsa ahade babu fara'a alhalin ita kuma bata san abinda tayi masa ba shikuma yaki yasanar da ita sai faman fushi yake yi,
Duk abinda tace tana so yana mutukar yin duk iya iyawarshi wurin nemo mata amma fa tsakaninta dashi babu sakin fuska dan komai yana yine kamar irin anyi masa dole dinnan,
Kwananta biyu akwance ta dan fara samun sauki,itama gaba daya acike take dashi sakamakon auren da taji zai yi kuma wai anty maamy zai aura,tana ta son ta kira abokan shawararta su dan tattauna su bata shawarar da ta dace amma babu waya a hannunta kuma tsoron tambayar Khalil take yi,rasa yanda zatayi tayi daga karshe sai umma barira ta samu da maganar lokacin ita kadaice adakinta tana sauraren fm radio shi kuma Aryan yatafi makaranta,tashi zaune umma tayi daga kishingiden da take sannan cikin alamun tausayawa da tausasa harshe tace,
"Kiyi hakuri Sa'adatu,tabbas kishiya nada ciwo kuma tana da zafi shiyasa ba kowacce mace ce take iya cin rabarta ba, da yawa mata a kishiya jarrabawar su take sai dai amma basu fiya cin wannan jarrabawar ba saboda gajen hakuri da kuma hawa dokin zuciya..... Idan akayi hakuri kuma aka kai zuciya nesa wallahi ba kishiya ba ita kanta rayuwar gaba daya mai wucewa ce,kina zaune mijin zai dawo ya sameki kuma har ma ki zama alkali atsakaninsu amma fa sai kin kai zuciyarki nesa, mutukar baki nutsu kin kama mutuncin kanki ba to a irin wannan gabar ne miji yake rainaki,danginsa suke rainaki,kishiya take rainaki,ke hatta sauran abokan arziki rainaki sukeyi mutukar baki ja girmanki kin yiwa fushinki da zuciyarki linzami ba,shi wannan zafin kishin da kan tasowa mata a lokaci guda shine ke sanadiyyar sasu aikata abinda zasu zo suna nadama da dana sani tsawon shekaru dan da yawan mata a wannan lokacin suke barin damarsu,miji yayita rarrashinsu amma suna fandarewa har shima yagaji yayi watsi dasu daga karshe idan ba ayi sa'a ba shikenan ansamu hanyar lalacewar zamantakewar da aka gina shekara da shekaru....."
Sake gyara zama umma barira tayi sannan ta fuskanci Hanan,
"Shawarar da ni dai zan baki 'yarnan shine..... Kishiya bata cinye uban kowa ba kuma kema bafa zata cinyeki ba,kiyi hakuri kici gaba da kyautatawa mijinki,nima na zauna da ita nasan zafinta kuma nasan ciwonta amma da nayi hakuri wallahi komai sai da ya zamto tarihi,to kema haka taki zata zama tarihi kamar ba ayiba......."
Jijjiga Kai Hanan tayi alamar gamsuwa da bayanan umman shiyasa neman shawarar manya amafi yawan lokuta take da dadi domin ko basu magance maka matsalarka ba zasuyi maka bayanin da kai kanka sai kaji dadi zuciyarka tayi sanyi,
"Nagode umma kuma insha Allah zanyi yanda kika ce......"
Cigaba da bata shawarwari umma tayi har tsawon wani lokaci kafin ta tashi ta shiga kitchen domin dorawa Khalil abinci ada tayi fushi tace bazata sake yimasa girki ba sai dai wacce zai auro din idan tazo ita taci gaba dayi masa amma kalaman da umma tayi amfani dasu wurin bata shawarwari sune suka sanyaya mata zuciya har taga rashin dacewar hakan ta sauya shawara,
Tasan daga shi har dan gaban goshin nasa zasuyi farin ciki da abunda zata girka musu yau shiyasa ta bada himma ta zage wurin ganin ta nuna kwarewarta a wannan fannin,
Zuwa yamma ta kammala komai nata suna tare da Aryan a falonta suna yin game,kokari takeyi taga tayi yaki da duk wani bacin rai tare da damuwa dake kokarin yiwa zuciyarta tsinke har yasamu wurin zama wannan dalilinne yasa take ta biyewa Aryan suka taru suka zama mashirmata.
Tun kafin Khalil yadawo ta shirya masa table bayan ta gyare masa sashensa tsaf yasha turaren wuta dan sudan mai bala'in kamshi,bayan sallar ishah yasamu zarafin dawowa kasancewar yau yaje garin zamfara ya halacci wani taro,
Kamar yadda yasaba wanka yafara yi yashirya cikin kananan kaya sannan yafito falo hancinsa na shakar kamshin turaren da Hanan ta saka masa sannan wani abun sha'awar shine yanda ta kawata table din sannan ta armasa shi da warmers masu kyau kanana,zama yayi yana budewa nan yaga funkaso ne yatashi sosai sannan yayi kyau sai miyar agushi tasha alayyahu itama tayi kyau sosai tun a ido gashi ta wadatu da naman kaji,sai lafiyayyen zobon da ta hada wanda yaji flavors daban daban ya wadatu da kankana da cucumber aciki,zuba funkason yayi yafara ci wanda yayi daidai da shigowar Aryan cikin falon, cinyarshi ya haye shima yasaka hannu yafara cin funkason wanda tunda aka sauke yake ci amma yakasa koshi gashi kuma baiyi wani auki sosai ba dan hatta umma ma saida ta bukaci kari akan guda hudun da Hanan ta zuba mata shi kansa Khalil din kwaya uku yasamu,
"Abba na ba kaci naka bane? Wannan fa nawane nima zanci....."
Makale kafada Aryan yayi yaci gaba da ci yana surutu,
"Nima zan kara ci uncle......."
Tare suka cinye sannan Aryan yafice,shikuma zama yayi nan falonshi aranshi yana tunanin to ko menene kuma yafaru da Abba Idris ke nemanshi? Dan dazu yayi masa text massage akan yaje gombe yana son ganinshi gobe yasan dai baya wuce maganar aurensu shida maamy,wayarshi yatashi yashiga bedroom dinshi yadauko yafito yasoma kiran layin maamy amma number busy,ajiye wayar yayi saboda yasan idan tagama zata kirashi amma kuma ga mamakinsa har ya kwanta bacci bata kirashi dinba shima kuma bai sake kiranta ba. Washe gari asubanci yayi yafita ta can office yawuce gombe domin amsa kiran Abba Idris wanda yake matsayin uba agareshi,
Bayani cikin nutsuwa abba Idris yayi masa akan maganar aurenshi da maamy cewa tsohon mijin maamyn wai yadawo yanata bibiya sai takoma d'akinta kuma dama tun farko matsalar ba daga gareshi bane daga mahaifiyar shi ne dan haka shi Khalil yayi hakuri yabarwa Abban jawad domin mammy takoma gidan tsohon mijinta,dama Khalil yasan za arina kuma za ayi haka dan tunda yaga take taken tsohon mijin mammy yasan da wata akasa,duk da baiji dadin abinda yaji ba amma godiya yayiwa Abba kuma yanuna baiji zafi ko ciwon abinda yafaru ba sai dai har acikin ransa baiji dadin boye masan da mammy tayiba shi baya son boye boye da nuku nuku cikin sha'aninsa koda yaushe yafi son mutum yazama open amma babu komai dan koba alaka ta so maamy ai yar uwarsa ce ta jini, sallama yayiwa abba yatafi batare da yashiga cikin gidanba.
Wannan al'amari shine sanadin rushewar maganar aurensa da maamy wanda ita Hanan bata saniba duk atunaninta maganar aure har yanzu tana nan daram shiyasa taci gaba da kyautata masa da yimasa duk wani abu wanda zai faranta ransa,ranar da aka daura auren mammy sai ranar Hanan tasan anfasa auren da Khalil dan abakin umma barira taji bayan umman sun gama waya da hajiyarsu Khalil,wani sanyi da annuri da farin cikine yarinka ratsa zuciyar Hanan da kuwa duk zuciyarta ta shiga cikin wani hali,babu bata lokaci ta shiga cikin kitchen domin jinta take yi awartsake yanzu,tuwon dai nasu na gado ta dora musu shida Aryan saboda basa gajiya dashi nan ta lailayashi tayishi lafiyayye miyar busasshiyar kubewa mai tsananin yauki wacce tasha kifi wadatacce,man shanu ta soya bayan ta sauke girkin,
Tun kafin Khalil din yadawo su umma ke santin wannan tuwon ita da Aryan ita dai Hanan dariya kawai tayi ta haura sama,bayan sallar magriba Khalil din yadawo daga gombe amutukar gajiye ga wata yunwa dake ciciyarshi,kayan jikinsa ya sauya daga manya zuwa kanana sannan yazo yahau table nan yafara kwasar girkin Hanan wanda ke barazanar cire masa kunne dan tsabar dadi,yana dab da kammalawa Hanan tashigo itada Aryan wanda ta sakoshi agaba wai ya tayata tambayar Khalil wayarta da yarike ya hanata tun sati biyu zuwa uku da suka gabata,
Ganin sun hade kai yasashi kallonsu yana cigaba da cin tuwonsa,
"Papa....."
Kallon Aryan yayi sannan yakai laumar tuwon da ya debo,
"Menene?"
Kallon Hanan yayi sannan ya kalli Khalil,
"Mommy infada?"
Girgiza masa kai tayi,
"Kabari har sai yagama cin abinci tukunna"
"Kai fadi..... Menene?"
"Uncle mommy ce tace wai kabata phone dinta...."
Yaji abinda Aryan din yafada sarai amma sai bai kulasu ba kawai yaci gaba da cin abinsa har ya kammala lokacin tuni har lokacin sallar ishah yayi dan haka bai zauna a falonba yamike zuwa cikin bedroom dinshi hakan ya tabbatarwa da Hanan cewa bazai bata ba shiyasa kafin yafito ta tashi tafita shikuma Aryan yabishi zuwa cikin bedroom din tare sukaje salla suka dawo,itama sallar taje ta yi,bayan ta idar ta na zaune kan abin salla Aryan yashigo yace taje Daddy yana kiranta,tashi tayi batare da ta cire hijabin jikinta ba tabishi suka tafi,
Yana hakimce kan sofa ya dora kafarshi daya akan center table yana ta faman yimata bincike awayar tata,zama tayi akujerar dan nesa dashi kadan,
"Me kuke cewa dazu keda d'anki?"
Taji yafada har lokacin idanuwanshi na kan wayarta yana ta faman yimata bincike ita dai fatanta Allah yasa kar ya kalle mata sirrin da ta ajiye a WhatsApp,dan duk ranar da hajja hasinah tayi posting din abu mai amfani starring dinsu takeyi ta adana bata gogewa,
"Baki jine?"
"Inaji..... Cewa nayi ka taimaka kabani wayata zanyi amfani da ita gida....."
Bai amsa mata ba har tsawon mintuna biyu sannan cikin alamar tuhuma taji yace,
"Waye mujahid?"
Sosai tambayar tabata mutukar mamaki sannan lokaci guda saima ta nemi amsar da zata bashi ta rasa dan sai ta kasa gane wayema mujahid?
"Ina tambayar ki waye mujahid?"
Shirun taso sake yi amma kuma ganin ya tsareta da idanuwanshi mayalwata yasata yin kasa da kanta sannan tace,
"Dan makarantar mu ne..."
"Kar kiyi min karya dan already nasan gaskiya,kawai ina son sake tabbatarwa ne,wayeshi?"
Ji tayi yawun bakinta na neman kafewa,
"Ya taba cewa yana sona......"
"Tsohon saurayinki ne kenan?" Taji yafada bayan yaja wasu sakwanni,
"Uhmmm"
"Bai san kinyi aure bane?"
"Yasani..."
"Ok"
Daga nan cigaba yayi da tambayar contacts dinta kusan kowa sai ya tambayeta waye shi sai dai abinda yabata mamaki shine sam bai tambayeta waye wannan wanda yake turo mata text massage dinba ko bai ganiba?
"Ita wannan hasinah din itace malamar ku kenan?" Taji yafada babu zato babu tsammani, sunkuyar da kanta kasa tayi tana jin kunyar duniya na lullubeta saboda tasan yaga abinda taketa addu'ar Allah yasa kar yagani,
Baiyi mata maganar ba ya mika mata wayarta bayan ya gama karanta duk abinda idonshi yasauka akai,
Hannu biyu tasa ta karba ta tashi tafita cike da murna tana zuwa part dinta ta saka wayar a charge tashiga wanka,bayan tafito tagama shirin bacci ta dauki wayar ta kunna data ta leka WhatsApp domin sosai tayi missing dinshi shiyasa har 12 saura takai yau a online,kai ashe waya ma rahama ce bata san da haka ba har saida Khalil ya kwace mata wayarta.
Washe gari Khalil yabar kasar yatafi k'asar Rwanda,tunda yatafi kuma ta shiga missing dinshi har ta kasa hakuri sai da ta tura masa massage,
Yana kwance adaki har yafara bacci yaga massage din nata murmushi yayi ya mayar mata da reply,
_Me kika fi missing atare dani?_
Itama murmushin tayi lokacin da taga tambayar da yayi mata saima ta rasa amsar da zata bashi dan haka tayi shiru kawai. Satinshi daya yadawo,aranar da yadawo bai shigo gidanba sai dare bayan duk sunyi bacci washe gari da safe yatafi gombe bayan yadawo da daddare yakira Hanan falonshi,
"Ki shirya gobe za muje gombe Muneerat ta haihu....." Ya fada yana rike da wata jotter da pen yana rubutu amma bata san abinda yake rubutawa ba,
Tun adaren tayi shirinta ta hada kayanta set biyu sai ko kayan bacci da inner wears,humrar da hajja hasinah ta kawo mata ranar da tazo ta saka cikin akwatin kayanta sai da ta tabbatar tagama hada komai sannan ta kwanta,
Washe gari bayan ankai Aryan makaranta Khalil yaje office yafito suka nufi gombe bayan sunje store ta sai kayan baby,duk yau tunda ta tashi jikinta babu dadi ahaka dai suka karasa da rana fatse fatse nan ta samu tarba kamar yadda aka saba yimata,saida suka fara zuwa gidan Khalid suka ga baby anan Muneerat ke yimusu albishir din wai sunan Khalil Khalid yasakawa jaririn,ba karamin dadi Khalil yajiba nan ya ajiyewa Muneerat damin kudin da Hanan bata san ko nawa bane amma dai yan dubu dubu ne sabbi fil dasu,daga nan suka tafi cikin gida can Hanan ta samu tarba ta musamman awurin su hajiya da su zarah, bedroom din da take sauka idan tazo yauma anan aka sauketa,tunda tazo tashiga cikinsu sarah suna shan hira har dare, Khalil kuwa dama bata kara sakashi a idonta ba kuma shima agarin zai kwana.
Misalin karfe 11 da wurin rabi tana kwance suna chaten da yaya shamsu nan yake sanar da ita rashin lafiyar abbansu wai ciwon koda sunje asibiti yau,ai agigice tasa hijabi ta fita ta nufi bangaren Khalil tana hawaye,
Fitowarshi falon kenan bayan yafito daga wanka yashirya bata tsaya yin knocking ba ta bude kofar ta shiga, kallonta ya tsaya yi yana son jin ba'asin kukanta,
"Abba nane baida lafiya wai ciwon koda..... Dan Allah kasa akaini kano yanzu" haka take ta fada sam taki barinsa ma yafurta koda kalma daya saiko uban hawayen dake ta faman bin kumatunta kamar anballe bakin fanfo,hannunta yakama akaron farko ya zaunar da ita kusa dashi har jikinsu na gogar juna saboda kusancinsu kuma har lokacin yana rikeda hannunta,hakuri yasoma bata domin dare yayi yanzu bazai yuyu akaita kano a wannan lokacin ba,kuka ta fashe dashi hakan yabashi damar sakata acikin jikinsa yana rarrashinta,tun shigowar ta kamshin jikinta ke neman rikita masa lissafi domin humrar hajja hasinah yau ta shafa wato giredi nan da nan ta tayar masa da hankali,ita kuwa yau mamakinsa ne ya cika mata zuciya ganin ya biye mata harda rarrashi shiyasa ta bararraje taci gaba da shagwabarta.......................鉁嶐煆?
_Wannan littafin na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din._
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:15 AM - Ummi Tandama: 48
***D'aukarta yayi gaba dayanta ya dorata kan cinyarsa wanda hakan yayi mutukar bawa Hanan kunya sosai, rungume ta yayi cikin jikinsa yana shafar bayanta alamar rarrashi,ji tayi kamar ta nutse kasa saboda tsananin kunya,shi kuwa gogan hankalinsa ne yakai kololuwar tashi saboda sosai kamshin jikinta ya rudashi kuma ya jefashi cikin kogin bukatarta,
Cikin dabara yasamu ya rabata da hijabin da ke jikinta wannan ba shine karo nafarko da yafara ganinta ahaka ba amma wannan yana da banbanci da na lokutan baya,sosai yau dinnan Khalil ya dauki dumi domin wata irin matsa yayi mata sai faman aikin sinsinar jikinta yake yi sakamakon kamshin da jikinta keyi wanda ke kara masa kaimi yana ingizashi gareta,cak yatashi da ita yanufi cikin bedroom dinshi yana rike da ita,ita kam idanuwanta arufe suke ta runtse su dan ba zata iya hada ido dashi ba cikin wannan yanayi,
A saman katafaren gadonshi yayi musu masauki bayan ya rage hasken dakin izuwa haske marar karfi, jikinta har rawa yake yi saboda rashin sabo ga kuma tsoro duk da cewa abun yazo mata bagatatan batare da shiri ba,tun kafin ya aiwatar da kudirinsa shima nasa jikin ya dauki rawa babu bata lokaci wani matsanancin zazzabi da ciwon kai suka rufeshi nan take batare da ya cimma burinsa ba,
Kasa aikata komai yayi sai ko uban kakkarwar sanyi da gangar jikinsa keyi kamar ana kwara masa kankara,
"Sa'adatu lullube ni........ Sanyi nake ji"
Gaba daya duk ta rude itama ganin abinda ke faruwa domin wani irin rawa jikinsa keyi, lullubeshi tayi da bargo amma yanda yake jin sanyi na kadashi gani yake yi kamar bata rufa masa komai ba shiyasa yayi azamar jawota jikinsa ya rungume jikinsa ya dauki zafi sosai,
Haka suka kasance zuwa wani lokaci yanata kakkarwa har lokacin yana rungume da ita kamar zai mayar da ita can cikin cikinsa,ya dan fara samun bacci sama sama ciwon ciki ya turnikeshi kamar zai mutu har da su yunkurin amai amma kuma yakasa, Hanan kuka tafara yi tana son ta tashi taje cikin gida ta kira su hajiya amma ya riketa tsam kamar me,kuka take ta faman yi tana yimasa sannu shi kam ko magana ma yakasa yi sai yunkurin amai yake ta yi cikinsa na murda masa haka suka kusan kwana dan sai kirjin asubah sannan yasamu ciwon ya lafa masa har bacci yayi nasarar daukarshi,sakashi agaba Hanan tayi tana kallonsa cikin tausayawa har lokacin yana manne da ita yana bacci,ita kam sai bacci barawo domin tana cikin hali na zullumi dan yanda taga Khalil din yayi ba karamin tayar mata da hankali yayiba dan kamar wanda zai mutu haka yazame mata fa,
Misalin karfe 7:30 na safe ta farka nan idanuwanta suka sauka akan bawan Allah Khalil da keta faman baccin wahala duk yagama jigata takai kimanin mintuna biyar tana kallonsa sannan da dabara ta raba jikinta da nashi ta tashi, kayan baccinta ta maida jikinta sannan ta shiga bathroom,bata wani jima acan sosai ba tagama abinda zatayi ta fito tazo tayi salla,bayan ta idar ne ta samu zarafin kallon dakin,daki kam komai yaji ne babu ma abinda yafi burgeta irin dan karamin farin gadonshi wanda ke girke cikin dakin,mikewa tayi ta nufi bakin gadon nan idonta yasauka kan wani madaidaicin hoto dake ajiye kan bedside drawer dinshi,zama tayi ta dauki hoton tana dubawa bakinta abude mamaki karara kwance saman fuskarta domin badan tasan cewa ba ita bace ta dauki wannan hoton to da babu abinda zai hana tace itace saboda tamkar kara aka tsaga da ita da wacce ke jikin hoton tana sanye cikin purple din atamfa tana dariya, Allah mai iko to ko wannan itace mahaifiyar Aryan? Ta kissima hakan acikin ranta,tajima tana kallon hoton kafin ta ajiyeshi ta juya ga Khalil wanda ke kwance ya dunkule wuri daya,so take ta tasheshi yayi salla amma tana tsoron kar kuma yatashi da ciwon cikin tunda ansamu ya lafa masa,
Bargon da yake ciki ta dan yaye tafara tashinsa har lokacin jikinsa akwai zafi sosai,riga mai nauyi yasa ta dauko masa yasaka sannan ta rikeshi ya sauka daga kan gadon yashiga bathroom,daurewa kawai yayi yai sallar amma shi kadai yasan abinda yake ji,tun akan abin sallar yafara rike ciki dakyar ta taimaka masa yakoma saman gado ya kwanta nan tafita zuwa cikin gida da sauri domin sanarwa dasu hajiya. Cikin lokaci k'ank'ani aka kira Dr yazo yafara dubashi amma ciwo kamar karashi akeyi,gaba daya hankula sun tashi musamman ma Hanan da hajiya,wurin azahar yasamu ciwon cikin ya lafa dan har yasamu damar yin bacci, Hanan na zaune awurinsa yaya shamsu yakirata awaya saida taji hankalinta yatashi gabanta ya fadi nan ta amsa wayar jikinta na rawa tunda shima Abban nasu tasan baida lafiya,
"Yaya shamsu yajikin Abban?"
"Jikinsa da sauki Hanan gamu ma agida..."
"Kajini shiru banzo ba ko? Shima Abban Aryan ne yatashi da ciwon ciki shiyasa wallahi amma zanzo..."
"A'a kiyi zamanki ki kula dashi tukunna.....ga Abban ma"
Jin Abba ya karbi wayar yasata fashewa da kuka, Nan Abba ya dan kwantar mata da hankali yace mata yama samu lafiya dan har fita zaiyi anjima,saida suka gaisa da mamaye sannan sukayi sallama ta kashe wayar ta zubawa Khalil ido kamar lokacinne tafara ganinsa, tausayinsa take ji har can cikin ranta wanda bata san daliliba koda yake kila tausayin yanada nasaba da irin son da take yimasa,
Zuwa la'asar ya farka da wani azababben ciwon cikin ga yunkurin amai amma yakasa yin aman ganin dai abun kamar gaba yake kara yi Zaid ya kwashesu suka nufi asibiti can aka bashi gado aka kwantar dashi,daren ranar kuwa daga shi har Hanan basu runtsa ba saboda murkususun da yaketa faman yi sai asubah sannan yasamu bacci,
Misalin karfe 7 nasafe su hajiya suka zo harda wani dattijon bafulatani tare suka shiga cikin dakin sannan ya tsaya akan Khalil yana kallonsa har na wani tsawon lokaci daga bisani yajuya ya kalli hajiya ya kalli Hanan sannan yace,
"Wannan aikin shaidanu ne,ko shakka babu sihiri ne kuma mai karfin gaske sai dai Allah yabamu nasarar warwareshi cikin sauki...., Yanzu hajiya abani kwana uku zanje innemo makarin wannan asirin dake jikinsa,amma zan aiko jikina salisu zai kawo masa tsumin da zaisha saboda wannan ciwon cikin dake damunsa, Allah yabashi lafiya...."
"To shikenan nasalla,mun gode, Allah yasa adace,mun gode" hajiya ta fada tana sharar hawayen dake idonta,ita dai Hanan tana tsaye tarasa ma wanne irin tunani zatayi,shikuma Khalil haka rayuwarshi take daga acutar dashi sai acutar da danshi to duk suwaye keyi masa wadannan abubuwan? "Makiya mana" zuciyarta tabata amsa,wuri ta samu ta rafka tagumi tanata tunane tunanen da bata san dalilinsu ba,
Zuwa yamma aka kawo sakon tsumin da za abawa Khalil wanda duk yayi wujiga wujiga dashi babu ci babu sha sai wahalar ciwo,tunda yasha maganin yasamu saukin ciwon cikin domin ba kamar jiya ba yau har yana iya tashi yayi salla kuma ansamu yasha ruwan zafi, Hanan kam koda yaushe cikin hawaye take lallai dan adam ba abakin komai yake ba komai kudinsa komai mulkinsa yanzu shi Khalil ga kudin ga mulkin ga zaratan masu tsaron lafiyarsa amma duk ciki babu wanda ya isa ya dauke masa ciwon dake tare dashi sai sarki Allah.
Cikin kwanaki biyun da suka yi a asibitin za a iya cewa da sauki tunda yana tashi kuma yana iya cin abinci sai dai fa yunkurin aman da yaketa yi kuma yakasa yinsa,yana kwance yanzunma bayan yagama yunkurin aman Hanan na yin salla nasalla yashigo dauke da wata yar batta irin wacce fulani ke zuba ruwa aciki, gaisheshi Hanan tayi sannan tabashi kujera ya zauna yana fuskantar Khalil,
"Moddibo......... Insha Allahu andace kuma anyi nasara domin ansamo makarin cutar dake jikinka shekara da shekaru,amma sai kayi hakuri da abinda zaka ji daga gareni,matarka itace tayi maka sihirin mallaka,sihirin da bazaka taba kusantar wata 'ya mace ba koma bayan ita,idan har kayi koda yunkurin aikata hakanne to zaka iya rasa rayuwarka......."
Shiru Khalil yayi yana nazari acikin ransa,yanzu Ramlat itace ta aikata masa wannan mummunan aikin? To saboda me? Awanne dalili?
"Saboda ta kasance ita daya tilo acikin zuciyarka da rayuwarka mana...." Zuciyarshi tabashi amsa,
"Ba dan Allah yasa hajiya ta kirani ta sanar daniba to da haka zska kare rayuwarka sai dai wani kadari na ubangiji..... Yanzu ga wannan tashi kasha"
Idanuwansa fal da hawaye yatashi zaune ya karbi maganin yakafa kai yafara sha amma ko hadiya uku kwakkwara baiyi ba yaji wani mugun amai yataso masa,karbe maganin nasalla yayi ita kuma hanan ta taso da sauri,
"Samo masa wani abu amai zaiyi..."
Cikin sauri ta dauko wata silver ta kawo masa riketa yayi bayan ta zauna akusa dashi nan yaci gaba da kakarin aman kamar zai amayar da dukkan abinda ke cikin cikinsa gaba daya,zuwa can yasoma wani irin amai domin gashi ne curi curi yake amayar dasu abun ba kyan gani gwanin ban tsoro,yasha wahala mutuka sannan yasamu nasarar amayar da gashin tas nan nasalla yakarba yafita harabar asibitin yaje ya binne yasake dawowa,
Daga Hanan har Khalil mamakine keta faman dawainiya dasu saboda jin abinda nasalla yace,kai amma gaskiya mata na aikata kuskure,yanzu wannan daukar hakki har ina? Ita gashi wacce ta aikata hakan tariga da tabar duniyar to koma dai tana raye ai da cutarwa,
Shi kuwa Khalil abin yatsaya masa arai haba shiyasa ranar da Ramlat zata rasu ta rinka neman gafararsa tana cewa ya yafe mata to ko dama wannan yafiyar take nema? Gaskiya mata ba abun yarda bane, Ramlat ta cutar dashi da yawa sannan ta cutar da wani ma tunda kila ba dan Allah yakawo karshen abunba da ahaka zai kare rayuwarsa,
Adaren ranar aka sallamesu suka koma gida domin jiki yayi sauki kuma ansamo bakin zaren,wanka yashiga yayi yafito yana zaune bakin gado yana rike da turare Hanan tashigo dauke da tiren abinci ganinshi babu riga yasata niyyar komawa da baya,
"Shigo mana...." Yafada kamar wani marar lafiya koda yake marar lafiyar ne amma dai muryarshi ta sake yin sanyi kalau,
Kanta a kasa ta ajiye masa ta mike zata fita,
"Ina zaki je?"
"Zan koma canne..."
"Can ina?" Ya tambaya bayan yasoma fesa turaren ajikinsa,
"Wurin su hajiya"
Shiru yayi baice komai ba har saida yamike tsaye domin dauko rigar da zai saka sannan taji yace,
"Ki shirya gobe dasafe za akaiki ki gano abbanki"
Cikin fara'a da farin ciki yaga ta dunkule hannayenta wuri daya sannan tace,
"Tom nagode"
Daga haka ta tashi tafita kuma bata kara komawa sashen nasa ba ita dama tun can asali tayiwa Khalil uzuri duk wannan faman shassharetan da yakeyi bai wani dameta sosai ba ashe ashema bai laifinsa bane bawan Allah,
Shima anashi bangaren tunanine kala kala yaketa shiga yana fita cikin kwakwalwarshi,gaskiya Ramlat tayi masa abinda bai taba tunanin zatayi masa ba amma ya yafe mata kuma yana yimata fatan samun rahamar ubangiji. Daren ranar sam bacci baiga idonsa ba sai bayan da yayi sallar asubah sannan ya dan samu baccin,ita kuwa Hanan da wuri tagama shirinta zuwa karfe 8 suka kama hanyar kano saboda aranar zasu dawo,
Lokacin da taje gida ta samu jikin abbansu da sauki babu laifi sai lokacin taji hankalinta ya kwanta domin taganshi kalau dashi nan aka shisshigo da kayayyakin da tazo dashi, agurguje tajewa anty salaha sannan suka juya gombe ita da sabon drivern Khalil mai suna attahir. Tana komawa gombe adaren ranar suka koma Abuja domin acewar Khalil yana da uzururruka da yawa acan,
Karfe 9 da wasu mintuna suka shiga gida cikin murna su umma suka zo suka taryesu ita da Aryan wanda har lokacin baiyi bacci ba,
Ita dai sashenta ta wuce shikuma Aryan yabi abbanshi part dinsa,
Wanka tafara yi sannan ta gabatar da sallolinta tana idarwa ta sauka kasa ta nemawa kanta abinda zata sakawa cikinta,tana kokarin tashi taji shigowar text massage,
_Zo ki dauke Aryan._
Ganin abinda Khalil yaturo mata yasata mikewa direct tawuce part dinsa, Aryan na falo kwance kan sofa shi kadai,daukarshi tayi tafita zuwa dakinsa taje ta kwantar dashi,takoma nata har ta kwanta taji shigowar wani text massage din,
_Had'o min coffee._
Mikewa zaune tayi tana kunkuni ita kadai,
"Shima Abban Aryan akwai saka aiki wallahi,sam bazai bar mutum ya huta ba"
K'asa ta sauka ta hada masa coffee din sannan ta wuce part dinsa,baya cikin falon dan haka taje gaban kofar bedroom din nasa akaro nafarko dan ba taba shiga tayiba, knocking tayi har zata juya tajiyo muryar shi yana cewa,
"Come in"
Dukan uku uku kirjinta yafara yi sannan wani dan banzan tsoro ya shigeta lokaci guda,kamar wata sakarya haka ta tsaya kafin daga bisani ta kama kofar dakin ta murda tashiga............................鉁嶏笍
_Wannan littafin na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din._
*_Ummi Aisha_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:15 AM - Ummi Tandama: 49
***Yau kam tantagayyar yar kauye Hanan ta koma lokacin da ta shiga bedroom din Khalil, bedroom din ya hadu ya hadu karshen haduwa,komai na ciki farine kama tun daga kan tafkeken gadon baccinshi kirar Turkish bed sai wani dan karamin wurin hutawa mai dauke da kyawawan fararen kujeru zagaye da center table atsakiyarsu,gaba daya idanuwanta sun kasa tsayawa wuri daya sai kaiwa da kawowa suke yi a sassan bedroom din,
Yana kishingide kan wani lilo wanda ke can nesa da gadonshi hannunshi rike da novel na turanci wanda da alama karantawa yake yi,sanye yake da riga armless marar nauyi da kauri sai bakin wando mai santsi,
Cikin sassarfa ta dosheshi hannunta rike da coffee din,jikinta har wani rawa yake yi kadan kadan wanda bata san dalili ba,harga Allah a daidai wannan lokacin da Khalil zaice takoma inda tafito da zata fi yin murna da hakan,kamar wanda zai zaneta ko zai rufeta da duka yau haka take jin bala'in tsoronshi,
Har kasa ta durkusa lokacin da ta karasa gareshi wanda ita kanta bata san dalilin hakanba, hannunta taji ya hada dashi lokacin da ta mika masa coffee din,dagota yayi ya zaunar da ita kan lilon a gefenshi sannan ya ajiye coffee din kan stoll,
Tun shigowar ta kamshin dake manne jikinta yake barazanar tarwatsa kofofin hancinsa dan mutukar sanyi da dadi,tamkar wacce aka zarewa laka ajikinta haka tazama yau dan sam bata cikin nutsuwarta gaba daya,
Wata irin fargaba da tsoro ne keta faman shigarta tun bayan shigowarta cikin dakin,tajima tana burin wannan rana sannan kuma ta dade tana rokon Allah akan yanuna mata ranar nan amma yau sai gashi tana jin inama tana da damar mayarda hannun agogo baya,inama wannan ranar takoma da tayi dunbin farin ciki domin babu komai cikinta inbanda tsoro,damuwa da tarin zulumi,
"Uncle zan koma....... Bacci nake ji....." Ita kanta bata san lokacin da ta furta hakanba,
Littafin hannunshi taga ya mika mata,
"Babu inda zakije,yau hira zaki tayani and tare zamu kwana......"
Tamkar zakaran da aka tsoma cikin ruwa yayi tsumu tsumu haka tayi jin abinda yace ya sake rikitata da burkitata wannan fa shi ake kira da bazata,ita dai yau tana tsoron wannan rana,jin ya rungumo kafadarta ya karata da jikinsa yasata saurin kallonsa, murmushi yasakar mata cikin rada taji yace,
"Meke tsorataki ne? Dama haka kike da tsoro?"
K'asa tayi da idanuwanta saboda bazata iya cigaba da kallonsa ba,
"Fara karanta min wannan novel din...... Am all ears"
Littafin tabi da kallo kamar wata sokuwa,
"Ke nake jira....." Taji yafada cikin muryar rada,kasa karanta littafin tayi domin gaba daya tagama tsorata dashi,lallai komai dokinka da wannan ranar dolenka kayi ladab idan tazo,
"Bani littafi na tunda ba zaki karanta minba...."
Karba yayi ya ajiye saman stoll sannan ya dauki coffee dinsa da ke ta faman turiri ya bude yafara kurbarsa da zafinsa wanda hakan har mamaki yaso bata,
Sai da yashanye tass sannan ya ajiye dan karamin flask din saman stoll yajuya ya kalleta,cikin azama tayi kasa da idanuwanta,
"Tunda kin ki karanta min novel to bani labari...."
"Bacci nakeji...... Dare yayi"
Agogo ya kalla sannan ya kalleta,
"Nikuma yanzu dare na yafara, sai 2 ko 3 nake kwanciya bacci..."
Ido ta zaro sannan ta toshe bakinta da hannunta guda daya,
"Uncle dan Allah inje in kwanta?"
Yunkurawa yayi yatashi daga kan lilon yana kallonta,
"Ai nafada miki yau tare zamu kwana,oya tashi muje"
Kasa tashin tayi saboda tsabar fargaba da tashin hankali,har yasoma tafiya ya juyo yaga ta nan zaune bata ko motsa ba,dawowa yayi da baya bata farga ba taga ya tarairayeta gaba dayanta yanufi kan gadonshi da ita nan jikinta ya cigaba da rawa kamar mai rawar sanyi,ajiyeta yayi sannan ahankali taji yace,
"Yi baccinki anan....."
Daga haka yashige cikin bathroom ita kuma taci gaba da tsittsilla ido tana bin dakin nashi da kallo,wai tayi bacci to tayaya zata iya bacci anan? Ahaka taga yafito ya karasa kan abin sallarshi da alama alwala ya dauro,salla taga yayi raka'a biyu duk yanda akayi shafa'i da wutri zai gabatar,
Anashi bangaren shima yana son yace ta tashi suyi sallar nafila amma ganin irin tsoron da ya bayyana atare da ita yasashi kawai ya rabu da ita sai shi kadai yayi nafilfilinsa bayan ya idar da addu'o'insa yamike ya nufi gadon,tana ganin haka ta mayar da idanuwanta ta kulle cike da fargaba,gaba daya hasken dakin ya kashe sai wata yar blue light marar haske nan Hanan ta sake samun kanta cikin faduwar gaba tare da zulumi,
Abayanta taji kwanciyar shi sannan cikin nutsuwa ya juyo da ita suna fuskantar juna,
"Wannan hijabin zai takura miki..."
Bai jira cewarta ba yacire hijabin ya ajiye agefe sannan yajata ya sakata cikin jikinsa,
Ji tayi kamar ta saki fitsari awando saboda fargaba da tsoro da suka taru suka kanainayeta shi kansa ya lura da hakan shiyasa saida ya hada da dabaru da wayo, bakinsa taji yana laluben nata wanda ke kamshin splash kamshin kadai ya isa ya sanyawa mutum nutsuwa acikin zuciyarsa,shikuwa tun bayan lokacin da yarabata da hijabin jikinta wani sanyayyen kamshi ke barazanar rusa masa tunani nan duk yabi ya susuce,
Kuka kam ta shashi har ta goda Allah,har komai ya kammala bata daina wannan kukan ba domin jinta take kamar ana kokarin rabata da numfashinta saboda duk ta jijji rauni ayanda yazo mata kamar sabin shiga shima haka ya zama yau,
Rungumeta taji yayi acikin jikinsa cikin muryarshi wacce bata fita sosai yana rarrashinta,
" Kiyi hakuri kinji...... Nine ko? Sorry,ke dince kinada gardama sa'adah,sannu yi shiru bazan kara ba......"
Wadannan sune kalaman da yaketa faman rada mata acikin kunnuwanta ahaka har bacci ya kwasheta,sai da ya tabbatar tayi baccin sannan yatashi yashiga toilet yau kam mararsa sakayau yake jinta sakamakon fitar da abinda yajima yana damunsa da yayi tsawon shekara da shekaru,bazai taba mantawa da wannan ranar ta yauba acikin tarihin rayuwarsa,
Fitowa yayi bayan ya tsaftace jikinsa sannan yabi gefenta ya kwanta bayan ya sauya kayan jikinsa,
"Sarkin tsiwa..." Yafada ahankali yana kokarin sakata ajikinsa,yamutse fuska yaga tayi cikin baccinta sannan ta turo masa dan madaidaicin bakinta, kissing din bakin nata yayi kafin ya lumshe idanuwansa yana rungume da ita tsantsam akirjinsa,
Wani baccin dadi ne yayi awon gaba dashi mai cikeda dunbin ni'ima marar misaltuwa domin rabonsa da yasamu bacci mai dadi irin wannan tun Ramlat tana raye,baccinsa yasha na dan wani lokaci daga bisani yatashi yashiga toilet domin tuni anjima da fitowa daga masallaci, bude ido Hanan tayi tana jin jikinta duk yayi tsami ahankali ta lallaba ta maida sutturarta ta dauki hijabinta ta fice daga dakin tana dingisawa dakyar lokacin da taje corridor kuwa saida ta tsaya ta dan huta sannan ta karasa part dinta,kai tsaye toilet ta shiga ta tara ruwan zafi sannan ta shiga ciki,
Wanka tayi tai brush sannan tafito har lokacin tana jin zafi da radadi ajikinta ahaka ta canja kaya tayi salla bayan ta idar taje ta rufe kofarta tun daga falo sannan ta dawo tabi lafiyar gado ta lulluba ta kwanta babu jimawa wani bacci mai dan karen dadi ya kwasheta.
Shi kuwa Khalil bayan yafito daga bathroom dinshi sai yaga gadonshi wayam babu Hanan babu alamarta,
"Har ta gudu kenan....." Yafada acikin ransa,
Salla yayi sannan ya nade bedsheet din da ke kan gadon yawuce dashi toilet wanka yayi yafito yashirya cikin sauri saboda yanada meeting na musamman da mr president sannan da yuyuwar zai iya barin k'asar ayau zuwa k'asar Denmark,
Suit yau yasha yatsuke kuma ba karamin kyau yayi ba,agogonshi ya daura sannan yafita,tun daga corridor yafara jiyo karadin Aryan wanda Attahir sabon driver ke rike da hannunshi cikin shigar kayan makaranta,
"Good morning Papa" Aryan yafada tare da rungumeshi,
"Morning lovely son"
"Uncle yau mommy ba itace ta shiryani ba umma ce,wai mommy ta makara..."
"Ehh Aryan,maza kaje akaika school kada kayi late...."
Part din Hanan ya nufa bayan su Aryan sun koma kasa,kofar tata akulle take gamm nan yayita faman knocking amma shiru domin tana can cikin bedroom dinta tana ta sharar bacci bata ma san yana yi ba,
Gajiya yayi da knocking din yawuce domin har yaso ya dan makara.
Hanan kuwa ba ita ta tashi daga bacci ba sai misalin 12 na rana wannan dinma yunwace ta tada ita,dan mayafi kadai ta yafa sannan ta sauka kasa,umma na babban falon kasa tana sakar tabarma,saida suka gaisa sannan tawuce dining table ta zauna tayi breakfast,bayan ta gama ta sake komawa wurin umma,duk yanda taso da ta boye yanayin da take ciki saida umman ta gane dan har magana tayi mata tace ta daure ta gasa jikinta sosai da ruwan zafi zata ji dadi,cike da kunya ta tashi ta koma sama tana jin dan zazzabi zazzabi ajikinta amma bai sauka sosai ba,shawarar umma tabi ta sake gasa jikinta sosai da ruwan zafi daga nan tasake kwanciya kafin lokacin salla yayi,wani sabon baccinne yasake daukarta cikin baccin zazzabi ya dan rufeta wanda ita kanta tasan na tsananin wahalar da ta shane,har Aryan yadawo daga makaranta tana kwance cikin bargo da zazzabi ajikinta bata samu fitowa ba sai zuwa bayan magriba lokacin ta danji dama dama atare da ita.
Khalil kuwa yau bai samu zama ba duk da yana cikin sabgogi masu tarin yawa amma yana ta gwada kiran layin wayar Hanan amma akashe baya samunta daga karshe lokacin da sukayi waya da Aryan shi ke sanar dashi wai bata da lafiya lokacin da Khalil din ya tambayeshi wai ina mommy,suna gama waya da Aryan yaturawa Dr Al'amin text massage akan yaje yaduba Hanan saboda shi bazai samu damar komawa gidanba dan ta can office zasu wuce airport.
Hanan bata san cewa Khalil yasan rashin lafiyarta ba,bayan tayi wanka tayi salla ta sauka kasa har lokacin jikinta akwai zazzabi kadan duk kuma tayi sanyi komai tana gudanar dashi cikin rashin kuzari,suna zaune falo Aryan nata wasa akan dokin robarshi Dr Al'amin yazo,gyara mayafinta tayi sannan tace yakaraso,
"Ranki yadade oga ne yaturo ni yace bakida lafiya inzo indubaki...."
Jin abinda Dr yace bayan sun gaisa sai duk kunya ta kamata to shi Abban Aryan din waye yasanar dashi bata jin dadi? Kodai shi da kansa yasan dole hakan tafaru tunda yasan abinda ya aikata? Cike da kunya tayiwa Dr bayanin yanda take ji nan ya hada mata magunguna yabata yatafi,
Abinci ta dan ci sannan tasha maganin tasake komawa sama ta kwanta,haka taci gaba da kwanciyar nan har zuwa dare kuma sai lokacin ta kunna wayarta domin tana son kiran gidansu dan taji ya Abba yakara ji da jiki,
Mamaye ta fara kira bayan sun gaisa sannan ta kira abbaa wanda ke tare da yaya shamsu sun dan jima suna hira daga bisani sukayi sallama,suna gamawa ta ajiye wayar tashiga wanka, lokacin da tafito tana tsaka da shirin bacci kiran Khalil yashigo,rasa yanda zatayi ta dauki wayar tayi domin wata irin matsananciyar kunyarsa take ji har kiran ya katse bata iya dagawa ba,wani kiran ne yasake shigowa akaro nabiyu wanda shi kansa Khalil bai san dalilin zuciyarsa na nacewa lallai lallai sai taji halin da Hanan take cikiba wai yau shine harda kiran ta sau 2 gaskiya taciri tuta domin hakan ba dabi'arsa bace,
Wayar ta d'aga amma ta kasa cewa komai sai shiru da tayi,numfashi ya dan sauke ahankali daga kwancen da yake sannan cikin taushin murya yace,
"Bacci kike yine?"
Jin abinda yace yasata furta, "A'a" Ahankali,
"Me kike yi?"
"Wanka nayi ina shiryawa....."
"Inzo in tayaki?"
Shiru tayi sakamakon jin abinda yace,gaskiya mutumin nan shima A ne,
"Uhmmm?" Taji yasake bukata,kasa magana tayi amma dai tana rike da wayar a kunnenta,
"Ya jikin naki?"
"Da sauki...." Ta fada muryarta na dan rawa,
"Kinsha maganin?"
"Uhmmmm"
"Allah yakara lafiya...."
Shiru tayi ba amsa,jin har lokacin ta kasa sakewa dashi yasashi yimata sallama ya katse wayar,karasa shiryawa tayi ta kwanta aranta tana sake jinjina rashin kunya irinta da namiji,shikuma Abban Aryan irin nasa salon muguntar kenan yasha coffee mai zafi yakare akanta,lumshe idanuwanta tayi tana murmushi duk da tasha wahala amma moment din yayi mata dadi sannan zata yita ajiyarshi acikin kwakwalwarta har zuwa karshen rayuwarta,da tunanin daren jiya bacci yasamu nasarar yin gaba da ita. Washe gari ras ta tashi sai dai dan abunda ba arasa ba kuma yau dinma wuni tayi akwance wayarta akashe dan har ta kwanta bacci bata bude ba,shi kansa Khalil sai awurin umma yaji lafiyar ta jin umma tace masa lafiya lau yasashi sauke wani gwauron numfashi sannan yayi mata sallama ya katse wayar,
Washe gari tunda ta tashi take shargallenta domin ta wartsake ta warke ras yanzu bata jin ciwon komai kuma sunsha wasansu da Aryan dayake weekend ne,har bayan sallar ishah suna tare afalonta dake sama suna kallo saida yayi bacci sannan tashiga wanka bayan ta kaishi cikin bedroom dinta ta kwantar dashi,rigar bacci ta saka bayan ta shafa humrarta mai sanyin kamshi, wayarta ta landline dake ajiye kan bedside drawer itace tafara ruri nan ta dauka dan jin waye domin dai duk yanda akayi acikin gidanne,
"Meyasa wayarki akashe? Hado min coffee ki kawo min yanzu....." Jin muryar khalil yasata jin cikinta ya tsure to yaushe yadawo? Gashi kuma wai takai masa coffee,ita fa bata manta da kaiwa coffee din ranar nan ba,anan cikin bedroom dinta tabar Aryan ta saka hijab har k'asa sannan tafita zuwa kitchen, mintuna kalilan tagama hada masa ta dauka tafita,yauma baya cikin falo yana can cikin bedroom dinshi hakan yasake tsinkar mata da gaba,cikin fargaba da tsoro tashiga bedroom din nashi nan dinma baya ciki,ajiye masa coffee din tayi tana kokarin juyawa takoma taji motsin fitowarsa daga toilet,tunda tajuya sau daya ta kalleshi bata sake marmarin kallonsa ba,
"Ina zakije kuma?
Taji ya tambayeta idanuwanshi akanta,
"Uhmmm...... Dama.... Dama Aryan zanje inkai dakinshi"
"To je ki kaishi ki dawo"
Kai ta daga sannan ta fita amma bata da niyyar dawowa dan harga Allah ita yanzu tsoron Khalil take yi,shiyasa lokacin da ta koma bata dauke Aryan din ba tabarshi adakinta zasu kwana tare,
Shiru shiru Khalil yaga bata dawoba har yagama komai nasa, k'arfe 1 na dare agogon kan bedside drawer dinshi yanuna turaren midnight mai tsadar yasake fesawa sannan yafita yanufi part din Hanan,
Ganinsu kwance tare da Aryan yasashi yin dan murmushi, Aryan din ya dauka yafita dashi yakaishi dakinsa ya kwantar sannan yadawo bedroom dinta,bacci take yi sama sama taji kamar andauketa,jinta tayi kamar acikin mafarki shiyasa tasake kankameshi tana shakar kamshin jikinsa bayan ta lafar da kanta cikin kirjinsa. Yana rike da ita akirjinsa har part dinshi cikin bedroom dinshi,akan gadonshi ya kwantar da ita nan ta wartsake daga baccin da take yi jin ya ajiyeta,dan bude idonta tayi kadan nan ta hangoshi yana kurbar coffee daga tsayen da yake rike da kugunshi da hannunshi guda daya cigaba tayi da kallonsa har ya shanye,sai da taga ya ajiye yana kokarin juyowa sannan tayi gaggawar rufe idanuwanta, murmushi yayi yarage hasken dakin sannan ya nufi kan gadon,
Kamar yadda ta tsammata yauma bai saurara mata ba ko kadan dan gaba daya gajiyarshi akanta ya sauketa,tasha kuka har muryarta ta dashe,kamar yadda take zargin da biyu yake shan coffee din nan da alama zarginta yazama gaskiya dan da asubah ma sai da yafita da kansa yaje kitchen ya hado yazo yasha tana kallonsa,rage mata yayi itama yamika mata wai tasha, girgiza kai tayi idanuwanta har sun tara kwalla,
"Kisha zakiji dama dama...."
Tana kokarin sake yin musu yaje yakai cup din bakinta nan ta tashi tasha duk da bawai so take yiba. Dana sanin shan coffee din ta tsinci kanta tanayi domin wahalar yanzu har tafi ta daren jiya sai dai shi uban gayyar taga kamar yanzun yafi zakewa fiye da jiyan, jikinta duk yayi tsami ahaka bacci ya dauketa tana rungume ajikinsa yana dan jijjigata alamun lallabawa.
Misalin karfe 9 nasafe ta samu nasarar tashi daga daddadan baccin da ya dauketa mai cikeda hutu domin ko babu komai jikinta da ruhinta sun dan huta,idanuwanta ne suka sauka akan Khalil wanda ke tsaye gaban mirror yayi crossing legs dinsa yaharde hannuwanshi a kirjinsa sanye cikin farar t shirt da farin wando,yanda take kallonshi haka shima yake kallonta kamar zai hadiyeta,
"Good morning" Taji yafada ahankali cikin muryarshi mai sanyi da taushi gamida zaki haka kuma mai cikeda dadin saurare,kai kawai ta daga masa tasoma yunkurin sauka daga kan gadon nashi ma'abocin girma da laushi,
"Hey..... Where are you going?"
"Bedroom dina zan tafi"
"No,kwanta ki huta anan"
Matsawa kusa da ita yayi ya tarairayeta ya sake kwantar da ita sannan yaja duvet ya rufeta, abayanta tajishi shima ya kwanta sannu ahankali ya rungume ta bayan yakai fuskarshi saman tata,irin yanda ya kanannadeta ya kanainayeta ko kwakkwaran motsi ta gagara yi,jin dumin jikinshi da sanyin kamshinsa da ya cika mata hanci bata san lokacin da bacci ya sake d'aukarta ba,shima baccin yayi cikin farin ciki da nutsuwa har zuwa 12 na rana,itace tafara farkawa har lokacin tana kanannade cikin jikinsa sai faman sharar baccinsa yake yi,dan murmushi tayi wanda ita kadai tasan dalilin yinsa sannan ahankali ta daga ido ta kalleshi domin yanzu suna kallon junane,idonshi taga shima yabude wad'anda ke cike da bacci da ido yake tambayar ta menene? Kai ta girgiza masa hakan yabashi damar sake matseta ajikinsa yana shirin komawa wani baccin,
"Uncle yunwa....."
Bude idonshi yayi ya kalleta babu shiri ta dauke nata idon,
Dan sakinta yayi daga rikon da yayi mata hakan yabata damar tashi duk kunya ta cikata dan dakyar take iya kallonshi, ahankali ta sauka daga kan gadon tafita ta nufi sashenta,ada babu abinda take buri kamar zuwan wannan lokaci sai gashi yazo yanzu kuma tana fatan samun rangwame,wanka tashiga tafara yi sannan bayan tafito batare da ta ko shirya ba ta nufi kitchen taje ta hada tea tafara sha sannan takoma bedroom dinta ta shirya sama sama saboda yunwar da takeji,riga da skirt ta saka na atamfa coffee colour sannan ta shafe jikinta da turare tafita duk jikinta babu karfi sosai,
K'asa ta sauka taje ta zuba abinci sannan ta shiga wurin umma suka gaisa nan umman ke bata labarin mutumin nata Aryan wanda saida yagama casa rigamarsa sannan ya tafi makaranta,dariya Hanan keyi har tagama karyawa sannan tafita ta nufi dining table, Khalil ta shiryawa nasa breakfast din kan wani babban faranti dan tasan shima da wahala idan ya karya,kinkima tayi ta nufi sama, lokacin da ta shiga baya cikin dakin da alama wanka yashiga,ajiye masa tayi akan center table tana kokarin fita yafito,
"Ina zaki? Zo..."
Ahankali tajuyo bayan tayi kasa da kanta ta nufeshi,zama yayi gefen gado sannan yakamo hannunta da nashi,
"Dauko min cream din can na shafa...."
Asanyaye ta karasa gaban mirror ta dauko ta dawo batare da tasake kallonsa ba saboda iya farin wandone ajikinsa iya rabin cinyarsa, hannunta yasake kamawa sannan ya zaunar da ita saman cinyarsa,
"Yaufa muna da baki amma kinsa na manta...." Ya karasa maganar yana kallon agogon dake ajiye kan bedside drawer, dan kallonsa tayi jin abinda yace wai itace tasa yamanta shi dai yasa,jin ana kiran sallar azahar yasashi tashi domin shiryawa dama ita kam tajima tana neman hanyar guduwa hakan yabata damar tserewa,
Cikin kwanaki biyu kacal har Hanan ta sauya,duk da ta rame amma hakan bai hana fatarta yin fresh ba dan har wani sulbi take yi tana sheki gefe daya kuma ga fargaba da ladama dake sake tsurar da ita tana faman karewa kamar kudin guzuri kana ganinta kaga amarya domin tayi wani irin kyau na musamman,
Yau dai takama ranar juma'a kuma yau Khalil yace mata su abbanta zasu zo shiyasa tun bayan fitar Khalil din ta shiga kitchen ta dorawa su abba girki,misalin karfe 1 na rana suka karaso shida yaya shamsu,murna wurin Hanan ba a magana nan ta shiga gabatar musu da kayan motsa baki da abinci,
Tana tare dasu suna gaisawa Abba nasanar da ita dalilin zuwansu Khalil yakaraso wannan dalilinne ma yasa bata gama jin abinda Abba keson sanar da itaba. Ita dai ta lura tsakanin Khalil da abbanta akwai aminci mai karfi domin yau dinma sai hira suke yi cikin raha da farin ciki kuma hatta abinci ma tare suka ci,
Bayan sallar la'asar Khalil yace ta fito suyi sallama dasu abba zasu wuce,wasu hawaye ne suka fara kokarin zubo mata tun kafin ta karasa,
"Uwar masu gida.... Mijinki yadage akan lallai lallai sai naje k'asar chairo anduba ni saboda wannan ciwon nawa duk da nace masa yabar kudinsa amma yadage..... Kici gaba da yiwa mijinki biyayya, Allah yayi muku albarka,tare da shamsuddini zamu tafi"
"To Abba Allah yasa aje asa'a, Allah yabaka lafiya..."
Hawaye ne suka cigaba da wanke mata fuska har su Abba suka tafi tare da Attahir drivern Khalil wanda yadauki Aryan suka tafi,duk abinda take yi Khalil na ganinta,ganin ta zauna kan kujera tana kuka yasashi karasowa hannunta yakamo ya hadata da jikinsa ahaka yanufi sashensa da ita..................................鉁嶐煆?
_Wannan littafin na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din._
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/15/20, 3:50 PM - Ummi Tandama: 50
***Tana rungume ajikinsa har cikin falonshi wanda ya wadatu da sansanyan kamshi mai dadi,
Zama yayi kan kujera ya zaunar da ita ajikinsa yana kallonta,
"Wannan kukan na menene.....? Meyasa wai bakya girma da kuka ne?"
Jin abinda yace yasata sake bare baki taci gaba da kukanta,kukan ne ya tsaya cak sakamakon harshensa da taji kan fuskarta yana kokarin lashe hawayen dake gudana kan fuskarta, cigaba yayi da lashe mata hawayen daga karshe ya tsaya akan dan kyakkyawan bakinta dake karawa fuskarta kyau da annuri,
Sun jima kadan aduniyar masoya mai cike da tsantsar so,kulawa da kuma farin ciki marar yankewa,dago lumsassun idanuwanshi yayi ya kalli nata idanuwan dake lumshe tayi luff tana amsar sakonnin da yake kokarin bata, hannunshi cikin rigarta yafurta,
"Tashi kije ki hado min coffee....."
Bubu shiri ta bude idonta,hada ido sukayi ta mayar da nata ta rufe tana makale masa kafada alamun A'a, murmushi yayi yashafi kanta,
"Yaushe kika fara kiwa?"
Shiru tayi bata ce komai ba,saida ya tabbatar ta saki zuciyarta kukan yatafi sannan yafita,ita kam cigaba da kwanciyar ta tayi har tsawon wani lokaci,saima da su Aryan suka dawo ne sannan ta samu ta tashi tabishi zuwa dakin kayan wasanshi wanda har aka kira magriba suna ciki bata saniba lokacin Khalil har yadawo yaje ya dauro alwala yashiga part dinta bai gansu ba,da yaje wurin umma shine take sanar dashi wai watakila suna garden ko kuma yaduba su dakin kayan wasan Aryan,
Yana bude kofar dakin kuwa ya hango Aryan akan dokin wasanshi mai taya ita kuma tana zaune kan kekensa,ta bayanta ya lallaba yaje ya rufe mata ido,wani gwauron numfashi taja sannan cikin faduwar gaba tace,
"Uncle...." Sakamakon kamshin turaren jikinsa da taji,
"Baku san lokacin salla yayi bane? Wasan ya isa haka sai kuma gobe, Aryan zo mutafi salla..."
Mikewa tayi daga kan keken babu zato taji ya hadata da jikinshi ta baya bayan yakamo waist dinta,kwacewa tayi ta gudu tafice daga cikin dakin,
Alwala taje itama tayi tai salla duk mamakinsa yacika ruhinta lallai ashe shima Khalil dan yine amma shine take yimasa kallon salihi,miskili ma'abocin girman kai da dagawa koda yake duk wanda bai fahimceshi ba kallon da zaiyi masa kenan saboda shi ko magana bai fiya sakin baki yayita yinta ba komai atakaice yake fadarshi,wurin umma ta sauka wanda can ta iske Aryan umma nabashi tuwo,
Bayan sallar ishah sashen Khalil suka shiga ita da Aryan,zaune suka sameshi da laptop akan cinyarshi ga kuma waya makale a kunnenshi yanayi,
"Agogo sarkin aiki....." Ta fada acikin ranta,samun wuri tayi ta zauna idanuwanta akan TV amma jikinta na bata idanuwan Khalil akanta suke domin duk tajita atakure takasa sakewa,dan satar wurin da yake tayi nan taga yayi mata kyarr da ido ko kiftawa bayayi,amma koda suka hada ido sai ya basar,tun safe ya lura da ita bata sakin jikinta yanda yakamata sai wani dingishi dingishi take yi tana tafiya kamar wacce ke taka kaya,
Sai bayan da yagama wayar sannan yamayar da hankalinsa kan Aryan wanda ke kokarin yimasa ta'adi ajikin laptop dinshi,tana jinsu bata tanka ba har tsawon wani lokaci ahaka bacci ya dauke Aryan yana kan cinyar Khalil,
"Zo...." Taji yace idanuwanshi na kan system dinshi,kamar bata so haka ta tashi ta nufeshi tanata faman harararshi ta gefen ido saboda ita kadai tasan irin wahalar da yabata duk yabi ya raunatata,
"Gani...."
Daga kanshi yayi ya kalleta sannan ahankali yace,
"Wai meke damunki ne naga kina yin komai sanyi sanyi.... Baki jin dadi ne?"
Saida ta dan turo baki sannan tace,
"Ni lafiyata kalau..."
Murmushi yayi acikin zuciyarsa yace, "to za ayi min halin ne na rashin kunya?"
Amma afili kuma sai yace,
"To shikenan tunda lafiyar ki kalau"
Aryan ta dauka ta fita,saida ta kaishi dakinsa ta kwantar dashi sannan ta wuce nata part din ta yi wanka da ruwan zafi sannan tazo ta shasshafa turare da humra masu kamshi sosai wadanda ke sanyawa zuciya nutsuwa,wata farar rigar bacci ta saka marar nauyi sannan ta dora dogon hijabi pink ta fita bayan ta dauki wayarta,ita kanta bata san dalilinta na zuwa sashensa ba amma dai haka kawai ta tsinci kanta da nufar sashen,
Lokacin da ta shiga bedroom din nasa yana gefen gado kwance yana waya da sabon PA dinsa,katse wayar yayi sannan ya mika mata hannu,cike da kunya ta kama nasa nan yajata jikinsa,
"Tashi ki kawo min coffee...."
Makale kafada tayi kamar dazu,
"Jikinane babu karfi,bacci kuma nake son inyi"
Duk da taji abinda yace kin tashi tayi domin atsorace take dashi,
"Ok ni bari naje da kaina..."
Tun kafin ya karasa ta rikeshi gam gam ta yadda bazai iya tashi ba,
"Nidinma banida ikon zuwa da kan nawa?"
"Uhmm" tafada tana mai daga masa kai,
"To shikenan kwanta kiyi bacci...."
Kin kwanciyar tayi har saida ta tabbatar cewa dagaske shima baccin zaiyi, ajikinsa ya rungume ta tsantsan yana shakar kamshinta.
Hakace taci gaba da faruwa duk Hanan tabi ta sakawa ranta tsoro da fargaba wannan dalilinne yasa har gobe bata dan murmure ba gaba daya ma ji take yi kamar ta tafi gidansu ta huta amma abun haushi ranar da Khalil yasa aka kaita kanon ma wuni guda tayi ta dawo yaki yabarta ta kwana haka ta kwana tanata yimasa buntsire buntsiren baki tunda tafi kowa sanin dalilin nashi na hanata ta kwana,
Bayan zuwanta kano da kwana biyu suka tafi gombe gaba dayansu saboda bikin saukar alqur'ani da zasu halarta na su Sarah,tunda sukaje hajiya ta sake jan Hanan ajikinta domin ta sake karewa amma kuma tayi kyau ba laifi,ranar walimar kuwa har anty maamy Hanan tagani amma ko gaisawa basuyi ba saboda suna zazzaune su uku da Lubnah da Muneerat da anty maamy tazo sai kawai ta tsallake Hanan ta gaggaisa da sauran tabe baki Hanan tayi aranta taje aje dai tunda ba aurar mata miji ba,
Washe gari khalil yace su shirya zasu koma nan hajiya tace A'a yaje shi kadai su Hanan yabarsu su dan huta tunda ba zuwa suke yiba sai ta kama,badan yasoba haka yasa Aryan agaba suka tafi saboda shi yana zuwa makaranta, Hanan kam murna tarinka yi har acikin zuciyarta dan ko babu komai zata huta da fitinar Khalil,
Tun bayan tafiyar su hajiya ta maida hankali wurin kulawa da Hanan tana sake gyara ta ta hanyar sawa ahado mata tukudi na musamman domin wannan ramar tata bata yiwa hajiya dadi, kullum suna waya da Khalil da Aryan wanda gidan sam baya yimusu dadi saboda rashinta,
Satinta biyu Khalil yazo daurin aure kuma yasamu ya karaso gidan lokacin da yaga Hanan sai yaga ta dan murmure ba kamar daba, murmushi yayi ya shafi kumatunta yana fadin,
"Yar gidan hajiya me hajiyan take baki ne kike cika haka?"
"Bacci"
Wani murmushin yasake yi,
"Bacci take barinki kiyi? Wato nan kuma dani akeyi kenan ana nuna min nine ke hanaki bacci ko? Zaki dawone"
Makale kafada tayi tana cewa saita fadawa hajiya,ranar ma duk yanda yaso sutafi tare da ita sukoma Abuja hajiya cewa tayi yabarta ta kara kwana biyu,bai damuba saboda shi kadai yasan shirin da yakeyi.
Bayan tafiyar shi da kwana uku yaturo driver yazo ya tafi da ita wai akwai inda zata rakashi,aranar da ta koma aka gama dukkan shirye shirye bayan sallar magriba driver yakaita airport wanda wannan shine karo nafarko da zata hau jirgin sama atarihin rayuwarta,gabanta sai dar dar yake,tana shiga taganshi tsaye yana jiranta sanye da kananan kaya jeans da t shirt,tare suka zauna ga kujerarshi ga tata yana rike da hannunta,
"Yau kuma gudu ya kare ko? Zamuje inda babu hajiya ai sai muga ta karyar gudu"
"Dan Allah kayi hakuri....." Tafada idanuwanta na cikowa da kwalla,
"Ban hakura..."
Kuka tafara yi hakan yabashi damar dan rungume ta kadan yana shafar bayanta babu bata lokaci bacci ya dauketa ba ita ta tashi ba saida jirginsu ya sauka,
Yana rike da ita har cikin motar da zata sadasu da lafiyayyen hotel din da zasu sauka,ita kam yar kauye ta zama domin bata taba ganin hadadden birni makamancin wannan ba ko acikin mafarki kasa boye kauyancinta tayi har saida takaita ga tambayar shi lokacin motarsu na tsakiyar titi suna lilawa,
"Uncle nan inane?"
"Rome...... K'asar Italy"
Lumshe idanuwanta tayi ta kwantar da kanta akafadarshi bayan ta makaleshi kamar tana jin tsoron kada wani ya kwace mata shi,basuyi wata doguwar tafiya ba suka isa hotel din da zasu sauka. Ayanda ta dan lura kamar yana mutukar son k'asar Italy domin yana yawan zuwa akai akai,
Lokacin da suka shiga masaukinsu amutukar gajiye suke duk da cewa dai ba wani aiki suka yiba inbanda zama to amma zaman ma wani lokacin sai ahankali,
Itace tafara shiga bathroom domin yin wanka shikuma yana zaune yana duba wayarshi wacce take akashe tun bayan shigarshi jirgi sai yanzu ya kunna,sak'onni ne rututu suketa kokawar shigowa har har Hanan tafito kasancewar ba wani jimawa tayi ba kawai ta dan watsa ruwane ajikinta gashi tana fashin salla,
Yana zaune inda ta tafi tabarshi ta bude trolley bag dinta ta ciro pad da pant,dan daga kai yayi ya kalleta ganin pad din dake hannunta yasashi dan tsuke fuska,dan karamin tsaki yaja sannan ya ajiye wayoyinshi yawuce bathroom yana wani ciccin magani,
Kafin yafito ta samu ta shirya agaugauce tana kokarin saka night gown yafito saida ya harareta sannan taji yace,
"Karki saka wannan rigar baccin bana bukata...."
Daga haka yawuce gaban kayansa yabarta tsaye rike da riga ahannu, kayan baccinsa ya dauka zai saka hakan yasata juyawa tafita zuwa falo ta nemi wuri ta zauna ita bata saka rigarba sannan kuma ita bata ajiye ba,
Shi kam bayan ya gama shiryawa cikin fararen kayan baccinsa sallolin dake kansa yasoma gabatarwa,yana cikin sallar Hanan tashigo cikin dakin fuskarta awani rakwarkwabe kamar zata fashe da kuka,gefen gado tasamu ta zauna har lokacin tana rike da rigarta ahannu,tana nan zaune tana dan gyangyadi ya idar da sallar baiyi mata magana ba yatashi yafita mintuna kadan yadawo dauke da abinci,
"Sauko kici abinci...."
Batare da tayi musu ba ta sauka ta zauna suka fara cin abincin sai wani shasshan kamshi yake yi domin shi duk zatonshi Allah ya amshi addu'ar shi tasamu juna biyu tun a first night ashe da sauranshi,
Shine yafara tashi sannan yahaye gado ya bararraje yana latsa wayar shi ahaka itama tagama ta zauna saman gadon adan darare kamar mai jin tsoron wani abu, hannu yamika mata kamar koda yaushe takama sannan yajata jikinsa ya rungume cikin sanyin murya taji yana cemata,
"Tunda ga duvet yau bana bukatar wannan rigar baccin taki mai takura mutum......."
Ita kam ji tayi kamar ta nutse saboda tsananin kunyarshi,wai meyasa shi baya jin nauyinta ne? Har yagama rashin kunyarsa ita dai bata motsa ba haka idanuwanta ma bata budesu ba gashi inbanda bacci babu abinda take bukata amma koda tayi korafi sai cewa yayi ai yanzu lokacinsa ne ba lokacin bacci ba.
***
Kimanin watanni bakwai kenan da bikin mujahid da sumayya wacce yanzu haka take dauke da cikinta dan kimanin watanni bakwai din kuma tuni har ya bayyana tunda jimawa,
Zaune take afalo tana gogewa mujahid k'ananan kayanshi gefe daya kuma tana kallon tashar dake haska finanan turanci inda take kallon wani kayataccen Nigerian film mai suna the perfect couples,ahankali taga yabude kofa yashigo,musayar murmushi suka yiwa junansu sannan yazo ya dan rungumeta kadan ta bayanta,
"Matar alkhairi sannu da kokari....."
"Sannu da zuwa mijin arziki"
Dariya yayi yashafi cikinta,
"Ya babynmu?"
"Baby na lafiya dazun nan tagama motsi"
Murmushi yayi yai zaman dirsham shima kamar yadda yaga tayi sannan ya karbi gugar yaci gaba dayi,
"Kin san wani abu? Har yanzu inata nazarin sunan da yadace musakawa babynmu....."
"Wanne kake ganin zamu saka mata"
Kashe iron din yayi ya zuba mata ido,
"Akwai sunan da najima inada burin sakawa 'yata (Sa'adatu Hanan)"
Murmushi tayi ta gyara zamanta sannan ta kalleshi tana murmushi,
"To yanzun me zai hana ka cika wannan burin naka kayi mata takwara?"
"A'a ni tsorona kar kice da biyu nasaka sunan Hanan"
"Kaji yaya mujahid da wani magana,to ni ina ruwana dan kasawa yarka duk sunan da kayi niyya? Ni ai nadaina kishi da Hanan"
Murmushi yayi yasake rungumeta yana saka mata albarka tare da addu'ar sauka lafiya.
***
Washe gari Hanan bata tashi daga bacci da wuriba kasancewar ga uwar gajiyar da take addabarta sannan ga rashin bacci akan lokaci wannan dalilinne yasa har k'arfe 9 nasafe takai tana bacci batare da Khalil ya tasheta ba sanin ba salla zatayi ba, ahankali take bude idonta kamar bata so ko mai tsoron ganin wani abu tayi luff cikin bargo,bata ga Khalil ba hakan yabata damar cigaba da kalle kallenta acikin d'akin ahaka har idanuwanta suka sauka akan tamfatsetsen mirror din dake cikin dakin,
_Good morning beautiful!_
Abinda taga anrubuta kenan baro baro ajikin mirror din da red din janbaki, murmushi tayi ta tashi zaune tashiga wanka tana sake yaba kyau da haduwar hotel din wanda Allah ne kadai yasan adadin kudin da Khalil din yabiya,cikin farin ciki da annashuwa tayi wanka tafito tazo ta shirya cikin wata bakar riga iya gwiwa,tana kokarin fesa turare yashigo dauke da breakfast a hannunshi,tsayawa yayi kawai yana kallonta saboda ba karamin kyau tayiba,
Kayan hannunshi ta karba sannan ta danyi dage ta yiwa kumatunsa kiss,
"Good morning Uncle"
Rungumeta yayi yana shafar kumatunta,
"Morning mai period,how was your night?"
Murmushi tayi ta lumshe idanuwanta saboda ta lura period dinnan nata ya tsaya masa arai kuma yana jin haushinsa dan tun jiya yaketa faman yin tsaki da yaga pad,zaunar da ita yayi kan cinyarsa sukayi breakfast daga nan kwanciya suka sake yi har lokacin sallar azahar,zuwa yamma taci gayunta cikin jar doguwar gown mai stones tayi rolling suka fita,shi kansa Khalil din shima kananan kaya yasaka da black face ya sakaye fuskarshi,yana rike da hannunta suka rinka zuwa wurare daban daban na shakatawa da debe kewa sunata yin video call da Aryan,gaskiya k'asar tayi mata kyau sannan ta burgeta domin birnine na can kololuwar karshe basu suka koma gida ba sai karfe dayan dare amutukar gajiye. Ai ita kam kasa tabuka abun arziki tayi duk da taga shi lamarin nasa ba sauki,hannayenta ya kama gaba daya yakai jikinsa cikin rada yake cemata,
"Ke yar kauye ce......, Kamar kina tsoron tabani,ko har yanzu kunyar ce bata gama sakinki ba? Kin barni inata wahala ni kadai bayan ba wani abu zan samuba...... Kema kiyi wani abu"
Ahankali hudubar su anty badi'a tafara dawo mata cikin kwakwalwarta tiryan tiryan wacce suka yimata a gombe lokacin da za akawo ta,ji tayi kamar yanzu ne suke yimata amma kuma bata san ta yadda zata tunkareshi da wannan babban lamari ba saboda wallahi tana bala'in jin kunya ga tsoro wanda bata san ko na menene ba,
"Wai ke waya fada miki idan akazo wannan bangaren ana jin kunya? Idan haka zaki rinka barina babu kulawa,babu tarairaya sai dai kisaka ni gaba da kuka muna komawa gida zanyi aure......"
Ai tana jin haka bata san lokacin da ta bude idanuwanta ta kalleshi ba,
"Aure uncle......?" Ta tambayeshi bakinta har yana rawa,juyawa yayi yai rigingine batare da ya kalleta ba yace,
"Yes aure...... Kuma bazawara zan aura wacce tasan aure tasan yanda zata kula dani"
Shiru tayi tana kallonsa nan zuciyarta tasoma bugawa da wani irin karfi wanda tafi kyautata zaton na tsantsar kishine,gaskiya tana da zafin kishi na ajin karshe akansa,shima sanin tana da zafin kishin ne yasashi fadin haka ko wai zata nutsu ta gyara tunda yaga abin nata kamar harda sakarci,
Nutsuwa tayi tana saurarar fadan da zuciyarta keyi mata "kema hanan kina abu kamar wawiya, tunda har yafito ya nuna miki ga abinda yake so meyasa bazaki daure ki cije kiyi masa ba? Gashi nan ai kuna komawa gida yace zaiyi aure waya sanima ko mijin anty maamy ya mutu ya aureta shikenan kin zama yar kallo...." Wata kwalla taji ta zubo mata nan ta share kwallar sannan cikin sanyin murya tace,
"Uncle..... Kayi hakuri bazan sakeba"
Shiru taji yayi mata cikin dar dar taja jikinta zuwa gareshi ta rungumeshi tare da yimasa wani lafiyayyen kiss a kumatunsa irin yanda yake yimata, rungume ta taji yayi sannan cikin farin ciki taji yace,
"Yawwa to ko kefa,amma da kamar ba yar makaranta ba..... Ai ko a school ana practical ko?"
Kai ta daga masa,
"To kema lokacin da zaki fara practicing abubuwan da na koya miki yayi.... Don't be shy"
"Kai Abban Aryan akwai rashin ta ido...." Ta fada acikin zuciyarta,kamar mai shirin taba wutar lantarki haka take tabashi awani d'arare,haka dai da taimakon sa da komai ta dan tabuka abun arziki, rungume ta yayi yana cemata har yanzu batayi wani abun azo ayaba mata ba,yana shafar kanta har bacci ya dauketa shi kam tashi yayi ya tsaftace jikinsa ya dan gabatar da sallolin nafilfili zuwa karfe 3 na dare yaje ya kwanta abayanta tare shiga cikin jikinta sosai. Tsabar gajiyar da tayi ai har gari yawaye bata ko juya ba,shima Khalil din yau saida yamakara sallar asubah.
Ta rigashi tashi,bayan tafito daga wanka tana shiryawa shima yafarka,wankan yashiga shima yayi yafito rike da dan karamin towel daga shi sai gajeren wando,
Zaune yaganta tana kokarin daure gashinta ta saka wata yeluwar riga mai budadden kirji amma dan kauyanci sai ta saka mayafi karami ta rufe kirjin nata, zama yayi gefen gado yace,
"Zo kibani wannan jakar....."
Tana zuwa ya yaye mayafin yana fadin,
"Ba kiji abinda nafada miki jiya ba ko? Kina son nakara auren dai kenan....."
Girgiza kai tayi tana bata fuska,kan cinyarsa yadorata sannan cikin taushin murya yace,
"Zan auro yar birni tunda ke yar kauye ce,zan auro wacce ta iya soyayya,wacce zata rinka barmin surarta abude koda yaushe ina gani ba irinki da kike rufewa ba...."
"Nadaina....." Ta fada tana turo baki,shiru yayi mata yamaida kallonsa kan kirjinta wanda ya bayyana ta saman rigar da ta saka,
"Kaji uncle...." Kunya ce ta kamata lokacin da ta fuskanci abinda yake kallo,babu yanda ta iya haka ta daure ta biyeshi kafin daga bisani sukayi breakfast bayan yayi sallar azahar suka fita. Yauma kamar jiya sunsha yawace yawace dan basu suka dawo ba sai karfe 1:30 nadare, kuma yau dinma bai barta tasamu bacci ba sai wurin karfe 3 saura kwata shiyasa washe gari babu inda suka je a masauki suka wuni suna shan baccinsu sai da daddare ne suka samu dan fita gaban harabar hotel din suka mike kafa suka dawo, Hanan dai tana jin dadin kasar saboda ko ina ya hadu ashe shiyasa Khalil idan yazo yakoma suke ganin ya canja yayi kyau kamar wanda aka canjawa halitta ko fata.
Yau kam tun asubah suka fita tana sanye cikin purple din Dubai gown ta dan yafa mayafi karami akanta kafarta tasaka takalmi toms shima purple sai yar karamar side bag wacce ta rataya hannunta cikin na Khalil wanda yake sanye da fararen jeans da t shirt fuskarsa boye cikin bakin gilashin ido mai dan girma,kai masha Allah dan kasa boye farin cikinta tayi sai daukarsu selfie take ta faman yi har suka shiga cikin wani kyakkyawan jirgin ruwa mai daukar akalla mutane goma,tana zaune gefenshi ga kugunta ga nasa ya rike waist dinta da hannayensa kanta bisa kafadarshi. Sunyi doguwar tafiya har gari ya waye rana ta dan fito duk da bawai ranar mai kwal dinnan bace,awani hamshakin katafaren bakin ruwa suka sauka gaba daya ruwan kalarsa blue ce mai sheki da daukar ido sai ambaliya yake yi ga mutane tsilla tsilla suna hada hadarsu,kamata Khalil yayi yafito da ita yana rike da hannunta,
"Wai uncle ta ina duk kasan wadannan wuraren.....?"
"Tun ina yaro nake mafarkin zuwa wadannan manyan biranen na duniya tare da wata cute baby....."
Wani kyakkyawan masauki wanda aka gina akan tsauni atsakiyar ruwan suka je can Hanan tayita baje idanuwa tana kallo gaba daya takasa bambance tsakanin can Rome inda suka sauka da nan Florence ina ne yafi wani haduwa,
Gaskiya Khalil yayi kuma ya hadu domin ya zagaya da ita taga wurare ta karkashe kwarkwatar idonta sosai kuma ayanda ta lura shima dan harka ne wato dan soyayya ma'abocin son ashana da iyali,basu suka koma Rome ba sai dab da asubah,ko ba afada mata ba tasan gogan nata mutum ne mai son yawace yawace da harkar bude ido saboda ko agida Nigeria ba zama yake ba bare nan da yakeda yancin zuwa duk inda yake so. Kwanansu biyu adaki babu inda suke zuwa tun bayan dawowarsu daga Florence sai dai suci abinci susha soyayya suyi waya da yan gida,
Yammacin yau yagama shirya musu kayansu tsaf suka kara gaba zuwa birnin Venice dake nan k'asar ta Italy, Hanan duk da tana cikin murna da farin cikin zuwa wuraren da bata taba mafarkin zuwa ba amma adarare take da Khalil saboda yau zata samu tsarki duk da kwana biyu tasake dashi tunda suna zaune daki daya zasu kwana tare zasu tashi tare su wuni tare,
Yanzunma awani dan karamin hadadden hotel suka sauka,bayan sunci abinci sunyi salla Khalil yafita shi kadai yace ita ta kwanta tayi bacci,baccinta kuwa tasha kamar yadda yace,zuwa magriba yadawo hannunshi rike da wayarshi suna yin video call da Aryan,karbar wayar tayi suna yiwa juna dariya itada Aryan ko dariyar ta mecece oho,har Khalil yayi wanka yafito yayi salla basu gama wayar ba da zasu ci abincine yakarbe wayarshi ya kashe.
Shiru tayi tai jugum tana jimamin wannan lamari Khalil yace tare zasu yi wanka saboda ya kyalla ido yaganta tana yin salla, tunaninta ne yatsaya daidai lokacin da yashigo cikin dakin kasa tayi da idonta lokacin da taga yana kokarin rage kayan jikinsa,
"Oya muje...."
Tashi tayi kamar kazar da kwai ya fashewa aciki tawuce gaba yana biye da ita abaya har cikin bathroom din wanda ya hadu karshen haduwa,janta yayi cikin ruwa bayan ya warware towel din jikinta,tun tana jin kunya har ta warware ta saki jiki,daman yau kam ita kanta tasan babu daga kafa domin kamar Khalil baida hakuri da kawaici a wannan bangaren,duk da yau taji lamarin da sauki sai dai amma akwai tarin gajiya da tarin bacci wadanda suka hadu suka yimata rubdugu shiyasa ta wuni tana bacci washe garin ranar. Zamansu a Venice yafi na ko ina tsaya mata arai domin acan ne suka fi kulawa da juna da tattala juna tunda yanzu tafi sakewa dashi wannan kunyar tata da Khalil ke kira da kauyanci ta dan rageta,kayan shan iska take sakawa na wulakanci suyi ta shanawarsu da daddare kuwa sallama take yi da kowacce irin suttura komai kankantarta domin saukakawa gwarzon nata,
Tunda Khalil yafada mata saura kwana biyu su koma gida duk take jin babu dadi kamar kar su tafi saboda yanzu tayi sabo dashi ta shaku dashi yanzu suna komawa gida zai fara yimata wahalar gani sai dare yau yana kano gobe yana bauchi,zama yayi kusa da ita yana murmushi shigowar shi kenan,
"Hey...... Meyake damunki ne?"
Shagwabe fuska tayi kamar zatayi kuka,
"Nasan idan muka koma gida zan daina ganinka koda yaushe......"
Murmushi yayi yakama hannunta yana matsawa ahankali,
"Kekuma kina son ganina koda yaushe ko?"
Kai ta daga masa kwalla na shirin sauko mata,hadata yayi da jikinsa yana bubbuga bayanta alamar kulawa da rarrashi, ahankali ya zaro wani dan karamin akwati daga cikin aljihunsa ya bude yaciro dan karamin zoben gold mai mutukar kyau ya kama yatsanta,saida yafara zira zoben cikin yatsanta na tsakiya sannan ta dago tana kallonsa cikin farin ciki tasake rungume shi tana cewa,
"Thank you uncle...."
"I love.....you....." Yafada kamar mai koyon magana ai duk sai taji ta rude jin abinda yafito daga bakinsa kamar cikin mafarki,fuskarshi yasake mika mata taci gaba da yimasa ruwan kiss tako ina.
Ranar alhamis da yamma suka sauka a Nigeria,tsayawa kawai Khalil yayi yana kallon Hanan da Aryan lokacin da suka rukunkume juna suna murna,kamar yadda Hanan ta tsammata washe gari Khalil yasoma tafiye tafiyen nasa da yasaba kullum baya dawowa gidan sai dare wani lokacin ma sai tayi bacci. Wannan watanma da yaga tana period sai duk yabi ya bata rai ya tsuke fuska daga karshe sai cewa yayi umarah zai tura hajiya da umma barira da Aryan suje su tayashi da addu'a tasamu ciki tunda har yanzu yaji shiru,zaro ido Hanan tayi sannan cikin mamaki tace,
"Kai uncle dan rashin kunya hajiyan zaka fadawa haka?"
"Ni ai babu maganar da bamayi da hajiya,barima kiga..."
Ganin zai dauki wayarshi yasata rigashi dauka ta gudu,silifas dinshi yasaka yabi bayanta har zuwa sashenta,tsaye ya sameta a corridor tana yimasa bincike awayar,
"Duk abinda kika gani babu ruwana bincikenki ne yaja miki dan nayi budurwa jiya"
Murmushi tayi tai tsalle ta dale bayansa tana tambayar shi wai ina nura PA saboda kwana biyu bata ganinsa,riketa yayi Sosai abayanshi sannan yabata amsa,
"Na koreshi tun tuni......"
"Saboda me?"
"Saboda naga yana kokarin shiga gonata......."
"To Uncle kuma basai kabarshi ba iyakaci fa idan yagama nomanshi ya....."
Bata karasa ba taji ya birkitota tadawo gaba, makalkale shi tayi da kafafuwanta idonta cikin nashi yake kallonta,
"Kin kuwa san abinda kike fada? Shine fa wannan da yarinka yimiki text massage dinnan,harda sake sabon layi saboda yazaci bazan ganeshi ba....."
Shiru tayi aranta tana cewa lallai kam biri yayi kama da mutum ashe shiyasa idan yashigo cikin gidan koda yaushe idonshi akanta. Kamar yadda Khalil yace saida yatura hajiya da umma barira umarah amma banda Aryan saboda shi lokacin suna yin exams a school shiyasa Khalil yajira sai bayan yagama,suna yin hutu kuwa suka tafi tasu umarar shida Aryan da Hanan,bayan sun gama suka nufi k'asar Scotland daga can kuma suka wuce Australia, Hanan kam taga manya manyan biranen duniya kuma tasha tarairaya wurin Khalil,tun daga can take jin jikinta yana wani canja mata bata jinsa daidai amma dai bata fadawa Khalil ba har suka dawo gida Nigeria nan abu yaci gaba da karuwa kasala da ciwon jiki ga kuma yawan bacci dake damunta ganin duk kuzarinta ya ragu yasa Khalil kiran Dr Al'amin,test din farko da Dr yayi mata ya fahimci tana da juna biyu, Khalil ji yayi kamar ya goyata har Aryan yarinka fadawa wai yakusa yasamu sister ko brother,ita kam kyautar wata dambasheshiyar sarkar diamond yabata kuma tun daga ranar kulawar da yake bata ta karu lallaba ta yake yi kamar kwai. Koda cikin yagirma kuwa ai Hanan daina fita tayi wai ita kunya take ji kaza da kaza dariya Khalil yarinka yimata shikam yawonsa bashi nan bashi can yau yana wannan kasa gobe yana waccan...................................鉁嶐煆?
_Wannan littafin na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din._
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/17/20, 9:07 PM - Ummi Tandama: *Littafina na kudine ga duk wacce keda bukatar karantawa saita turo naira 200 ta account dina 3112877210 Aishatu Ibrahim first bank,sai aturo shaidar biya ta wannan number din 07044644433 ko kuma recharge card na MTN ko atuntubi marubuciyar kai tsaye ta wannan number din 07044644433*
*51*
***Fad'ar irin kulawar da Khalil ke baiwa Hanan bata bakine ko kuma kauyanci domin yanzu ne tagane ainihin irin soyayyar da yake ikirarin yana yimata kuma hatta hotunan Ramlat da ada yake ajiye dasu akan drawer gefen gadon baccinsa ayanzu duk ya kwashesu ya adana a inda yadace,
Hanan haihuwa ko yau ko gobe domin cikinta yagama tsufa kuma ya isa haihuwa,tunda ta tashi yau dai haka haka take jin jikinta amma da yake bata san takan abunba shiyasa bata kawo cewa haihuwa bace kuma dama jiya a sashen Khalil ta kwana shikuma sai shegen rashin hakuri duk da ga halin da take ciki lallabata yake yasha sha'aninsa, asubanci yayi yau yafita zaije kasar Ghana,
Abinci ta zubo soyayyen dankali da farfesun hanta ta zauna kenan agefen kujera taji wani abu ya tsurkuneta haka dai ta daure ta cuccusa dankalin tasha ruwa nanfa taji ciwo kamar karuwa yakeyi kafin wani lokaci har ciwon ya tsananta,umma ta kira awaya babu bata lokaci suka tafi asibitin da take zuwa awo wato alkhairi clinic and maternity,
Tun safe take nakuda amma har dare bata haihu ba, khalil yana can amma hankalinsa yana gida musamman ma da yakira hanan bai sameta ba wayar umma da Aryan kuma duk ba adauka idan yakira, daren ranar Hanan bata yi bacci ba saboda da ciwon nakudar ta kwana zuwa asuba ta haifo katon jaririnta sambalele,dakyar ta iya bacci saboda azabar da take ji atare da ita karshe ma saida aka hada da yimata allurar bacci,sai lokacin umma tasamu zarafin kiran yan uwa da abokan arziki ta sanar musu da haihuwar Hanan, ai tun aranar yan uwa suka yiwa garin Abuja cincirindo dan asibitin cika yayi taf da yan uwan Khalil da na Hanan shima Khalil adaren ranar yadawo, lokacin da yashiga d'akin tana kwance angama yimata karin ruwa tana bacci,goshinta yayi kissing ya shafi kumatunta sannan yafita cikeda farin ciki marar misaltuwa,ita Hanan bata san yanayi ba saboda baccine take yinsa kamar wata yar kwaya ga uban ciwon dake damunta wanda bai saketa ba har yanzu. Washe gari tunda sassafe Khalil yadawo asibitin shida Aryan,zuba musu Ido kawai tayi tana kallonsu saboda yadda suketa murna suna kwakwume da jaririn wanda Khalil yayiwa huduba da Muhammad Ayaan,
Kwananta uku suka koma gida kuma aranar kaf yan gidansu suka zo kafatanin ilahirinsu dan harda mamaye,ganin girman jaririn yasa anty salaha cewa ai dole tasha wahala ji jariri kamar dan kwana arba'in? Ita dai bata ma magana dan ko zama saida dabara sakamakon irin uban dinkin da tasha,tafiya ma wannan ba son yinta take yiba sai ta zama dole,
Lura da yanda take ciccije lips idan tana zaune ko tana tafiya Khalil yayi nan yasata agaba da tambayar menene matsalar? Turo baki tayi cikin shagwaba tace,
"Nida aka dinkeni kamar bayan kwarya......"
"Insha Allah anyi nafarko kuma anyi na karshe ai hakan bazata sake faruwa ba..."
Jin abinda yace yasata yin watsi ma da maganar saboda duk tunaninta bazai iya yin abinda yafada ba bata san shi abinda yake nufi ba shine bazai sake barinta ta haihu a k'asar nan ba gara yafitar da ita k'asashen ketare koda kuwa tattalin arzikinsa zai kare. Haka dai akayi suna aka gama mai jego babu cikakkiyar lafiya,anty salaha da umma barira sune ke tare da ita suna kula da ita,bayan suna da kwana biyu taji kamar akwai matsala nan ta fadawa anty salaha babu shiri suka koma asibiti wani dinkin aka sake yimata domin wancan ya warware,da kuka suka dawo gida tana ta kuka ahaka Khalil yazo ya sameta. Zama yayi kusa da ita ya rungumota jikinsa yana rarrashinta,
"Uncle zafi mutum kamar zai suma ko zai mutu ni wallahi bazan kara haihuwa ba ma......"
"A'a sa'adah,wahala ai mai wucewa ce insha Allah bazaki sake shan wahala kamar wannan ba wurin haihuwa..... " Dakyar yasamu ya rarrasheta ta yi shiru ta daina kukan nan aka cigaba da lallaba ta su umma na kulawa da ita,shi kuwa jariri dayake yana samun abincinsa yana koshi nan da nan yasake zama kato dan ko Aryan baya iya daukarsa sai dai idan yana zaune abashi shi,itama mai jegon ba abarta abaya ba wurin murmurewa da sake kara samun kumari domin itama ta cika tayi kiba kamar ba itaba sai yanzu ta yarda da batun mutane da suke cewa kudi na gyara mutum haka duk muninka yana kara maka kyau,kafin arba'in tasamu ta warke tayi fess da ita amma duk da haka bata sakin jiki da khalil kuma shima baya takurawa saboda yana son ta huta sosai,kullum da daddare dai yana kasancewa dasu itada Aryan da Ayaan su raba dare a sashensa suna hira,anty salaha kuwa ganin Hanan ta warke yasata tattarawa ta tafi saboda tabar yara agida duk hankalinta yana garesu,
Tunda anty salaha ta tafi kuma Hanan ta koma sashen Khalil da kwana itada jararinsu can suke tafiya suyi baccinsu cikin nutsuwa da kulawa domin ko tashin dare Ayaan yayi zaiyi rigima khalil ke daukarsa ya rarrasheshi. Watan Ayaan biyu Hanan ta shirya ta tafi gida kuma itace har gombe domin ziyara tayi ba kadanba saida tayi sati biyu taje nan taje can duk wasu danginta da na Khalil lungu da sako babu inda bata je ba takai Ayaan anganshi wanda kamarsu daya da Aryan saboda duk Khalil suka debo,
Kafin ta baro gombe saida aka yimata kunshi da kitso sannan Zaid ya mayar da ita, lokacin da ta koma bata samu Khalil ba domin yatafi k'asar chairo wanda bata san dalili ba,gyara jikinta taci gaba dayi har izuwa ranar da zai dawo,bayan dawowarta da kwana biyu shima ya sauka amma office yawuce bai karaso gida ba sai dare,
Kwalliya taci sosai cikin doguwar riga ta material tasha turare mai sanyin kamshi,yana dauke da Ayaan a kafadarsa wanda ya karbeshi hannun umma Aryan na biye dashi,
A sashensa ya sameta tana shirya masa table ganin irin adon da ta caba yasashi yin murmushi ya nemi wuri ya zauna,
"Sannu da zuwa uncle...."
"Yawwa.... Irin wannan kwalliya haka? Ko anshirya karbata ne yau?"
Murmushi tayi ta karasa kusa dasu,
"Kai uncle....."
"Ai tambaya nayi,kuma shiyasa nayi miki da yaren da Aryan bazai ganeba, anshirya karbata yau?"
Kafada ta makale tace "A'a"
"Karya kike yau dai dole akarbeni tunda ai anhuta kuma zafin haihuwar yatafi...."
Dariya tayi ta mika hannu ta karbi Ayaan tana fadin,
"Zo nan mubar uncle yaje ya shirya yazo yaci abinci..."
Tare suka rankaya zuwa dakin nasa banda Aryan wanda yakoma wurin umma,ita ta taimaka masa yayi wanka sannan ya shirya cikin kayan shan iska saboda shi mutumne mai jin zafi gashi baida wata kiba ta azo agani amma sai jin zafi,falo suka koma ta bashi abinci yaci daga nan tatafi sashenta domin yin shirin bacci. Yau kam tayi shirin da Khalil bazai kirata da yar kauye ba itama yar birni ta zama domin rigar baccin da ta saka kadai ta isa tabbatar masa da haka kuma kalar da yafi murada ce wato fari,
Yana zaune rike da wani littafi a hannunsa kishingide saman sofa acikin bedroom dinsa ta shiga,bayan ta kwantar da Ayaan ta nufeshi,acikin jikinsa ta zauna tana cire hijabin dake jikinta,
"Wow....... Kinyi kyau" yafada yana shafa kitson kanta,tun anan labari yasoma canjawa har suka dangana ga gadon barcinshi amma kuma yau sam ta lura kamar baida kuzari kai kamar ma dan ita yake jagorantar tafiyar bawai dan kanshi ba,
"Uncle ko inkawo maka coffee din ne?"
"No"
Ita dai yau ganinsa take yi kamar wani marar lafiya kuma duk zumudinsa yau kam jikinsa asanyaye yake,
Bayan wani dogon lokaci tayi bacci ta farka ta ganshi zaune ya tallafe kumatunsa da hannunshi abin yayi mutukar bata mamaki, cike da bacci ta tashi zaune,
"Uncle wai lafiya kuwa? Meke damunka ne?"
Kamata yayi suka kwanta ya kwantar da kanshi a kirjinta bayan ya rungume ta,
"Babu abinda ke damuna,muyi bacci..."
"A'a uncle wallahi da akwai abinda ke damunka..."
"Babu"
Jin yaki fada mata yasata tureshi ta mike zata bar dakin tana masifa,
"Tunda baka daukeni abokiyar shawararka ba,kuma baka kallona a abokiyar tayaka farin ciki ko sabanin haka...."
Tashi yayi ya rikota dakyar ya kwantar da ita tana ta zizzillewa,binta yayi ya saka mata nauyinsa ta yadda bazata iya tashiba,
"Nifa bazan kwana adakin nanba...."
Dariya yayi sannan ya shafi kumatunta,
"Kwana kuma na nawa sa'adah? Jiya kam ai kin kwana saura yau kuma..."
"To ba ka ki ka fada min damuwarka ba"
"Sa'adah banda lafiya......... Insha Allah zan koma chairo next month zasuyi min surgery....."
Tashi zaune tayi yunkurin yi ya hanata babu bata lokaci tafara hawaye tana ta tambayar rashin lafiyar dake damunsa amma yaki fada kawai dai yace mata wai wani abune shima bai san menene ba zasu yimasa aiki,dakyar ya lallaba ta suka koma bacci,tun daga ranar hankalinta yaki kwanciya duk tabi ta damu dan gani takeyi kamar mutuwa zaiyi yabarta,shima kuma komai nashi cikin sanyin jiki yake gudanar dashi dan daga karshe ma cewa yayi zaiyi resigning yabar aiki hajiya ta hanashi,haka dai yaci gaba da fita aiki kusan kullum yana fama da zazzabi mai zafi,
Lokacin da zai koma chairo din tare da Hanan suka tafi kuma aranar da suka je aranar aka yimasa aikin,yasha wahala ba kadan ba amma kuma anyi cikin nasara nan tayita zaman jinyarsa har yafara samun lafiya,kullum cikin amsa wayar yan uwa daga gida Nigeria take,satinsu uku acan ya warke garau kuma yaji sauki sai lokacin yake sanar da ita wai cancer ce ta kamashi amma bata girmama ba ita aka cire masa,
Gida suka koma yaci gaba da al'amuransa gefe daya kuma yana kulawa da iyalinsa, itama dagewa tayi tana kulawa dashi domin bata son wata ta kwace mata shi bugu da kari kuma mijin matacciya take aure idan batayi da gaske ba zaiyita kewar matarsa da tunaninta, abinda bata saniba shi yanzu baida lokacin kara aure ko kula mace awaje saboda atsarinshi mace guda daya ta isheshi rayuwa.
Ganin wanda takeyi dominsa baya ta kowacce mace sai iya ita kadai yasata sakin jikinta nan tafara kasuwancinta tabude restaurant da boutique mai hadeda wurin saloon da gyaran jiki da kwalliya duk na manyan mata,idan Khalil ya tsareta da tambayar wai me zatayi da kudi sai tayi dariya tace abunda akeyi dasu nan kuwa iyayenta take taimakawa wanda bata da kamarsu kuma duk da Khalil na iya bakin kokarinsa amma itama gara tayi nata haka kuma sauran yan uwa da abokan arziki ai basai tazo tana cemasa bani bani ba lokuta da dama da nata take yin amfani.
Rana tsaka kuma Khalil ya daukesu ya mayar dasu k'asar Paris saboda karatun yaransa itama ba abarta abaya ba ta fada tata makarantar inda taci gaba da karatu kuma su basu cika zuwa bama sai shine ke zuwa,amma wannan karon saida yayi 3 months bai jeba,kuka Hanan tasaka masa awaya washe garin ranar sai gashi yazo lokacin dama har ta yaye Ayaan,
A bedroom dinta ya sauka tunda dama 2 bedrooms ne daya nata daya nasu Aryan,
"Wai sai yaushe za abawa su Aryan kani ne..."
"Hum um babu rana,garinsa da nisa...."
"Garinsa akusa yake ai kuwa saboda saida nataro gajiya ta gaba daya sannan nataho"
Turo baki tayi tana harararshi,
"Muda ka manta ma damu kaje kayi zamanka...."
"No,ni na isa mantawa da zuciyata......... Zo kiji wani abu"
Janyota yayi ya rungume ta yana fada mata irin girman matsayinta cikin zuciyarshi daga karshe kuma yashiga nuna mata a bayyane da bakinsa da hannayensa da dukkan gangar jikinsa gaba daya yana kara jaddada mata shi nata ne ita daya haka kuma ta daina kiransa da mijin matacciya shi mijin rayayyiya ne domin tuni ya maye gurbin Ramlat da Hanan tsakaninsa da Ramlat addu'a ce amma Hanan itace abokiyar rayuwarsa har gaban abada zai cigaba da kulawa da ita da nuna mata kauna da soyayya har tsufansu, wannan karon akasar Paris tasamu ciki kuma acan ta haihu cikin kulawar doctors da Khalil wanda ya tayata nakuda ta haifo yaronta santalele wanda gaba daya su Aryan suka tare masa kyau domin tamkar balarabe haka yake nan Khalil yayi masa huduba da Abubakar saddiq yana tsokanar Hanan wai wannan karon babu kukan dinki to sai muce Allah yaraya yakaro kazantar daki.
ALHAMDULILLAH
Godiya ta tabbata ga ubangiji Allah madaukakin sarki wanda yabani ikon kammala wannan littafi mai suna mijin matacciya, Allah ya yafe mana kuskuren dake ciki ya hadamu acikin ladan gaba daya tare daku masu karatu,kamar yadda nafada book dina na kudine duk wadda ta karanta batare da ta biya ba to yar uwa kisani Allah yana kallonki,bawai book dina kadai ba duk book din da akace na kudine yakamata mu kiyaye daukar hakkin wani domin Allah yana gafarta abinda ke tsakaninka dakai bawa amma baya yafe hakkin wani murinka tunawa da wannan,ina mutukar godiya ga masoyana wadanda ke nuna min kauna kuma suke tare dani koda yaushe Allah yabarmu tare,sai mun hadu acikin labari nagaba,taku ahar kullum kuma akoda yaushe Ummi A'isha nagode.
_*Ummi Shatu*_馃憣馃徎