*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[61➖62]_*
............Koda su Ashir suka amso kuɗi a kotu ƙiri da muzu suka hana Alhaji Garba, hasalima shi baisan wainar da suke toyawa ba, dan yakoma sashen amaryarsa ya tare, kwata-kwata baya barin rana ta gansa, musamman ma da yanzu yasan yanada laifi a wajen ƴaƴansa akan abinda yayma mahaifiyarsu, toshi babban ma abinda yakeji a ransa gameda ita shine tsananin tsanarta, ko kaɗan baya sha'awar koda tunata ma.
A yau yay nufin kiran Abba ya tuna masa zancen kuɗinsa, amma sai wayar taƙi shiga, hakanne yasakashi maida akalar kiran ga yaransa na kasuwa akan su bincika masa Alhaji Zakari a shagonsa.
Mamaki ya kama Labaran, yace, “Alhaji wane kuma Alhaji Zakari za'a gani a kasuwa bayan shagon nasama yadawo naka?”.
Zaune sosai Alhaji garba ya tashi, dama kwance yake amarya namasa tausa, ”Labaran ban fahimci zancen nakaba ai nima, bani a warware”.
Labaran dai baiyi jayayya ba ya ɗakko labari tundaga tushe ya zayyanema Alhaji Garba, babu shiri kuwa ya rikito a gado, amarya na tambayarsa mike faruwa bai kulataba.
Sashen Hajia Deluwa ya nufa, wadda zuwa yanzu ka ganta dole tabaka matuƙar tausayi, dukta kuma ficewa hayyacinta, ƴan kuɗin da su Ashir suka amso miliyan goma suka bata, sukuma suka rabe sauran harda ƙanwarsu dake karatu. Shagon kuma yazama na yayansu saboda shine ya saya. Amma sai sam kuɗin basu gusar mata da damuwarta ba, itadai tafi buƙatar mijinta a gareta, babban tashin hankalinta na gaba kuma warin da takeyi, wanda hatta ƴaƴanta saisun toshe hanci suke iya zuwa inda take, jiya wata ƴar uwarta tazo gidan, amma sam kasa zama tayi tanata faman toshe hanci, ita kuma ko kaɗan batajin warin saima ƙamshinta na gayu datake zubawa a kullum........
Banko ƙofar da Alhaji garba yayine da ƙarfi yay matuƙar firgitata ta miƙe zumbur tana kallonsa,
“Alhaji lafiya kuwa?”.
Hannunsa toshe da hanci yace, “Ban kuɗina”.
Cikin sanyaya murya tace, “wane kuɗi Alhaji?”.
“O bama ki saniba ko? To wanda ƴaƴanki sukaje suka amsa a kotu”.
Baki ta taɓe cikin ƙarfin hali, “Yanzu dan ƴaƴanka sunci waɗannan ƴan kuɗin daga cikin abinda yake haƙinsu shine zakazo kanamin hayaƙi, idan ka mutu sukeda gadon su ai”.
Galala yay yana kallonta tamkar wani soko, yace, “Aiyyyy dama maganar danakeji a gari gaskiyane? Bakida buri saina mutu kuci gado keda ƴaƴanki, to aiko yau ɗinnan basai gobeba zaki kama gabanki, saidai kisa a biyo dare yau a kasheni, kosu su Ashirun suzo su karni gobe a raba muku gado, bankuma yadda keɗin jahila baceba sai yau wlhy, dama da ALLAH yayma namiji arziƙi to kullum burin mace ya mutu suci gado itada ƴaƴanta, shiyyasa kikaita korar min mata kina musu asiri ko?, to ai dama tuni bokan naki yazo ya sanarminin kafin ya mutu, dan har kasuwa yazo ya sameni ya faɗan duk tsiyatakun da kuka aikata, harda haukata yarinyar Alhaji zakari, wanan ne yasani burin barmasa kuɗin, dama ina masa barazana ya banine domin hakan yazama izinina a garesa ya kiyayi halayyar cin bashi, shine ku ƙwararru kukaje kuka amshi kuɗin, kisani wanan karon bazakuci a banzaba kamar yanda kuka sabaci, insha ALLAHU kuma saikin rigani mutuwa, kije na sakeki saki Uku, kuma a yau nakeson ki barmin gidana”.
Wani gigitaccen ihu hajia deluwa ta kwala ta yanke jiki ta faɗi a wajen babu rai.
Alhaji garba baibi takantaba yay fitowarsa.
A wanan mummunan yanayin autarta data dawo daga makaranta yau cikin ɗokin ganinta ta isketa, bata sanarma kowa zatazoba saboda ta basu mamaki, sai ita ta tarar da abin mamakin.
Itace takira baban yayansu a waya.
Ankai hajia deluwa asibiti a sanƙame, bakuma a samu farfaɗowarta ba sai washe gari, wanda har zuwa lokacin babu alhaji garba babu dalilinsa, ama ranar suka cane dubai yawon amarci shida amaryarsa.
Hajia deluwa dai sai yamma lis ta farfaɗo, saidai kuma tasamu mummunan ciwon ɓarin jiki, ɓarinta na dama baya aiki gaba ɗaya har ido ɗaya, saida ɗaya take gani shima bishi-bishi, baki kuwa ya karkace yana zirar da yawu.
Ƴaƴanta sun shiga tashin hankali matuƙa, sunyi kuka sosai dan suna ƙaunar uwar tasu, sai dai basuda yanda zasuyi.
Haka suka cigaba da jiyyarta, tun sunayin abun da marmari har suka koma biyan likitoci su kula da ita, suko suka koma kan harkokinsu, sai dai suzo su dubata. A kwana a tashi kuma sai dubiyarma ta fara gagararsu zuwa, dan saisu haɗa kwanaki biyu basu leƙata a asibitiba.
Likitoci suma suka fara ƙosawa da ƙazantarta, aiko suka kira su Ashir suzo su kwashi abarsu.
Wannan ne silar dawowarta gidan jiyya, har kuma sanan Alhaji garba bai dawoba, dan sunacan suna hutawarsu da amarya dake fama da ƙaton ciki, haihuwa yau ko gobe.
Tunda aka maido hajia deluwa gida fa babu mai mata kallon arziƙi, dan bilki mai aikima tuni ta gudu abinta, haka hajia deluwa zatayi kashinta da fitdari babu mai gyarawa, ga tsoro da ake bata kullum, taita ganin halittu masu ban tsoro, haka zataita kuka babu damar ihu, wanima lokacin dariya za'aita ɓaɓɓakawa, amma tarasa a inane, kokuma aita kuka, ko kukan dabbobi kala-kala, gaba ɗaya ta susuce, itaba mahaukaciyaba ita ba gawaba. Mai kula da itanma saita gadama take bata abinci tana toshe hanci, data zirara mata take baro sashen.
autarta kuwa ƙiri-ƙiri tabar zaman sashen, takoma sashen babanta, saitayi satima bata kalli sashen hajia deluwaba.
Ruwa a jallo hajia deluwa ke fatan ganin koda ɗaya daga cikinsu Jiddah ne ta nemi gafara, tasan dai bama kowane zai yafe mataba, dan ita kanta batasan iya adadin matan data salwantar ba akan kar'a zauna mata da miji, wasu jini ta sakar musu, wasu warin jaɓa, wasu hauka, wasu kuwa taita ɓarar da cikin da suka samu dan karsu haihu a gidan, watama muguntar data saka bokanta yayi ta manta kalarta, gashi a yau tana girban abinda ta shuka.
ALLAH ka shiryemu, ka tsaremu daga son zuciyoyinmu😔🙏🏻
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Yau dai kam a gida Jiddah ta yini abunta, sosai takema Abba hidima tamkar sauran ƴan uwanta, komai yace yanaso kafinma ya rufe baki an masa, yau kuma ƴan adamawa ma sukazo suka dubashi, amma basu kwanaba suka juya gida, kowa ya gansa saiya tausaya masa, dan sosai yanajin jiki.
Hajia Hindu ce dai da sauƙi sosai, dan harta fara ɗan takawa, ita babban tashin hankalinta yanzu kuɗin dake hannun ƙaninta, kwata-kwata takasa samun Number sa, takuma rasa wazata kira ya haɗata dashi, itama dai ƴan uwanta na zuwa jefi-jefi dubata, dan ba kowaba, acewarsu batada mutunci, mutum ko zuwa gidanta yayi tata masa yatsine-yatsine kenan, ko ta saka ƴaƴanta suyita maka rashin kunya.
★★★
Tun daga ranar duk bayan kwana biyu Jiddah sai tazo gida ta yini, kullum dare kuwa Aliyu sai yazo duba Abba, haka mijin aunty Nafisa ma, mazan su Aunty Hannatu ma duk sunzo, kasancewar ba'a kusa sukeba basa gajiyawa da kiran waya kullum safe da yamma.
Malam ma da tawagarsa yazo har gida ya duba Abba, yadai sha addu'oi kam.
Hakama dangin Umma duk sunzo dubashi.
Haka aka cigaba da jiyyar Abba dake matuƙar shan baƙar wahala karayar ƙugunsa, dan na ƙafar Alhamdllh harma an kwance, dukya rame yayi baƙi. Dolene ya baka tausayi saboda jigatuwa da yakeyi, zuwa yanzun kam yafara laushi.
Dan matar son nasa Hajia hindu ko ruwa wanan bata taɓa damuwa da zaman bashiba balle sannu da jiki, kullum cikin sakar masa habaici take da takalar su Umma fitina, idan anyi abinci sai tace bazasu ciba, yaranma harda kuka wai basu iya ciba, abinda yakuma birkitata kuma shine koro su kalifa da akayi daga makaranta, dan an kasa biya musu kuɗi, ta kafa tijara sai a siyar da motocin Abba biyu data kai yaran makaranta a biya musu su koma, Uncle yahya kuma yace bata isaba, tunda ba haƙinsu bane su kaɗai, kuma motocima ko an sayar jiyyar Abba za'a cigaba dayi da kuɗin, idan zata bari a maidasu ta gwamnati ta bari, dan kalifa ssce zaiyi, su Hussain kuma kwalfayin.
Amma sam saitace ƴaƴanta sunfi ƙarfin makarantar gwamnati, shiko Uncle yahya yace suyita zama babu karatu, dama ba islamiyya suke zuwa ba, danshi yagaji da iskancinta hakanan, tabarsu suji da jiyyar Abba amma taƙi, kullum cikin tadama mutane hankali takeyi a gidan, ga rashin kunyar su kalifa da basa ragama kowa harshi Abban.
Dan jiya da daddare zafi yasa akama Abba shinfiɗa a waje aka fiddoshi yasha iska, to babu wuta, Umma kuma tashiga da fitilar ɗaki zata ɗakko maganin sauro ta kunna, dan yanzu duk su Aunty Sauda sun koma gidajensu, sai dai suna ƙoƙarin kiran waya, sanan duk bayan sati biyu suna zuwa suyi kwana biyu su koma, Zarah kuwa an kirata hira tana gidan Uncle yahya, tare kuma suka fita da Walida tai mata rakkiya. Ihun Abba kawai Umma taji, aiko tafito a guje, kuka sosai da ihu yakeyi yana faɗin Hussain ya kasheshi.
Umma ta riƙe ƙafar daya riƙe yana ihu da tambayarsa miya faru?.
“Yagana Hussain ne ya takani, amma ko juyowa ya kalleni yaronan baiyiba ya fice abinsa”.
“Hussain kuma? To baya ganine kokuwa?....”
“To inda yana gani zai takashine baƙar annamimiya”. ‘Hajia hindu ta faɗa tana fitowa daga ɗakinta’.
Uffan Umma bataceba, saima hawayen tausayin Abba daya cika mata idanu, waya ta ɗauka takira Uncle yahya, babu jimawa yazo. Shikam kasa haƙuri yayi saida ya zane Hussain daya dawo.
Wanan duka kuwa shine yasaka hajia hindu zama taita tata ruwan bala'i a gidan har dare ya raba. Babu kuma wanda ya kulata sai Zarah data yaɓa mata baƙar maganar data kuma tunzurata, Umma kuwa tahau kan Zarah da faɗa tamkar zata daketa.
Anyi haka da kwana biyu Hajia Hindu tai shirin tafiya legas. Babu wanda maganar bata bashi mamakiba, Abba yace, “Maman kalifa legas kuma? Keko mizakiyi a legas dan ALLAH?”.
“kajimun musakin mutuminnan fa da wani zance, ina ruwanka da abunda zanjeyi acan? Kana kwance rigif tamkar wani tsohon ƙarfen Mota talauci yabi ya cinyeka kace zakamin iyayi, to wajen Harisu ƙanina zanje, shiyyace naje na amso kuɗi na maida ƴaƴana makaranta nasayi gida mu koma mubar wanan gayyar ƴaƴa da jikokin”.
“Humm Hindu kenan, yaushe shi Harisun yay hankalin nutsuwa waje ɗayan da har kikasan inda zaki sameshi balle yabaki waɗanan kuɗin da kika lissafo?”.
“Tofa, tanan kuma ka ɓillo, to ta ALLAH ba takaba, kana aibanta min ƙani ne, to saidai kagani akan ƴaƴanka da insha ALLAH saisun haifa maka ƴaƴan tsakar gida”. ‘Ta ƙare maganar tana nuna Walida dake bakin rijiya’.
Murmushi kawai Umma tayi tacigaba da fifita wutar gawayinta dazata ɗora abincin rana, walida ma da zatayi magana saita harareta damata nuni datai shiru.
Abba kam kasa cemata uffan yayi, saima ya maida kallonsa gasu kalifa dake leƙensu ta window suna kwasar dariya, kai kace wani Comedy film suka samu suke kalla. Cikin haɗiye wani Abu daya tsaya masa a makoshi ya ɗauke kansa kawai.
Hajia hindu taja dogon tsaki tabar wajen tana faɗin, “da kayi magana mana”
Daga jikin Window kalifa yace, “Mom aike boss ce, babu ubanda ya isa tanka miki idan kinyi magana. Shida Dady yama zama gurgu inashi ina faɗa damai ƙafa irinki, kema ba cazakiyi suyi cikiba, kin manta baya sonsu, cazakiyi ALLAH yasa a guntule ƙafafunsa”. Ya ƙare maganar da kwashewa da dariya su Hassan na tayashi.
Ba Abba kaɗaiba hatta da Umma saida maganar kalifa ta girgizata, walida kam kaɗan yarage ta afka rijiya saboda tsorata, Jiddah dake ƙoƙarin shigowa kam jakkar hannunta ta saki ƙasa sata hawaye da kallon su kalifa dake dariyarsu har yanzu.
“Lafiya kika tsaya nan?”.
Maganar Aliyu ta dawo da Jiddah hayyacinta, saurin duƙawa tayi ta ɗauki handbag ɗinta tana goge hawaye, taji daɗi da Aliyu baiji rashin tarbiyyar da ƙannen nasu ke zubama mahaifinsu ba.
Cikin murmushi ta ɗago ta kallesa, “Babu komaifa “Kalby, tuntuɓe nayi”.
Cikin raɗa dan kar ajisu saboda suna soro kuma gabda shiga cikin gidan, amma su Umma basa hangosu, itama taga su kalifa ne saboda window ɗin ɗakin da Hindu ke ciki yana saitin ƙofar sorone, “Kifa kula hajjaju ban gama amarciba”.
Gaba tai abinta tana murmushi, amma bata tankaba. Shima saiya biyota yana murmushin.
Ita tafara sallama ta shiga, kafin tace, “Tare suke”.
Tashi Umma tai ta saka hijjab, Walida tazo ta rungumeta tana murnar ganinta, dukda kuwa jiyama Jiddah tazo gidan.
Har Aliyu yayi gaisuwarsa yagama hajia hindu bata fitoba, kuma sarai tana jiyosa, hakama su kalifa Aliyu na shigowa sukabar jikin window ɗin suka koma ciki.
Jiddah bata zaunaba, tare suka koma da Aliyu, dama zasuje gaishe da Aunty Ruƙayyane datai mura, to hanyar gidn ta anguwarsu jiddah ne, shine Aliyu yace su biyo suga Abban, dan zuwa dare da wuya ya samu zuwa sunada majalisin dare na ƙarshen wata da akeyi a masalaccin ƙofar gidan malam.
Umma ta ɗakko magani a leda tanabama Jiddah. “Jiddah gashi idan kunje a jiƙa, maganin zakine Yaruwaiya nasa ta amsoma Maimunatu, jiya da Bunami zaizo yazo dashi, dan yanada ƙyau sosai, saura kuje kuƙi jiƙawa saboda ƴar banzar shiriritarku, kuna komawa gida dan ALLAH ki jiƙa matashi, ALLAH ya raba lafiya, ki gaidamin ita, ki kuma cemata tacigaba dashan farin zoɓonnan shima, gobe idan ALLAH ya kaimu Zarah zata kawo mata wani”.
“To Umma ALLAH ya saka da alkairi, yabama Abba lafiya”.
“Amin ku gaida gida”.
Aliyu dake jiyosu yay murmushi, shiyyasa yake ƙaunar Umma, baiwar ALLAHr tayi, akwai dattako, tunda cikin Maimuna ya tsufa bata gazaba wajen bata maganin zaƙi da duk wanda zai taimaketa ta haihu lafiya, yanda yasan zata iya taimakon ƴarta Jiddah ta cikinta haka takema Maimuna, har zuwa tai ta dubota sau biyu dayake Maimunan ta kwanta a asibiti har sau biyu, tundama cikin ya tsufa tace tabar zuwa duba Abba hakanan sai ALLAH ya sauketa lafiya, sanan duk wasu dabaru na mai ciki Umma faɗama Maimuna takeyi tamkar mahaifiyarta. Hakanne ya saka iyayen Maimuna suma jin daɗi, suka ƙara ɗaukar Jiddah da muhimmanci da janta a jikinsu, koda yaushe suna ƙoƙarin zuwa duba Abba, dan zuminci mai ƙarfi ya ƙullu.
Jiddah na fitowa Aliyu yay yunkurin rungumeta sai Walida ta fito dan musu rakkiya, hakanne ya sakashi matsawa baya yana susar gefen wuyansa da key ɗin mota.
Walida ta gimtse dariyarta dan ta fahimci abinda da za'ayi ganinta yasa aka fasa.
Sai da ta rakasu har mota. Aliyu ya kalleta bayan yama motar key, “Auta wai yaushe zaki dawo mana kwana ne? Daga zuwa sau ɗaya baki sakeba, ko gidanmu babu daɗi? Inama Zarah ban gantaba”.
“Yaya Zarah taje gidan aunty Nafisa ne”. Wlhy malam akwai daɗi sosai, hidimar gidace kawai kemana yawa, ga makaranta kuma, amma insha ALLAH weekend ɗinnan zanzo na sake muku kamar wancan, ALLAH yasama Aunty Maimuna ta haihu ina nan”.
Sheikh Aliyu yace, “Amin auta, ki gaida Zarah idan ta dawo, mu munyi hanyar ƙauyenmu”.
Jiddah ma ta amsa da amin.
Dariya Walida tayi tana ɗaga musu hannu har suka ɓacema gsninta.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Cike yauma massalacin yake da jama'a, tsit kakeji babu wata hayaniya, sai sautin muryar Sheikh Aliyu data karaɗe micrephone ɗin massalacin, bayani yake dalla-dalla bisaga abinda ke rage kuzarin namiji da wanda ke ƙara masa ƙarfi.
“Waɗan nan abubuwan dazan lissafo suna taka rawar gani wajen ragema namiji ƙarfinsa ƙwarai da gaske, ga wasu kaɗan daga ciki, sun haɗa da. Hawan jini, Maleria, Ciwon ƙoda, Ciwon sanyi, Ciwon hanta, Wasa da azzakari da hannu, Shan lemon tsami, Sammu (sihiri), Aljanar dare, Ciwon Sukari, Basir, Rashin samun ishashan Hutu, Yawan Bacin Rai, Yunwa (Qaranci Cin Abinci ). Indai kana tare da waɗan nan matsalolin dolene kazama ka kasa gamsar da iyalinka, na lissafo kaɗanne a ciki dan akwai abubuwa da yawa baya waɗan nan ɗin. Saikuma waɗannan magungunan dana ɗan tsakuro muku, Shi maganin ƙarin kuzarin Namiji, ya bambanta ne daga wani mutumin zuwa wani. Misali maganin da wani yasha yaji daɗinsa, ba lallai ne kai idan kasha yayi maka aiki ba. Amma dai ga wasu abubuwan da zanyi bayaninsu anan, kuma mutane da dama sunce sunyi amfani dasu kuma sunji daɗi”.
*_“1 MAN HABBATUS SAUDA_* : Ka samu shayin Na'a-Na'a wanda aka sanya Na'a-Na'a ɗin sosai. Ka zuba masa Man Habbatus Sauda cokali 1, sannan kasha. Safe da dare kafin kwanciya. Ko kuma ka samu ƙwan Tantabara ko ƙwan Kazar gida guda biyu ko uku, Ka zuba garin habbatus Sauda cokali 1 a ciki. Agauraya a soyashi da Man Habbatus Sauda ko Zaitun, sannan kaci”.
*_“SAIWAR GINSENG_*: Wani itace ne ingantacce wanda ake kawoshi daga ƙasar China. Idan Namiji ya yawaita amfani dashi zai samu ƙarin Kuzari da girma”.
*_“KANKANA_* : Kankana tana kunshe da irin sinadarin dake cikin ƙwayoyin Viagra. Don haka tana ƙara ƙarfin Namiji sosai, kuma ƴaƴanta suna ƙara ma Namiji girma ba tare da wata illa ga jikinsa ba. Ka samu ƙatuwar Kankana ka yanka bayan Magriba ko Isha'i ka shanyeta gaba daya. Kuma ka riƙa taunewa ƙwallon. In sha ALLAH U zaka ji bambanci mai yawa”.
*_“RUWAN CITTA_*: Ka samu Madarar Peak ko Luna, ka tsiyaya ruwan chitta ko kuma garinta daidai misali. Sannan ka samu garin Kustul Hindi cokali guda ka zuba aciki, sannan ka sanya zuma daidai Misali ka shanye, Minti 30 kafin kwanciya”.
*_“MAN JIRJEER_* : Yawancin Maza masu fama da raunin Mazakuta, Basur ne ke damunsu ko kuma Majinar Kwankwaso (Waist). Shi Man Jirjeer yana ƙone irin wannan Majinar ne, har majinar ƙirji. Don haka yana ƙara ma Namiji ƙarfi. Waɗanda suke zaune a ƙasashen Larabawa kamar Saudia ko Misra zasu iya samun ganyensa cikin sauki. Domin shi suke sanyawa a saman abincinsu kamar yadda muke amfani da Lettuce anan”.
*_6 ZOGALE_* : Ɓawon jikin itacen Zogale idan aka shanyashi aka dakashi, ana hadawa da Madara ko Zuma ana sha. Shima yana Qara kuzarin Namiji sosai”.
“Abin lura anan, yawancin waɗannan Magungunan ba wai daga yin amfani dasu sau daya ko sau biyu zaka ga canji gaba daya ba. Dole sai ka juri amfani dasu yau da kullum kana hadawa da Motsa jiki, kuma ka rage amfani da abincin zamani waɗanda suke kunshe da sinadarai masu ƙarfi. Irin su Lemon kwalba, Biscuits, Chocolate, Alawa, Succarine, Farin Magi, etc. Ka koma amfani da kayan sha irin na gargajiya kamar irin su Kunun aya, Mazarkwaila, ƴaƴan itace irin su gwanda, ayaba, Lemo, Karas etc”.
“Sai kuma za'a iya asamun tafarnuwa cokali biyar 5, Kurtafalu cokali uku 3, Citta cokali biyu 2, Fijil cokali biyar 5, Zuma kwalba daya 1. Sai a haɗasu wuri ɗaya a cakuɗa su da zumar kullum asha cokali biyu a yini kawai insha Allahu za'a samu da cewa da izini ALLAH . ALLAH yasa mu dace”...........✍🏻
Zamu cigaba a page na gaba😄🤝🏻
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke*🤝🏽🤝🏽🤝🏽
*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[63➖64]_*
..............“kala-kalar abincin dake samar da karfin maza/mata (sperm), da kuma kuzari a jikin ango da amarya”.
*_“HATSI:_* 1 Alkama ko kuma duk wani dangin abinci da ake samarwa daga gareta. 2 Shinkafa. 3 Wake. *GANYE*: 1 Albasa, Galik, Karas, Dankali, Kwakwa. *ƳAƳAN ITATUWA*: Ayaba, Mangoro, Tuffa, Abarba, Kankana, Lemo, Goba, Yazawa. *DABBOBI*: Tsuntsayen da suka halatta aci, Ƴan shila, Naman kifi, Agwagwa, Naman shanu, Hanta. *ABINDA DABBOBI SUKE SAMARWA*: Madara, Yogot, Ruwan zuma, Kwai, Bota”.
“HaƘiƘa su waɗannan dangogin abincin na kara ruwan maniyyi a jikin ɗan Adam, kuma suna motsar da sha'awar jima'i tare da samar da kuzari ga uwargida ko amarya ko shi kanshi angon. An samo daga sayyidina ALI KARAMALLAHU WAJAHAHU WA RIDIYALLAHU ANHU yace: wani mutum ya gayawa MANZON ALLAH S.A.W cewa bashi da ƴaƴa saboda rashin abinci mai sanya kuzari, sai MANZON ALLAH S.A.W ya umarce shi daya rika cin ƙwai”.
“Shawara ta farko kada ka taba yaudarar kanka da cewa dole sai kaga ( gaban ka ko azzakarin ka ). yayi girma cikin Gaggawa. kamar yadda Baka Iya komawa young boy haka azzakarin ka, Duk yadda ALLAH yayi halittar Sa, ka hakura da yadda ka samu kanka. Girman azzakari ba shine matsalarba, ka fahimci ya zaka Iya gamsar da Matar ka. Akwai hanyoyi da yawa ta yadda zaka gamsar da Matar ka. Akwai Matar da kalaman soyayyar ka kawai ya gamsar da ita. Akwai Wanda kiss kawai ya gamsar da ita. Akwai Wanda sai kayi da gaske sanna zaka gamsar da ita. Bari mu dauki matsala ta Biyu da kuma ta uku mu tattauna”.
“(Wato kiss & jima'i ) Kiss yana da matukar muhimmanci a rayuwar ma'aurata, Idan Baka taba kiss ba yana da kyau ka dauki 40minutes kana kiss da Matar ka. Amsar tana nan zaka bani. Jima'i yana bukatar wasa sosai ta yadda zaka Saki jikin ka kayi Mata wasa sosai, kada ka saka girman Kai zaka samu matsala. ka tambaya Matar ka, dan ALLAH Inaso Ki gayamin gaskiya menene Idan Na taba miki kikejin Daɗi. Idan kuma bata Baka amsa ba ka rubuta Mata a takarda 📝 ta Baka amsa”.
“Akwai Wanda abinda takeso farko ka fara taba Mata (N+Ɗ) (kuyi haƙuri abinda zai amfanemu ake taɓowa, amma wlhy duk kunyarku ta lulluɓeni🙈), Akwai kuma Wanda kalaman soyayya zaka dinga Mata kawai su gamsar da ita fiye da zatonka. Duk waɗannan matsalalolin Ku da kanku ya kamata Ku zauna domin gyarawa. gaskiyar magana kusan 80% Na mutuwar aure a yanzu jima'i shine matsala. Duk mace Mai lafiya sosai, ta rasa jidaɗin jima'i gaskiya duk soyayyar ta ga namiji zata Iya rabuwa dashi. ka daina shan kowanne magungunan Saboda girman azzakari”.
*“MAN ZAITUN- ORIGINAL*: Idan zaka kwanta ka Shafa ko ba sex zakayi ba sannan kasha cokali🥄 2. Yana taimakawa wurin karfin gaba. *MAN KWAKWA* yana taimakawa sosai ka dinga sha cokali daya ko cikin abinci ne. Waɗannan abubuwan Suna taimakawa sosai ka gwada”.
“Abinda muka faɗa dai-dai ALLAH ka bamu ladansa, wanda mukayi kuskure ALLAH ka yafe mana, ALLAH ya sakama malaman mu da alkairi damu gaba ɗaya.
سُبْحَانَكَ اَللَّهُمَّ وَبِحَمْدِكَ، أَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ أَسْتَغْفِرُكَ وَأَتُوبُ إِلَيْكَ.
*Subhanakal-lahumma wabihamdik, ashhadu an la ilaha illa ant, astaghfiruka wa-atoobu ilayk.*
_Tsarki ya tabbata a gare Ka, ya Allah, da yabo gare Ka. Ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Kai, ina neman gafararka, kuma ina tuba izuwa gare Ka._
*(Wanan Addu'ar Tashi daga Majalisi ce, (Domin Neman Yafewa Ga Abin Da Ya Gudana A Cikin Majalisin. A'isha, ALLAH ya yarda da ita, ta ce: MANZON ALLAH, tsira da amincin ALLAH su tabbata a gare shi, bai taba zama a wani majalisi ba, ko ya karanta Alkur'ani, ko ya yi wata sallah face ya cika da wadannan kalmomi. (Sai A'isha ta ce: Ya MANZON ALLAH! Na lura cewa ba ka taba zama a wani majalisi ba, ko ka yi karatun Alkur'ani, ko kayi sallah face ka fadi wannan kalmomi. Sai ya ce; "Kwarai. Duk wanda ya fadi wani alheri sai waɗannan kalmomi su zama kamar hatimi ne ga alherin da ya aikata, wanda kuma ya faɗi sharri, sai su zama kaffara ne gare shi)*.
Tuni Sheikh Aliyu ya sulale yabar massalacin, yabar mutane da tattauna wanan lecture ta yau, koda yaje yima malam sallama ma sai wani sunkuy da kai yake tamkar yana gaban surukinsa, shi malam ma dariya ya bashi, amma saiya danne baiyiba, yasan dai wannan lecture ɗince ta yau takawo wanan sinne kan, haka Aliyu yake da tsananin kunya, ALLAH ya bashi sani kuma bai gazaba wajen bayyanama mutane, sai dai ko faɗar yake zaka sameshi mai tsananin jin kunya a garesu. Shiyyasa inhar malam yasan Aliyu zaiyi wa'azi a wajen da zasu kasance inuwa ɗaya to bayama kallon inda yake, dan kuma sakashi a wata kunyar zaiyi, yauma fitowa yay daga massalacin tunda Aliyu yafara bayanin magungunan can, daga soro ya zauna yana saurarenshi yana murmushi.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Kasan cewar cikin Maimunatu ya tsufa sosai sai dukkan kulawar Aliyu da jiddah suka koma kanta, yanzu haka kowanne dare a sashenta yake kwana bisa amincewar Jiddahn, dan koda ranar girkintane idan yazo wajenta zai kusan raba dare, idanma yana da bukatarsa daya samu nutsuwa zai tsaftace jikinsa yakoma wajen Maimuna ya karasa kwanan. Bawai dan Jiddah batajin damuwar hakan bane ta hakura, a'a a ganinta wannan adalcine, dukda har yanzu bata san raɗaɗaɗin koda laulayin cikiba Maimuna na bata matuƙar tausayi, tanada tabbacin da ace itace a wanan yanayin babu abinda zai hana Maimuna sadaukar mata da Aliyu harta haihu, dan ayanzu hakanma ranar girkin Maimunan idan yakasance ranar batajin daɗi sosai, kuma bazata iya karɓarsa ba, Aliyu kuma yanada buƙata takan amince masa yaje ga jiddah ya samu nutsuwa, haka itama idan Jiddah na al'adah Aliyu yanada bukata kuma lafiyar Maimuna ƙalau takan yarje masa yaje ga Maimuna ya damu nutsuwa, wannan adalcin nasune ke ƙara dasa masa ƙaunarsu mai yawa a cikin ransa, shiyyasa kullum burinsa ya faranta musu da soyayyarsa da kuma abinda ALLAH ya hore masa, sanan ya tsare musu mutuncinsu bisaga haƙƙoƙin da ALLAH ya ɗaura masa.
Randa kuma ALLAH ya kawo saɓani a tsakaninsu sukan zauna su fahimci juna wajen warware abin, dan kowa dai yasan zama na yau da kulkum sai ALLAH, tsakanin harshe da haƙorima ana saɓawa balle zaman kishi kona mata da miji. Amma idan aka sanyama zuciya salama sai kiga komai yazo da sauƙi, to hakane ga zaman su Jiddah, Saɓani yakansha gittawa harma Aliyu ya fahimta ya zaunar dasu yamusu nasiha da sauraren tushen lamarin, atake kuma zaibama mai gaskiya haƙƙinsa ya nunama mai laifi kuskurensa, shima kuma yakan samu daɓanin tsakaninsa dasu, wanan kam daduk wadda yasamu sukan yitane a ɗaki su kaɗai batareda ƴar uwar zamanki tajiba kota sani, kuma ko afusaka bazata saninba, saboda kowanne ya iya takunsa daga Aliyun har matan nasa.
Lokacin daya iso gidan saiya iske Jiddah na kuka rungume da Maimuna daketa murƙususu. Hankalinsane sosai ya tashi, bai wani zauna jan jikiba ya ɗakko hijjab ya sakama Jiddah da Maimunan suka fiddata mota, asibitin dake kusa dasu wanda Maimuna keshan kwanci sukaje.
Haihuwace gadan-gadsn dan haka suna zuwa aka shiga da ita ɗakin haihuwa, kasancewar asibitin na kuɗine baya rabo da ma'aikata.
Jiddah sai kuka take, tama kasa tsayuwa waje ɗaya, ganin a rikice take Aliyu ya kamota ya sakata jikinsa ya rungume yana lallashinta.
“Addu'a take buƙata Jiddah, kiyi hakuri kibar kukan, muyi mata fatan ALLAH ya sauketa lafiya kinji”.
Kanta kawai ta iya ɗaga masa, tareda ƙara lafewa a jikinsa tana sauke tagwayen ajiyar zuciya............✍🏻
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻
*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[65➖66]_*
............Hajia hindu dai shirinta tai tsaf domin tafiya, Sai dai kuma ita kaɗai zata tafi bada yaraba, ƴan kuɗin da ake tarama Abba na dubiya tasaka Kalifa yabi duhun dare ya lalubesu tas, shima saida ya ɗiba rabonsa sanan ya kawo mata sauran.
Kafin ta kwanta kamar wasa ta gwada Number ƙaninta harisu kamar yanda ta saba, yaukam saiga waya ta shiga kamar almara, jikinta har rawa yake ta fara faɗin hello-hello tunkan a ɗaga.
Sai da takusa tsinkewa ne aka ɗaga wayar.
Cikin mamaki tace, ”Wanene? Ina kuma mai wayar?”.
Dariya yaron harisu yayi irinta basawa wadda harta tsorata Hindu, saida yayi mai isarsa sanan yace, “Wanan yakwana biyu a barzahu. Halan kece yayarsa da tai mana hanyar samun ƴan canji”.
Zumbur hindu ta miƙe dan bata fahimci maganar tasa ta farkoba, tace, “Eh wlhy nice, tun washe gari nake nemanku a raba kuɗin amma wayar taƙi shiga, dan ALLAH ina harisun yake?”.
Wani wawan tsaki yayi yace, “ke wai halan kanki baya kawo wuta ne, kajimin mumun mata, nace miki yana barzahu, bara na miki gwari-gwari danna kula ƙwaƙwalwar kifi gareki, dama Oga haris baizo amsar kuɗi danya raba dakeba, yazo amsane ya ware abinsa, shiyyasa ya saka miki Number busy yanda kokin kirashi bazaki samuba. Duk wahalar da mukasha wajen amso kuɗin nan muka wanke ƙafafunmu tundaga legas mukai masa rakkiya amma yay nufin cin amarmu, muko bazamu iya ɗaukaba, sati huɗu kenan muka caccake cikinsa da wuƙa muka aikashi gidan kowane shege da shegiya (lahira kenan), yanzu kema na ɗauki wayarkine danki daina wahalar nemansa ma, kisamu gobe kisa ai masa addu'ar uku data bakwai data arba'in, wainar da za'a bamu kirabama almajirai, muna miki gaisuwar ta'aziyyarsa fa, kuma karki damu sai da mukai masa salla kafin mu jefashi ruwa......”
Ƙitt ya yanke wayar.
Ihu kawai hajia hindu ta dage ta fasa, ta kware baki tana rusar kuka da kiran “Wayyo kuɗina, shikenan na mutu, Harisu ka talautani...”
Wanan ihune yay sanadin tashin su Umma a barci, sukazo suka rufu akan hajia hindu ana tambayar miya faru?.
Batareda tasan mi takeba tashiga sakin surutai akan yanda ta ƙulla makirci da haris aka amshe kuɗin Jiddah, harma da dukan da Abba yaci wanda gashinan ya zame masa sanadin doguwar jiyya.
Wannan lamari yayi masifar girgiza su Umma da Abba dake cikin ɗaki kwance yana saurarensu, jiyay hawaye kawai suna gangaro masa, matar daya fifita fiye da kowace ta aiko masa ɓarayi? Wadda yay burin guduwa da ita suci kuɗin tare, dama abinda ta ƙulla masa kenan shiyyasa ta lallaɓashi subari sai da safe su wuce, tini wutar kan Abba ta ɗauke gaba ɗaya, yaji komai yamasa ɗif, bayajin sautin komai, baya ganin komai sai duhu, daga haka bai sake sanin inda kansa yakeba kuma.
************
Washe gari Uncle yahya yasa aka kama hindu, dai bata cancanci cigaba da zama batareda ta fuskanci hukunciba.
Abinda yabata matuƙar tsoro da mamaki shine ko damuwa su kalifa basuyiba, sai Munner ne kawai ke kuka da riƙeta.
Abba kam saida aka kaishi asibiti, dan jininsa yayi ƙololuwar hawa sama.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Alhamdulillah ALLAH ya sauki Maimuna lafiya gabannin asubahi, sai dai tasha matuƙar wahala abin tausayi, ta haifi babynta Namiji mai kama da Sheikh Aliy masha ALLAH, bayan sun shiga sun dubata tana barci suka fito suka barta.
Rige-rigen ɗaukar jariri akai tsakanin Aliyu da Jiddah, ALLAH yabama Jiddah damar karɓa, shiko ya haɗa da Jiddah n da jaririn duk ya rungume, Jiddah ta ɗago tana kallonsa fuskarta ɗauke da murmushi ta furta,
بَارَكَ اللهُ لَكَ فِي الْمَوْهُوبِ لَكَ، وَشَكَرْتَ الْوَاهِبَ، وَبَلَغَ أَشُدَّهُ، وَرُزِقْتَ بِرَّهُ.
*_Barakal lahu laka fil mawhubi laka, wa shakartal wahiba, wa balagha ashuddahu, wa ruzikta birrahu_*.
_ALLAH Ya yi albarka ga abin da aka azurta ka da shi, kuma Ya sa ka godewa wanda ya baka (shi), kuma Ya sa shi ya rayu har zuwa ga matukar karfinsa, kuma a azurta ka da biyayyarsa._
Aliyu yakuma rungumeta yana amsawa da “Ameen ya rabbi Noorunnisa, nagode sosai, ALLAH ya kawomin kema ta tsatsonki”.
Murmushi kawai tayi tana sumbar goshin yaron, yanda takejin ƙaunar mahaifinsa haka shima takejin tasa ƙaunar.
★★★★★
Tunda gari yay haske bayan Aliyu yadawo sallar Asubahi yafara sanarma Malam, daganan sai Aunty Ruƙayya da Aunty Siyama da gidansu Maimuna.
Kafin kacemi labari ya gama zagaye dangi, zuwa tashin hantsi duk masu kusanci dasu sun iso asibitin, lokacin kuma Maimuna ta farka daga barcin datai na hutawa.
Zuwa ƙarfe sha biyu aka sallamesu suka koma gida tareda babynsu abin sha'awa, fuskar Aliyu kawai zaka kalla ka tabbatar yana tareda tsantsar farin ciki. Addu'oi dai yaro ya shashi tuni har yamasa huɗuba da suna Muhammad. Maimuna kam yanda yaketa nuna mata tattali har kunya abun yake bata, duk mintuna kaɗan ya kirata yace ya jikinta da babynsa.
Dukda Jiyyar Abba haka Umma ta fisge tazo tayi barka ita da maman sadiq, hakama su Aunty Nafisa tazo tayi, haka su aunty Hannatu duk sai da suka kira a waya sukaima Maimuna barka da shi kansa Aliyun.
*_Bayan sati ɗaya_*
Ranar da yaro ya cika sati da haihuwa aka raɗa suna a masallaci, da yamma akayi walima.
Su Jiddah ansha hidima, dan kuwa tayi lis da gajiya, tunda akayi haihuwarnan bata samun kanta, koda yaushe cikin hidima take, danma su Aunty Siyama na taimakonta da wasu ayyukan, da dare kuma Sheikh Aliy yay mata tausa har tayi barci yana jera mata sannu da saka albarka.
Washe garin sunan Maimuna ta koma gidan malam wankan jego badan Aliyu yasoba, ko Jiddah saida ta shiga damuwa, harda ƴar kwallanta kuwa.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Bayan sati ɗaya da sunan yaron Maimuna aka shiga kotu da hajia hindu wanda tagama jigata da fita hayyacinta wajen kwalawa .
Zan iya cewa wanan zaman kotu yazama silar tone-tone ne masu tada hankula, dankuwa hajia hindu bata ɓoye komaiba gameda yanda suka ƙulla karɓe ƙuɗin itada ƙaninta, sai dai tace ita batace su dokeshiba.......
Kafin ta rufe baki wata murya a cikin kotun tace, “Ƙaryane, tunda kika iya shirya kasheni shima zaki iya sawa a kasheshi”.
Gaba ɗaya jama'ar kotun juyowa sukayi domin son ganin mai maganar.
Zaune yake cikin ƙananun kaya, fuskarsa lulluɓe da hular rigar sanyi ƙatuwa dake a jikinsa. Babu mai ganin fuskarsa....
Alƙali ya yanke shirun da faɗin kowaye mai maganar ya fito.
Tunda ya taso kowa ya zuba masa ido, kansa a ƙasa babu mai ganin fuskarsa har yanzu, idanun hajia hindu kai kace faɗowa zasuyi ƙasa wajen son ganin wanene shiɗin?, sai zufa ke keto mata a kowanne sashe na jikinta.
Bayan an nuna masa ya tsaya a akwatin kotun Alƙali yace ya buɗe fuskarsa.
Wani murmushi yasaki kafin ya janye hular kansa fuskarsa ta dattijantaka alamun yanada shekaru ta bayyana. Ƙara hajia hindu ta ƙwalla tareda zubewa a sume, da sauri jami'ar tsaro taje ta yayyafa mata ruwa ta farfaɗo.
Hajia hindu sai sambatu take tana faɗin “Wlhy karku aminta dashi fatalwane, na rantse da ALLAH ba mutum bane fatalwane.
Banda murmushi babu abinda mutumin keyi, yayinda dukkan jama'ar kotun suka zuba musu ido sunason jin mike faruwa?.
Tsawatarma hajia hindu Alƙali yayi, dan haka ta nutsu tana maƙyarƙyatar tsoro.
Alƙali ya gyara zamansa yana faɗin, “bawan ALLAH kai ɗin wanene?”.
“Da farko dai ya mai shari'a sunan SHAZALI, ni ɗan asalin garinan ne, anan natashi nai wayo har zuwa samartakata, bayanan ne nabar garin kano dalilin rabani da akai da ita Hindu aka aurar da ita ga wanina, takaicin hakanne ya sakani barin kano, amma sai sonta ya hanani sukuni a inda nake, hakanne yasani yin waiwaye adon tafiya, na dadawo kano rama abinda mahaifinta yaymin, dan iyayenta sunce bazan aureta bane saboda tantirine ni, gashi babu wanda yasan sana'ata, babanta ya haɗata aure da ɗan abokinsa badan tana sonshiba. Da wanan damar nayi amfani wajen jawo ra'ayin hindu muka cigaba da soyayarmu a ɓoye da auren nata, harma takaimu ga fara aikata zina. wataran mijinta yazo ya iskemu awanan halin, shine ya saketa, tareda ƙwace abinda suka haifa, amma sam yaƙi sanarma iyayenta abinda yasa ya saketa, saidai yace kawai zamanne ya ƙare. Wanan shine cikar burina daman, Hindu tacigaba da zaman zawarci a gidansu, yayinda nikuma na maidata tamkar wata matata, ana cikin haka wata hanyar samu tazo mini, banyi baƙin cikin jawo hindu jikinaba na biya mata makka. Tayi mamakin a ina na samu kuɗin, dan nidai tasan ko sana'a banida ita sai kame-kame. Amma koda ta tambayeni saina ɓata rai akan ta rainani, haƙuri ta bani taje ta sanarma iyayeta, Koda wanan magana taje kunnensu sai suka ƙaryata, musamman babanta, amma mamanta sai ta nuna murnarta har tana jifan baban hindu da kalmar yanama ɗiyarta baƙin cikin cigabanta. Wannan magana ta ɓata ransa yace ya zare hannunsa daga kan hindu da harisu ƙaninta dayazama ɗan iskan gaske. Bata wani damuba muka tafi saudia aikin hajji, saida mukaje can nake sanarmata ma'anar zuwanmu saudia, dan satar kuɗin jama'a ƴan aikin hajji zamu rinƙayi, da farko taƙi, amma dana kalamayeta da daɗin baki saita amince muka fara, kafin kacemi mun tara kuɗi masu yawa, duk abinda muka samu wani abokina mazaunin saudia yake amsa yana tura mana ta banki. Dalilin haɗuwarmu da Alhaji Zakari kuwa ɗakinmu ɗaya ni da shi, wataran sai naji Alhaji zakari yana waya da labarin miliyan hamsin dayaci a banki zai faɗaɗa kasuwancinsa, tunda naji wanan batu sai hankalina ya tashi, dan haka nasami hindu da batun na yarda su ƙulla soyayya da Alhaji Zakari dan muci kuɗin, da farko taƙi amincewa saboda tana sona sosai, saida nagama lallaɓata da daɗin baki akan ai muna tare bamu rabuba, kuma zamu cigaba da Mu'amularmu sanan ta amince. tashiga jikin Alhaji Zakari har suka ƙulla soyaya tun'a can, muna kuma dawowa aka ɗaura musu aure dashi, shirinmu shine bayan kamar wata ɗaya mu mallake kuɗin tasa ya saketa. Sai dai tun bayan aureta da Alhaji Zakari muna tare muna cigaba da mu'amularmu, cikin farko data samu nasan nawane tabbas, dankuwa inada hujjata, abin daɗi kuma saita haifi namiji kamar yanda Alhaji Zakari yake buri, wanan ne yakuma sakata ƙin yarda tarabu da Alhaji Zakari, nayi-nayi amma taƙi, sai dai tace mudai cigaba da tarayya, bazanyi takaici kojin kunyar faɗama duniya abinda basu saniba, abinda yasa zan faɗa kuwa danya zama izina ga ƴan baya masu aƙida irinta Alhaji Zakari yaro, dukda ƙyautar da ALLAH yay masa saiya bijire masa, ya manta ALLAH shike bada haihuwa ga wanda yaso, yakuma hana wanda yaso, sanan shike bayarwa daga jinsin dayaso, mutane da yawa zasuyi mamaki idan nace su Kalifa ba ƴaƴan Alhaji Zakari yaro baneba, indan kacire autansu dabansan sunansaba........”
Tuni kotu ta rikice da ƙananun magana, Abba kam yama daskare acikin WheelChair ɗin dayake ciki, hakama Uncle yahya dasu Umma da Jiddah.
Alƙali ya buga gudumarsa alamar ayi shiru.
Tsit kotun tayi aka maida hankali ga Shazali daya cigaba da faɗin,
“Tabbas ƴaƴansa duk nawane, zama a iya gwada jinsu daduk dalilan da zasu tabbatar da hakan, bayan ta haifi ƴan biyu ne na matsa mata akan a kashe alhaji zakari mu kwashe kuɗin, amma sam sai tace bata yardaba, wai ba yanzuba, tabi ta tsarani da zance na yarda da ita. Sai dai danayi bincike saina gane wayo tamin, ni tama saka a kasheni saboda taci kuɗin ita kaɗai. Ban nuna mata na saniba har tayi ƙulla-ƙullarta a motata da nayi shirin yin tafiya a lokacin, daga baya muka canja komai na biya waɗanda tasaka su kasheni suka kaima babanta motar shi ya shiga ya mutu a lokacin. Daga baya bayan sunsha alhinin mutuwar babanta labari yazo mata nima na mutu, sai dai tana shirin samun dukiyar Alhaji Zakari itama ciki ya bayyana a jikinta, shine ta hakura saita haihu. To bayan haihuwar tatane kuma abubuwa sukaita faruwa ta gagara kashe auren ta gagara mallakar dukiyar tasa har wanan abun ya faru na ƙwatar kuɗaɗen Alhaji Zakari aka bama Alhaji Garba da ƴarsa, ta tura ƙaninta yaymusu fashi ya amshi kuɗin dan itama ta samu rabonta karta tashi a tutar babu, shine suka jibgi Alhaji Zakari saboda gardamar dayay musu, dama tace ko kasheshine ya kama ayi itadai kuɗin take buƙata, shikuma ƙaninta dama yajene da nufin amsar kuɗin ya hanata, nikuma na saka aka bishi aka amshe kuɗin shima aka kasheshi, dan nayi alƙawarin bazataci kuɗinba itama. Wanan bayanin danake muku duk ina samunsa ne ga direban gidansu, wanda ni yakema aiki tsawon shekaru ba tareda hindu ta saniba, na zaɓi zuwa na faɗi wanan sirrine domin Alhaji Zakari yasan ƴaƴan daya ƙwallafa rai a matsayin nasa to ɗayane nasa, ita kuma na nuna mata ramin mugunta ƙurarrene, ta gina kuma ta afka, sanan tasan ina nan a raye ban mutuba kamar yanda tayi fata”.
Kotufa takuma ruɗewa da ihu, daga masu ALLAH ya ƙara sai masu faɗin maganin Abba kenan, sai masu tsinema hindu da shazali, Su Jiddah kam kuka suke sosai, dan ita kasama daurewa tayi tafito daga cikin kotun itada Umma.
Da ƙyar Alƙali ya samu kotu ta nutsu, aka tambayi hindu abinda shazali ya faɗa gaskiya?.
Batayi jayayyaba ta amsa da eh hakane tana sharar ƙwala.
Alƙali ya yankema hajia Hindu hukuncin shekaru Ashirin a gidan yari, shikuma Shazali saboda kisa da yayi ɗaurin rai da rai.
Ihu Hajia hindu take tana kururuwa, amma ba'a sauraretaba aka fiddata, shazali ya roki alfarmar abashi ƴaƴansa, dan sukaɗai ke gareshi a duniya sai mahaifiyarsa. Atake kotu tace ta bashi, mahaifiyarsa tazo ta amsa.
Har aka wuce da hajia hindu da takoma tamkar mahaukaciya tanata sambatu su Uncle yahya basu iya motsawaba, saida kowa ya watse suka fahimci Abba a sume yake ma.
Da gaggawa aka ɗaukeshi zuwa asibiti mafi kusa........✍🏻
*_Abba kagani ba aima ALLAH wayo, kuma ba ai masa tilas_*.☹☹☹⛹♀
_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A 2020 INSHA ALLAH._
*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)
👇🏻karku bari ayi babuku
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke*🤝🏽🤝🏽🤝🏽
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*🙏🏻😭
*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[67➖68]_*
............Kuka sosai su Jiddah keyi, tunda suke basu taɓa gamo da makamancin wannan rikitacciyar rayuwarba, bakuma su taɓa kawo faruwarta a zahiriba sai yau, ashe abinda ke faruwa a films da hikayoyin marubuta yana faruwa a zahiri?.
Dafe kai Jiddah tayi saboda wani jiri dake neman kwasarta ƙasa, da sauri ta durƙushe a ƙasa tana toshe baki da hanci saboda wani warin magani daya doki hancinta.
Da hanzari Zarah da Walida sukai kanta suna tambayar lafiya? Hakama Uncle yahya, Umma nadaga tsaye tana kallonsu amma ta kasa koda motsa ƙafarta balle tazo garesu.
Da hannu tai musu nuni da Amai.
Zarah data fahimta tai saurin faɗin, “Yaya Jiddah Amai?”.
Kai ta ɗaga mata tana kuma danne bakinta dan gab yake da zubowa.
Kamata sukai da hanzari sukayo waje, bama su ƙarasa inda ya daceba tafarashi babi ƙaƙƙautawa, sauƙinma sunbar idanun mutane, sosai Jiddah ta galabaita, idonta sai lumshewa sukeyi, ga wani azababben ciwon ƙirji daya taso mata lokaci ɗaya, kafin kace mi tuni tagama fita hayyacinta, daganan bata sake sanin abinda ke faruwaba kuma.
★★★★★★
A hankali ta buɗe idanunta da sukai mata jingim saboda nauyi, ƙamshin turarensa ne yabata amsar shaidar yana kusa da ita, takuma ɗaga idonta da ƙyar takai dubanta gareshi, dishi-dishi take ganinsa.
Sheikh Aliyu da shima idonsa ke a kanta ya sauke ajiyar zuciya tareda kai bakinsa saman goshinta ya sumbata, hannunta dake cikin nashi ya matsa a hankali, kafin cikin sanyinsa ya ce, “Sannu Jiddatulkhair kinji, ALLAH yabaki lafiya”.
Bata iya cemasa komaiba, sai idanunta data maida ta lumshe hawaye na zirarowa ta gefen idonta.
“Ya isa kukan haka Hauwa'u, ki kwantar da hankalinki Abbanma ya farfaɗo, likitoci na Complain jininki ya hau, gashi kuma bake kaɗai baceba”.
Babu shiri takuma buɗe idonta tana kallonsa, kamarya ba ita kaɗai baceba? Kardai maganar dayaketa ambata mata kwanannan ace tazama gaskiya?. bayan tafiyar Maimuna wanka da kwana biyu saitaita fama da ciwon kai da jiki, ko tausar yay mata batajin ya daina, saiya fara cemata anya kuwa wanan ciwon nata bana ƙanin Muhammad ko ƙanwarsa bane? Ko kaɗan bata ɗauki batun da muhimmanci ba, dan itadai bayan ciwon kai babu abinda takeji sai ciwon jiki wanda take dangantawa da wanan hidimar haihuwar dasuka sha. Kwana biyu dayi mata wanan zance ya kasance da ita, tun a daren yaketa maimaita mata lallai tanada ciki, dan takuma canja masa gaba ɗaya. Ita maganarma kunya taita bata, taƙima yarda su haɗa ido balle ta yarda da maganarsa, yau kuma sai gashi yakuma maimaitawa, hakan kuma na nuni da cewar doctor ne ya faɗa musu.........
Hawayen dayake share matane yasata dawowa hayyacinta, ta kama hannunsa ta riƙe tana kallonsa, “Abbu Muhammad ina Umma yanzun?”.
“Sun wuce gida, sabod Abba ya matsa akaishi gida”.
“Dan ALLAH mu bisu to, inason ganin halinda Abbana yake ciki ko zuciyata zata samu nutsuwa”.
“Kinga kiyi haƙuri, dare yayi yanzun kalli agogo ɗaya saura na dare, insha ALLAHU da safe zan kaiki idan kinji ƙwarin jikinki”.
“Ni wlhy na warke”.
“To naji ya isa haka bar kukan Umm Muhammad”.
Murmushi tayi badan ta shiryaba, a duk sanda ya danganta sunanta matsayin Uwa ga ɗansa tanajin wani sanyi a ransa, hakama Maimuna yanzu gaba ɗaya takoma kiranta Umm Muhammad, tana yaba karamcin waɗannan bayin ALLAH a ranta a kullu yaumin, tamusu kutse a zamansu amma sai suka jawo hannayenta suka riƙeta da zuciya ɗaya, itako mizatayi ta biyasu dashi?. Ajiyar zuciya ta sauke saboda abinda taji Aliyu na mata, ta riƙe hannunsa tana tura baki kaɗan.
Murmushi yayi ya janye hannunsa yana tashi zaune, itama ya taimaka mata ta tashi, da mamaki tabi ɗakin da kallo sanan ta kallesa. “Yaushe ma na dawo gida to?”.
“Ai tun bayan farkowarki a asibiti sai likita ya fahimci warin magani da Asibitin yakeyine baƙyaso, dan yunƙurin amai kika fara farkawa dashi, shine yakuma miki allura, a lokacin kuma Zarah ta kirani da wayarki a ɓoye, dan Uncle yahya ya hana a kirani a tadamin hankali”.
Jiddah tayi murmushi tanajin ƙaunar kawun nasu wanda takeji ƙaunarsa tamkar mahaifi.
Da taimakon Aliyu tayi wanka sanan ta rama sallolin dake kanta, da ƙyar yasamu tasha tea ɗin daya haɗa mata, tana gama sha ma ta amayar dashi.
Kallo ɗaya zakai masa ka hango tsantsar tausayinta a gareshi, ya gyara mata jikinta sannan ya kamota suka dawo ɗaki suka kwanta yana saka mata albarka da jera mata sannu.
*WASHE GARI*.
Da ƙyar Aliyu ya yarda ya kaita gwammaja kusan ƙarfe ɗaya na rana, dan kallo ɗaya zakai mata ka fahimci batajin daɗin jikinta, gashi takasa cin abinci, tace, “sai taje gida zataci awara”.
Kana doso hanyar shigowa cikin gidan zaka fara jiyo kukan Abba da sambatun da yakeyi, cikeda sassarfa Jiddah ta ida shigowa, dan Aliyu yana mota saiya jira tamasa iso, mamaki ya kama Jiddah ganin duk ƴan uwanta zagaye da Abba dake riƙe da hannun Umma dana Uncle yahya yana kuka. Yana ganinta ya saki hannayen su Umma ya miƙa mata alamar tazo gareshi, ganin lamarin take tamkar a mafarki, dan haka tai tsaye takasa koda motsi, aunty Zulai da suma suketa sharce hawaye tazo ta kama hannunta ta kaita gaban Abba.
Durƙushewa Jiddah tayi takuma fashewa da kuka mai ban tausayi tana faɗin, “Abbanmu kayi haƙuri, ka ɗauki hakan matsayin ƙaddar da bata goguwa a rayuwar ɗan adam, dama rayuwa tana tafiyane da jarabawa kullu yaumin.......”
Abba ya katseta shima cikin kukan, “Jiddah wannan ba ƙaddara bace kawai, akwai son zuciya irin nawa, na bitilcema ni'ima da rahamar da Ubangiji yay mini ta ƙyautarku, na wulaƙanta mata masu ƙyawawan zuciya akan abinda basuke badawaba, nakasa sauke nauyin da ALLAH ya ɗoramin na tarbiyarku da haƙƙokinku a matsayina na mahaifi, na yofantar da matata da ɗan uwana, na wofantar da karatunku inata bautama ƴaƴan wasu. Kaicona da dukkan masu irin halayyata a duniya, wlhy ƴaƴana inajin matuƙar kunyarku a rayuwata da tsanar kaina........”
“Abba ka daina faɗar haka dan ALLAH, insha ALLAHU mu masu yafe makane, dan duk duniya bamuda kamarka, kuma bamu taɓa takaicin samunka a matsayin uba ba, sai dai abinda nakeson tuna maka Abba nau'in abinda ake samarwa a mahaifa na daga ɗiya mace ko Namiji ƙwan namijine ke badashi, sanan ALLAH ta'ala dai yace shine ya haliccemu baki ɗaya kuma ya sanyamu maza da mata domin musamu natsuwa da juna. Amma kuma seyace mafifici acikinmu shine wanda yafi tsoron ALLAH sannan kuma yace Maza sunada fifikon daraja akan mata saboda sadakin auren da suke biya dakuma ɗawainiyar ciyarda matan dasu mazan sukeyi, wannan kawai shine abunda yasa maza suka samu fifikon daraja akan mata. Amma kuma wannan baya nuna cewa su matan ƙasƙantattune kokuma basuda daraja. A'a akwaima matan da sunfi mazan daraja nesa ba kusaba kai akwai mace guda ɗaya wadda matsayintama yafi na mazanda suke rayuwa a duniya ayanzu dukkansu. Kukaranta ƙissar Maryam mamar Annabi Isa (AS) sadda aka haifeta se mamarta take cewa ai namiji ba kamar mace ba, tanuna bataji daɗiba dan ta haifi mace se nan take ALLAH yace shi yafita sanin abunda ta haifa, sekuwa gashi ya bayyana cewa wannan macen da ta haifa tafi duk mazajenda take tunani. Kaga kenan kasancewa mace ba aibu bane bakuma nakasu bane. Sannan Kaduba Nana Khadija uwar Muminai kuma kaduba Asiya matar Fir'auna kaduba irinsu Sayyidatuna Fatima ga irinsu Aisha dasu Ummu Shuraikh wadda saboda karfin walittakarta daga Aljanna kai tsaye aka miko mata ruwa tasha ta koshi, shin kanada wani namiji a yanzu wanda zakace yafi waɗancan matan daraja? Dan haka babu shakka maza da yawa masu wanan aƙidar suna kan kuskure, amma su sani kasancewa mace ba aibu bane bakuma gajiyawa bane, illa iyaka aduba tsoron ALLAH kawai da takawa, sannan idan kaduba sharhinda malamai sukaiwa hadisinnan na ANNABI (s.a.w) dayace ayiwa mata wasiyya da kyautatawa dakuma hadisin wanda ya raini mata biyu zuwa sama zasu kasance masa garkuwa tsakaninsa da shiga wuta, to waɗannan hadisan sun kore abunda mutanenmu suke faɗa, kuma su tabbatar da cewa mata sunada daraja, kuma suna daga cikin waliyyan ALLAH, sannan kuma ba kaskanci bane kasancewar mace, sannan kuma idan mace taji tsoron ALLAH to zata iya fin maza daraja. Malamai irinsu Zahabi idan kaduba Siyaru A'alamin Nubala yakawo tarjamar manyan malaman hadisi mata kuma shima daga cikin malamanshi akwai mata sunfi hamsin, sannan acikin Mizanul I'itidal yana cewa ba,a samu wata mace ba wadda tayiwa ANNABI (s.a.w) ƙarya, dan haka inkaga mace malamar hadisi to amintacciyace, ba'a tuhumarta da yiwa ANNABI ƙarya. Kai malamai dayawa sun ambaci falalar mata a wajaje daban daban saboda haka zamantowa mace babbar darajace matukar akwai imani da taƙawa, kuma acikin magabata akwai waɗanda har raba dare suke suna roƙon ALLAH akan yabasu ƴaƴa mata yabasu ikon musu tarbiyyah, wani kuma zuwa yake cikin danginshi yaroƙi su bashi ƴaƴansu mata domin ya rainesu, dan yasani cewa macece zaka raineta dandanan kasamu gidan aljanna, dan haka mata sunada falala sosai kuma duk mutuminda har yagama haihuwa be haifi maceba to yakamata ayi masa jaje. Amma koda ace mutum aduniya ƴa mace guda ɗaya tal ya haifa to wannan aimasa barka matuƙar ya iya jure tarbiyyarta. Mata babu shakka a musulinci sunada daraja sosai inhar sukaji tsoron ALLAH, sannan kuma duk wani malaminda kasani ya shahara a duniya to inka bincika zaka samu cewa mata sunyi ƙoƙari sosai a wajen tarbiyyarshi, hatta mamalan da suke karama juna sani daku anan idan da ace andaka ta iyayenmu mazane banda matan to da bamuzo kan wannan matsayinba. Kuje kuji tarihin Shafi'i mana ko Malik ko Abu Hanifa da Ahmad binu Hambal cikinsu wanene mace batai masa tasiba akan iliminsa? Imamul Bukhari albarkacin mace yazama abunda yazama a babin hadisi, hakaman Sibawaihi a fannin nahwu ya gagarane albarkan Mace. Ibnu Taimiya kuwa ai Taimiyar ma macece ba namijiba dan haka mata sunada tasiri sosai da amfani a rayuwa kuma duk wani wanda kaganshi a duniyarnan yana ƙafafa da tunƙaho to arziƙin macece, dan haka mata suma mutanene kuma banda sadaki da ciyarwa babu abunda maza suka daramu dashi. Amma kuma saurin kai mutum aljanna da saurin kaishi wuta to babu kamar mata, abu kaɗan zakaiwa mace ka samu aljanna kuma abu kaɗan zakayiwa mace katafi wuta. Kuma ana iya gane nagartan namijine tayadda akaga yana kulawa da matarsa da ƴaƴansa Abba”.
“Wlhy duk gaskiya kika faɗa Hauwa'u, nima son zuciyane ya lulluɓe ganina da jina, Yagana dolene na gode muku matuƙa keda yahya, ALLAH ne gatana kune gatana, kune kuka tsaya tsayin daki wajen ganin tarbiyyar ƴaƴana da haɗuwar kawunansu a waje ɗaya, ku kun kasance mutanen kirki ababen alfahari da kwaikwayo ga kowanne mutum, duk wanda ALLAH ya bama ƙyaƙyƙyawar zuciya irin taku yagama cin ribar duniya da lahira, dan girman ALLAH ku gafarceni akan kurakuraina kuda ƴaƴana, wlhy nayi nadama nayi nadama matuƙa......”
Daga Umma har Uncle yahya dasu Jiddah kuka suke suna faɗin sun yafe masa, suma ya yafe musu.
“Ba kuyimin laifin komaiba wlhy, koma kunyi mini na yafe muku tuni”.
Wannan rugun tsumi ya mantar da Jiddah Aliyu dake ƙofar gida, wanda shi tunima ya gaji da jiranta yashigo soron da nufin yin sallama, sai yaji kukan jiddah tanama Abba nasiha, hakane yasashi fahimtar akwai matsala kenan, saiya juya dan wannan ba huruminsa baneba ai.
Haka Jiddah ta yini a gida cikin ƴan uwanta batajin daɗi, awararma datasaka Walida ta sayo mata tanaci sai Amai, sosai tabasu tausayi sukaita jera mata sannu, data motsa Abba zaice “Sannu Jiddah kinji, ALLAH ya rabaku lafiya”.
A yau kam duk wanda ka kalla a ƴan gidan su jiddah zaka fahimci suna cikin tsantsar farin ciki, komai suna yinsa cike da walwala, gasu ga Abbansu a inuwa ɗaya suna hira da dariya, abinda bai taɓa faruwaba a tarihin gidan.
Sai dare Aliyu yazo yaga Abba ya ɗauki Jiddah suka tafi, saida ya kaita gidan malam ganin Muhammad da Maimuna sannan suka wuce gida.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Haka rayuwa taci gaba da tsabagen gudu da sauri, Jiddah nata rainon cikinta, ga soyayya da take samu ga mijinta mai tsayawa arai da ruhi, dolene ka gansu suyi matuƙar birgeka sosai. Watan Maimuna biyu a gida tadawo, yaronta yayi ɓul-ɓul dashi tamkar ta bani😁.
Tunda suka dawo ɗawainiyar Muhammad ta koma ga Jiddah, idan ka gansa hannun Maimuna nono zaisha kokuma barcin dare, hakanne yabama Aliyu da Maimoon ɗinsa damar cin soyayyarsu da kewar juna da sukayi.
Abba ma dai jikinsa Alhmdllh, dan zamu iya cewa ya warke sarai, sai dai kuma baya koda iya miƙewa, ko yaushe yana cikin wheelchair zaune, itace ƙafafunsa a yanzu, idan kaje gidansu Jiddah saikaga dukya canja saboda kwanciyar hankali takuma samuwa, sai dai matsalolin yau da kullum da baza'a rasaba. Muneer yana wajen Umma, ta kama ta riƙe tamkar nata, yayinda duk gidan suka ɗauki son duniya suka ɗora masa. A wanan yanayinne kuma aka shiga hidimar bikin zarah da mijinta Nazeer.
Su Jiddah kirjin biki, ga shagali ga ciki daya fito sosai kowa na gani, sai dai tanata kumshe abinta a hijjab kar a gani, dangi abokan wasa kam suka tasata gaba da tsiya, itadai nata murmushi, saisu Aunty Nafisa ne ke rama mata.
Wannan karonma Uncle yahya shine yayma Zarah komai, dan Abba yace basuda uban daya wuce Uncle yahya, shi hotone a garesu, bai isa zuwa rana tsaka ba yace zai wata fiffika akansu.
Ansha biki aka kai amarsu Zarah gidanta tana tiƙar kuka, hakama su Jiddah na tayata a gefe.
Kwanaki biyu da gama bikin Jiddah Mutuwar hajia deluwa ya baje gari, koda Jiddah taji sai da taimata Addu'ar samun rahmar ubangiji, Walida tace, “Tab, sannu yaya Jiddah, wlhy kinada zuciya mai ƙyau, duk abinda tai miki amma kike mata wanan doguwar addu'ar haka?”.
Murmushi kawai Jiddah tayi bata iya cewa komaiba.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Lokacin da cikin Jiddodon Uncle ya cika watanni goma cif ta haifo ɗiyarta mace santaleliya, murna a wajen ya Sheikh da Maimuna ba'a magana, hakama su Umma da sauran dangi, ranar suna yarinya taci suna Maryam, akasha walima da daddare.
Washe gari Jiddah tadawo gida wanka cikeda kewar ɗanta Muhammad da ya Sheikh ɗinta da ƴar uwarta Maimunatu.
Sosai Umma ta tsaya akan kula da jiddah, yanda Abba ke nunama Maryam soyayya har mamaki take basu, ko yaushe yana mamuƙe da ita, ko kukanta yaji yata faɗa kenan wai sakacin Umma da Jiddah ne, su dai su Umma sai dai kawai suyi dariya.
Ahaka Jiddah tagama wanka ta tattara ta koma ga ya Sheikh ɗinta, aka ɗora soyayya daga inda aka tsaya, yayinda dukkan kulawar Maryam takoma wajen Maimuna itama.
Haka rayuwa tacigaba da shurawa cikin amincin ubangiji da rahamarsa, wataran aji daɗi wataran ayi kuka.
*_BAYAN WASU SHEKARU_*
Rayuwa ta shura, gidan Sheikh Aliyu Abdul-ra'uff maina yazama na ƴaƴa da al'umma, yanzu kam shine magajin malam ɗin na gaske, dan ALLAH yayma malam rasuwa shekaru uku kenan da suka wuce, hakanne ya saka girman malma da hidimarsa ga al'umma duk ta dawo kan Aliyu.
A yanzu haka akwai ƴaƴa tara a gidansa, maimuna nada biyar. Muhammad, Ai'sha, Hauwa'u, Umar, Aliyu.
Jiddah nada huɗu, Maryam, Maimunatu, Abubakar, Usman.
Rayuwa mai cike da tarin farin cikice ke gudana a gidan ya Sheikh, ga girmama juna da sanin haƙƙin zaman tare, duk sun zama manyan mata, dan daga Maimuna har Jiddah sunyi ƙiba tamkar ba suba, sun zama iyaye alamun girma duk ya bayyana a garesu. A yanzu haka suke riƙe da islamiyyar mata ta ƙofar gidansu, yayinda suma basu zauna hakaba, suna neman ilimi a wajen mijinsu ga kasuwancinsu na hijjabai da sukeyi da jallabiyoyi daga ƙasar saudia, wanda Aliyu ne yay musu wanan hanyar.
Rayuwar gidan na tafiya dai-dai gwargwadon iko, ba wasu tarin kuɗine dasuba, babukuma talauci na an shiga uku an lalace.
************
Ɓan gaten su Umma ma masha ALLAH, tuni Walida ma tayi aure, yanzu haka dagasu sai Munner daya zama saurayi, yanata karatunsa ɓangaren shari'a, tsufa sosai ya kama Abba da Umma, musaman ma Abba da abin ya haɗa da lalurar rashin tafiya, dan har yanzu a Wheelchair yake yawo. Shida ƴaƴansa kam sai sambarka, dan sune ke riƙe da gidan yanzu, cinsu shansu suturarsu shida Umma da karatun Munner du ƴaƴansa matane keyi, bai nemi komai ya rasaba dai-dai gwargwadon iko.
Shiyyasa lokuta da dama yakan zauna yayta kuka idan ya tuna taɓargazar da yayi na butulcema ALLAH, duk sanda wani acikin ƴaƴansa yazo gidan sai ya maimaita neman gafararsa, hakama Uncle yahya.
Shidai saidai yace masa dan ALLAH abar tuna abinda ya wuce, komai ya wuce ai yanzu.
Shima Uncle yahya yazama dattijo sosai, furfura dukta taso masa, yaransa sun girma sunata ɗawainiya dashi harma da Abba, sanan sunata zuminci dasu Jiddah abin gwanin sha'awa.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Sheikh Aliyu maina kishin giɗe a falonsa yana kallon wani program a Sunnah tv, yayinda Maimuna da Jiddah ke gefensa suna tayasa hira da kallon program ɗin suma, daka gansu zaka fahimci tsantsar soyaya da kwanciyar hankalin dake tattare dasu, zukatansu fayau suke babu nukufurcin kishi mara ma'ana, hakama adalin mijinsu kulawarsa tana akan kowaccensu. A gabansa juk ne na kunin aya da yake dorawa.🙊😹
yarone da bazai wuce shekara 8 ba, ya shigo da kuka hannunsa riƙe da litatafai, yana sanye da Uniform ruwan ganye masu haske.
Harya shigo ya koma da baya danya tuna baiyi sallama ba, daga Sheikh Aliy harsu Jiddah babu wanda yamasa magana, saida yakoma yayo sallama suka amsa aka bashi izinin shiga sanan ya shigo, har yanzu kukan yakeyi.
Kai tsaye wajen Maimuna ya nufa ya faɗa jikinta yana faɗin “Ummina kinga Yaya Umar yasaka yaya Muhammad ya dakeni”.
Maimunatu tace, “Duka fa auta? A lallai yau babu maicin abinci a gidanan tunda aka dakarmin Auta, kai har Abbu bazamu yima maganaba shida Ammi”.
Baki Jiddah ta taɓe tana miƙewa da faɗin “Sai kukam kuƙi ci Ummi, kema kinsan tsokanar Usman da hana bakin mutane zama shiru, aini yayama baimin dai-daiba dabai barka a ƙofar gida ka kwanaba ya kullo mana gidanmu”. Ta ƙare maganar da hararar Usman dake lafe jikin Maimuna.
Murmushi Aliyu yayi shidai, rayuwar matansa na birgeshi, baka isa banbance ƴayan gidan na wanenenba idan har ba'a faɗi makaba......
Sallamar Muhammad daya zama ɗan saurayi dan kusan shekararsa 22 yanzu ta katsesu, daka gansa kaga cikakken Ustazu, ga tsananin kamanninsa da Aliyu sun fito ɓaro-ɓaro. Jiddah ce ta amsa masa sallamar tareda bashi izinin shigowa, tunda ya shigo Maimuna ke dalla masa harara.
Murmushi yayi yana sunkuy da kai, cikin muryarsa mai sanyi da batada maraba data mahaifinsa yace, “Afuwa Ummi, wlhy autanki ne bayaji, ki dinga bashi ruwan al'awa kozai dai-daita, muna karatu amma sai tsokanar ƴaƴan jama'a yake.....”
Jiddah ta katseshi da fiɗin, “I shurunka yarona, itama ai tasan halin abunta, ni sonaima kabarsa can ƙofar gida ya kwana ai”.
“Wai Ammi ashe yau Ummi zata hanani tuwo kenan a gidanan, gara dai mu lallaɓa ko Abbu?”.
Aliyu datun ɗazun yake musu dariya ƙasa-ƙasa yace, “Da gaskiyarka babban yaya, mu lallaɓa dai Ammi, kar Ummi ta turamu bayan ƙofa akan wannan autan nata sarkin shagwaɓa”.
Maimuna tace, “dakun taimaki kanku kam”.
Dariya duk suka ɗanyi, Usman ya sakko daga cinyarta yakoma wajen Aliyu ya zauna jikinsa, “Abbu!”.
Aliyu yace, “Na'am autan Ummi ta samune?”.
“A'a Abbu bata samuba, zance maka dai nama haƙura na daina kukan, shima yaya Umar ɗin na yafe masa”.
Rungumeshi Aliyu yayi tareda sumbayar goshinsa, “Yauwa autan Ummi mai halin manya, ai haka akeso, yanzu kaima kaje ka bama yaya Muhammad hakuri, kace bazaka sake rashinji a ajiba”.
“To Abbu”.
Gaban Muhammad Usman yaje ya durkusa, “Yayanmu kayi haƙuri kaji, kaga ALLAH yana tare da masu hakuri, indai nine zan dinga jin magana insha ALLAH, na daina tsokanar kowa a aji”.
Muhammad ya ajiye littatafan hannunsa ya ɗauki Usman ya ɗaga sama yana nufar kofar fita da faɗin “yawwa Autanmu, ALLAH ya maka albarka kaji”.
“Amin yayanmu” usaman ya faɗa shima suna gab da fita......
Da sauri Aliyu ya dakatar dashi ta hanyar kiran sunan Muhammad, hakanne yasaka Muhammad amsawa ya juyo, “Na'am Abbu”.
“Inasu Maryam suke? Banace kadaina shigowa gidaba sai kaga sun shigo?”.
“Afuwan Abbu, na biyo Usman ne dama amm......”
Sallamar sauran yaran ta hanashi ƙarasawa.
Maryam da Ai'sha kusan kansu ɗaya, sun zama ƴan mata masha ALLAH, sai Hauwa'u (Noor) da Maimoon (Amatallah) suma kansu ɗaya, sai sauran yaran maza Umar, Abubakar, Aliyu, yaran gwanin sha'awa, atare suka durkusa suna gaida iyayensu, dan tasowarsu kenan daga makarantar dare dake a ƙofar gidansu.✍🏻😢
*_ALHAMDULLAHI ALAH KULLI HALIN, GODIYA TA TABBATA GA UBANGIJIN TALIKAI, WANDA SHINE YABANI DAMA DA LOKACIN RUBUTA WANAN ƊAN LITTAFI NAWA, ABINDA NA FAƊA DAI-DAI ALLAH YA BANI LADANSA DAKU BAKI ƊAYA, WANDA NAYI KUSKURE ALLAH KA YAFE MANA DAKU BAKI ƊAYA DA KUKA KASANCE DANI_*
_Babu abinda zance da masoya sai godiya, nagode ƙwarai da gaske da Comments naku, da addu'oinku a gareni da mahaifina😭🙏🏻, wanan kaɗai da kukamin kun biyani ƙwarai da gaske, dan mai ƙaunarkane zai maka addu'a harma ya tuna da mahaifanka a ciki, ALLAH ya haɗamu a aljannarsa baki ɗaya, ina kuma godiya irin trillions ɗinnan musamman
*_MUTUM DA DUNIYARSA GROUPS_*
*_MASARAUTAR BILYN ABDULL_*
*_TASKAR LITTATAFAN HAUSA_*
*_KUNDIN HASKE_*
*_HUGUMA CONVERSATION ROOM_*
*_ZAUREN BIEBEE ISA_*
*_BENEFICAL WRITERS ASSO..._*
*_ZAUREN HASKE WRITERS_*
*_ZAUREN KHADIJA CANDY_*
*_HOME OF NOVELS_*
*_ZAUREN SADEEYER NOVELS_*
*_ALFAHARI NOVELS ONLY_*
*_NI DA AMARYATA FANS_*
*_MANSHAT NOBELS_*
*_ZAFAFA PAID GROUPS_*
*_SAIFUL-ISLAM FANS_*
*_WUTSIYAR RAƘUMI FANS_*
*_KAI MIN HALACCI FANS_*
Kunada yawa matuƙa, ina godiya ga sauran waɗandama ban lissafoba, harma waɗanda ban saniba kuda admins naku gaba ɗata😘😘😘❤❤❤❤💞💞💞💞💞💞🥰🥰🥰🥰💃🏻😁🤝🏻👍🏻
*_Daga ƙarshe muna muku albishir da zuwan zafafa biyar insha ALLAHU a ranar 7 ga watan janaury nan da muka shiga, muna fatan waɗanda basu sayaba zasu garzayo kusa suma ayi dasu, dan har yanzu hajarmu abuɗe take a gareku, shima wannan babban halaccine da zaku nuna mana wanda bazamu taɓa mantawa dashiba, zukatanmu sukuma yarda kuɗin masoyane na gaske😄🙏🏻🙈_*.
_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A 2020 INSHA ALLAH._
*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)
👇🏻karku bari ayi babuku
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*Karki bari ayi babu ke*🤝🏽🤝🏽🤝🏽
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*🙏🏻😭