"Wayyo Allahna Aunty Nazeer ya sakeni saki biyu,nashiga uku na lalace daga ina zan fara,Aunty asirina ya gama tonuwa,Amnah tayi nassarar rabani da Nazeer mai nayi mata zata min haka" Firdausi tace tana fashewa da matsanancin kuka,a fusace Aunty ta fito daga d'akin tana daka mata tsawa,
"Dalla rufemin baki kafin naci ubanki,abinda kike nema kika samu karki k'ara cewa Amnah ce tasa a sakeki,mai nata a ciki,hankalinki ya kwanta yanzu tunda kin k'arbi certificate d'inki a hannu,Amnah tana can hankalinta kwance,duk hak'urin Nazeer sai da kika kai shi Bango yamiki saki uku,ba irin abinda bakya mishi,amma haka yacigaba da hak'uri dake,kina tunanin da tsohon mijin Amnah kika aura kin isa kiyi mishi Rabin abinda kike wa Nazeer ai ba saki uku kawai zai miki ba,wlh sai ya miki shegen duka kafin ya sake ki, matuniyar banza,matuniyar wofi,kina matar aure, kifita bada izinin mijinki ba,kije kiyi kwana da kwanaki gaki ishashiya kawayenki duk sunfi ki wayyo tunda dukansu suna gidajen mazajensu asirinsu a rufe, ke kuwa gaki kin dawo cikin kanenki,sabida Zaman kanki kikeyi,yamiki kyau,yanzu ai kin shiga hankalinki,kuma wlh ke zaki koma soya awara kina siyarmin,tunda abinda kika zabawa kanki kenan ko nan da k'ofar gida ban yarda ki leka ba,kina gama idda zan had'aki da sallau mai wanki da guga ya aureki na huta," wani irin ihu Firdausi tasa da taji abinda Aunty tace, tana,
"Aunty ki taimaka min ki kira min Nazeer ya maidani d'akina wlh na tuba nadaina abinda nakeyi,wlh bazan iya rayuwar talauci ba,wa zan samu na aura mai irin rufin asirin Nazeer, wayyo Allahna na cuci kaina na baro k'aton gidana mai A C a ko ina," dariya Aunty ta kwashe dashi tace
"Aikuwa dai gashi kindawo gidan da babu Ac sai mifici,ga suyan awara ma da zaki fara zaki bar hajiya Firdausi ki koma Firdausi mai awara shashasha kawai"d'aki ta koma tabar Firdausi a tsakar gida sai kuka take,muryarta ya dashe sabida kukan datasha,sai da ta samu minti talatin a tsakar gida kafin ta iya shiga d'akinsu tana rik'e kai dan wani irin azababban ciwon kai takeyi.
Amnah kuwa sai data kwashi hour d'aya tana zaune a palo, kafin ta iya shiga d'akin Nazeer dan add'ua tarin gayi Allah yasa ba sakin Firdausi yayi ba,a zaune ta sameshi yana danne danne a system d'inshi,ko d'agowa bai yi ba ahaka ya amsa sallamar hankalinsa na kan abinda yake yi,cikin sanyin jiki ta k'arasa gefenshi ta zauna tana kallonshi,ganin bashida alamar ma ya bar abinda yake ne yasa tafara k'ok'arin magana,hannu ya daga mata yace " pls akwai abinda nakeyi mai mahimmanci,ki barni banaso nayi maganar daya danganci Firdausi na rufe babinta,"
"Nasani Nazeer ba zancenta zan ma ba,tambaya kawai nakeso nayi maka wane sak'o kace taje ta k'arba a gidansu,Allah yasa ba sakinta kayi ba Nazeer" ?Amnah tace tana mai kura mishi ido,.
"Na saketa Amnah bazan iya cigaba da zama da ba," sallati Amnah taringayi tana girgiza kai d'aurewa tayi tace "saki nawa kayi mata"?
" saki biyu nayi mata,Amnah dan Allah kidaina min zancen Firdausi ki barni nayi aikin dake gabana,kuka Amnah taringayi wiwi kamar ita aka saka, sai da Nazeer yabar mata d'akin.
aranar Amnah Sam batayi barci ba dan tunani taringayi Firdausi zatayi tunanin da saninta aka saketa,inda b'angaren Firdausi ma ranar bata ga barci ba,dan kuka ta kwana tana yi tana nadamar biyewa zuciyarta,gashi yanzu ta cuci kanta.
Rayuwa tayiwa Firdausi tsanani dan Aunty bata tausayawa mata ko kad'an wuni Firdausi takeyi tana aiki,abinka da bata saba da wahala ba tuni ta rame tayi bak'i kullum cikin kuka take,daddare kuwa kasa barci takeyi,tana tunanin d'aular data baro, yanzu Amnah kadai ke fantamawarta,sai ayanzu take k'ara nadamar abinda tayi tana ikon Allah ya wuce wasa Wai ita da take hajiyar kanta,take abinda ranta keso sai gashi,wai itace ta dawo tana soya awara,duk da duk wani abinda ta mallaka Nazeer yasa ankawo mata har da motarta,amma Sam bata jin dad'in rayuwarta,kullum tunaninta wa zata aura dazai kai Nazeer hakuri,dazai jure abinda take masa tana cikin rufin asiri ALLAH gashi ta tonawa kanta asiri,duk Wanda zata aura nan gaba tasan bai isa ya kama k'afar Nazeer ba,inta tuno yanzu Amnah kad'ai ce a gidanta yanzu takanyi kuka kamar ta had'iyi zuciya ta mutu,dan da ta k'wantar da hankalinta da yanzu tana gidanta cikin rufin asiri amatsayin uwargida,waya sani ma yanzu inta tashi aure taje ata biyu,uku ko hud'u,ire iren tunanin da Firdausi ke yi kenan idan tazo kwanciya barci.
B'angaren Nazeer kuwa hankalinsa a kwance yake,dan har wani k'iba yayi,dan yanzu bashida fargabar komai hankalinsa a kwance yake maida hankalinsa yayi kan Amnah yana tattalinta kamar kwai,dan yana masifar ji da cikin dake jikinta,inda Amnah bata nemi komai ta rasa ba sai dai ta godewa Allah,Abu d'aya take tunawa ya rage mata jin d'adi,Al ameen,bata San halin da yake ciki,dan kwanaki dataje gida,ta tarar da hajiya Mariya mahaifiyar Al ameen a gidan tana kuka,tana bawa Ummi labarin Al ameen yak'i ya yarda da kaddara ya hak'ura da Amnah babu abinda batayi ba akan yayi aure,yak'i yayi yace shi da aure har abada,tunda ya rasa Amnah ya gama aure, kuka hajiya Mariyar ta fashe dashi tana Ummi ta taimaka mata da add'ua,Amnah da zuwanta kenan tazo shiga ciki,muryar hajiya Mariya dataji ne yasa ta tsaya tana jin hirar da sukeyi ,toshe bakinta tayi sabida kukan daya taho mata na tsananin tausayin Al ameen dan har ga Allah tasan Al ameen na balain Santa itama San da take mishi har jibi bata yiwa Nazeer irinshi,kawai d'aurewa tayi ta cireshi aranta,amma yanzu maganar da taji hajiya Mariya nagayawa Ummi yasa tausayi da San Al ameen ya kara mammayeta,istigifari tayi da sauri ta goge fuskarta,tashiga gidan da sallamarta,d'urkusa wa tayi tana gaishesu Hajiya Mariya tayi Sauri ta d'agota ta rungume ta tana ce mata "'yar albarka shine kika manta dani kika watsar damu ko tuna ni bakya yi mai nayi miki haka"?
kuka Amnah ta fashe dashi tana "bahaka bane tana sane dasu," d'agota tayi daga jikinta tana k'are mata kallo tace "masha Allah Amnah Ashe ciki ne dake Allah ya raba lafiya,Ashe ma rabon cikin ne yasa kuka rabu da Al ameen, yanzu idan naje gida Nace mishi ya k'wantar da hankalinsa kina nan kin kusa haihuwa,idan zai nutsu ma yayi aure,yayi Allah ya Riga ya kaddara rabuwarku" Amnah batace komai ba sai murmushin yak'e datayi ta mik'e ta shiga d'aki,aranar da tausayin Al ameen ta wuni tana tunanin inya ji labarin tana da ciki ko ya zaiyi.
Al ameen da gabad'aya ya zama abun tausayi da k'arfin add'ua ya daina shaye shaye,yazama wani shiru shiru,wani islamiyya ya Shiga da manyan samari da magidanta suke zuwa duk bayan sallar Asuba da isha,hakan ne ya taimaka masa wajen samun nutsuwa yafara k'ok'arin cire Amnah a zuciyarsa amma San Amnah na nan daram aransa,wani Sain Idan San Amnah ya motsa mishi ya kanyi kuka yayi nadamar R🅰SHIN H🅰KURINSA ya janyo mishi ya rasa b'angaren rayuwarsa,ranar da hajiya Mariya ta fad'a masa taga Amnah har da ciki,gwara ma inzai cireta aransa yayi aurensa dan Amnah ta ma manta dashi,aranar Al ameen kamar yayi hauka wai Amnarsa tana d'auke da cikin wani,sai daya samu kwana uku yana rashin lafiya, bayan ya warke ya d'age da addua na Allah ya cire masa San Amnah a zuciyarsa da taimakon addua yafara manta Amnah,inda hakan yayiwa Hajiya Mariya d'adi,tafara kawo mishi tallan 'yan mata,Inda yace ya bata w'uka da nama ta zab'a masa mai hankali,dan shi yasan yagama auren so,Cikin farinciki hajiya Mariya ta zaba mishi wata 'yar kawarta Kubrah yarinya mai hankali,a shekarar ta gama secondary schools ,cikin kankanin lokaci manya suka shiga zancen aka sa rana,Inda Al ameen ko a jikinsa dan zai yi aurene kawai Dan ya farantawa hajiya Mariya.
Kwanaki da watanni nata shud'ewa cikin Amnah ya tsufa haihuwa yau ko gobe,inda Firdausi bayan ta gama idda zawarawa suka hau yi mata layi ita kuwa ko kallon inda suke batayi Dan duk cikinsu babu Wanda take ganin ya dace da ita, inda cikin gida kuwa ba k'aramin matsi take fuskanta ba dan daga Auntyn har kanenta babu Wanda ya barta,rashin mutunci kawai suke mata hakan data gani ne yasa tafara tunanin tsayar da wani ta aura ta huta da da abinda kanenta ke mata Dan duk sun rainata.
B'angaren Al ameen kuwa tunda aka d'aura mishi aure da kubrah bai tab'a kallon Inda take ba gaisuwa kawai ke had'asu sai kud'in cafene da yake ajiye mata,d'akinsa daban nata daban,hakan kuwa bak'aramin damun Kubrah yake ba,Dan ita tana San Al ameen,babu abinda batayi ba Dan taja hankalinsa,amma Al ameen bai San tanayi ba,shawarar ta yanke zata samu Al ameen ta mishi magana,aranar kwalliya tayi sosai da kananan kaya,tayi girke girke ta kame a Palo tana jiran dawowarshi,tana jin dirin motarsa gabanta ya hau fad'uwa.
[8/5, 9:01 PM] Sadnaf: R🅰SHIN H🅰KURI
Written by
💅💅SADNAF💞
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
*We don't just entertain and educate we touch the ❤ heart of the readers*
P.M.L
*Na sadaukar da shafin nan ga dukanin masoyana masu k'aunata da Wanda nasani da Wanda bansani ba Allah ya biya muku buk'atunku na alheri fatan alheri da kuke min banida bakin gode muku sai dai nace Allah ya saka muku da alheri duk wacce na tab'a b'atawa rai tayi hakuri ta yafemin kunsan dan Adam ajizi ne kana rayuwa ne baka San lokacin mutuwarka ba,Allah yasa mucika da kyau da imani kuskuren da nayi a littafin nan Allah ka dubeni da idon rahama ka yafemin*❤❤❤❤❤❤
*JINJINAN BAN GIRMA GAREKI ZEE ZEE,ALLAH YA ALBARKACI RAYUWARKI YA BIYA MIKI BUKATUNKI NA ALHERI ILYSVM* 💕💕💕💕
🔚
Page 30
Sunkuyar da kanta tayi tafara murza zoben hanunta tana tunanin yanda zata mishi magana dan tunda sukayi aure, magana mai tsayi bata tab'a had'asu ba,sallamar da yayi tareda shigowa ne ya katse mata tunanin da take,amsa sallamar tayi tana mik'ewa tana mishi sannu da zuwa,kau da kansa yayi,yabi ta gefenta da sauri yana amsawa,d'akinsa ya shige ya rufo k'ofar,Kubrah komawa tayi ta zauna tayi tagumi,tana tunanin shawo kan Al ameen sai tayi da gaske,ahaka ta zauna a Palo ya k'ara fitowa daga d'aki hanunsa rik'e da qurani,bai kalleta ba yace mata "natafi makaranta sai na dawo"
"A dawo lafiya tace tana binsa abaya dan ta rakashi,kafin ma taje bakin k'ofa har ya fice, girgiza kai tayi tana tunanin aikin dake gabanta,sak'a da warwara tafara yi tana Neman mafita,sai data kusa awa d'aya a zaune ganin tunanin ba zai fisheta ba yasa ta nufi d'akinta,tayi sallah,wanka ta k'arayi taci kwalliya da Riga da skirt yan kanti ba laifi tayi kyau kasancewarta fara tasa bak'in kaya duk da farin nata ta had'a da mai,turare ta fesa a kowane lungu da sak'o na jikinta ta fito ta kwanta a 3 seater, ba Al ameen ne yashigo gidan ba sai Tara da rabi,a lokacin har tafara bacci,k'ofar palon ya rufe yana k'ok'arin wucewa d'akinsa, juyowa yayi da sauri yana kallonta dan bai San ma tana palon ba,ganin barci take ne yasa ya dan tsaya yana k'are mata kallo,numfashinsa ne yafara fita da sauri da sauri,sakamakon wani irin Sha'awarta data fara fusgarsa dan rabonshi da mace tun lokacin da Amnah take zuwa gidanshi,Kubrah bud'e idonta tayi a hankali suka had'a ido, da sauri yayi hanyar d'akinsa ita kuma ta mik'e tana mishi sannu da zuwa,dining ta nufa ta d'auko trayn d'in data jera abincinsa ta nufi d'akinsa dashi,tura k'ofar tayi had'e da sallama,jin motsinsa da tayi a band'aki ne yasa ta Shiga ta ajiye farantin tafita waje dan tasan wanka yakeyi,bayan minti goma sha biyar ta koma d'akin,k'irjinta sai dukan uku uku yakeyi,dan bata san ta yanda zata yiwa Al ameen magana ba,sallama tayi tare da sunkuyar dakai,yana zaune akan gado dagashi sai vest da gajeran wando,yana dana waya, amsa sallamar yayi batare da ya d'ago ba,farantin data ajiye akan carpet ta d'auko ta ajiye agaban gadon ta zauna a kasa tafara k'ok'arin bud'e kulollin dan ta zuba mishi abincin,dakatar da ita yayi bai d'ago ba yace
"Kibarshi a
koshe nake na biya ta wajen hajiya naci abinci"
D'agowa tayi tana kallonsa nan da nan hawaye ya fara taruwa a idonta,magana tafara yi cikin rawar murya " Haba Al ameen meyesa kake min haka duk k'ok'arina a gidanan dan naga na faranta maka rai baka gani,tunda ka auroni wata uku kenan baka tab'a min magana ko na minti biyar ba,gaisuwa kawai ke had'amu inayi girki baka ci,bakasan a ya nake kwana ba,nasan tilasta maka akayi ka aureni ba sona kakeyi ba,amma ko yaya ne Al ameen kasama min gurbi a zuciyarka,zan faranta maka rai fiye da Amnah,"
d'agowa yayi da sauri yana kallonta tunda suke da ita sai yau ya tab'a kallonta ido cikin ido,girgiza kai yayi tare da cije lebb'ensa yafara magana
"Kiyi hakuri ba laifina bane nakasa sakin jiki dake ne matsayin mata ta nakasa cire Amnah a zuciyata,so d'aya tak Amnah nake yiwa shi duk da tayi aure tana karkashin wani,R🅰SHIN H🅰KURINA ya janyo min na rasata,Kubrah kiyi hakuri,nasan bana kyautata miki ki tayani da addua Allah ya bani ikon manta Amnah,dan tunda na aureki nake tunanin ta yanda zan fara rayuwar aure dake,dan rayuwata komai da Amnah na tsara,amma Allahu ya kaddara sai mun rabu duk da muna San juna,Kubrah bazaki gane ba ni kadai nasan mai nakeji a zuciyata,da ace hanun agogo zai koma baya tabbas da nafi kowa jin dadi,amma Ina bakin alkalami yariga ya bushe har jibi ina takaicin rashin kai zuciyata nesa" shiru yayi ya sunkuyar da kansa zuciyarsa na masa zafi Dan ji yake kamar a lokacin ya saki Amnah
Cikin tsananin tausayawa Kubrah ta goge hawayen dake zubo mata dan ita tausayi ya bata sabida itama ta San zafin rabuwa da masoyi tunda itama wanda taso arayuwa sun rabu sakamakon mahaifiyarshi data dage bazai aureta ba sai dai bayan ranta,cikin sigar lallashi ta matsa kusa dashi,ta kamo hanunsa tafara magana
" I know how you feel Al ameen nasan radadin rabuwa da masoyi,dan nima nan victim ce, amma inaso kasan wani Abu ba komai kakeso a rayuwa Allah ke baka ba,Allah zai iya jarrabtarka da abinda kafiso a rayuwa dan ya gwada imaninka yaga zaka iya cinyewa,idan kayi hakuri,sai ka ga a karshe ya musanya maka da Wanda yafi alheri,amma Al ameen kai ka kasa cinye jarrabawar da Allah yayi maka,ka rungume kaddara,Al ameen meyesa bazaka yarda da jarrabtar da Allah yayi maka ba ka mik'a masa al amuranka ya Isar ma,? Amnah ai itama tana balain San naka ta wuce tayi aurenta hankalinta kuma a kwance,kaga kenan ita ta rungumi kaddararta da hannu biyu,amma Al ameen kai ka kasa,pls move on with your life and accept your destiny,kamar yanda Amnah ta cigaba da rayuwarta" duk maganar nan da takeyi kansa a sunkuye yake sai hawaye ke zubo mishi,dan maganar da kubrah takeyi ta shige shi sosai,d'agowa yayi yana kallonta yafara magana" hakika na godewa Allah daya bani mace mai zurfin tunanin da hangen nesa insha Allahu daga yau zan yakice Amnah a zuciyata dafatan nima zaki tayani da addua?" Gyad'a mishi kai tayi tana murmushi,mik'ewa tayi tace mishi zataje ta kwanta,hanunta ya ruk'o ta juyo tana kallonsa,sunkuyar da kanta tayi sakamakon wani irin kallo da yake mata,can kasan murya yace mata "bazaki kwana anan ba"?shiru tayi takasa magana jikinta ya hau rawa, mik'ewa yayi ya janyota tafad'a jikinshi kafin ta anakara ya had'e bakinsu,tsayuwa gagararsu tayi sai da suka zube akan gado,nima na zube a Palo, dan abun yafi k'arfina,tunda ga lokacin Al ameen yafara k'ok'arin cire Amnah aransa,Dan ba laifi itama Kubrah tasan yanda zata kula da miji duk da bata kama k'afar Amnah ba.
B'angaren Firdausi kuwa ta samu ta tsayar da wani Alhaji dahiru mai takalmi dan acikin mane manta shine mai dan k'wari k'wari,matansa biyu,ita zataje a ta uku,bata wani sanshi,kawai zata aureshi ne dan ta huta da wahalhalun gidansu dan har jibi ita take soya awara,duk tayi bak'i ta rame,inta zauna ta tuna irin damar data samu a rayuwa ya kubce mata ta kanyi kuka,Alhaji Dahiru ya tura magabatansa can gidan yayan mahaifinsu Firdausi, inda suka tsayar da magana suka sa rana sati hud'u,ana saura sati biyu bikinta,watarana tana zaune a gindin murhu tana soya awara da yamma,Aunty tana yanka albasa da tumatir,sallamar Nazeer taji kamar a mafarki,ya shigo shi da little,dan hajiya Aliya mahaifiyar Nazeer kullum sai tacewa Nazeer yakai Little gidansu Firdausi taga mahaifiyarta,dan itama tasan Firdausi tana so taga 'yarta tunda kusan kullum ne sai Firdausin ta kirata ta tambayeta little,yawan magana da fad'a da hajiya Aliya ke yawan yi ne yasa Nazeer yasa lokaci ya shirya shi da little suka nufi gidansu Firdausi, sakin baki Firdausi tayi tabi Nazeer da little da kallo, dan Nazeer ya canja gabad'aya kamar ba shi ba dan ya zama Dan lukuti,ga wani fari daya k'ara yi,Aunty sallamar da yayi ta amsa ta mik'e tana mishi sannu da zuwa,tabarma ta shimfid'a mishi, ya zauna yana k'ara gaisheta bai lura da Firdausi ba,Aunty kuwa kamo hanun little tayi tana CE mata "kin mantani ko"? Firdausi hawaye dake zubo mata ta share ta kwashe awaran dake kan wuta tafito daga rumfar tana gaishe shi,juyowa yayi da sauri ya kalleta yana amsawa mamaki ne yabi ya cika shi dayaga yanda Firdausi ta canja satar kallon rumfar yayi yaga awara data soya girgiza kai yayi yace aransa "idan ka k'i shara massallaci kayi ta kasuwa,idan baka godewa niimar Allah ba ka godewa azabarsa."
wurin little tayi dake kan cinyar Aunty ta mik'a hannu tana k'ok'arin ruk'o hanunta,nok'ewa little tayi ta mak'e kafad'a alaman bazata zo ba,hawaye ne ya zubowa Firdausi tana "mamana kin mantani ko? K'ara mak'e kafad'a tayi ta mik'e ta koma kan cinyar Nazeer,binta tayi da kallo ta maida kallonta kan Nazeer suka had'a ido,kau da kansa yayi,wani kuka mai k'arfine ya k'wace mata tayi d'akinsu da gudu, Nazeer kuwa tausayinta ne ya lullub'eshi, mik'ewa yayi yana cewa " Aunty zai tafi dama little ya kawo dan ta musu weekend zai dawo ran lahadi ya d'auketa little ihu tafara zundumawa dataji za a tafi abarta,kankameshi tayi tana yakaita gurin Aunty Amnah ita bazata zauna anan ba,wani irin zafi k'irjin Firdausi yafara mata dataji abinda little ke cewa,Aunty kuwa ganin little bazata yarda ta zauna bane yasa tace mishi ya tafi da ita kawai,rafar Dari biyar Biyar ya Ciro daga aljihunsa ya ajiye akan tabarma yace mata " gashi bayawa "godiya tafara mishi tana sa mishi albarka,har bakin zaure ta rakashi,tana ya gaida su hajiya sai da yana dab da fita take CE mishi ta manta bata gaya mishi ba sati biyu masu zuwa zaa d'aurawa Firdausi aure,murmushi Nazeer yayi yaringa Allah ya Sanya alheri,yacewa Aunty ta turo mishi Firdausi ya mata Allah ya sanya alheri,Aunty k'wala mata kira tayi,tafito daga d'akin tana sanye da zundumemen hijabi har kasa,idonta yayi jazur sabida kukan data sha,hanyar waje tayi tana fitowa Nazeer dariya ta k'wace masa Dan tunda yake bai tab'a ganin Firdausi da hijabi ba,dariyar da Firdausi taga Nazeer yayi ne yasa hawaye ya k'ara zubo mata,sallama tayi mishi ya amsa yana kallonta,magana tafara yi tana ya yafe mata abinda tayi mishi tasan alhakinsa ke dawainiya da ita,ce mata yayi ya dade da yafe mata,anan ya mata Allah ya Sanya alheri ya mata nasiha sosai,dazai tafi ya d'auko check book ya rubuta 500k ya bata,godiya ta ringa mishi tana kuka ahaka yaja motarsa yatafi tana daga mishi hannu,aranar Firdausi taci kuka ta gode Allah.
A daren Ranar Amnah ta haifi santallelen d'a namiji awani tsadadden asibitin fad'ar murna da farincikin da Nazeer da familynsa suka yi bata bakine Dan Nazeer kud'i ya ringa rabawa ma'aikatan asibitin kamar bai San zafinsu ba,washegari aka sallamesu daga asibiti suka wuce Sabon gidan da Nazeer ya gina,yan uwa da abokanan arziki tururuwa suka ringa yi suna zuwa barka suna kashe kwarkwatan idonsu, Dan bak'aramin dukiya Nazeer ya kashe a ginin gidan ba,mai jego kuwa it a da babynta suna samun kulawa sosai, Amnah tayi kyau tayi wani fari kamar ba mai jego ba, shirye shirye aka ringa yi sosai dan Nazeer ya saki bakin aljihu,kasancewar Nazeer fittace kuma sananne, tuni gari ya d'auka anyi mishi haihuwa,inda Firdausi itama taji labarin haihuwar,Aunty ce tace ta shirya taje ta mata barka,tace zata je sai ranar suna,ana gobe suna daddare Amnah bayan tayi wanka ita da babynta tana zaune tana shan ferfesun kai da k'afa da aka zubo mata,Nazeer ne ya shigo d'akin ya zauna a gefenta ya d'auki babyn ya zuba mishi ido yana murmushi,kallon Amnah yayi yace,
"Kin iya haihuwa yaron nan dani yake kama" murmushi Amnah tayi ba tace komai ba,
"Wane suna kike ganin ya kamata musa mishi"? Nazeer yace yana kallonta,shiru Amnah tayi tafara tunanin dama ya yarda data ce mishi asa mishi Muhammad Al ameen, "kinyi shiru"
"Kasa mishi sunan da kake ganin ya dace kawai"
"Na baki w'uka da nama ki zabi sunan da kikeso" girgiza masa kai tayi tace ya zaba kawai gyad'a Kansa yayi yace "to shikenan ni nasan sunan da zan sa mishi" mik'ewa yayi,yayi hanyar waje tayi sauri tace "wane suna zaka sa mishi"? Juyowa yayi yace " Muhammad Al ameen " wani irin farinciki ne ya mamayeta Wanda hakan ya Gaza b'oyuwa a fuskarta,Nazeer kuwa ya zabi yasa sunan Al ameen ne sabida ya faranta mata rai Dan yasan har jibi tana San shi.
Washegari kuwa tun k'arfe shida na safe aka fara cika a gidan ,Shanuwa biyu Nazeer ya yanka da rago manya guda biyu, k'ofar gida ma acike yake da jamaa sai fito da kulolli ake, mai jego kuwa taci kwalliya ita da Muhammad Al ameen sai k'yalli suke,kayan barka kuwa kamar an bud'e kanti, k'arfe uku dai dai Firdausi da Aunty suka isa gidan tun a bakin gate Firdausi ta saki baki tana kallon gidan,har suka k'arasa ciki,gefe d'aya ta samu ta zauna tana bin ko ina da kallo,ko minti biyar batayi da zama ba,caterers suka cika mata gabanta da abinci kala kala,muryar Amnah ta juyo a bayanta tana bada oda a kai wa wasu abinci,juyawa tayi a hankali tana kallonta,sanye take da bugaggiyar shadda sai maiko take yasha aikin Senegalese, tasha tapka tapkan gold, hawaye Firdausi ta hau yi tana tunanin da yanzu itama tana cikin irin wanan daular,ganin Amnah ta ruk'o hanun little,sun yo inda take ne yasa tayi Sauri ta sunkuyar dakai,Amnah kuwa bata ganta ba tana dab da shiga d'akinta taji sallamar Siyama da Alawiyya dagudu Amnah taje ta rungumesu tana dama rai kanga rai,Inda Firdausi kuwa hawaye ya hau tsare a kumatunta,dan ganin da tayi sai kana dashi ake damawa dakai, yanzu su siyama sun dawo wajen Amnah,tana ganin sun shiga d'aki basu lura da ita ba yasa ta mik'e tayi waje,Aunty sai kiranta take tak'i juyowa,gida ta wuce tana isa ta zube akasa taringa kuka,dan zuwan datayi taga Amnah ya sa taji kamar ta hadiyi zuciya ta mutu
Can kuwa wajen suna mahaifiyar Al ameen ma tasamu zuwa suna ita da Kubrah Inda suka kaiwa Amnah kayan barka akwati guda,Amnah kuwa rasa inda zata sa hajiya Mariya tayi Dan murna,Dan gani take kamar Al ameen ne yazo,sai satar kallon juna suke ita da kubrah,dasuka tashi tafiya da kaya Niki Niki ta rakasu,ta bawa kubrah wani bak'in leda tace
Tabawa Al ameen, Kubrah kuwa data isa gida bawa Al ameen ledar tayi,tace inji Amnah cikin tsananin farinciki ya k'arba ya bud'e dambun nama ne a cikin ledar dayake Amnah tasan yana masifar San dambun nama,hannu yasa yadebo yazuba a bakinshi,Kubrah kuwa ganin yanda yake cikin farinciki ne yasa itama ta hau bashi labarin sunansa aka sawa yaron,cikin tsananin farincki ya rungume Kubrah yafara shafa cikinta yana itama inta haihu sunan Amnah zai sa Indai Mace ta Haifa.
Rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya,an d'aura auren Firdausi da Alhaji dahiru mai takalmi,inda aka mik'ata gidanta dake Court road ba laifi gidan yayi kyau,Firdausi kuwa ta kwantar da hankalinta ta cire komai aranta, tasha alwashin rik'e aurenta da hannu bibiyu,duk wani abunda ta mallaka ta siyar dasu tana juya kud'in ta dogara da kanta,bata tsayawa ta jira kud'in da Alhaji Dahiru zai bata, bata da matsala ko kad'an sai na kishiyarta Maryam data takura mata Dan ita uwargida babu ruwanta,kullum sai tazo taci mata mutunci,duk da ba a gida d'aya suke ba,Idan tazo Firdausi kan ci kuka ta gode Allah ta kuma tuna Ashe haka Amnah keji idan tayi mata rashin mutunci,atakaice sai da Alhaji Dahiru shima yayiwa maryam Saki d'aya Kafin ta shiga hankalinta ta daina takurawa Firdausi.
Amnah kuwa tazama hajiya Dan Nazeer yana kula dasu sosai, junior ya girma yayi bulbul abunshi.
B'angaren su Al ameen kuwa kubrah tayi nasarar sace zuciyarsa dan tana kyautata masa sosai,ya k'wallafa rai sosai acikin da ta ke d'auke dashi ,Dan burinsa ta haifi Mace yasa sunan Amnah.
Anan na kawo karshen novel din rashin hakuri Allah ya yafemin kuskuren danayi aciki sai kunjini a sabon novels dina
NASREEN
ANA WATA GA WATA
JIYA BA YAU BA
WANDA YAYI NISA .