Har ya mik'e zai fita ya je ya aiwatar da abin da zuciyar shi ke sak'a mishi, sai kuma wata zuciyar ta hane shi, tana ce mishi ba yanzu ba da sauran lokaci tukun, komawa ya yi ya zauna kan kujera, tare da dafe kanshi, ya cigaba da kitsa munanan tunane tunane acikin ranshi.
Lokaci nata tafiya, yayin da bikin su Meelat da Ado makaho yake ta k'aratowa, yanzu haka saura sati d'aya bikin su, zuwa yanzu idan kaga Ado makaho cewa zaka yi bashi bane, ya murje ya yi kyau, hatta suturun jikin shi masu tsada yake sakawa yanzu, hakama Inna, kuma inda suka birge kowa shine basu manta da wad'anda suka rab'u dasu ba, misali Malam, da Musa, sai Iro d'an jagoran Ado, suna yi musu Alkhairai masu yawa.
Tun da bikin ya k'arato koda yaushe suna tare, suna tattauna yanda bikin zai kasance.
Yau ma kamar kullum Zaune suke a wurin shak'atawar gidan su Meelat suna tattauna wa, Meelat ce ke ta lissafo mishi Abubuwan da za'a yi na shagalin biki tun daga gobe har zuwa ranar asabar, bayan ta gama zayyanowa Ado ya kalle ta, yace " Hajiyata ni in da zaki ji shawara ta ayi walima kawai ta wadatar, ba sai anyi wad'annan abubuwan da kika lissafo ba. "
Meelat tayi magana cikin shagwaba tace " Allah ka daina ce min Hajiyarka, suna me kyau zaka sa min ba hajiya ba, ta zumb'uro baki,
Ado ya yi murmushi, sannan yace " to zab'i sunan da kika fi so a kira ki da shi, tunda bakya son hajiya."
Meelat tace " nafi son ka kira ni da SWEETHART," Ado yace " an gama ranki ya dad'e, har tayi rau rau zatai k'orafi Ado ya yi maza yace au swthrt " dukkan su suka kwashe da dariya, sun cigaba da tattauna wa, ni kuma na kwashe inawa-inawa na yi gaba, domin nemo masu tayani d'auko muku labarin yanda shagalin bikin ya kasance.
RANAR BIKI
Hausawa suka ce rana bata k'arya, se dai uwar d'iya taji kunya, A yau ne ranar d'aurin Auren Masoya biyu wato Ado da Meelat.
Ko ina ka waiga mutane ne ba masakar tsinke, b'ullowa suke ta yi, kama daga kan tawagar Dadyn Meelat, abokan kasuwancin sa, tun daga kan na k'asar nan har fararen fata turawa sai da suka halarci wannan d'aurin aure, daga d'aya b'angaren kuma Malam ne da tashi tawagar Malamai ne gasu nan babu adadi har da d'alibai sun cika wurin.
Dana sake dubawa d'aya gefen Allah sarki bayin Allah, Nak'asassu ne gasu nan Birjik sun sha Anko iri d'aya sak da kalar kayan da Ango yasa, dakakkiyar farar shadda ce mai shegen tsada yai musu anko, kuma abin burgewar shine Ango yana kusa da Nak'asassu 'yan'uwan sa, hakan da ya yi yasa sun ji dad'i, kuma mutane kansu, sun basu sha'awa, shima sai ya burge kowa yanda bai manta da asalin shi ba, duk da daular da yake ciki a yanzu.
Can gefe kuma tawagar 'yan jarida na gani, har da marubuta duk sunzo ba idon su abinci domin lallai wannan Aure abun sha'awa ne da kuma burgewa.
A ranar kam titin nan sam babu hanyar wuce wa, domin mutane ne gasu nan bama ka ganin k'arshen ssu, wani d'an jarida naga ya d'ane sama yana gyara camerar sa, nace kama gama ka sauko ba ganin k'arshen su zakai ba, dan k'ara b'ulb'ulowa kawai suke, gaskiya ranar yanda kasan Ana ruwan mutane, Abin da zai baka sha'awa ma shine duk Drevobi da 'yan acab'ar da yazo wuce wa yaga tarin jama'a, yana tsayawa yai tambaya aka bashi labarin bikin sai kuka sun faka mota ko mashin sun fito suma a d'aura da su.
Bayan kowa ya hallara sai aka d'aura Aure a cikin wani tafkeken masallacin da Dadyn Meelat ya gina, wanda yake gefen titi kusa da gidan su Meelat d'in, Dubban, ko kuma ince Milliyoyin mutane ne suka shaida d'aurin Auren Meelat da Ado Makaho akan sadaki dubu goma, bayan An d'aura, anyi Addu'o'i sannan mutane suka fara raguwa, kowa sai zuwa ake ana yin musabaha da Ango, tare da yi mishi kyakkyawan fatan Alkhairi, sai da aka d'auki kusan Awa biyu sannan mutane suka gama watse wa.
Bayan an watse, sai Ango kawai da abokan shi Nak'asassu, Aminin Ango ne wato Musa a gefen shi, shiga motoci suka yi sai gidan su Amarya Meelat.
A ranar ko ina ka duba lungu da sak'o dake cikin garin kano maganar Auren kawai ake yi, tare da bayyana yanda d'aurin auren ya kasance, gidan redio, gidan Tv, mujallu, da dai sauran su.
Bayan sun iso gidan aka sauke Ango shi da abokansa a wani katafaren d'akin saukar bak'i, tun d'azu dama Meelat ke ta faman dank'arawa Ado kira, wai yak'i ya k'araso kuma tasan tun d'azu aka d'aura.
Yanzu ma itace shirye cikin rantsatsen less me shegen tsada, ta cancad'a kyau, sai ta koma tamkar aljana, dama kyakkyawa idan ya k'ara da kwalliya kyan yai yawa hmmmm ya kuke ganin kyawun zai kasance, nabar masu karatu su tantance a kansu.
Zaune take cikin k'awayen ta, Meelat da Rukeey, sauran duk 'yan uwa ne sa'annin ta, su Rukeey sai faman tsokanarta suke, ganin yanda ta had'e rai, su kuma sai k'ara zugata suke kamar zatai kuka.
Real khady ce tace " gaskiya Ango zai kwafsa mana, ya za'ai mu zauna a b'ata lokaci wajen tsantsara miki kwalliya dan ya gani amma ace shiru har yanzu bai zo ba, salon kwalliyar ma ta b'aci, haba wa nan da nan amarya Meelat tai rau rau kamar zatai kuka, wayarta ta lalibo, tare da k'ara gwada lambar shi, tana kira kuwa Ado dake d'akin bak'i yasa hannu cikin Aljihu ya ciro wayar shi ya d'auka kamar yanda meelat ta gwada mishi zaiyi da hannunshi ya rik'a d'auka tare da kara wa a kunne, tare da cewa " Swthrt! habawa sai da sassanyar muryar shi ta daki zuciyar ta, ta ratsa k'wak'walwar ta, tabi ta cikin jijiyar ta, Shagwab'e wa tayi, sannan tace " kana ina ne, baka d'okin gani na koh? "
Ado ya yi murmushi, sannan yace " banda abinki ina nake da idon ganin ki, ni d'okin da nake na kasancewa tare da ke ne har abada, " haba nan da nan b'acin ran Meelat ya tafi, farin ciki ya maye gurbi.
Meelat tace " kana ina ne? " Ado yace " gani a cikin gidan ku, a d'akin bak'i," haba wa tana jin haka ta mik'e da sauri, tare da fad'in " da gaske, to gani nan zuwa " Aje wayar ta yi, ta k'ara gyara jikin ta, tare da yafa mayafi, kallon inda su Real khady suke tayi, kowacce daga cikin su ta rafka uban tagumi suna kallon ta, Meelat ta yi magana da k'arfi cikin d'aga murya, tace malamai wannan kallon fa, sai kace tsofafin mayu, sannan ta kashe ido d'aya tace musu ya dai zaku kaini wajen Ango na ne, ko kuma in kai kaina? "
Rukeey ce ta kalli Real khady, Real khady ma ta kalli Rukeey, sai Meelat tai ficewar ba tare da ta jira su ba, mik'ewa Rukeey tayi tana fad'in " mu ma Allah ya aurar da mu, Real khady tace " Ameen dai, Meelat sun bani sha'awa yanda suke tafiyar da soyayyar su, har nima naji inaso inyi aure, " Rukeey tace Allah had'a mu da maza na gari, " Real khady tace " ameen dai, tashi muje kar taje ta kai kanta, dan zata aika indai Meelat ce, ace ina muke, tashi suka yi, suka bi bayanta da sauri.
_ni kam da bake bayan k'ofa a b'oye fitowa nayi tare da kwashe wa da dariya, nace ina dariyar shakiyancin naku da kukee wa Meelat ta tafi, ji nayi an bud'e k'ofa za'a shigo nai maza na fita ta window kar a ganni_
Anyi taro lafiya, kowa sai sam barka, Anci ansha, a ranar anyi k'wallo da baman shanu guda goma da aka yanke, a ranar babu wadda tai girki a unguwar, daga gidan sukai ta jida ana aikawa da iyali, kai irin wannan auren yasin shine ake samun lada tun kafin su shiga sun ciyar da bayi ba d'an kad'an ba.
Dare na yi, iyayen Meelat suka kira ta ita da angon ta, suka yi musu nasiha mai ratsa jiki, Meelat sai kuka take na rabuwa da iyaye, Dady ne ya mik'a wa Ado wasu makullai, tare da takardu a had'e, ya ce " wad'annan makullan takardun gida ne, da kuma makullan gidan, na baka halak malak, sannan sakamakon tsarkake zuciyarka da kayi ka auri 'yata ba don dukiyar ta ba, sai domin Allah, na baka kyautar million hamsin, zan sa a bud'e maka account da sunan ka, sai a zuba maka kud'in a ciki."
Ado ya sunkuyar da kai, k'walla na zubowa daga idanun shi, yace " Dady tunda nake ban tab'a tunanin shigowa rayuwa makamanciyar wannan ba, wallahi ban tab'a tunanin Meelat zata auri makaho kama na ba kwata kwata ban tab'a sa hakan a raina ba, nasan ta samu k'arfin guiwar aure na ne daga gare ku, domin Meelat 'ya ce mai biyayya, nasan bazata tab'a yin abinda baku yarda dashi ba, dady Kyautar 'ya da kai min a wannan matsayin nawa da nake ciki kad'ai ya ishe ni farin ciki har k'arshen rayuwa, wallahi dady bana buk'atar komai bayan wannan ku kuka nuna min tsantsa kuma k'olokuwar so a lokacin da kowa ke gudun mu, kun maida ni mai gata, a lokacin da nake cikin maraicin iyaye, bana buk'atar komai sama da wannan da na samu a rayuwata, dan Allah dady kabar kud'in ka da komai naka, kuma nai muku alk'awarin insha Allahu bazan tab'a bari naga Meelat ta shiga cikin damuwa ba har abada, zan saka mata da alkhairi ta hanyar kyautata mata kamar yanda nima kuka kyautata rayuwa ta."
Dady ya kalli Ado yace " Ado ka gode wa Allah, domin na bibiyi rayuwarka kaf tun daga farko, ba komai bane ya kaika shiga wannan matsayin sai Abu biyu, na farko shine juriya da kuma hak'uri da irin yanayin da Allah ya halicce ka, Abu na biyu kuma shine gode mishi da kuma rungumar k'addarar ka da kake a duk yanda rayuwa tazo maka, kuma dama Allah ya yi Alk'awarin muddin d'an adam ya gode wa ni'imar da Allah yai masa to zai k'ara masa, to kai ka kasance d'aya daga cikin masu godiya ga ni'imar da Allah yai musu, shi yasa ya saka maka da hakan, saboda haka ba mu bane muka canja rayuwarka, Allah ne shi zaka gode mawa, sannan babu kyau maida hannun kyauta baya, ka karb'a na bak ne saboda Allah, ko baka auri 'yata ba idan na samu labarinka zan iya taimaka maka fiye da hakan ma.
Dady ne ya sake mik'a mishi takardun gidan, had'e da makullan gidan, Ado yasa hannu ya karb'a tare da godiya sosai, har da hawayen shi.
Dady da Mumy suka sa musu Albarka, tare da yi musu fatan Alkhairi, suka fito Aka shiga da Amarya cikin mota, k'awaye da 'yan uwa suka shiga ragowar aka jasu sai rijiyar zaki, inda gidan da aka bawa Ado yake.
Bayan an kai amarya kowa ya watse, sai Amarya da ango, zama suka yi shiru kowanne daga cikin su yana jinshi a sabon yanayi, Ado kam harda mamaki da yake wai yau shine a cikin wannan matsayin, Meelat kuwa rufe take da wani mayafi har fuskarta ya rufe, se dai tana hango komai ita, kallon Ado tayi, tace " kayi shiru "
Ado yayi murmushi tare da cewa " farin ciki ne ya lullub'e ni, kuma sai ina ganin kamar a mafarki, Allah na gode maka, Meelat nagode da kika zamo silar canjin rayuwata, Inna tana gaishe ki, dan Allah Meelat karki juya min baya nan gaba, karki guje ni, sai kuma yasa kuka. "
_nikam nace ikon Allah, mata aka sani da kuka, amma wannan karon ango shi ya fanshi amarya_
Meelat ce ta b'ata rai, tare da cewa haba mijina, meyasa zan aureka in har zan guje ka a gaba, da zab guje ka tun kafin ka zama mijina zan guje wa auren ka, kasa a ranka mutuwa ce kad'ai zata iya rabamu insha Allah. "
Ado yace " Allah yasa, tashi muje mu yi Alwala, muyi sallah, mu nuna godiyar mu ga Allah, Meelat tace "to" sannan ta tashi cikin sauri domin aiwatar da umurnin mijin ta, taimaka mishi tayi suka shiga ban d'aki, suka yi Alwala, suka fito suka tayar da sallah, Bayan sun idar ya dafa goshin ta, tare da yin addu'ar da addinin islam ya koyar, sannan ya yi mata tambayoyi game da addininta, cikin ikon Allah ta amsa su duka, sannan ya saka ta ta mik'o musu ledar da suka shigo da ita, suka baje kaji a faranti, da farko Meelat tak'i ci, sai da ya yi ta janta da labaruka masu dad'i sannan ya samu taci kad'an, bayan sun gama suka yi wanka, tare da canja kaya, sannan suka yi kwanciyar su, ni kam nace asuba ta gari.
Muje zuwa
urs 🅱K😘💋
[1/7, 10:45 AM] Bk: 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
NAK'ASASSHE MA MUTUM NE
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
Writen by BILKISU Z. YA'U (🅱K)
_(Yar gatan exclusive)_
♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
_(Home of peace, honour and super writer's)_
SADAUKARWA GA: MEELAT A.H.K
Dedicated to:
KHADY LUV
_Kina aminci a fili, kuma kina aminci a zuciya. Na fad'a a fili, kuma na fad'a a zuciya, kece mace me cike da halarci a duniya, Ina sonki so irin mara yankewa d'innan my khadyluv_
Page 65 to 70
[1/13, 11:47 PM] Ruqeey Ce: 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
NAK'ASASSHE MA MUTUM NE
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
Writen by BILKISU Z. YA'U (🅱K)
_('Yar gatan exclusive)_
♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
_(Home of peace, honour and super writer's)_
SADAUKARWA GA: MEELAT A.H.K
Dedicated to:
NAK'ASASSU
_Wannan shafin naku ne NAK'ASASSU, Allah ya cigaba da kare ku da kiyaye ku, Allah ya k'ara muku hak'uri da juriya, Allah yasa ku dace a duniya, ku dace a lahira, Allah ya so duk wanda ya so ku, Allah ya ji k'an duk wanda ya ji k'an ku, wallahi BK tana k'aunarku sosan gaske, wannan shafin naku ne, kuyi yanda kuka ga dama dashi, bamai ce muku dan me_
MEELAT A.H.K
_Ina tayaki murnar fara novel d'inki mai suna_ TASU KALAR TARBIYAR, _Ina makaranta🗣🗣🗣🗣🗣 wallahi karku sake koda wasa novel d'innan tasu kalar tarbiyar ya wuce ku, akwai tarin fad'akarwa aciki, bugu da k'ari idan kana karantawa sai kaga tamkar a zahiri kake ganin abun ke faruwa, gaskiya MY MEELAT dole a jinjina miki wajen aiki da tsantsar basira gun tsantsara labarin daya dace, kinyi nisa karma wanda ya kiraki dan yasin bazakiji ba, kinyi nisa baki waiwayen baya, se dai mu biyo ki a baya, ubangiji ya k'ara d'aukaka ki, Ai na karanta Novel d'in TASU KALAR TARBIYAR, har na k'osa gari ya waye ki k'ara sambad'o mana ci gaban, Allah ya k'ara miki basira kiyta antayo mana novel's masu d'an karen dad'i da tarin fad'akarwa muna k'wamushewa, makaranta karku bari, ku sake, ku yarda, a baku labari, kowa ya nema ya karanta, kada ya wuce ku kuzo kuna cizon yatsa aha_
Page 70 to 75
Dukkan su tsoro suka ji, saboda yanayin yanda suka ji ana dukan k'ofar, har Meelat ta yunk'ura zata je ta bud'e da yake wannan karon da hijaf d'inta a jiki, Ado ya rik'e hannun ta, tare da girgiza mata kai, komawa tayi ta zauna, Ado ya mik'e, tare da dosar inda k'ofar take, ya bud'e wasu mutane ne tsaye su uku, maza biyu sai mace d'aya, wanda yake a gaba da alama shine babban su, yace " Yallab'ai barka da war haka, mu 'yan jarida ne, zamu iya shigowa? "
Ado ya yi ajiyar zuciya, sannan yace " Bismillah ku shigo, " matsa musu ya yi suka shiga suka samu waje suka zauna, Ado shima ya zauna kusa da matar shi.
Bayan sun gaggaisa Wannan mutumin wanda ya yi wa Ado magana yanzu ma shi ne ya yi magana yace " kamar yanda kuka ji mu 'yan jarida ne, kuma wajen ku muka zo, tare da neman alfarma daga gare ku, dan Allah muna gayyatar ku gidan talabijin d'inmu da gidan redion mu domin ayi hira da ku, muna rok'on ku da ku amsa gayyatar mu dan Allah.
Meelat tace " kuyi hak'uri gaskiya babu inda zamu je, Ado ya dakatar da ita ta hanyar d'aga hannu, sannan yace " yi shiru muji dalilan su akan haka, ko fad'a mana abinda yasa kuke so muyi hira daku, kuma akan me za'a tattauna? "
Shugaban su ya gyara zama sannan yace " Abinda yasa muke so muyi hira daku shine, na farko gaskiya kun burgemu ne, shine muke so a haska ko ina tare da k'wak'waran dalilan kasancewar ku tare, sannan kunga yin hakan zaisa mutane da dama su k'aru tare da fa'idantuwa akai, Nak'asassu zasu samu rangwamen irin abubuwan da ake yi musu, kuma idan aka yad'a kowa ya gani zasu so, suyi koyi da hali irin naku tabbas, kuma tambayar zamu so mu fi yiwa matarka ita ne, babban dalilinmu kenan. "
Ado yace " yaushe ne za'a gabatar da shirin? "
Mutumin yace " rana ita yau, ranar lahadi kenan. "
Ado yace " Allah ya kaimu, zamu yi shawara da ni da matata, tare da iyayen mu, in har sun amince shikenan. "
Mutumin nan ya yi godiya, sannan yace " ga number ta duk shawarar da kuka yanke sai ku sana damu, mungode sosai," ya bashi lambar wayar shi, sannan suka yi musu sallama.
Bayan bak'in 'yan jarida sun tafi sai Ado yace " SWTHRT me kika gani akan maganar mutanen nan, kin amince da buk'atar su? "
Meelat tace " in dai saboda dalilan da ya kawo ne to na amince, amma mu sanar da su Dady tukun. "
Bayan kwana biyu da yin wannan maganar sai suka shirya suka je gidan iyayen Meelat, kuma suka taki sa'a Dady yana nan, bayan an gaggaisa, sai Ado ya fad'a wa Dady abin da ke tafe dasu, game da hira da akeso ayi dasu wadda ta shafi auren su.
Bayan ya gama fad'a mishi Dady ya bada goyon baya akai, mumy ma haka, bayan sun d'an jima sannan suka tashi suka tafi gida, suna isa gida yasa Meelat ta saka mishi lambar wannan mutumin acikin wayar shi, bayan ta saka yace ta kira, bayan ta kira ta tabbatar ya d'aga sannan ta kara mishi a kunne, bayan sun gaisa da mutumin ya tabbatar da amincewar su d'ari bisa d'ari, tare da tabbatar mishi cewa ranar lahadi suna kan hany, mutumin ya yi mishi godiya sannan suka yi sallama ya aje wayar.
Tun kafin lahadin, tun daga ranar da suka yi waya da mutumin nan suke ta jin sanarwar tattaunawar da za'a yi dasu ta kafofin yad'a labarai, a rana sai an sanar sau wajen biyar, kowa ka gani jiran zuwan ranar kawai yake yi.
RANAR LAHADI
Su Meelat ne zaune a cikin gidan nan na arewa sun sha ankon shadda, hatta kwalliyar jikin shaddar iri d'aya aka yi musu, abin gwanin birgewa za'a fara gabatar da shirin kamar yanda aka tsara
Mik'a musu abin magana ya yi, tare da saita camera saitin su yanda kowa zaiga abinda ake gudanarwa, sai da suka gama dai-daita komai sannan wannan mutumin dake zaune kusa dasu ya kalle su yace " to zamu fara kun shirya?" suka ce " eh," juyowa ya yi, ya fara gabatarwa kamar haka:
_JAMA'A ASSALAMU ALAIKUM, BARKAN MU DA WAR HAKA, BARKAN MU DA SAKE SADUWA A CIKIN SHIRIN_
《》DUNIYA GIDAN ARO《》
_WANDA NI ABBA NA SHIRYA KUMA ZAN GABATAR, BAK'IN MU NA YAU SUNE MA'AURATAN DA BABU IRIN SU, WATO MEELAT DA ADO, INA FATAN KOWA ZAI K'ARA MURYAR AKWATIN REDION SHI GA MASU JINMU A REDIO, GA MASU KALLON MU IDO DA IDO KUMA SAI SU K'ARA K'ARAR TELEBIJIN D'IN SU."_
Nass dake zaune a d'akin shi yana duba hisnul muslim, kamar daga sama yaji sanarwa a tv, kallon tvn ya yi, yare da tattara hankalin shi a kai.
_Abba ya juya gun su Meelat yace " bak'in mu na wannan satin muna muku barka da zuwa wannan gida namu me Albarka "_
_Meelat da Ado suka amsa a tare " yauwa, jama'a assalamu alaikum "_
_ABBA: " shin ko zamu iya jin tak'aitaccen tarihin ku, ma'ana tarihin rayuwarku har zuwa tarihin soyayyar ku? "_
_Ado ne ya gyara zama tare da kwararo musu bayani daga farko har k'arshe, sannan itama Meelat ta bada nata tarihin rayuwar ta._
ABBA: " _Masha Allah, yanzu zamu karkato da tambayar mu gareki Meelat kafin mu dawo kan Ado, shin ko zaki iya fad'awa masu saurare abin da ya ja ra'ayin ki wajen zab'ar Nak'asasshe wato Makaho a matsayin mijin aure?_ "
MEELAT: _Amsa wa tayi a tak'aice tace " saboda shima mutum ne kamar kowa,"_
ABBA: _murmushi ya yi, sannan yace " tabbas maganarki haka take, amma zamu so jin abin da yaja ra'ayin ki ga zab'ar shi ne a matsayin miji?_ "
MEELAT: " _farko dai tausayin yanayin rayuwar da ya shiga ne a raina, daga baya kuma halayen shi kyawawa, da rik'o da addinin shi duk da baya gani, da kyakkyawar mu'amala da mutane suka ja ni ga auren shi, wanda na tabbatar samun irin shi sai an tona, haka zalika kafin a samu bara gurbi a cikin su sai an sha wahala gaskiya, saboda isu-isu Nak'asassu suke yin rayuwar su, kuma koda yaushe suna waje d'aya, wasu daga cikin su makafi ne, basa gani balle su sakawa ransu dogon buri a duniya, wasun su kurmaye da bebaye ne, basa magana kuma basa jin maganar kowa, kaga basu ji ba ma balle Abin duniya ya dame su, sannan wasun su guragu ne, to wad'annan ma su ta kansu suke yi, wajen barar ma dak'yar suke iya k'arasa wa, kuma kowanne daga cikin su abinda zai baka sha'awa dasu, kuma ya birge ka shine dukkan su sun fawwalawa Allah lamuran su, sun d'auki k'addarar su ta rayuwa, sun ci gaba da rayuwar su kamar kowa, sannan abin birgewa suna da had'in kai sosai._ "
ABBA: _Allah sarki, Allah ya cigaba da tallafawa rayuwar su, ko zaki fad'a mana Abu d'aya daga cikin abin da ake musu wanda yake baki haushi, ko kuma yake baki tausayi?_"
MEELAT: _Abu d'aya ne zuwa biyu, farko yanda ake gudun Auren su tamkar su suka halicci kansu, sai abu na gaba, yanda bama son yin mu'amala dasu, tsakanin mu dasu kawai mu basu kud'i mu wuce, bayan kowane rai yana buk'atar tallafi a rayuwa, ko'in kula da muke nuna wa a garesu yasa wasu daga cikin su suke jin duniyar tayi musu zafi, suji dama sun mutu sun huta,_"
tana kai nan a maganar ta sai ta fara kuka, ikon Allah, ashe ba ita kad'ai ba, hatta masu sauraro da dama kuka suke yi, ciki kuwa har da NASS da ke zaune shima yana kallo
ABBA: _Allah sarki, gaskiya babu dad'i kam, yanda ake yi musu sam babu kyautawa a ciki, domin suma mutane ne, kuma Allah ne ya halicce su, daga k'arshe shin wane irin kira, ko jawo hankali zaki yi ga mutane akan Nak'asassu?_"
MEELAT: _farko shawarata a gare su shine su ji tsoron Allah su daina wulak'anta Nak'asassu, suma mutane ne, kuma da ace bawa yana da ikon tsarawa kanshi rayuwar yanda yake so ya kasance to tabbas da babu wanda zai zo duniya a nak'ashe, kuma mu sani, ku ko ni kai kowa ma be da masaniyar ya kamannin shi zai kasance a gaba kafin mutuwar shi ta riske shi, in har muna tuna haka baza mu rik'a guje musu ba, saboda suma halittar su aka yi a haka basu suka halicci kansu ba, wasu kuma daga cikin Nak'asassun ma lafiyayyu ne tun farko, amma daga baya Allah ya jarabce su, ko ta hanyar hatsari da makamantan su, to idan kana tare da mutum hakan ta faru dashi sai ka guje shi? gaskiya muji tsoron Allah, mu sani cewa duk wani d'an adam me daraja ne har a wajen Allah (s.w.a), saboda ya fad'i acikin Qur'ani mai girma cewa ――hakika ya karrama bayin sa―― To Allah ma da ya halicce mu ya karrama mu, mu menene namu na wulak'anta juna ko gudun junan mu, gaskiya muji tsoron Allah, mu sani idan muna k'in bayin Allah ta dalilin halittar su tamkar muna jayayya da Allah ne tunda shine mahaliccin kowa._ "
ABBA: _tabbas abin da kika fad'i gaskiya ne, to wane irin jan hankali zaki yiwa mata da maza wad'anda ke shirin yin aure akan Nak'asassu?_ "
MEELAT: _" da zan basu shawara suji to da sun yi ta auren Nak'asassu, idan mace ce ta auri nak'asasshe to, babu ita babu tashin hankalin wata wai ita kishiya domin kuwa koda yaushe tana mak'ale da mijin ta, yana ta kanshi yaushe zai ma yi tunanin yin wani auren kuma, saboda haka duk wadda bata k'aunar kishiya to taje ta auri Nak'asasshe ta zauna lafiya abinta, kuma zata sha soyayya, domin sun iya kulawa da iyalan su,_
_shawara ta ga maza kuma idan sun tashi yin aure to su auri nak'asasshiya, babu su babu tension d'in matan zamani, su nak'asassu daman bayin Allah ne, sai yanda ya juya ta, sannan zasu ga biyayyar aure fiye da tunanin su, ina k'ara fad'i cewa tabbas wallahi yawancin Nak'asassu sunfi wasu masu lafiyar komai, se dai su nuna musu kyau ko kyan lafiyar jiki._"
ABBA: _"masha Allah, ina fatan duk wad'an da suke da niyyar aure sunji shawarar Meelat a garesu, shin wane shawara zaki baiwa wad'anda a yanzu haka suke zaune gidan aure da nak'asassu, ma'ana wad'an da suke auren nak'asassun?_"
MEELAT: " _to shawara ta a garesu shine suji tsoron Allah, su sani cewa akwai mala'iku hagun su da daman su, su sani aure ba abin wasa bane, wato babban abin tausayi shine Nak'asassu masu kud'i zaka ga_ _yawanci ana auren su ne dan dukiyar da suke tare da ita, daga k'arshe in anyi auren suyi ta zagayawa suna cin amanar matan su, yaje yana bin matanr banza kuma yana facaka da dukiyar iyayenta, idan mace ce itama haka, zata bar mijin ta a gida saboda nak'asasshe ne, taje tana bin mazan banza kuma tana facaka da dukiyar su,_ _wallahi nak'asassu masu kud'i suna matuk'ar bani tausayi, domin da wuya a sosu dan Allah, sai dan dukiyar su, sannan basa tantance irin son da ake musu mafi yawancin su, to duk wad'anda suke cin amanar aure kama daga masu zaune da nak'asassu har zuwa kan lafiyayyun su sani cewa akwai mutuwa, kuma akwai hisabi, mu daina d'aukar_ _duniyar nan kamar gidan zama, mu daina d'aukar aure abun wasa, aure bautar ubangiji ne, muji tsoron Allah tun kafin ya_ _horamu da azabar sa, jin dad'in duniya k'alilan ne, na lahira ne madauwami_"
ABBA: _"masha Allah, na tabbatar milliyoyin mutane ne ke sauraren wannan shirin, saboda haka wane shawara zaki bawa dukkanin mutane da kuma dukkanin ma'aurata?_ "
MEELAT: _" shawara ta ga dukkanin ma'aurata shine inhar sun yarda da cewa aure bauta Allah ne, kuma sunnar manzo ce, sannan in har mun yarda da cewa duniya makaranta ce, kuma gidan d'aukan sakamako walau me kyau ko mara kyau, to in har mutane suna tuna haka to wajibi ne su aje jin dad'in duniya, su aje dogon burin dake ransu su rungumi bautar Allah da gaskiya wato aure, tabbas duk wanda ya tsarkake zuciyarshi akan koma menene to Allah zai taimake shi, saboda haka bar bari rud'in duniya ya rud'e mu,_
_shawara ta kuma ga dukkanin mutanen duniya shine su sani cewa Nak'asasshe ma fa mutum ne, kuma tabbas ko kaffara bazan yi ba idan na rantse akan yawancin su sunfi lafiyayyun jin tsoron Allah, kuma babu wanda yafi wani a wajen Allah sai wanda yafi jin tsoron sa, kuma babu Nak'asasshe sai jahili "_
ABBA: " _tabbas babu nak'asasshe sai hahili, kuma nak'asasshe ma mutum ne, malama Meelat mungode sosai da amsa gayyatar mu da kuka yi, Allah ya saka muku da Alkhairi, bari na karkato gare ka da tambayoyi na malam Ado, shin zaka iya sanar damu dalilin da yasa ka amince da auren Meelat duk da irin matsayin ka da kuma yanayin da Allah ya halicce ka aciki?"_
ADO: " _to Alhamdulillah wato a ko'ina ina fad'i bayan inna ta, da malam, sai d'an jagora na Iro, a duniya babu wanda ya tab'a yimin halacci sama da Meelat, itace ta sa na tabbatar da nima mutum ne kamar kowa, kuma ta tabbatar min da zan iya rayuwa me kyau kamar kowa, koda yaushe tsakanina da ita sai kyautatawa, tunda muka yi aure bamu tab'a samun sab'ani ba a tsakanin mu, koda yaushe rige-rige muke yi wajen kyautata wa juna, itace ta nuna min so a lokacin da kowa ke gudun mu, tai mana kyakkyawan kallo a lokacin da kowa ke wulak'anta mu, a sanadin ta 'yan uwana nak'asassu suke rayuwar jin dad'i a yanzu, ni ko me zai hanani amince wa mata 'yar aljanna insha Allah irin wannan, wallahi ban tab'a tunanin zan kasance a cikin wannan halin da na tsinci kaina ba, ina godiya ga Allah, Allah ya saka mata da gidan aljanna."_
ABBA: " _Allhamdulillah, dama bawa baya cire rai da rahamar ubangiji, to wace shawara zaka baiwa mutane da kuma Nak'asassu 'yan uwan ka? "_
ADO: " _shawara ta ga 'yan'uwana Nak'asassu shine su ci gaba da hak'uri, tabbas me hak'uri yana tare da Allah, kuma su ci gaba da rungumar k'addarar ubangiji, sakamakon su yana gare shi_,
_shawara ta ga Mutanen duniya kuma shine muji tsoron Allah,mu tuna duk inda yake yana kallon mu, kuma duk wanda yaji k'an wani Allah zai ji k'an shi, sannan in har mun yarda Aljannar Allah muke nema to mu nisanci rud'in duniya, mu fuskanci abinda zai sada mu da ita."_
ABBA: " _to masha Allah, bak'in mu Allah saka muku da alkhairi, to jama'a kun dai ji yanda tattaunawa ta kaya tsakanin mu da ma'auratan nan biyu, wad'anda suke zaune da juna da zuciya d'aya, wad'anda su lahirar su kawai ita suke hange ba sharholiya da jin dad'in duniya ba, muna fatan masu kallon mu zasu yi koyi da hali irin na mutanen nan, kuma duka duka anan muka kawo k'arshen wannan shirin namu na_ 《》DUNIYA GIDAN ARO《》
_Bak'in mu Allah ya saka muku da alkhairi, amsa gayyatar mu kawai da kuke ya tabbatar mana da ku mutanen k'warai ne, baku da girman kai irun na wasu masu kud'in, munji dad'i sosai, kuma mun gode, Allah ya k'ara muku dank'on k'auna, ya k'ara tsarkake muku zuciyarku, Allah ya cigaba da sanya haske acikin rayuwar Auren ku, Allah ya zaunar daku lafiya, ya baku zuri'a d'ayyiba."_
_Meelat da Ado a tare suka amsa da " ameen_ "
ABBA: " _to jama'a anan muka kawo k'arshen tattaunawar mu ta yau, da manyan bak'in mu na yau wato Ma'auratan da babu irin su Ado da Meelat, muna musu fatan Allah maida su gida lafiya, ni Abba da na shirya na gabatar nake cewa Assalamu Alaiku_
Muje zuwa
🅱K😘💋
[1/13, 11:47 PM] Ruqeey Ce: 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
NAK'ASASSHE MA MUTUM NE
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
Writen by BILKISU Z. YA'U (🅱K)
_('Yar gatan exclusive)_
🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚
♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
_(Home of peace, honour and super writer's)_
SADAUKARWA GA: MEELAT A.H.K
Dedicated to
REAL KHADY (PRINCESS)
_Allah ya k'ara miki lafiya, yasa kaffara ne, Allah ya d'orar da lafiyarsa gareki, ya yaye miki dukkanin damuwarki, BK na mugun yinki da k'aunar ki over, wannan shafin naki ne ke kad'ai_
Page 75 to 80
Ana tashi daga shirin da ake gudanarwa su Meelat suka wuce gida, ko ina ka duba maganar bayin Allahn nan kawai ake yi.
Wasu samari na gani zaune, banda hirar su Ado makaho babu abinda suke yi, wani saurayi ne d'aya daga cikin wad'an da suke zaune a majalisar ya kalli dukkanin mutanen wajen yace " gaskiya bayin Allahn nan sun tunatar damu, nima insha Allah Nak'asasshiya zan aura," wanda yake kusa dashi sai yace " nima haka da yardar Allah," haka dai suka yi ta tattauna wa a tsakanin su, ni dai ina gefe ina jinsu, suna cikin haka sai ga wani mutumi yazo a mota ya wuce, wani gida dake kusa dasu ya shiga da motar ciki, sai wanda ya fara magana tun farko yace " kunga wannan mutumin da ya wuce irin su Meelat tai magana akai, shima fa matar shi makauniya ce, kuma dukiyar mahaifinta yake kai amma saboda baya tsoron Allah kullum sai ya rakici 'yan mata, haba ina jin haka da sauri na na fad'a cikin gidan domin inji yanda zata kaya ayau.
Ina shiga na tarda mutumin yabi wata hanya, da sauri na nabi bayan shi kar ya b'ace min, dan gaskiya gidan k'aton gida ne.
Yana yin kwanar dama wata k'ofa naga ya bud'e, tare da doka sallama, amma garin sauri bai tsaya ya rufe k'ofar ba, ni kuwa na lek'a da kaina, wata kyakkyawar mata na gani zaune a kan 2 sita baiwar Allah, amma makauniya ce kamar yanda samarin nan suka fad'i, sannu da zuwa tayi wa mijin nata, zama ya yi a kusa da ita tare da k'ura mata ido, tunani yake ina hankalinshi yaje da har ya fita yana neman matan banza a waje bayan matar shi tafi dukkanin matan da yake kulawa, sunan ta ya kira, ta amsa, sannan ya duk'ar da kai kamar tana ganin shi, yace " dan Allah ki yafe min duk abinda nayi miki da wanda kika sani da wanda baki sani ba, ayau ina takaicin irin zaman da muka yi dake, ina nadamar rayuwar da nayi a baya, ki yafe min," matar tace " na yafe ma duniya da lahira, Allah ya yafe mana baki d'aya. "
tun daga ranar yanayin zaman su ya sauya, banda tattali da kyautatawa babu abin da yake yi mata, ya tattara duk wani gangar shaid'an ya dank'awa shed'an kayansa.
………………………
Bangaren Nass kuwa a ranar da yaga wannan shirin da aka yi da su Meelat ya k'ara kusantar da kanshi ga mahaliccin shi, kuma a ranar ya yi kukan rasa mace kamar Meelat, se dai ya k'uduri aniyar kamanta hali irin nata, kuma a koda yaushe ya yi Sallah yana mata Addu'a ita da mijin ta, domin sune silar dawo dashi kan hanya.
Yau ma kamar kullum yana zaune a babban falo, haka Nass ya koma, idan har ba masallaci zashi ba ko d'aukar karatun litattafan addini da yake zuwa wajen wani malami, to babu abinda yake fitar dashi daga gida, Allah kenan me canja bawa a duk lokacin da yaso, gashi sa shagalallen yaro kamar Nass amma Allah ya shiryar dashi, Allah ka shiryar damu baki d'aya, ka k'ara kusanto da ruhin mu gareka.
Iyayen shi ne suka fito daga cikin d'aki, suka k'araso falon suka sami waje suka zazzauna, Nass yai maza ya tashi daga kan kujera ya sami waje a k'asan kafet ya zauna, sannan yace " Mumy Dady barka da fitowa," a tare suka amsa suka ce " yauwa, " cike da farin cikin canzawar d'an nasu.
Dady ya kalli Nass sannan yace " Nass nayi maka maganar d'iyar abokina amma baka ce komai ba," Nass ya duk'ad da kai sannan yace " Dady kayi hak'uri ka bar maganar wannan yarinyar, Natsatsiyar yarinya nake nema, kuma Nak'asasshiya nake so, ko gurguwa, ko makauniya, ko kurma, ko ba kyakkyawa bace, in dai tana da kyan hali to zan aure ta, kuma zan zauna da ita tsakani na da Allah. "
Dady da Mumy a tare suka zazzaro ido suna kallon shi, Dady yace " ka manta matsayin ka ne halan, ka rasa wadda zaka ce zaka aura sai Nak'asasshiya, to bada amincewar mu ba. "
Nass ya gyara zama sannan ya basu labarin Meelat da abinda ya faru a tsakanin su, sannan ya kunna musu recordin d'in da ya d'auka na hirar da aka yi da su Ado acikin shirin duniya gidan aro, bayan sun gama saurare sai Nass ya kalli iyayen nashi da jikin su ya gama yin sanyi, yace " Nak'asassun da kuke gudu d'aya daga cikin su shi ya yi silar canzawar rayuwata, Adon nan da kuke gani shi ya tunatar da ni, tunatarwar da ku kanku baku tab'a zaunar dani kunyi min ita ba, saboda haka dan Allah na rok'e ku ku barni na auri zab'ina, idan kun amince akwai wata yarinya dake nan kusa damu, amma kurma ce, se dai na yaba da dukkanin d'abi'u da kuma halayen ta, in kun amince sai ku nema min auren ta, Nass ya mik'e sannan yace naji an fara kiran sallar azahar bari naje masallaci na dawo. "
Dady da momy sun dad'e suna nazarin maganar Nass da kuma wanda suka ji a recordin tare da tattaunawa a tsakanin su, daga k'arshe suka yanke shawarar Aura mishi wadda yake so, tunda shi yaga zai iya kuma shi zai zauna da ita ba su ba.
A cikin sati d'aya aka kai sadaki da tarkacen aure, harda su lefe duk gabad'aya kuma aka tsaida ranar biki, rayuwa kenan su nass an shiryu kuma an kusa zama ango.
B'angaren su Meelat kuwa, har gida aka yi ta zuwa ana yi musu godiya saboda irin jawo hankalin da suka yi a shirin duniya gidan aro, haka rayuwar su ta ci gaba da gudana cikin aminci da yardar juna, yanzu haka Meelat tana d'auke da juna biyu wanda ya kai wata hud'u.
Yau asabar, kuma a yau ne dubbanin mutane suka shaida d'aurin auren Nass da matar shi mai suna Zainab, kuma a ranar yamma nayi aka kawo mishi ita gidan shi da yake kabuga, se dai muce Allah ya zaunar dasu lafiya.
BAYAN SHEKARA D'AYA
Ado ne zaune a kan kujera kusa da shi musa ne yake ta faman godiya, sakamakon kud'i da Meelat ta bayar aka bud'e mishi wani k'aton shago na atamfofi shadda, lesuna, ga takalma da jakunkuna, kai duk wasu kayan k'awa na maza da mata akwai su a ciki, tare da iro suke zaune a shagon, shine ado yazo godiya.
Wata yarinya na gani kyakkyawa kamar su d'aya sak da Meelat ta rugo da gudu wajen Ado ta d'are cinyar shi tana Gwarancin ta, Yasmeen kenan, yarinyar da Allah ya azurta su Meelat da ita kenan, 'yar shekara biyu a duniya, tana ta yi musu gwaranci suna yi mata dariya, Meelat ce ta fito daga d'aki, d'auke da lemo a tray, ta aje gaban Musa, sannan ta samu waje ta zauna, suka gaisa da Musa, ita ma yai mata godiya.
Suna cikin hira ne suka ji an kwad'a sallama, dukkan su suka amsa, tare da bayar da izinin shigowa, Nass ne shi da matar shi, wadda take da tsohon ciki haihuwa yau ko gobe, bayan sun sami waje sun zauna aka shiga gaggaisa wa.
Bayan sun gama gaisawa ne Nass ya kalle su duka, sannan yace " sunana Nass duk da nasan bazaku manta da ni ba, saboda irin abubuwan da na aikata muku, wannan matata ce, se dai kurma ce bata magana, matar tashi ce ta gaishe su da irin gaisuwar su ta kurame, sannan Nass ya cigaba da magana " nazo ne ni da matata domin neman gafararku akan abin da nai muku, tare da godiya me tarin yawa, tabbas ku alkhairi ne acikin rayuwata musamman ma kai Ado, sanadin ka komai nawa ya sauya, har bana so na tuna da rayuwar da nayi a baya, a kullum cikin yi muku addu'a nake Allah ya saka miku da gidan Aljannar sa, yasa ku gama da duniya lafiya, kuma in babu damuwa inaso a cigaba da zumunci, zumuncin mu ya d'ore har k'arshen rayuwa. "
Ado ya yi murmushi wanda ke bayyanar da tsantsar farin cikin shi akan wannan al'amari, sannan yace " wallahi mun dad'e da yafe maka har cikin zuciyar mu, mun manta da wani abu ya tab'a had'a mu da kai ko swthrt? " ya juya yana tambayar meelat.
Meelat tace " hakane mun manta da komai tun tuni Allah ya yafe mana baki d'aya, Allah ya baku zaman lafiya kai da matar ka tare da zuri'a d'ayyiba," gaba d'aya d'akin suka amsa da "
ameen "
Meelat ta ja Zainab suka yi d'akinta, yayin da suka bar su Ado suna hirarsu suma harda shewa tamkar sun dad'e da sanin juna.
ALHAMDULILLAH
_NAN NA KAWO K'ARSHEN NOVEL D'INA ME SUNA NAK'ASASSHE MA MUTUM NE,_
_INA ROK'ON MAHALICCIN MU ALLAH ABIN DA NAYI KUSKURE YA YAFE MINI, WANDA NAYI DAI DAI KUMA YA BANI LADAN,_
GAISUWA DA GODIYA GA: EXCLUSIVE WRITER'S FORUM,
_BAZAN TAB'A MANTAWA DAKU BA HAR ABADA, DOMIN KUWA HAR IN MUTU BAZAN DAINA K'AUNARKU BA, ALLAH YA SAKA MUKU DA ALKHAIRI, ALLAH YA K'ARA HAD'E KANMU TARE DA K'AUNAR JUNA_
MY BLOOD,
_KYAKKYAWAR YARINYA ME KAMA DA BALARABIYA, ME KYAWUN TARBIYYA TAMKAR DAGA SAUDIYYA, NAGODE WA ALLAH DAYA BANI MASOYIYA, WALLAHI KE TA DABAN CE, SHIYASA KOME NAKE YI SAI NA TUNA DAKE, ALLAH YA BARMU TARE_
KHADY LUV
_'YAR'UWAR K'WARAI, KOME NA ZAMA A KO'INA NAKE KINA RAINA, BAZAN TABA MANTAWA DAKE BA, INA MATUK'AR K'AUNARKI TARE DA ALFAHARI DAKE_
JANNART LAMEEDO
_MY JAAN KINA CIKIN RAN BK, A DUK INDA KIKE KI TUNA DA HAKAN KINJI MASOYIYA, ALLAH YA K'ARA MIKI LAFIYA_
MASOYANA
_NA NESA DA NA KUSA, NA FILI DA NA B'OYE, WALLAHI INA K'AUNARKU, SANNAN KUMA INA YIN KU, KUMA KUNE ABOKAI NA,, GODIYA A GAREKU🙏🏻😘_
_DAGA K'ARSHE BK KE CEWA NAK'ASASSHE MA MUTUM NE, KUMA BA NAK'ASASSHE SAI JAHILI,_
_SAI KUN JINI A SABON NOVEL DINA NAN BADA DADEWA BA_
ASSALAMU ALAIKUM🤝