Ya riga yai nisa cikin tunani lokacin da ta shigo sai da ta kira shi sannan ya ɗago ido ya kalleta. Farin idon sa ya koma ja saboda rashin bacci da damuwa.
"Noory" ta sake kira da murya mai jan hankali
"Leave" ya daka ma ta tsawa.
Ba ta damu da abinda ya ce ba, ta samu kujera ta zauna.
"I'm here to stay Noory" ta faɗa tana ƙanƙanta ido kamar za ta yi kuka.
A da wannan muryan yana raunata shi, a da wannan murya yana ratsa duk jikin sa ya bi kowanni jijiya na jikin sa, a da wannan murya yana sa shi jin wani farin ciki mai wuyar bayyanawa.
"Look, ban san mi ya dawo da ke ba, kuma ba na so na sani, ko ma minene ina so ki sani cewa you're not welcome"
(Maganansu ingautsan Larabci da turanci su ke. And ni kuma😁)
"Noory listen to me please, i love you, i still do"
"Get out"
"Noor..."
"Get out of here"
Ta san za a yi haka shi ya sa ta zo da shirin ta.
"Ba za ka iya korata ba"
Kallon mamaki ya ma ta at the same time sai maganan ta yai kama da abinda Farida za ta ce.
"Ina da 6% shares a kamfanin nan"
"6%" ya maimaita sannan ya sa dariya, tsayawa yai da dariyan lokacin da ta ce *"SABNAJ Inc."*
Farkon buɗe kamfanin sa kafin ta gama zama da ƙafarta, ya saida kaso ashirin da biyar a matsayin hannun jari ciki kuwa har da Sabnaj inc. Ya tuna lokacin kamfanin ta so siyan kaso shabiyar ne amma ya ƙi, daga baya aka koma kaso goma har kuma daga ƙarshe aka tsaida matsaya akan kaso shida. Abinda ya sani shine Sabnaj inc wata kamfani ce a ƙasar America.
"Yes Najeeb, i owned sabnaj"
"SABNAJ" ya furta a hankali. Sunan da su ka shirya sa wa kamfanin sa kenan kafin komai ya wargaje tsakanin sa da Sabreen.
"Sab for Sabreen and Naj for Najeeb. Do you still remember?"
Ta ya bai yi wani ƙwaƙwƙwaran bincike ba a lokacin har ya sayar da shares ɗin kamfanin sa ga Sabreen. Ko lokacin da kamfanin Sabnaj ta zo neman saka hannun jari bai yi niyyar karɓan su ba saboda yadda sunan kamfanin ya ke. Anas shi ya convincing ɗin sa akan ya amince mu su.
"Ina son na yi aiki a nan Noory, ina so na yi aiki kusa da kai. Na ɗau hutun acting na shekara biyu just to be with you. Na san kamfanin ka ta samu koma baya cikin watannin nan, i'm here to help"
"Nawa za ki sayar da shares ɗin ki?" Ya faɗa with serious face
"Ba zan sayar ba, i want to be with you"
"Miss Sabreen. Welcome to Najeeb constructions then"
"What!"
Murmushin yaƙe yai tareda sa hannun sa a haɓarsa ya furzar da iska a hankali ya ce " duk abinda ki ke tunanin samu a wajena ba za ki samu ba, nonetheless, i'm going to buy your shares. Now leave my office"
Murmushi ta yi ta ce " I'm going to fight for us Noory"
Tana tashi za ta fita ita kuma Farida ta shigo. Kallon-kallon su ka tsaya yiwa junan su. Kafin Sabreen ta janye kallon ta hanyar saka baƙin glass ɗinta ta fice daga office ɗin.
Farida ta ce "kurwata kur mayya"
Ƙarasawa wajen Najeeb ta yi wanda ke waya da Anas yana surfa ma sa masifa, dama tunda ya zo ba su haɗu ba. Yana ajiye wayan Farida ta ce "Sir Najeeb, wannan list ɗin da ka ce na yi akwai sunayen da ba su yi dai-dai da na cikin database ɗin ba ya za ayi?"
"Just do it anyhow?" Ya daka ma ta tsawa.
Jikinta ne yai sanyi, Najeeb ɗin da ta sani ba zai yi tsawa dan ɗan wannan abin ba.
"Sir Najeeb saboda Sabreen shine za ka min tsawa" ta faɗa a hankali
"Get out Mrs Jibo"
Wannan karan da ƙarfinta ta ce " Ba zan fita ba, ba zan fita ɗin ba. Ka gaya min matsayina? yanzu da wannan karuwar ta ka ta dawo, miye matsayina?"
Ɗago ido yai ya kalleta amma baice komai ba.
"Banda matsayi ko?, banda matsayin da ya wuce matsayin Sakatariyar ka ko?"
"Wanni matsayin ki ke so bayan wannan?" Ya maida ma ta martani.
"Amm..." sai kuma ta fasa maganar da za ta yi ta ce "na gode"
Juyawar da za ta yi ta ga Anas yana tsaye a wajen. Sauri ta yi ta bar office ɗin.
"Kai wanni irin mutum ne Najeeb, Farida matar ka ce fa yanzu"
"Sabreen ita ke da kamfanin SABNAJ"
"Wanni Sabnaj ɗin?"
"Kasan sarai abinda na ke nufi, also Sabreen wants to work here"
"shegiyar kuma ta nan ta biyo?"
" ba na son ganin Sabreen Anas"
"Its simple, ka siye shares ɗinta"
"Ta ƙi"
"Ka bar batun wannan, Najeeb yadda na sameku da Farida kwata-kwata bai dace ba. Kar ka manta matar ka ce fa"
"Matar da Dad ya sa dole na aura ba"
Anas ya harareshi ya ce "Matar da ka rusa shirin aurenta ba. I know you love her Najeeb, kar ka yi wasa da damar ka"
"Stop this nonsense Anas, ka san har yanzu ban yafe ma ka abinda ka yi ranan saturday ba"
"Ni dai na gaya ma ka" daga haka ya fita.
Samun Farida yai ta kwantar da kan ta a kan table tana hawaye.
"Farida" ya kira sunan ta a hankali.
Ta yi saurin ɗagowa tana goge hawayen.
"Dan Allah ki yi haƙuri"
Murmushin yaƙe ta yi ta ce " ba komai Ya Anas, ni dai abu ɗaya na ke buƙata a wajen ka"
Zama yai a kujera dan ya saurareta da kyau.
"Sharrin da aka min a wannan kamfani har ya sa Sir Najeeb ya ke ganin baƙina, ina so na wanke kai na ko ta halin ƙaƙa. After that, zan bar aiki a nan"
"I'm sorry 'yar uwa na ce zan sake bin bahasin case ɗin, abubuwa su ka shamin kai ban yi ba. But Insha Allah zan yi"
"Na gode"
"Farida" ya sake kiran sunan ta a hankali. Ta ɗago ta kalleshi.
"Najeeb na son ki farida, idan ki na son shi, ko da kaɗan ne, fight for him. Kar ki ga wai Sabreen ta dawo ki shiga ruɗu ko ki ɗauka shikenan ba ki da chance a wajen Najeeb. Ke ne ki ke da damar samun sa, har ki juyashi yadda ki ke so. But only idan ki ka cire shakka ko wani tsoro"
Maganganun Anas sun ba ta mamaki sosai, ta daure ta ce "Najeeb ba ya so na Ya Anas, ba zan iya ƙwallafa rai na a kan sa ba"
"Shikenan, ki zauna, ki zuba ido har Sabreen ta ci galaba akan ki. Idan hakan ta faru ina tabbatar mi ki da cewa ƙeyar Najeeb sai ya miki wuyar kallo"
Daga haka ya tashi ya fita.
Tunanin maganganun Anas ta shiga yi. Tana kokonton maganar amma wani ɓangare na zuciyarta na son gaskata hakan...
Ranan ba su dawo tareba saboda ta rigashi tafiya, ta barshi suna tattaunawa da Anas, ta san ba zai wuce akan fara aiki da Sabreen ta ce za ta yi da su bane.
A gajiye ta shiga gidan sai taga Sabreen da Mom su na hira a falo. Mom kawai ta gaisar ta wuce sama bayan ta aikawa Sabreen harara.
Tana ɗan jin ciwon ciki amma ba wannan ba ne a gaban ta yanzu. Mafita ta ke nema wa kan ta, ko da ba za ta samu Najeeb ba amma ba za ta bari Sabreen ta sameshi ba, dan Najeeb bai dace da karuwa ba. Ko yaushe ta fara damuwa da Najeeb oho...
As usual sai dare ya dawo, tana kwance akan gadon ya shigo. Ba ta kulashi ba dan ta kanta ta ke, tun da magriba ciwon cikin ta yai tsanani kuma ta duba ba ta da magani.
Bayan ya shirya ya sa Najdah ta kawo ma sa lemon tea. Ya zauna yana aiki a laptop yana sipping tea ɗin.
Tun ɗazu ta ke juye-juye a kan gadon bai lura da ita ba. Ta tashi zaune, ta yi rub da ciki, ta yi gotso duk saboda yadda ciwon mara da ciki ke jijjigata. Ƙarshe dai ƙasan gado ta sauko ta yi kamar sujjada tana ɗan jijjiga jikinta.
Ya gama abinda zai yi ya hau gado sai ya ga bai gan ta ba. Ɗazu dai ya gan ta a kwance kuma bai ji ƙaran buɗe ƙofar banɗaki ba balle yai tunanin wajen ta shiga. Ya share zancen ƙila kaya ta je chanjawa. Bai yi 5seconds da sake zancen ba ya ji nishinta.
Fara dube-dube ya ke har ya mirgino zuwa gefenta ya leƙa ƙasa ya ganta.
"Are you Ok?"
Girgiza kai kawai ta yi.
"Mi ya sameki?"
"Ina ruwan ka da ni. Ka damu da ni ne?"
Juyawa yai ya ƙyaleta.
Ta ɗan jawo pillow ta danne cikin ta da shi ta cigaba da nishi. Bata ankara ba sai ta ga ya kashe wutan ɗakin. Wani tuƙuƙin baƙin ciki ya zo ma ta har wuya, wato da gaske bai damu da ita ba.
"Wayyo Ummina, Wayyo Allah gatan marainiya. Wayyo Ummi"
Kunna wutar ɗakin yai ya tashi ya zo ya ɗauketa ya maidata kan gadon. Ya ce "mi ya ke damun ki?"
Ba ta kulashi ba ta cigaba da murƙusu a kan gadon. Lokaci guda ya tashi kaman an tsikare shi ya fita daga ɗakin. Minti biyar sai gashi ya shigo ɗauke da mug.
"Tashi ki sha magani"
"Ni ka bar ni, ka san abinda ke damuna ne?"
"Get up" ya faɗa da ɗan ƙarfi.
Ibrufen tab ya miƙa ma ta tareda ruwan ɗumi, ta amsa ta sha.
Ya ce " ki shanye ruwan"
Ta cigaba da shan ruwan ɗumin har ya ƙare. Ta miƙa ma sa mug ɗin ya karɓa ya ajiye a saman bedside drawer.
"Kwanta"
Kwantawa ta yi da bayan ta tana kallon idon sa. Rigan baccin da ta sa riga da wando ne masu laushi, wandon iya gwiwa ya ke.
Hannu ya sa ya kamo ƙafafuwanta biyu. Ta challa ƙara " Sir Najeeb me ka ke shirin yi?"
Wanni kallo ya watsa ma ta ta yi shiru. Ƙafafuwanta ya kama sannan ya tanƙwasu ta yadda cinyoyinta sai da su ka taɓa cikinta gwiwan kuma na taɓa nonuwanta. Ya sake stretching ƙafafun sannan ya sake tanƙwasasu. Haka ya ke yi har sai da yai kaman sau goma sannan ya sauke ƙafafun, ya sake ɗaga ƙafa ɗaya ya tanƙwasashi gefe. Ƙafar ta yi kaman triangle, sannan ya tanƙwasa ta koma ɗaya ɓangaren haka yai ta yi har sau goma sannan yai wa ɗaya ƙafan ma haka. Hannu ya sa zai ɗaga hips ɗin ta sama Farida ta yi saurin cewa "Sir Najeeb ina abu fa, kuma ba a abu idan ana abu"
Ya gimtse dariyar da ta zo ma sa ya ce " Bakin ki ne abu ai, ni ma ba na abu idan ba na so na yi abu musamman ma da wadda ba ta da abu"
Ya tallafo hips ɗinta ya ɗan ɗaga sama sannan ya mai da su ya sake ɗaga su a haka sai da yai sau goma.
Yana sake wani form of stretching ɗin ta yi saurin cewa " Sir Najeeb ka yi a hankali wandona zai yage"
Tsayawa yai yana kallon ta. Sometimes yana mamakin wai yarinyar nan ta yi makaranta. Most at times tana yin wassu abubuwan kamar 'yar ƙauye.
Sai da ya gama yi ma ta yoga dan ta samu relieve sannan ya kashe wuta ya kwanta.
A cikin duhun Farida ta dubi gefen sa ta ce "Sir Najeeb ya aka yi ka iya wannan abin, Allah na ji sauƙi sosai"
"Sleep Mrs Jibo" ...
...................
Kamar yadda Sabreen ta nema haka washe gari aka ware ma ta office a second floor. Da ta zo ta gani ta ce ba ta so sai a top floor inda office ɗin Najeeb ya ke. Anas ya ce sai dai ta yi manage ahaka zuwa kwana biyu. Ba ta da haƙurin kwana biyu dan haka ta ce ba za ta zauna ba.
Kamar yadda Anas yaiwa Farida alkawari hakan ya sa ya kira Yakubu su ka fara reviewing ɗin case ɗin Farida da aka yi kwanan baya.
Najeeb ya jima yana zaune yana aiki, Sabreen ta sa shi a gaba da kallo. Ya ce ta tafi ta ƙi tafiya sai yai kamar bai san da zaman ta ba a wajen.
Farida ba ta office lokacin da Sabreen ta zo ta wuce. Ta dawo daga kai saƙo ta zauna tana yin aiki sai ta tuna ya kamata ta chanja pad. Ta ɗau jakar ta ta nufi office ɗin Sir Najeeb tunda banɗakin sa ya fi clean.
Yana zaune ya ji hannun Sabreen a kafaɗar sa. Ya juyo a fusace.
"Whats the meaning of this?"
"I know you missed my touch Noory" ta faɗa tana ƙara shigewa jikin sa.
"To karuwancin har a office" muryan Farida ta dakatar da ita.
Dukkan su su ka kalli Farida da ke tsaye ta sa hannu a kafaɗa.
"Miss celebrity you're stepping beyond your boundary" ta ƙaraso har gaban ta ta nuna ta da yatsa.
Kamar yadda ta ce mata she has his heart haka itama ta kwaikwayi maganan ta ta ce " fuck off old woman, i am his wife"
Sabreen ta cize leɓe tana huci.
"As as as, mai guri ta zo sai mai tabarma ta naɗe"
"Wow! I like your courage" ta faɗa tana haɗiye duk wani baƙin ciki da ta ke ji.
Har ta fita Farida ba ta bar cewa as as as ba.
Ta juyo ta kalli Najeeb da ya zuba ma ta ido yana ganin shaƙiyancin da ta ke wa Sabreen. Not minding ko waye Sabreen ɗin.
"An dai ji kunya, mace ta gudu ta barka shekara takwas amma ka gan ta yanzu jikin ka ya fara rawa kamar mazari" ta yi wani juyi sannan ta wuce banɗaki.
....................
A hankali ta fara barbaɗa tankaɗaɗɗen yajin da ke hannunta, tun daga pillow zuwa duka bedsheet ɗin. Bedsheet ɗin ba fari bane balle a gane. Tana gamawa ta fice daga ɗakin ta maida roban yajin zuwa kitchen. Ta haura sama abinta.
Sabreen ta dawo tayi wanka ta shirya cikin rigan baccinta ɗan filili da shi. Ta kwanta akan gado. Juyawar da za tayi sai ta ji zafi a wuyanta da cinyoyinta da ke buɗe. Ta sa hannu ta sosa wuyar ai sai ya zama kamar ƙara zafi ta yi wa wajen. Ta yi wuf ta tashi tana sosa ko'ina ajikinta...
Farida ta baza kunne tana sauraron ko saƙonta ya kai inda ya ta ke so, saboda haka ma ba ta kunna Tv ba, Shi kuma Najeeb na aiki a laptop. Lokaci ɗaya su ka ji an kurma ihu.
Da farko Najeeb ya ɗauka ko ƙaran daga TV ɗin Najdah ne tunda ya ga Farida ba ta kunna Tv ɗin su ba. Ihu da ƙaran ya cigaba da ƙaruwa hakan ya sa ya miƙe zumɓur ya fita, Farida ta bi bayan shi da sauri.
Lokacin da su ka isa ƙasa su Daddy da Mom ma sun iso ƙasan su na kan Sabreen da ke ta soshe-soshe tana ihu...
*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......
*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
0️⃣2️⃣9️⃣
https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref
𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
*(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*
*wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi, ga mai so zai iya tuntuɓar 08137311900*
Sabreen na ganin Najeeb, ta yi kan sa tana sose-sose, ya riƙeta yana tambayar miya ke damunta amma ba magana sai kuka tana ƙara shigewa jikin Najeeb kaman jikin sa ne zai ma ta magani.
Mom ta tafi da gudu ɗauko car key. Chak ya ɗauketa za su fita dai-dai nan Farida ta sa kuka itama tana wayyo cikina wayyo cikina.
Najeeb ɗauke da Sabreen ya juyo ya ga Farida har ta kai ƙasa tana riƙe da ciki.
Dad ya ce ajiyeta ka ɗauko matar ka.
Sabreen ba ta ji mi aka ce ba amma ganin Najeeb na shirin sauketa sai ta sake ƙanƙame wuyan Najeeb tana kuka.
Chan gefe ma Faridan kuka ta ke yi Mom ta yi kan ta tana ƙoƙarin ɗagata tana tambayar miya sameta.
Tunanin Najeeb ko dai ciwon cikin period ne amma kuma she was normal throughout yau, tunda yau kwana na uku kenan da farawanta.
Farida cikin kuka ta fara cewa "Mom ulcer, ulcer na ne ya tashi"
Bai san ko maganar Daddyn ne ta shige shi ba, ko kuma dai ya zaɓi tallafawa Farida ne akan Sabreen ɗin. Amma tsintar kan sa yai da sauke Sabreen ya nufi wajen da Farida ke murƙususun ƙarya a ƙasa. Daddy da Mom su ka tallafawa Sabreen su ka fita da ita. Daddy na cewa yai sauri ya ɗauko Farida. Faridan na hannun sa ya ce su tafi da Sabreen zai taho da Farida.
Ba tareda ya ji nauyin ta ba haka ya haura da ita sama dan ya ɗauko key ɗin motar sa, har da ce ma ta sorry.
Ya ɗauki key ɗin su ka fito still yana ɗauke da ita. Kafin su isa wajen motar sa motar su Daddy ta fice daga gidan. Sai da ya ajiyeta sannan ya zago da gudu ya shiga wajen zaman driver, yana ƙoƙarin tada motar ya ji ta ce "Sir Najeeb mu koma cikin gida, idan na sha Gestid ma zai lafa mun"
Kallon ta ya tsaya yi cike da mamaki da takaici, sai yanzu ya lura fiskarta ba ɗigon hawaye ko ɗaya. Lokaci guda zuciyar sa ta ankara da cewa lallai Farida na da hannu wajen abinda ya samu Sabreen, yanzu haka wani abin ta sa ma ta a ɗaki.
"You lied?" Ya faɗa da ɗan ƙarfi
"Sir Najeeb Allah Wallahi ina da ulcer, na ji alamun zai tashi ne shi ne ya sa na tareshi tun kafin ya zo"
Zaro ido yai waje lokaci guda kuma ya kwashe da dariya har da dukan steering.
"Now i'm very certain that you're crazy Mrs Jibo"
"Sir Najeeb da laifi idan mutum ya tari rashin lafiya ne?"
Sai da ya sha dariyar sa sannan ya ce " faɗamin gaskiya mi ki ka yiwa Sabreen?"
"Ni ba abin da na ma ta. Ance idan duka yai yawa na kai ake karewa. Da ka je kana dakon ɗaukar wata ƙatuwar banza ba gara ka ɗauke ni ba, har lada za ka samu a hakan fa"
"So, kin ƙirƙiri ciwo ne kawai dan na ɗauke ki?"
"Allankatafir ba haka ba ne. Ciwon a jikina ya ke tun asali"
" Ok ok, so yanzu mi za ki ce da su Dad? Su ma za ki gaya mu su taro ciwo ki ka yi?"
"Cewa zan yi na sha magani na warke"
"Ni kuma sai na kai ki asibitin, a taro miki ciwon da kyau"
Ganin yana ƙoƙarin ta da motar ne ya sa ta yi saurin buɗe ƙofa ta fita da gudu. Yana gani ta fita ya kwantar da kan sa ajikin kujera yana murmushi. Shi kan sa mamaki ya ke, a da ya tsani yawan surutun ta amma yanzu ya na jin nishaɗi idan tana yin wasu abubuwan.
Ya jima a cikin motar yana tuno wassu abubuwa da su ka faru a baya. Yana fitowa zai koma cikin gida Daddy ya kirashi yana tambayar ya aka yi ba su iso ba. Cewa yai cikin Faridan ya lafa ta ce ba sai anje asibiti ba.
Daddy ya ce "to Alhamdulillah, Allah ya ƙara lafiya"
Yana kashe wayar ya fara mamakin ƙaryar da yai saboda Farida.
Duƙunƙunewa ta yi ajikin bargo tana tsoron mi Sir Najeeb zai yi dan ta tabbata ya gane ita ta yiwa Sabreen wannan abu.
Yana shigowa ta sake duƙunƙunewa ta na rintse ido.
"Ki gayamin gaskiya mi ki ka sa ma ta?"
Ta yi shiru ba ta kulashi ba.
"Idan ba ki gayamin ba zan gayawa Dad ƙaryan da ki ka yi"
Ta ɗan buɗe idon ta ta leƙo shi yana tsaye yana kallon ta.
"Borkono ne, dakakken borkono na sa ma ta a bedsheet"
"You're a criminal Mrs Jibo, ya kamata a kama ki"
"Allah ya kiyaye"
Wucewa yai ya shiga banɗaki dan ya sake wanka...
Farida na ganin ya shiga banɗaki ta san ba fitowa zai yi da wuri ba ta yi wuff ta tashi ta fita daga ɗakin. Ɗakin Sabreen da ke ƙasa ta je ta cire bedsheet ta karkaɗe sannan ta juyashi baya ta shimfiɗa, filon ma ta ma sa haka sannan ta fito.
*(yau na ci yaji dayawa, hakan ya tada min ulcer na. That's d trigger for writing this scene😁. Ni ma daga yau irin na Farida zan na yi, zan dinga taro ulcer tun kafin ya tashi, saboda idan ya zo kar ya wahalar da ni😂)*
.......................
Su Daddy na zuwa aka duba jikin Sabreen wanda har ya feso da ƙuraje abinka da jar mace. Magani aka ba su aka ce ta shafa. Mom ta karɓa ta shafa ma ta. Likitan cewa yai allergy ne ba komai ba.
Mom ta ce da sun koma gida za a chanja ma ta ɗaki tunda ta ce daga kwanciya a gado ta fara jin zafi da ƙaiƙayin.
Lokacin da su ka dawo gida ƙarfe shabiyu na dare ya wuce. Ɗakin Najma da ta ke sauka idan ta zo su ka wuce da ita. Mom ta je ta ɗebo ma ta kaya a wancan ɗakin da ke ƙasa.
Sai da su ka tabbatar ta kwanta a wannan gado lafiya kafin su ka bar ɗakin...
Farida ta yi bacci kafin su dawo amma Najeeb ya ji dawowar su, sai dai ko leƙowa bai yi ba.
Yau da asuba Najeeb ya fito daga wanka yana sa kaya sai ga siririyar tusa ta fito. Farida da ke shirin shiga banɗaki ta leƙo inda ya ke dan sarai ta ji tusan.
"Sir Najeeb ka ji abin da na ji kuwa?"
Yai gyaran murya ya ci gaba da saka belt ɗin da ya ke ba tareda ya kulata ba.
"Sir Najeeb fitar tusa na ji fa, kuma ba ni na yi ba. Ba ma irin warin tusa na bane"
Ɗagowa yai ya kalleta ran sa a haɗe.
"Ke wai bakin ki ba ya iya yin shiru ne?"
Ɓiiiit sai ga tusan ta kuma fitowa.
Ta kama baki tana faɗin "Lahaula! Sir Najeeb ashe kai ne. Ina ga basir ke damunka, ka nemi magani"
Hannu ya kai zai buge bakinta ta ja baya da sauri tana dariya. Sai da ta shiga banɗaki ta leƙo da kan ta ta ce "Sir Najeeb tusan ka irin ta yara. Kasan ance tusa kala uku ne akwai Ɓiiiit na yara, booooot na manya, alanrankiɗibobot na tsofi"
Tana faɗin haka ta banko ƙofar banɗakin...
Ya na tsaye yana naɗa tie amma dariya ya ke ciki-ciki. Cikin zuciyar sa yana maimaita abin da ta ce. "Where on earth did she know all this" ya tambayi kansa.
Kafin ta fito ya riga ya shirya ya fita. Lokacin da ya kai ƙasa ya haɗu da Daddy.
"Morning Dad"
"Morning ya jikin Aisha?"
"Da sauƙi" ya faɗa yana tuno abin da ya faru jiya.
"Allah ya ƙara ma ta lafiya, za ka koya ma ta mota ne ko za ka enrolling na ta a driving school? Ka ga ba daɗi Najdah na hawa mota ita ba ta da shi"
" Ehm Ehm..." ya rasa abin faɗa.
"Shikenan duk abinda ka yanke ya yi dai-dai"...
...................
Saboda abinda ya faru ranan Sabreen ba ta fita ba. Lokacin da Najdah ta dawo ne ta ke jin abinda ya faru a bakin Sabreen ɗin, saboda ba ta kwana a gida jiya ba, gidan Uncle Sulaiman ta kwana.
Najdah ta tashi ta je ɗakin dan ta tabbatar da zargin ta. Sai dai Adama ta riga ta chanja bedsheet ɗin kuma an gyara ɗakin dan haka ba abin da ta gani.
Da ta dawo ta ce da Sabreen ta san wanda ya sa ma ta abu a gado. Sabreen ta zaro ido tana tambayar waye?...
...........
"Khalidah ban gane mi ya ke faruwa ba? Kin min alƙawarin zan samu wannan sakatariyar Najeeb ɗin amma daga dawowata ki ke min zancen banza wai Najeeb ya aureta. Ya aka yi haka? Ba kin tabbatar min plan ɗin mu zai tafi dai-dai ba. Zai koreta a aiki ni kuma na sameta"
" Alhaji matawalle ban san ya zan ma ka ba. Ba fa kai kaɗai ka ke jin zafin abin nan ba. Kai damuwarka ka kassara Najeeb ni damuwata na samu Najeeb. Kai buƙatar ka ta biya ka sa Najeeb ya rasa babban project wanda hakan ta jawo ma sa asara, ni kuma fa? Mai na samu banda ƙara haɗa Najeeb da sakatariyar sa"
"A'a Khalidah bayan kassara Najeeb kin min alƙawarin samun sakatariyar sa, Farida sunan ta ko?"
" Alhaji Matawalle ka fita a office ɗi na, ka bar ni da takaici da ƙuncin da zuciyata ke fama da shi"
"Kar ki kawomin zancen banza Khalidah, ba na neman abu na rasa"
"Ya zan ma ka ne? Ka je ka ɗauki Farida ma na idan ka isa"
"Haka ki ka ce ko" ya girgiza kai ya fita daga office ɗin.
Yakubu ya koma da baya lokacin da ya ga Alhaji Matawalle na shirin fitowa. Dama ya zo kawo wa Khalidah wa su takardu ne ya ji ƙarshen hiran na su. Jin sunan Farida ya sa ya fasa shiga office ɗin.
.......................
Wannan weekend ɗin da Aneesa ta zo ne ta lura da cikin jikin Maijiddah. Ba ta san lokacin da ta ce "Sweetheart yaushe wannan yarinyar ta samu ciki?"
AbdulWahab bai kulata ba ya cigaba da cin abincin da ya ke yi.
"Sweetheart magana fa na ke"
"So ki ke na bayyana mi ki abinda mu ka yi ta samu ciki? ko so ki ke ki san sau nawa mu ka yi kafin ta samu ciki?"
"AbdulWahab zai kai 4 months fa"
"Allah ya sauke min ita lafiya amin"
"Abinda ma za ka ce kenan? Bayan ka gama cin amana ta da yarinya ƙarama, wanda a haife ka haife ta har kana da bakin cewa Allah ya sauketa lafiya"
"Ya nuna ina da lafiya kenan, kuma kin ga ina da damar ƙaro irin Hauwerh biyu idan ina so, kin ga in shiga nan in shiga nan"
Aneesa ta cillar da cokalin hannun ta.
"Wallahi ba zai yiwu ba. Ba ka isa ba AbdulWahab"
"Ki cigaba da aiki a Abuja, zan cigaba da aiki a nan kuma da idon ki za ki dinga ganin sakamakon ayyuka na ma su kyau da tarin lada. Alhamdulillah da na kasance musulmi, na ke da damar auren mace fiye da ɗaya. Kin ga musulunci ya min rana"
Juice da ke glass cup a gaban ta ta ɗauka ta watsawa AbdulWahab tana zage-zage. Bai ƙara cewa komai ba ya tashi ya bar wajen.
"Ka dawo ma na, ka dawo mu ƙarasa maganar, macuci kawai"...
Wannan weekend ɗin gaba ɗaya cikin faɗa su ka yi dan AbdulWahab dena shiga sabgar ta ya yi. Tana komawa Abuja ta sanar da Mama Maijiddah na da ciki, ga mamakin ta sai Mama ta ce "Allah ya raba lafiya"
"Mama kin ji mi na ce kuwa? Su baby da Alizah su na gab da samun step siblings"
"Na ji kuma na gane, idan kina son haihuwan ke ma sai ki dena planning ki koma tara 'ya'ya rututu kamar Kaza"
Aneesa ta rasa bakin magana, dan inda ta dosa Mama ba ta bi nan ba.
A ranan da ta je office ta nemi a maida ita Lagos ko kuma ta ajiye aiki. Su ka ce za su duba.
.......................
Da ke tun ƙarfe ɗaya Najeeb ya fita kuma ya riga ya ce ma ta ba zai dawo ba sai yamma shi ya sa ta tattara ta fito dan ta koma gida. Tana fitowa ta hango Sabreen da wassu police biyu su na tahowa. Mamaki ya kamata ta ɗan tsaya dan ta yi gulman me ke faruwa.
Sabreen ta nuna ta tana faɗin "she's the devil, arrest her"
Farida ta zaro ido " arrest me for what?"
"Ran ki shi daɗe za ki bimu zuwa station mu mi ki wassu tambayoyi"
"Ƙwal ubanchan, na bi ku station a dalilin me. Kun san ko wacece?"
Ɗaya police ɗin ya kwantar da murya ya ce " dan Allah ki yi haƙuri mu je, mu ma daga sama aka samu"
Sabreen sai hararanta ta ke.
"Shikenan barin kira miji na" ta fito da wayarta daga jaka ta fara kiran Najeeb sai dai da ke inda su ke ba service sai bai shiga ba. Jikin Farida yai sanyi, ta tura ma sa text kawai ta bi police ɗin nan...
Bai duba wayar sa ba sai ƙarfe biyar da rabi bayan sun dawo kamfani. Yana duba missed call ya ga har da numbar Farida ga kuma text ɗin ta. Ya buɗe text ɗin ya ga ta rubuta *Sabreen ta arresting ɗi na*
"Arrest?" Yai saurin kiran numbar Faridan ya ji ta a kashe. Da sauri ya fara dialling numbar Anas ya na fita daga office ɗin da gudu...
Shi da Anas su ka isa gida dan numbar Sabreen ɗin da Najdah ta turo mu su an ƙi ɗaga kiran su.
Hankali kwance su ka samu Sabreen tana zaune a falo tana cin apple.
"Where's she?" Ya daka ma ta tsawa
" who?"
"Dont be stupid Sabreen, where is she?"
Juyar da kai ta yi gefe ba ta amsa ba.
Ƙarasawa yai wajen ya fincikota yai waje da ita Anas ya bi bayan sa...
............
Tun da su ka shiga mota ya ke faɗa abin mamaki Sabreen ta ce ba za a fitar da Farida ba saboda abin da ta ma ta...
'Yan station ɗin ma sai da su ka san sun taɓo matar babban mutum. Tun da su ka shiga Najeeb ke ta masifa. Anas ne ma ya ke ƙoƙarin bashi haƙuri dan kar a samu matsala a wajen.
Ba'a jima ba aka taho da Farida. Yana ganin ta ya ƙarasa wajen ta da sauri. Ya riƙe hannunta kawai sai ta faɗa jikin sa ta fara kuka.
Duk wani formalities Anas ne ya tsaya zai yi, dan Najeeb kan jan hannun matar sa yai su ka bar wajen. Sabreen ta bi bayan su tana faɗin ba zai yiwu Farida ta tafi haka ba bayan abinda ta yi ma ta. Najeeb bai kulata ba har su ka isa bakin mota. Zai taimakawa Farida ta shiga Sabreen ta riƙe ma sa riga, ta fara kukan munafurci.
"Noory she wanted to kill me, ita ta sa min yaji a gado jiya. I almost died Noory"
Bai yi yunƙurin yafce hannunsa daga riƙon da ta ma sa ba illa matsawa yai kusa da Farida ya ɗan sukuyo dai dai saitin fiskarta. Ba tareda wani tantama ba ya haɗe bakin su. Farida ta ƙwalalo ido saboda mamaki da shock da ta ji lokaci guda.
Sabreen ta sake rigan Najeeb tana kallon yadda Najeeb ke kissing Farida zuciyarta na tafarfasa, ji ta ke kamar zuciyar zai bulluƙo ya fito.
Farida ta yi saurin janye bakin ta saboda tunowa da ta yi a public place su ke. Da rinannun idanun sa da su ka ƙanƙance ya ce "kiss me" ba ta san ya akayi ta jefar da kunyar ba kawai ta tsinci kan ta da haɗe bakin su not minding a inda su ke...
# Team Farida
# Team Najeeb
# Team Sabreen
Ina sauraron comments ɗin ku.
*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......
*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
0️⃣3️⃣0️⃣
https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref
𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
*(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*
*wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi, ga mai so zai iya tuntuɓar 08137311900*
Murmushi kawai ta ke yi tunda su ka fara tafiya. Idon ta na gefen titi amma hankalin ta ba a titin ya ke ba. Har yanzu tana jin taste ɗin zaƙin bakin sa a nata bakin. Ba ta taɓa sanin haka kiss ke da daɗi ba sai yau. Lokacin su na soyayya da Lukman ya taɓa kissing hannun ta da goshi amma banda lip to lip kiss. Shi kam Rayyan ba su taɓa irin haka ba, Rayyan ya na tsoro da shakkar Farida shi ya sa ko hannun ta bai taɓa riƙewa ba sai dai ko a rashin sani.
Yau ta samu first kiss ɗin ta, kuma da Sir Najeeb, Sir Najeeb fa. Ta sa hannu ta rufe bakin ta saboda tsikar jikan ta da ya tashi lokacin da ta tuna abinda ya ce "kiss me".
"Did they hurt you?"
Ai ta tafi duniyar tunani ba ta ma ji abinda ya ce ba. Duk wani cin mutunci da ta shirya za ta yiwa Sabreen lokacin ta na cell ta watsar da shi. Ƙwaƙwalwarta ba abinda ya ke tunowa sai wannan moment ɗin.
Chan ƙasan zuciyar sa ya ke neman dalilin da ya sa ya kissing ɗin ta amma ya rasa. Chan ya baiwa kan sa amsa da Sabreen. Yes ya yi haka ne saboda Sabreen, saboda ta gane cewa he's over her now. Amma must he resort to kissing her? Yanzu sai ta rena shi. Wata zuciyar ta ce but it was the best kiss you ever had. Ko dan ya jima bai yi kiss ba ne, dama da Sabreen ne kawai, no one else. First kiss na shi in 8yrs felt different. Kaman wani ƙaramin yaro haka ya lashe lips ɗin sa da harshe. Garin haka ma saura kaɗan ya buge wani mai Keke.
Har su ka isa gida ba wanda yai magana. Farida ce ta fara shigowa dan ta fita ta bar shi a mota. Tana tafiya tana jin ta a sama fiskar ta ɗauke da murmushi.
Najdah ne da wata tsohuwa a falon lokacin da ta shigo. Ba ta ma lura da su ba sai da tsohuwar ta ce "amarya lafiya?" Farida ta juyo sai ta ga tsohuwar duk da kuwa kuɗi sun ɗan ɓoye tsufan, amma kuma a yadda ta gan ta za ta haifi Daddy.
Ta yi saurin ƙarasawa wajen ta ta tsugunna "Hajiyata dan Allah ki yi haƙuri ban gan ki ba ne"
"Na ga alama ai, kin tafi birnin soyayya ko. Ina angon" kafin ta ba ta amsa sai ga Najeeb ya shigo.
Yana ganin Hajiya Mama ya washe baki " tsohuwa yaushe a gari?"
Yana ƙarasowa wajen ta ta ɗauki sandarta ta ɗaga sama za ta kwaɗa ma sa ya ja baya da sauri.
" ke fa tsohuwa kin dawo kenan za ki fara cin zalin mutane"
"Ungo na ka Najeebullahi, tun jiya na dawo amma shi ne ba za ka kawo min amarya na gan ta ba"
"To ke kiji da ƙafar ki ma na, amma sai shegen yawo"
Farida dai kallon Najeeb da Hajia Mama ta ke da su ke dramar su na Kaka da Jika. Najeeb was jovial amma ba kaman tsakanin sa da Mom ba wanda tun zuwan ta abin ke ɗaure ma ta kai.
Hajia Mama ta kalli Farida ta ce "kin ga mijin kin nan ke ce rufin asirin sa. Haka yai ta yawo ƙaton tuzuru da shi, sai da Allah ya kawo ki"
Farida ta yi murmushi.
"Sai ki kula da shi sosai dan ɗan duniya ne"....
Ta fito daga wanka bayan sallar Isha ta fara jin hayaniya a ƙasa. Ba ta tantance ko muryan su waye ba ne amma daga yadda maganar ta ke haɗakar larabci da turanci ta san ba zai wuce Sabreen ba ne...
"Big B mi ya sa ka ke bin bayan ta, kai kan ka ka san ita ta yi wannan abin and she needs to be punished for that"
" walau ita ta yi walau ba ita ba, dukkan ku biyu babu wanda ya ke da ikon arresting ɗin ta, especially you Sabreen. Ina so ki nisanci iyalina"
"Big B amma..."
"Najdah!" Ya daka ma ta tsawa. Kallon shi ta yi sannan ta haura sama da gudu.
Ya juyo ya kalli Sabreen ya ce "next time ki ka yi ƙoƙarin taɓa lafiyar mata ta, i wont take it lightly"
Cike da tuƙuƙin baƙin ciki ta ce "you dont love her, do you"
Haɗiye miyau yai sannan ya ce "go back to Hollywood you dont belong here"...
Ɗakin Najdah ya fara zuwa Lokacin da ya haura sama, amma ta ki buɗe ma sa ƙofa. Dan haka ya juya ya shiga ɗakin su.
Yana shiga ɗakin ya gan ta bakin gado tana kuka. Jikin sa yai sanyi ya ƙarasa wajen ta yana tambayar minene dan a tunanin sa ko a cell ɗin an mata wani abu ne.
"Mi ya faru?"
Tana kuka tana jan majina ta ce "Baba ya rasu"
Kan sa ya ɗaure dan Anas ya taɓa ce ma sa Farida marainiya ce to yanzu kuma wani Baban ne ya rasu.
"Your father?" Ya sake tambaya.
"Kaka na ne"
Ya jawota jikin sa yana lallashin ta.
"Yanzu Ummi ta kira ni, dan Allah Sir Najeeb zan je Jos gobe"
Ya gyaɗa kai ya ce "its ok"
Sun jima tana kwance a jikin sa tana hawaye tana faɗa ma sa kyawawan halayen Baba. Bai bar wajen ta ba sai da ta yi bacci, lokacin kusan sha biyu saura na dare. Da ya gyara ma ta kwanciya sannan ya je yai wanka ya shirya cikin kayan bacci sannan ya zo ya kwanta amma kafin yai bacci sai kusan ƙarfe biyu. Tunani ya cika ma sa kwanya.
Washe gari da sassafe ta shirya, ya sa Iliya ya kaita har Jos. Lokacin da motar ta bar cikin compound ɗin ƙarfe shida da rabi na safe. Yana shigowa cikin gida Daddy ya kira shi, da ya je tambayar sa yai gameda abinda ya faru jiya dan ya ji maganar a wajen Mom.
Bayan ya ma sa bayani sai Daddy ya ce " ka yi katanga tsakanin ka da Sabreen, ban hana ka ƙara mace ba idan ka ga ba za ka iya zama da Aisha ita kaɗai ba, amma ka sani. Ba zan taɓa amincewa da Sabreen a matsayin suruka ba. Ba wai dan ta rabu da kai ta dawo ba, sai dan ba zan bari ka haɗa zuri'a da macen da zata iya gurɓata ma ka rayuwa ba. Ina sane da lokacin da Mahaifiyar ka ta ke kuka kullum saboda Sabreen ta na shirin auren wani kafiri ɗan ƙwallon ƙafa har ta ke sukan addinin musulunci da ya hana aure tsakanin kafiri namiji da mace musulma. A hira da aka yi da ita shekaru uku da su ka wuce, cewa ta yi sallah na takura ta, wai anata abu ɗaya kullum ba hutu. Wannan ba macen aure ba ne. Idan har ka nuna za ka auri Sabreen to za ka yi nisa da ni da iyalina. Za ta zauna a nan ne kawai saboda alaƙa ta jini da su ke da shi da Nabilah amma bayan nan ba na so wani abu ya kuma shiga tsakanin mu"
Najeeb ya gyaɗa kai.
"Ya maganan gidan ka, anyi interior decoration ɗin?"
"An kusa a gama"
"Ok Allah ya nuna ma na"...
Yau dai throughout a office jin sa ya ke wanni iri. Musamman idan ya zo fita ya ga ba ta kan kujeran ta.
Da ke Jummu'a ne kuma ranan hutu ne an haɗa ƙwarya-ƙwaryan party amma bai iya tsayawa a wajen ba. Anas ne ya tsaya ya wakilce shi, daga sallar jummu'a gida ya wuce yana jin jikin sa ba daɗi. Ba wai ba shi da lafiya ba ne amma kuma jikin sa is weak.
Yana shiga ɗakin sai ya ji ɗakin ya ma sa faɗi kaman ba ɗakin sa ba, there's something missing. Ƙanshin ɗakin ya sauya tun zuwan Farida saboda haɗuwar turarukan sa da na ta kalolin turaren. Har ta fasalin ɗakin ya sauya. Ya tuna ranan da ya shigo ya ga tana chanja arrangement na wasu abubuwan a ɗakin.
"Sir Najeeb ɗakin ka yana buƙatan polish"
Ya tuna yadda yai ta gwaleta yana cewa ta hargitsa ma sa ɗaki.
Ya na shiga wajen closet ya tuna ranan da ya ke chanja kaya ta shigo lokacin gajeren wando na jeans ne a jikin sa ba riga.
" Sir Najeeb, idan ka na gida sai ka yi ta sa gajerun wanduna kaman wani ɗan firamare"
Yai murmushi tunowa da yai da kalolin tusa da ta lissafto ma sa ranan...
Lokacin da ya gama abubuwan da zai yi yana kishingiɗe a kan gado ya ji gadon ya ma sa daban. Tun da ta zo kullum za su kwanta akwai pillow a tsakanin su, jiya ne kawai su ka kwana ba pillow.
A hankali ya sa hannu ya fara shafa gefen da ta ke kwana wanda ya ke empty yanzu. Ya tuno ranan farko da za su kwana a kan gadon faɗan da su ka yi, daga ƙarshe da tunanin kissing ɗin da su ka yi jiya bacci ya tafi da shi.
Washe gari da safe Daddy ya ce su je su yiwa Baffa Musa ta'aziya. Tare su ka je a chan ne ana taɗi wanda tsakanin Daddy da Baffa Musan ne dan shi banda ya haƙuri da ya ce bai kuma cewa komai ba. Cikin taɗin su Baffa Musa ke kawo rayuwar da Farida ta yi. Daga wannan gida zuwa wannan gida kafin daga baya ta zauna a wajen Kakannin ta.
Daddy ya tambayeshi ko miyasa bai ɗauki Farida tun da wuri ba. Baffa Musa ya ce "Hmm Faridan, tun tana yarinya ta ke da baki. Ko hutu aka kawota sai ta yi ta ƙorafi, Baffa garin ku akwai zafi, ba zan zauna ba"...
Lokacin da za su tafi Baffa ya ce da Najeeb " ka kula min da ita dan Allah. Ka da ranan gobe Ubanta ya ce ban riƙe amanar tilon 'yar sa ba"
Najeeb ya ce Insha Allah...
........................
Yau sati ɗaya kenan da ba ta nan. Cikin sati ɗayan nan ya rasa ganewa kan sa. Bai ma cika son fita ba, dama wajen aiki ke ɗebe ma sa lokaci to yanzu ana hutu. Sabreen washe garin da Farida ta tafi itama ta yi tafiya, bai san inda ta je ba kuma bai damu ba dan shi idan ta tashi ne to kar ta ƙara dawowa.
Yau da ya je wajen Hajia Mama ne ta ke cewa ya kira ma ta Farida ta ma ta ta'aziya.
Kwana uku da Farida ta yi a Jos ta yi su cikin rashin jin daɗi, na farko ga rashi da su ka yi, na biyu kuma Sir Najeeb da ya shareta. Kullum da tunanin sa ta ke kwana ta tashi, amma shi ko text bai ma ta ba balle ya kira ya ma ta ta'aziya. Duk da kuwa ranan da ta taho ta tura ma sa text akan sun isa lafiya amma ko reply bai yi ba. Wasu lokutan har mafarkin suna tare ta ke, haka kawai tana zaune sai ta ji kaman muryarsa a kunnen ta yana faɗin "kiss me" har tunanin ko ta fara hauka ta ke yadda waɗannan kalmomin biyu ke sa ta jin wani nishaɗi da farin ciki...
Tana ganin wanda ya kirata mamaki haɗe da wani farin ciki ya mamayeta, sai da wayar ta kusa katsewa sannan ta ɗauka.
"Sir Najeeb shi ne sai yau?"
"Aishatu, kuna lafiya ya haƙuri?" Muryan Hajia Mama ya doki kunnen ta maimakon muryan Najeeb...
Hajia Mama na kashe wayan ta kaiwa Najeeb sanda.
"Ashe ko ta'aziya ba ka je mu su ba. Kakan matar ta kan"
"Kai Tsohuwa, ba munje gidan uncle ɗin ta ba. Miye sai mun je har Jos. Will that bring back the dead?"
Hajia ta sa ke ɗaga sanda yai gefe da sauri yana dariya...
Kaman yadda Hajia Mama ta nema kuma ta sa Daddy ya ma sa magana dole ya shirya zai je Jos. Shi sau ɗaya ya taɓa zuwa garin kuma aiki ne ya kaishi.
Ya fito kenan ya tarar da Anas da Najdah a falo su na magana.
"Kai ba na son takurawa fa, she's still in school" Najeeb ya faɗa yana hararan Anas.
Anas ya ce " an gaya ma ka ni irin ka ne da sai na zauna har 35yrs. Ai ni kafin watan shidan sabuwar shekaran nan zan angonce"
"Shege, to Baby sai ta ƙare karatu tukunna"
"Wallahi ba ka isa ba, ka san tun yaushe mu ke shan ruwan kanwa kuwa"
"Ɗan iska, to ka bi ni a hankali ko in hanaka, dama Musty yana gaba dani saboda na hana shi, ka ga idan ka yi wasa sai na bashi ita"
"Kai na a ƙasa babban yaya, mu na neman tubarrakin ku"...
Sai da su ka jima su na wasa da dariya kafin daga baya bayan Najdah ta bar falon Anas ya shiga bayanin abinda ya kawoshi.
"Najeeb, Farida ita ke da gaskiya da kai da kamfani you owed her apology"
Najeeb ya gyara zama yana sauraron sa.
"Khalidah da Alhaji Matawalle su su ka kitsa komai. The money from VESTAC inc. Alhaji Matawalle ne ya sa aka tura supported by Khalidah. Shi ya shirya yadda za a sace ma ka takardun zanen ka a kuma ɓata modelling da ka yi. On the other hand kuma Khalidah ita ta kawo shawaran a framing Farida. Duka evidences da mu ka haɗa yana nan" ya miƙa ma sa wata ƙatuwar envelope.
Idon Najeeb ya rine yai ja tsanar Khalidah da Alhaji Matawalle na ƙara shiga ran sa.
"Kai ka san wani mataki ko hukunci za ka ɗauka idan aka koma aiki ranan monday" ...
..............
Ba dan ya riga ya shirya tafiya ba da ba abin da zai sa ya tafi. Ƙusan ƙarfe uku ya isa Jos, address ɗin da Yakubu ya bashi ya bi, da tambaya kuma ya isa har layin su. Bai gama shan mamakin layin ba sai da ya isa gidan. He cant believe a irin wannan gida Farida ta yi rayuwa. Ba wai dan bai saba ganin gidaje haka ba a'a sai dan yadda Farida ke gudanar da rayuwar ta with boldness and cofidence, ba ta shayin shiga ko'ina. A ko yaushe ji ta ke dai-dai ta ke da kowa, duk daraja ko kuɗin ka kuwa.
Yaro ya kira ya ce a ma sa magana da Farida dan tun a bakin layi ya ajiye mota saboda mota ba ta shiga layin.
Ana yiwa Farida kitso yaro ya shigo wai ana sallama da Anty Farida.
"Ni kuma? Waye?"
"Bai gaya min ba"
"Ya yake" Farida ta sake tambaya tana sawa ranta kwaɗayin ya kasance Sir Najeeb ne ya zo.
Yaron ya ce " fari ne, dogo, kaman balarabe ya ke amma ya iya Hausa" ai yaro bai gama bayani ba ta tashi daga gaban Umma Binta ƙanwar Ummi da ke ma ta kitso.
"Ka je da gudu ka ce ma sa ina fitowa yanzu"
"O'o amaren zamani kenan, Farida wannan zumuɗi haka"
Ai ba ta ji me Umma Binta ke cewa ba ta riga ta shige ɗaki za ta ɗau hijabi...
Ya bawa ƙofan gidan baya yana tsaye hannayen sa duka biyu su na cikin aljihu, hankalin sa ya tafi wajen wassu yaran Birom da ke wasa a ta wajen kwata yana mamakin yadda yaran ba sa ƙyanƙyamin wajen.
Yana sanye da baƙar shirt da baƙin hoodie jacket sai baƙin jeans.
"Sir Najeeb" muryan ta ya doki kunnen sa. A hankali ya juyo yana kallon ta, ba ta wani chanja ba sai dai idon ta ya ɗan nuna rama may be saboda kuka ne dan ya san ba ta wasa da abinci.
"Ashe za ka zo, shi ne ko ka faɗa min. Mu shiga ciki"
Sai da ya ɗau minti ɗaya ya na kallon ta kafin ya bi bayanta su ka shiga gidan...
Da ke kwana na tara kenan da rasuwan duk an watse sai iyalin sa kawai. A daddafe ya gaisa da su. Kusan awa ɗaya yai a gidan saboda yadda 'yan uwa da maƙota ke zuwa gaida mijin Farida wanda yawanci gulma su ke zuwa saboda su ga mutumin da ya sa aka fasa aurenta da Rayyan, su ga ya ya ke. Sai dai kowa ya zo da Masha Allah ya ke tafiya baki buɗe. Sun ga kyau, sun ga kuɗi, sun ga aji, sun ga ƙasaita...
Lokacin da zai tafi bayan ta raka shi wajen motar sa ya ce " za'a koma aiki monday yaushe za ki dawo?"
"O'o ni Aisha Farida, dan aiki kawai za a neme ni. Ni kam dole idan na koma a chanja min matsayi ya kamata a upgrading ɗi na, na bar matsayin sakatariya"
" ki na son ƙarin matsayi ne?"
"Haba Sir Najeeb wa ya ƙi cigaba a duniya"
Bai san ya ake zuwa gai da sarakai ba shi ya sa bai zo da komai ba. Ya dai bar musu dubu ɗari a gefen ɗrinks ɗin da su ka kawo ma sa wanda ko taɓawa bai yi ba...
Har motar sa ta ƙule Farida ba ta bar wajen ba. Tana ƙissima abubuwa dayawa a ranta. Zuwan Najeeb ya sa Najeeb ya ƙara samun wani matsayi na daban a zuciyar ta...
*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......
*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
0️⃣3️⃣1️⃣
https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref
𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
*(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*
*wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi, ga mai so zai iya tuntuɓar 08137311900*
*yau na san team Najeeb sai sun min bulala😂. @team leader a ajiye tissue a kusa*
Yana hanya ta kirashi lokacin koma fita daga Jos bai yi ba. Ya saƙala bluetooth ya amsa kiran.
"Sir Najeeb shi ne har da ɗawaiyina haka. Mun gode Allah ya ƙara buɗi. Allah ya kai ka lafiya"
Amin kawai ya ce ya kashe kiran.
Da ya isa Kano yana so ya kira ta amma ya ka sa. Sai ya ɗauko wayar zai danna numbar ta sai ya fasa ya ajiye, ana huɗu da yai haka sai ga text ɗin ta ya shigo tana ma sa ya hanna da fatan ya isa lafiya.
"Na isa" kawai ya daure ya rubuta ya ma ta reply da shi. Maimakon ta haƙura a haka sai ta kuma turo da wanni text ɗin.
"Sir N mi zan taho ma ka da shi? ina son zuwa Wase gobe"
Bai san ina ne Wase ba, dan haka ya minimizing wayar ya browsing sunan nan ya gane wata ƙaramar hukuma ne a Jos.
Ya ma ta reply da "ok"
Ta sake turo wani saƙon " Sir N ba ka faɗi abinda zan kawo ma ka ba"
Ya na so ya ajiye wayar ya shareta amma zuciyar sa ta hanashi
"Kan ki" ya tura ma ta ba tareda ya gama tantance ma'anar faɗin hakan ba.
"Kan kifi? Sir N kan wani irin kifi"
Ganin reply ɗin ta ya sa shi murmushi. Ya ɗan jima kafin ya tura ma ta "Mrs Jibo sleep"
Good night kawai ta sake turowa daga nan ba ta kuma turo da wani saƙon ba. Shi ma ya ajiye wayar sa gefe ya kwanta.
.......................
Safiyar Sunday ya aika ma ta da Iliya driver akan ya je ya ɗauko ta. Ita kam tana chan tana kan haɗa kayan tsaraba da za ta zo da shi. Sai da Iliya ya kusa isa cikin Jos sannan ya kira ta ya ce ya kusa isowa.
Wani matsayi ta ke kuma hangowa kan ta idan ta koma Kano. Ya sa an kawota da mota ya kuma turo ma ta driver ya dawo da ita. Wannan karramawar sai Mrs Jibo ai...
Lokacin da su ka isa gida ana kiran sallar maghrib. Iliya ya je ga kira Friday su ka shiga da buhun dankalin turawa da ta zo da shi da kuma wata ƙatuwar jakan ghana-must-go.
Ɗakin Mom ta je dan ta gaidata ta samu ba ta nan, ta wuce ɗaki ta shirya ta yi sallar la'asar da magariba...
Ƙarfe tara ta sauko ƙasa dan ta nemi abinda za ta ci, ba komai a dining ɗin hakan ya sa ta shiga kitchen shi ma wayam. Yunwa ta ke ji dan haka ta tsaya ta girka noodles da soyayyan ƙwai, ta fito ɗauke da plate ɗin shi kuma Najeeb ya shigo.
"Sir Najeeb" ta kira sunan sa. Juyowa yai ya ganta tsaye riƙe da plate da cup
Sai da ya gama kallon ta daga sama har ƙasa sannan ya juya ya tafi. Ta bi bayan sa da baki buɗe.
A dining ta zauna ta ci abincin ta dan idan ta haura sama za ta ji ƙiwuyar saukowa, sai da ta gama ci sannan ta wuce ɗaki.
"Sir Najeeb irin ba ka ji daɗin ganina ɗin nan ba, ko sannu da zuwa babu"
Bai kulata ba hakan ya sa ta gane akwai abinda ke damun sa dan bayan bai kulatan ba fiskar sa ya nuna yana cikin damuwa.
"Sir Najeeb ba ka da lafiya ne?"
"Please stop talking" abinda ya iya faɗa kenan ya gyara kwanciya a kan gado.
Tabbas akwai abinda ke damun shi dan Najeeb ba ya bacci da wuri, sannan duk rintsi sai ya yi wanka ya sa kayan bacci kafin ya kwanta.
Kaman yadda ya buƙata ɗin, shirun ta yi tana tunanin ko me ke damun shi.
Har ta kwanta Najeeb bai tashi b, ba kuma baccin ya ke ba dan idon sa a buɗe lokacin da ta leƙa shi...
Washegari da ta shirya ta fito ne ta haɗu da Tasallah a kitchen wanda ke shaida ma ta Mom ba lafiya an ba t gado.
"Ayya ashe shiya sa jiya da na dawo na ji gidan shiru. Ya jikin ta?"
Tasallah ta ce da sauƙi. Maimakon office da ta yi niyyar zuwa sai ta wuce asibitin lokacin Iliya ya kawo Adama za ta ɗauki wassu kayan buƙatu sai su ka tafi tare.
Ta yi mamakin yadda Mom ta faɗa haka. A wajen Najdah ke cewa " tunda yanzu ke ki ke juya Big B sai ki sa ya zo ya ga Mom. Kin wani yanko ƙafa kin zo irin son a sani ɗin nan"
Farida ta kalli Najdan sannan ta kalli Mom da ke kwance tana bacci.
"Na san da cewa ba kya son ganina tareda yayan ki, amma ki sani shi ya kawo ni gidan ku ba ni na kawo kai na ba. Tun farko-farkon zuwa na ki ke ta ƙananun magana akai na, ban tanka mi ki ba. Kar ki sa na kalle ki da idon Aisha Farida dan ba za ki ji daɗi ba. Ki bini a hankali mu tafi a yadda mu ke yanzu"
Najdah ta yi tsaki, ta ɗau waya ta fara latsawa.
Farida ta fice daga ɗakin gudun kar ta fara masifa ta tada Mom daga bacci. Amma tabbas za ta ware lokacin Najdah nan ba da daɗewa ba...
Kai tsaye Najeeb constructions ta wuce sai dai da ta je office ɗinta kama baki ta yi saboda chanji da ta gani, office ɗin ta da na Najeeb ya koma kusan guda ɗaya, maimakon gini da ke tsakanin su yanzu wani tinted glass ne ya raba su wanda daga office ɗin sa yana iya hango komai a na ta office ɗin amma ita kuma ba za ta ga na sa ba.
" ba dai wannan Sir Najeeb ya ke nufi da matsayi ba"
Ba ta gama zama ba Najeeb ya shigo ran sa a ɓace. Yanzu ya fito daga board meeting.
"Sir Najeeb ashe Mom ba lafiya shi ne ba ka gaya mun ba"
"Get back to work Mrs Jibo"
Gwiwanta yai sanyi ba dai duk wani zumuɗi da zaƙalewan da ta ke yi a kan sa duk na banza ba ne.
"Noory" muryan Sabreen ya dawo da ita daga tunanin da ta ke.
Murmushi Sabreen ta yi ganin Farida a wajen. Da alama itama daga wajen da Najeeb ɗin ya fito ta fito.
Ganin Sabreen ya sa ta ma tuna da zancen ta, ita harga Allah ta manta da wata Sabreen.
"Noory, you are just taking it personal, i'm here to work"
"Kar ki sake kirana da wannan sunan. Here and anywhere else i am Najeeb to you"
Ta ɗan ji haushi saboda a gaban Farida ya faɗa. Amma ta dake ta ce "fine"
Farida ta fice daga office ɗin ta koma na ta duk da ta san daga inda ta ke su na kallon ta.
Wani yanayi ta tsinci kan ta ciki. Sabreen ta fara aiki anan, mi hakan ya ke nufi? Kenan watarana Sir Najeeb zai aiketa wajen Sabreen ko Sabreen ɗin ta ba ta saƙo dan ta kaiwa Sir Naheeb. Ba zai yiwu ba, dole ta ajiye aikin nan. Ba za ta yi aiki tana ƙarƙashin Sabreen ba, wannan cin fuska ne.
"Congratulations 'yar uwa. Finally gaskiya ta fito" muryan Anas ya doki kunnen ta.
"Wani gaskiyar?" Ta tambaya tana ƙoƙarin ɓoye damuwar ta.
Zama yai zai ma ta bayani sai ga Sabreen ta fito.
Tana ganin su ta yi wani murmushi sannan ta juya tana catwalking ta fita.
Anas ya juyo ya kalli Farida wanda itama bin bayan Sabreen ɗin ta yi da kallo.
Ya ce "asirin wanda su ka kitsa mi ki sharri ya tonu. Gaskiyar zance ta fito"
"Haba! Yaya na wani ɗan Alatsinen ne ya ke son ganin baya na"
"Wallahi Khalidah ce"
"Ban yi mamaki ba dan za ta rina"
Nan ga shiga labarta ma ta yadda aka yi gaskiya ta fito.
Da kotu za su shiga amma an settling case ɗin tsakanin Kamfani da su saboda Alhaji Matawalle ba ya so a je kotu domin ya na siyasa kuma ya na son fitowa takaran senator. Na biyu kuma Alhaji Tukur mahaifin Khalidah ba ya son wargaza alaƙar sa da Najeeb, 8% shares na shi a kamfanin shi ya san kuɗin da ya ke samu, shi ya sa shima ya zaɓi teburin sulhu.
Alhaji Matawalle zai biya kamfani taran miliyan ishirin ita kuma Khalidah za ta biya Farida miliyan biyu.
" 'yar uwa mun yi kuɗi fa. Dan Allah ayi kason da mu"
Farida murmushi kawai ta yi dan ba wannan ba ne damuwar ta.
Ranan duk wani ɗokin dawowa Kano da ta yi ta ji Kanon ya fita ma ta a kai. Da yamma bayan ta dawo Baba Sabuwa ke kiran ta akan 'yan uwan Najeeb sun kawo lefen ta yau da safe. Su kan su ba su san da zuwan ba ko karramawar kirki ba a mu su ba.
Farida kin ga kaya ki godewa Allah gaskiya domin an zuba dukiya a lefen ki. Yanzu ya za ayi? Za a kawo mi ki shi chan gidan kun ne ko ya?
"Baaba Sabuwa duk yadda ku ka yi" ta faɗi hakan ne saboda ko kaɗan maganar lefen bai sa ta ji raɗaɗin da ta ke ji ya ragu a zuciyar ta ba...
........................
Yana shigowa Daddy ya kirashi tambayar sa yai ko ya je ya duba Mom ya ce bai je ba.
"Yanzu Najeeb ka kyautawa kan ka, da girman ka da ilimin ka amma ba za ka kyautatawa mahaifiyar ka ba. Duk abinda ta yi ma ka bai kai ace tana kwance a asibiti yau kwana uku ka kasa zuwa ka dubata ba. Najeeb tsinuwa ka ke nemawa kan ka?"
Maganganun Daddy su na shiga su na fita ta ɗaya kunnen ne, saboda ba jin su ya ke ba hankalin sa ya tafi wani wajen. Jini kawai ya ke gani malale a ƙasa ga kuma gawar Aisha...
Daddy ya gama ma sa wa'azi sai Najeeb ya tashi ya fita ba tareda ya ce komai ba...
Tuƙi ya ke amma zuciyar sa na tuno ma sa abun da ya faru shekaru da su ka wuce. Duk da yanzu ya girma kuma ya san ƙaddarar Aisha ne ta zo da haka amma wannan trauma ɗin da ya dasu a ransa tun yana yaro ya ƙi sake shi...
***
Cikin Aisha na wata takwas abin ya faru. Immediately Adam ya saki Nabilah ta tattare yaranta ta bar ma sa gida. Sai dai hakan bai sa Najeeb ya dena zuwa wajen Aisha ba. Idan ya taso daga makaranta chan zai wuce sai dare ya dawo. Mom ta ma sa faɗan amma baya ji.
Ana haka sai ɗaya daga cikin ma su kula da Aisha ta yi tafiya saboda Maman ta da ta mutu. Ganin haka ya sa Najeeb ya dawo wajen Aisha da zama duk da kuwa akwai Mrs Beverly tareda ita. A kwana na uku da ya koma wajen Aisha, Mom ta zo da ƙarfin tsiya ta tafi da shi gida ta hana shi zuwa wajen Aisha. Abu da renon turawa sai ya fara maida ma ta magana akan ba ta isa ta hana shi fita ba, Ya fita da gudu.
Mom ta nemi restraining order daga kotu akan ba ta yadda ɗan ta ya je gidan Aisha ba saboda tana tunanin Aisha za ta ma sa lahani. Da ke Najeeb under 18 ne sai ya zama dole yana ƙarƙashin kulawar iyayen shi. Ranan da letter ɗin ta fito haka Mom da jami'an kotu su ka je su ka ɗauko Najeeb tareda faɗawa security ɗin gidan ko da wasa kar ya bari Najeeb ya shiga gidan.
Daren ranan yai wani mummunan mafarki akan Aisha ta mutu hakan ya sa da safe ya kira Daddy da ke Belgium a kan ya sa baki yana son zuwa wajen Aisha.
Mom ta ce indai ya na America yara za su zo wajen sa amma Yaran ta ba za su je wajen Aisha ba. Da Najeeb ya fita school bai je ba sai da ya fara biyawa wajen Aisha ya ga tana lafiya kafin ya tafi.
Yammacin ranan da ya dawo ya samu Mom tana masifa akan Aisha ta dameta da kira. Najeeb bai kulata ba sai da Najma ta dawo ta ke ce ma sa yau ta ji tausayin Aisha domin ta kira kusan so biyar amma saboda ba ta magana ba ta iya ba da saƙon da ta ke son faɗa ba. Ƙila tana son ganin ka ne.
Hankalin Najeeb ya tashi, tunda su ka raba gida Aisha ba ta taɓa kira ba. Ta kira sau biyar kam yana nufin tana cikin matsala ne. Haka ya fita da gudu ya je ya ɗau keken sa ya tafi gidan Aisha duk da kuwa Mom tana ƙwala ma sa kira akan ya dawo.
Da ya je gidan tun daga falo ya fara kiran Aisha amma ba ta fito ba ya duba Mrs Beverly a kitchen ba ta nan sai ya haura sama da gudu. Kai tsaye ɗakin Aisha ya shiga. Amma mi sai ya ji kukan jinjira, yana duba gefen sa ya ga Aisha kwance ga jini duk ya ɓata wajen. Irin jinin da ya gani sai da wani jiri ya kusa kada shi ya dafe gini na wasu mintuna kafin ya ƙarasa wajen ta yana jijjigata amma ba ta tashi ba. Cikin kuka ya je ƙasa da gudu ya kira emergency line na police...
Yana tsaye aka zo aka ɗauke gawan Aisha, duk abinda idon sa ke sa ma sa shine Mom ce ta kashe Aisha. Ranan shima asibiti ya kwana dan yana tsaye a wajen bayan ansa gawar Aisha a mota ya faɗi ya suma...
Ko da bayan autopsy na Aisha ya fito kan ba kashe ta aka yi ba, haihuwa ta yi ita kaɗai jini ya tsinke ma ta kuma rashin Mutum a kusa da ita ya sa ba a kawota asibiti da wuri ba har ta mutu.
Najeeb bai daina ganin Mom a matsayin wanda ta kashe Aisha ba. He was very traumatized a lokacin da har ta kasance baya iya bacci sai da magani. Ya jima yana visiting therapist kafin daga baya aka ce ya dawo normal amma still a hakan bai koma dai-dai da Mom ba.
Rasuwan Aisha ya sa Mom ta saduda da rayuwa, ta nemi Adam ya maidata dan ta kula da Najdah...
"She wanted her dead all along, she's evil" abin da ya faɗa kenan ya buga steering ɗin motar. Idon sa na buɗe amma duhu ya ke gani, yana ƙoƙarin saita motar ta shi wata babbar mota ta zo ta buge motar sa, motar Najeeb ta yi sama sannan ta dawo ta faɗi ƙasa...
*sorry ba Morning post gobe sai da rana Insha Allah*
*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......
*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
0️⃣3️⃣2️⃣
https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref
𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©️
*(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*
*wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi, ga mai so zai iya tuntuɓar 08137311900*
*wannan page ɗin na ki ne ke kaɗai Anty nah Surayyah. Wishing you health, wealth, peace, grace, mercy and joy amin. Allah ya ƙarawa rayuwarki ta Oga da ta yaran ki albarka amin. Happy birthday🍾🥂🎂*
Tana zaune sai cika ta ke tana batsewa, abu ɗaya ta sani shi ne ta ajiye aiki da Najeeb sannan kuma dole ta rama abinda Sabreen ta ma ta. Ba za ta bar karuwan nan ta sha banza ba.
Tun tana duba agogo tana jiran Najeeb har bacci ya ɗauketa akan Sofa...
Daddy kam bayan fitan Najeeb kiran matar sa yai su ka yi hira, da ke jikin tan da sauƙi, dan likitan ya ce za'a iya sallamarta gobe.
Ƙarfe shaɗaya na dare wayar sa ta fara ringing, daga kan gado ya sa hannu ya lalubota ya ɗara a kunne dan ko gama gane numban da ya kira bai yi ba.
Abin da aka ce ma sa ne ya sa ya tashi zaune yana maimaita Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raju'oun jikin sa na ɓari.
Ɗaukan key yai ya fita daga ɗakin da sauri duk da kuwa pyjamas ne a jikin sa...
Tunda aka shigo da shi ake ƙoƙarin tsaida jini, yadda jini ke zuba a jikin sa da ma gefen kansa ka ce duka jikin sa zai tsiyaya zuwa ɗan ƙanƙanin lokaci.
Wani na ganin Najeeb Adam Jibo a jikin ID card ɗinsa ya gane ko ɗan waye, shi ya sa aka kira numban Daddy...
Yadda Daddy ke jinsa gani ya ke ba zai iya jira har Iliya ya taso daga BQ ya zo ya kai shi ba duk da an hana shi tuƙi da dare saboda idon sa.
Yana fitowa yana ƙwala sunan Malam Aminu maigadi akan ya buɗe gate, yadda ya ke kiran, shi kan sa Maigadi sai da ya tsorata... Ikon Allah ne kawai ya kai shi asibitin lafiya amma ƙila da shi ma hatsarin zai yi.
Yana zuwa aka ce har lokacin likitoci na kan sa. Jikin sa rawa ya ke bai iya zama ba yana safa da marwa zuciyar sa cike da addu'o'i. Tsabar rikicewa ko fitowa da wayar sa bai yi ba daga mota...
Anas ƙarfe huɗu da rabi na asuba aka kira shi, ya fito daga banɗaki kenan ya yi alwala ya ji kira kafin ya ɗauka ta katse. Ganin Daddy sai hankalin sa ya tashi, lokaci guda zuciyar sa ta raya ma sa ƙila Mom ce ta rasu. Duk da kuwa jiya da ya je dubata ya ga jikin ta da sauƙi sosai, to amma mutuwa ko da ciwo ko ba ciwo sai an tafi. Yana ƙoƙarin sake kiran Daddy kiranshi ya kuma shigowa ya ɗauka da sauri.
Maimakon Daddy ya ce ma sa wani abu ne ya samu Mom sai yai ma sa maganar Najeeb, Najeeb da su ka rabu lafiya ƙalau jiya.
"Daddy ya rasu ko?" Ya faɗa hawayen da su ka cika idon sa su na gangarowa.
Daga ɓangaren Daddy ya ce " a'a, yanzu likitocin su ka fito amma bai farfaɗo ba har yanzu"
Yai hamdala tareda cewa gashi nan zuwa...
Zuwa ƙarfe bakwai na safe asibitin ya cika da 'yan uwa. A wannan lokacin ne Uncle Sulaiman ya sa aka maida Daddy gida saboda ya chanja kaya.
.....................
Farida ba ta farka ba sai ƙarfe biyar lokacin da alarm ɗin ta yai ta ruri ba kakkautawa. Da ƙyar ta sa hannu ta jawo wayar ta katse alarm ɗin. Mafarki mai daɗi ta yi, itada Najeeb su na zaune a wani lambu, kanta na kan cinyar sa yana wasa da gashin ta.
" I love you Aysherh" ya faɗa idon sa cikin na ta.
"I love you too Sir Najeeb"
Hannun sa ya sa ya ɗan matse bakin ta ya ce "ba na hana Sir Najeeb ɗin nan ba"
"Sorry my champ"
Ta ɗan ɗago kanta ta kissing goshin sa sannan kumatun sa sannan hanci. Ganin ta tsaya ya sa yatsa ya nuna lips ɗin sa.
Ta girgiza kan ta. Ya ɗan yi ƙanƙan da ido alamar tausayi. Murmushi ta yi tareda haɗe bakin su...
Ta tashi jiki a mace ta shige banɗaki, wannan mafarki da ta yi ya sa ta sassauta jin haushin sa da ta ke ji.
Lokacin da ta zo gaban madubi, kallon kanta ta yi ta fara gwada maganan da za ta yiwa Najeeb ta yadda zai tabbatar ran ta ya ɓaci ya kuma ɗauki maganarta serious.
A hankali tana fari da ido ta ce "Sir Najeeb, gaskiya idan Sabreen za ta yi aiki a kamfanin ka to ni zan ajiye aiki na"
Ta yi tsaki ta ce ba haka bane barin sake. Wannan karan ta haɗa rai ta ce "Sir Najeeb zan ajiye aiki na"
Sai ta kwaikwayi muryan sa ta ce " good for you"
"Good for you kawai za ka ce min? Ka na tunanin idan na ajiye aikin akwai wanda zai iya yi ne?"
Da muryar sa ta ce "dayawa ma"
" Sir Najeeb, Allah ni kaɗai ce za ka iya jura. Ba wanda zai iya juran faɗan ka. Kai ba mace ba amma sai shegen mita"
"Aysherh" ta ji muryan sa a bayanta. Da sauri ta juya amma ba kowa. Ta rufe ido tana tuno kiss ɗin su na ranan...
Saboda ta tsara ba za ta koma aiki ba shiya sa da ta gama azkar ɗin ta ta sauko dan ta taya Adama aiki.
Tana saukowa ta haɗu da Daddy wanda shigowar sa kenan, ganin sa sanye da kayan bacci ga kuma damuwa shimfiɗe a fiskar sa ta yi tunanin ko wani abu ne ya samu Mom.
"Daddy ya jikin Mom" ta faɗa cike da tararrajin mi zai ce
"Alhamdulillah da sauƙi 'ya ta"
"Lah ba mu ma gaisa ba" ta faɗa tana tsugunnawa ta na mi shi ina kwana.
Tausayin ta ne ya kama Daddy. A yadda ya ga Najeeb ɗazu zuciyar sa ta karaya. Yanzu idan Najeeb ya rasu wanni hali Aisha za ta shiga? Auren da bai wuce sati shida ba.
"Aisha ki shirya yanzu, idan na fito za mu je asibiti Najeeb ba lafiya"
Dum ƙirjinta ya buga "Najeeb ba lafiya, mi ya same shi?. Allah sarki ashe shi ya sa bai kwana a gida jiya ba." Tambayar da ke yawo a kanta kenan.
Amma duk yadda aka yi rashin lafiyar Najeeb mai tsanani ce dan kuwa Daddy ba zai damu har haka ba idan minor abu ne.
Komawa ɗaki ta yi dan ta ɗau gyale da jakar ta...
Iliya ne ya ke jan su, cikin motar shiru ka ke ji. Ganin yadda Daddy ke ta yawaita faɗin Lahaula Wala Ƙuwwata Illah Billah lokaci zuwa lokaci sai Farida ta ƙara tsorata da lamarin. Ba dai Najeeb ya rasu ba ne, idan Najeeb ya rasu ina za ta sa kan ta...
Sai da su ka isa asibitin sannan Daddy ya ce " 'ya ta ina so ki kwantar da hankalin ki dan Allah. Insha Allah komai zai zo da sauƙi, Najeeb ya yi hatsari jiya da dare"
Dafe ƙirjinta ta yi da sauri lokaci guda kuma numfashin ta ya tafi hucin gadi na 'yan wasu sakanni.
Hawaye ne su ka fara zirya a idon ta su na gangarowa.
"Ba kuka za ki ma sa ba, addu'a za ki ma sa Aisha"
Tafiya su ke amma ƙafafuwanta ji ta ke kaman ba ajikin ta su ke ba, she's not feeling them ko kaɗan.
Har su ka isa wajen su Anas hawaye ta ke. Yadda ta ga an cika wajen sai hankalin ta ya ƙara tashi.
Daddy ya tambayi ɗanuwan sa ko likitan ya ce wani abu. Uncle Sulaiman ya ce sun ce ƙarfe tara za a ma sa CT-scan aga mi ya hana shi farfaɗowa dan sun ce su na zargin ƙwaƙwalwar sa ta kumbura ne.
Anas ya raka Farida gallery na theater room ɗin inda ta hango Najeeb kwance ansa ma sa life support system. A lokacin ta fashe da wani irin kuka mai taɓa zuciya. Anas ya ɗan dafa ta ya ce " dan Allah ki dena kuka addu'a za ki ma sa abinda ya ke buƙata kenan"
"Mutuwa zai yi ko?, mutuwa zai yi tun ban nuna ma sa yadda na ke son shi ba ko?, Ya Anas ba zan iya jure rashin sa ba"
Shi ma dai Anas daurewa kawai ya ke amma ya karaya da halin da ya ga abokin na shi....
Zuwa yamma an tabbatar mu su da cewa akwai jini da ya daskare a ƙwaƙwalwar Najeeb wanda idan ba acire ba ƙwaƙwalwar za ta yi ta kumbura ne har kuma ta iya jawo ta dena aiki gaba ɗaya wanda ƙarshen zancen dai mutuwa ce.
Abun ka da ma su dukiya tuni aka kira Dr Sajid Usman Abdallah dan ya zo ya jagoranci aikin da za a ma sa. ( ga wanda ba su san Dr Sajid ba an bar ku a baya 😂 ku karanta Mutum mugu ne. Yana nan a wattpad, za ku ga yadda Angon Zaytunah da Naziha ya sha goggonmayar rayuwa. Yai fama da zafin kishin Zayty da kuma rashin kamun kan ta. Sannan ya zo yai dakon soyayyar Ziha yarinyar da shekara ashirin da biyar cur ya ba ta, But aka ce love is blind☺)
Ranan Alhamis aka saka aikin kuma har lokacin Najeeb is in comatose. Kwana biyun nan Farida ta yi su ne akan sallaya. Kaso biyu cikin uku na daren sun tafi a sallah da roƙon Allah ne sauran kaso ɗaya kuma ya tafi a kuka da tunani.
Mom ma da aka sallamota wani tashin hankalin ta shiga dan sai da ta suma lokacin da ta je ta ga ɗan ta kwance a asibiti rai a hannun Allah...
Sun yi aikin awa shaɗaya akan Najeeb kuma Alhamdulillah an cire jinin da ya daskare ba matsala.
Sai dai Dr Sajid ya ce akwai yiwuwar Najeeb zai cigaba da zama cikin coma na tsawon lokaci. Amma, ba abinda ya fi ƙarfin addu'a...
Wata ɗaya kenan da ta wuce, wata ɗaya na kuka da roƙon Allah, wata ɗaya da tun ana cewa zai iya farfaɗowa gobe har aka zubawa sarautar Allah ido.
An tabbatar da case ɗin Najeeb ta shiga PVS (persistent vegetative state) yanzu kam sai randa ya farfaɗo kawai amma ba maganar ana tsammanta zai tashi nan kusa.
Duk wani wanda ya san Najeeb Adam Jibo sai da su ka tausaya ma sa. Shi ba mai bacci ba, shi ba mutuwa ba. Yana nan yana numfashi amma gashi a kwance ba abinda zai iya yi.
Wannan wata ɗayan da a ka yi Farida ta zama certified nurse a wajen kula da Najeeb. Tunda aka dawo da shi ɗaki na musamman da aka gyara saboda shi Farida ta koma kwana da shi. Duk yadda Daddy ya hana ta ƙi. Ita ke goge ma sa jiki safe da kuma yamma, har turaren sa ta je ta kwaso tana fesa ma sa. Ta ce Sir Najeeb ba ya son ƙazanta kuma yana son ƙanshi.
Zuwa yanzu ta rage yawan kuka da ta ke. Tana asibiti yanzu 24/7 duk da kuwa an ce ba sai an zauna da shi ba tunda ba wai tashi zai yi ya buƙaci abu ba kamar normal mai jinya. Idan ka ga ta je gida to ta je ɗauko wassu kaya ne. Kullum da safe da kuma dare sai Daddy da Mom sun zo sun duba ta tareda duba Najeeb da fatan cewa ko da na ɗan ƙaramin lokaci ne zai buɗe idon sa.
Farida ta chanja ta zama silent. Ko Sabreen ne ta zo duba Najeeb ba ta kulata, fita ma ta ke ta ba ta waje har ta gama tsiyarta ta tafi. Wanda iya ka daɗewar ta minti ishirin ne...
Yau ma ta na kwance gefensa tana ɗan shafa gashin sa da ya fara tohowa saboda lokacin da za a masa aiki aske gashin aka yi yai ƙwaranƙwal.
Taɗi ta ke ma sa kamar yadda ta saba yi.
"Sir Najeeb a ina ma mu ke"
Ta ɗan yi murmushi ta ce "yawwa na tuna, ranan da na fara jin wani abu gameda kai shine ranan da aka zo aka rescueing na mu daga hannun su Joseph. Ban ganewa zuciyata ba tun daga ranan. Ko da na dawo office kullum idan na kalli idon ka sai na ji wani abu ya taso min daga chan ƙasan zuciya ta, shi ya sa ko ina magana da kai na ke avoiding haɗa ido da kai. Ko da yaushe ina ƙoƙarin yaƙi da zuciyata saboda wani sabon al'amari da ya dinga taso min da shi gameda kai ba mai yiwuwa ba ne, na dinga tabbatar wa kaina ka fi ƙarfi na, na dinga nunawa kai na, Najeeb Adam Jibo ya fi ƙarfin Aisha Farida Salihu. Amma ka san me? Bayan ƙaddarar aure ta shiga tsakanin mu sai...."
Sallamar Anas ya katseta daga labarin da ta ke wa Najeeb.
Sai da su ka gaisa ta ke tambayar sa ya aiki?
" 'yar uwa abubuwa fa ba daɗi. Riƙe kamfani kaman Najeeb constructions sai ma su zafi irin Najeeb ɗin. Kin san Allah daga jin zancen halin da Najeeb ya ke sai kowa ya fara fidda asalin halin sa. Aka dena bawa aiki mahimmanci ana sako-sako da duk wani ayyuka da ake yi. Can you imagine wai anyi board meeting akan wai ba su yarda na jagoranci kamfani ba"
Farida ta zaro ido " to amma Ya Anas ba kai ke riƙeta ba idan Najeeb ba ya nan?"
"Haka ne amma kin san na 'yan kwanaki ne wannan. Najeeb bai taɓa tafiyar da ta wuce sati biyu ba. Yanzu kuma wata ɗaya da sati uku kenan ba ya nan. Farida abubuwa sun fara ja baya. Ba ni da zafi kaman Najeeb hakan ya sa kowa fara abinda ya ga dama"
"Amma ka gayawa Daddy?" Ta tambaya tana mamakin wannan al'amari, mutuwa Najeeb yai ba amma har an fara juya ma sa baya, Mutane kenan
"Mun tattauna da Daddy kuma ya amince da shawarar da na kawo, ya ce mu yi magana da ke ɗin"
Ta ɗan gyara zama dan ta fahimci zancen sosai.
"Farida riƙe Najeeb constructions ba zai tafi dai-dai ba sai iron man kaman Najeeb. Ki na da zafi, za ki iya taka kowa sannan za ki iya shugabanci. Kin zauna da Najeeb kin ga yadda ya ke gudanar da al'amuran sa i'm sure kin tsinci ilimin shugabanci a tareda shi. Farida ki koma aiki, wannan karan ba matsayin sakatariya ba sai matsayin CEO"
"Allah ya kiyaye Ya Anas. Wani zance ne wannan. Saboda ni ce na kawo son shugabanci duniya sai mijina na asibiti ba lafiya sai na tsallakeshi na tafi wajen aiki" ta goge hawaye ta ce " ina nan da shi anan har ranan da zai farfaɗo"
"Farida na san ki na so ki kasance tareda Najeeb, amma ba kya ganin kina da hakki akan kula da dukiyar sa. Barin gaya mi ki halin da mu ke ciki yanzu. Kamfanin da ta ke da major shares bayan Najeeb tana so ta janye hannun jarinta ko kuma mu mu sake sayar ma ta da kaso arba'in a ciki. Kin san mi hakan ke nufi? Yana nufin su na so su mallaki kamfanin ta ƙarfi, zai zama Najeeb 35% ne kawai na shi a ciki kuma kinga kamfani ta bar hannun Najeeb. Ke 'yar kasuwa ce kin san yadda za ki yi ki kawo cigaba a wannan kamfani ki kuma ceceta. Ni Architect ne ban da wani ilimi mai zurfi a wannan fanni. Najeeb da ki ke gani bayan karatun Engineering da Architecture da ya yi yana da degree a fannin kasuwanci sannan yana da certificates dayawa a ɓangarori ma su yawa musamman leadership. Hakan ya sa komai ke tafiya ma sa dai-dai"
"Ya Anas ba zai yiwu ba. A nemi wani ko cikin cousins ɗin Najeeb amma ban da ni. Ba zan iya ba"....
"Farida......"
.................................
Wata baƙar Marcedez benz ce ta shigo Kamfanin Najeeb constructions. Lokacin da motar ta tsaya an kai kusan minti biyu kafin aka buɗe ƙofa. Wata haɗaɗɗiyar mata ce ta fito daga ciki ta owners corner. Tun daga takun ta ka san mace ce mai aji da kuma girma. Kai tsaye ta shige kamfanin security ɗin wajen yana mata good morning ta amsa ma sa ta hanyar ɗaga hannu.
Anas ne ya nufota yana gaisheta lokacin da ta iso top floor ɗin. Tare su ka jera su ka wuce conference hall ɗin inda za ayi board meeting.
Kujeran da ta zauna an rubuta CEO a jiki waje ne da Najeeb ke zama lokacin yana da lafiya. Waje ne da bayanshi ba wanda ya taɓa zama a wajen idan ana taro haka.
Sai da ta ja numfashi ta sauke sannan ta ce *"suna na Aisha Farida Salihu, Mrs Najeeb Adam Jibo kuma acting CEO Najeeb constructions har zuwa lokacin da miji na zai samu lafiya ya dawo"*
Ta kalli fuskokinsu mai cike da tarin tambayoyi ta ce *ko da me ja?*....
*Tantarantarantaran. Daga secretary sai CEO wannan ƙarin matsayi har haka @team Farida kuna da aiki a gaban ku. @team Najeeb, sorry Najeebullahi ya tafi hutu, sai kun ganshi kawai dan nima ban san ranan dawowar sa ba😀*