Wajen awanni biyu da shigar da Kaka, kafin su Abbu su fito, sai dai basu ba ma kowa damar ganin sa ba, sabida a time ɗin sun yi masa alluran barci; yana cikin barci, domin ba sa son ayi hayaniya da zai ja har ya farka daga wannan barcin.
Gaba ɗaya iyalan gidan sun kasa kataɓus a ranan, ko jirgawa sun kasa yi a baƙin ƙofar, sai da su Big Dady suka yi musu magana ne, akan "su tafi gida," sannan ne su Hajiya suka koma gida, yayinda su Ɗahira kuma suka koma bakin aikin su, but jefi-jefi suna kewayo wa ko Kaka ya farka.
Har dare be farka ba, haka ilayan Doctor Al'ameen suka kwana a cikin wani hali a wannan ranan, sai washe gari aka samu ya farka, sai dai sosai suka shiga farin ciki a ranan, sabida Kaka ya samu sauƙi tamkar ba shi ba, babu wanda yayi tunanin zai tashi da lafiya haka, sai ga shi har magana yana iya yi, kuma yana iya yin sallan sa, domin tunda ya tashi ya buƙaci a kai sa yayi alwala, sai da ya gabatar da sallolin da ake bin sa, sannan ya samu yaci abinci daƙyar, aka ba shi magani ya sake komawa barci, sakamakon alluran da aka sake mishi, sabida ana son ya sake samun hutu sosai.
A ranan haka mutane sukai ta zuwa duba sa, gaskiya Kaka na mutane ne, ba ga talakawan ba; ba ga attajiran ba, manyan mutane kama daga ko wani gari duk ana ta zuwa gaishe shi, har mutanen Maiduguri dangin su duk sun zo wasu daga ciki duba sa, su Hajiya Ikram, Hajiya Laila tun a ranan suka shigo Kaduna.
Kwanan sa biyar a asibitin yana samun kulawa daga ƴaƴan sa da jikokin sa, ya samu sauƙi sosai, sai dai sun hana a mayar dashi gida dole sai ya ƙara samun sauƙi
Shi da kansa ya matsa musu dole suka sallame sa ya koma gida, a ranan sun ga mutanen anguwa, suna ta ɓulɓulowa gaishe da Kaka, da waɗanda suka je asibiti, da waɗanda ma basu je ba duk sun biyo sa gida.
Bayan kwana uku da sallamo sa ne, wanda ta kama ranan Lahadi, ya saka aka tattaro masa iyalan gidan
Bayan kowa ya hallara ya soma musu jawabi akan abinda ya sa ya tara su, ba komi bane illa maganar aure
"Fodio da takwara na da ku zan so ma, har yanzu shiru ban ji kun kawo min maganar wacce kuke so ba?" Yayi maganar idanun sa a kan su
Shiru suka yi ko wannen su, don basu yi zaton akan hakan ya tara su ba. Sai da Abba yayi musu magana kafin Baffa ya buɗi baki yace, "Kaka Ni dai har yanzu bamu gama daidaitawa da wacce nake so ba, but I will bring it to you in a short time, Calm down baza ka mutu ba insha Allahu sai ka ga auren mu".
Sosai maganar Baffa ya ba wa waɗansu dariya, sabida yanda yayi maganar cikin barkwanci
Abba kuma daƙuwa yayi masa yace, "ka ga naka Baba na, ba maganar wasa ne ya tara mu anan ba kaji ko?"
Duƙar da kai Baffa yayi yana sosa ƙeya yana murmushi
Haka zalika ma Kaka murmushin yayi yace, "to takwara na Allah ya kawo ta lafiya, sai dai a wannan gaɓar lokaci zan ba ku, sabida ina so nan da wata ɗaya kacal ayi auren ku mu huta, ba wai ku kaɗai ba, ina nufin har ƴan matan, gaba ɗayan ku zaku fid do da miji ayi muku aure".
Sosai maganar Kaka ya razana Ɗahira dake kusa dashi, dasauri ta ɗago kai ta zuba masa manyan idanuwan ta, kamar an tsikare ta kuma tace, "Kaka, do you mean us?"
Kallon ta yayi yana murmushi yace, "Yes, my wife, I hope all of you will be married in just one month, domin tabbas na san ba zan jima ba a duniyar nan, wannan ciwon ya ɗaga min hankali, shiyasa na yanke shawaran gaba ɗayan ku; ku fitar da mazajen aure sai a haɗa dana yayyin ku, zuwa nan da sati ɗaya na ba ku ko wacce sai ta turo wanda zata aura, kun ji ko?"
Gaba ɗaya amsa mishi suka yi, ban da Ɗahira da tunanin ta ma ya bar duniyar
Sai kuma Usman da tun sanda Kaka ya soma zancen, ya ɗaure fuskar sa tamau, ko ɗago kai ya ƙi yayi, bare kuma yasa baki.
Daga haka Kaka ya sallami kowa taron ya tashi
Ai kamar jira Ɗahira take yi tuni ta bar parlour'n, sabida ruɗewa har so tayi ta bangaji Usman da yazo ficewa shima, Allah ya tsare hakan be faru ba ta dawo hayyacin ta
Wani banzan kallo ya watsa mata yayi hanyar Part ɗin su hannayen sa biyu cikin aljihu.
Ɗahira bata bi ta kansa ba, tunda ba ta shi take yi ba, yanzu hankalin ta duk a tashe yake, burin ta kawai ta ƙebe tayi tunani, "shin ita wa take dashi ne da zata kawo a matsayin miji? Wannan tunanin shi ne yayi matuƙar wargaza mata duk wani walwalan ta da nutsuwar ta.
Tana shiga Part ɗin su, ta shige ɗakin su ta yaɗa zango a kan gadon ta, buga tagumi kawai tayi ta hau tunanin mafita, bata ankara ba sai ga hawaye
"Innallillahi wa'inna ilaihi raji'un! What is going to happen to me? By the time I get married no one has ever said he loves me, so who will I choose as my husband?" Tayi maganar a cikin zuciya tana me share hawayen da bayan hannun ta
Sai kuma ta saka hannu ta ɗauki wayan ta ta hau lalubo Numban Masoyin ta na ɓoye, wanda tayi serving Numban sa da My LOVE. Shiru tayi tana tunanin me zata yi, sai kuma ta soma kiran Numban, sai dai a kashe yake, wani yawu me ɗaci ta haɗiye cike da baƙin cikin da taji ya tokare mata maƙoshi, bata taɓa jin haushi irin na yau ba a duk sanda tayi yunƙurin kiran sa, amma wayan a kashe. wannan maganar me muhimmanci ne shiyasa ba ta so suyi sa a text message, tafi son ta Kira sa suna jin muryan juna, sannan ta faɗa masa abinda take so ta sanar masa.
Sai dai babu yanda ta iya haka ta tura masa text message kamar haka:
_"Now everything is over between us. If you really want me, then I need you to explain yourself to me at this time. I don't want you to talk to me again unless you do what I need you to do."_
Abinda ta rubuta kenan ta tura masa, sai ta kwanta tana lumshe idanun ta, tare da zaman jiran reply ɗin sa.
Bata fi mintuna goma da tura saƙon ba, sai ga reply ɗin sa ya shigo
Da sauri ta tashi zaune ta janyo wayan tana duba wa, sosai tayi farin ciki da amsar da ya bata, murmushi kawai take saki tana karanta wa
_"I am also waiting for this day to be beautiful, insha Allahu zuwa gobe zan bayyana miki kaina, just choose me when I come to you."_
Take tayi mishi sending ɗin time ɗin da zai zo, ƙarfe 03:00pm. Tana tura masa ta kwanta tana zuba murmushi, tunanin kawai yanda haɗuwar na su zai kaya take yi, take ta lumshe idanuwan ta tana sake dulmiya a kogin tunanin masoyin nata.
⚫⚫⚫⚫⚫
Baffa dake tsaye kan benen Part ɗin su, yana tura mata text ɗin ya saki murmushi me fid da haƙora, ya sani dole ne wannan ranan zata zo, amma yanzu ya rigada ya gama shirya mata, ya shirya yanda zai fito fili ya bayyana ƙaunar sa ga masoyiyar sa, domin samun mallakan ta a matsayin matar sa, wanda ya daɗe yana tsimayen zuwan ranan
Wani kyakykyawar murmushi ya sake saki cike da farin ciki a ransa, shafa suman kansa yayi kafin ya soma taka wa ya wuce Part ɗin su, shiga yayi da sallama a bakin sa
Hajja Fatu dake zaune tana jiran dama shigowar sa ne, shiyasa ta zauna a parlour'n zaman jiran sa. Amsa mishi sallaman tayi tana murmusawa tace, "yauwa Baffa na, taho ka bani labarin surukar ta wa".
Dariya ya saki yana isowa wajen ya zauna tare da faɗin, "kai Hajja wai dama jira na kike yi?"
"Iyi wlh, ai tunda kafaɗa na kasa zaune na kasa tsaye ina so inji wacce me sa'ar ce ta same ka?"
"Uhmmm Hajja kenan! Ko dai Ni ne me Sa'ar dana same ta, ke kanki Hajja sai kin yaba da zaɓi na, because you will never have a Daughter-in-law like her, I know you will be very happy if you know who she is".
Cike da farin ciki Hajja tace, "yauwa ɗan albarka, wlh idan ka samo wacce tayi dai-dai da ra'ayina, you must finish everything for me, domin da ita ne zan riƙa ɗagawa a gidan nan, sannan zan fi kowa fariya".
Baffa dai murmushi kaɗai yake zuba wa, yana kallon Mahaifiyar ta shi
"Ina jin ka yarinyan ƴar gidan wane ne?"
"Hajja ba wata bace sai Ɗahira wacce kika sani na gidan nan".
_To fa nan ake yin ta. Ya kuke ganin za'a kaya?_
_Hajja zata amince da zaɓin Baffa?_
_ko kuwa Ɗahira zata amince da Baffa a matsayin Mijin ta?_
_me zai faru?_
_ta Comments ɗin ku kaɗai zan tabbatar da cewa kuna so in ci gaba, idan kuma ba kwa so falillahil hamdu, dama hutu nake son tafiya, sai mun haɗu a next week._
[6/2, 3:32 PM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR'S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL._
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* 🧝🏼
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
```( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
𝗝𝗜𝗞𝗔𝗥 𝗟𝗔𝗪𝗔𝗟𝗜 𝗖𝗘✍️
𝗪𝗮𝘁𝘁𝗽𝗮𝗱: 𝗨𝗺𝗺𝘂𝗗𝗮𝗵𝗶𝗿𝗮𝗵👈
𝗦𝗔𝗗𝗔𝗨𝗞𝗔𝗥𝗪𝗔
𝑁𝑎 𝑠𝑎𝑑𝑎𝑢𝑘𝑎𝑟 𝑔𝑎 𝐹𝑎𝑚𝑖𝑙𝑦 𝑛𝑎 𝑔𝑎𝑏𝑎 ɗ𝑎𝑦𝑎. 𝗚𝗢𝗠𝗔'𝗦 𝗙𝗔𝗠𝗜𝗟𝗬.
*EPISODE Twenty Three*
Zumbur Hajja ta miƙe sabida jin bazatan maganar ɗan nata, cikin tsantsan takaici tace, "kana kuwa cikin hayyacin ka Al'ameen? Ɗahira?.. Ɗahiran ce kake nufin zata zamo suruka ta?"
Shima Baffa miƙe wa yayi a wani irin yanayi, domin dai tabbas ya san akwai matsala tunda yaji Mahaifiyar sa ta kira sa da sunan sa na ainihi, cike da alhini yace, "Hajja to mene ne laifi idan na so Ɗahira? Na ga ai ita ƙanwa ta ce ko?.."
Be rufe baki ba Hajja tace, "kai da Allah ja can mara hankali mara tunani, wanda be san inda yake masa ciwo ba, ka rasa wacce zaka so sai Ɗahira? To ban amince ba, idan har Ni na haife ka, to, babu ta yanda za'a yi ka auri wannan yarinyan".
Sosai hankalin Baffa ya tashi da jin zantukan mahaifiyar na sa, cikin matuƙar damuwa yace da ita, "Hajja wai me Ɗahiran tayi miki ne da kike son jifan ta da baƙin fenti? Mene ne aibun ta shi nake son sani?"
A fusace take kallon sa tace, "aibun ta kake son sani ko? To na tsane ta ne ba na ƙaunar ta, ba na son ta zamo suruka ta, idan ko ka bari hakan ta faru, na rantse da Allah sai na tsine maka albarka".
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!!". Abinda kawai Baffa yake faɗa kenan yana bin ta da kallo
Ita kuwa zama tayi tana huci kamar zakanya, sai kuma ta sake kallon sa tace, "umarni nake ba ka, idan har ka bari wani ma yasan da zancen kana son ta a gidan nan, to har abada bani ba kai, tun wuri kaje ka nemo wata ka aura, ko kuma Ni in zaɓa maka zaɓi na".
Baffa shiru yayi har yanzu idanun sa a kanta, sai dai a wannan lokacin komi ya tsaya masa cak daga duniyar tasa, be san sanda hawaye suka soma sintiri a fuskar sa ba, sai jin ɗumin su yayi saman kuncin sa.
A dai-dai lokacin ne Shakira ta shigo part ɗin, kallon Yayan nata tayi dake hawaye, kafin ta mayar da idanun ta kan Hajja dake faman karkaɗa ƙafafu fuskarta a matuƙar ɗaure, nan da nan hankalin ta ya tashi ta ƙariso da sauri tana tambayan "me ke faruwa?"
Lumshe ido kawai Baffa yayi, sai ya buɗe ya ja ƙafafuwan sa ya nufi hanyar ɗakin sa, yana shiga ya faɗa kan gadon sa ya soma tsiyayar da hawaye, sosai yake kukan zuci, zuciyar sa na tafarfasa, babu abinda ke dawo masa a kwanya sai maganganun Hajja, "shin taya ma hakan zai faru? Taya zai iya cire ƙaunar Ɗahira da ya jima yana dakon sa? Ina sam bazai yiwu ba, idan kuwa hakan ta faru, ya tabbata mutuwa zai yi".
**** **** *****
Hajja duk abinda ke faruwa ta sanar wa Shakira
"Ai dama na sani, ba tun yau ba dole ne akwai soyayya a tsakanin su, I already understand Hajja."
Hajja said, "Then why didn't you tell me in the first place, sai da abu yayi nisa? Yanzu da ace ban tambaye sa ba haka zai je ya faɗa ma mutanen gida ga wacce yake so, kinga kuwa babu ta yanda za'a yi in hana faruwan hakan, na tabbata wlh sai anyi auren nan, tunda dama iyayen ku babu abinda suke ƙauna sama da su ga anyi haɗin zumunci a gidan nan, ina sam wlh ba dai da ɗana ba, dama Yusra ko Fadila yace yana so sai in bar sa, amma ya rasa wacce zai jajibo min sai ƴar A'ishah, maƙiyiya ta" .
Shakira tace, "Nima kai na Hajja na so raba su tun farko, ina wannan ƙawar tawa da muka taɓa zuwa da ita gidan nan Ayush?"
Hajja gyaɗa kanta tayi tace,"yes I understand her, wacce kuke sintiri a asibiti tare lokacin ciwon Kaka".
"Eh ita, wlh she really loves Baffa Hajja, kawai ki haɗa sa da ita tunda shima Yayan ya saba da ita".
Ɓata fuska Hajja tayi tace, "sam ɗana bazai auri ƴar talakawa ba, da ace dai suna da hali ne, amma tunda basu dashi ban amince da ita ba, Ni yanzu na tsara wacce zai aura, idan be samo wata ba, zan haɗa sa da Sa'adatu ne, yanzu ma ɗauko min wayata in Kira Mahaifiyar ta muyi magana, gwara ta dawo nan ko ya ganta ya so ta".
Tashi Shakira tayi don ɗauko mata wayan, duk da a ranta bata ji daɗin haɗin ba, amma ko ba komi Yayan ta bazai auri Ɗahira ba.
Sa'adatu yarinya ce wajen ƙanwar Hajja Fatu, Hajiya Amina wacce tayi aure a Legos. Dama tun farko Sa'adatu ta jima tana ƙaunar Baffa, sai dai shi ya ƙi amince wa da ita sabida bata yi masa ba, wayewar ta yayi yawa, akwai ta da rawan kai.
⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫
*WASHE GARI*
A ranan Ɗahira ta tashi ne cikin walwala da farin ciki, burin ta kawai anjima yayi ta sanya masoyin nata a idanu, koda ta gama shiryawa cikin Abaya baƙa me kwalliyan stones, sai ta yafa gyalen shi ta saka flet shoes, sallama tayi wa Aunty Amarya ta fito ta shiga cikin motan ta
Koda ta isa asibiti Direct office ɗin Baffa ta wuce, sai dai babu shi, domin Office ɗin ma a rufe yake, tayi mamaki sosai amma bata tsawwala ba, sai ta wuce Office ɗin ta.
⚫⚫⚫
Ɗan adai-daita sahu ne ya sauke Ayush a bakin Hospital ɗin, kuɗin sa ta biya sa sannan ta shigo cikin asibitin
A dai-dai lokacin ne Shakira ta shigo itama da motan ta, parking tayi ta fito tana gyara zaman mayafin ta
Hango ta da Ayush tayi ne yasa ta nufo ta tana washe baki, tana ƙarisowa suka soma gaisawa kafin suka jero suka nufi cikin asibitin, Office ɗin Shakira suka wuce kai tsaye.
Sai da suka zauna kafin Shakira tace, "I called your phone yesterday but it turned off. What happened to her?"
"Wlh kuwa babu caji ne, kuma ban samu na kai an saka min ba sai daga baya, yanzu ma na amshe ta wajen me shago".
"Okay, I want to talk to you. kin san jiya Tsoho me ran ƙarfe ya taso da babban zance?"
Ido Ayush ta tsira mata tana gyara zaman ta tace, "I wonder what happened?"
Sai da ta sauke ajiyan zuciya kafin tace, "uhmmm! Jiya gaba ɗayan mu yace mu fitar da miji, su Ya Baffa kuma su fitar da mata, we will be married in a month". ta ƙare maganar da murmushi
Waro ido Ayush tayi, sai dai bata iya magana ba
Sai Shakira taci gaba da faɗin,
"But do you know what? There is a problem, because Hajja tayi wa Ya Baffa mata".
Still shiru Ayush tayi tana kallon Shakira
"Lafiyan ki ƙalau kuwa Ayush? I'm talking you are silent".
"To ai maganar taki ne tazo min a bazata. Now you mean I will not marry Dr. Baffa?"
Taɓe baki Shakira tayi tana janyo wasu files gaban ta tace, "to ban dai sani ba, amma idan har kin yi ƙoƙari kin saka ya Baffa ya so ki a ɗan ƙanƙanin time ɗin nan, to tabbas zaki iya auren sa, domin Hajja ta ba shi zaɓi, duk wacce ya kawo zata aura masa, sai dai ban da Ɗahira, kin ga kuwa burina ya cika, dama ita ce ba na so".
A ran Ayush tsaki taja tana cewa, "aikin banza ta jiƙa shi tasha mana, Ni yanzu ba tashi nake ba, matsala ta na ga gwani na". A fili kuwa sai tace, "ƙawata yanzu shi kuma Dr. Usman kin san wacce yake so ne?"
Kallon ta Shakira tayi, kamar tana tunani sai kuma tace, "taya zan sani? Ai sai nan da sati ɗaya idan Kaka ya buƙaci ganin mu".
"Haka ne! To bari inje, yanzu ina da aiki da yawa".
"Ok".
Da fitan Ayush ta shige Office ɗin ta, jikin ta na rawa ta soma sintiri a Office ɗin, ko kaɗan ta kasa yin tunanin da zai kai ta ga mafita, duk wata hanya da zata bi domin magana da Usman abun ya faskara, ta jima tana bibiyan sa a facebook amma har yanzu bata samu yayi mata reply ba, kusan kullum sai ta tura masa saƙon soyayya amma a banza
Tsaki ta ja tana zama akan kujeran ta, wayan ta ta sake ɗauka ta shiga facebook ta hau yin masa text, ga dai shi yana online amma bata samu reply ba. Ayush kamar tayi kuka ta ajiye wayan tana buga tagumi
Jin ƙaran shigowar text, tayi tunanin shi ne tayi saurin ɗaukan wayan, sai dai wata best friend ɗin ta ne tayi mata magana, dogon tsaki taja kafin ta yi mata reply, charting suka soma yi, anan take faɗa mata halin da take ci, kasancewar ita ƙawarta Safra ta tambaye ta "kwana biyu ina ta shige?" Shi ne ta soma bata labari aiki ne ya riƙe ta, har suka gangaro kan matsalan ta
Nan Safra tayi mata alƙawarin taimaka mata, ta yanda zata samu Usman a hannu, nan ta sanar mata nan da kwana biyu zata shigo Kadunan, kasancewar ita tana Zaria ne tana karatu
To a nan ne dai hankalin Ayush ya kwanta, duk da bata san Safra sosai ba, kasancewar a Facebook suka haɗu, amma ta yaba da wayewar ta, tasan zata iya taimakon ta, tunda tafi ta sanin kan duniyar.
⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫
Ƙarfe 01:30pm. Yau Ɗahira ta tashi daga aiki, tana komawa gida ta shiga ɗakin mahaifiyar ta
Aunty Amarya looked at her in surprise and said, "ah a yau kuma da wuri kika dawo?"
Murmushi Ɗahira tayi tace, "yes Mama".
"Are you all right?"
Still Murmushi Ɗahiran tayi tace, "akwai baƙon da zan yi ne anjima Mama, shi ne na dawo tun yanzu".
Aunty Amarya smiled and said, "Masha Allah! May Allah bring him peace".
"Ameen Mama". Ɗahira ta amsa mata, sannan ta fice tayi ɗakin su
Kwanciya tayi don ta huta, zuwa anjima sai ta tashi ta shirya.
Bata fi mintuna goma da kwanciyar ba, Fadil ya shigo ya sanar mata Aunty Amarya na kiran ta
Koda taje kiran, Aunty Amarya kallon ta tayi tace, "in ce dai kin shirya abinda zaki tarbi baƙon naki?"
"A'a Mama".
"To haka ake yi ne? Ki je ki shirya masa wani abun, koda yake ki buɗe Fridge ɗina zaki ga markaɗaɗɗen kayan miya dana saka, anjima zan yi amfani dashi, sai ke kiyi amfani dashi ɗin kiyi masa miya zai fi".
"To Mama". Ɗahira ta amsa mata tana yin wajen Fridge ɗin
Da kallo Aunty Amarya tabi ta dashi har ta fice, sai ta saki murmushi kawai, a ranta tana ma ɗiyarta fatan dacewa da Miji na gari.
Ɗahira da fitar ta kichen ta nufa takai kayan miyan ta ajiye, sannan sai ta koma kan dainning taci abinci, tana gamawa ta koma kichen ta soma haɗa abincin baƙon ta, shinkafa da miya tayi masa, sannan ta haɗa Juice Kala biyu, sai tayi masa farfesun kifi, kasancewar shi suke dashi, dayake Abbu yafi son kifi shiyasa ba sa rabo dashi a koda yaushe, za su iya rasa Nama na kwanaki a gidan amma ban da kifi.
Time ɗin da ta gama komi ƙarfe 02:40pm. Tayi, da sauri-sauri ta zuba a cikin coolars masu kyau, sannan ta wuce ɗaki tayi wanka, tana fitowa ta shirya cikin riga da skert na atamfa me ruwan silver, sai ratsin fari kaɗan-kaɗan, sai tayi make-up tayi ɗaurin ɗankwali me kyau da ya ƙara fito da kyawun ta
Zama tayi gefen gado tana kallon agogon ɗakin, har ƙarfe uku tayi ta wuce ma, wayan ta ta ɗauka tana kallo ko zata ga message ɗin sa, but babu, dole tayi zaman jiran sa.
[6/3, 9:25 AM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR'S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL._
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏼
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
```( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
𝗝𝗜𝗞𝗔𝗥 𝗟𝗔𝗪𝗔𝗟𝗜 𝗖𝗘✍️
𝗪𝗮𝘁𝘁𝗽𝗮𝗱: 𝗨𝗺𝗺𝘂𝗗𝗮𝗵𝗶𝗿𝗮𝗵👈
𝗦𝗔𝗗𝗔𝗨𝗞𝗔𝗥𝗪𝗔
𝑁𝑎 𝑠𝑎𝑑𝑎𝑢𝑘𝑎𝑟 𝑔𝑎 𝐹𝑎𝑚𝑖𝑙𝑦 𝑛𝑎 𝑔𝑎𝑏𝑎 ɗ𝑎𝑦𝑎. 𝗚𝗢𝗠𝗔'𝗦 𝗙𝗔𝗠𝗜𝗟𝗬.
*EPISODE Twenty Four*
Har ƙarfe 04:30pm. Ɗahira tana zaune jiran masoyin ta, amma babu shi, kuma babu text ɗin sa, ta ɗauki wayan ta tana ajiye wa yafi sau a ƙirga, daga ƙarshe ta tura masa message, but babu reply, dole ta haƙura ta tashi tayi sallan Asar, sannan taci gaba da zaman jiran sa, ji kawai take yi tamkar ta ɓarke da kuka, amma haka ta daure, a ranta tana ba shi uzuri; Maybe wani abu ne ya hana sa zuwa
Har aka kira magriba Ɗahira na zaune bakin gadon ta, ta zuba tagumi tana ta tunani. Tashi tayi ta gabatar da sallan tukun ta koma ta zauna.
Aunty Amarya aiko Fadil tayi yazo ya kira ta, koda taje sai Aunty Amarya ta tambaye ta "ko bazai zo bane?"
"I don't know either. Mama, I still keep quiet, and at three o'clock we made it come."
Ajiyan zuciya Aunty Amarya ta saki, tana kallon Ɗiyarta ta da damuwa ya nuna a fuskarta kafin tace, "to kiyi masa uzuri,
maybe there is something stopping him from coming, Allah yasa dai lafiya".
"Ameen". Ɗahira ta amsa tana ficewa
Ɗaki ta koma ta kwanta tana lumshe idanun ta, jin ƙarar shigowar text, da sauri ta tashi zaune tana ɗaukan wayan ta, nan da nan murmushi ya suɓuce mata ganin Masoyin ta ne, buɗe wa tayi jikin ta na rawa ta soma karanta wa
_"Ban san da bakin da zan baki haƙuri ba Ɗahira, tabbas nasan zaki fahimce ni sabida ke me yiwa kowa uzuri ne, kuma na san kina da kirki da sanin Ya kamata. yau na so in bayyana a gaban ki, in nuna miki tsantsan ƙaunar da nake miki, sai dai kuma abu mafi girma ya shigo rayuwar mu, bazan ɓoye miki sirri na ba Ɗahira, na zaɓi faɗa miki ne kar ki ga laifi na, wanda na san zaki fahimce ni kiyi min uzuri. Mahaifiya ta ta haramta min zuwa gare ki, domin ta ce "idan har na aure ki bata yafe min ba," ta rigada ta zaɓa min matar da zan aura, don Allah! Kiyi haƙuri domin ba'a son Raina zan bar ki ba, sai don bin umarnin mahaifiya ta, amma ki sani ina matuƙar ƙaunar ki, har in koma ga mahalicci na bazan taɓa dena son ki ba."_
_A.A.A. Masoyin ki._✍️
Lumshe idanuwan ta tayi, hawayen dake tsiyaya akan kuncin ta tun soma karanta text ɗin; suka ci gaba da kwaranya, wani irin ƙunci ne ya tokare mata maƙogwaro, wanda daƙyar take iya haɗiye yawu
Dauriya dai me dauriya sai da ta gwada yin shi, amma ta gaza, dole ta zube kan gadon ta hau rusa kuka, kuka take yi sosai zuciyarta na mata zafi tamkar zai faso ƙirjin ta
Taya ma zata iya jure wannan halin da take ciki, meyasa zai mata haka? Meyasa zai tafi ya bar ta a lokacin da take buƙatar sa cikin rayuwan ta? Ya tafi ba tare da ta gansa ba, ya tafi ba tare da tasan sunan sa ba, dama ashe ba son ta yake yi ba? Meyasa to ya koya mata ƙaunar sa?...
Fadila ce ta shigo ɗakin, ganin Ɗahira a wannan halin, sai tayi saurin ƙarisowa wajen ta hankalin ta a tashe, ta hau tambayan ta "lafiya?"
Cikin kuka Ɗahira ta bata amsa,
"He is gone ..! Wlh I really love him, ban taɓa son wani ba sai shi, meyasa zai tafi ya bar Ni?.." ta kasa ƙarisa wa illa kukan da taci gaba da yi, hawaye na ambaliya a kyakykyawar fuskar ta
Sosai Fadila ta tausaya mata, riƙo ta tayi tana faɗin, "ki nutsu Ɗahira, tell me what happened, shin wane ne shi wanda ya tafi ya bar ki?"
Ɗago idanun ta da suka kaɗa suka yi jazur tayi ta aza akan Fadila, cikin raunin murya take faɗin, "wanda muka yi alƙawarin aure dashi, ya ce min Mahaifiyar sa ta haramta masa aure na, me zai saka yayi min haka? Me zai sa in ba aure na zai yi ba ya zo ya koya min son sa? Meyasa tun farko ya zo wuri na?" Taƙarishe maganar cikin kuka
Da mamaki take kallon ta, sabida ta san babu wanda ke zuwa wajen ta, tunda take bata taɓa ganin Ɗahira ta kawo baƙonta gidan nan ba, "shin aina shi kuma wannan suke haɗuwa?" Tayi ma kanta tambayar, sai dai babu me bata amsa, dole ta kawar da zantukan daga ranta ta soma rarrashin ta. Ta daɗe tana rarrashin ta, amma Ɗahira ta kasa yin shiru, dole ta haƙura ta bar ta, ta miƙe tabar ɗakin.
Kuka sosai Ɗahira tayi, kukan da ke fitowa daga zuciyar ta. Tunda take bata taɓa yin soyayya ba, koda da rana ɗaya bata taɓa son wani ba, amma kuma ta rigada ta kamu da ƙaunar wannan bawan Allan da bata san ko shi waye ba, bata san sunan sa ba, ko kaɗan baza ta iya juran rasa shi ba, soyayyan gaskiya take mishi, taya lokaci ɗaya zai tafi ya bar ta a lokacin da take matuƙar buƙatar sa? Wannan amsoshin su suke yawo a zuciyar ta, wanda ya ƙara haddasa mata cinkushewar baƙin ciki a ranta
Allah ya gani ita baƙuwa ce a soyyayya, ko kaɗan baza ta iya juran wannan yanayin ba.
Har Fadila ta sake dawowa ɗakin Ɗahira na kwance tana kuka
"Wai don Allah Ɗahira baza ki dena wannan kukan da kike yi ba? Taya kuka zai miki maganin matsalan ki? Ke fa ba ƙaramar yarinya ba ce". Cewar Fadilan tana kallon ta daga bakin gadon ta da ta tsaya
Ɗahira bata ce komi ba, illa miƙe wa da tayi ta shiga Toilet, alwala tayi ta fito ta soma gabatar da sallan isha'i da aka daɗe da yi, har ta idar tana zaune a wajen ta kasa tashi, sai ma haɗa kanta da gwiwowin ta da tayi; tayi shiru tana tsiyayar da hawaye
Fadila dake kwance tana faman latsa waya, ta kalle ta tace, "I forgot I didn't tell you, Aunty Amarya is calling you".
Shiru Ɗahira tayi mata
Ita kuma bata sake bi ta kanta ba, taci gaba da charting ɗin ta ita da K.B, tana yi tana sakin murmushi.
Sai da kusan mintuna goma suka shuɗe sannan Ɗahira ta tashi ta fice, babu kowa a Parlour, kai tsaye ta wuce ɗakin Maman ta. Sai da tayi sallama aka ba ta iznin shiga sannan ta shige
Aunty Amarya na zaune akan sallaya, shi kuma Abbu na gefen gado zaune yana waya, da alamun wayan me muhimmanci ne shiyasa gaba ɗaya attention ɗin sa ya ba wa wanda suke wayan ne
Durƙusa wa gaban Aunty Amarya tayi, cikin dashashshiyar muryan ta na wanda tasha kuka tace mata "ga ta".
"Ya naga kamar kin yi kuka? What's wrong with you?" Aunty Amarya asked her this question keeping an eyes on her
Sake sunkuyar da kanta ƙasa tayi, in a weak voice and said, "nothing".
Shiru Aunty Amarya tayi na ɗan wani lokaci, sai kuma tace, "je ki kici abinci, kar ki kwanta da yunwa kin ji ko?"
Gyaɗa mata kai tayi tana miƙe wa ta fice
Aunty Amarya tabi ta da kallo cike da tausayin ɗiyar ta ta, tabbas ta san akwai ɗinbim damuwa a tattare da ita, kuma ta gane kuka tayi, amma kuma ba ta son ta dame ta da tambaya a wannan lokacin ne har sai ta samu sauƙin damuwar nata..
"Har kin sallami Maman nawa ne?"
Maganar Abbu ya katse mata tunanin ta, sai ta juyo tana kallon sa, ta ce, "eh, na ga ai kana waya ne, kuma bata ci abinci ba shi ne nace ta je taci. Ko in Kira ta ne?".
"No. Let her eat her food."
Koma wa Aunty Amarya tayi ta zauna, don har ta rigada ta yunƙura zata tashi.
⚫⚫⚫
Ɗahira na fita bata ci abincin ba ta koma ɗaki, domin baza ta iya saka komi a bakin ta ba, ko da taci kuwa, baza ta ji daɗin sa ba.
Tana shiga ta haye kan gadon ta ta kwanta, sai dai ta daɗe kafin ta samu barci ya ɗauke ta, gaba ɗaya tunani ya hana ta sukuni, sai daƙyar ta samu tayi barci.
Washe gari da zazzaɓi ta tashi, dole ta sake komawa ta kwanta bayan ta yi sallan asuba, har gari ya waye bata farka daga barcin da ya ɗauke ta ba.
Kowa ya hallara wajen Breakfast amma ban da ita
Aunty Amarya tambayan Fadila tayi "where is she?"
Sai ta faɗa mata, "she was sleeping, she didn't wake up".
Har ta ce "taje ta taso ta sabida kar tayi lattin zuwa wajen aiki"
Amma Abbu ya ce, "su bar ta".
Har suka gama Breakfast ɗin, shi da Fadil suka fice, Umma ta shige ɗakin ta, yayinda Fadila kuma ta koma cikin Parlour ta zauna abun ta tana aikin latsa waya
Aunty Amarya har ta koma ɗaki, sai kuma ta kasa jure wa, don tasan Ɗahira sarai, tunda ta kwanta ba lafiya ba, bare yanda take son Aikin ta, haka kawai yau ranan aiki ba zata ƙi fitowa ba in babu Dalili
Ɗakin ta wuce kanta tsaye don ta duba ta. Tana shiga ta hange ta saman gado ta rufe kanta da blanket, da sauri ta ƙarisa wajen gadon ta saka hannu ta yaye saman kanta, fuskar ta take kallo tana kiran sunan ta
A hankali Ɗahira ta buɗe idanuwan ta da suka yi ja, ta aza su kan Maman ta
"Baki da lafiya ne, me ke damun ki?" Ta jero mata tambayar a yanayin damuwa
Cikin matuƙar sanyin murya da ciwo yake cin ta tace, "zazzaɓi ne ya rufe Ni Mama".
Cike da tausaya wa take mata sannu, kana tace mata, "ta tashi tayi wanka, inyaso sai ta sha magani bayan taci abinci".
Babu yanda ta iya haka ta miƙe, da taimakon Aunty Amarya har ta ƙarisa Toilet
Ita kuma Aunty Amarya ta fice haɗo mata Breakfast don ta kawo mata har nan cikin ɗakin. Bayan ta haɗo mata ta kawo mata ta zauna zaman jiran ta.
Kamar shuɗewar mintuna sha biyar Ɗahira ta fito a Toilet, ɗaure take da towel me tsawo iya ƙasan gwiwan ta, sai ta saka wani da ya rufe mata kanta zuwa kafaɗun ta
Tana fitowa Aunty Amarya tace, "yi maza ki shirya ki zo ki karya ki sha magani, kina likita amma kina wasa da shan magani, wataƙil ma tun jiya da kika yi kukan naki zazzaɓin ya kama ki amma kin zauna baki sha magani ba".
Kallon ta Ɗahira tayi da sauri, sai kuma ta kawar da kanta cike da sanyin jiki ta kariso gaban Sip ɗin kayan su, buɗe wa tayi ta ciro doguwar rigan atamfa. Sai da tagama shirya wa kafin ta iso gaban aunty Amarya dake bakin gadon ta, a ƙasa ta zauna ta tanƙwashe ƙafa ta soma shan tea ɗin da ta haɗa mata, tana yi tana haɗa wa da bread kamar yanda Aunty Amarya ta umarce ta, sai dai tana cin ɗaya biyu taji kamar zata yi amai, ta kalli Aunty Amarya ta marairaice fuska kamar zata yi kuka tace, "zan yi amai bazan iya ci ba".
"To shanye tea ɗin ki sha maganin".
Ajiye bread ɗin tayi da ƙwan, ta sha tea ɗin, har sai da takusa shanye wa kafin ta amshi maganin ta kora da sauran
"Ina jin ki, Why are you crying? What's wrong with you?"
Sunkuyar da kanta Ɗahira tayi don bata san me zata ce mata ba
"Ina magana kin yi shiru, meyasa zaki zauna ki saka damuwa a ranki har kiyi irin wannan kukan da ya haddasa miki ciwo? Bayan kin san halin kanki abu kaɗan ne yake haddasa miki ciwo idan kin saka damuwa?".
Matso hawaye Ɗahira tayi, har yanzu ta kasa yin magana tunda bata san yanda za'a yi ta faɗa ma Mahaifiyar nata matsalan ta ba
"Ko sabida ya ƙi zuwa ne kike kuka?"
Ɗaga mata kai tayi, kafin ta cire kunya ta sanar mata komi
Ajiyan zuciya Aunty Amarya ta sauke, cike da tausayin ɗiyar ta tace, "ki yi haƙuri haka Allah ya so dama ba shi ne wanda zaki aura ba, Allah ya musanya miki da wanda ya fi shi, amma ki dena saka damuwa a ranki kinji? ki fauwala wa Allah komi, ai Kakan ba cewa yayi zai zaɓa muku wani ba idan baku kawo wanda zaku aura ba, don haka ki dena saka maganar auren nan na damun ki".
Gyaɗa mata kai tayi
Sai da ta sake tausan ta kafin ta fice ta bar ta
Sosai maganar Maman ta ya sanya ta jin sanyi a ranta, dama ita yanzu damuwar ta yanda kowa zai kai zaɓin sa, amma ita ban da ita.
A haka ta saki jikin ta a ranan taci gaba da walwalan ta, sai dai bata je aiki ba ta bar wa gobe.
[6/4, 11:07 AM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR'S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL._
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏼
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
```( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
𝗝𝗜𝗞𝗔𝗥 𝗟𝗔𝗪𝗔𝗟𝗜 𝗖𝗘✍️
𝗪𝗮𝘁𝘁𝗽𝗮𝗱: 𝗨𝗺𝗺𝘂𝗗𝗮𝗵𝗶𝗿𝗮𝗵👈
𝗦𝗔𝗗𝗔𝗨𝗞𝗔𝗥𝗪𝗔
𝑁𝑎 𝑠𝑎𝑑𝑎𝑢𝑘𝑎𝑟 𝑔𝑎 𝐹𝑎𝑚𝑖𝑙𝑦 𝑛𝑎 𝑔𝑎𝑏𝑎 ɗ𝑎𝑦𝑎. 𝗚𝗢𝗠𝗔'𝗦 𝗙𝗔𝗠𝗜𝗟𝗬.
*EPISODE Twenty-Five*
Kamar yanda Hajja Fatu tace zata kira Hajiya Amina su yi magana, hakan kuwa tayi, sun gama ƙulle-ƙullen su a waya, kafin suka yi sallama akan zata turo Sa'adatu gobe-goben nan kamar yanda ta buƙata, yanzu ɗin ma don ba ta kusa ne da sun yi waya.
Washe gari zuwa yamma sai ga Sa'adatu ta dira garin Kaduna
Hajja Fatu zuwa tayi har ɗakin Baffa ta tasa shi gaba akan "lallai-lallai sai ya je ya ɗauko Sa'adatu a airport".
Ba da son ransa ba haka ya tashi ya saka riga a saman Singlet ɗin dake jikin sa, ya fito ya wuce ya shiga motar sa ya bar gidan, a cikin mota in banda tsaki da yake saki babu abinda yake yi, kaso mafi rinjaye na zuciyar sa yana ga Ɗahira, ya rasa meyasa zuciyar sa ta kasa nutsuwa da halin da ya saka ta, yana ji a jikin sa tabbas tana wani hali a sanadiyar Text ɗin da ya tura mata, amma ya zai yi? Bazai iya zuwa ya same ta ba, bazai iya jure ganin damuwa a kyakykyawar fuskar ta ba, ya gummaci ƙaurace mata har sanda komi zai dai-daita. Lumshe idanuwan sa yayi yana buɗe wa sai ga hawaye sun zubo masa a kunci, hannu ya saka ya share yana jan numfashi cike da takaicin Mahaifiyar sa, zuciyar sa sosai take mishi ƙunci fiye da tunanin mutum, yana ji a ransa bazai iya jure wa ba, bazai iya auren kowa ba face Ɗahira, dole ya sake yi wa mahaifiyar shi magana, ko zata iya tallafa wa rayuwar sa, Allah ya gani ba ya ƙaunar yarinyan nan da za'a liƙa masa, sannan kuma bazai iya zuwa ya tunkari wata ɗiya mace da sunan so ba, bare har ya iya auren ta, ita dai Ɗahiran da Hajja ba ta so ita zuciyar sa ke so..
Be fasa tunanin sa ba har sanda ya dangana ga airport ɗin, tunda ya faka motan ya hange ta, sabida kasancewar ta doguwar mace, idan har ta tsaya cikin mutane nan da nan ake iya gane ta, ga ta fara kuma tana ƙara wa dana kanti
Ya ɓata lokaci cikin motan kafin yaja numfashi ya buɗe ya fito, yana hangen ta sai faman waige-waige take yi tana duba agogon dake ɗaure a tsintsiyan hannun ta. Lumshe idanu yayi ya sake buɗe wa a kanta, kamar bazai taka ya isa wajen ta ba, sai kuma ya daure cike da baƙin ciki ya nufe ta, fuskar sa babu ko alamun walwala
Sai da ya dangana ga inda take tsaye, sannan ne ta hange sa, ai nan ta saki murmushin da ya bayyana haƙoran ta, wanda da gani kasan tana cikin tsantsan farin ciki, kiran sunan sa tayi tun kafin ya ƙariso
Sai ya kau da kai yana sake ciccin magani, ya tsaya cak a wajen
Ɗaukar jakar ta tayi ta nufo sa tana sake washe baki, tana iso wa wajen sa ta soma gaishe sa cike da fara'a, amma yanda ya amsa mata ne sai walwalan ta ya ragu
"But yaya lafiya dai ko?" Tayi masa tambayar tana kallon sa
Be ce mata komi ba ya juya ya nufi motar sa
Sai ta tsaya kawai tana kallon sa baki sake, duk da ta san ba ya son ta amma ai suna mutunci sosai ba kamar yanda ya nuna mata haka ba, "so what's wrong with him?" Tayi wa kanta tambayar har yanzu tana tsaye a inda take. Sai da taji horn ɗin motan sa kafin ta ankara, taja akwatin ta ta nufi motan, buɗe bayan tayi ta saka akwatin kafin ta shiga gaban motan ya ja suka bar wajen.
A cikin motan ma babu abinda yace mata, duk da kuwa ta sake tambayar sa abinda ke damun sa, amma yayi mata banza, har suka kai gidan ya sauke ta yaja motar sa ya bar gidan
Tsaye tayi a wajen tana bin motar har ya ɓace wa ganin ta, sai kuma jiki a sanyaye taja Trolly ɗin ta tayi cikin gidan, duk wanda ta gani a hanya gaishe sa take yi har ta isa Part ɗin Hajja Fatu
Sosai Hajja Fatu tayi murna da ganin ta, nan tayi ta nan-nan da ita har ta cika mata gaban ta da kayan ciye-ciye
Ruwa kawai ta ɗauka tasha, sannan ta kalli Hajja Fatu tace, "Hajja where is Shakira I didn't hear her movements?".
"Ai kuwa Shakira tana wajen Yusra, amma yanzu zaki ga ta zo tunda ta san an tafi ɗauko ki".
Gyaɗa kai Sa'adatu tayi, kafin ta sake cewa, "Hajja is something happened to Yaya Baffa? na ga tunda muka zo be ce min komi ba ne?"
Murmushin yaƙe Hajja tayi tace, "bar shi nan yanda kika ganshi, shi ya san me ke damun shi".
Langaɓe fuska tayi tace, "eyya Hajja taya zan bar shi bazan damu ba? kinga fa shi ɗin Yayana ne, wlh baki ga tunda muka biyo hanya duk na gama damuwa da halin da na ganshi, ko dai Ni ce ba ya son gani?".
Hajja tace, "Taya Zaki ce haka? Ina ruwan shi dake da zai ce ba ya son ganin ki? Kin San tunda nayi masa maganar bazai auri yarinyan da ya zaɓa bane, shi ne ya dena min magana, ko abinci ma ba ya ci a nan, ya dena walwala gaba ɗaya, Ni kuwa bazan yarda ya aure ta ba bayan ga ki kina son shi, muddin idan be kawo wacce yake so ba, to ke ce matar sa da yardan Allah kamar yanda muka tsara".
Washe baki Sa'adatu tayi, cike da farin ciki tace, "Allah ya amsa bakin ki Hajja ta. Amma to wace ce wacce ya ke so ɗin?".
"Kar ki damu ba sai kin san ta ba, don ba na son ma maganar tariƙa tsawo azo kuma a samu matsala, maganar ta faɗa kunnen wani".
"Haka ne Hajja, amma ai Yakamata ki sanar dani tun wuri, don wlh har na ji tsanar ta a raina, kinga kuwa gwara in santa in San yanda zan yi zama da ita koda watarana na ganta".
Taɓe baki Hajja Fatu tayi tace, "ai kin ma santa tunda ba wata ƴar nesa bace, Ɗahira ce ta nan gidan".
"What ..! But wlh Hajja I hate this girl so much, God forbid that you forbid her, Allah yasa gwara da kika hana, don wlh wannan yarinyan idan ta aure sa babu ke babu ɗanki, domin irin su ne masu raba uwa da ɗan ta, sai dai ki riƙa hangen sa daga nesa".
"Ai nima shi na gani, ya rasa wacce zai aura sai ita, ba ga shi ba muna gani a wajen uwar ta, yanda take juya Al'ameen, Bilkisu kuwa ta zama abun kallo kamar ba ita ce matar sa ta farko ba, sai abinda tace za'a yi, ke wlh in gaya miki duk iyayen nasu maza sun fi ƙaunar ta, idan har wani abu zai fito daga hannun su to ita suke ba ma wa, ko Kaka shima idan zai yi shawara da matan gidan ita yake kira, komi yace A'isha, uhmmm wlh abun yana baƙanta mini Rai, shiyasa na matuƙar tsanar ta sabida gaba ɗaya Kaka ya rage nuna min kula wa kamar baya, burina kawai ta bar gidan nan tunda Innar ku Safiyya bata aure sa ba, to nima bazan samu kwanciyar hankali ba har sai na kora ta ta bar gidan nan. Mu dai bar maganar nan ki ci abinci tukunna".
"Ok Hajja". Sa'adatu tafaɗa tana saka hannu ta buɗe coolarn
Daga nan sauya hiran suka yi, inda Hajja take tambayan ta mutanen gida da basu gaisa ba.
⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫
Gaba ɗaya a kwanaki biyun nan da suka wuce Ɗahira ta sauya, ba komi ya sauya ta ba illa kewar masoyin ta, a kullum ranan duniya zata ɗau wayan ta sau babu adadi don ganin ko zata ga message ɗin sa, sai dai kuma har ranan ta wuce baza ta ga ko me kama da Numban sa ba, ta kasa haƙura har kiran Numban tayi, amma kuma a kashe ne kamar ko yaushe, duk ta rasa nutsuwar ta ta saka wa kanta tunani, kullum bata da aiki sai tunanin sa, idan ta je Office ma zama take yi tayi ta faman tuna sa, har mafarkin sa tana yi wai ga shi sun haɗu, tabbas sosai take son bawan Allan nan da ya guje ta, ta kasa cire sa a ranta ta saba da rashin sa, ga shi ya tafi ya bar ta koda sunan sa ne bata sani ba, illa kawai A.A.A. da ya rubuto mata a ƙarshen text message ɗin da yayi mata na ban kwana, kuma duk iya tunanin ta na ganin ta gano ma'anar A.A.A ɗin ta kasa, haka zata zauna ta saka wannan sunan ta saka wancan sunan don ganin ta ba shi suna, amma ko wanne ta saka sai ta ga be dace ba.
Ga shi tana son tayi magana da Baffa, koda zai ba ta shawara ne, amma kuma ta kasa ganin sa shima, shi kaɗai ne wanda zata iya faɗa masa damuwar ta amma kuma duk idan taje office ɗin sa ba ta ganin sa, dole yau bayan ta shirya zata wuce aiki, sai ta fara wuce wa Part ɗin su ta duba sa, wataƙil akwai abinda ke damun sa ne ba ta ganin sa a Hospital, Tabbas tana ji a jikin ta ba ya zuwa ne, idan da yana zuwa dole zai neme ta.
A time ɗin su Hajja Fatu duk sun tafi aiki, illa Sa'adatu dake zaune ita kaɗai a Part ɗin, tana Parlour ne tana Breakfast tana latsa wayan ta, sai ta jiyo sallaman Ɗahira da ta shigo parlour'n, ɗago kai tayi tana kallon ta, sai ta ɓata fuska tana kau da kanta
Ita kuwa Ɗahira fara'a ta saka a fuskar ta tana cewa, "ah ah yau Sa'ada ce a gidan na mu? Saukar yaushe ba mu da labari?"
Sa'adatu bata ɗago kai ba, sai tsaki da taja tana kai loman abinci
Hakan sai ya sanyayar wa da Ɗahira jiki, bata sake cewa komi ba tayi hanyar ɗakin Baffa
"So, Ma'am, where are you going?"
Juyo wa Ɗahira tayi tana kallon ta, hakan yasa suka haɗa ido
Sai Sa'adatu ta banka mata harara tace, "dama kin bar wahalar da kanki a kan Ya Baffa, domin kuwa shi ɗin nawa ne Ni kaɗai, ba'a yi macen da ta isa ta ƙwace min shi ba, don haka idan ma zaki nemi mijin ki a can wani wajen ki nema, domin dai Baffa nawa ne, nima kuma tashi ce".
Baki sake Ɗahira take bin ta da kallo, a haƙiƙanin gaskiya Sa'adatu ba wai haushi ta ba ta ba, illa dariya da maganar nata ya bata, wanda har sai da ta murmusa, a ganin ta in ba hauka ba, Taya ma zata ce ta zo wajen Baffa ne domin neman soyayyar sa, bacin ta san da cewa shi ɗin yayan ta ne, ko kaɗan bata taɓa kallon Baffa a matsayin wanda zata iya aure ba, ba wai don wani abu ba, a'a, sai dai tana mishi kallon wanda suka fito ciki ɗaya, duk yanda mutane suke fassara su bata taɓa koda kallon abun hakan ba, "to meyasa su suke wannan tunanin?" Ta tambayi kanta idanuwan ta akan Sa'adatu tamkar da ita take yi, sai dai yanda tayi maganar a hankali babu wanda zai iya ji bare ya bata amsa. Ajiyan zuciya ta sauke sannan ta juya taci gaba da tafiya zuwa ɗakin nasa, don a ganin ta ɓata lokaci ne ta zauna tana biye wa Sa'adatu, tasan ciwon kanta, duk da a girme dai baza ta girmi Sa'adatu ba, amma kuma za su yo sa'anni da juna.
Tana zuwa ƙofar ɗakin ta cinma a rufe yake, bata yi ƙoƙarin buɗe wa ba duk da kuwa tana tare da keey ɗin ɗakin shi a cikin nata, tunda tasan shi dai ta zo nema ba wani abun ba, shiyasa ta juya ta wuce tabar Part ɗin baki ɗaya, ko kallon inda Sa'adatu take zaune ma bata yi ba. Motan ta ta hau ta wuce Hospital, tana isa ta fara zuwa Office ɗin Baffa, amma kuma babu shi sai dai Office ɗin a buɗe yake, kai tsaye lefter ta hau ta koma Office ɗin ta, ta soma duba Patients ɗin ta, tunda a time ɗin har sun soma zuwa.
[6/4, 3:02 PM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR'S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL._
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏼
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
```( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
𝗝𝗜𝗞𝗔𝗥 𝗟𝗔𝗪𝗔𝗟𝗜 𝗖𝗘✍️
𝗪𝗮𝘁𝘁𝗽𝗮𝗱: 𝗨𝗺𝗺𝘂𝗗𝗮𝗵𝗶𝗿𝗮𝗵👈
𝗦𝗔𝗗𝗔𝗨𝗞𝗔𝗥𝗪𝗔
𝑁𝑎 𝑠𝑎𝑑𝑎𝑢𝑘𝑎𝑟 𝑔𝑎 𝐹𝑎𝑚𝑖𝑙𝑦 𝑛𝑎 𝑔𝑎𝑏𝑎 ɗ𝑎𝑦𝑎. 𝗚𝗢𝗠𝗔'𝗦 𝗙𝗔𝗠𝗜𝗟𝗬.
*HIKIMAR FARILTA SALLAH*
```An farilta sallah domin a cikin ta akwai godiya ga Mani'imcin sarki jalla Ta'ala, wanda yake shi ne macancancin godiya da yabo, kuma shi ne kaɗai muka keɓe shi da ruku'u da sujada. Ba wani mahaluki da ya dace da wannan. Idan wata masifa ta sami mutum yakan yi maza ya fake da Allah ta yin Sallah, kamar dai yadda Allah yayi umurni a cikin suratul Baƙara, aya ta 45 da cewa:
"Kuma ku nemi taimako da yin haƙuri, da Sallah".
Ganawar da bawa yake yi da Ubangijin sa a cikin Sallah ita ce bauta wadda take ƙarfafa zumunta tsakanin bawan da Ubangijin nasa. Ubangiji kuma yana yi wa bawan baiwar darajar samun kusanta da shi. Hikima ce kammalalliya da aka farilta sallah, don kuwa ta yin Sallah ne ake kankare wa bawa zunubai, muddin dai ya yi sallah yadda ake so.
An ruwaito cewa annabawan da suka wuce, ko wannen su yana da Sallah da yake ibada da ita. Sallolin suna da lokatai biyar; asuba, azahar, la'asar, lokacin faɗuwar rana da na isha'i. Ashe za mu lura cewa Allah ya tara wa Annabi da al'umma tasa sallolin dukan annabawan da suka gabata.
Allah ya sa mu dace.```
*EPISODE Twenty Six*
*SUNDAY*
Gaba ɗaya sun taru a General Parlour kamar yanda al'adan gidan yake, sai da suka gama raha da nishaɗin su, sannan Kaka ya soma magana da cewa, "Kai Fadil ki rawo Fodio tunda ya ƙi zuwa".
"To Kaka". Fadil ya amsa mishi da sauri yana tashi ya fita
Babu jima wa sai ga Fadil ya dawo, ya isar da saƙon zuwan Usman
Kamar mintuna biyar da shigowar sa ne, Usman ya shigo yana ciccin magani, fuskar nan ko alamun fara'a babu, babu wanda yayi masa magana sai Big Dady dake faman hararan sa, sai dai shi ɗin be ma san yana yi ba, tunda be kalli kowa ba, ya samu wuri ya zauna gefen Baffa, sannan ya gaishe su yana latsa wayan sa
Kowa ya amsa, banda Big Dady da hakan ya ƙular da shi, a fusace ya ce, "kai Usman wannan wani irin ɗabi'ar banza ce? Ina ce gaishe mu kake yi amma kanka a waya?"
Sai a lokacin Usman ya ɗago kansa, sai dai be ce komi ba, illa jikin sa da yayi sanyi ya zame hannayen sa daga wayan ya bar sa a saman cinyan sa
Zai sake magana Big Dady, sai Kaka ya tare shi da faɗin, "bar wannan maganar Noor, mu Yi abunda ya tara mu, kasan halin wannan yaron meyasa kake son ɗaukan zafi da shi ne?"
"Baba wlh abun Usman sake gaba yake yi ba baya ba, kamar shi har sai an zauna ana faɗa mishi dai-dai da wanda ba dai-dai ba? Nan ya bar mu muna zaman jiran sa tsawon lokaci, duk sabida shi aka ƙi cewa komi, amma kuma ya zo yana wani sabga daban bayan yasan da cewa magana me muhimmanci ne ya tara mu".
"Well enough to stop talking, ban san ka da wannan halin ba Noor Kar ka soma ka ji ko?" Kaka ya sake faɗa idanun sa kan Big Dady
Gyaɗa kansa yayi, kana yace, "to Baba Allah ya huci zuciyar ka".
Murmushi Kaka yayi, yayinda su Abba da Abbu suka amsa da "Ameen, sai haƙuri ai".
Kaka ya ce, "to ina jin ku, ya muka kwana a maganar yaran nan ne? tunda yau dama na ce zamu sake zama akan maganar".
Abba ne ya ce, "ai Baba duk na tambaye su kuma na ce su turo mun su, kuma sun zo mun yi musu tambayoyi da Yaya (Yana nufin Big Dady) sannan na bincika duk na gano inda yaran suke, har na saka ayi min bincike a kansu. Uwata kuma da Usman har yanzu ba su ce komi ba akan maganar, shi kuma Baffa ɗazu Mahaifiyar tashi take faɗa min Sa'adatu ta wurin ƙanwar ta Hajiya Amina yake so".
Kaka yace, "to Masha Allah Baba na". Sai ya mayar da kallon sa ga Ɗahira da ke gefen sa ya ce, "Matata har yanzu abokin takaran nawa be shirya bane da baki gabatar da shi wajen Iyayen naki ba?"
Shiru Ɗahira tayi kanta a ƙasa
Sai da Big Dady yace, "Daughter you're talking, are you okay? No problem?"
Bata ɗago kai ba tace, "Daddy, I don't have anyone to introduce me to."
"Baki da wanda zaki gabatar kuma?" Cewar Big Dady da Abba da suka haɗa maganar a tare
Sai kuma Big Dady ya ƙara da faɗin, "ko dai kin tsaya ruwan ido my Daughter? Amma maganar babu wanda zaki gabatar ai be taso ba".
Jikin ta a sanyaye tace ,"Daddy wlh da gaske nake yi, wanda muke soyyayya da shi ya ce "ya fasa aure na, sabida Mahaifiyar sa ta zaɓa mishi wacce zai aura".
Daga Aunty Amarya har Abbu da su Big Dady sai da jikin su yayi sanyi, haka zalika Kaka da yayi zugum yana kallon ta ya kasa furta komi
"Yanzu Uwata babu kuma wanda zaki iya gabatar wa ne?" Cewar Abba da yayi maganar a sanyaye
Gyaɗa kanta tayi, don haka kawai taji hawaye ya cika mata ido, a ganin ta abun da kunya a tara su a gaban jama'an gidan ace ta kawo zaɓin ta, amma kuma bata da shi, babu wanda zata iya nuna wa a matsayin gwanin ta, kamar ta ƙatuwar budurwa da ita, a ƙalla yanzu kaɗan ya rage ta cika 26 cif-cif...
Muryan Kaka ya katse mata tunanin ta, sai ta saka hannu tana share hawayen da ya zubo mata tana ci gaba da sauraron shi
Tambayan Usman yayi kamar yanda yayi mata
Usman ɗago kai yayi yana kallon kakan, fuska babu walwala a daƙile ya ce, "Babu".
"Meye kuma Babu?" Abba ya tambaye sa
"I mean har yanzu babu wacce nake so".
Shiru gaba ɗaya parlour'n ya ɗauka, ana jiran aji wani yayi magana a kan hakan, amma babu wanda ya iya cewa komi, har Kaka kuwa, kowa juya maganar nasa yake yi a mizanin hankalin sa
Kaka kallon Abbu yayi ya ce, "Takwara kun yi maganar da Yayar taku?" (Hajiya Ikram, Yana nufin akan Khabeer da ke son Fadila)
"Eh Baba, Yaya yayi maganar da ita".
Big Dady yace, "mun yi maganar, har mun tattauna da mijin ta, babu matsala tunda su ma a shirye suke, za'a haɗa gaba ɗaya dana Isma'il da Shamsiyya". (Sauran yaran Hajiya Ikram, su uku kenan zata aurar itama, har da K.B)
Gyaɗa kansa Kaka yayi yace, "Masha Allah gaskiya nayi farin ciki matuƙa, Allah ya sanya albarka gaba ɗaya".
"Ameen ameen". Suka amsa gaba ɗaya
"Yanzu duk abinda kuka ga ya dace sai ayi, kun san dai idan za'a saka ranan nace muku kar ya wuce wata ɗaya? Sai ayi komi a tsanake zuwa watanni biyu, na ƙara lokaci, a lokacin idan Fodio da Matata sun kawo nasu sai a haɗa baki ɗaya, don baza ayi babu su ba. Kai kuma Fodio kayi ƙoƙarin samo mata tun kafin Ni in zaɓa maka kana ji ko?" Kaka yayi maganar ta sigan barkwanci
Be ce komi ba kamar yanda kuwa babu wanda yayi tunanin zai ce.
Daga nan dai aka bar zancen aka kama wani, inda waɗanda suke da abun yi suka bar wajen.
Ɗahira bata wani tada hankalin ta ba akan maganar, ta bar wa Allah zaɓi, a ganin ta idan ta saka damuwa kanta zata cuta, tunda dama bata iya saka damuwa a ranta ba, da zaran ta saka, to shikenan ta dinga ciwo kenan, duk idan ka ga tana ciwo to tabbas da akwai abinda ke damun ta ne, ba ta iya jure wa damuwa ko kaɗan a ranta, bata da dauriyan hakan, domin zuciyar ta ba ta iya ɗauka, shiyasa ba ta shiga sabgar kowa idan har be shafe ta ba, sabida ta san matsalar kanta.
Aunty Amarya har ɗaki ta kira ta, tayi mata nasiha akan hakan
Amma sai Ɗahira ta nuna mata babu komi, har da fara'an ta
Hakan ya kwantar wa da Aunty Amarya hankali matuƙa, ko babu komi taji daɗi a yanzu, tunda ta san dole ɗiyar ta zata shiga wani hali na rashin masoyi, tabbas rashin Masoyi abu ne me ciwo ga duk macen da ta isa aure amma babu ma nemi, sai dai Allah ya zaɓa mana mafi alkhairi.
⚫⚫⚫
Fannin Usman ma, da dare Daddy ya Kira sa ya titsiye sa akan maganar, a cewar sa "ai wannan shirmen banza ne, shirmen hofi. Ta ya zai ce be da wacce yake so duk girman sa, shekara kusan 33 yana musu wasa da hankali". Tsiya-tsiya sosai Big Dady yayi masa, kuma ya ba shi umarnin "lallai-lallai ya kawo mata zuwa nan da lokacin da Kaka ya ce, idan ba haka ba, zai ɗau mummunan mataki a kansa"
Hajiya na zaune tana jin su, sai dai bata ce komi ba, tunda itama ai tana ƙaunar ganin ɗan nata yayi aure, shi ne babban ɗa a gidan, amma har yanzu be yi aure ba, duk da a ganin ta ai ba wani shekaru ne masu yawa da shi ba, amma ta yanda za'a ganshi da girma, ƙannin sa su ƙara ganin girman sa, ai sai idan yana da mata, itama zata so ta ga jikokin ta ta wajen shi, ai abun kunya ne ma ace yanzu Yusra zata yi aure shi be yi ba, sannan ga ɗaya ƙanwar sa can a ɗakin miji har da ɗan ta, shi ƙaton banza ya zauna.
Shi kuwa Usman ko a jikin sa, tunda a ganin sa dai babu wanda ya isa yayi masa auren dole, don haka be tashi yin aure ba yanzu sai sanda yayi niyya, duk a cikin mata har yanzu be ga wacce tayi dai-dai da ra'ayin sa ba, yana da burin ra'ayin auren mace zaɓin shi da koda yaushe zuciyar sa take raya masa, kuma har yanzu be dace da kalan ta ba, don haka sai sanda ya same ta sannan ne zai yi aure, mata yanzu ba sa gaban sa, shiyasa ya ɗauki maganar Kaka ba ta da wata muhimmanci, bare shi rayuwan boko ya saka wa kansa, har yanzu gani yake yi be kai matakin da har zai iya ajiye mata ba, ɗawainiya ya hau kansa tun da ƙuruciyar sa ya tsufa da wuri.
⚫⚫⚫
Baffa kuwa sosai ya shiga damuwa a wannan ranan, har kuka sai da ya sha ya ƙoshi, ya kuma gode wa Allah, ga shi yana ji yana gani zai bar zaɓin shi babu yanda ya iya, yana kallon wacce yake ƙauna bata da wanda zata iya gabatar wa face shi, amma kuma Mahaifiyar shi tayi masa iyaka da ita.
Ya tuna sanda ya je har ɗakin ta yana kuka ya sake mata maganar "ta amince ya auri Ɗahira, in yaso duk wacce take so ya aura, shi wlh zai aure ta, koda kuwa mata huɗu zata haɗa masa, idan har da Ɗahira to ya amince".
Amma sai buɗan bakin Hajja tace, "kai Al'ameen ka ji Ni da kyau, Ni Ɗahiran ce ba na so ka aura, bazan taɓa haɗa tsatso da A'ishah ba, domin kuwa na tsane ta a raina, ban taɓa faɗa maka hakan ba, amma yanzu sabida maganar nan ka saka ina bayyana maka sirrin dake raina, to wlh idan har ka kuma sake tayar da maganar nan ma, ban yafe maka ba".
Kuka sosai Baffa ya fashe da shi, be iya furta komi ba sabida tsaban tashin hankali, wai yau Mahaifiyar sa ce take furta masa kalmar nan duk a sabida wani dalili nata mara tushe, ko a mafarki be taɓa tunanin akwai abinda zai iya bayyana wa mahaifiyar sa yana so ba, ta kasa mishi, sabida ya san tana ƙaunar sa, duk abinda yake so to itama tana so, hakan be taɓa faruwa ba, shiyasa yake ganin abun tamkar almara. ranan ya sha kuka kamar babu gobe, har zazzaɓi ya kwana da shi a ranan. Allah ya ɗaura masa ƙaunar Ɗahira kamar ransa, amma ga shi a lokaci ɗaya ya rasa ta, abinda be taɓa tunani ba ko da a mafarki, ya rigada ya saka wa ransa ita ɗin tashi ce, tunda be taɓa tunanin akwai wata matsalar da zai shiga tsakani ba, ko da ma akwai, to, sai dai a wajen Ɗahira, ita ma kuma be taɓa tunanin zata iya cewa ba ta son sa ba, tunda ya san girman son da take mishi, ya san Ɗahira a kansa zata iya yin komi sabida farin cikin sa, shaƙuwar su ya wuce misali, babu ɓoye-ɓoye a tsakanin su.
[6/5, 9:22 PM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR'S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL._
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏼
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
```( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
𝗝𝗜𝗞𝗔𝗥 𝗟𝗔𝗪𝗔𝗟𝗜 𝗖𝗘✍️
𝗪𝗮𝘁𝘁𝗽𝗮𝗱: 𝗨𝗺𝗺𝘂𝗗𝗮𝗵𝗶𝗿𝗮𝗵👈
𝗦𝗔𝗗𝗔𝗨𝗞𝗔𝗥𝗪𝗔
𝑁𝑎 𝑠𝑎𝑑𝑎𝑢𝑘𝑎𝑟 𝑔𝑎 𝐹𝑎𝑚𝑖𝑙𝑦 𝑛𝑎 𝑔𝑎𝑏𝑎 ɗ𝑎𝑦𝑎. 𝗚𝗢𝗠𝗔'𝗦 𝗙𝗔𝗠𝗜𝗟𝗬.
*EPISODE Twenty Seven*
"Dakata da Allah Ayush! Wani taimako kike so in miki ban da wanda nayi miki? Kin tambaye Ni Numban sa na baki wannan kuma ya rage naki, in yaso ki je ki same shi da soyayyar ki, in kuma kin kasa Wannan kuma damuwar ki ne, amma kar ki ƙara zuwa min da banzan maganar nan taki akan Ni ce zan sanar mishi, ina ruwana a ciki?" Shakira take maganar cikin fusata
Ayush dake zaune a gaban table ɗin ta, idanun ta sun cika da ƙwalla, hannu ta saka ta share tana kallon ta tace, "fine naji, sabida na gama miki amfani shiyasa kike son watsa min ƙasa a ido, don kawai na nemi taimakon ki akan nawa soyayyar? Babu damuwa". Ta ƙarishe maganar tana miƙe wa zata bar Office ɗin
Da tsaki Shakira ta raka ta, bata ce komi ba ta mayar da hankalin ta kan wayan ta, sai yanzu ma take dana sanin amince wa tayi ƙawance da local irin wannan, don da farko a tunanin ta ƴar masu kuɗi ne irin su, shiyasa tayi saurin amince mata, amma yanzu gaba ɗaya dana-sanin yin ƙawance take yi da ita, ta bar ta ne kawai saboda tana mata aiki a kan Baffa da Ɗahira, amma kuma yanzu tunda komi ya ƙare a tsakanin su baza ta iya juran raini wajen ta ba...
Tsakin ta kuma ja cike da takaici.
⚫⚫⚫
Ayush kuma na fita ta tsaya bakin ƙofar ta gama share hawayen ta, a fili ta furta, "wlh wlh sai kin yi nadamar sani na a duniya Shakira, yanda ban yi farin ciki ba kema baza ki taɓa yi ba, idan har kin ga kin samu kwanciyar hankali wajen mijin da zaki aura, to, tabbas nima na samu abinda nake so ne, amma mu zuba dani dake, ba a Shana a zauna lafiya".
Tana gama faɗar hakan tayi hanyar Lefter don zuwa office ɗin Usman, so take yi yau ayi ta ta ƙare, baza ta iya barin soyayyar sa a zuciyarta ba, tana shan wahala ko da yaushe be ma san tana yi ba, dole yau zata bayyana mishi soyayyar ta, ko da zata samu sukunin zuciya, ga shi duk shawaran da Rumanatu take ba ta be yin tasiri, ita kuma Safra da tace zata taimake ta har yanzu bata sake jin ta ba, ko a waya ma Numban ta ya dena shiga, wannan dalilin ne yasa ta nemi taimakon Shakira, Amma kuma ta watsa mata ƙasa a ido, ita a ganin ta Shakira tana da hanyar da zata taimake ta domin mallakar Usman, shiyasa kai tsaye ta je da ƙoƙon baran ta..
Sanda ta isa bakin Office ɗin, tsaya wa tayi tana gyara zaman Labcoat ɗin ta, sai da ta gyara fuskar ta sannan tayi Nocking, sai dai babu answer, haka ta sake yin wani, sai da ta ɓata time a wajen kafin ya ba ta iznin shigo wa, buɗe ƙofan tayi ta shiga
Yana zaune ne kansa a saman table, ga duk kan alamu barci ne ya so ɗaukar sa sai yaji Nocking ɗin ta, amma kuma duk da haka be ɗago ba yana jiran yaji abinda ke tafe da ko ma wane ne
Ɗan numfashi taja kana cikin ƙarfin hali tace, "Doctor wajen ka na zo, can I sit?"
Sai a time ɗin ya ɗago kansa ya bi ta da kallo, ganin ta da Labcoat ya tabbatar masa da itama ma'aikaciya ce a Hospital ɗin, sai dai be iya ce mata komi ba illa sake haɗe rai da yayi yana kau da kansa daga kallon ta, tare da gyara zaman sa yana jingina bayan sa kan kujeran, har da ɗaga kansa sama yayi ya sake mayar da idanun sa ya rufe ruf
Ayush dai na tsaye tana kallon sa, sosai take jinjina halin miskilanci irin na bawan Allan nan, tabbas idan har ji da kai ne da taƙama, gami da izza, idan har ka zo wajen sa to ka gama samu, ko kai uban waye ne sai ya nuna maka wannan halin nasa, abun a jinin sa yake, sai dai in ka zage sa amma dole ne sai ka kwashi haushi a zaman ka da shi
Sai da ta ɗan ja wasu sakwanni tana tsaye ko zata ji yayi mata iznin zama kamar yanda ta buƙata, amma be ce komi ba, kuma ga duk kan alamu ba shi da ninyan cewa ɗin, don haka ta ja ƙafafun ta ta nemi wuri ta zauna jiki a sanyaye, shiru tayi don bata san ta ina zata fara ba, a tunanin ta abinda ta ɗauka ɗin sauƙi ne da shi, amma kuma sai da ta bayyana gaban sa ta gane hakan ba me yiwuwa bane ta sauƙi a gare ta, tabbas kwarjinin sa da tsantsan cika idanun sa bazai bar ta ta samu sukuni har ta faɗi abinda take so ba. haka ta shafe tsawon mintoci tana zaune ta kasa yanda za'a yi ta sanar masa da abinda ke ranta.
Shi kuma Usman tuni ma ya manta da wanzuwar ta wajen, domin ba kaɗan ba barci ne yake son kwasar sa, sabida jiya be samu yayi ishashshen barci sosai ba, kuma yau ɗin kafin ya zo Office ya wuce wani wuri, daga can ma ya wuto nan, shiyasa barcin yake son ya ci ƙarfin sa a yanzu.
Daure wa sosai Ayush tayi, ta ara wa kanta jarumta ta soma magana da faɗin, "dama I have come to tall you that.." sai tayi shiru ta kasa ƙarisawa
Tun soma maganar nata ya buɗe idanun sa da suka soma sauya kala, sai dai be motsa daga yanda yake ba, har yanzu fuskar sa na kallon sama ne, yana jiran yaji abinda ya kawo ta, domin dai zai iya cewa be ma taɓa sanin ta ba a nan Hospital ɗin, shiyasa zuwan nata wajen sa yake ba shi mamaki, duk da kuwa ba yau ya saba ganin hakan ba, amma kuma ita ɗin ya dangana hakan da zuwan ta a kan aiki ne..
Sauya maganar nata tayi da faɗin, "my name is Ayush Abdulkarim, wacce take tura maka saƙo a facebook, kuma kwanaki biyu kenan da soma maka magana ta WhatsApp". Sai ta sake yin shiru
Sai a time ɗin ya ɗago kansa sosai yana sauke rikitattun idanun sa a kanta, sosai ya haɗe rai a wannan karon fiye da tunanin me tunani, wanda har sai da ya sa Ayush ta sunkuyar da kanta da sauri sabida ba ƙaramin tsorata tayi da kallon nan da yake mata ba, tabbas tuni ya gane ta da bayanin da tayi masa, sabida yanda take damun sa a facebook; kullum sai ya ga saƙon ta, that's why tana faɗar sunan nata ya gane.
Be ce komi ba, kamar yanda itama ta kasa yin magana, tsawon lokaci kafin taji muryan sa ya daki dodon kunnen ta
"Get out". Ya bata umarni cikin natsatstsiyar muryan sa
Nan da nan sai ga hawaye sharr sun soma kwaranya a fuskar ta, tana kallon sa tace, "don Allah ka taimake Ni kamar yanda Allah ya taimake ka, wlh wlh zan iya rasa raina idan har ban same ka ba, Ina son ka, ina matuƙar ƙaunar ka, don Allah.."
Tsawan da ya daka mata ne, yasa tayi shiru babu shiri
"Out". Ya faɗa tamkar ana masa dole cikin murya me amo, domin maganar nan da ta saka shi har kanshi ya soma sara wa, dama ga shi yana buƙatar hutu da barci
Miƙe wa tayi idanun ta na tsiyayar da hawaye ta bar Office ɗin.
Lumshe idanun sa yayi yana sake jingina bayan sa da kujeran, ya rasa meyasa yanzu mata suka ɓaci, shin ina suka bar kunyan su ta ɗiya mace har suke iya zuwa su sami namiji su faɗa mishi suna son sa? Sosai yake mamakin yanda duniya ta sauya, ko zai mutu ne ai bazai iya auren mace irin wannan local ɗin ba, in ba raini ba kamar yarinyan nan ta zo har gaban sa tana faɗa masa tana son sa, tsaban takaici ma tsaki yaja ya miƙe ya ɗauki keeys ɗin motan sa ya bar Office ɗin.
⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫
*WEDNESDAY*
Cikin sauri take tafiya kasancewar tayi late, har ga shi 10:03am. Ta yi, wajen motan ta ta ƙarisa ta saka keey tana shirin buɗe wa, sai ta hangi Baffa shima ya fito daga bayan gidan
Tafiya yake yi yana waya kansa a ƙasa yana tsola ƙafafuwan sa tamkar yana ƙwallo
Mayar da ƙofan tayi ta rufe ta taka ta nufi inda yake, be ganta ba har sai da taƙariso wajen, inda daddaɗan turaren ta ya doki hancin sa, da sauri ya juyo suka haɗa ido
Murmushi ta sakar masa, don ganin sa ba ƙaramin faranta ranta ya yi ba, tun zaman da suka yi last two weeks wajen meeting bata sake ganin sa ba. bata yi magana ba ganin yana waya
Sai dai shi gaba ɗaya tunda suka haɗa ido ya rasa sukunin sa, wayan kawai yake yi amma hankalin sa ba ya tare da shi, duk da kuwa ya kawar da idanun sa daga kanta. Ɓata lokaci yayi yana wayan yaƙi ya yanke, sai kamo wani zancen yake yi kasancewar da abokin sa yake wayan.
Ita kuma tana tsaye ta harɗe hannayen ta a ƙirjin ta tana kallon sa, shiru tayi kawai idanun ta a kansa, sosai take ganin sauyi a tattare da Baffa, gaba ɗaya yanzu ta ga kamar ya sauya mata, kwata-kwata ba ya son ganin ta, idan ba haka ba tasan babu yanda za'a yi a kwana a hantse be nemi ganin ta ba, koda kuwa ta waya ne, amma yanzu tsawon satikai kusan uku kenan ana shirin wata ba ya neman ta, tana ganin kamar akwai wani abinda ke damun sa, yanda gaba ɗaya ya sauya har wani rama yayi...
"Keee!"
Tsawan da aka daka mata ne ya sanya ta dawo hankalin ta cikin matuƙar tsoro
Ba ita kaɗai ba, har ta Baffa da ya juya baya a yanzu ɗin yana ci gaba da wayan sa, sai da ya tsorata da tsawan da aka yi
Sa'adatu ce tsaye ƙiƙam gaban Ɗahira, ta kame ƙugun ta da hannayen ta biyu tana faman huci tamkar zaki, ba komi ya fusata ta haka ba illa fitowar da tayi tana shirin fita, sai ta hangi Ɗahira gaban Baffa ta ƙure sa da idanu ko ƙyafta wa ba ta yi, ga shi kuma har ta iso wajen tana mata magana amma bata ji ta ba, hakan ya sa ta daka mata tsawan nan
Bata bari kowa yayi magana a cikin su ba tace, "uban meye kika tsaya kina kallon sa tamkar zaki cinye sa? Ko dai wani makircin zaki ƙulla iyeee? Ki faɗa idan ba muna-furci da makircin da ke ran ki ba; meye ya kawo ki bayan shi kina kallon sa be ma san kina yi.."
"Kee Sa'ada are you crazy? Kin san da wa kike magana kuwa?" Cewar Baffa a matuƙar fusace da ɗaga murya
Kallon sa Sa'adatu tayi, sai ta zaro masa ido tace, "hankali na ƙalau kuwa Yaya, so nake in San meye alaƙan ka da wannan yarinyan? Ina ce Hajja ta raba ku meye kuma ya sake haɗa ku? Ok har yanzu kana son..."
Mari ya yarfa mata, wanda har sai da yasa ta soma ganin taurari, ba ita kaɗai ba har Ɗahirah dake kusa da ita, bata san sanda hannun sa ya gilma ta gefenta ba, hakan yasa ta tsorata taja baya da sauri tana shirin faɗi
Saurin taro ta Baffa yayi, hakan yasa ta faɗo kansa tamkar ya rungume ta.
A wannan lokacin shi kuma Usman ya fito gida, babu inda idanun sa ya sauka sai a kansu, tsaya wa yayi kawai yana kallon su cike da mamaki. Janye idanun sa yayi daga kallon su yana jan tsaki a fili, a zuciyar sa kuwa cewa yake, "dama daga gani idan wannan sheɗaniyar yarinyan bata ja hankalin maza sun faɗa tarkon ta ba ai ƙarya ne, waye ya san ma ranan da kuka soma hakan". Motan sa ya ƙarisa ya shiga ya ja ya bar gidan.
A can kuwa wajen su, Baffa ya kasa cire Ɗahira a jikin sa, while itama ta kasa motsa wa, domin sosai ta tsora ta, sai da ta gama dai-dai ta nutsuwar ta kafin tayi yunƙurin janye jikin ta.
Sa'adatu da tayi mutuwar tsaye na daga tsantsan mamakin marin da Baffa yayi mata, ga kuma takaicin ganin su haɗe da juna, shi ne yasa ta kasa koda ƙwaƙƙwaran motsi, illa bin su da kallo da take yi.
Ɗahira na janye jikin ta ta juya ta wuce ba tare da ta furta komi ba
Baffa be iya dakatar da ita ba, duk da kuwa yana son tsayar da ita ɗin, har ta shige mota yana bin ta da kallo, sahun gudun Sa'adatu da kukan ta kawai ya ji, ya juya yana kallon ta wanda har ta kai ƙofa ta shige cikin gidan. Ajiyan zuciya ya sauke yana bin wayan sa dake ƙasa da kallo, be ma san sanda ya wuntsilar da ita ba garin taro Ɗahira. Lumshe idanun sa yayi a hankali ya furta, "Ina son ki Ɗahira! Ina matuƙar ƙaunar ki! Kuma ba zan taɓa dena ƙaunar ki ba har na koma ga mahalicci na".
⚫⚫⚫
Ɗahira motan ta kawai take ja tana tunani, ko kaɗan ta kasa gane takamaiman abinda ke damun ta
Tsaki kawai ta ja ganin tana son damun kanta da tunanin banza, ƙara Speed ɗin motan tayi tana kallon agogon hannun ta
Dai-dai ta isa kusa da Hospital ɗin, tana shirin shan kwana ta shiga, bata kula sosai ba, Ashe wata mota babba na ɗan gote ta dumfaro. shi kuma can ɗaya side ɗin me machine ya dumfaro da gudu yana shirin gilma motan, sai motan tayi ciki da shi, Wanda machine ɗin da me machine ɗin tuni sun yi hanyar su daban, inda machine ɗin ta zo kan motan Ɗahira da har ta kusa tura kan hancin motan ta cikin Hospital ɗin, sai ji kake yi motar nata tayi ƙuuuuuuu.. saboda wani wawan burki da taja kasancewar buguwan da machine ɗin tayi a kan motan ta, yayi matuƙar tsorata ta har ta rasa nutsuwar ta gaba ɗaya taja burki a take tana salati
Can kuwa wajen babban motan nan tuni tayi ciki da wasu motan da suka dumfaro ta, nan da nan motoci da mashina suka harhaɗe aka haɗa babban hatsari, jini ya soma ambaliya a titin, machine ɗin nan na saman motan Ɗahira, inda wata motan kuma ta bugi motan nata tuni tayi ratsa-ratsa.
Kankace me mutane sun soma zuwa ceton rai, nan da nan wajen ya hargitse da hayaniya. Allah yasa kusa da asibiti ne, nan akai ta zaro mutane ana nufan asibiti da su.
[6/7, 8:19 AM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR'S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL._
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏼
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
```( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattapad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
𝑁𝑎 𝑠𝑎𝑑𝑎𝑢𝑘𝑎𝑟 𝑔𝑎 𝐹𝑎𝑚𝑖𝑙𝑦 𝑛𝑎 𝑔𝑎𝑏𝑎 ɗ𝑎𝑦𝑎. 𝗚𝗢𝗠𝗔'𝗦 𝗙𝗔𝗠𝗜𝗟𝗬.
_Wannan shafin naku ne Masoyana, kar ku ce ban gaishe ku ba😅, to ku shaƙata da wannan na ku ne kyauta, ina ƙaunar ku nima, har da waɗanda suka ɓoye kansu, Ni *JIKAR LAWALI* ina matuƙar jin daɗin nuna soyayyar ku gare Ni, idan baku Fans to babu Ni ce._
*EPISODE Twenty Eight*
Su Abbu na cikin Office ɗin Big Dady, inda suke meeting a kan shigo da magani da za'a yi musu, da sauran abubuwan da asibitin yake buƙata. A lokacin ne labarin mummunan hatsarin da ya afku a wajen Hospital ya iso gare su, ai tuni sun fito don zuwa su ba da agajin gaggawa
Sai da suka sauka downstairs ne, labari ya riske su da Ɗahira hatsarin ya ritsa. Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un tashin hankalin da suka shiga baki ma bazai iya bayyana shi ba, kankace me sun ruɗe gaba ɗaya kowan su sai sharce gumi yake yi, musamman da suka ga yanda ake shiga da masu hatsarin rai a hannun Allah. Nan su ma suka bi ayari fannin emergency rooms
Su Baffa da Fadila basu fito gida ba ma, labari ya kai musu, tunda shi Baffa dama be yi ninyan shiga ba yau, sai yamma, amma tuni sun ruɗe da su Aunty Amarya sun taho asibitin, sai dai an kasa sanar wa Kaka tunda ba'a san halin da take ciki ba yanzu.
Lokacin da suka iso asibitin, a reception suka tarar da su Aunty Zainab da Yusra da Shakira, tunda su ba fannin su bane, su Big Dady kuma na ciki.
Haka DOCTORS da staff's suke ta sintiri suna ba da taimakon gaggawa
Baffa wuce su yayi ya bar su nan, shima ya nufi emergency rooms ɗin, duka tagumi suka yi har Hajja Fatu, domin itama taƙi shiga tunda itama ba fannin ta bane. Aunty Amarya ne kaɗai a wajen take share hawaye, sai Fadila da tayi zugum tana tunanin ƴar uwan ta a ranta, har bata san sanda ƙwalla ya zubo mata ba, babu abinda take tuna wa sai fitowar ta gida yanzu da abinda ya faru, dayake ta side ɗin windown ɗakin su suka tsaya, shiyasa tana kallon draman da suka yi da su Sa'adatu daga saman bene. haka Allah ke lamarin sa, da mutuwa ne sai a aiko musu a ce ta mutu.
Allah ya taƙaita, Ɗahira bata wani ji rauni sosai ba, sai dai suman da tayi ne har yanzu bata farka ba, ta samu buguwa a kanta har da ciwo, sai kuma gwiwar ƙafafuwan ta da suka ƙuƙƙurje. Alhmadulillah gaba ɗaya ahalin sun samu kwanciyar hankali musamman da suka shiga suka duba ta, time ɗin tana barci tunda an yi mata alluran barci, ba'a haɗa ta da kowa ba a ɗakin da take, sauran suna can rooms ɗin, sun daɗe wajen ta, inda suka je ɗaki-ɗaki suka duba sauran mara su lafiyan.
Sai da ta farka kafin su Aunty Amarya suka bar asibitin, tare da masu aiki suka koma tunda sun kawo musu abinci.
Ɗahira tana samun kulawa sosai wajen su Abbu, barin ma kar ace Doc. Sa'id, domin kasancewar fannin sa ne, shi yayi ruwa yayi tsaki yana kula da ita, abu kaɗan ya matso kusa da ita yana tambayan ta abinda ke damun ta, sai hakan ya faranta ran iyalan gidan, musamman su Abba, don a tunanin su akwai wani abu a tsakanin su, tunda itama Ɗahira sosai ta saki jikin ta dashi, ta yanda ma ta nuna sanayya a gare sa.
Hakan ko kaɗan be ma Baffa daɗi ba, shiyasa be wani zauna ba ya bar wajen, domin bazai iya zama yana kallon wani banza yana hira da ita ba, da kuma bata kula wa sosai.
Usman kam koda ya san abinda ke faruwa, ko leƙowa be yi ba, yana Office ɗin sa, sai da Big Dady ya kira sa yayi masa faɗa, sannan ne ya zo ya duba ta, kuma komi be ce mata ba, kamar yadda itama bata ko kalli inda yake ba. Haka ya juya yabar ɗakin yana taɓe baki.
Babu wanda ya sanar wa Kaka, har sanda su Abbu suka dawo gida, sannan ne suka sanar masa cikin nutsuwa, amma duk da haka sosai ya ɗaga hankalin sa, cewa yayi "dole sai an kai sa ya duba ta". Ga shi lokacin dare ne. Dole haka suka fito gaba ɗayan su, Big Dady Abba da Abbu suka nufi asibitin.
Umma ce da ɗaya daga cikin ƴan aikin su za su kwana da ita, bisa umarnin Abbu. time ɗin ma tayi barci sanda suka zo
Sai a nan hankalin Kaka ya samu sukuni tunda ya ganta a kyakykyawar yanayi. Sun jima kafin suka baro asibitin.
Washe gari da safe ma ya saka aka sake kawo shi
Lokacin Ɗahira na zaune tana shan tea da aka haɗa mata suka shigo, taji daɗin ganin su, nan tabi su ɗaya bayan ɗaya tana gaishe su
Kowan su na amsa mata cike da kula wa, tare da tambayan ta ya jiki?
Murmushi tayi tace, "it's so easy".
Big Daddy yace, "Are You sure my daughter babu abinda ke damun ki?"
Gyaɗa kanta tayi tana sake tabbatar masa da cewa, "Yes my Dady".
Murmushin farin ciki gaba ɗaya suka yi
Kaka yace, "ai gaba ɗaya kin ɗaga min hankali Matata, a jiya kasa barci nayi, ban ma karya ba na taho duba ki, ashe ke ga shi har kin samu saka abinci a cikin ki, kin bar Mijin ki cikin tashin hankali".
Ɗahira murmushi ta sakar masa, tana langaɓe kai tace, "eyya Miji na, ban sani bane ai, ka ga da ban ci komi ba nima kamar kai, na tausaya maka matuƙa tsoho na".
Dariya gaba ɗaya suka yi har Kaka da ke faɗin, "Ja'ira".
Itama dariyan tayi cike da farin ciki. Haka suka ci gaba da hira na ɗan wani lokaci, inda su Big Dady suka tafi Offices ɗin su suka bar Kaka a nan, don ya ce, "ba yanzu zai koma ba".
Doc. Said ne ya shigo da sallama a bakin sa
Suka amsa mishi suna kallon sa, musamman ma Kaka
Shi kuma murmushi yayi ya iso wajen yana durƙasa wa har ƙasa ya gaishe da Kaka
Kaka ya amsa cike da fara'a da jin daɗin girmama sa da yayi
Ɗahira bata bari ya sake magana ba, ta gaishe shi itama
Amsa wa yayi yana kallon ta yana murmushi, sannan ya tambaye ta "ya jikin nata?"
"Alhmadulillah". Ta amsa mishi da shi
Zama yayi gefen kujeran da ke kusa da gadon ta yana kallon ta, kafin kuma ya ce, "Yakamata a wanke miki ciwon idan kin gama ko?"
Ajiye Cup ɗin hannun ta tayi tana cewa, "ok Doctor I'm done ai".
Miƙe wa yayi ya soma haɗa magunguna
Ita kuma suna hira da Kaka, inda yake tambayan ta "wane ne wannan?"
Dariya tayi tace, "Kaka Doctor ne shima ai".
Gyaɗa kansa yayi yana bin Doctor Said da kallo
A haka dai har Doc. Sa'id ya gama abinda zai mata, sannan ya zauna ana hira da shi
Sosai a nan Kaka ya sake fahimtar akwai wani abu a tsakanin su, inda lokaci ɗaya ya ji farin ciki a ransa, shiyasa ya sake jan Doc. Sa'id a jikin sa, ko ba komi nan da lokaci kaɗan zai ga auren Jikar tasa, ko kaɗan ba ya son ƴan uwan ta su yi aure su bar ta, sosai hatsarin nan ya sake ɗaga masa hankali.
Ana haka su Aunty Amarya suka zo
Ɗahira taji daɗin ganin su sosai, nan ta sake sakin jiki ana ta hira gaba ɗaya, ga shi sosai take farin cikin yanda ake ba ta kula wa, musamman su Big Dady, da zaran mintuna ƙalilan ya wuce za su taho duba ta.
Sai yamma duk suka tafi har Kaka.
Kwanan ta biyar a asibitin tana samun kulawa, kafin aka sallame ta, ta koma gida tana ci gaba da jinya. A haka har ta samu sauƙi sosai, inda ta nemi ta koma bakin aikin ta, amma sai Abbu ya hana ta tunda har yanzu ɗingishi take yi.
Sai da aka shafe kusan sati Uku kafin ta warware, sannan ta koma bakin aikin ta, zuwa yanzu sosai Ɗahira da Doc. Sa'id suke mutunci, koda aka sallame ta a Hospital be taɓa zuwa gidan su ba, amma kuma suna waya sosai, hakan yasa suka saba, har ita Ɗahira tana tunanin son ta yake yi, sabida yanda yake ba ta kula wa ainun, shiyasa ma ta sake sakin jiki sosai da shi, sai dai har yanzu kalman da take so taji a bakin sa ya ƙi ya sanar mata, ko kaɗan ba ta ƙaunar a sake zaman meeting ba tare da tana da tsayayye ba, sai dai babu yanda zata yi tunda be ce yana son ta ba har yanzu, sai ma daga baya ta gane yana da mata har da ƴaƴa biyu, amma hakan be ɗaga mata hankali ba, a ganin ta idan yana son ta zata iya auren sa, tunda duk wani ɗabi'u na kirki shi yake nuna mata, sai dai lokaci na ta ja babu wannan kalman a bakin Doc. Sa'id, ga shi har yanzu saura sati biyu auren ƴan gidan.
Kamar yanda suka saba meeting ranan Lahadi, haka wannan Lahadin aka tara su, Ɗahira aka soma tambaya, amma tace musu "bata da wanda take so" maganar ya girgiza su
Kaka yace, "kina nufin wannan Doctorn har yanzu be yi miki ba?"
Kallon Kaka tayi tace, "Kaka ai ba soyayya muke yi da shi ba, it's just Friendship".
"Uwata dama ai ta hakan ne soyayya take ƙulluwa, ke dai kawai ki sanar mana idan da akwai wani abu a tsakanin ku, kar ki zauna ki ce zaki ja mishi aji kinji ko?"
Gyaɗa kanta tayi kafin kuma tace, "amma Abba wlh be taɓa cewa yana so na ba, kuma ma yana da iyalan sa".
Shiru suka yi duk kan su, kafin kuma Kaka ya sake Tambayan Usman da cewa, "to kai kuma Fodio aina taka take?"
"Nima Kaka har yanzu ban samu wacce nake so ba".
"Kana nufin har yanzu maganar da muka yi maka baka ɗauke ta da muhimmanci ba?" Big Dady ya faɗa yana kallon sa
Shiru Usman yayi kansa a ƙasa
Nan Dady ya dinga faɗa kamar zai ari baki, kuma ya ce "dole sai yayi aure da ƴan uwan sa, idan be samo matan ba shi yana da hanyar da zai samo masa"
Kaka ne ya tsayar da shi da faɗin, "ƙyale shi Noor, duk hakan be ta so ba, yanzu dai aci gaba da hidiman biki kar a fasa, su kuma Allah ya kawo musu na gari, lokacin su ne be yi ba babu yanda zamu yi da su".
Daga haka ba'a sake yin wata maganar ba, aka sallami kowa.
Inda daga ranan gadan-gadan aka ci gaba da hidimomin biki, ko wanne fanni suna nasu, tunda kowa a cikin su zai aurar, illa Aunty Amarya ce kaɗai da babu ita, amma kuma komi da ita ake yi ana Fadila, duk ita take shirin komi, sai ƴan uwan Umman dake nasu, duk da suna yaɓa mata maganganu amma ko bi ta kansa ba ta yi, abinda yafi ɗaga mata hankali yanda gidan duk ya cika da mutane, babu hiran da suke yi sai na Ɗahira, wai "har yanzu bata da mashinshini, tayi kwantai, maza ma tsoron zuwa wajen ta suke yi, bare su furta mata suna son ta." Kowa ba ya lura ba ita kaɗai bace a gidan da baza ayi auren ta ba, har da Usman, shi da yake ma babban su amma yaƙi auren, amma ita kaɗai ake gani
Sanda Ɗahira ta soma jin ƙananun maganganun nan bata wani damu ba, sai dai yanda ƴan uwa suke taran ta da maganar, har wasu suna mata Shaƙiyanci suna yaɓa mata magana, sai abin ya soma damun ta, amma babu yanda zata yi haka take barin abun a ranta, duk da ita bata cika iya ɓoye damuwa a ranta ba, ko ya ya ne idan har tana da damuwa sai ka gane..
Gida fa ya sake cika maƙil inda har an soma events, duk da ba kowa bane ke wajen, wasu sun tafi can Katsina, Hajiya Laila ma can ta tafi, sai su Firdausi da sauran ƴaƴan ta masu aure da suka zo nan, Aunty Zainab ma da ita da Aunty Amarya, ana gobe suka wuce can a bisa umarnin Kaka, tunda ba za'a bar Hajiya Ikram ita kaɗai tana biki babu ƴan uwa ba, kowa ya zo nan ya shantake, wasu ma zuwa gobe ranan bikin za su wuce idan za'a kai Fadila can, sai su kwana biyu wasu kuma su yi kwana ɗaya.
Tun ana kwana biyu Sa'adatu ta koma Legos, sai ranan bikin za a kawo ta.
⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫
Dafa ta Fadila tayi, hakan yasa tayi firgigit tana kallon ta
"What are you thinking sister, I'm talking to you are you quiet?"
Murmushin yaƙe Ɗahira tayi, sai ta gyaɗa kanta tana son mayar da hawayen dake cikin idanun ta tace, "nothing".
Cike da tausayin ta Fadila tace, "don Allah ki dena saka damuwa a kan maganganun su Inna, ko ma su waye ne zasu yi miki gori don Allah ki dena saka damuwa kinji, ke baki ga yanda kika faɗa bane? Ana bikin mu amma gaba ɗaya kin tsame kanki a cikin mu".
Shiru Ɗahira tayi, don bata san me zata ce mata ba
Sai itama Fadilan tayi shiru, sai dai bata tashi a wajen ba. Tsawon lokaci suna a haka kafin Fadilan ta kalle ta tace, "Sister, there is something I want to tell you, akwai maganar da naji wajen Hajja da Shakira, shiyasa naga dacewan in faɗa miki".
_What do you think Fadila will tell her? 🤔_
_mu je zuwa yanzu aka soma._
[6/8, 8:45 AM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR'S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* 🧝🏼
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
```( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattapad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_
*EPISODE 29 & 30*
Idanu Ɗahira ta zuba mata tana jiran taji me zata faɗa
Fadila tace, "na lura a gidan nan Hajja ba ta ƙaunar ki, kuma ba ita kaɗai ba har ta da Shakira, domin tasha sanar dani abu game dake domin ta haɗa mu faɗa, ban taɓa biye mata ba, sabida narigada nasan abinda ke cikin ranta. A kwanaki biyu da suka wuce na ji su suna zancen ki, maganar rashin samun tsayayye ne da baki dashi, suna faɗin hakan yayi musu daɗi, har suna cewa Allah yasa ma ki dauwama a haka baza ki taɓa aure ba, sannan Hajja take cewa koda ma kin samu, ita tayi alƙawari baza ta taɓa barin ki ki zauna da mijin ki lafiya ba, duk yanda za'a yi sai tayi don raba ki da Mijin, sai ta mayar dake ƙaramar bazawara idan kin yi aure, idan kuma baki yi ba, zata bi duk hanyan da taga zata iya wajen hana ki aure".
Tun soma maganar nata Ɗahira take tsiyayar hawaye, sosai zuciyar ta ke suya da zancen nan, "wai dama tsanar da Hajja take mata har ya kai haka ne?"
Bata san cewa a fili tayi tambayar ba, sai jin muryan Fadila tayi tana cewa, "yafi haka ma, baza ki san haka ba sai nan gaba kaɗan idan kin san wani sirrin. Sister Ni abinda nake roƙon ki dashi har na sanar miki da zancen nan, saboda ki san maƙiyan ki ne, ki san yanda zaki zauna da su, sannan ki san hanyar da zaki ɓullo wa al'amarin, ki riƙe addu'a domin baki san ta ina za su biyo miki ba, don Allah ina sake roƙon ki, duk wanda zaki aura Sister, ki kasance me mishi biyayya, ki zauna da mijin ki lafiya ko don ki ba ma Maƙiya kunya, Ni ƙanwar ki ce, but I beg you by God, ki tuna magana ta ko bayan ba na nan".
Sosai a wannan lokacin Ɗahira take hawaye, har da shashsheƙan kuka
Itama Fadila tuni nata hawayen sun zubo, cikin rawan murya tace, ""I miss you Sister, please .. please ki nemi kariyan Allah domin ki guje wa afkuwar wani abu, ba na son wani abu ya same ki ta silan maƙiya.."
"Keee Fadila meye haka? Me kuke yi haka? Kukan meye?" Ƙanwar Umma da suke kiran ta Inna Sailuba take faɗar hakan, shigowar da tayi
A tare suka bi ta da kallo, sai dai babu wanda ya tanka mata, illa ƙoƙarin share hawayen da suke yi
Tsaki taja tana bin su da kallo itama tace, "tashi dalla kin zauna ta saka ki gaba tana kukan muna-furci, idan ba ta son rabuwa dake ne itama tayi auren mana, in ba hassada kuma take miki ba. Ki tashi nace ga Naja'atu can ta dawo ku je gidan me lallin".
Kamar yanda basu ce mata komi ba ɗazu ɗin, haka yanzu ma babu wanda ya tanka mata, sai dai Fadila ta miƙe tsaye ta wuce zuwa waje. Itama Inna Sailuba ɗin sai bin bayan ta tayi tana sababi har da kumfan baki, "wai Fadila ta raina ta, tana faɗa mata gaskiya amma Ɗahira ta fi ta a wajen ta". Duk da kuwa tasan cewa halin Fadilan ce ƙyaliya da Miskilanci. Kankace me sauran jama'an da ke zaune a Parlour sun amshe zancen, nan suka soma aibata Ɗahira da ita da uwar ta tunda sun san ba ta nan, suna me zagin su da yin musu gori akan Ɗahiran.
Lumshe idanu Ɗahira tayi tana me sake jin zafi sosai a ranta, sosai take kukan zuci babu me rarrashin ta. Ganin baƙin cikin su zai iya kashe ta, sabida ita bata saba jure irin waɗannan ƙananun maganganun ba, sosai suke damun ta a zuciya, sai damuwar kuma ya haifar mata da ciwo, shiyasa ta tashi tafito ta nufi cikin gidan, kasancewar yamma ta soma shiyasa babu wasu mutane sosai a waje, ta inda tasan ma baza ta same su ɗin ba ta nan tabi ta wuce sashin Hajja
Akwai mutane sosai a parlour'n suna zazzaune suna aiki, kasancewar parlour'n akwai duhun magriba har ta wuce ɗakin Baffa babu wanda ya kula da ita, bare ma a shaida ta, bare kuma gidan biki kowa sha'anin gaban sa yake yi.
Keey ta saka ta buɗe ƙofan bayan ta taɓa taji a rufe yake, ta tura ta shiga sannan ta mayar ta rufe, Direct Kan gadon sa ta nufa ta faɗa ta soma rusa kuka, kawai so take yi ta fitar da duk wani ƙuncin da ke damun ta, domin kuwa muddin bata fitar ba, dole ne tayi ciwo. Sosai tayi kukan babu me rarrashin ta, sai da ta gama ta miƙe zaune ta buga tagumi tana me ci gaba da tunanin zuci
"Ita bata ga makusa a jikin ta ba, duk inda mace me ji da class, me ji da kyawu da tsafta, gami da ilmi ta kai, to meyasa har yanzu ta rasa masoya? Meyasaka har yanzu ta rasa wanda zai ce mata zai aure ta? Ta san tana da farin jinin jama'a, kama daga mazan har matan, babu wanda ba ta harka da su, amma kuma babu wanda ya taɓa buɗe baki yace mata ya zo gare ta ne don soyayya, wanda kuma zai kai su ga aure, sai dai su zo a matsayin tana burge su, tunda tana burge su why baza su sanar mata suna ƙaunar ta ba? Ko kuma dama tana da makusa ne wanda be dace ta samu mijin aure ba?"
Runtse idanuwan ta tayi hawaye na sake silalo mata, cikin muryan ta da ya dishe sosai sabida kukan da tasha tace, "Allah gani gare ka, kai kace a roƙe ka zaka amsa, har yanzu bazan gajiya ba, kuma na san cewa kana ji na. Allah ka zaɓa min abinda yafi alkhairi a rayuwa ta, idan har auren nan ne alkhairi a gare Ni, ya Allah ka zaɓa min miji na gari, idan kuma babu alkhairi a tare da Ni, ya Allah zan rayu ina me gode maka, saboda haka ka tsara min rayuwa ta. Zaɓin ka kaɗai nake nema ya Allah, a duk sanda kaso ikon ka a kaina, a lokacin Ni kuma zan amsa ina me godiya a gare ka ya Allah, Allah na tuba ka yafe min". Ta ƙare maganar tana sakin wani sabon kukan
Ta jima tana yi kafin ta tsakaita tana me miƙe wa, sai hannun ta ya bigi drowan gadon wani abu ya faɗo, kasancewar ɗakin da duhu sai ta saka hannu zata laluba, hakan yasa ta kama wayan da tayar hannun ta na latsa wa a rashin sani, take a nan hasken ta ta kawo
Ƴar ƙaramar waya ce Nokia, wayan tabi da kallo, kamar ta ajiye sai kuma zuciyar ta ta bata umarnin latsa wa, take a nan ta danna ta ta cire ta a keey, nan ya bayyana wajen Text message, kasancewar daga wajen ne ba'a fita ba ta shiga keey
Rawa jikin ta ya soma saboda ganin text ɗin da ake turo mata, take ta koma ta zauna tana ci gaba da karanta wa, tabbas gaba ɗaya text ɗin da ake turo mata ne anan
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un... Kar dai ace Ya Baffa shi ne Masoyin ta na ɓoye?" Tayi maganar a fili tana ɗaura hannun ta ɗaya dake rawa a baki
"Ya Allah..." Ta sake faɗa tana kai idanun ta dake tsiyayar da hawaye kan wayan, ci gaba da karanta text ɗin tayi, sai kuma ta koma ta shiga ta duba Numban, take a nan taga Numban nata ne
Lumshe idanu tayi tana jin wani irin raɗaɗi a ranta, babu abinda ya faɗo mata a rai sai text ɗin sa na ƙarshe
"Hajja..!" Ta furta a laɓɓan ta tana me buɗe idanun ta
"Why Hajja? Me nayi miki? Dama ke ce kika hana Ni aure a wannan gaɓar? Ke kika raba ni da Masoyi na na haƙiƙa? Me nayi miki da zafi haka?".
Miyau ta haɗiye sabida jin wuyan ta ya cinƙushe da tuƙuƙin baƙin ciki, cikin kuka tace, "Ya Baffa meyasa ka kasa bayyana min kanka a matsayin wanda kake so na? Meyasaka ka zaɓi ɓoye min kan ka? Ashe dama da kai ne nake soyayya ban sani ba? Tabbas da baka ɓoye min kan ka ba, da duk haka be faru ba, ga shi Hajja taci galaban raba mu. Meyasa?.." ta kasa ƙarisa maganar dole tayi shiru
Tun soma maganar nata Baffa ya buɗe ƙofan ya shigo, yana tsaye bakin ƙofan yana jin komi, cikin tsananin ƙaunar ta tare da zallan tausayin ta yace, "Ƙaddara ce Ɗahira".
Saurin ɗago idanuwan ta tayi tana bin sa da kallo, duk da kuwa bata ganin sa sosai, amma hakan be sa ta kawar da idanun ta a gare sa ba
Yaci gaba da faɗin, "Nima sai daga baya na gane nayi wauta, tabbas da na bayyana soyayyar ki a fili, da duk hakan be faru ba, da mutanen gida sun goya mana baya, da Hajja bata ci galaba a kan mu ba. sai dai yanzu kuma babu yanda zan yi, sabida Hajja tarigada tayi min iya ka da hakan, idan har na bari wani yaji, tsinuwar ta shi ne zai ta bibiya ta, ban san ya zan yi ba Ɗahira, amma wlh ina tsananin ƙaunar ki, ke nake so a zuciya ta, kuma har na mutu bazan taɓa dena son ki ba".
Da gudu ta tashi tana toshe bakin ta, ta zo ta wuce sa ta bar ɗakin
Shima be hana ta ba, ko motsi ma be yi ba, illa runtse idanun sa da yayi hawaye na zubo masa kan kuncin sa.
⚫⚫⚫
Direct ɗakin Maman ta tawuce, ta shiga ta kulle kan ta ta hau rusa kuka babu ji babu gani, kukan da ke taɓa mata zuciya, yake ƙara mata raɗaɗin da ke cinkushe a zuciyar ta. Sosai tayi kukan wanda har ya haifar mata da ciwon kai me tsanani
Ita da kanta ta rarrashi kanta tayi shiru, sai dai duk yanda taso ta danne abun da take ji a ranta, ta kuma jure baƙin cikin dake zuciyar ta, ta kasa, gaba ɗaya rauni ne a zuciyar ta, waye zai rarrashe ta? Waye zai kwantar mata da hankali har taji sanyi a ranta? Ya faɗa mata tayi haƙuri haka ƙaddaran ta take?
Lumshe idanuwan ta tayi, hawayen dake maƙale a cikin idanun ta suka zubo saman kuncin ta, ta saka hannu ta share tana me miƙe wa zaune, kanta ta riƙe tana jan majina
"Allah Sarki Mamana, da ace kina nan ke ce zaki share min hawaye na. Meyasa ne Ni kuwa bani da Sa'a a rayuwa ta? Menene aibu na? Shin me na tare wa Hajja da ta tsane Ni har haka? Ya Allah.. ka saka min juriya domin in tsallake wannan jarabawar taka".
Miƙe wa tayi ta wuce Toilet ta ɗauro alwala ta fito, sallan magriba da isha'i ta gabatar, sannan tayi shafa'i da wutri, ta jima tana kwararo addu'a tana hawaye kafin ta shafa ta miƙe
Ta san Abbun ta ba anan zai kwana ba, sabida jama'a masu biki, kuma dama Aunty Amarya ce ke dashi, shiyasa ta kwanta a ɗakin tunda tasan ba ma zai zo Part ɗin ba.
Daƙyar a ranan barci ɓarawo ya ɗauki Ɗahira.
⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫
Ranan Saturday 25 March 2021. Aka shaida ɗaurin auren *AL'AMEEN ABUBAKAR AL'AMEEN* tare da Amaryan sa *SA'ADATU ABDULLAHI*
*SHAKIRA ABUBAKAR AL'AMEEN* da Angon ta *SAHABI MAHMUD*
Sai *YUSRA NOOR AL'AMEEN* tare da Angon ta *SULAIMAN HABIB*
*FADILA AL'AMEEN AL'AMEEN* da Angon ta *KHABEER ALH. MUNIR.*
Ɗaurin auren da ya tara dubban jama'a ta ko ina, sai dai mu ce Masha Allah.
Zuwa huɗu ko wacce aka kai ta ɗakin ta bisa umarnin su Big Dady, Fadila aka wuce da ita Katsina da sauran jama'a. Yusra kuma da Shakira duk a nan Kaduna za su zauna, gidan Yusra ma ya fi kusa da gidan su, kuma duk ka su biyun za su ci gaba da aiki a Hospital ɗin su, sabida sai da aka yi yarjejeniya da mazajen nasu kuma sun amince.
Inda Baffa zai zauna kusa da gida ne, gini ne da aka yi musu shi da Usman a gefen gidan su, ga Gate ɗin gidan su ga nasu, sai dai kuma ta ciki a kwai ƙofan da aka yi wanda zai riƙa kai su cikin gidan su, ba sai sun yi wahalan fito wa ta Gate ba, wannan duk tsarin Kaka ne, shi ya siya filin kusa da gida, sabida yafi so iyalan sa su zauna waje ɗaya, har filin Fadil da yake ƙarami akwai shi an ajiye masa, idan ya tashi aure sai ya zauna a nan ɗin
Part ɗin Baffa dana Usman suna kallon juna ne, komi iri ɗaya aka yi musu, ɗakuna uku ko wanne da Toilet a ciki, sai babban Parlour da kichen a ciki da kuma wani Toilet, sannan idan ka fito waje ko wanne yana da faranda a ƙofan ɗakin, komi dai masha Allah, domin ba kaɗan ba an kashe kuɗi a ginin nan, su Big Dady duk suka yi musu komi babu ko ƙwandalan su, kayan ciki kuma suka bar musu su yi da kan su
To Part ɗin Baffa dai ya tsaru sosai, domin zance kuɗi yayi kuka a nan, iyayen Sa'adatu sun kashe mata kuɗi sosai, don ganin sun fito da ɗiyar su, itama zuwa dare aka kawo ta, can babban gidan aka fara kai ta, sai da aka kai ta wajen Kaka yasa mata albarka, sannan su Big Dady suka haɗa su da Baffa suka yi musu nasiha sosai. Daga nan kuma suka wuce wajen Hajja, inda itama tayi wa Baffa faɗa da nasiha sosai, akan "ya riƙe ta da amana, kar taji kar ta gani wajen ya muzguna mata, domin ita ɗin ƴar uwan sa ce, idan kuma aka ce ta kawo ƙarar sa, to wlh sai ta ɓata masa rai".
Shi dai be ce komi ba, har ta ƙarashe faɗan ta ta sallame su, suka nufo gidan su.
Sai mu ce Allah ya ba da zaman lafiya Amare.
⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫
Ɗahira dai taci bikin nan ne ba a daɗin rai ba, domin kuwa fama take yi da matsanancin zazzaɓi me zafi, kowa be san halin da take ciki ba, ko Kaka da take zuwan mishi hira, ƙin zuwa tayi bare ya san me ke faruwa da ita, shima be neme ta ba tunda ya san sha'anin biki ne
Fadila ita ke matsa mata tasha magani, domin sosai take bata tausayi, ita duk a ganin ta tana damuwa ne saboda rashin auren ta, bata san cewa Ɗahira ta kasa jure rabuwan da suka yi ne da Baffa ba, har yanzu abun na cin mata rai, shiyasa dole ciwo ya kamata.
A haka Aunty Amarya ta dawo ta tarar da ita babu lafiya, hankalin ta yayi matuƙar tashi, duba da yanda ta dawo ta ganta gaba ɗaya ta rame a ɗan kwana biyu kacal da ba ta nan, babu wanda ya duba lafiyan ta, har kuka sai da Aunty Amarya tayi, nan ta kira Abbun su take sanar mishi
Shima hankalin sa ya tashi sosai, tare da ɓacin rai da ya nuna a kan Umma, tunda ai ita ce take zaune da su, amma ta kasa kula da ita, ga shi gida ya hargitse da ƴan biki, shi kansa ba kwana a Part ɗin yake yi ba, kuma ko da yana son ganin yaran sa, yawan jama'a bazai bar sa ganin su ba, shi duk a tunanin sa da ita ake bikin
Dole aka ɗaura mata drip, sabida sosai take jin jiki, duk hankalin su Kaka ya tashi matuƙa, irin su Hajja Fatu kuwa murna fal ciki, domin duk a ganin su baƙin cikin rashin auren ta ne ya saka mata damuwa
Su ma su Kaka abinda suke tunani kenan, shiyasa tayi matuƙar ba su tausayi, a ranan Kaka ya zauna da ƴaƴan sa meeting, inda suka yanke shawaran kawai za su haɗa auren Ɗahira da Usman, tunda dai baza su zuba musu idanu suna kallon su sun ƙi aure ba, sai dai babu wanda ya tayar da zancen, sun bari sai nan da kwana biyu, lokacin an gama huta wa da bikin nan da suka yi.
Itama Ɗahiran sosai take samun lafiya, tunda ana kula da ita sosai
Baffa dai sau biyu yana zuwa gaishe ta, yanda Ɗahiran ta nuna masa ne, yasa shi jin daɗi, domin ko kaɗan bata sauya masa daga yanda suke da ba, gaba ɗaya ta nuna masa tamkar wani abu be faru tsakanin su ba, duk da a zuciyarta tana jin ƙaunar sa. Hakan sai ya mishi daɗi sosai, shima sai ya saki jikin sa yana jan ta da hiran da suka saba
A ranan na ukun ne da zai zo, suka taho da Sa'adatu don ta duba ta, amma daƙyar ta taho, don sai da suka yi faɗa da Baffa ɗin, da cewa tayi, "ba ta zuwa" amma da ya nuna mata ɓacin ran sa, dole ta biyo sa
Suna zuwa tayi mata ya jiki ta miƙe zata tafi, sai ta ga Baffa ma gyara zaman sa yake yi be da ninyan tafiya, ta kalle sa tace, "a'a ya haka kuma? Kai da za mu tafi kuma kake shirin zama?"
Kallon ta yayi, sai ya harare ta, sabida akwai Aunty Amarya a wajen, dayake suna zaune a Parlour ne har Ɗahiran. Kawar da kansa yayi ya soma jan Ɗahira da hira
Sai ta ja dogon tsaki tana faɗin, "Da kai fa nake yi ka zauna ina magana?"
A fusace Baffa ya kalle ta yace, "Ni sa'an wasan ki ne wai Sa'adatu? Ni ne zaki tasa a gaba sai ka ce ɗan ki?"
Murguɗa baki tayi ta hau jijjiga jiki, sai dai bata iya cewa komi ba sabida ganin yanda ya taso mata a fusace
Aunty Amarya ce tace dashi, "ya isa haka Miji na, tashi ka tafi tunda baka san me take buƙata ba, ka je kaji ka dawo anjima".
"But wlh Aunty Amarya this girl..."
"ya isa tashi ka je kaji?" Ta katse sa da faɗan haka cikin lallami
Miƙe wa yayi yana kallon Ɗahira da ta kawar da kanta yace, "Sweet sister I'm leaving, I will be back soon, we have something to talk about, Allah ya ƙara lafiya kinji?"
Gyaɗa masa kai tayi, a wannan karon tana kallon sa tayi masa murmushi tace, "to Yaya na, na gode".
Fuuuu Sa'adatu ta wuce ta bar parlour'n
Shima bin bayan ta yayi bayan ya sake yin ma Aunty Amarya sallama
Aunty Amarya ci gaba tayi da ɓare lemon dake hannun ta, a ranta sosai take mamakin abinda yasa Sa'adatu take kishi da Ɗahira, domin tuni ta gane abinda ke zuciyar ta, sai dai kuma bata san cewa da Baffa Ɗahiran tayi soyayya ba
Ɗahira kuwa gyara wa tayi ta kwanta kan two sittern da take kai, tana lumshe idanu tare da faɗa wa duniyar tunani, ita ko kaɗan abubuwan da Sa'adatu take yi ba ya damun ta, amma duk idan ta tuna da yanzu ita ce a makwafin Sa'adatu ɗakin Baffa, abun na mata zafi sosai a zuciya, har ta zubar da hawaye.
⚫⚫⚫⚫
Kai tsaye gidan su suka nufa, Sa'adatu tariga shi isa, inda ta zauna a kan ɗaya daga cikin kujerun parlour'n ta tana faman karkaɗa ƙafa, sosai ta cika tayi maƙil tsaban kishi, ita ko kaɗan yanzu ba ta ƙaunar Baffa ya raɓi Ɗahira, gani take yi hakan zai saka mutanen gida su san me ke faruwa tsakanin su, kuma ta san ako yaushe za'a iya kawo mata ita a matsayin kishiya, tunda ita ɗin ƴar uwan sa ce, baza su yi la'akari da daɗewan auren ba ko rashin sa.
Shigowar Baffa ne ya dawo da ita daga guntun tunanin da ta afka
Kallon ta yayi kamar yanda take kallon sa yace, "ke wai Sa'adatu wani irin baƙin kishi ne kike son ki shigo min da shi gida na? Wato rashin hankalin naki ya kai har ki shiga tsakani na da ƙanwa ta? A kan me zaki riƙa min haka? Ke fa baki isa ki hana Ni abinda nayi ninya ba, kuma idan Allah yace Ɗahira mata ta ce, wlh daga ke har wacce take ɗaure miki gindin baku isa ku hana ba".
Sai kawai yaga ta fashe masa da kuka, cikin kukan take cewa, "wlh tallahi kamar a kunnen Hajja, wato kana nufin Ni da ita ba mu isa mu hana ka kula wancan yarinyan ba ko? Kenan Hajja bata da mutunci a wajen ka? Da kake cewa kar na shiga tsakanin ka da Ƙanwar ka; ai ba Ni ce na raba ku ba, wlh na gaji da abinda kake min, tunda ba ka gani na da mutunci ƙarar ka zan kai". Tana ƙare zancen nata ta tashi fuuuu ta fice tana ci gaba da kukan ta
Direct cikin gidan ta nufa, inda ta wuce Part ɗin Hajja don Kai ƙaran sa.
Ta bar sa nan tsaye da sakakken baki, sosai ransa ya ɓaci da abinda ta faɗa, "kenan shi be da ikon da zai mata faɗa, sai ta ɗibi ƙafafu ta kai shi ƙara wajen Mahaifiyar sa? Anya zai iya wannan auren kuwa?"