" Waike kin rufe kofar ne, saboda karna dawo, to ai na daɗe da dawowa kin makare cikin tollet, jawota yayi ta faɗo jikinsa, mannata yayi da jikin sa tare da jawo bargo ya rufe su, cikin raɗa yake cemata.
" kifa kwantar da hankalin ki, ni babu abinda zan miki, bacci kawai zamuyi.
shuru Nasreen tayi tare da laɓewa s jikinsa, hanun sa khabeer yasa ya zagaye ƙugunta, a haka bacci ya ɗauke su, suna jin bugun numfashin juna, da asuba khabeer shine ya fara buɗe idon sa, jin kiran Sallah, tashi yayi tare da ɗauro alwala, sannan ya dawo ya tashi Nasreen, buɗe idonta tayi da ƙyar tsabar baccin dake cikin idon nata, sallah khabeer yace ta tashi tayi sannan shima khabeer ya fice zuwa masallaci.
Daƙyar Nasreen ta samu tayi Sallah idonta na rufewa, yau ko karatun da ta saba yi bata samu damar yiba ta koma ta kwanta, khabeer kuwa saida yayi karatu cikin masallacin, har alfijir ya keto kafin ya shigo cikin gidan, ɗakin Nasreen ya nufa, tana Bacci ya kwanta gefen ta tare da jawota jikinsa, ahaka shima Bacci ya ɗauke Sa.
Ƙarfe goma da rabi dai-dai Nasreen ta buɗe idonta, ganin ta, tayi kwance bisa ƙirjin khabeer, yana Baccin sa Hankali kwance, haka kawai Nasreen ta tsinci kanta da ƙare masa, kallo sagensa dake kwance luf shiyafi ɗauke mata hankali, hanun ta, ta ɗaga da niyar shafo sajen sai kuma tayi saurin sauke hanun ta, tashi tayi da kyar jin har yanzu kasan ta, yana mata zafi duk da dai ba sosai bane, tollet ta shiga tayi wanka tare da brush, sannan ta fito ɗaure da towel ta rufe jikinta da hijab, mirror ta nufa, ta shafe jikinta da mayuka, batayi wani makeup ba, powder kawai ta shafa sai lipstick, sannan ta feshe jikinta da turare, kayan da suka sayo da SADIQ ne, Nasreen ta dauko Black ɗin doguwar riga, wanda tasha stone, yafa ɗankwalin tayi akanta sannan ta fice zuwa falo, da kanta Nasreen tayi mopping din falon, turaren wuta ta dauko ta saka cikin falon sannan ta shiga ɗakin khabeer nanma ta gyara shi, tasa turaren, tsaf Nasreen ta gyara part ɗin nata take kuwa ya ɗauki ƙamshi lungu da saƙo, ɗakin nata shima ta gyara shi, sai gadon da khabeer yake kwance a kaine kawai bata gyara ba.
Kitchen ta shiga da niyar ɗaura musu breakfast, sai dai kuma duk iya dube duben ta, cikin kitchen ɗin bata samu wani Abunda ya danganci abinci ba, haka dole ta fito daga kitchen, tana ƙare masa kallon barnar kuɗin da akayi cikin kitchen ɗin.
Ɗakin khabeer ɗin ta koma tuno cewa bata sauya masa bedsheet ɗinsa, ba, ta shiga domin sauya masa.
Shiko khabeer a hankali ya buɗe idonsa, wayan ya gani babu Nasreen, tunani yayi ko tollet ta shiga, wani irin ƙamshi ne, ya bugi hancinsa, wow wonderful, wannan wani irin turareni khabeer ya furta, dandai shi tunda yake cikin gidan bai taɓa jin irin wannan ƙamshi mai daɗin shaƙa ba, cikin gidan, sai dai ƙamshin airfresh da Zuhura ke amfani dashi, tashi yayi ya nufo nasa ɗakin da niyar yayi wanka, turus yayi ya tsaya a falon yana ganin ikon Allah, yanda aka gyara falon, sai tashin ƙamshin turaren wuta da yake yi, yasan dai su Asabe basa gidan, sun tafi ƙauyen su hutu, bare yace sune sukayi wannan aikin, to kodai Nasreen ce, ya ayyana cikin ransa, ɗakinsa ya shige bisa mamakin sa, sai yaga Nasreen tana ta famar kintsa masa ɗakin.
Sunan ta yaki, ta ɗago kanta ta kallesa, kafin ta maida kanta ƙasa, ƙara sowa yayi kusa da ita tare da cewa.
" Meyasa zaki fito kiyi wannan aikin bayan kinsan ba jin daɗin jikin ki kike yiba, wannan aikin ai ya miki yawa, akwai ƴan aiki wanda zasu miki so ba sai kin wahalar min da kanki ba.
Murmurshi Nasreen tayi tare da mayar masa amsa da cewa.
" A'a bana bukatar ƴan aiki, domin kuwa ni aiki ba wani abu bane mai wahala a wajena, na saba dashi sosai, dan haka ni zanyi aikina da kaina bana bukatar taimakon Wani.
Murmurshi khabeer yayi cikin jin daɗin yanda Allah ya masa sauyi da mace ta gari cikin kanƙanin lokaci, Allah shine abun godiya, shigewa tollet yayi ya barta tana faman shimfiɗa, bedsheet.
Ko kafin khabeer ya fito daga wanka Nasreen ta gama gyara ɗakin tayi ficewar ta, falo.
Jin buga ƙofar da Nasreen taji ana yine yasata nufar wajen, buɗe kofar tayi, sai taga Nana da Khadijah, suna tsaye riƙe da basket a hanun su, murmurshi Nasreen tayi musu tare da musu sannu da zuwa, faram faram Nasreen ta karɓe su, suna wasa da dariya, basket ɗin suka ajiye sukace gashi inji momma breakfast ne, tace a kawo muku, godiya Nasreen ta musu, sun ɗan juma suna hira har khabeer ya fito ya samesu, sosai yaji daɗin yanda yaga ƴan uwan sa, sun sake a cikin gidan nasa, suna hira, saɓanin Zuhura da kullum take cikin ɗaure musu fuska.
Da zasu tafi har compaunt ɗin gidan Nasreen ta rakasu, Daniel ya maida su, sannan Nasreen ta dawo cikin gidan.
Alhamdulillah yanxu Rayuwa tayiwa Nasreen da khabeer daɗi, sosai khabeer yake jan Nasreen a jikin sa, tun tana ɗari-ɗari dashi, yanxu harta sake dashi, wani irin shaƙuwace ta shiga tsakanin su, wanda ko aiki ma daƙyar Nasreen take barin khabeer ya fita, yau ki manin watan Nasreen biyu cikin gidan khabeer, yayin da ta fara zuwa makarantar ta, inda take karantar Low, gidan khabeer fah ya samu sauyi hatta su Daniel sunsan Ogan su yayi sabuwar amarya, tsabar mutuntawa da Nasreen ke musu, su Asabe kuwa yanxu basa girki cikin gidan domin kuwa Nasreen itace take yin kayan ta, iya kacin su da aiki sharar tsakar gidan ne, shima kanshi khabeer tunda ya auri Nasreen bai ƙara zuwa gidan su yaci abinci ba, na matarsa yake ci, wata rana Nasreen da khabeer suna zaune a falo da daddare, suna hira, yayin da Nasreen tayi filo da kafar khabeer, khabeer ne ya nisa yace.
" Baby ina son fah gobe zanje gidan su ABOKIYAR ZAMAN KI ZUHURA zamuyi magana maybe ta dawo jibi, tunda daman na daɗe da maida Auren mu, so ina son gobe zaki shirya da safe, tunda baki da lectures, zamuje gidan yari mu gaishe da Momy Sarah tunda kinga bata sanki ba, ya kamata kuga juna, daga nan kuma zan shige dake, gida wajen momma, so idan na dawo daga gidan su Zuhura zan biyo na ɗauke ki, sai mu dawo gida koh.
Wani irin bugawa ƙirjin Nasreen yayi, jin khabeer ya ambaci sunan Zuhura, wani irin kishin Zuhura taji cikin ranta, amma tsabar iya duniyanci da Nasreen tayi da kuma ƙara samun cikakkiyar wayewa da itayi yasata nunawa khabeer tama fishi son dawowar Zuhura.
" Shikenan Abban Allah ya kaimu goben, ya kuma dawo da ummin junior gidanta lfy, goben idan muje gidan momma, ina son zamu dawo da junior, gidan nan, ya kamata ace shima yanxu yana tare damu.
" Murmurshi khabeer yayi tare da shafo fuskar Nasreen Yace.
"An gama Baby na, duk abunda kikace haka za'ayi kinsan yanxu na zama mijin tace, sai yanda kikayi dani.
Dariya Nasreen tayi tace.
" Kardai ka zugani kasa kaina yata girma na manta cewa mu biyu ne, a wajen ka.
Dariya shima khabeer yayi haka suka ta hiran su, gwanin ban sha'awa.
Yau Nabiya tun safe take kwara amai ga hajijiya dake damunta, ta rasa inda zata saka Ranta, SADIQ duk ya fita hayyacinsa, ganin farin cikin sa kwance babu lafiya, gyalen ta, ya ɗauko mata, ya tallafe ta, har mota, asibitin Dr Abubakar bukar suka nufa, binciken doctor na farko ya gani cewa Nabiya nada shigar ciki, har tsawon wata ɗaya.
Murna wajen Sadiq ba'a magana, dubu hamsin ya ajiye doctor yace goron Albishir.
Tun a mota SADIQ ya dannawa khabeer kira yana ɗauka ya fara ce masa.
" To Uban ƴan gori yaudai gori ya kare, tunda an kusa fara kirana da Daddy.
Dariya khabeer yayi, sosai kafin yace............
Kuyi hkr da wannan Wlh yau ina busy ne, shiyasa nace da babu gara ko kaɗan ne, na muku typing.
*Share*
*And*
*Comments*
*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*
*(Ummu Nasmah ce)*
[1/24, 3:14 PM] MAKAMAR KAINUWA 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏
⛏⛏⛏⛏
*SARA DA SASSAKA*
*(Baya Hana Gamji)*
*Toho*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
🌳🌳🌳🌳
*Story And Writing*
*By*
*Rasheedat Usman*
*(Ummu Nasmah)*
🤳🏻
*08147537180*
*(MAKAMAR KAINUWA)* 👸🏻
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*d̸e̸d̸i̸c̸a̸t̸e̸d̸ t̸o̸*
*Aྂlྂlྂ wྂrྂiྂtྂeྂrྂsྂ oྂfྂ kྂaྂiྂnྂuྂwྂaྂ iྂnྂaྂ yྂiྂnྂkྂuྂ iྂrྂiྂnྂ sྂoྂsྂaྂiྂ dྂiྂnྂ nྂaྂnྂ aྂlྂlྂaྂhྂ yྂaྂ kྂaྂrྂaྂ mྂaྂnྂaྂ bྂaྂsྂiྂrྂaྂ tྂaྂrྂeྂ dྂaྂ hྂaྂzྂaྂkྂaྂ*
___________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________
*P*•••••••7️⃣4️⃣ to 7️⃣5️⃣
" Ehh lallai abu yayi kyau, shege na waje na, ashe daman haka ka iya aiki, kace bugu ɗaya ka yiwa ƙwallon ka, ta faɗa raga, kallon Nasreen yayi yace kinji ƙaninki, SADIQ har ƙwallon sa, ta faɗa raga, ya kusa zama Daddy.
Murmurshi Nasreen tayi, tare da farin cikin samun ƙaruwa da ƴar uwarta tayi.
" Kwarai kuwa, kaga ai na fika ƙoƙari tunda gashi ni an gani a ƙasa, kaga daga yau ka fara kirana da Daddyn boy, ka kuma cewa matarka ni ba surikin ta, bane.
Dariya khabeer yayi
Suka cigaba da magana da Sadiq cikin wasa da dariya, Kafin ya masa fatan Alkairi, tare da samun ƴan biyu, kashe wayar khabeer yayi ya shiga cikin ɗakinsa, tare da fitowa da key ɗin mota, tare da kwalin waya riƙe a hanun sa, zama yayi kusa da Nasreen tare da kama tafin hanun ta, ya ajiye mata, makullin motar tare da ajiye mata shima kwalin wayar bisa cinyarta, Yace.
" Nasreen wannan key ɗin mota ne dana saya miki tare da waya, ina sane tun shigowar ki, gidana ban baki waya ba, har kika fara zuwa school, ba komai yasa nayi haka ba, illah kawai na gwada hakurin ki, naga zaki iya Zama Babu waya, duk da kina ganin mata da yawa cikin makaranta, waɗanda basu kaiki ko nace basu kai mijinki shiba, sai kuma naga haƙurin ki, domin kuwa hakan ya nuna min cewa ke bakya daga cikin matan da suke ganin abu hanun wani suce dole suma sai sunyi, ina fatan zaki gafarce ni, bisa hanaki waya da nayi da wuri.
Wow Nasreen wani irin daɗi taji cikin ranta domin kuwa ta kwan biyu tana ƙaunar waya, buɗe kwalin wayar tayi tana dubata cikin xunuɗi, waya ce mai kyau ƙirar Iphone 11 mai shegen kyau wacce zatayi dubu ɗari Uku ko huɗu, kallon khabeer tayi tace.
" Na gode sosai Abban junior Allah ya saka da Alkairi, ya ƙara buɗi, naji daɗin wannan kyautar sosai, sai dai ita wannan key ɗin motar ne, nake ganin kamar........
Da katar da ita khabeer yayi ta hanyar cewa.
" Kike ganin me zakiyi da ita tunda baki iya mota ba koh?
Murmurshi Nasreen tayi ganin khabeer har ya gano Abunda take son cewa, girgiza masa kai tayi alamun ehh.
" To karki damu nida kaina zan fara koya miki motar, idan bana nan kuma, daniel zai koya miki, so karki damu da wannan.
Murmurshi Nasreen tayi ta rungume khabeer tana masa godiya cikin murna.
Washe gari da safe Nasreen Bayan ta tashi tayi dukkan ayyukan ta, na cikin gidan, ta shiga kitchen ta haɗa musu breakfast, tare da yiwa Momy Sarah girki na musamman, ferfesun kaza ta mata, sannan ta mata sakwaran doya da miyar ƙwai, sai drink da ta mata, kunun Aya tare da zoɓo, sai kuma ta dama mata kunun shinkafa mai rai da lfy wanda yasha.
Kusan goma da rabi Nasreen ta gama aikin girkin, sannan ta jera nasu breakfast ɗin bisa daining, na Momy Sarah kuwa, a Basket ta shirya shi, ɗakin ta taje ta shirya, ta fito cikin atampar ta, java Holand green color, ɗinki ya mata kyau sosai a jikin ta, feshe jikinta tayi da turare, sannan ta nufi ɗakin khabeer, yana kwance yana shan Baccin sa domin kuwa baida time ɗin tashi, gefen sa, ta Zauna cikin kwarewa wajen iya tashin miji a Bacci, a hankali take hura masa iska cikin kunnen sa, yayin da hanunta ke shafa kansa, a hankali ya buɗe idonsa, ƙamshin jikin Nasreen shine ya fara dukan hancinsa, lallausan murmurshi ya mata tare janyo ta, ta faɗo jikinsa, murmurshi itama Nasreen tayi tace.
" Abban junior, kamata yayi ka tashi, fah ka shirya, kasan wajen zuwan mu, da yawa ina son muje har gidan su Nabiya, mu dubata.
Murmurshi khabeer yayi tare da cewa.
" Ba yauba zuwa gidan SADIQ, ki bari sai nan da kwana biyu, yanxu tashi ki haɗa min ruwan wanka.
Tashi Nasreen tayi ba musu ko jayayyan cewa sai taje gidan Nabiya, tayi banɗaki, ta haɗa masa ruwan wankan, kusan karo sukaci khabeer zai shiga ita kuma Nasreen tana fitowa, jawo hanun ta khabeer yayi yace.
" Muje ki taya ni wankan koh Baby na.
Dariya Nasreen tayi tare da cewa muje to, sanda khabeer ya shiga cikin tollet ɗin, Nasreen ta kwace hanun ta fito da gudu tana cewa
" Naƙi wayon salon ka sani wani sabon wanka.
Murmurshi khabeer yayi yace.
" Zaki shigo hanuna, zan rama ai.
A falo Nasreen ta zauna jiran fitowar khabeer.
Bai wani juma ba, ya fito cikin shirin sa, daining suka zauna, bayan sun gama breakfast ɗin ne, khabeer yacewa Nasreen taje ta ɗauko hijab ɗinta su wuce, yana so zai shige office idan ya kaita gida, bayan sun dawo daga prissing.
Nasreen bata wani juma ba, ta fito sanye da hijab har ƙasa, abun ya burge khabeer sosai, domin kuwa yana mungun takaicin ganin matar Aure sanye da gyale a jikinta, ta fita unguwa, basket ɗin Nasreen ta dauka suka shige gidan yarin.
Khabeer bai wani sha wahala ba, wajen ganin Momy Sarah, a office ɗin shugaban gidan yarin suka zauna aka fito musu da Momy Sarah.
Allah sarki rayuwa, Momy Sarah tayi baƙi ta rame har wani tsufan wahala tayi, tana ganin khabeer saita fashe da kuka.
Tausayin ta ya kama khabeer sosai ganin yanda rayuwar Momy Sarah ta koma, zama tayi ta fuskanci khabeer tace.
" khabeer kaine tafe yau, gaskiya naji daɗin zuwan ka, ya mutanen gidan Kowa yana lafiya dai koh.
" Kowa yana lafiya, Momy, Momy kin rame sosai, ki rage yawan damuwa, dan Allah damuwar dai bata da amfani, ki ɗauki ƙaddarar ki, Momy dan Allah.
Murmurshi mai ciwo Momy Sarah tayi, kafin tace.
" Khabeer ko bansa tunani a cikin zuciyata ba, dole nayi baki na rame, Babu abinci mai kyau, khabeer Babu walwala, haka kullum muna cikin bauta, khabeer taya bazan rame ba khabeer.
Shuru khabeer yayi, domin maganar Momy Sarah gaskiya ce, tabbas rashin walwala na saka rama.
Katse masa shurun sa, Momy Sarah tayi da cewa.
" Wacece wannan khabeer, kodai itace amaryar taka da Daddyn ku yake sanar dani kayi ne?
" Itace Momy, sunan ta Nasreen, Nasreen ga Momy Sarah, mahaifiyar Khadijah da Khalid.
Sai a lokacin Nasreen ta gaishe da Momy Sarah, amsawa Momy Sarah tayi cikin sakin fuska, tare da sawa Rayuwar Auren su, albarka, nasiha sosai Momy Sarah tayiwa Nasreen, *(🤔 ikon Allah wai yau Momy Sarah ce da nasiha, lallai duniya tafi gabaruwa iya jima Allah yasa mu dace)*
Basket ɗin da Nasreen ta taho dashi ta miƙawa Momy Sarah, khabeer sun juma sosai suna ganawa da Momy Sarah, domin kuwa shi kansa shugaban prissing ɗin bai isa bawa khabeer time ba, cikin prissing ɗin domin kuwa yana da right dinda zai iya zuwa ya gana da koma waye cikin wajen.
" Momy mu zamu wuce, zamu bar miki basket ɗin, duk sanda Khalid ko daddy suka zo zasu taho dasu, dan Allah Momy karki saka damuwa cikin ranki.
Cikowa idon Momy Sarah yayi da hawaye tace.
" Zan rage insha Allah khabeer, na gode sosai da wannan ziyarar da kuka kawo min, khabeer idan kaje gida kacewa fatuma dan Allah ta kulamin da yara na, mussaman Khadijah itace ƙarama tana bukatar kulawa.
" Momy karki damu, insha Allah su Khadijah baza suyi kukan rashin ki ba, momma zata kula dasu kamar yadda zata kula da Nana.
" Shikenan khabeer na gode sosai, Nasreen na gode Allah ya baku zaman lafiya, yayiwa Rayuwar Auren ki, albarka.
Da amin Nasreen ta amsa, sannan sukayi Sallama, suka tafi Momy Sarah na jin kamar ta bisu.
Cikin mamaki da al'ajabi Nasreen taga khabeer yayi hanyar gidan Nabiya shida yace ba yanxu ba, kallon sa tayi cikin murmurshi tace.
" Abban junior, naji daɗi sosai, gaskiya dan harna cire rai.
Murmurshi khabeer yayi tare da cewa.
" Lura da hakan da nayi yasa, nace bari na kawoki, Baby na, domin ina son ganin ki, cikin farin ciki koda yaushe, yana faɗin hakan ne ya danna hom a kofar gidan SADIQ ɗin.
Da sauri mai gadin ya fito ya buɗe get, ɗin khabeer na ƙoƙarin shiga, mai gadi ya dakatar dashi da cewa, ai oga Sadiq basa nan sun fita shida Madam.
" Oh shit khabeer yace tare da cewa okey ba damuwa, juyawa yayi yanaa cewa Nasreen.
" Amma dai gaskiya wannan ɗan iskan surukin naki ya cika yawo, bari muje gida na kirasa naji inda yaje ɗan iskan gari.
Murmurshi Nasreen tayi tace.
" Daman Allah ya ƙaddara bazamu haɗu ba, ina ga gobe muyi clear da ita cikin school.
Allah ya kaimu khabeer yace, sannan suka cigaba da hiran su, har suka shigo cikin gidan nasu.
A falo suka taradda momma zaune tana kallo, Babu kowa sai ita kaɗai, sallama sukayi momma ta amsa tana musu lale maraba, zama Khabeer yayi tare da cewa.
" Momma ina yaran naki, naganki ke ɗaya cikin gidan.
" Suna school, tun safe sai 5:00pm zasu dawo, Nasreen sannu da zuwa kece yau tafe cikin gidan namu.
Murmurshi Nasreen tayi tace.
" Ehhh nice momma, daga ƙasan da take zaune tace, na sameku lfy momma.
" Lfy lau Nasreen, cewar momma, yau zamu wuni kenan.
" Ehh momma, sai dare zan tafi.
Tashi khabeer yayi yana cewa.
" To momma bari na tashi na tafi tunda ni kin manta dani cikin gidan.
Murmurshi Momma tayi tace.
" Naga ƴata ne, ina zan tuna dakai, yawwa khabeer jiya Daddyn ku ke sanar dani cewa, gobe su Kubra zasuje maka kususun matar ka Zuhura.
" Ehhh Momy haka ne, insha Allah gobe Zuhura zata dawo.
" Gaskiya banso ka dawo da Zuhura cikin gidan kaba, domin kuwa Hankali zata ɗaga maka cikin gidan ka, kana zaune lfy.
' a'a Momy hakan bazata kasance ba insha Allah, komai normal zai tafi.
" To Allah yasa, sai ka dawo Allah ya kiyaye hanya.
Da amin khabeer ya amsa yana kallon Nasreen ƙasa-ƙasa ganin yanayin ta, ya sauya jin an ambaci sunan Zuhura.
Kafin ya fice daga cikin gidan.
Nasreen tun tana ɗari-ɗari da momma harta sake da ita, wunin Ranar Nasreen itace ta yiwa momma girki, har su Nana suka dawo daga school, Nasreen ta shiga cikin su, Babu nuna girman, suka cigaba da harkokinsu.
Khabeer tun 4 na yamma yake gidan su, Zuhura suna shan hirar yaushe gamo, sosai khabeer ya jawa Zuhura kunne game da gidan sa, Zuhura dai ta amince da duk wani sharaɗin khabeer, sanda ya tashi tafiya, dubu ɗari biyu ya ajiye mata, yace koda wani hidimar da zatayi.
Ƙarɓa Zuhura tayi tare da yiwa khabeer godiya, karo na farko kenan a wajen khabeer daya taɓa jin yayiwa Zuhura kyauta ta gode masa, har tsakar gidan nasu wajen motar sa, Zuhura ta rakasa, tana ɗaga masa hanu yaja motarsa ya fita.
Gidan su ya koma ɗaukar Nasreen sosai yaji daɗin yanda ta sake cikin kannen sa, suna hira, ita kanta momma cewa take sai yanxu tasan tayi suruka, sanda Nasreen suka zo tafiya momma turaruka masu tsadar gaske ta bata guda uku, tare da mata albarka.
" Godiya Nasreen tayiwa momma sosai, tare da alkawarin da su Nana suka mata kan cewa ranar monday suna, zuwa gidan nata, kafin suka nemi hanyar gidan su.
A gajiye Nasreen ta shigo cikin falon tare da zubewa saman kujera alamun ta gaji.
Murmurshi khabeer yayi tare da cewa.
Raguwa kawai kafin ya shige nasa ɗakin.
Nasreen ta ɗan juma cikin falon kafin itama ta nufi nata bedroom ɗin, shirin bacci tayi tsaf kafin ta shige ɗakin Baccin nasu ita da oga khabeer, a daren Ranar Nasreen sun rayashi da Angon ta khabeer sosai.
Washe gari da safe Nasreen tunda ta farka da asuba bata maida bacci ba, saboda tana da lectures by 9, part ɗinta ta gyara, har ɗakin mijin ta, sannan ta ɗaura breakfast, bata yi wani Abu mai nauyi ba, kasancewar bata da ishashen time, ruwan tea kawai ta dafa wanda yasha na'a-na'a da ɗanyar citta da kanan fari, sai kwai data soya, sai kuma ta tafasa Indomie, a gaggauce tayi breakfast ɗin sannan tayi shirin school, ɗakin khabeer ta koma ta samu yana bacci, peper da biro ta ɗauka ta masa rubutu tare da ɗaga wayarsa ta ajiye ƙasansa ta fice zuwa ɗakin junior.
Yana zaune shi kam yana shirin school, kallon Nasreen yayi yace.
" Good morning Momy.
"Morning junior haw Are You.
" Fine momy, harkin fito, wai da so nake mu fita tare idan an ajiye ni school sai a wace dake, tunda kuna gaba damu.
" To kaga tunda Allah yasa ka shirya muje kayi breakfast sai mu wuce, da sauran time, kaine ma nake ganin kamar kayi let.
Fita sukayi tare junior yayi breakfast, sannan suka wuce school, daniel shine ya sauke su.
Nasreen darect Class lectures ɗinsu ta shige, sai wajen 11 suka fito daga lectures ɗin.
Department ɗin su Nabiya Nasreen ta shige, ta samesu ita da khady suna zaune, sai famar chart suke, Zama Nasreen tayi gefen su tare da cewa .
' Barka da hutawa Momy Nabiya ashe kuma mun sami karuwa, jiya muje gidan ku, nida Abban junior, mai gadin ku yace kun fita.
" Ehh munje gidan Hajiya, kin kusa Zama Momy dai zakice yar rainin wayo, kinga mubar wannan maganar, kinga wannan yarinyar ta kusa dake ta nuna khady, faɗa zaki mata, wai khamal ne yake sonta, tana so tana kaiwa kasuwa, to Wlh kibar jan ajin hanka karya tsinke.
Dariya Nasreen tayi tace, to Hajiya Khadijah kinji Abunda, ƙawar ki, take gaya miki kibar jan Ajin haka, to meye ma, aibun khamal, naga dai yana da nutsuwa da hankali.
Mtss kema dai Aunty Nasreen kina kula iskancin Naby, yo to da ita maiya hanata son khamal ɗin tunda ita ya fara cewa yana so.
Dariya sosai Nabiya tayi sannan tace.
" Aini time ɗin akwai yayanki cikin zuciyata, shiyasa.
Dariya itama khady tayi sannan tace.
" Zanyi tunani akansa naga wani matsayi ya kamata na basa.
" Dako ki Kyauta cewar Nasreen sun juma suna tadi kafin daniel yaxo ya ɗauki Nasreen, sanda suka biya ta makarantar su junior suka dauke sa, sannan sukayi gida.
Yau dai Allah yayi dawowar Zuhura cikin gidan ta, tare da Aunty kubra suka shigo cikin gidan, sai ƙanwar mahaifiyar Zuhura, Ummu Kulsum, duk sun watse sunbar Aunty kubra, tace ita sai ta
Ta jira khabeer yazo Kafin ta koma.
Ƙarfe takwas kuma dai-dai khabeer ya shigo, cikin gidan, part ɗin Nasreen ya shiga ya sameta Zaune ita da junior sai shiririta suke yi, murmurshi khabeer yayi tare da kaɗa kansa ya zauna gefen su, yana cewa.
" Wato kudai hankalin ku ya tafi can wata uwa duniya bakwa jin sallamar mutum.
Murmurshi Nasreen tayi tace.
" Sannu da dawowa, muna game bamu ji shigowar kaba.
Shima junior sannu da dawowa yayiwa mahaifin nasa.
" Ina kuwa zaku jini hankalin ku ya tafi wata uwa duniya, am kina sane da cewa Zuhura ta dawo koh.
Dam gaban Nasreen ya buga cikin ƙarfin hali da danne ƙishin ta, tace.
" Ka dai cemin zata dawo yau, amma bansan har ta ƙaraso ba, tun ɗazu na gama girki aida na aika musu, amma yanxu ma, bata ɓaci ba, akwai sairan abincin bari na bawa junior saiya kaimusu.
" Okey ba damuwa bari ni na shiga ciki na rage kayan jiki na.
A fito lfy kawai Nasreen tace masa kafin ta tashi ta shige kitchen ɗin ta, fitowa tayi da abinci cikin basket tacewa junior gashi yakai part ɗin mamansa, ƙarba junior yayi yana murna, yayi part ɗin Zuhura.
Zama Nasreen tayi ta kwantar da kanta bisa kujerar falon tana jin wani Abu mai ɗaci cikin ƙirjin ta, cikin ranta take cewa, shikenan fah yanxu mu biyu muke da khabeer.
Fitowa khabeer yayi, ya zauna tare da kwantar da kansa bisa kafaɗar Nasreen, Yace.
" Baby tunanin me kike haka.
" Babu komai, kawai kaina ke ciwo, ya aikin.
" Alhamdulillah yanxu kinga ƙarfe tara, ki tashi muje part ɗin Zuhura, ina son magana daku.
Dato Nasreen ta amsa masa, sannan ta shiga ɗakin ta, ta ɗauko hijab ɗinta, suka shiga part ɗin Zuhura.
A falo suka samesu har Aunty kubra, zama Nasreen tayi tare da gaishe da Aunty kubra,
Cikin sakin fuska, Aunty kubra ta amsa har tana zolayar Nasreen.
Gaishe da Zuhura Nasreen tayi.
Cikin mamaki da al'ajabi, fuskar Zuhura A sake ta amsawa Nasreen gaisuwar ta, Babu wani haɗa rai.
Aunty kubra ce tacewa junior ya tashi ya tafi ɗaki ya kwanta dare yayi, sannan ta maida dubanta ga Zuhura tace.
" To Zuhura gashi dai Allah ya dawo dake gidan ki, sai dai ina son na miki faɗa akan abu ɗaya zuwa biyu.
Zuhura ki rage kishi cikin ranki, ki zauna lafiya da mijinki da *ABOKIYAR ZAMAN KI* domin kuwa babu Abunda yafi zaman lafiya daɗi, ki Rungumi mijinki da ɗanki, kishiya dai ba part ɗin ku ɗaya ba, bare kice zaki ke ganin ta hankalin ki yana tashi, idan har tayi wani Abu da bai dace ba, ki mata faɗa a matsayin ki na babba.
Sai Abu na biyu, ki gyara zamantakewar ki da dangin mijinki, mussaman mahaifiyar mijinki, kiyi mata biyayya iya iyawar ki, ki dage da addu'a Allah ya rage miki kishi cikin ranki.
Wannan shine abinda nake son tunatar dake.
Nisawa Zuhura tayi tace.
" Aunty kubra insha Allah, zan gyara, ko a yanzu naga darasin rayuwa, insha Allah bazan ɗauki Nasreen a kishiya, a matsayin ƴar uwa zan ɗauketa, haka kuma dangin mijina, zan gyara zamantakewa ta, dasu, tabbas basuji daɗin zama dani ba, amma ina da tabbacin yanxu zan gyara.
Kallon Nasreen tayi tace.
Nasreen ki yafe min abunda na miki zuwan ki cikin gidan nan, kuma ina fatan zamu zauna lafiya.
Murmurshi Nasreen tayi tace.
" Insha Allah Aunty nikam ta wajena babu wata matsala, zamu zauna lafiya insha Allah.
" Alhamdulillah Aunty kubra tace, tare da yiwa itama Nasreen ɗin faɗa, shima khabeer yayi musu nasu nasihar, kafin ya tashi ya raka Aunty kubra, daniel ya maida ta gida.
Koda ya dawo har bakin part ɗin Nasreen ya rakata yana rarrashin ta, kiss ya mata a goshin ta sannan ya wuce part ɗin Zuhura.
Nasreen tunda ta shiga ɗakin ta, take jin zuciyarta, Babu, Baccin ma kasawa tayi, domin kuwa ta saba kwana jikin khabeer, gashi ya tafi ɗakin matarsa ya barta cikin kewa.
Daƙyar bacci ɓarawo yayi nasarar sace Nasreen.
Da asuba kuwa da murɗa Nasreen ta tashi ga amai da take ta kwarawa, sai jiri, gagara fitowa tayi ta gyara ɗakinta, bare kuma girki.
Tashin khabeer da safe yaga sauyi sosai, domin kuwa kamshin daya saba tashi yaji ya doki hancinsa yau babu shi, haka kuma ɗakin babu gyara, fitowar sa, ma falon su Asabe ya samu suna girki kamar yadda suka saba mata, tsuka khabeer yaja tare da shigewa yayi part ɗin Nasreen ko zai samu Abunda zaici.
Shigar sa part ɗin Nasreen, yaga ko gyara part ɗin batayi ba, cikin mamaki ya dubi daining nanma wayam Babu komai, ɗakin Nasreen ya nufa da sauri, kwance ya sameta a ƙasa, sai kwara amai take, da sauri ya karasa ya rikota jikinsa tare da mata sannu, ɗagata yayi ya kaita tollet ya sake mata ruwan ɗumi, a kanta, ya wanketa tas sannan ya naɗoto a towel, ya ajiye ta saman gadon ta.
Gyara wajen da tayi aman yayi sannan yaxo ya ɗauki doguwar riga ya zura mata tare da hijab, yana mata sannu, ya kamota suka fito waje da niyar zuwa asibiti.
A motar ya ajiye ta, sannan ya shiga part ɗin Zuhura da sauri, tana zaune ya sanar da ita cewa Nasreen bata da lafiya zasu Hospital, Addu'ar samun lfy Zuhura ta mata, har bakin motar ta biyo khabeer tana yiwa Nasreen sannu da jiki.
Gwajin farko doctor ya gane Nasreen na ɗauke da ciki na tsawon wata biyu, sosai khabeer yayi murna, koda suka dawo gida sun sami Zuhura zaune cikin part ɗin Nasreen tana jirar dawowarsu ita da junior, koda khabeer ya sanar da Zuhura Nasreen na ɗauke da ciki, bata nuna ɓacin ranta ba, saima farin ciki da tayi.
Su SADIQ ma sunji labarin samun cikin Nasreen, sosai sukayi murna, har zuwa sukayi shida Nabiya suka wuni.
Alhamdulillah rayuwa yanxu ta yiwa khabeer daɗi domin kuwa, matansa sun haɗa kansu, Zuhura ta ajiye komai ta Rungumi Nasreen hanu biyu, yanxu Nasreen ta fara gyarawa Zuhura abubuwan ta, yayin da ta ke koya mata girki, ko wani girki tare suke shiga kitchen suyi, cikin Nasreen dana wata huɗu khabeer ya biyawa Zuhura da momma da Umma mahaifiyar Zuhura, da kuma Ammi kujerar Hajji, ita kuma Nasreen yace sai Allah ya sauƙe ta, lfy zasuje tare dashi.
Kowa yayi farin ciki da wannan abun Alkairi da khabeer yayi, haka kuma momma tayi murna sosai da hadewar kan Nasreen da Zuhura.
Ranar asabar Nasreen da Nabiya suka shirya da niyar zasu ƙauyen su, zasuyi sallama da Ammi kafin su wuce Hajji, shirye shirye sosai khabeer yayiwa Nasreen na zuwa kauyen su, kayan abinci ma dasu zannuwa da shaddodi, wajen mota guda wanda zasu kai tsaraba.............
Mu haɗu daku a next page wlh na gaji.
*Share*
*And*
*Comments*
*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*
*(Ummu Nasmah ce)*
[1/27, 6:20 PM] MAKAMAR KAINUWA 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏
⛏⛏⛏⛏
*SARA DA SASSAKA*
*(Baya Hana Gamji)*
*Toho*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
🌳🌳🌳🌳
*Story And Writing*
*By*
*Rasheedat Usman*
*(Ummu Nasmah)*
🤳🏻
*08147537180*
*(MAKAMAR KAINUWA)* 👸🏻
*بسم الله الرحمن الرحيم*
🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚
Deducated to All fan's of Sara da sassaqa.
___________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________
*P*••••••••7️⃣6️⃣ to 7️⃣7️⃣
Nabiya itace ta biyowa Nasreen ta gidan ta, cikin Nabiya ya fito sosai domin kuwa, yanxu cikin ta, wata bakwai, da SADIQ baiso Nabiya taje ba, yaso ace saita haihu, amma Nabiya tace ita ina, dole sai taje sunyi Sallama da Ammin ta, Da daniel suka tafi, ƙarfe huɗu na yamma suka shiga cikin RUGAR ARƊO,
Da sauri naji Nasreen na cewa daniel ya tsayar da motar, gefe daniel yayi parking, da fitowa Nasreen tayi domin gaskatar da Abunda idanunta suke gane mata, tabbas kuwa mamace, cikin bola sai tsince-tsince take, ta fice hayyacinta, idan ba kasanta farin sani ba, bazaka taɓa cewa ita bace, nufar wajen Maman Nasreen tayi cikin sanyin jiki, Nabiya da taga da gaske Nasreen fah wajen Mama zata nufa, ta fito itama da sauri tasha gabanta tana Cewa.
" Ina kike ƙoƙarin zuwa haka, da sauri.
Muni Nasreen tayiwa Nabiya da Bolar da mama ke ciki tace.
" Kina nufin kice min baki gane Mama ba, mamace fah wacce take uwa a garemu, wacce mukayi rayuwa a hanun ta, Nabiya itace fah take rayuwar bola.
Taɓe bakin ta Nabiya tayi tace.
" Saime dan mamace, ni Wlh ba Uwata bace, domin kuwa da uwata ce, da bata azabtar da rayuwata, wacce rayuwa mukayi a hanun ta banda rayuwar wulaƙanci da tozarta, Rayuwar Bola Kuma yanzu ma ta farata, ki rufawa kanki asiri da Abunda yake cikin ki, ki raba kanki da zuwa wajen mahaukaciya, danko saita illata ki, ita ko a jikin ta.
" Hmm Nabiya kenan, koma me Mama ta mana ya riga da yawuce, ya kamata kibar tunashi, kamata yayi ki ramawa duk wanda ya miki sharri da alƙairi, zanje wajen Mama koda kuwa zata kasheni, domin kuwa ni har gobe ina ɗaukar Mama a matsayin uwar da ta haifeni, dan haka ki bani hanya na wuce, tunda ke baki da zuciya mai kyau.
Shuru Nabiya tayi, yayin da maganganun Nasreen suka ratsa jikinta, cikin sanyin jiki ta kaucewa Nasreen daga hanya, shi kanshi daniel da yake tsaye gefe baisan wacece Mama ba, ya tausayawa halin da take ciki.
Ƙarasawa Nasreen tayi wajen Mama, ta sunkuya, cikin cikowar hawaye dake ƙoƙarin zubowa daga idanunta tace.
" Sannu Mama.
Bata kulata ba, saima kallon ta, da tayi tana dariya tare da miƙomata wani ƙwano mai tsatsar gaske, sai a lokacin hawayen dake idanun ta, sukayi nasarar zubowa, ta miƙa hanu ta karɓi kwanon ƙarasowa Nabiya tayi, ta dafa kafaɗar Nasreen tace.
" Mama bata da hankali a jikin ta, wanda zata saurareki, ki tashi mu tafi.
Tashi Nasreen tayi hawaye na zuba cikin idanunta, suka shiga cikin mota, a ƙofar wani gida mai kyau ginin zamani sukayi parking, kallon daniel Nabiya tayi tace.
" Yaka tsaya anan kuma, mu ƙarasa mana.
" Nan ne gidan naku Madam.
Zaro ido sukayi Dukansu biyu, cikin haɗin baki sukace.
" Gidan mu kuma, wani gidan namu, da yake kewaye da zana.
" Shine dai, Madam ku shiga za kuji koma menene.
Shiga sukayi, cikin gidan cikin al'ajabi da mamaki. Aikuwa Ammi suka tarar zaune tana tsinkar karkashi, Yayin da wata matashiyar budurwa, take mata shara, da sallama suka shiga cikin gidan, murmurshi ɗauke fuskar Ammi ta amsa.
Zama sukayi gefen Ammi Nasreen ce tace.
" Barka da gida Ammi, da fatan mun sameki lafiya.
" Lfy lau sai Alkairi, sannun ku da zuwa.
Yawwa Ammi cewar Nabiya tare da gaida ta, itama wannan budurwa zuwa tayi ta gaishe dasu Nasreen.
Cikin rashin hakuri Nabiya tace,
" Ammi ya naga gidan nan ya sauya ya koma ginin zamani, Baba ne yayi sabon gini.
Murmurshi Ammi tayi, itama cikin mamaki tace.
" Wai daman bakuji labarin wannan ginin ba?
" Ehhh wlh Ammi ba muji ba, gaskiya.
" Ikon Allah cewar Ammi, to mijin Nasreen dai shine yayi wannan ginin, Kuma ya kwana biyu dan zaikai wata huɗu, har wuta da Ruwa na soler yaja mana wajen guda shida cikin RUGAR Nan, sai ko albarka ake masa tare da Nasreen kunga harda mai mana wanke wanke da shara ya ɗauko, ni nayi tunanin ma, ya sanar daku.
Zaro ido Nasreen tayi, tace.
" Ko kaɗan wlh Ammi bai sanar dani ba, amma gaskiya ya kyauta, Allah ya saka masa da Alkairi, gashi ma ya biya miki Hajji.
" Ehhh wlh, nidai gaskiya Babu Abunda zance da khabeer sai Allah ya saka masa da Alkairi, ya ƙara masa sabon buɗi, tabbas ya nuna min ƙauna, tun kafin ya Auri ƴata, ya kasance suruki gareni.
Nabiya ce tace,
" Ammi naji daɗi sosai, khabeer ya kyauta, gaskiya bamu da bakin da zamuyi masa godiya sai dai Addu'a.
Nasreen ce tace.
" Ammi Baba baya nan ne.
" Yana nan yaje gidan Goggo, baima juma da fita ba.
Ammi da yaranta sunsha taɗi wunin ranar kayan da suka taho dashi kuma daniel ya nemi yara aka jibgesu cikin, ɗaki ɗaya dake cikin gidan.
Baba kuwa bai shigo gidan ba sai sakaliyar la'asar, cikin murna da ganin mahaifin nasu suka gaisa, sai kuma Nasreen ta kawowa baba zancen Mama.
" Baba yanxu dan Allah haka za'a bar mama cikin rayuwar Hauka, sai kace wacce bata da gata, gaskiya Baba ya kamata a nemawa Mama magani.
Nisawa Baba yayi kafin yace.
" Nasranatu, daman kinbar maganar salamatu, abunda ta shuka, shine take gurbewa, kinga kuwa kowa yaci ladar kuturu, saiya masa aski.
' a'a Baba bai kamata ake tuno Abunda ya wuce, gaba ya kamata mu kalla ka sakawa duk wanda ya maka sharri da alƙairi wannan shine ake kira jin ƙai, idan ban manta kaine kamin wannan huɗubar Baba.
" Hakane Nasreen tabbas nine, sai dai ina son ki sani cewa ni banida kuɗin da zan iya kashewa salamatu na magani, domin kuwa hanuna bai cuɗi bayana ba, su Kuma masu maganin yanxu kuɗi suke buƙata.
" Tabbas kana da gaskiya Baba, ni zan biya duk wani kuɗin maganin da za'a yiwa Mama, karka damu da kuɗi Baba, neman lafiyar mama shine a gaban mu, jakarta Nasreen ta ɗauko, tare da fito da rafar kuɗi wajen dubu ɗari tace gashi Baba, wannan kuɗin Abban junior ne ya bamu shi nida Aunty Zuhura, a fara amfani dashi, a ɗauko mai maganin, kafin nan.
Karɓa Baba yayi tare da yiwa Nasreen albarka cikin rayuwar ta, ita kanta Nabiya ta jinjinawa, Farar zuciya irin na Nasreen, wacce ta mata sharri ta saka mata da Alkairi, danko wlh ita ko kuɗi sun mata yawa gara ta, zubar dasu, akan tayiwa Mama magani.
Washe gari da safe, su Nasreen suka shirya da niyar cewa zasu gidan Goggo daga nan zasu biya gidan mai gari, wajen ƴar gwal daga nan kuma zasu wuce gidan su Indo.
Sun sami Goggo tana zaune, kan taburmar ta, cikin farin ciki Goggo ta tarbe su, bayan gaisuwa ne, Goggo, saita fara kuka, cikin tashin hankali Nasreen tace.
" Goggo lafiya kike kuka.
" Dole nayi kuka yaran nan, idan na tuna da cin mutuncin dana muku, gashi Allah ya muku sakayya, Kuma wlh duk sharrin salamatu yasa na muku haka, ku yafeni dan Allah, mussaman make Nabiya da mukayi sanadiyyar barinki rugar nan.
Murmurshi Nasreen tayi tace.
" Goggo ai komai ya wuce mun yafe ki, Allah ya yafe mana gaba ɗaya.
Godiya Goggo tayi musu, kafin suka ta taɗin yaushe gamo, sai da azahar suka bar gidan Goggo inda Nasreen ta ajiye Goggo dubu ashirin, itama Nabiya dubu goma ta bata, gidan mai gari suka yi.
A sunkuye suka sameta, sai zabgar wanki take, ga kuma tsohon ciki haihuwa ko yau ko gobe, dakyar ma take tafiya, gashi tayi baƙi ta rame, wankin ma da gani ba nata kaɗai bane zai kai na mutum Uku, sallama Nasreen sukayi, ɗago kanta Ƴar gwal tayi, sam bata gane su Nasreen ba, sai da sukayi magana.
" Nasreen kune tafe, sannun ku da zuwa, tun jiya ai naji labarin zuwan ku, mu karasa ciki.
Shiga sukayi cikin ɗakin nata, yayin da yaran gidan sukayi ca a kansu suna kallon su, gaisawa sukayi kafin Nabiya tace.
" Ƴar gwal kece haka, kike wanki Abunda bakya yi, wani irin bauta kike haka, kinga kuwa yanda kika rame.
Kuka ƴar gwal tasa cikin kukan take ce musu.
" Haka nake fama kullum, nike wankin junguɗo dana mahaifiyar sa, duk wani aikin cikin gidan nan nice nake yinsa, ga duka da nake sha hanun junguɗo duk sanda yasha ya bugu, mutanen garin nan suna cewa alhakin kune yake binmu nida mahaifiyata, kuma tabbas haka ne muddun baku yafe mana ba, alhakin ku bazai barmu ba, cikin kuka ta ƙarasa maganar.
Nasreen da tayi shiru, tana tausayawa halin da ƴar gwal take ci, kafin tace.
" Mun yafe muku, Kuma insha Allah Mama zata samu Lafiya, ki cigaba da haƙuri, a gidan Auren ki, insha Allah komai zai wuce, jarabawa ce, kuma insha Allah zaki cinyeta.
" Na gode sosai Nasreen Allah ya saka da Alkairi, na gode.
Sanda suka tashi tafiya, dubu goma Nasreen ta bawa ƴar gwal, sannan suka wuce gidan su Indo, abun haushi Nasreen bata samu Indo ba, wai taje rugar Abba tauɗo garin kakanun ta, Nasreen taji haushi sosai, sai sako ta bari tace a bawa Indo idan ta dawo, Atampopi ne, kala shida anyi ɗinki dai-dai jikin Indo, sai dogin riguna, sannan suka fito sukayi gidan su.
Kwanan su Nasreen uku cikin rugar, Baba kaf ya rabar da kayan Abincin dasu Nasreen suka kawo, Mama ma, an kira mai magani, ya kamota tare da sa mata mari, aka adana ta, a wani ɗaki, ana mata magani, randa suka cika sati ranar suka dawo cikin Gombe, da tarin tsarabar ƙauye.
Nabiya suka fara sauƙewa kafin sukayo gidan, IPS khabeer, babu kowa cikin gidan, sai masu gadi, cikin mamaki Nasreen ta leƙa part ɗin Zuhura, shima ta gansa kulle, to ina sukaje ta ayyana cikin ranta, nata part ɗin ta nufa, tasa key ɗin dake hanun ta, ta buɗe, duhu baƙiƙƙirin dakin, ƙoƙarin nemo wajen wuta take ta kunna sai taga an kunna hasken ɗakin tare da cewa
" Happy birthday to you !! Happy birthday to you.
Ware idanun ta, Nasreen tayi ganin khabeer da Zuhura sai junior tare dasu Asabe.
falon nata kuwa an masa ado da boloon da wasu abubuwa masu sheƙi, dariya tayi cikin farin ciki ta tafi da gudu ta rungume khabeer, juyi khabeer yahau yi da Nasreen yana.
" Happy birthday to you my angel.
Dariya Nasreen keyi sosai, kafin khabeer ya sauƙeta taje ta rungume Zuhura.
Itama Zuhura dariya tayi tace happy birthday to you, duk dama kin manta da auntyn ki, kikaje kika rungume miji, kega ƴar miji daɗi, ko Kunyar ɗanki junior bakyaji koh.
Dariya Nasreen tayi, tace.
" Kai Aunty duk fah murna ne ya cika min ciki.
Dariya sukayi duka, kafin suka yanka cake, bayan su Asabe sun fita ne, suka zauna suka khabeer tsakiyar su, cikin alamun gajiya Nasreen tace wash nagaji Wlh.
Dariya khabeer yayi cikin zolaya yace.
" Oh Sarkin raki, wani gajiya kikayi, ba wani aiki kikayi ba, kinje a mota kin dawo a mota, tsabar raki kice kin gaji.
Kafin Nasreen tayi magana Zuhura ta riga ta ta hanyar cewa.
" Kaji Abban junior da wata magana, aidole momyn junior ta gaji, kasan masu juna biyu basu cika son zaman takura ba.
Dariya Nasreen tayi tace.
" Yawwa Aunty faɗa masa dai ko zaifi gane yaren ki.
Magana khabeer zaiyi Zuhura tayi saurin rufe masa bakinsa da hanun ta, tace kinga momyn junior maza tashi kije na haɗa miki ruwan wanka, ki samu kiyi kixo kici abinci, sai ki samu ki huta.
Haka kuwa akayi Nasreen wanka taje tayi sannan ta fito suka ci abinci, Bayan sun gama cin abincin ne, khabeer ya dubi matan nasa, cikin ƙaunar su, Yace.
" Alhamdulillah da farko ina mai godiya ga Ubangiji daya haɗa min kan Matana, wanda basa zaman kishi, sai Zama na Amana da yarda da juna, gaskiya ina jin daɗin hakan sosai, sannan ina muku Albishir da cewa, insha daga ku babu wata, na rufe babin Aure cikin rayuwata, saidai kuma na gidan Aljanna wato hurul'aini, sai kuma Albishir na biyu da nake son na muku shine, na buɗewa Zuhura babban super market a nan cikin babbar kasuwa, mai suna *ZUHURA SUPER MARKET* ke kuma Nasreen na buɗe miki gidan man fetur da kuma Oil zuwa gas mai suna *mrs Khabeer Oil and gas* wanda na yanke shawarar cewa zan dawo dasu Baba cikin garin Gombe, yaxo ya shugabanci wannan gidan man.
Rasa bakin magana su Nasreen sukayi cikin farin ciki da murna, sosai suka godewa mijin nasu tare da masa fatan Allah ya ƙara masa buɗi, miƙawa kowa takarda yayi mai ɗauke da shaidar ya mallaka musu.
Ranar wata talata da daddare Nabiya ta tashi da naƙuda, SADIQ bai wani ɓata lokaci ba, yayi Hospital da ita kafin ya kira Hajiya a waya ya sanar da ita, sosai Nabiya tasha wahala wajen haihuwa, inda cikin ikon Allah da asubar ranar Laraba ta haifi ƙaton Yaron ta, na miji mai kama da ubansa sak, Nasreen da taji labari, sassafe suka tafi ita da Zuhura da khabeer, sai ɗaga Yaron Nasreen take tana juyashi, Hajiya ce tace.
" Saura ke Nasreen, kema Allah ya sauƙe ki lfy, cikin kunya Nasreen ta amsa da Amin.
Ammi ma taxo ta, kasancewar sun dawo cikin Gombe da zama, Baba na kula da gidan man Nasreen.
SADIQ kuwa sai rawar kai ake an samu Yaro, karfe uku na yamma suka sallame su, suka dawo gida.
Da Baba yaso ɗauko Goggo daga ƙauye taxo ta zaunawa Nabiya, sai dai Babu Halin hakan kasancewar tana kula da Mama wajen bata magani, kuma alhamdulillah yanxu Mama ta fara samun sauƙi.
Ranar suna Yaro yaci sunan *NURUDDEEN* marigayi, sosai Nasreen da Ammi suka ji dadin karan da SADIQ ya musu, aiko Yaro yaga gata wajen Nasreen da khabeer, ita kanta akwati Uku tayi ɗaya cike yake da kayan baby ɗaya kuma da Atampopi da less, sai ɗaya kuma kayan shafe-shafe na jarirai, shima khabeer ba'a barsa a baya ba, wajen bajinta.
Shiko SADIQ ba'a magana Abunda yayi, cikin farin ciki da annashuwa aka watse daga taron sunan.
Rayuwa yanxu tayiwa kowa daɗi itama Mama ta samu lfy ta kuma roƙi gafarar su Nasreen, tare da Ammi, amma Baba yace shi sam bazai maida ta gidan saba, anyiwa baba roƙon duniya amma yaƙi, haka ya bawa, Mama takardar sakinta, taci gaba da rayuwar ƙauye.
Ammi kuwa, da momma sunje sunyi aikin hajjin su, lfy sun dawo sai fatan Allah ya amshi ibada, ranar dasu momma suka dawo a ranar Nasreen ta tashi da nata naƙudan, cikin dare suna kwance da khabeer sai taji kamar ana mintsinin ta, a jikinta tun tana daurewa, har haƙurin ta, ya ƙare domin kuwa yanxu bayanta ke mata ciwo gadan-gadan tashin khabeer tayi cikin tashin hankali, kallon yanayin ta, da khabeer yayi ya gane cewa haihuwa ce, baiyi ƙasa a gwiwwa ba, ya ɗauke ta tare da kiran Zuhura a waya yace taxo Nasreen Babu lfy, bayan Zuhura taxo itace ta haɗa duk wani kayan da mai haihuwa take buƙatar su,, sai asibitin Baba didi, cikin ikon kuwa Nasreen bata wani juma ba, ta haifi yaranta biyu kyawawan gaske mace da namiji, Zuhura Itace ta fara riƙe yaran a hanun, sai kuma taji cewa itama tana sha'awar haihuwa, ƙarbar su khabeer yayi yayi musu kiran sallah a kunnen su, tare tauna dabino ya samusu a bakin su ya kuma basu ruwan zamzam, tare da musu addu'a, sanda aka gamawa Nasreen komai aka fito da ita ɗakin hutu sannan suka kira kowa suka sanar dasu, take kuwa asibitin ya cika da ƴan uwa da abokan arziki, kowa na murnar samun twins ɗin da akayi, Nabiya ma, da little Nuruddeen, ba'a barsu a baya sunxo sunga yara, daman shi Sadiq baya gari yana Abuja.
Dawowar su, gida Hajiya mahaifiyar SADIQ da kanta ta zaunawa Nasreen.
Ranar Lahadi da dare, ana gobe suna khabeer ya shigo ɗakin Nasreen yake sanar da ita cewa yayiwa Baba mai suna, sunan Yaron Musa, ita kuma macen Momy Sarah yayiwa takwara, taci sunan saratu, Nasreen taji daɗi sosai.
Washe gari suna ba'ayi wani bidi'a kasancewar khabeer yace baya so, Nasreen ta samu kaya sosai domin kuwa kowa ya nuna bajintar sa.
Khabeer komawa yayi part ɗin Zuhura gabaki ɗaya da zama kafin Nasreen tayi arba'in, aikuwa Nasreen bayan tayi arba'in tasha gyara sosai wajen Hajiya, ciki da waje, yaranta kuwa sunyi ƙiba, gwanin sha'awa, sai kace ƴan wata Uku, Ranar da khabeer ya dawo ɗakin Nasreen kusan zaucewa yayi, tsabar zumar da Nasreen ta masa.
Yanxu Nasreen ta koma makaranta inda take tafiya da nani yana kula mata da Aslan da Aslamy wanda da haka take yiwa yaran nata laƙabi.
*A gurguje*
Bayan shekara goma
Da gudu wani matashin yaro ya fito yana Cewa.
" Abba !! Abba !! Abba.
Khabeer dake zaune falo yana riƙe da waya a hanun sa, yace
"Wai menene Aslan nake shan wannan kiran.
" Abba wai inji bros junior bazaka je ɗauko Momy Sarah damu ba, nida Aslamy.
Murmurshi khabeer yayi tare da cewa.
" Inji waye, zuwa daku kai dashine dai baxan jeba, gashi ma har kun shirya momyn ku kawai muke jira, kinga Ahlan da shuhuda ma sun shirya, ya nuna mata wasu yara biyu dake zaune gefe suna wasa ba tare da sun kula suba, wanda Nasreen ta sake haihuwa bayan Aslan da Aslamy.
Dariya yaran sukayi tare da koma part ɗin Zuhura da gudu suna murnar dasu za'aje.
Tashi khabeer yayi tare da shigewa ɗakin Nasreen, yaga me take taƙi fitowa har yanzu, tana zaune gaban mirror tana ƙoƙarin ɗaura sarƙa a wuyan ta, karɓar sarƙan khabeer yayi ya ɗaura mata, tare da ɗaura kansa bisa kafaɗar Nasreen Yace.
" Baby na kinga yanda kikayi kyau kuwa kin koma yarinya ƙarama, kamar bake bace kika ajiye yara huɗu.
Dariya Nasreen tayi tace.
" Ai dole na zama yarinya, yanda Abban junior ke shagwaba Ni.
Dariya khabeer yayi tare da cewa.
" Sai kika tuno min sanda kike ƴar ƙauye, amaryar junguɗo, wayaga Nasreen gidan junguɗo mashayi.
Dariya Nasreen tayi sosai kafin tace.
" Da kuwa ina can ina fama da wahalar surfe da bautar gida, gaskiya anso lalata rayuwata sai Allah ya dubi zuciyata ya turo min da hasken rayuwata Khabeer ya taimake ni, ya fiddani daga ƙangin bauta ya dawo dani Mutum ta hanyar inganta Rayuwata da hasken ilimi, gashi yanxu har na gama karatuna ina jiran aiki kuma naje har garin ma'aiki na sauke farali, shiyasa a kullum nake daɗa ƙaunar ka HABIBINA.
Murmurshi khabeer yayi tare da cewa.
" Ki daina tuna Abunda ya wuce farin cikin zuciyata, nice ya kamata na miki godiya, sakamokon haska min gida da kikayi, ki daina tuno waɗanda suka miki mugunta, domin basu isa su tare miki hanyar samun kiba, ko kin manta karin maganar nan ne ta Hausawa da suke Cewa *SARA DA SASSAQA BAYA HANA GAMJI TOHO*
ALHAMDULILLAH ANAN NA KAWO KARSHEN WANNAN LITTAFIN, INA ROƘAR UBANGIJI ABUNDA NAYI KUSKURE YA YAFE MIN, ABUNDA NA FAƊA DAI-DAI KUMA YA BANI LADANSA, ALLAH YA BAMU IKON AMFANI DA DARUSSAN DAKE CIKIN WANNAN LITTAFIN.
Anan nake ce muku bissalam sai mun sake haɗuwa daku cikin sabon Novel ɗina mai taken, *RUƊANIN ZUCIYA BIYU*
*SHARE*
*AND*
*COMMENTS*
*ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN✍🏻*
*(UMMU NASMAH CE)*