Addu'ah kawai yake,jin yanda jikinta ya gama saki,wani irin tashin hankali ya ziyarce shi lokaci guda..
Kallonta yake ba tare da ya saniba wasu hawaye masu d'umi suka shiga tsere akan kyakykyawar fuskansa...
Bayyana irin tashin hankalin da YAH BOSS ya tsinci kansa a ciki shi yasa ya manta matsayinsa na likita wanda ake da buk'atar juriyarsu...
Kamar mace haka ya zage yana ruwan hawaye...
Ganin tafiyan na masa nisa,yasa ya d'ago a fusace ya hau fad'a wa drivern
''Dan Allah MALAM idan ba zaka k'ara sauriba ka fice ka ban guri''
Cikin fad'a² yake maganar wanda shi kansa drivern yayi mamaki ganin yanda ya masa masifar,tsawon shekaru yana aiki tare da su amma hakan bai tab'a faruwaba....
Kai ya kad'a yana jinjina al'amarin,lallai kai da gani kasan ba k'aramin matsayi ke gareta ba a gurinsa...
Speed en ya k'ara kamar yanda aka umarce shi,dan gwammacewa yayi gara ya k'ara gudun da ya barshi yayi driven a cikin irin wannan halin....
Kafin cikar wasu mintinoni sai gasu tsaye bakin wani *SPECIALIST* da aka rubuta *BAREWA CLINIC* dake kan *ZARIA ROAD* a *KANON DABO*...
Basu wani b'ata lokaci ba sukayi parking...
Kamar y'ar baby haka ya d'aukota tana kwance cikin hannunsa,ya nufi cikin hospital en da ita....
Duk k'ok'arin NURSES akan su karb'eta hanawa yayi,sai tambayansu yayi ina ne A nd E...
Tsayawa sukayi za su masa iskaci,a fusace idanunsa cike da masifa ya hau musu fad'a...
Suna nan tsaye wani DR ya k'araso gurin har ya gota kuma ya dawo,Kallon JABEER yayi da mamaki ya furta
DR.JABEER me ya kawoka nan yana bin hannunsa da kallo..
NURSES en ya kalla cikin rud'ewa da yake yana aiki da hospital en,ya musu maganar ai maza a kaisu A nd E na gurin...
Da yake sunsan waye DR. SAIF babban likita ne,yasa cikin sauri suka rakashi...
Da harara ya rakasu,har zuwa room en.....
Wasu NURSES mata daban DR SAIF ya turo su kula da lamarin JIDDAH,ko kafin su zo tuni JABEER har ya bata taimakon gaggawa,inda ya mata allurai,had'e da d'aura mata drip....
Sai a lokacin hankalinsa ya d'an kwanta,bayan an canja mata d'aki...
Zama yayi kan wani kujera yana kallonta,yanda take sauke numfashi peacefuly ba kamar d'azun ba....
*************
Can a gurin dinner kuwa hankulansu MAMMY yak'i kwanciya,tun bayan barowarsu,take k'ok'arin kiransa sai dai kiran ya k'i shiga...
Kowa sai faman trying yake amma sam wayan yak'i tafiya...
LITTLE kam tun dawowarta ta birkice banda kuka babu abunda take...
MAMMY ce tayi k'arfin halin kiran DADDY ta shaida masa halin da ake ciki,hankalinsa shi kansa sai da yayi rabin tashi,take kuwa ya shiga neman line en YAH BOSS....
Cikin sa'a kuwa wayan ya shiga sai dai har ya k'araci kiran ba a d'auka ba...
Ci gaba yayi da kira,sai da ya jima yana kira,idan ta shiga haka za ta k'araci ringing enta ta katse...
Haka aka watse daga Dinner en,ga dangin Amarya JIDDAH da YAH BOSS kam abun bai musu dad'i ba,haka dai suka koma gidan,suna sauraron dawowarsu,duk da yanzun in sun kira wayan na shiga sai dai ba a d'auka...
Haka suka fawwala lamarin ga ubangiji....
***********
Sai da ta shafe tsawon awanni 3 tana bacci kafin ta farka...
Bud'e idonta tayi,tana k'arewa d'akin kallo,ko ba a fad'a mataba ta san dai a asibiti suke..
Ganinsa kusa da ita kansa a kife wanda hakan da yayi bazai bawa mutum damar ganin fuskansa ba,da gani kasan ko dai mutum na cikin tsananin tashin hankali,wanda ya sa yayi hakan ko kuma bacci ya d'an d'aukeshi bai sani ba...
Batayi tunanin idon sa biyu ba,shi yasa ma tayi k'ok'arin d'ora hannunta tana shafa suman dake kansa...
Har lokacin yana zaune closer da gadon,kansa na kusa da gefen cikinta...
Bai san ta farka ba,sai da yaji lallausan hannunta yana zagaye akansa..
Cikin sauri ya d'ago,ganin idanunta a bud'e kuma a kansa yasa ya damk'e hannunta gam,kamar zai had'esu da nasa..
Murmushi ta masa,tana k'oka'rin mik'ewa,Dakatar da ita yayi ya shiga k'ok'arin rabata da gadon...
Da sauri ta dire k'afafunta a k'asa ta mik'e da kanta...
Ji tayi abu na bin k'afafunta da sauri kamar ana tsiyaya mata ruwa..
Ko bata tambaya ba tasan mene ne,take ta durk'eshe a gurin ta fara aikin ruwan hawaye...
'Dagota yayi,yana shirin tambayanta yaga jini ya d'an taru a inda ta tsuguna..
Kansa ya dafe a hankali ya furta
''Ohh!ya Allah''
Sakinta yayi ya shiga toilet en,ya had'a mata ruwa,dawowa yayi bai tsaya b'ata lokaciba ya nad'e hannun rigansa,ya rabata da gurin,sai da ya shiga da ita toilet en sannan ya direta,yana fad'in
''Kiyi wankan bari na dawo yanzun''
Har da zai bama Drivern sak'o sai kuma ya fasa..
Nurse yasa a tura mata da zasu zauna kafin ya dawo,duk da ba wai nisa zaiyiba...
Key en ya karb'a ya fice,baiyi wata tafiya mai nisa ba ya riski *SAMMANIN FATIHU MALL* da yake duk a kan titi d'aya suke..
Tunani ya shiga yi na abunda zai siyama,kallon kansa yayi,sai a lokacin ya kula da yanda jini ya b'ata masa kayan jikinsa...
Take kuma ya gano dalilin da ya sa mutane ke binsa da kallo tun da ya shiga MALL en...
Girar sama da ta k'asa ya tamke ya sha mazu a bunsa...
Wucewa yayi ya d'auka abunda zai d'auka,cikin basket...
Can daga b'angaren *BOTIQUE* ya nufa ya zab'a mata wani dogon riga pink colour,shima ya d'auka one set..
Ya nufi kan counter,lissafi suka masa ya biyasu,ya d'ebi kayan ya sauka k'asa harabar da yayi parking..
A seat en gefensa ya ajiye,hasken da yaga phone nasa yayi dake zube a baya, ya mik'a hannu ya d'auka...
Dai² lokacin da kiran ya katse coz dama wayan a silent yake...
'Daukan phone en yayi domin duba wanda ya kiran,missed calls ne rututu daga DADDY da sauran y'an gidan...
Saurin bin kiran yayi,tana shiga DADDY yayi saurin amsawa
''Hello!JABEER kuna ina ne yanzun?tun d'azun muke ta k'ok'arin kiranku amma ba a d'auka''...
''Ehhh!DAD muna *BAREWA CLINIC* ,buh yanzun muma zamu taho dan yanzun haka jikin da sauk'i''....
''Ka ga idan jikin bai dai²ta ba kada ka b'oyemin,ka bari zuwa da safe sai a sallameta,gudun tashin ciwon''...
''No DAD da sauk'i sosai''
''To shi kenan sai kun dawo Allah ya k'ara afuwa''
''Ina ita JIDDAN?''
''Na d'an fita ne,bama tare amma yanzun zan koma''
''Ok toh Allah yasa kaffara ne''..
DADDYN ya fad'a yana hanging kiran...
Sai da ya sauke dogon ajiyan zuciya kafin ya jaa motan yayi gaba,tafiya kad'an ta kawo shi hospital en...
Parking yayi ya kwashi kayan zuwa ciki...
''Room en an gyara shi,sai k'amshi yake..
'Dakin ya k'arewa kallo kafin ya kira sunanta...
''HAYATEEY!''
Tana daga cikin toilet en tayi masa magana
''YAH ganifa a toilet''
''Ok dama kayan na kawo miki''
Kasa magana tayi,tana tsaye sai juya hannaye take tunaninta yanda za ta karb'i kayan...
Jin shiru yasa ya sake fad'in
''HAYATEEY kina jina kuwa?''
''Eh!in....in..a....ina jinka.....''
Tana magana sai hard'ewa kalmomin suke..
''Ok toh maza bud'e ki karb'a,kinga zamu wuce gida yanzun BABA na jiranmu a waje''....
''Toh bani amma ka rufe idonka,pleassseeee''...
Tayi maganan tana cizon d'an yatsanta...
Shi kam dariyama maganarta ta bashi...
Kad'an ta d'an bud'e k'ofan,sai da ta lek'a taga ya d'an juya baya,tace
''Bani toh''
Tana mik'a masa hannunta...
Mik'a mata yayi idanunsa a kulle amar yadda ta buk'ata,da sauri ta maida k'ofan ta rufe,bata wani jima ba ta fito tayi kanta a k'asa,ta nemi guri ta zauna...
Sai da yayi dariya mai sauti sannan ya d'auka nasa kayan ya shiga toilet en,ruwa ya watsa,then kuma ya shirya ya fito...
Ta had'a kayan guri d'aya,yana fitowa ya kalleta..
''Oya taso na d'aukeki mu tafi''
Wani kallo ta masa tana mak'e kafad'a,wani murmushi yayi ya ci gaba da matsowa inda take...
''Yarinya daga baya kenan,da dakika mak'alemun baki san da haka ba sai yanzu?
Maza taso ni mu wuce,dare na dad'a yi,yana mik'a mata hannu''...
Bata k'i amsan hannun nasa ba,tayi saurin d'ora nata akan nasa,coz tana jin k'afanta sun rik'e,ya ko rik'eta gam,suka fice...
After anyi discharging nasu,suka dauki hanyan gida.....
*_#UHMMM!naji dad'in yanda kuke nuna kulawa akan wannan novel Allah ya bar k'auna..._*
*_~#D WAY U DROP UR COMMENTS, IS D WAY THAT I ADD MORE TYPING...~_*
*_~#TEAM J²~_*
*_REAL SMASHER._*🤞🏻😘
[5:26AM, 4/21/2018] rєαl ѕmαѕhєr💃🏻: 💠💠 *RAYUWAR WANI......*
_{ơŋɛ'ʂ Ɩlıʄɛ...}_
💠💠
🌹
*Viawattpad@realsmasher01.*
*©® 2018.*
*19/ąpril,2018.*
*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ...*
*ცყ.*
_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._
*~__________________________~*
*ADDU'O'IN KIRAN SALLAH.*
_IDAN MUSULMI YAJI ANA KIRAN SALLAH,ZAI DINGA MAIMAITA ABUNDA YAJI ANA FA'DA,SAI DAI BANDA *HAYYA ALAS-SALAH* DA *HAYYA ALAL FALAAH*,ZAI CE *LAA-HAULA WALA K'UWWATA ILLA BILLAH*._
*_~#HISNUL-MUSLIM.~_*
*~_________________________~*
_My sisi *KHADIJA SALIHU* ina tayaki murnar fara sabon novel enki,Allah yasa yanda kika fara lafiya ki gama lafiya,Allah yasa jama'a su amfana da sak'on da ke cikinsa._
*~_________________________~*
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)........*
*℘ąɠɛ 83↔84*
Cikin wani irin yanayi da ita kad'ai tasan dauriyar da take wajen tafiya,haka ta hak'ura take take k'afafuntan,har suka k'arasa shiga parlor...
Cike parlorn yake da jama'a y'an biki,kowa na jiran ganin dawowarsu..
Suna shigowa kuwa akayi caaa a kansu sai sannu akema amarya..
Wata abokiyar wasan su YAH BOSS ce ta matsa kusa da shi tana fad'in
''Ango tunda amarya ba lafiya mai zai hana a d'aga sai ta samu lafiya''..
Ai ko kafin ta k'arasa tuni YAH BOSS ya d'ago yana jifanta da wata uwar harara,take kuwa mutanen gurin suka fashe da dariya''...
Tashi yayi ya nufi sama ba shiri,dan shi irin wad'annan wasannin ba wani burgeshi suke ba,shi yasa ma baya wani sakin fuska ayisu da shi..
Da k'yar MAMMY ta kori kowa daga parlorn coz dama dare yayi,haka suka fashe,kowa ya nemi makwancinsa...
Hannun JIDDAH ta kama suka nufi d'aki,ta zaunar da ita,da kanta ta had'o mata abinci,ta sata a gaba sai da ta ci sosai duk da yadda take yatsina fuska kamar mai had'iyan magani haka MAMMYN ke kallonta fuskanta babu alamar wasa har sai da tace ya isheta,sannan ta d'auka kayan tayi waje tana mata sannu had'e da sai da safe...
**********
Da misalin k'arfe 11:00am Dank'am bakin MASALLACIN na *USMAN BIN AFFAN* dake k'ofar gadon k'aya yake saboda dubban jama'ar da suka halacci d'aurin auren..
Ko ina ka duba dan adam ne,sai hasken tufafi dake haske idanun al'ummah saboda yawanci fareren kaya ne da kuma kaloli masu haske a jikinsu...
Wasu motor da suka zo gurin a lokacin,su jama'ah suka fara bi da kallo..
Haka aka bud'e motor en,fitowa yayi sanye cikin wani d'anyen boyel wanda da gani babu tambaya kasan naira tayi kuka,kalarsa light green,yayin da aka masa aiki da army green,yayi masifar kyau acikin kayan,nan wasu ke fad'in
''Ango FAROUK kenan,d'ayan bai k'araso ba?''...
Ko kafin su k'arasa,sai ganin wata motor en sukayi da ta wuce ta farko a kyau da tsaruwa,tayi parking a gabansu,nan suka bi moter da kallo,basu gama tsinkew da lamarinba sai da suka ga ya fito,cikin shiga irinta FAROUK
''Kamar had'in baki''
Inji wasu dake gefe..
Nima kuwa na basu amsa da cewa ''ai wannan yafi had'in baki,dan kuwa sai kunga amaren tukun''...
Taro yayi taro inda ba a wani d'auki dogon lokaci ba,bayan k'arasowar angwaye aka soma d'aurin auren...
Auren YAH BOSS da JIDDAH aka fara in da aka d'aura akan mafi k'arancin sadaki,dan DADDY dagewa yayi akan ba k'arya yake soba shi albarka yake nema,after kuma aka d'aura na LITTLE da FAROUK,d'aurin auren da ya samu halartar manyan mutane,daga b'angaren DADDY dama ABBAN FAROUK coz shima babban mutum ne da aka san shi...
********
A gida kuwa tun wayewar garin ake fama da JIDDAH,dan tun safe take aikin kuka,rarrashin duniya tak'i yin shiru,har kowa ya hak'ura ya zuba mata ido...
Y'an d'aurin aure na fara dawowa,aka soma neman YAH BOSS dan sun san shi ne remote control nata..
Sam an neme shi an sarasa cikin jama'ar da suke dawowa,wasu y'an kai tsegumi aka samu suka kirashi,cikin abinda bai fi minti 5 ba ya bayyana a gidan,mutane sai tsiya suke masa,shi kuwa gogan ya toshe kunnuwansa...
Haka yaita ratsawa ta cikin jama'ah har bedroom ensu,a can kan gado ya hangota ta k'udundune,kanta a cikin cinyoyinta tana ta faman kuka............
*#KUYI HAK'URI DA WANNAN,UZURI YASA BANYI TYPING DA WURIBA,IN SHA ALLAH ZAMU HA'DU A NEXT PAGE...*
*_~#TEAM J²~_*
*_REAL SMASHER._*🤞🏻😘
[3:40AM, 4/22/2018] rєαl ѕmαѕhєr💃🏻: 💠💠 *RAYUWAR WANI......*
_{ơŋɛ'ʂ Ɩlıʄɛ...}_
💠💠
🌹
*Viawattpad@realsmasher01.*
*©® 2018.*
*21/ąpril,2018.*
*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ...*
*ცყ.*
_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._
*~__________________________~*
*ADDU'O'IN KIRAN SALLAH.*
_IDAN MUSULMI YAJI ANA KIRAN SALLAH,ZAI DINGA MAIMAITA ABUNDA YAJI ANA FA'DA,SAI DAI BANDA *HAYYA ALAS-SALAH* DA *HAYYA ALAL FALAAH*,ZAI CE *LAA-HAULA WALA K'UWWATA ILLA BILLAH*._
*_~#HISNUL-MUSLIM.~_*
*~_________________________~*
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)........*
*℘ąɠɛ 85↔86*
Babban rigansa a hannu,sai kayan ciki kad'ai,dafa kanta yayi wanda k'amshinsa ya sanar da ita ko waye a kusa da ita,ta kasa d'agowa ta kalleshi kamar yadda kukanta ya k'i tsayawa...
Kan neck nata ya tab'a wanda ya matuk'ar d'aukan zafi,uwa ana kara mata wuta saboda har wani huci jikintan yake yi...
Ciki² ya furta
''Ya salaam!''
Fuskarsa na nuna damuwa,d'ago kanta yayi yana bin kumburarrun idanunta da kallo,hatta da ita kanta fuskan ta canja yanayi...
Hawaye ya shiga goge mata da handkeey yanda take kallonsa yasa ya kad'a mata kai,alaman baya son kukan...
Shiru tayi sai ajiyan zuciya da take saki akai²...
Waya ya d'auka,kiran farko ta d'aga..
''Had'omin abinci ki kuma tahomin da magani,ina d'akinku''
Yana gama bada umarnin ya kashe,ba tare da ya jira jin me zata ceba...
Bata jimaba tayi nocking,har lokacin bai zauna ba,sakinta yayi ya nufi k'ofan,kad'an ya bud'e ya amshi sak'on ya mai da k'ofan ya kulle...
Ajiyewa yayi kan bedside drawer,ya shiga nad'e hannun rigansa..
Ita kam baiwar Allah JIDDAH yana sakinta ta sake kwanciya,tana juya masa baya,wasu hawayen suka ci gaba da sakkowa akan pillow en da tayi matashi da shi...
Toilet ya shiga,a wani k'aramin container ya zuba ruwa,fitowa yayi ya duba cikin closet ensu,wani k'aramin towel ya d'auka,a kusa da ita ya ajiye kayan inda ya sauke tray en abincin,ya kuma maye gurbin da container da ta kawo na ruwa...
'Dagata yayi ta zauna,sai k'ok'arin dad'a zamewa da taci gaba da yi,bai bari ta kai ga kwanciyan ba ya jinginata jikinsa,yana zare zip en riganta,sai da ya rabata da shi,ya rage mata daga ita sai inners,towel en yasa a ruwan ya shiga matsewa yana goge mata jikinta..
Har sai da ya tabbata jikintan ya d'an saki kafin ya k'yaleta,ya janyo trayn,yana k'ok'arin bata abinci tana kauda kai,wani kallo da ya watsa mata shi yasa tayi saurin bud'e bakin,a hankali yake bata tana ci,kad'an taci lokacin da taji tana yunk'urin zata dawo da shi,haka nan ya barta ya bata maganin had'e da ruwa...
Tattara kayan ya shiga yi ya jinginata jikin pillow,yana jaa mata duvet en,rigansa da hula ya d'auka ya fita yana rufe mata k'ofa,komai da yayi k'ok'ari kad'ai yake coz ya Riga ya fad'a wani hali,har ya shigo ya fita baya ga wayan da yayi bai ambaci ko da ''A'' ba ne haka ya fita ya barta..
Tana ganin ya fita ta silale ta sake kwanciya,kanta kuwa banda sara mata babu abunda yake kamar zai fashe haka ta dafe shi, hawayen na dad'a tsiyayowa ta gefen idanta,daga haka wani wahalallen bacci ya d'auketa...
********
Gurin reception da yawa suka wuce,shima dalilin wayan da aka masa ne yasa ya dawo gidan..
A can *NI'IMA GUEST PALACE* ya tarar dasu,mutane sai hidima suke,sun ci sun sha,daga nan kuma bak'i suka shiga yi musu sallama masu haramar barin garin nayi,haka suka fara sallama da angwaye cike da fatan alkhairi aka soma watsewa,DADDY kuwa tuni ya bar gurin...
Haka aka bar angwaye da manyan abokansu,suna fira cike da nishad'i da zolayar juna..
Shiru yayi ya zubawa guri d'aya ido,ko tunanin me yake??
FAROUK da ya ankara da yanayinsa shi ya dawo kusa da shi yana tab'a shi...
''Ya dai BIG BROSS kayi shiru?''
''Bar d'an air,tunanin anjima yake''...
Fad'in wani abokin aikinsa kenan,gaba d'aya kuwa suka sa dariya,banda shi YAH BOSS da ya dad'a d'aure fuska,shi a dole baison raini...
A cikin zuciyarsa yake ayyana
''Yanzun ko wane hali take ciki?ta tashi daga baccin ko kuwa,ta ci abinci ko bata ciba?''
Tambayoyin da suka dameshi kenan,ganin bazai iya jurewa ba,yasa ya kira LITTLE dake tsakiyar jama'a anata hoto da ita..
Da sauri ta bar cikin hayaniyan,wasu na tsokanarta suke fad'in
''Dan gulma shi ne har da barin gurin''
Ita dai bata tanka musu ba tayi hanyan da babu jama'a sosai,tana d'aukan kiran yayi wani siririn ajiyan zuciya,kafin ya fara tambayanta jikin JIDDAH...
''Da sauk'i sai dai bata tashi ba har yanzun''
''OK!''
Kad'ai yace,can kuma ya ce
''Idan ta tashi ki kirani''
Daga haka ya datse kiran.....
**********
Zaune suke gaban DADDY su uku YAH BOSS,JIDDAH da kuma LITTLE kowacce kanta a k'asa banda kuka babu abunda sukeyi,nasiha yake musu mai ratsa zuciya wanda shi kansa YAH BOSS en kana kallon yadda idanunsa suka canja zaka san nasihan ta ratsa shi,yana gamawa MAMMY ta d'ora da nata,sai da ta musu nasiha sosai ta kuma tsoratar dasu kan sab'awa miji,kafin ta musu fatan alkhairi da zaman lafiya...
Tana matse k'wallan da ya tarun mata a gefen fuskanta,sallamansu DADDY yayi,nan suka tashi jiki babu k'wari suna rusar kuka,kusa da k'afan DADDY suka durk'ushe kowacce ta d'ora kanta akan k'afarsa sai kuka suke da k'yar DADDY ya sa a zo a tafi da su,nan suka koma gurin MAMMY sun k'ank'ameta suna kuka,haka itama ta rik'esu,nan kuwa kukanta ya bayyana su sunayi itama tana yi...
Da k'yar aka rabasu,hska aka sauko da su,ko wacce aka nufi moter da ita a moter d'aya aka sasu,har lokacin suna faman abu d'aya,sai da aka fara kai JIDDAH,aiko sun kama juna k'am suka rik'e,IKHRAM dake rawar kan rakiya,ta shiga tsakaninsu haka suka rungumeta suna kuka tana yi,HUBBEEY na gefe itama tana matsar hawaye,nanma sai da k'yar aka b'anb'are su a jikin juna,jama'a da dama sai da sukayi musu kuka ganin yanda suka zama abin tausayi,haka aka barota ita d'aya,da wayo da komai, suka nufi gidan LITTLE da yake cikin unguwa d'aya ne duk RIJIYAR ZAKI ne,sai dai banbancin line...
An baro amare a gidajensu sai kuma addu'an fatan alkhairi,da zaman lafiya,bak'i kuma Allah ya huta gajiya...
***********
Gidan shiru sai ita kad'ai,tana ta faman kukanta,tana jin tsaiwan motoci,sai dai bata ji shigowansa ba,saman gadon ya hauro,hannayensa a saman sholders enta ya juyota suna fuskantar juna...
Da farko ta so ta tsorata sai dai ganin shi ne yasa ta fad'a kan wider chest ensa ta kwantar da kanta hawaye na ci gaba da biyo fuskanta...
'Dagota yayi yana girgiza mata kai
''Kin san nafi kowa jin b'acin rai a duk lokacin da zanga hawaye a kan fuskarki,ko kuwa kina so raina ya b'aci ne?''
Da sauri ta shiga kad'a masa kai,tana goge fuskan da hannayenta.
Murmushi yayi mata yana sumbatan porehed enta...
Hannunta ya kama ya jaa zuwa parlor yana fad'in
''Muje ku gaisa da bak'i,kukan kuma ya isa haka,kada rashin lafiya ya kamamin ke''
Da sauri ta kalleshi,shi kuma ya kad'a mata kai,kanta a k'asa har suka isa parlor bata yarda ta d'agoba...
Haka suka gaisa,sai tsokanarta suke,ita dai bata iya cewa komaiba,saima dad'a duk'ar da kanta da tayi,har suka k'ara ci zancensu suka musu fatan alkhairi da addu'an zaman lafiya,daga haka suka mik'e da niyyar tafiya..
Har lokacin kanta na k'asa tana zaune kusa da YAH BOSS...
''To amarya mu zamu wuce duk da dai rowar fuskan ake mana,sai wata rana idan mun sake kawo ziyara''..
Fad'in wani mai surutun tsiya kenan...
YAH BOSS dake zaune ko tari baiba,saima tab'e baki da yayi,mik'ewa yayi ya rakasu,sukayi masa sallama suka d'auki hanya,sai da ya rufe ko ina sannan ya dawo,a inda ya barta a nan ya taddata,hannunta ya jaa ya kaita har d'akinta sannan ya fice..
Bayansa tabi da kallo tana sauke ajiyan zuciya a hankali...
Kayan jikinta ta shiga ragewa,wanka tayi ta saka kayan baccin da ta gani cikin closet en dake d'akin,ta feshe jikinta da sihirtattun turarukan da MAMMY ta had'a musu,light en d'akin ta rage,tana kwanciya ta ja duvet en ta rufe jikinta,bata jima da kwanciya ba ta shigo tana kallon shigowansa tayi saurin rufe idanunta...
Hasken ya kunna,kwance ya ganta,ta k'udundune cikin duvet,murmushi yayi ya kashe..
Tana jinsa ya hauro kan bed en,nanfa k'irjinta ya soma dukan d'ari..
Janyota yayi ya had'e su guri d'aya,yanda yaji jikinta na rawa ya tabbata ba bacci takeba,aikuwa tsoronta ya dad'a bayyana...
A kunne ya shiga fad'a mata wasu maganganu masu dad'i,wanda yasa tuni jikinta ya saki,alaman dake nuna tayi bacci kenan..
Fuskanta ya lek'a ganin tana sakin numfashi a hankali yasa ya tabbatar da tayi bacci...
**********
*GIDAN FAROUK*
Kukan da LITTLE keyi shi ya tabbatarmin da mai afkuwa ta faru...
Su FAROUK an zage sai rarrashi yake,amma kamar zugatama yake..
Kwance take a jikinsa,tana ta fanan zuba shagwab'a...
Lallab'ata yayi da k'yar,ya kwantar da ita ya nufi toilet,ruwa ya tara bayan yayi wanka,ya dawo ya d'auketa,a cikin ruwan ya sata,matar da ta fara bacci bata san lokacin da ta mik'eba tana shirin fita jin yadda ruwan zafi ya ratsata,haka ya maida ta,kukan da ya tafi ne ya dawo,da k'yar ya samu yayi mata wanka sai raki take masa..
Dawo da ita yayi ya kwantar da ita kan jikinsa yana sa mata albarka,ita kuwa tana jinsa,haka bacci ya d'auketa,cike da farin ciki mara misaltuwa yayi bacci cikin nutsuwa da bai tab'a samun kansa a ciki ba...
*********
*GIDAN MAMMY*
Tun da aka fita dasu MAMMY ke zubda hawaye,DADDY ke ta bata hak'uri amma tak'i dainawa,ganin abun nata ba na k'are bane yasa ya kalleta yana fad'in
''Tashi ki d'auko mayafi saiki kaisu da kanki''...
Jin furucinsa shi yasa tayi saurin tsaida kukan nata,tana mai mik'ewa ta bar gurin babu shiri...
Murmushi ta saki irin nasu na manya yana girgiza kai....
*********
Ko da asubah shi kad'ai ya tashi,ya jima yana musu addu'ar samun zaman lafiya da fuskantar juna,kafin ya wuce masallaci...
Da ya dawo ma,jallabiyan jikinsa ya rage,ya sake kwanciya yana rungume da ita a cikin jikinsa...
Da safe ta rigashi tashi,hakan yasa ta zare jikinta daga nasa,d'an nesa da shi ta zauna ta buga tagumi,nan ta shiga aikin kallonsa kamar an dasa mata T.V,ganin yana motsi yasa tayi saurin zura k'afanta a k'asa za ta tashi,da sauri ya fizgota ta fad'o kan jikinsa...
Ita abunma tsoro ya bata,idanunsa har lokacin a kulle,ya ratsa hannayensa ta saman cikinta...
Batayi tunanin idanunsa biyuba,sai jin maganarsa tayi cikin kunnenta a hankali...
''Kallon me kikemin,kamar wacce take cinema?''
Kunya kalamansa suka bata,ta dad'a kulle idanunta,tana d'ora hannayenta a kansu...
''Ko kinyi tunanin ban ga tashinki ba,duk abunda kike ina kallonkifa''
Dad'a k'ank'ameshi tayi,tana jin kamar k'asa ta bud'e ta shige...
''Oya! tashi muje muyi wanka,kada bak'i su zo,suganmu haka''...
K'in tashi tayi shi kuma ya d'agata ya nufi toilet da ita,ganin da gaske yake,ta hau bashi hak'uri
''Dan Allah YAH kayi hak'uri ka fita,zanyi da kaina''...
''Uhmm!lallaima yarinya zaki ga na fita,ba indafa zani,idanma zaki daina wannan kunyar ki daina''
Tsaiwa tayi tana kallon ikon Allah,fir YAH BOSS yak'i fita,idanunta ta kulle............
*A YAU NE ABBANA YA CIKA KWANAKI 40 DA RASUWA,INA BUK'ATAR DAN ALLAH DUK WANDA YA KARANTA POSTING ENA NA YAU YA SANYA SHI CIKIN ADDU'AH DAN ALLAH..ALLAH YA MASA RAHAMA TARE DA 'DAUKACIN AL'UMMAR MUSULMI DA SUKA RIGAMU CIKAWA,ALLAH YA KYAUTATA K'ARSHENMU...AMEEN...*
*_~#TEAM J²~_*
*_REAL SMASHER._*🤞🏻😘
[11:05PM, 4/22/2018] rєαl ѕmαѕhєr💃🏻: 💠💠 *RAYUWAR WANI......*
_{ơŋɛ'ʂ Ɩlıʄɛ...}_
💠💠
🌹
*Viawattpad@realsmasher01.*
*©® 2018.*
*22/ąpril,2018.*
*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ...*
*ცყ.*
_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._
*~__________________________~*
*ADDU'AH BAYAN GAMA KIRAN SALLAH.*
_A LOKACIN DA LADANIN YAYI KALMAR SHAHADA SAI MAI SAURARO YACE:-_
_WA-ANA ASH-HADU AN LAA ILAHA ILLALLAH,WAHDAHU LAA SHARIKALAH,WA-ANNA MUHAMMADAN ABDUHU WA-RASULUH,RADHIYTU BILLAHI RABBAN WABI MUHAMMADIN RASULAN WA-BIL ISLAMA DIYNAN.._
*BAYAN YA GAMA SAI YAYI SALATI GA ANNABI (S.A.W),SANNAN YA 'DORA DA FA'DIN...*
_ALLAHUMMA RABBA HAZIHID-DA'AWATITTAAMMAH,WAS-SALATUL K'A'IMA ATIY MUHAMMADANUL WASILATA WAL-FADHIYLAH,WAB'ASHU MAK'AMAN MAHMUDANIL-LAZIY WA'ADTTAH,INNAKA LA TUKHLIFUL MIY'AD.._
*DAGA NAN KUMA SAI MUTUM YAYIWA KANSA ADDU'AH,DOMIN YIN ADDU'AH TSAKANIN KIRAN SALLAH DA IK'AMA KARB'AB'B'IYA CE..*
*_~#HISNUL-MUSLIM.~_*
*~_________________________~*
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)........*
*℘ąɠɛ 87↔88*
Tsaiwa tayi idanunta a kulle tana tunanin mafita...
Jin shiru yasa tayi k'ok'arin bud'e idanunta cikin dabara
Ganinsa tayi ya juya mata baya, cikin sand'a ta nufi k'ofa,ta taki sa'a kuwa k'ofan a bud'e take,itama kuwa bata yi k'asa a guiwa ba ta bud'e ta fice,tana fita ta kulle ta waje gudun kadama ya fito...
Zama tayi a saman bed tana dariya sama²....
Duk abunda tayi baiga lokacin da tayi yunk'urin guduwa ba,sai k'aran kulle k'ofa da ya katseshi, cikin sauri ya juya,sai dai gurin da ya direta wayam babu kowa....
Kai ya girgiza yana murmushi,haka yayi wankan har ya gama,towel ya d'aura da kuma k'arami a hannunsa yana goge jikinsa,ya nufi k'ofan..
Handle en ya shiga murd'awa,jin tak'i bud'ewa yasa shi fad'in
''HAYATEEY!oya bud'emin na fito''
Wani tsoro ne ya ziyarceta tana zaune,kamar mara gaskiya ta shiga raba idanu,sam ta kasa tashi,shi kuma sai magana yake mata...
Can kuma ko me ta tuna,ta mik'e cikin sauri ta bud'e,tana gama murza key en ta juya zata bar gurin..
K'afa ya sa mata wanda sanadiyyar hakan ta tafi zata fad'i,cikin wata razananniyar murya ta saki wani d'an marayan ihu....
Hannu yasa ya fizgota,wanda hakan da yayi shi ya dad'a rud'ata,cikin wani irin yanayi ta damk'esa gam,kamar wacce take tunanin za a kwace mata shi...
Kuka tasa masa,tana bugun k'irjinsa,shi kuwa da farko dariya ya soma mata,kukan da ta soma yi masa ne yasa shi fara rarrashinta,cikin hikima ya kaita har tsakiyan toilet,bai jira ta sake yunk'urin guduba,ya sata cikin kwamin wankan da ya cika shi da ruwa...
Runtse idanunta tayi,a tunaninta ya fita,saijin hannunsa tayi a jikinta yana k'ok'arin rabata da kayan jikinta...
Wani ihuu ta sa masa,shi kam ko ta kanta bai biba,ya cigaba da abunda yake ba tare da ya saurara mataba,haka ta ci gaba da kukanta,ko ladan rarrashi bata samuba sai da ya kammala zaresu tsaf...
Bayyanar jikinta waje,shi ya haddasa masa had'iyan miyau,yana bin gaba d'ayan jikinta da kallo,jin shirun da tayi shiya haddasa masa bud'e ido a tunanin tama ya fita ne,sai dai me tana bud'ewa taga ya kafawa na......ido ko k'iftawa baiyi..
Da sauri tasa hannu tana rufewa,had'e da dad'a kulle idanunta tana masa ihuu..
Gajeran murmushi yayi ya kama hannayenta yana k'ok'arin bud'ewa,ita kuma tana dad'a kare abunta,kokawa sosai suke acikin toilet...
Hakane yasa ya zare towel en jikinsa,ya koma cikin kwamin wankan..
Tana jin ya shiga ta mik'e zata bar gurin,da sauri ya dawo da ita,a jikinsa ya kwantar da ita...
Cikin kunnenta yake mata magana k'asa²...
''Please HAYATEEY me kike son aikatawa,kina son b'atamin rai ne?''
Da sauri ta girgiza masa kai
''Ok!idan bakya so raina ya b'aci ki tsaya haka kinji''
Gaba d'aya jikinta rawa yake,amma haka ta shiga girgiza masa kai
Wani murmushin ya sake yi,wanda ban san me hakan ke nufiba...
Jikinta ya soma bi yana shanshanawa,tun daga wuyanta ya soma sakin mata wasu zafafan kisses,har ya gangaro kan fuskanta.......
Kamar an dasata haka ta zama,shi kad'ai yake kid'ansa kuma shi yake rawar,sai dai ya juyata,ta zame masa kamar mutum-mutimi...
Ko me ta tuna kuma tayi saurin zare bakinta a nasa,kallonta ya shiga yi da idanunsa da suka soma canza launi..
''Pardon please YAH'' tana had'e hannayenta,idanunta har lokacin a kulle...
Jikinsa ya wanke ya fita daga toilet en gaba d'aya...
Kuka tasa a toilet en,ko ba a fad'a mata ba yayi fushi ne,haka ta k'ara ci kukanta tayi wankan ta fito jiki babu k'wari...
Ko da ta fito bata tarar da shi a d'akin ba,haka ta zauna a kan tsool ta buga tagumi,da k'yar ta shirya ta fito parlor..
Nan ta tarar da shi kwance kan sofa,idanunsa a kulle,kusa da k'afarsa ta zauna kafin ta soma magana
''YAH kayi hak'uri please''....
Bai tanka mata ba,har ta k'araci ban hak'urinta ta tashi,d'akinta ta koma ta kwanta hawaye nabin fuskanta...
Wannan wane irin al'amari ne,daga kawota jiya harta wayi gari da kuka,ita bata tsinci komai a ranar ta ta farko a gidan miji ba,sai b'ata masa rai bayan d'inbin nasihar da iyayensu suka musu,ta rasa yadda za tayi,hakan yasa ta mik'e tana share fuskanta,wayanta ta janyo tana neman line en SIS enta,sai dai taji an ce mata switch-up..
Tunani duk ya mata yawa hakan yasa ta shiga neman line en HUBBEEY...
Tana d'auka da tsokana ta soma fad'in
''Amarya a gidan YAH BOSS''
Kukan da taji tanayi shi ya dakatar da ita daga tsokanar da take mata,cikin kid'imewa take tambayarta...
Sai da k'yar ta samu tayi shiru,kafin kuma ta soma magana
''Sis ina cikin wani hali,ki bani shawara please''
''Shawaran mene?kin sani a damuwafa''
''Fushi yake da ni''
Ta k'arasa tana sake sakin wani kukan..
''No Sis karkiyi haka,kin masa lefi ne shi yasa kikaga yayi fushi,ki yi shiru tukun,ki saurari abunda zan fad'a mi,yanzun kije ki bashi hak'uri da alk'awarin bazaki sake ba''
''Allah kuwan na bashi,ko kallona ma baiyiba bare ya kulani''
Dafe kai HUBBEEY tayi tana runtse ido
''Ya nemi wani abune kin hanashi ba?''
Tayi tambayar ba tare da yak'inin hakan bane...
''Haka ne sis,sai dai kin san bani da tsarki yanzun,kuma Allah ina jin tsoro sosai''....
''Kinga yanzu abunda nake so dake kiyi maza ki jashi a jiki,coz idan kikayi sakaci wollahi kina kallo zai dinga bin wasu a waje,saboda k'adangarun bariki ba saurara miki za suyi ba,idan zaki mik'e tsaye ki tarairayeshi toh,duk abunda ya nuna miki yana so koda baki so ki hak'ura ki nuna masa kin fishi so''....
Haka suka jima tana ta bata shawarwari kan zamansu da hanyoyin sa zata bi ta kyautata masa...
''To sis na gode sosai,in sha Allah zan gwada''
''Yawwa!maza kije ki sake bashi hak'uri,anjima zan zo da yamma''
''To shi kenan sai kin zo en,Allah kawoki lafiya''
Suka amsa da ameen dukansu....
Tashi tayi ta koma parlor don ta sake bashi hak'uri,sai dai bata tarar da shiba,haka ta zauna ranta na masifar suya,duk haushin kanta da b'ata masan da tayi ya dameta...
Nocking en da akayi yasa ta tashi ta bud'e,ai kuwa sai ganin IKHRAM tayi ta toge k'afa ta sha kwalliya,tana zuba uban smile...
Hanya ta bata tana maida mata murmushin itama...
A parlor suka zauna,IKHRAM en tana gaisheta,ta dai yi k'ok'arin sakin jikinta gudun kar IKHRAM en ta ganota,haka suka shirya komai kan dinning da taimakon IKHRAM en...
''Wai ni kuwa ADDANAH ina BB ne?''
Sai da tayi yak'e tukun tace
''Ina ga yana d'akinsa''
Wani irin kallo IKHRAM en tayi mata na rashin fuskanta,kai kad'ai ta kad'a ba tare da tayi magana ba,suka koma parlor,tsaf suka gyara ko ina na gidan,suka turareshi,ko ina sai k'amshi ke tashi...
A parlor ta bar IMHRAM tana fad'in
''Ina zuwa CWEETY''
Binta tayi da kallo har ta b'ace mata
Sama ta haura,d'akin dake opposite da nata ta nufa,a hankali ta murd'a handle en k'ofan,ta shiga da sallama...
Kwance ta tarar da shi fuskan nan uwa bai tab'a dariya ba,haka ya kalleta yana jiran jin me zata fad'a
''YAYANAH!Abinci na jiranka''
Duk maganar tana yine kanta a k'asa sam tak'i yadda su had'a ido,kuma cikin sanyi tayi maganan..
''Ina zuwa''
Haka ta juya jiki babu k'wari,shi kuma ya bita da kallo yana murmushi...
''Yarinya kad'anma kika gani,zan gyara miki zama,ta yanda ko kallonki nayi zaki san me nake nufi''
Da haka shima ya biyo bayanta,a parlor ya tarar da IKHRAM,har k'asa ta gaida shi,ya amsa fuskansa a sake kamar ba shiba,har suka kammala,sai fira suke da IKHRAM...
Ita kuwa baiwar Allah duk jinta take a damuwa,haka taita binsu da kallo,ba tare da tace ko uppan ba...
Yini sukayi suna fira tsakaninsu,sai dai su tashi suyi sallah,su sake dawowa,ko da ranama MAMMY ta bawa driver ya kawo musu abinci...
Suna ta hira Sallaman HUBBEEY ya katsesu,cikin murna JIDDAH take kallonta,suna gaisawa da YAH BOSS ta janyeta sukayi d'akinta,nan kuwa suka dasa sabon shafi na karatu,ranar bata bar gidanba sai bayan Maghreb inda YAH BOSS da kansa ya maida IKHRAM,tare da HUBBEEY...
Tun tafiyar HUBBEEY,JIDDAH keta tunanin anya zata iya abunda tace kuwa?
Da k'yar ta samu mafita tunanin maganar HUBBEEY da take cewa
_''Idan bazaki iyaba ai shi kenan,kina kallo wallahi k'adangarun bariki zasu janye shi,ki tsaya kallon ruwa kwad'o ya miki k'afa,itafa rayuwar nan malama an daina duhun kai,amma idan baki yadda ba,kiyi sakaci ki gani''_
Wannan maganar da ta tuna yasa ta sauke ajiyan zuciya mai nauyi..
''Zan gwada komai wahala,ba zan tab'a sakacin da zan b'ata masa raiba,sai dai ko cikin rashin sani,duk da shima bana fata''....
Tashi tayi ta shige toilet ta jima a cikin ruwan wankan da ya turaruka iri daban²...
Ta gama kwalliyanta tsaf nan kuma ta soma tunanin kayan da zata sa...
Tsayawa tayi tana k'arewa kayan da HUBBEEY ta fito mata da shi,d'aya bayan d'aya take d'agawa tana kallo gaba d'aya ita kam bata ga na sawa ba anan...
Again tasake duban kayan tayi tagumi...
''Idan kikaji ance k'i gudu,to sa gudu ne bai zo ba''
Daga wani b'ari na zuciyanta ta samu hope na sawa...
Wani black three qurter ta d'auka da sea-green en riga,a ganinta sunfi dama² acikin kayan,ta saka ta kama gashinta a tsakiya da ribbon...
Kowa ya ganta zai so ya sake kallonta,sai dai abun haushin har ta gama yayinta a parlor bata ji motsinsa ba...
Guiwanta sunyi sanyi,haka ta nufi d'aki ta kwanta,damuwa duk ya rufeta,a nan bacci ya d'auketa...
Sai after 11:00pm ta farka,wanka ta sake yi ta saka nighteey enta wasu masu arnen kyau,dai² lokacin idanunta suka sauka kan Wall-clock,ido ta fiddo waje,cikin sauri ta cire na jikinta da tayi niyyar sawa...
Wata k'aramar riga slick ta sa,iya kacin tsayinta saman guiwanta sai da ta k'arewa kanta kallo sannan ta juya da niyyar barin d'akin tana k'ara turaruka a jikinta,da k'yar ta fita ta nufi d'akin data gansa d'azun....
Kwance yake da phone a hannunsa,jin an turo k'ofan yasa ya d'aga kai yana kallonta...
Numfashinsa sai da yayi season na wucin gadi,amma taurin kansan yana motsawa ya juya mata baya...
Hakan da yayi da irin kallon da ya mata kafin ya juya,su suka tabbatar mata hak'anta zai cimma ruwa..
Murmushi tayi ta nufeshi,ta bayansa ta kwata hannayenta na jikinsa ta rungumesa...
Hak'uri taci gaba da bashi,shi kuma yak'i kulata,ta kansa ta mirgina ta koma suna fuskantar juna...
Sake juyawa zai yi ita kuma tayi saurin hawa samansa,ta hana shi abunda yake niyya...
''Pardon please QURATU-AYNIY ban sake yi maka laifi ko da a mafarki,please ka yafemin''...
Ta k'arasa tana hawaye..
K'arshen rud'ewa sai da yayita,abubuwan sun masa yawa,ba shiri ya hau shafa bayanta,yana rarrashinta,da k'yar tayi shiru kafin tace
''YAYANAH bafa kace ka yafeminba''
Uwa wacce za tayi wani sabon kukan take maganar cike da shagwab'a
Lips enta ya d'an ciza ganin yadda ta turo masa su
Ai kuwa ta sake sa masa sabon kukan tab'ara ita dai sai ta rama,dariya yasa mata daga haka wasan ya sauya salo,zuwa wani bigire na daban.........
***********
Yau tsahon kwanaki hud'u kenan da kaisu,soyayya gami da shak'uwa ya dad'a shiga tsakaninsu,zuwa yanzun sun riga da sun saba da juna fiye da tunanin mai tunani...
Tana tsaye a kitchen dai² lokacin tana son had'a stew saboda yamma yayi,ya shigo cikin kitchen en,rungumeta yayi ta baya kansa na dai² kan neck ta,hannayensa kuwa ya zagaye su a k'ugunta...
''Wai kam HAYATEEY sai yaushe zaki soma sallah ne?''
K'irjinta sosai ya shiga bugawa da k'arfi,duk ta rikice,ta kasa magana...
A ranta kuwa fad'i take
''Wayyo Allah tawa ta k'are duk ranan da YAH yasan na samu tsarki,nasan zan fad'iwa y'an garinmu''
Take ta tuno yanda LITTLE ta bata labarin taci wahala,ai kuwa sai ga gumi na sakko mata,ta shiga sharewa,kuma har lokacin bata bashi answer ba............
*_~#TEAM J²~_*
*_REAL SMASHER._*🤞🏻😘
[10:31PM, 4/23/2018] rєαl ѕmαѕhєr💃🏻: 💠💠 *RAYUWAR WANI......*
_{ơŋɛ'ʂ. Ɩlıʄɛ...}_
💠💠
🌹
*Viawattpad@realsmasher01.*
*©® 2018.*
*23/ąpril,2018.*
*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ...*
*ცყ.*
_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._
*~__________________________~*
*ADDU'AR BU'DE SALLAH.*
_BAYAN AN YI IK'AMA_
_ALLAHUMMA BA'ID BAINIY WA-BAINA KHA'DAYAYA,KAMA BA'ADTA BAINAL MASHRIK'I WAL-MAGRIBI,ALLAHUMMA NAK'K'INIY MIN KHA'DAYAYA,KAMA YUNAK'K'AS-SAUBUL ABYADU MINAD-DANAS, ALLAHUMMAGHSILNIY MIN KHA'DAYAYA BIS-SALJ,WAL-MAA'I,WAL-BARAD.._
*_~#HISNUL-MUSLIM.~_*
*~_________________________~*
_Ina matuk'ar godiya da addu'o'inku gareni,Allah ya k'ara mana lafiya da nisan kwana mai amfani...Shukhran oll dearies._ ❤
*~__________________________~*
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)........*
*℘ąɠɛ 89↔90*
Juya kanta kad'ai take ta kasa amsa masa,hannunta a baki tana d'an cizonsa,duk iya hangentan ta kasa samo amsan da zata bashi...
A hankali ya d'an d'aga kansa jin shirun nata yayi yawa,yana k'ok'arin maidawa ne ya sake maimaitawa cikin wani irin yanayi..
''HAYATEEY baki jini bane?''
Da sauri ta fara magana cikin sark'ewar baki
''N...O......NO...Najika YAYANAH!''
Yanayin yanda ta amsa masane bai yi ba,shi ya haddasa masa dad'a d'aga kansa yana juyo da ita suna fuskantar juna,dad'a rungumeta yayi,cikin magana k'asa² ya soma fad'in
''Me ya faru dake ne?
Yanzun na taddaki lao amma naga kin wani birkice yanzun''
''Nifa lao nake,babu abunda ya sameni''
Tana yi tana murmushin da da kad'an yafi kuka...
Binta kad'ai yayi da kallo,haka ya kyaleta ba dan ya yarda ba,bai sake ce mata komaiba,yayi shiru...
Da k'yar ta kammala aikin da takeyi,tsaf ta gyara gurin,har lokacin yak'i barinta,yana manne da ita haka take aikin..
''YAYANAH bari na kai sauran kayan na dawo'',kanta a k'asa take maganar...
K'in sakinta yayi,sai da yaga duk ta nuna damuwa,sannan ya amsa da kansa ya nufi dinning,shi ya k'arasa setting dinning en,ita kuma ta kammala wanke abunda tayi amfani dashi,fitowa tayi tana goge hannunta,tayi hanyan d'aki..
A baya ya biyota har bedroom en,ya tarar data tana cire kayanta zata wanka,zuwa yayi ta bayanta ya sake tsaiwa yana tayata k'arasawa...
''HAYATEEY na miki magana d'azun kin tsaya kina bani wahalaba?''
Juyowa tayi,dan kam zuwa yanzun har tayi tunanin abunda za ta fad'a
''No YAYANAH sam abunda kake tunani ba haka yakeba,kawai dai har yanzun ban riga da na samu tsarki bane shi yasa kaji bance maka komaiba''
Tana maganan idanunta a k'asa
Kallon yanda take magana,tak'i yadda su had'a ido yayi,yasan shirya masa zancen tayi,tun da tak'i yadda su had'a ido da ita,wanda ya tabbata da gaskiya takeyi ba abunda zaisa bata kalleshi ba...
K'yaleta yayi bai kuma mata magana ba...
Sai can kuma ya ce
''Ok!muje toh na miki wanka,maghreb ya kusanto''
Kafad'anta ta mak'ale tana cuno baki,kafin tayi wani yunk'urin tuni ta tsinci lips enta cikin nashi,anci sa'a kam zuwa wannan lokacin tana k'ok'arin maida masa,duk wani salo da yasan zai rikitata shi yake mata,ta hakane kad'ai yake samu idan ta kasa d'aukan lesson en zata maida masa da kwatankwacin abunda ya mata...
Sun jima a haka sunata faman tsotse juna,da k'yar suka tsaya,sunama juna kallon da su kad'ai suka san ma'anarsa,murmushi sukayi dukansu,d'agata yayi ya nufi hanyan toilet en..
''Pleasse YAYANAH ni ka saukeni,kaga inafa da nauyi,zanyi wankan da kaina,ka fara yi tukun''
Bai saurari abunda take fad'a ba,sai da ya direta a toilet en,haka ba dan taso ba sukayi wankan suka fito,suna fitowa ya nufi masallaci,ita kuwa ganin ya fita,tayi saurin komawa toilet en,wankan tsarki tayi sannan ta d'auro alwala,a gaggauce ta zura dogon riga da hijab ta kabbara sallah,har ta idar bai dawo ba,ai kuwa sai murna take...
Har akayi ishaa bai dawoba coz dama d'abiansa ne hakan
JIDDAH ta gama had'a muguntanta,kan bara ta bari ya gane ta dawo sallah ba,tana yi tana dariya ita d'aya,haka suka koma rayuwa,da dare zata sa kayan da dasu da babu duk d'aya kuma da sunan kayan bacci,da rana kuma ta matse cikin english wears kamar baturiya haka zaku ganta,idan bashi da inda zashi haka zasu yini cikin so da nunawa juna kulawa ta musamman...
Yau ranan ya kama one week dai² da aurensu,wanda yayi dai² da kwanaki 3 da samun tsarkinta,ko sallah za tayi bari take sai ya tafi masallaci takeyi...
Da yake yau ya d'an fita gidan MAMMY tun yana hanyan Kabuga yake kiranta,amma shiru bata amsa ba..
Dai² lokacin kuwa tana toilet ta idar da alwala,har ta fito ta kabbara sallanta..
Wani traffic da aka had'a shi ya hana shi k'arasowa da wuri,sai tsaki yake saki...
Tana idarwa kuwa lokacin tana tsaka da nad'e pray mat en ta jiyo horn ensa,da sauri ta k'arasa ninkewa ta kwashe ta d'ora kan bedside drower,cikin sauri ta fita dan taronsa...
A bakin stairs en suka had'u tana murmushi take fad'in
''YAYANAH sannu da dawowa,ya MAMMYNMU?''
Hannu ya bud'e mata,aiko ta shige jikinsa,yana rufewa yake fad'in
''Duk lafiya alau,MAMMY da IKEEY na gaidaki''
''Allah sarki MAMMYNAH,ina amsawa,wai YAYANAH yaushe zaka kaini na ganta Allah duk ina jin kewanta?''
A kunnenta ya rad'a mata
''Sai ranar da na maidaki cikakkiyar mace''
K'irjinta sai da yayi wani mugun bugu,da yasata tai tari babu shiri
Sannu yaita jero mata yana patting bayanta
''Kawai dai bara ka kainiba,shi ne zaka ce wai saika mai dani wani cikakkiyar mace,da an fad'a maka ba cikakkiya bane?''
Ido ya bud'e yana kallon yanda take zuba masa fitsara,sai abun ya masifar birgeshi yanda takeyi kamar wata *BABY DOLL*.
Amma sai ya b'ige da fad'in coz bai son ta daina
''Ooooo!HAYATEEY ni kikema fitsara ba?''
''Nifa ba da kai nake ba,da wanda yayi magana nake''
Ta k'arasa tana hararan gefe
''To da wa yayi maganan idan baniba,cewa za kiyi da kai nake''
''Allah kuwa YAH BOSS ba da kai nake ba''
Tuna kalman da tayi amfani da shi yasa tayi saurin dafe bakinta,tana kallonsa
Murmushi yayi yana zare hannunta daga kan bakintan
''Haaaaa!yarinya zakiyi bayani duk ranan da na rik'eki,wato ninema BOSS koh? a inama kika samo wannan sunan?''
K'if k'if ta shiga yi da idanunta na rashin gaskiya,tana kad'a masa kai
''Am sorry YAYANAH baran sakeba kaji? pleaseee''...
Duk tana yine kamar za tayi kuka
''Ok!is fast,muje ki tayani nayi wanka''
Babu musu kuwa suka haura sama bed room ensa suka shiga,wanda k'arshe dai tare suka wanke juna,suna yi suna wasa sai da suka b'ata lokaci sannan suka fito...
Juyawa tayi zata fita yayi saurin rik'ota
''Ina zakije ne baki gama aikinki ba ai''
''Pleaseee YAH yanzun zan dawo,kayana zan d'auko''
Janyota yayi ya zaunar da ita kan stool
''Zauna ina zuwa,barinje na d'auko miki GIMBIYATA''
Ya fad'a yana mata winking,duka suka sa dariya,da sauri ya fita,ya nufi bed room enta,shigansa d'akin ya nufi Waldrop enta,har ya gama d'aukan abunda zai d'auka ya juya,dai² kan bed side drowernta ya hangi pray mat enta da hijab..
Wani dariya yayi kafin ya juya ya fita..
Yanda ya barta haka ya tarar da ita,har inda take ya k'arasa yana murmushi,itama murmushin tayi masa,kayan ya ajiye ya nufeta,mai ya shiga shafa mata,itama haka sunayi suna tsokanar juna..
''HAYATEEY!wai wannan wane irin abune yak'i tafiya,nifa na gaji Allah hak'urina yana neman gazawa''
Cike da shagwab'a yake maganan
Idanta uwa zasu fad'o kan kallon da take masa,har sai da ya hura mata iska,sannan ta dawo duniyarta
''Kaima dai YAYANAH idan na samu tsarki zan b'oye maka ne?amma idan baka yarda kana iya dubawa''
Ba tare da tayi tunanin komai ba tayi maganar,shi kuwa kallonta yayi,a ranshi kuwa fad'i yake
''Zaki san ni kika cewa na duba''
Amma a fili sai cewa yayi
''Sure?''
Yana d'age gira d'aya,da wani kallo na kin yima kanki wauwauta yarinya
Kai ta kad'a masa,shi kuwa dama mai jiran k'iris,aiko ya kinkimeta sai saman bed,yana fad'in
''Ok!let see,i have to check by my self''
Gaba d'aya ta kasa nutsuwa,ganin da gaske yake,tuni ta hau bashi hak'uri
''Pardon pleassse!YAYANAH bafa da gaske nake ba''
Ci gaba yayi da tafiya,a tsakiyan bed en ya direta,daga ita sai towel data d'aura iya kacin tsayinsa cinyanta...
Magiya take masa,shi kuwa fad'i yake
''No HAYATEEY dubawafa zanyi,bayan ke kika bani permission en yin hakan,mene na damuwa,so gara mikima kiyi shiru,dan ba fasa dubawa zanba''...
Towel en jikinta ya kama zai ja,da sauri ta kai hannu zata rik'e,ya rigata fisgewa,komawa tayi kalar tausayi tana k'ara bashi hak'uri,sam ya garara saurara mata...
Wasu zafafan kisses ya shiga aika mata,jinsu take kamar saukan ruwan sama,ba tare da ta shirya amsaba ta shiga maida masa,duk da yanda take jin k'irjinta na shivering kamar zai tsage...
Sai da ya gama rud'ata da salon da bai tab'a mata irinsa ba,ya gama birkitata ya tabbata taje linter signing kad'ai take jira ya mata, sannan ya shiga karanto addu'ar da (ANNABI (S.A.W) ya koyar damu,domin neman kariya daga shaid'an,,,,,la'ananne) wato (addu'ar saduwa da iyali)
_(ALLAHUMMA JANNIBNASH-SHAI'DANA,WAJANNIBASH-SHAI'DANA MAA RAZAK'ATANA).._
_(Wannan addu'ah ba iya maza kad'ai aka keb'anceba,har mata,saboda halin mantuwa..)_
Take kuwa ya kunna kai zuwa fadar tata,yana ci gaba da addu'o'i a zuciyansa...
Wani uban zogi,rad'ad'i had'i da azaba ne suka ziyarceta lokaci guda,tako fasa wata irin k'ara,tana bashi hak'uri...
''Dan Allah YAH kayi hak'uri,wallahi baran k'ara fad'aba,,,,,wayyyoooo Allah zai kasheni, MAMMYNA ki zo ki ceceni,zai k'arasa ni......
Ruwan hawaye kuwa ba a maganarsu,sai ya da kai take gefe,abun gwanin tausayi,ta rasa maceci,sunan y'an gidan kuwa babu wanda bata kira ba,kan neman ceto,shi kuwa bai saurara mata ba,sai da ya samu abunda yake buk'ata...
Jinsa yake kamar wanda akayiwa bushara,lokacin da nutsuwa tazo masa,ya kula da irin ta'asar da yayi,tsam ya k'ank'ame abarsa a jikinsa kamar uwa da take tsoron za a rabata da jaririnta....
Albarka kuwa babu irin wacce bai samata ba,kan farin cikin da yake ciki a ranan...
Kukanta take risga uwa ranta zai fita,tun sautinsa na fita har ya dawo sai hawayen kawai ke fita,sautinma ya gama b'oyewa....
Duk rarrashin da yake mata tak'i yin shiru..
''Ok! tunda bara kiyi hak'urinba barin k'ara second round,tunda haka kike so,bana son ki sawa kanki wani ciwon''
Fuskan nan babu wasa yake magana,hakan yasa ta k'ank'amesa tana yin shiru,sai ajiya zuciya da take saukewa akai²......
Murmushi yayi yana sumbatan forehead enta,ya kwantar da ita,ya nufi toilet,fuskansa a sake da alaman jin dad'i a tare da shi...
Ruwa ya tara ya dawo ya d'auketa,aciki ya sanyata,aiko ta saki wani d'an marayan kuka,ci gaba yayi da rarrashinta,da k'yar ya lallab'ata tayi shiru...
Tsaf ya wankesu su duka,yako nad'ota a towel ya dawo da ita ya kwantar tana jikinsa,a haka ya lallab'ata take kuwa bacci ya d'auketa tana fama da ajiyan heart har lokacin...
Kallonta yake cike da so da kulawa,yana tuna shirmen da tayi masa,shi kad'ai yayi dariya yana fad'in
''Allah sarki HAYATEEYNA na baki wahala kam,to ya na iya,hakan ya zama dole ne shi yasa''
Shi kad'ai yake maganarsa,yana murmushi...........
_#Haaaaaaaa! Gaskiya kun bani dariya sosai kan comments enku na jiya,ina mik'o gaisuwa masoya gaskiya na jinjina.Y'an *SMASHER/HUBBEY NOVEL GROUP* wollah muna k'aunarku kuma muna tare da ku irin wujiga-wujiga ennan.Allah barmu tare.._
*_~#TEAM J²~_*
*_REAL SMASHER._*🤞🏻😘
[2:35AM, 4/25/2018] rєαl ѕmαѕhєr💃🏻: 💠💠 *RAYUWAR WANI......*
_{ơŋɛ'ʂ Ɩlıʄɛ...}_
💠💠
🌹
*Viawattpad@realsmasher01.*
*©® 2018.*
*24/ąpril,2018.*
*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ...*
*ცყ.*
_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._
*~__________________________~*
*ADDU'AR BU'DE SALLAH.*
_BAYAN AN YI IK'AMA_
_SUBHANAKALLAHUMMA WABI-HAMDIKA,WA-TABARAKSMURABBIKA,WATA'ALAA JADDUKA,WALAA-ILAHA GHAIRUKA_
*_~#HISNUL-MUSLIM.~_*
*~_________________________~*
🎂🎂🎂
🎊🎉🎊
🍻🍻🍻
*HAPPY BIRTHDAY DEEZOH*
💃💃💃
_May it be the best day of your life thus far, & may your happiness grow with each passing day through the many many birthdays that surely are ahead of you._
🎁🎁🎁🎁🎁🎁
_Once again happy bufday sis *KHADIJA SALEEHU.*_
🌹🌹🌹
🎂🎂🎂
💃💃💃💃
*~__________________________~*
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)........*
*℘ąɠɛ 91↔92*
Rayuwarsu mai cike da tsafta haka suka ci gaba da gudanarwa, babu wani abu da yake hanasu nunawa juna soyayya da kulawa ko da kuwa a gaban waye..
Yau tunda suka tashi take ta faman zuba masa SANGARTA shi kuma sai biye mata yake,duk abunda take yana biye mata..
Tana kwance saman jikinsa,ta d'ago fuskanta uwa za tayi kuka,ta kalle shi,shima itan yake kallo yana jiran jin abunda zata fad'a
''YAYANAH!''
''UHMM!Ina saurarenki HAYATEEYNA''
''Allah na gaji da zama guri d'aya,nifa tunda nazo ko bakin get ban tab'a zuwa ba,bare nasa ran zuwa naga MAMMYNA,kuma kai kullumfa sai kaje''
Dariya yasa mata,ita ko ganin yana son waske zancen tasa masa kuka
''Allah ni ka kaini naga MAMMYNA,in ba haka ba kuma''...
''In ba haka ba me?''
Ya tambaya yana sake mata dariya
Kuka sosai take tana bugun k'irjinsa,shi ko ya dad'a matseta a jikinsa,fuskanta ya rik'e,idanunta sai fidda hawaye suke
Harshensa yasa yana d'auke duk wani layin hawaye dake fuskanta,k'arshe ya dire cikin bakinta,jin haka yasa kukan nata tafiya babu shiri,idanunta a kansa..
Biye masa tayi sai da suka gama jagwalgwala juna,sannan yayi sama da ita yana tsokanarta,ita ko ko kulashi tak'i yi,haka yaita janta da fira iri² amma tak'i sakin jikinta..
Wanka ya mata,abunda kullum tare suke amma yau saboda tana fishi tak'i kula shi,tsaf ya shiryata shima ya shirya,kayan da ya d'auko musu su suka sa ta kalle shi,bakinta da alamar tambaya,amma saboda tana fushi da shi ta k'i yin magana sai kumbura fuska take..
Duk wani motsi da take yana kallonta,sai da ya gama sannan ya d'aukota har packing lot ya direta,yana k'ok'arin bud'e motern ta bud'e baki da k'yar tace
''Wai ni YAYA ina zamu ne,naga ba kace min zan rakaka ko ina ba''
Murmushi kad'ai yayi ya bud'e motern ya sata,shima ya zagaya ta d'ayan b'arin ya zauna,har ya fice daga gidan bai ce mata komaiba,sai da suka d'auki hanya sannan ya juyo ya kalleta,sai faman cika take..
Kansa ya d'auke yana fad'in
''Yau kuma YAYAN ba naki bane?''
Baki ta murgud'a masa tana magana k'asa²
''Yarinya yi maganarki a fili,dan in na kama ki zaki san ni kikewa k'unk'uni,ba sauraramiki zanba''
Yana wani mugun murmushi...
Hanyan gidan MAMMY da taga sun nufa shi yasa ta saurin kallonsa da mamaki,fuskanta da tsantsan murna,ta fad'o jikinsa wanda hakan da tayi yasa shi saurin samun guri yayi packing yana d'agota..
"Kina so mu dad'i ne ko?"
''Na gode YAYANAH kamin komai,ban san wane irin godiya zan maka ba''
Yatsansa yasa kan bakinta,yana murmushi
''Ba buk'atar ki godemin,hak'k'ina ne kula da duk wani abu da zai saki farin ciki''
Wani warm hug ta dad'a bashi,ta manna masa kiss a kumatu,sai murmushi take saki tana masa kallon da shi kad'ai yasan ma'anarsa
''Gaskiya baby ba haka ba''
Yayi maganan yana shagwab'e fuska
Dariya ta saki tana kallonsa
''Me kuma ya faru?''
Ta tambaya duk da tasan me yake nufi
''Ai kin san ko me nake nufi,ko kuma so kike na miki explaining?''
Kai ta d'aga tana k'unshe dariyanta
''Ai kin riga kisan bana son kiss a kumatu''
''Sorry dearnah a ina kake so to?''
''Ban sani ba,kina neman ki rainamin hankali,bar abinki ba na buk'ata''
Yana gama fad'a ya fisgi moter sai gidan MAMMY
Duk maganar da take bai ko saurareta ba,har suka k'arasa sai d'age mata kai yake,rabuwa tayi da shi
Ko da suka je bai kulata ba ya fice abinsa,itama kuwa da d'an gudunta ta shiga parlor tana k'walawa MAMMY kira..
Jin muryan kamar a mafarki,yasa MAMMY saurin fitowa daga kitchen,tana fad'in
''Muryan wa nake ji kamar doughterna?'
''Nice MAMMYNA''
Suka rungume juna,MAMMY na jin dad'i uwa ta shekara bata ganta ba
Zamewa tayi tayi k'asa tana gaidata,cike da farin ciki mara misaltuwa MAMMYN ta amsa,ko YAH BOSS bata bi takansa ba,sai da suka gama murnan ganin juna sannan ta iya amsa gaisuwarsa
Ganin ranan MAMMY ba tashi suke ba yasa ya mata sallama zai je ya dawo,aiko haka suka rashe a nan JIDDAH na zubawa MAMMY sangarta
Sai dare ya dawo,yana shigowa kuwa,JIDDAH ta hau b'ata rai ita a dole bata son tafiya,badan taso ba haka suka baro gidan bayan sunyi dinner a can,MAMMY na dad'a yi musu nasihan su zauna da juna bisa hak'uri,haka suka d'auki hanyan nasu gidan...
Motern shiru uwa babu masu rai aciki,can ta tuna dalilin shirun nasa,ta gefe ta saci kallonsa duk ya wani b'ata rai
Juyowa tayi tana dariya,ya ko bita da kallo
''Allah ko YAYANAH sam b'ata fuskanan da kayi bai maka kyauba''
Baki ya tab'e bai ce komai ba,ya ci gaba da driven ensa,sai lokacin taji duk ta damu
Cikin sanyi ta shiga bashi hak'uri,k'in kulata yayi ,ita ko hakan da ya mata shi ya dad'a sata jikinta ya k'ara sanyi,ta san idan batayi wani abuba akan wannan fushin nasa haka har suje gida a haka zasu zauna,ko gama yanke hukunci batayi ba ta kamo fuskansa,cikin salonta da tasan idan ta aika masa sak'o baya musa mata,da sauri ya tsada motan a gefen hanya
Ya biye mata,kusan minti biyar suna abu d'aya,ganin yana k'ok'arin wuce gona da iri yayi saurin dakatar dashi,murya a shak'e
''Am sorry YAYANAH muna kan hanyafa ''
Da k'yar ya jaa motan da mahaukacin gudu
Ita ko JIDDAH riganta ta shiga gyarawa,dan kad'an ya rage ya gama cire kayan dake jikinta
Gudun da yake ne yasa ta kalle shi
''YAYANAH please gudun fa yayi yawa,kar mu watse kan kwalta''
Kallonta kad'ai yayi yana murmushi,tare da rage malejin gudun motern..
Basu wani d'auki lokaciba suka isa gidan nasu...
Wanka sukayi kafin suka kwanta cike da nutsuwa da kwanciyar hankali.....
********
Kimanin watanni uku da sati guda da auren su kenan..
''YAYANAH pleasee dan Allah ina jin son abu mai sanyi''
A kaikaice ya kalleta kamar wanda bazaiyi magana ba
''Abu mai sanyi kuma HAYATEEY kamar me?''
''Emmmmm! yawwa! kamar ice cream haka,irin wanda yayi k'ank'ara ennanfa,ba na son mai ruwa ko kad'an''
Yanda ta dage tana bayani shi yasa shi yi mata wani kallo cike da zargi iri daban²,da haka ya fita nemo mata abun da take so...
Tun daga ranan ya zamo ice cream kusan shi ne abincin cinta,duk wani abu da zata ci sai ya dawo..
Sosai abun ya bawa YAH BOSS mamaki,amma babu yanda ya iya,cikin dabara ya mata test,nan ko ya hango ciki kwance a jikinta d'an wata d'aya da sati biyu,murna kam ba a magana gurin YAH BOSS,take ya sanar da MAMMY babu ko kunya,itama tayi murna sosai da jin labarin,bata yi k'asa a guiwa ba ko ta sanarma DADDY...
Ranarma kuwa gidan MAMMY suka nufa a can suka tarar da LITTLE tana fama da cikinta da ya soma bayyana,can suka yini dukansu,sai d'awainiya MAMMY take da su,komai aka dafa JIDDAH bata so,k'arshe dai da k'yar tace 'DAN WAKE da manja take sha'awa,babu b'ata lokaci kuwa MAMMY da kanta ta mata..
Shi kad'ai ta iya ci,in da tasa masa uban yaji,tana ci tana jann baki alaman yajin yayi yawa,ko da YAH BOSS ya k'wace kuka ta dasa har da birgima a k'asa...
Sai da MAMMY tayi da gaske sannan ya bata...
Tun daga ranar ya zama YAH BOSS ya koma bata kulawa ta musamman,ko kad'an bai so yaganta a damuwa duk abunda ta nuna tana so shima ko Yana sonsa.....
《《》》
Rayuwar MEINERH (LITTLE) da FAROUK rayuwa ce mai cike da jin dad'i,tare suke gudanar da duk wani abu da ya shafi rayuwarsu,gidan nasu gwanin sha'awa yanda suke rayuwa...
***********
*6 MONTH LEAPS.*
Kwance take saman sofa tana waya,jikinta sanye da singlet,da gani kasan tana buk'atar shan iska ne,duk kuwa da yanda parlorn yake a sanyaye...
''Pleasse YAYANAH za ka kawomin ko?''
''A'a babyna ban son kina shan sanyi sosai''
''Nifa Allah idan ban sha ba,zan iya mutuwa ne''
''Sorry baby amma kam ni baran siyo ba''
Kuka tasa masa had'e da kashe wayan tana jifa da shi kan sofa...
Jin ta kashe yasa ya hau dariya,yana fad'in
''HAYATEEYNAH ba dai rigima ba''
Haka ya gama aikin da yake,cikin sauri ya d'auko hanyan gidan,ko kafin ya k'ara so sai da ya tsaya ya siyo mata ice cream,masu k'ank'ara...
Yana shigowa cikin parlorn,sanyin gurin sai da ya bashi tsoro,kansa ya d'aga,nan yayi arba da k'arfin A.C en gurin,remote ya d'auka ya rage,a kan sofa ya hangota tayi rub da ciki,cikin sauri ya nufeta ya d'agota yana mata birkitaccen kallo
''Haba HAYATEEY kina so ne ki illatamin BABYNAH''
''Ni ka k'yaleni bacci nake yifa,ka wani tasheni''
''Tambayanki nake,kin san irin matsalan da wannan kwanciyan ke haifarwa kuwa?''
Bata kulashi ba ta shiga zamewa zata kwanta
''Pleassee dear ka k'yaleni ni''
''Ok zan k'yaleki amma banda irin wannan kwanciyan,promise me Bara ki sake ba''
kanta ta juyar bata ce komaiba,shi kuma ya janyo ledan da ya shigo da shi,dan ya san shi kad'ai ne abunda zai sa ta sakko daga fushin da take...
''Oyahhh!mik'e ki amsa sak'onki''
Da k'arfinta ko ta mik'e ta zauna tana murna,jin ya ambaci sak'o tana bin hannunsa da kallo,tun kafin ya bata har ta soma tand'e baki...........
*_~#TEAM J²~_*
*_REAL SMASHER._*🤞🏻😘
[5:54AM, 4/26/2018] rєαl ѕmαѕhєr💃🏻: 💠💠 *RAYUWAR WANI......*
_{ơŋɛ'ʂ Ɩlıʄɛ...}_
💠💠
🌹
*Viawattpad@realsmasher01.*
*©® 2018.*
*25/ąpril,2018.*
*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ...*
*ცყ.*
_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._
*~__________________________~*
*ADDU'O'IN RUKU'U.*
_SUBHANA RABBIYAL-AZIYM3_
_SUBHANAKALLAHUMMA RABBANA WABI-HAMDIKA ALLAHUMMAGHFIRLIY._
_SUBBUHUN,QUDDUSUN,RABBUL-MALA'IKATI WARRUUH.._
*_~#HISNUL-MUSLIM.~_*
*~__________________________~*
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)........*
*℘ąɠɛ 93↔94*
Cikin wani irin yanayi ya kalleta,yana binta da wani irin birkitaccen kallo,kafin ya ajiye cotainer en ice cream..
Kan cinyanta ya d'ora hannunsa yana binta da ido,ko kafin ya kai ga yi mata magana har ta riga shi..
''YAYANAH please ka bani,Allah na gaji da jira''
''Pleasse HAYATEEY karki sake irin wannan mik'ewan na rok'eki''
Ya fad'a har da had'e hannayensa guri d'aya...
''Ni Allah ka bani,nafa k'agu na sha''
''Zan baki amma sai kin min alk'awarin bara ki sake ba''
Hannayensa ta janye daga kan cinyoyinta ta sauka k'asa,take ko ta soma dira k'afafu tana masa tab'ara,ganin za ta soma birgima a gurin yayi saurin rik'eta...
''Me yake damunki kam HAYATEEY?''
''Ni tunda baraka bani ba ka kyale ni,naga dai ai bani nasawa kaina son abunba''
Da sauri ya rufe mata baki,yana janta,kan sofan ya zauna yana zaunar da ita kan cinyansa..
Containern ya d'auko,yana bud'ewa kuwa ta hau lek'a robbern uwa ba ita zata sha ba..
''Pleasse YAYANAH kayi sauri,kaga miyauna har tsinkewa yake''
''Allah koh?''
''Sosai ma,nifa sai jamin rai kake,idan bara ka bani ba na hak'ura''
Ta fad'a tana narke masa fuska uwa za tayi masa kuka..
''Bana son kina shan k'ank'ara ne,ki jira kad'an nayi melting nasa''
''Ni Allah baran yarda ba''
Ganin da gaske take,har tana shirin tashi,shi yasa yayi saurin rik'eta,ya hanata tashi..
Bashi da zab'in da ya wuce ya bata,haka ya shiga bata kuwa,yanda yaga tanayi shi ya sa ya soma kallonta,har wani lumshe idanunta take,tana kad'a kai uwa wacce ta samu wani abincin da bata tab'a samun irinsa ba......
Tsaf ta shanye robber biyu manya,wanda ya mak'ale a gefen bakinta da bata tand'e ba,ya kamo fuskanta ya juyo da ita..
Kallonsa tayi tana murmushi,dai² nata ya matso da fuskansa harshensa yasa ya shiga mata cleaning wajen,dariya tayi masakafin tace
''Shukhran QURATTU-AINIY''....
Bata samu damar k'arasawa ba,ta tsinci bakinta cikin nata..
Idanunta ta shiga k'iftawa saboda batayi tsammanin faruwar hakanba...
Gudun kar tayi laifi yasa ta biye mishi,suka shiga farantawa juna....
Bayan y'an kwanaki,tana zaune ita d'aya a parlor,ta janyo phone enta dake kusa da ita...
Line en HUBBEY ta shiga kira,tana d'auka ko tahau fad'in
''Sannu uwar zumunci,wato tunda an kawo ni dake,bari ki manta dani''
''Laaaa! Sistonah wollah ba haka bane,kinga yanzunma gidanki zanzo,nace ba sai na fad'a mikiba,kawai sai dai ki ganni,amma Allah ba haka bane''
''To shi kenan Allah ya kawoki lapia''
''Yawwa toh sai na zo''
Tayi hanging kiran,tana kwanciya...
Har bacci ya fara d'aukanta,taji alaman door bell na k'ara,cikin alamu na mai bacci ta nufi k'ofan parlor,tana bud'ewa,sukayi arba da LITTLE ta wani kama k'ugu,wani kallo ta jefi JIDDAH da shi kafin cikin fad'a ta soma magana
''Wato dan rainin hankali irin naki,shi ne ko kizo gidana kiga yadda yake''
''Ke ni dillah rabu da ni,ke en zuwa kikai da zaki wani hau yimin fad'a kamar wata y'arki''
''Hakama za kice?''
''Yo gashima kin fad'a''
Tayi k'wafa zata juya,kome ta tuna kuma ta dawo
''Amma dai kin san gara ni dake,tunda ranar da aka kawoki har dani aka zo ko?''
''Sai me kuma,wannan ma ai ba zuwan kanki bane''
''Shi kenan ai,ni dillah bani guri na wuce''
''Au ai nayi tunanin kin fasa zama ma,da naga kamar tafiya za kiyi ko?''
''Ban sani ba''
Tana doka mata harara,ta wuce tana neman gurin zama..
''Mutum daga zuwansa sai neman masifa''
Tana hararanta ta bi bayanta...
Ba a fi minti goma ba HUBBEEY ta k'araso,da murna ranan suka yini,wanda sun jima rabonsu da had'uwa kamar haka..
Suna tsaka da hira HUBBEEY ta kalle su tace
''Y'an uwa kunsan wani abu kuwa?''
Da mamaki suka kalleta,sai da tayi dariya tukun sannan tace
''Anfa sa ranar aurena''
Gaba d'aya suka had'a baki wajen fad'i
''Meeeyyyyyy?''
Aiko take ta sake sakin wata dariyan
''Lallai kin zama y'ar rainin wayo,shi ne har asa rana bamu sani ba?''
''Kudai yi hak'uri,kun san ba daga ni bane,wallahi ABBAH ya riga ya tsaida lokacin,muma daga baya ya fad'a mana''
''Kan uba,wallahi k'arya kike,taya zaki raina mana hankali kice wai baki sani ba''
Dariya tasa sosai,sukam sun sata gaba suna kallo,sai da tayi son ranta sannan ta kalle su..
''Uhmmm! yanzun dai mubar wannnan maganar coz babu lokaci sosai,kun sanfa yanzun saura 3 weeks fa''
''Meeeeyyyyyy!''
Suka sake had'a baki,suna kallon juna,su kad'ai kuma suka sa dariya..
''Shegen son gulma irin naku,har wani had'a baki kuke''
''Wai waye wannan mai nasaran da har ya saye zuciyanki,MR'S BOKO?''
''Amma wollahi JIDDAH baki da dama,sunan da kika rad'amin kenan?''
''Yo ba dole ba,tunda na ga samarin University basa gabanki''
''Ke dai bar y'an rainin wayo,bason Allah ke kawo suba''
''Wollahi kuwa,Allah dai yamana mai kyau''
''To ai shikenan,yanzun ya ake ciki,tunda lokaci ya k'ure mana gara muyi abunda ya kamata koh kuwa ya kukace ?''
Fad'in LITTLE tana kallonsu.....
Haka ne kam,shawaran abunda yayi saura za muyi kawai....
Nan suka shiga shawaran yanda zasuyi komai sun zauna suna ta fama,k'arshe dai suka yanke shawaran zasu sake had'uwa kafin sati guda ko da a gidan MAMA ne,daga nan suka shiga firan duniya,da yanda zasu koma skul nan da one week..
Sai yamma sannan HUBBEEY ta tafi,in da ta bar LITTLE a can,a cewarta idan SWEETHEART ya dawo zasu wuce gidan tare....
*2 WEEK LETER.*
Sati biyu kenan da had'uwarsu,kamar yadda suka yanke shawaran zasu dunga had'uwa duk sati,haka kuwa akayi,a ranan suka d'auka hanya sai gidan MAMA,duk da kuwa suna had'uwa a skul,coz satinsu guda kenan da komawansu skul,kullum kuma suna tare...
A ranan suka gama tsaida duk wani abun da zasuyi,na game da sha'anin biki,a ranan ma kuwa sai da suka kira telansu da zai musu d'inkunan fitan biki.....
Kowacce ta nufi gidanta......
*A WEEK LETER.*
Rana bata k'arya sai dai uwar d'iya taji kunya,kwanakin da sukayi saura har sunzo sun shud'e,har ancinye wasu kwanakin daga cikin satin bikin....
Kamar ba amaren da akayi bikinsu ba da jimawa idan ba mutum ya cika da tsananin sa ido ba,ba lallai ne ya gano cikin dake JIDDAH ba,sai dai ko na LITTLE da yake bata da wani timbi da zai b'oye cikin nata,haka suka fito fuskokin nan sun sha make up...
Da sauri ta fito daga cikin gidan,dai² haraban gidan ta tsaya tana waige²,motersa daya kunno kai cikin haraban gidan yanzun ta saki murmushi ganinsa kusa da ita,yana yin parking ta zagaya ta d'ayan b'arin tana sakin k'ayataccen murmushi da ba kowa takewa irinsa ba...
Sai da ta dai²ta zamanta sannan ta kalle shi cikin k'auna tana fad'in
''YAYANAH ba kace nayi kyau ba''
Tanayi tana fari da idanunta
''Bako sannu da zuwa,za kimin zancen wani kwalliyanki?''
'''Eyyaaaehhh !mana YAYANAH am sorry,ka zo lafiya?''
''Lafiya lao HAYATEEYNAH''
Cike da kulawa yayi maganar yana dubanta..
''Kwalliyan ya miki kyau sosai,sai dai gyara kad'an da zan miki,su make-up artists en sunyi mistake''
''Gyaran me kuma YAYANAH?''
''Matso kiga zan gyara miki da kaina''
Cikin nuna rashin damuwa ta tura masa fuskanta
''Gyaramin YAYANAH kaga suna so na k'i yin kyau''...
Bata k'asa ba,taji ya soma tsotsan lips enta,sai da ya shanye lips-stik en tsaff sannan ya kalleta,yana mata dariyan mugunta
Uwa za tayi kuka haka ta bishi da kallo..
''Haba dan Allah ya zaka shanyemin jan bakinah?''
''Saboda bana so ne''
Kallonsa tayi tace
''To idan kuma ina sofa?''
''Na san bara ki so abunda bana so ba''
Murmushi kad'ai tayi
''Har yanzun baku gama shirin bane?''
''A'a mun gama dan har an soma tafiya,mu kad'ai mukayi saura''
Suna cikin firan ne aka fito da Amarya HUBBEEY aka sanyata a mota...
Take kuwa kowa ya soma yin gaba,a baya suka bisu har gurin dinner wanda ya masifan tsaruwa,MR DJ ya saki dumaa,ranan an gyagije uwa ba gobe...
Duk k'ok'ari irin na JIDDAH kan ta tashi YAH BOSS ya kafa ya tsare duk inda zata yana biye da ita...
Sam ya hanata motsi,sai sai ta kalleshi tayi murmushi,duk wanda ya kallesu yaga tsantsan masoya,mutane sai maganarsu suke,duk inda kuwa suka gifta sai anyi maganarsu,haka taro ya watse,inda a washe gari akayi MOTHER'S EVE...
Ranan sunday da safe aka d'aura auren HABIBA IDREES da angonta ABDULLAH,tun da yamma aka d'auki amarya sai gidan ta dake unguwan TUDUN YOLA,gida ya tsaru dai² gwargwado,abunsu babu k'arya a ciki,haka mutane suka soma watsewa....
JIDDAH da LITTLE sun zo mata sallama,ta rik'e su atafau barasu tafi ba,da k'yar suka samu suka tsere...
A bakin k'ofa suka tsaya,suna dariya
''To AMARYA Allah ya bamu alkhairi,Allah kawo k'azantar d'aki''...
Wani kuka tasaa,su ko suka fice suna mata dariyan mugunta......
#To nima dai nace Allah bamu alkhairi amarya,a sha amarci lafiya........
*_~#TEAM J²~_*
*_REAL SMASHER._*🤞🏻😘
[9:15PM, 4/26/2018] rєαl ѕmαѕhєr💃🏻: 💠💠 *RAYUWAR WANI......*
_{ơŋɛ'ʂ Ɩlıʄɛ...}_
💠💠
🌹
*Viawattpad@realsmasher01.*
*©® 2018.*
*26/ąpril,2018.*
*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ...*
*ცყ.*
_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._
*~__________________________~*
*ADDU'O'IN 'DAGOWA DAGA RUKU'U.*
_SAMI'ALLAHU LIMAN HAMIDAH.._
_RABBANA WALAKAL HAMD,HAMDAN KHASIYRAN,'DAYYIBAN MUBARAKAN FIYH.._
HISNUL-MUSLIM.
*~__________________________~*
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)........*
*℘ąɠɛ 95↔96.*
Tun suna hanya take jin jikinta duk yana mata ciwo,jinta take uwa wacce akawa duka,duk gab'ob'in jikinta a d'aure,ita kad'ai sai juyi take a kan seat en...
A hankali ya kwatar mata da seat en yanda za tafi jin dad'in kwanciya,juyowa tayi ta kalleshi fuskanta d'auke da murmushi,idanun kuwa da gani kasan bacci ne cike a cikinsu...
''Shukhran HABEEBEEY!''
Baiyi magana ba ya mayar mata da murmushin shima,yana maida hankalinsa akan driven en da yake...
Ko kafin suje gida,har ta fara bacci,da kansa ya d'auketa har bedroom sannan ya shimfid'eta saman bed..
Ruwa ya had'a mai d'an karen d'umi,ya dawo cikin dabara ya zare kayan dake jinta,yayi hanyan toilet da ita..
Jinta cikin ruwa shi ya bata damar bud'e ido,ta narke fuska uwa zatayi kuka..
''Haba dan Allah HABEEBEEY nafa fara bacci zaka wani tashe ni''
''Sorry HAYATEEY idan namiki wankan zaki fi jin dad'in baccin''
Bata kuma cewa komai ba,har ya gama mata wanka ya dawo da ita ya kwantar,har ya juya zai koma ta dakatar da shi..
''HABEEBEY ina ice cream ena?''
Kallonta yayi shi yama manta da sak'on nata,tsaiwa yayi uwa mai nazari,can kuma dabara ta fad'o masa
''Bari nayi wanka na fito,sai na d'auko miki koh?''
Kai ta kad'a masa tana y'ar dariya,har wani gyara zama take,saboda za ta sha kayan kwad'ayi..
Wayanta dake ring a saman bedside drower ta janyo,da sallama ta amsa...
Sai da ta soma dariya kafin tayi magana
''Amarya bakya laifi,ko da kuwa kin kashe d'an masu gida''
''Muguwa kyace haka mana,tunda kun tsere kun barni wato ba ruwanku da abunda zai sameni ko,ae shi kenan''
Da sauri tayi magana
''Sai munyi waya gobe,ga sunan shigowa''...
K'it ta kashe wayan,ita ko JIDDAH nan taita dariyanta..
Line en LITTLE ta kira,a wahale ta d'auka,nan JIDDAH ta labarta mata yanda sukayi da HUBBEEY..
''Bar y'ar air yanzun ta kirani nima,za tamin iskanci,nima na tsigeta,ko an fad'a mata dama zamu zauna mata zaman d'aki ne?''
Sun jima suna shak'iyanci,hango YAH BOSS na tahowa yasa tayi mata sallama tana fad'in
''Sis sai da safe ga YAH BOSS nan,mu kwana lapia''
Kalamanta na k'arshe su yaji,kallonta yayi yana murmushi yace
''Ke dawa kike waya kuma,ba bacci kike jiba?''
Dariya tayi kafin tace
''Ai kai ka hanani baccin''
''A'a fa HAYATEEY ni ban hanaki ba''
''Allah kuwan kaine ba ruwa kasaminba kaga kuwa dole na tashi''
''Ok toh!zo na miki tausa sai kiyi baccin koh?''
''Toh ai ban sa kaya ba,kagafa towel kad'ai ne a jikina''
''No!ba sai kin saba,hakama is ok''
''Kasanfa ban saba kwanciya a hakaba''
''Yeahh!yau kuma ni nake son ganinki a haka,ko ban isa ba?''
''A'aa YAYANAH harma kayi yawa''
''Oyaahh!kwanta toh na miki tausa sai kiyi baccin,nasan akwai gajiya a tare dake''
''Laaa!HABEEBEY banfa sha ice cream en ba''
Kansa ya dafe,coz shi har ya manta da maganan ice cream en..
''Ok ina zuwa''
Ficewa yayi ya d'auko ice cream en a cikin freezer,duk ya zama k'ank'ara,ya dawo ya tarar da ita a zaune tana jiran dawowansa,da murnanta ta kalleshi tana ta faman zuba smiling....
Tana gama sha kuwa,ta nufi toilet ta wanke bakinta,daga ita sai towel iya cinyanta,fararen cinyoyita duk suna bayyane,tun daga yatsunta yake kallonta,dogayen k'afafuntan da suka bayyana su suka dad'a jan hankalinsa,bai sauke eyes ensa ko ina ba,sai kan k'irjinta da ya dad'a cika,hannunta ya kamo ya kwantar da ita ya shiga matsa mata jiki a hankali,sosai take jin dad'in tausan da yake mata,har wani lumshe idanu take...
Ji tai ya zare towel en jikinta,a ranta ta furta
''Nasan za a rina,wai an saci zanin mahaukaciya''
''Tafiyan tsutsa yake mata a jiki,wanda yasa ta soma dariya,kafin itama ta biye masa suka lula wata duniyar......
*NEXT MORNING.*
Tun da safe HUBBEEY ta kirata,ai ko tana d'auka ta hau k'orafi
''Muguwa kyayi dariya mana,dama kunsan da haka ba kuyimin bayani ba,wallahi zamu had'u ne saina muku rashin mutunci''
Banda dariya ba abunda take,haushin dariyan ya k'ular da ita ta kashe tana k'wafa....
Wata uku da auren HUBBEEY,ranar wata laraba,tun rana LITTLE take fama da nak'uda uwa bazata rayuba haka aka d'unguma da ita asibitin AKTH nan ta sumb'ulo jaririyarta k'atuwa da ita y'ar gwanin sha'awa,kyakykyawa gwanin burgewa,nan dangi sukaita faman murna sun samu k'aruwa...
Gida FAROUK ya dawo da ita,nan MAMMY taita d'awainiya da ita,ranan suna yarinya ta ci sunan MAMAR FAROUK wato FATIMA ZAHRA,kowa sai son barka yake inda ake kiranta da ZAHRA...
A ranar da tayi arba'in MAMMY ta tarkata da kayanta ta sallamesu,bayan gyara da ta sha,tamkar wata amarya haka ta koma...
Watan BABY ZAHRA uku a duniya,amma kamar y'ar watanni 5 ta dad'a girma,gwanin sha'awa,yarinya kamar jinin larabawaa....
JIDDAH koh duk ta shiga damuwa,yanda cikinta ya bayyana yanzun duk jinta take a takure,har lissafi take na ranar da zata sauke,duk da ya k'ara mata kyau,hakan ba zai hana a gano yanda gab'ob'inta suka dad'a bud'ewa ba,ta dad'a zama uwar mata...
MAMMY da kanta ta tasa YAH BOSS akan ya dawo da JIDDAN gida,shi ko babu kunya yace
''MAMMY dan Allah ki bar wannan zancen,zuwa wankan nanfa ba addini bane,so ni gaskiya bani da sha'awar barinta zuwa wani wankan gida''
''K'aniyarka JABEER''
Ta masa dak'uwa,tana harararsa
Kansa a k'asa,yak'i yarda su had'a ido,ambatar sunansa da tayi,wanda tun tasowarsa bai tab'a jin hakan daga bakinta ba,shi yasa ya kalleta..
Cike da jin kunyar abunda tayi itama ta mik'e,sai da taje dai² k'ofar d'akinta sannan ta d'an waigo tana fad'in
''Ka tabbata ka kawomin ita cikin wannan satin,inba haka ba,ranka zai mummunan b'aci''...
Tana gama fad'a ta shige,har ya bar gidan bata kuma fitowa ba....
Kwanaki uku tsakani kuwa ya dawo da ita,fuskar nan uwa zaiyi kuka,haka ya fice daga gidan ko sallama ba wanda yayiwa...
Da darema da ya dawo daga gurin aiki,lokacin da ta kawo masa abinci sai b'ata rai yake,uwa ita ta masa laifin...
Haka ya zauna sai da ya raba dare a gidan,ita ko MAMMY d'aki ta shige tace idan ya fita ya jaa musu k'ofan,ganin ta fara lumshe ido alamar tana son yin bacci yasa ya d'aketa sai d'akinsa da yayi zaman gwaurantaka....😜
''HABEEBEY!Me kuma zanyi nan d'akin?''
''Ni zaki taya kwana,kinga baran iya bacci ba ni kad'ai''
''Uhmmmm! kaima dai HABEEBEY da wani magana kake,to me zai hanaka baccin?''
''Tunaninki ne zai hana ni,kinga zanta mafarkinki cikin dare,amma idan kina kusa da ni,bazan yiba''
''Da gaske HABEEBEYNAH?''
''Ehhh!mana,ko kina so nayi?''
''A'aa bana so''
Ta fad'a tana k'unshe dariyan da ya taho mata
''Dariyama kikemin koh?''
''Ni na isa namaka dariya,ai da anmin bulala''
''Waye zai dakarmin HAYATEEYNAH?''
Ya fad'a yana fiddo ido waje...
Sai da tayi dariya mai isarta ganin yanda yayi da idanunsa,sannan ta kalle shi tace
''Kai mana''
''Ni kuma da kaina zan dakeki?''
''Ehhh mana,dan bakasa bulalaba ae ka ban wahala a kan bed''
Tana fad'a tayi maza ta kulle idanunta,dariya sosai yayi lokacin da ya ajiyeta kan bed..
''Ai ko tunda haka ne,yanzunma ki shirya amsan wani bulalan,yau kwana zakiyi ba bacci''
Yana dariya yake maganar...
''Allah Yaya ba ruwa na,kagafa BABYNMU dama duk ya takurani''
''Da gaske kike ya takuraki?''
''Sosaima kuwan Allah,duk mutum bai da kwanciyar hankali''...
Tana yatsina fuska tayi maganar...
''Ke dai fad'i gaskiya,ko dai ni kike buk'ata shi yasa kika ce haka?''
Yana kashe mata ido d'aya....
''Kai HABEEBEY Allah ka koyi fassara mutum,ni ba haka nake nufiba to''
''Ok!let me find d truth''
Ya soma haurawa kan bed en yana mata dariya k'asa²...
''Nifa Allah babu ruwana,ka bari HABEEBEY''
''Nifa ba abunda zan bari,sai na gaisa da BABYNAH,so nake na miki bulalar da ko gobe nema ki haihu,tunda BABYN nawa ya takuraki,kinga ya k'yale MAA nd PHAA ensa su huta''....
Daga haka ko bai sake bata damar yin maganaba ya had'e bakinsu guri d'aya yana mai aika mata sak'onni iri daban²,suka shiga faranta ran junansu.........
*_~#TEAM J²~_*
*_REAL SMASHER_*🤞🏻😘
[4:58AM, 4/29/2018] rєαl ѕmαѕhєr💃🏻: 💠💠 *RAYUWAR WANI......*
_{ơŋɛ'ʂ Ɩlıʄɛ...}_
💠💠
🌹
*Viawattpad@realsmasher01.*
*©® 2018.*
*28/ąpril,2018.*
*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ...*
*ცყ.*
_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._
*~__________________________~*
*ADDU'O'IN 'DAGOWA DAGA RUKU'U.*
_SAMI'ALLAHU LIMAN HAMIDAH.._
_RABBANA WALAKAL HAMD,HAMDAN KHASIYRAN,'DAYYIBAN MUBARAKAN FIYH.._
*_~HISNUL-MUSLIM.~_*
*~__________________________~*
_Kumin afuwa Fan's nayi mantuwa a last page da na na *RAYUWAR WANI* nasa "2nd to the last page, to kuyi hak'uri wannan shi ne maimakon wancan,na gode sosai muna nan manne da juna.._ *#1 Luv my fan's.💃*
*~__________________________~*
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)........*
*℘ąɠɛ 97↔98.*
Cikin dare ko wani azababben ciwo ya farkar da ita,ciwo sai kace ba zai lafa ba haka taita fama da shi,ya dank'a ya saki....
Da ciwon ya ciyota ta sauka k'asa kanta na gefen gadon ta kifa shi......
Juyawa tayi ta kallo side en da yake,hankalinshi kwance yake bacci,haka taita fama da ciwo,zuwa wani lokaci ciwo ya dad'a kunno ta,ai bata san lokacin da ta kai masa wani mahaukacin naushi ba..
A firgice ya mik'e dan ko yaji dukan,coz a bazata ya zo masa,kallon gefensa yayi,yaga ta dunk'ule guri guda,sai juya kai take,ita kad'ai ta rik'e baya,ana jimawa zata koma ta dafe maranta....
Da sauri ya sakko yana rik'eta,kallo d'aya da ya mata har ya shiga damuwa...
''HAYATEEY meke damunki?''
Su HAYATEEY ba baki sai ido,mararta da bayanta ta shiga nuna masa,take ko ya hau aikin murza mata dan ya fahinci abunda take nufi,can ciwon ya d'an lafa mata ta kwantar da kanta a kafad'arsa tana sauke numfashi d'ai²....
Haka ya zuba mata ido yana kallonta shi kad'ai yasan me yake ji game da ciwon nata,kuma lokacin dare yayi sosai...
Har bacci ya kuma d'aukanta,wajejan Asubah ta sake farkawa da wani gigitaccen ciwon da yafi na farko,nan ko babu shiri YAH BOSS ya sunkuceta yayi waje,ko MAMMY baibi ta kan ya fad'a mata abunda ke faruwa ba,yayi hospital da ita....
Har gari ya soma wayewa amma labari bai canza ba kuma shima baiyi tunanin sanar da MAMMYN ba,duk ya shiga damuwa,baya ga addu'ah babu abunda yakeyi,yana kanta ya hana kowa zuwa gurin....
Wajen k'arfe 7:30am BABYN ya kunno kai,bayan d'imbin wahala da JIDDAH ta sha,ba ita kad'ai ta sha wahalar ba,dan ko tare sukayi nak'udar da YAH BOSS,da taimakonsa ya zaro BABYN cikin ikon Allah,tsananin murna yasa ko wanke babyn ba ayiba ya rungume abunsa yana jin tsananin k'aunarsa na ratsa masa zuciya....
Kallon HAYATEEYN nasa yayi yaga tayi laga² kan bed en tana mai da numfashin wahala,nan ya shiga mata sannu,ai ko tana d'agowa tace dawa Allah ya had'amu ba kaiba...
Sak'on harara ta fara aika masa,cikin wahalalliyar murya ta furta
''Kai da jin dad'i ni kuma da wahala''
Ta k'arasa tana murgud'a masa baki..
Dariya sosai yayi,ya jaa hancinta
''Bari inyi miki gyara''
''Ba wani gyara ni Allah na yafe gyarankan nan''
Dariya sosai maganarta ta bashi
''To shi kenan tunda bakya so,ai da kanki zaki zo har in da nake''
''Tabbbb Allah ba amin ba,haka kawai ka sake d'irkamin wani cikin,in zo ina haifewa da k'yar''
''Haba HAYATEEY kifa dena fad'a dan kam Allah zaki kawo kanki,kuma ai naga tare mukayi nak'udan har haihuwanma''
''Ba wani nan''
''To shi kenan na ji,barin gyaraki da BABYNMU koh?''
Sai lokacin ta d'an saki fuska tana fad'in
''YAYANAH wai me muka samu ne?''
''Oohhh!yanzun kuma kin sakko?''
''Uhmmm dama ba fushi nayi ba ai,d'an nunamin BABYN''
Ta wani marairaice fuska...
Haka sukaita shirmensu,kafin ya goge babyn da zaitun,tsaf ya gyara su duka,ita ko sai mamaki take.......
Suka d'auko hanyan gida yana rungume da babynsun....
。。。。。。
A gida ko tun safe MAMMY da ta tashi,ta nemi JIDDAH ta rasa,ranta idan yayi dubu ya kai mak'ura wajen b'aci...
A ranta ko fad'i take,''lallaima yaron nan wato ni zai mayar sakara da zai d'auke matarsa daga gidan,zasu zo duka su sameni....
Tana tsaka da wannan tunanin suka shigo parlorn da sallama....
Da k'yar ta iya amsawa,tana binsu da kallon mamaki,fuskokinsu d'auke da fara'a suka nufe ta...
''Meye nake gani haka?''
Tayi tambayar tana bin hannun YAH BOSS da kallo ganinsa d'auke da abu cikin towel na jarirai fari sol...
Murmushi yayi yana mik'a mata,ita ko cikin JIDDAH tabi da kallo,ganin alamun ba gizo idanunta ke yi mata ba ta amshi yaron fuskanta da tsananin farin ciki,tana fad'in
''Sannu doughter,masha Allah,Allah ya baki lafiya''
Shi ko gogan sai amshewa yake da ameen,fuskarnan sai doka murmushi yake uwa an masa bushara,bakinsa yak'i rufuwa.....
Wani kallo MAMMY ta masa a kaikaice tace ''To sarkin fitsara,ya akayi ka san bata da lafiya?''
Sosa kai ya shiga yi ba tare da ya iya bata amsa ba,yayi shiru..
''Allah ya kyauta,Allah kuma ya shiryamin ku''
Tana gama fad'an haka ta mik'e ta nufi kitchen,ta shiga had'a mata abinci da masu jego suka fi buk'ata,dai² lokacin da ta fito ta nufi d'aki,ruwa ta tara sai turiri yake,duk abunda take suna zaune parlor sun tusa babyn a gaba suna kallo..
Fita tayi tasa BABA mai gadi yasamo mata almajiri,aikensa tayi ya samo mata ganyen darbejiya,bai d'auki lokaciba ya dawo da shi da uban yawa,ta amsa ta sallame shi,shigowa tayi har ta wuce su ta dawo tana fad'in ''Doughter,taso ayi wanka ko?''
Mik'ewa tayi tana bin bayan MAMMY har toilet suka shiga,aiko nan ta zauna,MAMMY tana yarfa mata ruwan farko ta fasa ihuu ''Wayyoo YAYANAH zan mutu''
Kamar an tsikare shi ya mik'e yana bin hanyar d'akin MAMMY,a bakin k'ofa ya tsaya yana jin yanda suke fama da MAMMY ita ko sai kuka take tana kiranshi..
Kasa jurewa yayi ya hau bugun k'ofar yana fad'in ''MAMMY dan Allah ki bar wankan nan,kar ki k'onata''
Sai rok'onta yake,tayi masa banza,sai da ta k'are wankan,sannan ta fito ta barta ta k'arasa..
A bakin k'ofa ta tarar da shi yana d'auke da babyn,harara ta watsa masa ta fice ta barshi nan..
Da k'yar ta iya zama cikin ruwan zafin ta gasa jikinta,towel ta d'auro ta fito,sai narke fuska take uwa za tayi kuka,har lokacin yana bakin k'ofan,tana bud'ewa ko ya rik'ota har bakin bed yana shirin zaunar da ita tayi saurin mik'ewa
''Mene ne kuma HAYATEEY?''
''Barin k'arasa gyara jikina tukun''
''Ok toh baby''
''Ni ka dena cemin baby,nafa girma''
Sai wani fari take yi,kuwa ba ita ta gama raki yanzun ba..
''Oohh!haka nefa,sorry toh baran sake fad'aba''
Ya fad'a yana murmushi..
MAMMY ce ta shigo tana kallon ikon Allah tana shirin magana babyn ya fara kuka ''to rasai bani yaron na gyara shi,ga shima har ya fara kuka da gani yunwa yake ji''
Amsarsa tayi ta wanke shi tsaf,ta shirya shi cikin kayan sanyi masu kyau na jarirai,sai canyara kuka yake,JIDDAH ta kalla tana d'ora mata shi a cinya ''maza a bawa baby abinci kafin na dawo'' ta fice daga d'akin..
'Dago babyn tayi tana kallonsa tana murmushi,ita kam ma sai yanzun ta kalleshi sosai,ta shagala da kallon babyn tajiyo hannun YAH BOSS a cikin riganta,da sauri ta kalleshi...
''Haba HAYATEEY kina kallon yana kuka kin tsaya kallonsa,oyaa feed him''
Murmushi tayi lokacin da ya k'arasa fito da...... ya shiga sawa babyn a baki,lokacin da ya kama kuwa wata sabuwar azaba taji har tsakiyan kanta,ido ta rufe tana cije lip enta,wani ihuu tasa tana kallon YAH BOSS
''Tabbbb wallahi YAYA da zafi,in ba sai dai a hak'ura da bashi abincin,dan ni dai baran iya ba gaskiya''
Tana fad'a koh ta fito da abunta daga bakin babyn,shi ko kuka yasa jin an yanke masa jin dad'insa sosai yake kuka ko takansa bata biba ta maida cikin riga..
''A'a HAYATEEY hak'uri fa za kiyi,kinga shi ne abin da zai ci ya rayu,kin ga yana kuka,ki tausaya masa mana''
''Nifa gaskiya YAYA ka denamin dad'in baki,dan bazan iyaba gaskiya,sai dai a bashi madara''
Idanunsa ya zaro yana fad'in
''Madara fa kikace baby''
''Eeehh!mana ai abinci ne shima''
Suna tsaka da jayayya MAMMY ta dawo ta tarar da su a haka,shi yana lallab'ata ita ko tana k'i,kallon tuhuma tayi musu ganin sunyi tsuru-tsuru
''Kin bashi abincin ne?na ga har yanzun yana kuka''
''Yawwa MAMMY gara kisa bakima wallahi,wai ba zata ba shiba ita zafi,wai sai dai a bashi madara''
''Zancen banza kenan,kin bashi ko kuwa sai na sab'a miki?haka aka miki ke?''
Ba shiri ta shiga kiciniyar fito da shi tana matsar k'wallah,ta sanya mishi a baki take ya sake yin shiru ya hau tsotsa,haka ya ci gaba da sha,ita ko azaban da take ji ya hanata magana,yana saki ta samu sa'ida...
A bincin dake hannun MAMMY ta ajiye tana fad'in ''ga shi nan ki tabbata kin cinye kafin na dawo''
''HAYATEEY taho na baki kinji''
Harara ta watsa masa ta zame ta kwanta,tana rufe ido sauran hawayen dake ciki suka k'arasa zubowa..
Tasowa yayi ya d'agata yana fad'in ''yi hak'uri ki taso ki ci abinci kin ji,kinga in ba haka ba,babyn baze samu abin da zai ciba nan gaba''
''Ni ka kyale ni,bacci zanyi,bayan fad'an da kuka jawomin,za ka wani dame ni da maganar abinci,baran ci ba en,ai dai ciki nane ko?to ban ci'',haka yayi ta fama da ita ta k'i..
''Ok toh barin kirawo MAMMY''
Da sauri ta rik'e shi ''A'a karka kirata zan ci to naji'',murmushi yayi ya d'auko ya shiga bata da haka har ta ci da yawa,sai da yaga alamun ta k'oshi sannan ya kyaleta...
Wayanta ta d'auko dake ring tana karawa a kunne da sallama
''To mara mmm shi ne babu labari kin haihunma?''
''Ke ni rabu da ni,wane labari zan baki banda azaba da nake ta sha tun da na haihun''
Dariya taita mata ita ko tayi k'wafa tana fad'in
''Bashi a gidan b'arawo rance ne''
'Dif ta kashe,tana kwanciya...
Kafin wani lokaci gidan har ya fara cika da jama'a wad'anda MAMMY ta sanar da su haihuwar JIDDAN...
Sai baccinta take hankali kwance,shi ko ANGON K'ARNI yana zaune zaman gadinsu,shigowar da MAMMY tayi haka ta tarar ya buga tagumi yana kallonsu yana murmushi..
BABYN ta d'auka za ta fita, ''MAMMY ina kuma zaki kai shi?''
''Gidanku'' ta masa dak'uwa tana yin gaba da fad'in
''Siyar da shi zanyi''
Ta fice ta barshi yana sosa k'eya..
''Wai kam MAMMY ina mai jegon ne?''
Fad'in LITTLE da tazo tun d'azun..
''Tana bacci''
''Haaa!zama ta tashi ne wollahi'' ta nufi hanyan d'akin
''Allah baki ikon tashinta''
Da shi ta soma arba tana bud'e k'ofan d'akin,aiko bata k'arasaba ta rufe ta dawo,MAMMY ce ta kalleta tana d'an murmushi ba tace komaiba.MAMMY ai sai ki cemin yana ciki...
''Waye a acikin?'' ta tambaya uwa bata sani ba, ''YAH BOSS mana''.
''Au wai da gaske wannan sunan har yanzun kuna fad'ar sa?''
''Uhmm!'' kad'ai ta iya cewa,taja baki tayi shiru..
Suna tsaka da fira gidan a cike,DADDY ya shigo kana kallonsa kasan yana cikin tsananin farin ciki,aiko MAMMY ta bi bayanshi hannunta d'auke da BABYN,a parlornsa ta tarar da shi,hannu kad'ai ya mik'a mata,ta bashi tana murmushi,kallon yaron yayi yana murmushi,sai yake ganin uwa JABEER ensa ne yana jinjiri,saboda tsananin kama da suke da yaron..
''An masa khud'ba?''
Abunda ya iya tambaya kenan
''Barin tambaya inji,dan yaron nan akwai shi da shiririta wollahi''
K'asa ta sauka,har lokacin yana zaune,
''Ka yiwa yaron khud'ba kuwa?'',ta tambayeshi,juyowa yayi yana kad'a mata kai ''A'a, daman DADDY nake jira ya dawo'',fita tayi ta koma don sanar da DADDY halin da ake ciki,haka ya masa kiran sallah had'e da khud'ba,ya kuma ambace shi da MUHAMMAD AL'AMEEN...
Tashi tayi tana mik'a,juyowan da za tayi suka had'a ido,murmushi ya sakar mata yana matsowa inda take,k'ok'arin sauka tayi daga gadon,ya rik'ota
''haba mana HAYATEEY fushin ne baki gama ba har yanzun?'',
A kan k'afarsa ya zaunar da ita yana rungumeta tsam a jikinsa,ko kad'an ya hana mata ta tashi,magana yake shirin yi,MAMMY ta shigo d'akin
''Me zan gani ni y'asu?maza tashi ka fice kafin na b'ata maka rai fitsararren banza'',nan ta kore shi,yana fita ta juyo kan JIDDAH da take ta faman sadda kai k'asa, ''ke kuma idan baki daina shige masa ba ke zai baro,kina fama da d'anyan jego kya dad'a kwaso wani cikin'',ai kuwa jin haka jikinta ya dad'a lak'was..
Haka MAMMY ta barta duk tunani ya dabaibayeta...
Tun daga ranar kuwa ta shiga taka tsantsan,ko kusa da shi bata yarda taje,duk iya yinsa har ya hak'ura ya zuba mata ido,kullum kuma a cikin gidan yake kwana,amma har yau MAMMY bata ankara ba...
Ranar suna kuwa anyi shagali dan uwa za a sake aurensu haka aka gudanar da taron suna,jama'a da dama sun halarci gurin, taron suna yayi albarka sosai,mai jego da d'ansu AL'AMIN sun samu kyaututtuka na ban mamaki...
Nan HUBBEEY ta zo sai fama take da laulayi,suko sai dariya suke mata,suna tsokanarta da ta harbu....
Kowa ya shiga ya fita,situru sunyi kuka,dan kamar biki ake haka taron ya kasance,da yamma ko aka wuce gurin walimar sunan inda aka gudanar da ita a *THE APICENT* taron da ya samu halarta manyan mutane,a nan DADDY ya gabatar musu da kyaututtukansa inda ya mallakawa JIDDAH da LITTLE manyan motoci k'irar MATRIX kowacce colour en tata daban,sai godiya ake ta tayasu,nan DADDY ya kuma sanar da jama'a cewa wannan taron ba iya taron walimar haihuwan takwaransa bane,har da taron walimar taya iyaye ga jaririn murnar bud'e sabon asibitin da aka jima ana aikinsa,nan aka kira JABEER a matsayin shugaba na asibitin tare kuma da gabatar dashi ga sauran mutanen gurin...
Haka taro ya watse anata sam barka,kowa ya nufi gidansa cike da gajiya...
Haka rayuwarsu ta ci gaba da gangarawa cike da nasarori ta ko wane b'angare,ko wane gida idan zaka shiga sai rayuwarsu ta baka sha'awa saboda yanda suke gudanar da rayuwarsu cike da so da kuma girmama juna,abun gwanin burgewa....
Tsawon sati hud'u kenan da haihuwarta,jaririnsu ya dad'a girma iya wad'annan kwanakin,sam ya dena zuwa kusa da ita,idan yazo k'ark'ari ya ga baby,haka zai raba dare yana masa wasa,idan yayi bacci kuma ya kaishi d'akin ya kwantar,mafi yawan lokaci idan ya shiga haka zai ganta tayi bacci,sai dai ya k'are mata kallo ya gama had'iyan yahu yayi gaba..
Yauma shigowa yayi da niyyan kwantar da baby AL'AMEEN,ji yayi bazai iya hak'uri ba ganin wani azababben kyau da ta dad'a,ai ko ya kwantar da shi ya hauro kan gadon,cikin bacci taji ana shafa mata jiki,da sauri ta bud'e ido a hankali,ganina kusa da ita a tsorace ta kalleshi tana fiddo idanu waje,sai jaa baya take,biyota ya shiga yi
''Please HAYATEEY hak'urina ya gaza,duk iya yina akan nayi nesa dake na kasa,pleasee ki taimakeni,ina cikin wani hali komai zai iya faruwa da ni''
''Ni gaskiya YAYA kayi hak'uri,wallahi ina jin tsoron abunda zai faru''
Ci gaba yayi da bata hak'uri,duk hanyar da ya biyo za ta doje,ganin ta k'i yarda yasa ya mik'e a fusace,zuciyarsa na sak'a masa plan en da yasan muddin yayi amfani da shi yasan baza ta k'iba,nunata ya shiga yi da yatsa
''Ni kikaiwa haka ko?to ki rik'e abunki,zanje waje na nema da kud'ina'',juyawa yayi zai fita yana wani murmushin mugunta.......
Da gudu ta taso ta rungumeshi ta baya,hawaye har sun fara zuba daga idanunta,''Pleasse YAYANAH karkamin haka,ko da can baka nemi matan waje bare yanzun,wollahi na yarda koma mene kayi amma kamin alk'awarin bazaka tab'a neman wata a waje ba''
Yana jin yadda kukanta ke ratsa masa zuciya,amma sai ya dake yana k'ok'arin k'wace jikinsa,sai wani pretending yake mata,shi a dole ta k'yale shi,baya so...
Sosai take kuka,ganin da gaske yake ta zagayo ta gabansa suna fuskantar juna,bata jira komaiba ta had'e bakinsu guri d'aya,nata salon ta shiga aika masa da ya sa shi shiga shock sai da ta gama birkita masa lissafi sannan da k'yar suka zube saman bed,sun nunawa juna yanda suka yi missing kansu,sun raya daren cike da so da k'aunar juna,kafin bacci yayi gaba da su...
*_~#TEAM J²~_*
*_REAL SMASHER._*🤞🏻😘
[8:49PM, 5/1/2018] rєαl ѕmαѕhєr💃🏻: 💠💠 *RAYUWAR WANI......*
_{ơŋɛ'ʂ Ɩlıʄɛ...}_
💠💠
🌹
*Viawattpad@realsmasher01.*
*©® 2018.*
*1/mąყ,2018.*
*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ...*
*ცყ.*
_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._
*~__________________________~*
*ADDU'O'IN 'DAGOWA DAGA RUKU'U.*
_SAMI'ALLAHU LIMAN HAMIDAH.._
_RABBANA WALAKAL HAMD,HAMDAN KHASIYRAN,'DAYYIBAN MUBARAKAN FIYH.._
HISNUL-MUSLIM.
*~__________________________~*
*GAISUWA TA MUSAMMAN Y'AN UWA RABIN RUHI,WOLLAH INA MATUK'AR K'AUNARKU..* 💔💔💔💔
_AUNTY KHADIJA MMN K²_
_AUNTY HASSY (GOLDEN VOICE)_
_AMINA HARUNA HALLIRU (MEINERH)_
_AMINA SALIS MUSA (LITTLE)_
_HABIBA IDREES (HUBBEY)_
_SAFIYA BALA (MOM HANAN)_
_MURJA SALIS (NA'IKKE)_
_HAFSAT MAI SHERRIF_
_FATIMA IBRAHIM (MUNEERAH)_
_AYUSHA ILYAS_
_HALISSA ADAMOU (MY LISSA)_
_KHADIJA S DOGARAI (LIPTON)_
_HALIMATU SADIYA MUH'D (LEEMA)_
_RABI'ATU ADAM MUHAMMAD_
_AUSHA ABDULLAHI ABUBAKAR_
_HUSSAINA HUSSAIN TIJJANI_
_AISHA SHEHU JIBRIL (MOM IRFAN)_
_RAMLATU NURA (MMN KHAIRAT)_
_REAL MAE DAMBU._
_AUNTY MAIMOUNATH_
_RUQAYYA HASSAN UTHMAN_
_FATIMA A¹ (PHERTEENJEEY)_
_FATIMA A² (FATEEY AFIRST)_
_QUEEN HAFSY_
_HAUWA (QUEEN HAUSEY)_
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_
_QUEEN ACID_
_MARDIYYA M²_
_AISHA WHITE (DOUGHTEEY)_
_MAMAN BOY_
_KHADIJA DEE_
_PRINCESS ESHAT AYSM_
_AISHA SADA MACIKA_
_HAWWER A SARKI (NAMECY)_
_REAL NASBASH_
_BILLY S FARI_
_FA'IXA (ANFA)_
_FAUZIYYA._
_MUHIBBAT INDIA_
_AYUSHA_
_FATEEY TAMBARIY_
_AISHA A.YABO (FULANI)_
_KHADIJA SALEEHU (MY DEEZOH)._
_RAHEEMA_
_REAL RAHAMA NA LELE_
_AISHA ISAH (MUMMYS FRIEND)_
_SAWWAMA A_
_HEARMEEBRAERH._
_SARAH ADIYA (SARARA)_
_SUMMY NICE_
_AYUSHER MUHAMMAD_
_DIDILURV_
_NUSAIBA GENTLE LADY_
*_ARADU WANNAN SHAFI YAYI MUKU KA'DAN SABODA YAWANKU,ALLAH YABAR ZUMUNCI,MU KASANCE HAR A ALJANNAH..._* *ONE LUV MY PEPS* 👌💓
*~_________________________~*
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)........*
🔚
🔚 🔚
🔚
*℘ąɠɛ 99↔END.*
Haka suka shafe ragowar kwanakinsu,duk ranar da yaji bazai iya hak'uriba zai lallab'a ya kwashi gara abunsa,coz satinta biyu da haihuwa ta samu tsarki,kwana suke farantawa juna rai,asuba nayi zai lallab'a ya fice,ba shi zai dawo ba sai gari ya gama wayewa...
Ana gobe zasu cika kwana arba'in suna tsaka da faranta ran junansu,wanda sunyi nisa cikin wata duniya ta daban,
MAMMY ta shigo lokacinma ko AL'AMEEN ta shigo kawo mata shima ranan akasi aka samu yayi bacci ya tashi dan ko gurinta ya koma kwana,salati tasa wanda ya jawo hankalinsu,cike da tsananin kunya JIDDAH ta k'udundune cikin bargo,shiko ficewa yayi yana sauke kai yak'i yadda su had'a ido..
Ajiye mata shi tayi ta fice bata ce komaiba,sai da ta tabbatar ta fita sannan ta tashi ta d'auke shi,yaro yayi k'ato da shi,gwanin sha'awa,ta gama bashi abincin tasa shi a kafad'anta har yayi gyatsa,ci gaba tayi da jijjigashi har bacci ya d'aukeshi,aiko ta kwantar da shi tana kallonsa,sam ranar tak'i mai dashi gurin MAMMY k'arshe a gurinta ya kwana,ranan kam YAH BOSS tun da ya fice bai dawo ba,direct gidansu da tun ranar da jiddah ta baro shi,shima bai k'ara kwana cikinsa ba,sai dai yaje ya duba ya fito,gyara yasa akayi sosai an kwashe komai an sauya gidan ya koma uwa sabo saboda gyaran da ya sha...
Shi kad'ai idan ya kalli gyaran da akayi sai yayi mirmushi,yana ayyanawa a ransa,gobe zai kasance da HAYATEEYNSA babu abunda zai k'ara rabasu.Haka ya wuni shi kad'ai sai tunani yake,k'arshe sai nan ya kwana saboda kunya yake ya koma gida su had'u da MAMMY,duk kewarta ta cika masa ko ina na jikinsa..
Aiko babu shiri MAMMY ta tattara kayansu washe gari,tun da safe ta rattabawa JABEER en kira, ''Maza rasai kazo ka kwashe matarka da d'anka kubarmin gida,ina nan ina jiranka''....
Ta kashe wayan...
Ko minti ashirin bata yiba,sai gashi cikin wata dakakkiyar shaddarsa sai k'amshi yake bazawa,yana ta uban murmushi.Sam yak'i yarda su had'a ido da MAMMY..
Haka MAMMY ta sallamesu ta kuma had'asu da mai rainon AL'AMIN en suka k'ara gaba,cike da d'oki suke tafiya,ko kulawa da mai rainon ba suyiba suke ta harkokin gabansu har suka k'arasa gida,haka suka ci gaba da kula da AL'AMIN cikin so da k'auna.
*ONE YEAR LEAP.*
Haihuwan AL'AMIN da shekara d'aya,bakin CONVOCCATION ARENA dake cikin BAYERO UNIVERSITY KANO cike gurin yake da dandazon mutane tamkar ranar idi,hakan ya ganar dani taron yaye d'alibai ake...
Cikin GRADUATION GOWN blue da ratsin purple a wuyansu suka fito,fuskokinsu na nuna tsantsan farin ciki,nufo gurin da y'an uwa da abokan arziki suka yi kowacce fuskarta kar da annashuwa...
Anyi taro lafiya an watse lapia kowa ya d'auka hanyan gida cike da murnan wannan rana mai cike da tarihi mara misaltuwa...
Shekaran AL'AMIN d'aya da watanni uku,wanda yayi dai² watanni uku da kammala karatunsu har sunje CAMP sun fito,inda DADDY ya shiga ya fita aka barsu a nan cikin kano,nan JIDDAH ta soma sabon laulayi,bata wani tashi hankalintaba,coz tasan yadda yake da k'aunar yara,hakan yasa taitunanin babu wata hanya da zata kyautata masa sama da cika masa gidan da yara....
Shiko YAH BOSS ko da ya gane tana d'auke da juna biyu murna yaita yi abunsa,data sanar da shi kuwa nan taga tsantsar murna ganin yanda yake farin ciki,itama ta shiga tayashi,ta kuma ci gaba da rainon cikin jikinta,take ko YAH BOSS yasa ta yaye AL'AMIN ya maida shi gurin MAMMY duk da dama ya saba da ita sosai,kuma ba wani yini a gidan ba...
Zuwa wannan lokacin ko HUBBEEY ta haihu da d'anta namiji mai kama ABBANSA,k'ato da shi uwa d'an turawa mai sunan ABBAN HUBBEEY suna ce masa AYMAN....
Rayuwarsu mai cike da tsabta haka lokaci yaci gaba wucewa cike da nasarori ta ko wane b'angare,ko wane gida idan zaka shiga sai rayuwarsu ta baka sha'awa saboda yanda suke gudanar da rayuwarsu cike da so da kuma girmama juna,abun gwanin da tsabta.......
*SOME MONTHS LEAP.*
Zaune take da cikinta da ya soma tsufa,wayanta tayi k'ara,sunan LITTLE ta gani yana lilo akai wacce a yanzu ta zama BIG MAMA..
''Hellooo MAMAN UKU''
''Ke rufan asiri d'ayan ma na iya saukewa bare har kikemin fatan uku,ya baby ZAHRA?''
''Kinganta tana ta faman jan wayanma wai sai na bata ta miki magana''
''Allah sarki babyna,ina kewanki''
''Uhmm!nace anjima zamu zofa kinsan zamu je gida kan kayan IKRAM da za a kawo ko?''
''Eehhh! haka ne amma sai YAH BOSS ya dawo''
Karaf a kunnensa lokacin yana shigowa ya dawo daga aiki a gajiye,wani murmushi yayi yana k'arasowa kusa da ita...
Maganarsa kad'ai taji,dan bata ji shigowarsa ba,dai² tana ajiye wayan taji muryarsa yana fad'in ''Ke da wa kike waya?''
''Har d'an tsoro ya bata,ta juya tana kallonsa,harfa ka bani tsoro''
''Eyyeerrrhh!sorry HAYATEEY''
''Ammm! YAYANAH anjimafa zamu gidan MAMMY ina fatan baka mantaba?''
Ummm!
Har ya juya ya dawo
''HAYATEEY yau kam sai kin fad'amin waye YAH BOSS ennan,na jima inajin kuna fad'a,idan na tambaya amin wayo,to yau kam babu wani wayo da zakimin sai naji''
''Pardon HABEEBEY,Allah bansan me zan ce maka ba''
''Akan wannan en ne baki sani ba?tambaya nefa kawai ehh ne ko a'a fa kawai''
''Ni dai Allah ban san me zan ce maka ba''
''It's ok'' ya furta yana d'aukan wayanta,kiran da ta amsa last ya bi yasa a handsfree..
''Hello madam ta YAH BOSS sha alwashi''..
Bata k'arasaba ya katse kiran,dan ko ya gama fahimtar ko waye mamallakin sunan,juyowa ya kalleta yana murmushi
''No more hidden again''
A d'an tsorace ta d'ago ta kalle shi,ganin irin kallon da yake mata,da kuma murmushin dake kan fuskarsa yasa ta yi wata sanyayyar ajiyar zuciya...
Gefen bed en ya zauna yana kallonta,har lokacin ta kasa magana,kansa ya d'ora akan k'afafunta da suke mik'e,cikinta ya dad'a girma,uwa wacce za ta haifi yan uku....
''HAYATEEY wato ni nema BOSS koh?''
''Allah YAYANAH''......
Shiiiiiiiii
Ya d'ora hannunsa kan lips enta,''ban son jin komai''
''Da gaske?''
Da murnarta tayi maganar tana kallonsa,kai ya kad'a mata yana lumshe ido uwa mai jin bacci..
Cikin kansa ta nutsa yatsunta ta shiga sosa masa suman kansa,shiko ya dad'a gyara kwanciyansa a jikinta...
''HABEEBEY bacci kuma za kayi?''
''Eehhh HAYATEEY,amma ba jimawa zanba''
''Ok tamm!''
Har tayi shiru kuma ta furta
''Ammmm!HABEEBEY kasan mesa muke ce maka YAH BOSS?''
Tana y'ar dariya tayi maganar...
'Dagowa yayi yana juyowa
''Sai kin fad'amin yanzun,duk da farko banso tambayar dalilinba,coz naga kin tsorata,amma tunda kinyi niyya oyaah tell me''
''Allah HABEEBEY koh yanda kake had'e fuska da har tsoron mu had'u nake,barinma ace ni kad'ai,uhmmmmm nafa jima ina tsoronka''
''Me yasa HAYATEEY?''
''Yanda kake tsare gida ina mutum ya isa yayi wani k'wak'wk'waran motsima,shi yasa fa muke ce maka YAH BOSS,coz baka son raini''....
Dariya yayi mai isarsa,sannan ya kalleta
''To ae HAYATEEY kinma bawa kanki amsa kinga ni raini ne bana so,amma yanzun ae kin san waye ni ko?''
Ya tambaya yana mata winking...
Dariya tasa kafin ta ce ''Sosai ma kuwa,ai sai dai na bada labari''
''Uhmmmm! HAYATEEY kenan wai tsorona kike,kamar wani dodo''
''Yo HABEEBEY ae kai en ne lokacin fa ko dariya bakayi a gabanmu,ko saboda mene ohooo!''
Dai² kunnenta ya kai bakinsa,''kin fa riga kin san dalilin raini ne bana so''
Tab'e baki tayi,''ni fa har yanzun ban daina jin tsoronka ba''
''Da gaske?''
''Ehhh!mana''
''Me ya janyo hakan to ?''
Kamar mai tunani ta d'an karkace kai gefe,kafin ta kalleshi idanunta har sun fara canza colour
''HABEEBEY za ka iya tuna wata rana da wata yarinya ta zuba maka ruwa,a bakin wani eatry?''
Kallonta kad'ai ya shiga yi,yayin da k'wak'walwarsa ta tafi aikin tunanin wannan al'amarin,ko kafin ya kai ga yin magana ta katse shi da fad'in
''Ni ce dai wannan yarinyar da nake cikin daud'a da rashin gata,ni ce wannan yarinyar da ta watsa maka ruwa a rashin sani,ni ce kuma wannan yarinyar da ka fidda hannu ka tsinkawa mari,a dai² lokacin da nake neman d'auki''......
Kuka ne ya ci k'arfinta,maganar na rabewa,ita kuma tana ci gaba da k'ok'arin magana..
Da sauri ya janyota jikinsa,yana mai rufe mata baki da hannu...
Hannunsa ta zare daga bakinta tana goge fuskarta,''Tun a wannan ranar tsoronka ya shigeni sai ina ganin kamar ko wane lokaci zaka kumamin abunda yafi na had'uwarmu ta farko,duk da k'arancin shekaruna,sai dai kuma daga baya ka sauya min tunani na,ta hanyar nunamin k'auna wacce ban tab'a tsammaniba''
Ta d'an dakata tana murmushi,murmushin shima yayi duk da kuwa magaganunta sun sa yaji jikinsa yayi sanyi,lallai dole ne sai ya dad'a jajircewa ta inda zai mantar da ita wannan tunanin,dad'a k'ank'ameta yayi,a kunnenta ya shiga fad'a mata kalamai masu sanyaya zuciya duk dan ya mantar da ita maganar da ta d'auko masa....
''Na gode HABEEBEY da nunamin tsantsar k'aunar da ban tab'a tunanin samunta daga kowa ba,Allah ya biyaku da mafificin sakamako''
''Ameen HAYATEEYNA''
''Amma ban son wannan maganar kinji?ko dan halin da kike ciki,ba a son mace mai ciki da damuwa,kin fahimta?''
Kai ta kad'a masa
Kallon juna suka tsaya yi na wani lokaci,kafin ya dad'a matsowa,cikin kunnenta ya rad'a mata
''HAYATEEY barin miki gyara yanzun''
Tana dariya ta furta
''Allah ko HABEEBEY na yafe gyarankan nan,coz duk lokacin da za kamin gyara nasan k'arshe result en baya wuce''.........
Saurin toshe nata baki yayi,yana mata dariya
''Aifa kam HAYATEEY sai nayi gyaran nan''
''Ni dai kam na yafe gyaran nan naka''
Sai narke fuska take
Cike da shagwab'a shima ya furta
''Uhmmm uhmmm nifa sai nayi''
K'ok'arin ture kansa gefe tayi,shi ko sai dad'a matsowa yake,suna ta dariya abunsu,da haka har ya samu yayi winning akanta,inda labari ya canja salo suka lula cikin duniyar MARS...................
_Sai kuma fatan Allah ya sauketa lafiya............_
*ALHAMDULILLAH!*
*ALHAMDULILLAH!!*
*ALHAMDULILLAH!!!*
_Anan na kawo k'arshen wannan novel na *RAYUWAR WANI* inda nayi kuskure ubangiji ya yafemin,inda kuma nayi dai² ubangiji ya had'amu a ladan...._
_Sai kuma mun had'u a cigaban novel ena da na riga na fara wato *Y'AR GARUWA* da yardar Allah,ina muku fatan alkhairi masoya a duk inda kuke cikin duniyar nan,Allah ya sadamu da alkhairinsa....Ameeen._
_Masoya ina sanar daku littafi na sisterna mai sunan *AUREN ALJANA* da zai fito nan bada jimawa ba,kada ku sake a baku labari........._
*AUREN ALJANA*
_Kada ku manta sunan_ 👇👇👇
*AUREN ALJANA!*
*AUREN ALJANA!!*
*AUREN ALJANA!!!*
_NA MARUBUCIYAR ZAMANI_
*HABIBA IDREES (HUBBEEY)*
*AUREN ALJANA!!!!*
_Zai zo muku bayan sallah idan Allah ya nuna mana,da rai da lafiya......_
*FOR CORRECTION OR COMMENTS JUST CONTACT ME*
*@ 08125527472*
_Taku har kullum nake muku fatan alkhairi *REAL SMASHER*_....
*_~TEAM J²~_*
*_REAL SMASHER._*🤞🏻😘