Ranar daurin aure.......
Ta ɓangaren Naufal kamar ba yau bane bikinsa, babu wani kuzari a tareda shi. Komai sanya sanya yakeyi kamar auren dole.
Kawai ɗaci yakeji a ranshi gashi baiji haka ba sanda akayi masa auren dole da Fadeela, duk abinda yaji locacin wancan biki na wannan ya ninka.
Ji kawai yakeyi kamar ya gudu, haka yaje daurin aure ya dawo. Kiran Fadeela yayi, tana kallo bata ɗauka ba. Abla ke zaune a wajen saita dauka ta kara mata a kunne.
"Yaya tana jinka" Abla ta faɗa da karfi. Kwata kwata yanzu Deela ta daina magana. An kira Doctor sunce tana suffering from emotional and psychological stress.
yana cikin abinda yasa hankalin Naufal ya tashi sosai saboda baya son yayi nesa da ita in her time of need.
Anty Saudah tace abar mata ita tayi jinyarta harta samu sauki. Baiso haka ba amma babu yanda zaiyi. Haka ya soma ma Deela magana ta waya, as expected jinsa kawai takeyi amma batace uffan ba.
"Baby Kiyi hakuri kinji, har an ɗaura auren" a sanyaye ya faɗa, duk yana jin haushin kansa. Ita kuma Fadeela hawaye ta soma yi.
Kawar da wayar tayi ta haye chan kurya ta kwanta,,wani kishi kawai takeji. Tama rasa inda zatayi focusing anger ɗinta.
Ga mutuwar Miemie, ga ɓatan Pha'eexah gashi kuma yanzu anyi mata kishiya.
Duk a ciki yanzu abu ɗaya tafi ɓukatan daidaituwan shi watau fitowan Pha'eexah duk inda ta shiga.
Ita kuma Yasmeenah tayi buki yanda takeso saidai babu ango, anyi raye raye da sauran su babu kama hannun yaro. Yanda Instagram suka dauka bikin ta taji dadi sosai.
Yan Uwan Mama sukaje daukota tunda Anty Saudah bazata iya ba. An kaita ɗakinta an barta daga ita sai halinta wanda shi zai kwaceta ba kyauba.
Wajen 10 na dare ta soma kiran Naufal domin ya dawo gida, amma dayake wayar yana silent yasa baiji ba. Abun ya kuwa bata haushi sosai ta cika tayi fam kamar zata fashe.
Huci takeyi tana jiran isowar Naufal, aiko kaddara ya riga fata saboda wajen 11 na dare ya shigo. Shi tun wajen 8 yayi ma Deela sallama saidai bai je gida ba sai yanzu.
Yana shiga cikin falo yayi sallama, sauraren wakar Psquare takeyi mai taken Away cikin dare, tayi connecting da Aux spot na home theater.
Ko kallonsa batayi ba balle ta amsa mashi, shima yaji daɗin abin sosai saiya haye sama. Da sauri ta boye shi tana kokarin chapke masa riga.
"Naufal meye haka halan ka mance yau kana cikin dakina ne?"
"toh idan ɗakin kine me zan maki? Ke bazaki biyoni ba" tafiya ya cigaba dayi saboda bashida lokacin ta.
Haka ta rinka binsa tana masifa, baice mata komai ba saboda baya cikin mood din tashin hankali, yau kwanan Miemie shida da rasuwa.
Yana tafe tana binsa tana surutai, a cikin ɗakin Deela orange colour ya shiga dama nan yake kwana kuma duka kayansa yana wajen.
Ita kuma duk zatonta ɗakinsa ne balle ta gani kato, daidai tayi kan gado tana jiran sa. Shikuma bayi ya shiga yayi wanka tukun saiya fito.
"Ke tashi mu tafi" ya faɗa kana ya soma tafiya, gyara kwanciya tayi ta mirgina sosai saita soma magana cikin shagwaba.
"mine please Barci nakeji"
"Eh yasa nace tashi mu tafi, kokuma a ɗakin matana kikeso ki kwanta"
zumbur ta mik'e da sauri tana kyankyamin gadon.
"Dama dan Wulakanci ɗakin wancan ka shigo dani?"
"Nine nake maki wulakanci? Besides wayace ki biyoni kinga ina tafiya" Nan ya barta ya fice abinsa.
Da sauri tabi bayansa tana sababin zuwan ɗakin Deela datayi, baiko kulata ba ya shige nashi dakin.
Kerere ta tsaya mashi akai tana wani yatsine fuska, "Jekiyi alwala kuma ki dauko hijab" harda bazata ba saita soma tafiya.
Ta daɗe kafin ta dawo Kai da zaka zata an aiki baiwa garinsu ne. Data dawo akwai alamun wanka a tareda ita kuma sanye take Lingerie mai bala'in fitsara.
Ko kunyar kanta bataji ba irin yau aka daura masu aure bari ta saba tukun, kuma ga overall a hannunta amma bata daura a kai ba.
Yauki takeyi kamar ɗanyen kuɓewa, saita auka jikinsa tana magana cikin shagwaba, "Mine nayi missing ɗinka amma sai wani basarwa kake yi"
"Malama sallah zamuyi tukun" saiya tureta ya mike saboda yanzu saita ɓata masa lissafi.
"Idan kana tunanin banyi Isha'i bane toh wallahi nayi tun around 9, kallonta yayi yana mamakin cewa batasan ma'aurata suna nafila tareda addu'a domin kariya against all odds ba.
"nafila zamuyi"
"Ohhh bari nayi alwala"
"Tun dazu me kika tsaya yi?"
"Wanka nayi ko baka lura bane?"
"Na lura mana" ya faɗa yana sake kallonta tareda hadiye miyau me zafi.
Ta fito saita koma downstairs domin ta dauko Hijab, haushi yaji sosai saboda datayi abinda yace babu busy body da haka bai faru ba.
Yanzu yana tuna abinda yake cema Fadeela lokacin akan ta cika busy body, ashe bai aura busy body wancan lokacin ba sai yanzu.
Data dawoda wani zungureriyan Hijab har kasa, tada sallah yayi saiya ja masu raka'a biyu. Daga nan saiya rinka jero addu'a. Ya lura sai kwafa takeyi tana murje ido wai ita a dole barci takeji.
Bai bariba saida yayi san ranshi kana ya shafa, tana mikewa bata ninke hijab ɗinba yadda ya dace illa chukurkuɗe wa kamar shargi ta cilla chan gefe.
Zuwa tayi ta rugumesa tana mashi shagwaba, "Inace yanzu kika gama mitsike ido kina tura baki"
"Hahaha" ta bushe da dariya "Mine nikake jama aji koh" bayasan wani dogon zance saiya kashe wutan ɗaki suka kwanta.
4:30 am....
Ya tashi yayi wanka sannan ya dauro alwala, zama da Fadeela ya koya masa irin extra salloli bayan sallan wajibi. Tada Yasmeenah yayi a hankali domin ta tashi tayi wanka koda rakatanil Fijr ta samu.
A fusace ta dago jajayen idanta, "Meye haka kake tadani sai kace mara imani, duk rashin barcin daka hanani bai isheka ba sai kuma na samu hutu kake min hassada"
Dogon tsaki taja kana ta fizge bargo ta mirgina da kyau. Shikuma ya tsaya sororo yana kokarin gane abinda tace, "Wai yana mata hassada, yanzu meye abin hassada a barci" yake faɗa cikin ransa.
Wucewa Masjid yayi abinsa, bai dawo ba sai wajen bakwai saura. Koda ya dawo ɗakin Deela ya shiga ya kwanta a kan gadon ta, yanzu wani santa yana mamaye masa zuciya.
Gashi yanzu tayi masa nesa, yanzu yasan ma'anar 'Appreciate the little things that you have' amma babu komai. Nashi jarabawar kenan.
Kiranta yayi a waya, tana kallo amma bata ɗauka ba. A fizge tayi barci jiya, Naufal Kawai take tunawa yana chan da wata wanda ba ita bane.
Haka Naufal ya gama kwakwan so yayi magana da ita amma babu hali. Dama wanka zata yi, wucewa tayi taje wanka yadda ya dace. Kirjinta zafi yakeyi kamar me saboda abincin little one.
Ita har yanzu tana jin alamun little one a ranta, tana wanka tana kuka. Koda ta dawo Abla ta gani gefen gado tana mata murmushi.
A fizge Abla tana yanayi da Miemie sosai, bambanci tsakanin su shi ne kalar fata da kuma shekaru. Sai bayan mutuwar Miemie duk inda Abla taje sai ayita kuka harta koma zaman ɗaki.
Ita Abla daidai shiru shiru ce kamar Fadeela Unlike Miemie dake magana da fara'a sosai.
Naufal yana kwance a ɗakin Deela yasan cewa zuciya tayi, ta saba daukar wayan dukda bata cewa uffan, shi kadai yake surutan sa.
Sake kira yayi sai Abla ta dauko, "Hello Yaya ina kwana"
"lafia lau ina Momyn Pha'eexah?"
Gata bari na bata" ta mik'a ma Deela amma ko kallon wayar batayi ba. Asali ma haɗe rai tayi.
"Yaya tana abune ka bari anjima" Abla tace. Murmushin takaici yayi ta ɗayan ɓangaren saboda yasani sarai taki karban wayan ne Abla ta kasa gaya mashi.
Bayan ya kashe wayar, yaso yaje ya duba Yasmeenah amma ya lura ta iya masifa gashi shi yanzu tashin hankali ne bayaso.
Kawai kwanciyarsa yayi barci ɓarawo yayi gaba dashi. Bai farka ba sai wajen tara da rabi, da salati a bakinsa ya mike yana hamma.
Bayi ya wuce ya gasa jikinsa da ruwan zafi, kayansa da tuni ya dawo dashi nan ɗakin ya dauki sweatpants da t-shirt ya saka.
Ita Yasmeenah wajen goma saura ta tashi, tana zaune akan gado ta soma mitsike ido tana mika. Murmushi takeyi sosai saboda daren aurenta ya kai mata karo. Yanzu kawai hanyar da zata malleke shi ita kaɗai zatabi.
Gaskiya bazata iya sharing mijinta da kowa ba, figigiyan kayanta ta mayar jikinta tayi hanyar ɗakinta, sam bazata iya shiga bayinshi ba tayi wanka saboda yayi kura.
Tana isa downstairs bataga Naufal ba duk zatonta breakfast yaje siyo masu, murmushi tayi ta shige bayi.
Ta fito daga wanka ta chaba kwalliya kamar me shirin zuwa biki, daga nan ta saka wani crop top wanda hoton Taylor Swift take saita haɗashi da pink leggings.
Zura Hijab dinta tayi zatayi sallah kuma lokacin karfe 11. Shikuma Naufal rarraba ido yakeyi ko zai ganta amma shiru.
Zaune yake akan Couch yana kallon BBC lifestyle, kamshin turare yaji saiya ɗaga ya ganta. Babu karya tayi kyau ainun, murmushi suka sakar ma juna.
Zuwa tayi ta zauna dab dashi, a hankali ya soma magana, "kin tashi lafiya?"
"Lafiya lau"
"Ya jikin ki?"
"I'm fine, har kaci breakfast ɗinka ne?"
"Bangane ba, wani breakfast kuma? Ke nake jira ki tashi kiyi mana"
Kallon takaici tayi masa bcs ta rasa me zata ce, "Nine zan dafa abinci daga kawoni jiya sai kace wata bazawara"
"Yanzu don kin girka ma cikin ki abinci ya zama zawarci? "
"Eh" saita murguda masa baki tana ware ido alamun marasa kunya.
"Kinsan cewa Fadeela batada karfin jikin da zata yi maki girki, kuma anyi rasuwa balle su Anty ko Abla suyi. Please why can't you be understanding mana"
"Kasan Allah bazan yiba, besides idan baka lura ba barina fahimtar dakai. Bafa yar aiki ka auro ba, nifa matarka ce"
"Yanzu danke matana ne saiki barni da yunwa"
Ko kallonsa batayi ba, asalima daukan remote tayi ta canza channel which abinda Deela bata masa. Sam babu raini tsakanin shida ita, amma wannan tun jiya take gasa masa magana san ranta.
Big Brother ta kunna, wani dan gidan aka nuna saita daka tsalle tana murna, "Kai TTT kana burgeni"
Kwafa Naufal yayi yaje ɗaki ya dauko wallet ɗinshi, daga nan wani Kiosk dake bakin anguwan su yaje. Kayan shayi ya siyo da kwai da sardine.
Inda ya barta nan ya sameta sai kallo takeyi, "Bisola meye haka?" Yasmeenah ta faɗa tana ɓata rai.
Dire ledan yayi akan centre table.
"Okay ga kayan shayi na kawo, Latte zaki haɗa min sai kuma ki soya kwai tareda sardine. Ba wani aikin wuya bane"
Bata ko kalleshi ba, asalima haɗa rai tayi. "Tunda ba wuya saika yi da kanka mana"
"Sannu me wayo! Kai ka hakince akan Couch zata takura min" baiso tankawa ba amma yace gwara ya kwaɓeta kafin raini ya shiga tsakanin su.
"Meye haka kikeyi tun dazu? Don ina kyaleki shine kike so ki raina ni"
"Ni dai ka daina min ihu tunda bakai ka haifeni ba" ta faɗa ciki ciki,
Mikewa yayi ya shiga kitchen ɗin Deela ya dauko Mug, hawa sama yayi ya shiga bayi ya ɗebo ruwan zafi.
Daukar kayan shayin yayi ya nufa dinning, komawa kitchen yayi ya dauko cokali da plate. Zuba sardine din yayi saiya haɗa coffee mara madara ya soma sha.
Yanayi yana haɗa bread da kifi, ya tabbata idan ya biye ma Meenah yunwa zai iya kaishi lahira.
Yana cikin ci sai itama tazo domin ta saka wani abu cikin bakinta, ko kallonsa batayi ba ta fara gabza bread da sauran sardine ɗin. Bata sha shayi dama bata sha.
Baice mata komai ba har suka gama brunch (Breakfast /lunch). Komawa yayi kan couch ya canza channel. Zuciyar shi sai zafi yakeyi yana tafasa, baima san yadda zasuyi ba wajen abincin rana.
Lallai hankali baiwa ne kuma ba'a shekaru suke ba, Yasmeenah ta girma Fadeela da kusan shekara biyu amma Deela ta fita hankali. Suna zaune suna kallo saiga Huzaifah ya shigo da Haisam.
Ba Naufal ba har Meenah sai da tayi mamakin ganin su, musamman Huzaifah. Haushin Meenah Naufal yakeji saboda bata wani gaggawa ta rufe jikinta. Ita kuma ba yau suka saba ganinta haka ba.
Haka shigarta yake ko cikin gidansu, kayanta kenan su leggings da bom shorts. Mikewa tsaye tayi domin ta kawo masu ruwa. Tana tafe tana juya jiki which yana yinta ne.
Gashi duk jikinta rawa yakeyi kamar ka saka ruwa cikin leda. Huzaifah ya kalleta sosai kuma yaji daɗi har cikin ranshi.
Ta dawo da chi exotic da kuma dubulan da alkaki which dama tazo da abinta na tarban baki. Su Huzaifah sunci sunata hira, itama sama sama takeyi saboda sun daina shiri da daɗewa.
Bayan almost 40 mins saiya tashi wai su tafi, dama yazo yaga lafianta ne a matsayin sa na babban Wanta. Zata mike ta rakasu sai Naufal ya fincike ta. Dole ta zauna sai shi ya rakasu.
"Wancan Huzaifah meye matsalar sa?" Naufal yake tambayar Meenah bayan ya dawo daga rakiya.
Dariya Meenah tayi tana rausaya kai saita soma magana cikin yauki, "haba Mine kar kace kishi kake yi?"
"Ba maganar kishi bane kawai i dont Like him ne, koko im not allowed to say my mind. Besides Bakiga yadda yake kallon ki bane"
"Haka yake idan ma yadda ya kalleni ne, i think nature dinsa ne. Kosu Lubna da Laila haka yake kallon su."
"besides munyi faɗa i think ya gane kuresa yasa yakeso yayi squashing ɗin komai. Everything ya zama past tense tunda yanzu nayi aure"
"Koba wannan ba he is my brother for heaven sake ai bazan iya hanashi zuwa wajena ba. Its just kamar nace Abla karta zo ko Bilqees.. Kaga ai its not even making sense mana"
"He is not Abla ko Bilqees, kuma Nidai i hate him"
Ya faɗa sai yayi hanyar upstairs, "better learn to like him saboda bazan rabu da family ɗina ba wai a dole nayi aure" ta mayar masa. Dama haka take, duk me kace saita baka amsa.
4:30pm....
Naufal ya idar da sallah saiya saka manyan kaya saboda suje su gaishe da yan gidansu. Baici komai ba banda cikinsa da ke wakar yori yori.
Ita kuma Yasmeenah Big Brother Nigeria take Kallo abinta a falo, da yunwa ya soma ɗibarta saita dauko bread ta ajiye gefe tana tsakura. Ko azahar batayi ba balle wani la'asar.
Ga kuma sauran exotic wanda su Huzaifah suka sha bata kawar ba.
Shita rinka gyangyama. Yana saukowa ya ganta tana kallo, "jeki shirya zamu gidan gona"
"Meyasa?" tace tana wani kallonsa.
"Bcs i say so" ya faɗa saiya fice ya wuce chan bakin gate domin yasha iska kuma ya jirata.
Rai a jagule taje ta soma shiri, lace ta saka mai ɗan karan tsada, ɗinkin kimono akayi saita dauki mayafi. Fuskanta shake da makeup, yana ganinta yayi fuska kamar bai ganta ba.
Data gaji da tsayuwa saita fara sababi, "Haba kace zamu fita kuma ka shanya ni kamar kayan wanki, idan bazaka ba saika min bayani na koma daki. A duniya wulakanci ne bana so"
Yaji kunya sosai saboda dukda Maigadi yana nesa da inda suke dole yaji saboda yadda ta ɗaga muryanta chan kurya. Wai yau matarsa ke daka mashi tsawa kamar ɗanta.
Idan baiyi wasa ba Yasmeenah tana dab da mayar dashi mijin Hajia. "da makeup zaki gidan mutuwa"
"Toh ba saika faɗa minba,sai ka shanyani kamar wata shargi" soma tafiya tayi tana gogewa da haɓan gyalenta.
Shima tasowa yayi suka shiga mota, babu wanda yace komai sai tafiya akeyi, itace tayi connecting wayar ta da Aux ta kunna wakar Wizkid mai suna Daddy Yo. Haka ta rinka yi har suka isa ciki.
Sama sama tayi ma kowa, ita yanzu bata damuda kallon dasuke mata ba saboda bakin alkalami ya bushe yanzu Naufal nata ne.
Koda aka haɗasu ana masu nasiha akan hakuri da sauran al'amura na rayuwa, attention ɗinta yafi karkata akan TV while ita Deela kanta yana kasa.
Bayan nan aka kawo masu abinci suci, daga ita har Naufal sunci sosai saboda yunwa yana addabar su, tuwan shinkafa ne da miyan taushe sai kuma kunun aya.
Abba ne ya shigo yana neman Abla ta kaima Khattab abinci saboda rabonsa da gidan tun Miemie na raye.
Dama Naufal ya gama ci saiya tashi domin su gaisa, a garden ya iske Khattab yana wasa da Sunflowers.
Tausayin shi yake sosai saboda Miemie ta shuka da hannunta.
Khattab yana ganin Naufal ya mike da fara'arsa, hakuri ya soma bashi akan rashin zuwa bikinsa da baiyi ba. Acewarsa kwanan sa huɗu a asibiti sai dazu aka sallame shi.
Jaje Naufal yayi mashi sai yace su koma falon baki ya zauna, Naufal saiya koma ciki domin ya faɗa ma Abla inda zata kai abinci.
Yana zaune ya kifa kansa akan cinyarsa, baisan da zuwanta ba saiya ganta a gabansa. Baya ya matsa a firgice har saida ta tsorata.
"Haskena kin dawo ne?" ya faɗa a tsorace. Sai kuma ya fara mika hannunsa dake rawa yana so ya taɓa fuskarta yaji ko itace ɗin.
#NiDaDiyata
*Dedicated to all the family of this book, because yanzu mun zama yan uwa*
~Yarinya Mai DIMPLΣS~©Exquisite Online Writers
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
💦 Ni Da Diyata 💦
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Written by DIMPLΣS
Wattpad @Aynarh_dimples
💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦
✨✨✨Page 37 ✨✨✨
On the authority of Abu Dhar Jundub bin Junadah, and Muadh bin Jabal that the messenger of Allah said : "Fear Allah wherever you are, and follow up a bad deed with a good one and it will wipe it out, and behave well towards people." Tirmithi narrated the Hadith and said it was fine, and in another version, said ture and fine.
**********
Ikon Allah Abla ta tsaya gani, duk ya ruɗe babu gaira babu dalili, though ranta yana bata cewa kila shima yana ganin gizon da akace tanayida Miemie. Sai dai ba wani big deal bane dazai rude haka kamar yayi gamo.
Bata hanashi taɓa fuskarta ba saida itama ta kafa mashi ido kamar yadda ya kafa mata. Yana taɓata yaji mutum ne saiya sake baya ya rufe idonsa. Rufa ke keto masa duk ya firgita, saiga Naufal ya shigo.
“Yauwa Abla dama ke nake nema”
Kallon Khattab yayi yaga ya sukurkuce, Cikin damuwa ya soma masa magana.
“Lafiya kake zufa duk Ac dakin cikin nan?”
“I think shima yana ganin Miemie a fuskata ne” ta amsa a sanyaye
“Ohhh! Of course Abla ne, yes im not running mad” Khattab ya faɗa yana ajiyar zuciya a hankali, handkerchief fari ya ciro daga cikin aljihunsa ya share zufan Fuskarsa.
Da farko ya dauka yayi gamo ne, sai kuma ya sha hauka ya somayi. Zuwan Naufal ba karamin relief ya bashi ba. Ita kuma mikewa tayi ta bar wajen tana matse kwalla.
Abin ya fara isanta, hala mutane basu lura itama tana missn Miemie bane, duk inda taje sai an firgita kuma ba’a lura itama tana jin ciwon abun cikin ranta.
Shi kuma fasa cin abincin yayi saiya tafi gida kawai, kwanciyar rub da ciki yayi akan gadonsa. Kawai tunanin yanda Abla batada bambanci da Miemie ne yakeyi. Magrib aka kira saiya tashi ya wuce masjid.
A hanyar gate ya haɗu da Lili tana dawowa daga anguwa, da gudu ta karasa inda yake ta rungume sa. Dama rabon data haɗu dashi tun shekaran jiya.
“YaKhattab naji daɗin ganinka Wallahi”
“Na hanaki rikeni, wai meyasa bakya jine?”
“Toh fah ji wani sanabe, wallahi iyayi da kakeyi kamar baka jin dadi idan na rike ka bani mamaki yakeyi”
“Eh naji nidai sakeni kawai kinga masallaci zani kafin na makara”
“Anaso ana kaiwa kasuwa” tace saita sake shi. Harya soma tafiya wajen taku biyar haka saiya juya, “Lili” ya kirata.
Itama waigowa tayi tana rarraba idanu, “ya akayi ne Yaya?”
“Am mani mutuwa amma bakiyi min gaisuwa ba, mutuwa fa ba abin wasa ne!”
“Toh ni ina ruwana dan budurwa ka ta mutu? Wallahi banki ba duk wanda ta ganka tace tana so ko cikin ranta ne toh ta gangara lahira” ta faɗa tana hura hanci.
Murmushi yayi mai bayyana bakin ciki, cikin gadara ya bata amsa. “toh saiki zauna gadin duniya idan kina tunanin bazaki mutu ba, kuma mutuwar nan yana kan kowa balle kice banda ke”
“chan ta matse maka” saita barshi wajen ta nufa cikin gida. Shikuma girgiza kai yayi yana murmushi, nan ya tuna da Miemie daya kirata a waya sunsha dariya. “Allahu Musta’an” ya furta a fili saiya nufa Masjid.
*****
Yasmeenah ta rinka hura ma Naufal wuta akan su tafi, ko sallar Magrib da kyar ta bari sukayi. Ita bama zata yiba saboda ana binta bashin azahar da la’asar kuma da kunya kaje gidan mutane kana jero salloli.
Yana dawowa ta mike wai a dole sai ta tafi, kamar kyamar gidansu takeyi taki sakin jikinta, bata lura cewa Deela bata haɗa komai dashi ba amma ta mayar da gidansu kamar nata.
Yaune ake sadakan bakwai amma Abba ya umarce shi akan yayi zamansa, da wata matar arziki ne da tun safe ta tilasta suje.
Haka sukayi sallama da yan gida suka tafi, tun bayan da akayi masu nasiha bai sake ganin Deela ba. Koda ya aika Bilqees ta kirata bata ko kalleta ba.
A Vanilla joints suka tsaya ya siyan masu shawarma, burger da milkshake. Daga nan ya tsaya a Chuchu Stores ya siya bread, milo, Madara, Indomie, sardines da sauran su.
Ita hakima ta hakince cikin mota tana duba Instagram, hotunan celebrities take kallo musamman ma maza tana jindadi hankali kwance. Ya dawo shake da kaya amma ko ta taimaka masa, asalima yi tayi kamar bata san yana jiran ta tayashi buɗe kujerar baya ba.
Haka ya ajiye kayan a kasa saiya buɗe da kansa kana ya sake dauka daya bayan daya ya rinka sakawa ciki. Bayan na saiya zaga ya shiga ya soma tuki. Ko irin ‘Sannu da kokari Maigida’ bata ce ba. Tuki ya soma yana tunainin ko ta daina sanshi ne kokuma kawai iya shege ne...
“Bazaki taimaka min bane kin ganni sai wahala nakeyi” tana yatsina fuska ta dauki ledar Shawarma da burger kawai tayi shegiwarta ciki.
Daki ta shiga ta ajiye, saita buɗe shawarma tana ci. Tanayi tana kallo ko bin kan Naufal batayi ba. Shima ya watsar da zancenta ya nufa Masjid domin yayi sallah isha.
Saida taci tayi nat kana ta wuce hanyar ɗakinta, a locacin tayi wanka tareda daura alwala.Jero train ɗin sallolinta ta soma yi. Ita bata kwana batayi sallah ba amma bata fiye sallah akan lokaci ba, duk dare zatayi abinta.
Wani pink nightgown mai laushin gaske gashida sansti ta saka. Saita saka palms din barci ta nufa hanyar ɗakinsa.
Shikuma ya dawo daga Masjid yaga falo duk burbushin abinci wanda taci ta bari, daukan nasa yayi ya tafi ɗakinsa. Baici ba saida ya kintsa.
Ya gama ci yana shan ruwa daga bedside fridge ɗinsa saita shigon tana masa murmushi, dakewa yayi amma bata damu ba.
Shagwaba ta soma masa, daya mata maganar behaviour ɗinta na ranar saita bashi hakuri wai kawai she is overwhelmed by everything ne. Ba laifi ya sauko daga fushin sa daga nan sukayi kwanta.
After six weeks...
Fadeela ta soma samun sauki sosai, har yanzu bata magana amma ta rage yawan kuka kamar yanda ta mayar ibada. Kuma tana ɗan murmushi koda sau ɗaya ne a rana.
Kullum cikin addu’a take a zuciyarta Allah ya bayyana mata ɗiyarta. Har tayi arba’in ta soma sallah da kanta tana rok’on fita daga cikin matsalan.
Naufal da kanshi ya dauko mata donkey, paints dasu sauran kayan masu painting. Taji daɗin abin sosai saboda yanzu batada wani sana’a sai shi.
Kowa yana murna yadda ta fara mayar ma Allah komai ta dauki dangana. Yakan zo dubata sau biyu, da safe idan zashi office sai kuma da yamma idan ya dawo kafin ya wuce gida.
Ta ɓangaren aurenshi da Yasmeenah kuwa babu abinda ya canza. True colour dinta ya bayyana sosai, samsam bata da kunya ko kadan. Gatada tsiwa yana cewa kule zata ce chas.
Abinda ke bashi haushi shine rashin iya girkinta. Kwata kwata bata san yadda ake sarrafa ɗanyen abinci a mayar daffafe ba. Kawai managing yakeyi saboda bayaso ya tsinka ta wajen iyayen shi ya rinka cin abincinsu har su gane.
Sau da dama yakan kira Abla ko Bilqees suzo tayata aiki duk a zatonsa hannunka mai sanda yake mata, ita kuma bata san wannan ba suna zuwa take naɗe kafa ta fara kallon Korean series ta barsu su kadai cikin kitchen din.
Gajiya yayi da ɗabiarta ya hanasu zuwa , dama suma basa santa at all. Ta rinka daka masu ihu kenan kamar yaranta, abin yafi bama Abla haushi ita dake sa’a da ita.
Ita Abla ta gama Nysc ta soma aiki a Ministry for Women affairs, ita kuma Bilqees za'a shiga 300l.
******
Shikuma Huzaifah baya kwana uku cikarkiya baije ya duba Yasmeenah ba, shakuwa ne sosai ya shiga tsakanin su. Kullum cikin tambayarta yake ko tanada wani matsala wala na kuɗi kona Naufal.
Tun tana ɗari-ɗari dashi harta sake mashi sosai. Musamman yanda idan zaizo yakan kawo su shawarma da chocolate wata rana harda ice cream da kasarshiyar kaza.
Sukan sha hira sosai tana jin daɗin company ɗinsa, Hilal dai bai taɓa zuwa ba amma sauran yan uwanta duk sunje wasu sau daya wasu kuma biyu.
Naufal ya nuna bacij ransa a fili amma bataji ba, sau da dama abin ya jawo masu tashin hankali amma tace bazata daina sake mashi ba.
Thou bai taɓa shiga ɗakinta ba amma bata kiba idan tayi wanka sanye da towel tazo falo suna hira tayi shafa da kwalliya...
Sau da dama tana ba shi kanshi Huzaifah labarin irin faɗan da sukayi da Naufal akanshi, ‘sis kina wuta fah, wallahi bakida dama’ yake cewa.
Wata rana suna cikin hira ya ce, ‘yanzu kina samun ciki kika haihu kema za’a maki kishiya’
“Akan me za’a min kishiya”
“Konine matana ta dauki ciki cikin early years ɗin auren mu to zan mata kishiya dole”
“Kai daban mijina daban!””
“We are all guys, kuma tunanin mu daya ne. Idan zan baki shawara ki dauka toh ki bari nan gaba saiki haihu”
Ajiyar zuciya yayi yana kallonta,yana ganin kamar maganar shi ya fara tasiri cikin ranta saiya soma magana da full confidence babu inda inda, “nifa dan uwanki ne bazan cutar dake ba, mufa maza bama son takura kuma kinsan tara yara ba karamin takura bane”
“Shikenan zanyi tunani” ta faɗa a sanyaye.
“Da yafi maki Lil Sis”
Murna fal cikin ranshi saboda hakkunsa ya kusan fara cinma ruwa, wani smug kallo kawai yake mata ta gefen ido kuma yana kara ma jikinta kallo.
Yau sanye take da blue crazy jens wanda yasha yanka ta wurin cinya da gwiwa, saita haɗashi da chiffon top mara hannu. Yana kallonta yana haɗiye miyau saboda kwanan nan bashida wani katabus sai tunanin ta. Ko barci yanzu gagaranshi yakeyi saboda yanda take masa yawo cikin rai.
Yasa saiya zo ya ganta yake jin daɗi, saidai inda abin yake zuwa mashi da sauke tana bashi free show din jikinta koba duka ba amma yana samun banza. A hankali zai koya mata sanshi harta rabu da mijinta ta koma mashi.
Ita kuma abinda Huzaifah ya faɗa mata ya soma mata yawo a cikin kanta, tabbas akwai kamshin gaskiya a tareda zancen saboda gashi Fadeela bata gida kuma ta lura tun kanta haihu take chan gidan. Ita yanzu duk wani hanya da zata bi ta malleke Naufal take nema, idan rashin haihuwa zai zame mata mafi saukin toh shi zata bi.
Yanzu idan Naufal ya dawo zata faɗa mashi suyi tsarin iyali, sai wani zuciya ya raya mata cewa gwara tayi abinta ita kaɗai babu wanda ya sani.
Chuchu Stores and Pharmacy taje ta siyo contraceptives kala kala na kamfani daban daban. Haka ta rinka shan abinta bada sanin Naufal ba.
Three months later........
Koda Naufal yaga batada ciki bai damu ba saboda Fadeela itama haka tayi kafin komai ya daidaitu mata. Bashida wani buri daya wuce ya tara iyali sosai, gashi har yanzu ba’a ga Pha’eexah ba.
Saidai IG baban Khattab yace har yanzu suna kan case din baza’a huta ba sai anga karshen abin. Shikuma Khattab ya koma bakin aikinsa yanayi sosai.
Sunyi kacha kacha da Lili har yayi sanadiyar barinta gidan su, yaji dadi sosai saboda yanzu yana samun ya wataya.
Saidai har yanzu zancen wata budurwa kuma baiyi ba. Bayada lokacin kallon wata ‘yamace kuma. Soyayyar Miemie yana nan fal cikin ransa kamar basu rabu ba, ya rasa inda zaiyi da irin abun.
Wata rana yana zaune cikin office ɗinsa, wayarsa ya dauka yana kallon screensaver ɗinsa wanda hoton Miemie ne bai cire ba. Kawai daukar mukullin motarsa yayi saiya nufa gidan gona.
Ya shiga anyi gaisuwan mutunci da Anty da kuma Deela, yanzu ta murmure ta soma magana sama sama tunda dama surutu ba ɗabi’arta bane.
Shiru yayi baice komai ba, ya rasa Dalilin zuwan shi gidan.
“Lafiya dai koda wani matsala ne?”
“Lafia lau Mommy” ya amma yana inda inda.
Suna cikin haka saiga Abla ta shigo cikin falon tareda sallama. Deela da fara’arta ta daga ta kalleta “Wata sabon gani, Abla kin share ni”
“Ba haka bane Momyn Pha’eexah, Boss dina tayi tafiya zuwa Abuja yasa nike komai a office. Wallhi Yanzu banida wani isarshen time”
Zama tayi akan Couch na 2 seater Kusa da Fadeela, “Ina wuni Anty?”
“ina gajiya Abla ya aiki?”
“lafiya ya gida?”
“Alhamdulillah, yasu Mamanki?”
“Duk kalau suke”
Suna gaisuwa amma attention ɗin Khattab yana kanta, tabbas itace ke masa sukuku cikin rai kuma dalilinta yazo gidan nan. Soyayyarsa da Miemie yayi zurfi yanda bazai iya maye gurbinta da wata mace ba amma ya rasa gane dalilin da yana jin wani iri idan yayi tunanin Abla.
“Ina wuni Khattab” Abla tace, dayake yayi zurfi wajen tunani saida ta sake maimaitawa kafin ya amsa.
“Lafia lau” ya iya cewa saboda yadda zuciyar sa yake gudu da sauri. Mikewa yayi ya tafi.
Kai tsaye ɗakinsa ya wuce, kanshi ya soma mashi zafi gashi zuciyar sa yana mashi wani irin barazana. Sam baya so ya yarda cewa yana san ta ne, amma ya kasa daina tunaninsa.
Saida ya ganta ya lura ba Miemie yake tunawa ba illa ita. Tirkashi! Yanzu ya zaiyi? Haka yake tunanin yadda zaiyi over coming problem ɗinsa.
Ya yanke shawarar yaje ya sameta saboda zuciyarsa yana mashi barazana bugawa idan bai samu abinda yake so ba.
Bayan Isha ya tafi gidan gona, a bakin gate Mai gadi ya faɗa mashi cewa ta tafi gidansu. Dayake ya taba kai Miemie gidan sanda take raye so bai wahala ba.
Ya aika ayi mashi iso da ita, shikuma yana zaune cikin motarsa yana addu’a saboda gabansa yanata faɗi na rashin dalili. Ita kuma tana kwance akan gado ta gama rubuta wani proposal haka.
Whatsapp ta shiga tana ɗan karance karance littafin hausa mai suna “A Dalilin Mene” wanda UmmieeJafar ta rubuta. Maigadi yayi sallama wai ana nemanta a bakin kofa.
Koda ta tambaya wanene yace gaskiya cikin dare ne kuma baiga fuskarshi ba,saidai ya ce ai mashi iso da Abla. Dayake ta riga tayi shirin kwanciya, saita daura dogon riga da kuma Hijab wanda ya wuce gwiwanta da kadan.
Sallama tayi data isa wajen motarsa, ya fito yana jingine. Saida ya amsa ta gane Khattab. Nan taji gabanta ya faɗi saboda idan abinda take tunani yake so yayi zata tsayar dashi tun kafin komai yayi nisa.
Na farko dai ita ba Miemie bace, saboda haka babu gurbin dazata maye mashi. Bayan sunyi gaisuwa sai sukayi shuru na kusan minti biyar , kana ganinsu kasan akwai tension tsakanin su.
Kawai nazarinta yakey, tabbas wannan ba Miemie bace, koh ɗabi’un su ya bambanta sosai. Miemie bazata taɓa ganinsa tayi shiru ba, saidai kuma Miemie tana sanshi, wannan babu wani abu datake ji mashi a ranta.
Haka suka gama tsayuwa ya kasa cewa komai sai kawai yayi mata sallama ya tafi. Itama sallama tayi ta wuce cikin ɗaki.
Abla irin matan nanne masu kwarjini da ba kasafai zaka iya gaya masu aininhin abinda ke ranka ba. Ita ma taji dadi bai kawo mata wani shirmeba.
Bawai tanada wani tsayayye bane amma bata tunanin zata iya soyayya dashi, ita tana ganin cin amana ne wajen mai rasuwa Miemie.Babu abinda bata sani na Khattab daga abincinsa, kayansa, colors da sauran abinda ya dace wani ya sani akan ka. Miemie idan ta dawo daga taɗi takan bata labarin shi sosai.
So wannan amanar yasa bazata iya betraying trust ɗinta ba even in death. Kawai Khattab ya dauki na damu ya nema wata chan daban.
Shikuma yanzu duk bayan kwana biyu sai yaje dubata, sometimes ya kanyi siyayya ya kai mata. Bai taɓa faɗa mata dalilinsa na zuwa ba, asalima basa hira daga gaisuwa sai bayan wajen 20mins haka ko 30 sai ya tafi shikenan kuma sai gobe ko jibi. Infact ko number dinta bashida shi itama haka batada nasa.
Duk sanda ya zo ya tafi abu ɗaya take faɗi a ranta, ‘Iska na wahalar da me kayan kara”
Shikuma yasan cewa every disappointment is a blessing in disguise, baisan abinda zai faru nan gaba but he is optimistic about everything. Yasan cewa Allah baya baka abinda bazaka iya handling ba.
Komai rabo ne da kuma lokaci, idan babu rabonka a cikin abu duk yanda kaso bazaka samu ba, dama zabin Allah yake nema a koda yaushe.
#NiDaDiyata
_Yarinya Mai DIMPLΣS_©Exquisite Online Writers
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
💦 Ni Da Diyata 💦
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Written by DIMPLΣS
Wattpad @Aynarh_dimples
💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦
✨✨✨Page 38 ✨✨✨
Abu Hurairah (May Allah be pleased with him) reported: The Messenger of Allah (Sallallahu 'alaihi wa sallam) said, "There are two statements that are light for the tongue to remember, heavy in the Scales and are dear to the Merciful: 'Subhan-Allahi wa bihamdihi, Subhan-Allahil-Azim [Glory be to Allah and His is the praise, (and) Allah, the Greatest is free from imperfection]'."[Al-Bukhari and Muslim].
********
Wani Laraba haka wajen sha biyun rana, ina zaune cikin Office dina saiga Sadeeq ya shigo. Bayan munyi sallama sai yayi min korafin yunwa.
Nan take gabana ya faɗi saboda gidana ba inda za’a kai bako bane, Aminu shima ya shigo wai a dole sai sunje gidana cin abinci. Babu noke noke da banyi ba amma sukayi burus dani.
Haka na tashi ina Hasbunallahu wa ni’imal wakeel inatayi har muka kai gidana. A parking lot mukaga Motar Huzaifa, nan jikina yayi la’asar. Yanzu Huzaifa bashida timetable na zuwa gidana, baisan safe balle rana. Koda yaushe zuwa yakeyi.
Su kuma su Huzaifa da Yasmeenah sun zama besty 5 and 6. Suna jin daɗin company ɗin junarsu. Babu tashin hankali da batayi dani akan abin kuma na nuna mata bacin raina amma tayi kunnen uwar shegu.
Suna zaune a falo suna kallon sabon India mai suna ‘Dilwale’ wanda Kajol da Sharukhan sukayi acting. An kai wajen wani waka haka sai Yasmeenah tayi rewinding ɗinsa daga farko. Toh dama laptop din Huzaifa suke kallo dashi.
Nan ta soma babbaka rawa, su crip walking takeyi saita haɗa da azonto daga nan sai tayi ending dinshi da dab.
Su kuma su Naufal ana cikin tafiya akaji karar waka, nan take raina ya ɓaci. Gashi kuma nazo da baki. Yau tabbas sai na ji kunya. Dama duk wanda baiji bari yaji hoho!
Fatana ɗaya kada na risketa tana zabga rawa tunda karamin aikinta ne. Aikuwa kaddara ta riga fata saboda babbaka rawa take yi abinta. Sororo muka tsaya bakin kofa muna kallonta.
Huzaifa yana daga kwance ya hakince a 3 seater kai zaka ranste shine mijinta. Amshi yake mata “Go Meenah! Go Meenah!! Go go go Meenah !!!” ita kuma sai dancewa take yi. Dariya ya bushe dashi sannan ya naushi iska tareda tafa hannayensa sai yace “Tirrrrrr yarinyar nan bakida dama wallahi”
Itama dariya tayi saita juya ta ganni tsaye bakin kofa da baki. Da gudu tazo inda nake ta sumbace bakina babu kunyar mutanen dake wajen.
“Mine ka bani mamaki bansan yanzu zaka dawo ba”
“Nida gidana saina tambaya izininki kafin na shigo?”
“No bahaka bane im not expecting you, at least ko waya da kayi min amma bawai kawai ka fado min ba without a warning” ban kulata ba saboda ina dab da marin ta, karyan iskanci takeyi nazo na iske ta tana rawa gaban wannan gwaskar shine zata wayanace.
Sai kuma ta juya ta gaida su Aminu kana tayi introducing Huzaifa as Big bro dinta.
Shikuma Huzaifa ya mika masu hannu suka gaisa, nidai ban mika masa ba saboda na tsane shi. Da baki muka gaisa saiya tafi, har yakai bakin kofa saiya juyo yace, “Lil sis gobe da safe zanzo na karɓa laptop dina saboda munada board meeting”
“okay Yaya Huzzy dont worry yau ba zanyi barci ba zan kwana ina kallo har saina gama”Daga gira yayi daga nan sai ya tafi. Ni yanda yake behaving ban taba zaton yana anything for a living ba saboda baya zuwa aiki at all, kullum yana gidana. Wata rana har Saturday and Sunday.
Shigowa falon muka yi gashi kacha kacha babu gyara, su ledan Oasis ne birjik dasu gwangwani na maltina da pepsi wanda aka sha aka rage. Ga kuma burbushin cake daga kan kujera har kasan carpet.
Da sauri taje ta fara tattara wa, gashi rigar ta doguwa ce amma ya matseta tsam. Duk wani haushi da kunya ya kamani kawai bance komai ba. Itace ta fara magana, “Please kuyi hakuri dama inaso na gama kallo ne tukun kafin nayi shara”
“Karki damu amarya lantarkin gida, ai bakya lefi koda kin kashe dan masu gida” Aminu yace yana kallon fuskar Naufal. Ni kuma haɗa rai nayi saboda nasan iskanci yake min.
Wucewa tayi ta dauko ragowar cake dasu shawarma ta kawo mana, nidai banci ba saboda yadda na tsane Huzaifa bana iya cin abinda ya kawo. Su dai su Sadeeq sunci.
Ta kwashe tarkacen da zata iya tsincewa saita ce, “Kuyi hakuri banyi abinci ba, yanzu sharp sharp zan maku taliya”
“Au bama ki daura ba kenan?” Aminu yace yana dariya.
“Wallahi kuwa, nifa house chores is not my calling, i really hate it... Kawai saboda ina san Mine ne yasa nakeyi”
“Toh fah!” Aminu yace
“Mazaaa kaji ance saboda ana sanka ne ake yi a haka” Sadeeq yace.
Ni kawai ban kula suba banda chanza channel zuwa Aljazeera na soma kallon labarai.
Wucewa tayi kitchen domin ta daura sanwa, wanke wanke ne shake a wajen. Gashi batazo da Dish washer ɗinta saboda kitchen dinta is too small. Wasu daga cikin sun fara yauki saboda tun na jiya dana shekaranjiya ne.
Haka ta matsar da wanda zata iya saita dauraye tukunya ɗaya. Saita daura ruwa akan gas, manja ta saka bata ko soya ba saita saka tomato paste. Bata saka albasa ba saboda bata so hannunta yayi wari sai kuma ta zambada barkono.
Dauko kifi tayi daga fridge mai kankara, dayake akwai sanyi dayawa, da kyar ta wanke. Ko scales din bata cire ba, haka kashin dake ciki ba duka suka samu daman fita ba.
Cikin ruwan dake tafasa ta tsumbula saita saka spaghetti ɗaya ma gardawa uku. Maggi kuwa ta saka kusan goma ma taliya leda daya.
Babu kamshin dake tashi bazaka zata ana girki cikin gidan ba, ko su Naufal mamaki sukeyi har yanzu bata daura ba saiga abinci a cooler ta fito dashi.
Ta ajiye masu akan dinning table saita koma ta cigaba da kallonta. Ta hada masu Ginger drink mai dan karan zafi, Aminu yana sakawa a baki saida ya fito dashi. Hawaye ya soma gangaro masa saboda zafin dayaji.
Sun buɗe cikin cooler sai sukaga taliya kitub ya chabe, gashi mai isheshi ba. Kawai addu’a sukayi kada yayi rashin daɗi. Sun zuba ma kansu amma bazai ishesu ba saidai managing.
Naufal ya fara kaiwa baki, zare ido yayi saiya toshe bakinsa da hannunsa. Da sauri ya dauki zuwa yakai baki tunda bazai iya shan ginger dinba. Tauna yakeyi amma abincin yaki wucewa, saida ya sake korawa da ruwa tukun.
Gaban Sadeeq ya faɗi sosai saboda a duniya abinci mara daɗi ne baya so. Haka suka ci abincin suna zare ido tareda shan ruwa, kuma kowane cokali saika kora da ruwa saboda babu inda zai wuce da kansa. Kwata kwata bashida dadi kamar an wanke kan mahaukaciya!
Sun gamaci sai nishi sukeyi kamar sunyi aikin karfi, “Amarya mun gofe fah, Allah ya saka maki da alheri da duk abinda kikayi mana” Sadeeq yayi mata ba’a.
“Haba dont mention, it’s my pleasure” ta amsa tana yauki, dayake bata ciba so bata san how horrible abincin yake ba. Ba Aminu kawai ba har Naufal saida ya bushe da dariya saboda sun san abinda Sadeeq yayi.
“Amaryar Naufal kina sha’aninki, Allah ya barku tare” Aminu yace yana kyallara ido ma Naufal.
“Amin summa Amin” ta amsa.
A hanyar rakasu sai mashi iskanci sukeyi, “Ashe dama haka kake kwasan dadi, yasa naga kayi fari fat kamar fatalwa. wannan shine kaikayi ya koma kan mashekiya”Sadeeq yace.
“Aikuwa dai, kaso musguna ma Deela babu gaira babu dalili shi ne Allah ya kama ka” Aminu yace.
“Nifa kasan har daina magana yayi min, don kawai ina bashi shawara akan ya bar zancen auren nan. Amma yanzu me gari ya waya ka dawo gida ga wani katon banza ya hakince yana kallon matar ka tana mashi rawa” Sadeeq yace yana kwafa.
“Wallahi na rasa yadda zanyi da ita ne, kamar ta raina nine” Naufal yace a sanyaye.
“Ai babu tantama ta gama rainaka, if not bazata yi haka ba, but ai duk tsuntsun daya kirawo ruwa shi yake duka”Aminu yace.
“Allah dai ya kare” Sadeeq yace. Daga nan suka yi sallama suka wuce.
**********
Soyayyar Abla sai kara zama yake a zuciyar khattab, bata bashi fuska at all. Kullum saidai yazo yayita inda inda baya iya cewa komai. Gashi har yanzu bashida number ɗinta.
Wata rana yana zaune a cikin Office dinsa saiya dauki alwashin yau zai gaya mata abinda ke cikin ransa. Ya tashi bayan yayi Maghreb saiya tafi gidan su Abla.
Maigadi ya fada mashi cewa Abla bata dawowa, dafa kansa yayi yana tunanin inda take sai kawai ya yanke shawara ya tafi gidan gona ya dubata tunda bashida number ɗinta balle ya kira ya tambayeta.
Ita kuma Deela ta samu sauki sosai, ta mayar ma Allah komai saboda yanzu har magana takeyi. Ta murmure sosai har Naufal yana tunanin yayi mata maganar komawa ɗakinta koba komai zai samu abinci sosai.
Tunda yanzu bawai yana samun abinci isarshe bane, Yasmeenah da kanta tace mashi ya rinka cin lunch dinsa a waje saboda bazata dauki nauyi ba.
Missing fadeela yakeyi sosai saboda ko kadan bazata mashi haka ba, dama Hausawa sunce idan baka gode ma alherin da Allah ya baka ba zaka gode ma azabarsa.
Ita Abla daga wajen aiki kai tsaye gidan gona ta wuce saboda Deela tanata mata korafi akan ta watsar da ita. Suna zaune akan gado suna shan fruits salad suna hira cikin dakin Miemie wanda yanzu ya zama na Fadeela.
Fadeela tace mata ta kwana ita kuma tace batada su brush da kayan sawa. “Indai wannan ne matsalar ki karki damu zan baki”
“Allah ya barmin ke matar Yaya”
Wayan Fadeela ya soma ringing sai taga sunar Khattab baro baro akan screen.
“Assallamu alaikum”
“Waalaikumus salam Khattab ya kake ya aiki?”
“Alhamdulillahi” sai kuma sukayi shiru na wasu dakikai kadan.
“Dama Anty ina kofar gidane bansan ko Abla na kusa ba kice mata ta fito”
“Eh gata gefena, babu damuwa” daga nan suka kashe wayar. Deela da fara’arta ta soma magana, “Khattab huh! Gaskiya naji dadi sosai”
Hada rai Abla tayi sosai, bata kula Deela ba kuma batada niyyar fita waje yau saboda zuwansa ba karamin takura bane a wajenta.
“Tashi mana ki fita kin barshi a waje, wulakanci bashida kyau dai”
“Saurayin Miemie ne fah!”
“Wani Miemie kuma? Wanda ta rasu ko wata daban, yarinya na ciki kabari kina lakata da wani saurayi. Koko shi Khattab din katako ne da bazai sake aure ba?”
“Nifa bawai wulakanci nakeso nayi masa bane, kawai banaso mutane su ce na kashe sister dina domin in aure saurayinta”
Deela bushewa da dariya tayi sosai. Ashe Anty tana jinsu, a hasalce ta fara magana, “Bada bakinsu zasuyi magana ba, sufa suke kiɗansu kuma suke rawar su. Fatan Alheri kawai zakiyi ki mance da komai”
“Kuma idan zan baki shawara kiji tofa kiba yaron nan haɗin kai, haba sai kace shi kadai yazo duniya, ya gama wahala da Miemie yanzu kema zaki saka mashi ciwon kai”
“Ai kuwa dai, yana kokarin sosai ga shida kamala” Deela tace. Ita dai Abla bata ce komai ba kawai zata yi nazarin abinda suka ce ne. Anty ne ta cigaba da magana, “Sau nawa kuma sai kiga Miemie bata rasu ba an fasa da ita ayi dake... Idan fa shine mijinki babu yadda zakiyi gwara kisan me kikeyi”
Haka ta tashi rai bai so ba ta saka mayafi ta wuce wajenshi, sallama tayi mashi sai suka gaisa. Daga nan tace masa su wuce cikin Falo amma yace ta barshi cikin motar sa.
Sunyi shiru for like 45mins, ita tana wasa da yatsunta shikuma ya kafa mata ido. Dama yaso ya kureta ne yaga ko zatace wani abu amma batayi ba. Tun dayake zuwa wajenta basa kai 30mins, mostly 20mins saiya tafi.
“Saidai na kashe ki amma bazaki ce komai ba” bata amsa ba kawai kanta yana sunkuye da kasa.
“Abla”
“Na’am”
“Inaso idan zaki min magana ki rinka kallona”
“Toh” saidai kuma bata kalleshi ba.
“Abla me kike min haka? banida wani tunani yanzu banda naki.... Please Abla answer me ko zanji saukin radadin danake ji.
“Ni babu abinda nake maka” ta fada a sanyaye, shikuma kaima steering duka yayi.
“Haba Abla ji yanda kike treating dina kamar nayi maki wani laifi, bafa ni na saka ma kaina ba. Allah ya daura min. Though nasan kina tunanin zanyi replacing Miemie dake ne but Wlh komai dana ke jin maki its different”
Shiru tayi kawai tana nazarin abinda yake faɗi, “Abla tunanin me kike yi? Kin tsane ni koh... Meyasa kike min haka?
“Nifa ban maka komai ba tun dazu kace nayi maka wani abu”
“Kamar ya bakiyi min komai ba, shirun nan is killing me. Nafiso ki saki jiki ki rinka mini magana please”
“Toh ai kaima baka magana”
Dariya ya soma, “Haba baiwar Allah ta ina kikeso nayi magana bayan kin haɗa rai....salan ki wanka min mari. Please oooo i like life” Murmushi kawai tayi daga nan saita soma hamma alamun barci.
Wayarshi ya fitoda akan ta karanta mashi lambarta, ita kuma sai ta amsa zata saka da kanta amma yaki, dole ta rinka kiran masa yana yi da kanshi. Saidai kuma idan tace 7 sai yace 5, haka taketa gyara masa har suka gama.
Da gangan yayi mata haka duk salon bata lokaci da ita kuma tace wani abu ko babu dadi. Yayi alkawarin kiranta anjima yaji amsar da zata bashi akan batun su.
Nan yayi flashing number dinsa sai yace tayi saving ya gani, Khattab ta rubuta mashi.
“Haba mana, Khattab kawai zaki rubuta. Babu dan Baby ko Sweetie yanda yan mata keyi” dariya kawai tayi tana mamakin yanda he is free and very fun.
“Okay ni bari nayi saving ki ga naki” ‘Haskena’ yayi storing dashi. Nan fuskanta ya canza saboda kowa yasan Miemie ce Haskensa. Dariya yayi saiya ce, “Allah ya bani Haske da farko sai kuma ya dauke mani ita. Nayi dangana shine ya sake bani wata”
Daga masa kai tayi alamun ta gane. Itadai kawai tana tunanin irin amsar dazata bashi anjima ne.
Tana isa daki taga Deela tana gyara drawer, kayan suna ne take sake jerawa da kyau. Daga nan sai suka ga Cd plate da aka yi video covering amma basu kalla ba. Fadeela nata ninke kaya daga gefe ita kuma Abla ta dukufa tana kallo a laptop.
An nuna Miemie sosai saboda ko ina tana wajen kamar MTN, ga shi little One itama sai dariya takeyi. Video din yana kunshe da happy moments sosai.
Ita kuma Deela cin karo da kayan Anty Anisa tayi, “Allah sarki baiwar Allah tana chan port Harcourt” Deela tace cikin ranta. Haka ta gama ninke kayan ta ajiye cikin drawer. Saidai kuma wani abin mamaki bazata tuna sanda sukayi sallama da itaba.
Though kuma dai akwai jama’a gashi kuma ya dade da faruwa saboda kusan wata shida kenan idan baima fiba.
Abla na cikin kallo saita tsandara ihu saboda sledgehammer din da akayi amfani wajen kashe Miemie ta gani cikin video.
‘Haba Abla meye na ihu kamar ba musulma ba, ni duk kin firgita ni”
Hawaye na gangaro mata tace, “Nasan wanda ya kashe Miemie”
Da gudu Fadeela ta karasa wajen domin ta gani itama, Abla tayi rewinding amma Deela bayan mutum take kallo. Gashi kuma bata gane ko wacece ba.
“Abla nifa bangane ba.... Wai waye wannan? Kin ganta ranar suna ne?”
“Eh mana Anty, baki gane.......”
#NiDaDiyata
*Shout out to Lubna Sufyan, Hussaina Ubandiya, Sumy Gaya, Jidda, Feeyah Galadanchi, Taatuh, Rukky Mt, Kharriya, Mrs Chubado, Asiya Ahmad, Basira Sabo, Fulani, Asmeebae etc, Thank you from me to you*
#AinauMardiyah[2/3 11:00] DIMPLES: ©Exquisite Online Writers
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
💦 Ni Da Diyata 💦
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Written by DIMPLΣS
Wattpad @Aynarh_dimples
💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦
✨✨✨Page 39 ✨✨✨
An-Nawwas bin Sam'an (May Allah be pleased with him) reported: I heard the Messenger of Allah (Sallallahu 'alaihi wa sallam) saying, "The Qur'an and its people who applied it, will be brought on the Day of Resurrection preceded with Surat Al-Baqarah and Surat Al-'Imran arguing on behalf of those who applied them."[Muslim].
*******
Kuka Abla ta fashe dashi ta kasa magana, “Ki fada min wacece mana tunda ke kin ganeta”
“Anty ki kalla da kyau mana, yanzu baki gane wannan Anty Anisa bace?” Ras! Gaban Deela ya faɗi, kara kallon video din tayi kuma lallai babu makawa wannan Anty Anisa ce. Kuka ta barke dashi wiwi saboda bata taɓa tunanin Anty Anisa zatayi haka ba.
Anty Anisa ta kasance mace ce mai mutunci, batada kyashi ko kadan. Duk cikin asibitin anfison ayi mu’amala da ita. Gata da bala’in fara da tausayi. Ko sanda Fadeela ta haihu haka tayita ɗawainiya da ita. Kowane safe kafin ta tafi aiki saita duba ta. Sun zama kamar yan uwa cikin kwanaki kalilan.
Video din na cikin playing kanshi sai aka kyallara Anty Anisa da goyo a bayanta. Anan kuma kallo ya koma sama wajen Deela. Kuka tayita rizgawa saboda kowa yasan Anty Anisa shekarar ta goma da aure amma bata taɓa batan wata ba.
Anty Saudah ne ta shigo domin taji dalilin kukansu, anan Abla ta nuna mata itama. Nan kafarta ya soma rawa saboda tashin hankali. Bakin gado ta samu ta zauna tana jimamin wannan abu.
Wai yanzu ace mutum bashida tawakkali, idan zata dauki Pha’eexah meye na kashe Miemie kuma. Saidai kuma tasan cewa Miemie bazata bari a dauki Pha’eexah hakanan ba babu wani dambe.
Fadeela nata kuka bata ma iya cewa komai, babu mamaki idan ciwonta ya tashi ne. Anty ce ta kira Naufal da Abba a waya wai suzo yanzu yanzu.
Naufal a rude ya tashi duk zaton sa Fadeela ta rasu ne, Yasmeenah tana tambayarsa amma bai kula ta ba. Addu’a yakeyi kawai kada worst nightmare ɗinsa ya zama gaskiya. Shima Abba tunaninsa kenan.
Nan aka zayyana masu tareda nuna masu video, cikin kuka murya kasa kasa Deela tace bata tuna sanda Anty ta tafi ba saboda kwata kwata basuyi sallama ba. “Dama ni na tsaneta wallahi” Naufal yace
Anan aka kira baban Khattab aka gaya mashi. Nan take ya kira ma’aikatan shi wanda suke wakiltan case din domin su soma aiki gadan gadan.
Haka aka kwana ranar cikin kunci sabida bakin ciki sabo fal kamar ranar akayi mutuwar. Naufal bai koma gida sai wajen shadayan dare. Haka Yasmeenah tayita zumbure zumbure kamar zata fashe.
Washe gari wajen karfe 8, Yan sanda Uku ne a bakin Asibitin. Nan aka soma masu tambaya daya bayan daya akan al’amuran Anty Anisa. Kowa ya shaideta akan kyawawan ɗabi’unta. Kuma gashi ba’a faɗa masu dalilin tambayar ba. An tambaya sabon address ɗinta Kokuma number ɗinta amma babu wanda ya sani.
An kuma tambaya inda mijinta ke aiki amma shima wayam saboda ya canza aiki dab da tafiyarta. Anje tsohon inda yake aiki amma ba’ayi dace ba saidai number ɗinsa.
Nan take akaje Company ɗin Airtel tareda police report direct wanda IG ya rubuta masu. Daga nan sai akayi tracing number ɗin. Anan aka gane ba Port Harcourt takeba kamar yadda tace.
Tana cikin Abia state ne a wani gari da ake kira Isiala Ngwa. Anan aka kira police din state ɗin suje su duba asalin zancen.
Motaci uku ne shake da yan sanda da kuma mobile police akan babura suka nufa hanyar garin. Sun isa sai babban cikin su yayi knocking a kofar gidan. Da kanta ta bude saiya fara mata bayanin yana so ya bincika cikin gidan saboda wani case dayake aiki akai.
Da sauri tayi kokarin rufewa saboda tasan zancen dayake yin magana akai. Nan take ya hankade kofar kafin ya rufe. Wawan mari ya wanka mata kana wasu yan sanda da bindigogi suka sauko daga cikin Hilux dinsu.
Wata yar sanda ta hamɓareta da kafa kana tace, “Yeye woman see how you fine reach but you go dey steal pesin child, Ewu(akuya)” Anan yar sandan ta saka mata handcuffs sai sauran suka shiga cikin gidan gadan gadan.
Mijin Anty Anisa yana kan dinning yana karin kumallo sai kawai yaga yan sanda sun dunkareshi, wani sergent ya wanke fuskar shi da mari.
“Kaine kake ajiye yar sata koh?”
“Ranka ya dade yar sata kuma?”
“Ina yarinyar take?” kafin su karasa magana saiga Pha’eexah tana rarrafe ta shigo falo. Wasu yan sanda suka maza suka dauke ta.
Nan take ta tsandara ihu, “Yi shiru Ihsaan ba abinda zai faru dake” Anan aka tasa keyar Anisa da Mijinta Aysar zuwa office din yan sanda.
Su kuma su Naufal sun hau private plane din office din babban Khattab zasu Abia domin ayi dasu. A cikin jirgin akwai Naufal, Abba, IG, Grand Kadi sai Khattab.
Ita Deela tace zata amma aka hanata zuwa, dole ta hakura ta zauna a gida. Daren ranar ta kwana tana sallah saboda bataso taji wani labari ko Pha’eexah ta mutu ko wani abu.
Su Anisa da Aysar suna nan tamke a bayan canta, An kwace ma Anisa dan kwalinta da takalmi haka kanta bude, shima Aysar babu hula kansa da kuma takalmi.
Su kuma yan sanda nan suka bude chapter dinsu, ashar suketa watsa masu kowa naji. Har sauran wanda ke cikin cell tareda Anisa saida suka zageta. “Aboki naso u wicked reach, ahhha i no fit kill pesin as u see me so. Na fight i fight with my madam na him i enter here.... I swear you are wicked” saita mauje ma Anisa baki kuma tace idan tayi kuka saita kusan karya ta.
Shikuma Aysar abin mamaki yake gani wai ance sunyi sata, su dai Ihsaan dinsu watace tayi cikin shege a asibitin su Anisa shine ta basu kyauta.
Su Naufal an ajiye su a cikin conference hall zaa fara maganar case gadan gadan. Su Anisa an shigo dasu daure da handcuffs saboda ga Grand kadi basai an shiga Court ba.
An kawo baby Pha’eexah ta girma sosai tayi wayo. Tun kafin a soma Magana DPO ɗin wajen yasan cewa yarinyar Naufal ce. Ga kalan idanun ga kuma yanayin fuskar.
Shima Aysar yana haɗa ido da Naufal yaji kunya saboda yasan shine babban Ihsaan dinsu. Shi aka fara tambaya yayi bayani.
Nan ya zayyana masu cewa Anisa da dadewa tace zatayi masu adopting yaro. Toh sai kuma akayi transferring dinshi. Kiran shi tayi wai ta samu kuma ita zata bar aiki sabida tanaso ta raine yarsu da kyau.
Shi bai zirgi komai ba saboda har magana yayi da uwar yarinyar sanda aka haifeta, kuma suna waya akai akai.
Dukda bayanin da yayi saida aka zazzage shi tas kuma aka bashi daurin shekara ɗaya da rabi a gidan yari.
Shiru akayi sabida anzo wajen gwaskar watau Anisa. Su Naufal basu ce komai ba, shi ko Khattab wasu hawaye suka taru masa cikin ido. Tabbas yasan Anisa saboda sun haɗu a asibiti kuma suna shiri da Miemie sosai. Domin har tana cema Miemie bazata bari tayi aure ba sai tayi masters. Ita kuma Miemie tayita zumbure zumbure daga nan.
“Ke kuma Anisa fara bayanin ainihin abinda ya faru?”
“Ranka ya dade babu abinda zance saidai kuyi hakuri”
“Waye sa’anki anan... Ki fara bayani nace” IG ya zare mata ido. Kuka ta fashe dashi wanda tun dazu takeyi saita ce, “Kuyi hakuri bada gangan naso na kashe ta ba, dama naso na firgitata ne amma saita kamani da dambe wai bazata bani Pha’eexah ba”
“Ba abinda muka tambaya ba kenan, daga farko zaki fara bayani”
Shiru tayi batace komai ba, wata Yar Sanda taje ta wanketa da mari, nan take jini ya barke mata ta hanci. Yar sandar tace, “Oga Abeg give me 5mins make i handle dis idiot”
Wani Dan sanda daban ya nufota tareda hamɓarinta, sai kuma ya shaketa kamar zai cire mata rai. Bata ma iya ihu saboda azaba, hawaye kawai takeyi. Da hannu tayi alama ya daina zatayi magana. Yanka mata mari yayi guda biyu tukun saiya sake ta. Kallon dayan yar sandan yayi kana yace, “see how it is done”
Dariya tayi saita ce, “you try small” kallon Anisa tayi dake zaune a kasa, harara ta watsa mata saita mike da sauri. Cikin kuka ta soma magana.
“Banyi niyyar cutar da Fadeela ba, kamar Kanwata na dauketa amma kafin taga Pha’eexah na rigata. A hannuna ta fito. Nan take soyayyarta ya shiga raina. Bana wani tunani sai nata”
“Toh dama nayi ma mijina magana zanyi adopting amma ban samu ba, shine nace bari na tafi da Pha’eexah garin nan babu wanda ya sani. Toh wata mata makwabciyar mu nake ba kudi ta kira a matsayin mahaifiyar Pha’eexah”
“Shikuma Aysar nace masa watace tayi cikin shege kuma batada wadata yasa ta bani ita, sai muka ce zamu rinka kiranta Ihsaan.”
“Saidai kuma Miemie tana bani matsala, koda yaushe tana tareda ita, har labari naji tare ma suke kwana, kwata kwata bata bari ta huta suna tare” daga nan sai Anty Anisa ta fara magana cikin faɗa faɗa tana zare ido kamar yar daba.
“Shine kawai nace zanyi maganinta, banyi niyyar kashe ta ba saboda ban iya kisa ba, kawai naso nayi mata shegan dukane kuma naɗan karya mata wani sashe na jikinta”
Salati kowa keyi saboda idanun Anisa bashida maraba da yan ta’adda. Itama magana takeyi tana zare ido kamar ba mutumiyar kirki mai shakenken murya da suka sani ba.
“To sai nayi gurizin sledgehammer daga kasuwa abina, na fada ma Deela zan bar gari saboda bana so a zargeni. Naji dadi da Amaryar Naufal tazo sai hankali Fadeela ta fita daga kaina”
“Sun fita zasu rakata sai naga Miemie zaune da Pha’eexah kamar yarta, shine na sidada na shiga anan muka soma kokawa. Nayi mata alkawari idan bata matsa min zan kwada mata amma taki”
“Shine na auna mata, amma ba akai naso auna mata ba. Tsautsayi ne wannan. Ina ganin yadda jini ya fara fita daga kanta. Tana rokona nayi hakuri na taimaketa, amma lokacin bana jin kira na kyaleta bansan ko ta mutu ba”
“Wajen cradle din Pha’eexah naje, kyakkyawa mai shiga rai. Nan take na dauke Diyata na goya a baya. Sai kuma nayi tunanin idan forensic suka shigo zasu ga prints dina a wajen. Saina goge inda na taba, cradle, jikin Miemie etc. Saina fasa turare tareda kyasta ashana”
“Daga nan saina rufe kofa na tafi da key” kuka ta fashe dashi saita durkusa kasa. “Dan Allah karku rabani da Ihsaan dina, itace farin cikina. I deserve to be a mother, please kada ku raba NI DA DIYATA... Bani na haifeta ba but she is mine”
Naufal ne yaje ya wanketa da mari, “Bakida hankali, Allah ya isa tsakanin mu dake bazamu taba yafe maki ba. Kuma Allah saiya binma Miemie hakkinta.... Shashasha muguwa azzaluma”
Saiya dauki Pha’eexah amma taki sakewa dashi, kuka ta fashe dashi saboda bata san shi ba. Kallon Anisa takeyi tana mika mata hannu alamar tazo ta dauketa. Dariya Anisa tayi sosai saita ce, “Kuna ganin kun raba Ni Da Diyata amma abinda baku sani ba shine bazata sake daku ba saboda ni ta sani, kuma sai kun shiga kuncin da kuka saka ni”
Kallonta ake yi saboda kamar tanada tabun hankali, if not ga iyayen yarinya amma tana kiranta Diyarta. Grand kadi ne yanke mata life in prison, abinda yasa yayi haka bai bata ɗaurin rai da rai ba saboda idan akayi mata wannan nan take zaa wanke mata laifinta wajen Allah, amma idan aka bata wahala a duniya kuma taje lahira ta hadu da Mahaliccinta.
An kuma barta a Prison din Abia saboda koba komai kabilu zasu ci ubanta sosai, shikuma Aysar Bauchi aka mayar dashi. Nan take yayi ma Anisa Allah ya isa tareda saki uku kyawawa.
********
Ita ko Fadeela Naufal na gaya mata anga Pha’eexah gatama a hannu sa, kukanta taji ta waya, abin yayi mata ciwo amma tasan idan suka ba yarinyar lokaci zata saba dasu itama.
Tun daga waya Naufal ya soma ma Fadeela maganar komawa, “Baby we have been through alot, kawai ina tunanin ki dawo dakinki mu raina Pha’eexah tare please”
“Okay in sha Allah” dama itama abinda suka gama magana da Anty Saudah kenan. Yanzu an saka one week saita koma.
Sun dawo garin Bauchi kowa sai murna yakeyi, saidai kana ganin Pha’eexah kasan tana jin dadi saboda jikinta yayi fluffy yayi kyau. Deela bata damuba da Pha’eexah bata sake da ita ba, tasan cewa komai lokaci ne. Yarinyar tafi sakewa da Mommyn Deela, ita ke bata abinci da goyata.
Shikuma Naufal yaje Chuchu Stores ta ɓangaren furnitures yace suzo su canza ma Deela kayan ɗakinta duka. Komai aka canza saidai the same colour ne.
Yasmeenah ta shiga tashin hankali sosai saboda yanda Naufal yake rawar kai anga Pha’eexah gashi kuma Fadeela zata dawo. Tunaninta daya, saboda bazata iya zamada kishiya ba wallahi musamman yanda ta saba wataya wa ita kadai.
Dole ta nema yanda zata ruguza abin as soon as possible.
#NiDaDiyata
*Kawayena ban mance daku ba, soyayyarku yana cikin raina. Nana Haruna, Xobeaderh, Khadija Tawan, Xee Harun, Aisha Kirya, Maman Jawahir, Hadiza Pate, Rabie Saeed, Faiza Adamawa and of course not forgetting Maman Eemad*
#AinauMardiyah
[2/3 22:59] DIMPLES: ©Exquisite Online Writers
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
💦 Ni Da Diyata 💦
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Written by DIMPLΣS
Wattpad @Aynarh_dimples
💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦
✨✨✨Page 40 ✨✨✨
Season Finale
********
It was narrated from Abu Bakr Siddiq that he said to the Messenger of Allah (saas): "Teach me a supplication which I can say during my prayer." He said: "Say: Allahumma inni zalamtu nafsi zulman kathiran wa la yaghfirudh-dhunub illa Anta, faghfirli maghfiratan min 'indika warhamni, innaka Antal-Ghafurur-Rahim (O Allah, I have wronged myself greatly and no one forgives sins but You, so grant me forgiveness from You and have mercy on me, for You are the Oft-Forgiving, Most Merciful)."
*********
Yanzu saura kwana biyu Deela ta dawo gidan aurenta, babu irin shirin da ba’a yi mata ba kai zaka zata yanzu zatayi auren fari.
An kaita wani Saloon mai suna Loobnerh spa and make over. Anan aka gyara mata gashinta, k’umba, dilke da kuma kunshi. Tayi kyau tayi fresh sosai saboda harda Snail and charcoal spa anyi mata.
Sai sheki takeyi itama tana feeling kanta, Anty Saudah ta saka aka daka mata su kuka, yaji, kuɓewa busarsa sannan ta saka aka nika mata su garin danwake da kuma gero.
An siyo mata kayan cefane dayawa wanda zatayi stocking a fridge da zai dade mata. Komai chas ana jiran kawai ranar komawanta watau Friday yayi ne kawai.
Ita kuma Abla da Khattab shakuwa ne sosai ya kullu ya tsakanin su. Ta sake mashi sosai though shi baya ganin haka amma yana mata uzuri saboda hayaniya da surutu ba yanayinta bane.
Mommyn shi tazo tayi ma Fadeela murna kuma daga nan taga Abla, ta yaba sosai da zabin dayayi. Fatan Allah ya kara daidaita tsakanin su takeyi saboda ita yanzu ta samu sirika.
Shima Khattab yana jiran a dan kwana biyu ne saboda yayi ma Daddyn sa maganar zuwa gaisuwa wajen su Abba.
Yasmeenah hankali a tashe ta kira Laila ta fada mata abinda yake faruwa. Laila tace mata ta kwantar da hankalinta itama ai zata haihu kuma zaiyi rawar kai akanta .
Anan Yasmeenah take fayyace mata cewa ta kusan wata uku tana shan contraceptives. Salati Laila tayi tana fada mata ta cuce kanta gwara ta daina. Fada ta hauta dashi tana mata mita akan wani iskanci ne da aurenta batayi haihuwar fari ba zata sha abin.
Besides bata lura Naufal is a Family man bane, tun wuri gwara ta daina kafin Fadeela ta kwace Naufal gaba daya. Nan tayi tunanin zuwa asibiti ta duba lafiyar mahaifanta taji ko zata iya daukar ciki.
Washe gari ta shirya ta tafi asibiti akayi mata test wanda zata karɓa gobe. Dama bawai tana tambayar Naufal bane idan zata fita. Daga nan saita biya gidansu Lubna ta dauke ta suka wace Saloon ayi mata makeover kafin kishiyarta ta raina ta.
Gyaran gashi tayi dasu kunshi, daga nan ta wuce boutique ta siya English wears masu yawa saboda tana so tayita ma Deela feleke sosai.
Ita tasan cewa Fadeela batasan yadda ake saka irin kayan ba, ta tabbata koda yaushe tana cikin manya manya kaya marasa shape.
Koda ta dawo bata girka masa abinci ba wai tana fushi dashi, shima bai damu ba saboda kwata kwata gobene Deela zata dawo. Tea and bread yasha ya kwanta abin shi.
Kiran Fadeela yayi suka sha hirar soyayya kafin suka kwanta, yanzu Pha’eexah ta sake dasu ba kamar da ba, sun siyan mata kayan wasa masu yawa saboda ta samu ta saki jikinta.
Next day around 9:30 am....
Yasmeenah ne ke zaune a gaban Dr tana jiran ya kawo mata results ɗinta. Kallonta yakeyi ya kasa gaya mata sakamakon ta.
“Malama Yasmeenah, kinada aure ne?”
“Eh Doctor”
“Yaranki nawa?”
“Banida shi Doctor”
“Toh meya kaiki shan maganin hana haihuwa, koko mijinki ne yace kiyi haka?”
“Lafia Doctor kake min bincike haka? A ina aka taɓa haka? Mallam dalla bani results dina in wuce... Aikin banza aikin hofi daga zuwa asibiti sai kuma akace na gaya maka sirrina” kallonta yayi cikin mamaki kana ya mike mata results ɗinta.
Fizgewa tayi ta balla masa harara kana ta mike tsaye, ta soma tafiya harta kai kofa sai yace, “Results dinki yana reading bazaki iya haihuwa ba saboda mahaifarki ya lalace sanadiyar contraceptives kala kala da kike ta dirka”
“Karya kake munafuki bokan bature... Mts” tace saita wuce. Ta tafi motarta ta shiga saita kara dubawa. Nan take ta rude tareda fashewa da kuka.
Ta dauki wayarta zata kira Naufal saita tuna sanda tayi abinta bai sani ba, lambar Huzaifa ta kira, bugu daya ya dauka. Kuka ta fashe mashi dashi nan take ya rude. Ce mata yayi ta tafi gida gashinan zuwa ya sameta.
Shikuma yau ya dauki alwashin kashe k’ishinsa a jikinta, ya lura ta raina masa wayo ta mayar katako. Amma yau zai bata mamaki, duk wannan rawar da take keyi gabansa tareda saka bom short zaiyi maganinta.
Ya dauki alwashin saiya gwangwaje a jikinta son ran shi, idan yaso ta gaya ma Naufal ya sakota daga nan yama aureta baki daya.
Dama leggings da yar top ke jikinta saita daura abaya dazata fita, yanzu ta cire tana zaune akan one seater tana kuka. Huzaifa ne ya shigo da wani smug face yana wani kallonta. Gashi dama tayi gyaran jiki sai sheki takeyi, nan take ya kara jinta cikin birinin ransa.
Nan yaje dab da ita ya rike mata hannu yana murzawa a hankali. Magana ya soma da muryansa na yaudara, “Toh menene dan bazaki haihu ba? Ai ba kowane namiji ke son yara ba, besides idan yana sanki bazai dameshi ba”
Da jajayen idanta ta watsa mashi harara, wata rana idan yayi magana saika zata mahaukaci ne. “Kamar ya ba kowane namiji keson yara bah? Bora kake so na zama akan bana haihuwa?”
“Ni kinga idan ina son mace zan so komai akanta”
“Look mallam bana san shiririta anan, haba ina serious talk kana kawo min zancen ka... Aurenka zanyi da kake gaya min haka!”
“Sorry my dear, ba haka nake nufi ba, come close and give big bro a hug.... Everything will be alright in sha Allah”
Tashi yayi yana kokarin jawota jikinsa, ita kuma saita noke, “C’mon lil sis im just trying to cheer you up”
Babu wani gardama ta yarda, ita tasan bata san shi kuma babu yadda zata kashe aurenta akan shi. Besides bayau suka saba hugging ba a matsayin au na yan uwa.
Tana makale a jikinsa tana kuka a hankali, kirjinsa ne ya soma bugu da karfi, gaskiya soyayyarta yayi zurfi cikin ransa. Ya yanke shawara akan ya samu rabonsa wajenta kafin ya mutu.
Shikuma Naufal yaje ya dauko Family ɗinsa, Abba ya zaunar dasu yayi masu nasiha sosai akan aure. Daga nan sai suka wuce gidansu Deela suma su Grand kadi suyi masu nasu, shi masu albarka akayi sai Mommy tace bata yafe ma Fadeela ba idan ta bar gidanta da sunar yaji.
Murna fal zuciyar Naufal, bai taba daukinta ba kamar yau, baya ma behaving kamar yanada wani mata a duniya. Gashi soyayyar Pha’eexah sai kara dasuwa yake cikin ranshi.
Yana tuki hannunsa daya yana makele dana Fadeela kamar wani zai kwace mashi ita. Anan ne Deela tayi masa maganar Abla da Khattab.
Mara misaltuwa ya nuna saboda tuntuni Khattab ya nuna shi mutumin arziki ne kuma he will be honored ace shi sirikinsa ne.
Sun isa gidansu sai yaga motar Huzaifa, tsaki yayi cikin ranshi tareda faɗin, ‘Aikin kenan’
Shikuma Huzaifa a hankali ya soma shafa Meenah, yanayi kamar yana petting ɗinta ne amma tsantsan iskanci ke ranshi.
Daga nan saiya kaima bakinta chapka da nashi, tureshi tayi tana mashi kallon mamaki, “Meye haka yaya?”
“Nifa munafunci ne bana so, kamar ya meye haka... Baki lura da abinda ke shirin faruwa bane”
“Look Huzaifa bana san iskanci, dama manufan ka kenan koh? Oya maza maza ka barmin gidana kafin ranka ya baci”
“Dama zan tafi amma saina yi abinda ya kawo ni wajen ki, dayake kin raina ni koh.... Kiyi ta seducing dina kamar bakisan me kike yi ba. Ke jahilar ina ne? Bamu hada uwa da uba dake ba amma ki rinka abinda kika dama a gabana all in the name of civilization.... Well okay dear nima im going to be civil on your body”
Nan ya finciko ta ya matse da jikinsa, tana kokarin tureshi amma ta kasa. Kissing dinta yayi kokarin yi saita yanka mashi cizo. “La la la la dan ubanki ni kika ciza? Yau sai na nuna maki baki iya bariki ba”
Nan ya fige rigarta saida ya yaga tas, jikinta ya bayyana ita kuma ta fashe da kuka tana kokarin rufe kirjinta da hannayenta amma duk a banza. Wani ja’irin dariya yayi saiya fito da wani kwaya daga aljihunsa ya saka a baki ya haɗiye.
Nan idansa ya canza kala babu alamar wasa a tareda shi, tana kokarin dambe dashi ya yanka mata mari, amma bata hakura ba sabida bazata iya barin wani wawa yaci amanar Naufal ba.
Nan ta cigaba da kici kici dashi amma kwayar daya sha ya soma aiki a jikinsa, kuka takeyi tana naiman taimako amma babu wanda zai taimaka mata. Tsine mashi takeyi da iyayensa da kakaninsa amma duk a banza.
Yakushi takeyi amma ina, daya ga tana bata mashi lokaci saiya nakada mata duka wanda ya sakata likis ko numfashi zafi yake mata idan tayi. Ta zama abin tausayi sosai saidai kuma ita ta jawo ma kanta.
Nan ya fashe da dariya, baiyi wata wata ba ya keta mata haddi a cikin falonta, hawaye kawai ke gangarowa daya bayan daya, sukuma su Fadeela sun shiga falo saiga Huzaifa yana kokarin mayar da kayansa.
Salati suka somayi saboda kowa yasan abinda ya faru, nan gaban Huzaifa ya faɗi. Gadan gadan Naufal ya nufa inda yake ya soma auna mashi naushi.
Dukansa yakeyi kamar Muhammad Ali wani shahararen boxer a Amerika. “Dan ubanka da matana zaka yi iskanci a cikin falona dan bakada hankali” ya farfasa mashi baki da hanci duk ya kumbura mashi fuska.
Nan yayi mashi las kana ya ingiza shi waje da ragowar kayansa a hannusa. Ita Deela nadaga gefe rike da yarta suna kuka. Dama ita ta fara sai Pha’eexah ta chapka.
Ita kuma Meenah wanda zuciyar ta yana mata radadi, kawai mamakin cin amanar da Huzaifa yayi mata take. Maganar taji daga sama kamar saukar mashi.
“Ba iskanci ba koh? Jeki dan ubanki nayi maki saki uku. Sai ki goma gidanku kuci gaba” nan ta rinka kokarin tashi tana so ta roke Naufal amma ya fizge hannun Deela sunyi hanyar upstairs.
“Mine karkayi min haka, na ranste da Allah raping dina yayi”
“Kanki kika raina amma bani ba, kuma ke kika san wannan saboda ni na riga sake ki.... Kuma Allah ya isa cin amata da kikayi”
Wajen 9pm.....
Naufal yana kwance akan gado, ya gama gaya masu Abba abinda ya faru da Yasmeenah. Kuma ya kira Abban Huzaifa ya gaya mashi komai.
Yaba Naufal hakuri sosai tareda mashi fatan alheri, shi karin kanshi shedancin yaransa ya fara kaishi bango. Ita kuma Yasmeenah akwati daya ta dauka ta tafi gidansu ta gayama Mommy abinda ya faru kuma ta roketa taje ta bama Naufal hakuri.
Zagin ta tas tayi sannan tace mata sanda take barin Huzaifa koda yaushe cikin gidanta bayan tasan halinshi bata san da zancen ba, saboda haka yanzu ma babu ruwanta.
Duniya yayi mata zafi tana kaico da hali irin nata, tabbas Huzaifa ya cuceta kuma bazata yafe mashi ba. Sai wani karamin murya cikin ranta yace Huzaifa bai cuceta ba ita ta cuce kanta.
Fadeela tana kwance jikin mijinta tana tuna irin obstacles din dasu kayi over coming, lallai duniya akwai abubuwa kala kala.
Ko sau daya bata taɓa tunanin Anty Anisa zata iya abinda tayi ba, wai ace mutum babu tawakkali samsam cikin al’amuran sa. Kome Allah ya baka koya hanaka duk yanada kyau ka gode masa, bakasan alherin dake gaba ba. Sai kuma Yasmeenah da wani gardi a dakin aurenta. Koda yake tsautsayi babu yadda baya giftawa kuma Allah ya rabamu da irin wannan.
Shiko Naufal yana makale da matarsa da kuma yarsa, Hamdalah yakeyi yau he has his complete family with him. Wani tunani ya faɗo mashi cikin rai. Tuntuni dayake kiran Deela bad luck but asalin Bad luck din itace Meenah.
Na farko yana haduwa da ita aurenshi ya lalace da Deela, a lokacin ya koya karya kamar tubabben sarki.
Na biyu yarsa ta bace bayan haduwarsu, na uku kuma ga mutuwar Miemie. Sannan kuma anyi kwartanci a falonsa.
Yasan chamfi haramun ne but Yasmeenah is really a bad luck. Yanzu babu abinda zaice face Allah ya raka taki gona.
Six months later......
Rayuwar Meenah yazama darasi ga mutane dayawa, ko ina taje zunɗenta akeyi. Tayi kuka harta gode Allah. Gashi duk samarinta na da sun gudu suna tsoron kada su aureta ta rinka kawo masu kwarto cikin daki.
Shidai Huzaifa yace idan tanaso zai aureta, da farko bataso ba asalima restraining order tayi placing tsakanin su. Amma daga baya tayi ma kanta karatun ta natsu, yanzu batada mahaifa so gwara ta rufa ma kanta asiri tunda yace yaji ya gani.
Fadeela kuwa ana kaiwa da komawa saboda yaune bikin Abla da Khattab. Kowa ya taru ana masu fatan alheri.
Khattab burinsa ya cika saboda zai aure Haakensa mai haska mashi zuciya. Itama Abla ana rawar kai za a zama amarya. Gaba daya kowa bakinsa kamar gonar auduga domin murna.
Baby phaexah an fara tafiya so cute kuma yanzu ta saba da iyayenta na asali. Naufal kuma an murmure sai sheki yakeyi saboda Deela tana kula dashi yadda ya dace.
Komai nasu gwanin ban sha’awa kuma suna fahimtar junansu yadda ya dace. Ko sunyi fada basa kwantawa da junansu a cikin rai.
Ya bude mata katon art studio inda ake exhibiting paintings kuma suna tallafa ma young talented artist. Gashi kuma su Mr Sutter suna kokarin bashi head din branch dinsu ya wakilci Nigeria gaba daya.
Komai yana zuwa masu da sauki tabarakta masha Allah. Idan Deela ta zauna ta tuna abinda ya faru da ita a baya babu abinda take jin dadi sai irin hakuri da mayar ma Allah komai da tayi. Tasan cewa hakuri yanada fa’ida a musulunci kuma ko Hausawa sunce mai hakuri zai dafa dutse ya kuma sha romonta.
Gashi yanzu tana ganin fa’idan hak’urin sosai. An daura aure ankai Abla Gidanta a GRA bashida nisa da gidan iyayen Deela.
Naufal ya kira Deela domin yaji Lafianta, “Hello baby nayi missing dinki fah, wannan bikin ya kware ni dayawa”
“Other half karka damu gamu nan zuwa”
“gaku nan zuwa dawa?”
“NI DA DIYATA mana, who else?”
“Iyye masu yarinya, please ya kamata ayi mata kani koh babyna?” dariya Fadeela tayi sosai sai tace “Soon.... In sha Allah very Soon”
“Okay babyna saikun zo, dont forget to remember i love you so much kinji koh?”
“I love you too, sai mun iso”
ALHAMDULILLAH RABBIL ALAMIN, anan na kawo karshen wannan littafi mai suna Ni Da Diyata. Allah ka bamu ikon amfani da darusan ciki.... Amin
Wannan littafi na sadakar dashi zuwa kawata Xaynarb B Idreez (Maman Eemaad), ke ce Ni da diyata saboda without you babu shi. Allah ya albarkace Muhammad Eemad... Amin.
Sannan best friend dina Nanah Fatima, Allah ya albarkace kawancen dake tsakanin mu. Ga yabon girma ga sauran Kawayena kamar su Xee Haruna,Aisha Sulaiman, Xobeaderh, Xeemee, Khadija, Aisha Kirya, Hadiza Pate, Rabie Saeed thanks from me to you.
Idan kuna tunanin kunsan DIMPLΣS kuma bakusan cewa inada kannen kamar su Ummiejafar(Pha’eexah) da kuma UmmieKhaleel (Aysha) then you have no idea of who i am. I don’t know the correct word to explain how amazing you cuties are. I really appreciate everything you do towards me...Allah kuma ya albarkace rubutun da kukeyi ya kuma kareku daga sharrin mashanranta... Thanks so much cuties.
Ban mance daku ba, Ummie Rilwan(Fatima), Sumy gaya, Jidda, Asmeebae, Red Butterfly etc.
Kuna raina writers kamarsu Lubna Sufyan, ZeeNaseer, Sadnaf, Cute Zarah, Lemmcy, Fulani, Rash Kardam, Hamagee, Fiyya Galadanchi, Fatty Azland, Xoubie, Mjay, Hussaina Ubandiya, Momyn Sultan, Badiya Yusuf, Zainnundeen, Kdeey, Ayusher, Natty Gal, CwtJidda, Mmn Shukra, Ummul khairi etc.
Fatan Alheri ga wattpad fans dina, thanks so much cupcakes, i love you guys so much, you’re comments was superb and it kept me going... You guys made Ni Da Diyata the number one story under Spiritual for weeks #OneLoveSweethearts
Facebook groups kamarsu Ummu Maryaem Novels and Deyart Yusuf Novels.
WhatsApp groups kuma kamar DIMPLΣS, Ummiejafar Novels, Xarah Bukar Novels 1, Hamagee Novels, Marubuci, Matan Arewa, kema ki Girka, Hausa Novels, Rash Kardam Novels, Gidan Buki etc.... Thanks so much.
Naku daban ne, Exquisite Online Writers saboda daku nake tinkaho, Allah ya sake hada kanmu kuma ya karemu daga sharrin mashanranta.
Kada ku mance you can only reach me on Wattpad @Aynarh_dimples for any comments or recommendations. Also check my new book dat will be posted there titled ‘Yan Gidan Gwaiba. Da fatan shima za’a amfana dashi.
Subhanakallahuma wa bi hamdika, Ashadu Allah ilaha ilallah, Astagarifullah wa atubu ilayhi.
Ainau Mardiya also known as yarinya Mai DIMPLΣS