Dukkansu suka gyada mata kai sannan suka shiga cikin dakin,
Babban dakine, wanda yake cike da majinyata
A gefen kofan dakin an kafe abun kashe gobara
An bi bangon dakin an lillika hotunan sassan jikin dan adam
.
Babu wani sauti dake tashi a cikin dakin in ba na nishin majin yata, da kuma sautin kukan masu kula da su ba
.
Duk tsananin rashin tausayin mutun muddin yayi duba ga wayannan mutane sai yaji wani abu ya darsu mai a zuciya
Wani daga cikin majinyatan barin kansa ne ya fafe, likitoci sun yi kokari ganin sun dinke masa
.
hawayene kadai ke kwaranya akan kumatunsa
Abdullahi bai san lokacin da shima ya fara zubar da kwalla ba sakamakon ganin halin da mutanen suke ciki,
"Mutum ba zai taba sanin cewa duniya ba komai bane face wata karamar gida a gareshi wacce take cike da kayan alatu masu janyo hankulan sa ga barin aikin Allah , shi isa manzon Allah SAW yake cewa mu yawaita ziyarar marasa lafiya,
"
Abdullahi ne yake zancen zuci
Suka karisa wajen da aka kwantar da mujahid
.
Ga wanda yasan ustazu mujahid indai aka nuna masa shi ayanzu bazai taba yarda cewa shine ba
Ustazu mujahid daya kasance mutum kakkaura mai wadataccen haske, amma yanzu ya koma yankwanne fuskarsa tayi duhu, ya rame sosai ta yadda kasusuwan jikinsa suka fito fili
Yana kwance akan gadon asibitin baya iya numfashin kirki,
Gaba dayan jikinsa ya yankwane
.
Abdullahi ya dafa hannunsa yace
"In Allah ya yarda mujahid zaka samu sauki"
Mama hafsa ta zauna a wani kujera dayake fuskantar gadon da mujahid yake kai tace "ameen"
.
Abdullahi ya dubi mama hafsa yace "mama"
"Na'am" tace tana dubansa
"tun yaushene ya fara wannan ciwo"
Abdullahi ya tambaya
Mama hafsa ta dukar da kanta kas tace "ni kaina ban san lokacin da wannan ciwo yakama shi ba, tun lokacin da ka tafi KANO sai ya kasance ya dena fita ko'ina kullum yana kulle cikin daki
Hatta makaranta ya dena tafiya izan na tambayesa ko me ke damunsa sai yace dani zazzabi ne babu yadda banyi da shi ba akan muzo asibiti amma yaki
,
Iyaka saide na sayo mashi magungunan zazzabi na kawo mai,
Tun waccan satin na fara lura da yanayin jikinsa yadda ya rame ya koma kamar ba shi ba shi isa na takurasa sai yab fadamani abun da ke damunsa ,
Muna cikin hakanne sai kuma Allah ya kawo ka"
.
Abdullahi ya jinjina kai yace "Allah ya bashi sauki,"
,
Wata nurse ce ta tunkaro su tana sanye da uniform din da aka kayyade ma nurse,
Tana isowa wajensu tace "sannun ku"
"Yauwa sannu dai" Abdullahi ya amsa
"Kune ku ka kawo wannan majinyacin"
Ta fada tana nuna mujahid wandaa yake kwance yana barci
"Eh mune muka kawo shi" Abdullahi ya fada
"Likitan daya dubashi yace yana son ganin ku yanzu " nurse din ta fada
Abdullahi yace "a ina likitan yake"
"Biyone na kai ka"
Nurse din ta fada batare da ta tsaya jIn mai zai kara cewa ba ta juya ta fice daga dakin
Abdullahi ya juya ya dubi mama hafsa yace mata "mama ki jira bari naje naji ko menene"
Ta gyada masa kai
Cikin sauri Abdullahi yabi bayan Nurse din,
.
Wani bangare suka bi sannan Nurse din ta tsaya a gaban wani ofishi
Ta juyo ta dubi Abdullahi "wannan shine ofishin likitan yana ciki "
"Nagode yar uwa" Abdullahi ya fada yana kallon nurse din
Yai sallama tare da murda hannun kofan, sannan ya shiga
Babban ofishine mai madaidaicin fadi, ofishin na dauke da tangamemen teburin gilashi wanda ya kusan cinye rabin ofishin, kalandun sassan jikin dana adam da hotunan kiwon lafiya sune a mammane a bangon ofishin,
Likitan wanda ya kasance Dogo launin tarwada yana sanye da riga T shirt da wandon jeans ya dora farin lab coat a kan rigan , sannan ya rataya magwajin numfashi a wuyansa ya dubi Abdullahi ya ce mai "maraba da zuwa ga wuri zauna"
Ya nuna daya daga cikin kujeru biyun da ke gaban teburin gilashin da tai masu iyaka
,
Abdullahi ya zauna sannan yace "likita ni dan uwan majinyacin daka ce kana bukatar wanda suka kawosa ne,"
"Ok, menene Sunan ka"
Likitan ya tambaya
"Sunana Abdullahi"
Abdullahi yabashi amsa
"Abdullahi a gaskiya munyi wa majinyacin ku gwaji test ga sakamakon da gwajin ya bayar"
Likitan ya fadi yana mai miko wa abdullahi wasu takardu
Abdullahi yasa hannu ya karba yana mai dudduba wa
Lokaci daya fuskarsa ta canja kala, alamun razana suka bayyana a akan fuskarsa cikin jan numfashi Abdullahi yace "kanjamau! Karyane wallahi, taya ma za'ace mujahid yana da Aids, mutumin da ba ruwansa da kowa baya shigan harkan mata,"
Ya dubi likitan yace "likita inajin kayi kuskure wajen bani result dinnan, kila result din wani kabani bana dan uwana ba"
.
Likitan yayi murmushi yace "ka kwantar da hankalinka wannan result din dan uwanka ne, shi yasa ma kaga nace a kirawo min kai don bana son na fada maku hankalin mahaifiyarku ya tashi, kuma ciwon yaci jikinsa sosai, dun ybamu da tabbacin ko zai iya rayuwa"
.
RUDIN SHAIDAN
Gajeran labari
Marubuci
Shuraih Usman
© Shuraih 99% - 2018
Part 7
Karshe
.
Likitan yayi murmushi yace "ka kwantar da hankalinka wannan result din dan uwanka ne, shi yasa ma kaga nace a kirawo min kai don bana son na fada maku hankalin mahaifiyarku ya tashi, kuma ciwon yaci jikinsa sosai, dun bamu da tabbacin ko zai iya rayuwa"
.
"Inna lillahi wa inna ilaihirra ji'uun"
Kalmar da Abdullahi ya runga fada kenan
Bai jira cewan likitan ba ya mike tsaye ya nufi kofan dakin,
.
Kai tsaye ya nufi dakin da aka kwantar da mujahid yana zuwa ya iske mujahid ya farka saide da gani kasan yana cikin mayuwayacin hali duba ga yadda yake ta faman son yai magana amma ya kasa
.
Abdullahi ya dafa kafadarrsa kwalla na gangarowa daga idanunsa yace "kar ka damu abokina Allah zai baka sauki, amma ni nasan wannan ba yin kanka bane, babu tayadda za'ai ka aikata hakan, don ba dabi'arka bace"
,
Mama hafsa ta dubi Abdullahi "me likitan yace ma ka,"
Abdullahi yace " ba komi mama "
Mujahid ya kalli mahaifiyarsa bakinsa sai murkususu yake, alaman yana son ya fadi wani abun,
Ganin haka yasa Abdullahi ya karkato kansa gareshi ya fara biya masa kalman shahada,
Jin abdullahi ya na biya masa kalman shahada yasa mama hafsa ta fara kuka, don tasan cewa shi kenan dan data mallaka daya tilo zai tafi, tafiyan da bazai sake dawowa ba,
,
Duk yadda Abdullahi yaso mujahid ya yi kalman shahada amma abu gagara a haka har Allah ya karfi ransa batare da ya biya kalman shahada ba
,
Sosai Abdullahi ya girigiza da wannan lamari
Lokacin daya ga bakin mujahid ya tsaya ga yin kakkarwar dayake, jikinsa yayi sanyi
Ya sanya tafin hannunsa ya rufe masa idanuwa yana mai cewa "Allah ya jikanka abokina"
.
**********
Ahalin garin keffi da kewayanta sun yi jimami sosai na rashin, dan uwa,amini kuma malaminsu da sukai, wanda yake kokari sosai don ganin ya gyara halayensu
,
Allah ya jikansa yai masa rahma ,
Ai mujahid mutumin kirki ne
"Ayya yaron kirki' Allah ya jikansa"
"Malam mujahid , Allah yai masa Rahma"
.
Addu'o'I da fata nagari wanda mutane da dama suke mai kenan,
Wanda ko kokwanto basa yi Aljanna itace makomar mujahid
******
.
"Nan kuma ina ne , me nake anan"
Mujahid ne yake fadin haka lokacin daya tsinci kansa a cikin wata iriyar duniya mai tsananin duhu,
Ihu da ifacen jama'a su kadai kunnuwa ke iya saurara,
Cikin firgici mujahid ya fara waige waige yana kallon wajen fuskarsa cike da Al'ajabi
,
Babban filine shimfide fetal, ko'ina ka duba a cikin filin mutane ne maza da mata Tsirara haihuwar uwarsu,
Mutanen suna kuka da idanuwansu yayin da wasu bakaken halittu ke gana masu Azaba
,
Wani bakin haske ya bayyana a gaban Mujahid a hankali hasken sai kara yawa yakeyi yana dunkulewa waje guda, wata kakkausar muryace ta fito daga cikin hasken ta yace "sannu da zuwa bil'adama, wanda ya kasance mai sabon ubangijinsa, ina yimaka albishir da tarin Azabobi kala kala"
,
Mujahid ya tsorata ainun da jin wannan zance duk da bai ga mai maganar ba yace
"Ta yaya akayi na zamo mai sabo, ni da dukkan rayuwata na gina tane akan turban gaskiya,
Ni da na kasance a kullum ina bautan Allah ba dare ba Rana,
na kasance A kullum sai nayi tsayuwan dare, babu satin da bana Azumin lada,i na kyautatawa iyayena, ina bin umarninsu,ban taba aikata wani Sabo ba, ina kyautata Sallah ta, da dukkan Aiyukana, ban taba yin wani Abu don Riya ba, ina kyautata zamantakewana da Al'umma , a iya sanina laifi daya ne na taba aikatawa a ban kasa "
,
Mujahid yayi shiru ga barin magana a daidai lokacin da kakkausar muryan ta sake fadin "wannan laifi da ka aikata shine babban kuskurenka a duniya, Manzon Allah yace a cikin ku bil'adama akwai wata Tsoka izan tsokar nan ta baci toh dukkan jikinku ta baci, haka izan tsokarnan ta gyaru to ba shakka dukkan jikinku ta gyaru, wannan tsokar itace zuciya,
amma kai sai ka biyewa Son Zuciyarka ka aikata mafi munin alfasha, wanda ya bata dukkan wasu kyawawan aiyukan ka na baya,
Ka kasance kana aikata aiyuka masu kyau, kana Sallah akan lokaci, kana Azumtar watan Ramadan, Qiyamul laili ,da sauran ibadu duk kana yi,
Amma daga karshe sai ya kasance ka maye gurbin kyawawan ayyukanka da mummunan Alfasha wacce Allah yai Hani da ita, ka biyewa son zuciyarka har shaidan ya samu Nasara akanka toh yanzu zaka tarar da makomarka"
.
Muryan na gama fadin haka, sai wannan bakin hayakin ya bace bat
Alokaci daya sai kunnuwan mujahid suka tsinkayo mashi wani Kara da rugugi ,
Cikin sauri ya daga kansa sama don ganin me ke wannan rugugin, jin rugugin ta sama yake zuwa
,
Mulmulallun manyan dutsuna ne,suke saukowa daga sararin samaniya wani abun mamaki dayake tattare da dutsunan shine Wutar dake ci a jikinsu
.
Mujahid ya fara neman taimako ganin cewa dutsunan kasa suke yiwowa
"Ataimakeni, dan Allah wani ya taimaka ma....."
Maganarsa ta katse lokacin da wata katuwar dutsen wuta ta kusanto kokon kansa,
Wani radadime da zafi ya ziyarci kwanyansa alokaci guda kafin ya sanya hannunsa ya kare a daidai lokacinne dutsen ya sauko a kan mujahid
"Ataimakeni"
"Ataimakeni
"Ataimakeni"
Mujahid ya farka firgigit daga nannauyan baccin data shammaceshi tun shigowarsa cikin ofishin
,
Ya daga kai ya na kallon inda yake
Cikin ofishinsa ne na makarantan Mu'azu bin jabal yana zaune akan kujera ga tarin tulin littafai da takardu a gabansa,
Fuskarsa dauke da alamun firgici, a fili mujahid ya furta"inna lillahi wa inna ilaihi rra ji'un"
.
Sai ayanzu hankalinsa ya kwanta daya fahimci ashe mafarki yake, ya daga hannunsa sama yace "ya 'Allah na rokeka kada ka sanya wannan mummunan mafarkin dana yi ta zama gaskiya, ni ina cikin bayinka salihai kuma da yardan ka zan kasance a cikinsu har izuwa mutuwana, mata, kudi da sauran kawan Duniya baza su taba janyo mani ra'ayina ko su sayi imani na ba ya Allah ka kare ni daga sharrin Shaidan, don kuwa babu dan adam din daya tseracewa RUDIN SHAIDAN a rayuwa"
.
Azuciyarsa kuwa yana jin tsanar mace na darsuwa ainun,
Tarin farin ciki ne ya ziyarci zuciyarsa yayi hamdala daya tuna cewa duk wannan dogon Al'amarin rayuwan mafarkine
.
Kofan ofishin ya bude
Kyakyawan matashi, ya shigo a guje ko sallama babu, cikin dimuwa ya dubi mujahid yace "lafiya mujahid naji kana neman agaji"
"Lafiya abdullahi, wani Mugun mafarki ne nayi wanda ya firgitani ainun "
Mujahid ya fada
Abdullahi ya sauke ajiyan zuciya "nagode Allah, Ai na zata ko wani abun ne ya faru,"
Sai a sannan mujahid ya lura da hannun Abdullahi inda yaga wata fankaceciyar shebur din kwashe shara,
"Me kuma zakai da cebur "
Abdullahi yayi murmushi yace " na sanka daa tsoron kadangaru, shi isa kaga na zo da shi koda ya kasance kadangare ne ya tsorata ka"
"Assha kadangare sai yasanya ni rafka wannan ihu" mujahid ya fada yana kokarin harharda wasu takardu da suke kan tebur din
Abdullahi ya juya zai futa har ya kai bakin kofa sai ya juyo ya dubi mujahid yace "au na manta ma ban fada maka ba, wata budurwa tana can a waje wai wajenka tazo,"
,
Mujahid ya tsaya da harharda takardun yace "budurwa kuma, wacece ita"
"Bansanta ba amma yadda na lura da yanayinta tana cikin wani hali na rayuwa, don kuwa kuka take yi, ta dai ce min wai dakwai wani batun da take son ku tattauna da ita"
,
Zuciyan mujahid ta buga da karfi
"Uztaz gaskiya yana da kyau mu samu wajen zama domin
kuwa , dogon zance ne zamuyi, don bazan taba
runtsawa ba muddin ban fadi maka ba"
Mujahid ya tuna kalaman Rufaida a mafarkinsa da irin yanayin daya ganta,
Alamun firgici suka bayyana karara a fuskarsa cikin in ina yace "ba,ba,bbb ta fada mmmm ka sunan ta ba"
,
"Ta ce dani sunan ta RUFAIDA wai daga LAFIYA tazo musamman don ta gana dakai"
Abdullahi ya fada cikin kokonto
,
Cak dukkan wasu sinadaran kuzarin jikin mujahid suka tsaya ga barin aiki, zuciyarsa ta fara bugawa sau uku a dakika daya,
Akalla sai da ya samu kansa a cikin wannan yanayi na dakiku 30 kafin ya mike cikin kuzari yace
"RUFAIDA !"
Abdullahi ya dubeshi shekeke yace "ko kasanta ne"
"A'a bansanta ba Amma na wayeta a MAFARKI"
Mujahid ya bashi amsa
"Kaman yaya ka wayeta a mafarki"
Abdullahi ya sakee tambaya
"Dogon labarine zan fada maka anjima amma yanzu kaje ka sanar da ita cewa ba nanan"
.
****
Minti daya kenan da fitan Abdullahi daga ofishin dukda sassanyar iskar da fankar ofishin ke badawa hakan bai hana mujahid jikewa da gumi ba zuciyansa sai bugawa take,
,
Ya tashi ya fito daga ofishin ya nufi bakin gate din makarantar adaidai wajen wani katanga ya tsaya ya leko da kansa, yadda ya leko din sai ya fi kama da BARAWO yayin dayaje SATA
,
Ya hango Rufaida a tsaye da Abdullahi yana koramata bayanai,
Ya dafe kirjinsa sakamakon ji dayake tamkar kirjin zai fashe,
"Inna lillahi wa inna ilai hirra ji'uun"
Ya furta
Shakka babu ya gane fuskar rufaida ta mafarkinsa wannan fuskar bazai taba mancewa da ita ba har karshen Rayuwarsa
********
Abdullahi da mujahid suna tafe cikin makaranta sun dumfari sashin ofis din Abdullahi, mujahid ya na baiwa Abdullahi labarin mafarkin sa na jiya da kuma yadda mafarkin yake so ya zama gaskiya,
"Allah ya karemu daga RUDIN SHAIDAN"
Abdullahi yafada bayan ya gama sauraren labarin mafarkin mujahid yace Ameen
,
Suka dunguma dukkansu suka shige cikin ofishin
********
"Kwan kwan kwannn kwann"
"Waye wannan"mujahid ya fada daidai lokacin ya fito bayin dake cikin dakinsa yana sanye da jallabiya ya dau makulli ya nufi kofan dakin ya bude,
Mujahid ya dubi karamin yaron da bazai wuce shekara goma sha biyu ba yana tsaye a kofan dakinsa yace "nasir ya akayine"
Yaron da aka kira da nasir din yace "yaya wata mata ce a waje wai sunanta RUFAIDA, wai tana neman ka"
,
Duniyarce ta fara juyawa mujahid da sauri ya dafe kansa yace ma nasir "kace mata bana nan"
"Toh yaya"
Yaron ya juya da gudu ya nufi waje
Mujahid ya dawo cikin dakinsa ya zauna yata tunane tunane,
Kome ya tuno oho, sai ya mike zumbur ya fara hada kayayyakinsa a cikin jaka ,
Cikin kankanin lokaci yashirya cikin fararen Jampa, ya dau jakarsa ya rataya da sauri ya fice daga cikin dakin,
Ya futo kofan gidansu , babu kowa a layin sai yara da ke ta wasannin su ya yafuto kaninsa da hannu, da gudu kanin nasa yazo
Mujahid yace mai "kaje umma na kiranka"
"Toh? Amma yaya zakaje inane"
Nasir ya tambaya
"Kaduna zan tafi" mujahid ya bashi amsa
"Yaya in zaka dawo ka kawo min tsaraba"
"In Allah yayarda, kuma banda rashin ji"
,
Kai tsaye Tasha mujahid ya nufa yana zuwa ya hau motar KADUNA
........
ALHAMDULILLAH
.
Anan na kawo karshe wannan gajeran labarin nawa
Dafatan ya fadakar kuma ya wa'aza