A hankali ya sauke ajiyar zuciya wadda take nuna tsananin farin cikin da yake ciki, “Hii there My Queen, My Happiness, My Amour, My Bride! Sunayen naki suna da yawa fa, amma kullum zan dinga kiran ki da guda daya wanda nasan sai mun dauki shekara basu kare ba, how are you?" kunya ta kama ni na sadda kaina kasa, yau ko sallama ban iya nayi ba balle in gaida shi, haka kawai naji wani nauyi da matsananciyar kunyar shi sun dabibaye ni.
A hankali kuma kamar wadda aka tursasa na bude baki nace “Ina yini Abbu?!" ni kaina sai da nayi mamakin muryata, it was very low kamar wadda take rada, ban yi tunanin yaji abinda nace ba sai da naji yaja wani sharp breath har yana hadawa da lumshe ido, “Masha Allah!" ya furta a hankali yana kallona da lumsassun idanuwan shi, ya Allah!! Da ace yasan yadda kallon yayi affecting dina da yayi gaggawar dauke idanunshi daga kaina saboda nasan ba zai so amaryar shi ta zube kasa kila hakan yayi sanadiyar karyewar kafarta ba, sai ya ci gaba da kallona kawai. Na samu nace “Ya hanya?" duk don in katse kallon da yake jifa na dashi da kuma hirar da zukatanmu suke yi, yace “Alhamdulillah, akwai gajiya kam amma tunda mun iso lafiya ai shikenan, besides ni tunda na ganki ma naji ni kamar an dauke min duk gajiyar dake tattare dani" nayi kasa da kaina, yace “Dad dinki ya bada sakon gaisuwa a kawo miki, ya damka min amanar ki har sai da sashen karbar sakonni a kwalwata ya cika, he even threatens me, heol!!" ya wani yi rolling idanu tare da dan chuckling, na kalle shi ya haske ni da murmushin nan nashi da yake sa ni yin abin da ban shirya ba, ba shiri na sakar mishi murmushin. Yayi cocking kanshi gefe guda, “ko ke fa! Keep smiling like that baby, yau fa rana ce ta musamman a gare mu bai kamata ace murmushi ya kau daga kan fuskar ki ba.... Hmm, how I wish gidana za a kaiki yau din nan, da sai na nuna miki kaunar da babu namijin daya taba nunawa wata ‘ya Mace a duniyar nan, na saka ki a cikin farin cikin da baki taba tsintar kanki a ciki ba, amma tunda hakan ba zai samu ba zan rike komi har sai an kaiki gidana baby, ranar...." sai kuma yayi shiru yana girgiza kai, “it will be a surprise, sai kin zo kawai zaki gani" ya duba agogon hannunshi, motar ya bude ya fito da leda ya miko min, tun kafin in amsa nasan ko menene a ciki, kaza ce gasasshiya sai tashin kamshi da tururi take yi, yace “bana son farin cikin ciyar da amaryata a daren aurenmu ya wuce ni duk da cewa ba ni da kaina zan ciyar dake ba" nasa hannu na amsa tare da mishi godiya, yace “you must be tired, jeki ki kwanta, nima zuwa zan yi inyi barci don ji na nake yi very exhausted Allah ma dai yasa in iya yin barcin" ni dai ban tanka mishi ba na daga Baki da kafa a lokaci guda nace “sai da safe".
Suddenly naji an janyo hannuna an dawo baya dani, kafin inyi yunkurin kwace hannuna da kaina gabadaya ko kuma ma in tantance abinda ya faru na tsinci kaina akan faffadan kirjin Abbu, yasa hannu daya ya dago habata ya kalli tsakiyar idanu na, abubuwan dana karanta a idanunshi a lokacin suna da yawa, zallan so, tsabar kawa, raw lust Ya Allah I couldn't take it, idanuwana na kame don ba zan iya cigaba da karbar sakonnin dake fita daga cikin idanunshi ba, naji hucin numfashin shi akan fuskana ban taba kawo komi ba sai da naji bakin shi akan nawa, it was as if duniya ta tsaya cak da juyawa, ya dago ya kalli fuskana da idanuwan suke rufe yace “it's something that I've wanted to do decades ago but being the good man I am holding it in, I Love You Nafeesah!!" abubuwan sun yi wa kwalwa ta yawa a lokacin har na rasa da wanne iri ne zan ji, his sudden kiss ko kuma sudden kalmar yana so na daya furta?? Na daga idanuna da suka min nauyi na sauke su a fuskar shi, kallona yake fervently, sai naji ni kamar wata danyar nama a gaban zaki, da dan sauri na janye hannuna daga nashi hannun, cikin sauri na juya na fara tafiya ina jin kamar wadda ake turawa don har ga Allah ban san ina nake jefa kafa na ba, ni kaina nasan ikon Allah ne ya kaini daki, nayi jifa da ledar daya bani akan slab na zube akan gado kamar kayan wanki na rufe kaina rikib da bargo, Firdausi ta bini da kallo baki a bude naji dadi da bata yi magana ba. Allah kadai yasan lokacin dana share a kwance a cikin bargon nan, daga karshe dai na mike saboda ihun da cikina yake yi na yunwa, tun macaroni din da muka ci da Ramlah da rana ban kara cin komi ba, na sauka daga kan gadon na dauki plate na bude ledar har da yoghurt a ciki mai sanyi duk da zafin kazar ya rage mishi sanyi, na dora ta akan plate da fork da er wuka na kai kan dan karamin bench da muka mayar kamar dinning na dora, na dauko kofuna da yoghurt din suma na ajiye, da hannu na wa Firdausi nuni alamun ta taso don ba zan iya daga baki in mata magana ba ma. Ta taso ta zauna a gefena tana wabi smirking, “Anya zan iya cin kazar amarcin nan kuwa? Idan aka tashi tambayana ita ya zan yi kenan?" nayi banza da ita na fara cin kazar, itama ta fara ci. Tace “ni naga kin wani firgice ne ko dai anyi abin ne?" na harareta tayi dariya kasa-kasa tace “dama sai dana gaya miki ai, mu dai ki rufa mana asiri ki bari sai mun kaiki kafin ki samu ciki kinji??" nan ma ban tanka mata ba, to ai ko nayi niyar tanka mata ma bani da kuzarin yin hakan. Ita kanta kazar jin ta nake yi tayi wani iri na bakina bana jin dadinta, sai yoghurt nayi ta kwankwada don shine mai sauki tunda hadiya kawai zanyi, sauran kazar Firdausi ta nade a cikin takardar ta ta saka a cikin fridge dinta. Littafai na dauko na dare kan study table ni ala dole zan yi karatu, koda na zauna babu abinda yake yawo akan littafin sai fuskar Abbu da murmushin shi, duk yadda naso inyi karatu a daren ranar abin yaci tura dole na hakura na koma kan gado na kwanta hannuna dafe da lebena wanda har lokacin nake jin tausasan lebunan Abbu akan su, it felt so awkward yet so good my body was shaking with desire.
Sai bayan da nayi sallar asubahi sannan na samu na kara bitar karatu. Karfe tara muka fara exam dinmu muka fito kafin sha biyu, daga nan barci nayi don jiya kam ban samu nayi barcin kirki ba. Sai da su Ni'ima suka zo sannan na tashi daga barci lokacin wajen karfe biyu ne, sai da nayi sallah sannan muka shiga shirye-shiryen zuwa wajen Reception din. Suka wanke min kai suka kafar dashi kafin suka gyara min shi sai sheki yake yi da tashin kamshi, nayi wanka na fito nan ma aka shiga yin kwalliya kuma. Da aka kira la'asar muka yi saurara muka yi sallah sannan muka ci gaba, na zura doguwar rigar shaddar da Abbu ya kawo min, Ramlah ta daura min dankwalin rigar yayi kamar gwaggwaro, na saka dankunne, sarka da awarwaro masu ratsin brown a ciki, muna cikin yin shirin wanda aka turo ya dauke mu ya yi waya yace ya iso, da yake suma a shirye suke sai duk muka rankaya muka tafi. Wata er ubansun Range Rover ce baka tana ta sheki tazo daukar mu, aka bude mana muka shiga maza biyu ne a gaban motar don haka muka shiga baya muka tafi, daya daga cikinsu ya juyo muka gaisa har da yin shakiyancin su na abokanan ango, su Firdausi ne masu tare min ni kam kaina yana kasa, duk inda muka wuce sai an bimu da kallo wanda probably nasan cewa motar suke kallo don kuwa haduwarta ya wuce misali.
Tafiya muke yi a hankali har Hotoro, aka yi horn a kofar wani gida aka bude muka tura hancin motar muka shiga, anyi decorating din wajen da kayan ado da ake yi wajen bukukuwa ga kujeru an shirya, wajen cike yake da mutane ana ta hada-hada, aka yi parking sannan muka fita. Wasu mata gungu guda suka zo suka ja mu har wajen da na tabbatar saboda ango da Amarya aka yi shi saboda wajen ya fita daban, wasu royal kujeru guda biyu a kasan canopy an sa tuntu akai a kasa kuma an shimfida wani babban carpet me fadi da laushi. Mai gayya mai aiki Abbu yana zaune a kujera daya, munyi anko da kayan jikinshi shadda light brown mai surfanin zare dark brown, leather brown cover shoes da hular zanna bukar itama brown, kaina a kasa yake ban yi gigin daga ido na dubi Abbu ko tarin mutanen da hankulan su ya dawo gare mu har suka taimaka min na zauna a kujerar kusa da Abbu, in a wink sun bace daga wajen, photographer yazo ya fara haskemu da flashes ya dauki kamar guda goma kafin ya tafi. Abbu ya dan matso saitin kunnena ya rada min “kin yi kyau sosai amaryata" na danyi murmushi ina wasa da yatsun hannuna. Mutanen wajen basu da yawa duk da haka na hango wasu daga cikin dangina na Malumfashi mazan, Aminu, Haruna da Samir duk diyan kanne da Yayin Daddy ne, a matan wajen kuma na hangi Anty Amina da Anty Rahina, Sadiya, Saratu, Da Halima su kuma cousin din su Sadiya dinne, sauran matan kuwa da zasu kai guda goma ban san su ba na dai yi zaton kila matan abokan Abbu dinne. Ba wani bata lokaci aka fara gabatar da walimar, wani daga cikinsu ya bude taro da addu'ah, ya mana fatan alkhairi ana yi ana raha ana ta shan dariya saboda jokes din da mutumin ya dinga cracking, daga nan kuma aka yi en ciye-ciyen snacks da aka raba da kuma drinks, daya bayan daya suka dinga zuwa kowa da matar shi, mu gaisa dasu su mana fatan alkhairi su bamu kyauta, wani a cikin wrapping sheet wani kuma a envelope har su Anty Aminah dasu Ni'imah, daga nan kuma aka shiga daukar hotuna kamar me?! A haka har duhu ya fara shigowa, sannan ne fa aka kara rufe taro da addu'ah muka fara sallama dasu suna shiga motocin su suna tafiya, kafin dai a kira magriba an barmu daga mu sai mu, su Anty Ameenah ma suka mana sallama suka tafi, su Ni'imah sun bi mazajen su sun tafi sai Ramlah tabi bayan su Sadiya. Muka shiga falon matar gidan mai suna Farha ta mana jagora ni da Firdausi har cikin bedroom dinta muka yi sallah, matar tana da fara'ah ga kirki, muna gama sallah muka fara hira wadda yawancin ta akan rayuwar aure ne, challenges din dake cikin shi da shawarce-shawarce akan zamantakewa da kuma wasu shawarwarin da suka sa ni sunke kaina cikin gyale na, tace “kunya kike ji? Wallahi idan kika ce zaki saka kunya cikin rayuwar aurenki to zaki samu cikas kuwa more especially ke mai kishiya, ai wallahi dagewa zaki yi ki cire kunyar nan ki kama mijinki tsam kafin kishiya ko wata a waje ta miki kwacen shi" na gyada kaina cikin yarda da maganganunta. Su Abbu basu shigo gidan ba sai bayan sallar Isha, Farha tayi-tayi damu akan mu tsaya mu ci abinci muka ce a'ah, ta bude wani karamin Kit, tana bude shi wani kamshi mai dadi ya hade dakin, ta dauko kwalaben humra guda biyu ta bani ita kuma Firdausi ta bata turare, tace min “sai dai humra din nan ki bari sai kin tare kafin ki fara amfani da ita Zai fi" muka mata sallama muka fita waje inda Abbu yake jiranmu, muka sake sallama da Farha da maigidanta muka shiga mota muka tafi. Babu wanda yayi magana a cikin motar har muka isa makaranta, Abbu yana yin parking Firdausi ta bude motar ta fita bayan ta wa Abbu sai da safe shi kuma ya mata Allah huta gajiya. Tana fita kamar wanda yake jira ya kamo hannuna, bai damu da yadda nayi gaggawar kwace hannuna ba ya sake janyo hannun nawa yana caressing da thumb dinshi, “kunshin nan yayi kyawu sosai, idan ya goge ki sake yin wani kinji? Shima idan ya goge ki sake wani, I'd like to be seeing it kinji??" na gyada mishi kai a hankali, yayi murmushi “good girl, amma ni sai wani noke-noke kike yi da wani kauda fuska, kin daina min magana, laifin me na miki iye?" ban yi magana ba sai kaina dana girgiza yace “ikon Allah! Aikuwa ba zamu yi haka dake ba, za kina bude baki ne kina min magana idan ba haka ba kuma raina zai baci fa, and u wouldn't like me idan hakan ya faru, ok?" na sake gyada kai, sai kuma nayi sauri nace “toh" yace “na fara nema mana visa fa, wani gari kike so kije for our honeymoon?" na dan zare ido, “honeymoon?" yace “ehh mana, da kin gama exams kin koma za a dawo min dake daga nan kuma zamu tafi honeymoon dinmu" nace “amma da aka ce sai session dinnan ya kare?" ya wani zaro ido kamar wadda ta fadi wani sabo, “ses... me? Ni dai nasan da bakina baki ji na fadi haka ba koh?" nace “ai nayi zaton haka ne" tun kafin in gama yake girgiza kai, “no! Ba haka bane. Gidan da zamu zauna is ready, komi ya riga ya kammala, kun gama jarabawar ku to me zan jira kuma? kin dai san ba zan barki kici gaba da zaman hostel ba kuma yanzun ma don we've already agreed on it ne shi yasa kika ga nayi shiru amma maganar gaskiya ban jin dadin zaman ki anan" na wani yi rau-rau da idanu, ya dage gira, “Allah baby kina jin dadin ki, kuka zaki yi kuma, me na miki?" ya kai hannunshi na dama ya tallabo kuncina dashi yana caressing din kuncina, hannunshi was very warm, na lumshe idanu na a hankali, na jiyo yatsar shi a saman idanu na yana shafawa, “zan ga yadda zamu kare da rigimar ki baby, dama ana haka ne? Daga magana sai ki kama kuka irin daddyn ki ya shagwaba ki koh?" na turo baki tare da janye fuskata daga hannunshi wadanda suka fara sanya min sayingsanyin jiki, murmushi kawai yayi. “Wadannan kyautukan da kika samu ban san ya zanyi dasu ba, do u have any idea ko wajen da zaki ajiye su?" nace “ka ajiye min su a wajenka" yace “to shikenan, zan kaisu gidanmu in ajiye, idan kin zo sai mu bude tare koh?" na rufe fuskata shi kuma yayi dariya, “nasan akwai kudi a ciki su kuma zan saka su cikin account ko ya kika ce?" nace hakan ma yayi, nan ma yace ok. Muka dan yi shiru na dan lokaci kafin ya duba hadaddiyar agogon fata dake daure a lallausan hannunshi, “to nine, yakamata kije ki kwanta yanzu koh?" nace “to, sai da safe" dama duk a wani takure nake ji na, na kama murfin motar zan fita ya sake janyo hannuna da bai jima da saki ba ya juyo dani, “not so soon baby, babu ko sallama?" na danyi frowning in confusion, wace sallama yake so muyi bayan wadda na mishi yanzu? Ban kai ga furta abinda nayi niyya ba naji ya hade goshina da nashi waje guda, irin sallamar jiya ya min sai dai ta yau tafi zurfi da demanding, ya sake ni a hankali idanunshi a lumshe, har lokacin goshin mu a hade yake, numfashi yake ajiyewa a hankali can kuma sai ya sake ni gabadaya, “Goodnight Amour" ya fada cikin whisper, cikin salubewar jiki na fita daga cikin motar. Ina shiga daki text dinshi ya shigo wayata, “make sure to eat something kafin ki kwanta, sweet dreams" na girgiza kai kawai na ajiye wayar akan gado na fara zare kayan jikina, ruwa na watsa na dawo nayi shirin kwanciya barci. Ba wata yunwa nake ji ba don haka na kwanta kawai, Abbu da Al'amuran shi masu ban mamaki suke min yawo a kwalwa, abubuwan da yake min were very new to my innocent life, ban san ya zan kamanta abinda nake ji a cikin raina ba amma ina jin kamar abin is wrong, anya ban yi kuskure ba kuwa?? Nayi juyi akan gado tare da tura kaina cikin pillow.
~Hii there dearies, so me zaku ce game da chapter din yau?
#TeamAbNaf! Hahh! Wata Fan ta kirkiro da sunan nan, ya burge ni kam sosai, what did you think?
#AnaTare
*♡Jeedderh♡*
[12:22PM, 2/18/2018] +234 703 300 1537: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*®°•Fikrah Writers Association°•*🖋
*49*
I love you so much Baby na Abbu na
Ranar Talata bamu yi exams ba sai ranar Laraba. Misalin karfe tara muna cikin exam hall muna jiran invigilators su shigo, sanye nake da doguwar riga dinkin Stella sai mayafi dana yafa mai yalwar fadi, fuskata daga hoda sai kwalli ko janbaki ban shafa ba saboda a sukwane na fita ranar don na kusa makara. Much to my surprise na tsinci Abbu cikin invigilators din, idanunshi suka zagaye ajin har sai da suka lalubo ni ya sakar min kyakkyawan murmushin shi da sai da yasa naji gwiwoyina sun sage, a dan kunyace na maida mishi martani tare da sadda kaina kasa ina tuno yadda muka rabu dashi a jiya da yamma da yazo wajena, yana insisting lallai sai munje ya nuna min gidan da zan zauna ni kuma nace mishi ba sai na gani ba, da yaga alamun ba zan bishi ba sai ya fara min abubuwan nashi da har lokacin kwakwalwata ta kasa daukar su ko sabawa dasu, da kyar na samu na zame na tsere.
Lokacin dana sake kallon inda yake hararata yake yi kasa-kasa fuskar shi na nuna bacin rai, gabana ya fadi, crap! Me nayi? Ko dai tun laifin jiya ne har yanzu yake fushi dani don naga tun daga lokacin bamu sake waya ba kamar yadda bai turon text ba duk da cewa dai na tura mishi wani yau da safe amma bai turo min da reply ba. Aka fara raba mana answer booklet ya dauki wasu yayi row din dake gefenmu na dama, yadda na bishi da ido haka na tsinci idanun yawancin ‘yanmatan ajin suna bin shi da kallo, naji wani takaici da bacin rai yana lullube ni, meye nasu na Kalle min miji? Sai naji kamar in tashi in fidda shi daga cikin ajin, na dai daure ban yi anything silly ba har ya juyo ta bangarenmu. Yazo saitina ya tsaya yana kokarin ciro booklet din, kamshin turaren Armani Code ya mamaye wajen naja na shaka har da lumshe ido, a hankali nace mishi “Abbu good morning!" lokacin daya danyi leaning akan desk din da nake ya ajiye mun takardar, “me yasa kika fito da wadannan kayan a jikin ki?" ya fada muryar shi na nuna bacin rai da distaste, na kalleshi tare da kallon kayan jikina, saboda Allah meye aibun su? Gyalena mai fadi ne ya rufe duk inda ake bukatar ya rufe, kafin in samu ince wani abu ya kara gaba zuwa ga desk din bayana, na danyi shrugging slightly na fara rubuta sunana akan takardar.
Ana bamu question paper na fara rubutu, Abbu ya jingina da window din gefenmu na hagu saitina, duk da ban daga kai na kalleshi ba amma nasan da cewa idanuwanshi a kaina suke don kuwa naji su, don haka zan iya cewa jarabawar ranar cikin takatsantsan nayi ta, ko motsin kirki ban yi ba. Ranar ni na fara submitting, ban tsaya jiran komi ba na bar hall din a tunani na zan iya tsere mishi kafin ya fito, sai ganin shi nayi ya wuce ta gabana, “follow me!" kawai yace yayi wajen parking lot, na sadda kaina kasa in surrender, nabi bayan shi na bude motar daya riga ya mata key na shiga, ina zama ya juyo glaring at me, “na tambaye ki baki bani amsa ba, nace me yasa kike yawo da wadannan kayan?" na daga gyalen jikina ina kallonshi, “naga fa gyalen bashi da matsala babba ne, kuma ya rufe min jiki meye marabar su da hijabi?" yaja motar muka tafi, “it's transparent for Goodness sake, ki duba kiga dazu da muka shigo, hannu da wuyanki duk a waje suke. Maza nawa na gani suna kallonki kina a matsayin mata ta?" juyawa nayi na kalleshi, ashe muna taya daya, “daga yau na hana ki saka gyale ko wani iri ne, be it mai kauri ko transparent I don't care, wear hijab wadda zata dinga rufe miki dunduniya!" na zaro ido, “to ai ni hijabai na gabadayansu ma basu kai biyar ba kuma da guda biyu kadai nazo makaranta" ya daga baki cikin mamaki kamar zai yi magana sai kuma ya rufe bakin, ya sake budewa yace “akwai hijabai a cikin kayan lefenki, idan kin tare ma zan dinka miki wasu for now sai kiyi amfani da wadanda kike dasu kafin ki koma" nace “Abbu....?" ya juyo ya kalleni fuskarshi na nuna rashin jin dadi, “r u arguing with me Nafeesah?" nayi saurin girgiza kaina, “to meye?" sai kawai na sake girgiza mishi kai, muka cigaba da tafiya ba tare da munyi magana ba, wani tunani ya darsu a raina. Na hade fuska tare da turo baki nace “to in dai haka ne sai dai kaima ka daina sa irin kayan daka sa yau, Allah kadai yasan iya adadin matan da suka dinga kallonka yau, kai duka ‘yanmatan ajinmu were looking at you with interest in their eyes" daidai lokacin yayi pulling motar zuwa cikin lot din dake gaban hostel dinmu yayi parking, ya kwashe da dariya cikin farinciki da wani abu mai kama da humor, na kura mishi ido ina kallonshi relieved and amazed, at last! Yayi more than murmushi.
Sai da yayi dariyar ta ishe shi sannan ya kalleni, “ni kuma meye aibun tawa shigar?" Armani pants ne a jikinshi da open neck top, ire-iren kayan da suke boye shekaru da girman da yayi su fito da xallan yarinta da kyawun shi. Na turo baki ban amsa ba, hannuna ya kamo ya rike a cikin nashi yana caressing, “girl, Ashe kema kin iya kishi? Ni indai nine baki da matsala dani, ki fadi duk irin kayan da kike so in dinga sawa zan sanya babu musu, m all urs Amour" na sadda kaina kasa ina blushing, na duba naga duk cikin irin kayan da yake sawa babu wanda basu mishi kyau, sai na kauda hirar na fara kokarin janye hannuna daga nashi wanda ya fara sa min tashin tsigar jiki. Ya kalleni fuskar shi a dan hade, “na kula baki son ina rabar ki kwana biyun nan Nafeesah, mai yasa?" duk da maganar da yayi sai dana janye hannuna daga nashi na saka su cikin gyalena, shiru nayi kawai, to in ce masa me? Ina jin kaina kamar wata traitor ko mai laifi idan ya taba ni, I'm feeling awkward idan ya taba ni, feelings ne da ban saba jinsu a cikin rayuwata ba hakan yasa na fara having second thoughts, ko dai don yana abokin Dad ne na kasa sakewa da Al'amuran shi? Ya kuta kawai, “zaki gama kewaye-kewayen ki ne ma ki dawo hanya Nafeesah, ina so zan wuce gida yanzu, me kike so in kawo miki anjima?" nayi saurin girgiza kaina, “babu komi" frankly speaking zan fi so ace ba ma sai ya dawo ba, ya tabe baki “sai wani guduna kike yi fa, kin manta cewa komi wayon amarya sai an sha man ta?" na kalle shi, wani murmushin mugunta ne akan fuskar shi da yasa naji wani tsoron shi yana shiga ta, ya kamo hannuna duk nokewar da nake yi sai da ya kai bayan hannuna saitin bakin shi ya sumbata, nayi saurin bude motar na janye hannuna na fita, sai dana fitan sannan na leka ta tagar motar nace “Abbu a gaida su Hafsy, sai anjima" yayi murmushi kawai yana gyada kai, na juya da sauri na wuce.
A haka har muka gama exams dinmu, ina ta kauce-kauce yayin da Abbu bai fasa abin shi ba sai ma abubuwa da suke karuwa kullum. Kwana biyun nan ya dameni akan wai shi fa lallai sai ya kaini naga gidan mu, ni kuwa nasan muddin na taka kafa naje gidan to sunana sorry, kila warning din dasu Ni'imah da Firdausi suke yi mun na in daure kar in tare da ciki ya tabbata. Tun a ranar da nayi exams dina na karshe na fara hada kayana, na kira Daddy a waya yace washegari zai turo a zo a dauke ni saboda ranar sai da yamma muka gama exams din, nace mishi don Allah ya turo direban tun da safe mu tafi, a matukar kagauce nake da in tafi gida, I have to clear my thoughts and brain kuma nasan gidanmu ne kawai zai bani wannan natsuwar, ga kewar su Daddy da nake yi kamar me, hakika nayi kokari, watanni biyar rigis ba tare dana saka su a cikin idanuna ba. Na kira Ramlah da tace tare zamu wuce Kadunar da ita na sanar da ita, tace zata shirya sai mu biya ta gida mu dauketa nace to muka yi sallama.
Karfe tara na safe kayana sun kammala waje daya, nayi wanka na shirya cikin riga da siket na atamfa, hijabin data zame min mayafi na ajiye a gefen gado a linke, na dauki wayata na fara buga game don ya dan kashe min time kafin direba ya zo. Kiran Abbu ya shigo wayata, gabana ya fadi sosai gabadaya na manta bamu yi sallama dashi ba saboda doki, na dauki wayar na kara a kunnena, “meet me at my office" kadai yace ya kashe wayar, na bi wayar da kallo kamar ba zan tashi ba, can kuma na mike na saka hijabina, Firdausi bata dakin taje rubuta jarabawa don haka na rufe dakin na fita. Zaune na same shi akan kujera fara dake a tsakiyar ofishin da alamun jirana yake yi, na maida kofar na rufe na zauna akan kujera dake fuskantar shi na zauna, fuskar shi sam babu yabo babu fallasa hakan yasa naji sanyin jiki ya mamaye ni, Allah dai ya taimakeni muyi rabuwar aminci yau don na kula da cewa rigima yake ji yau. Murmushi nayi a sanyaye nace “Abbu ina kwana? Ka tashi lafiya?" yace “ke zan tambaya ai, amma ni kin tambayeni tashina lafiya bayan kina neman hana min abinda yake nawa ne?" na dan zamo daga kan kujerar da nake zaune nace “don Allah Abbu kayi hakuri, idan kayi hakuri ma duka kwanaki nawa suka rage kafin a kawo maka ni gabadaya kayi yadda kake so dani?" ya lumshe idanun shi tare da maida kanshi ya jinginar da kujerar da yake zaune, “I tried Nafeesah, I really do. But I can't anymore, all I ask for u is just half an hour, please ki zo muje gidana, I so badly want you Nafeesah!!" na kura mishi idanu, idanun shi a lumshe suke har lokacin, Abbuna ne a gabana yake rokona, da ace zan iya da na mishi abinda yake so domin samun farin cikin rayuwar shi, sai dai ba zan iya din bane, I'm still not ready for it. Mikewa tsaye nayi a hankali, hanya mafi sauki in bar mishi ofishin kafin in kara bata mishi rai, nasan ba zai fasa tambayana ba, ni kuma in yaci gaba da tambaya it's either inyi abu daya cikin biyu; ko dai in sallama mishi ko kuma inyi denying wanda duka cikin biyun babu wanda zai mun dadi, nace “Abbu don girman Allah kayi hakuri, kayi hakuri na wata da watanni ma balle na en kwanaki? I am very sorry, zamu wuce Kaduna yanzu don Allah kar kayi fushi dani Abbu..." na juya cike da sassarfa zan fita. Ban ji lokacin daya tashi tsaye ba sai maganar shi dana jiyo daga bayana, “Please Mana Nafeesahh!!" Ya fada cikin wata irin murya wadda ta narke cikin tsantsar qauna da soyayyah. Kaina na fara girgizawa a tsorace, "Bazan iya ba. Kai fa Abokin Babana ne please kayi hakuri, bazan iya ba wallahi!!" idanunshi ya zuba min wadanda suke a lumshe kamar na mashaya, dama a yawancin lokuta a haka suke, sai dai na yau sun banbanta dana sauran lokutan. Na yau cike suke da wata irin soyayyah, zallar qauna, pure lust, I can sense them radiating from his body. Muryarshi ta kara yin kasa sosai “ina tunanin mun riga da mun gama wannan maganar Nafeesah? saboda Allah mutane nawa kika san sun yi aure irin namu kuma suna zaune lafiya har ma da zuria a tsakaninsu, ko a cikin tarihi ki duba fa, Sayyadah Aisha RTA diyar Sayyidina Abubakar ce wanda ya kasance babban Amini makusanci a wajen manxon mu (S. A. W) nasan kin san da haka ba sai na sake gaya miki ba" maganganun shi haka suke sai dai na kasa convincing kaina da zuciyata" nace “yeah, I know.., I just need time please kayi hakuri" ya girgiza kai, “na gaya miki ba zan iya bane Nafeesah, it's not as if wani sabo ne nake shirin aikatawa" Kai na ci gaba da girgizawa hawaye na sauka akan kumatuna, ya zanyi da raina da rayuwa ta ne ni kam? Ban san ya aka yi ba sai ganin shi nayi a gabana, kafin inyi wani yunkuri yayi pinning dina da bangon ofishin, "I love you Nafeesah....I want you n I know you do, u just don't want to admit it!" "no.... No... I... I" na fara fada cikin in'ina kafin inji wasu tausasan lebba sun hana ni karasa maganar. Lebena na kasa ya kamo ya fara tsotsa cikin wani irin passionate kiss, a hankali na lumshe idanuna tare da kamo nashi leben na sama nima na fara tsotsa, ya saka hannu daya ya zagaya dashi ta kuguna ya kara matso dani zuwa gare shi tare da zura harshen shi cikin bakina muka fara hadamammen kiss, ihu ake a cikin kaina da kwalwata, “Ya Allah! What am I doing? He's my father's Friend for Heaven's sake!! Cewar wani sashe na zuciyata, but hell! I couldn't let him go, sai ma kara rike shi da nayi tsam....
Karan da wayata ta dauka baby kakkautawa ne ya dawo da hankulanmu cikin ofishin, a matukar kunyace na janye jikina daga nashi yayi saurin janyo ni ya rungume a cikin kirjinshi, duk yadda naso in kwace abin yaci tura ina ji ina gani haka na Hakura har wayar ta gama burari ta katse, numfashi yake saukewa a hankali har ya dawo cikin natsuwar shi, ya hade goshina da nashi yana kallona ni kuwa naki hada idanu dashi, murmushi ya saki a hankali, “kin gani koh? We need each other Nafeesah, amma kina hana kan ki abinda zuciyar ki da gangar jikinki ke so, why?" a hankali na daga baki nace “kayi hakuri" ga mamakina sai naji yace “na hakura Nafeesah" na daga kai cikin mamaki na kalleshi, ya daga kafada, “to me zan yi idan ba hakurin ba? Kin san cewa ba zan taba tursasa ki ga yin abinda baki so ba, zan jira har a kawo ki din sai dai kada ma ki roke ni wani abu a wannan lokacin don ba zan ji ki ba...., muje in kaiki hostel din" ya zari makullin mota ya fita, na bishi da kallo ina murmushi, saukin kan Abbu yana burge ni sosai da sosai, Allah ya yaye min fargabar nan da wasi-wasi da nake ji ko na samu na faranta mishi rai kamar yadda yake kokarin faranta min. Na bi bayanshi na fita daga ofis din ya rufe muka tafi. Koda na duba miss call din da aka min direban da daddy ya turo min ne, na kira shi ya sanar dani ya iso nace mishi gani nan. Koda muka isa mun dauki lokaci muna hira da Abbu kafin muka yi sallama dashi akan cewa zamu yi waya, ya kama hannuna yayi kissing bayan hannun kamar yadda ya mayar dashi al'adar shi tun ina jin abun banbarakwai har nazo na saba da hakan yace “m gonna miss you baby" nace “me too" a kunyace, yayi murmushi, da haka yaja motar shi ya tafi. Firdausi ta taya ni dauko kayana muka lode su a bayan booth, daga nan muka yi sallama da ita ita sai nan da kwana biyu zata gama nata exams din, na shiga mota direba yaja muka wuce Kaduna bayan mun dauko Ramlah. Karfe biyu a Kaduna ta mana, da gudu na shiga gidan ina ihun kiran Mommy, ta fito daga kicin tana goge hannunta da kicin towel, na tafi da guduna na rungumeta ina murna, ta janye ni daga jikinta tace “ke tafi can ni, wannan yarinya ban san yaushe zaki girma ba ni kam" na kara shigewa jikinta ina tsalle abina, sai da Ramlah ta shigo sannan na sake ta. Suka gaisa da Mommy kafin muka shiga dakina muka yi wanka muka yi sallah, sai a lokacin na kira Abbu na sanar dashi mun sauka, nan muka danyi hira muka yi sallama sannan muka fita falo muka ci abinci. Da yamma Daddy ya dawo muka sha hira da murnar ganin juna, ko da dare ma dai hirar muka yi har sai da dare yayi sannan na musu sallama na wuce dakina. Washegari Anty Uwani tazo ta daukemu ni da Ramlatu muka tafi gidanta bayan ta sa mun dauki kayan sawar mu kala biyar, ban san me zamu yi ba na dai ji suna maganar Gyaran jiki ita da Mommy ni kam ban maida hankali wajen sanin lallai sai na san me zamu yi ba.
#TeamAbnaf
#OneLove
*♡Jeedderh♡*
[12:22PM, 2/18/2018] +234 703 300 1537: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*®°•Fikrah Writers Association°•*🖋
*48*
Ranar Talata bamu yi exams ba sai ranar Laraba. Misalin karfe tara muna cikin exam hall muna jiran invigilators su shigo, sanye nake da doguwar riga dinkin Stella sai mayafi dana yafa mai yalwar fadi, fuskata daga hoda sai kwalli ko janbaki ban shafa ba saboda a sukwane na fita ranar don na kusa makara. Much to my surprise na tsinci Abbu cikin invigilators din, idanunshi suka zagaye ajin har sai da suka lalubo ni ya sakar min kyakkyawan murmushin shi da sai da yasa naji gwiwoyina sun sage, a dan kunyace na maida mishi martani tare da sadda kaina kasa ina tuno yadda muka rabu dashi a jiya da yamma da yazo wajena, yana insisting lallai sai munje ya nuna min gidan da zan zauna ni kuma nace mishi ba sai na gani ba, da yaga alamun ba zan bishi ba sai ya fara min abubuwan nashi da har lokacin kwakwalwata ta kasa daukar su ko sabawa dasu, da kyar na samu na zame na tsere.
Lokacin dana sake kallon inda yake hararata yake yi kasa-kasa fuskar shi na nuna bacin rai, gabana ya fadi, crap! Me nayi? Ko dai tun laifin jiya ne har yanzu yake fushi dani don naga tun daga lokacin bamu sake waya ba kamar yadda bai turon text ba duk da cewa dai na tura mishi wani yau da safe amma bai turo min da reply ba. Aka fara raba mana answer booklet ya dauki wasu yayi row din dake gefenmu na dama, yadda na bishi da ido haka na tsinci idanun yawancin ‘yanmatan ajin suna bin shi da kallo, naji wani takaici da bacin rai yana lullube ni, meye nasu na Kalle min miji? Sai naji kamar in tashi in fidda shi daga cikin ajin, na dai daure ban yi anything silly ba har ya juyo ta bangarenmu. Yazo saitina ya tsaya yana kokarin ciro booklet din, kamshin turaren Armani Code ya mamaye wajen naja na shaka har da lumshe ido, a hankali nace mishi “Abbu good morning!" lokacin daya danyi leaning akan desk din da nake ya ajiye mun takardar, “me yasa kika fito da wadannan kayan a jikin ki?" ya fada muryar shi na nuna bacin rai da distaste, na kalleshi tare da kallon kayan jikina, saboda Allah meye aibun su? Gyalena mai fadi ne ya rufe duk inda ake bukatar ya rufe, kafin in samu ince wani abu ya kara gaba zuwa ga desk din bayana, na danyi shrugging slightly na fara rubuta sunana akan takardar.
Ana bamu question paper na fara rubutu, Abbu ya jingina da window din gefenmu na hagu saitina, duk da ban daga kai na kalleshi ba amma nasan da cewa idanuwanshi a kaina suke don kuwa naji su, don haka zan iya cewa jarabawar ranar cikin takatsantsan nayi ta, ko motsin kirki ban yi ba. Ranar ni na fara submitting, ban tsaya jiran komi ba na bar hall din a tunani na zan iya tsere mishi kafin ya fito, sai ganin shi nayi ya wuce ta gabana, “follow me!" kawai yace yayi wajen parking lot, na sadda kaina kasa in surrender, nabi bayan shi na bude motar daya riga ya mata key na shiga, ina zama ya juyo glaring at me, “na tambaye ki baki bani amsa ba, nace me yasa kike yawo da wadannan kayan?" na daga gyalen jikina ina kallonshi, “naga fa gyalen bashi da matsala babba ne, kuma ya rufe min jiki meye marabar su da hijabi?" yaja motar muka tafi, “it's transparent for Goodness sake, ki duba kiga dazu da muka shigo, hannu da wuyanki duk a waje suke. Maza nawa na gani suna kallonki kina a matsayin mata ta?" juyawa nayi na kalleshi, ashe muna taya daya, “daga yau na hana ki saka gyale ko wani iri ne, be it mai kauri ko transparent I don't care, wear hijab wadda zata dinga rufe miki dunduniya!" na zaro ido, “to ai ni hijabai na gabadayansu ma basu kai biyar ba kuma da guda biyu kadai nazo makaranta" ya daga baki cikin mamaki kamar zai yi magana sai kuma ya rufe bakin, ya sake budewa yace “akwai hijabai a cikin kayan lefenki, idan kin tare ma zan dinka miki wasu for now sai kiyi amfani da wadanda kike dasu kafin ki koma" nace “Abbu....?" ya juyo ya kalleni fuskarshi na nuna rashin jin dadi, “r u arguing with me Nafeesah?" nayi saurin girgiza kaina, “to meye?" sai kawai na sake girgiza mishi kai, muka cigaba da tafiya ba tare da munyi magana ba, wani tunani ya darsu a raina. Na hade fuska tare da turo baki nace “to in dai haka ne sai dai kaima ka daina sa irin kayan daka sa yau, Allah kadai yasan iya adadin matan da suka dinga kallonka yau, kai duka ‘yanmatan ajinmu were looking at you with interest in their eyes" daidai lokacin yayi pulling motar zuwa cikin lot din dake gaban hostel dinmu yayi parking, ya kwashe da dariya cikin farinciki da wani abu mai kama da humor, na kura mishi ido ina kallonshi relieved and amazed, at last! Yayi more than murmushi.
Sai da yayi dariyar ta ishe shi sannan ya kalleni, “ni kuma meye aibun tawa shigar?" Armani pants ne a jikinshi da open neck top, ire-iren kayan da suke boye shekaru da girman da yayi su fito da xallan yarinta da kyawun shi. Na turo baki ban amsa ba, hannuna ya kamo ya rike a cikin nashi yana caressing, “girl, Ashe kema kin iya kishi? Ni indai nine baki da matsala dani, ki fadi duk irin kayan da kike so in dinga sawa zan sanya babu musu, m all urs Amour" na sadda kaina kasa ina blushing, na duba naga duk cikin irin kayan da yake sawa babu wanda basu mishi kyau, sai na kauda hirar na fara kokarin janye hannuna daga nashi wanda ya fara sa min tashin tsigar jiki. Ya kalleni fuskar shi a dan hade, “na kula baki son ina rabar ki kwana biyun nan Nafeesah, mai yasa?" duk da maganar da yayi sai dana janye hannuna daga nashi na saka su cikin gyalena, shiru nayi kawai, to in ce masa me? Ina jin kaina kamar wata traitor ko mai laifi idan ya taba ni, I'm feeling awkward idan ya taba ni, feelings ne da ban saba jinsu a cikin rayuwata ba hakan yasa na fara having second thoughts, ko dai don yana abokin Dad ne na kasa sakewa da Al'amuran shi? Ya kuta kawai, “zaki gama kewaye-kewayen ki ne ma ki dawo hanya Nafeesah, ina so zan wuce gida yanzu, me kike so in kawo miki anjima?" nayi saurin girgiza kaina, “babu komi" frankly speaking zan fi so ace ba ma sai ya dawo ba, ya tabe baki “sai wani guduna kike yi fa, kin manta cewa komi wayon amarya sai an sha man ta?" na kalle shi, wani murmushin mugunta ne akan fuskar shi da yasa naji wani tsoron shi yana shiga ta, ya kamo hannuna duk nokewar da nake yi sai da ya kai bayan hannuna saitin bakin shi ya sumbata, nayi saurin bude motar na janye hannuna na fita, sai dana fitan sannan na leka ta tagar motar nace “Abbu a gaida su Hafsy, sai anjima" yayi murmushi kawai yana gyada kai, na juya da sauri na wuce.
A haka har muka gama exams dinmu, ina ta kauce-kauce yayin da Abbu bai fasa abin shi ba sai ma abubuwa da suke karuwa kullum. Kwana biyun nan ya dameni akan wai shi fa lallai sai ya kaini naga gidan mu, ni kuwa nasan muddin na taka kafa naje gidan to sunana sorry, kila warning din dasu Ni'imah da Firdausi suke yi mun na in daure kar in tare da ciki ya tabbata. Tun a ranar da nayi exams dina na karshe na fara hada kayana, na kira Daddy a waya yace washegari zai turo a zo a dauke ni saboda ranar sai da yamma muka gama exams din, nace mishi don Allah ya turo direban tun da safe mu tafi, a matukar kagauce nake da in tafi gida, I have to clear my thoughts and brain kuma nasan gidanmu ne kawai zai bani wannan natsuwar, ga kewar su Daddy da nake yi kamar me, hakika nayi kokari, watanni biyar rigis ba tare dana saka su a cikin idanuna ba. Na kira Ramlah da tace tare zamu wuce Kadunar da ita na sanar da ita, tace zata shirya sai mu biya ta gida mu dauketa nace to muka yi sallama.
Karfe tara na safe kayana sun kammala waje daya, nayi wanka na shirya cikin riga da siket na atamfa, hijabin data zame min mayafi na ajiye a gefen gado a linke, na dauki wayata na fara buga game don ya dan kashe min time kafin direba ya zo. Kiran Abbu ya shigo wayata, gabana ya fadi sosai gabadaya na manta bamu yi sallama dashi ba saboda doki, na dauki wayar na kara a kunnena, “meet me at my office" kadai yace ya kashe wayar, na bi wayar da kallo kamar ba zan tashi ba, can kuma na mike na saka hijabina, Firdausi bata dakin taje rubuta jarabawa don haka na rufe dakin na fita. Zaune na same shi akan kujera fara dake a tsakiyar ofishin da alamun jirana yake yi, na maida kofar na rufe na zauna akan kujera dake fuskantar shi na zauna, fuskar shi sam babu yabo babu fallasa hakan yasa naji sanyin jiki ya mamaye ni, Allah dai ya taimakeni muyi rabuwar aminci yau don na kula da cewa rigima yake ji yau. Murmushi nayi a sanyaye nace “Abbu ina kwana? Ka tashi lafiya?" yace “ke zan tambaya ai, amma ni kin tambayeni tashina lafiya bayan kina neman hana min abinda yake nawa ne?" na dan zamo daga kan kujerar da nake zaune nace “don Allah Abbu kayi hakuri, idan kayi hakuri ma duka kwanaki nawa suka rage kafin a kawo maka ni gabadaya kayi yadda kake so dani?" ya lumshe idanun shi tare da maida kanshi ya jinginar da kujerar da yake zaune, “I tried Nafeesah, I really do. But I can't anymore, all I ask for u is just half an hour, please ki zo muje gidana, I so badly want you Nafeesah!!" na kura mishi idanu, idanun shi a lumshe suke har lokacin, Abbuna ne a gabana yake rokona, da ace zan iya da na mishi abinda yake so domin samun farin cikin rayuwar shi, sai dai ba zan iya din bane, I'm still not ready for it. Mikewa tsaye nayi a hankali, hanya mafi sauki in bar mishi ofishin kafin in kara bata mishi rai, nasan ba zai fasa tambayana ba, ni kuma in yaci gaba da tambaya it's either inyi abu daya cikin biyu; ko dai in sallama mishi ko kuma inyi denying wanda duka cikin biyun babu wanda zai mun dadi, nace “Abbu don girman Allah kayi hakuri, kayi hakuri na wata da watanni ma balle na en kwanaki? I am very sorry, zamu wuce Kaduna yanzu don Allah kar kayi fushi dani Abbu..." na juya cike da sassarfa zan fita. Ban ji lokacin daya tashi tsaye ba sai maganar shi dana jiyo daga bayana, “Please Mana Nafeesahh!!" Ya fada cikin wata irin murya wadda ta narke cikin tsantsar qauna da soyayyah. Kaina na fara girgizawa a tsorace, "Bazan iya ba. Kai fa Abokin Babana ne please kayi hakuri, bazan iya ba wallahi!!" idanunshi ya zuba min wadanda suke a lumshe kamar na mashaya, dama a yawancin lokuta a haka suke, sai dai na yau sun banbanta dana sauran lokutan. Na yau cike suke da wata irin soyayyah, zallar qauna, pure lust, I can sense them radiating from his body. Muryarshi ta kara yin kasa sosai “ina tunanin mun riga da mun gama wannan maganar Nafeesah? saboda Allah mutane nawa kika san sun yi aure irin namu kuma suna zaune lafiya har ma da zuria a tsakaninsu, ko a cikin tarihi ki duba fa, Sayyadah Aisha RTA diyar Sayyidina Abubakar ce wanda ya kasance babban Amini makusanci a wajen manxon mu (S. A. W) nasan kin san da haka ba sai na sake gaya miki ba" maganganun shi haka suke sai dai na kasa convincing kaina da zuciyata" nace “yeah, I know.., I just need time please kayi hakuri" ya girgiza kai, “na gaya miki ba zan iya bane Nafeesah, it's not as if wani sabo ne nake shirin aikatawa" Kai na ci gaba da girgizawa hawaye na sauka akan kumatuna, ya zanyi da raina da rayuwa ta ne ni kam? Ban san ya aka yi ba sai ganin shi nayi a gabana, kafin inyi wani yunkuri yayi pinning dina da bangon ofishin, "I love you Nafeesah....I want you n I know you do, u just don't want to admit it!" "no.... No... I... I" na fara fada cikin in'ina kafin inji wasu tausasan lebba sun hana ni karasa maganar. Lebena na kasa ya kamo ya fara tsotsa cikin wani irin passionate kiss, a hankali na lumshe idanuna tare da kamo nashi leben na sama nima na fara tsotsa, ya saka hannu daya ya zagaya dashi ta kuguna ya kara matso dani zuwa gare shi tare da zura harshen shi cikin bakina muka fara hadamammen kiss, ihu ake a cikin kaina da kwalwata, “Ya Allah! What am I doing? He's my father's Friend for Heaven's sake!! Cewar wani sashe na zuciyata, but hell! I couldn't let him go, sai ma kara rike shi da nayi tsam....
Karan da wayata ta dauka baby kakkautawa ne ya dawo da hankulanmu cikin ofishin, a matukar kunyace na janye jikina daga nashi yayi saurin janyo ni ya rungume a cikin kirjinshi, duk yadda naso in kwace abin yaci tura ina ji ina gani haka na Hakura har wayar ta gama burari ta katse, numfashi yake saukewa a hankali har ya dawo cikin natsuwar shi, ya hade goshina da nashi yana kallona ni kuwa naki hada idanu dashi, murmushi ya saki a hankali, “kin gani koh? We need each other Nafeesah, amma kina hana kan ki abinda zuciyar ki da gangar jikinki ke so, why?" a hankali na daga baki nace “kayi hakuri" ga mamakina sai naji yace “na hakura Nafeesah" na daga kai cikin mamaki na kalleshi, ya daga kafada, “to me zan yi idan ba hakurin ba? Kin san cewa ba zan taba tursasa ki ga yin abinda baki so ba, zan jira har a kawo ki din sai dai kada ma ki roke ni wani abu a wannan lokacin don ba zan ji ki ba...., muje in kaiki hostel din" ya zari makullin mota ya fita, na bishi da kallo ina murmushi, saukin kan Abbu yana burge ni sosai da sosai, Allah ya yaye min fargabar nan da wasi-wasi da nake ji ko na samu na faranta mishi rai kamar yadda yake kokarin faranta min. Na bi bayanshi na fita daga ofis din ya rufe muka tafi. Koda na duba miss call din da aka min direban da daddy ya turo min ne, na kira shi ya sanar dani ya iso nace mishi gani nan. Koda muka isa mun dauki lokaci muna hira da Abbu kafin muka yi sallama dashi akan cewa zamu yi waya, ya kama hannuna yayi kissing bayan hannun kamar yadda ya mayar dashi al'adar shi tun ina jin abun banbarakwai har nazo na saba da hakan yace “m gonna miss you baby" nace “me too" a kunyace, yayi murmushi, da haka yaja motar shi ya tafi. Firdausi ta taya ni dauko kayana muka lode su a bayan booth, daga nan muka yi sallama da ita ita sai nan da kwana biyu zata gama nata exams din, na shiga mota direba yaja muka wuce Kaduna bayan mun dauko Ramlah. Karfe biyu a Kaduna ta mana, da gudu na shiga gidan ina ihun kiran Mommy, ta fito daga kicin tana goge hannunta da kicin towel, na tafi da guduna na rungumeta ina murna, ta janye ni daga jikinta tace “ke tafi can ni, wannan yarinya ban san yaushe zaki girma ba ni kam" na kara shigewa jikinta ina tsalle abina, sai da Ramlah ta shigo sannan na sake ta. Suka gaisa da Mommy kafin muka shiga dakina muka yi wanka muka yi sallah, sai a lokacin na kira Abbu na sanar dashi mun sauka, nan muka danyi hira muka yi sallama sannan muka fita falo muka ci abinci. Da yamma Daddy ya dawo muka sha hira da murnar ganin juna, ko da dare ma dai hirar muka yi har sai da dare yayi sannan na musu sallama na wuce dakina. Washegari Anty Uwani tazo ta daukemu ni da Ramlatu muka tafi gidanta bayan ta sa mun dauki kayan sawar mu kala biyar, ban san me zamu yi ba na dai ji suna maganar Gyaran jiki ita da Mommy ni kam ban maida hankali wajen sanin lallai sai na san me zamu yi ba.
#TeamAbnaf
#OneLove
*♡Jeedderh♡*
[12:22PM, 2/18/2018] +234 703 300 1537: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*®°•Fikrah Writers Association°•*🖋
This page goes to you, Jedderhs World Group Members, Lobi you dearies sosai da sosai.....
Shafin yau Tukuici ne a gare ki Mayrowh, thank you and lobi you too.....
*50*
Munyi nisa sosai kafin kukan da nake yi ya dauke, Anty Shafa ta miko min handkerchief na share fuska ta dashi, ta bude Jakarta ta ciro kayan kwalliya ta juyo da fuskata ta gyara min kwalliyar dana bata, na juya kaina ga window din motar na fuskanci waje zuciyata cike fal da tunanika iri-iri. Karfe shida muna cikin Kano, kai tsaye unguwar Galadanchi aka wuce damu gidan su Abbu. Can muka tarda mutane na jiran isowar mu, dakin Hajiya Siyama Mahaifiyar su Abbu surika a wajena muka sauka, aka damka musu Amana ita da Dattijan da muka samu a dakin nata, daga nan kuma aka kaini dakin Hajiya Fati nan ma dai gaisuwa da bada amanar ne, bayan an gama aka dauke ni zuwa wajen mahaifin su, ya mun nasiha sosai mai shiga jiki tare da addu'o'i, ya bada abin Sallah, Carbi da Turare aka bani a matsayin tsarabar gidan aure daga nan muka koma cikin mota sai gidan Aurena a Sharada phase 2.
Gida ne flat mai kyau, dakuna uku manya duk an yi jere, akwai toilets a cikin kowane daki, kicin, sai toilet daya a cikin falo kila na baki ne.
Su Ni'imah sune en jagora har zuwa dakina, sai da muka shiga daki Anty Ameenah ta yaye min gyalen kaina duk da haka kin daga kaina in kallesu nayi, Su Anty Shafa daya dakin aka kaisu ni kuma su Ramlah suka zauna a tare dani, nan dai muka dauro alwala muka yi sallah, kasancewar lokacin Sallar Isha'i yayi yasa muka yi har Isha'i din. Muna gamawa aka dire mana plates din abinci, Macaroni jollop da lemuka, tsakanina da Allah cikina a cike yake shi yasa na dinga tsakurar abincin, Sadiya data fara nauyi haihuwa ko yau ko gobe duk da ita aka yi jigilar gaisuwa da ita ko nauyin cikinta bata ji, tace “Amaryar Babban Yaya ya dai baki cin abinci ko dai kazar amarcin kike jira?" na harareta kasa-kasa ganin gasu Anty Ameenah a gefenmu suna zaune, Ni'imah tace “ta fa riga da taci kazar amarcinta tun ranar da aka daura aure, muma ba har muka ci saura ba?" na kuwa kai mata mintsini a cinya tayi tsalle gefe guda tana sosa wajen, Ramlah tace “ku kyale yarinyar nan, tun dazu take nuku-nuku kamar ba ita bace tace tana son auren, lokacin da yunwa zata taso mutum ya nemi abinci kuna ihu?" duk suka sa ihun, “Gida!!" tace “kun gani?!" ni kam sai na tashi na bar musu wajen kawai, na koma kan bencin dake gefen gado na zauna ina satar kallon kayan dakin, komi na ciki silver ne da black, gadon irin kananun Italian beds dinnan ne medium king size sai wardrobe data kusa cinye bangon dakin na gefen dama, dressing mirror, end of bed table, rug carpet, labulaye silver, sai sauran kananun tarkace da ba za a rasa ba amma kayan sunyi kyawu sosai, babu wata hayaniya irin ta kayan dakin zamanin nan.
Su Anty Ameenah suka mana sai da safe suka tafi suka barmu da su Anty Shafa da Ramlah, er hirarraki muka yi kafin Anty Shafa tace yakamata mu kwanta haka, ni na fara shiga toilet nan ma kayan ciki har ba a magana, katoton Jacuzzi tub, sinks, akan canters kuma mayuka ne tun daga na gyaran fata har na gashi ne da turaruka abin ba a cewa komi, na tari ruwan dumi na dan yi relaxing saboda warware gajiya kafin na dauro babban towel na fito na danyi en shafe-shafe na fita, Ramlah ta shiga.
Wardrobe na bude da niyar duba kayan barci, baki na bude a tsorace ina kallon cikin wardrobe din. Layi daya atamfofi ne wasu ma ko dinga su ba ayi ba, sai daya na laces, daya nasu jallabiya ne da dai dogayen riguna, daya nasu materials, saitin kayan barci kuwa sai da suka kwashe biyu, na zaro riga daya na daga ta sama, it looks more like a lingerie yawancin kayan barcin duk ire-iren su ne.
Na juya da rigar a hannuna ina nunawa Anty Shafa, “meye haka Anty?" tace “kayan barci mana" na kara kallon kayan, “you didn't mean... Ni zan saka su koh?" ta harareni, cikin gatse tace “a'ah ni zan sa..., ko kuma shi mijin naki!" na gumtse dariyata nace “amma Allah Anty kayan suna nuna jiki da yawa fa" tace “yi mun shiru malama, don suna nuna jiki sai me? Ina ce dai hakan ba Zunubi bane? Idan kin san ta yadda aka yi kayan nan suka zo nan ba zaki zauna kina ce mun wai suna nuna jiki ba, I specially went to Kamfanin da suke sarrafasu na bada oda, don haka tun kafin raina ya baci ki saka kayan nan, besides kayan nan na arziki ne idan kika yi comparing dinsu da wasu kayan, koda yake ke da kanki zaki san amfanin su kizo kina nema na" sai na gumtse baki na juya na maida rigar na fara laluben kayan sa wa, da kyar na lalubo riga da wando suma dai sai a hankali, wandon 3q, rigar mai hannun vest gasu silk, lokacin Ramlah ta fito nan muka bi lafiyar gado. Anty Shafa kuma ta ajiye katifa a tsakar dakin muka yi light off muka kwanta, kamar jira yake, sakon Abbu ya shigo.
*“Sleep??"* nayi gaggawar tura mishi da, *“about to.... How was your day?"* ya turo *“dama nasan ba zaki iya barci ba baby na, tun yau fa baki ji murya ta ba balle kiga text dina, nima ina kewar ki baby na nasan da kyar barci ya dauke ni yau, amma kar ki damu, na yau ne kawai..., daga gobe babu wanda zai sake shiga tsakaninmu da yardar Allah"* lokacin dana karanta sai da er dariya ta kufce min, kai Abbu is full of self confidence. Na tura mishi *“says wanda yake da mata., plus ni fa barcin ne kawai bai zo ba amma babu wanda nake kewa sai Mommy da Daddy na!"* na tura ina dariyar tsokana, nasan kila har gari ya waye yau muna musayar sakonni ne, sai kuma har barci ya dauke ni bai dawo da reply ba.
Sai da muka tashi sallar Asabar naga amsar daya maido mintuna kadan da fara barci na, *“zaki ce haka ai tunda har yanzu baki zo hannu ba, gobe war haka ki maimaita abinda kika fada yanzu please...." nayi murmushi kawai na maida wayar kasan filo na fada toilet. Muna gama Sallah muka koma wani barcin, sai karfe tara na safe muka tashi. Muka yi wanka muka kimtsa, an kawo mana abinci daga gidan su Abbu muka fita parlour muka karya. Falon madaidaici ne wanda ya dauki wasu rantsattsun beige couches guda biyu an jera su daya ta kalli gabas daya kuma ta kalli arewa, sai wasu Everette chairs navy blue guda biyu suna fuskantar couch daya, a tsakiya kuma an saka babban teburin gilashi kasan shi wasu woods ne suka tokare shi, a sama kuma an dora flower base mai kyau, sai lamp mai kama da bishiya, kasan parlor hardwood flooring aka yi, kai komi dai na falon ya fita very unique, muka hau kan dinning mai cin kujeru takwas muka karya.
Dakina muka koma Anty Shafa sai cafta take sauke min tana karawa duk da wasu abubuwan duk tuni ne take yi mun. Karfe daya munyi sallar Azzuhur sai ga Abbu shi da abokan shi biyu, nayi sauri na dauko hijabi na dora akan kayana, falo muka fita muka gaisa dasu, ban yi gigin daga ido na kalli kowa ba. Ramlah ce tayi jigilar entertaining dinsu, ni kam suna fara cin abubuwan data kai musu nayi wuf na fada daki. Gefen gado na samu na zauna, ban jima ba sai ga Abbu shima ya shigo. Kai tsaye inda nake zaune shima yazo ya zauna a gefena, hannuwana duka biyun ya kamo da daya hannunshi, dayan kuma yayi amfani dashi wajen dago kafadata, ya wani rausayar da kai, “me nayi ne yau kuma Babyn? Babu gaisuwa, babu murmushi, babu kallo?" na sadda idanuna kasa tunda ya rike fuskar, duk yadda naso in daga baki in gaida shi kasawa nayi, wani irin nauyi da kunyar shi da ban taba ji ba naji sun dabaibaye ni, ya nisa, “bari in maida su AbdulHameed gida in kuma dauko direban da zai maida Anty gida sai in dawo gare ki gabadaya koh?" ya kai hannuna bakin shi yayi kissing as usual kafin ya fita.
Yana fita su Anty suka fara shirye-shiryen tafiya, nayi rau-rau da idanuna nan Anty ta samu abin fada, abin mamaki kuma bayan kamar awa daya da taji direba yazo sai kuma ta hau sharar kwallah, nan na rungumeta ina kuka, Ramlah ma tana gefe tana matsar kwallah, Abbu da kanshi ya leko ya sanar da ita zuwan direban. Ta mike tana share hawayenta tare da rataya jakarta, ta kamo hannuna ta rike cikin nata, “to Nafeesah, sai watarana, Allah ya baku zaman lafiya da maigidanki da abokiyar zaman ki, hakurin nan dai da kowa yake gaya miki kiyi da biyayya shi zan kara jaddada miki, sai kinyi exercising hakuri sannan ne zaki ci ribar rayuwar aure duk da nasan ki da hakuri amma dole sai kin kara kinji? Allah ya miki Albarka" na gyada mata kai ina hawaye.
Ta sa kafa ta fara tafiya Ramlatu ta bita a baya nima na bisu, a bakin falo Abbu ya dora min hijabin dana saka lokacin da abokan shi suka zo, muka karasa fita har shi. Ina tsaye har Anty Shafa ta shige mota Ramlah ma ta shiga different mota tunda ita gidan Anty Haleemah ta nufa. Direba ya tashi motar suka tafi muna daga musu hannu har maigadi ya maida gate ya rufe, wasu hawaye suka kara gangaro min a kumatu, shikenan an tafi an barni ni kadai. Abbu daya tsaya a bayana ya sakalo da kanshi ta wuyana tare da zagaye ruwan cikina da hannuwanshi, duk da halin da nake ciki sai da naji wasu abubuwa na min yawo a jikina, a hankali yake magana, “m sorry Baby, In Shaa Allah ni zan maye miki gurbin su Daddy dinki kinji? Stop crying kinji? Yau ce rana ta farko fa da zamu rayu karkashin rufi daya a matsayin ma'aurata, rana ce mai matukar muhimmanci don haka babu kuka ok?" na gyada kaina a sanyaye, ya sake ni ya juyo dani ina fuskantar shi, hannu yasa ya goge hawayen fuska ta, ya kama hannu na yana min murmushin nan nasa mai kwantar min da hankali muka koma cikin falo. Muna shiga aka kira sallah, ya shiga dakina yayi alwala ya tafi masallaci ni kuma na tada kabbarar tawa a daki abina.
Bayan na gama sallar falo na koma na zauna ina kallace-kallace har Abbu ya dawo daga masallaci Maigadi ya biyo shi a baya da kuloli a hannunsa, na tashi na karbi kulolin na shiga kicin na fito na plates da cokula, Abbu yana kan dinning table a zaune naje ina wani sunke-sunken kai na zuba mishi abincin na tura gaban shi, nima na zuba nawa naja kujera da take fuskantar shi na zauna. Tsam naga ya mike dauke da plate dinshi a hannu, na bishi da ido cike da mamakin abinda zai yi naga yaja kujerar gefena ya zauna, abincin plate dina ya juye a cikin nashi plate din, yace “daga yanzu we share one plate, spoon, and if possible har kujerar zama kin gane?" ni kam dai nawa gyada kai ne, jina nake kamar wata sabuwar halitta. Cikin sanyin jiki muka fara cin abincin, idan yaci sai in karbi cokalin shi nima inci haka har muka gama cin abincin na tattara kayan na kai kicin na wanke kafin na koma falon, yana zaune yana waya ya miko min hannu, a kunyace naje na zauna a gefenshi, yaci gaba da amsar wayar shi ni kuma naci gaba da kallona, ya gama wayar ya janyo hannuna cikin tafukan hannayen shi duka, kunshin da aka sake min yake shafawa da alamun yana son kunshi sosai, ya fara ja na da hirarraki duk don in samu in sake dashi amma ina, na kasa. Yau dai gabadayan shi ya koma min kamar wani bako, irin awkwardness dinnan da ake ji when you were stuck up with a total stranger a waje daya shi nake ji, bai takura akan lallai sai na saki jiki dashi ba.
Sai da aka kira sallah sannan muka tashi, yace min sai bayan sallar Isha zai dawo nace toh. Daki na shiga nayi Alwala na fito nayi sallah, akan abin sallar na zauna ina tilawa har aka Isha na tashi nayi na hada da Shafa'i da Wutiri.
Gefen gado na koma na zauna na dauko wayata, babu caji ma a ciki. Anty Shafa na kira na tambayeta ko ta sauka lafiya, nan muka gaisa da ita ta ba Mommy wayar muka gaisa kafin Anty Shafa ta sake amsar wayar, wata riga ta kwatanta min a cikin kayan barci na tace ita zan saka idan zan kwanta nace mata to, kafin muyi sallama ta kara jaddada min in saka rigar fa nace mata to dai. Bayan mun yi sallama da ita Ramlah na kira, ta daga da shakiyancin ta wai ina na baro angona nake danna mata kira da dare? Nan muka fara hira har Abbu ya dawo daga masallaci misalin karfe tara, na mata sai da safe na ajiye wayar ba tare dana kula da tsokanar da take jifana dashi ba.
Dangin fruits ne ya dawo dasu sai gasasshiyar kaza, na dauko plates da wuka na kawo, muka zauna muka ci duk da dai tsakura kawai nayi fruits dinne ma dai na ci sosai, ya tsiyaya fresh milk mai sanyi a cikin cup ya miko min shima ya zubawa kanshi, na amsa na kafa kai na shanye ta ban bar ko digo ba. Ya kalleni “kin koshi?" na gyada kai, yayi hamdala shima ya karasa shanye nashi madarar. Na hada komi na kai kicin, na wanke na wankewa, sauran fruits da kazar kuma nasa a fruit. Ya leko kicin din ya tsaya a jikin kofa yana kallona, jin idanunshi a kaina yasa na juya, murmushi yayi yace “have you prayed?" na gyada kai, ya rausayar da kai gefe, “idan kin gama kije ki dauro alwala ki same ni a dakina" ya juya ya tafi ya bar ni ina zare idanu.
A sanyaye na gama shirya kayan na koma daki, wanka na fara yi na daura alwala ba shafa lotion mai kamshi na fito, cikin wardrobe na lalubo rigar da Anty Shafa tace in saka. Wata silk trim gown light purple wadda ta kai rabin cinyoyina, gabadaya saman rigar lace ne mai kama da net, na zura rigar ina karewa kaina kallo ta cikin mirror, gabadaya cinyoyina a waje suke kamar yadda ilahirin kirjina yake waje kai har ma cibiyata, ta yaya ma zan iya fita gaban Abbu a haka? Ni kaina kunyar kaina naji, nayi kamar in cire rigar sai na fasa, after dress na laluba na dora, na dauki hijabi na saka na fesa turare a jikina tun daga na jiki har na kaya.
Kafewa nayi a tsakiyar daki ina tunanin ta yadda zan karasa dakin Abbu, inje in ce me? Ni ba wawiya bace, nayi karatu daidai bakin gwargwado na kuma san muhimmancin sallar dana yiwa alwala yanzu kamar yadda nasan abinda zai biyo bayan hakan. Gabana yayi wani irin bugu just for the mere thought of it, me zai faru yau kam? A dan tsorace na kalli kofa jin ana taba ta, Abbu ya shigo dakin amma ba gabadayan shi ba, ganina a tsaye ya dan yi frowning, “me kike yi? I've been waiting for you fa" nace “ai.. Ehh dama yanzu zan zo ai!" ya kara bude kofar alamun in wuce, ba musu na bi ta gefenshi na wuce gabana na dukan tara-tara, ina jin lokacin da ya kashe wutar dakin tare da rufo kofar, gabana yaci gaba da luguden daka da yake yi har kafafuna na rawa. Yayi gaba na bishi a baya kamar wadda take jan kafar ta. Dakin shi shima ba wasu tarkace bane, daga gado wanda zai iya kwasar mutane uku, sofa, bedside table da lamps, walk-in closet sai toilet. Dakin zagaye yake da rug carpet mai zane baki da fari kamar jikin zebra. Ya shimfida mana abin sallah ya umarce ni da in bi bayan shi, Nafila ya fara jerawa sai da muka yi raka'ah takwas, ya fara jero mana addu'ah samun zaman lafiya mai dorewa da zuri'ah mai Albarka a rayuwar auren mu ina amsawa da ameen a cikin raina.
Ya tashi ya nade abin sallar, ban yi yunkurin mikewa ba ina zaune a inda ya barni ina satar kallon shi, dakin kayan shi ya shiga, ba a jima ba ya fito sanye da pyjamas na Marks and Spencer masu taushi ash color, ya latsa wani abu mai kama da remote hasken dakin ya dauke ya fara kawo wani jan haske an jima kadan sai blue ya kawo. A hankali naga ya daga kafafun shi ya fara takowa inda nake zaune, duk taku daya sai bugun zuciyata ya karu. Yasa hannuwanshi biyu ya daga kafaduna tare da mikar dani tsaye, hijabin jikina ya cire ya ajiye akan abin sallar, ya kai hannu yana kokarin balle maballan doguwar rigar jikina, da sauri nasa hannu na rike, daya hannun ya saka ya rike min hannun ya cigaba da balle buttons din rigar, ina jin lokacin da rigar ta sulale daga kafaduna ta sauka akan tafin kafata, da sauri na rufe idanu na don nasan ba zan taba iya hada idanu da Abbu ba.
Hancin shi ya kai cikin gashin kaina ya shaki kamshin, a hankali kanshi ya fara gangarowa har ya kawo wuyana ya fara wani shinshinata, “Masha Allah baby! I like this scent.... Really!" ya fada cikin wata irin murya da ban taba jin shi da ita ba, faduwar gabana ta karu, rawar jikina ta linka ta da, a hankali naji wani abu mai sanyi da lema yana tracing din ilahirin wuyana da samar kirjina, a rikice naji kafafuna sun fara sulalewa kasa yayin da gangar jikina ta bisu zamu zube gabadaya, ji nayi an daga ni sama cak an dora akan gado, ba bata lokaci ya biyo bayana ya dora leben shi akan fuskata ya fara bin ilahirin fuskata da ruwan kisses har da lasa kamar wata alewa har ya gangaro wuyana, ai gabadaya wuta dauke min tayi, na manta a duniyar da nake, na kasa tuna a inda nake, babu abinda nake fahimta da ganewa sai lebuna, harshe da hannuwan Abbu da suke yawo a gabadayan sassan jikina. Haka kawai naji hawaye suna zubo min wanda ban san dalilin su ba duk da dai nasan cewa hakan baya rasa nasaba da sabuwar rayuwar da Abbu yake kokarin jefa ni ciki. Goshina ya hada da nashi yayin da hannun shi yake share min hawayen dake gangarawa suna shiga har cikin kunnuwana, “why baby??" ya rada min a kunne, tsikar jikina ta tashi a take rawar jikina ya karu, wasu hawayen suka kara zubo min, yace “nooo baby, don't cry please. Please kar ki hana ni mallakar ki Nafeesah, I really want to do this please??" ni wacece da zan hana shi abinda yake mallakinshi ne, ni wacece da zan hana shi samun farin cikin shi?? A hankali nayi nodding kaina, yace “thanks baby... I won't hurt you I promise, I'll be gentle In shaa Allah! I love you" hannu nasa na rungumo shi kawai ina hawaye, and that is the invitation he needed, ya hade bakina da nashi yana tsotsa exploringly kamar zai hadiye ni.
Ba a dauki lokaci mai tsayi ba dakin ya cike da sautin shesshekar kukana, tun ina daurewa tsananin azabar da nake ji har na saddakar na bude baki na fara kuka da magiya har ina kokarin ture shi daga kaina, abin yafi kafin tunani na duk da cewa bai kai ma rabin zafin da nake hangowa ba irin wanda naji ana bada labari, amma azabar is still unbearable. Sai daya nutsu ne ya ankara da kukan da nake zubawa kamar wadda ake zarewa rai, ya fara jijjiga ni a hankali yana tafin bayana ba tare da yayi magana ba. Sai da numfashin shi ya dawo normal naji yayi magana, “I am sorry, did I hurt you?" a hankali na girgiza mishi kai, duk da akwai zafi amma nasan bai kai wanda za ace yaji min ciwo ba. Ya gyara min kwanciya a jikin shi tare da janyo bargo ya rufe mu, “ok, yi barci baby" muryar shi was soft, very soothing. Na lumshe idanuna ba bata lokaci barci yayi awon gaba dani. Cikin barci naji lokacin daya tashi ya shige toilet, na kara kudundunewa a cikin bargo.
Sai da asubahi sannan na farka shima wasu tausasan hannuwa ne naji suna shafa min kumatu, na bude idanuna inda naci karo da fuskar smiling Abbu, “Hii sleeping cutie pie, a tashi koh?" na dan motsa, slight pain din da naji ya ratsa ni yasa na maida kaina cikin bargo a sukwane, sai lokacin kwalwata ta tariyo min daren jiya. Yayi chuckling kafin naji an daga ni sama daga ni har bargon na fara wutsilniya amma bai dire ni ba sai cikin bath tub wanda aka tara ruwa mai dumi a ciki. Ya zare bargon jikina ya ajiye akan dressing table, ya dawo ya fara kokarin min wanka. Duk yadda naso ya fita ya kyaleni sai hakura nayi, ya taimaka min nayi wanka tare da dauro alwala, ya dauko towel mai fadi ya nade ni a ciki ya kara ciccibana muka koma daki. Rigar jiya ya dauko ya saka min kaina yana kasa na kasa hada idanu dashi duk da tsokanata da yake yi, nan ya tafi masallaci ya barni na lallaba na hau kan abin sallah na tada kabbara. Ina gama sallah na koma kan gado na sake nadewa saboda barci, ina jin sanda Abbu ya dawo ya hau kan gadon ya nado ni cikin jikinsa, na kuwa kara shigar da kaina cikin faffadan kirjin sa na lafe.
~Hahhh, If you were ask to say One Word for this night, what will you name it?
~Wa zai iya shiga kwalwar Abbu ya fada mana abinda yake cikin zuciya da Ruhin shi??
~Have a very nice and wonderful Weekend Dearies., Love you
#TeamAbbu
#OneLove
#AnaTare
*♡Jeedderh♡*
[12:22PM, 2/18/2018] +234 703 300 1537: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*®°•Fikrah Writers Association°•*🖋
*51*
Hasken rana daya haske min idanu ne ya katse min daddadan barci mai cike da natsuwa da nake yi. Na bude idanu na a hankali na sauke su akan agogo, karfe tara da kwata. Na maida dubana zuwa ga curtains din dakin wadanda aka daga sama, hakan ya ba haske da zafin rana damar lekowa ta cikin manyan windows din dakin. Abbu baya kan gadon kuma nasan da kyar idan yana toilet, ko ina ya shiga? Na tashi a hankali na nufi tagar da niyar rufewa, wani dan guntun murmushi ya subuce min lokacin dana yi tozali da terrace garden a bayan dakin, shuke-shuken roses da different flowers and plants ne wadanda suka kawata wajen matuka, ga wooden couch nan mai raga-raga kamar anyi saka a tsakiyar wajen inda zaka zauna ka huta, naja numfashi na shaki kamshin furannin har ina lumshe ido, sai dana gaji da tsayuwa sannan na saki curtains din, komawa nayi na yaye zanin gadon na je dakina na dauko wani na dawo na shimfida shi kuma dayan na jefa a cikin washing machine na shanya shi a nan cikin toilet din wajem da aka tanada musamman for laundry. Kayana na tarkata na wuce dakina, na jiyo motsi a kicin amma ban leka ba. Ruwa na tara mai dumi na shiga na kara gasa jikina don har lokacin ina jin zafin wajen, na daura babban towel a jikina na fito na zauna a gaban dressing mirror nayi goge-goge da shafe-shafe, kwalliyata nayi kamar yadda ya zame min Al'ada, na fesa turaruka masu kamshi mai kwantar da hankali, jiya naga Anty Shafa tana jera su a kan dresser din nasan ita ta sai min tunda Arabian perfumes ne ita kuwa yawanci irin turarukan da take amfani dasu kenan.
Kofar dakin aka turo aka shigo, cikin sakan daya na juya na kalli wanda ya shigo na maida kaina kasa na dukunkune a tsakanin cinyoyi na. Ya tako a hankali har ya iso gare ni, kaina ya dago nufin shi in kalle shi amma na jimke idanuna, murmushi yayi mai sauti, “yau kuma a haka zamu gaisa Baby na?" nayi shiru ina kokarin janye fuskata amma yaki bani damar hakan sai ma mikar dani tsaye da yayi ya kalmashe ni a cikin jikinsa, ya dora habar shi a kan gashin kaina yace “babu gaisuwa ne yau?" kaina na kan kirjin shi na girgiza alamun a'ah, kaina ya sake dagowa nayi saurin kara rufe idanuna, peck naji ya bani a kunci da lebena kafin ya sake ni gaba daya, “it's okay, na fahimta. Kunya ta ake ji ko? Yanzu zan fita a dakin, yi sauri ki shirya kizo mu yi break fast, yau da kaina na tattare hannun riga ta na hada miki break fast" idanuna suka yi walai cikin rashin sanin nayi hakan da tsananin mamaki, dariya yayi tare da dan jan hancina, “thank goodness I've got to see this beautiful eyes, yes ni na hada break fast now yi sauri kizo muci kafin ya huce, ko In zo in shirya ki da kaina?" wayyo nayi saurin girgiza kaina, yayi er dariya ya fita. Wardrobe na bude na ciro wani tausassan yadi ruwan madara riga ne da siket na saka, na lalubi silifas mai taushi na zura tare da yafa dankwalin a kaina da yake babba ne na fita.
Yana zaune akan kujera yana duba waya ina fitowa ya tashi tsaye tare da wucewa wajen dinning nima na bi bayan shi, kujera yaja min na zauna a darare shima yaja ta kusa dani ya zauna. Kwallin kula daya ce a wajen sai flask na ruwan zafi da cups da kayan shayi. Ya hada mana tea tare da daukar plate ya bude kular ya juye abundance ke ciki, nayi shagaraa da baki ina kokarin tantance abinda yake gabana. What did you expect? Konanniyar wainar kwai ce tayi bakikkirin da ita, yasa fork ya yanki kadan ya kai bakinshi kamar mai testing, yace “kar ki samu da bakin da tayi pa, bata yi komi ba" a sanyaye na dauki fork nima na kwaikwayi yadda yayi, abu na farko daya fara ratsa min harshe shine dan banzan gishiri sai kuma dacin konewar da tayi ya biyo baya, ganin yana kallona yasa na takura tun karfina na hadiye kwan, take zuciyata ta tashi, ya daga min gira, “ya??" na dage tun karfina na kakaro yaken tare da mishi 👌 alamun good, yayi murmushi. Wata na sake cirowa na kai baki, wannan karon na jima a bakina kafin na iya hadiyeta. Na ja kofin shayin na fara sipping, gani ba gwanar shan shayi da madara bace. Shi kanshi daya kai loma ta biyu gani nayi ya dakata yana kallona, “kamar gishiri yayi yawa koh?" nace umh. Ya kara kai ta uku bakinshi na bishi da kallo tsigar jikina har tashi tayi, ba shiri ya furzar da ita ya lalubi kofin tea ya kora dashi.
Kallona yayi yace “sorry baby, ko zaki zan sama mana wani mu ci? Da alamu na manta yadda ake girki ko don na jima ban yi ba?" kamar jira nake, na tashi na hade kan kayan na nufi kicin. Store dinmu shakare yake da kayan masarufi wanda nasan kila zai iya daukarmu shekara kafin mu ci rabin kayan, murmushi kawai nayi tare da girgiza kai, Daddy!.
Cikin mintuna talatin na gama soya chips da plaintain, nayi vegetables sauce na dauka na kai mana muka yi break. Na tashi na hade kayan waje guda Abbu ya biyo ni da wasu. Na ajiye kayan tare da juyawa, da sauri Abbu ya riko hannuna, ban kalleshi ba na sadda kaina kasa, yace “are you ok Nafeesah?" na gyada mishi kai a hankali, yace “please Ki daina jin kunya na haka Baby, kin riga da kin zama ni kamar yadda na zama ke. I need you to be free, frank and comfortable idan muna tare, bana jin dadin hakan da kike yi. I know it'll be awkward, but still kiyi trying mana kinji?" na gyada mishi kai, yace “noo, amsa min da bakinki" na daga bakin da kyar nace “toh" ya kai bakinshi kan nawa ya dan tsotsi leben nawa kafin ya dago yana murmushi, “datz you baby...., zan fita yanzu me zan kawo miki?" nace “babu komi" yace “k, ki kunna kallo ko ki shiga dakina a study room akwai kayan exercise ko kuma just do anything so that you won't be bored don zan dan jima, sai na dawo" nace “a dawo lafiya, Allah ya kiyaye hanya" yace “Ameen Nafeesah ta" ya juya ya fita bayan ya bani peck a goshi. Ni kuma na fara wanke kayan da muka karya dasu.
Yinin ranar a kiraye-kirayen waya da chatting nayi shi, babu wanda ya leko gidan kamar yadda ban ga kiran kowa a waya na ba sai na Abbu yana tambayana me nake yi? Lokacin ina study room dinshi bayan na gama gyaran dakinshi da nawa dama gidan gabadaya, sai kuwa Anty Shafa data kira bayan rana ta daga sosai tana sanar dani a ranar da dare zata bi jirgi ta koma gida, na mata godiya game da Alkhairanta a gare mu, muka yi sallama da ita tana jaddada min in fa dinga shiga ruwan zafi har naji kunya ta kama ni. Daga nan naci gaba da gudanar da harkoki na. Abbu bai shigo gidan ba sai bayan la'asar, sai lokacin nayi lunch ko ince muka yi. Ba laifi na dan sake dashi ranar, ba wani awkwardness da strange feelings irin na jiya sai er kunya wadda itama kafin dare yayi na neme ta na rasa, not that I care don ni fa duk abinda zai saka Abbu na cikin farin ciki shi nake aiming yayin da yace shi fa kunyar nan ta dame shi don haka na jefa ta cikin kwandon shara.
Ranar ma a dakin shi na tarda shi bisa umarnin shi bayan nayi wanka na wadata jikina da turare, ya mana light off tare da jana cikin jikinsa ya fara lalubata at first shiru yayi, but lokacin da naji hannunsa a kan kirjina and things started becoming steamy, sai nayi sauri na janye bakina daga cikin nashi, jikina yana er rawa saboda tunano wahalar daren jiya, a hankali nace “Abbu ban warke ba fa!" muryar shi was hoarse and low at the same time yace “I know... Babu abinda zan miki baby, just a good night kiss" sai daya gama samun natsuwar shi ta hanyar ‘good night kiss' kamar yadda yace sannan yayi cuddling dina a cikin jikinshi kanshi a tsakiyar kirjina barci mai dadi ya dauke mu.
Ranar kam ya daga min kafa, wadda ta biyo bayanta kuwa yaki daga kafar despite magiyata da kukan shagwaba wadanda daga baya na fahimci cewar su suka kara karfafa mishi gwiwa ma, ranar data biyo baya ma haka and the day after that.... Soon, na zama gogayyiya kuma expert a cikin sabuwar rayuwar da Abbu ya bude min kofar ta. Mun kara karfafa Rayuwar aurenmu ta hanyar girmama Juna da shimfida kyakkyawa kuma tsaftacciyar rayuwar aure, kulawa da junanmu da tausayawa. A cikin en kwanakin kam duk wanda ya ganmu yaga wadanda suke kan ganiyar cin amarcinsu, na dan rame kadan amma still na kara yin fresh saboda kwanciyar hankalin dana samu. Abbuna kuwa ya kara kiba, jikinshi ya kara yin fresh ko ba komi nasan dadadan girke-girken da nake mishi kadai sun isa sa shi yayi kiba.
A kwana na biyar da tarewa ta, har ranar babu wanda ya leko gidanmu, Abbu ma bai cika fita sosai ba. Ina zaune da safiyar ranar a falo sanye da wasu Pakistan riga da wandon su, na gyara gashina ya kwanto har gadon bayana yana ta sheki da kamshi. Gate naji an bude, nayi murmushi nasan Abbu ne ya dawo daga fitar da yayi. Na kara gyara zamana ina fuskantar mota, yana shigowa na tare shi da murmushi. A bakin kofar ya tsaya shima yana murmushin, hannu ya mika min alamun inje, babu musu na tashi na fara tafiya cikin jan hankali ina jujjuya jikina kamar wadda take rawa, kasa daurewa yayi in karasa ya taka da sauri ya taro ni tare da rungume ni. Sai daya gama welcome kiss dinshi and stuffs sannan ya umarce ni da in dauko hijabi zai nuna min abu a waje, na shiga daki na saka na fita na same shi yana jirana, hannuna yaja muka fita compound din gidan, dalla-dallan motoci biyu Land Rover Discovery fara da Vibe ja daga ganin su sabbi ne saboda yadda suke ta sheki a cikin soft hasken ranar ta alhamis. Ya miko min keys guda biyu, cike da tsananin mamaki nake kallon su kafin na maida kallona ga motocin, da kyar na iya kakaro “wadannan keys din fa Abbu?" yayi murmushi much like a grinning, “for you baby!" na zaro idanu na cikin mamaki, “duka?" ya zagaya ta bayana tare da rungume ni, “wannan..." ya nuna min jar vibe din, “is from me.... Wannan kuma..." ya nuna farar Discovery din, “is from your Daddy" nace “Dad kuma?" ya daga kafadar shi, “yanzu aka kawo ta daga can Kaduna, sai dana fada mishi cewa na sai miki amma yace shima tunda ya siya sai ki hada duka biyun kiyi amfani dasu" Daddy, my Dad! He's really the best. Ban fada mishi ba amma already ya riga yasan da irin motar da nake muradi, nayi tsalle na juya tare da rataye hannayena a wuyan Abbu ina dariyar dake nuna tsananin murna da godiyar da nake mishi duk da bakina bai furta ba. Ya miko min kumatun shi ba bata lokaci na bashi peck a kunatun, peck din daya koma deep mouth to mouth French kiss in a wink, in another wink na tsinci kaina a tsakiyar gadon Abbu, kayan sawa suna yin koina a cikin dakin....
Later da yamma na kira Daddy na mishi godiyar Mota, “Haba Uwata bari mana kar ki bata min rai? Meye abin godiya dan uba yayi wa diyar sa abinda yake responsibility dinshi ne? Beside saboda wa nake neman kudin idan ba ke ba uwata? All I wish for you is to be happy kin gane? Sannan zan tura miki da kudin sadakin ki ta account gobe in shaa Allah" nayi saurin cewa “Daddy ka bar su a wajenka pls" yace “aah, ai hakkin ki ne Nafeesah kuma ma ni bana son kudin ki" nace “to a ba Mommy" yace “itama bata so" ba shiri na saki dariya, nan muka yi sallama dashi.
Washegari kuwa ya turo min da kudin, dubu dari biyu bayan dubu dari ne sadakin, na kira ina tambayar shi dalili sai cewa yayi ai sabida in dinga ba baki da kuma sauran kashe-kashe saboda baya son in cika tambayar mijina, sai kawai nayi murmushi tare da mishi godiya.
Ina zaune Abbu ya fito daga dakinshi yana gyara karin hularshi cikin shirin tafiya masallacin juma'ah. Na tashi na taya shi kafa hular tare da raka shi har bakin kofa, yace “In kawo miki su Hafsy ne su miki yini?" da sauri kuma cike da doki nace “ehh, please Abbu" yayi dan murmushi tare da juyawa ya tafi ina mishi Allah ya kiyaye hanya. Yana tafiya na fada kicin na hau shirya musu cookies da kayan motsa baki ga kuma abinci, ina kicin din ma suka shigo gidan su da Abbu da ihun su suna kiran sunana, da sauri na fita waje nan suka kwashi ihu suka rugo suka rungume ni, nima na rungume su ina murnar ganinsu, sai da muka nutsa sannan na dago kai ina kallon Abdullahi dake gefen Abbu a tsaye, na mishi dan murmushi ba tare dana damu da yadda bai yi joining dinsu ba. Daga baya dai muka tashi muka koma cikin falo, na dauko musu duk abubuwan dana shirya musu nan fa hira ta barke, bayan mun ci abinci Abbu ya tafi daki ya dan kwanta kafin a kira la'asar ya barmu muna ta hirarrakin mu, har baya muka fita muka danyi wasanni kafin muka dawo falon. Yini guda suka mana sai bayan magriba Abbu ya maida su gida, don Hafsy ma da kafewa tayi anan zata kwana sai da kyar Abbu ya lallasota ta hakura suka tafi. Na hada su da tarkacen sweets, chocolates da tarkace dai iri-iri suka tafi.
#TeamAbnaf
#OneLove
#AnaTare
*♡Jeedderh♡*
[12:22PM, 2/18/2018] +234 703 300 1537: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*®°•Fikrah Writers Association°•*🖋
*52*
Ban sani ba shagala ce ko kuwa mantuwa? Zancen cewa angwaye kwanaki bakwai suke yi a dakin amaren su su koma na uwargida, kai in fact na manta cewa ma ina da abokiyar zama kwata-kwata a lokacin, na manta cewa bani kadai bace wadda take da Abbu, na manta cewa Abbu yana da wasu iyalan daya kamata ya kula dasu. Muna cikin cin abinci yake fada min cewa washegari idan zai je gidan Mubeenah zai dauko cousin dinsu Zaynab diyar wata kanwar mahaifiyar su zata dinga zuwa tana taya ni kwana. Na maida spoon cikin plate dina na ajiye ina kallonshi cikin alamun tambaya, and that was when it downed on me, ranar na cika sati daya cif da tarewa which means washegari zai fita daga dakina. Jikina yayi wani irin sanyi har yana hadawa da rawa na dai daure na cije na gyada mishi kai naci gaba da tura abincin da taste dinshi ya bace a bakina.
Duk yadda naso na daure in nuna mishi hakan bai dame ni ba kasawa nayi, sai daya fahimci sanyin da jikina yayi. Ya riko hannuna ya zaunar dani akan cinyar shi tare da dago fuskata, na daga idanuna da suka fara cika da ruwa na kalleshi, yace “come on mana baby kar ki bayar dani, meye kwanaki biyu kadai? Besides, zan dinga zuwa kullum ina ganinki kinji? Kuma zamu kasance a waya a koda yaushe don haka ki daina bata ranki, ni naki ne ok? Oya, give me that gorgeous smile of yours baby" na kuwa saki murmushin tare da dora kaina akan kirjin shi.
Washegari da safe ya tattara ya tafi bayan ya jira Zainab tazo, yarinyar tana da kirki ga fara'ah, na dan girme mata da shekaru tunda shekarunta ashirin. Na raka Abbu har bakin mota duk da sallamar da muka gama yi a daki, yaso ya kaini gado a lokacin nace a'ah, ba zan shiga hakkin abokiyar zamana ba don nima bana so a shiga nawa hakkin. Haka ya tafi ina daga mishi hannu har sai daya fita daga gidan maigadi ya maida gate ya rufe kafin na juya cikin gida cike da kewar Abbu, zama nayi muka dan yi hira da Zaynab kafin na shige dakina na kwanta don jiya Abbu bai barmu mun yi barcin kirki ba.
☆☆☆☆☆
“Wannan yace a cikin abinci kamar miya ko fate zaki zuba mishi yaci, manta kowa kenan. Ina mai tabbatar miki da cewa idan har yaci wannan maganin to wallahi sai dai uwarshi ta sake haihuwar wani, kin dai ga yadda mijin Umaimah (er autar su) yake mata, uwar shi ma yanzu sai Umaimah taso yake ganinta balantana wata banzar bazara wai ita kishiya, kema to haka zaki mallakeshi..., wannan kuma...." Saddiqa ta fito da wani ruwa a cikin kwalba tana nunawa Mubeenah, “...a cikin ruwan wankan shi zaki zuba mishi, shi kuma zai sanya mishi matsanancin son ki ne, ya zama babu wata ‘ya mace a cikin idanuwan shi sai ke ina fada miki, boka Saddar ya bani tabbacin a ranar zai dankarawa ita waccar banzar kishiyar taki saki uku, shi da kara aure kuma sai a lahira. Don haka ki kula sosai, ki bi komi a hankali yadda ya dace don hakan mu ya cimma ruwa kin gane?" kamar wata kadangaruwa ta gyada kai, “yauwa, ina turaren dana kawo miki last week nace kiyi tsuguno dashi?" Mubeenah ta gyada kafada, “turare? Na ma manta inda na jefa shi" Saddiqa ta maka mata harara, “wai ke banzar wani gari ce? Duk inda yake ki lalubo shi kiyi tsuguno dashi yau ba gobe ba, yaushe girkin ki zai fita?" tace “gobe da safe" tace “bamu da lokacin batawa kenan, yau yakamata yaci maganin, yayi wanka kuma ya kusance ki kina jina? Abubuwan nan da muke yi is all for u Mubeenah, kin dai san kaf danginmu babu mai kishiya sai waccan banzar yarinyar (Shakira) don kishiyar Umaimah hoto ce, don haka kema ba zaki biyo sahu ba kin gane??" Mubeenah tace “ehh".
Tayi murmushi, “yauwa., kudin aiki dubu dari da hamsin tashi maza ki dauko min" Mubeenah ta zaro ido, “dari da hamsin?" ta harareta, “to meye dari da hamsin matukar an samu biyan bukata?" Mubeenah ta gyada kai, “hakane kam. Sai dae babu kudi a hannuna sai dai idan Ibrahim ya dawo sai in amsa a wajen shi" Saddiqa ta yago hakura, “to babu damuwa, amma to dari biyu zaki tura min tunda dai nasan kema in kika tashi ba a dari biyun zaki tsaya ba" suka kwashe da dariya.
Nan taci gaba da kitsawa Mubeenah abubuwa har yamma ta gabato sannan ta mata sallama ta tafi bayan ta kwashi manyan atamfofi biyu da lesuna cikin kayan da aka kaiwa Mubeenah na fadar kishiya bayan ta gama kwashe musu albarka, ji fa!. Mubeenah ta dawo daga rakiyar ta ta tsaya ta leka dakin Abbu, tun jiya daya dawo daga gidan Nafeesah ya leka ya gaya mata ya dawo tare da fada mata ya raba musu girki kwanaki bibbiyu bata sake ganin shi ba. Yanzu ma baya nan gashi akwai maganganu da take so suyi.
Dakinta ta koma, magungunan da Saddiqa ta kai mata suna zube akan gado, ta zauna a gefen gado tare da kura musu idanu kamar wadda take muhawara, ta saki ajiyar numfashi tare da tashi tsam ta dauki magungunan. Toilet ta shiga ta zazzage su a cikin masai tare da yin flushing, dama turaren data kai mata Harira ta ba ta jefa shi cikin kwatami. Daya daga cikin manyan abubuwa da Mubeenah bata so kuma bata ma yarda dasu ba shine bin malamai da bokaye, tana mamakin yadda mata suke yarda da karerayi da soki-burutsun bokaye da malamai, a ganinta in kura na maganin zawo to tayi wa kanta mana?? Shi yasa tasu ta matukar zuwa daya da Shakira kanwar su, sam bata cikin harkar bin malaman da sauran en uwansu suke yi, ta kan ce ita tafi ganewa tayi yaki akan abu ta yadda idan ta mallakeshi zata yi alfahari da cewa saida ta share zufa ta sha wahala kafin ta same shi ba wai a ruwan sanyi ta hanyar bokaye da yan tsibbu ba, kuma gaskiyarta.
Tunda gari ya waye take leke-leke da zarya daga falo zuwa dakinta. Ta kula kwata-kwata ya daina zama a cikin gidan, tana mamakin inda yake zuwa cikin kwanaki biyun daya mata. Tana nan zaune a daki taji tashin muryoyin su dasu Qaseem wadanda suke hutun makaranta ranar, Sai data ji shiru alamun ya shiga dakinshi sannan ta tashi tsam!.
“ok baby sai na iso, kar ki manta anjima da yamma dai zamu fita in fara koya miki tuki" na danyi tsalle daga zaune din da nake, “yeyh! Abbu na, sai kazo. Please ka taho da wuri fa!" yayi er dariya, “missing me that much??" dariya kawai nayi na kashe wayar. Shima dan murmushi yayi ya ajiye wayar yaci gaba da shirya takardu a cikin brief case din shi.
‘Baram!! Karan sautin turo kofar dakin nashi kenan kamar tashin duniya. Tun kafin ya juya yasan ko waye ya shigo, haka take shigowa dakin babu knocking balle sallama, kofar dakin ma haka take turo ta, duk ranar data shigo a hankali to ranar nema take a wajen shi.
Bata yi magana ba ta coge a bakin kofa, shi kuwa yaki daga kai ya kalleta yaci gaba da abinda yake yi har ya gama ya rufe brief case din. Wardrobe ya bude ya fara ciro kaya, ta kankance idanu cike da masifa ganin yadda yake abubuwan shi kamar bai san da Allah yayi ruwan tsirarta a cikin dakin ba.
“Ibrahim! Ina so muyi magana da kai!" ta fadi kanta tsaye cikin izza, ya juya a hankali tare da kallonta. Wani malulun bakin ciki da bacin rai suka kawo mishi wuya, wasu pyjamas ne a jikinta daga ganinsu sun dauki lokuta ba a wanke ba, ta kawo wata hular beanie ta maka a kanta fara ce amma tayi bakikkirin ta dafe alamun ta kwana biyu, gashin kanta da yayi cukus-cukus a cikin hular ya maida ta kamar irin sababbin kamun nan. Ya hade fuska sosai wadda tasa ta shiga hankalinta ba shiri amma hakan bai hanata yin dibar albarkar data kawo ta ba. “Ibrahim mai kake nufi da nine, an kawo amarya ban ga kalarta ba, ka kama ka killace ta a waje guda saboda ita er goal ce, er nasiha ta hadin kai da naji mazaje na hada matansu waje guda su musu kai baka yi hakan ba, ka dawo daga gidanta kaxo nawa amma har ka gama kwanakin ka amma sau daya na saka ka a cikin idanuna, anya Ibrahim baka dauko hanyar da amaryar ka zata raina ni ba kuwa??" ya jingina da jikin wardrobe din yana watsa mata kallon uku-taro, sai data dire aya sannan ya ajiye numfashi, “killace amarya kamar yadda kika ce nayi sabida ta kai matsayin a killace ta dinne, Nafeesah ba er gwal bace er diamond ce Mubeenah. Kawo amarya gidanki damka amana ni na hana saboda ban ga dalili ba, ke kanki ya kike kula da taki rayuwar balle har ki kula da rayuwar er wasu? Maganar rashin gani na da baki yi ina ji kin manta ne, dama can muna daukar satika ma bamu ga juna ba alhalin muna gida daya yanzun ma ina ga ai bata canza zane ba koh?" tayi tsuru tana zare idanu, maganar daya fada haka take, ita kanta bata san dalilin sako maganar ba, kawai maganar has been eating her brain ne dole ta fade ta ko ta samu sawaba.
Tayi gyaran murya tare da cewa “whatever! Amma kasan dai saboda Allah baka kyauta ba, kuma naji ance ka sai mata manyan motoci har guda biyu bayan ni ka bar ni da tsohuwa ina fama, tun kafin tafiya tayi nisa zaka fara shimfida rashin adalcin da ake cewa dama a jinin ku maza yake?" yayi murmushi cike da takaici, dama yasan duk inda zata je ta dawo dai maganar kenan. Ya daga kafada, “mota yeah, ni na sai mata daya Daddyn ta ya sai mata daya, ina ce kema lokacin da aka kawo ki an sai miki mota?" “karya ne!" ta fadi cikin hargowa, “karya kake yi kai ka sai mata, motar da kake fada ai Mahaifinka ne ya sai min da kudinshi ba naka ba mai ya hana kai ka saya min da kudin ka ko kuma yanzu daka sai mata nima ka sai min idan ba rashin adalci ba??"
Ranshi ya baci sosai, ya sha daukar fiye da haka daga wajen Mubeenah, ya sha jin munanan kalmomi daga gareta duk yana shanyewa amma yau baya jin zai iya shanyewa. Yana da hakuri sosai, sai dai duk ranar da aka kai shi bango akwai matsala. Tun daga tsawar daya daka mata Mubeenah tasan cewa ranar ta tsallake layin hakurin Abbu. Idanunshi sun juye saboda bacin rai, “enough Mubeenah! Ya ishe ki, ya ishe ni haka nan. Mota bani na sai mata duka biyu ba amma da ace idan nayi hakan Nafeesah zata karba happily da wallahi sai na sai mata fiye da mota biyu. Kin san saboda me? Saboda Ina Son Ta!! Saboda tana kula da farin cikina, saboda ita kadai nake kallo in san cewa yes! Ina da mata, in san cewa akwai wani da zan ba umarni kai tsaye yayi, akwai wadda bata zartar da komi sai da yawuna, akwai wadda zan bugi kirji ince Matata ce in kuma nuna ta a koina cikin duniyar nan ba tare da fargabar zata muzanta ni ba. Saboda ita kadai ce take bani hakkina ba tare da na biya ta ko sisi ba, saboda itace matar da nake sa ran zata haifa min yara ta kuma shayar dasu ba tare dana biya ta kudin shayarwa ba!! Saboda... Nafeesah itace komi nawa!! Zaki ga laifina idan na sayi jirgin sama na damkawa wannan matar kuwa?".
Mubeenah tayi shiru kanta a kasa, tunda take dashi bai taba mata ihu irin na ranar ba, bai taba daga murya kamar haka ba, duk abubuwan daya fada ta aikata har da ma wadanda bai fada ba duk tayi kuma sun faru, kalma daya data doke ta... “Kana Son ta?? Ni fa?! That means baka so na kenan?" without second thought ya gyada mata kai, “kwarai Mubeenah! Ni dake duk mun san cewa zaman hakuri da zaman ‘ya‘yanmu muke yi, amma zancen ‘so' kin san cewa babu shi a tsakaninmu" ta fara girgiza kai, bai jira mai zata sake ce mishi ba ya warci brief case dinshi a fusace ya ratsa ta gefenta zai fita, kofar dakin ma ko albarkacin ta rufe ta bata samu ba, tsoron shi daya Allah yasa cikin yaran babu wanda yayi over hearing din conversation dinsu yasan may be ya saka confusion a cikin kansu. Ranshi ya kara baci da wannan tunanin, daga bayan shi ya juyo muryarta a kausashe “Nafeesah!...." tun ma kafin ta gama fadin abinda tayi niyya ya juyo a fusace, “don't you ever dare drag her into this, ba irinki bace ita saboda haka ke kici gaba da laluben duniya ki barta taci gaba da laluben lahirar ta!" ya juya a fusace ya bar gidan zuciyar shi na azalzalarshi cike da bacin rai ko sallama bai wa yaran nashi ba da suke dakinsu suna kallo.
Mubeenah ta bishi da kallo cikin bacin rai na maganganun daya yaba mata yanxu, fargaba da tsoron anya bata bari kwabarta tayi ruwa ba kuwa? Dana sanin ina ma tayi amfani da magungunan da Saddiqa ta kawo mata???
******
Muna gama waya dashi falo na koma ina jiran karasowar shi. Ina cikin zaman jiran ne Zaynab ta fito daga dakin dana ware mata a sukwane tana ihu, “Anti Nafeesah.... Anty Sadiya ta haihu yanzu!!" nayi ihun nima tare da direwa cikin murna, sai da muka gama iface-ifacen na tambayeta abinda ta haifa tace Mace. Ba bata lokaci ta shirya ta tafi ganin baby. Na zauna ina jiran dawowar Abbu impatiently ina jin kamar inyi fuffuke inje inda suke. Ina dakina ina canza kaya daga shigar da nayi ta wani mini daya tsaya min a gwiwa da half vest mai hannu daya ta taryar Abbu zuwa riga da zani na atamfa, ban san ya dawo gidan ba sai dana leka waje naga motar shi a fake sannan. Abin ya bani mamaki, nayi tunanin zai shigo dakina direct idan bana falon kamar yadda yake yi, ban kawo komi a raina ba na nufin dakin da saurina cike da doki. Na tura kofar ko sallama doki bai bani damar yi ba na fara zuba mishi bayanai, “Abbu yanxu Sadiya ta haihu, kazo ka kaini in ga baby ka ji??" kwance yake yayi rub da ciki ya tura kan shi cikin filo, na zauna a gefen gadon ina dan jijjiga shi alamun ya tashi, “Abbu.... Abbu kaji?" nan ma shiru babu magana, ban sani ba common sense ne ya dauke min ko kuwa? Ban yi tunanin ina takura mishi ba ko barci yake yi naci gaba da jijjiga shi, “Abbu kazo ka kaini in ga baby kaji? Abbu??"
Juyowa yayi a fusace, cikin muryar dake hauhawa da bacin rai yace “Oh God Nafeesah!! Will you please just shut up and leave me alone??" jikina yayi sanyi ganin yadda fuskar shi take cike da bacin rai, “amma Abbu.." na fara magana in protest, “leave me alone!!" ya fada cikin karaji, sai kuma naga ya dafe kanshi da sauri, ya lumshe idanunshi na en sakanni kafin ya bude su, “please!!" ya fadi cikin sanyin murya wannan karon. Jiki na rawa na tashi na fita daga dakin ina tambayar kaina me ya hau kan shi??
Kujera na laluba na zauna cikin tsananin sanyin jiki, ban iya daurewa kwallar data taran min ba sai data gangaro kan kumatuna, gabadaya sai na dora laifin fushin Abbu a kaina. Watakila ni na dame shi da hayaniya har ranshi ya baci, kila barci yake yi na tashe shi da hayaniya kun san yadda mutane kan zama moody idan sun tashi daga barci balle shi da naje ina jijjigawa abinda Anty Shafa tace mata basa tashin mazajen su daga barci ta wannan hanyar. Ko kuma yana bukatar kadaici ne ni kuma ban kula da hakan ba? Idan haka ne kuwa ai laifi na ne. Tashi na sake yi na koma dakin, lekawa nayi kamar munafuka wannan karon yayi rigingine, na shiga dakin a hankali tare da maida kofar na rufe, barci yake yi. A hankali na dauki bargo na rufa mishi, na juya kenan naji an riko hannuna na juya da sauri. Ya bude idanunshi da suka shige ciki har sun canza kala ya kalleni dasu, take naji wani irin bacin rai na shige ni. Na samu kaina da tuhumar kaina da responsibility na bacin rai da yake ciki, a hankali nace mishi “kayi hakuri Abbu!" janyo ni yayi na fada kan gadon tare da jana jikinshi ya rungume ni, ina jin yadda zuciyar shi take bugawa da sauri, yace “noo, am sorry! I shouted at you bayan baki yi mun laifin komi ba" na kwantar da kaina akan kirjinshi ina shafa saitin zuciyar shi da hannuna, “Allah ya huci zuciyar ka Abbu na. Wanda ya bata maka rai bai kyauta min ba ni kam tunda nima yasa nawa ran ya baci" kuma gaskiya na fada, raina ya baci kwarai daga ganin bacin ran dake dankare akan fuskar shi. Yayi dan murmushi tare da jan bargo ya rufe mu dashi muka shiga barci.
Koda muka tashi ran shi wasai babu bacin rai a tattare dashi. Da yamma na lallaso shi da kyar muka je gidan Sadiya muka ga baby don da cewa Yayi wai ya za ayi in fara fita ina amaryar sati daya? Da kyar da jibin goshi ya bar ni bayan na dauki alkawarurruka da dama wadanda sirrin mu ne, daga can muka wuce ya fara koya min mota sai gab da magrib muka koma gida. Kwana biyu da yin haka visar mu ta fita kasashen ketare yawon bude ido (honey moon) ta fita. Da kaina na zauna na fitar da kasashe biyar wadanda nake matukar so da burin ziyarta a rayuwata. Muka fara shirye-shiryen tafiya amma fa bayan anyi sunan Sadiya.
~Daga yanzu ba zaku dinga ganin posting dina akai-akai ba gaskiya, mun koma school kuma things are somehow... Kun dai san lamurran en makaranta ina fata za ayi mun uziri?
#TeamAbnaf
#AnaTare
*♡Jeedderh♡*
[12:22PM, 2/18/2018] +234 703 300 1537: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*®°•Fikrah Writers Association°•*🖋
*53*
A rana ta uku da haihuwar na kara komawa gidan Sadiya daga can bayan Abbu yaje ya dauke ni da dare muka biya ta can babban gida gidan su Abbun muka gaida iyayen shi, Hajiya Siyama mutuniyar kirki ta amshe mu da hannu bibbiyu har da dan guntun fadanta wai me yasa ya barni na fara fita yanzu? Har tana karawa da cewa wai ai su a zamanin su amarya sai tayi rabin shekara kafarta bata taka kofar gidanta ba., na kama baki a raina na kara da lallai kuwa! Bayan mun gaisa ta saka mana albarka muka wuce sashen Hajja Fati itama muka gaida ta. Nan ta hada ni dasu tarkacen daddawa da sauran su. Mahaifinsu kuwa kwaryar zuma farar saka mai kyau ya bani, daga nan muka juya gida hannu riki-riki da tsaraba.
Ranar sunan kuwa da safe na tafi. Muna ta ayyuka da tsare-tsaren wajen da baki zasu zauna bayan falo. Sai bayan la'asar su Anty Mubeenah suka iso gidan ita da yaranta lokacin muna can bayan gidan muna suyar samosa wadda ake ba baki.
Ni'imah data kai wa su Anty Ameenah wadda muka soya ta dawo, ta daddabo ni tare da rada min “ga fa uwargidan ki can tazo!" naji kamar zuciyata zata faso kirjina saboda bugawar da tayi, ganin yadda nayi kuru-kuru da ido yasa tayi dariya, “haba babe cool mana, sai kace wadda zata cinye naman jikin ki?" nayi murmushin yake kawai.
Ni'imah ba zata gane halin da nake ciki ba, ba wai tsoron Anty Mubeenah nake ji ba, kawai ina fargabar yadda karon mu da ita zai kasance a matsayina na matar Abbu-Mijinta a halin yanzu, nasan ko kallon banza ba zan samu ba wannan karon, fatana daya mu rabu da ita lafiya ba tare da rayuka sun baci ba. Don haka nayi gefe daya da tunanin naci gaba da rolling din da nake yi.
Har inda muke Hafsy ta lalubo ni, nan ta zauna tana ta zuba min labarai har muka gama, aka shiga da wadanda muka yi ciki mu kuma muka shiga BQ muka yi wanka muka gyara jikinmu.
Wata uwar sun shadda muka saka a matsayin ankon suna, dark purple ta sha aikin pink din zare, Ya Allah! Zo kuga yadda na fita a cikin kayan nan. Kyawuna ya fita sosai kamar ka sace ni ka gudu, muka tsaya muka dan karkashe flashes kafin muka koma cikin gida. Bayan dogon hesitating da tunanin zanyi ko ba zan yi ba, daga karshe dai nayi sallama dakin maijego na shiga cikin dakiya duk da cewa zuciya na wani mayen tsere take yi a cikin kirjina.
Ina shiga muka hada idanu da ita kamar wadda take jiran isowa ta, ni da ita muka yi stilling a waje guda, ni na fargabar abinda zai je yazo ni yayin da a nata 6angaren ban san dalili ba.
Ta janye idanunta a kaina, yayin dana daga kafa da kyar na karasa shiga cikin dakin. Gefen gado kusa da maijego na zauna nesa da inda Anty Mubeenar ta zauna ita da kanwar ta Shakirah wadda sai dana zauna na kula da ita a wajen hakan ya kara min fargabata, a tunani na ko taron dangin cin kaniyata suka yi.
Da dan murmushina cike da yake na dubi inda take zaune nace “Anty Mubeenah ina yinin ku?" ta dage kai sama yadda kasan ba da ita nake ba, sai Shakirah ce ta amsa da er fara'arta har da cewa “su amare ne?, Ai naso lekawa har gidan naki mu gaisa Allah bai nufa ba tunda bamu samu zuwa biki ba, Allah ya sanya alkhairi!" na amsa da “Ameen" a hankali kuma a dan kunyace ina satar kallon inda Anty Mubeenah take a zaune koma ince a hakimce, to ta dare kan gado tare wani baje-baje yadda kuka san kan gadonta tana kallon kowa daya bayan daya kamar wasu bayinta ko irin en duniya dinnan da daurin kallabinta ture-ni-kaga-tsiya dinnan wanda ya fito da daddagaggiyar keyar ta gashi duk a cunkushe, sosai matar take bani mamaki. Kamar ta ace tana da saloon guda amma gashinta bashi da maraba da wata Inna ko Goggo a kauye wadda bata san menene ma'anar Relaxer, Shampoo ko Stretcher da stuffs dinnan ba.
Tashi tsaye tayi tana jan hannun Shakira tana magana kamar mai gunaguni, “Malama tashi mu tafi koh?" Shakirar ta maida ta ta zaunar tace “haba ke kuwa, ba mu jima da zuwa ba fa! Bari mu dan jima mana" ta koma ta zauna tana wasu guna-guni, fuskar nan tayi wani sha6ar babu kyawun gani, na kauda kallona daga gun su kafin cibi ya zama kari kuma.
Anty Ameenah ta shigo dakin, “Nafeesah kin ci abinci kuwa?" na dan girgiza mata kai, “A'ah Anty, bana jin yunwa ne" ta dan hade fuska, “a‘ah ban yarda ba, maza-maza tashi ki nemo abinci.... Ko don ma ina zuwa" ta juya ta fita daga dakin.
Tana fita su Hafsy su duka ukun suma suka shigo, dama kai tsaye Hafsy wajena ta taho, su kuma biyun sai da suka matso kusa sannan suka lura dani. Qaseem ne yayi tsallen murna ya karaso wajena shima yayin da Abdullahi yayi gefen mahaifiyar shi. Yaran suka zauna a gefena muka gaisa da Qaseem, na kalli inda Abdullahi yake zaune cikin er tsokana nace “su Abdullahi babu magana ne??" ya kalleni sosai kafin ya dauke fuskar shi ba tare da yayi magana ba. A take na sha jinin jikina, tun ranar da suka je gidana na kula da wasu canje-canje a tare dashi dama kawai ban yi tunanin wani abu bane mai girma amma yanzu kam, na hangi babban lamari a tare da yaron.
Muna nan Anty Ameenah ta dawo dakin hannunta dauke da plate shake da fried rice, coleslaw, da naman kaza a sama ta miko min plate din, na zare ido cike da mamaki na kalleta nace “Anty ina zan kai wannan abincin?" tace “cikin ki mana! Ni anya ma kuwa kina cin abinci yadda yakamata Nafeesah?" na sadda kaina kasa ina dan murmushi kawai. Ta zauna a gefen gado sai a lokacin ta kula dasu Mubeenah a zaune, Shakirah ce ta fara gaida ta, tayi dan murmushi ta amsa ta dauke kanta ga mayar da bakin da suke cikin dakin. Na jijjiga kai a hankali ina kara jinjina halin Mubeenah a cikin raina.
Ni dasu Hafsy muka fara cin abincin, har ga Allah turawa kawai nake yi. Ga rashin jin yunwa, ga tunanin sauyawar dabi'un Abdullahi a gare ni, abin ya daure min kai sosai. Muna cikin cin abincin naga ya tashi ya fita daga cikin dakin, da sauri na tashi na bi bayan shi.
A can bayan gidan wajen wasu shuke-shuke na same shi a zaune, ya kurawa shukokin idanuwa very lost in his thought, sai dana zauna a gefen shi sannan ya kula dani. Yayi saurin dauke kanshi ya sadda shi kasa. Dan murmushi nayi tare da gyara zama na sosai. Muka yi shiru muna kallon shukokin, can nace mishi.,
“Ka tsane ni koh Abdullahi?" da alamun tambayar tawa ta bashi mamaki sosai, da sauri ya dago ya kalleni yana girgiza kai alamun a'ah, sai dana sake ajiyar zuciyar relief a hankali kafin nace “kar ka boye min komi Abdullahi. Nasan cewa dama dole zaku tsane ni, nazo na aure muku mahaifi na zama kishiyar mahaifiyar ku, ko ba haka ba?" nan ma ya girgiza kai da sauri.
Nayi shiru tare da kura mishi idanu, idan ba haka bane ba to menene? Na juya na fuskance shi sosai tare da riko hannayen shi nace “to idan ba haka bane ba Abdullahi menene? Me yasa kake avoiding dina? Last time da kuka zo gidana dama haka kake sakewa kamar ni bakuwar ka ce wadda baka taba gani ba, you hurt my feelings you know... Now, gaya min, ni ce koh?" ya sake girgiza kai, a hankali kamar mai tsoron yin maganar yace “Abbu ne!!".
Na zaro ido cike da mamaki ina kallon shi, “Abbu da kan shi? Me ya maka? Fada min zan mishi magana kaji??" ya kura min idanu kamar ba zai yi magana ba, can kuma yayi maganar da tasa na kusa sakin fitsari a wando saboda tsananin mamaki. “cewa yayi baya son Mommyn mu!!" ya fada muryar shi na dan rawa yayin da idanun shi suka cika da hawaye.
Da gaske gabana ya fadi, duk wata kalma ta bace daga cikin kaina. Cikin sanyin jiki na kura mishi idanu nace “shi Abbu din ne ya fada maka haka da bakinsa?" yayi saurin girgiza kai, “a'ah, Mommy ya fadawa. Ni kuma lokacin naje dakin shi ince ya kai mu gidanki mu yini, shine naji yana gaya mata cewa baya son ta ke yake so!" na dafe saitin zuciyata dake bugawa, ba wai na jin dadin maganar ko fluttering ba, na takaici da wani dan tsillin jin haushin abinda Abbu yayi. A tunani na sai mazajen da basu san inda yake musu ciwo bane suke irin wadannan halaye, ashe ba haka bane.
A lokacin na fahimci cewa wasu iyayen su suke sa ‘ya‘yan su su tsani kishiyoyin iyayen su. Babu yadda za ayi ace a yabi wata ba uwar yaro ba, ko a fifita wata akan uwar yaro bai ji haushin abin ba koda uwar tashi bata da kyawun hali kuwa. Kamar dai abinda yake faruwa yanzu, wanda ba zan taba bari hakan ya faru ba. Mun gina amintacciyar rayuwa ni da yaran, they trust me, suna so na, suna girmama ni, ba zan taba bari hakan ya taba amintar mu ba.
Nace “shi yasa ka tsane ni kenan?" yayi shiru kan shi a kasa, “lokacin da naji labarin zaki auri Dad dinmu, frankly naji haushi. Me yasa muna kallon ki a matsayin yaya a gare mu zaki buge da auren Abbu? Daga baya kuma sai na fara tunanin hakan ai ba laifi bane ba, kuma zamu zama muna tare dake a koda yaushe saboda believe me muna son ki wallahi. Har lokacin da muka zo gidanki ina cikin confusion, daga karshe dai nazo nayi concluding cewa Kaddarar ki ce hakan don haka na kauda tunanin komi a cikin raina nayi niyar rungumar ki da zuciya daya. Saboda haka ne ma nayi niyar sa Abbu ya kaimu gidan ki mu yini in kuma baki hakurin abinda ya faru ranar farko da muka je gidan ki. Sai kuma na kare da jin maganganun dasu Abbun suke yi..., I was afraid! Naji tsoron cewa zaki iya sa wa Abbu ya tsani Mommy ya daina kula ta, muma yazo ya tsane mu ya daina son mu sai ke da baby idan kin haihu..., irin yadda Daddyn su abokina Ameer ya musu lokacin daya kara aure!".
Na fahimci irin tsoro da fargabar da yake ciki, na matsa tare da kamo hannun shi sosai. Nace “look Abdul, ni ba irin matar Baban su Ameer abokin ka bace kaji? Ba zan taba bari wani abun cutarwa yazo kusa da ku ba balle in cuce ku da kaina. Sannan Abbun ku yana son Mommyn ka kaji?" yaron ya kalleni sosai with so much hope in his eyes sai da naji kamar zan yi kuka. Fuskar shi ta washe da murmushi, “da gaske Anty Nafeesah?" na daga mishi kai da sauri, “sosai ma. Yafi son ta akai na ma. Kawai ranar ai ya fada min, yana so ne yaga abinda zata yi ne shi yasa yace haka. Wasa yake mata!!" na karasa maganar cikin cije baki.
Yayi ajiyar zuciya, “har naji dadi wallahi, da har na fara ji Abbu ya fara bani haushi!" da sauri nace mishi “kul! Kar ka sake maimaita irin haka kaji Abdul? Ko me iyayen mu suka mana bamu da damar jin haushin su a cikin ranmu kana jin mu? Duk abinda zasu yi suna da dalili don haka mu dinga musu uziri ka gane?" ya gyada kai cikin fahimta, “na gane. Nagode sosai Anty Nafeesah! Kiyi hakuri kuma" na shafa tattausar tattaurar sumar kanshi ina murmushi, “are we good now?" shima ya gyada kai yana murumushi. Nace “zo mu koma cikin gida kaga yamma tayi kila su Mommyn ka suna neman ka. Kada fa ka sanya damuwar komi a cikin ranka kaji?" ya gyada kai. Naja hannun shi muka tafi.
Aikuwa su Anty Mubeenah na waje suna neman shi, ganin mu tare fuskar ta ta danyi frowning da ban san ko na menene ba. Na daure duk da sanyin da gwiwa ta tayi muka karasa har gaban motar su, wanda kafin muje sun shige ciki, Abdullahi ya bude baya ya shiga na leka ta jikin taga ina musu Allah ya kiyaye hanya, Anty Shakira da yaran suka amsa cikin fara'ah yayin da mai gayya Mubeenah ta dauke kai gefe, ni dama nasan za a rina. Suka ja motar suka tafi, na sauke ajiyar zuciya a hankali na juya zuwa cikin gidan, lokacin an fara kiran Sallar Magriba.
Bayan Isha'i Abbu yazo ya dauke ni, na wa su Anty Ameenah sallama na tafi suna ta min godiyar hidimata a gare su, daga ta gangar jikina har ta jakata. Na bude murfin motar gefen mai zaman banza na zauna, Abbu ya kalleni da murmushi a fuskar shi. “ya ne baby?" na kakaro murmushin yake kawai, yayi zaton gajiya ce don haka ya tashi motar muka tafi.
Muna zuwa gidan na dafa mishi jollop din Spaghetti, ban zauna ci ba don cikina a cike yake already. Daki na shiga na watsa ruwa, na dauro alwala na yi sallar Isha'i tare da yin Shafa'i da Wutiri. Yan shafe-shafe nayi tare da zura kayan barci. Wando iya gwiwa da riga mai budadden wuya, har yau ban warke daga cuta ta ta jin suffocation idan na kwanta da riga ba, saukin dana samu shine Abbu baya ma bari na na kwana da riga, idan ya tafi gidan Anty Mubeenah ne nake amfani da riguna irin wadannan saboda ina sakewa a cikin su.
Nayi sallama a nutse na tura kofar dakin, yana kan sallaya yana Nafilfilin shi na duk dare daya saba yi. Na wuce kan gado tare da kwanciya na juya baya daga inda yake sallar na kalli bango zuciyana cike da sake-sake, ina so inyi mishi maganar ina kuma tsoron abinda zai auku ko yaje ya dawo, amma a ganina yin maganar kamar ya zama dole ne.
Ina jin lokacin daya gama sallar ya wuce gaban dresser yayi shafe-shafe da feshe-feshen turaruka kafin ya kashe wutar dakin. Ya hawo kan gadon ya kwanta a bayana tare da janyo ni jikinsa, hannunsa ya fara laluba na yayin daya kai bakinsa gadon bayana yana manna short short kisses zuwa bayan wuyana, kafin in lalubo hanyar yin protesting ya san yadda yayi ya batar min da hankali, da sauri na juya na sarkafe hannuwana a wuyan shi tare da sakar mishi jikina gabadaya, ina nufin mallaka mishi....
Yayi rigingine akan gado yana ajiyar numfashi, kaina yana kan kirjinshi yana shafa gashin kaina a hankali. “as usual, that was amazing baby, I love You!" ya fada tare da kissing din kaina. Ire-iren kalaman shi kenan a yawancin dararen ko ince lokutan da duk muka kasance tare dashi. Duk yadda naso kar inji dadin kalmar hakan bai yiwu ba, naji zakin ta tamkar zuma. Na kara shigewa cikin jikinshi tare da dora lebbana a tsakiyar kirjinshi na sakanni da basu fi biyar ba na kara maida kaina na kwantar a kirjin shi.
Wucewar mintuna masu dama, mun yi shiru ne kawai babu wanda yayi magana. Wata masaniya ta taba bani shawarar cewa lokuta irin wadannan wato lokutan bayan gama Auratayya, lokuta ne da suke kawo fahimtar juna da kara sa shakuwa a tsakanin ma'aurata, I tried, n it really works. Wani lokaci mu kan tattauna game da feature dinmu, rayuwar mu, idan ma da matsala sai mu tattauna akan ta mu warware ta. Na jefa mishi tambayar “me yasa kake so na Abbu?" maganar taje mishi a bazata saboda shirun da yayi na dan lokaci kafin yace “I don't really know, amma kyawawan halayen ki, kulawar ki a gare ni da tausasawar ki ina ji sune jigon abubuwan da suka ja ra ayina game da ke" nayi dan murmushi kawai, “I am sorry to say, but idan zaka rike son da kake min a cikin zuciyar ka zan fi son hakan" yayi shiru na dan lokaci kafin yace “saboda me?" nayi shrugging, “ina so in samu farin ciki mai dorewa da kai Abbu, ina so in rayu da iyalan ka cikin aminci da lumana da yarda da juna, idan kana fadawa kishiyata kana so na a gabanta me kake tunani hakan zai jawo min??" tashi zaune yayi sosai, nima na zauna tare da jan bargo na rufe jikina.
“me kike nufi? Kun hadu da Mubeenah a wajen suna ko? Me ta fada miki? Tana kokarin ta raba ni da wadda take so na ko? That..." nayi saurin katse shi, “ba ita bace, yes mun hadu da ita amma ko kalma daya bata hada mu da ita ba" ya kalleni sosai, “idan ba Mubeenah ba a wajen wa kika ji maganar?" nace “kayi hakuri, amma ba zan iya fada maka ba" ya kalleni, “daya daga cikin yaran ne koh?" shirun da nayi ne yasa ya gaskata zarginshi, hannu ya kai yana yamutsa sumar kan shi, “God!! Abinda nake jin tsoro kenan".
Na kara matsawa kusa dashi, “saboda haka ne nake so plssss ka daure, kada kayi sanadin da zai sa yaran su tsane mu daga ni har kai. Kaga hakan ba zai mana dadi ba" muryar shi cike da bacin rai “no way! Ita bata so na sai kuma ta hana ni son wanda yake so na??" nace “babu wanda ya hana ka son abinda ke son ka Abbu, amma kaje kana ihun kana son kishiyarta a gabanta da yayanta, hakan babu kyau. Zai jawo consequences masu dama wanda hakan ba zai mana dadi ba" ya dan girgiza kai, “I was angry!" nace “shi yasa Annabin mu SAW ya umarce mu da yin shiru idan muna cikin fushi, you should've just keep quite ko ka bar inda take lokacin da ranka ya fara baci. Ni dai don Allah kada ka sake yin hakan kaji Abbuna??!" na fada cikin sanyin murya mai dauke da roko, ya kura min idanu cikin duhun dakin kafin ya sake ajiyar zuciya., “naji! Na fahimta, hakan ba zai sake faruwa ba. Na gode, Allah ya miki albarka!" matsawa kusa dashi nayi na dare kan cinyar shi na kamo fuskar shi na rike cikin hannuna, “har kullum fahimtar ka a gare ni da saukin kan ka su suke kara saka min natsuwa da jin dadi Abbu na, Allah ya barmu tare ya kara mana son juna" yayi murmushi, “if you are that happy then show me!" ba bata lokaci na hade bakina da nashi. Kafin wani lokaci na tsinci kaina a karkashin shi, “you up to another round??!" ya fada hoarsely idanunshi na sheki da farin ciki da sha'awa, na daga baki zan bashi amsa but instead na buge da furta “Abbu....!!".
Washegari ya koma gidan Anty Mubeenah, Zaynab ta dawo da yake idan ya tafi can ne take zuwa, ranar da zai dawo kuma sai ta koma gida. Naje gidan su Anty Ameenah na musu sallama har can babban gida sai da naje, ranar daya dawo gidana da dare jirginmu ya daga zuwa Las Vegas, Paris.
~Hii! Nasan kwana biyu zaku ce shiru babu labari na, kamar yadda na fada muku karatu ne ya sako ni gaba. On that note, nake so na baku hakuri saboda zaku ji ni shiru diff na wasu lokuta saboda exams da zan fara ranar wannan litinin din. But kar ku damu shaa, In shaa Allah ba zata dauke mu lokaci mai tsayi ba. Don haka ina baran addu'ah daga gare ku, In shaa Allah idan na dawo zamu daura ba tare da bata lokaci ba!. This January In Shaa Allah!!
#TeamAbnaf
#OneLove
#AnaTare
*♡Jeedderh♡*
h*NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*®°•Fikrah Writers Association°•*🖋
In Dedication to *Beloved Anti Zee*
*54*
Cikin tsakiyar dare muka isa birnin Las Vegas, already mota daga hotel din da Abbu ya kama mana tana jiran mu a airport din, muka zuba abubuwan da muka taho dasu a bayan motar muka shiga direban yaja muka tafi sai Bellagio Hotel, babban hotel ne dake tashe a cikin birnin LV musamman kasancewar shi a cikin tsakiyar manyan waje na shakatawa da wasanni.
Garin ko ina haske tal kai kace ranar Allah Ta'ala ce, mutane suna ta shige da ficin su suna gudanar da al'amuran rayuwar su kamar ba tsakiyar dare bane.
Muna zuwa babu bata lokaci receptionist din wajen wata farar yamutsattsiyar baturiya mai fara'ah ta bamu keys da number din dakinmu dake can sama, kayanmu tuni suka riga mu isa don haka muma muka shiga elevator muka tafi har hawa na goma na biyu, dakin babba ne living room da bedroom duk a hade suke waje guda sai babban toilet dake hade da dakin, komi na ciki guda biyu ne alamun it was meant for couples.
Muka rage kayan jikinmu muka fada bandakin muka yi wanka da ruwa mai dumi don warware gajiya, muka yi alwala muka fito Abbu yaja mu muka yi Shafa'i da wutiri daga nan muka haye kan babban gadon dakin ko abinci bamu nema ba don ma wai mun ci abinci a cikin jirgi, ba bata lokaci kuwa barci ya dauke mu.
Washegari misalin karfe goma na safiyar ranar acan, mun tashi mun yi wanka mun shirya, muna zaune akan daya daga cikin sofa din dakin daya daga cikin ma'aikatan wajen ya kawo mana abincin da muka yi oda, nan muka zauna muka karya. Muna gama karyawa Abbu ya sauka kasa yace zai je ya dawo.
Na leka ta babbar tagar dakin ta gilashi wadda ta kusa cinye rabin bangon dakin, curtains din kuma anyi gefe dasu hakan ya bani damar hango titin kasar a cikin safiyar ranar, mutane da suka koma min kamar kwari da ababen hawa suna ta kai komon su, na sarkafe hannuna a kirji ina kallon su ina sake-saken abubuwa a cikin raina har Abbu ya dawo.
Ya zauna akan sofa tare da mika min hannunshi alamun inje, babu musu na tafi na zauna akan cinyar shi. Ya danyi kissing gashin kaina da goshina, nayi murmushi kafin ya ciro Sim Card wanda ake amfani dashi a kasar sabo ya bani, dama nashi tun a washegarin ranar da safe ya saka nashi a waya ya kira yaran har ma muka gaisa dasu. Tsallen murna nayi a jikinshi na rukunkume shi ina murna, dariya kawai ya dinga yi. Tashi nayi na saka a wayata na kira su Mommy da yake akwai credit a ciki, na sanar dasu mun sauka lafiya, na kira su Ni'ima da Ramlah muka shiga hira har sai da Abbu yazo ya kwace wayar sannan na kashe. Yinin ranar a daki muka yishi Abbu bai sake fita ba. Sai da yamma yace in shirya mu fita, na shirya cikin rigar jallabiya ocean blue, na dora gyalenta a kaina nayi rolling, Abbu kuma yasa pants na KC da riga body hock muka jera muka fita bayan mun rufe dakin.
Idan ka ganmu a lokacin kasan cewa kaga perfect match couple wadanda suka dace da juna ta kowane fanni. Hannuna yana sarke ana Abbu muka fita wajen hotel din, a hankali muke tafiya ta gefen titi inda aka tanada saboda masu tafiya da masu tuka keke. Yanayin weather din surrounding din gwanin dadi da burgewa, iska mai sanyi yake kadawa yana wasa da tufar mu, wani dan karamin garden ne muka je, wajen yana ta kamshin furanni da shuke-shuke iri-iri, it was breathtakingly beautiful! Masha Allah!! Abinda na dinga maimaitawa kenan bakina a bude, Abbu dariya ya dinga min da alamun ba sau daya yazo wajen ba. Yaja hannuna muka shiga zagaya wajen, wajene na shakatawa sosai, ga masu sayar da kayan makulashe iri-iri, jefi-jefi zamu ci karo da gungun mutane a waje, either wasu suna kide-kide da raye-raye ko kuma wasu suna su karate, wasa da wuta, da sauran abubuwa dai masu kayatarwa da birgewa, mu kan tsaya mu dan yi kallo ko mu sayi wani abun na motsa baki. Da lokacin magrib yayi muka samu kebantaccen waje Abbu ya tada sallah muka fara, abin mamaki wasu couple suka yi joining dinmu, bayan mun gama muka gaisa dasu nan muka tashi muka cigaba da zagaya wajen dasu, matar Hanan shi kuma mijin Amir mutanen Syria ne, suma sun zo yawon bude idanu ne, gasu da fara'ah da son mutane nan da nan muka saba dasu.
A wata karamar restaurant muka dakata, a tsakiyar garden din take ga haske yanayin setting din wajen kanshi abin kwantar da hankali ne. Babu wasu mutane masu yawa a wajen, ga kida a hankali dake tashi daga background din wajen, very romantic. A table daya muka zauna dasu Hanan, nan ma'aikatan wajen suka zo, mazan suka yi placing order yayin da ni da Hanan muke ta kashe selfies abinmu.
Muna hira a hankali dasu har muka gama cinye Chicken pepper soup, potato chips and salsa da Rich Maccaron da suka mana oda, bayan mun gama sun dauke kayan aka kawo mana chocolate cake guda biyu, Ya Allah! Ban san lokacin dana fara tafi ba ina giggling lokacin da naga cake dinmu dauke da sunana ni da Abbu, ansa Happy One Month Marriage Anniversary a jiki, kafin ince me! Amir ya tattaro mutanen wajen wai su zo su taya mu murna, nan suka zagaye mu suna tafi da er wakar su, muka bushe lights din candle din kafin muka yanka, Abbu ya saka min a baki nima na saka mishi, daga nan ya kama hannuna muka fita filin wajen muka dan juya haka nan, m not fond of waltz bama iya taka ta nayi ba haka nan dai nabi bayan Abbu, hannunshi daya ya rike kuguna dayan kuma ya rike hannuna na dama ya rike da nashi, yayin da nawa hannun na hagu yake kan kafadar shi, a hankali yake juyawa damu yana bin tattausan taushin kidan dake tashi, I was happy, really! Murmushi nake kamar wata sakara, Ya Allah! Farin cikin da nake ciki a lokacin ban taba tsintar kaina a makamancin shi ba, har ban so kidan ya kare ba, Abbu yaja hannuna muka koma seats dinmu, tafi da shewa da mutanen wajen keyi ya ragu kafin su koma wajen zaman su, nan muka karasa cinye cake din muka yi Sallar Isha'i kafin muka yi sallama dasu Hanan bayan mun yi alkawarin zamu hadu dasu washe gari.
Nayi zaton daki kawai zamu koma mu kwanta, ga mamakina koda muka shiga hotel din wani wajen muka nufa, mutane na tsaitsaye sun zagaye wani abu mai kama da round about, wajen babu wadataccen haske sosai amma hakan bai hana ka ganin mutanen dake wajen. Abbu ya janyo ni jikinshi sosai, bakinshi ya kai saitin kunnena ya rada min “are you ready?" na bude baki na a hankali nace “for what?" kafin ya bani amsa kawai naga ruwa yayi fitar burgu daga round about dinnan yayi sama, Ya Allah!! 'watching fountain show at Bellagio Hotel with Husby!' abinda ya fara fado min a rai kenan a matsayin status daya dace ace nayi a lokacin, na rukunkume Abbu cikin tsananin farinciki har ma na rasa kalmar mishi magana, kyawawan mintuna shida ruwan nan na sama da kasa in a waves, wasu nata daukar hotuna da videos mu kam muna tsaye muna ta kallo har show din ya kare. Abbu ya sake ja na muka tafi cinema dake nan cikin hotel din, muka sayi popcorn da soft drink muka sayi tikitin romance movie muka shiga, sai karfe goma sha daya muka koma dakin mu, kafin mu yi wanka, Shafa'i da wutiri da sauran abubuwa sha daya da rabi tayi already.
Na kwantar da kaina akan gado idanuna a lumshe ina tariyo abubuwan da suka faru ranar, Abbu ya hayo gadon tare da janyo ni jikin shi, kaina ya dora akan kirjinshi yana shafa gashin kaina a hankali na kara lafewa a jikin shi, “how was today?" naji ya tambaye ni, na zagaye kugun shi da hannuwa na, “it was wonderful and unforgettable Abbu" ya danyi murmushi, fuskata ya dago daidai saitin fuskar shi, “am relieved to hear that baby!" ya fada a hankali kafin ya hade bakina da nashi....
Kwanan mu biyar a Las Vegas, mun je wajaje masu dama na shakatawa da bude ido irin su HooverDam, The Venetian, mun je The Freemount Street mun kalli light show dinsu, tafiyar mu dai kam tayi yadda ya kamata, mun huta sosai mun kuma darji soyayyar mu, a kwanan mu na shida muka wuce zuwa Paris. A can muka bar su Hanan da tuni muka saba dasu, kaya da tsarabobin da muka saya kuwa Abbu ya tura mana su zuwa Beijing inda can ne kasa ta karshe da zamu ziyarta.
Muna kwance a dakin Hotel din da muke tunda muka isa Paris yau kwanakinmu biyu kenan, kaina yana kan cinyar Abbu shi kuma yana duba jarida, na dago na kalleshi, “wai ni Abbu ya zancen siyasar da ake cewa zaka fita naji shiru har yanzu?" ya kalleni yace “ai tuni na janye" na gyara kwanciyata a jikinshi, “me yasa Abbu?" yace “kawai.... Abin ne kawai naji ya fita daga kaina, dama kuma tun farko Hajiyar mu bata yi na'am da abin ba.... Ya ne?" nayi saurin girgiza kaina, “babu komi Abbu na... Kayi tunani me kyau sosai da kayi hakan" yayi kasa-kasa da idanuwanshi yana kallona cikin alamun tambaya, murmushi nayi tare da shafo tattausan sajen fuskar shi nace “da gaske babu komi Abbu, nima bana son siyasar nan fa!" yayi murmushi, datz very good ai. Nace “yau kuma ina zamu je Abbu?" shiru yayi kamar mai tunani, can ya duko saitin kunnena kamar zai min rada, “surprise!" baki na turo cikin shagwaba, “kai Abbu!" yayi dariya tare da maida kanshi ga jaridar hannunshi, ni kuma na lalubi wayata na kira Hafsy muna hira tana bani sakon abubuwan da zan sayo mata.
Ranar bamu fita ba sai da yamma, muka shirya muka fita kasan hotel din wanda bashi da nisa da Eiffel Tower, daga cikin dakuna ma kana hango tower din kamar ka mika hannu ka taba ta. Tunda muka zo nake so muje amma Abbu yana cewa ba yanzu ba, mun dai yi yawace yawace sosai mun je manyan restaurants, wajajen shakatawa dana hutawa, har wani Modern Museum of Art muka je Center George's Pompidou muka kalli hotuna iri-iri, mun shiga wata karamar Art Market inda masu zane suke baje basirar su a wajen nan aka zana hoton mu ni da Abbu, ko a haka muka tsaya it was really worth it.
Muna sauka kasa muka hadu da Vincent wadda take guiding dinmu idan zamu fita, mata ce mai fara'ah da ban dariya wadda tasan kan aikinta sosai, cikin harshen turanci muka gaisa da ita yayin da suka juya yare ita da Abbu zuwa French. Na turo baki na tsaya a gefen shi har suka gama maganganun su kafin ya kamo hannuna yana dan murmushi, “can we?" na maida mishi martanin murmushin. Vincent na tafe muna binta a baya har gaban Tower din, lokacin dana ganni a gabanta I couldn't believe my Eyes!! Na kai hannuna daya baki yayin dana kankame hannun Abbu da dayan cikin tsananin farin ciki, Abbu bai gajiya da bani mamaki da farin cikin dake gigitani tunda muka baro Nigeria. Sai dana yi calming down Vincent nata mun dariya, sannan ta mana nuni da matakalar da ake hawa can sama, tace “mu je!" na zaro ido ina kallonta tare da nuna mata elevator da mutane suka yi cunkuso a wajen, nace “ba dai steps dinnan kike nufi zamu hau ba koh?" tayi murmushi, “dear, believe me it's worth it. Mutanen nan da kika gani kila sai muje mu dawo wasu basu samu sun je ba, kuma idan kika hau elevator dinnan babu abinda zaki gani ki bada labari... Mu je!" na kalli Abbu ya min murmushi, a hankali muka daga kafa muka bi bayanta..
Kafin mu karasa sama na jigata kwarai da gaske, hawa steps din bene dari bakwai da hudu ba abu bane mai sauki lol, wai don ma muna dan tsayawa mu huta, ko kuma mu dan yi hotuna a wajajen da suka burge mu. At last! Bayan lokutan da suka fi awa biyu sai gamu on top of Eiffel Tower! Dana leka kasa ko tracing din mutane ba ka gani, sai kayi zaton cewa dots dots ne, but it was amazing really!! Na daga kai na kalli sararin samaniya, yadda ta zama soo close dani kamar in mika hannu in kamo kyakkyawar rana da take shirin faduwa saboda kusancina da ita. Mun jima a gun sosai, sai da muka huce har lokacin Magrib yayi sannan ne muka bi ta elevator muka sauka kasa, sai lokacin na yarda da maganar Vincent, sam banji dadin tafiya ta cikin elevator ba.
Sai data raka mu har hotel kafin ta mana sallama ta tafi, muka tsaya a wata restaurant anan wajen Hotel din, na zauna a lounge wajen da aka tanada don hutu yayin da Abbu ya tafi yayi sallah kasancewar ina fashi, bayan ya dawo muka ci abinci, Bhajia, steak da lemu mai sanyi. Daga nan muka sake komawa kasan Tower din inda bamu fi minti biyar da zuwa ba aka fara Fire Work! Woah, sai lokacin na fahimci dalilin da yasa Abbu yake ce min in jira ashe saboda show din ne. Naji dadin hakan sosai kuwa ba kadan ba, ban taba ganin abinda ya burge ni ba kamar kallon fireworks dinnan, idan ina kallo a cikin film jikina har rawa yake yi don burgewa, yau da aka yi displaying abin a gabana sai naji na rasa bakin magana in fayyace wa Abbu halin da nake ciki, kawai na sarkafo wuyan shi na hade bakina da nashi, ina ji ya fahimci sakon da nake son isar mishi, ya rungume ni sosai yana shafa bayana, a hankali na janye daga jikinshi ina dan murmushi cike da jin kunya, sai lokacin da ihu da iface ifacen mutanen wajen ya shiga kunnena na tuna inda muke, nan na karkata hankalina ga display din.
Bayan mintuna sha biyar aka gama display din muka koma dakinmu, Abbu yana Sallah na kira Daddy na fara bashi labari, ranar kam har sai daya gaji da saurare ya min sai da safe, na turo baki nace “Daddy har ka gaji dani koh?" dariya yayi yace ni na isa in gaji da jin story daga bakin Uwata? Na gaji ne, ga kuma Mommy dinki can tana jirana mu ci abinci" nace “to Daddy sai da safe, a gaida Mommy" muka yi sallama na ajiye wayar. Toilet na shiga na yi wanka na fito na shirya, already Abbu na kan gado don haka na bi bayan shi muka kwanta.
Daga Paris muka wuce Sao Paulo, Brazil. Kwanan mu biyar a can muka wuce Amsterdam, can kuma muka yi kwana hudu muka karasa Beijing. Kwananmu biyu a can bana lekawa ko can da nan saboda tsananin gajiya, sai a kwanaki na uku muka fita muka je kamfanin su Abbu.
Babban Kamfani ne Masha Allah! Shi kanshi ofishin Abbun wani wawakeken ofishi ne daya isa ace an gina wani karamin gida. Muna zuwa suka shiga meeting, ya hada ni da PA dinshi, Chao Shang muka zagaya kamfanin wanda ya dauke mu lokaci mai tsawo sosai kafin muka sake komawa ofis dinshi, har sai da nayi barci akan kujerar hutu kafin ya dawo, nan ya tashe ni muka koma hotel din da muka sauka.
Mun sha yawo a Beijing kamar Hauka, satin mu daya, mun je kananun garuruwa da kauyukan su mun bude idanu, mun shiga kasuwa mun yi siyayyar tarkace iri-iri da kayayyaki, Abbu dai duk inda muka je kayan jarirai ne yake saya unisex har da kayan wasanni inyi ta mishi dariya. Satinmu daya cif muka hada namu-i-namu muka dawo bayan Abbu ya hada mana kayayyakinmu an auna su a container amma fa sai da muka biya ta Bangladesh wajen Aminu kanin su. Kamanninsu da Abbu har ta baci, gashi da fara'ah da dan banzan tsokana, yana karantar Mechanical engineering ne a nan University dinsu. Already ya mana booking daki a hotel, don haka yana dauko mu daga airport can ya wuce damu, muka yi wanka muka yi Sallah muka yi abinci muka kwanta. Ranar duk nacin Abbu sai kyaleni yayi don ina jin kaina akan gado barci yayi awon gaba dani, ina jin yana lalubata amma na ma kasa daga hannu balle in maida mishi Martani, ina ji yayi kuta tare da furta bashi naci kafin ya janyo ni jikinshi. Aikuwa sai daya biya bashin nan da asubahi har sai daya kara min da alakoro.
Kwananmu biyu a can muka harhada namu ya namu muka wuce Najeriya cike da kewar Aminu da muka saba dashi sosai, shi ya zama idanun mu a can duk da cewa ba wasu yawace-yawace ne muka yi a can ba na azo a gani.
Saukar dare muka yi don haka muna yin Sallah sai barci, washegari aka yi ta zuwa sannu da zuwa da ganin gidan Amarya da wasu basu zo sun gani ba. Tsawon kwanaki uku ana ta shiga da fita kafin kafa ta daga, na tunkari Abbu da zancen ina so in je gida in ga su Daddy, idanu ya kura min a nutse lokacin kwanan shi daya a gidana, kamar ba zai yi magana ba can kuma yace “yaushe kike son zuwa?" nace “idan ka tafi gidan Anty Mubeenah gobe sai in tafi in dawo jibi" idanu ya xubo min sosai yana kallona kamar wadda notin kanta ya kunce dinnan, “haba Nafeesah! Kwana kuma? A'ah sam ban yarda ba gaskiya, za dai kije ki yini a can wannan kam na yarda amma ban da kwana" na turo baki gaba, “haba don Allah ka bar ni, yaushe rabon da in gansu har na manta fa, kuma ma sai fa nayi ziyarce-ziyarce idan naje can" yace “gaskiya ba zan iya ba Baby, kawai kije ki yini sai ki dawo" tashi nayi ina dira kafafu ni ban yarda ba nayi fushi na fada daki, ya bini da kallo yana dan murmushi.
Da yake dare ne mun gama cin abinci already, wanka na shiga nayi na shafa lotion mai kamshi sosai na aloe Vera, na shafa wani Arabian perfume mai kamshi sosai na fito dakin daure da towel a kirjina, Abbu yana zaune a gefen gado cikin pyjamas ya rungume hannuwa a kirji yana kallona, dauke kai nayi naje na bude wardrobe na fara binciken kayan barci, ban ji lokacin daya tashi daga kan gadon ba sai ji nayi an daga ni sama cak! Na dan saki kara cikin tsoro tare da kara rukunkume shi, kan gado ya dora ni tare da biyo bayana. Na fara mirginawa zan sauka yayi saurin janyo ni tare da pinning dina akan gadon ta hanyar rike min hannuwa. Kallon juna muka tsaya muna yi, a hankali ya saukar da bakinshi kan nawa ya fara tsotsa a hankali, da fari mutsu-mutsu na fara amma daga baya, wadannan effects da charming na Abbu a duk lokacin da fatar shi ta hadu da tawa suka sa na manta da zancen fushi na biye mishi...
A hankali yace “kiyi hakuri" nace “umh?" cikin daukewar hankali don bansan akan abinda yake ba da hakuri akai ba, yace “maganar xuwan ki gida, please ki daure kije ki musu yini kawai kinji Baby, please?" nayi shiru ina sauraren bugun da zuciyar shi take yi a hankali, numfashi naja nace to shikenan! Ya kara jana cikin jikinshi sosai, “oh Nafeesah! Shi yasa nake kara sonki a cikin raina kullum. Jibi zaki tafi da safe sai ki dawo da yamma ya miki?" na gyada mishi kai tare da kara shigewa cikin jikin shi.
Ranar Assabar muka dauki hanya ni dashi sai Kaduna. Misalin karfe Goma muna cikin gidanmu, kasa bari nayi mu shiga tare, na bazama da gudu nayi cikin gidan ina kwalawa su Daddy kira, a kofar falo muka ci karo dasu, nan na hada su duka su biyun na rungume a jikina, sai lokacin nasan ashe ba karamar kewar su nayi ba, har da yan guntun hawaye na. Sai da muka gama murnar ganin juna sannan muka karasa cikin falo, Daddy ya fita suka gaisa da Abbu wanda yace xai je ya dawo da yamma mu tafi, ya tafi bayan ya sauke tulin tsaraba da nayo musu daga sassa-sassa na garuruwan da muka da muka je.....
~Hii there my Lovie Dovie Fans!! Ya kuke? Miss Me?? Yeah, I can smell that. Kar ku damu, me too I miss you bhohhot kwarai da gaske. So I just steal some time ne haka na dan yi typing not that mun gama exams, har yanzu muna yi addu'o'inku are still needed., ina fata kun ji dadin chapter din ta yau??. And Wattpadians!! Ehh, naga comments da Votes suna kasa ne ya dae?? Yau dai ga chapter nan, I need to see bunches of ur Votes ta haka ne zaku nuna min how happy u guys are. Please comment line by line saboda ta haka ne nake sanin what is in u guys minds, and hu knows? Kila zuwa nan da ranar Talata ku sake ganin wata chapter, deal???
#TeanAbnaf
#AnaTare
#OneLove
*♡Jeedderh♡*
*NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*®°•Fikrah Writers Association°•*🖋
Shafin yau dungurungum naku ne mutanen Fikrah!!! Kungiya mai ban mamaki da ban Al'ajabi...., Allah ya albarkaci Alkalumanku da sauran marubuta baki daya......
*55*
Yinin ranar dungurungum a tsakiyar Mommy da Daddy nayi shi, sai bayan Azuhur ne naje gidan Anty Uwani, daga gidan Anty Uwani na lelleka gidajen kawaye na da abokan Mommy muka gaggaisa, bayan La'asar na koma gida inda muka sake dasa wata hirar dasu Dad, har wajen karfe biyar da rabi sannan Abbu ya dawo daukana. Gabadaya ji nayi yinin ranar yayi min saurin karewa, nan nayi narai narai da idanuna kamar zan saki kuka, Mommy taja hannuna muka shiga daki muka bar su Abbu da Daddy suna hira. Mommy ta saka ni a gaba tana bani shawarwari da tambayana game da rayuwar aurena, Daddy ya leko yace in tashi mu tafi, Mommy ta ciro ingantattun turaruka da magunguna ta bani a cikin leda tace sauran bayani zata kira ni. Haka muka yi sallama dasu Daddy kamar kar mu rabu dasu, muka shiga mota suna daga mana hannu muka tafi. Sai gab da Isha'i muka karasa gida kuwa....
*Washegari.....!*
“Yauwa, datz good.... Oya, juya shi a hankali mu karya kwanar can....." a nutse, hankalina gabadaya a kanshi nake bin instructions din da yake bani. Wai mota ce yake koya min duk da cewa dai dama ko a gida Daddy ya fara koya min motar dama, ban dai maida hankali bane wajen koyon kawai. A haka yana bani instructions har na maida mu gida, bayan maigadi ya bude mana gate mun shiga, na yi parking tare da kashe motar na juya ina kallon Abbu da yake kallona yana grinning ear to ear, thumbs up ya min nayi giggling, ya kamo hannuna yayi kissing bayan hannun yace “you are really a fast learner Amour, da alamu gobe da kan ki zaki je ki dawo" murmushi nayi na shafa bayan hannunshi dake rike da hannuna tsam nace “ai dama fa kaine kaki yarda, amma tuni na kware, n yes, I'm a very fast learner, always smart!" ya wani yamutse fuska tare da scrunching hanci, “anya?? Akwai abinda na koya miki amma har yau kin kasa kwarewa" baki na daga zan yi musu kafin na tuna abinda yake nufi, da sauri na bude murfin motar na fita a kunyace, bayana ya biyo yana “tsaya mana baby" amma ban tsaya ba sai a cikin daki, ya shigo yana er dariya kasa-kasa, baki na turo ina kallonshi, ya tsaya a gefena tare da kamo fuskana ya rike, “fushi kika yi koh? Ai gaskiya na fada ko karya nayi?" na ciza lebena na kasa, “haka kace koh? Ni kuwa sai na baka mamaki" gira ya dage sama alamun yana challenging dina, “oh really? Bring it on then" murmushin mugunta na saki tare da matsawa gaban shi seductively ina kallon fuskar shi, ga kunya ina ji amma I don't want to lose don haka na jefa kunyar a cikin kwandon shara na rufe for the time being, in yaso daga baya na dauko ta sai in wanke...
Bayan kamar awa daya na fito daga bayi ina goge jikakken gashina da towel, yana zaune a gefen gadona yana kallona cikin murmushi. Naja kujera na zauna tare da jona dryer ina kafe gashin kaina, yayi gyaran murya, “I admit" na juya na kalleshi tare da yin murmushi cike da kunya, “na fada maka ai!" yayi er dariya “yes Babe, shi fa dayan?" idanu na zaro sosai, ya daga min gira yana er dariya, wani dan tuntu mai kama da soso na dauka na jefa mishi, ya cafe tare da komawa kan gadon rigingine ya kwanta, na girgiza kai tare da cigaba da goge gashina.
Cikin kwana biyu kuwa na kware sosai, yau da kaina na kai shi gidan Anty Mubeenah da yake ranar girki yake komawa hannunta, bata nan ma lokacin da muka je sai yaran, bayan mun gaisa da Harira na dauki yaran muka je gidan Anty Rahina data sha zazzabi kwana biyu muka duba ta, daga can muka wuce gidan Ni'imah dake ta laulayi, muka karasa gidan Anty Ameenah, a takaice sai da yamma na maida su gida har lokacin kuma Anty Mubeenah bata dawo ba. Na musu sallama na wuce gidana inda na tarda Zainab tana jirana.
**** ****
Bayan sati daya muka koma makaranta, da kaina nake tuka kaina zuwa lectures wata rana kuma Abbu ne yake kaini. Yanxu en class dinmu duk sun san wanda na aura, na share kwanaki kafin su daina tsokana, shakiyanci da taya ni murnar aure, a haka dai muka ci gaba da karatun mu.Yau Abbu zai yi wata tafiya zuwa birnin Ikko taron karawa juna sani, daga wannan taron ne muke fata za a bashi matsayin Professor idan ya dawo. Da yake kwana na ne ranar ni na taya shi hada kayan shi wadanda zai bukata. Tafiyar kwanaki shida ce zai yi. Ni na raka shi har airport, sai da naga tashin jirgin su sannan na koma gida cike da kewar Abbu na, har yau na kasa sabawa da rashin shi a kusa dani.
Kasancewar muna waya dashi, chatting, sometimes ma har video call, shi yasa ban ga tsayin kwanakin da yayi ba, kwanaki shidan na cika kuwa ya dawo, zai karasa kwana daya a gidana kafin ya koma gidan Anty Mubeenah. Na tare shi da murnata da tarin delicious abinci dana hada mishi kafin muka dire a gado inda muka nunawa juna tsananin kewar juna da muka yi. Washegari ya koma gidan Anty Mubeenah.
*****
Muna gama lectures da misalin karfe biyar na ranar Alhamis, na fito daga class din a dan gajiye na nufi parking lot inda nayi parking Vibe dita, na bude murfin motar kenan zan shiga naji an kira sunana, “Malama Nafeesah??" na juya ina kallon matashin saurayin daya kira sunana cikin mamaki da alamun tambaya, nace “na'am, lafiya??" Wata envelope brown ya miko min, “sako ne?" na kalleshi “sako? Daga wa??" ya girgiza kai, “I was just asked to pass it to you" na jijjiga kai, hannu nasa na amshi envelope din tare da mishi godiya, “ok thanks" yayi nodding kan shi kawai ya juya ya tafi. Na bishi da kallo kafin na gyada kaina kawai na bude motar na shiga tare da mata key bayan na jefa envelope din a bayan motar, ina kokarin yin kwana na juya na dan kalli gefe na na dama kadan kafin na wuce.
Koda na isa gida wanka na fara yi tare da dora abinci naci, Abbu yana gidan Anty Mubeenah Zainab kuma taje gida da yake yanzu na saba da zama ni kadai. Da dare Abbu ya leko ya min sai da safe kafin ya tafi da yake sai washegari ne zai dawo gidana. Yana tafiya na kashe wutar gidan naje na kwanta. Haka kawai envelope din da aka bani ta fado min a rai, na tsinci gabana da faduwa sosai. A raina na raya sai washegari zan duba. Washegari Abbu ya dawo, da yake sai karfe goma nake da class bayan mun karya ya wuce dani makaranta. Da aka tashi sai na biyo adaidaita ya dawo dani gida don shi Abbu ya wuce masallaci.
Zan wuce ta gaban motar idanuna ya sauka a bayan motar na hangi envelope din nan, motar na bude na dauki envelope din na shige cikin gida, abincin rana na daura bayan na gama nayi wanka na kimtsa jikina na zauna jiran Abbu. Out of frustration na jira, na janyo envelope dinnan na bude. Hotuna suka fado daga ciki lokacin dana bude ta, na dauki hoto daya na bude. Abbu ne sanye da kayan dana gane su riga shirt brown mai bakaken lines da wando trouser baki, suna daga cikin kayan dana hada mishi lokacin da zai tafi Lagos. Yana zaune a wani waje kamar na shakatawa suna magana da what? Wata Mace ce amma ta juya bayan ta don haka babu fuska, na dan yamutse fuska tare da bude wani hoton, su dinne dai a waje guda amma a tsaye da alamu zasu tafi, na bude wani, ido na zaro ganin matar nan a jikin Abbuna!! Ya dora hannunshi akan kafadar ta, cikin rawar hannu na bude wani hoton... Da sauri na runtse idona ina jin ana min wani lugude a kirjina, Abbu shi da wata kwance a kan gado babu riga a jikin su, Abbu shi da wata kwance akan gado wata Watsattsiya tana shafa shi da filthy hannuwanta, Abbu na!! Abbu na.... Abbu dai mijina shi da wata akan gado.... Gado dai a kwance wata banzar bazara ta dora filthy mouth dinta akan precious and luscious lips din Abbu na!! Innalillaahi Wa Inna Ilaihi Raji'un..... Na kwala ihu tare da yin watsi da hotunan suka zube a tsakiyar dakin ko wanne yayi nashi wurin, wasu zafafan hawaye suka shiga zubo min a kan kumatuna..., does that mean Abbu has been lying to me?? Haba, biri yayi kama da mutum, sau tari na kan tambayi kaina taya Abbu mutum mai matsananciyar sha'awa yake iya rike kanshi daga matan banza bayan baya samun yadda yake so daga wajen matar shi?? Na yarda dashi, nayi amanna dashi, nayi zaton cewa idanun shi suna ga halalin sa ne, Ashe......!!
Ghen! Ghenn!! Ghennn!!! Toh fa!! Ga wata sabuwa inji en caca!! Me kuke tunanin zai faru da wannan hargitsi da rikici daya danno kai cikin rayuwar Auren su??
Wai shin! Me Nafeesah ya kamata tayi ne yanzu? Please comment so I'll know ur opinions....
Soooo, wattpadians!! Da alamu sakona ya iso gare ku, shi yasa nima na cika alkawari na ture karatun exam din gobe na muku typing, tunda ance kyan alkawari cikawa, so keep it up.... In shaa Allah Friday ok???
#TeamAbnaf
#OneLove
#AnaTare
*♡Jeedderh♡*
NI DA ABOKIN BABA NA....!!!
©•°jeedderh Lawals°•
®°•Fikrah Writers Association•°🖊🖊
_Soooo guys!! Alhamdulillah na gama exams dina lafiya.. Na gode sosai da addu‘o‘in ku a gare ni. Duk da haka I still have some things to take care of, saboda haka ba lallai ne ku dinga ganin posting dina kullum ba duk da cewa zan dinga iyaka kokari na ganin cewa kun samu posting akai-akai, so with this being said, can we continue??
*56*
Lokacin da aka kira sallar La'asar lokacin ne hankalina ya dawo cikin jikina, na tashi da kyar da bin bango ina jin jiri na shiga toilet nayi alwala na fito nayi sallah, akan abin sallah naci gaba da zama na kurawa hotunan dake watse a tsakiyar dakin idanu gabadaya kwalwata ta kasa nema min mafita akan abinda ya kamata inyi.
Nayi tunanin in jira Abbun ya dawo in kwashi hotunan in watsa mishi a fuska, wata zuciyar tace shake shi zan yi har sai ya gaya min gaskiyar abinda ya faru, wata tace kawai in tashi in bar mishi gidan shi bai kamata in ci gaba da zama da maha'inci ba, tunanika barkatai har ta kai ga bana fahimtar abinda zuciyoyina suke kullawa da warwarewa. Cikin wannan halin na jiyo karar mota alamun dawowar Abbu daga masallaci, na tashi da kyar naje bakin kofa na tsaya ina hangen shi yana fitowa daga cikin mota hannunshi dauke da leda, agogo na duba. Awowi uku da suka wuce ya kamata ace ya dawo gidan, ina ya tsaya? Na samu zuciyata da saka tunanika marasa dadi, ina kallon shi ya taho da waya makale a kunnenshi, at the last step da zai hada shi da kofar falon, wani tunani ya dar su a cikin raina. Abbu na ne fa? Abbu na dai the gentle and good man dana sani ba wani ba, mutumin dana zauna a gidan shi na tsayin watanni shida ba tare daya taba rike yatsan Hannuna idan ba mistake ba, da ace dan iska ne kamar yadda nayi zato anya zai iya kyale ni kuwa bayan da ace yaso ya lalata ni da tuni yayi hakan? Mutumin da ko bayan aurenmu sai daya jira da ixini na da komi kafin ya kusance ni?? Dana kara tuno wasu abubuwan sai na samu kaina da sake kallon hotunan idanuna na hango katon question akan kowannen su zuciyata na tamvaya na anya kuwa babu lauje a cikin nadi??.
Da sauri na koma na hau tattare hotunan na janyo drawer ta gefen gado na watsa su ciki tare da fadawa toilet da sauri na, dole in zauna in sake tunani kafin in yanke hukuncin abinda ya dace inyi, ina rufe kofar bayin naji shigowar Abbu dakin....
Ganin bana dakin yasa ya fita daga dakin tare da maida min kofar dakin ya rufe. Na kurawa kaina idanu a jikin mirror ina kallon reflection dina, kwalliyar da nayi ta hade da ruwa da hawaye ta maida ni kamar zombie. Ruwa da sabulu nasa na wanke fuskana na kara yin wata kwalliyar kafin na fita, akan kujera na gan shi a zaune. Yana ganina ya saki murmushi mai taushi, yayin da naji gabana ya fadi sosai, anya zan iya daurewa kuwa? Don a daidai lokacin zuciyata tana kitsa min in ci kwalar shi ne kawai. Na daure na kakalo murmushi wanda nasan ko fatar bakina bai gama hadewa bama, a sanyaye na karasa kusa dashi na dan duka tare da cewa “Abbu sannu da zuwa" ya amsa yana murmushi, “kin ga na dade koh?" na gyada mishi kai kawai, yace “wai gidan Rahina na biya, shine ta hado ni da kaya ma tace in kawo miki" ya miko min ledar daya shigo da ita na amsa tare da dubawa, turaren wuta ne sai wani kamar na tsuguno idan ban manta ba naga irin shi cikin kayayyakin da aka hado min daga gida. Na maida ledar na rufe tare da kallon shi nace “abinci?" ya lumshe idanu tare da gyada kai, “please, m hungry... Very" da ace zuciyana cikin kwanciyar hankali take da babu abinda zai hana ni kamo fuskar shi in bashi sumba a baki, a yanzu kam koda tunanin ya fado cikin raina I found it disgusting sosai. Sai kawai nayi wajen dinning table ban ko yi magana ba yayin da naji lokacin daya tashi ya biyo bayana.
Abincin na hau zuba mishi, gabadaya cikina a cushe yake nasan sam babu abinda zai shiga cikina a lokacin don haka na zuba mishi iya wanda zai iya ci kawai, ina gamawa na tura mishi su gaban shi na juya da niyar tafiya yayi saurin sa hannu ya riko hannuna, ji nayi kamar garwashi ya taba ni, kallona yayi sosai, “ina zaki je haka? Ba zaki ci abincin bane?" na girgiza kai tare da kallon shi, “naci tun dazu da naga baka dawo ba" ya kara kallona kamar wanda bai yarda da abinda nace ba kafin naga yayi murmushi tare da jan kujerar gefen shi tayi baya ya zaunar dani, “ok, zauna ki taya ni hira toh, kin san cewa dai bana jin dadin cin abinci idan ba kya gefena koh?".
Haka na zauna tare da kurawa kasan carpet din idanu ina ta saka da warwara, ban san lokacin daya gama cin abincin ba, ya juyo dani na fuskance shi, “baby, me ke damun ki ne?" ya fada cikin nuna damuwa da halin da rashin walwalata a gare shi, nima nasan cewa yaudarar kaina kawai nake yi idan har nace wai zan iya pretending inyi behaving kamar yadda na saba.
Na girgiza kaina kawai, “babu komi Abbu, bana jin dadin jikina ne kawai" da sauri ya dora hannun shi akan goshina yaji babu zafi, ya dawo dashi wuya nan ma komi normal, yace “amma jikin ki lafiya lau... Are you sure ba sai mun je asibiti ba??" nayi saurin gyada kai, “m ok" yace “idan kin ji da wani abu don't hesitate fa, ki sanar dani" na gyada mishi kai, yayi murmushi tare da cewa “good girl" fuskana ya matso daidai tashi tare da kawo bakin shi saitin nawa, ina fahimtar abinda yake shirin yi nayi saurin kauda kaina gefe ta yadda leben shi ya kare da sauka akan kumatuna ba lebe na ba, ya dago ya kalleni cike da alamun tambaya, da sauri na tashi na tattara kayan da yayi amfani dasu na kai kicin. Wanke su nayi tare da dora abincin dare, ya leko kicin din ganin ina girki yazo ya kashe gas din, a hankali na dago na kalleshi amma ban yi magana ba, kafada ya daga cikin alamun tsokana “hey chill! Ba sai kinyi girki ba yau, zan fita in sayo mana abinci" sai kawai na juya na sauke tukunyar dana dora na zubar da ruwan tare da rabawa ta gefen shi na fita.
Ina gaban wardrobe dina ina shirya kayan ciki wadanda na ciro su daga ciki musamman saboda in dauke hankalina daga tunanika, Abbu ya sake shigowa dakin. Gefen gado ya samu ya zauna yayi tagumi tare da zuba min idanu wadanda seriously na dinga jin su a cikin jikina kamar me?? Kokari nake kawai naci gaba da aikina. Can kasan zuciyata ina so in mishi maganar, sai dai ina matukar tsoron abinda xai fito daga bakinshi, ina tsoron ya amsa min da ehh shine don a hakikanin gaskiya ban san ina zan jefa rayuwata idan hakan ta kasance ba.
Haka muka wanzu har aka kira sallar Magrib, Abbu ya tashi ya shiga toilet dina ya fito daure da alwala ya wuce masallaci, sai dana ga fitar shi sannan ne nima na dauro alwalar naxo na tada kabbarar sallah, anan kan sallayar na zauna bayan na gama ina laxumi har aka yi Isha'i nayi sallah. Tashi nayi na nade abin sallar, ina ta en kimtse-kimtse na wanda a zahirin gaskiya basu da amfani ina yi kawai don kada su dauke mun tunani, Abbu ya dawo daga masallaci. Dakin kawai ya leko yace in fita mu ci abinci. Na fita falon na same shi har ya fiddo plates waje, naje gefen shi na zauna kawai.
Gashin nama ya xuba mana cikin plate din da yoghurt a cikin cups, na sa cokali muka fara ci daga cikin kwano daya. Ba wai don wani abu ko yunwa nake cin abincin ba, kawai saboda bana so Abbu ya dame ni da korafi ne don a lokacin ko kadan bana so inyi magana, gabadaya raina a jagule yake. Abu na karshe da nake bukatar yi shine in kadaice a waje guda in nemi mafita a cikin rayuwata data aurena gabadaya.
Duk da halin da nake ciki hakan bai hana ni jin dadin naman ba har ma ban san lokacin dana bude ciki naci naman sosai ba, sai dana ji cikina ya cika kafin na kora da yogurt din, lokacin Abbu ya ture kwanon gefe alamun ya koshi don haka na tattara kayan na kai kicin, sauran kayan duk na saka su a cikin freezer na fita falo. Abbu yana zaune akan kujera yana kallon labaran kasa, na shige shi zuwa dakinshi da yake yanzu yawancin kayana ma suna dakin don ragewa kaina wahalar je ka dawo daga wannan dakin zuwa wancan. Toilet na shiga nayi brush na fito na shirya cikin kayan barci tare da fesa en turaruka na kwanta. Not that barci nake ji ko kuma gajiya, kawai ina gujewa Abbu ne.
Misalin karfe tara Abbu ya shigo dakin, ina jin alamun shigowar shi na kara lafewa akan gado kamar mai barci. Ina ji ya gama duk abubuwan da zai yi kamar su brush, shafa turare, sa kayan barci da sauran su. Ina jin lokacin daya kashe wutar dakin kafin inji alamun hawan shi kan gadon, na kara sakankance jikina sosai. Ina jin lokacin daya janyo ni jikinsa, duk da ihun da naji ana min a kunne akan in kwace jikina sharewa nayi, bana so inyi abinda zai sa Abbu yayi zaton idanu na biyu. Ina jin shi yana lalubata wanda da da ne tashi zanyi koda barcin nake yi in shige cikin kirjin Abbuna mai fadi, yau kam ban yi hakan ba.
Bayan lokaci mai tsayi naji alamun yayi barci, a hankali na zare jikina daga nashi tare da juya mishi baya, wasu siraran hawaye suna gangaro min a kumatu, ban san yaushe barci ya kwashe ni ba. Da asubahi Abbu ya tashe ni daga barci ya wuce masallaci. Ina kan sallaya ina karatu lokacin daya dawo daga masallacin, kan gado ya hau ya kwanta rigingine, ban motsa daga inda nake ba har sai da gari yayi sha, na rufe al-qur'anin na mayar dashi inda ake ajiye shi na fita daga dakin. Kicin na shiga na fara shirya break fast.
Abbu ya shigo kicin din, ina tsaye ina wanke hanta a jikin sink, ya tsaya a daidai gefena na dama. Kwana daya kacal daga ni har shi mun yi wani zuru-zuru damu, hannu yasa ya kamo habata a kokarin shi nason mu hada ido, sai nayi kasa da nawa idanun na hana shi ganin kwayar idanu na. Muryar shi tayi kasa sosai cike da damuwa yace “hey, me ke faruwa da ke ne Nafeesah?" na kara yin kasa da kaina na kasa magana, ya kara matsowa kusa dani sosai har ina jin saukar numfashin shi a kaina, fuskana ya sake dagawa sama, “talk to me Nafeesah please..... Look at me" yadda yayi maganar kamar wanda yake rokona yasa na daga idanuna na kalli nashi idanun, tsananin damuwa da kulawa dana hanga a cikin idanunshi suka sa ban san lokacin da hawaye suka zubo min ba, sai dana ji dumin su akan kumatuna sannan na ankara...
Abbu ya ida hade er tazarar dake tsakaninmu tare da rungume ni kam a jikinsa, a hamkali ya kai hannu bayana yana shafawa a hankali alamun rarrashi, hakan ya kara karya min xuciya sosai... Na zagaye hannuwana a bayan shi tare da fashewa da kuka ba tare dana shiryawa hakan ba.....
#TeamAbnaf
#OneLove
*♡Jeeedderh♡*
NI DA ABOKIN BABA NA....!!!
©•°jeedderh Lawals°•
®°•Fikrah Writers Association•°🖊🖊
*57*
Bayana yake tapping a hankali ba tare da yayi magana ba, ina jin yadda zuciyar shi take bugawa da sauri ban sani ba bacin rai ne ko tausayi na? Shi dai ya bar wa kan shi sani. Hannu yasa ya kashe gas din dana kunna, yaja hannuna ba musu na bi bayan shi muka fita daga cikin kicin din. Daki ya kaini ya zaunar dani a gefen gado yayin da shi kuma ya zauna a kasa a gabana ina fuskantar shi.
Sai dana gama shesshekar kukan da nake yi da komi, ya tashi yaje kan mirror ya dauko tissue ya miko min, hannu nasa na amsa na goge fuskata dashi. Wajen daya tashi ya koma ya zauna ya kalleni..., “ok, ina sauraronki. Fada min, me ya faru??".
Idanu na kura mishi cikin tunani, shin in gaya mishi ko kuwa in yi shiru? Shin in nuna mishi hotunan ko kuwa zan ci gaba da boyewa ne ina kwarar mu?? Ganin nayi shiru ba tare da nayi magana ba yasa ya kara matsowa gab dani, ya kamo hannuwana ya damke cikin nashi tare da dora su akan cinyata, murya can kasa wadda ta dakushe cike da damuwa yace “Kalle ni Nafeesah!" na dan yi hesitating na en dakikai kafin na daga kai a hankali na kalli kwayar idanun shi, take jikina yayi sanyi sosai, na kasa daurewa kallon tsananin kulawa, so da kauna da suke cikin idanun shi sai na kara yin kasa da kaina.
Yace “Nafeesah, idan ban manta ba na fada miki cewa babu boye sirri a tsakaninmu, ba zamu boyewa junan mu Abu ba komi tsananin munin shi kuwa, amma meye yanzu kike yi? You are hiding something from me Nafeesah, kin saka ni cikin damuwa gashi na rasa gane matsalar balle in magance miki ita, please tell me Nafeesah, tell me me ke damun ki??" rikon da yayi min a hannuna ya kara karfi, ajiyar zuciya na sauke a hankali. That's it! I couldn't do this anymore, kawai bari inji ta bakin shi in yaso komi ta fanjama shi kenan.
Naja numfashi a hankali tare da tashi cikin sanyin jiki bayan na zare hannuna daga cikin nashi, ya juya ya bini da kallo. Drawer din na bude na ciro hotunan cikin faduwar gaba na koma inda yake, sai dana lalubi gefen gado na zauna kafin na mika mishi hotunan, ya kalleni sosai kafin yasa hannu ya karba, na kura mishi idanu sosai ina so in ga yadda zai karbi ganin hotunan..
Idanun shi suka fito waje sosai kamar wadanda zasu fado kasa, nuna su yake yi da hannunshi kamar wani tababbe, da kyar ya iya kakaro sautin “Naffee..sah.... Daga ina??..." cikin rawar murya yana nuna min hotunan, na kura mishi ido ina kokarin karanta kalar tsoro dana gani a cikin idanuwan shi, na tsoron asirin shi ya tonu ne ko kuma na wani abu daban?? Nace “ba kai bane ba koh Abbu??" na kura mishi idanu cikin tsananin tsoron jin amsar da zata fito daga cikin bakin shi. Kai ya girgiza min da sauri, “bani bane ba Nafeesah., I promise you bani bane ba!".
Wani irin sanyi ya xiyarci zuciyana da gangan jikina gabadaya, na silale daga kan gadon na fada cikin jikin shi na rungume shi kankam kamar zan tsaga shi, nadama ta shige ni sosai. Da ace tun a jiyar na mishi magana da hakika bamu yi kwanan rashin sukuni da bacin rai ba, da ace tun a jiya din na mishi magana da ban ji bugun zuciya da ya dinga yin kamar zai kashe ni ba, da ban kwana cikin dacin rai da fargaba ba..... Nasa kaina a cikin wuyan shi ina kuka a hankali wanda sautin shi baya fita sai jikina da yake rawa saboda danne kukan da nake yi.
Abbu ya zaunar dani a kasan carpet din yasa hannu yana share min hawayen, sai da kukan yayi kasa kafin naji ya fara magana a nutse. “waye ya baki hotunan nan? Yaushe kuma?" naja shessheka kafin nace “ban san ko wanene ba, kawai dai wani yayi mun sallama sai ya bani yace wai sako ne tun shekaranjiya, sai jiya ne na bude" ya kura min idanu kamar wanda yake mamakin abinda nace mishi.. Can yayi magana a hankali, “kuma shine kika boye min, why??"
Na girgiza kaina kawai, yace “look Nafeesah!” na daga kai na kalleshi, yace “na fahimci tsoron abinda zai biyo baya ne ya hana ki fada min. Naji dadin hakan kamar yadda naji haushin boye min din da kika yi. Daga yanzu kada ki sake yi mun irin haka don Allah kinji? Kome ya faru kada kiji tsoron fada min, ta haka ne kadai zamu gina rayuwar aure mai inganci irin wadda nake so kin gane??” na gyada mishi kaina a nutse.
Hotunan ya sake dagawa yana kara kallonsu daya bayan daya yana girgiza kai idanunshi jawur, “Wallahil-Azeem bani bane Nafeesah. Ban taba bin mata ba, ban taba kusanta kaina da zina ba, bane bani!” hannunshi na rike cikin nawa ina gyada kai, “wallahi na yarda da kai Abbu. Ban san me yasa na kasa fada maka ba tun farko, amma ba zan sake maimaita hakan ba” hancina ya dan ja a hankali yana dan murmushi, nima nayi. Hoto daya ya dago yana nuna min, “kalli nan ki gani” na kurawa hoton ido ina kallo, hoton Abbun ne a tsaye babu riga a jikin shi yayin da macen da aka nuno su tare har lokacin ba a ganin fuskarta a kwance akan gado, nace “me zan gani?” kirjin mutumin jikin hoton ya nuna min, “nan, kin ga babu alamun tabo dina” na kama baki cike da tsananin mamaki, ya aka yi ban kula da haka ba? Ba mamaki saboda idanuna sun rufe ne shi yasa. Wani tabo ne a kirjin Abbu kusa da kafadar shi, tabo ne babba wanda yace lokacin da yaji ciwon it took him almost 3 months kafin ciwon ya warke amma tabon yana nan, yanzu dana kalli mutumin jikin hoton sai naga babu alamun tabon, kai karewa ma dana kare mishi kallo sam sai naga Abbuna yafi na jikin hoton kiba, to idan ba Abbu bane waye?.
Abbu ya kuta, “da alama wani ne yake so ya shiga tsakanin rayuwar auren mu Nafeesah, shine yasa aka yi photo editing din wani da fuskana aka kawo miki don ki tada balli, koma waye yayi haka ya gina ramin kuskure mai zurfi wallahi, I wouldn't spare him!”.
Wani tunani ya darsu a cikin raina, da sauri na kauda tunanin. Abbu ya kalleni “menene?” na girgiza kai, “m not sure don zargi bashi da dadi. Amma ranar da saurayin ya bani envelope din lokacin ina kokarin karya kwana, naga the same saurayin a tsaye shi da Dr Lubah... Ganin su kawai nayi, ban sani ba ko tana da hannu akan hakan?” Abbu ya dunkuke hoton hannunshi, “Dr Lubah!!! Zata aika, ta sha fada min zata yi duk abinda zata yi duk abinda zata yi wajen ganin cewa ta raba ni da farin cikina. Ban yi zaton da gaske take ba, I thought kawai tana fada ne don cika baki ashe da gaske take? So she can stoop this low kawai don ta raba ni dake?” nace “ni fa kawai ganin su nayi tare, bani da tabbacin ko ita ce” yace “ki ma daina wani tantama, she's the one” nace “zato dai bashi da kyawu, kamata yayi ka bincika kafin ka yanke hukunci” yayi shiru kafin ya gyada kai, “haka ne kuma, zan bincika in shaa Allah.... Now.., food!” dan murmushi nayi tare da mikewa na nufi kicin shima ya biyo bayana.
Ranar tare dashi muka yi girkin, muka koma falo muka karya muna hirarrakin mu cike da nishadi, ranar ko nan da can Abbu bai fita ba, yana manne dani kamar chewing gum. Da haka rayuwar auren mu ta koma normal kamar, ko ma in ce fiye da da.
Bayan kamar sati biyu da yin haka, ina zaune a falo Abbu ya dawo daga office. Da murnata na tare shi, na taimaka mishi yayi wanka tare da cin abinci. A wajen cin abincin ne yake bani labarin yadda suka kare da Dr Lubah yace; “ai kin amsa laifinta tayi sai dana kai karar ta ga hukumar makaranta sannan, yanzu dai an mata warning game da haka. Ance idan ta sake a bakin aikinta, shine fa bayan mun fito wai take bani hakuri wai sharrin shaidan ne, ni dai na gaya mata idan ta kara bari ma muka hada hanya da ita to ta tabbatar sai na kai karar ta” nayi dariya nace “ashe da gaske ita din ce dai?” ya girgiza kai, “ai ki daina wasa da lamarinta, matar bata da mutunci da kike ganinta. Sai da maganar ta kai ga sauran malamai nake jin ashe an taba kwantar da wata budurwa a asibiti data taba ganinta a tsaye ita da saurayinta, itace fa ta dauka ta maka mata a kai. Sai daga baya ma ake fada mata ashe er uwar saurayin ce, sanadin rabuwar su dashi dai kenan" na kama baki cike da mamaki, nace “to Allah ya shirye ta tare da masu hali irin nata” Abbu yace “ameen”...
A karshen watan muka koma ainihin gidan da zamu zauna. Wani dankareren babban gida a cikin Lamido Crescent, flat ne da dakuna bila adadin. Babban falo daya dauke saitin kujeru biyu, kicin, store, sai wani corridor wanda idan ka bishi zai sada ka da wani karamin falon inda anan Dinning yake sai dakunan much ni da Anty Mubeenah. Dakin mu ciki ne da falo, sai dakin Abbu, na yara da kuma study room inda muke zuwa mu yi karatu abinmu. Komi na gidan sabo ne dal wanda Abbu ne ya dauki nauyin yin hakan, duk da dai akwai daki na musamman anan kusa da dakina wanda aka ajiye min jeren da Daddy yayi min.
Zaman gashi nan kadaran-kadahan. Muna zaune lafiya daga uwar har yayanta da maigidan, batun hali a wajen Anty Mubeenah har yanzu bata canza zani ba, tana nan kamar da da rashin kula da kanta, mijinta da rayuwar aurenta gabadaya. Abbu ya dauko en aiki wadanda suke zuwa suyi shara, goge-goge da sauran su, da kaina nake girki na in kuma gyara dakunan mu dana Abbu. Ina ji shi yasa hatta da yaran suke dokin zagayowar ranar girkina saboda dadadan abincin da nake dafa musu ba kamar abincin Harira da har lokacin tana manne damu ba.
Ranar va sai ga en uwan Anty Mubeenah a gidan ba?? Shakira da Umaimah kamar daga sama. Muna falo ina koyawa Hafsy assignment lokacin, na daga kai da er fara'ata saboda nasan ba abin arziki ne ya kawo su ba, na gaida su. Suka amsa suna wani yatsine yatsine, wai “ina uwargida ran gida mai babban matsayi a gidan Ibrahim Galadanchi?” abin ma ya bani dariya, na girgiza kai kawai. Umaimah taja tsaki, “kamar fa wannan dangin masu kwacen mijin kallon uku-saura take mana, irin wuyanta ya isa yanka dinnan” Saddiqar tace “kyaleta, karyar banza take. Yo ni Allah na tuba idan da ba don albarkacin Mubeenah ba wannan er tsakin ta isa in kalleta? Taci gaba da abinda take yi wallahi yanzu zan kwantar da mutum a kasa”.
Daidai lokacin Anty Mubeenah ta shigo falon, ganin en uwanta ta hau fara'ah, Umaimah tace “yauwa Yaya, wannan er iskar matar fa tana nema ta raina mana hankali, kinga wani kallo da take jefa mana ni da Anty Saddiqa??” Mubeenar ta kalle su kafin ta sake kallona, dan murmushi tayi ni na ma yi zaton ko zagi zata auna min, sai kawai naji tace musu “ko zo muje daki mana” da alamu suma abin ya basu mamaki ganin yanda suka hangame baki, can Saddiqa ta gyada kai, ta jefa min harara ta shura takalmi tayi gaba Umaimah tabi bayanta, Anty Mubeenah ta kallemu tace “kiyi hakuri fa!” tayi gaba ba tare da taga yadda na hangame baki a dimauce na bita da kallo ba, abin ya matukar bani mamaki kwarai ba kadan ba. Nayi zaton zata goyi bayan en uwanta ne su hadu su zageni kila ma har da duka kamar yadda naji ana bada labari, sai naga akasin haka, har da bada hakuri ma. Na jinjina kaina tare da tsintar kaina ina mata addu'ar Allah ya dawo da ita kan hanya.
Da zasu tafi ma haka suka same mu a falon ni da Hafsy, ko er Allah ya kiyaye hanya din da na musu Allah bai basu ikon amsawa ba. Na tabe baki tare da daga kafadata, basu dameni ba ko Kaden, in dai muna zaman lafiya da abokiyar zama na to shikenan ni kam.
*****
Ba a wani jima ba aka yi auren Harith shi da Ikram, na samu da kyar an bar ni naje wajen daurin aure. Wannan shine zuwana Kaduna na uku tun bayan da aka min Aure.
Ni'imah ta haifi santaleliyar yarinya mace taci sunan Halima mahaifiyar Basheer sai suke kiranta da Amal. A daren ranar ina kwance akan gadona a gajiye Abbu ya shigo dakin da yake ranar girki ta ce. Kan gadon ya hayo ya dauki kafafuna ya dora akan cinyoyin shi ya fara matsa min su, idanu na lumshe tare da kara lafewa akan gadon. Abbu yace “dube ta don Allah! Sai kije kiyi ta faman yin aiki da kai da kawo sai dare yayi kuma kizo ki dinga min raki” cikin muryar barci nace “to Abbu menene a ciki, yiwa wani yiwa kai balle su Ni'imah ne fa, idan na hidimta musu kamar kaina na hidimtawa” ya kuta, “just wait and see, idan kika haihu duk wadda bata miki wahalar da kike musu ba sai na bata musu rai” dan murmushi kawai nayi tare da maida idanuna na lumshe.
Ya juyo dani na koma rigingine, hannu ya kai yana dafa cikina, “wai ni tsaya, har yanzu ban yi ajiya anan wajen bane duk kokarin da nake yi?? Lokaci ya fara ja fa, muna bukatar jin kukan jarirai a gidan nan” nace “Allah bai kawo ba har yanzu Abbu” yace “ki ce in kara kaimi kawai” da sauri na girgiza kai, “a'ah, ba sai ka kara ba wallahi. Zan taya mu addu'ar Allah ya kawo su kawai Abbu” kai ya girgiza kamar wani karamin yaro, “naki wayon....” wuta ya kashe mana tare da janyo ni cikin jikinsa...
So how r u doing outta there #TeamAbnaf?? Abubuwa ne suka min yawa fiye da tunaninku shi yasa kwana biyu kuka ji ni shiru. We are almost there in shaa Allah?? Just about 2-3 episodes?? Ina fata zaku ci gaba da hakuri?? Enxs
*♡Jeedderh♡*
*NI DA ABOKIN BABA NA...!*
*©Jeedderh Lawals*
*®Fikrah Writers Association* 🖊🖊
*58*
*BAYAN SHEKARU BIYU DA RABI!*
Na fito daga dakin Abdullahi hannuna dauke da tarin kayan wankin dana fiddo mishi. Duka yaran suna zaune akan kujera, Abdullahi da Qaseem suna game na Super Mario, Hafsy kuma tana wasa da wayata. Anty Mubeenah kuma tana gefen Hafsy tana duba jarida.
Abdullahi ya kalleni yayin dana harare shi nace “kalleshi dirty guy kawai, sai aukin fi'ili da gayu, idan ya dau wani wankan sai kayi zaton abin har dakin shi ne sai ka shiga labari ya sha babban” Abdullahi yayi kasa da kai yayin da Qaseem yasa dariya, shima na harare shi.., “see who's laughing! Jiya dana shiga dakinta kasa numfashi nayi sai dana sa mask, wai anya kuna ma yin wanka??” Anty Mubeenah ta dan saki dariya, da sauri na juya na kalleta. Ganin ina kallonta yasa ta dauke kanta da sauri, nayi dan jim ina kallonta.
Kwanaki biyun nan ina ganin wasu canji a tare da ita, fuskarta tayi rama sosai, haka zan ga ta zauna tayi shiru cikin tunani gashi har zuwa lokacin bata bani fuskar da zamu yi sabon da zan tambayeta abinda yake damunta ba. Damuwar da take ciki na damu na, I really want to help. Na juya kaina daga kanta a hankali na tunkari kofa, Shuaibu mai mana wanki da guga na ba kayan na koma falo.
Na kallesu, “daga yau duk wanda ya cire kaya kar ya kuskura ya maida su cikin drawer, a sa a laundry bin sai a wanke, kuna ji na? Manya daku saboda Allah amma wallahi Hafsy ta ma fiku tsafta” Abdullahi ya turo baki yana hararar Hafsy da take mishi gwalo, yace “ai saboda ita gyara mata daki ake yi, mu fa?” na Harare shi, “saboda ita yarinya ce, ku kuma kun girma, kayan da aka cire should always be put in a laundry bin ok??" suka gyada kai, nace “good!" na wuce dakina.
Ina shiga karan wayata ya min oyoyo, na dauki wayar tare da duba sunan mai kiran, ganin waye yasa na dauka da shakiyanci na “amarya, amarya!!" daga can cikin wayar Ramlah ta amsa, “ke dallah can! Aure fiye da wata biyar amma kina wani ce min amarya?" watanni biyar da suka wuce muka sha bikinta ita da Ayan wanda ana daurawa suka wuce states inda a can ne yake aiki, bayan bikin da wata daya muka gama karatun mu, yanzu dai fitar sakamako muke jira kawai.
Nace “haba wata biyar ne fa kawai ba wasu watanni ba, Allah na tuba ni ko da ‘yayan ki ma amarya zan dinga ce miki" taja tsaki, “to Allah ya kyauta miki, ya zancen turarukan da na turo miki? Kin amso su kuwa?" nace “ai da kanta ma ta kawo min har gida, Masha Allah sun yi kamshi sosai, kuma suna da kyau wallahi" tace “ai sai dana fada miki, yanzu ya za ayi wajen sauran abubuwan nan da nace a kawo min?" nace “idan na hada komi zan kira ita Nadiya din, sai ta taho miki dasu koh?" tace “to shikenan... Ina Abbu?" nayi murmushi, “Abbu yaje Beijing, suna da wani meeting ne a kamfani shine ya tafi" tace “ranar nan ai na kalli show din da aka bashi award din best prof na Universities din fadin Nigeria, naji ana maganar bashi VC a BUK koh?" na gyada kai, “yeah, he deserve it ai" tace “indeed, ana fadar ayyukan shi da sadaukarwar shi indai ta fannin karatu ne ai, Allah ya kara taimako" na amsa da “ameen" daga haka muka yi sallama da ita.
Toilet na fada na dauro alwala na fito nayi sallar La'asar, bayan na gama na hau en gyare-gyare a dakin babu kakkautawa da yake ba wani aikin yi ne dani ba duk da cewa ranar girki na ce dai. Wajen karfe biyar na tashi na shiga kicin din, Anty Mubeenah tana tsaye a gaban gas cooker da frying pan akai da alamu tana frying abu, na kalleta cike da mamaki ita kuma ta kalleni da blank expression, tunda muke da matar nan sai ranar na taba ganinta a kicin wai da sunan girki, sai na dake kawai na shiga cikin store na fito da duk abubuwan da zan bukata. Da yake babban kicin ne, kuma yawanci komi na amfani a kicin din guda biyu ne sai na kunna wani gas din na fara girkina. Cikin kankanin lokaci kamshi ya bade ko'ina na gidan, ta gefen ido nake kallon Anty Mubeenah ina wasi-wasin dalilinta na yin girki yanzu. Har ta gama soya dankalin ta juye a cikin plate ta kashe gas din ta fita, na tabe baki naci gaba da aiki na. Ba a jima sai gata ta fado kicin din, ta tangwarar da plate din a cikin sink ta juya kamar cikin fushi.
Sai dana gama girkina idanu na ya sauka akan dankalin, na dauki kwara daya na kai bakina, frowning nayi. Dankalin tauri kamar danye ga dan banzan gishiri da yaci. Na gyada kai a hankali tare da zubar da dankalin na wanke kayan dana bata naje na jera girkin na shige daki. Wanka na fara yi kafin nayi sallah na jira aka kira Isha'i nayi kafin na fita falo muka fara dinner. Tun a wajen jikina ya fara rawa, sanyi yake shigar ko wace kofa ta jikina sosai.
Hafsy ta kalleni tace “Anty Nafee, jikinki rawa yake yi baki da lafiya ne?" nace “zazzabi ne, yanzu zan shiga in sha magani ai" tayi shiru tana kallona, can tace “ko dai in kira Anty Raliya?" nayi saurin cewa “a'ah da wannan daren? Mura ce take shirin kama ni zan sha magani" tace “to Allah ya sauwake" bayan mun gama cin abincin muka dan yi kallo kowa ya wuce dakin shi. Shirin kwanciya barci nayi naja bargo na rufe jikina, rawar sanyi nake yi ina jin kamar an watsa ni cikin ruwan kankara hakorana har haduwa suke yi waje guda. Ina cikin wannan halin Hafsy tazo ta same ni, da sauri ta hayo kan gadon tana jijjiga ni amma na kasa daga kai in kalleta, fita tayi da sauri sai gata ta dawo ita da Anty Mubeenah. Da sauri ta dago ni tana tamvayar lafiya?? Ganin na kasa yin magana yasa ta hau daga drawers har ta lalubo paracetamol, Hafsy ta miko ruwa Anty ta bani maganin nasha na koma na kwanta. Ba a jima ba barci ya dauke ni, ban san sanda suka bar dakin ba.
Da asubahi koda na tashi babu zazzabin sai mura data min mugun kamu, nayi sallah ina ta atishawa da tari ba kakkautawa. Na shirya break fast na kai kan dinning na ajiye, ina cikin shiryawa din Anty Mubeenah ta fito daga dakinta, nan ta min ya jiki na amsa da sauki tare da mata godiyar dawainiyar ta a gare ni a daren jiya, ta wuce dakinta. Nima dakina na koma na kira Abbuna muka sha hirar mu har sai da Hafsy ta leko ta kirani sannan muka yi sallama na fita muka karya. Yaran makaranta suka wuce ni kuma na zauna anan falo ina kallo Anty Mubeenah kuma ta shige dakinta, na kula kwana biyun nan bata cika fita ba.
Wajen karfe goma na safe sai ga su Anty Ameenah da Anty Rahila sun zo wai ashe Hafsy ce ta kira su a waya tace musu bani da lafiya, na kama baki ina dariya nace “Lallai ma Hafsy! Zazzabi ne nayi jiya da dare fa, mura nake yi sai kuma nayi wankan yamma ina jin shine ya saukar mun da zazzabin, amma shine har da shela??" Anty Raliya tace “ai ba shela bace ba Nafeesah, gaskiya ce. Idan wani abu fa ya faru??" nace “babu abinda zai faru ma in shaa Allah. Ai Hafsy din da Anty Mubeenah suka kula dani" na lura da kallon mamakin da suka jefe ni dashi kafin suka basar, Anty Ameenah tace “To Allah ya kara lafiya" nace “Ameen" sai ga Anty Mubeenah ta fito, nan ta samu waje ta zauna suka gaisa, basu jima ba suka mana sallama suka tafi suna jaddada min idan dai naji ciwon ya dawo in kira su fa, nace toh.
*****
Mun fito daga cikin jifatu ni da Hafsy mun je shopping, ina kokarin bude mota mu shiga naji an kira sunana daga bayanmu cikin wata irin murya da naji kamar na san ta, “Nafeesah??" ga namaki na koda na juya Muneer na gani a tsaye, dauke a kafadar shi wata dan yaro ne zai kai kimanin shekaru hudu kila. Ya matso yace “Allahu Akbar! Ashe dai ke din ce, ya kike?" nayi murmushi, shekaru masu yawa sosai rabon da mun hadu kenan tun ma kafin in bar Kadpoly. Nace “lafiya na qalau Muneer, kai fa?" ya kalli Hafsy dake tsaye a gefena tana kallon shi cikin alamun rashin sanayya, yace “diyar ki ce?" ni abin sai ma ya bani dariya, ya kalli zankadediyar budurwa kamar Hafsy yace wai diya ta?? Nace “ehh, baka ga muna kama ba?" sai yayi er dariya, ya nuna min yaron hannunshi yace “dana kenan, Suleiman... Ke fa?" na daga kafada, “Allah bai kawo ba har yanxu" yace “to Allah ya kawo masu Albarka" nace “Ameen" daga haka muka yi sallama kowa ya shiga motar shi yaja. A cikin mota nayi murmushi tare da gyada kai cikin kara sakankancewa da Girma na Subhanah! Lallai Hausawa sun yi gaskiya da suka ce wani baya auren matar wani kamar yadda wani baya haihuwar dan wani...
A daren ranar misalin karfe sha daya na dare na fito daga dakina da niyar zuwa kicin dauko ruwa, naci karo da Anty Mubeenah Zaune akan kujera cikin duhun falon wanda hasken dake waje ne daya dan shigo ta labulaye yasa na ganta, da farko tsoro ta bani kafin na dan matsa zuwa gabanta nace “Anty Mubeenah baki da lafiya ne?" ta dan dago a firgice ta kalleni kafin ta kauda kai, kai ta girgiza tace “lafiya ta qalau... Babu komi" kamar zan yi magana sai na fasa, na tunkari kicin kafin in dakata dalilin kiran sunana da tayi “Nafeesah...!" na juya a hankali na kalleta “ma'am?" ta dan daburce, “umh... Koda yake ma ba komi, je ki kawai" na juya naje na bude fridge na dauko ruwa mara sanyi na sha anan cikin kicin din na maida goran ciki na fita.
Har lokacin Anty tana a yanayin tagumi kamar yadda na fara samunta daga farko, har zan wuce sai kuma na fasa. Na koma kusa da ita na zauna sosai ina fuskantar ta, hannunta na kamo cikin nawa na rike, a hankali nace “Anty Mubeenah..."...
*Gaisuwar ban gajiya zuwa ga en matan Amarya Anty Zee da sister Husnah.... Allah ya huta gajiya ya kuma kawo mana naku bikin mu sha shagali, lol.
~Ni Da Abokin Baba na fans, ya kuke? Sannan me kuke tunani game da canjin halin Mubeenah???
*♡Jeedderh♡*
*NI DA ABOKIN BABA NA...!*
*©Jeedderh Lawals*
*®Fikrah Writers Association* 🖊🖊
*59*
Nace “Anty Mubeenah.... Ni ba karamar yarinya bace ba, kina cikin damuwa naga hakan rubuce akan fuskar ki. Kai ko makaho ya shafa ki yasan cewa kina cikin damuwa.. Nasan cewa ban kai matsayi ko girman da zan zama abokiyar shawarar ki ba, amma idan kina ganin babu damuwa kuma zaki iya, y can't u just tell me?? I'll be a good listener and a judger" tayi shiru tana kallona cikin nuna can I trust you? Na kai daya hannuna na shafa bayan hannunta ina mata murmushi reassuringly, nace “trust me, wallahi u r safe with me... Ki yarda dani".
Numfashi ta ajiye a hankali, “na yarda dake Nafeesah, ke mutum ce ta gari mai hankali da natsuwa. Ina tunanin kila ki tsane ni akan abubuwan da na aikata...!!" tayi shiru tana kallona nima na kalleta ban yi magana ba sai data yi radin kanta kafin taci gaba da magana.
“Kamar yadda nasan cewa kin kula da yanayin zamana da Ibrahim Zama ne kawai muke yi wanda babu armashi ko na kankani. Auran hadi aka mana da Ibrahim ba tare da son mu ba, lokacin ina da wanda nake so. Haka aka kaini gidan Ibrahim ba don naso ba tunda duk yadda naso inyi akan kada ayi auren abin ya faskara. Ibrahim yana kyautata min a matsayin shi na wanda baya so na ma, amma ni na kasa yakar zuciyata akan ta so shi. Ina can ina karewa Mahmud wanda nake so mutuncina wanda kullum sai mun yi waya dashi ya jaddada min in rike mishi amana dai. Duk batanci na duniya babu kalar da ban yiwa Ibrahim akan ya sake ni ba amma yayi biris dani hakan shi yake kara min jin kin shi a raina. It took us almost a year kafin mu kusanci juna, shima ni da kaina naji ina son yin hakan na kai kaina gare shi. Daga nan muka ci gaba da rayuwar ma'aurata amma fa idan naga dama don wani lokacin ko ya neme ni ma sai inyi refusing dinsa, idan kuma ya matsa to sai dai ya biya ni kudin sannan..." tayi shiru hawaye ya zubo mata, yayin da nake jijjiga kai cikin mamaki. Ban taba zaton cewa alakar Abbu da Anty Mubeenah tayi muni irin haka ba, Anty taci gaba...
“Cikin haka na samu cikin Abdullahi, yeah naji dadin samun cikin saboda a lokacin zugar en uwana tayi tasiri akaina da suka ce idan na fara haihuwa a gidan Ibrahim yayana zasu zama magada saboda duk da cewa a lokacin yana karatun masters, amma yana da kudi don bai dogara da kudin mahaifin shi ba, ya dogara da kanshi. Sai dai bayan haihuwar Abdullahi da wata takwas dana kara samun wani cikin mai dan banzan wahala sai naji ina dana sani akan amincewata akan haihuwa. Mun sha danbarwa da Ibrahim akan cikin nan, nayi yunkurin zubar dashi sau ba adadi Allah ya nufa sai da yazo duniya. Wallahi Nafeesah sai da muka tsadance da Ibrahim ya biyani sannan na shayar da jaririn. Watan shi bakwai na yaye shi, babu ruwana da harkar yaran su duka shi yasa zaki ga shakuwar mu dasu bata yi zurfi sosai ba kamar yadda suka shaku da Ibrahim.
Bayan shekaru biyu na sake haihuwar Hafsy, daga nan ne naje asibiti aka saka min loop a mahaifa ta saboda bana son haihuwa da Ibrahim...."
Na zaro idanu waje sosai cikin tsananin mamaki, “loop Anty?" ta gyada kai, “abin ya ba Ibrahim haushi sosai, ya jima yana fushi dani kafin ya sauko ya hau lallashina akan in je a cire min ni kuma nayi biris dani har ya gaji ya daina yace zai karo aure, at first na firgita da jin haka daga karshe da naji shiru sai nayi zaton cewa tsakuwa ce yake taunawa don aya taji tsoro sai kwatsam naji zancen auren shi da ke. In fada miki na firgita ma bata baki ne, na shiga shock bana kadan ba sai dai na cije saboda a gani na bana son Ibrahim meye nawa na jin haushi don zai kara aure? Sai daga baya na fahimci I was wrong! Ina son Ibrahim rashin kulawa irin nawa ne ya hana ni gane hakan, sai daga baya ne bayan ya daga min murya a karo na farko a tarihin rayuwar auren mu, sannan na fahimci halin da zuciyata take ciki game dashi amma ban san ko ta wace hanya zan sanar dashi ba Don haka naja bakina nayi shiru. Amma a en kwanakin nan gabadaya na rasa abinda yake min dadi, shi kuma kamar ya sani, yanzu ko kiran shi nayi a waya baya dauka ma. Zuciyata tana azabtuwa da hakan ba zan iya cigaba da jurewa ba, amma da wani ido zan kalli Ubangijina bayan abubuwan dana aikatawa mijina? Tell me, bayan duk my man and abubuwan nan dana aikata, da wani ido kike so in kalli Ibrahim??".
Na kalleta tun daga sama har kasa, tabbas ta banbanta da Mubeenar dana sani a da. Wannan Mubeenar ba wadda take cike da self esteem bace, sai wata Mubeenah wadda nadama take nukurkusarta. Tausayinta ya mamaye ni matuka.
Nace “kada ki ce haka Anty, shi Allah Gafurur-Raheem ne, yana yafe kuskuran damu muka aikata a gare shi matukar tuban muke nema da gaske. Abbu ma haka ne, ina tabbatar miki da cewa shi zai fi ma kowa jin dadin canzawar ki Anty" ta kalleni da sauri, “da gaske?" na gyada mata kai ina murmushi. Tace “to yanzu me kike so inyi?" nace “abu na farko daya kamata kiyi shine kije ki cire loop din jikinki, bayan hana haihuwa yana da side effects a jikinmu ba kadan ba, bana tantama kibar jikinki loop ne ya assasa miki ita" ta gyada kai cikin nuna yarda da abinda nace, “nima nayi tunanin haka. In Allah ya yarda gobe zan koma asibitin a cire min" nayi murmushin jin dadi, “we will do the other things later then... Bari inje in kwanta haka nan" na mata sai da safe na wuce.
Har na kusa kofata naji ta kira sunana, “Nafeesah!" na juya a hankali, “it was not bad opening up to you.." nayi murmushi sosai, “Anytime Anty" na shige dakin tare da rufo kofata na koma kan gado na kwanta. Tunanin yadda muka kare da Anty na dinga yi, na tsinci kaina da addu'ar Allah yasa ta dore a haka, Allah kuma ya bamu zaman lafiyar da a kullum nake mana addu'ah. Da haka barci ya dauke ni cike da mafarkai iri-iri, mafi yawa daga cikin su shine na wani kyakkyawan yaro da yake bina da tuffa a hannu, na tashi da dan murmushi a fuskata. Addu'a nayi na shafa a fuskata na tashi na fada toilet na dauro alwala nazo nayi sallah.
Da yake ranar Anty ta karbi girki, ban fita falo ba sai da karfe tara tayi. Yara sun tafi makaranta, dana tambayi Harira Anty Mubeenah tace tace a fada min ta tafi asibiti, nayi murmushi kawai. Abinci na zauna naci, nayi gefe da plates din a zuciyata ina raya lokacin barin Harira gidan yayi.
Lokacin da Anty ta dawo har dakina ta leko ta same ni, tace “sun rubuta min magunguna in sha na sati daya sai in koma a cire min" nace “to Allah yasa mu dace" tace “ameen."
Daga ranar alakar mu da Anty Mubeenah ta canza, su kansu yaran sun yi mamaki kuma sun ji dadin hakan kada ma dai Abbu yaji labari wanda nake updating din shi da duk abinda ke faruwa. Ni'imah ta sake haihuwar diya Mace, a ranar muka je muka yi barka ni da Anty Mubeenah. A cikin mota muna dawowa nayi shiru ina tunanin anya a duniya zan ma haihu kuwa? Na tuna ina cikin shekarar aure ta uku kenan zuwa hudu amma har yau shiru babu bayani ko batan wata ban taba yi ba. Mommy tace wai itama hakan ce ta faru da ita, sai a cikin shekararta ta biyar ne sannan ta samu cikina, nayi ajiyar numfashi a hankali ina addu'ar idan da rabona Allah ya kawo masu albarka.
Anty Mubeenah taje an cire mata loop din, sai dai ance sabida jimawar abin a jikinta babu wata kulawa irin yadda ya kamata, ya taba mata mahaifa saboda haka da kyar mahaifar ta iya daukar ciki nan gaba. Hankalinta ya tashi kwarai da jin haka ni na dinga kwantar mata da hankali har ta nutsu. Ni na bata shawarar shiga From My Kitchen Institute da yake Allah ya budawa mai makarantar Hadiza Dogon Daji ta bude reshe anan Kano bayan na Abuja, inda ta fara koyon salon girke girke ina kuma taimaka mata da wasu abubuwa. A gefe guda kuma na dora ta akan weight loss da slimming. Kullum muna gym muna aikin motsa jiki. Abbu ya dawo yayi sati daya ya tafi wata seminar inda daya dawo za a bashi VC.
Cikin wata daya kacal idan ba mugun sanin Anty Mubeenah kayi ba idan ka ganta a hanya ba zaka gane ta ba. Wannan kibar marar fasali da rashin gyara duk ya tafi babu shi, ta dawo tayi wani fresh da ita Masha Allah! Duk da dai har yanzu da sauran kibar amma ta ragu sosai. Musamman ta siya form din wata islamiyah anan bayan gidanmu inda take zuwa daukar karatu kowace rana da yamma, karfe hudu zuwa shida. Ko a yanzu kam Alhamdulillah! Zama na da kishiyata ya canza, idan ka ganmu zaka yi zaton cewa wasu shakikai ne ba kishiyoyi ba.
Result dinmu ya fita, sakamako yayi kyau sosai. Nayi clearance da komi, Abbu kadai nake jira ya dawo in nemi izinin shi in fara aiki da Lab din Aminu Kano Teaching Hospital.
Muna zaune akan dinning muna cin abinci, ranar Anty Mubeenah ce mai girki kuma ita ta dafa mana abincin da kanta don tuni muka sallami Harira bayan mun danka mata kudi masu tsoka da zata ja jari dasu, duk da cewa har yanzu dai sai a hankali amma she's improving sosai. Ta kalli plates dinmu, Jollop spaghetti da sauce din hanta, soyayyiyar agada, da coleslaw. Ita kuma nata taliyar ce kadai sai tulin vegetables akai, ta kai spoonful of cabbage bakinta ta taune ta hadiye da kyar, ruwa ta tsiyaya ta kai bakinta. “Nafeesah! This is a torture wallahi! Haba!! Wata na nawa bani da abincin daya wuce kabeji? Gaskiya na gaji haka nan wallahi, I want to eat chicken!!" ta fada da karfi tana watsa hannuwana sama kamar wata yarinya, aikuwa nan muka samu abin dariya, ni da yaran muka kwashe da dariya sosai, ta nuna mu da yatsa “dariya ma kuke yi koh? Just wait nauyina ya dawo 65, idan na fara cin nama a gidan nan..." Qaseem yace “Mommy, Anty Nafeesah tace ko kin kai 65 din sau daya zaki dinga cin nama a sati fa!" ta harare shi, “inji wa? Kai dai ku jira in rage nauyin, babu wanda zai hana ni cin nama" ni dariya ma ta hana ni magana. A haka dai muka gama cin abincin cikin raha, na taya Anty Mubeenah muka kwashe kayan muka kai kicin muka wanke, daga nan na koma daki na kwanta wai in dan runtsa kafin La'asar tayi.
Ihun yara na jiyo a falo suna ga Abbu, haba! Na dira daga kan gadon da sauri na fita. A karamin falo muka ci karo dashi, tsaye a tsakiyar su Hafsy cikin suits bakake da farar shirt, na danne dokin in rungume shi da naji naje gefen shi kawai na zauna ina murmushi. Sai da yaran suka gama murnar su ya basu chocolates da tarkace ya tura su dakinsu sannan ya juyo gare ni.
Nade ni yayi cikin jikin shi cikin tattausar rungumar nan tashi. Nima na mayar mishi da wadda tafi tashi taushi, mun jima a haka muna jin dumin jikin juna kafin na zare jikina daga nashi a hankali, na kalleshi ina dan murmushi, “ya hanya?" ya jingina kan shi da jikin kunya, “it was tiresome but Alhamdulillah tunda na iso lafiya" nayi murmushi “you must be kam... Yakamata ka watsa ruwa koh?" na mike da brief case dinshi a hannuna.
Ya mike shima yana sassauta neck tie din wuyan shi, daidai lokacin Anty Mubeenah ta fito daga dakinta. Sanye take da doguwar rigar Shadda wadda tabi jikinta sosai, now that I look at her very well, tana da diri da halittun jiki Masha Allah. Haka kawai naji wani abu ya makale min a wuya ganin yadda Abbu ya saki baki yana kallonta yayin da take kallon shi cike da so da kewa. Ganin kallon nasu ba mai karewa bane ba yasa na danyi gyaran murya sai lokacin suka dauke idanunshi a kan juna, na danne takaicin daya zo mun wuya nayi dan murmushi tare da cewa “dama wanka wai zai je yayi, amma tunda gaki bari in barku tare, inje in dan kwanta" na mikawa Anty brief case din, ban jira sun ce wani abu ba na shige dakina da sauri na maida kofar na rufe.
Numfashi na dinga ajiyewa da sauri kamar wadda tayi tsere, tabdijam! Idan har haka zan dinga ji idan naga Abbu tare da Anty Mubeenah to akwai matsala, lallai yakamata in san abin yi.
Da dare muka hadu a dinning wajen cin abinci, daga jin taste din abincin nasan cewa Anty really put her best effort don kuwa yayi dadi sosai, duk yadda taso taja Abbu da hira a wajen abun ya faskara har naji ta bani tausayi, sai dai wani sashe na zuciyata na raya min cewa kawai burga ce yake yi, amma a dokance yake da ita, hakan shi yake kara tunzura ni.
Bayan mun ci abincin muka hada kan komi muka kai kicin muka dawo falo, Abbu da yaran shi suna hirarrakin su, sai muka ja kujera ni da Anty Mubeenah muna tamu hirar har wajen karfe tara da rabi, na tashi na musu sai da safe na shige dakina.
Wanka nayi na dauro alwala, anan cikin bayin nayi shafa ina karfafawa kaina gwiwa daga munanan tunanika da zuciyata ke kitsa min, babu abinda ya canza, Abbu yana nan a yadda yake kamar yadda Anty Mubeenah take, nayi dashe a zuciyar Abbu wanda babu wata 'ya macen data isa ta dakusar min dashi, sai dai ta nemi wani gurbin tayi nata dashen, da wannan naji karfin gwiwa ya shige ni. Don haka koda na fito nayi tozali da Abbu akan gado, murmushi nayi naje gefen shi na zauna. Lafiya lau muka yi sallama dashi, na raka shi har bakin kofa ya tafi bayan ya manna min pecks a kumatu da goshina. Na maida kofar na rufe, kan gado naje na kwanta na janyo wayata nayi en dube-dube da chatting har dare yayi kafin na kashe wayar nayi addu'ar kwanciya barci na shafa. Filo na janyo na rungume a kirjina na rufe idanuna, can kasar zuciyata Istigfar na dinga janyowa da hailala saboda korar shaidanin dake saka min abubuwa a cikin raina...
~Lol! Su Malama Hajiya Mubeenah an dawo kan hanya fa! Wa yaji dadin canzawar ta kuwa? Ni dai naji
~N please ina baran addu'o'inku...
#TeamAbnaf
#OneLove
*♡Jeedderh♡*
*NI DA ABOKIN BABA NA...!*
*©Jeedderh Lawals*
*®Fikrah Writers Association* 🖊🖊
*60 FiNaLe*
Alhamdulillah! Rayuwa mai cike da inganci da zama lafiya muke shimfidawa mu da mijinmu. Mun hade kawunan mu waje guda domin samun kwanciyar hankalin mijinmu. Yes, akwai kishi, sai dai kishin zamani muke shimfidawa ba wai na dabbobi ba, kowa tana iyaka kokarinta wajen ganin ta faranta ran mijinta domin samun ragamar zuciyar shi don haka a takaice dai Abbu ya zama sha lelen mu.
Lokacin Hajji yazo, Abbu ya biya mana kujera mu duka banda Hafsy, muka je muka sauke farali. Bayan mun dawo naje Kaduna nayi kwana daya na dawo muka ci gaba da gudanar da rayuwar mu a nutse.
*****
Kallon shi nake yi idanuna na shekin bacin rai da tashin hankali, “ban gane ba? Kamar ya ba zan yi aiki ba, akan me??” tunda muka dawo daga aikin hajji na dame shi da maganar son fara aikina amma yayi biris dani, sai ranar ne ya bani amsa da cewa ai ba zai barni wae inyi aiki ba, duk wahalar dana sha!.
A nutse ya kalleni cikin sanyin murya mai cike da lallashi yace “to menene abin tada jijiyar wuya kuma? Kin dai san cewa ba tun yau ba nasha fada miki cewa bani son mata na su yi aiki, nafi so su zauna a gida su kula min da gidana da iyalina. Beside Nafeesah baki nemi komi kin rasa ba a gidannan, aikin me kuma zaki je kiyi saboda Allah?"
Na cure baki waje guda ina yamutsa fuska, “to ni nace ne dama saboda kudi zan yi aiki ne? Kawai sabida ina so inyi aikin ne, m bored to death! Baka barina ina fita ina ganin mutane sai abu mai muhimmancin gaske ya taso, baka barina inje gidanmu in musu kwanaki sai dai wuni.... Ni wallahi idan ba so ake yi mutum kadaici ya kashe shi ba a bar shi yayi aiki!"
Kallona yake yi baki a dage cike da mamaki, tun da muka yi aure iyakata da Abbu Nafeesah yi kaza, ince toh., ko kuma Nafeesah ba zaki yi kaza ba ince toh. Amma yau yaga gabadaya na wani canza ne, abinda bai taka kara ya karya ba, maganar aiki ba tun yau ba yayi making it very clear ba zai bar matar shi tayi aiki ba amma gashi ina tonon fada da maganar.
Na kawar da kaina daga kallon da yake min na mamaki, “a’ah! Yo mutum sai yaki fadin gaskiya haka kawai! Idab ma bazan yi aikin ba a dinga barina ina fita mana, amma kullum ni a garkame a gida kamar wata furzuna? Da yake ita er gaban goshi ce naga babu ranar banza da ba zata fita ba amma ko a jikin ka sai ni, me nayi maka ne saboda Allah??" kwalla ta ciko idanuna, da sauri na juya na shige dakina. Kan gado na kwanta ina ajiyar numfashi idanuna a lumshe. Kwana biyun nan zuciyata a wuyana take, kome aka yi da wanda ya kai da wanda bai kai bama jin haushin shi nake yi. Na dan ja siririn tsaki, meye ma na wani sako zancen Anty Mubeenah? Duk da cewa dai abin yana ci mun tuwo ne a kwarya, kun ganta nan kullum tana waje yawo, yawace-yawacen nan nata har lokacin bai ragu ba, karewa ma watarana sai ta fita sannan take fada mishi duk da cewa dai an samu saukin kin fada mishi da bata yi. To ni kuma Fisabilillah kullum ina garkame a gida, idan yara suka tafi school Anty ma ta fita ni kadai ake bari inyi ta gantali a cikin gida, abin ya dame ni sosai.
Ina jin lokacin da aka taba kofa alamun an shigo cikin dakin, bayan juya baya da nayi sai na lumshe idanu na. Ya zauna a gefen gadon da nake kwance, yace “wai Nafeesah me ke faruwa ne? U never go against my words n you never raise ur voice on me, naga maganar aikin nan fa tun ba yau ba na fada miki cewa ba zan iya barin mata ta tayi aiki ba. Mubeenah tana da degree akan computer science ni na hana ta aiki but in return sai na bude mata saloon din can, ba gashi yanzu komi ya zama even ba? I'll do the same to u, Dan Allah kar ki maida maganar nan ta zama babba ranmu ya baci Nafeesah!"
Nayi shiru kawai ina sauraronshi. A en kwanakin nan kwata-kwata zuciyata a wuya na take, abu da wanda ya kai da wanda bai kai ba sai inji raina ya baci, akwai ranar da ina jan jagira hannuna ya kubce ta bata mun fuska, wani irin bacin rai ya ziyarce ni a lokacin, duk abubuwan da suke kan dresser din sai dana yi wurgi dasu suka fado kasa, abin zai baku mamaki da dariya idan kuka ga yanda na tsaya a kansu ina wani huci kamar tsohuwar macijiya, sai daga baya da fushin ya tafi kuma na dawo ina dariya da tu'ajjibi. Akwai kuma ranar da kadan ya hana in mazge Hafsy saboda nayi abinci tace gishiri yayi yawa, bayan a hakikanin gaskiya taste din bakina ya bace nayi ta zabga uban gishiri a cikin abincin ni da kaina dama sai dana yi tunanin haka amma data fada sai naji haushi.
Abbu ya dan tabo ni tare da juyo ni ina fuskantar shi, shiru nayi ina kallon kyakkyawar fuskar shi, ina so in gano laifi ko aibu a cikin abubuwan daya fada amma na kasa. Ban san abinda yasa nake fada dashi akan maganar aikin nan ba, lokacin da nake gida har addu'ah nake yi akan Allah ya kawo min miji wanda zai tsaya min akan komi kamar yadda Daddy yayi wa mommy, gashi yanzu na samu amma kuma na rasa abinda yasa na kasa yarda da hakan, m behaving really strange kwana biyun nan, wasu bakin halaye dana kasa gane su.
“Nafeesah??! Talk to me mana uhm?? Bana so muyi fada akan maganar nan please, kin dai san babu abinda zaki nema a duniyar nan da ba zan kasa miki shi ba, ba zan gazawa hidimomin ki ko kadan ba kin ji? Kuma In shaa Allah ba zan taba bari kiyi dana sanin kin yin wannan aikin ba, ok?" kai na gyada mishi a hankali, yayi murmushi a hankali, “uwww thanks my baby..." ya sadda kanshi saitin fuskana zai yi rewarding dina da kiss, naja wata doguwar shakuwa data sa ya dakata yana kallona, daga haka kuma ba sai kakarin amai ba? Na tashi da gudu na shige bandaki, sai dana amayar da duk abubuwan dana ci a take, Abbu yana tsaye a gefena yana dan bubbuga bayana har na gama aman, ya taimaka min na wanke bakina ya kaini kan gado ya kwantar ya koma toilet din.
Kafin ya fito na dukunkune cikin bargo ina rawar sanyi sosai, hankali tashe ya tarairayo ni jikin shi yana taba wuya na, waya ya dauko ya kira family doctor dinmu, Doctor Salmah. Bayan kamar mintuna arba'in ta iso, lokacin zazzabin ya sauka sai jikina da yayi wani irin sanyi kamar an min duka, kasala duk ta lullube ni. Tayi duk wasu gwaje-gwaje da zata yi, daga karshe dai ta bani wata kwalba tace inje inyi fitsari a ciki, na dafa kafadar Anty Mubeenah muka shiga toilet, ta fita ta bar ni nayi fitsarin ina gamawa ta shigo muka koma dakin, Docta ta amsa kwalbar ni kuma na koma kan gado na kwanta, muka yi zuru-zuru muna kallonta tana saka strip a cikin kwalbar fitsarin.
Bayan kamar minti goma ta dago abin yadda duk zamu gani, bamu fahimci komi ba sai da muka ji tace “mashaa Allah!! Farfesa matar ka na da juna biyu!!" a rikice na kamo hannun Abbu na rirrike kamar zan tsinke mishi shi, ya kamo wuyana ya hada fuskata da tashi waje guda yana furta wasu addu'o'i da ake son mutum ya dinga furta su cikin halin tsananin farin ciki. Anty Mubeenah ta dafa kafadata ko ban fada ba nasan tana murna da abinda taji ne. Docta tayi er dariya ta fara tattara kayanta tana fadawa Abbu bata bincika ko watan nawa ba saboda haka ya kaini asibiti washegari a duba da kuma lafiyata data jaririn yace toh. Nan ta mana sallama ta tafi bayan Abbu ya mata kyautar da bai san adadinta ba don hannu kawai ya saka a cikin aljihun shi ya damko kudi ya mika mata.
Ranar kam naga tattali da kulawa ba daga mijina ba ba daga 'ya'yan mijina da en uwanshi ba, ba daga kishiyata ba ba daga Iyayena ba kada ma dai Daddy yaji labari. A ranar ya kirani shi da Mommy ban ma san wanda ya sanar dasu zancen cikin ba suka taya ni murna da addu'o'i iri-iri Mommy kuma yadda zan kula da kaina take fada min tana nanatawa kamar karatu.
Cikin wata hudu ne lokacin da muka je aka duba, babu wata damuwa ko matsala a tare dani sai hawan jini wanda ba wani damuwa bani tunda dama it's a normal thing a wajen mata masu ciki, an dai bani abubuwa da zan dings ci da kuma abubuwan daya kamata inyi da wanda ba zan yi ba domin rainon cikina cikin sauki da kwanciyar hankali. A cikin mota a hanyar mu ta dawowa daga asibitin Abbu ya riko hannuna yana shafawa a hankali yace “ya zancen aiki ya tafi koh?" na gyada mishi kai ina murmushi. Yayi er dariya tare da cewa “ai Doctor Salmah ta fada min cikin jikin ki ne yasa kika zama short tempered woman, haba! I was wondering dalilin da yasa mutum mai sanyin hali irin ki ya zama mai fada da zuciya cikin dan kankanin lokaci, amma tun da na gano kan abin, zamu dinga kiyayewa bacin ranki don tace hakan zai iya sawa jinin ki ya hau..... Allah ya sauke min ke lafiya baby" nayi murmushi nace “Ameeen Abbu nah..!".
Cikina sai daya shiga watanninshi na bakwai sannan ya fara girma saboda da babu wani girma kuma babu laulayi ba komi sai fresh da nayi da kuma cin abinci da shan tatacciyar madara. Kafin in shiga watan haihuwa ta kuwa na zama shirgegiya, zama da kyar tashi da dabara. Kullum na kan zagaye gidan sau hudu ko biyar don ance hakan yana da kyau sosai. Yanzu dai haihuwa kadai muke jira, komi is ready, hatta da cokalin da za a ba baby ruwa dashi ranar da aka haife shi an siyo an ajiye, komi unisex Abbu yake siyowa kuma guda biyu, duk da dai naki yin scanning amma Abbu da Anty Mubeenah har ma da sauran mutane suna cewa wai girman cikina irin na en biyu ne, don Abbu ma cewa yayi wai yana mafarkin ya ganni ina wasa da yara biyu ina miko mishi su, ni dai fatana kawai Allah ya sauke ni lafiya.
Ranar wata Talata na tashi da matsananciyar nakuda, nan muka kwasa Zuwa asibiti. Nakuda nayi mai tsawo da wahala kusan yini daya ina abu daya, abin ya gigita ni. Ban taba sanin cewa zafin nakuda nake yi ba. Abbu da yayi jan ido ya shigo labour room din sai waje aka yi dashi saboda dana shiga mood din “ duke kai ne ka janyo min wannan wahalar..." abin bai yi kyawu ba. Sai zuwa bayan Maghrib Baby ya fito, nan na fara ajiye numfashi, sai dai me? Wani ciwon ne ya sake turnike ni kafin kace me?! Wani yunkurin sai ga wani babyn. Na maida kaina kan gadon asibitin na kwantar ina ajiyar numfashi da karfi, nurse din data karbi haihuwar ta duba yaran tace “Masha Allah!! Maza ne Allah ya raya miki su!!". Tuni yaran suka hade dakin da kukan da aka san lafiyayyun jarirai nayi. Nan dai aka shirya mu muka fito tsaf damu. Throughout lokacin babu abinda nake furtawa fili da ciki sai ‘Rabbir-ham huma kamar Rabbiyaani Swigaara...!!' wa Mommy na da duk wasu matan duniya, haihuwa is really not a simple thing.
Ana fito damu Abbu da yara suka shigo, nan fa suka lullube yaran suna murnar samun kanne, Abbu dai ya samu ya lallabo yazo inda nake ya tallabo ni a cikin jikin shi ya rungume yana shafa bayana. Ya dago goshina ya bani peck a kumatuna, “well-done Baby, kinyi kokari really! Allah ya albarkace ku ke da ‘ya‘yanki" nace “ameen... Wani irin baby kuma? Ga babies dinka can" ya juya ya kallesu ya juyo ya kalleni yana murmushi, “me na fada miki? You were going to give me twins, next year ma haka, n the other year, n the other too...!" na zaro ido ina cewa “mutuwa kawai kake rokar min!" yayi dariya tare da saki na yaje ya dauki yaran, Anty Mubeenah kuma ta matso tana jera min sannu.
Sai washegari aka bamu sallama muka wuce gidanmu muka cigaba da karbar barka har zuwa ranar suna inda yara suka ci sunan Abdul-Qadir da Mukhtar (Sunan Daddy na) muna kiran Abdul-Qadeer Ameer shi kuma Mukhtar Daddy. Aka yi taron suna aka watse aka bar mu da yara da Dattijuwa Hanne daga Malumfashi muna wankan jego.
Cikin dan tsakanin Abbu ya bude min babbar plaza wadda Daddy na ya cike min rabin shagunan plazar da kaya ana kula min dasu, rayuwa ta ko wani fanni tana gara mana cikin dadi da kwanciyar hankali babu abinda zamu ce da Ubangijin mu sai dai Godiya....
*****
“Ameer!! Daddy!!!" na fito falo ina kwalawa yaran kira, Anty Mubeenah dake kicin tana dambun nama duk da ba girkinta ba ne, tana taya ni hada abubuwan motsa baki da muka saba yi saboda baki da kuma emergency food. Ta leko tace “ya aka yi ne ake neman dears haka?" naja tsaki, “yaran nan daure su zan fara yi a jikin gado gaskiya, kullum jan magana da barna kamar wasu beraye? Kwalbar turare na mai kyau fa kawai suka dauka daga kan mirror suka hada ta da bango, shine da suka ga ta fashe suka tsere" Anty tayi Dariya tace “aikuwa yanzu suka bi su Qaseem garden wai suna tennis" nayi kwafa, “I'll just go and register them a makarantar su Qaseem ma kawai ko na samu sawaba da sanyin zuciya" Anty tayi dariya tana girgiza kai tace “ke da yaran nan naki koh?" ni kuma na juya zuwa dakina.
Abbu yana kwance akan sofa yana karatun jarida da yake ranar hutu ce, ya miko min hannu na karasa gefen shi na zauna ina turo baki, yayi dariya “yau naji ikon Allah! Ni da bani na bata miki rai ba sai kuma fushi ya dawo kaina, dama ana haka ne?" na turo baki “Allah ni wannan yaran naka ka saka su a makaranta kafin su saka min hawan jini, kullum sai sun shigo sun min barna ni da Antyn su. Hafsy yanzu da makullin dakinta take yawo saboda Ameer. Kayan dakin yaran nan babu abin dauka duk sun bata, jiya suka balle wardrobe din da muka sayo musu last week a Prada saboda Allah meye haka??"
Abbu ya kwashe da dariya har da kwanciya akan kujera, nayi kuta, “na kula dama kai kake daure musu suna rainin wayau. Yara ba a isa a musu magana ba kawai sai ka hau cewa wai yara ne, har sai yaushe zasu girma??" ya juyo dani yana kallon idanuna, “sai wani kumburewa kike yi kina fada baby, Anya?? Kin san da cikin su Ameer ma fa haka kika dinga yi?" da sauri na dukunkune fuskata a kirjin shi. Ya shafa kaina yace “da gaske ne hasashe na kenan? Masha Allah La Quwwata Illaa Billah! You are going to bless me with another child again... Ohh Nafeesah the thing I have for you.... You Are Indeed a Blessing!!" na kara rungume shi a jikina sosai. Kamar yadda a shekaru masu dama da suka wuce, nake jin zill da duk farincikin duniya idan naji ni a kirjin mijina, yanzun ma hakan take. Har yau muna son junanmu, har yau muna girmama junanmu, har yau muna rungumar junanmu a halin farin ciki ko akasin sa. Babu abinda ya ragu daga son da muke wa junanmu.
Ya dago fuskata yace “that call on a celebration... Tunda yara suna nan zamu fita gobe, party and welcome our little princess... Mata zaki haifo mana yanzu baby.... Hafsy tace tana so ta koyi kitso, kinga idan muka samu mace shikenan sai ta koya a kanta koh?" na zaro ido ina dariya tare da kara shigewa cikin jikinshi, “Noo... Guda daya ta isa Abbu... En biyun nan ba sauki daga haihuwar har rainon, kana dai ganin yadda muke fama dasu a gidan nan" ya hade fuska ta da tashi har hancina yana gogar nashi... “haka kike tunani dai....". Kokarin zurfafa abin yake yi, har na saddakar na lumshe idanuna, yana gab... Saura kiris... Kawai sai barammmm!!! Karan turo kofa da sauri..... “Mammiiieeee!!!!" nayi sighing tare da bude idanuna, fararen kayan dana saka musu yanzun nan kafin su fasa min turare, sun yi dikin-dikin da datti da yake ba a jima da gama ruwa ba. Na zaro ido, “what??!" na fara kokarin tashi, Ameer ne ya fara xubawa a guje nan Daddy ya bi bayan shi, na juya na kalli Abbu, shrugging yayi tare da daukar jaridar shi yana murmushi, na girgiza kai tare da mikewa nabi bayan yaran ina kwala musu kira kamar dai yadda na bude shafin......
*_Alhamdulillah! Masha Allah Laa Quwwata Illa Billah!!_* It has been really a very big hell of a ride, right?! But Mashaa Allah!! Mun kawo karshen shi.
Littafin NI DA ABOKIN BABA NA kirkirarren labari ne, baya da nasaba da rayuwar wani/wata, idan wani abu yazo daya da naki/naka, to wannan 100% arashi ne kawai.
Ina mika dimbin gaisuwa ta zuwa ga Dimbin masoya, mabiya Littafin Ni Da Abokin Baba Na! The Facebookians, Wattpadians, Whatsappians, and all, thanks ya very much da duk kaunar ku a gare ni yayin Posting din littafin, gyarerekin ku da karfin gwiwar ku, I Appreciate!!
Gaisuwa ta Musamman zuwa ga mutanen Fikrah! Kungiya ta hadin kai da ban mamaki, Ina gaishe ku da kuma godiya a gareku baki daya.
Abokiya, Yaya kuma Kanwa ta gari; Anty Zee, Alkhairin Allah ya kai miki a duk inda kike.
Masoya, mu tara a littafina na gaba mai zuwa cikin hukuncin Allah! Har kullum, it's Jedderh Lawals!!
N it happens to be my Birthday today you know....