Tana fita napep ta tare ya kaita gidan su. Tana shiga ta fashe da kuka tare da fad'awa kan kujerar d'aya daga cikin falon.
"Ke lafiya kuwa kamar wadda aka yiwa mutuwa?"
Cewar yayan ta Shamsu yana kallonta, Fateema bata yi shiru ba tana ta kuka Shamsu ya tashi ya dinga mata fad'a yace idan baza tayi magana ba ta tashi ta koma inda ta fito. Mama ma kallonta take yi tana jiran jin abinda zata fad'a ranta cike da addu'ar Allah yasa ba tsakaninta bane da mijin.
"Ke wallahi karki bari na tashi tsaye dan sai na fasa miki baki, aikin banza kawai kiyi magana shine zaki tsaya yiwa mutane kuka."
"Mama Sadeeq ya munafurce ni, Mama be ta6a gaya min matarsa Aisha nada ciki ba sai yau da muka gani gashi har ya fito. Wallahi bazan koma gidan saba yaje can su k'arata munafiki kawai, dama ance duk wacce ta d'auki namiji uba toh lallai zata mutu ma..."
Mtwww "Shut-up Fateema, bakida hankali ne? Toh sakinki kike so yayi?!"
"Nidai kam bazan koma ba yaje can su k'arata."
"Toh idan ya sakeki sai kizo na aureki nine kawai idan na aureki za'a haramta min k'ara aure bare har matar ta rigaki haihuwa."
"Yaya Shamsu ka aureni kuma?!"
"Eh toh kince maza ba 'yan goyo bane, kinga ni uwa d'aya uba d'aya muke ki goyani na goyaki babu mejin haushin wani, amma ko barin Sadeeq kikayi toh wani mijin zaki aura kuma shima wata ran zai miki wani abun sannan ba lallai ki kuma samun saurayi ba sai da kema ki shiga gidan wata."
"Umma...."
"Karki min magana Fateema, dai-dai gwargwado kina da ilimin addini shin na zamani ne ya rinjayi da addininki ko kuwa wani saban iskancinne haka? Karki manta wannan auran nasu had'in Allah ne duk wanda yace zai ja da ikonsa akan lamarin toh bazai kwana cikin jin dad'i ba. Fateema karki manta nima da yanzu bani bace mahaifiyarku, amma kinga da yake Allah yayi ta hanyata zai samu haihuwa sai ya d'auke matarsa ta farko da kyar mahaifinku ya yadda ya aureni da yace ya gama aure amma a satin da na tare a satin na samu cikin yayan ku ki gaya min da mahaifinku yayi butulci ya kafe akan bazai sake aure ba ta wace hanya zai sameku tunda Allah yayi yana da rabonku a duniya?!"
Fateema ta kuma fashewa da kuka tare da mik'ewa zaune tace.
"Toh Umma kiyi hakuri wallahi sharrin shaid'anne, amma kuma me yasa koda wasa be gaya min ba ya yi min shiru sai yau naji na kuma gani?!"
"Hmm Fateema kenan, toh ko tunda kuka yi auran Sadeeq be ta6a kusantarki bane har sai da aka yi musu aure da ita Aishan?!"
"Kai Umma.."
Fateema ta fad'a da alama nauyi tambayar tayi mata, kallon Yaya Shamsu tayi k'asa-k'asa kawai suka had'a idanuwa ya zabga mata harara tare da cewa.
"Ke..! Kallon me kike yi min haka? Ko kin d'auka bansan meye auran ba sai ke kika sani.??"
Da sauri ta zaro udanuwa hannunta a baki tana girgizawa tare da kallon Umma Fateema taga Umman ma ita take kallo, lallai Yaya bashi da kunya ma wallahi a gaban Ummansu. Koda yake itace ta kallesa dole yayi mata bayani.
"Fateema karki yadda ki nunawa mijinki bak'in cikinki akan cikin matarsa, ina son ki nuna masa kinfishi son cikin ma. Sannan karki bari abban ku ya dawo ya ganki a cikin gidan nan wallahi kinsan ranki ne zai 6aci abanza, gara kije kiyi zaman aurenki har Allah ya baki kema wata rana idan kina da rabo."
"Toh Umma, amma dan Allah ki tayani da addu'a dan wallahi ina jin zuciyata nayin zafi da nauyi."
"Kidena sawa a ranki insha Allahu zaki ji bakya ji shaid'an ne kawai yake son shiga cikin lamarinki, ki yawaita azkar zakiji dad'in ranki."
Wayarta ce dake cikin jaka taji tana ta ringing amma tak'i d'agawa dan tasan baxai wuce Sadeeq ba ita kuma bata shirya abinda zata ce masa ba. Tashi tayi suka yi sallama Yaya Shamsu yace bari ya kaita gidan da kansa, suna tafiya yana k'ara bata shawarwari wani maganar ma har mamakinsa takeyi lallai yayan nata aure kawai yake jira amma babu abinda be sani ba.
***
Shi kuwa Sadeeq k'arfe tara yaje d'aukar su amma aka ce Fateema bata nan, duk an duba bata gidan ya kira ta yafi sau goma amma ba'a d'agawa hakan yasa yace INdo ta fito su tafi. Gidan Fateeman suka fara biyawa amma akulle hakan yasa Sadeeq tafiya yakai INdo gida tunda ranar a gidan Fateema yake.
"Malam Sadeeq d'an tsaya a can gurin me balangun can na kan kwana ka siya min."
Kallonta yayi sai yaga ita kalle-kalle takeyi abinta cikin mamakin daya mak'ale mai a wuya yace.
"Cutie ballangu kuma."
"Eh dan Allah kace su sa yaji daban."
"Ikon Allah shi kike son ci kenan."
"Eh, akwai fura da nono da ake damawa a gurin, ana sa kwakwa da ayaba da madara please dan Allah itama ka siyo min."
Dai-dai lokacin suka tsaya a gurin ya kalleta tare da cewa.
"Toh ke ya akayi kika son nan gurin harda abubuwan da ake siyarwa.?!"
Juyawa tayi ta kallesa suka kalli junansu tayi murmushi tare da cewa.
"Bafa zuwa nake yi ba da kai na, a'a ina dai bawa khaleefa yana siyo min nima rannan ne Abba ya aiko min dashi. Naci naji dad'i shine nake bayarwa yana siyo min."
"Okey yanzu naji batu na d'auka kinyi tunanin nan ma kauyan Sani ne, kowa zai iya fita san ransa."
Baki ta turo tana yatsina fuska ya fita, leda biyu yayo musu sannan ya dawo motar yana kallonta yaga still a shagwa6e fuskarta take ya shareta domin so yake su k'arasa gida zaifi jin dad'in lalla6a ta.
A bakin gate ya tsaya ta fito suka shiga gidan, tun a parking space ya rik'ota tana turesa yayi niyar d'aukarta sai dai yana ganin bazai iya ba sabida cikinta gashi ba laifi INdo kamar (Ummi Aisha take ba ruwa na lol).
"Goya ni toh."
Sadeeq ya zaro idanuwa jin abinda ta fad'a, yana kamo hannunta suna tafiya yace.
"Ina tunanin yadda zan iya d'aukarki ke kina cewa na goyaki kin manta abinda yake cikin ki ko."
"Toh gaskiya tunda kayi niyya malam Sadeeq to ka goya ni."
"A'ah cutie ni ba niyya nayi ba, cewa nayi Ina tunanin yadda zan d'aukeki kekuma ma goyo zaki ce."
A bakin k'ofar d'akin ta tsaya ya ajiye leda d'aya kusa da k'ofar yaje ya tayar da gen ya d'auka ta shiga ciki amma sai ya ganta tayi kalar tausayi ta kuma turo baki yayi dariya.
"Mata problem. Nan kiyi can tayi Allah ya sa in iya muku."
'Daukarta yayi suka shiga ya dinga k'ak'aro nishi tana dariya, yana ajiyeta ya zauna ya d'aura kansa akan cinyarta.
"Masha Allah sati d'ayan da nayi a garin nan yasa kin kuma yin k'iba, nan gaba sai kin kasa tashi cutie Aisha."
"Ni kadena cemin nayi k'iba."
"Na dena ina balagun naki?ko bazan ci ba?!"
INdo tace. "Kaje kuci kaida Fateema nima kaga mu biyu zamu ci wannan."
"Nak'i wayon wannan zanci."
Tashi yayi yaje ya shigo da ledar ya kuma zuwa ya d'akko plate da zo6o tare da kofina ya ajiye, anan falon ya rage kayan jikinta ta zauna daga under wear sai have vest kasan cewar yanzu bata sanya bra tana d'an takura mata ciwon k'irji.
Kallonta yake tamkar zai shige cikin jikinta farat d'aya, remote ta d'auka tare da kunna TV ta juyo zata ci naman taga sai kallonta yake cikin mamaki tace.
"Wai ya haka ne?!"
Sadeeq ya shafa k'eya tare da komawa kusa da ita ya zauna ya sanya hannu ya rik'ota tare da kwanciya a bayanta murya sassanya yace.
"Aisha banyi tunanin zaki dawo haka ba, lokacin da kuna j.s one ko k'irg..."
Bata bari ya k'arasa ba tayi saurin rufe mai baki da hannunta. Dariya ya dinga yi ta d'auki naman tafara ci sannan ta sakar mai baki yace.
"Zanci."
'Daukowa tayi ya rik'e mata hannu, fuskarta ya kama sannan ya sanya bakinsa a hankali cikin nata sai faman zaro ido takeyi. Gani tayi ya ciro na cikin bakin nata yana k'arasa taunawa ta bishi da kallon mamaki, yanzu kam ta tabbatar da cewa Sadeeq yana sonta, a shirye yake tsab da ya shiga cikin rayuwarta yayi mata duk abinda take so. Jiyayi kawai ta rungumesa tsam a jikinta a hankali kuma yaji tana zubar da hawaye ya d'agota yace.
"Sorry na 6ata miki rai ko? Bazan sake ba, bana son ganin hawayenki musamman ace nine silar zubar su."
Sabo ta d'akko tasa mai a bakin yayi murmushi ya fara taunawa idanunsa akanta, tana ganin ya fara taunawa itama ta rintsa ido tare da kai nata bakin cikin nasa kamar yadda taga yayi mata ya tura mata shi a bakinta da kanshi sa6anin shi da ya ciro nata da harshensa.
"Ashe ba haushi kikaji ba d'azu?!"
Ya fad'a yana lasar lips d'inshi. Juyawa tayi tana murmushi ta fara dangwala yaji tana sawa a baki. Mik'ewa yayi yana gyaran rigarsa yace.
"Na tafi na tabbata duk inda taje yanzu ta dawo, idan na isa zan kiraki."
"Toh a gaida ita."
"Ba rakiya?"
Dariya tayi ta mik'e suka fita tare, kamar karsu rabu haka sukeji amma babu yadda zasu yi dole ya fita ita kuma ta rufe gidan ta koma ciki zuciyarta fal Sadeeq domin ya tafine ya barta da abinda bazata ta6a manta shi bakoda da second d'aya ne.
****
A falo ya zauna tare da d'aukar laptop d'insa daya bari jikin charge. Fateema na jinsa ta d'an Lek'o har lokacin tunanin abinda zata cemai takeyi, ganin tana k'arasa 6ata lokaci yasa tayi shahada kawai ta shiga falon tana sanye cikin kayan bacci me wando k'arami wanda ko cinyarta be gama rufewa ba.
Kusa da k'afarsa taje ta zauna, shafar k'afar ta farayi wanda take cike da kwantaccen bak'in gashi. Sak'e mak'alo k'afar tayi sannan ya saki mai kuka a hankali hawayen na sauka a k'afarsa, har cikin zuciyarsa yake jin kukan amma ya shareta yana aikinsa, ganin haka yasa ta fara magana.
"Baby kayi hakuri dan Allah, wallahi raina ne ya 6aci akan abinda ka 6oye min kaida Aisha."
Jin abinda ta fad'a ne yasa shi cewa,
"Me kuma muka yi? Duk abinda muka yi Fateema ya dace idan har na kiraki ki amsa min amma kikak'i toh ina kikaje ma tukunna..?"
"Kayi hakuri baby, yanzu duk matsayin da nake a gurinka na matarka ace ka kasa gaya min cewar Aisha ciki gareta? Ko kana ganin kamar zan cutar da itane? Wallahi kaji dalilin da yasa kawai da na gani yau kawai sai na tafi gida, can kuma ina zuwa Yaya Shamsu ya dinga min fad'a, baby kayi hakuri da 6ata maka rai danayi dan Allah."
Zuciyarsa ce tayi sanyi jin itace ma take basa hakuri, ture laptop d'in yayi tare da janyo ta jikin sa. Gashin kanta da bata mai kitso ya dinga shafawa sannan ya numfasa yace.
"Kamata yayi tunda nine na kaiku duk abinda zai faru ki tsaya naxo na d'auke ku, amma ba komai nasan sharrin iblis ne. Sannan kuma ke ya kamata nayiwa wannan k'orafin cewar baki sanar min da cewar Aisha nada ciki ba sabida ku na bari tare har tsawon 3months amma baki gayan ba sai da na dawo na gani why baby?!"
Fateema ta d'ago tare da kwantar da kai cikin maganar tace.
"Wallahi ban ta6a lura ba kuma dai gaskiya bana wannan tunanin ganin nima har yanzu babu. Sai d'azu da na ji Hawwa na fad'a kuma na gani a zahiri."
Sadeeq ya sake kamota tare da cewa.
"Kinga kenan duk babu me laifi, Fateema bana son ki tashi hankalinki domin ina sonki a duk yadda kike. Kema Allah ba mantawa yayi dake ba domin da yawan aikin ne toh da yaci ace kema yanzu kin kusa ma saukewa amma fa Allah me meyi, yanzu three months da tafiya ta ita kuma cikinta wata hudu kinga kenan bayin kaina bane. Ina son dan Allah karki tayar da hankalinki rashin haihuwarki bazai rage soyayyarki ba a cikin Zuciya taba *I love you* Fateema Allah shine shedata."
" *I love you too* baby nima ka taya ni da addu'a na samu kafin na mutu."
Shhhiiii yayi mata bayan ya d'ora yatsansa akan lips d'inta. Shiru tayi sannan ya janyo ledar da ya shigo da ita taje ta d'akko cup's ta zuba musu furar suna manne da juna suna cin abin su idansa akan agoga yana son ya kira INdo kamar yadda yayi mata alk'awari.
Daya rasa yadda zai yi kawai sai ya tura mata text message.
"Affuwan cutie na ba credit da yawa a ciki gashi masu shops sun rufe, zamu had'u gobe I love nd miss you (#DeepKiss)."
Yana ganin sak'on ya tafi ya gogesa tas daga cikin wayar (tamkar miss Xoxo da take da cutar clearing masseges).
INdo na kwance ta gama duba littafin ta taji shigowar sako, a hankali d'aya bayan d'aya (word by word) ta karance sakon kafin ta tattarashi ciki kwakwalwarta ta sake nanata sakon gaba d'ayan sa sannan tayi murmushi ta kashe wayar ta kwanta, wani sabon yanayi na soyayyarsa yana shigarta haka ta dinga murmushi ita kad'ai a kan gado har bacci ya d'auketa.
Yayin da shi kuma yake can suna soyewa da Fateema wadda itama fatan ta da burinta da addu'arta a daren be wuce itama Allah ya azurtata da ganin gudan jininta ba.
*HAJJA CE*👈
[7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*
♥♥
♥
A true life story
Na
*K.A.S Precious Hajja ce*👈
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)
*DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu.
*VOTE me on wattpad @Hajjac*
Page *36*
Gurin d'ayar nurse d'in ta k'arasa ta bawa baby boy d'in kafin ta dawo gurin ta kalli Sadeeq dake shafar kan INdo yana hura mata iskar bakinsa ganin bata bud'e ido ba.
"Angon k'arni leave us please kafin a gama shirya ta."
Da kyar Sadeeq ya iya yin magana ba tare da ya kalli nurse d'in ba yace.
"Ki fara duba ta tukunna naga tayi haka bata k'ifta idanuwa sosai."
"Ah karka damu wannan ba wani abu bane ba, kawai wahalar haihuwa ce kad'an bamu guri tunda kaima ka bamu gudun mawa."
Tashi Sadeeq yayi yana kallon INdo wadda idanunta ke a rufe sannan ya fita. Maman Sayyid mak'ociyar su da suka zo tare ta kallesa tana zaune ta mik'e duk da cewar tajiyo kukan jariri tace.
"Malam Sadeeq yayi ita d'in?!"
"Sun ce zasu gyara sune but ni banga ita Aishan tana wani abu ba da zai nuna min cewar komai normal ba."
"Insha Allah komai lafiya lau karka damu shi yasa banso ka shiga cikin ba naso ace kawai sai dai a kiraka ace kazo ka gansu."
Numfashi yaja tare da yi mata godiya sannan ya wuce masallacin dake cikin asibitin kasan cewar anata kiran sallan asuba. Kafin ya dawo daga massalacin an gama kintsa su duk da basu zo da kayan haihuwa ba, nurse d'in da ta k'arbi haihuwar tana siyar da kayan babies ta sanyawa yaron ita kuma INdo ta bata sabon zani wanda shima itake siyarwa ta d'aura tare da bata maternity pad da pant.
Resting room aka maida su Maman Sayyid na zaune kusa da ita tana mata barka INdo kuwa ji take wani girim-girim ganin cewar wai yau itace ta haihu ga d'ama har tana bashi yana shi.
Sadeeq kuwa sai da ya gama sharara addu'a sannan ya fito daga massallacin har gari ya d'an fara yin haske. Yana shiga reception yaga Fateema tana kalle-kalle tana juyowa kuwa ta ganshi dai-dai lokacin nurse ta fito ta nuna mai d'akin da aka kaisu.
"Baby ina kwana? Ya su Aishan?!"
Ta fad'a tana kallonsa kai da ka ganta kasan itama tunda ya sanar mata suna asibiti bata samu wani ishasshen bacci ba. Hannunta ya kama ganin babu mutane suka shiga cikin d'akin da su INdo ke kwance Maman sayyid na ganin su ta mik'e daga bakin gadon tana musu murna.
Rufe idanuwa INdo tayi dan wata irin kunya takeji azo aga ta haihu. Yaron Fateema ta k'ar6a tana kallonsa yana ta bacci yasa yatsansa babba a cikin bakinsa, ta k'arasa wajan Sadeeq dake zaune a wajan INdo ya rik'o hannunta yana murmushi ganin yadda tak'i bud'e ido.
Jaririn ya kar6a yayi mai hud'u ba sannan ya ciro wayarsa, su Mama ya kira ya sanar dasu yayin da Fateema ta kuma kar6an yaron ta zauna kusa da Maman sayyid. Yaron jawur dashi me kyau k'irjinta ya dinga bugawa tana dannewa sabida jinsa take inama daga nata cikin ya fito sai dai baza ka gane hakan ba sabida tayi nasarar fin k'arfin zuciyarta.
"Wai cutie wa kikejin kunya a gurin nan da kika k'i bud'e idanuwanki.?!"
Kad'a kai tayi still idanta a kulle yayi murmushi tare da mik'ewa ya fita. Gurin doctor yaje dan yana son a basu sallama su tafi gida dan kar a cika asibitin.
"Mu wuce gidan Mama Fateema."
Ya fad'a bayan ya dawo d'akin. Da sauri INdo ta juyo tana yin kamar zata yi kuka tace.
"Gidan Mama kuma? Ni dai wannan karan baza ni gidan Mama ba can gida za'a maida ni."
"Aisha wane gidan za'a maidake bayan haihuwar fari ce.?!"
Sadeeq ya tambayeta bayan ya mik'ar da ita zaune.
"Sani, ni dai can zan tafi gaskiya."
"Au lallai gidan namu ne bazaki zauna ba?!"
Shiru tayi tana tutturo baki su Fateema suka yi dariya kafin tace.
"Gaskiya ranka ya dad'e a al'adance haka ake yi, a kaita gida har tayi arba'in ko sittin sannan sunyi kwari ita da baby sai a dawo dasu."
"Haka ne kam."
Maman sayyid ta sake gasgata zancen, Sadeeq ya shafa kai lallai akwai kwarbai kenan duk da ba zama yake yi ba ai zai so ya zauna dasu ko na d'an wani lokaci ne tayaya zai bari su wani tafi kauyan Sani.
Account number d'in nurse d'in ya k'ar6a dan zai tura mata kud'in kayanta sannan ya siya magungunan me jego suka wuce can gidan INdon kasan cewar tak'i yadda ya kaita gidan Mama wannan karan da hankalinta dan haka bazata yadda taje gidan sirikai wankan jego ba.
Suna komawa kuwa 'yan uwa suka fara zuwa dole tasa Sadeeq kwasar yanashi-yanashi na gidan ya tafi dasu gidan Fateema.
"Allah sarki, dama rabon wannan yaron ne Allah ya d'auke Habu. Gashi daga tafiyarsa har Allah ya bada arzik'in yaro zuk'e-k'e tubarkallah."
Cewar k'anwar abban su Sadeeq da tazo ganin d'ah. Hakama duk mutane suka fad'a duk wanda yaji labarin haihuwar wanda hakan sai da yasa INdo yin kuka sabida surutun mutane da tada mata da baya.
Haka aka dinga zarya zuwa gidan INdo da nufin idan anyi suna za'a maida ita sani bayan Mama ta nunawa Sadeeq amfanin komawar tata tunda tafi son can. Ba k'aramin k'ok'ari Sadeeq yayi ba wajan ganin ya fita kunyar mejego da baby harma da mutane, Fateema ma be barta haka ba sai da yayi mata na fitar suna sannan itama da su Ummanta sunyi rawar gani sunyi musu kayan barka tamkar ba kishiya ce ta haihu ba.
"Cutie me jego, naga alamar haihuwar nan wata wawuyar kunya ta sanya miki why?"
INdo ta tura mai baki ya sanya hannunsa yajasa tayi 'yar k'ara tare da d'an dukan hannunsa. Rungumeta yayi kafin yace.
"Toh me ake buk'ata na gobe wanda ba'ayi ba.?!"
"Ba komai hakan ma mun gode."
"Toh gobe dai nasan ganinki zai min wahala sabida mata dan ba shigowa zanyi ba, idan ma kuna son wani abun ki kira Mubasheer ko khaleefa sai ki sanar musu."
INdo ta kallesa, wani irin tausayinsa takeji sabida ganin hidimar da yayi tundaga kan abincin sunan da za'aci zuwa kayan rabo na sunan da ragunan da za'a yanka ga kayan barka dayayi musu yace.
"Allah yasa ayi taro lafiya cutie, please karki fushi da kowa kinga duk wanda kika gani zuwa yayi dominki domina domin marigayi infact dai kowa yazo ne dan tayamu farin cikin samun k'aruwa. Na tafi sai gobe zuwa dare zan samu mu had'u."
Kai ta d'aga sannan ya juya zai tafi, da sauri tasa hannu ta rik'osa sabida wani sassanyan sonsa daya kuma shigarta a d'an tsayuwar da suka yi. Rungumesa tayi shima yasa hannu ya rik'ota yana shafar bayanta murya na rawa yaji tace.
" *I love you* Sadeeq forever, I'm also wishing you all the best in your life. You are always by me, to share simple joys and each Nd every need and now with out your loving presence I'm very lonely indeed I love with all my life my husband..."
A yadda yaji tana fitar da words d'in ba k'aramin tsumashi suka yi ba, a hankali ta dinga jerosu dan ba k'aramin k'ok'ari tayi ba. K'ok'arinta da kuma son ganin tayi abu yake k'ara sonya shi cikin k'aunarta, ya d'ago da fuskarta cikin lumshe ido ya zura bakinsa cikin nata. Kissing juna sukeyi cikin wani irin shauk'i har Sadeeq yaji yana neman fita a hayyacinsa sannan ya kyaleta da kyar ya shafi fuskarta sannan ya bar d'akin da sauri sabida yasan mutane na nan sun sawa d'akin ido suga mintuna nawa zaiyi a ciki.
'Yan saye duk sunje da 'yan uwan Inna daga dawakin tofa su Uwani, Sahura, Rukayya, su Maryam haka 'yan kauyan sanin nan suka yo mota guda suka zo duk da ance su bari zata dawo amma wasu suka ce ai daman basu san gidanta taba dan haka sai sunje.
Washe gari suna yaro yaci sunan Abubakar dan haka ko ajikin kalandu da key holders da sauran abubuwan da akayi aka sanya mai Abubakar A (Ayman) wanda Fateema ce ta za6i lak'anin yace wa INdo yana son ta bari a sanya mai tunda dama shima uban sunansa ne dan ayi mata kara.
'Yan kauyan nan an samu shinkafa dasu zo6o lemukan jarka da sauransu suka dinga lodawa cikin jakunkunan su, gidan ya cika mak'il da al'umma su Xoxo sai nan-nan ake da little Sadeeq (ayman) duk nacin yayya Nabee ta hanata d'aukarsa sai dai ta kallesa a hannunta. 'Yan grps da fad'ar yawansu bazai musaltuba suma sai salfie suke da mejego dan a samu na sawa a status da dp, su Sis Mom s/fulani, princess meenat, Olo, aunty jidda musa, mmn ansar, ummi k.d, mmn sadeeq³ aunty baraka, yayya Ummi s/fulani aunty Fatee, sis Ummi A shitu, Heedah, Muhmeelat, redbutterfly, B s fari, meela adeel, ummul m, mrs splined (ko? Sunan ne na 'yan gayu Allah yasa na iya rubutawa dai-dai lol) su Sum-Q, Kaumi shaddad, matar shehi, my Halymah, (yasin da yawa kuyi hakuri dan idan nace zan jeroku ta6...) Duka masoyan INdo da Fateema duk sunje kuma sunci sunsha alhamdulillahi taro yayi sweet mejego an yi fitar suna ta kece raini.
Yamma nayi 'yan sumaila suka kama hanyar komawa bayan sun jajjada ma INdo cewar ta taho musu da naman sunan su.
K'arfe tara na dare Sadeeq yazo k'ofar gidan yana fitowa daga mota mutane dake wajan suka dinga mai barka fuskarsa cike da farin ciki.
"Yaya Sadeeq kenan kwana biyu."
Yaji an fad'a cikin nok'e murya, kallonta yayi bayan ya zare glass d'in idansa. Sanye take cikin wani fitinannan material anyi mata d'inkin riga da skirt sun d'ameta sosai, gashi kwan lantarkin k'ofar gidan ya haske su ya zabga mata harara cikin tsuke fuska yace.
"Chuchu wai banace ki dena yin irin wad'annan banzayen d'in kunan ba? Wallahi Zan je na samu uncle Ahmad d'in wata k'ila baya lura da yadda kuke rayuwarku."
"Kai Yaya Sadeeq yanzu nan meye na rashin dai-dai a cikin rayuwata..?!"
Tayi maganar tana d'aga mayafin jikinta, tsaki yaja tare da kara wayarsa a kunne taji yana cewa.
"Cutie lalla6o kizo waje ina mota."
Mayar da wayar yayi cikin aljihu tare da komawa cikin mota chuchu ta matsa jikin murfin ya kalleta tare da cewa.
"Matsa ki bani guri."
"Kai Yaya Sadeeq dan Allah, wai kana nufin kace har yau baka gane inda Zuciya ta take ba akan ka? Please Yaya Sadeeq tun kafin na mallaki hankalin kaina nake sonka amma sai wani shareni kake yi ko banyi maka ba Yaya Sadeeq?!"
"Ke! Zaki matsa ki bani guri anan ko sai nayi ball dake."
Turo baki tayi tana sake matsawa kusa dashi, cikin nuna izgilanci tace.
"Hmmm Yaya Sadeeq duk matanka nasan tarihinsu kuma duk cikinsu babu wacce takaini komai ba kamar wannan aunty Aishan me jego, ita da ko wayewar ma anan gurinka tayi 'yar kauye da..."
Kwaf... Taji ya kwad'e mata baki da phone d'in daya d'akko, dai-dai kuma lokacin INdo ta fito tayo gurin motar Sadeeq yace.
"Chuchu bar gurin nan kafin raina ya kuma 6aci, k'atuwar banza sakarya kawai."
Kuka tasa ganin harda jini ya fito INdo taga ta tafi tana kuka ta shiga motar shima ya kulle suka kalli juna tace.
"Me kuma ya sanya chuchu kuka my super glue? Allah yasa dai ba wani abun kayi mata ba tana da kirki."
"Cutie rabu da ita rashin kunya takemin. Kinga bama wannan ba ya taro hope kunyi komai cikin jin dad'i da wal-wala..?!"
Hancinsa INdo taja tana murmushi jin dad'i sannan tace.
"Kana sona mijina Allah ya shi albarka ya k'ara bud'a maka hanyoyin samu, mu kuma Allah ya bamu ikon yi maka biyayya kamar yadda kake iya k'ok'arin ka wajan ganin ka faranta mana."
"Amin Ummi ayman ina jin dad'in yabon nan da yake fitowa daga bakinki. Ina d'ana baki taho min dashi ba, kinsan yaufa tun asuba rabona dashi."
Dariya tayi sannan ta zuge jakar hannunta ta fito da kud'ad'an ciki wanda duk na barka ne. Mik'a mai tayi be kar6a ba ya kallesu tare da cewa.
"Uhmm k'arin bayani tukunna cutie ai bakya mik'on Kud'i haka ba bayani ba."
"Toh ka kar6a mana ai zan maka bayani, kud'in da mutane suka bani ne na barka. Ka kar6a kayi amfani dasu kaga akwai k'ananu nima sai nayi wani abun ko idan za'a nema."
Dariyar shima yayi zuciyarsa fara kal, chuchu na can gefe a tsaye tana gunguni sauran 'yan uwa na mata sannu amma idanunta suna kan motar Sadeeq haushi kamar zata had'iye motar.
"Cutie wannan ai naki ne, ni babu abinda zan kar6a Allah yayi miki albarka ya albarkaci yaron da kika Haifa min Ina alfahari dake Ina sonki har cikin k'ahon Zuciya ta."
Kowa dad'i yake ji sun dad'e a cikin motar kafin ya duba agogo ya kalleta cikin yanayi nasan nuna rashin son abinda zai fad'a yace.
"Zan tafi, gobe insha Allah ance za'ayi suyar nama acan gida kinga kar a 6atawa masu gidan idan an kammala za'a kawo jibi idan Allah ya kaimu za'a kaiku sumaila sai kuma kinyi arba'in."
"Ko baka son na tafi ne..?!"
Yayi murmushin yake domin harga Allah baya son suna rabuwa amma ya zai yi ko ta zauna fitina zai dinga jawa kansa gashi kuma zai koma kwara Fateema baza ta bishi ba wannan karan sabida zasuyi wani taro a makarantar da take aiki dole ya barta taje. Hannunta ya kamo tare da cewa.
"Cutie karki damu kije ki dawo hmmmm zaki shaaaa."
Da sauri ta bud'e motar suna dariya bata bari ya k'arasa, lek'ansa tayi sunata dariya yace.
"Idan kin shiga kicewa Fateema ta fito mu tafi."
Baki ta turo ya shafa kansa ganin harta mai fassara ya kashe mata ido d'aya sannan ta tafi, tasan komai shi kenan yanzu shida Fateema zasu cigaba da zama sai taji wani iri a cikin zuciyarta da kyar ta iya fad'an sakon sannan Fateema ta fita, chuchu na ganin haka ta kalli su Haleema tace.
"Kuzo muje wajan Yaya Sadeeq ya rage mana hanya duk da munyi fad'a."
Tashi suka yi da sauri suka k'arasa wajan motar yana kokarin tadawa suka rok'esa, sai da ya fara dank'arawa Chuchun harara kafin yace.
"Ku shiga amma wallahi badan halinku ba ku dukan sakarkaru kawai."
Shiga suka yi ya ya dinga jan Fateema da hira dan ya denajin muryoyinsu musamman ta Chuchun da take kamar ta gyare kyar-kyar-kyar. Yana zuwa suka fita chuchu ta kallesa shi kuma yak'i bari su had'a idanuwa sabida mugun haushinta yake ji sabida yadda yaji zata ta6a mai mutuncin matarsa uwar d'ansa.
****
Washe gari bayan anyi suyar nama an kasa kowa an bashi. INdo ta kimtsa musu kaya itada ayman da Nafeesah da daddare Sadeeq yazo gidan ya kuma siyo mata wasu abubuwan da zata buk'ata na ayman sannan ya tafi.
Washe gari da kanshi ya shirya zuwa kaisu sumaila tun a hanya suka fara jin kewar junan su sai dai yayi mata alk'awarin zuwa duk sanda ya dawo kano.
Yana kaisu ya juyo dan INdo har kuka tamai wanda da kyar ya lalla6a ta sannan ya tafi bayan ya bata kud'i tak'i kar6a sabida akwai na barkar data samu a hannunta...
*HAJJA CE*👈
[7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*
♥♥
♥
A true life story
Na
*K.A.S Precious Hajja ce*👈
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)
*DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu.
*VOTE me on wattpad @Hajjac*
*Shafin yau naki ne m sweet heart SOFIYYA GALADANCI, I love you Allah ya nuna mana ranar Auranki da rai da lafiya nasan ke ko...?🤨kawai dai Allah ya k'ara miki baseera dear Bari nayi tsit*❤💘
Page *38*
Alama yayi mata da hannu ta saki labulen da aka nannad'e aka d'ora akan k'ofar d'akin. Murmushi tayi tare da zaro idanuwa tana girgiza kai alamar a'a, ganin haka yasa shi matsawa yana kallon k'ofar ganin babu me kallonsa yayi saurin sauke labulen INdo tace.
"Kai.. Kai... Kai! ba ruwa na nidai Inna ce fa ta d'aga shi wai sabida akwai zafi."
Hannu yasa ya janyo ta kusa dashi yana kallon fuskarta, ya kaleta ya kalli Ayman a hankali ya kai bakinsa saman goshinta ya sumbace ta INdo tasa hannu ta bayansa ta rungume shi itama sannan ta kallesa tace.
"Ka zauna ka tsaya."
Hannunsa cikin nata suka zauna yana kuma rik'e da Ayman.
Kwantar da Ayman yayi a gefe kasan cewar yana cikin towel sannan ya juya yana kallon INdo wanda ke kallon k'irjinsa dan wani iri taji da yadda yake mata wani irin kallo.
"Sannu da zuwa, ya gurin su Mama?"
"Kin yi kyau cutie na, kinyi kamar ba me jego ba dan babu wani alamun da zai nuna hakan meye sirrin?"
"Inna ce."
Ta bashi amsa tana wasa da yatsun hannunsa yayi murmushi tare da matso da ita kusa dashi yana mak'alota jikinsa.
"Ko kawai ma idan zan wuce mu tafi tare tunda kun gama wanka ai kin fara sallah ma ko cutie?"
INdo ta zaro idanuwa tana kallansa yayi murmushi yana d'aga mata girarsa kafin yaji tace.
"Ta6... In bikafa kace? So kakeyi insha zagi kenan a cikin garin nan, kasan mu bazan koma gidan ka ba dole sai an yi garar barka sannan za'a maida ni."
Kallonta yayi cikin rashin fahimtar maganarta ta sannan ta d'an zame ta janyo kayan abincin ta tsiyaya mai lemo ya kar6a har yana cewa.
"Cutie ban gane abinda kike nufi bane wace irin garar suna? Kuma wazai kai? Wa za'a bawa.?!"
"Kayan abinci ne ake kawowa gidan su me jego,su anan sun maida hakan kamar ibada dan haka idan miji be yi ba sai abin ya zama gori har jikokin mutum."
"Ikon Allah, Allah guda d'aya amma garuruwa daban-daban ni ban ta6a ji ba koda wasa wallahi. Toh idan kuma mijin bashida halin yi fa sai ayi ya ya cutie?"
INdo tana gyara k'afar Ayman ba tare da ta kallesa ba tace.
"Idan miji beyi miki ba shikenan sai a rabu dashi baza a mayar da ita ba. Idan aka ga ya takura da zaryar zuwa gidan su kuma sai ad'auke ta a kaita inda bazai sake ganinta ba har sai ya kawo kayan."
Sosai mamaki ya cika masa zuciya, lallai akwai d'inbin gyara a cikin kauyan nan amma banda haka ya za'ayi a hana miji matarsa akan abinda ba alkurani bane ya wajabta shi ba. Lallai yadda ya k'agu ta koma su tafi kwara state tare dole yaje a harhad'o a kawo,yarinyar tayi tsada da yawa daga wannan sai ace maka wannan.
"In zuba maka yanzu ko sai kayi sallan azahar naga an kusa kirawo wa."
"Bari sai nayi sallah cutie, dawo nan in dinga jin duminki a jikina."
Matsawa tayi ya rungumeta, yana yawo a jikinta da hannunsa ita kuma ta lumshe ido tana sauraransa. Sallamar su Uwani suka jiyo Sadeeq yayi saurin zame hannunsa daga jikinta yana yatsina fuska yace..
"Su waye?"
"Inajin su Maryam ne naji muryar su da Uwani da Sahura."
"Kai nashiga uku ni Sadeeq, wai hardasu nake aure ne da kullum na shigo garin nan sai sunzo sun samin ido? Ko 'yan uwanku ne cutie?"
"A'ah k'awaye nane amma kuma su haka suke duk inda sukaji labarin wani abun tofa sai ka gansu sabida dama ba wani tambayar miji fita suke yi ba."
"Ai munafukai ne wallahi."
Ya fad'a a kufule kafin ya matsa sun shigo cikin d'akin bakunansu a washe.
Zama suka yi daga bakin k'ofar amma hakan be hana warin ranar jikinsu da kaurin icen girki shiga cikin hancin Sadeeq ba ya tuna da tuni itama INdon haka take amma Allah ya d'aukaka ta.
Da kyar ya amsa musu a ciki-ciki sabida yadda suke kallansu suna rik'e ha6a sabida sunga sun manne jikin juna.
"Cutie zanyi alwala."
"Okey toh bari akawo ruwa k'ofar gida, ko zaka yi anan ciki."
"A'ah Inna na nan da dai bata nan sai nayi."
Tashi yayi suka d'an ra6e ya wuce sannan INdo ta fito suma suka bita a baya, tunda tazo gida suke bibiyarta ganinta suke tamkar Matar wani shugaban me rik'e da wani muk'amin.
Ruwa ta zuba tasa mayafi takai mai wajan mota sannan ta koma ciki.
Hira suka farayi dasu har aka idar da sallah Sadeeq ya dawo daga massalaci dan har tsayawa yayi suka d'anyi hira da principal d'in tsefawa makarantar su INdo daya bari.
Nafeesah ce ta kuma fita ta shigo dashi sannan INdo ta bishi su kuma su Uwani suka ci gaba da hira da Inna duk da bata cika sanya musu baki ba.
"Cutie Ina baby na kika kaishi?"
"Inna ta goyashi ko na kar6osa?!"
"Ah no kyalesa kar ace nayi rashin kunya."
Waina ta zuba masa da miya sannan ta matsa kusa dashi, had'e hannuwa yayi a k'ijinsa tare da bud'e baki alamar ta bashi da kanta.
Murmushi tayi tana girgiza kai ta fara bashi kunnuwansa har motsawa suke yi sabida yadda miyar tayi mai dad'i idan ta bashi sau d'aya itama sai ya tura mata wanda ta kuma d’ebowa yasa mata a baki haka suka dinga yi har suka kusa cinyewa yace ya k'oshi.
"Cutie gaskiya ranar Sunday zaki koma zanyi duk iya yadda zanyi na tabbatar da an kawo kayan nan, sannan direct za'a wuce dake can gidan marigayi acan zaki ci gaba da zama an raba gado Abba yace idan kin koma zaizo yayi miki bayani kinji.?!"
Kifta idanuwa ta shiga yi alamar hawaye take son karsu fito ya janyo ta tare da kamo fuskarta yana san saka kwayar idanunsa cikin nata.
"Karki zubar min da hawaye kinga nima ina tattala nawa, keda ma ba'ayi miki da yawa ba tunda an baki me kamadashi iri d'aya sak sannan kina cikin zuciya ta kamar rai. Ni kuwa tare muka taso mu kwana tare muyi fad'a mu shirya ba tare da kowa ya sani ba, shine ni nine shi amma yau babu shi."
"Ka d'auka kaima a ranka nice shi tunda dama silarsa ce ta sa muka zama abu d'aya dakai, na zame maka shi kaima karka sake yin kuka mun riga munyi *MUSAYAR ZUCIYA* ni da kai fatana a yanzu shine na zama tauraruwa kamar yadda yake so yaga na zama kayi min addu'a malama Hannatu tace addu'ar miji akan matarsa tana saurin kar6owa."
Bakinsa da yake ta motsi tun d'azu shi ya zura cikin nata cikin wani mugun tausayinta da wata azababbar kaunarta da soyayyarta da ta taso mai. Kissing d'in ta yake cikin wani irin salo wanda yasa INdo ta kasa gane kansa, ya shagala kawai suka ji muryar malam Hamza a tsakar gida amma Sadeeq ji yayi tamkar a tsakiyar d'akin yayi sabida tsabar tsoro.
"Na tafi cutie kar nayi abun kunya a gidannan a d'akin baba dan naga kema ba hanani zaki ba."
Dariya INdo take yi sosai wanda tasa Sadeeq kallonta yana hararata dan har rik'e ciki takeyi ya matsa can bakin k'ofa-k'ofa tare da maida hularsa yana jiran shigowar malam Hamza d'akin dan yaji Inna tana cewa suna ciki.
"Matsoraci kawai Abu Ayman, uhm...uhm..uhm.."
INdo ta fad'a cikin dariya ya juya yana mata gwalo shima. muryar malam Hamzan yaji a bakin k'ofar Sadeeq yayi saurin d'aga labulen ita kuma INdo ta fara matsar da kayan da suka ci abinci kamar masu gaskiya.
"Baba sannu da shigowa, gashi duk mun tsare maka d'akin."
Sadeeq ya fad'a yana gyara zama tare da turo hula gaba yana kuma mai da ita baya alamar kunya ya keji.
Malam Hamza yayi dariya tare da k'arasawa cikin d'akin ya zauna a bakin gadon sa yana cewa ba komai Gaidashi Sadeeq yayi cike da girmamawa har suka d'an fara hira ita kuma INdo ta kwashe kayan ta fita dasu can su Uwani aka ci ragowar ana jinjinawa INdo ganin duk da kud'inta tayi wannan shagalin.
Malam Hamza da Sadeeq sun jima suna hira kafin malam Hamza ya fita INdo ta shiga tare da d'ora mai ayman akan k'afarsa kasan cewar ta kar6o masa shi dan tasan yana son ganinsa.
"Cutie ni kikawa dariyar mugunta ko? Hmmm zan rama ai zaki zo inda nake."
"Toh ai kaine da abin dariya wallahi."
"Za dai mu had'e you will see."
Kallon ayman yayi tare da cewa.
"Cutie wannan da wa yake kama sam na kasa ganewa?!"
"Ban sani ba nima kasan ance ba'a gane kamanin jarirai harsai sun fara girma."
"Ki dinga karanta mai ayatul kursiyu kina tofa mai a mad'igarsa ai kin iya ta ko?"
Tana kallonsa yatsan hannunta k'arami a cikin bakinta tace.
"Eh na iya mana."
"Matso nan toh kiyi min inji ko dai-dai ne."
Cikin jin wani iri dan kar ta kakare ta matsa jikinsa ya rik'ota, a hankali ta fara karanto mai inda yaji zata 6ata wani gurin sai ya gyara mata harta gama sannan yace.
"Yauwa ki dinga yi mai Allah ya kare mana shi daga sharrin shaid'anu."
"Amin abu Ayman."
"Zan wuce sai kinzo cutie ki yo shiri sosai dan wannan karan hmmmm."
Dariya ta kuma yi sannan ya zaro kud'i 10k ya bata ko zata yi wani abun idan zata dawo sannan ya mik'e itama ta tashi suka rungumi juna kamar basa son rabuwa cikin yanayi na ba haka aka so ba Sadeeq ya bata Ayman sannan ya fita suka yi sallama da Inna su Uwani sai subirbid'a mai addu'ar sauka lafiya suke yi dan har lokacin suna gidan.
A zaure Sadeeq yaga malam Hamza kan wata guntuwar tabarma yana gyaran redio suka yi sallama bayan ya ajiye mai 5k yana ta godiya.
Yana shiga mota INdo tazo nan ma suka yi sallama ji yake tamkar ya tafi da ita amma ba yadda zai yi dole ta fita yaja motar ya tafi cike da kewarta ji yake ma tamkar basu had'u ba kamar yanzu ne ma yake kan hanyar zuwa ya gansu....
*HAJJA CE*👈
[7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*
♥♥
♥
A true life story
Na
*K.A.S Precious Hajja ce*👈
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)
*DEDICATED TO:* Sanah Isma'il Matazu.
*VOTE me on wattpad @Hajjac*
Page *39*
Tunda Sadeeq ya koma gida be sanar da kowa zancen da suka yi da INdo ba kasan cewar baya son duk wani abinda zaija ayi mata gori akai ba. Gidan k'anwarsa Hawwa yaje suka yi magana hakan yasa duk abinda ya siyo ita yake kaiwa ga shirin gidan da ake yi mata wanda zata koma.
Cikin kwana biyu ya gama had'awa washe gari ana sauran kwana biyu INdo ta dawo yasa aka kai hawwa gidan su INdon takai kayan. Sosai aka dinga murna ana yiwa INdo barkar cewar mijinta ya fitar da ita kunya da kayan da babu wacce aka ta6a yiwa kowacce mace irinsa a kauyan. Shiri tayi sosai ciki da waje Rukayya ta kawo mata kayan INdo ta sake yin wani sassanyan kyau sam bata bari a sauya mata ak'idar da take da ita dan yanzu a kauyan akwai 'yan matan da suke kwaikwayar shigarta da kwalliyarta har yafa mayafi ma.
***
"Gaskiya Fateema kina da hakuri, ki duba ki gani a cikin shekara d'aya da auranku kishiyarki tayi zaman gidaje gashi yanzu mijinku d'aya amma zata koma wannan uban gidan na alfarma ke kina wannan duk da cewar shima yana da kyau amma nata yafi girma da kuma kyau ya kamata kema kiyi bori wallahi asan yadda za'ayi dake."
Cewar wata malama da suke k'awance da Fateema tun zuwanta school d'in. Numfasawa Fateema tayi tana jin k'irjinta na bugawa zuciyarta na zafi dan ta tabbatar da zancen aunty Hafsat gaskiya ne, gashi uwa uba ita bata haihuwa duk da bata fitar da rai da rahamar ubangiji ba a kan samun ciki.
"Amma ni ina ganin ba wani abun d'aga hankali bane Hafsat ganin dama tun farko a cikinsa ta fara zama, karki manta gidan mijinta ne na farko kafin tazo mu had'e. Kuma a k'ishin-k'ishin d'in da naji cewar an bashi gidan kinga dan ya mayar da ita baxan d'aga hankalina ba tunda itace ta fara zama a cikinsa."
"Lallai Fateema toh ai nan gaba na san zaki gane abinda nakeso ki fahimta."
Murmushi tayi kawai bata son nuna hassada akan lamarin tunda taga wanda ya narka kud'in yayi abunsa Allah be barsa yaji dad'in da ya tanadarwa rayuwarsa a cikin gidan ba. Idan ta tashi hankalinta akan abun itama Allah sai ya d'auke ta aga ta tsiya tunda kamar yadda Ummanta ta fad'a auran Sadeeq da Aisha Had'in Allah ne.
Shiga yayi gidan ya tarar tayi tagumi sam ba taji shigowarsa ba sai tsayuwar sa taji Sadeeq ya zauna a gefenta yana kallonta. Murmushi tayi mai sai dai iyakarsa le6anta kasan cewar ita kanta taga yadda yake rawar k'afar dawowar matarsa dan yakan iya gaya mata zata dawo kusan sau biyar arana duk shigowa sai ya gaya mata hakan yake bata mamaki har take tunanin ko yanzu ya dena sonta ne, duk da cewar be sauya mata ba yana nuna mata soyayya fiye da tunanin me tunani.
"Baby tunanin me kike yi haka?"
"Babu komai baby kawai ina tunanin rayuwa ne."
"Hmmm da alama dai zaman kad'aicin nan ne yasa ki shiga tunani, toh na dawo kuma bazan fita ba yau ina tare dake soyayya zamu yi."
Yayi maganar yana rik'ota yana shak'ar k'amshinta, ita ma tayi k'ok'arin Kawar da abinda yake damun cikin ranta.
"Kai baka gajiya da aiki ne baby?"
"Ehmm kinsan ai ked'aya ce yanzu, kuma duka duka yaushe na dawo ai kinga nayi k'ok'ari baby."
Dariya tayi tana shafa kanshi ya lumshe idanuwa. Wato mata biyu Lafiya ne daga nan kayi nan babu fargaba bare tashin hankali dole maza suyiwa Allah godiya daya basu wannan damar. Sai gaf da magriba ya samu ya fita bayan sallan isha'i suka yi waya da INdo sannan ya shiga gidan ba tare da Fateema ta gane sunyi ba. washe gari ya tafi Sumaila kauyan Sani yaje ya d'akko matarsa.
Yana zuwa ya buga mata waya ba'a d'auka ba sai gani yayi Sagiru ya fito, gaisawa suka yi sannan ya sanar masa cewar tana wanka Sadeeq yace ba komai sannan Sagiru ya koma gidan. Tana fitowa ta buga mai ya katse ya kirata da kanshi dan shine yafi can-cantar yin hakan ba itaba.
"Cutie meye nayin wanka, da kin bari idan mun koma gida sai muyi tare."
"Hahaha..lallai a haka kake son na bar Sani zuwa cikin gari ko? Ban yadda ba gashi na fito kaya kurum zansa sai mutafi."
"Shikenan ai tunda abun 'yar haka ne, ki turo a kawo min yaro na mu fara gaisawa nayi missing d'insa."
"Okey shi zaka fara gani ba niba ma ko?shi kenan bari a kawo shi sai ku tafi ni saina zauna a gidan."
"Wayyo cutie ki rufamin asiri I can die idan kika k'i bina Zuciya ta zata iya shiga rud'ani zan iya rasa nutsuwa ta. Cutie kin zamo wani jego a cikin rayuwata Ina sonki dan zan iya cewa nafi m twinnie kaunarki Ina jin zuciyata na bugawa a duk lokacin dana tuna cewar bani na fara nuna miki soyayya ba but ki yadda cewar ni d'in ina wahala a cikin raina da rayuwata idan bake a kusa dani, please kiyi sauri ki fito mu tafi dan Allah."
"Gani nan fitowa barima a fara fito da kayan namu."
Tana fad'a ta ajiye wayan sannan ta lek'a tsakar gida ta kira su shehu suka fitar da kayansu. Tsab INdo ta shirya Nafeesah ta shirya Ayman sannan ta fitar dashi, sai da suka gama shiryawa ta fita kallansa tayi ta glass d'in motar tare da cewa.
"One minute."
Mak'ota suka shisshiga suka dinga yi musu sallama har sai da suka zagaye unguwar sannan suka koma Sadeeq ya gaida Inna sannan INdo suka yi sallama da kowa na gidan suka shiga mota Sadeeq yaja zuciyarsa shar daya juya yagan su sai yaji wani farin ciki yana kuma ratsashi.
"Cutie me d'ah, wai ke dan Allah bakya mamakin hakan?"
"Bana yi, kai da ace fa marigayi be d'akko ni daga Saye ba da inajin yanzu 'ya'yana biyu ko uku da wani saurayi na salele."
"Toh naji abar maganar waye wani salele ba ko dad'in ji. Cutie nayi missing d'inki amma ke da alama kamar bakiyi nawa ba."
"Abu Ayman kenan, karka fad'i haka domin zaka zalince ni. Kawai ba yadda zanyi ne ko na nuna babu yadda zanyi tunda ko a gidan ka na zauna dole baka nan amma nayi missing dinka dan ma akwai Ayman ina kallonsa Zuciya ta na ganin kamar kaine shi yasa kaga banyi ramar rashinka ba."
Dariya yayi hannunsa na ta6o k'afar Ayman, haka suka dinga hirar yadda suka yi rashin juna har suka k'arasa k'ofar gidan marigayi wanda zata ci gaba da rayuwa a cikinsa.
K'irjinta ne ya dinga bugawa Sadeeq yaje ya bud'e gate ya shigar da motar duk yana ganin yadda ta sauya jikinta yayi sanyi hannunta dafe da k'irjinta idanunta a rufe. Hannunsa INdo taji a wuyanta hakan ya sake tayar mata da hankali kawai sai ta sakar masa kuka mai sauti.
Ayman ya k'ar6a kafin yayi wani abun su Haleema sun fito suna musu oyo-yo kasan cewar suna ciki sune 'yan taryar su.
"Cutie ya haka? Kuka? Ohh ya subahanallahi danasan zaki kuka da wallahi baxan yadda na kawoki gidannan ba, cutie bakya sona ko? Please dan Allah kiyi shiru bazan iya barin ki fita daga motar nan ba alharin kina kuka dan kinga mun shiga nan gidan ba. Ki dinga sawa a ranki nine Abubakar Sadeeq gaba d'aya ki tuna cewar kina da irinsa kamar yadda nima nake ganinki a matsayinsa please."
Share mata fuska yayi sannan yasa hannu a baya ya d'akko jakarta ya zare powder da kanshi ya shafa mata ya gyara mata fuskar ya sakar mata murmushi tare da cewa.
"Kinfi ma kyau yanzu da nayi miki kwalliyar kin ganki kuwa Son Sadeeq k'in wanda ya rasa zuk'i..."
Dariya yaga tayi sannan yayi unlock d'in motar su Haleema suka bud'e tana kar6ar Ayman tana cewa.
"Wai toh me kuke yi a motar kuka dad'e aunty Humaira."
"Toh gulmammiya ina ruwanki bana son saka idofa."
"Sorry broth sannun da hanya."
Shareta yayi yana hararta INdo dasu Aminatu suka shiga ciki shima yabiyo bayansu. Kujerun d'ayan falon na ciki wanda ba'a shiga su aka dawo mata dashi falon farko kasan cewar da nata aka kai mata can gidan Sadeeq dining room d'inta yana nan tad'al-tad'al tayi fuskarta nason yin hawaye amma murmushi kwance a fuskarta lokacin da take tuno yadda suka yi rayuwa da marigayi,Sadeeq ya shiga tare da kama hannunta ya nufi bedroom su Haleematu suka zare idanuwa hannu rik'e da ha6a sannan suka ta6e baki.
Suna shiga ya jata jikinsa suka tsaya wajan madubi yana kallonta. Hannu ya d'ora saman k'irjinta yana wasa dashi bakinsa saitin kunnanta yace.
"What happen to my cutie angel ne? Aisha I love you but naga ke har yanzu akwai marigayi a cikin zuciyarki kin kasa sanyani a ranki why.?”
Numfashinta na sama-sama sabida yadda taji yana mata murya a sark'e tana narke mai sabida yadda k'afarta take neman kasa d'aukarta tace.
"Wa yace maka baka cikin raina? Shin duk yadda nake cewa kana cikin raina kazama ni nazama Kai duk a tatsuniya kake d'aukar su?"
Juyo da ita yayi yana kallonta yace.
"Na kasa ganewa but prove me now."
A hankali ta sanya hannu a wuyansa ta sargafo shi tare da had'e hancinsu guri guda cikin salo ta zuro bakinta cikin nasa Sadeeq yayi saurin kar6ar sakon tare da rik'ota shima. Kukan Ayman ne ya sanya suka tsaya da abinda suke yi jin kamar hanyar d'akin aka yo dashi, sadeeq na matsawa sai ga Sajida da Ayman tana cewa.
"Aunty Humaira wai kuka yakeyi inji yayya Haleema."
Kar6arsa tayi sannan ta fita Sadeeq ya zauna a bakin gado yana cewa.
"Wallahi munafincin Haleematu ne dama naga take-taken su nasan ganin gulma."
INdo tayi dariya tana k'ok'arin ba Ayman.... Sadeeq ya mik'e yana cewa.
"Bari naje na maida su gida bana son kinibibin yaran nan."
"A'a dan Allah ka rabu dasu kana ganinfa ko gaisawa bamu yi ba."
"Yanzu cutie kin fison su zauna akan ni na zauna?!"
"A'ah ba haka nake nufi ba, amma kaga ba dad'i ka kyalesu basu yi niyar tafiya ba toh ka kyakesu dan Allah."
"Shikenan toh bari naje d'ayan gidan ai Fateema na nan."
Yana fad'a ya fita INdo ta bishi da kallo, ai dole yace haka tunda ta dawo gurin sa. Tashi tayi ta koma falo wajan su haleema suka fara murnar dawowa da hirar yaushe gamo.
Sai da akayi magariba sannan su Haleematu suka tafi ita kuma ta cigaba da gyara kayanta. Har kusan tara na dare Sadeeq be shigo gidan ba hakan ya 6atawa INdo rai ganin ko dai ya dawo da itane dan ya fara wulak'anta ta. Shirin bacci suka yi itada Ayman gashi ko gen ba'a kunna musu ba kuma bata damu ba domin a can gidan su ko wearing na nefa basu dashi, tana gamawa tayi kwanciyar ta zuciyarta na k'una ta janyo pillow ta rungume tare da rufe idanuwa.
Sai wajan 10:15pm ya shigo hannunsa rik'e da ledoji, kayan ya ajiye a falo sannan ya fita ya tayar da injin taja tsaki tamkar yana gurin ta kuma rufe idanuwa dan ba k'aramin haushinsa takeji ba na watsar da su d'in da yayi.
"Cutie..! Cutie..!"
Yaji shiru sai ya shiga cikin d'akin, kwance ya gansu da alama sunyi bacci ya lalla6a ya k'arasa kusa da ita yana son juyo da ita yaji tayi tauri hakan ya tabbatar masa da cewar idanunta biyu.
"Haba cutie ba Oyo-yo shine zaki zo ki wani kwanta tashi muje falo."
"Sorry bacci nake ji ka koma inda kafi so."
"What..?!"
Banza tayi mai ya kuma komawa wajan fuskarta yana matsa hannunta yace.
"Amma ki bari sai munzo kwanciya sai muyi wannan wasan but yanzu dai taho muje falo."
"Nace kayi tafiyar ka wajan matarka, nasan dama can itace za6in zuciyar ka bani ba da aka lik'a maka, toh kaje katafi gurin Fateema daka fi so na bar mata kai. Banda mutuwa ma me fallasa ai da hakan bata faruba bare kamin wulak'anci harda cewa toh kaima ka tafi wajan Fateema shine sai yanzu goma da wani abun zaka ce ka dawo in tashi."
Ta k'arasa maganar cikin kuka tare da tura fuskarta k'ark'ashin pillon da kanta yake kai. Ba k'aramin tashin hankali Sadeeq ya shiga ba jin abinda take fad'a, ya janyo ta yana lallashi kan ta sanar mai da abinda yayi mata amma tak'i, har zai rabu da ita yaji bazai iya ba sabida zuciyar da take tsananin sonta tak'i jin haushinta sai ma k'ara k'ask'antar da kansa da yayi yana cewa.
"Kinga ba wai da gangan kika ga nayi dare haka ba no, ana yin sallahn magrib muka tafi gidan wani malami nida Abba bamu dawo ba sai bayan sallahn isha'i naje nakaisa gida sannan nayo muku siyayya naje ko dad'ewa banyi ba a gidan Fateema nayo nan amma shine zaki min wulak'anci ko? Shikenan tunda har kin fara yi min mumunan zato."
Yana fad'a ya fara k'ok'arin sauka a gadon sai kuma yaji ta rik'osa, itama bazata iya fushi dashi ba ya lek'a fuskarta ta kallesa sannan ya tashi tare da d'agata suka nufi falo.
"Cutie ki dena min saurin fushi bana so yana sani cikin damuwa da tashin hankali kinji?!"
"Toh amma nima ka dena barmin gidan ka dad'e baka dawo ba tunda kana garin."
"Insha Allahu."
Ya fad'a, kitchen taje ta d'akko plate da cups ta dawo. Gashasshiyr kaza ce da aka sanya mata kwai tasha kayan lambu ga yajin tafarnuwa suka zauna suka ciyar da juna ranar sunyi kwanan farin ciki marar bayyanawa bare rubutawa.
Satin INdo uku da dawowa da kyar da nuna jajircewar shine mijin ba ita ba ta yadda zata bisa zuwa kwara state sabida ta kafe ita karatunta zata koma amma yak'i har kuka tayi suka yi fad'an kwana biyu amma yaki sakkowa dole ta hakura ta bisa suka tafi aka bar Fateema...
Nd Page finale is loading🤨
#love you
#my fan's
*HAJJA CE*👈
[7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*
♥♥
♥
A true life story
Na
*K.A.S Precious Hajja ce*👈
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)
*DEDICATED TO:* Sanah Isma'il Matazu.
*TUKWAICI GA:-* Dota Fateema (Marok'i).
*DAN JIN DAD'INKI:-* Billy S Fari.
*VOTE me on wattpad @Hajjac*
*End*
Page *40*
Tun a cikin mota suke yin fad'a k'asa-k'asa yadda ba kowa ne zai gane ba bare aji. INdo mita kawai take masa sabida tsabar ta gaji da zama bata ta6a yin tafiya irin me nisan haka ba gashi tun a cikin motar ta fara ganin ban-bancin kano da inda za suje domin duk cikin motar yare ne basufi su shida bane hausawa kuma suma ba wai zaune suke a guri d'aya ba kowa yana kan kujerarsa. Wani yare dake kusa dasu yana ta kallon Ayman ya zuro hannunsa yana shafar kanshi tare da tambayar INdo ya sunan d'an cikin yarbanci k'irjin INdo ya dinga bugawa jin bata gane abinda yake nufi ba, sai kallon mutumin take shi kuma yana faman kuma tambayarta. Kallon Sadeeq tayi kawai taga yayi tamkar baya jinsu yana karanta jarida tasa hannu ta zunguro shi ya kalleta sannan ta kawar da kai tare da cewa.
"Ana maka magana fah."
Kallonta yayi yana k'umshe dariyar sa kafin ya kalli bayeraben sai taji ya gaya masa sunan Ayman bayeraben ya jinjina kai bakinsa a washe ya cewa Sadeeq yaron yana da kyau Sadeeq yayi dariya duk babu abinda INdo taji a cikin maganar gashi sai dariya bayeranen yake hakan ya sake k'ona mata rai domin abinda take gudu ne yake shirin faruwa wato a dinga magana bata son me ake cewa ba. Sun tsaya anyi sallah anci abinci an rage mara sannan suka kuma d'aukar hanya ran INdo ba k'aramin 6aci yayi ba har suka k'arasa garin cikin tsakiyar dare. Duk da tayi bacci a mota amma ji take tamkar bata ta6a yin bacci a rayuwarta ba, ko wanka bata yi ba dakyar ya samu tayi sallan magrib da isha'i tabi lafiyar gado.
Da kyar Sadeeq ya samu ta farka k'arfe takwas tayi sallah dan tunda ta kwanta ba tayi juyi ba, ko kukan Ayman bataji sai dai shi ya farka ya ciro.. sannan ya samai abincinsa a baki idan ya saki kuma sai ya mayar mata sam bata sani ba sai da tazo suna gaisawa yake bata labari suka dinga dariya. Fita Sadeeq yayi ita kuma ta shiga taga yadda gidan yake bayan ta goya Ayman. Be jima ba ya dawo hannunsa rik'e da leda yaje kitchen ya juye musu abincin daya siyo musu suka tafi falo.
"Wannan kuma bak'in abun menene haka."
"Amala ce da miyar ayayo da dad'i kuma cutie ci kiji."
Zama tayi suka faraci tana sawa abaki ta dinga yatsina fuska daga k'arshe ta matsa ta had'iye ta cikin bakinta da kyar. Sadeeq ya kalleta cikin mamaki yace.
"Cutie ya haka? Ba kya ci ne?"
"Gaskiya bana ci wallahi wannan abu a samo min wani."
Shima jiyayyi sam ba zai iya ci ba duk kuwa da son amala da yake yi. Kallonsa tayi tana goge hannu cikin shagwa6e fuska tace.
"Kuma ni yunwa nakeji wallahi kamar inci babu, ko cinyeka nayi ji nake bazan k'oshi bama gashi da Ayman ya farka zaice zai sha kuma babu komai a ciki wallahi duk ya tsotse."
"Kai cutie wai ba komai a ciki, toh duk meye wannan abun a ciki?!"
Yayi magana yana kallonta da mamaki, ta kuma narkewa cikin nuna jin yunwa sosai tace.
"Shikenan tunda baka yadda ba, ni dai ka samo min abinci."
Tashi yayi da sauri tun yanzu yaga ban-banci tsakanin su da Fateema domin duk abinda ya siyo ko bata ta6a ciba toh zata ci amma ita common amala tace wai ba dad'i. Tunani ya dinga yi yana neman abinda zai siyo mata gasu da shegen tsadar abubuwa daya rasa yadda zai yi kawai sai yaje gurin wata k'awarsa cinyere da take dafamai abu idan bezo da Fateema ba yasa ta dafa mai indomie da ruwan tea ya kar6a ya kai ma INdo, harda su murmushi tayi mai sabida ganin abinda zata iya ci. Kad'an yaci kasan cewar bata damesa ba ita kuwa taci sosai kad'an ta bari tasha tea sannan walwalarta ta dawo taje kuma ta dinga narke mai tana takura mai.
Satinsu d'aya da zuwa garin babu inda INdo take zuwa ko lek'e batayi ba, aranar kuma ya fara fita gurin aikinsa yana tafiya ita kuma tana gyaran gidan sai ga wasu 'yan mata kowacce da 'yar bingilar riga da mini skirt suka shigo.
"Madam excuse us,can we come in please?"
INdo ta bisu da kallo ita kuwa me ya had'a ta da arna da har suke neman shigo mata gida? Ganin tayi shiru ne yasa d'aya daga cikin su tace.
"We are friends of your husband,can you let us in..Mrs sadeeq?!”
"Me..? For what reason??"
"Don't get wrong Mrs sadeeq,we are friends of sadeeq ,we just came by to see his newly born baby”
Shi kuma ya rasa da suwa zai yi k'awance sai da mata dan rainin hankali, toh baxata bada d'an su ganshi ba bama su da kunya basu santa ba kawai zasu wani zo k'ilama k'arya suke salon su sace mata d'ah ne.
"Madam please..."
"Eyyah m sorry he is sleeping.."
Ta fad'a tana d'ari-d'ari kar su gano cewar 'yar koyo ce a cikin yaren turancin. Suka ce zasu dawo anjima ko gobe, suna fita ta kulle gidan bata bud'e ba sai da ya dawo ya buga mata waya taje ta bud'e.
"Ya aka yine cutie wallahi yanzu kin fiye rigima kamar ma k'aruwa take yi. Sam kamar baki haihuba yanzu kuma meye ya faru ko yaro nane ya ta6oki ne..?!"
Yana rik'e da hannunta suka shiga falon ta kuma had'e rai ya juyo da ita suna kallon juna yace.
"Gaya min menene ko kina nufin dad'ewa nayi ban dawo ba?!"
Zaunar dashi tayi taje ta kawo ruwa yasha kad'an sabida baya tare da k'ishi dan kar tayi zargin wani abun ne yasa shi yasha. Zama tayi Ayman na kan kujera yana bacci ta kwantar da kanta a cinyarsa yana jan hancinta tace.
"Bayan ka fitane wasu mata arnaye gunduma-gunduma suka shigo su hudu ko wacce da wani banzan skirt, wai dan son maidani wata sakarai suke ce min sunzo ganin Ayman ne wai ka gaya musu kanada d'ah."
"Ohh su Juliet ne da blessing sauran ne dai ban gane ko suwaye ba. Toh kin basu sun ganshi ko?"
"Kut in basu kuma..?! Wai kaima ka d'auka har yanzu bani da hankali ne? Kawai ban san su ba baka yi min bayanin su ba zan d'auki d'ana na basu, lallai da hankalina wallahi yanzu ba dah bane."
Kallonta yake shi yanzu baya ganin wani aibunta komai tayi sai yaji zuciyarsa ta aminta da abun koda kuwa yana son yi mata gyara. Hannunta ya rik'o ya sumbata sannan ya fara shafar fuskarta yace.
"Cutie su Juliet mak'otan mune wannan benan na jikin mu shine gidan su, please ki bari kuyi mutunci musulunci be hana ba suna da kirki basuda matsala suna ganin girmana sosai."
"Lallai in rasa da wad'an da zanyi k'awance sai da arna wallahi ba ruwa na bazan yi ba sam."
Shafa kanta yayi lallai ashe akwai gwarmai domin idan yazo da Fateema suna zuwa kuma bata kyarar su hakan yasa suka saba ita kuma ko me ta d'auki Christians oho mata. Share zancen yayi ya d'agata tare da janta suka shiga kitchen dan yaga alamar har lokacin haushin bak'in basu barta ba.
"Cutien Sadeeq da Ayman a dafa min wannan abun."
Yafad'a yana ciro wani magani a cikin aljihunsa, tana tsaye tasa shi ya d'akko tukunya tace ya tari ruwa a sink ta kunna gas ya zuba maganin yana dariya k'asa-k'asa dan dama yasan INdon sa tun a tsefawa 'yar rigima ce dan haka yanzu in tayi abin bazai damesa ba sosai kuma tafishi gaskiya tunda bata sansu ba tayi hankali da ta hanasu dan za'a iya zuwa a damfareta hakan kuma da tayi ta nuna mai ba da kowa zata dinga yadda ba kamar yadda wasu suke ganin hakan cinyewa ne sai kuma an cucesu suzo suna kuka. Har ya dahu suna kitchen d'in tana ta6ara.
"Muje falo naga wasu littattafan turanci, tunda maganin ya dahu kafin ya huce na karanta maka kaji."
Hannunsa ta fara jah yayi saurin rik'ota tare da girgiza mata kai ta had'e rai. Maganin ya d'auka ya kai bathroom ya juye cikin bahon wankan Ayman sannan ya mayar da tukunyar kitchen ya kalleta ta zauna kan kujera sai cuno baki take yi ya zauna kusa da ita yana rik'o hannunta murya a sark'e yana narke mata idanuwa yace.
"Cutie rigima, zo muje ai naki ne shiga ciki zaki yi."
INdo ta zaro idanuwa fuskarta a d'aure tana mai wani irin bahagwan kallo, ganin yadda take kallansa a hagunce yasa shi shafar fuskarta yace.
"Whats wrong?"
"Shin bakajin nutsuwa dani ne ko kuwa dai wani abun kakeji a tattare dani? Ko kuma me kake nufi malam Sadeeq da zaka kawon abu wai in shiga ciki...?!"
Hannu yasa ya rik'e kansa tare da rintsa ido jin yadda ta mayar mai da abunsa. 'Dagowa yayi idanunsa jawur sabida yadda ransa ya sosu dajin abinda tace ba tare da yayi magana ba ya d'auki phone ya kira Fateema bayan ya had'iye 6acin ransa.
"Hello baby na ya aiki? Yasu my sweet Ayman?!"
"Lafiya lau baby ya skull kin dawo ko?"
INdo ta mik'e zata bar gurin yayi saurin rik'ota ta fara k'ok'arin kwatar kanta dan wani haushinsa takeji. Ji tayi ya cigaba da yin wayarsa hankali kwance kafin taji yace.
"Ammm baby ko kina son na taho miki da wannan ganyen maganin naga wannan zuwan ma na kawo shi kina so?!"
"Woww babyna ina so mana dan Allah kaje ka siyo karya k'are please my awesome husband."
"Okey tom zan kawo miki insha Allahu bye zan kiraki anjima."
"Thank you baby a gaida min da Ayman my son."
"Insha Allahu."
Kashewa yayi yana kallon INdo wadda still fuskarta a had'e take. Janyo ta yayi ta fad'o jikinsa tana turesa ya matseta tare da zura kansa saitin wuyanta yace.
"Banyi tunanin cewar akwai abinda zan saki kiyi amma ki tsaya tuhumata ba, Aisha ko wuta na rura nace kishiga hakan ya nuna min bazaki shiga ba sabida bakya sona da kina sona duk abinda zan ce kiyi bazaki tsaya wani tunani ko gaddama ba sai gashi kinyi na gani shi kenan na gode Allah yaso ina da wadda ta yadda dani 100%."
INdo najin haka ta saka kuka shi kuma ya tureta ya juya kan kujerar yayi kwanciyar sa duk da yanajin kukan har cikin k'ahon zuciyarsa. Tashi tayi a hankali tana kukan ta shiga bathroom, shiga tayi cikin ruwan tana ciki tana jan majina yayi murmushi ya kuma k'i bin bayanta, bata fito ba har sai dashi kansa yaga dacewar lokacin tafito yayi amma tak'i fitowa.
Zaune ya ganta a ciki ta saka fuskarta tsakankanin jinyoyinta sai gunjin kuka takeyi, k'arasawa yayi ya tsugunna a gabanta tare da saka hannu ya fara k'ok'arin d'ago fuskar ta amma tak'i ta kafe. Taurin kai na INdo sai addu'a ya mik'e tare ya d'agota cikin nuna k'arfi sannan ya fito da ita suka shiga bedroom yana rungume da ita suka zauna a bakin gado.
A gabanta ya zauna tare da rik'o hannunta kanta a k'asa idanuwanta a rufe sai faman sauke ajiyar zuciya takeyi. Kallon fuskarta yakeyi cikin tsananin sonta da kaunarta yace.
"Cutie nine fah ya kamata nayi kuka sabida kin kasa yadda dani, cutie i love you..ban san yadda zanyi na misalta miki ba duk abinda kikaga nayi dan ina sonki ne. Cutie koda kikaga na dage sai kin biyoni nan karkiyi tunanin cewar ko bana son kiyi karatune a'a ina son zuwa dake ne sabida ko bayan rai na kiyi alfaharin kema naje dake inda nake zuwa shi yasa kika ga na dage sai kin bini amma duk abinda nayi miki na rashin dad'i cikin sani ko rashinsa kiyi hakuri ki yafemin."
Hawaye suka kuma zubo mata ya tashi ya zauna kusa da ita tare da janyo ta jikinsa yana buga bayanta cikin muryar kuka take magana.
"Ni ka dena bani hakuri bayan baka min komai ba, nice zan baka hakuri sabida nice nake 6ata maka rai amma dan Allah abu Ayman kayi hakuri ka dinga yafemin koda a cikin zuciyar kane nasan ina 6ata maka rai dan All..."
A hankali yasa hannunsa ya toshe mata baki yana kad'a mata kai alamar tayi shiru, da sauri ta rungumesa suka k'ank'ame junansu cikin shauk'i. Basu fito ba sai da kowa yasan ya farantawa d'an uwansa sannan suka yi wanka suka ci gaba da soyayyarsu yana kuma koya mata karatunta cike da kwarewa yadda kuma zata gane ta fahimta duk da cewar tana d'an dad'ewa kafin ya zauna a kwakwalwarta danma understanding takeyi ba wai hadda ba.
Bayan sati uku
Lokacin sun cika wata d'aya da zuwa cikin ikon Allah kuma ya samu INdo ta fara sakarwa su blessing fuska sai dai yawanci sunfi yin wasa da Ayman kasan cewar turancin INdo ba nisa yayi ba kamar su da yazama shine yarensu na biyu da suke ji bayan inyamuranci. Itama takan d'an lek'a gidan su amma ba sosai ba dan su kan yi yarensu wanda yafi bawa INdo haushi sabida ko "zo" bata iya ba su kuma sunfi yinsa.
Sosai suka sake kulla babin soyayya dan zaman su anan su biyu ya kuma kulla sabuwar alak'a dan har basa son wani yayi nisa sukanji har zazza6i amma da an had'u sai a warke zuciyar su ta riga ta zama d'aya, duk abinda d'aya yakeji wala na dad'i ko rashinsa sai duk sunji yanayin a jikinsu, ciwon kai idan d'aya yayi sai d'ayan ma yayi koda kuwa fad'uwar gaba ce wannan yanayin yana basu mamaki da al'ajabi, sun kuma sake tabbatar da cewa sunyi *MUSAYAR ZUCIYA* ya kar6i tata itama ta k'ar6i tashi suna kula da junansu sannan ta rage yi masa taurin kai musamman da yake karanto mata tarihin annabawa duk dare idan sunje bacci.
Ayman yana ta wayo suna kula dashi sosai sannan koda second d'aya Sadeeq be ta6a manta Fateema ba yakan buga mata waya a rana kusan sau biyar yayi missing d'inta sosai domin ko wacce mace tana da nata matsayin a zuciyar miji musamman da ya kasan ce ita ya fara furtawa kalmar So ya kuma fara auranta ya fara saninta a matsayin matarsa. Yana jin dad'in zama da matansa su duka musamman yanzu da soyayyarsa ta kuma zama a cikin zuciyar INdo, yafi ta sonta amma yakan daure domin karya d'ora mata girman kai karta dinga d'aukar kanta a wani abun tunda yanzu ne yake d'orata akan sabuwar rayuwa dan yanzu ne take kuma sanin komai na rayuwa duk abinda ya d'orata akai zai ga shi takeyi bata ta6a k'etare duk wani abu da ya karanto mata ya fassara mata.
Watansu biyu suka shirya komawa lokacin INdo ta kuma wayewa tayi kyau tayi k'iba ta zama tamkar wata k'aramar hajiya tayi dam kwanciyar hankali ya fito a jikinta da yanayinta dama yadda take gudanar da abubuwanta dan takanji zata iya gogawa da ko wacce irin mace a fad'in duniyar nan duk da cewar iliminta bema kai na Fateema ba amma yadda zata gudanar da wani abun sai mutum ya rantse ko tana kanyin master's ne.
*****
Kwance take a jikinsa tana kuka domin ba k'aramin rashinsa tayi ba wata biyu ba wasa bane a gurin miji da mata musamman idan basu tare. Gashinta yake shafawa yana kuma rik'e da hannunta yana matsawa Sadeeq yace.
"Baby dan Allah kiyi shiru kinga dai ba zuwa nake garin can ina yawo in dawo ba, kinsan abinda nakeyi kinfi kowa sani tun kafin kowa ya sani hatta Abba kin fishi sanin me nake zuwa inyi dan haka bana son kukan nan please yana sani cikin shakku da kokwanto."
"Toh baby amma dai ka dena dad'ewa dan Allah. Ko kuma ka tattaro ka dawo nan kano shikenan kana tare damu koda yaushe."
"No... Fateema bana son zaman garin nan ga sa'ido sai dai ke idan kin yadda ki ajiye aikin ki idan zan tafi sai na tafi dake na ajiyeki a can kinga na huta kina can bani da fargaba ita kuma Aisha tana nan kun hutar dani ma."
"Nayi shiru baby nigara ku dinga tafiya da ita can babu kowa d'an uwa dangi duk babu sai sababbin da zaka yi na hakura zan dinga jiranka har lokacin da zaka dawo."
"Ummm kaji me wayo, wato ke k'ink'i bina sabida aikin ki. Amma ni kina son na dawo nan da zama shi kenan kullum a ce mijinku yana guri d'aya baya zuwa konan da can toh na gano ki kuma nak'i wayon."
Ya fad'a yana mata cakulkuli a cikinta suna ta dariya dan baya son yaji ta sako mai zancen rashin haihuwarta sabida shi be ta6ajin haushin hakan ba ko yaji sonta ya ragu a'a kullum yana jin sonta musamman da take mai biyayya da nuna soyayya.
Haka Sadeeq ya cigaba da rayuwa da matansa cikin kwanciyar hankali duk da wani sa'in yakan fuskanci matsala ta kowane 6angare amma yakan warware ta cikin hikima ta yadda ya san halin kowacce a cikin su. 'Daukar su yayi su duka sukaje aka yi musu hoto ya bud'a su ko wane gida yasa d'aya guda d'aya babu kuma wadda ta nuna mai bata so.
****
"Hello, Rasheedat. Okey ai zan shigo nan da 11:00 tuna sai 11:30 ko.? Okay sai na shigo."
Kwance yake akan kujera INdo na k'ok'arin zuba masa fruits salad duk tana jin abinda yake fad'a ranta yayi mugun 6aci zuciyar ta na zafi kishi ya turniketa sai faman had'e gira takeyi. Tashi tayi jikinta har rawa yake yi taje takai mai fruit salad d'in ya d'ago ya kalleta ganin yanayinta yasa shi riko hannunta ta fizge ya kuma rikowa ta kuma k'ok'arin fizgewa ya janyo ta kusa dashi ta zauna kirjinta sai dokawa yake yi Sadeeq yace.
"Toh yau kuma me Sadeeq sarkin 'yan masu laifi yayiwa cutien sa cikin 'yan sakanni.?!"
"Ba komai kyale ni zan shiga d'aki."
"Toh ki fara bani na gama sha sai kije kiyi aikin ki."
INdo ta kuma yin kicin-kicin a kufule tace.
"Ka kira Rasheedat ta baka mana amma ba ni ba."
"Rasheedat kuma cutie? Kin santa ne ko kuma dan kinji muna waya ne zuciyar ki ta fara halin nata."
Turo baki tayi tana harare-hararen gefe ta kasa cewa komai, Sadeeq ya janyo ta jikinsa yasa hannu a tsakiyar k'irjinta yaji yadda yake bugawa cikin tashin hankali ya mik'e zauna dan da a kwance yake yana rik'e da ita.
"Subahanallahi cutie kishi ne haka? Rasheedat ba budurwata bace d'alibata ce yau zanyi musu lecture shine take tambaya na shin zanje nace eh su shirya shikenan fa."
Sadeeq yana jin sanda ta sauke wata muguwar ajiyar zuciya sannan ta kallesa ya sakar mata murmushi tace.
"Toh banda basu da kunya meye na bugo maka, su ba students bane baxasu jira har kaje ba zasu wani bugo maka waya. Ina monitor da bazai bugo ba sai ita tana mace banzar kawai."
"Ta6 cutie har ina cewa zan k'ara aure sai kema na barki anan ki cigaba da karatunki Fateema tayi aikinta ita kuma amaryar na barta acan kwara gidana na Ilorin kunga an huta da zirga-zirgar fitar ku."
Share sa tayi ta d'ibi fruit d'in a cokali ta sanya mai a baki, yana dariya ya kar6a har ta gama bashi sannan ya janyo ta k'irjinsa yace.
"Cutie I love you zan iya mutuwa a duk sanda kika juya min baya, ki kula damu dani da yaro na dama wad'anda zaki haifamin nan gaba please cutie."
Sumbatarsa tayi a goshi sannan ta kwantar da kanta a saman k'irjinsa tana shafar kansa tace.
"Nima ina sonka my super glue, your my Biggest comport..my breath... My heartbeat.. Kai my everything but ka dena min zancen zaka k'ara aure, a cikin shekara d'aya kayi mata biyu sannan kace kana shekara ta biyu zaka yi ta uku ai sai ka jamana surutu. Dan Allah ka barmu mu biyu ka dena tunanin wata idan ba haka ba zanyi kuka."
"Yi muga irin kukan da zaki yi idan zan k'ara au..."
Tayi saurin toshe mai baki da nata kafin ta cire ta kalli cikin idanunsa daya bud'e su a hankali duk sun zama na rigima tace.
"Haka zanyi uhm..uhm..uhm..ahhh..wayyoooo...!"
Suka kyalkyale da dariya Sadeeq ya rungumeta akan kujerar yanajin k'aunarta har cikin ransa. Sun dad'e suna faranta ran juna duk sun manta da rigimar su ta baya Sadeeq ya kawar da rayuwarta ta baya a cikin ransa yana ganin tamkar dama a hakanta ya santa. Watan Ayman takwas kenan har gidan Fateema ake kaisa ya d'an jima kafin a dawo dashi tana son yaron har cikin ranta domin tana masifar son mahaifinsa.
*****
K'arfe takwas ya shiga gida, zaune ya ganta tana gyarawa Ayman kwanciya a falo, dariya yayi har yana rik'e ciki ganin yau kuma da salon da za'a siyeshi can ta tsuke cikin riga da wando nan kuma tayi mai shigarta daya santa a real INdon ta zamanin tana kauyan sani.
"Kai malam Sadeeq he wani kallona kakeyi he kace baka sanni ba."
Wayyo dariya Sadeeq ya tsugunna agurin ya dinga yi dan gani yake tazo mai da wani sabon salon soyayya. Ta dashare mai baki tare da k'arasawa wajan sa tasa hannu ta rik'osa da nufin ya tashi aikuwa ya janyo ta itama ta fad'a kansa suka dinga dariya cikin shauk'i.
"Cutie I love you so much."
"I love you too Abu Ayman."
"Allah yajik'an M tiwwine yasa rahama ta baibayesa yasa yana cikin farin ciki kamar yadda muke a yanzu."
"Amin ya Allah."
Ta fad'a tana wasa da ma6ullayen rigarsa nan suka dinga hirar baya suna dariya. Shirye-shiryen bikin Haleematu suka farayi Sadeeq yayi k'ok'ari sosai dan da su biyu suke had'uwa suyi komai shi yayi kayan d'akin hawwa Abubakar kuma yayi na falo amma yanzu baya nan daga shi sai Abba suka dinga yin komai. Duk matan sa kuma sun zage anyi komai dasu cikin farin ciki dajin dad'i, suna nan kuma har yanzu a tare mijin su yana sansu iya gwargwado yana bawa kowacce hakkinta.
ALHAMDULILLAH.
Allah na gode maka daka nuna min farkon labarin nan da kuma k'arshensa, Allah kaine abin godiya kuma abin alfahari alhamdulillah. Allah kajik'an marigayi kasa aljanna ce makomarsa da aiyukan alkairinsa. Duk wad'anda suka rigamu gidan gaskiya a cikin musulmai Allah ka yafe musu mu kuma kasa mu cika da kyakkyawan aiki.
Dole na godewa masoya masu kaunar Hajja ce da kuma rubutunta, hakika wannan novel d'in ya sadani da mutane masu d'in bin yawa wad'anda baki baxai iya fad'ar yawansu ba, haka kuma hannu bazai iya k'ididdige yawanku ba sai dai nace Allah yabar soyayya da kauna tsakaninmu yasa sakon ciki ya amfanar daku. Nasan na 6atawa wasu rai toh dan Allah kuyi hakuri, nasan na farantawa wasu rai toh kuma kun faranta min, nasan na nishad'antar da wasu nima kun sani nishad'i kusani reader's kune jigon saka duk wata writer cikin farin ciki haka kuma kune kuke saka writer cikin damuwa domin idan bakwa karantawa bazataji dad'in yin rubutun ba duk kuwa dason yin rubutunta nidai na gode muku masoya na fili dana 6oye na kusa dana nesa bazan iya lissafoku ba domin hakan ya janyo min fitina harma wasu daga cikin wad'anda nake alfahari dasu suka gujeni sabida ban yi musu dedication ba amma still suma idan sun karanta karshen page dinnan suyi hakuri ni 'yar Adam ce me laifuka kala-kala a doran k'asa suyi hakuri but bazan manta dasu ba a cikin zuciya ta ba.
*K'ANWATA STYLISH.*:-Dake aka shirya za'ayi rubutun nan kika gudu kika barni, but ba komai nasan dama ke lazy writer ce (smile) nayi na gama kuma na gode miki da sake zakulo min muhimman abubuwan cikin labarin Allah ya barki da mijinki Lafiya keda k'anwarki Abler.
*MISS XOXO:-* Bazan iya kammala rubutu na ba ban sakoki ba koda kuwa wasu zasuji haushina, kin taka muhimmiyar rawa a cikin rubutuna ta yadda nake hanaki bacci nake hanaki jin dad'i har sai kin bada taki gudun mawar hakan kuma yasa labarin ya tafi cikin tsari da jin dad'in karanta shi, Allah yayi miki albarka ya nuna min lokacin auranki autarees Ina alfahari dake ked'in masoyayyar Hajja ce wanda babu algus.
Ina alfahari da duk me bin labarina grps d'in da nake ciki da wanda bana ciki Ina alfahari daku. 'Yan wattpad ina alfahari daku Ina sanku har cikin kalbina kud'in na daban ne. My co-writer's da suka bi labarin nan ku sani naji dad'i sosai duk da wasu na sansu wasu kuma ban sani ba amma sun karanta Ina fatan duk wacce taga gyara ko kuskure zata yi min domin Ina son hakan Allah ya k'ara baseera da kwarin ido. Olo my one &only Ina alfahari dake ked'in aminiya ce ta kwarai.Tare da aunty na Maijidda musa da yayata barrister Fateen Bch.
*HAJJA CE NOVELS GRP*❤👍😍
*HASKE WRITER'S:-* kungiya ta Ina alfahari daku Allah ya k'ara baseera ya k'ara had'e kawunan mu amin.