*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @KhadeejaCandy
5⃣1⃣
Inna ta tsorata sosai da abunda na fada mata hankalinta duk sai ya tashi.
“Taya zaki iya shiga cikin wannan lamarin Nawwara?ke fa mace ce ba namiji ba, kuma irin wadannan mutanen hatsarine rabarsu”
“Nima abunda na ke ta tunani kenan! Ona ganin aiki zan sa Jibril ya koma sai mu koma tare kin ga duk wani taimako zan iya bashi ta nan kuma ina lurar da shi akan wasu abubuwan”
“Gaskiya Nawwara ina jin tsoro, karki je ki janyo mana wani abun na daban kuma”
“Babu komai Inna ba zan fito kiri da muzu na fada masa abunda yake faruwa ba, ta dabara zan yi”
“Kina tunanin hakan ba zai haifar da wata matsala ba?”
“Inshallah ba zai haifar ba”
Ta kawar da kai ba dan ta yarda din ba, ni kuma ina ganin bana da wata mafita sai wannan.
JIBRIL POV.
Lokacin da Noor ya ji cewar Momynsa ba zata zo ba sai duk yanayinsa ya canja ya koma cikin jin bakinciki da damuwa, duk yadda Jibril ya so kar ya bata rai sai da Noor ya bata kuka ma sai da ya yi. A gado daya suka kwanta under one bedsheet, misalin biyu da rabi na dare Jibril ya farka ya shiga bedroom ya dauro alwala ya fito ya shinfida carpet ya soma sallah nafila da a yanzu ta soma zame masa jiki.
Kuka ya yi sosai yana neman yafiyar Allah akan abubuwan da ya gabatar marasa kyau sannan ya roko Allah bukatunsa tare da neman shiriyar Allah. Be san yadda zai karanta qur'ane ba but yasan yadda zai yi iistigifari da hailala da kuma tasbishi da kuma salatin Annabi. Yana zaune saman carpet din har aka yi asalati sannan ya tashi ya fita zuwa masallaci.
Misalin takwas da rabi Noor ya farka a lokacin Jibril na kitchen yana hada musu breakfast, ko da Jibril ya fito ya samu Noor tsaye bakin kofar bedroom yana ta kallon falon.
“Good morning Noor”
Sai kawai ya saka dariya kamar ba shine ya kwanta da fushi jiya ba, kuma ya rufe ido wai yaji kunya an gaishe shi. Jibril ya aje kayan da ke hannunshi saman dinning sannan ya nufo Noor ya duka daidai shi ya kama hannayensa ya rike.
“Ka tashi lafiya?”
“Lafiya kalau, Dady na manta ban tashi ba sai yanzu”
“Yeah ai kara ka yi bachi mai kyau ka samu ka huta ko?”
“Momy da wuri take tada ni na yi sallah”
“Yanzu ma ai lokaci be kure ba muje bedroom ka yi sallah”
Tare suka shiga bedroom din Jibril ya taimaka masa ya wanke bashinsa sannan yaa yi masa wanka ya yi alwalah sannan ya daura masa tawul suka fito yana dauke da shi. Ko da ya fito wayarsa na ringing da sauri ya dauka ya kara a kunne.
“Assalamu Alaikum Malam, okay gani nan fito”
Sai ya zaunar da Noor saman gado.
“Jira ni a nan ina zuwa”
Number Rabi ya nemo ya tura mata sakon daga bisani ya yi mata transfer na kudi i zuwa account dinta dan ta siyoma Noor tufafi, ko da ya fito Malamin na tsaye waje kusa achabansa yana jiran fitowarsa, cikin girmamawa Jibril ya mika masa hannu suka gaisa sannan ya dora masa da.
“Na san yau ya kamata ace mun fara but yau ina tare da yarona kuma yanzu idan mun gama karyawa zan kaishi gida, so ina baka hakuri zuwa gobe sai mu fara, kuma in fa hali ina son bayan mun yi da safe mu yi da yamma”
“Ba matsala, zamu iya farawa gobe din Allah ya kaimu amman kamar wane lokaci?”
“Irin takwas na safe haka, da dare kuma tara na dare nasan bayan wannan lokacin ina gida, sai salarinka nawa ake biyanka per month?”
“Aa ranka ya dade bana son sisinka, zan koya maka komai saboda da Allah”
“Kai amman ina godiya sosai Allah ya saka da alheri”
“Amin amin sai dai littafan da za a siyo”
“tau kamar nawa za a kashe?”
“Zamu siyo ahalari sai kuma husnul muslim da kuma dan goma mai hade da bakaken harufan arabi ta yadda zai maka sauki ganewa”
“Kana da account ne?”
“Eh akwai”
“Okay ina zuwa”
Wayarsa ya bude ya yi masa transfer 10k na siyen littafan, har Malamin na cewa kudin ya yi yawa sai ya ce ya dauki sauran abunda ya rage. Cikin dadin rai ya dawo parlour saboda yana jin ya fara taka wani mataki na gyara rayuwarsa, abunda yake ta kokarin yi shine ya zama uba na gari gurin Noor wanda zai yi alfahari da shi ko bayan ransa.
Da kansa ya yi feeding Noor sannan ya shiga wanka ko da ya fito Rabi tana parlour zaune ta kawo masa kayan Noor da ya bukaci taje ta siyo, ita yasa ta shirya Noor, shi kuma ya shiga ciki ya shirya kansa sannan suka fito tare harabar gidan ita ta wuce shi kuma ya kama hanyar gidansu Nawwara tare da Noor dake gaban Mota.
Jibril ne ya fara fitowa cikin motar sannan ya zagaya ya budewa Noor ya dauko ya dorashi kofar gidan.
“Shiga ciki ka ce da Mamanka ina waje”
Da gudu Noor ya shiga cikin gidan, bayan few seconds ya dawo ya ce
“Wai ta ce ka shigo”
Wani dogon numfashi yaja ya sauke sannan ya dora kafarsa a kofar gidan ya shiga bakinsa kumshe da sallama.
“Wa'alaikaissalam”
Inna da amsa masa, sai ya zube a gurin yana kwasar gaisuwa kai baka ce ma shi ba ne, kansa a kasa yana mai jin kunyar Inna sosai kamar yau ya fara haduwa da ita.
“Tashi Jibril shigo ciki, ashe an sallami Noor”
“Eh an sallame shi jiya shine naje da shi gida”
“Allah ya kara lafiya”
“Amin ya rabb”
Daga haka ya mike tsaye.
“Bari na wuce daman wani gurin zanje na ce bari na fara kawoshi”
“To an gode”
Tashi ya yi ya juyo ba dan kuma yana da gurin zuwan ba, yace hakan ne kawai saboda ya kare kansa, yana son ya tambaya ina Nawwara kuma yana jin kunyar haka ga alheri yana son ya yi ma Inna kuma be san yadda zata kalleshi ba. Bayan na fito ya nufi motarsa sai yaji Muryar Nawwara ta kirashi.
“Jibril”
Ya juyo da sauri ya dawo zuwa inda take.
“Nawwara kina lafiya”
“Lafiya kalau”
“Am sorry about yesterday”
Ya fada yana kallon yanayinta sai kawai ya ga murmushi a fuskarta abunda ya bashi tsoro da kuma mamaki a lokaci daya, dan ya yi zaton wata bakar maganar zata fada sai kawai ya ji ta ce
“Never mind, ni har na manta da wannan ma, amman Jibril ka ce min zaka canja ko?”
Ya kara matsowa kusa da ita.
“Na canja Nawwara ba wai zan canja ba, Wallahi na canja”
“Idan har ka canja zaka zama uba na gari Jibril, kuma da na gari gurin Mahaifinka”
“Abunda na ke kokarin yi kenan ganin na zama uba na gari wa Noor”
“Miyasa zaka mikawa Siraj ragamar kamfanin mahaifinka?”
“Saboda na yarda da shi kuma mahaifina ya yarda da shi, kuma ba zan iya jan raganar kamfanin ba a yanzu”
“Saboda mai?”
“Saboda ke Nawwara tunanina da damuwata duka akanki suke”
Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce
“Ya kamata ka yarda da kaddara Jibril, ka yarda abunda ya sameka da wanda zai sameka nan gaba duka daga Allah ne, ka daina saka tunani a cikin ranka saboda ni matar wani ce, idan har ka yarda da kaddara ina son ka cireni a cikin rayuwarka, Jibril ina son ka nuna min irin son gaskiyar da kake min ta hanyar maida hankalinka akan rayuwarka da kuma ta danka, ina son ka min alkawari Jibril cewar ba zaka sake shan cocaine ba, kuma zaka maida ragamar kamfanin mahaifinka a hannunka, ina son ka zama jarumi Jibril”
Kallonta yake yi ido cikin ido yake karantar gaskiyar kalaman dake zuciyarta, duka abunda ta rokeshi yayi zai iya yi matukar hakan zai faranta ranta.
“Na miki alkawari Nawwara zan yi duka abunda kika fada”
“And lastly ina son ka cireni cikin ranka Jibril, ka yi focusing akan rayuwarka ta nan gaba da kuma ta danka, ka sa a ranka ko babu Nawwara zaka iya rayuwa, domin can baya babu ni a duniyarka, a yanzu ma idan babu ni zaka iya, na tabbatar min da canjin da kake cewa ka yi Jibril ka zama namijin gaske”
Ya gyada mata kai yana murmushin da yafi kuka ciwo.
“I promise you Nawwara zan yi dukan abunda kike bukata”
“Zan maka addu'ah, kuma ina son na koma aikina tare da kai”
“Zamu koma yaushe kike so?”
“Allah ya kaimu, but Nawwara ina fatar ba za ki hanani kusanci da dana ba, kuma ba za ki hanani kyautatawa family ki ba”
“Na fi kowa son ka yi kusanci da Noor Jibril saboda na san ko nayi aure ba zaka bar ni naje da shi, so tun yanzu ina son Noor ya saba da kai sosai da sosai, matukar wannan canjin da na gani a yanzu a tare da kai ya tabbata zan fi kowa farinciki Jibril I'm ever ready to help you ko dan saboda Noor”
Matsowa ya yi kusa da ita kamar zai taba ta sai dai yasan babu wannan damar domin bata son ya tabata kuma shi ma kansa yana son sabawa kansa da wannan.
“Thank you so much Nawwara, Wallahi Ina son ki sosai ina son ki yarda da wannan”
“Na yarda Jibril”
“Ina jin kamar mafarki na ke Nawwara, you actually changed”
Ta yi murmushi tare da sanda kanta kasa abunda ya kara burge Jibril ya ji wani sonta na kara shigarsa, sai dai kalamanta na cewar ya fitar da ita daga ranshi be masa dadi ba, but shi kansa yasan yana bukarta cireta a ranshi ko dan ya samu sukuni a rayuwarsa.
MUSTAPHA POV.
Yau kwanansa biyu da dawowa daga asibiti, tun lokacin da Hajiyarsa ta yi ma Nawwara wannan furucin ransa ya sosu matuka yake jin rashin dacewa da kyautawa abunda Momynsa ta yi.
Dan haka ya yanke shawarar yau sai ya kaiwa Nawwara ziyara saboda ya bata hakuri kan abunda ya faru, dan haka yana fita sallah magariba be dawo ba ya wuce gidansu Nawwara, ya taki sa'a yana aikawa kiranta sai gata ta fito cikin Hijabi sai kamshin turare take, sallama ta fara masa sannan gaisuwa ta biyo baya, daga nan kuma sai dukaninsu suka yi shiru ita tana jiran abunda zai fada mata shi kuma yana tunanin ta ina zai fara, da ta fara gajiya da shirun ne yasa ta ce
“Ya jikinka? Sorry ban je na dubaka a asibiti ba”
Yayi mamakin jin furuncinta domin sam be tsammaci ma zata fito ba balle har ta kula shi haka har da tambayar jikinsa.
“Naji sauki sosai Nawwara, ina son na baki hakuri akan abunda Momy ta yi miki last time...”
Ta daga masa hannu.
“Mahaifiyarka tana da gaskiya Mustapha, na kaina uwa ce kuma uwa kadai tasan abunda wata uwar take ji game da danta, ni kaina ba zan yarda dana ya rasa rayuwarsa akan wacce bata san zafinsa ba, wacce na san ba zata taba aurensa ba.
Mustapha ya kamata ka yi tunani, ni da kai ba daya ba ne, ballanta wani abun ya shiga tsakanin ni da kai, yar uwata ka yi ma fyade taya kuma ni zan aureka? Zuciyarka ta daina yaudararka abunda ba zai taba tabbatuwa a gareka ba, ka daina hangen abunda ba naka ba, Ina tunanin mutuwar Habiba ta canja mana rayuwa dukanmu, ta zamo silar shiriyarka, shin miyasa ba zaka tsayardar tunaninka guri daya ba ka yi abunda zai fiddaka?
Duk yadda zaka so ni aikin banza ne, saboda komai ya riga ya lalace, a zan boye maka Mustapha soyayyarka ba zata taba samun gurbi a zuciyata ba ko da kadan ne, ka daina wahalar da rayuwarka akaina, ka yarda kaddara ce a haka sai kaga Allah ya kawo maka mafi alherinta”
“Thank you Nawwara na gode da kika fada min gaskiya, har gobe ina alfari kuma zan kasance a cikin alfari da son ki har abada, domin son ki ya canja min rayuwa, ya sa na zama kalar da ban taba tsammanin zama ba”
Ya fada idanuwansa na cika da kwalla.
“Ina maka fata ta gari Mustapha, domin ni Bilal zan aura kai ma ina maka fatar samun matar da zata so ka sosai kuma iyayenka su so ta tadda zaka ji dadin zama da ita”
“Thank you but ina son ki taya ni da addu'a domin abun ba sauki”
Ya fada yana murmushin karfin hali tare da share hawayen da suka zubo masa.
“Zan taya ka, ina maka fatar alheri”
Ya dade a tsaye yana kallonta yadda zai yi rayuwa babu ita yake hange, ya san gaskiya ta fada masa shi kanshi yana jin kamar ba zata aureshi ba, sai dai a ganinsa idan har bata aureshi ba ba zai taba gamsuwa cewar ta yafe masa ba, but kalaman da tayi masa a yanzu yasa shi canja tunaninsa kuma ya samu gansuwa a ransa cewar Nawwara ta yafe masa har zuciyarta, ya riga yasan matukar yana son ya shirya da iyayensa dole ya rabu da ita, duk da yana jin a yanzu ta zama wani bangare na jikinsa.
Kamar marar lafiya haka ya dawo gida nan da nan sai zazzabi ya rufe sai dai be bari mahaifiyarsa ta sani ba.
*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @KhadeejaCandy
5⃣3⃣
Jina yi kamar bana da karfi a jikina na kasa shanyar da na ke, sai na zauna a gurin gabana nata faduwa.
“Nawwara”
Inna ta kirani saboda ta lura da yanayina, sai na kasa amsa mata saboda kukan da ya cika min zuciya nasan ina bude bakina zai fito.
“Lafiya miya faru? Dawa kike waya?”
“Bilal ne, tambayata yake wai Noor ya dawo”
Na fada ina ta kokarin danne kukana.
“Kamar ya? Ba tare suka fita ba”
“Tare suka fita”
“Amman shine zai kira ya tambaya ya dawo bayan kuma ya san tare suka je? Wane irin rainin wayo ne wannan?”
Cewar Sakina tana matse zanen Inna.
“Wata kila wani abun ne ya faru, ina ji jikina ba dadi”
“Tun jiya na lura da ke sai dai nasan matsalar bata wuce tsakaninki da Bilal ba shiyasa ban yi magana ba, sabodana bana son ina yawan shiga fadanku, amman babu abunda zai faru da Noor Inshallah”
Ajiyar zuciya na sauke ya share guntun hawayen da ya zubo min na tashi na koma bakin kofar dakinmu na zauna, Sakina ta cigaba da wanke kayan. Haka muka zauna shiru har aka kira magariba Bilal be sake kirana ba gabana kuma be daina faduwa ba. Bayan na sallah isha'i na dauki waya na zimmar na kira Bilal sai kuma nake ganin rashin dacewar hakan, saboda ya saba fita da Noor su kai har dare basu dawo ba, dan me yanzu zan soma kiransa ai sai ya zargeni yace ko dan munyi fada ne, haka na maida wayar muhallinta na aje, kamar Inna ta san abunda ke raina sai kawai na ji ta ce
“Karki ji kunyar kiranshi Nawwara, ki kirashi mana ko muma hankalinmu zai kwanta”
Ba musu na daga wayar na kira number Bilal amman har ta gama ringing be dauka ba, haka na jera masa kira hudu be daga ba, daga baya kuma sai naji wayar a kashe, hakan ya kara fadar min da gaba, ina kokarin fadawa Inna cewar wayarsa a kashe take sai ga sakon Jibril ya shigo.
_Nawwara Noor ya dawo? Ina son gani dana zan aiko da mota yanzu_
Ni kuma na yi saurin mayar masa da sakon cewa basu dawo ba, sai ya sake aiko min da wani
_Dan Allah karki shiga tsakanina da dana Nawwara na roke ki, kiyi min duk abunda zaki min amman karki hana min Noor_
_Idan sun dawo zan fada maka_
_Gani nan zuwa na dauki dana_
_Aa karka zo_
Bw sake cemin komai ba, nasan be yarda da ni bane yana ganin kamar ina kokarin hana masa Noor ne.
“Inna na ta kira na kira be daga ba daga baya kuma sai aka kashe wayar”
“Allah dai yasa lafiya”
Cewar Inna ni kuma na amsa da Amin, kamin mu hada baki gurin amsawa Jidda da ta shigo a yanzu kamar marar lafiya, ina kallonta na san ba lafiya ba, sai dai ban kawo cewar maganar Noor bane saboda a tunani bata san sun fita ba. Kasa gaisawa ta yi da Inna sai kawai ta sakar min ido hawaye ya soma mata zuba
“Ke lafiyar ki?”
Na tambaya ina dafata.
“Nawwara”
Sai kuma ta yi shiru kamin ta cigaba.
“Dazu da Bilal ya fita da Noor wai ya tsaya da shi a AGG MALL ya siya masa chocolate shine sai yaga wani abokinsa suka tsaya gaisawa, wai Noor ya fito daga ciki ko da suka gama gaisawan ya nemeshi ya rasa”
Nina mike tsaye da sauri Inna kuma ta dinga furta
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”
Sakina kuma ta dora hannu saman kai tana kiran
“Mun shiga uku”
“Yanzu ina shi Bilal din yake?”
Inna ta tambaya hankalinta a tashe.
“Yana can gidansu, wai besan yadda zai fada muku ba shiyasa be zo ba tun dazu, nima yanzu yake fada min kuma ya ce ya bada report gurin yan sanda da gidan radio”
Ni dai ban iya cewa komai ba ban da hawayen da nake, muna haka naji tsayawar mota a kofar gidanmu wanda hakan ya tabbatar min da cewar Jibril ne kuma daman yana kusa da unguwar a lokacin da ya kira.
“Ga Jibr.. Il nan... Yace tafiya zai yi da Noor”
Na fada muryata na rawa.
“Ki fita ki fada masa gaskiya dole ne ya sani”
Inna ta umarceni, tashi na yi na fita ina hawaye, nasan Jibril ba zai yarda ba amman ya zama dole na fada masa, ko da na fito yana jingine jikin motarsa yana danna wayarsa da alama ni zai kira.
Fitowata tasa ya dago kai ya kalleni yanayin yadda na ke tafiya na doso shi yasa ya kunna fitilar wayarsa ya haska fuskata.
“Karki fara min complain ba gurinki na zo ba Wallahi, kawai zan dauki dana ne kuma nasan idan ban zo da kaina ba ba zaki bari taje ba, and i need to be with my son”
“Jibril.... Noor ...... Noor”
Na kasa magana saboda kukan da ya ci karfina. Ya sakar min ido sosai yana son jin abunda zai fito daga bakina.
“Noor ya bata....”
“What? How?”
Na kasa magana sai kuka na ke.
“Look Nawwara, idan ma kin shirya hakan ne dan ki samu nisanci da ni to wannan ba hanya ba ce, dan zan iya jure komai ban da rashin Noor, dan Allah ki canja tsari”
“Wallahi ba wasa na ke ba Noor ya bata”
Ya tsaya kallona dan tabbatar da zancen da nake gaskiya ne ko akasin haka.
“Kamar ya Noor ya bata bata ya bata ya bata as how?”
Ya tambaya yana mai daga murya tare da hannyensa sama, ni kuma sai kuka na ke ina ta kokarin rufe baki.
“Ki daina wannan banzan kukan naki ki fada min yadda aka yi dana ya bata”
Na razarana sosai saboda yadda ya katsa min tsawa da kuma irin bacin ran dake cikin muryarsa.
“Da suka fita da Bilal shine suka tsaya Agg mall siyen chocolate sai ya nemi Noor ya rasa”
Ya yi dariya marar sauti
“Ki ce Bilal ya sace min yaro ya siyar ko kuma ya boyeshi ya nemi kudin fansa”
“No Bilal ba zai yi haka ba, Wallahi Bilal ba zai taba cutar da Noor ba”
“To wa zai cutar da shi waya batar da shi a yanzu?”
Ya fada a tsawace.
“Wallahi Bilal ba zai cutar da Noor...”
Hannunsa ya daga zai mareni sai kuma ya kaiwa gilashin motarsa bugun yana wani irin huci.
“Akan dana zan iya taba kowa Nawwara kuma kowa da kowan nan har da ke, idan kin san wani abu ne kula da Bilal tau ki gaggauta kanwace shi tun wuri”
Yana fadar hakan ya bude motarsa ya shiga ya bar ni nan tsaye ina aikin kuka, sai ga Sakina ta fito da gudu ta nufi hanyar Babban gida, ni kuma na juya na koma, ko da na shiga Inna na ta buge bugen waya tana kuka kamar yadda Jidda take.
Ko da tara na dare ya yi gidanmu ya cika da jama'a makota da kuma yan uwa, maza suna suka shiga gari inda ake sa ran za a ganshi har Agg mall din anje amman ba a ganshi ba, ko da Baba Sulaiman ya aika Sakina ta kira masa Bilal sai ta dawo ta fada mana cewar wai yana police station an tafi da shi tun dazu, kowa yayi mamakin wanda zai kulle Bilal a wannan lokacin sai da Baba Sulaiman da Inna suka fada cewar Jibril ne, a ranar duk wanda yake cikin gidan nan ya tabbatar da cewar Noor yana da Uba.
Ni da Inna da Mama turai da Baba Sulaiman da Sakina da kuma Jidda muka kwasa muka je station din, daidaikun mutanen unguwa suka bimu saboda gulma. Mun tararda Jibril a can sai mahaifin Bilal da mahaifiyarsa tana ta kuka, sai wani kanensa daya.
“Ina Bilal din yake?”
Inna ta tambayi Mahaifinsa sai ya amsa mata cikin rashin dadin rai.
“Yana can ciki sun ce ba zasu fito da shi ba, tun dazu muke a nan tsaye babu irin rokon da ba mu musu ba”
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”
Cewar Inna, ni kuma na doshi gurin Jibril sai yayi saurin tashi ya fice daga station din, da gudu na bishi ina kiran sunansa daker ya juyo ya kalleni fuskarsa babu annuri.
“Minene”
“Wallahi ba Bilal ba ne ya sace shi”
“Ke kika sace shi”
“Wallahi ba Bilal ba ne, dan Allah ka kyale kasan yan sandan nan basa da mutunci zasu iya ji masa fa”
“Ke ta Bilal kike ni kuma ta da na nake, babu ruwana da alakarku ya fito min da da na ya zauna lafiya”
Yana fadar hakan ya bude motarsa ya shiga ya barni nan tsaye.
Wasa wasa aka kwashe kwana uku ana abu daya, Jibril ya ki bari a saki Bilal saboda yana zargin shi ya batar masa da da, ita kuma mahaifiyar Bilal da yan uwansa suna dora laifin akaina, a ganinsu ko da da gaske Bilal ya batar da Noor ai be cancanci a ayi masa irin wannan wulakancin ba, har fade take wai danta be taba zuwa cell ba sai dalilina, babu irin magiyar da bana ma Jibril amman kullum maganarsa daya Bilal ya fito masa da da, ni da shi baka iya tantance waye ya fi shiga damuwa, sai dai Jibril ya fini shiga tashin hankalin sosai saboda haukacewa yake kokarin yia kan neman dansa, har mahaifinsa sai da ya zo har sokoto saboda wannan maganar Noor, kullum mafarki na Noor sai dai har yanzu zuciyata bata zargin Bilal. Ranar talata ranar da mahaifin Jibril wato Alhaji Baahir ya yasa a kashe maganar gurin yan sanda muna station mu dukanmu Jibril ya saka Bilal gaba yana masa magiya har da kukansa.
“Dan Allah dan Annabi Bilal ka fada min inda da na yake? Idan kudi kake so ka fada min zan baka ko nawa ne, kuma Wallahi na maka alkawari ba zan bari a ama ka komai ba, amman Noor shi kadai ya rage min ka tausaya min Bilal dan girman Allah”
Bilal ya kasa magana sai hawaye yake, gaba daya kamaninsa sun canja.
“Wallahi Bilal be dauki Noor ba”
Na fada cikin kuka, sai mahaifiyar Bilal ta kwatse ni.
“Ke dan Allah can rufewa mutane baki, baki fada tuntuni ba sai yanzu tsohuwar munafuka, ko da yake Allah ya kara ai kai ka ce ka ji ka gani”
Ban kara mata magana ba, har muka fito station din, muna dawowa gida sai ga Jibril ya iskoni har gida be tsaya a waje ba ya shigo cikin gidanmu da sallama ba tare da ya nemi uzinin shiga ba, ban tabbatar da irin ramar da yayi ba sai a wannan lokacin idanuwansa sun fada sosai. Gaban Inna ya je ya risina yana hawaye kamar karamin yaro
“Inna na rokeki ki saka Nawwara ta fada min wani abu akan batan da na, shi kadai ya rage min a duniyar nan, yau kwana hudu kenan ba a ga Noor ba, duk wanda ya dauke ke Noor rayuwarsa yake so ba kudi na ba, da kudi nane da yanzu an kira an ce na bayar, babu inda ban duba ba, babu irin binciken da ban sa anyi ba amman an kasa ganin Noor”
Inna ta kasa ce masa komai, ni da nake zaune nesa da ita na kalleshi cikin hawaye na ce
“Ban san komai a akan batan Noor ba, idan kuma baka yarda da ni ba, zaka iya sakawa a kulleni kamar yadda ka yi ma Bilal”
“Na rasa mahaifiyata Nawwara a lokacin da ban san miye duniya ba, ban sani ba ko zan iya jure rashin Noor”
Haka kawai ya fada ya mike tsaye ya shafa kansa ya fice. Sai da ya fice sannan Inna ta ce
“Miyasa baki fada masa gaskiya akan abokinsa ba? Mai yiyuwa shi ya sace Noor”
“Idan kuma ba shi bane fa Inna? Sai mu dauki laifin mu dora masa? Mai yuyuwa yan satar mutane ne suka sace shi ko kuma yan garkuwa da mutane sai mu dauki laifin mu dora masa?”
“Amman idan ba a bullowa wannan matsalar da wuri ba zata iya zama babba, kina da dalili da hujja mai karfi ta zargin wannan mutumen kuma shi kadai ya rage a yanzu wanda zamu iya zargi”
Tabbas ni kaina zuciyata a yanzu Siraj take zargi, amman ina cikin kwankwanto saboda kar na yi zargi na jefa rayuwarsa cikin matsala daga karshe kuma ya zama ba shi din ne ba. Ina jin kewar da na sosai kullum mafarkinsa na ke yadda muke rayuwa da shi a cikin gidan yana ta min gizo a ido wani lokacin har ji na ke kamar yana kirana.
JIBRIL POV.
Daga gidansu Nawwara kai tsaye ya nufo gida har ya iso be daina hawaye ba, zuciyarsa kuna bata daina kuna ba, nan da nan ya fara tarin jini sai da ya saka tissue ya goge, babu wanda idanuwansa suke son gani kunnuwansa suke son jin muryarsa a yanzu irin Noor, daman tun kamin faruwar hakan jikinsa yake masa ba dadi ashe na rabuwa da dansa ba, rabuwansu na karshe ya tuno lokacin da yaje daukarsa yace Bilal zai fita da shi, rumgumar da ya yi masa ya dingajin kamar yanzu yake masa ita.
“Ina kake Noor ina kake?”
Ya tambaya yana buga sitarin motarsa yana kuka sosai kamar makaramin yaro.
“Miyasa nake ta rasa abubuwan da suke da muhimmanci a rayuwata ne? Miyasa ne? Allah karka karbi rayuwar da na a yanzu da na fi bukatarsa Allah kada ba basu damar cutar da shi Allah ka kubutar min da dana”
Kamar zai fadi haka ya fito daga motar yana kuka be damu da ma'aikatan gidan su ga kukansa ba shi dai matsalarsa da isheshi. A falo ya zauna yana ta misalta irin yadda Noor yake idan ya zo gidan, sai kuma ya dauko wayarsa ya bude gallery yana kallon hotunan Noor da kuma wanda suka yi tare.
“Wa zai min haka a duniyar nan? Mina tarewa wani? Bilal mi na maka? Oh Allah”
Ya mike tsaye yana share hawayensa, a dare kasa bachi yayi kamar dai ko wane dare yana ta aikin sallah da rokon Allah ya fito masa da dansa, kudi mai yawa ya diba ya bawa Malamin nan mai koya masa karatu akan yasa a yi masa addu'a Allah ya bayyana masa dansa.
Yana zaune yana shan ruwan tea kamar kullum domin tun da abun ya faru baya cin komai sai ruwan tea maganinsa ma ya daina sha. Sai ga Kiran Abbah ya shigo wayarsa cikin yanayin damuwa ya daga.
“Assalamu Alaikum”
“Wa'alaikassalam Jibril ka zo gida yanzu nan ina jiranka”
“Okay”
Yana kashe wayar ya mike tsaye ya shiga bedroom ya canja kayan jikinsa daga jallabiya zuwa kananan kaya, a gaggauce ya fito saboda yasan yau Abbah zai bar sokoto yasan dalilin kiransa ba zai wuce ya fada masa Maganganun hakuri ba.
Ko da ya isa Abdullah fodio road ya tararda Abbah tare da wani bako, bayan sun gaisa sai Abbah ya gabatar masa da shi.
“Ga Dsp Sani Muazu nan na fada masa komai akan case din Noor, abunda yasa na ce kasa a saki Bilal saboda a bullo masa ta wata hanyar, tun da har ya kwashe kwana uku a station da duk irin wahalar da ake bashi be fadi gaskiya ba zai taba fada ta hanyar tsiya ba, so wannan dsp ya san yadda xai bibiyi Bilal har a gano gaskiyar lamarin”
“Thank you Abbah”
Abbah ya dafashi.
“Ka kwantar da hankalinka Jibril Noor dinka yana nan lafiya kalau, kuma za a gano shi da yarda Allah duk wani bayani sai kanyi masa ni yanzu zan wuce”
Sai da Abbah ya koma ciki yayi yan mintuna sannan ya fito Jibril ya raka shi har gurin mota suka yi sallama dan baya jin xai iya binsa har airport, bayan Abbah ya wuce ne Jibril ya dawo ya cigaba da yi ma Dsp bayani akan abunda ya sani a game da Bilal sai Dsp ya nemi hoton Bilal da addirensa da komai nasa.
Suna haka wayar Jibril ta yi ringing yana dubawa ya ga Number Siraj cikin sauri ya dauko a tunaninsa ko zai sanar da shi wani abun ne, domin shi ma ya damu sosai akan batan Noor duk wani shiga da fita da ake tare da shi ake yinsa.
“Hello Siraj”
“Jibril kana ina ne?”
“Ina nan Abdullah Fodio Road lafiya?”
“Nawwara ce ta kirani a waya tana kuka tana min magiya wai na fada mata inda danta yake”
“What? Ita da kanta?”
“Yes ita ce ni abun ya bani mamaki ne”
“Kana ina ne? ”
“Ina gida”
“Bari naje na sameta”
Yana kashe wayar ya mike tsaye yana kallon Dsp
“Taso muje can inda zamu samu hotonshi”
Tare suka fito sai Dsp ya shiga motar Jibril suka nufo gidansu Nawwara. Sai da ya tsaya nesa da gidansu Bilal ya nunawa dsp gidan sannan ya karaso kofar gidansu Nawwara, kiranta ya yi ya sanar mata yana kofar gida yana son magana da ita sai ta ce ya shigo ciki.
Ko da ya shigo ya sameta tsakar gida tana aikin kuka duk ta rame ta yi baki sosai kamar ba ita ba, sai da ya gaisa da Inna sannan ya zauna saman tabarmar da Inna ta shinfida masa yana kallon Nawwara har cikin ransa yake jin kukanta.
“Ki yi hakuri Nawwara dan Allah ki daina kukan nan kina tada min da hankali”
“Jibril Siraj ne ya sace Noor”
Ta fada cikin kuka.
“What?”
Ya kalli Inna sai kuma ya maida dubansa gurin Nawwara a tunaninsa bakinciki ne yake son taba ta.
“Listen Nawwara...”
“Wallahi ba karya na ke ba, shi ya kade Noor kuma yana cikin plan dinsa kashe Noor da ni da kuma kai”
“Okay na ji shikenan zan masa magana”
“Ba hauka na ke ba Jibril ka tambayi Rabi ka ji ita ta fada min komai, shiyasa na koma aiki tare da kai nasa ka karbe kamfanin daga hannunsa ya dawo hannunsa shine yake kiran Abbah ya fada masa komai saboda ya lalata maka rayuwa yasa ka fara shan cocaine, kuma shi ya kade Noor da mota lokacin da suka taso makaranta, Noor ya ganshi shiyasa ya ki yarda su yi ido hudu da Noor saboda karya nuna shi”
“No Nawwara Bilal ne ya kade Noor”
“Ba shi ya kade ba, lokacin da Noor ya yi hadari Bilal yana kamfaninka yana aiki, shine duk ya tsara wannan Jibril ka karda da ni, Rabi ce ta fada min komai idan bata fada min ba babu yadda za ayi na sani”
Wayarsa ya dauko ya kira Rabi tana dauka ya ce.
“Duk inda kike ki zo ki same ni yanzu nan gidansu Nawwara”
Be tsaya jiran abunda zata ce ba ya kashe wayar ya kira Siraj.
“Siraj ka zo nan gidansu Nawwara gani nan na iso”
Nan ma kashe wayar yayi sannan ya kalli Nawwara.
“Siraj ba zai min haka ba, babu dalilin da zai sa Siraj ya sace Noor”
“Wallahi da gaske nake Siraj ne ya sace shi”
Siraj ya riga Rabi isowa duk da kasancewar ta fishi kusa da unguwarsu Nawwara, bayan ya shigo cikin gidan ne sannan Rabi ta iso, Nawwara na ganinsu ta mike tsaye tana hawaye
“Rabi fada masa gaskiya fada masa abunda kika fada min akan Siraj”
Rabi ta nuna kanta.
“Ni Kuma? Mina fada miki ne?”
Nawwara ta girgiza kai.
“Karki min haka dan Allah ki fadi gaskiya”
“Gaskiyar me zan fada? Ni ban san komai akai ba”
Inna ta matso kusa tana kallon Rabi da mamaki ta ce
“Yar nan ki ji tsoron Allah ki fada gaskiya, ke fa kika sami Nawwara a cikin gidan a nan kika fada mata cewar Siraj so yake ya kashe Jibril da ita kuma shi ya kade Noor”
“Haba Inna da girmanki be kamata ki yi wannan maganar ba, bata dace da ke ba, ni gaskiya ban san komai a kai ba”
Jibril ya kalleta
“Look Rabi ki fada mana gaskiya”
“Sir Jibril ban san komai a kai ba, idan ma wani abun ne ai kai zan sama na fadawa gaskiya ba Nawwara ba”
Faduwa Nawwara ta yi kasa tana kuka da tureturen kasa kamar mai aljanu, hakan yasa Jibril zargin tana kokarin fita hayyacinta ne. Sai ya kalli Siraj
“Siraj yi hakuri dan Allah ka je gida yanzu zamu kaita asibiti Rabi ku wuce kawai”
Siraj da tuni gumi ya gama keto masa ya juyo a firgice ya fice, sannan Rabi ita ta fice hankalinta sam baya jikinta.
Sai Dsp nan ya kira Jibril gefe yana tambayarshi alakar da shi tsakaninsa da Siraj, Jibril be boye masa komai ba ya fada nasa sannan Dsp ya bi bayan Rabi.
NAWWARA POV.
Ba zan iya cewa ga halin da na ke ciki ba, ni dai nasan bayan abunda ya faru a gidanmu Inna da Jibril sun kawo ni asibiti shi ma sama sama nake gani kamin Jibril din ya shigo ya yi min allura, sai yanzu da na farko sai na ke ganin komai kamar a mafarki hudun da na hango a window ne ya tabbatar min da cewar dare ya yi domin ko da abun ya faru da safe ne misalin tara zuwa goma.
Tashi na yi zaune sai naga drip a hannuna, tunawa da Noor yasa idanuwa cika da kwalla, dakin babu kowa sai kayan tea da dan karamin freezer, ina haka Jibril ya turo kofar dakin ya shigo.
“Sannu”
Ya fada yana cire min drip din a hannu.
“Ka yarda da ni Jibril Wallahi Siraj ne”
“Na yarda Nawwara”
Ya fada sannan ya cire safar hannunsa ya shi ya shiga hada min tea. Wayarsa ce ta yi ringing sai ya aje hada tea da yake ya yi picking.
“Eh miya faru? Da gaske? Okay gani nan zuwa”
Haka kawai na ji ya fada sai ya juyo ya kalleni.
“Anga Noor police sun tafi da shi asibitin Uduth za a duba shi”
Da sauri na sauka saman hospital bed din hankalina a tashe.
“Jibril zan je”
Tare muka fita, a waje muka hadu da Inna sai duk muka dugunduma gaba daya muka nufi Uduth din dake gawon nama.
Kamin a isa har jin na yi kamar na runtse idona na ganni gaban asibitin. Muna isa parking space din na asibitin na bude na fito da sauri ni da Inna sai dai duk da haka jibril ya rigamu isa Emergency din kasancewarsa Namiji kuma ya hada da gudu, muna isa muka tararda Dsp din nan na dazu tare da wasu yan sanda sanye da uniform. Muna isa sai ya tare mu wai Jibril kawai zai shiga ya ga Noor ba tare da ni ba.
“Kamar ya ni ce mahaifiyarsa fa”
“Na sani amman shi zai shiga”
Zan kara magana Inna ta rike ni ta ce ta Jibril din ya shiga, sannan ta shiga kiran yan'uwa tana sanar musu a waya. Jibril ne ya fara shiga ni da Inna muka tsaya ina ta jin kamar na yi tsalle na shiga na gani. Muna haka Jibril ya fito a daya daga dakunan dake Emergency din fuskarsa da hawaye, kamin ya karaso kusa da mu ya zame kasa ya fadi yana kokarin rike wata kofa dayan hannunsa na danne da zuciyarsa.
*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @KhadeejaCandy
5⃣5⃣
JIBRIL POV.
Haka ya fito harabar asibitin hawaye na bin fuskarsa, babu komai a zuciyarsa na sai tausayin dan sa, kansa kuma empty har ya rasa da ina zai fara tunani akan Siraj. Be damu da tsakar dare ba ne ya shiga motar ya kamo hanyar sama road. A bakin gate dinsa ya tsaya cikin mota ya kira mai gadinsa a waya ya zo ya bude masa gate sannan ya shiga ciki ya faka motarsa ya fito jikinsa babu gwari ya shiga falonsa, saman sofa ya jefar da makulin motarsa ya shiga bedroom ya cire kayan jikinsa sannan ya daura tawul ya shiga bathroom.
Gaban madubin da ke bandakin yaje ya tsaya ya kallon still hawaye ba su daina masa zuba ba.
“Why Siraj mi na maka?”
Ya tambaya kana ya fashe da kuka sosai ya fadi kasa zaune ya dafe kansa. Kuka ya yi sosai mai sauti kamar mace sannan ya tashi ya nufi shower ya sakarwa kansa ruwa, ya lumshe ido yana ra sauke ajiyar zuciya a hankali. Sai kusan hudu da rabi na asuba ya fito daga bathroom din shi ma dan wayarsa dake ta ringing ne. Gaban madubi ya karasa inda wayarsa take ya dauka ya duba, number Abbah ce yana ta kiransa cikin hanzari ya yi picking.
“Assalamu Alaikum Abbah”
“Jibril kana lafiya?”
“Lafiya kalau”
“Am sorry na kiraka da dare, na damu ne kawai and Jibril ka yi hakuri da yadda rayuwa ta zo maka dan Allah, dsp ya yi min bayanin komai nasan kana cikin tashin hankali dazu shiyasa ban kiraka ba, gobe muna nan zuwa tare da yan'uwan Rabi ka kwantarda hankalinka ka ji”
Sai kawai ya fashewa Abbah da kuka.
“Ba ni da wani sauran kwanciyar hankali Abbah, na rasa komai kuma saboda ni komai ya faru Abbah ni ne silar komai”
“Aa Jibril ba kaine ba, haka Allah ya tsara babu yadda za'a yi ka tsalleke karka sa komai a rana ka”
“Toh Abbah thank you”
Ya fada yana share hawayen idonsa, sannan ya aje wayar ya kalli kansa a madubi.
“Al-hamdulillah Allah na gode maka, komai ka yi daidai ne, Allah kai ka tsara min haka a rayuwata ban isa na tsalleke ba, Allah ka bani hakuri dauka abunda duk ka rubuto zai faru da ni, ka yafe min abunda na maka Allah, ka karbi rayuwata ina mai shauki da murnar haduwa da kai, Allah karka karbi raina ina mai bakinciki da damuwa kusantar ka”
Yana gama fadar hakan yaji wani irin rahama da natsuwa sun sauko masa a zuciya. Komawa ya yi bathroom din ya yi alwala ya fito ya saka jallabiyarsa ya yi nafila sannan ya tsaya jiran assalati ya dora da asuba, bayan ya gama ya zauna ya yi azkar na safiya tare da istigifari da salatin Annabi, sannan ya karanta abunda ya sauwaka a qur'ane sannan ya tashi ya nufi freezer ya dauki ruwa mai sanyi ya sha. Sannan ya dawo ya shiga bathroom ya yi wanka yana fitowa ya shirya cikin farar shadda ya dauki hanyar station.
Ya yi rashin sa a ko da ya isa ya tarar ya an wuce da shi gidan yari kai tsaye ba a station aka aje ba, a nan ya kira Dsp ya bashi hakuri akan ya yi hakuri har zuwa anjima idan Abbah ya zo. A dole ya hakuri ya koma cikin motarsa ya dauki hanyar asibitin Uduth.
Hasbiyallahu yake ta karantawa cikin mota saboda ya samu salama a zuciyarsa, a izuwa yanzu ya fawwalawa Allah komai. Yana faka motarsa ya fito ya nufi cikin asibitin, dakin da Noor yake ya nufa mai tsaron gurin ya bashi damar shiga ne saboda ya nuna masa shaidarsa ta likita mai zaman kansa.
Nawwara kawai ya samu a ciki tana zaune saman carpet tana tilawar a qur'ane da kai, ta yi matukar burgeshi hakan sai ya kara masa sonta da sha'awar zama da ita amman ya san babu wannan damar domin a yanzu ya riga ya tabbatar da cewar Nawwara ta masa nisa.
“Assalamu Alaikum”
Ya yi sallamar yana duka kofar sai ya tsaya a bakin kofar yana jiran izinin shiga. Juyowa ta yi ta kalleshi idanuwanta sun yi fari sosai fuskarta ta kode kamar ba ita ba, wani irin tausayinta ne ya kamashi har sai da ya yi daukerwa wutar seconds biyar sannan ya numfasa.
“Wa'alaikassalam shigo mana”
Sai ya maida kofar ya rufe sannan ya karaso ciki yana duba dansa.
“Ya jikinsa?”
“Likita ya ce da sauki ta duba shi, amman dai har yanzu be farka ba”
“Zai farka ki kwantar da hankalinki kinji?”
Ta gyada masa kai.
“Ya naki jikin”
“Na ji sauki”
“Ina Inna?”
“Taje gida”
“Ke kadai aka bari”
“Kasan asibitin ba a bari mutune su shiga sai 4pm”
Ya dan yi shiru yana kallon ta ita kuma tana kallon Noor.
“Abbah zai zo anjima tare da yan uwan Rabi”
Can kasa kasa ya sinkayo muryar Nawwara ta na cewa.
“Laifina ne, ni sakarya ce wani lokacin, na kan dora wani abu da ba muhallinsa a wani muhallin, da a ce ban yi wannan maganar ba da Rabi tana nan raye”
“No no no karki zargi kanki Nawwara, daman can haka Allah ya tsara, ba laifinki ba ne laifina ne, kuma shi Siraj din yana gidan yari yanzu haka yan sanda sun cika masa file sun turashi, kuma za a yanke masa hukuncin abunda ya aikata”
Kokarin kwantar mata da hankali yake, domin a yanzu tausayinta yake baya son abunda zai daga mata hankali ko kadan baya son damuwar Nawwara a yanzu, gani yake ta sha wahalar rayuwa a yanzu be kamata ace ta sake shiga wani halin ba.
Sun dauki lokaci a haka yana ta lallabata yana ta kokarin kwantar mata da hankali, daga baya ya dauki wayarsa ya kira Candy Restaurant ya yi order abinci da za a kawo su Nawwara. Sai sha daya da kwata ya bar asibitin a lokacin Inna ta dawo sai suka gaisa da ita sannan ya fito tare da Nawwara suka shiga mota saboda zuwa gurin Siraj, tun da suka shiga motar Nawwara bata kalli inda Jibril yake ba, shi kuma ya kasa dauke idonsa daga barin kallonta har suka isa.
Abbah kawai suka tarar sai step mother din Jibril da kuma babban yayansa da wani abokin Abbah, da dsp. Abbah ya damu sosai da ganin yadda Jibril ya koma ya rame sosai ya yi wani fari kamar marar jini.
Tare suka shiga da Nawwara da Jibril sannan dan gandireba ya fito musu da Siraj anyi handcuffed dinsa.
Da dingishi ya fito wani gurin a kansa har jini ya bushe masa, har ya zauna be daga kai ya kalli Jibril ba, Dukaninsu babu wanda ya zauna, Jibril ya matsowa kusa da shi sai Dsp din ya shiga tsakani.
“Ba sai ka taba shi, ai hukunci za a yanke masa dai dai da abunda ya aikata, abun jindadi ma ya amsa laifinsa da kansa, kuma mutane da muka kama a gidan da aka aje Noor sun fadi cewar shi ya saka su kuma be karyata ba”
“Ba komai zan masa ba tambayarsa kawai zan yi”
Jibril ya fada yana jin kamar ya kama wuyan Siraj ya shake.
“Mina hana maka Siraj? Mina maka ka aikata min haka? Me ka nema na hanaka? Mi Rabi ta maka? Me Noor ya maka?”
Ya dago kansa da idanuwansa da suka kumbure saboda duka, har baya iya gani da idon sosai gaba daya an canja masa kamani kamar ba shi ba.
“Baka min komai ba Jibril sai alheri, ni kaina ina jin rashin kyautawa a abunda na aikata, sai dai babu yadda zan yi saboda zuciya ta dibeni tun farko, abun da na ke ta kokarinyi da gani na fika Jibril, saboda ina bakincikin ace ni ne a karkashinka ba kai ne a karkashina ba, irin rufin asirin da Allah ya baka na so na samu da karfi sai ya gagara, na sa an kashe Rabi ne saboda ta tona min asiri ta ci amanata kuma na san nima kasheni za ayi, a a yayinda ita kuma za a yafe mata kuma za a yaba mata, Noor ya ganni lokacin da na yi kokarin kasheshi shiyasa na sace shi nasa a kashe shi saboda kar wata rana ya fadi sai gashi Rabi ta lalata komai”
“Hassadace ta cuce ka Siraj ka ci amanar kanka kuma daman hassada ga mai rabo taki ce, mun dauki amana mun baka sai ka cuce mu Allah ya waddaranka Siraj”
Cewar Abbah cike da bacin rai. Jibril ya matso kusa da shi ya chakumi wuyansa ya matse game yana kokarin aikashi lahira, daker aka kwaci Siraj a hannun Jibril har aka wuce da shi Nawwara kawai yake harara idonshi na kanta.
“Ka kwantar da hankalinka Jibril kotu za ta yi komai, litanin din nan muke son fara zaman kotu alkali zai yanke masa hukuncin ai”
Cewar Dsp yana rike da Jibril ta dake ta faman huci. Daga gidan maza station suka wuce saboda wasu statement din Nawwara da za a dauka. Sun yi awa daya a gurin sannan suka baro gurin tare da tawagar yan sanda zuwa rinjin sambo gidan wani dan'uwan Rabi da take zaune a gidansa. Ko da suka je sun tararda jama'a anyi dandazo a gurin duk kuwa da kasancewar an rufe gidan gaba daya kuma sun bar police uku da zasu yi gadin gurin.
Suna isa police din suka bude musu gidan, Nawwara ce a baya tare da Jibril, ya yinda Dsp yake can gaba tare da su Abbah da kuma wasu police din.
“Are you sure zaki iya kallon gawar Rabi? Ance fa dadsatsata suka yi”
Tsayawa ta yi cak sai ya kalleshi.
“Idan kin san zai daga miki karki kalla”
Sai kawai ta fashe da kuka.
“Duk laifina ne”
“Ba laifinki ba ne, haka Allah ya tsara”
Kamin ta kara cewa wani abu sai ga wayarta tana ringing, Baba Sulaiman ya kira ya ji inda suke ya zo, da kanta ta tsaya tana masa kwatanci sai Jibril ya shiga ciki ya bar nan waje tsaye.
Shi kansa da yaga gawar Rabi sai da hankalinsa ya tashi domin datsata aka yi aka mata guntu-guntu ko ina ya bace da jini, suna cikin gurin su Baba Sulaiman da wasu kanenn mahaifin Nawwara suka iso, isowarsu ta yi daidai da isowar yan uwan Rabi kana kallonsu zaka gane ba hausawa ba ne dukansu yanayin shigarsu da kuma tsagen da ke fuskarsu, da kuka suka shiga cikin gidan maza uku mata biyu a nan suka yi ta ihu har da mai faduwa tana tashi tana buga kasa. Daker suka tsagaita kuka har aka dauko gawarta aka fito da ita zuwa motar police.
NAWWARA POV.
Ana fitowa da gawarta hankalina ya tashi sosai lallai mai rai ba komai ba ne, duk kyau rabi da far'arta sun tafi kenan, a gurin na raina kaina saboda ina ganin kamar sakacina ne yasa hakan ta faru, amman Jibril ya yi kokarin dorawa kansa laifin ko kuma ya ce min haka Allah ya tsara zai faru, mahaifin Jibril ne yaso a tsaya a yi mata jina'iza a nan amman yan uwanta suka ki, a dole tasa ya hakura ya bawa police kudin mai dan su rakasu har can kogi inda iyayenta suke, a ranar yan uwanta suka juya suka koma a mota tare da gawarta da kuma rakiyar yan sanda.
Mahaifin Jibril kuma muka dawo asibiti tare da shi ya duba Noor ya yi masa addu'a tare da step mother dinsa, sannan ya yi mana bankwana akan cewar zai koma abuja a yau gobe tun da safe zai hau wani jirgin yaje kogi saboda ayi jana'iza a tare da shi, sosai ya so Jibril ya bishi amman Jibril ya ki wai sai yaga idon dansa, Abbah ya sashi gaba yana ta masa nasiha sosai akan rayuwa da kuma abubuwan da suka faru.
Da yamma lis Abbah ya yi mana sallama ya bar asibitin kasancewar an kira an fada masa jirginsa ya kusa tashi.
Mutane na ta zuwa ganin Noor makota da kuma yan'uwa da abokan arziki ciki har da wasu familyn Jibril da suke garin nan da kuma abokansa. Gurare takwas da rabi na dare Jibril ya bar asibitin saboda kiranshi da aka yi, ko minti goma ba ayi ba sai ga Jidda ta shigo tare da Mustapha i was very surprised dana gansu tare saboda ni na ma dauka Mustapha baya kasar nan dan tun lokacin da nayi magana da shi ban sake hada hanya da shi ba, hankalin Jidda ya tashi sosai har da kukanta Mustapha kan yana tsaye kan Noor yana masa kallon da ban san na minene ba.
“Ya aka yi aka barku kuka shigo?”
Na tambaya bayan Jidda ta zauna har yana kokarin bude abincin da ta zo da shi. Sai Mustapha ya kanne min ido daya yana murmushi
“Cin hanci na bayar”
Na sauke kaina kasa, sai ya yi yar dariya kadan ya ce.
“Allah ya kara sauki ya tsare gaba, kai gaskiya an yi arziki da mun rasa yaro mai kyau, ni da nake son na hada surukuta da ke, dan gaskiya idan na haifi ya mace sai ta auri Noor ko kuma da na ya auri yarki”
Ya fada yana dariya kamar babu abunda ya dame shi, ni dai bance masa komai ba, Jidda kuma ta kasa daga kai ta kalleni duk tabi ta tsargu.
“Ba ganin danki kawai na zo ba Nawwara, na zo na fada miki cewar na samu matar da na ke so”
Sai Jidda ta yi saurin kallonshi.
“Haba Mustapha wannan wane irin magana ne, baka ga halin da take ciki ba? Ko ma minene ai ni ya kamata na fada mata”
“Na ga kamar ba zaka iya fada mata ba ne, shiyasa ni na zabi fada mata da kaina”
“Amman dai ba a yanzu ya dace ka yi wannan maganar ba”
“Fine ba zan kara ba”
Ya fada yana daga hannunsa sama tare da yin murmushi. Ina tunanin Mustapha ya yi min haka ne saboda bakinciki ya yi min yawa a tunaninsa zan ji zafi idan ya ce ya samu wacce yake so duk da nasan ba zata wuce Jidda ba domin alamu sun nuna hakan, ko rantsuwa na yi bana kaffara Mustapha ya so Jidda ne kuma zai aureta ne saboda na ji bakinciki tun da aminiyata ce, kuma yana son bakinciki da nake ciki na rashin lafiyar Noor ya karu akan kishi ne saboda na ki shi, ni kuma na kasa damuwa saboda daman can bana son shi kuma ina ganin sonshi a idanuwan Jidda dan haka sun fi dacewa da juna duk kuwa da kasancesar ta kasa fada min ne saboda karna zargeta ko kuma na yi tunanin wani abu.
Basu wani dade sosai ba Mustapha yasa hannunsa aljihu ya dauko kudi mai dan dama ya aje mana saman gado tare da yi mana addu'ar Allah kara lafiya, sannan ya yi gaba sai na kamo hannun Jidda ya riketa har sai da ya wuce sannan na kalleta na ce
“Amintakarmu ta fi karfi mu boyewa juna abu”
“Nawwara ban yi nufin boye miki ba, kawai ban san yadda zaki kalli abun ba ne”
“Ta fuska mai kyau zan kalleshi Jidda, na san ke aminiyata ce kuma ba zaki taba cin amanata ba, Wallahi ko da Mustapha be furta da kansa yana sonki ba zan hada soyayyarku saboda dacewar da kuka yi da juna, kuma ina ta tabbacin idan har ya aureki ba zai sake wata rayuwa marar kyau ba”
“Ba a yanxurya kamata mu yi maganar nan ba Nawwara, ki kula da Noor please”
Ta fada tana dafa kafadata sannan ta wuce. Ni kuma na dawo na zauna na saka Noor a gaba ina ta kallonsa zuciyata cike da tausayinsa. Misalin goma na dare Jibril ya dawo, yana shigowa dakin Noor na farkawa da kuka yana kiran sunana.
“Momy Momy”
“Gani nan”
Na yi saurin kama hannunsa.
“Momy sun yanka ni wasu sun ce zasu kashe ni”
Sai Jibril ya yi saurin karasowa ya kama dayan hannunsa kuma ya shafa kansa.
“Shiiiiiiiiiii you're safe kana kusa da Momy da Daddy babu wanda zai taba ka”
“Daddy sun ce sai sun yanka ni sun yanka min ciki ma, kuma sun buga min kai”
Sai kawai yasa dariya.
“Ashe Noor dina ba jarumi ba ne, kadan fa suka yanka ka, kuma na sa police sun kama su”
Matsawa ya yi sosai ya kwanta gefen Noor ya rumgumeshi ya matse hannunsa cikin nasa.
“Allah ya baka lafiya ya raya min kai Noor kai kadai ka rage min sai Abbah na”
Tashi na yi na fita wajen kiran likita saboda ya ce idan Noor ya farka a kirashi.
_________________________________
Ku yi hakuri da wannan 🙏🙏🙏.
*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @KhadeejaCandy
5⃣6⃣
A GURGUJE....
Bana tunanin Bilal yana da wata hujja ko dalili na yin fushi da ni, duk kuwa da kasancesar Jibril ya sa an daureshi kuma an masa kai wulakanci da kasa guguwa a fuskar yan uwansu, amman idan har zai min adalci babu hannu a ciki balle kafata, sai dai shi ya kasa fahimtar hakan domin tun lokacin da abun ya faru zuwa yau be taba daga waya ya kirani ba, idan kuma na kirashi sai ya dinga min magana cikiciki kamar baya son magana da ni, sau uku Baba Sulaiman yana daukar mutane suna dubashi bayan sallamoshi daga asibiti, ni kan ban jeba domin Inna taje ba bata dawo da farin rai ba duk da bata fada min abunda suka mata ko suka ce mata ba, na fahimcin hakan ne a fuskarta da kuma yanayinta.
Al-hamdulillah sauki yana ta zuwa ma Noor ta ko ina domin a farko ya firgita sosai har na dauka ko kwakwalwarsa ta tabu ne, sai dai kulawar da likitocin Uduth da kuma addu'o'in da muke sai komai ya daidaita, tiyatar da aka masa ma cikin sati biyu ya samu sauki su kansu sun yaba da irin kyau fatar Noor, yana samun kula sosai da sosai wani abun da Jibril yake masa har mamaki yake bani kamar zai dauke sa ya cinye, a dan zaman da muka yi na asibitin Noor har ya sagarce abu kadan zai fara kuka yana kiran Daddynsa. A zaman da mukayi asibiti sau biyu Jibril na aman jini a gabana abun har sai da ya bani tsoro domin na dauka zuciyarsa ko kuma hanjin cikinsa zai amayar gaba daya, sai dai shi sai ya nuna kamar be damu ba, da alama abun ya zame masa jiki.
Ana gobe za a sallamemu daga asibiti muka yi zaman kotu na karshe akan case din Baba a ranar na sha mamaki ashe matar da ta lakawa babanmu sata yayar Siraj ce daamn ina ganin alamaun haka sai dai ban tabbatar da sai yau da aka yanke hukunci na karshe, saboda yan uwan Siraj da suka zo sune wadanda aka tsaya masa a lokacin da aka yi shigar kotu ta farko case dinsa. Hukunci kazafi alkalin ya yanke mata su kuma aka yanke musu hukuncin kisa bisa ga shaidu da hujjoji kwarara da aka gabatar gaban kotu. Na yi farincikin sosai da sosai a wannan ranar daga ni har Inna da duk wani mai son ganin na kwatowa Baba hakkinsa, na yaba ma dpo daya tsaya kai da fata wajen ganin ya bi mana kadin mu. Abunda ya faru abun mamaki ne kuma abun a yabawa masa ne domin ba ko wane dan sanda bane zai kashe mutum kuma an hukunta shi kamar yadda doka ta ce, a ranar na ji kamar na zuba ruwa kasa na sha saboda farinciki mutane na ta zuwa har gida suna mana murna.
Washe garin ranar aka sallamo Noor daga asibiti, a abun mamaki sai ga Zinatu ta zo ganinsa wani sukuku da ita kamar ba ita ba, na yi mamakin ganin ta zo gida dubashi bayan bata taba zuwa asibiti ganinsa ba. Da fari jajanta mana ta farayi akan abunda ya faru sannan ta dora da bayaninta.
“Na san zaki yi mamakin rashin zuwa ganin Noor asibiti ko? Wallahi Jibril ne ya hanani, saboda na kirashi ina jajanta masa abunda ya faru sai ya gargade akan karna yarda na kusanci dansa, saboda yana ganin akwai aminci da shakuwa sosai a tsakanina da Siraj wata kila yana zargin zan masa wani abun ne”
“Ayyah kin san dole ne ya tsorata kuma ya yi taka tsantsan saboda abubuwan da suka faru”
“Amman ai ba halina daya da Siraj ba, miyasa zai yi tunanin haka”
“Ban da abinki Zinatu ai shi hali ba a fuska akae ganeshi ba, shi ma Siraj din ai bamu dauka cewar zai yi haka ba, ni kaina a yanxu ba kowa zan yarda da shi ba balle kuma shi”
“Haka ne, ni kaina da be koremu daga kamfanin ba, na kudiri aniyar aje aikin domin ba zan iya aiki inda ake ɗari ɗari da ni ba”
“Ya sa kun aje aikin ne?”
“Eh kwana biyu da faruwar hakan duka ya canja ma'aikatan kamfanin, yanxu kuma yana nan yana daukar wasu”
“Ayya abun be yi dadi ba sorry”
“Ba komai Allah kara lafiya, amman gaskiya Siraj ya bata mana suna Allah ya isar mana”
“Amin Amin shiyasa ake son ka yi taka tsantsan da mutanen duniya ai”
Tayi min wani kallo sai kuma ta mike tsaye tare da daukar jakarta ta yi min sallama ta fice. Inna ta zo ta zauna kusa da ni tana fadin
“Ki yi hankali da wannan ma domin kin san ba yarinyar arziki ba ce”
“Na sani Inna amman Allah ya fita kuma shi zai tsare mu”
“Haka ne”
Firar Siraj muka bijiro da ita, a nan nake labarta Inna wasu abubuwa da bata sani a lokacin da ina aiki tare da shi, mun dade muna fira mutane kuma nata shigowa suna mana barka da dawowa ga Noor a tsakar gida yana da game da dayar wayar Jibril daya bar masa ya buga game kamin ya karba.
Bayan sallah magariba Bilal ya kira ni i was very surprised da na ga kiransa domin rabon daya kirani har na manta, gabana ne ya shiga faduwa sosai sai kuma tsoro ya kamani kamar ba zan daga ba sai kuma na daure na dauka, na yi tunanin wata maganar zai fada min sai ya ce min gashi nan kofar gida na fito.
Sai da na canja Hijab din da ke jikina sannan na sanar da Inna itama kanta ta yi mamaki, ni dai jikina a sanyaye na fito. Sai na same shi a daidai inda ya saba tsayuwa yana jingine da ginin gidanmu sanye da kananan kaya.
“Assalamu Alaikum ”
Sai ya dago ya kalleni, sai kuma ya yi murmushi.
“Kin tsorata ko sarkin tsoro?”
Na yi shiru ban ce masa komai ba, sai ya sauke ajiyar zuciya ya ce
“Ki yi hakuri da duka abubuwan da suka faru, na so naje ganin Noor asibiti sai dai ban samu dama ba, saboda Mama ta furta cewar bata yafe min ba idan na taka asibiti ganin Noor ke ko waya na kira na tambaya jikinsa bata yafe min ba, wannan dalilin ne ya hanani zuwa ganinsa”
“Ba komai, Mama tana hujja ai nima kuma ban kyauta ba”
“Babu abunda kika na rashin kyautawa, face fifita son Jibril akan nawa da kika yi”
“Haba Bilal karka dauki zigar mutane mana duk wanda ya fada maka haka ya yi maka karya”
“Ba fada min aka yi ba, gani na yi da idona”
“Babu abunda ka gani Bilal kawai kana son ka yi amfani da wata damar ne ka ci min fuska”
Sai ya gyara tsayuwarsa ya kalleni
“Ki rantse min da Allah a yanzu nan babu son Jibril a zuciyarki!”
Sakin baki na yi ina kallonsa sai idanuwa suka cika da hawaye, na kasa karyata kaina balle kuma na karyata shi, Allah yake son na rantse da shi taya zan yi rantsuwa akan abunda ba ni da tabbaci ni kaina a yanzu ba zan iya cewa akwai son Jibril a zuciya ko babu abu.
“Kin gani? Kina son shi har gobe Nawwara, dan haka karki yaudari kanki, wannan dalili yasa na ke jin kamar ba zan iya aurenki ba saboda zuciyarki tana gurin Jibril ko da na aureki gangar jikinki kawai na aura”
“Wannan ne kawai dalilin?”
Na tambaya hawaye na bin fuskata.
“Ba wannan ne kawai ba, mahaifiya bata son ki Nawwara kowa ma a gidanmu baya son ki sai ni, wani lokacin abunda iyaye basa so babu alheri a cikinsa, and ko na aureki ba zamu taba jindadin zaman aure ba abubuwa za su yi ta faruwa wadanda ba zasu mana dadi ba.
Ban yarda Jibril ya fini son ki ba, amman na yarda son ki yafi yima Jibril illa sama da ni, Nawwara Jibril yana da ciwon zuciya wanda zata iya bugawa a kowa lokaci ta rasa ransa kuma ke kadaice maganin wannan ciwon nasa, na san zakiyi mamakin inda na ji ko? Na samu labarin ne ta hanyar abokan aikinmu da muka yi aiki a kamfaninsa tare, idan na aureki a yanzu na shiga tsakaninki da muradin zuciyarki kuma na shiga tsakanin Noor da Jibril na raba masa hankali gida biyu,
Last two weeks da suka wuce Jibril ya kirani muka hadu a Shukura Hotel da shi, kin san abunda ya yi min? Gafarata ya nema akan abubuwan da suka faru kuma ya rokeni da na rike masa dansa amana kuma na tarbiyantar da shi, da za ayi gasar son ki Nawwara da ni zan zama gwani kuma zakara, amman a wannan lokacin sai da na raina kaina saboda tausayin Jibril da ya kamani, saboda ya canja Nawwara saboda ke mutumen da baya kallon kowa da kima amman har ya nemi ya yafe masa kuma na masa alkawarin ba zan bari komai ya samu dansa ba, har ma ya yi ikirarin mayarda ni aikina, but yanzu idan baki aureshi ba kin san irin halin da zai shiga? Wata kila rayuwarsa marar kyau zai koma yi, kuma Noor ma ba zai ji dadi ba domin a yanzu ya saba da mahaifinsa, ya kamata ace shi ma yasan dadin mahaifa kamar ko wane da,
Dukan abunda Jibril ya yi miki abaya ya yi ne a cikin jahilci yanxu kuma ya dawo yana neman yafiyarki ya kamata ki yafe masa he deserved a second chance so that ya gyara duka laifin da kuskuren da ya yi, kuma shi ya fi cancanta da ya zauna da ke a yanzu saboda ya goge miki zargin da duniya take miki, kuma zaki samu ingattaciyar rayuwa ke da iyayenki wacce ni ba zan iya baki ita a yanzu ba, ko da zan iya baki sai nan gaba amman shi yana da abun duniya wanda ya kamata ace kema kin jidadi kuma kin more hakurin da kika yi,
Abu na karshe da zan fada miki shine, dukan mu ran mu a hannu Allah yake, amman masu ciwo irin na Jibril basa dadewa a duniya, kuma Jibril be da wanda zai iya tsawata masa a yanzu sai mahaifin da bashi da lokacinsa, ga jarabasar cin amanar da Siraj yayi masa wannan kadai ya isa yasa ki tausaya masa, ina son ki Nawwara amman son da nake miki na ki samu farinciki ne bana na aureki ba yan uwana da iyayena su saki a gaba, kuma ina son ki auri Jibril ko dan saboda Siraj da Zinatu, domin idan baki aureshi ba mamaki ya auri Zinatu wanda baki san iya abunda hakan zai haifar ba”
Hawaye nake babu kakkautawa kamar yadda shi ma yake.
“Kar tausayin wani yasa ka cutar da kanka kuma ka cutar da ni Wallahi ina son ka Bilal ina sonka sosai”
“Na san kina so na, amman ko mun yi aure zamu yi ta samun matsala ne kawai Nawwara, kuma ina da kishi sosai ba lallai ne muji dadin zaman aure ba, na san yanzu ba zaki fahimta ba, amman a nan gaba kadan zaki gane gata ne na yi miki kuma na yi ma kaina, ni dai zan bi zabin iyayena wanda ina tunanin Allah zai bani wacce zan so siye da ke saboda na yi ma iyayena biyayya, kuma in da rabon na aureki sai kiga na aure ki din gaba”
Durkusa na yi a gurin na hade hannayena ina rokonsa
“Ka yi ma Allah da annabi ka aureni Bilal zan iya jure duk wani cin fuska da wulakanci da zaka min ko na yan'uwanka Wallahi ina son ka, Bilal sauran fa sati biyu da kwana uku ayi auren nan dan Allah karka janye, kuma ko da ka fasa aurena ba zan taba auren Jibril ba, igiyar aure ba zata sake shiga tsakani na da Jibril ba”
“Idan har baki auri Jibril ba Nawwara to son da kike min na karya ne...!”
Ya fada a tsawace sannan ya share hawayensa ya yi tafiyarsa abunsa ya bar nan ina aikin kuka. Da kuka na shigo gida ina labartawa Inna abunda Bilal ya yi min sai tasa salati tana mamaki karfi hali irin nasa. Misalin tara da rabi Jibril ya kirani a waya wai gashi nan kofar gida ya siyowa Noor abu, a lokacin idanuwa sun kumbura kaina kuma yana mugun ciwo saboda kukan da nayi, nasan ba dan ni ya zo ba, amman ina da bukatar magana da shi saboda abunda ya faru tsakanina da Bilal hakan yasa na fito a lokacin yana tsaye shi da Noor yana bare masa ayaba.
“Noor shiga gida”
Na fada cikin muryata dake nuna na yi kuka har na gaji, ba musu Noor ya taka a hankali ya shigo cikin gida, ni kuma na kalli Jibril na ce
“Rokon Bilal ka yi ka ce karya aureni ko?”
“Miya kawo wannan maganar kuma?”
“Ban sani ba, duk abunda ka yi be isheka ba sai ka saka Bilal a gaba ka rokeshi”
“Wallahi ban rokeshi ba Nawwara, ni dai na masa magana ne akan ya rike min Noor da amana a matsayinsa na wanda zai aureki kuma na nemi yafiyarsa akan abunda ya faru daga karshe kuma na ce zan maidashi aikinsa ya ce min baya so yayi applying wani gurin sai dai idan wani abun ya fada miki daban wanda ba wannan ba”
Na dafe kaina ina kuka.
“Ki yi Hakuri Nawwara ban san haka zai bata miki rai ba da ban yi ba, nasan komai nayi a gurinki bana gwaninta”
Ya fada da muryarsa mai nuna tsantsan nadamarsa. Kasa ce masa komai na yi sai ya juyo na dawo cikin gida cike da zazzafan zazzabi.
MUSTAPHA POV.
Har yau har gobe son Nawwara na nan cikin zuciyarsa, sai dai ba kamar da ba, yana son ya auri Jidda ne kawai saboda Iayayen sun ki yarda da Nawwara kuma yana jin Jidda zata maye masa gurbin Nawwara ko ba komai hakan zai kara wanke shi a idon Nawwara ta yarda zata yarda ya canja har abada, kuma yasan hakan zai kara kusancinsa gareta, a tunaninsa idan ya auri Jidda hakan zai yi ma Nawwara zafi kasancewar aminiyarta ce, kuma yana yawan ayyanawa a ransa cewar ko Nawwara tana kasa giɗa sai ya aureta amana dai ko da ta tsufa ne dan shi har gobe be cire rai daga aurenta ba.
Momynsa ta yaba da Jidda ganin ita budurwa ce kuma ba a mata irin shaidar da ake yi ma Nawwara cewar ta haifi shege, mahaifinsa ma ya yaba da ita duk kuwa da kasancesar ba ita ya so ya aura ba, amman ganin ita ce zabinsa a dole ya amince da ita.
Ba zai ce baya son Jidda ba iya abunda ya sani yafi son Nawwara da Jidda sau dubu ma ba dari ba, irin soyayyar da Jidda ke nuna masa ne ma yasa yanzu ya maida hankali sosai a gurinta har manyan suka shigo cikin, duk da kasancewar ba a saka ranar auren ba iyayensa sunje sunga iyayen Jidda kuma an tsaida magana akan cewar satin sama za a yi musu engaged.
Duk irin shakuwa da so da kauna da ya shiga tsakaminsu har yau Jidda bata taba labarta Nawwara komai ba, ba dan kuma tana son boye mata din ba, sai dan tana nuna kamar ba zata kalli abun ta fuskar daya dace ba, tana ganin kamar Nawwara zata zargeta cin amanarta duk kuwa da kasancesar ta san cewar Nawwara bata son Mustapha amman bata san ta wace fuskar zata kalli alakarsu ba.
*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @KhadeejaCandy
5⃣4⃣
JIBRIL POV.
Wani irin nauyi zuciyarsa ta yi masa har ta kai kafafunsa ba sa iya daukarshi, yadda ya ga Noor yana ta masa yawo a idanuwa, but Nawwara da ya hango ta fadi zaune tana hawaye, sai tausayinta ya lullube masa zuciya, a kokorin mikewa ya yi tsaye ya tunkareta yana kokarin buye damuwarsa.
“Ya mutu ko?”
Ta tambaya cikin rawar muryar da kuka ya dakishe mata ita.
“No lafiyarsa kalau”
Ya fada yana kokarin tare hawayen da suke son zubo masa. Daukar Numfashi Nawwara ta fara yi idanuwansa na kokarin rufewa kamar wacce za a cirewa zuciya. Inna kuma ta dora hannu saman kai ta fashe da kuka tana rika Nawwara.
“Help us please”
Jibril ya fada yana karasawa kusa da ita, hankalinsa a tashe dan shi a yanzu ba nata yake ji ba na Nawwara yake ji, sai wasu Nurses suka zo da gudu suka rikata suka dauketa suka dorata saman gado suka nufi wani bangare da ita, shi kuma ya juyo ya dawo dakin da Noor yake kwance kamar gawa likita biyu ya tarar a gurin sai Nurse daya da ta mika masa wasu takardu Jibril ya saka hannu sannan suka dauki Noor din suka fita da shi zuwa dakin tiyata.
Jinginawa Jibril ya yi da kofar gurin ya lumshe ido hawaye suka zubo masa, zuciyarsa na ta raya masa kamar Noor ba zai rayu ba, an yanka masa ciki da wuka har hanjinsa sun bayyana ga gefen fuskarsa ma ya kumbura. Sai da ya share hawayensa sannan fito daga dakin ya nufo gurin da Dsp din yake wani irin bakinciki da bacin rai na fisgarsa.
“Dsp taya haka ya faru? Na fada maka idan har kun gano inda yaron nan yake ku fada kamin ku yi komai”
Dsp be ce masa komai ba sai da suka fito daga Emergency din sannan ya kalleshi ya ce
“Aikinmu muke yi Jibril da ace na tsaya kiranka da wata kila yaron nan be rayu ba, domin a can cikin daji muka dauko shi, can cikin arkilla tanki can cikin dajin nan dake saman dutse”
“Ina Siraj din yake?”
Ya tambaya yana sauke ajiyar zuciya.
“Yana can station nasa a tsare shi, karka damu da wannan”
“Rabi fa?”
“Am sorry jami'an mu gawarta kawai suka samu”
“How”
Ya tambaya a rude.
“We don't know yet but idan komai ya laba zamu bincika”
Kansa ya daga sama ya kalli taurari zuciyarsa na mugun quna.
“Siraj...”
Sai yasa yatsansa ya share hawayen da ke gefen idonsa. Juyowa ya yi ya dawo ciki, tafiya yake amman ji yake kamar ba taka kasa yake ba, numfashinsa ba ji yake kamar ba a jikinsa yake ba, yana karasowa kofar Emergency Inna na isowa cikin tashin hankali.
“Noor ya mutu ko?”
Dsp ne ya shiga mata bayani Jibril kuma ya doshi dakin tiyata yana safa da marwa, gabansa sai faduwa yake.
Awarsu biyu a dakin tiyatar sannan suka fito da Noor unconscious, da sauri Jibril rika gadon da Noor yake ya kai hannunsa ya taba gefen wuyansa sannan ya sauke ajiyar zuciya. Daya daga cikin likitan biyu da suka masa tiyata ya san Jibril farin sani saboda sun yi aiki a tare asibitin Abuja, shi ya dafa Jibril ya ce
“Ka kwantar da hankalinka, tiyata ta yi kyau sai dai ka masa fatar samun sauki”
Kai kawai Jibril ya iya dagawa ya saki gado ya rike ginin gurinsa saboda mugun ciwo da zuciyarsa take, daker ya mike tsaye daidai ya bi bayan Nurses din har suka isa icu suka canjawa Noor gado saka dora masa oxygen sensor sannan suka masa wata allura a hannu mai hade da drip, sannan likitan ya dauko wani abu mai guda biyu mai kamar iron ya hada shi ya goga sannan ya kurga 1 2 3 ya danna gaban Noor dai dai zuciyarsa.
Sai ga Noor ya numfasa da mugun karfi sai kuma ya lumshe, numfashinsa ya shiga nunawa a sensors.
“Al-hamdulillah”
Shine abunda Likitan ya fada da duka Nurses din kasancewarsu musulmai. Wani irin lumshe ido Jibril ya yi ya bude bakinsa kunshe da godiyar Allah.
NAWWARA POV.
ban san iya awa nawa na yi a sume ba ni dai na farka na ganni saman gado oxygen na sanye a fuskarta, abunda ya faru ne ya soma dawo min zuciyata na ta nuna min cewar da na ya mutu. Ban san akwai mutum a kusa da ni ba har sai da na fara hawaye.
“Am sorry Nawwara Noor yana nan raye an masa tiyata kuma an yi nasara”
Kallo daya na yi masa na kawarda fuskata, sai na rika kokarin sauka saman gadon.
“Babu inda zaki iya zuwa a yanzu karfe uku na dare ne, kuma babu wani karfi a jikinki a yanzu, Inna tana tare da Noor ni ma bata san ina nan ba, Sakina aka sa ta kwana da ke tana waje”
“Ya mutu ko?”
Na tambaya ina kuka duk da nasan amsar ba zata min dadi ba amman ina da bukatar jinta, sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce.
“Be mutu ba”
“Dan Allah karka boye min Jibril ka fada min gaskiya”
“Zan raka ki yanzu ki ganshi”
Saukowa na yi daga kan gadon duk da babu kwarar kuzari a jikina, sai dai na samu gwarin guiwar tafiya ne saboda jin cewar zan ga Noor ne hakan ya tabbatar min da cewar basu kashe shi ba kenan. Hankalina ya tashi sosai lokacin da na ga halin da Noor yake cikin, duk kokarin da Inna da Mama Turai suka yi na hana ni kuka hakan be yi tasiri ba sai da kuka sosai kamar Noor din ya mutu ne.
“Ina aka ganshi? Waya masa haka?”
Na tambaya ina kallon Jibril a zuciyata kuma ina jin cewar zan iya daukar ma dana fansa a kan duk wanda ya yi masa wannan abun. Be bani amsa ba sai ya juya ya fita ni kuma na bishi duk da babu wani kuzari a jikina Inna ta biyoni tana kirana sai ya juyo ya daga mata hannu alamar ta bari hakan yasa ta juya ta koma.
Haka na cigaba da binsa har muka koma dakin da aka kwantar da ni wanda ya kasance babu kowa a dakin sai ni da shi.
“Siraj ne”
Ya fada ba tare da ya kalleni ba.
“Amman da na fada maka karyata ni ka yi, da ace ka dauki mataki tun a lokacin da haka be faru da Noor ba, amman sai ka maida ni mahaukaciya”
Kallona ya yi da idanuwansa da suka rine suka yi ja sosai saboda kuka da kuma bacin rai ya ce
“Kin riga kin kira Siraj kin tuhume sa, ni kuma na kirashi tare da Rabi ne saboda na tabbatar da abunda kike fada, da ace na sa ana rike Siraj a lokacin nan da har yanzu Noor be bayyana ba, da ganga na kai shi asibiti saboda ya yarda cewar haukace take son kama ki, amman ban boyewa Dsp komai ba a game da Siraj, hakan yasa ya bi bayan Rabi saboda ni da shi duka mun lura da yanayinta, da ace ban turki Rabi a wannan lokacin ba da ba zata taba fadin gaskiya kamar yadda ta yi a yanzu ba, ashe all this while Rabi ta san inda Noor yake amman ta kasa fada saboda tana tsoron abunda zai biyo baya, Siraj ya bata yarda shiyasa ya fada mata inda ya aje Noor, and Nawwara na san idan har Rabi bata fada miki ba babu yadda za ayi ki san wani abu daya shafi kanfanina ko kuma rayuwata kuma na san idan har bata fada ba babu yadda za ayi Inna ta goya miki baya, i do believe you sai dai babu yadda za ayi na nuna hakan a gaban mutumen da na daukeshi kamar dan'uwa, Rabi da kanta ta fadawa Dsp inda Noor yake a lokacin da komai ya kure saboda isha'i ta yi a lokacin kuma ta fadawa police cewar rayuwarta tana cikin hatsari, but ko da suka je sun yi latti an riga an kasheta, Noor kuma suka same shi a cikin gidan da ta fada musu an yanka masa ciki”
Hannu nasa na rufe bakina saboda kukan da ke son ya ci karfina, sai na rika gadon na zauna ina kuka a hankali.
“Komai ya faru saboda ni Nawwara”
Ya fada yana hawaye tare da danne kukan da ke son kubuce masa.
“Rabi ta rasa ranta saboda ni, an yanka cikin Noor saboda ni, kin sake shiga tashin hankali saboda ni, da ace ban dawo rayuwarki a karo na biyu ba da duk haka be faru da ke ba, kina da gaskiya Nawwara, kina da dalilai na ki na, a duk lokacin da na kusance ki sai wani abu marar kyau ya faru da ke, ni ne silar lalacewar rayuwarki a karon farko, na dawo a yanzu da tunanin zan iya gyarata na saka miki farinciki saina sake bakanta miki wanda ba hakan raina ke so ba, but komai ya kare yanzu.
Na miki alkwari daga ranar da Noor ya ji sauki ya tashi, ba zaki sake sani a idanuwanki ba, balle na dame ki ba zaki sake kuka da ni ba, kowa ma ba zai sake kuka da Jibril ba, zan tafi wata duniyar wacce babu wanda na sani kuma babu wanda ya san sai na yi rayuwa a can har ta Allah ta kasance, saboda ciwon da ke jikina yana tabbatar min da cewar mutuwata tana kusa da ni a yadda na ke ji a zuciyata na san ko da wane irin lokaci zata iya bugawa na mutu, ina tsoron sake kusantarku ke da Noor wai Nawwara saboda kar wani abun ya same ku... Ki yi hakuri da duk abunda ya faru, but no matter what Nawwara har gobe ina son ki, ko da na mutu a yau na mutu da ciwon son ki ina son ki san wannan, ina son zuciyarki ta gansu cewar ni masoyinki ne ba makiyinki ba”
Yana fadar hakan ya juya ya fice be damu da ya share hawayen da suka bata masa fuska ba, ni kuma na bishi da kallo zuciyata cike da tausayinsa da na kaina da kuma na Rabi da Noor...
*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @KhadeejaCandy
5⃣8⃣
Kaina ya yi nauyi sosai ta ya zan iya watsa kasa a gaban manyan mutane kamar wadannan? Mi zai biyo baya idan na ce ban amince ba? Wane irin fahinta Baba Sulaiman da Baba Dahiru zasu min?
“Ban zata zai aiko da wuri haka ba, shiyasa ban fada muku ba”
Na fada yayinda nake maida kaina kasa.
“Yanzu dai ba wannan ba, kin amince ko baki amince ba?”
Baba Dahiru ya tambaya. Sai da na sauke ajiyar zuciya sannan na amsa.
“Na amince”
“Al-hamdulillah, Allah ya miki albarka Nawwara kin ceci rai”
Abunda ya fito daga bakin Mahaifin Jibril kenan fuskarsa shinfide da farinciki.
“Tashi ki koma gida”
Cewar Baba Sulaiman, haka na taso kamar marar lakka a jiki na fito daga gidan na nufo gida, tun a hanya kuka ya fara kamani amman ban yarda na yi ba sai da na iso gida, ina shiga na fashe da kuka kamar an min mutuwa.
“Lafiya miya same ki?”
Inna ta tambaya tana rike da tsintsiya. Faduwa na yi zaune.
“Inna wai iyayen Jibril ne suka zo neman aurena?”
“Ban gane suka zo neman aurenki ba”
“Mahaifinsa ya turo da wasu mutane ya ce ni nace su zo, wai su nema masa aurena, shine Baba Sulaiman da Baba Dahiru da Baba Audi suka kirani suka tsareni suna tambayar wai na amince ko aa”
“To mi ya faru?”
“Na ce na amince”
“Shine kuma kika zo nan kina kuka”
“Ni bana son shi Inna ba zan aureshi ba”
Sai Inna ta nuna ni da tsintsiyar da ke hannunta.
“Wallahi kin yi kadan karyar karya take Wallahi, wato ni gani ice mai dadin zama shine zaki zo nan kina min kukan ba zaki aureshi ba ko? Ni da kika raina ai miyasa baki fada musu tun can ba”
“Baba Audi zai iya yanka ni”
Na fada cikin kuka.
“Oo to sai ni da nake rarrashin ki zaki xauna kina min kuka kamar yadda karamar yarinya ko?”
“Wallahi ko an daura auren nan ba zan tare ba”
“Tashi kije gasu can ki fada musu tun basu tafi ba, ko kuma ni na yafa mayafina na je na fada musu kina nan kina kukan ba zaki yi auren ba”
Jin haka yasa na yi saurin tashi na shige dakin Inna dan nasan duk Baban Audi ko Baba Dahiru suka ji wannan maganar na shiga uku yanxu bayan na ce na amince kuma na ce ban amince ba ai zasu ce ina musu wasa da hankali. Kuka na yi sosai dakin Inna rayuwar da zan yi gidan Jibril nake hangowa, taya zan rayu da mutumen da ya wulakanta ni? A yanzu ma zai iya kara wulakanta ni saboda yana ganin a bagas ya same ni kamar wacan lokacin, kuma zai yi ta tunanin ina son sa wanda hakan zai bashi damar sake wulakantani kuma na san har duniya ta nade Jibril ba zai taba sanin mutuncina ba.
Sai da yamma Baba Sulaiman da Baba Dahiru suka zo gidan tare da kwalaye minti da cingan da sauran abubuwan da ake kawo wa na baiko, suka labartawa Inna abunda ya faru, ta nan nake jin sun yanka sadakina dubu talatin abokin Abbah ya biya dubu dari kasa, kuma sun saka kwana shida da suka rage na aurena da Bilal sun maye gurbinsu da Jibril. Baba Sulamain har dadi yake ji wai yafi son haka ta yadda Bilal kawai da familynsa zasu ji an daura min aure.
A daren ranar kasa bachi na yi sai na kwana ina raya daren da sallah nafila da karatun qur'ane Allah na mikawa lamurrana har yanzu ban cire rai daga auren Bilal ba.
JIBRIL POV.
Tunda su Abbah suka kama hanyar gidansu Nawwara gabansa ke ta faduwa yana sauraren irin amsar da zasu dawo da ita, Abbah na kiranshi ya tsaya karanta addu'a sannan ya daga zuciyarsa cike da fargaba.
“Kana ina?”
“Ina gida Abbah”
“Ka zo gida ka same ni yanzu”
“Abbah bata amince ba ko?”
“Ta amince har mun biya sadaki kuma kwanakin da suka rage na wacan da bata aura ba aka maida da naka”
Rudewa ya yi yana tsaye ya zauna sai kuma ya sake tashi tsaye.
“Abbah are you serious?”
“Ah wasa na ke da kai? Ko wasa ake da lamarin aure?”
“No no i mean thank you gani nan zuwa”
Abbah ya kashe wayar yana murmushi. Sai Jibril ya fadi ya yi ma Allah sujudar godiyar, sannan ya mike tsaye yana wani irin dariya kamar mahaukaci har da jjjiga jiki, zuwa can kuma ya fara rawa takawa ya farayi a hankali a hankali kamin ya fara yi da karfi har da su kada kwankwaso, sai kuma ya yi tsalle ya fada saman kujera.
“Oh my God i just can't believe this Al-hamdulillah Allah”
A take ya fara hango irin rayuwar da zasu yi da Nawwara idan aka daura musu aure, ya dade yana ta ayyana irin jindadi da gatan da zai nuna mata sannan ya tuna cewar Abbah yana can yana jiranshi kuma yau zai bar garin. Cikin hanzari ya fita gida, zuciyarsa fari kal saboda farinciki, har ya yi kamar ya kira Nawwara sai ya tuna da riske yayi mata sai ya fasa dan yasan tana nan tana fushi da shi. Ko da ya isa ya samu su Abbah na cin abinci shi kan ko ruwa kasa sha ya yi saboda farinciki, rabon da ya yi farinciki irin wannan har ya manta, kallo daya zaka masa ka gane yana cikin farinciki.
Wasu batutuwan Abbah ya tattauna da shi akan auren bayan ya fada masa yadda komai ya gudana. Sannan suka tsaya tsara yadda za ayi.
“Zan ba Hajiya ta hada mata kayan sawa na tufafi da komai da komai da ake, kai kuma sai ka bata kudin da zata yi hidima da wuri saboda kar lokaci ya kure, na fadawa iyayemta bama son komai, saboda haka idan an daura aure sai ka fara gyaran gidan kamin nan da wata daya ka gama sai ta tare”
“No Abbah a cikin week din nan ma za a iya komai a kudi ne matsalar kuma da an bada kudi za ayi komai a cikin lokaci, kuma ba dole sai furniture ba dole sai anyi order a abroad ba a nan ma Kano Kaduna ma za a iya samu na wajen, Abbah na fi son ana daura auren ta tare ranar gudun kar wani abu ya shiga”
Abbah ya dan tsaya kallonsa ya so ya fahimce cewar cilastawa Nawwara yayi sai kuma ya tuna da irin son da yake mata ko da ita din bata son shi ba matsala ba ne. Su yi maganganu sosai akan auren da kuma yadda za a tsara komai, ciki har da zancen da Jibril ya bijiro da shi cewar baya son a yi masa taso sosai gurin daurin auren domin ba kowa yake son a sanarwa ba.
Bayan sun gama Jibril ya raka Abbah da babban yayansu da kuma abokin Babansu da Kannen mahaifinsa airport suka hau Jirgin Abuja, shi kuma ya dawo gida.
Tun daga ranar Jibril ya fara shirye shirye, a bokansa na baya da baya ja a jikin saboda abotarsa da Siraj yanzu kan ya zubar da wannan halin yaja kowa a jikinsa, sai dai be yarda ya yi amini a cikinsu ba domin a yanzu ya wayance da duniya.
NAWWARA POV.
Tun da aka saka lokacin Inna ta cigaba da shirye shiryenta kamar yadda ta fara, babu yadda Jidda ba tayi ba akan na je gurin gyaran jiki amman na ki, duk wani shirye shiryen da amarya take idan an kusa aurenta ni ban yi ba, ban da rama da baki ma babu abunda na yi, ranar da step mother dinsa da yayanta da wasu familyn Jibril suka kawo lefe ma na sha kuka sosai, basu karbi komai ba, ni ban ma san za a kawo lefen ba dan tun lokacin da aka saka mana rana ban taba daga waya na kira Jibril ba, shi ma kuma be kirani ba ko gaisawar da yake da Noor sai ya daina. Idan har zai yi wata magana da ta shafi auren sai dai ya kira Baba Sulaiman, idan kuma ya bukaci ganin Noor sai ya aiko da direbansa ya daukeshi a akai masa shi.
Bilal kuma ban sake saka shi a idona ba, duk da ba fita na ke ba tun lokacin da aka saka min rana, Mama Turai ce take zuwa tana bani shike-shike na itatuwa da wasu abubuwa wasu na kan sha saboda fadan da take min, wasu kuma da na kafaici idonta sai na zubar. Ni dai bana shirin komai duk wani shiri daya danganci auren Inna ce take yi tare da Sakina da Jidda sai kuma yan uwnata da kuma yan Babban gida.
Ina jin yadda suke shirya za su yi walima ni dai Uffan ban ce musu ba, a nan naji cewar Jibril ya ce ranar da aka daura auren zan tare, ji na yi kamar na rabe biyu saboda bakinciki. Kallo daya zaka min ka fahimci cewar bana son auren. Ana sauran kwana uku a daura auren familyn Jibril suka kawo danyin abinci kama daga shinkafa da duk wani abu da za a sarrafa a ranar bikin, sannan suka bada kudi mai yawa na hidima. Cikin kudin ne Inna ta diba ta gyara gidan aka cike inda duk da fashe aka shafe gidan sam kai bama ka ce gidan mu ba ne.
Yau ta kama Assabar ranar da aka saka dauren aurena da Bilal, yau na tashi cikin damuwa da tunani, tun bakwai da rabi na safe Bilal ya turo min sakon da ya hanani sukuni.
_I love you so much Nawwara, na yi abunda na yi ne saboda ki samu farinciki, ni san Mama ba zata taba bari ki samu farinciki a gidana ba ina miki fatar alheri_
Ina gama karanta sakon hawaye suka wanke min fuska, wani abu marar dadi ya zo ya tsaya min a zuciya.
Karfe Goma dai dai na safe aka daura aurena da Jibril, a lokacin ne na fara kuka kamar an min mutuwa a ranar sai da na fita ran kowa daga Inna har yan uwan babana da yan'uwanta duk suka kasa fahimtata, Mama turai ce ta yi min fada sosai hakan yasa na daina kukan na koma yin na zuci.
Da hudu na yamma aka yi walima a a Women development center, walimar da ta bawa kowa da mamaki saboda kayan da aka rana, ko da yake wasu sun riga sun ji cewar mai kudi zan aura, daman na san wasu gulma ce ta kaisu domin ni bana shiga mutane balle kuma biki amman aka taro sosai ga yan uwan Su Jibril suka yi nasu takeaway daban suka rabawa mutane. Malama Aisha ta yi nasiha sosai akan zamankewar aure da kuma hakuri da tsabta nidai duk abunda take fadi jinta kawai na ke dan ban shirya yi ma Jibril ko daya ba.
Misali takwas na dare ya aiko da motoci daukar amarya motocin har sun yi yawa, Jidda ce ta cilasta ni ta yi min kwalliya ba dan na so ba, ta dauko min wata farar farar atamfa na saka, bayan na saka Inners farare sannan na saka fararen takalmi da farin gyale, Inna na min nasiha tana kuka kamar yadda nima na ke yi, sai aka wuce da ni babban gida su Baba Sulaiman da Yakunbo suka min tasu nasihar sai aka saka ni a mota ina ji ina gani aka dauki hanyar Sama road da ni. Na yi zaton gidan kai tsaye za a wuce da ni ganin ni bazarawa ce amman sai da aka biya wani babban gida inda yan uwan Jibril suka sauka aka kaini gurin Step mother dinsa da wasu kanen mahaifiyarsa da gwaggonsa suka min nasiha sannan aka sake sani a mota. Ba mu yi tafiya mai nisa ba muka isa wani katon gida mai farin fentin da gate golden color, ko ina na gidan haskene kamar da rana.
Ana fitowa da ni daga mota na done kaina kasa ban sake dagawa ba har aka shiga da ni bedroom din gidan, da kafar dama na shiga kuma tare da bismillah. A tsayar gadon na zauna fuskata a bude hawaye kawai na ke ganin hakan yasa Jidda ta ja min mayafina ta rufe min fuska, yan uwansa suna ta daukata hoto wasu kuma na ta kokarin ganin fuskata sai Jidda ta hana.
Bayan kamar minti arba'in Jibril ya shigo tare da abokansa sai zolayarsa suke, a gafe gado ya zauna, sannan wasu daga cikin abokansa suka shiga yi mana nasiha daga karshe suka rufe da addu'a. Ina jin lokacin da suka fita tare da nawa yan uwan da kuma Jidda, suka bar mu mu kadai a cikin dakin. Mun kusa minti talatin daga ni har shi babu wanda ya ce da wani uffan, baka jin komai sai shesshekar kukana.
A hankali na ji ya kai hannunsa ya yaye mayafina ya dago fuskata, hawaye yake kamar yadda nima na ke yi.
“Ki yi hakuri Nawwara na san ba ni kike so ba, na san na yi miki kutsu a rayuwarki, amman ina da tabbaci zaki auri Bilal nan da wani dan lokaci kadan, da shi zaki yi rayuwa dawwamamma irin wacce kike so”
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya cigaba.
“Ada na yi tunanin idan an aureki zan kasance a cikin farinciki, amman wannan hawayen da na gani a idonki ya sani jin babu dadi kuma ya sani jin nadamar cilasta miki aurena”
“Ba zan taba son ka ba Jibril, ka rabani da komai nawa, idan har kana da kunya a idonka ba zaka taba kai hannunka ka taba jikina ba, jikin macen da ka hada hotonta da wani ka ce karuwa ce mai neman maza da aurenta, ka rabani da mutumen da yake so tsakani da Allah saboda kawai ka samu farinciki, to bari na fada maka, ka kara matsowa da mutuwarka da bakinciki da damuwa da nadama a kusa da kai”
Na fada ciki kuka. Sai ya yi saurin dauke kansa ya sauke wani numfashi da alama maganata bata masa dadi ba. Tashi ya yi tsaye ya cire Babbar rigarsa ya aje.
“Taso mu yi sallah”
Ya fada cikin muryar da ke nuna rashin jindadin da ke cikin ransa. Ban masa musu ba a nan na sauko saman gadon sai ya wuce gaba ya nuna min inda bandaki yake ya bude min, na shiga ciki na yi alwala ko da na fito ya shinfida carpet da alama shi da alwalar ya shigo.
Wardrobe ya bude ya dauko Hijabi ya miko min na saka sannan ya yi gaba ni kuma ina baya ya kabbatar sallah nafila.
Bayan mun gama ya yi addu'a nima na yi tawa addu'ar sai juyo ya rika goshina ya soma karanta addu'ar da annabi ya koyar da mu wacce miji yake rika goshin matarsa ya karanta saboda niman tsarin da zaman lafiya.
اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ خَيْرَهَا وَخَيْرَ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّهَا وَشَرِّ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ
Allaahumma 'innee 'as'aluka khayrahaa wa khayra
majabaltahaa 'alayhi wa 'a'oothu bika min sharrihaa wa sharri maajabaltahaa 'alayhi.
Na yi mamakin jin wannan addu'ar daga bakin Jibril lallai ba da wasa ya riki karatun qur'ane ba tun da har ya iya maida hankali ga yin addu'o'i ma. Bayan ya gama ya tashi ya dauko manyan ledoji ya aje a gabana tare da plate da cups. Ni kuma na mike tsaye na nufi hanyar da aka shigo da ni wato falo.
“Zo ki ci abinci mana”
“Bana jin yunwa”
Ita ce kawai amsar da na bashi na nufo falo na zauna, sai kuma na kasa yin kukan da na fito yi, haka na zauna a saman manyan kujerun alfamar ina ta kallon yadda aka tsara falon, ba dan ina ganin sha'awa ba sai dan na rasa abun yi zuciyata cike da tunanin Bilal. Har sha biyu ina zaune falon ni kadai kuma Jibril be fito ba. Jin na yi na tsallawa da kayan dake jikina kasancewar atamfar ta matseni sosai hakan yasa na tashi na koma dakin dan dauka wasu tufafin domin Jidda ta fada min inda ta aje min kayan da zan canja idan zan kwanta.
Aabunda na tarar ya tashi hankalina sosai, Jibril ne kwance kamar matacce ga jini nan gefensa da alama amai ya yi. A firgice na kai hannu na taba shi amman be motsa ba.
“Na shiga uku Jibril Jibril Jibril”
Shiru be amsa ba balle ya motsa, tun ina girgizashi kadan har na fara yi da karfi ina kuka, hannu na kai daidai hancinsa sai na ji baya numfashi hakan yasa ni fasa ihu na fito a firgice falo ban san lokacin da na fito harabar gidan ina ihu ba. Ban san da akwai mai gadi ba har sai da ya taso ya nufoni yana tambayar lafiya.
“Jibril ne ya suma ya ya ya mutu”
Na fada cikin Matsainancin kuka da tashin hankali. Tare muka dawo dakin da shi babu abunda ke fita bakinsa sai Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, yana girgiza Jibril tare da fadin
“Mai gida Mai gida”
Amman Jibril be motsa ba.
“Mi ya same shi”
Ya tambaya yana cigaba da girgiza shi cikin tashin hankali na ce
“Wallahi ban sani ba, ni ma ina falo ko da na shigo na ganshi haka”
Wayarsa ya ciro ya kira wani wanda ban san ko wanene ba, cikin kankanen lokaci mutumen ya iso a nan na gane direban da Jibril yake aikawa a gidanmu ne. Tare da taimakonsa suka saka Jibril a mota nima na shiga muka dauki hanyar asibitin One On One Special Hospital.
Muna isa aka karbeshi aka shiga dashi wani dakin suka shiga bashi taimakon gaggawa, sai direban ya dawo yana cewa na kira iyayensa na fada musu.
“Babu waya hannuna tana hannun Mamana”
“To ki kira line sai ki sanar musu idan kina da number a kai”
Ya fada yana mika min wayarsa. Cikin hanzari na karba na saka numberta na kira, sai da tayi ta ringing har ta katse na sake kira sai a na uku Inna ta dauka cikin muryar bachi.
“Assalamu Alaikum”
“Inna Nawwara ce ni ce, muna asibiti Jibril ba lafiya ya suma ko ya mutu”
“Wani abun kika masa ko?”
Na yi shiru na kasa amsawa sai kuka nake.
“To kin kyauta, kuma bari kiji na fada miki ko mutuwa ya yi karki kuskura ki dawo inda na ke, ki nemi wata uwar can ba ni ba fitsararriyar yarinya”
Tana fadar hakan ta kashe wayar. Sai na mika masa ina kuka kamar zan hadiye zuciya na mutu.
“Ki kira mahaifinsa ki fada masa”
Kuka da nake ya hanani fadin bani da numbersa numfashina har gargada yake. Shi da kasan ya kira Abbah ya fada masa, kusan a tare suka iso da Inna da wasu yan uwan Inna.
“Miya sameshi”
Shine abunda mahaifin Nawwara yake ta tambaya, ni kuma na kasa magana saboda kuka, Inna kan ban da hararata babu abunda take. Bayan likitoci sun gama bincikensu daya daga cikinsu ya zo yana ma Abbah bayanin cewar Jibril yana da heart attack kuma da alama an bata masa rai ne shiyasa wannan dogon suma.
“Zuciyarsa ta buga a yanzu, kuma an barshi ya dade ba a kawo shi asibiti ba, ban da Allah ya masa tsawon rai da yanzu ya mutu, da alama an bata masa rai ne ko kuma be samu wani abu da yake so ba ko ya rasa wani abu, so shawarar da zan baku ku yi kokarin kawarda duk wani abu da zai bata masa rai saboda in ta sake bugawa gaskiya zaku rasa shi yanzu ma sa'a ce kawai da kuma rabon shan ruwa a gaba”
“Mun gode likita zamu kiyaye”
Shine abunda Abbah ya fada, kallo daya ya yi min ya dauke kansa, ya nufi dakin da Jibril ya ke ya shiga, har su Inna suka shiga aka barni nan ni kadai tsaye kamar marar gata. Su Inna ne suka fara fitowa ban san ko karfe nawa a wannan lokacin amman tabbas dare ya yi sosai amman hakan be hana Inna da yan'uwanta bin daren au koma gida ba. Bayan Abbah da yayan Jibril sun fito tare da wasu yan uwansa mata na shiga, sai na tararda wasu yan uwansa a cikin dakin, sai dai ina shiga duk suka fita waje aka bar ni ni kadai.
Zaunawa na yi saman kujerar dake kusa da gadon ina hawaye, sai na dora kaina saman gadon da yake kwance ina kallon fuskarsa. Oxygen ne a bakinsa sensor na nuna yadda numfashinsa ke tafiya, tausayinsa ne ya fara kamani da kuma tausayin kaina a lokaci daya...
*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @KhadeejaCandy
6⃣0⃣
Jihadin da na yi ba duk mace ba ce zata iya yinsa, zama da mutumen da ya nuna maka ba kaunarka, yanzu kuma ya dawo yana son ka kamar ya mutu.
Annabi ya yi gaskiya da ya ce mu yi so kadan kuma mu yi ki kadan domin wata rana masoyinka ya kan iya zama makiyinka ko kuma makiyinka ya zama masoyinka, har ga Allah ya yarda Jibril yana so na kuma i believe without me there is no Jibril. But for what Jibril did to me is unforgivable pain, hada hotona da hoton wani namiji shine abunda na ke gani a duk lokacin da na kalli fuskar mijina.
Ina cikin hada masa tea na ji hannayensa zagaye da kunkuruna ya dora fuskarsa saman wuyana yana goga min hancinsa a gefen fuskata.
“Karki wahalar da kanki gurin hada tea nan ba zan iya shan sa a yanxu ba”
Ya fada saitin kunnena kadan-kadan kamar mai rada.
“Saboda me?”
“Saboda ban wanke bakina ba kuma ban rama sallah da ake bina ba, kara ki bari kawai har muje gida”
“Fine zan je gida da kaina sai na dauko maka brush din da toothpaste”
Kokarin juyowa na ke amman sai ya ki bani dama saboda ya ji dadin yadda muke tsaye a haka.
“Kar wani ya tarar da mu a haka fa”
Ya sakeni sai na juyo na kalli fuskarsa yana murmushi sai ya dora hannayensa saman kafadata ya hade goshinsa da nawa.
“To miye a ciki haramun muka aikata?”
Har na bude baki na yi magana sai a turo kofar dakin aka shigo hakan yasa dukanmu muka tsargu ganin Abbah ne, bama kamar ni da nafi jin kunya, domin shi nuna yayi kamar be yi komai ba ya zauna saman gado yana gaisheshi.
Nima gaisuwar na mika masa ga mamakina sai ya amsa min sai dai fuskarsa babu yabo ba fallasa. Kofa na nufa da zimmar fice sai ya kirani hakan yasa na juyo ma dawo still kaina na kasa.
“Ki yi hakuri da abunda na fada miki, raina ne kawai ya bace amman dukan wani furuki da na yi agareki bana da nufin aikata ko daya kawai dai na ce ne dan an tsorota ki”
“Ba komai Abbah”
Na fada sai Jibril ya kalleni ya kalleshi
“Wani abun ne ya faru?”
“Lokacin da kake unconscious na fada mata masu Maganganun da basu da ce ba, saboda na yi tunanin ko da hannunta a abunda ya faru da kai ne”
“Aa ita ma bata san abunda ya same ni, domin na turata kitchen ta dauko plate kawai sai na ji jiri ya dibeni ban sake sani inda nake ba”
Abbah ya juyo ya kalleni.
“Amman Nawwara shine baki fada ba, kika kyale ina ta miki fada?”
“Ba lallai ne ka saurareni a lokacin ba, amman yanzu komai ya wuce, bari na je na dauko maka brush din”
Na karasa ina kallom Jibril sai ya kada min kai.
“Amman kisa direba ya kai ki karki hau Napep”
Da kai na amsa masa sannan na fice zuciyata cike da jindadi da kuma rashin jindadin da ban san na minene ba. Harabar asibitin na nufa inda aka faka motoci a nan na samu direansa da ban san sunansa ,bayan mun gaisa ya tambayani mai jiki sai na ce masa ya kai ni gida. Gida bayan na shiga shi kuma yana mazaunin direba kamar kullum.
Ko da a muka isa gida wato sama road ina hawayen da bansan na minene ba. Bayan ya faka motar na bude na fito ina share hawayena na nan na samu damar kallon wani bangare na gida, irin tsarin nan na manyan masu kudi gurin faka motoci an kawata ko kna da furanni masu kyau da daukar hankali. Babbar kofar shiga falon kuma tana da stairs biyar an kawata gefen karfen stairs din da furani kamar gidanjen turawa ko kuma na ce na indiya.
Ina shiga na samu falo kamar yadda na barshi, sai dai komai na falo fari kamar fentin gidan, ya kawata falon da hotuna na da na Noor sai kuma na Abbah da na Mahaifiyarsa, amman babu nasa ko daya. Lokacin da na shiga bedroom sai na manta da abunda ya kawo ni gidan kawai na hau gyara dakin saboda ya bace da jinin da Jibril ya amayar jiya da dare.
“Allah ka bani ikon jure komai”
Ya roka yayinda na ke dauke kazar jiya da har ta soma yauki, bayan na gyara ko ina na shiga bandaki na hada ruwa na yi wanka, sannan na fito na shafa mai na dauki atamfa maroon color na saka, gaban madubi ya zo na tsaya ina kallon kaina kitson da aka min ya kwanta a kaina sosai gashina ya yi baki kuma ya sauko har gadon bayana. Kamar a mafarki na hango mutum ta cikin madubi ya doso inda yake fuskarsa dauke da murmushi, saurin juyowa na yi na kalleshi.
“Ya aka yi ka zo”
“Baki ji mota ba?”
Ya fada yana muna min window.
“Sam ban ji ba”
“Hankalinki yana iya?”
“Yana can asibiti gurin mijina”
Goshinsa ya hade da nawa ya kama hannuna na dama ya shinsshina ya lumshe ido.
“Ya akayi aka barka ka fito? Na san dai babu likitan da zai sallami mai jiyanci irin a yau din na asibitin bayan kuma jiya da dare aka kai ka”
Be amsa min ba sai na ji kafarsa saman tawa yana goga min ita a hankali.
“Su Momi suna waje suna jiranki”
Ya furta sai ya sakeni ya yi baya baya yana murmushi har ya isa bandaki, sannan ya bude ya shiga. Ajiyar zuciya na sauke a hankali sannan na dauki mayafi na ya rufe kaina na nufi falo.
JIBRIL POV.
Zaune yake ruwan shower na dukan kansa, sai dai hakan be hana hawaye zubo masa ba, kuka yake kukan da be san na minene ba farincikin dawowar Nawwara a duniyarsa ko kuma bakincikin kwanakin da yake ji a jikinsa su suka rage masa, wanda hakam ba zai ba shi damar rayuwa irin wacce yake so a tare da ita mai tsowo ba?
Bayan na gama wanka yaje gaban madubi ya wanke bakinsa sai ya bude cabinet ya dauko maganinsa ya sha, sannan ya juya ya fito daga bathroom din. A gaggauce ya shirya cikin farin yadi marar nauyi sannan na fashe jikinsa da turare ya fito falo. Hajiya ya samu wato Step Mother dinsa tare da sisters dinsa a zaune suna ta fira da Nawwara sama sama.
A ranar wuni suka yi baki daga masu zuwa ganin amarya wandanda ba su san an kwantar da Jibril asibiti ba, sai masu zuwa diba shi idan sun je asibiti ace musu ya dawo gida. Abbah dai tun asibiti suka yi sallama da shi Hajiya ce kawai ta jira taga jikinnasa kamin ita ta kama hanyar abuja gobe.
NAWWARA POV.
Sai kusan isha'i sannan kowa ya watse, muka shiga gyara gidan ni da Jidda da Sakina, sai da muka gyara ko ina muka masa tas sannan muka kunna turaren wuta gidan ya dauki kamshi.
“Gaskiya Nawwara kin da ce, ga mijinki yana son ki duk abunda kike so shi zai miki, yan uwansa ma ba baya ba suma na ga suna son ki”
Ta fada tana karewa falon kallo. Ni kuma na yi murmushi na ce
“Ni ko kin ga duk wannan dukiyar bata gabana, na rasa dalilin da zai sani na ji dadin zama a gidan nan”
“Aiko kara ki fara ji tun yanzu, domin wanda kike takama da shi ya yi aure rana daya da ke”
“What? me kike nufi”
“An daurawa Bilal aure da wata yar'uwarsa, Mamansa ta ce ba za a daga ranar ba tun da kowa ya san an saka rana kara kawai ya auri yar'uwarsa wata yarinya ce da ake riko a gidan”
Na ji babu dadi, dan nasan ba dan yana son ta ne ya aureta ba sai dan kawai mahaifiyarsa ta cilas masa.
“Hakika ta yi dacen miji mai kawaici da sanin ya kamata, miji mai gudun kukan matarsa mai son duk wani abu da zai faranta rai”
“Kuma ba ki ganta ba, ta ninka ki kyau sau ashiri”
“Ina ruwana”
Na fada ina harararta, ita kuma ta sa min dariya, sai da Jibril ya dawo sannan suka fice suka barmi cikin rashin dadin rai. Ina ta kokarin kawai da abunda yake zuciyata gudun kar Jibril ya zarge ni ko kuma damuwata ta saka masa damuwa, iya inda far'ata take na yi kokarin nemota na yabama fuskata. Bayan na fito wanka na hada masa nasa ruwan na fito daure da tawul da kuma Hijab a jikina. Tun da na fito daga bathroom din ya sakarmin ido yana ta kallona har na zauna bakin gado kamar yau ya fara ganina. Hakan yasa na soma tsarguwa.
“Ga ruwan wanka can na hada maka”
Murmushi ya yi sai ya bar jikin kofar dakin da yake tsaye ya nufoni ya zauna daf da ni ya kawo fuskarsa kusa da tawa har muna iya juyo mumfashin juna. Jin bakinsa daf da nawa yasa na runtse idona na dauki numfashi ina sauraren yadda yake watsa da yatsansa a gefen fuskata.
“I love you”
Ya furta muryarsa can ciki kamar marar kuzari, ji nayi yana huramin iska kamshin sweet candy a hankali daga saman goshina zuwa bakina. Lokaci daya na daina jin iska hakan yasa na bude ido sai na gashi tsaye yana kallona fuskarsa da murmushi. Hannayensa yasa ya tasheni tsaye ya rumgumeni tsantsan a kirjinsa.
“Ina son ki sosai Nawwara”
Ya furta yana kokarin ciremin Hijab din da ke jikina, ni ko gabana sai faduwa yake, hannuna ya rika ya dora saitin zuciyarsa, wani irin bugawa na ji zuciyarsa na yi da karfi har sai dai na tsorata, Dagowa na yi na kalleshi sai ya sauke idonshin cikin nawa yana min wani kallo mai wuyar fassara, hannunsa ya kai ya kama fuskata ya soma sumbantar bakina. Kasa kasa na ke saboda na kwaci kaina shi kuma sai biyoni yake hakan yasa muka fada saman gadon a tare. Dariya ya soma yi kamar yadda nima na ke dariyar, kunya tasa na yi saurin juyowa na kife fuskata cikin Bedsheet, sai ya dora kansa a bayana yasa yatsansa yana wasa da wuya. Sai da ya sumbanci kunnena sannan ya tashi daga bayana da dora kansa.
“Babe-Naj gaskiya wankan nan tare ya kamata mu yi shi”
Ya fada yana kokarin jan tawul din da nake daure da shi, hakan yasa na yi saurin sauka saman gado ina zare ido.
“Na fa yi nawa wanka kuma ka gani”
“Gaskiya ban gani ba”
Ya dosoni gadan-gadan hakan yasa na haye gado na koma can karshe ina ta kokarin rike tawul din dake son subucewa daga jikina.
“Ki sauko nan kawai Hajiyata”
“Aa gaskiya haka kawai na yi abuna kuma ka ce sai na sake wani”
Na fada ina turo baki, sai ya yi dariya.
“Fine”
Kokarin hawan gadon yake ni kuma na sa masa ihu.
“Tsaya tsaya zan sauko, amman Wallahi na yi wankan kwarai”
Tsayawa ya yi na sauko da kaina fuskata kamar na fasa kuka ina daga masa na ce.
“Dan Allah karka cilasta min wanka tare da kai Wallahi na yi wanka na kwarai”
Kyaleni ya yi har ya juya sai kuma ya juyo da sauri ya janye tawul din dake jikina, rudewa na yi na rumgume shi ina kokarin fashewa da kuka. Shi kuma sai ya fashe da dariya ya duka ya dauko tawul din ya daura min.
“Yi hakuri”
Kuka na ke da gaske har da hawaye domin na ji haushi kuma na ji kunya sosai musamman rumgumar da na masa. Sai ya nufi bathroom yana ta kyalkyatar dariyar mugunta kamar ba shi ba, ni ma har na soma dariyar kaina.
Sai da ya shiga bandakin ni kuma na je na kulleshi daga waje.
“Sai ka fadi wanda ya aikeka ka yi min haka nan ko kuma ka kwana a bandakin nan”
“Yi hakuri idan na fito sai ki rama”
“Ni ba zan rama ta yadda ka yi min ba, sai dai ta wannan hanyar”
“Ashe ke matsoraciya ce ma, karki yarda na fito sai na miki abunda ya fi wannan yarinya”
“Waye yarinya?”
“Ke mana, kin san da auren kauye aka min da yanzu na haifeki”
“Sannu Baba”
Na fada ina dariya, da gangan na ki bude shi har na shirya cikin kayan bachi na nufi falo inda ya aje ledodin da ya shigo da su dazu. Zaunawa na yi a dinning din na ci abincina sai da na koshi sannan na bude freezer na dauko ruwa na sha.
“Al-hamdulillah”
Na furta ina mamakin yadda na soma sakewa a gidan kamar ba ni ba, ina kokarin maida ruwan na ji hannayensa kan kwankwasona, ba shiri na saki goran ruwan ya juyo da sauri ina ihu.
“Ya aka yi ka fito”
“Aljanine ni, waya ce ki ci amin abinci”
Shi ma kayan bachi ne a jikinsa irin kalar nawa sai dai na shi na maza ne nawa na mata. Hannayensa yasa ya daukeni kamar wata yar baby, ni kuma na dora hannayena saman wuyansa.
“Mrs baki da kunya, jiya fa aka kawo ki gidan nan amman har sakin tawul kike gabana”
Na yi saurin boye fuskarta a kirjinsa ina dariya.
*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @KhadeejaCandy
5⃣7⃣
JIBRIL POV.
Cike da bacin rai ya isa gida, abunda ya kasa ganewa miyasa Nawwara ta kasa sakewa da shi ne miyasa abu kadan zata rika ganin laifinsa, sai yaushe zata fahimci irin son da yake mata? Yaushe zata gane duk wani kalami marar dadi daga gareta yana taba masa zuciya, har sai yaushe Nawwara zata fara sanin ciwonsa?
“O.... Ya Allah”
Ya jefar da keys dinsa ya fadi zaune saman kujera yana sauke ajiyar zuciya. Can Bilal ya fado masa a rai sai ya maida laifin a kansa daman baya son ganin laifin Nawwara, yana da bukatar jin ta bakinsa da haka dole ne ya kirashi, wayarsa dake aljihu ya ciro ya nemo number Bilal ya aika masa da kira, ta dade tana ringing kamin ya dauka.
“Hello”
“Bilal a Maganganun da muka yi a akwai wata magana dana fada maka wacce bata kamata ba ne?”
“Babu”
“Dan me zaka je ka samu Nawwara ka fada mata mun yi magana? Ba dan kowa ya sani yasa na kiraka ba sai dan ganin da na yi hakan ya dace”
“Nima dacewar na gani shiyasa na aikata abunda na aikata, na fada na fasa aurenta ne kuma gobe zan tura a karbo min kayan aurena da na kai gidansu shine kawai abunda ya tada mata hankali take ganin laifin”
Jibril yay saurin mikewa tsaye, maganar ta zo masa a baibai ya fasa aurenta as how shi ba ko dazun da Nawwara take ta kuka tana masa bala'i be tsaya ya tantance takamaimain dalilin da yasa ta haka ba, kawai abunda ya fi ji maganar sa da Bilal da yayi kuma ta ji.
“Ban fahimce ka ba?”
“Na fasa aurenta na ce, hakan yasa tayi tunanin ko kaine ka yi min wani abu sai na fada mata haduwarmu”
“Am amman miyasa ka fassa aurenta?”
“Saboda mahaifiyata bata son auren”
Yana fadar hakan ya kashe wayar be jira ya kara jin abunda Jibril zai ce ba. Farinciki ne da bakinciki suka zo masa a lokaci daya. Ya fasa aurenta yasa shi farinciki but what if shine dalilin fasa auren? Hakan zai sa Nawwara ta kara tsanarshi, bayan haka yasan Bilal yana son Nawwara idan shine yake kokarin aurenta kuma sai wani ya kwace masa ita ya zai ji?
“Amman kuma ai mahaifiyarsa yace da Bilal yana da niyar fasa auren Nawwara saboda da da tuni yayi, ina tunanin abunda ya faru ne yasa mahaifiyarsa ta hana ya aureta”
Ya furta a fili sai ya fadi zaune saman sofa ya lumshe ido.
“Wow da ace zan ganki matar nan da na miki kyauta mai tsoka”
Can kuma ya bude ido.
“I hope you're not fooling me, no he's not ai da Nawwara ba zata yi kuka ba har tana zargina”
Shi kadai yake ta maganarsa ransa fari fal ba zaka ce shine ya dawo gidan da bacin rai ba. Mikewa ya yi tsaye yana ji a ransa cewar addu'arsu ce Allah ya amsa kuma gana ganin he deserved happiness again tun da rayuwarsa ba mai tsawo ba ce. Wayarsa ce dake kan sofa ta yi ringing sai ya juyo da sauri.
“Nawwara”
Ya furta gabansa har bugawa yake da karfi, yana daukar wayar ya ga number Abbah lumshe ido ya yi.
“Oucccc am such a fool taya Nawwara zata kirani yanzu ba bayan fushi take da ni”
Bude idonsa ya yi ya danna picking ya kara a kunne.
“Hello Abbah”
“Jibril kana lafiya?”
“Lafiya kalau Abbah ya Abuja”
“Al-hamdulillah ya Noor yaushe zaka shigo”
“Da dai cikin satin nan ne amman yanzu ban sani ba gaskiya”
“Ya dai kamata kasa lokaci ka zo”
“Wani abun ne?”
“Akwai maganar da ya kamata mu yi”
“Ba zamu iya yi ta waya ba?”
“Magana ce mai muhimmanci zai fi kyau idan kana nan zaka fi fahimtar abun”
“Idan magana mai muhimmanci ce ka fada min a waya dan bana tunanin zuwa yanzu”
“Magana ce akan aurenka Jibril be kamata kana zaune haka nan ba, yarinyar nan da keke so aure zata yi, zama haka ba ba zai maka ba, na sha baka dama ka fitar da wacce kake so sai ka ce sai Nawwara kuma yanzu gashi yarinyar nan aure zata yi, dole ne idan ta yi aure zaka karbo dan ka dan ba zamu barshi can ba, babu yadda zaka yi ta gujeka kuma ta zauna da danka, na san ka yi kuskure kuma ka zalinceta amman ai an bata hakuri so dole ne ka nemi matar aure wacce zata rike maka yaronka”
“Haka ne Abbah amman har yanzu ba a daura mata aure ba ba lallai ne ta auri yaron da yake son ta ba”
“Wai kai ba zaka cire ranka a gareta? Yanzu dai mun yi magana da Hajiya (Step Mother din shi) akwai wata yarsa margayi Alhaji Dahiru wato Salima wacce ta fito sai kaje ka gani idan kana sonta ba zamu cilasta maka ba, amman fa bazawara ce yaranta hudu sai dai duka yaran suna hannun Babansu”
“No Abbah wanda zai auri Nawwara ya fasa aurenta saboda mahaifiyarsa ta hana just saboda abubuwan da suka faru tsakanin mu, shine sai Nawwara ta bada damar na tura nawa magabatan”
Abbah ya dan yi shiru kamin ya ce
“Jibril ka tabbata?”
“Yes Abba, jiya take fada min haka kuma kasan yadda na ke son ta Abbah, ni yanzu abunda na ke so da kai kasa rana cikin satin nan ka zo ku ga iyayenta”
“Jibril ka tabbata”
“Yes Abbah”
“Shikenan zan samu iyayenka na nan mu yi magana”
“Thank You”
Daga haka Abbah ya kashe wayar, sai Jibril ya yi murmushi.
“Idan ma karya ne Bilal yake ai idan Abbah ya zo dole familynta zasu fada masa gaskiya”
Ya fada kana na nufi kitchen dan hada kansa tea.
NAWWARA POV.
Na ci kuka sosai a daren nan, na kasa yarda da abunda Bilal ya fada min na san yana so na dan me mahaifiyarsa zata shiga tsakaninmu? Miyasa idanuwan wasu suke rufewa su kasa fahimtar komai sai kansu. Washe gari da asuba bayan na gama sallah na dauki qur'ane na karanta Yasin wato zuciyar qur'ane, Suratul Yasin tana da fa'idodi da yawa ga musamman ga mutumen da yake cikin matsala da damuwa ta matsalar mijin matukar ka karanta sau goma sha biyar zama daya idan ya gama ya roke Allah bukatarsa idan da hali sai mutum ya yi sadaka, ba ni da halin karanta Yasin sha biyar hakan yasa na karanta ta sau daya na karanta Ayatul Kursiyo dari domin ita ma tana da nata fa'idan sosai kuma idan Allah ya amsa maka kamar yankan wuka yake, bayan na gama na roki Allah ya zaba min abunda duk yafi zama alheri a rayuwata, sannan na aika Jamila ta siyo min kosai na yi sadaka, a lokacin Sakina har ta shirya mana abun kari sun yi breakfast ni ce kawai ban ci komai ba tun tashina.
Dakin Inna na shiga na gaishe ta a lokacin Sakina ta gama shiryawa ita da Jamila suka kama hanyar makaranta, bayan sun fice Inna ta kalleni ta ce.
“Nawwara ki yi hakuri da yadda rayuwa ta zo miki, kuma ki yarda duk abunda Allah ya zaba miki shi yafi zama alheri a gareki, ni dai ina nan ina ta yi miki addu'a, dan haka ki daina sa kanki a damuwa, tashi kije ki zuba abinci ki ci”
Na tada kai na kalleta idanuwa cike da hawaye.
“Amman Inna kina ganin wannan dalilin kawai ya isa yasa Mahaifiyarsa ta hana shi aurena?”
“Ya isa mana, idan kika duba daman can ai ba sonki take ba, kuma tana ganin an wulakanta mata da, ni kaina babu irin maganar da bata fada a gabana ba lokacin da na ke zuwa duba shi, amman idan har Allah ya rubuto ke matarsa ce Wallahi bata isa ta hana ba, ki sawa kanki wannan”
Na gyada mata kai na share hawayena sannan na mike tsaye ina amsa sallamar da naji wani namiji na yi a waje, bakin kofar na nufa babu mayafi a jikina hakan yasa na leka da kai na yayinda jikina yake cikin gidan, wani saurayi saman babur hannunsa rike da ledoji sai ya miko min.
“Ga sako daga Candy Restaurant Jibril ya ce a kawo ma Noor”
Kamar ba zan karba ba, sai kuma na mika hannu na karba ba tare da na ce masa komai ba, dakin Inna na dawo na aje ledodin tare da fadin.
“Wai Jibril ya aiko a kawo ma Noor, ni ban gane masa ba ya raina abincin gidan nan ko mai?”
“Ba raini ba ne, yana ganin dacewar hakan ne kawai”
“Ina Noor din?”
“Yana bandaki tun dazu ya shiga”
Cewar Inna sai gashi ya shigo dakin yana tafiya a hankali.
“Momy gurin kaikayi yake min”
“Karka sosa dai ciwon zai iya tashi”
Na fada masa, sannan na juya na koma dakinmu jin wayata na ringing. Jibril ne yake kirana katse kiran sai ya sake bugowa cikin fushi na dauka
“Wai ba zaka daina kirana ba ne?”
“Amman kin san ba ke na kira ba Noor na kira dan me zaki dauka? Na ce ina son magana da ke ne? Da na na kira kuma kin sani na ce zan siya masa waya saboda na rika kira ta nan kin hana ya kike so na yi”
“Akan me zaka aiko masa da abinci bayan kuma kasan muna da shi”
“Ta nan kika bullo kuma? Na aiko masa ne saboda na san ya saba da abincin ba zai iya cin wani abinci bayan wannan ba a yanzu, kuma ina da hakki na ciyar da dana bana son wata dogowar magana da ke dan Allah ki bashi waya na tambayi lafiyarsa ko kuma na zo gida yanzu na duba shi”
Kashe wayar na yi na koma dakin Inna sai gashi ya kira na mikawa Noor suka gaisa, sun dade suna waya daga karshe Noor ya fita daga dakin ya koma can gurin bandaki yana magana kadan-kadan da alama wani abun yake fada masa, sannan ya dawo ya kawo min wayar.
“Momy wai ya ce yana gaida Inna da kowa da kowa amman ba da ke ba”
Ya fada yana dariya, tabe baki na yi na tashi naje ya dauko kofi na zuba koko nasa suga na dawo dakin na zauna ina sha, domin shi kadai na ke jin zan iya sha kasancewar bana cikin dadin rai. Guraren goma da kwata ina yi ma Noor wanka tsakar gida sai ga Baba Sulaiman ya shigo bakinsa kumshe da sallama. Ina kallonsa nasan ba lafiya ba
“Baba ina kwana?”
“Lafiya kalau ina mahaifiyarki?”
“Tana daki. Inna fito ga Baba”
Na kwara mata kira bayan na bashi amsa. Sai ga Inna ta fito sanye da Hijabinta ta zauna bakin baranda tana gaisawa da shi.
“Na ce masa ko akwai abunda ya shiga tsakanin Bilal da Nawwara ne?”
Na tsayar da wankan da nake ma Noor na kalleshi gabana na faduwa. Sai Inna ta ce
“Miya faru”
“Ya aiko yanzu nan wai a bashi kayan aurensa ya fasa kuma wai ya yi magana da ita ya fada mata yace ta fada mana zai aiko ya karba”
“Sulaiman ai gaka ga yarka waka a bakin mai ita ta fi dadi”
Inna ta fada tana nuna masa ni.
“Ke Nawwara ya aka yi?”
“Jiya ne da yazo ya ce wai mahaifiyarsa ta ce bata yafe masa ya aureni ba, shine ya ce ya fasa aurena...”
Na fada ina kokarin fashewa da kuka.
“Daman Wallahi sai da muka raya a haka dukan mu sai da muka yi maganar nan, daman nasan irin rigingimun da suka faru ba zata bari ya aureki ba, Yakunbo ma sai da ta ce haka, amman matar nan ba ta yi tunani ba sam”
“Ni kaina na zargi hakan ganin irin maganganun da suke ta fada gabana”
“Ni kaina ina jin wasu abubuwan sai dai ka toshe kunnenka tun da ba a taruwa a zama daya, kuma a unguwar nan ma har a abunda ya kai unguwarmu babu abunda mutane basu fada ba, kuma kin san mutane da zuga Allah yasa haka shi ya fi alheri”
“Amin, nima haka na ce kuma in mijinta ne babu wanda ya isa ya shiga tsakaninsu”
“Tau Allah ya kyauta daman dai na ce sai na ji ta bakinta ne kamin mu bada kayan, Allah ya baki wani”
Ya fada ganin irin hawayen da nake, sannan ya mike tsaye ya fice cike da damuwa, daman kayan ba a nan suke ba, tun da aka kawo lefen aka maida shi can gurin Yakunbo kasancewar nan gidan ba Namijj kuma ina tsoron kar a biyo dare a tararda mu. A gaskiya na ji babu dadi na ji ni a cikin wani kalar yanayi mai kamar an yi min mutuwa, ban tabbatar da cewar Ina son Bilal sai a wannan lokacin, yanzu shikenan an raba mu kenan? A wunin ranar kasa sukuni na yi a cikin gidan mu, ana kiran la'asar na dauki Hijabi na nufi gidansu Jidda. Ina shiga na fashe musu da kuka daga ita har Maman Nura wato mahaifiyarta sai da hakalinsu ya tashi, sun tausaya min kuma sun nuna min rashin jidadinsu a fili lokacin da na labarta musu abunda ya faru.
“Yanzu duk soyayyar nan da kuka yi da Bilal ace be aureki ba gaskiya abun be yi dadi ba”
Cewar Jidda, sai Mahaifiyarta ta ce.
“Ni daman Wallahi ban dai fada ba ne, amman na san ba duka iyayene zasu iya bari dansu ya auri bazarawa ba, ko mai aure daya balle mai biyu kuma har da da, yanxu kuma ga abunda ya faru”
“Amman ni Wallahi da zaki min wani abu da kin auri Jibril ko dan mahaifiyarsa ta ji haushi, kuma ga Noor sannan mutumen yana son ki sosai, kin ga sai ma ya maiye gurbin kwanakin da suka rage a daura miki aure da shi”
Jidda ta fada, sai mahaifiyarta ta karba nata.
“Ni dai haka na gani, wani lokacin abunda kake so ba lallai ne ya zama alheri a gareka ba, kuma so da yawa kana kin abu ya zama shine alheri a gareka, ki baiwa Allah zabi kawai”
Wani irin abu na ji ya daki zuciyata, sam bana jin zan iya kara zaman aure da Jibril, indai har ban aure Bilal ba to be cancan na auri Jibril ba, taya ma zan yi zaman aure da mutumen da ya wulakanta ni ya nuna min ba ni muhimmanci a rayuwarsa.
“Na baiwa Allah zabi kuma na san zai zaba min abunda duk yafi zama alheri a gareni, amman ina jin kamar ba zan iya zaman aure da Jibril ba”
Jidda ta dafani.
“Zaki iya Nawwara, tunda kina son Noor kuma kina son farincikin danki, karki damu da rashin son da kike masa, abu mai muhimmanci shi yana sonki kuma so mai tsanani, kuma kinsan hausawa na cewa mai son ka be ganin ramarka, kuma kara ka auri wanda sonshi ya fi na ka yawa zaka fi jindadin zaman aure fiye da wanda ke kika fi sonshi, zan cigaba da miki addu'a kamar yadda na ke yi ma kaina Insha-Allah”
Hawayena na share na gyara zamana, ita kuma ta tashi ta fita saboda kiranta da aka yi a waya. Sai kusan magariba na baron gidan na dawo gida.
Bayan na yi sallama magariba na zauna ina ta karanta lahaula wala'kuwwati da carbi adadin da zan iya, saboda tana yaye damuwa kuma matukar kana cikin damuwa ka lizinci karanta ta Allah zai maka mafita.
Can kusan sallah isha'i na kira wayar Bilal sai suka nuna userbusy haka na yi ta trying suna amman na kasa samu daga karshe na gane ya saka number ta a blacklist ne. Wasa wasa aka kwana uku a haka na kasa cin abincin kirki saboda tunani, ba damuwa ce ta dame ni ba damuwar Bilal ce ta dame ni domin na san yana so na, kuma mutane da yawa zasu masa dariya idan har be aureni ba, duk na bi na rame kamar marar lafiya, jikina babu wani kuzarin kirki kasancewar bana iya cin abinci mai nauyi sai fura ko koko ko tea.
Ranar da aka kwana hudu da faruwar hakan ina zaune, da misalin biyar da rabi na yamma sai ga Asiya yar wajen Baba Sulaiman ta zo kiran wai na zo Baba Sulaiman da Baba Dahiru suna kirana, gabana ya fadi da farko kuma naji tsoro sai dai ance karka ji tsoron kira ka ji tsoron laifi da ka yi, kuma ina tunanin addu'a ta ce Allah ya amsa wata kila iyayen Bilal ne suka dawo a gyara maganar.
Sai da na fadawa Inna sannan na dauki Hijabi na saka muka fita tare. Muna shiga zauren gidan gabana ya fadi ganin Baba Sulaman da Baba Dahiru da kuma Baba Audi wato kanen mahaifina da yayyensa a zaune saman tabarma tare da Mahaifin Jibril da abokinsa wanda suka zo tare lokacin da wadancan abubuwan suka faru da kuma Yayan Jibril da wasu mutane maza da ban wayancin fuskarsu ba a zazzaune.
Sallama na fara yi bayan sun amsa gaishesu sai Baba Sulaiman ya nuna inda zan zauna, ba musu na zauna kaina a kasa gabana sai faduwa yake ina jiran jin dalilin kiran.
“Jibril ne ya aiko da iyayensa su nema mishi aurenki kuma ya ce kun yi magana da shi akan cewar zai aiko kin amince, amman mu baki fada mana ba, hakan yasa na ce ba za a yanke hukunci ba sai an kiraki an ji ta bakinki”
Na yi shiru ban ce komai ba, still kaina a kasa zuciyarta cike da tsanar Jibril. Sai Baba Audi ya katsa min tsawa.
“Ki bude baki ki yi magana mana, dukan mu ba yara balle ki tsaya yi mana wasa, da baki muke son jin amsarki ba da shiru domin ke bazawara ce ba budurwa ba, cewar kin amince shi zai tabbatar mana da cewar kin amince haka Annabi ya ce”
Dago kaina na yi na kallesu dukansu ni suke kallo amsata kawai suke son jin...
*Shafin nan na ku ne Khadeeja Candy Novels more Especially Maman Hafiz*