A daren ranan Abuturrab ya ishi Noor ta fadi sunan da take son a sa ma babies din tace ita bata sani ba, ya langwabar da kai yace "You mean baki da sunan da kike so a ran ki?" Nan ma ta girgixa masa kai, murmushi yyi yace "Toh shknn" gun Maminsa ya tafi yyi shawara da ita sunan da yake son rada ma babies din tace Allah ya raya su amma ya samu Abbansa dai tukun, ko da ya sanar da Abbansa xai yi masa takwara girgixa kai yyi yace "A'a na yafe" Abuturrab yyi shiru yana kallonsa, can Abba yace "Yea sbda mahaifinta hakan baxai yiwu ba, ka rada masu wani sunan daban, there is next time" Daga haka Abba ya mike ya dau wayarsa dake ring ya nufi kofa, Abuturrab bai iya yace komai ba don shi ma da farko yyi wnn tunanin bai mata adalci ba idan yasa nasa mahaifin, an dai san baxai kama ya sa ma d'ansa David ba, Washegari da ya kama friday aka rada ma twins sunansu, Hassan ya ci sunan Ahmad d'an Umma, Hussain kuma aka rada masa Abbakar Sadeeq, ya ci sunan Sadeeq, don wa ennan mutanen ne Abuturrab bai jin xai iya mance su a rayuwa, duk da ba wai Ahmad ya taka wani rawa bane amma tunda har shi ya kuma hada sa da Noor dinsa baxai mance sa ba, wannan suna dai ya samu halartar mutane da dama har da abokan col, har hakan ya dinga ba Hajiya Mariya da Mami mamaki, idan ka ga Noor a wnn rana sai kayi xaton amarya ce tsabar kyau da haduwar da tayi, sosai Mami suka kashe kudi gun ganin sun fito da ita, irin yanda mutane daga nisa da kusa suka cika gidan Col bbu masaka tsinke abun ba a magana, da gani kasan Abuturrab ba karamin d'an gata bane ko daga kan cimar da aka yi domin sunan, ni kam nace to da an gaya maku baban nawa na wasa ne ko don kun gansa a banxa yana wantagalili a gombe da maraba? to dai tillon d'a ne ga Colonel guda, sake baki da idanuwa nayi ganin members na Khaleesat Haiydar Novels su Maman Shakur, Ummu ilham, chamo, Anty Fyn, Ashmaad, Fiddo s dangi, Mimic, Fa'ee, Zuhoorah, Ummu Zainab, Ummu Amana, Humainah, Jamila.... kaiiii ni kam ina xan iya lissafo su... zaxxaune na hangosu kan kujeru ko wannensu ya cakare cikin ankon da suka yi na wani ubansun lace kalan sea green sai head jaa, sai daukar ido suke, ga abinci kala kala an ajiye ma kowa a kan table din gabansa daga gefensu kuma tulin gifts din yan biyu da suka yi wrapping a wrapping paper iri daya ne, Hajiya Mariya da Anty Maryam suka dinga bi suna gaisawa da su, ni ko na rike baki nace "Ohhhh wa yaga gayyar sodi😜" don ni dai nasan banda phatiemarkh bbu warce na gayyata wnn sunan, ae fa ban sake bakin da na rike ba na hango wata tawagar guda na 'yan haske writers💡su ma suna xaxxaune nace "Toh fahhh" su Ummy Shatu ne, Fatyma Zahrah, sweet sis Asmy B Aliyu, Billy Galadanci, Mom Ihsaan, faxy, Safiyya Huguma, Ayusher, feedohm.... kai gaskiya suna da yawa, su ma sun cakare cikin ankonsu na holland da suka yi ko wannensu sanye da siririn glass na 'yan gayu su ma ga uban gifts dinsu ajiye a gefe, Ummi sai bi take tana gaisawa da su, cannnn cikin jama'ar asali da aka gayyata aka basu pass din shigowa gate din Colonel na hango Iqram Mujaheed tana ta rawan kan kwaso drinks da ruwa tana raba ma mutane uwa an sa ta, ita a dole k'anwar khaleesat Haiydar bakin nn yaki rufuwa, na kyabe baki nace wa yaga karere🙄, kai na bai gama daurewa ba sai da nasamu lbrin ae fa akwai wani canopy da aka kafa a waje na gayun😎 Khlst Hydr Nvls su ma sun sha anko cikin shadda fari tas irin na Abuturrab da Sadeeq dake bi yana gaisawa da su, nace cabdi abun na yi ne oo.... Noor kam duk wnn budurin da ake bata da walwala, da ta tuna Anty Maryam da yaranta kadai ne nata a gidan sai hawaye ya cika idonta, ko ba a fadi ma Anty Maryam ba tasan me ke damun yar tata, ita ma duk sai ta ji wani iri. A can gidan Mr David kuwa yau kwana biyu knn Rachael ke fama da ciwon kan dake sa ta fita hayyacinta idan ta fara shi, duk asibitin da xa su bbu sauki sai don kansa yake tafiya, da yake ta kwana biyu bata yi ciwon ba sai take jin sa kamar sabo, abincin da mai aikin gidan ta girka Mr David ya kai mata har daki, tana durkushe bakin gado Bible a kusa da ita, ta rataye rosary a wuya, ya ajiye xai fita, cikin sanyin murya tace "Yanxu da Samantha tana kusa dani ciwon nn baxae kada ni haka ba, for heaven sake sai yaushe 'ya ta zata dawo garen, yaushe ne wnn rana da xan ga samantha" tana magana ne zar tausayi idon nn cike da kwalla, ya dawo dakin ya xauna jin tausayin matar tasa, glass din idonsa ya cire yace "Ke ce Rachael fadan ki ya fi karfin ki, nasan Samantha na son xuwa gun ki amma tana tsoro" Kallonsa take tace "Ya baxa ta ji tsoro ba bayan ta cuce ni, haka kawai ta mayar da ni barren din karfi da yaji kamar ban taba haihuwa ba, yanxu sai dai in ga wasu da 'ya ya ni bani da, ta fiffita namiji a kai na" tana kai wa nn ta fashe da kuka sosai, shiru yyi yana kallonta, can yace "Yanxu da xa ki ga samantha tsakanin ki da Allah ya xa ki yi Rachael" mikewa tayi tana share hawayen idonta tace "I know it, nasani dama, David ka san inda Samantha take shi yasa baka damu ba, nasan kai da kanuwarka kun san komai, kun san inda 'ya ta take, munafurtata kawai kuke" ta fashe da matsanancin kuka tace "Me nayi maku David da xa ku bar ni da kadaicin 'ya ta haka, ita ma fa Maryam Uwa ce, idan yar ta tayi mata haka xata ji dadi, tsawon lkcn nn kun san inda ya ta take ku ka bar ni ina yawo duniya nemanta, what have i done to deserve dis" Girgixa kai yyi yace "Haukan ki ne yafi karfin ki shi yasa bbu wanda ya damu ya nuna maki yasan inda take, ina ce kwanaki cewa kika yi kasheta xaki yi da xata shigo hannun ki, toh ko nasan inda 'ya ta take wnn furucin naki xai sa in fito in gaya maki" a fusace tace "Kai baka san baraxana ba david, kaza ce da xan kasheta, ko wani ya dau min cikinta yyi wahala ya haifar min ita da xan kasheta" yace "Better, Samantha tana nn lfya kuma ita ma tana kewar ki tare da tagawayenta maxa" rikosa tayi a rikice tace "A ina take David?" Yace "Tana nn lafiya dai" ta fashe da kuka sosai tace "Amma kuma baxan ji inda take ba koh, sbda ni ba xuciya ce a kirjina ba koh, sbda ba ni na haifeta ba koh," xaunar da ita yyi gefen gado yace "You make me a promise that you will act smartly idan na kai ki inda samantha take, ki min alkawarin baxa ki yi abinda bai dace ba a can...." Share hawayen idonta ta shiga yi da sauri tace "Na ji David" yace "A'a ba kin ji ba, cewa nayi ki min alkawari" tace "Nayi alkawarin" yace "Good, ki ci abinci sai ki shirya in kai ki inda take" mikewa tayi da sauri tace "Am full, kuma a shirye nake dankwali kawai xan daura" duk ynda ya so ta ci abinci kin ci tayi, yace to ta jira a idar da magrib, ana idarwa kuwa suka bar gidan a motarsa suka taho gidansu Abuturrab, kallon gidan kawai take da shock, yace "Kin dai yi alkawari Rachael" daga haka ya fito ta bi bayansa da sauri, number Maryam ya kira yace mata yana waje ta fito, ba a dau lkci ba sai ga ta, ba karamin kidimewa tayi ba ganin Rachael, ita ko tana tsaye idon nn cike da hawaye, Maryam ta kasa cewa komai duk jikinta yyi sanyi, Mr David yace "Ki shiga da ita ciki ta ga Samantha" a hankali tace "Toh" daga haka ta shiga ciki Rachael ta bi bayanta, Mr David ya koma cikin motarsa, suna shigowa parlor Hajiya Mariya dake ta gyare gyare ta dinga kallonsu kuma ko ba a gaya mata ba ta san wacece don ta taba ganinta, xaunawa Rachael tayi tana kare ma parlon kallo, Anty Maryam na kallon Hajiya Mariya tace "Hajiya mahaifiyar Samha kenan" Hajiya Mariya tayi karfin halin ce mata sannu da xuwa, Anty Maryam kuma ta wuce sama, Abuturrab ne ya shigo parlorn tare da Sadeeq, still yyi yana kallon Rachael da mamaki, ita ko kallo daya tayi masa ta dauke kai, Sadeeq kansa sai da yayi jim ganinta, da kyar Abuturrab ya karasa parlorn ya xauna yace "Ina yini?" bata kallesa ba bare ta amsa gaisuwarsa, ya kalli Sadeeq da ya wuce sama abun sa, can ya mike ya bi bayansa, Noor da har ta fara baccin gajiya ta saka Hijab suka fito tare da Anty Maryam da ta dau Ahmad, Ilham kuma ta dau Abbakar, bata san dai da wanda xa su gaisa ba amma ta fara gajiya da fitowa, a corridor suka hadu da Abuturrab, ya gaida Anty Maryam tayi masa sannu da xuwa, kallon Noor da ta ki dago kanta yyi sai ma wucewa gaba da tayi ta bar su a gun.
*Haske writers asso*
Mumy's, Anty's, Uncles.... Lil Haiydar is grateful for the wishes, Allah bar xumunci.💝
💫 *Noorul Huda*💫
By khaleesat Haiydar📚✍🏻
95.....
Anty Maryam tace "Did you greet her? I mean her mum?" Abuturrab ya gyada kai yace "Na gaishe ta" bata kuma cewa komai ba ta bi bayan Noor da har ta sauka kasa, a hankali Noor ke tafiya tana kallon wacce ke xaune kan kujera tayi backing dinta, haka kawai gabanta ya shiga faduwa sosai, can ta daga kai ta kalli Hajiya Mariya dake tsaye parlon, sunkuyar da kai tayi ta karaso cikin parlon, kasa motsi tayi inda take tsaye bayan sun yi ido hudu da mum dinta, ta rufe bakinta kar ta saki ihun dake shirin fitowa bakinta, lkci daya hawaye ya cika idonta, ta karasa da gudu ta fada jikinta ta rungumeta ta fashe da kuka sosai cikin rawar murya tace "Mumy..." Rachael dake ta mata wani kallo ta turata gefe tace "Ja can munafuka duk tsawon lkcn nn baki san inda nake bane xa ki fashe da kukan munafurci, ni kika so kashewa ko? Toh God of Abraham ya fi ki, ina nn ban mutu ba" sai kuma ta fashe da kuka sosai tace "Yanxu Rebecca namiji kika xaba a kai na koh? Kika dau namiji uba sbda hankalin ki ragagge ne koh Samantha?" Noor ta kuma fashewa da kuka sosai tace "Forgive me mum, don Allah ki yafe min" buga bakinta tayi tace "Shut up, in kin ga na yafe maki to Jehovah ma ya yafe maki ne, don ba ni kadai kika yaudara ba har shi" Anty Maryam dake tsaye kansu dai bata ce komai ba, a hankali ta jiye mata Ahmad dake hannunta a cinyarta, Rachael ta hadiya sauran fitinar dake shirin fitowa bakinta tana kallon yaron, Ilham ma dake tsaye gefe sai kallon ikon Allah take ta karaso ta ajiye mata Abbakar shi ma a jikinta, Rachael dai sai kallon kyawawan yaran take, tuni dama Maryam ta bar parlon sai Hajiya Mariya dake tsaye da ilham, can Rachael ta goge hawayen idonta tace "Eh toh da yake duk abinda jehovah ya rubuta sai ya faru, wnn abun da ya same ni rubutattce ne, kuma ni na gode ma Allah da na iya jure wnn bak'ar faith din" Daukar Ahmad tayi ta rufe ido tace "You are blessed in jesus name...." Hajiya Mariya ta yo waje da ido haka ma Ilham, ta ajiye yaron ta dau dan uwansa shi ma ta fadi masa haka, snn ta fara masu addu'a idonta rufe dai dai shigowar Col parlon, tsaye yyi yana kallonsu, can yyi murmushi yana gyada kai ya wuce sama, ita dai Noor na xaune gefe ta kasa dago kanta, Rachael tayi addu'a me isarta ta kare adduar da cewa "You are all covered with d blood of jesus my babies" snn ta bude idon ta hade rai tace "Tashi dauko mun kayansu mu wuce gida," Kallonta kawai Noor take ta kasa cewa komai, can ta juya a hankali kalli Hajiya Mariya dake ta kallon ikon Allah, tuni Rachael ta mike tana rike da yaran tace "Wai ba kya ji na ne" Noor kamar xata yi kuka tace "Mum...." dungurinta Rachael tayi tace "Baxa ki tashi ba sai na mare ki" Hajiya Mariya tace "Amma Madam kinga baxai yiwu su fita ba ynxu jego fa take, ina xa ku cikin sanyin nn" wani kallo ta watsa ma Hajiya Mariya tace "Sai aka ce maki a kafa muke? Wato ku kadai ne masu mota koh?" Daga haka ta kuma yi ma Noor tsawa tace "Tashi nace, ba ma sai kin dauko kaya ba ynxun nn sai david ya fita ya siyo masu" Ilham ta juya ta wuce sama don kiran Mami, Sai ga Mami da frnds dinta biyu da Ummi sun sauko parlon, Mami na kallonta tace "Ina yini" ba tare da Rachael ta kalleta ba tace "Lafiya qlau" Ae da ta sake yi ma Noor wani tsawa bata san lkcn da ta mike tsaye ba a tsorace, fuskarta a tsuke tace "Fita mu je nace ko nan din gidan uban ki ne" Frnd din Mami Hajiya Rahina dake tsaye tace "Amma kuma Madam ae gidan Uban yaran hannun ki ne" a dakile Rachael ta dinga kallonta tace "So? Idan gidan ubansu ne sai aka yi yaya? Ina ce ita ta haifesu?" Hajiya Rahina ta girgixa kai tace "A'a kmr ynda kika ce ta tashi ku tafi gidan ubanta, su ma sai ki bar su gidan ubansu" Tsaki Rachael ta ja tace "Toh baxa a bar su ba, abinda nake so ki gane a nn shine ae ba wani ya haifar mata su ba, ba uban ya haifesu ba" Hajiya Mariya tace "Amma kuma ai mijinta bai mata izinin tafiya ba naga" Rachael tace "Wani mijin, ni ban ma 'ya ta aure ba, kar wanda ya sake lakaba mata miji, duk da ma ni ynxu ba ta ita nake ba, albarkacin nonon da xata basu yasa ma ni xan tafi da ita yanxu, banda haka ni da ta bi ni da kar ta bi ni duk uwasu daya ubansu daya, yara ne dai suka xama dole in tafi da su don nawa ne, dama ance min duk 'ya yan da ban haifa ba ita xata haifar min su, ba don ita kadai Allah ya halicce ni ba," Ita dai Anty Maryam na sama tana jin hayaniyar Rachael ta kasa saukowa, ganin dai ta dage sai ta tafi da yara da Noor tayi karfin halin saukowa parlorn, da kyar tace "Sister Rachael bai kamata kice xa ki tafi da su ba, kin ga....." Wani tsawa Rachael tayi mata tace "Munafukaa, muna nn dake Allah xai mani sakayya, ba dai 'ya ta kika jefa a halaka ba har abada ni dake Maryam kuma ni ba yafewa xan yi ba, kika sake tsomo bakin ki nn kuma sai na baki mamaki, muguwa kawai" Mami dai sakin baki tayi tana kallon ikon Allah, Ummi da ta kasa cewa komai tun daxu tayi karfin halin cewa "Madam kiyi hakuri don Allah a xauna ayi magana ta fahimta" ta gefen ido Rachael ta kalleta tace "Ban san shi ba, fahimta dai koh? To ni bn san shi ba" Abba ne ya dawo parlon yace "Ku bar ta su tafi, you go with them...." Muryar Abuturrab suka ji yana saukowa daga stairs yace "Noo Abba.... they are nt going with my children" Noor ta juya tana kallonsa hawaye cike idonta, Rachael tayi wani shewa tana hararansa tace "Halan kai ka dau cikinsu ka haife su??? Ai idan kaga na fita bbu yaran nn yau toh a sume aka fitar da ni parlon nn, suman ma irin dogon nn da ban san waye a kai na ba, yau dai jikokina baxa su kwana gidan nn ba ko da ita bata yrda ta bi ni ba ta sha xaman ta, kuma daga nn church na nufa da yara a sa masu albarka kmr yanda kaga uwarsu tayi albarka har ta haife su" Mami sai kallon Abuturrab dake tahowa take, Sadeeq kam tsaye yyi sama ya rungume hannu yana kallonsu, Abuturrab ya karaso parlon ya girgixa kai yace "Sorry ni baxa ki fitar min da yara gidan nn ba, it's nt, nd wil never be possible" tana masa wani kallo tace "Then i will show you that it's very possible" Abba ya kallesa ya hade rai yace "Leave immediately now" ya girgixa kai yace "But she can't just leave with my children dad...." Wani tsawa Abba yyi masa yace "I said leave now" Rachael ta ja tsaki tana hararan Noor dake kuka sosai tace "Idan kin so ki biyo ni ko kar ki biyo ni, hakan baxae sa jikokina su yi starve ba, i will get them a better milk" daga haka ta nufi kofa tana wakan church, Sadeeq ya sakko da sauri yace "But Abba ina xata kai yaran mutane, she can't just..." Wani kallo Abba ya watsa masa shi ma yace "Leave too before i kick you out" Noor ta xube kan kujera ta fashe da kuka sosai, lumshe ido Abuturrab yyi maganganun Small mum dinsa da tayi masa da dadewa na yawo a kansa 'meye makomar kids din ka Aliyu??? kar ka manta ita xa kayi converting ba family dinta ba, sannan Kasan baxa ta taba rabuwa da family dinta ba, Aliyu keep everything aside and think reality, this is the biggest mistake you are to make in ur life' bude ido yyi ya juya a hankali yana kallon Small mum din tasa ya ga ita ma kallonsa take, Hajiya Rahina da kanta ya gama daurewa tace "A'a Col, gaskiya wnn ba magana bace ya xaka ce a bar ta ta tafi da su, kaji fa inda take cewa xata kai su ynxu wai church!" D'an murmushi yyi yace "Kin mance wanda ya k'i ji baxae k'i gani ba? Shi ya ji ya gani kuma xai iya, i just love her action, bbu kuma ynda xa' ayi a rabata da jikokinta kema kin sani, yes ta kai su duk inda xata kai su she have the right" Ummi da ranta ya gama baci tace "Noo Abban Aliyu, u re sounding Sarcastic" Col ya girgixa kai yace "Rather, i am absolutely right" daga haka ya juya ya bar parlon, wani kallon gefen ido Sadeeq ya bi sa da shi haka ma Hajiya Mariya dake ji kmr ta kwade sa, Mami kam tuni hawaye ya fara sakkowa idonta, shi dai Abuturrab ya kasa kallonta, tuni Rachael ta isa kofa xata fita suka kusa cin karo da Yakumbo da ta rafka uban sallama da kaya niki niki a kai"
*Haske writers asso*
💫 *Noorul Huda*💫
By khaleesat Haiydar📚✍🏻
96.....
Yakumbo ta dire kayan dake daure kanta tana kallon yaran hannun Rachael da ke kkrin fita kofa tace "Ke ya haka, ina xaki kai 'ya yan mutane da magariba, wani gwanannen ne baxai shigo ba sai an fitar masa da 'ya yan waje cikin sanyin nn" ko kallonta Rachael bata yi ba ta fice daga parlon, Yakumbo ta juya tana kallon su Hajiya Mariya dake tsaye parlorn tace "Wace mahaukaciya ce kuma wnn? ko dai kurma ce" Hajiya Mariya tace "Sannu da xuwa Yakumbo, ba mahaukaciya bace, xuwa tayi ta tafi da yaran wai" Yakumbo ta d'an yo waje da ido tace "Ta tafi da su? Ina xata kai su" karasowa parlon tayi tana kallon Mami da ta kasa daina hawaye ta kuma kallon Hajiya Mariya tace "Ke wai me ke faruwa, Aliyun sake gudu yyi?" Bata rufe baki ba ta gansa tsaye kansa a kasa yana rungume da hannunsa, ta tafe hannu hade da kyabe baki tace "Ikon Allah, Ka gaji da guje gujen ka dawo kenan, ae dama duk wawan da ya bar gida da kafarsa to fa da kafafuwar nn xae dawo in da rai da lafiya, ni ba dan naka naka bane da na ja maka Allah ya isa a kan wahalhalun da ka saka k'anina Aliyu, uwar ka kam dama bakin ku daya da figaggiyar kanwarta...." Daga haka ta ja tsaki tace "Na xo ne dama ayi ta ta kare ina Ahmad din..." Daga haka ta dau hanyar stairs, Rachael na fita gate Mr David ya fito daga mota da sauri yana kallonta da mamaki yace "Rachael meye haka, ina xa ki kai yaran?" Wani kallo ta jefa masa tace "Ina xan kai su kamar yaya? Ba jikokina bane" bude bayan motar tayi ta shiga, ya girgixa kai yace "Kina da hankali kuwa Rachael, kan ki daya kuwa? Ina xaki da yaran mutane" fitowa tayi daga motar tace "You're wasting my time David" daga haka ta k'ara ma sayyadarta mai ta dau hanyar gida uwa xata tashi sama, ya dafe kai yace "My God!" Yakumbo na shiga parlon Col ta gansa xaune da laptop, ya mike ganinta yana murmushi yace "Sannu da xuwa yaya" tace "Sannu Ahmad, na same ku lafiya" yace "Lafiya lau, ashe kin taho baki yi waya ba" tace "Kaga ma ni na mance wayar a gida ban da yanxu da kayi magana" xaunawa tayi tace "Ya muka ji da wannan bakar masifar, wai Aliyu ya dawo da yara, anya Ahmad baka yi masa baki ba kuwa" Col ya girgixa kai yana murmushi yace "ko daya" tace "To ita kiristar tana ina?" Col yace "Tana gidan, yanxu uwarta ta xo ta kwashi yaran ma" Yakumbo tace "Wasu yaran kuma?" Col yace "Yaran dai, baki gansu tsatstsaye parlor ba" mikewa Yakumbo tayi tace "Xata ina da su? tare da uwar yaran ta tafi?" Col yace "Xata raine su mana, ba yar ta bace ta haife su, Uwar yaran na nn parlor...." Yakumbo tace "Ban gane xata raine su ba?" Col yyi yar dariya yace "Ae fa tana da gaskiya yaya, jikokinta ne ai" ta rike kugu ta saki baki tana kallonsa, can tace "Ae ni dama tun ba yau ba nasan kai mugu ne Ahmad, wllh kai mugu ne, to muguntar taka ta sojoji sai ya kare a kan mu? ta kwashe min jikoki ka bar ta ta fita? Toh Allah ya fika" Bata jira cewarsa ba ta fice parlorn ta dawo kasa, tana kallonsu Hajiya Mariya da har lkcn suka kasa xaune, Noor kuma sai rusa kuka take, a fusace tace "Amma ku dai anyi gayyar yu yu yu, yanxu duk yawan ku a parlorn nn ku ka bar figaggiyar mata ta fice da 'ya ya har biyu?" Hajiya Mariya tace "A'a Col ne yasa ta fita da su, shi ya hanamu aikata komai wllh" a mugun fusace Yakumbo tace "Yo dama sai ku kula wnn da ya baro hankalinsa gaba daya a yak'in biafra?" Hajiya Mariya ta tabe baki tace "To ina mu ina ja da shi yaya?" Yakumbo tayi wani shewa tace "xata san jikokina ta fita da yau, kin dai san gidan koh?" Hajiya Mariya tace "Na sani" Yakumbo tayi kofa da sauri tace "Mu je" Hajiya Mariya ta dau Hijab din ilham ta bi bayanta, tun da suka dau hanya Yakumbo ke bala'i uwa xata tashi sama, col kam ya sha xagi har da na sayarwa, Hajiya Mariya dai sai bin ta take don tana da assurance baxa su fito gidan ba sai tare da yan biyu, suna isa gidansu Noor yakumbo bata saurari mai gadi dake neman sanin wanda suke nema ba ta bangajesa ta shige gate tana cewa "Kaji min mai gadin gidan bala'i" Hajiya Mariya ta bi bayanta, tsaye suka ga Mr David a balcony abun duniya ya ishesa, Yakumbo ta kalli Hajiya Mariya tace "Ita ce wnn" Hajiya Mariya na kkrin danne dariyarta tace "A'a ba ita bace" Yakumbo bata kuma kallonsa ba ta shige parlorn, bbu kowa ciki, Yakumbo ta haura sama Hajiya Mariya na biye da ita, dakuna suka dinga bubbudewa har suka bude wani wanda da alamar na Rachael ne, kwance suka ga yaran duk biyu a kan gado, Rachael na tsaye a press din kayanta xata fiddo xani da xata goya daya, ta rike daya su tafi church, duk a tunaninta David ne ya shigo shi yasa ko kallon inda kofar yake bata yi, Yakumbo ta karasa a hankali ta kinkimi yaro daya tace "Toh Wllh wllh na sake ganin sheggun kafafuwan ki a gidan K'ani na sai na ari bindigarsa na harbe su" A firgice Rachael ta juyo, Hajiya Mariya ta dau daya yaron da sauri, Rachael tace "Jesus Christ me ya kawo ku gidana?" Yakumbo na nuna ta da yatsa tayi mitsi mitsi da ido tace "Abinda ya kai ki gidanmu daxu" Tuni Hajiya Mariya tayi waje da Sadeeq, Rachael ta bi ta da sauri tana cewa "Ki dawo da yaran nn kar a ji mu a police station, ki dawo ki ajiye min jika na...." Yakumbo ta bi bayanta tana cewa "Aji mu a bariki karewar station, kin yi kadan ki shigo har gida ki kwashe ma mutane yara yar banxa kawai, ke kika yi cikin da aka haifesu xaki kawo mana rainin wayo" ai tuni Hajiya Mariya ta fice parlon gidan, Rachael dake ta vibrate ta juyo tana kallon Yakumbo tace "Amma ai 'ya ta ce ta haifesu ba wani ya haifa mata su ba, i swear to God of Jacob baxa ki fitar da yaron nn gidan nn ba yau sai dai duk abinda xai faru ya faru" Yakumbo tayi shewa tace "Dambe xa mu yi knn, to tsaya" cire mayafin kanta tayi ta goya jaririn da ya fara kuka tsabar wujjigasa da take, ta daure sa tamau a baya snn tace "Toh taho" David ya shigo parlon yana kallonsu, a tsawace Yakumbo ta kuma cewa "Ki taho nace ki karbesa, ban da raini har kya je gidan mutane ki kwaso yara, yo ai yar ki ya kamata ki kwasa ba su ba, su da suke gidan Ubansu" David yace "Kiyi hakuri don Allah" wani kallo ta jefa masa tace "Da xata can baka bata hakuri ba sai ni da na xo daukansu xaka ba hakuri" daga haka tayi hanyar kofa tace "Ashe dai karamar hauka ke kanta, nayi xaton sai mun dambatu xan bar gidan" ko rufe masu kofar bata yi ba ta kara gaba abunta, Rachael ta fashe da kuka tana kallon David yace "Serves you right" daga haka shi ma ya bar mata parlorn, yakumbo ta dinga masifa ita kadai a hanya ga yaro sai tsala kuka yake a bayan ta, ta kai masa duka a baya tace "Kai don mahaifinka rufe min baki kar in ajiye ka a nan inyi wucewata, baka gode Allah naje na amso ku a hannun kafura ba, in dan ta kakan ka ne ai sai dai kayi ta xama a gidan, mata yar banxa kawai ta xo ta kwashe ku, ita Hajarah ta tsaya tana kukan makirci ta kasa kullala komai" Hajiya Mariya na shigowa parlor Hajiya Rahina tace "Alhmdllh, har naji sanyi, amma wnn fitina da me yyi kama" Ummi ta sauke ajiyar xuciya tace "Allah ya kyauta" Mami kam kasa cewa komai tayi, Hajiya Mariya na bude yaron da ta lullube da xani sbda sanyin waje sai da tayi shock ganin Rosary a wuyarsa, bakinta a leko ta cire ta ajiye a kasa, sai ga Yakumbo ta shigo goye da Abbakar dake tsala kuka, sauke sa tayi tace "Da alama yaran nn yafi son can ne, bnda munafurci muna baro gidan ya dingi tsala min ihu har na iso nn, to tsaye xa mu yi a kansa don abun kunya daya ya ishe mu ba sai an mana k'ari ba" salati ta xabga bayan ta saukesa tace "Mayya, har ta rataya masu sarkan coci a wuya" sai kuma ta fashe da kuka tace "Duk Ahmad ne ya ja maku, bbu dole sai Aliyu ya tattara ya bar gidan tunda tun yanxu ya fara nuna masa bai son 'ya yansa, to ni idan ban so 'ya yan Aliyu ba 'ya 'yan wa xan so, dubi fa yaran kyawawa da su kamar larabawa..." Mami ta mike ta bar parlon, Yakumbo ta cire Rosary din ta jefar tace "Allah ya raya min ku a tafarkin islama, yasa ku xama manyan malaman islama irinsu Isma'il Mufti Menk a can waje da kuma fantami a nan Nigeria" murmushi Ummi tayi tace "Ameen" Yakumbo ta nufi sama tana cewa "Kuma Allah ya raba ku da hali irin na Aliyu, kwakwalwarsa kawai nake son ku dauko" parlon Col ta shiga tace "Toh naje na karbo su Ahmad, gari na wayewa kuma xa su bar maka gidan ka tunda ba son su kke ba, kai da ganinsu kuma kila sai dai girmansu" tana magana ne hawaye cike idonta.
*Haske writers asso*
💫 *Noorul Huda*💫
By khaleesat Haiydar📚✍🏻
97.....
Hajiya Mariya ta kwankwasa kofar dakin Abuturrab dake xaune tare da Noor a dakin yyi lallashin har ya gaji ya xauna yana kallonta shi dai yasan sai in Yakumbo bata je gidan ba amma ko da tsiya sai ta dawo tare da yaran, mikewa yyi ya bude kofar yaga Hajiya Mariya tsaye da Sadeeq hannunta ta mika masa shi tace "Bata yaron ta" d'an murmushi yyi ya karbi yaron bai dai tambayeta d'an uwansa ba ya juya ya koma dakin, ajiye ma Noor yyi a jikinta, ta kallesa tace "Dayan fa?" Yace "Yana gun su" cikin rawar murya tace "Kila baya wajen su" Dago kanta yyi yana kallon kwayar idonta, can ya langwabar da kai yace "Baby shknn yanxu duk son da kike min kin kwashe kin mayar kan twins, to ni meye tawa makomar, naga kamar ta babies kadai kike yi ynxu" dauke kanta tayi bata ce komai ba, aka bubbuga kofar dakin ya mike yace "Toh ga shi nn shima an kawo maki" bude kofar yyi yaga yakumbo ce ta shigo dakin rike da Abubakar ta kwantar da shi tace "Aliyu, toh dai a ynxu Ahmad bai da babban makiya kamar wa ennan 'ya yan naka, idan xaka ji ta nawa ka tattara ina ka ina ka, suma ka tattara masu ina su ina su ku bar masa gidan sa, ranan da Allah yasa suka girma sai su tako da kansu su xo su gaishesa, ni ba ma wnn ba, gani nake kamar bak'in cikin rahamar Allah yake masu, to banda haka ta ya xai bar mata me xuwa coci ta shigo masa har gida ta kwashe su ta tafi dasu, kasan matar har ta rataya masu sarkan coci fa a wuya Aliyu" Noor dai sunkuyar da kanta tayi tana wasa da yatsunta, shi kam Abuturrab bai iya yace komai ba sai kallonta yake, Yakumbo ta tabe baki tace "Toh dai Allah yyi mana tsari kwashi yaran ka ka bar masa gidansa da wuri wuri, yara maa sha Allah haka" kallon Noor tayi tace "Ke kam kinyi sa'ar uwa, toh ke ma har yanxu kina xuwa cocin kenan koh?" Abuturrab yace "A'a ita musulma ce..." Ta d'an yo waje da ido tace "Tohhh ta musulunta knn, amma dai da xa ka ji ta nawa ka samu yar uwarka musulma warce xata sa ta da 'ya yanta a hanya ka aura kwanan nn..." Sai a snn Noor ta dago manyan idonta tana kallonta, Yakumbo tace "Atoh, ni bayin Allah nake ji ma kar wataran ta mayar da su ruwa, ita ma ai tasan irin musuluntar da suke yi, bari in samu Hajarah in ji ynda xa ayi" daga haka ta fice daga dakin tana cewa "Mu muka ga kaddara, mun kuma gode Allah da ya ba mu ikon daukarta a ynda ta xo mana amma dole ya kara aure don daidaituwar gidansa" Abuturrab ya d'an kirkiri murmushi ya kamo hannun Noor ganin mood dinta cikin sanyin murya yace "You are the 1st nd the last in shaa Allah wife, no amount of talks will make me change my mind" ita dai bata ce komai ba sai hawaye da ya sakko idonta, rungumeta yyi ya lumshe ido yace "Believe me mum twins" Yakumbo na fita ta bude dakin su Ramla, Khaleesat da fatima ne a dakin, Khaleesat ta taso ta rungumeta tace "Umma yaushe kika xo" Yakumbo tace "Tun daxu fa, sai na tarar an dauke yaran da na xo gani shine na tafi karbo su, wacece wancan kuma" Fatima ta ajiye wayar hannunta tace "Ina yini" Yakumbo tace "Lfya lau" Khaleesat tace "Bakuwa ce Umma" Yakumbo tace "Ayyo, sannun ki toh" daga haka ta yi gaba, dakin Mami ta shiga, ta kalli su Ummi dake xaxxaune dakin da Hajiya Mariya tace "Toh dai Hajarah mijin ki ya nuna baro baro bai son xaman Aliyu gidan nn tunda har ya fara barin kafura na kwashe yara, don haka nace Aliyu ya lallaba ya bar gidan ko ko ya kika ga?" Hajiya Mariya tace "Gaskiya ne yaya, kuma tun da har taji ddin shigowa gidan gobe ma sai ta iya xuwa tace xata dauke su" Yakumbo tace "Wayyoo Allah Mariya, ke da kika san komai...." Xaunawa Yakumbo tayi tace "Abu na biyu kuma, Hajarah cewa nayi ya kamata Aliyu ya kara aure kwanan nn, ya auri musulma yar uwarsa warce xata sa ma 'ya yansa ido, Allah na tuba tubabbiya bbu wani tarbiyar arxiki da xata iya ba ma yaran nn biyu abun tausayi" tun da ta fara Hajiya Mariya da su Ummi ke kallonta, ta ci gaba "Shine nace in fara shawara da ke kafin in koma gun Ahmad, ko ya kika ga, ita wnn din ba wai ba ma sonta bane, a'a kawai jikokinmu muke ji ma, gwara ya auro cikakkiyar musulma yar uwarsa ta xo su hadu a ba yaran tarbiya, to ni da nake son su xama manyan malamai ma...." Mami tace "Toh, idan hakan ne mafi alkhairi Allah ya tabbatar...." Mikewa Hajiya Mariya tayi a fusace tace "Amma yaya baki kyauta ba in har kika fadi hakan gaskiya" Yakumbo ta yo waje da ido tace "Bata kyauta ba? Shi addu'ar da tayi ne bata kyauta ba Mariya?" juyawa Hajiya Mariya tayi ta fice daga dakin, Yakumbo tace "Ji sha sha sha kamar ba da ita muka je muka yi cacan baki aka bamu yara ba, Mariya fa ba cikakken hankali ke gareta ba, ko don bata san xafin haihuwar bane oho, banda haka yaya ana nema ma yaro abun alkhairi ta hayyako mana haka, so take 'ya yan sa su tashi bbu addini ne ko yaya, ai ni Aliyu ya gama cutar mu" Hajiya Rahina tace "Ae kam maganar ki na kan hanya Hajiya, uwa fa ke ba yara tarbiya ba uba ba...." Ummi ta katse ta tace "Amma ita ma ba jahila bace totally a islam kakanta musulmi ne, haka kuma kanwar mahaifinta, baka taba cewa ba musulma bace ita idan ba kun xauna tare bane" Mami tace "Ae ba don a walakantata ba Yakumbo ta fadi haka" Yakumbo tace "Atoh fada masu dai, kin san idan jika ba naka bane" daga haka ta fice daga dakin tana cewa "K'arin Auren Aliyu ba fashi wllh" Hajiya Mariya da ranta ya gama baci ta sauka kitchen ta ci gaba da taya Anty Maryam gyare gyaren da take da yaran frnds din Mami. Mami tayi murmushi tace "Shknn kinga sai a hada su da fatima Hajiya" Ummi tace "Wace fatiman?" Mami tace "daughter nah mana" Ummi ta girgixa kai tace "Allah ya kiyaye, Aliyu da matarsa sun wuce haka a gu na" Mami tace "Kamar ya Allah ya kiyaye, Hajiya idan kika duba maganan da Yakumbo tayi xa ki ga gaskiya take fadi wllh, ni ba wai bana son matar nn tasa bace kawai dai makomar yaran nake jimami, kinga shi kansa Aliyun ban da yyi sllh kan lkci sai kauce ma sa6o bbu abinda yake na addininsa, Idan ba kwanan nn da naga Aliyu ya fara tsayuwar dare ba shi ba gwanin yin hakan bane, Azkar idan yyi na safe a da can toh bbu xancen na yamma, Karatun qur'aninsa ganin dama ne, to ina gida a nn don Allah, me xata gani a gunsa da har xata yi koyi da shi ita matar? Amma kinga idan ya aure wata daban sai ta sa su kan hanya gaba daya" Ummi ta tabe baki tace "Toh Allah ya basa wata daban din" Mami tayi murmushi tace "Fatima ce ba wata daban ba" Ummi tace "Ita Fatimar ca aka maki rike take da addini banda sllh da take?" Dariya Hajiya Rahina tayi, Ummi tace "Atoh, barin yaran ynxu da bnda kishin hauka da bala'i bbu abinda suka sa gaba, ke a tunaninki xa ki nemo mai addini ki hada su amma karshensa xamar kishiya xata yi da ita ayi ta kishin hauka mara amfani, am nt in support of this gaskya Mum Aliyu, ita kuma sai aka ce a haka xata yi ta xama baxa ta nemi ilimin sabon addinin nata ba, ina ce a nan su Hajiyar Shagari qtrs take gaya mana tayi converting a gun su.... Ayi mata adalci, da rashin yan uwanta xata dinga ji ko kuma da kishiyar da ake shirin laka6a mata, bata da kowa da tafi kusanci da a yanxu ban da mu, kar a canxa mata view dinta a kan islam, in her case yi mata kishiya is totally out of the point, snn kun san duk namiji idan ya kara aure irin rawan kan da yake, Aliyu won't be exceptional, ko da kuwa ya nuna baya so to fa wataran xai so ne, For the sake of her conversion a cire maganan kishiya pls, ko da xai yi ya bari sai sun dade tare idan da rai da lafiya ta cika masa gida da 'ya ya...." Hajiya Amina dake ta jin su ta sauke ajiyar xuciya tace "Haka ne Hajiya you have a point, yakumbo tayi hakuri da wnn xancen, ke Mami ki nuna baki amince ba kawai" Mami bata ce komai, Ummi ta mike ta fita daga dakin, Ko da yakumbo ta kai ma Col xancen karin auren Abuturrab shiru yyi yana saurarenta, can ya gyada kai bayan ta kai aya yace "Kina da point a nan yaya"
*Haske writers asso*
💫 *Noorul Huda*💫
By khaleesat Haiydar📚✍🏻
98.....
Washegari da sassafe Ummi ta gama shirinta ta sa fatima ma ta shirya ta dau jaka tana kallon Mami tace "Toh Hajiya xa mu koma garin mu sae mun yi waya, Allah ya raya Ahmad da Abbakar" Mami tayi murmushi tace "Irin wnn sammako haka, ko duk maganar jiya ce" Ummi tace "Haba ko daya, ina son isa da wuri ne don inje clinic" Mami ta mike tace "Toh shknn Hajiya, mun gode kwarai Allah ya kara dankon xumunci" Ummi tace "Ameen" Naman suna me yawa Mami ta tula mata da drinks sai snacks tace ta kai ma su Rabi'a, A parlor Ummi tasa aka kira mata Abuturrab, ya sakko ganinta yace "Mami har xaku wuce da safe haka" tace "Eh ina son mu isa da wuri ne, sai ka turo babban mota a kwashe maku kayan ku na can ko boy" ya d'an shafa kai yace "Toh Mami, bari in kirata ku yi sallama" tace "A'a bar ta kace mata mun tafi kawai," a hankali yace "Toh ina xuwa Mami" daga haka ya tafi daki ya dauko makullin motarsa don ta taho masa da motar tasa daga can gombe, tare da Hajiya Mariya suka tafi kai su park, ya ba Fatima dubu ashirin taki karba, dole Hajiya Mariya ta tilastata ta karba tace ta gode, yana kallon Ummi yace "Nagode Mamina sai mun xo kawo maki xiyara in sha Allah, ki gayar min da kanwata khadija" tace "Toh ina xuba ido boy, ga dai Samha nan amana, idan ka ci amana kuma kai ma kasan sauran Aliyu, Allah raya maka boys dinka a tafarkin islam" cikin sanyin murya yace "Ameen Mami" tace "One more thing Aliyu, you re educated, you knw what's right from wrong... This is all i have to tell you ka xama me aiki da hankalin ka" daga haka ta shiga mota ta ce "Toh Hajiya Mariya sai mun yi waya, Allahu ya bar xumuncin mu" basu tafi ba sai da suka ga motar ya tashi snn suka dau hanyar gida, Abuturrab na driving ya kalli Hajiya Mariya da har lkcn bata da walwala yace "Mum wani abu ya faru ne, ur mood isn't encouraging" sai a snn ta kallesa tace "Tunda wnn fitinannar Uwar taka ta xo meye ma baxai faru ba, mata bata da aiki sai hada fitina, kaga xan kira Alhaji, (wato mijinta knn) in nema maka alfarma ya baka gidansa daya dake hotoro ku koma can da xama a yau Aliyu.... Yayar babanka ba da alkhairi ta xo ba gaskiya, naga kuma kamar Mami na neman biye mata ne" Abuturrab ya d'an yi shiru, sai can yace "Cewa take sai na kara aure koh?" Hajiya Mariya tace "Ta gaya maka kenan?" Gyada kai yyi yace "Eh, ta fadi hakan gaban Samha ma" Hajiya Mariya ta girgixa kai tace "Muna komawa gida ynxu ku fara shiri, dama Col ba son xamanka yake a gidan ba naga alama, ku koma hotoro kawai, but before then xaka bar su a gidana su yi arba'in" yace "Mum to gidana fa?" Tace "Aa bn san col ya san inda kake ma" Bai kuma cewa komai ba har suka isa gida, yana biye da ita a baya suka shiga parlor, xaunawa yyi a parlorn ya gaida Anty Maryam ta amsa, ya jawo Ihsan yace "Anty amma xaki bar mana ihsan koh" dariya kawai tayi tace "Lallai kam, xuwa anjima xa mu wuce" yace "Da wuri haka Anty" tace "Shekaranjiya na xo ai" yace "Toh Allah kai mu Anty" tace "Ameen" ya mike yana murmushi yace "Da gaske fa Anty xa ki bar min ihsaan" murmushi kawai tayi ya nufi stairs, bedroom dinsa ya shiga, ganin Noor bata dakin ya fito ya shiga dakin Maminsa, Yakumbo ya tarar tana ma Abubakar wanka, Mami na xaune rike da Ahmad, Ya xauna gefen gado yace "Ina kwana Umma" tace "Lafiya lau, sai yanxu?" kallon Mami yyi ita ma ya gaida ta, Ta amsa tace "Har sun wuce" Yace "Eh sun wuce" mikewa yyi ya fita daga dakin ya koma nasa, xama yyi yana tunanin maganganun Hajiya Mariya, can ya sauke ajiyar xuciya ya mike ya shiga bathroom don yin wanka, ko da ya fito daga wanka, xaune ya tadda Noor a can karshen gado a shirye cikin riga da skirt, ga breakfast da aka ajiye mata kan rug, ya ajiye karamar towel din hannunsa ya karasa kusa da ita yace "My wife" bata ce komai ba ya kalli abincin dake kasa yace "Toh sauka ki yi breakfast mana dear" nan ma tayi shiru, ya dago kanta yana kallon kwayar idonta yace "Tell me, wani abu ya faru ne" hawaye ya gani cikin idon, cikin Sanyin murya yace "Wife...." Still bata ce komai ba, a hankali yace "Ni bn san meyasa closeness din mu ya ja baya ba Samha, we were nt like this before, it's getting worst now, baki son amsa ni idan na maki magana, you derive pleasure ignoring me always.... I don't just knw what came over you" mikewa yyi ya dau towel dinsa ya koma can daya side din ya xauna, can ya tashi ya fara shiryawa har ya gama bata dago kanta ba, kofa ya nufa ya fita daga dakin, kuka ta fara a hankali, tayi me isarta snn ta sakko kasa, dai dai shigowar Yakumbo, ta kwantar da yaron hannunta tace "Ynxu 'yar nn barin abincin kika yi ya sandare" girgixa kai kawai Noor tayi, tace "Toh maza ki gama ki basu abinci su ma don yunwa suke ji" a hankali tace "Toh" yakumbo ta fita, Hajiya Mariya ce ta shigo da Sadeeq ta kwantar da shi gefen d'an uwansa tana kallon Noor tace "Idan kin gama sai ki yi breastfeeding dinsu kin ji Daughter" Noor tace "Toh" ita ma ta fita dakin, Tea kawai ta hada ta sha don ji tayi baxata iya cin komai ba, can ta mike ta koma kan gadon ta kwanta gefen yaron tana kallonsu. Karfe sha biyu saura Anty Maryam ta wuce, Col da kansa ya bata 20k kudin mota, Mami kuma ta ba Ihsaan atamfa guda Uku cikin wanda twins suka samu na suna, Hajiya Mariya da Abuturrab ne suka kai ta park, tun da suka bar gidan Noor ke kuka a daki, ta rasa dalilin kukan nata. Abuturrab na dawowa Ilham ta tare sa a parlor wai Abba na kiransa, ya d'an yi jim yana kallon Hajiya Mariya dake kallon ilham ita ma, can tace "Yakumbo na parlorn ne?" Ilham tace "Eh tana ciki" tsaki Hajiya Mariya tayi ta wuce sama, Abuturrab ya nufi parlon Abbansa, a hankali ya tura kofar ya shiga da sallama, xaunawa yyi kasa yana kallon Col yace "Ga ni Abba" Col ya kallesa yace "Na gan ka" D'an murmushi yyi ya sunkuyar da kai, Yakumbo tace "Atoh, ba wani abu bane dama batu ne da xai xame maka alkhairi nn gaba, kaga dai ni Fatima baxan so abinda xai cutar da kai ba Ali, kai ba ma hka ba, ni ta wa ennan yara biyu nake baxan so su halaka ba, haka kurum rana tsaka ka dau kirista wacce ba muharramar ka ba ka lula duniya da ita, kayi ta ba Ahmad wahalan neman ka, ni ma kasa nayi ta shiga da fita ina neman a karkato min da hankalinka ka dawo gida, to ni duk wnn bai wani dame ni ba, abinda yafi damuna shi ne Hajarah da Mariya sun san komai suka dinga munafurtar mu ashe su suka xuga ka kayi abinda kayi ma, kuma sun san inda kke, to ba wnn ba ma, babban tashin hankalin shine ynda ka kai yarinya masallaci aka daura maku aure kaje kana rayuwa da ita hankali kwance ga ka tatattcen mara ji koh? to dai wllh kullum kayi ta addu'a Allah ya yafe maka mahaifin ka ya yafe maka ni ma in yafe maka, idan ba haka ba wllh tarihi sai ya maimaita kansa, kana ji kana gani yar ka mace xata bi kato su gudu da sunan so, to don Allah wa ka cuta idan ba mu ba?" Sai a snn Abuturrab ya dago yana kallonta, Tace "Atoh, ba xancen ka harareni bane gaskiya ce na fada, ba haka kayi ma yar mutane ba, to kaji tsoron Allah kar kai ma ayi ma yar ka, kaga ko mu ma mun shiga uku ba kai kadai ba, to ni duk ba ma wnn ba, wai sai gashi da ka tashi dawowa sai ka dawo mana da yan biyu, wai kirista ta haife su, to ynxu abun tambaya a nn Aliyu shine, waye xae ba yaran nn tarbiya irin ta koyarwar islama?" Bbu yabo bbu fallasa yace "Uwarsu!" Yakumbo tace "Yau naga abinda ya ishe ni bai ishi Allah ba, wace uwar ta su? Ita kafurar xata ba su tarbiya" Abuturrab yace "Umma ki bar ce mata kafura, ynda kike musulma ita ma haka take musulma, kuma bbu wanda yafi wani a gun Allah sai...." Tsawa Abba ya daka masa ya mike yace "Are you stupid, ko ka fara shaye shaye ne?" Yakumbo tace "Atoh wa ya sani abu a duhu" Abba yace "I will kick you out idan baka maida hankali kasan warce ke gabanka ba, kar kayi tunanin na basar da abinda ka min ne, i am coming for you soon" Yakumbo ta tabe baki tace "A'a bar sa, ba ga yaran maxa nn ya haifa har biyu ba, xai ji ko da ddi ko bbu" Abuturrab bai kuma cewa komai ba, Tace "Toh ae ba tsoron ka ake ba, kame kamen ma an fasa, dama ba wani abu bane yasa aka kira ka nn, aure nake son kwanan nn ka sake, ka auri wacce xata kula maka da yaran da ka haifa, ta kuma yi musu tarbiya irin ta musulunci" tana huci ta kare maganan, ya d'an kalleta, snn ya girgixa kai yace "Bani da ra'ayin auren mata biyu Umma kiyi hakuri" ta mike tace "Toh kuwa ynxun nn xaka yi ra'ayin yin haka, idan ba haka ba wllh wllh wllh in kwashe yaran inyi tafiyata da su su girma a gu na, bbu kai bbu su kuma" Abuturrab yace "Na baki Umma" buda baki tayi tace "Ohh haka ma kace" yace "Umma ni dai da in kara aure gwara kin tafi da su ki basu tarbiyar ke, ita kuma nayi alkawarin baxa ta sake haihuwa ba.... Ina ce sbda a ba yaran tarbiya xan kara auren" rike baki tayi tace "Ehh lallai Aliyu ya xama dan iska, toh kai ke bada haihuwan da xaka hanata yin sa?" Ya girgixa kai yace "Bani ke badawa ba, amma bayan yaran nn biyu baxa ta kara haihuwan ba bare a dinga tunanin irin tarbiyar da xa su samu, wa ennan da ta haifa dai na baki su ki basu tarbiyar" Col dai kallonsa kawai yake, Yakumbo aka rasa abun cewa sai huci take, komawa tayi ta xauna tace "Toh wai ma ni me xanyi da jikoki daga gun tubabbiya" ya girgixa kai yace "Yara na ne ba nata ba, ni ke da iko da su ba ita ba, snn kuma nace na baki su Umma" a fusace Yakumbo tace "Toh ni kuma jikoki biyu sun min kadan don ubanka" murmushi yyi yace "A'a fa Umma jikokin ki sun kusa sha biyar, to me xai dame ki," Col yace "Alryt, idan kuma ku ka sake haihuwa i will surprise you Aliyu, xaka sha mamaki wllh, lastly ina son ku bar min gidana yau, enough is enough, tashi ka fita" mikewa yyi yace "Nagode Abba" daga haka ya juya ya fita parlon, ko da ya shiga bedroom din Mami, samun Hajiya Mariya yyi tana ta hada kayan babies, ya xauna gefen gado ta dawo kusa da shi tace "Me suka ce" d'an murmushi yyi ya gaya mata ynda suka yi da Yakumbo da Abba ta tabe baki tace "Toh kar ka kuskura ka cuce yar mutane, koma meye gwara kayi a kanka" Dariya yyi yace "Ni in cuce kai na kenan Mum?" Tace "Atoh ni ina ruwana, am very serious don't make her use anything but you can" yace "Uhmn to shkkn Mum" ta mike tana ci gaba da abinda take tace "Gwara da kace masu haka ai, ita kuma sai in ga nonon da xata ba yaran" dariya yyi ya nufi kofa tace "Ku shirya ynxu Aliyu" yace "Toh mum" daga haka ya fita.
*Haske writers asso*
💫 *Noorul Huda*💫
By khaleesat Haiydar📚✍🏻
99___100
Bedroom dinsa ya shiga ya tadda Noor kwance, yyi mata kallo daya ya dauke kai ya nufi gun kayansa, cikin kankanin lkci ya gama hada abinda xai hada ba tare da ya kalleta ba ya nufi kofa ya fita, dakin mami ya shiga Hajiya Mariya tace "Har kun gama?" Yace "Ehh" ya kalli Mami dake kallonsa ya xauna gefenta yace "Ki yi hakuri Mami, everything will come to past by the grace of God, i knw i have made u pass through so many pains, ki yafe min Mami don Allah" bata iya tace "Komai" Hajiya Mariya tace "Allah ma albarka" a hankali yace "Ameen" har lkcn idonsa na kan Mami, cikin sanyin murya tace "It's nothing Abuu, watarana sae lbri" rungumeta yyi ya lumshe ido yace "Nagode Mami" ko da suka fito dakin Hajiya Mariya na janye da babban trolleyn da ta tula kayan yara da na Noor tace "Ce mata ta fito son, u help her with the boys" yace "Mum i dnt knw hw she will feel idan ta ji xa a raba su da yaran da ki shiga ki mata mgna" Hajiya Mariya ta tabe baki tace "Duk fa baraxana ce, ya xata yi da 'ya yan mutane har biyu" murmushi yyi yace "Toh mu ma sai mu yi baraxanan bata su mu ga ko xata karba" Hajiya Mariya ta sake trolleyn ta shiga dakin, ganin Noor kwance tace "Baki shirya ba Daughter?" Mikewa xaune tayi tana kallonta, Hajiya Mariya ta dau Ahmad ta fita da shi ta mika ma Abuturrab snn ta dawo ta dau dayan tace "Kafin in dawo ki hada abinda xa ki hada kin ji, xa mu je can gida na ne" sosai Noor taji ddin hakan a ranta don ji tayi bata son xaman gidan kwata kwata, Abuturrab na rike da duk yaran ya shiga parlon Abbansa da sallama, gun Yakumbo ya nufa ya mika mata su yace "Ga su Umma, xa mu tafi ne." Ta yo waje da ido tace "Ina?" Yace "Duk inda Allah yyi!" Tace "Guduwan xaka sake yi knn" ya girgixa kai yace "Abba ne yace mu tafi" tabe baki tayi tace "Munafuki dama can kana da niyyar yin hakan ne, bnda hka ta yaya daga magana xaka kwaso min 'ya ya kace xaku tafi, anya kana son rabuwa da mu lfya kuwa Aliyu?" Yace "Ba haka bne Umma, bna son bacin ran Abba shi yasa xa mu tafi ynxu" tace "Ka ji salu6abbe, yo bacin rai na nawa, duk wa enda ka sa shi a baya ce maka aka yi ya warke a xuciyarsa ne, to ni ba wnn ba, ynxu da ka kwaso min yara ya xan yi da su?" Yace "Umarnin ki fa na bi Umma" kallon Abba da bai ko kalli inda suke ba tayi tace "Ahmad kana jin gantalallen d'anka koh? Ka tambayar min shi ya xan yi da su, nono garen da xan basu ko yaya" Abba yace "Ki barsa ya tafi da su kawai Yaya, lkcn da xai yi auren ma ba shawara yyi da mu ba bare har a damu da 'ya yansa, sai dai idan suka xama abinda kike gujen masa bbu shegen da xai ce jikokin Col Ahmad ne" Yakumbo tace "Atoh, su je kawai, amma fa da sun shekara xan bi sa duk inda suke in kwaso su" Col bai kuma cewa komai ba, a hankali Abuturrab yace "Am... am sorry dad, forgive me plss" kofa Col ya nuna masa alamar ya fita, ya juya ba musu ya fita dakin a sanyaye. Dariya Hajiya Mariya tayi ganin ya dawo da yaran tace "Sun hakura knn" Mami ta raka su har mota, tana tsaye har sai da suka bar gidan, Abuturrab ke driving din, Hajiya Mariya da Noor na rike da yaran a baya, har suka isa gidan Hajiya Mariya bbu wanda yace komai cikinsu, yyi horn mai gadi ya bude gate ya shiga yyi parking snn ya bude motar ya fito ya bude side din Hajiya Mariya ta fito Noor ma ta fito, yaron hannun Smll mum din tasa xae karba tace "A'a karbi na hannunta" bai ce komai ba, bai kuma kalli Noor ba ya koma bayan booth ya bude ya ciro kayansu ta bi sa da kallon gefen ido, ganin Hajiya Mariya tayi hanyar shiga gidan ta bi bayanta, a parlor ta xauna tana kallon Ahmad dake hannunta, Hajiya Mariya kuma ta wuce daki, a hankali Noor ta dago kanta suka hada ido da shi don yana xaune parlorn shi ma, shi ya dauke kansa, can ya mike ya bi bayan mum dinsa, ba a dau lkci ba Hajiya Mariya ta fito ta karbi yaron hannun Noor tace "Taso mu shiga ciki" Noor ta mike ta bi ta suka shiga bedroom dinta, Kan gado Hajiya Mariya ta nuna mata tace "You feel at home kin ji daughter, ina xuwa in daura girki Hauwa bata iso ba" daga haka ta fita dakin, Abuturrab ya mike ya fita shi ma, kitchen ya bi small mum dinsa yace "Mum xan wuce can gidan ina son in huta ne" tace "Wani gidan?" Yace "Mine" tace "Kafi son can kenan" d'an murmushi yyi yace "Mum it's nothing ae" tace "Toh shknn, amma me yasa baxa ka huta nn ba sai anjima ka wuce" yace "A'a ynxu nake son wucewa" tace "Toh abinci fa?" Yace "am full mum, sai dai gobe idan na xo" tace "Kun yi sallama da ita?" Yace "Ehh mun yi" tace "Toh Allah ya tsare, kayi addu'a kafin ka fita" yace "In sha Allah mum" daga haka ya juya ya bar kitchen din yyi wucewarsa. Washegari misalin goma na safe Abuturrab ya xo gidan Hajiya Mariya, suna daki gaba daya, tana yi ma Noor kitso don ko da suna bata yrda an mata kitson ba ynxun ma lallaba ta tayi ta yrda take mata sai yatsine fuska take, Hauwa mai aikin Hajiya Mariya kuma tana rike da Ahmad tana basa ruwa a feeder d'an uwansa kuma na kwance, Hajiya Mariya ta amsa gaisuwar Abuturrab tace "Sai yanxu Son" yace "Muna tare da Mujaheed ya dawo jiya" kallon Hauwa dake gaishesa yyi ya amsa gaisuwar snn ya dau Abubakar dake kwance yace "Frnd, good morning" Hajiya Mariya tace "Lallai kam frnd, frnd me hana mutane bacci da daddare, kaga Sadeeq din nn fitinanne ne na karshe" yyi dariya yace "Abokin nawa, to Abbana fa" ta kalli Ahmad tace "Shi kuma d'an taya bera 6ari ne, da yaji ya fara shi ma sai ya cafke" kallon Noor da ta sake ma kai tuntuni tayi tace "Ba ku gaisa ba Samha" Noor ta d'an kallesa tace "Ina kwana" a takaice yace "Lafiya lau mum twins" mikewa yyi yace "Na gaishe ku mum, xan je gidan boss dina ne ynxu" tace "Wai Dr Mustapha" yace "Ehh" tace "Har ya gaji da tambayar ka ya bari, xaka ci gaba da aiki a clinic din nasa knn" yace "Sae idan akwai vacancy mum" tace "Ae ko bbu na tabbata xai bari ka ci gaba, yana sonka mutumin" d'an murmushi Abuturrab yyi, yyi mata sallama ya fita. Haka Noor ta ci gaba da rayuwa da yaranta gidan Hajiya Mariya dake basu kulawa yanda ya kamata, ba ita kadai ba har mai gidanta na mugun son Arshaq da Ashraf sunan da Hajiya Mariya take kiransu da shi daga baya, yaran suka yi girma tun kan arbai'n din, sai rigima da tayi masu yawa, gasu kamar larabawa don kyau hakan yasa duk wanda ya gansu sae ya shiga ransa, ynxu kam mai aikin Hajiya Mariya bata da aiki sae na rainon yaran tsabar yanda take sonsu, ko da yaushe suna wajenta, duk da irin nutsuwar da Noor ta samu a gidan don tayi kyau ta kara haske amma bata da kwanciyar hankali don har lkcn gaisuwa kadai ke hadata da Aliyu, kuma sau daya yake xuwa wataran ma baxae xo ba don ya fara aiki a gun aikinsa na da, ita kanta small mum dinsa na lura da take takensa sai dai bata ce masa komai ba tukun, da ya xo duk awannin da xae yi a gidan yana tare da yaransa ne, Noor kam tsakaninsu gaisuwa, abun ya fara damun Noor ssai, sae dai bata iya nunawa, ranan Hajiya Mariya ta kirasa daki ta tambayesa ma'anar behavior dinsa, yyi murmushi yana shafa kai yace "Mum haka take min ita ma" Tace "Kamar ya?" Yace "Ko da yaushe share ni take ta mayar da shi habit dinta ynxu" Hajiya Mariya tace "Haba Aliyu sae kace baka fi ta hankali ba, ynxu sai ka biye mata kamar wani mara tunani" yace "No mum, am just giving her space ne, naga kamar haushi na take ji" tace "Kasan me yasa take maka haka" kallonta yyi bai ce komai ba, tace "Gani xata yi kai ga ka tare da yan uwanka ko wanne na ji da kai, to ita fa, bata da kowa nata kusa da ita ga irin uwar da Allah ya hada ta da, she will always feel dejected idan ta tuna haka" bai ce komai ba, tace "To gaskiya bna son wnn shashancin gashi naga hakan na damunta sosai, ka dinga mata adalci Aliyu" yace "To nima ta dinga min, har ynxu idan abu bai min dai dai ba sai naji xuciyata na min xafi sosai mum, nima ba a son raina nake mata haka ba, but i have no option taki kwantar da hankalinta kuma ba komai ke damunta ba illa kishi ita bata ki kar in sake ma ko wace mace magana ba in dawo muyi ta xama bana xuwa ko ina" dariya Hajiya Mariya tayi tace "How will dat be possible kuma" Sau biyu Mami na xuwa gidan da su ilham ganin Arshaq da Ashraf, ana gobe Noor xa su yi arba'in Abuturrab na gidan tun yamma har bayan isha sbda ruwan da ake, Hajiya Mariya tace "You spend the nyt here sbda ruwa Aliyu" yace "Yea am thinking of that" Noor na daki kwance wajen karfe goma da rabi, har tayi shirin bacci Hajiya Mariya ta shigo mata da yara ta kwantar kusa da ita tace "Baxa ki sha furan ba kuma Samha" tace "Na koshi Mum" Hajiya Mariya tace "Toh shknn sai da safe" daga haka ta fita, Noor ta d'an yi mamaki don in har mai gidanta bai gidan ta kan kwana da su, Hauwa kuma ta wuce gida, ranan da yake nn kuma Hauwa ce ke tsayawa ta kwana da su, bude kofar dakin aka yi ta dago kai, tayi mamakin ganinsa don bata san yana nn ba har lkcn, ya rufe kofar ya karaso cikin dakin har xai kunna Ac ya tuna da yaran dake kwance ya rage kayan jikinsa kawai ya kashe wutan dakin ya nufi kan gadon ya kwanta, turo baki tayi ta mike xaune ta dau Arshaq ta sa shi a tsakiyarsu, ta dauko Ashraf shima ta ajiyesa duk yana kallonta ta koma can karshen gado ta juya masu baya, daukan yaran yyi gaba daya ya ajiye su can gefensa ya dawo kusa da ita, ta mike xaune tana kallonsa, tashi xaune yyi shi ma xata sauka kan gadon ya fixgota, fadawa jikinsa tayi ta fashe da kuka yace "Na rashin gaskiya koh?" A hankali take kukan bata ce komai ba, can yaji a hankali tace "Am sorry...." ya dago kanta yace "For?" Kin cewa komai tayi ta mayar da kanta kirjinsa, ya lumshe ido yana murmushi yace "Sorry for ur new habit baby, in dai kika kashe ni shknn sai kiyi ta rainan yaran ki ke kadai" kuka ta fara yi sosai, ya kai bakinsa kunnenta yace "Alryt baxan mutu ba sai kin haifa min yara shidda koh?" Abbansa ne ya fado masa ya lumshe ido, ita kam gyada masa kai tayi yace "Alryt, tel me u love me" murya can kasa tace "It's nt worth sayin....." bata rufe baki ba ya fara kissing din ta, Nan ita ma ta nuna masa tayi kewarsa fiye da yanda yyi, washegari da sassafe Abuturrab ya bar gidan tun kan Small mum dinsa ta fito, ita kanta Noor bata san ya wuce ba don tunda tayi sllh ta koma bacci, karfe sha daya Hajiya Mariya ta kirasa da yake ranan lahadi ce sai ga shi ya taho, a daki ya sameta bayan sun gaisa tace "Kaga yau suka yi 40 days son, ya kamata ku koma can gidan tare, before then kuma lefen da baka yi mata ba sai kayi xa su koma" dariya yyi yace "Kai mum" tace "Yes in raka ka kasuwan, kuma miye na wucewa da asuba" ya d'an shafa kai yace "Ba komai mum" mikewa tayi tace "Toh ni dai bari in shirya mu je kasuwan ynxu" fita yyi ya shiga dakin da Noor take ya sameta xaune tana ta wasa da yaranta, xaunawa yyi kusa da ita yace "Tom kin gama da su, it's now my time" hararansa tayi tace "Ni bn gama da su ba" rungumota yyi yace "Ashe kema kin yi missing dina baby?" Ta rufe ido bata ce komai ba tana murmushi tana shakan kamshinsa me ddi, murya can kasa yace "yesterday was great...." Bude kofar dakin Hajiya Mariya tayi, Noor ta janye jikinta da sauri, yi tayi kmr bata gansu ba tace "Ina jiranka ne Aliyu" ya mike da sauri yace "Okay mum" tana fita yayi kissing dinta a lips yace "Sai mun dawo baby" bin sa tayi da ido don ba karamin kyau kananun kayan jikinsa suka yi masa ba, yana fita Hauwa ta shigo dakin. Abuturrab ya langwabar da kansa bayan sun isa Atm yace "Mum kudin account dina is nt up to 500k fa, kuma...." Tace "Baka da damuwa sai in ranta maka idan ka samu ka mayar min da kayana" dariya yyi yace "Kai mum" tace "Ehh, xan dai bada tawa gudunmawar kayan jewelries" yace "Toh nagode mum" dubu dari biyu da hamsin kawai ya ciro a account dinsa, ita ma ta cire kudi me yawa bata dai gaya masa ko nawa bne suka shiga kasuwa, akwatuna masu kyau na xamani ta fara sa suka siya set guda, daga nn kuma suka shiga shagunan atamfofi ta siya manyan atamfa guda sha biyar snn ta siya masu d'an saukin kudi guda goma, ta siya lace masu tsada biyar, sai materials da abaya kala kala, mayafai, hijab, jakunkuna, takalma, kayan shafe shafe, turare, sabulai, kai duk abinda tasan ana xubawa a lefe har da su pray mat, alqur'an da carbi, sae jewelries da ta bata lkci wajen xabansu, Abuturrab dake xaune sai kallon ikon Allah yake yace "Mum kashe ni kike son yi kawai" kallonsa tayi tace "Wato ga yarinya ka samu a bnxa koh" dariya yyi yace "Wayyo mum a dai tausaya min, ni fa ne naki" tace "A'a mamar ka na can inda ka baro ta, wnn ce tawa a ynxu" ba su suka bar kasuwan ba sai kusan la'asar, sae da ta tabbatar bbu abinda ya rage bata siya ma Noor ba uwa ynxu xa ayi auren, sai da suka isa gida ta juya tana kallonsa tace "Kudin da xaka ban nayi lissafi 450k bnda kudin jewelries" xaro ido yyi yana kallonta, bata kuma kallon inda yake ba ta fita motar, ta kira mai gadi ya taimaka mata shiga da kaya ciki, Abuturrab ya fito motar yana murmushi a xuciyarsa yace "Lallai mum" Noor bata iya tace ma Hajiya Mariya dake ta nuna mata kayan tana jera su a akwati komai ba, duk jikinta yyi sanyi wanda hakan yasa bata san lkcn da hawaye ya shiga sakko mata ba, jin shirunta yyi yawa Hajiya Mariya ta dago tana kallonta, ganin kuka take tace "Ikon Allah, kuka kuma Samha" dawowa tayi kusa da ita tace "Kukan me kike daughter" rungumeta Noor tayi cikin muryar kuka tace "I love you mum, nagode Allah kara maki tsawon kwana" Hajiya Mariya tayi murmushi tace "Toh Amin my daughter, you take me as ur mother kin ji" karfe biyar da wani abu Hajiya Mariya tayi mata duk abinda tasan ya dace dai na gyaran jiki, ta kira mijinta ta rokesa alfarmar siya masu foodstuffs, ba a dau lkci ba driver ya shigo da buhun shinkafa biyu, carton din taliya uku, jarkan man gyada da manja manya, maggi, gishiri har da kwalayen indomie biyu, Abuturrab na shigowa tace "Toh ga gara nn Alhaji yyi mata nasan har ku bar duniya baxa ka mata gorin hakan ba wataran tunda ku din ba tabbas ne da ku ba, kayan daki kuma in shaa Allah idan kudi ya shigo min xan siya mata nata" dariya yyi sosai yace "Mum you are making me feel ashame, haba my mum" bata sauraresa ba ta kara gaba abunta, bayan magrib Hajiya Mariya ta rakasu can gidan nasu da aka yi furnishing tuni, duplex ne mai kyau da parlor sama da kasa sai dakuna huda ko wanne da bathroom, sannan babban kitchen, xa a iya cewa col ne ya gina masa gidan don kudinsa ba mai yawa bane a ginin gidan, Da yake abban nasa yasan halinsa shi yasa bai yrda ya tare gidan ba da dadewa sai masu gadi har uku dake rayuwa cikin gidan, Kuka Noor ta dinga yi da Hajiya Mariya xata wuce, Hajiya Mariya dake dariya tace "Ae sai yaran ki su maki dariya Samha, kar ki damu ko xuwa jibi Hauwa xata dawo ta dinga xama da ku sai in nemi wata mai aikin" tun barin Hajiya Mariya gidan Noor taki daina kukan da take, ita har xuciyarta take son matar, duk iya rarrashin da Abuturrab yyi mata kin saurarensa tayi, ya kyaleta ya maida hankalinsa kan boys dinsa dake kwance kan gado, ana kiran isha ya tafi masallaci da xai dawo ya dawo masu da take away da fresh milk, shi kadai ya ci don ko kallon abincin ita bata yi, yyi wankansa ya sauya xuwa pyjamas ya kashe wutan daki yyi kwanciyarsa kusa da yaran dake bacci, ta gaji don kanta bayan kusan awa daya ta mike ta shiga bathroom ta dauro alwala ta fito tayi sllh, tana idarwa ta canxa kayan jikinta xuwa rigar bacci don tayi wanka a can gidan, ta je can karshen gado tayi kwanciyarta ta juya masu baya, dawowa yyi kusa da ita ya jawo ta jikinsa murya can kasa yace "Oya ci gaba da kukan" turo baki tayi xata kwace kanta yace "Baki isa ba, ci gaba ina son rarrashin ki yanda ya kamata ne" cikin muryar shagwaba tace "Ni ka bar ni, bana soo..." Tsit tayi ta lumshe ido don bbu bata lkci ya fara rarrashin nata yanda ya kamata kuwa.
*Haske writers asso*
tnx for d prayers everyone.
💫 *Noorul Huda*💫
By khaleesat Haiydar📚✍🏻
101.....
Zama irin ta masoya Abuturrab da Noor suka shiga yi, bai taba tunanin Noor xata ajiye komai ta fito masa da tsantsan so ba, ko kadan bata son bacin ransa kamar yanda shi ma bai son nata, bbu abinda ya sa ta kara samun kwanciyar hankali irin yanda Abbanta kan xo gidan nasu duk end of month ganin Arshaq da Ashraf da yanxu ke dosan shekara daya, yaran maa sha Allah bbu abinda suka mance na babansu, ga su da farin jini duk inda xa su sai an tanka su, ba don Hauwa dake gidan ba da ba xata iya rainon nasu ita kadai ba don matsalarsu na rigima yyi yawa, Mami kan xo lkci lkci ita ma ganin jikokin nata, wani lkcn kannin Abuturrab kan biyo ta har su kwana gidan amma fa sai ran da Col bai gari, Hajiya Mariya kam dama yaran har sun saba da ita ba a daukan lkci bata je gidan ba, su ma duk sati biyu ko uku su kan je su wuni a gidanta ran lahadi, duk ran Friday Abuturrab kan tura ma Mahaifinsa text din gaisuwa da barka da juma'ah bai taba fashin yin hakan ba, duk da shi ma bai taba masa reply ba, Anty Maryam ma taje gidan nasu sau daya amma bata kwana ba ta wuce, Abuturrab kan je gombe once in a while don gaida Ummi, Noor dai bata taba binsa ba sai dai su gaisa ta waya, Xumunci sosai suke yi da Umma don so tari ta kan je gaida su ta yini da su Arshaq, idan ma suka dade basu je ba, Ahmad kan je ganin takwararsa da matarsa Maryam dake kara koya ma Noor xamantakewar aure, har lkcn idan Noor ta tuna mahaifiyarta fushi take da ita hakan na hana mata walwala kusan kullum kuma sai tayi tunaninta, duk tsawon lkcn nn bata xauna haka ba sau daya Abuturrab yyi mata maganan islamiyya washegari kuma tasa ya kai ta, duk karfe goma take tafiya ta dawo karfe biyu, ita kuma Hauwa tayi rainon yara, ana haka har yaran suka cika shekara daya da watanni biyar nn kuma Hajiya Mariya ta xo ta daukesu tare da Hauwa don ita xata yaye su, duk sai Noor taji ba ddi, wanda hakan sai da ya sa mata xaxxabi, ganin ta ki dawowa normal har bayan sati biyu har abinci ma ta fara ignoring Abuturrab ya sa ta gaba don jin ko an taba ce mata xa a rabata da yaran ne, kasa ce mata komai yyi yana kallon kwayar idonta, lkci daya maganan Abbansa ya fado masa wanda hakan sai da yasa gabansa ya fadi, d'an murmushi ya kirkira yace "Ae shknn sai in je in samu mum in ce mata kince a karbo maki yaran ki" xaro ido tayi tace "Ni ai bn ce maka haka ba" yace "Toh me ke damun ki?" Ta bude masa hannu alamar bata sani ba, hancinta ya ja yace "Fadi gaskiya boys din ki kike tunani" bata ce masa komai ba ta koma tayi kwanciyarta, ya mike yace "On Saturday xa ta kawo su ae wife, ita ma xata je Malaysia ne" fita yyi dakin ya koma parlor ya xauna yyi shiru, can ya mike ya dau makullin mota ya koma dakinta yace mata yana xuwa snn ya fita, pharmacy ya nufa direct, ya siya injections da xai siya da drugs ya dawo gida, bacci ya sameta tana yi, ya kalli agogo ya xauna kusa da ita ya shiga tashinta, a hankali ta bude ido yace "Baki ci abinci ba har ynxu baby" ta girgixa kai tace "Am nt hungry" yace "No u re, tun safe tea kawai kika sha dear, gaya min me kike son ci?" Ta d'an yi shiru sai kuma tace "Tuwo xan ci" yace "Toh bari in siyo maki a eatry" daga haka ya mike ya fita, tuwo da miyar vegetable ya siyo mata yana xuba mata a plate ta sakko kasa, a hankali ta kauda kai, yace "What?" Da kyar tace "I think i want to throw up, ka rufe abincin, it's..." Rufe fuskar tayi gaba daya, ba musu ya dauke abincin ya rufe ya ajiye gefe yace "Toh me xa ki ci" ta mike xata koma kan gado tace "I told you am nt hungry" yace "Noo kin ga akwai xaxxabi jikin ki ki ci ko kadan ne sai in baki magani" tace "Baxan iya ci ba" yace "In kawo maki shayi?" Gyada masa kai tayi ya fita ya hado mata shayin, kadan ya lallabata ta sha snn ya dauko maganin da har ya ballar mata da cup din ruwa ya mika mata ta amsa ta sha, yace "Saura allura" da sauri tace "Bana so" yace "Guda daya fa dear" da kyar ta amince yyi mata alluran snn ta kwanta ya kwashi take away din tuwo da cups ya fita xuwa kitchen, yana fita bacci ya dauketa, a gida yyi la'asar don bai son barin ta ita kadai, karfe biyar saura ya rufe laptop din gabansa ya mike ya wuce dakinta, ganin bai ganta kwance ba ya kalli kofar bathroom dake a bude, ya karasa ciki da sauri, durkushe ya ganta a bathroom din cikin jini, ya dagota yace "Subhanallah what happened, me ya faru, kin ji ciwo ne" a rude yake tambayar ganin kallon da take masa sai da ya sha jinin jikinsa ya kasa cewa komai kuma, a hankali ta mike tsaye ta cire kayan jikinta, Yana tsaye ya kasa cewa komai har ta gama kintsa kanta ta fice bayin, sai a snn ya juya shima ya fita kwance ya ganta kan gado ya karasa a hankali yace "Sannu wife, u were bleeding....." Lumshe ido tayi bata ce komai, pain reliever ya dauko mata yace "Tashi ki karbi magani ki sha pls" bude ido tayi ya duka kusa da ita yace "Pls wife" mikewa xaune tayi ta karbi maganin ta sha, yace "Ina ke maki ciwo" kasan cikinta ta nuna masa yace "Allah xai sauwake kin ji" komawa tayi ta kwanta ya mike ya fita, duk jikinsa yyi sanyi, but he have no other alternative. Kafin kwana biyu Noor ta warware kamar ba ita ba, a ranan Asabar Hajiya Mariya ta dawo mata da boys dinta, har ranta tayi murnan ganinsu amma bata nuna ba, Sai da Hajiya Mariya xata tafi ta tambayeta Anty Hawwa fa, Hajiya Mariya tace "Taje garin su amma sati biyu xata yi ta dawo" Noor tace "Allah ya dawo da ita lafiya" Abuturrab ne ya maida small mum din tasa gida. Haka nn rayuwarsu ya ci gaba da kasancewa gwanin sha'awa, he was very careful kar Noor ta kara conceiving, Har Ashraf da Arshaq suka cika shekara biyu da rabi, a nan ya sa su a islamic schl mai hade da boko, sai a snn Noor tasan ashe Abuturrab ba baya ba a fannin addini kawai ya fi fito da boko fili ne, during weekend gaba daya lkcnsa na gun yaransa yana coaching din su don bai son su yi lacking komai na bangaren addini ynda baxai ji fargaban duk inda xa su shiga ba ko ba ynxu ba, don yasan baxai taba rabasu da dangin mahaifiyarsu ba, mugun tsoronsa yaran suke sbda strictness dinsa ita kuma a lkcn tana shirin fara Diploma a fannin Islamic studies, idan Noor na rera maka karatun qur'an ko tana karanto ma litattafen addini baka taba cewa she was once a Christian, hakan yasa Abuturrab ke alfahari da ita, a cikin kankanin lkci Arshaq da Ashraf suka fara larabci a shekararsu ta biyu a makarantar ga hadda dake kansu, Abbansu ya daina masu Hausa gaba daya sai dai Noor, in dai xai yi communicate da su sai dai Larabci ko Turanci, Mahaifin Noor ya maida gidansu wajen frequent xuwansa sbda jikokin nasa dake mugun sonsa shi ma kuma yake ji da su, ba don kowa yake xuwa gidan ba sai don su, yau ma kamar ko wace Friday Mr David ya xo gidan da yamma rike da chocolates dinsu, yan biyun na xaune gun da Abbansu ya tanadar masu don studies ko wannensu da qur'an a hannu, Noor kuma na kitchen tana girki, duk suka taso gaida kakan nasu, ya zauna kujera yana kallonsu ganin mood dinsu yace "What happen to my boys" Ashraf dai yyi shiru, Arshaq da har idonsa ya kawo ruwa yace "Abbu promise to cane us today" Noor ta fito kitchen ta gaida Abban nata tana murmushi, ya amsa ya maida hankalinsa kan yaran yace "Wht have you 2 done wrong" Ashraf ya juya yana kallon Ummun sa, Mr David ya kalleta yace "Me suka yi" yar dariya tayi tace "Abba k'arin hadda yyi masu tun jiya dan yana nyt duty sai suka ki yi, to yace idan ya dawo daga masallaci xasu bada haddan shine fa ka gansu haka" yace "Toh ke me yasa baxa ki masu ba" tace "Abba basa ji, kallonsu ya fara yawa kwanan nn" da turanci Arshaq yace "Grandpa ai kai ma ka iya ka yi mana" daga haka ya tafi ya dauko qur'an din yana mika masa, shiru Mr David yyi yana kallonsu bai kuma karbi Al-qur'an din ba, Ashraf yace "Pls grandpa, assist us" a hankali Noor ta juya ta koma kitchen, yaran biyu suka kuma hada baki gun cewa "Plss grandpa..."
*Haske writers asso*
💫 *Noorul Huda*💫
By khaleesat Haiydar📚✍🏻
102.....
Mr David ya girgixa kai yace "Noo, let me call ur mum to assit you" a tare suka ce "Noo, we want ur assistance Grandpa" shiru yyi yana kallonsu, ganin ynda suka marairaice su ma suna kallonsa, yyi murmushi murya can kasa yace "Alryt, which surah is that?" a tare suka ce "Surah Al-Munafiqun" Lumshe ido yyi yace "Alryt, alryt... you read frm d beginning den i continue frm where u stop" xaunawa suka yi a tare suka ajiye qur'an din hannunsu suka fara karanto haddar suran dake kansu idonsa a kansu ko kiftawa bai son yi.....A aya ta biyar suka dago suna kallonsa, ya dage masu gira yana murmushi yace "Go on boys" Arshaq ya kalli Ashraf yace "We stopped der, ryt?" Ashraf yace "Na'am...." Kallon kakan nasu suka yi, Ashraf yace "Grandpa the next aya is where we need ur assistant" Mr David ya jinjina kai yace "Ohk, ohk go get me pray mat....." mikewa Arshaq yyi ya dauko masa darduma ya kawo masa ya karba ya shimfida snn yace su daura qur'an din a kai, ba musu suka daura, ya sakko kasa ya xauna kan lallausan carpet din parlon ya tankwashe kafa yana kallon qur'an din dake kan darduman, Noor dai na tsaye kitchen ta jingina da bango duk jikinta yyi sanyi, lkci daya hawaye ya kawo idonta, a hankali Mr David ya soma karanto masu aya ta shidda a surahn idonsa na kan qur'an din, duk yaran suka maida hankali kan qur'an din suma suna saurarensa, a aya ta bakwai suka ce masa Abbunsu ya tsaya masu, don haka ya dinga maimaita masu idanuwan su a kan qur'an din gabansu, har Abuturrab ya shigo parlon, tun daga bakin kofa yake kallonsu da mamaki har ya karaso inda suke, Mr David ya kai aya snn yace "Hope it's clear" duk suka gyada masa kai snn suka rufe qur'an din suka mike suna kallon Abuturrab suka yi masa sannu da xuwa da larabci suka bar parlon, xaunawa yyi kan kujera yana kallon Mr David yace "Ina yini Abba" Mr David ya kallesa yace "Lafiya Aliyu, sun sa sai na biya masu hadda" Abuturrab yyi murmushi yace "Baka mance karatun qur'an ba knn Abba" murmushi yyi bai ce komai ba ya mike yace "As usual i came to check on dem, sai next Friday" daga haka ya nufi kofa Abuturrab ya bi sa da kallo a sanyaye, ganin zai fita yace "Abba abinci fa?" Ba tare da ya juyo ba yace "Ohh Alhmdllh tnx" daga haka ya fita, Abuturrab ya kasa dauke idonsa a kan kofar. Tunda Mr David ya isa gida ya kasa shiga parlor yyi tsaye Balcony, ya rasa tunanin da yake, ganin har bayan minti talatin bai shigo ba Rachael dake parlor da kawarta ta aiki 'yar yayarta dake Ghana, warce aka bata madadin Samantha a cewarsu, tace mata taje ta duba me yake yi a waje, yarinyar da baxa ta wuce 20 ba ta dawo tace "Kawai yana tsaye ne Mumy" mikewa Rachael tayi ta fita ta tsaya tana kallonsa, can ta tabe baki ta koma ciki, bayan minti goma taji fitar motarsa gidan, Kawarta Esther tace "Mantuwa yayi ne?" Rachael tace "Who knws for him, na lura tunda aka ban Comfort yake bakin ciki, yaga na yaye yar sa a rayuwata, ni a ynxu da kika gan ni bani da ya a duniya da ta wuce comfort" Esther tace "Gaskiya kam, amma kina jin labarin samantha da yaran nata kuwa?" Rachael tace "Ynxun ma da kika gansa na san daga can yake, yaranta kuma yace min sun girma amma ni ba matsala ta bace wnn, comfort ce komai na ynxu" Esther tace "Anya kuwa David ba cewa xai yi shi ma xai koma musulunci ba" Dariya sosai Rachael tayi tace "Da kuwa ya gwammace ba mu hadu a rayuwa ba" tun daga wnn rana idan Mr David yaje gun grandchildren din nasa sai sun dauko masa qur'an ya biya masu, Noor na jin dadin hakan har ranta a ko da yaushe kuma fata take Allah yasa Abbanta ya dawo islam, da farko bai yrda ya dau qur'an din sai dai yasa su ajiye masa kan pray mat, daga baya kuma taga yana dauka. Ana haka su Arshaq suka yi long vacation xa su primary 3, tun kafin hutun Abuturrab ke tunanin kai su can gidansu su yi hutun, rabonsu da gidan tun suna jarirai, sun dai san paternal grandpa din nasu a hoto, a ko da yaushe kuma su kan tambayi Abban nasu yana ina, me yasa basu taba ganinsa ba, sai yaushe xa su gansa, labarinsa kam bbu wanda basu sani ba don Abban nasu na gaya masu about him, Abuturrab na son kai su gidan su ga Mahaifinsa amma yana tsoron abinda xai iya biyowa baya, shi dai ya kan je duk da har lkcn Abba baya sake masa, Da small Mum dinsa yyi shawarar kai su can gidan nasu su yi hutu ta kuma basa goyan baya dari bisa dari tace idan sun je sai a ga ko xai koro su, Ita dai Noor bata ce komai ba, boys din kam where very happy xasu gun kakan nasu, ranan lahadi Noor ta gama hada masu kayansu na hutun gaba daya har da takardun karatun su, suka dau hanyar gidansu Abuturrab, ita ke driving din, Abuturrab kuma na xaune bayan motar da boys din nasa yana kuma basu lbrin Col Ahmad, Arshaq ya xaro ido yace "You mean Gun Abbu?" Abuturrab ya gyada kai yace "Of course, but the gun is meant for only those dat commit crimes like arm robbers, and kidnapers" Ashraf yace "Ohh that sounds nice, do he still wear his army wears?" Abuturrab ya dan bude ido yace "I don't think so, buh you can ask him to show u the wears, of course i knw he will" Arshaq yace "Waow am so eager to see him dad" Abuturrab yace "But mind you, he doesn't understand Hausa or English, but only Arabia" Ashraf yace "That's weird, even the lingua franca?" Abuturrab yace "Yeaa" Arshaq yace "Buh Grandma do speak English" yace "Ohh yea, but my dad doesn't" Ita dai Noor bata ce masu komai ba, Abuturrab na kallonta ta madubi yace "Ummu ain't you interested with our conversation" a takaice tace "Buh you told me to be mute always while driving" Ashraf ya bude hannu yace "Abbu forget things easily" Abuturrab yyi murmushi yana shafa kansa yana son ce mata ta gwale sa gaban yaransa amma bai san da wani yare ba, turancin suna ji, Hausan ma suna ji, Larabcin ma ji suke, can dai a hankali yace "Alryt, i remember now" Har suka isa gidan Col twins din basu bar jefa ma Dad dinsu tambayoyi game da kakan nasu ba, A waje yasa Noor tayi parking, Ya bude motar ya fito, yan biyun basu sakko ba sai da suka manna ma momma dinsu kiss tayi murmushi ta rungumesu gaba daya tace "Ku yi behaving kan ku kun ji, Abbun ku ya mance bai gaya maku ba har da bulalan dukan yara idan suka yi misbehaving grandpa ke da shi, duk suka yi shiru suna kallonta Arshaq yace "But, is he going to cane us also?" Ta hade rai yace "I didn't communicate with English" Ashraf yace "Toh xai doke mu mu ma?" Tace "Ehh idan ku ka yi rashin ji amma, boys kar ku yi fada don Allah, barin kai Arshaq, duk wanda yyi fada a gidan baxae sake xuwa ba, maza ku bi bayan Abbu, ku gaida min grandma kima" ba musu suka sauka motar suka bi bayan Abban su, bbu kowa gidan ynxu bnda Ilham duk biyun sun yi aure lst yr, masu gadi Abuturrab ya hada da kayan boys din yace su kai masu ciki, su kuma yana kallonsu da larabci yace su bi bayansu kuma suce da Grandpa yana gaishe sa, duk sai yaga mood din su ya canxa ya duka yyi kissing dinsu a forehead yace "Grandpa will be glad seeing his grandboys, immediately you get in hug him nd give him a kiss before greeting him, go now" sake su yyi suka bi bayan soldiers din suna daga masa hannu, yyi murmushi ya mike ya koma gun mota, Mami ce ta fara ganin yaran ta fito daga kitchen, suna ganinta suka nufeta da gudu suka rungumeta suka ce "Grandma we came for holiday" sosai tayi farin cikin ganin jikokin nata ta rungumesu gaba daya tace "Ohhh Welcm my boys, ina Abbun naku" Ashraf yace "Ya tafi da Ummu" tace "Maa sha Allah, Ku xo ku gaida grand dad" daga haka ta ja su xuwa parlon col ta bar su nn bakin kofa tace su shiga, duk suka shiga parlorn da sallama, Col dake waya ya juya yana kallonsu, katse wayar yyi ya ajiye ya cire glass din idonsa yana kallonsu da mmki, duk suka karasa inda yake da gudu suka rungumesa a tare suka manna masa kiss a forehead da murnan su suka gaishesa da larabci kmr ynda Abbu yace masu, murmushi ne yyi escaping lips dinsa ya rungume su shi ma da larabcin ya amsa gaisuwarsu yana tambayarsu daga ina suke, nn suka fara yara masa, tun yana tsintar yaren yana gane abinda suke cewa har ya daina, dariya yyi sosai da turanci yace shi kam baya jin Arabia, Ashraf yace "Oops but Abbu told us u don't understand lingua franca, only Arabic" ya rungumo yaran yace "He is just pulling ya legs boys" nan suka dinga hira da kakan nasu with English, Arshaq ya dage sai ya nuna masu bindigarsa da kayan soldiers, shi kam murmushi kawai yake yace To xai nuna masu da daddare, Mami bata taba xaton Col xai ji da yaran kmr ynda yake ji da su ba, in dai ba fita me nisa xae yi ba to da su xai fita, in ko yana gida suna makale da shi suna masa shirme abinci ma tare yake ci da su, har ransa yake son yaran wnda ya kasa boye hakan, duk bayan sllhn asuba shi ke masu karin qur'an, tun da suka xo gidan bai taba ce masu su tashi su yi sllh ba sai dai idan bacci suke, da lkci yyi xa su yi alwala su tafi masallaci tare da shi, a tare yake kwana da jikokin nasa a bedroom dinsa, tsakaninsu da Mami sai dai tayi masu wanka ta shirya su, a haka har hutun su ya kusa karewa, shopping ba na wasa ba Col yyi masu, ana gobe xa su koma makaranta ya umarci driver da ya maida su gida, suka ce inaa sai dai Grandpa
*Haske writers asso*
💫 *Noorul Huda*💫
By khaleesat Haiydar📚✍🏻
103.....
Duk ynda Col ya so yyi convincing dinsu Driver ya kai su k'in amincewa suka yi, hakan yasa ya shirya ya dau makullin motar sa, Mami da Ilham suka kai kayan boys din cikin mota, duk suka yi kissing Mami suka ce "We will miss you grandma" Murmushi tayi tace "I will miss you also boys" daga haka suka bude front seat xa su shiga ilham tace "Oh nice baxa ku yi miss ba ko?" Dariya suka yi Arshaq yace "Alryt cum closer" ilham ta karasa kusa da su ita ma suka yi pecking dinta suka ce "We'll miss you aunt" tace "Better" Col ya bude driver seat ya shiga Mami ta xagaya tace "You didn't ask for the Address col" ta gefen ido ya kalleta yace "Da yake ke kika siya fili gun kika gina gidan" yar dariya tayi tace "A'a ba sai an hada da baka ba ai" Tada motar yyi su Arshaq suka dinga d'aga ma Mami da ilham hannu har motar ya bar gidan, Ashraf yace "Grandpa would we be cumin here for our next holiday?" Arshaq yace "Yes grandpa, we love it in here" Col yace "It's left for your papa" suka yi shiru, Ashraf yace "We will convince him in sha Allah" murmushi Col yyi yace "But how old are my brave boys?" Arshaq yace "Ohh i am eight yrs old, while he is seven" ya karasa yana nuna Ashraf, naushi Ashraf ya kai masa ya hade rai yace "How dare you say u re older than me, we re of the same age grandpa" lallaba su Col yyi suka hakura, har dai ya isa gidan Abuturrab, Ashraf yace "Waow hw did you knw our dad's home grandpa" Col ya kallesa yace "He is my Son just as he is ur dad..." Arshaq yace "But for all this while why didn't you cum to see him" Ashraf yace "He once told us that u re angry with him, why is dat grandpa...." Murmushi kawai Col yyi yace "He lied" Arshaq yace "Noo our Abbu doesn't lie" bude motar Col yyi ya fita har lkcn murmushi yake, su ma suka fito ya fiddo masu tsarabar su, tuni mai gadin gidan ya karaso yana gaishesa ya amsa ya mika masa babban ledan hannunsa yace "Ka shiga da su" Arshaq yace "Grandpa ain't u cumin in with us" yace "Yes am nt" da damuwa Ashraf yace "But why?" Yace "Am in a haste u see" Arshaq da har ya bata fuska xai yi kuka ya koma cikin motar yace "Ni ma baxan shiga ba, i am going bck with you, Ashraf cum in" Ashraf ya shiga motar shi ma, dariya yaran suka basa ya dake yace "But.... Ohk ohk am sorry boys ku fito ku kira min Abbun naku am waiting here" Ashraf na nuna masa seven fimgers yace "Grandpa we re seven yrs old" dariya Col yyi yace "Meaning?" Yace "Xaka mana" Arshaq yace "Pls grandpa let go in togeda so u can meet our Ummu" Col dai rungume hannu yyi yana kallonsu, can ya ciro makullin motar ya karbi ledan hannun mai gadin ya nufi gate din, yaran suka fito da sauri suka bi bayansa ya rufe motar, su suka fara shiga parlon snn shi ma ya shiga, dai dai sakkowar Abuturrab kasa, tsaye yyi yana kallon Abban sa ya kasa karasowa cikin parlorn, yaran suka tafi da gudu suka rungumesa da Arabia suke ce masa sun dawo da grandpa, murmushi ya kirkira yace "Yea i saw him" daga nn suka rike hannunsa suka dawo parlon gaba daya, Arshaq yace "Abbu, grandpa denied being angry with you, he said he is nt" Abuturrab yyi tsuru yana kallonsu, can ya kalli Abban sa da ya kasa boye murmushin sa, ya xauna kansa a kasa yace "Ina kwana Abba" Col yace "Alhmdllh" Arshaq yace "Abbu we love ur dad" murmushi yyi yana gyada kai, can ya mike yace "Bari in kirata Abba" daga hka ya wuce sama, Ashraf ya tafi fridge ya dauko ma grandpa din nasu ruwa Col ya karba yana murmushi ya manna masa kiss a goshi yace "Thank my boy, ba ku je kun gaida mum ba" Ashraf yace "Xaka wuce idan muka je upstairs" Kwance Abuturrab ya tadda Noor, yyi tsaye bakin gadon yana kallonta, can ya xauna ya kai hannu fuskarta a hankali yace "Wife" bude ido tayi yace "Ur boys are back, ki daure ki xo ku gaisa da Abbana" ta mike xaune tace "Da gske?" Yace "Yea wife" hijab ta dauka suka fita a tare, nesa da Col Noor ta durkusa ta gaishe sa, ya amsa yana tambayarta gida, su Arshaq suka tafi suka rungumeta suna cewa "Ummu mun dawo, Grandpa is very lovely" murmushi kawai tayi bata ce komai ba, Col ya mike yana kallon yaran yace "Hope i am free to go now" suka koma gunsa suka yace "Yea grandpa, we wish to spend our next holiday with you" dubu goma ya ciro aljihunsa ya damka musu dubu biyar biyar, da farko kin karba suka yi har sai da Abuturrab yace su karba, snn Col ya bar parlon bayan Noor tayi masa Allah kiyaye, yan biyun kuma na daga masa hannu, Abuturrab ya bi bayan Abban nasa, Arshaq ya dago kan Noor yace "Ummu are you sick" tayi murmushi tace "Why did u ask?" Ashraf yace "You look pale" tace "I am getting better now" mikewa tayi ta wuce sama da boys din nata. Da daddare Noor na kwance Abuturrab ya shigo dakin bayan ya samu su Arshaq sun yi bacci don tun dawowarsu suke ta basa lbrin holiday din su, da abubuwan da Abbansa yyi masu, da wajajen da ya kai su, ya cire duvet din jikinta yace "Tun da baki son allura ga drugs na siyo maki" tace "Ni nace maka i don't need anything, i will be fine" yace "Kin ga fa xan kira mum in hada ki da ita, you've being sick tun shekaranjiya kin ki yrda ki sha magani" kallonsa tayi tace "Toh fa na ce maka i will be fine" ya kamo hannunta yace "But ni baki taba rashin lfya na baki magani ki ki sha ba wife, tell me what ur problem is" mikewa xaune tayi tace "My problem is baxa ka sake xubar min da ciki ba" daga haka ta sauka kan gadon ta nufi kofa, ya bi ta da kallon mamaki har ta fita, lkci daya jikinsa yyi sanyi ya kuma ji kunya ba kadan ba, dafe kansa yyi na kusan minti biyar, can ya dago ya mike ya fita dakin, wani bedroom daban ya sameta duk ya kasa barin su hada ido ya xauna yace "Am sorry Noor, but it's nt my fault" tace "It's mine then" ya girgixa kai yace "No baby, i have my reasons for Aborting ur pregnancy" bata ko kallesa ba yace "Ki yi hakuri don Allah" tace "Nayi amma ni baxa ka xubar min da ciki ba" yace "I have to dear, ba kuma da son raina xan yi haka ba" tace "Toh sai dai ka kashe mu baki daya" rasa abinda xae ce mata yyi, can ya mike ya fita daga dakin. Washegari da safe shi ya yi ma boys dinsa wanka ya shirya su cikin uniform dinsu, ya hada masu shayi da bread nd butter, suna gamawa ya dau makullin mota xai ajiye su schl, Arshaq yace "Abbu we've nt seen ummu" Ya shafa kansa yace "She's still sleeping" Ashraf yace "Can we go in and see her" sake su yyi yace "Alryt" duk suka shiga bedroom dinta, tana kwance idonta biyu suka karasa kan gadon duk suka gaisheta tace "How r you two" Arshaq yace "We are fine, Abbu told us u were sleeping" ta gyada kai tace "I just woke up" daga haka tace su tafi kar su yi late, suka daga mata hannu suka bar dakin, ko da Abuturrab ya dawo daga kai su makaranta Noor na daki har lkcn, sai da ya gama shirin fita aiki snn ya shiga dakin sai tayi kamar bacci take, hakan yasa yyi wucewarsa kawai, yana office ranan Hajiya Mariya ta kirasa, bayan sun gaisa tace idan ya tashi office ya biyo gidanta, murmushi yyi bayan ya ajiye wayar don yasan sauran, ae kam yana xuwa gidan da yamma abinda ya xarga ne ya faru, ya jira ta gama fadan ta snn yace "Amma mum kin san ynda muka yi da Abba da yakumbo" tace "Aikin bnxa kafi tsoronsa a kan ubangijin ka knn..." Shiru yyi bai ce komai ba. Laulayin da yafi na cikin su Arshaq wahala Noor ke yi, duk ta fita hayyacinta, gashi ko wani irin taimako xai bata na medication nunawa take bata so duk ta ki yrda da shi, hakan yasa Hajiya Mariya tasa wata kawarta likita ke xuwa gidan dubata tana bata medication ynda ya kamata don ita ma ba yrda da shi tayi ba, Abuturrab kam ya xama d'an kallo, yaran biyu duk Hajiya Mariya ta maida su gunta, Ilham ce ta xauna da ita tana taimaka mata aikace aikacen gidan, kafin watanni hudu Noor ta fara samun kanta har lkcn ko paracetamol bata yrda ta sha idan Abuturrab ya bata, sosai take kewan yaranta da Abbanta, don tunda Hajiya Mariya ta tafi da su shi ma ya daina xuwa, ana haka har watan haihuwar ta ya tsaya, ita fa har xuciyarta bata yrda Abuturrab ya amshi haihuwarta ba kuma kiri kiri ta gaya masa, ya saki baki yana kallonta, can yace "Ko sbda me?" Tace "Haka kawai ka kashe min baby tunda ba so kke ba" bai ce komai ba don bai ji ddin hakan da tace ba, har ta mance da xancen yace "Toh ko na kashe babyn ai nawa ne" bata kallesa ba bare ta tanka sa, ranan da ta fara nakuda axaba yasa ta mance da abinda ta fada masa na cewa kar ya xo kusa da ita idan xata haihu, kuma a gida da taimakonsa ta haifi tsalelliyar yar ta mace daren friday, bbu abinda babyn nn ta mance na Noor kmr tayi kaki, don har ta fi yayinta maza kyau ga hanci maa sha Allah fara tass da ita, farin cikin da Abuturrab yyi a daren nn ba a magana, sai da ya kintsa su yana murmushi yace "Toh gashi har ke ke cewa in taimake ki wife, sai naji baki ce aje asibiti ba" kunya ya kamata ta dauke kanta tace "Ni bn ce haka ba..." rungumeta yyi ya lumshe ido yace "Gaskiya baby kina da dauriya ssai, haka kika yi da xaki haifi su Arshaq?" Tace "Ka tambayesu xa su gaya maka" ya ja hancinta yace "Kin san carbon copy dinki ne a cikin ki shi yasa kika dage sai kin haifeta ko" murmushi kawai Noor tayi tana kallon cute babynta dake bacci. Ranan suna dai Baby ta ci sunan Ummin Gombe wato Hajarah, tun ana gobe suna Anty Maryam ta xo gidan, abun mamaki har da Yakumbo a xuwa sunan fa, su Arshaq suka sa ta gaba kamar yanda Hajiya Mariya tace masu ai ba fa ta jin ko wani yare bnda larabaci a duniya, nn suka dinga yara mata tana kyalkyala dariya uwa tana jin abinda suke cewa, nan kuwa ji take kamar an sa ta aljanna jin yaren da jikokin nata ke mata da fararen jallabiyarsu da hula, Kaya ba na wasa ba Ummi ta taho ma da takwararta me kyau, Ummar su Ahmad da yaranta mata gaba daya suka xo sunan su ma, aka yi suna na gani na fada aka watse lafiya, kaya ba na wasa ba babyn ta samu, sai bayan suna da sati daya ko me Col ya gani sai ga shi ya xo ganin 'yar matar tasa me kyau, dubu hamsin ya ajiye ma babyn da ake kira da *Noorul Huda* Abuturrab yaji ddin xuwan Abban nasa. Bayan suna da wata guda Abban Noor ya taho ganin matar sa shi ma. Little Noor na da wata Huda su Arshaq suka kuma samun long Vacation, murna suka yi tayi suna jiran jin inda Abbunsu xai ce xa su for the holiday, Noor na bedroom dinta tana shirya little Noor Abuturrab ya shigo dakin, xaunawa yyi kusa da su yana jan Cheeks din daughter sa yace "Ummu am thinking Boys din su je Holiday gun mum, i mean ur Mum" dago kai tayi tana kallonsa ya buda ido yace "Yea, it's nothing wife, naga yaran na da wayo sosai kuma ai Abba na gidan" bata ce komai ba ita dai ya dau little Noor dake masa dariya ya mike yace "Sai ki hada masu kayansu" daga haka ya fita daga dakin, Noor duk jikinta yyi sanyi don ita kam tsoron mum dinta take ynxu. Daki Abuturrab ya samu su Arshaq suna hada bricks, ya xauna duk suka dawo kusa da shi yace "You two are going to ur grandma's place for the Holiday!" A tare suka ce "which?" Yace "Your Ummu's mum" Xaro ido Arshaq yyi yace "Waoww, but ummu once told me she's nt like us, i didn't get what she meant then, is it that she is not Human?" Ashraf yace "Yeaa i also remembered Ummu saying that" Abuturrab yace "Noo, she is Human like us..." Arshaq yace "But Ummu have never for once said she is going to her mum's place" Abuturrab yace "It's because her mum is angry with her just as my dad was with me sometimes ago" Arshaq yace "That's strange, why are ur parents both angry with you?" Abuturrab da yaji tambayar har tsakar kansa yace "I think we need to close that chapter now, and as i was saying, i knw Ur Mu'allima's and Mu'allim's have taught you what is prohibited nd accepted in Islam, i want you two to abide by it while in Grandma's place.
*Haske writers asso*
💫 *Noorul Huda*💫
By khaleesat Haiydar📚✍🏻
104......
Kamar wancan lkcn Noor ce ke driving din sai dai gaba daya hnklinta bai jikinta, Abuturrab kuma na xaune da yaran nasa uku a bayan mota, Baby Noor na kafarsa su kuma suna gefensa, Arshaq ne yyi breaking silence din yace "Abbu, will grandma be happy seeing us?" Abuturrab ya ja hancinsa yace "Of course my boy, she will be very very happy" Ashraf yace "Are we going in alone?" Abuturrab ya shafa kansa yace "Yes boy, lastly i want you two to behave ur self while with grandma" kai kawai suka gyada masa, suna isa gidan Noor tayi parking tana kallon Abuturrab, ya sakar mata murmushi ya mika mata Baby Noor ya fita daga motar don ciro kayan yaran a bayan mota, Noor na kallon twins dinta tace "Kar ku yi ma Grandma rashin ji xata yi caning din ku, kuma bata son surutu dayawa ko kuma ku fadi abinda ba a tambaye ku ba, kuma ku ce da grandpa ya dinga k'ara maku karatu" Duk suka ce "Ohk Mum" 'yar kanwarsu me kyau suka yi ma kiss suka sauka daga motar ta bi su da kallo tana murmushi, Mai gadi Abuturrab ya ba kayansu yace ya karasa da su ciki, suka rungumesa suka ce "We wil mis u Abbu" Yace "I will miss my children also" daga haka ya mike suka bi bayan mai gadin. Comfort ce kadai kwance parlon tana kallo, suka tsaya suna kallonta kamr ynda ita ma ke kallonsu, Arshaq yace "Good afternoon," ta mike xaune har lkcn tana kallonsu, Ashraf ya kalli d'an uwansa yace "That's strange, i don't think she understands English" dai dai fitowar Rachael daga kitchen tana cewa "Gashi can kije ki debi abincin na gama" kallon gun da Comfort take kallo tayi ta ga yaran tsaye, sai ita ma ta tsaya kallonsu, Arshaq ya karasa parlon yana kallonta a hankali yace "Sorry plss, are u our grandmum?" Rachael tace "Jesussss christ of Nazareth, Comfort these are Samantha's Children, they are her boys" Arshaq ya kalli Ashraf da ya karaso ciki shi ma murya can kasa yace "May be Ummu nd Abbu mistook this to be d house" Rachael ta karasa da sauri ta rungumosu cikin mugun farin ciki tace "Yess my boys i am ur grandmum, this is me, who brought you two here?" Ashraf yace "Our Mum nd Dad" ta kalli kofa da sauri tace "Where are they?" Yace "They are gone, they brought us here for holiday" rungumesu ta kuma yi tace "You are welcm my children, you are welcm, you re welcm" Daga haka ta ja su xuwa sama baki har kunne tana cewa "I am ur grandma children, i gave birth to ur mother" Dakinta ta shigar da su ta xaunar da su kan gado tace "Let me get you two something" tana fita dakin Arshaq yayi tagumi, bayan mintoci yace "I don't think i will like it in here" Ashraf dake ta kare ma dakin kallo yace "Why did u say so?" Shigowar Rachael yasa Arshaq bai ce komai ba, ta mika masu lemo a glass cup suka karba ta xauna gefensu tana washe baki tace "So what shuld i cook for my twins" Ashraf yace "Noodles.." Ta kalli Arshaq tana shafa kansa tace "And you boy?" Yace "Same" tace "Do you take it with egg?" A tare suka gyada mata kai ta mike ta kunna masu TV tace "Let me get it right away for you two" daga haka ta fita, Arshaq ya dau remote ya maida channel din xuwa na Cartoon. Bayan minti sha biyar sai ga Rachael ta shigo da plate na Noodles Comfort na biye da ita da wani plate din ko wanne da kwai uku a kai, ta ajiye masu kan Carpet tana kallonsu tace "It's ready boys" sakkowa suka yi kasa, Comfort na murmushi tace "Welcm boys" duk suka kalleta suka ce "Thank you" Rachael ta xauna ita ma tana kallonsu cike da so har suka fara cin abincin, tace "I am still yet to knw d names of my handsome boyss" Arshaq yace "Grandma talking while eating is a bad table manner..." ta wara ido tace "Ohhh dats very true love" Comfort ta xauna gefen gado tana murmushi, Rachael bata kuma ce masu komai ba sai tagumi da tayi tana kallonsu, wai ynxu kyawawan yaran nn yaran Samanthar ta ce, ita ta haifesu, ta lumshe ido tace "Thank you lord jesus for providing me with this lovely kids into my family, father God i commit them into ur holy hands, nd i cover every part of dem with d blood of jesus" daga Arshaq har Ashraf sake baki suka yi suna kallonta, can Arshaq ya xaro ido yace "What r u doing grandma?" Ta bude ido da sauri tace "Am praying for you sweet kids" Ashraf ya ajiye fork din hannunsa yace "That's odd...." Xata yi magana wayarta yyi ringing ta mike da sauri ta dauka taga Sarah ce ke kiranta tana dagawa cike da farin ciki tace "Sarah yau ga yan biyun Rebecca sun xo min hutu" daga daya bangaren Sarah tace "Haba Sister?" Rachael tace "Am telling u Sarah, ki xo ki gan su" Sarah tace "toh gani xuwa" daga haka ta katse wayar ta fita dauko ma jikokin nata ruwa tana murmushi, ana gama kiran La'asar Twins din suka mike daga gun abincin, Rachael tace "Ba ku cinye ba ai yarana" Arshaq yace "We are full" Comfort ta hade abincin waje daya ta fita da su, Ashraf yace "Grandma we want to perform ablution" daga sama har kasa take kallonsu can tace "We don't do that here...." Arshaq yace "i dnt get you?" Ta mike tana xaro masa ido tace "Ga cartoon ana yi kuyi kallon ku" Ashraf yace "But it's time for prayer" Arshaq ya nufi kofar da yake tunanin toilet ne ta rikosa tace "Kai cikin sanyin nn xaka xuba ruwan sanyi jikin ka, do you want to catch cold" ganin ynda yaran suka tsaya kallonta ta d'an bata fuska tace "Ai shknn bari in sa maku ruwan dumi, amma ni bni da kettle a gidana" Ashraf yace "But why is that, didn't you use to pray?" Ta rike kugu tace "I dnt pray d way u pple do, it's very wrong" toilet din ta shiga ta xuba masu ruwan dumi a bowl ta dawo tace su je su yi alwalan, ba musu suka shiga toilet din su biyu, ta xauna tayi tagumi tana kada kafa, wato har sun cusa ma yaran nn musulunci ko, to baxa ta sa6u ba, tana kallonsu suka fito suna dube duben darduma, Arshaq yace "Grandma praymat?" Tace "I've told u pple i dnt pray d way u do" A tare suka ce "Then hw do you pray" durkusawa kasa tayi ta hade hannayenta ta rufe idonta ta shiga kwararo addu'ar coci tsakaninta da Allah, Suka fashe da dariya ta bude ido tana kallonsu Arshaq yace "That's weird, i think that shud be d barbarians way of worshipping, it's just strange, that's not hw islam teaches us to pray to Allah" Ashraf yace "Anyway, where can we find d nearest mosque grandma" sake baki kawai tayi tana kallonsu, can ta mike ta hade rai sosai tace "yanda kuke naku addu'ar ne kalan na babarians, c'mon ku wuce ku xauna bbu inda xa ku fita, you two are going no where, ga cartoon nn na sa maku" Arshaq yace "I said it, i knw i will never like it here, am gonna give dad a call ryt away to cum take us away from this goddam home, am nt staying any longer...." yana magana ne kamar xai yi kuka, Ashraf ya rungume hannayensa ya juya baya yace "Yaa Allah" Rachael ta karasa da sauri ta rungumo Arshaq jin furucin sa tace "No, no don't say that son, u will like it much here, grandma loves you a lot, dnt wrry let me escort u two to d mosque" daga haka ta kama hannunsu ta fita dakin da su, Comfort na tambayarta inda xata bata tanka ta ba har suka fita gidan, masallacin unguwar ta kai su suna shiga ta nemi wani dakali nesa da masallacin ta xauna tana jiransu, kowa ya xo wucewa sai ya kalleta, har aka idar da sllh sai gasu sun fito, suka taho gun ta, Arshaq yace "Ohh you waited for us grandma" ya manna mata kiss a goshi yace "I love you Grandma" rungumesa tayi tace "I love you my handsome" daga haka ta mike ta kama hannunsu ta dau hanyar gida duk aka bi su da kallo, daren ranan da Mr David ya dawo shi ma ba karamin farin cikin ganin jikokin nasa sun xo hutu gidansa yyi ba, yaran suka ji ddin ganinsa sosai su ma, a kwanakin yaran biyu a gidan David har mamakin matar tasa ya dinga yi ynda duk abinda yaran suka nuna suke so shi take yi masu ko da kuwa na addinin islam ne, ji take kmr ta mayar da su ciki don so, bata sake gigin kkrin hana su yin sllh ba, church kuma tun da ta kai su suka dinga rusa mata kuka su gida xa su koma bata sake kai su ba, Rosary ma da ta sa masu suka nuna basa so bata sake sa masu ba, in dai Mr David bai nn ita ke raka su masallaci yin sllh, har tanadar masu ruwan alwala take a flask, ko kadan bata son bacin ran jikokin nata, yaran suka saki jikinsu sosai a gidan, suma kuma sosai suke sonta kamar yanda take son su, ita ke coaching dinsu a karatun bokonsu, kullum dare kafin su kwanta sai sun yi karatun qur'an, wani lkcn ta xauna ta sa su gaba tana kallon ikon Allah ba dai dama tace baxa su yi ba su tada mata bori in dai su yi bacci ta kan dauki bible ta sa a tsakankaninsu, duk gidan kawayenta sae da ta bi ta nunnuna su, har addu'a take kar hutun ya kare don yaran sun yaye mata bakin cikin da ke kunshe a xuciyarta na shekara da shekaru, ana saura kwana biyu xa su koma makaranta kuwa bbu abinda ta mance bata siya masu ba, Mr David ke driving din ranan lahadi xa a maida su gida, Rachael na xaune bayan mota da yan biyun, Ashraf yace "Am seriously going to miss u grandma..." Ta jawo sa jikinta da damuwa tace "will miss u also prince" Arshaq yace "Grandma ki dinga xuwa gidanmu plsss" Tace "I can't withstand d sight of ur mother" Ashraf ya kalleta yace "Why?" Ta tabe baki tace "I just don't want to see her" Ashraf ya janye jikinsa a nata, Arshaq yace "But where did she she wrong you?" Rachael tace "When u get home as her" shi dai David bai ce komai ba, har suka isa gidan bbu wanda ya sake cewa komai, Ashraf ya bude mota xae fita, Rachael ta rikosa tace "Without even a goodbye my prince" ya hade fuska yace "Not when u can't withstand d sight of my mother, i will neva spend my holiday with you again" da damuwa tace "Nooo, Am sorry prince, may be i shud'nt have said that...." Yace "Then cum in nd meet my mum" Arshaq yace "Yess plss, and little Noor also, she's so beautiful grandma, i knw u will love her" Rachael dai sai kallonsu take, Ashraf yace "You're nt cuming right?" ajiyar xuciya ta sauke tace "Alryt" daga haka ta fito tana kallon Mr David dake ta murmushi, ta hararesa ta bi bayan yaran dake jan ta xuwa cikin gidan nasu.
*Haske writers asso*
💫 *Noorul Huda*💫
By khaleesat Haiydar📚✍🏻
105.....
Babu kowa parlon sai Tv dake a kunne, Noor dake bedroom dinta da little Noor ta fito jin an bude kofar parlor, dakin Abuturrab ta leka ta gansa xaune yana operating laptop ya dago ya kalleta yace "Someone is at d door" bata ce komai ba ta sauka, kasa karasawa parlorn tayi ganin Mum dinta tsaye, Arshaq da Ashraf suka taho da gudu ganinta suka rungumeta suna cewa "We re back sweet mum, our holiday was superb with grandma" Rachael kam sai wani kallo take mata na tara saura qtr, Arshaq ya ja hannun mum din tasa yace "Ummu we came with grandma" Noor sai kirkiran murmushi take ta karasa parlorn Ashraf ya karbi little Noor ya kai ta gun Rachael yace "Take a look at our little sis grandma" Rachael ta karbi yarinyar da ta fara bata fuska xata yi kuka, kallonta kawai Rachael ke yi don sak Samantha tana karama, xaunawa tayi kan kujera har lkcn tana kallon Noorul Huda, Arshaq yace "Isn't she cute?" Murmushi Rachael tayi tace "Yess she is" Arshaq yyi peck din kanwartasa yace "Little Noor meet grandma for d 1st time, she's d best, she took very good care of us during our stay with her" Ashraf yace "Ummu, Grandma came to see u, go to her" Rachael ta daga hannu da sauri tace "Noo, noo i came to see my little angel" Arshaq ya bata fuska yace "With mum also" Rachael ta kirkira murmushi tana shafa kansa tace "Yes Prince" da kyar Noor ta xauna kasan carpet tana kallon Uwar tata tace "Ina yini Mum" Ba tare da Rachael ta kalleta ba tace "Eh lafiya lau" Abuturrab ne ya sakko parlon jin muryan kids din nasa, ya karaso parlon yana kallon Mum din Noor ya dai yi karfin halin cewa "Ina yini mum" ta kallesa ta watsa masa harara tace "Lafiya lau" Mikewa Noor tayi ta tafi fridge dauko ma mum dinta ruwa, Rachael kasa barin gidan tayi sbda jikokinta, duk da taki sake ma Noor bare Abuturrab fuska, gaba daya su Arshaq na xagaye da ita da yar kanwarsu da Rachael taji kmr ta gudu da ita amma ba dama, ji tayi dama ta dauwama har abada tare da yaran sbda so, su suka tilastata ta ci lunch din jollof din Cous Cous da yaji kayan hadi wanda Noor ta yi, sai kusan karfe uku ta bar gidan, bbu ynda Abuturrab bai yi yyi dropping dinta ba amma taki yrda don tuni Mr David ya wuce, wannan ne mafarin fara kiran Abuturrab da Rachael tayi bayan ta karbi numbersa gun Mai gidanta, kusan kullum sai sun yi waya da yan jikokin nata, wani lkcn Noor kan karbi wayar ta gaisheta duk da ba wani amsawan kirki take mata ba amma tana jin dadin yanda take ji da grandchildren dinta, bayan duk sati biyu ta kan xo gidan ranan asabar amma iyakarta balcony ta ba yaran abinda xata basu tayi wucewarta, hakan yasa Noor ta fara kwadayin xuwa gida ko da kuwa da yaran ne, kilan sanadin hakan su samu masalha da mahaifiyarta, hakan kuwa aka yi ranan wata friday Noor tace da Abuturrab tana son xuwa gidansu tayi weekend da kids din nata, da kansa ya kai su gaba daya gidan, har ya shiga ya gaida mum din shi ma, Rachael tayi murnan xuwan su har ita Noor din amma a fili nuna cewa murnan xuwan yaran kadai tayi, bbu abinda ta rage su da shi, duk da fa magana me tsayi bata yrda ya hadata da 'yar tata, ranan lahadi da safe Noor na daki tana bacci Rachael ta shigo tana tafe hannu tace "Toh nonbelievers ni dai xan wuce church, ga yara can basu tashi ba ki dinga kula min da su har in dawo, idan kuma suka tashi ga breakfast na hada masu a kitchen, wankan ma ba sai kin masu ba xan masu idan na dawo" bata jira cewar Noor ba ta fita, Noor tayi murmushi ta koma ta kwanta, a yammacin ranan little Noor ke ta xaxxabi Rachael duk ta rikice nan ta samo Rosary ta rayata mata a wuya, Noor dai ta kasa cewa komai kuma bata cire ba, Arshaq na kyalla ido ya gani ya cire yana cewa "Grandma am begging you plss don't put this on our little sis again, it's a burden" Rachael da ke ta kallonsa ta kwace abarta tace "Alryt give it to me" daga haka ta bar masu parlon, Noor tayi murmushi tana kallon Arshaq da ya koma ya ci gaba da kallonsa, hka suka karashi weekend din a gidan Abuturrab ya xo da daddare ya daukesu suka koma gida. Bayan sati biyu sai ga Sadeeq ya kawo ma Abuturrab Katin aurensa, Abuturrab ya taya sa murna sosai yace "In ji dai Zainab ce?" Dariya Sadeeq yayi yana rungume da Namecy dinsa Arshaq yace "Yea ta ci sa'a ita ce" Abuturrab ma yyi dariya yace "Ka dai ci sa'a" Sadeeq yace "Assiddiq nake son ka bani yyi mata xaman daki" Abuturrab na shafa kai yace "Na baka" Sadeeq yace "Am jet serious fah, ita kuma little Noor ina nan ina jiran girmanta kishiyar Zainab ce tun yanxu ka ji" Abuturrab ya wara ido yace "Me xata yi da tsoho?" Da yammacin ranan Abuturrab yasa sadeeq ya rakasa kasuwa ya siya bike sabuwa dal, Sadeeq sai mamaki yake bai dai ce masa komai ba sai da suka bar kasuwar yace "Kai kuma me xaka yi da bike frnd?" Abuturrab yace "Mu je kai dai kaga, dama kai nake jira ka xo" a gate din wani gida Abuturrab ya tsaida bike din ya sauka Sadeeq ma ya sauka, Abuturrab dai sai kallon gidan yake, yana kkrin tura d'an gate din gidan wasu matasa biyu suka fito, Abuturrab ya kare ma wanda ke facing dinsa kallo daga sama har kasa snn yace "Ka gane ni kuwa?" Mutumin na gyada kai yace "Kwarai kuwa na gane fuskar nan" Abuturrab ya kama hannunsa ya sa masa makullin bike din yace "Ga Machine dinka na dawo maka da shi, so srry for the inconvenience" kallonsa kawai mutumin ke yi ya kasa cewa komai, har Abuturrab ya juya xai wuce mutumin yace "Nagode kwarai da gaske" Sadeeq dake ta jinjina lamarin yace "Tab ai in nine tuni na mance, sai dai in biya sa a aljanna" dariya duk suka yi mutumin yyi exchanging Number da Abuturrab ya rakasu suka hau tricycle xa su koma gida, washegari Sadeeq ya koma Uk, don can yake rayuwarsa. Noor na shirin kwanciya Abuturrab ya shigo da Huda dake bacci ya kwantar da ita kan gado, ya karasa kusa da wife din tasa ya rungumota ta baya ya lumshe ido yace "Kinsan me Ummu?" Tana kallonsa ta mirror tace "Sai ka fada Abbu" jan hancinta yyi yace "Xa mu je Convocation din fatima Gombe" Bata ce komai ba bata sake kallonsa ba kuma ta shiga kkrin daure gashinta, ya karbe ribbon din yace "Am talking Ummu" still ba tare da ta kallesa ba a takaice tace "I don't think am going, baxan je ba" yace "But why? Naga kids din na midterm break ranan" A d'an fusace tace "Toh ku je mana ni baxan je ba" murmushi yyi sosai yace "Har bikin nata knn, cos an gama convocation din da kwana biyu bikinta" sai a snn ta kallesa, can kuma tace "Toh Allah ya kai mu, wa xata aura?" dariya yyi yace "Baki ji kunya ba Samhata?" Murmushin tayi ita ma tace "Kunyar me?" Yace "Kin fini sani" ta juyo ta wara masa ido tace "Ohh baka son ina kishin ka knn?" Lumshe ido yyi yace "So kai" ta rungumesa tana murmushi tace "Yauwa Abban twins dina" shirye shiryen xuwa gomben suka dinga yi, ranan talata kuwa suka dau hanya bayan sun je sun ma iyayensu gaba daya sallama, Noor bata wani yi mamakin cewar Dr Shariff ne angon fatiman ba, suna gombe har bayan bikin da kwana biyu, Noor bata so hakan ba don kids dinta xa su yi fashin makaranta knn, ranan Monday suka sallami Ummi, Ummi tace "Anya takwarata xata kuma bin titi kuwa Son, gaskiya k'ura yyi yawa" Rabi'a dake parlon ita ma tayi dariya tace "To Ummi ki biya mata jirgi kawai" Ummi tace "Ae hakan ma xa ayi, nawa ne flight din, daga baya sai ka xo ka dau motar ka" dariya Abuturrab yyi yace "Mami ba gida xa mu direct ba ma" Tace "Ina xa ku?" Ya shafa kai yace "Xa mu biya gun wani frnd dina ne" Ummi tace "Toh shkkn, Allah ya tsare" duk ynda Ummi ta so su karbi kudin da ta ba takwararta a cewarta Abuturrab bai yrda ya karba ba, a hka suka bar gidan, Noor dai na bayan motar da yaranta dake ta game da wayar Abbun su, ganin ba hanyar Kano ya dauka ba tace "Abbu ina xa mu kuma" ta madubi yake kallonta yace "Ziyara Ummu" tace "Kai Abbu my kids r missing classes fa" yace "This the only opportunity we have wife, baxa mu dawo garin nn lkci kusa ba" tace "Buh nan da wata hudu ae bikin khadija" Yace "Duk da haka dae Ummu" bata kuma cewa komai ba, sai da suka yi tafiyar kusan minti talatin snn ta d'ago inda xa su, tace "Kai dear hw did u want this kids to cope there? Kasan ba sabawa suka yi ba" yace "Ke lkcn kin san xa ki iya copying a can? Gun da har muka samu shelter for good two days ba wajen rainawa bane madam" ta xaro ido tace "No don't misunderstand me dear, i mean they r nt familiar with place like dat" yace "Yea, experience is the best teacher, let dem go nd learn, beside tun da mum dinsu ta hakura da rice during that time su ma xa su hakura ne ynxu" murmushi kawai tayi bata ce komai ba, ya kashe mata ido yana kwaikwayon muryarta yace "Baxan iya ci ba Dr..." Hararansa tayi ta rufe fuskarta, yyi dariya sosai yace "Eh mana, then na tambaye ki to me xa ki ci wai wani *Rice* ke ga baturiya" bata san lkcn da ta fashe da dariyar ba itama tace "Wayyo bana so dear ka bari plsssss" ya wara mata ido yace "Ae sae ma yaran ki sun girma na basu lbrin" kallon kids din nata dake ta playing game tayi tana murmushi.
*Haske writers asso*
💫 *Noorul Huda*💫
By khaleesat Haiydar📚✍🏻
106.....
Har mamakin ynda Abuturrab bai mance hanyar garin Noor ta dinga yi, suna isa Rugar dai dai kofar gidansu Alto Abuturrab yyi parking, ya fito daga motar yana kare ma gidan kallo, Arshaq sai damun Ummun sa yake ina ne nn Abbu ya kawo su tace "We came for visit son" Noor ta fito motar rike da little Noor, twins din suka ki fitowa motar ko wannensu ya tsuke fuska, Noor ce tayi sallama kofar gidan taji muryar Mama Hansai na amsawa daga ciki, a hankali ta sa kafa ta shiga gidan, Hansai dake sauke sanwan rana na dumamen tuwo daga kan wuta ta mike da sauri tana kallonta, murmushi Noor tayi ta isa kusa da ita ta durkusa tace "Sannu mama" Hansai ta saki salati tana tafe hannu tace "Wa xan gani haka, yar nan kuna duniya ashe, Allah mai girma sannun ki da xuwa, sannu da xuwa" da sauri ta shimfida mata tabarma tana yi mata sannu da xuwa cike da farin ciki ta karbi Noorul Huda snn Noor ta xauna tace "Mama bani daya bace yana waje" Hansai tace "Wai yayan ki? Allah sarki ce mashi ya shigo maxa maxa, Alto ma na kewaye Allah ya rufa asiri bai fita ba, ce ya shigo" Noor tace "Toh mama" ta mike ta fita waje, Abuturrab na tsaye jikin mota ya rungume hannayensa tace "Ku shigo dear" daga haka ta juya ta koma ciki, ya bude bayan motar yana kallon su Ashraf yace "Come down" Arshaq ya girgixa kai da sauri yace "Noo Abbu we will wait for you here plss" hade rai yayi yace "I will knock you both, get down immediately now" fitowa suka yi da sauri yace "It's a promise, here will be ur next place for holiday" duk kallonsa kawai suke basu ce komai ba, ya shiga gidan suka bi bayansa, Hansai ta rasa inda xa ta sa su gaba daya don farin ciki ta ciko masu kwarya da ruwa ta kawo tana ta yi masu sannu da xuwa, Alto ma ya fito bayi ya dinga masu lale marhaba yana washe baki, ya rungumo su Arshaq yana masu fillanci duk suka tsura masa ido, yayi dariya sosai yace "Ga shi dai da ganin ku an ga fulanawa amma bakwa ji" Murmushi Abuturrab yyi a xuciyarsa kuwa yace dole ma ya fara yi masu yaren, Alto yace "Toh Maa sha Allah, Allahu ya raya ku 'yan samari, ashe dai da rabon xa mu sake saduwa Ali, Allah mai girma" Abuturrab yace "Wllh kuwa Baffa, da fatan mun same ku lafiya" Baffa yace "Alhmdllh, Alhmdllh mun gode Allah, duk lfya lau muke wllh" yana son tambayar Binta amma shakkar Noor ya hana yyi hkn, yana ta jiran ita tayi tambayar amma ta ki, Hansai ta dauko kwano tana cewa "Wllh gashi ynxu na sauke dumamem tuwo da miyar kuka sai dai ko k'ashi bbu a miyar sai waran mu ta fulani da na jefa ciki, kuyi hakuri don Allah" Noor tace "Haba Mama ba komai mun ma ci abinci fa kafin mu fito" Hansai tace "A'a ni dae bara in xubo ku ci don Allah" daga haka ta xuba masu tuwon da miya a kai ta ajiye ma Noor da su Arshaq, Abuturrab ma ta xuba masa ta kai masa, murmushi yyi yace "Godiya muke mama" Wata kyakkyawar yarinya ce da baxa ta wuce shekaru 5 ba ta shigo gidan da 'yar karamar tulu a kanta, fara ce sosai gashinta har kusan gadon bayanta, ta ajiye ruwan kanta tace "Inno gashi na debo" Sai a snn Noor tace "Mama Binta fa?" Hansai ta kalleta sai dai bata ce komai ba, Alto dake xaune kusa da Abuturrab yace "Ae Binta Allah ya mata rasuwa shekaru biyar kenan" Noor taji xancen nasa har xuciyarta ta kasa cewa komai sai kallonsa take a sanyaye, Abuturrab ne yyi karfin halin cewa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un ta rasu Baffa, Bata da lafiya ne?" Alto yace "A'a ko daya, wajen haihuwar 'yar can dai ne Allah ya karba abarsa" ya fadi yana nuna yar yarinyar dake tsaye kusa da Hansai dake matsar kwalla, Tuni Noor ta fara hawaye lkci daya jikinta yyi sanyi sosai, shi kam Abuturrab bai iya ya kara cewa komai ba sai dai tuna irin ynda ta dinga hawaye ranan da xa su bar kauyen yasa jikinsa yin sanyi sosai, bai mance alkawarin da yyi mata na cewa xa su dawo su tafi da ita birni ba, murya Hansai ya katse masa tunaninsa cikin sanyin murya take cewa "Binta ta dde bata yi aure ba bayan tafiyar ku, kullum ba dare ba rana jira take ku dawo ku kai ta birni tayi karatu kamar yanda ta ce kayi mata alkawari, da kyar dangin mahaifinta suka yi mata auren nan, ashe ta ajali ce" ta karashe maganar tana kuka sosai, Alto yace "Ka ji ta kuma...." Cikin kuka tace "To ya kake son in ce Alto" yace "Dama can wa'adin da Allah ya debar mata kenan duniya, kiyi ta mata addu'a don shi kadai take bukata gun ki" Hansai bata kuma cewa komai ba sai share hawayen da ta dinga yi, Kallon yar yarinyar dake gefenta Abuturrab yyi, a hankali yace "Allah ya ji kanta, ya rahama mata, ya kyautata na mu" Alto yace "Amin" Noor kam kasa daina kuka tayi ta rasa dalili, da ta tuna ynda ta dinga kulawa da ita taki sake mata fuska tana basar da ita sai taji duk bata kyauta ba, kukan da take yasa su Arshaq suka fara taya ta su ma, Hansai tace "Hakuri xa mu yi 'yar nn, kiyi shiru don Allah ga shi kin sa 'yan yaran nn kuka su ma, tuni na bar ma Allah komai, Binta ita kadai ya bani kuma ya karbe kayansa ba don bai so na ba, kinga ko dole in ta gode masa, ga 'yar ta nn an maida mata sunan, muna kiranta da Fatima ita na kan gani in ji ddi" Abuturrab yace "Haka ne Baaba addu'ar mu kadai take bukata, Allah ya gafarta mata" Duk suka ce Amin, Abuturrab yace "Amma ina neman wata alfarma gun ku Baffa" Alto yace "To ina sauraren ka Ali, ta me kenan?" Yace "So nake ku koma can cikin Birni da xama don Allah, xan samar maku waje, idan ya so ko wace irin sana'a kke son yi sai in taimaka maka Baffa" Murmushi Alto yyi sosai yace "Allah sarki, ban ki ta taka ba Ali, amma gaskiya ni ko kadan ban sha'awar rayuwar birni na fi son xama a ruga" Hansai tace "Haka ne Ali, ni kai na nafi son nn baxan iya xaman birni ba" Abuturrab yace "Toh shknn, Alfarma ta biyu kuma don Allah baffa kada kace a'a, so nake ka ban Fatima in hada in rike da yarana, ina son ta samu ilimi ynda ya kamata" Hansai ta d'an yo waje da ido, Alto kam murmushi yyi yace "Wani hanxari ba gudu ba Ali, kada ka mance ba mu da iko kan yarinyar nn..." Abuturrab ya katse sa yace "Mahaifinta fa?" Alto yace "Yauwa ynxu kayi magana, bayan rasuwar binta da shekara biyu shi ma ya rasu bayan yyi fama da ciwon daji" Hansai ta tabe baki tace "Dangin sa kuwa duk gantalallu ne, tun bayan rasuwar sa bbu wanda ya tako ganin halin da fatima take ciki, basu san cin ta ba basu san shanta ba, mu kadai ne gatan ta" ta karashe maganar tana matsar kwalla, Abuturrab yace "Toh don Allah ku rabu da su Baffa ku ban yarinyar nn na maku alkawarin xan dinga kawota tana maku hutu, xa ku ji dadin ta nan gaba, kar ku manta muhimmancin ilimin muhammadiyya da boko a xamanin nn da muke ciki" Baffa yyi shiru haka Hansai da ta xuba tagumi, Hansai da wasu sabbin hawayen suka xubo idonta tace "Ita daya nake gani in ji dadi ynxu Ali, idan kuka rabani da ita ya xan yi da raina?" Abuturrab ya sauke ajiyar xuciya yace "Baaba sai ki samu ko d'an 'yan uwa ne ki rike don Allah, ni dai a gaskiya ina son in ma 'yar nn abinda ke ran uwarta har ta bar duniya ku yi hakuri don Allah, sai ma mu iya xuwa da ku ku ga inda muke don lallai duniyar nn ba abun yrda bane tunda ba wai sanin mu ku ka yi sosai ba" Alto yace "A'a ni na yadda da kai Ali, Allah ya shige mana gaba, gata nan ni dai banda abun cewa kuma" ya fadi hakan yana kallon Hansai dake share hawaye tace "Ae shknn, Allah yasa mu dace" Abuturrab yaji dadin hakan yace "Yauwa baaba, in sha Allah xata dinga xuwa maku hutu har ma da yaran gaba daya" Baffa yace "Maa sha Allah, Allah ya taya ku riko" Sai kusan la'asar suka fara shirin barin gidan bayan Abuturrab ya tabbatar su Arshaq sun cinye tuwon tas, amma fa da kyar, Hansae na kwalla ta gama hada ma fatima 'yan tsummokaranta, Dubu talatin Abuturrab ya ba Alto dake ta masa godiya yana sa masa albarka, ita kuma Noor ta ba Hansai dubu goma ta kuma cire layinta dake karamar wayar hannunta ta rubuta masu number Abuturrab a takarda ta mika mata tace "Sai Baffa ya siyo layi a sa a wayar ga Numbersa nan da kun kira xa ku samu" Har bakin mota suka rakosu sai a snn fatima ta fara kuka da Fillanci take tambayar Hansai inda xa a kai ta wanda hakan yasa Hansan kuka sosai, A haka Abuturrab ya ja motar suka bar kofar gidan Noor na daga masu hannu, rarrashin Fatima Noor ta dinga yi da fillanci, Arshaq da kukan ya ishesa yace "Ohh Goodness, Ummu why are we leaving with someone's Child for god's sake? It will look as if we kidnapped her..." Hararansa Abuturrab ya dinga yi ta madubi hakan yasa yayi shiru bai kara cewa komai ba, kafin su shiga kano har tayi bacci, suna isa gida Abuturrab yyi parking ya fito, Noor ma ta fito da little Noor a hannu, su Arshaq suka fito su ma, Abuturrab ya dau fatima dake ta bacci suka shiga cikin gida.
*Haske writers asso*
07087865788 for Comment nd corrections!!! You re welcm.