Da washe gari sukayi shirin tafiya saida suka fara biyawa gidan ammy suka mata sallama sannan suka shiga suka gaishe da momma da mamy dasu kawu baba
Kafin suka kama hanya suna tafiya suna hira cike da soyayya bun sha'awa har bacci ya kwasheta ta jima tana bcci bata farka ba saida suka iso *azare* ta bude ido tana miqa gamida salati ta kallesa yayi murmushi yace nisful hayatina kin tashi, wannan babyn nawa gasky yana saminke kasala dayawa,yatsine fuska tayi batare da tayi mgn ba, wani gate taga sun tsaya yana horn mai gadi ya bude musu suka shiga yayi parking ya fito ya zagaya ya bude mata y fito da ita , yace mu shiga ko tace to nan din inane? Hancinta yaja ya kashe mata ido daya yace idan muka shiga zaki gani ai
Sallama sukayi a parlorn' gwaggo mairo zaune itada jikarta salima yar gidan anty haula da gudu tazo ta rungume shuhada ,adeel yace ke ke bi ahankli dan Allah karki zubarmin da mata kasa kijawa ɗana karaya salima ta koma da baya tana tura baki gwaggo mairo tayi dry tace zo abunki jikata kyalesu
Shuhada mamaki ne ya hanata katabus ,gwaggo mairo tace to karaso mn ke kuma, kin wani ja kin tsaya awajan, adeel ne ya tashi yana dry yace aa fa gwaggo lallabamin ita kamo shuhada yayi ya zaunar da ita
Anty haula ta fito tana cewa ah lale maraban ku sannun ku da zuwa ,,,yace yauwa antynmu ya gida anty haula tace lpy lau ,shuhada ya jikin ?nan ma shuru tayi shi kuma ya tashi yace bari naje wani waje zan dawo ba jimawa. Zanyi ba sannan ya fice yabarsu ,,mamakin
sa kawai takeyi yanda ya sake baki yana mgn harda dry duk da mgnr ahankali take fitowa kamar mai koyon mgn amma tasha mamaki
Da kyar ta iya bude baki tayi mgn tace gwaggo mairo wannan gidan fa ?
Gwaggo mairo tahau dry ai wannan yaro adeel Saide Allah shi mai albarka nan gwaggo mairo da anty haula suka hau bata lbrn abin arziqin da adeel ya musu anty haula tace ya canzawa luqman mijin hindu mota tsohor motar luqman kuma yabawa baban salima ,,hawaye shuhada ta hau yi wani sabon son mijinta takeji ta ko ina a sassar jikinta yana mata yawo
Kiransa tayi awaya tace zataje gidan hindu yace wazai kaiki? Tace ni kadai zanje yace no ban yarda ba ki jirani zanzo na kaiki ,,sai gefen magriba yazo a mota tasa mesa tana shiga ta rungume sa tahau kuka tana zuba masa gdy tare da adduoi kala kala
Murmushi yayi yace ina matuƙar sonki my ashshuhada babu abinda bazan miki ba domin na sakaki farinciki ,,kiss tamasa a baki, ya shafo fuskarta yana murmushi ,ya tada motar sukaje gidan hindu nan hindu tadinga tsokanarta
Shuhada tace hindu wani ckn gareki ? Haba ke kuwa shuhada wani ciki ana zaman lpy, ba yanzu ba wlh saina huta hira sukayi sosai
Sai kusan sha daya adeel yazo ya dauki shuhada daga gidan hindu yace my ashshuhada muje hotel ko? zare ido tayi tace hotel kuma baby, gaskia aa nikam ka kaini gida ,asanyaye yace to shikenan tunda haka kikeso har suka isa bai mata mgn ba yana parking yace mata saida safe ,ki shirya gobe da wuri zamu tafi ,ganin duk ya sauya mata yasata cewa aa kajirani bari na shiga na dauko kayana mutafi
Baiyi mgn ba tashiga ta musu saida safe ta dauko kayanta
Ta fito ta samesa ya jinginu da sit ya lumshe ido ya ɗaura hannunsa a fuskarsa
Tace yi hakuri mijina nabata maka lkc ko wlh har sun fara bacci ne shiyasa
Ɗagowa yayi ya kalleta tana murmushi ya janyota jikinsa a hankali yafara mgn ashshuhadata meyasa baki son damuwata ? Fari tayi da ido sannan tace mijina kamin komai arayuwata dole naso farinckin tunda kaima kullum burinka kasani farincki, yanzu gobe zamu koma kadunan? Girgiza mata kai yayi alamun aa kafin ya kunna motar suka bar gidan hotel ya kama musu anan suka kwana
Da washe sukayi shiri amma saida suka fara biyawa sukayiwa su gwaggo mairo sallama dasu hindu
Tafiya sukeyi ahankali ita kuma tana masa hira yana jinjina kai alamun yanajin dadin hiran da take masa
Ganin sun dauki hanyar kauyen tanko yasa gabanta faduwa
Ta juyo da sauri ta kallesa ya kashe mata ido daya
Numfashinta bai gama tsayawa ba saida taga titin da aka tayar awajan layin tasha da kuma hanyar fadar mai gari
Hanyar wajan makarantarsu burleey ya dauka makarantar ma angyarata anyi mata penty sun danyi tafiya kadan kafin yayi parking ya fito daga motar yazo ya fito da ita tana juyawa idonta ya sauka awata babbar gini mai fadin gaske kanta taɗaga saman ginin sakamakon rubutu data gani wato *_IKLEEMAH AMADU PRIVATE HOSPITAL AZARE KAUYEN TANKO*
Da sauri ta juyo tana kallonsa ya kashe mata ido ya kamo hannunta suka jera har cikin asibityn wani dan qaramin bort tagani an rubuta *SHUHADA HELP*
Ai ana cewa ga *Dr Shuhada* tazo itada mijinta *Dr Adeel* nan jama'a suka kewayeta kowa ganinta yake sonyi har tabata sukeyi wasu suna mata gdy harta mai gari baban hindu shida kansa yazo har asibityn yana mata gdy domin takawo cigaba dayawa agarinsa harda wata makaranta mai suna *DR SHUHADA PRIMARY SKULL*
Kuka shuhada takeyi ta rungume mijinta jama'a sai masha Allah suke cewa domin sun burge kowa
Janta yayi suka koma mota tasake shigewa jikinsa tana kuka ,,,,
_hakika bansan da wani kalar baki zan yi maka godiya ba mijina kamin komai arayuwata kaci kamin burina dana mahaifiyata da burin mahaifina Allah yasakawa kawu baba da alkhairi Allah yasanya ku Aljannatul fiddausy ta cigaba da kuka_
_burleey ya ɗagota yana share mata hawaye yace ashshuhadata bana son kukan ki sbd ina sonki tun ranar da idona yayi tozali dake na fada kogin qaunarki amma bansan taya zan bayyana miki ba illa kishin da nake dashi ,idan naganki da wani,,,ji nake kamar na mutu ke harta fauzan idan naganku tare sainaji kamar ancaka min wuka azuciyata sbd ina tsananin qaunarki, lkcn da kawu baba yace zai hadani dake aure ranar banyi bacci ba sbd murna ashshuhada bansan iyakar adadin son da nake miki ba ,ranar dana aunaki na tabbatar kina dauke da jarirna acikin ki ranar saida nayi kuka sbd farinciki ina matukar qaunarki matata dan Allah karki barni ki zauna dani har abada kita haifamin yara kyawawa masu kama dake_
Murmushi tayi hawaye na zuba a idonta ta kamo hannunsa ta daura akan cikinta tace masu kama damu
Dan kowa yace muna kama miye sirrin? Murmushi yayi yana shafa fuskarta yace sbd dama tun fil'azal jinsinmu daya ne dake kawai an haifemu awaje daban daban ne ,,kwantawa tayi ajikinsa ta lafe tace innata tayimin addua ranar da zatayi bankwana da wannan duniyar kasan wace addua ce?
Ya girgiza kai ,,cewa tayi Allah yabani miji nagari wanda zai soni tsakani da Allah ya qaunace ni ya kula dani ,alhamdulillah gashi na samu mijin da yamiye min gurbin komai arayuwata duk yadda zan furta inasonka yafi karfin haka azuciyata da komai na ,, na mallaka maka zuciyata gangar jikina da duk komai nawa dagota yayi yace da gske ? Ta rufe ido ta gyada masa kai yace ok muje masauki saina tabbatar da hakan ya kunna motar ta hau dry ,,
Wani dan qaramin gida tagani parlor daya bedroom ma daya sai kitchen da toilet,gidan qarami ne kam sosai, amma ya tsaru yayi kyau matuka haka tadinga santyn gidan yace namu ne nasa aka mana sbd idan munzo duba kauyenmu basai mun dinga kame kame ba tunda kinga lkc lkc zamu dinga zuwa muna ganin abinda ke wakana ,kawu baba yace zamuje niger amma sai kun haihu tunda kun kusan haihuwa
Zare ido tayi tace zeeyadat da raeena sun kusan haihuwa dai amma duka duka nawa watansa biyar ne fa
Ya zaunar da ita yace nasani ai bakwaini zaki haifamin ,,,ta dafe qirji dan Allah karkamin wannan fatan bakwaini fa basu cika zama ba ,,,yace to naji Allah dai ya fito mana dasu lpy ta amsa da ameen
Da yamma liqis tace zata je ta dubo yan uwanta yace muje na rakaki
Sun fita suna tafiya yana riqe da hannunta suna hiran soyayya yan mata da samari kowa saiya kallesu yace dama shine
Suna ckin tafiya sukaji ana kiran sunan *shuhada* abayansu juyowa sukayi ahankali tana ganinsa ta ganesa yakubu ne
Ya karaso inda suke yace kin ganeni kuwa? Shuhada tayi murmushi tace eh nagane ka yakubu ko? Ya washe baki yace eh dama so nake na.........mtswwwwwwww dallah malam ya isa haka kazo ka tare matar aure agaban mijinta kana so kace mata uban me ? Sosai burleey ya shiga zazzagawa yakubu rashin M bayaji baya gani kallonsa kawai shuhada keyi ,yakubu ganin lamarin da gaske ne yace yallabai Allah yabaka hakuri da sauri ya juya yatafi haryana tuntube
Idon burleey har yayi ja tsananin kishi yace oya juya mu koma bazakije ba nafasa,nan tahau basa hkr da kyar ya hakura nan ma yace saide su juya su koma gida tasa liqab tace my baby kaga fa juna biyu gareni idan nasa dauke min numfashi yakeyi da kyar dai ya hakura suka tafi
Tana zuwa kofar gidan tun bata shiga ba tafara ambaliyar hawaye
Sallama ta hauyi taga yaran gidan ahargitse yaran nuratu suna dambe dan aikinsu kenan yaran sale kuma barna
Nuratu da sale har sun koma tsofaffi sbd wahala gidan ya qara lalacewa sai wari gidan keyi burleey kasa daurewa yayi yafice shuhada ta rungumi nuratu tana kuka itama nuratun kukan takeyi
Ta kalli yaya sale tace to yanzu sana'ar me kakeyi yace mata ba komai ,tace to mai zai hana shagon yaya mansur na da ka cigaba da amfani da ita muga abunda Allah zaiyi kudi ta dauko dubu talatin tabasa ya karba yana kuka tare da gdy
Tace yadikko fa nuratu tace bamu gansu ba sahura ma bata jima da dawowa ba tana can tana fama da cutar HIV shuhada tace innalillahi wainna ilayhirrajiun sahuran? Nuratu ta sharbe hawaye tace eh ai mukam munga ishara hakika samun uwa tagari ba qaramin rabo bane har gobe bazamu daina roqonki gafara ba
Sosai shuhada take kukan tausayin su har magriba tukunna burleey yazo ya dauketa suka koma gida jikinta amatukar sanyaye
Burleey ya janyota jikinsa ahankali yace meyasamu *matar adeel burleey*?
Hawayen da take riqewa ne suka zoba ta kwanta ajikinsa
_Allah sarki rayuwa ni *SHUHADA* wai yau nice na zama abin nunawa ana alfahari dani bayan nice wacce za atasheta tsakar dare da ruwan sanyi aturani rafi dibar ruwa naci duka na wuni da yunwa na kwana adakin tare da awaki duk sanyi da duhun dare haka nake kwana abarin dakin da gininta ya zube gashi babu kofa ta yadda dukkan wani mahaluqi zai iya shigowa ya cutar dani sai gashi Allah ya qareni nazama abin alfahari duk sbd kaine mijina_
Adeel yace kidaina tuna baya ki fuskanci gaba muyi rayuwarmu kowa yayi nagari dan kansa yanzu ina wa inda suke mikin?
Lallashinta yadinga yi harta ware tadawo daidai nan suka hau video call da yan family house dasu ammy harda abbi kafin suka komayi dasu raeena raeesa zeeyadat shukra mihik sai kusan karfe daya sukayi sallama nan ma saida burleey yayi mgn
Kwanansu biyu a kauyen tanko
Suna kula da marasa lpy duk inda adeel yake shuhadarsa tana tare dashi yana manne da ita baya bari tayi mgn da maza
Har kauyen maqobta ana kawo marasa lpy kauyen tanko sbd adeel ya zuba likitoci da nurse's sosai wanda kuma suka san aikinsu dan ba sanya balle wasa
Sallama sukaje yiwa mai gari aka hada musu kayan tsaraba
Kafin suka kama hanya
Suna tafiya awajan gefen bakin hanya sukaga yara suna jifar wasu mahaukata mata su biyu har adeel ya wuce da mota shuhada tace tsayaaa.....tsayawa yayi da sauri yace menene haka? Bata basa amsa ba ta fice sakamakon hango yadikko da talatu, koran yaran tayi ta dubi yadikko wacce ido daya babu kafa daya arube harkazalika talatu ma haka dukkan kafarta biyu sun rube hardasu tsutsa
Shuhada kuka taje zata tabasu da sauri burleey yajata yana yatsine fuska yace miye ne kam baki da hankaline ?keda kuka baya miki wuya
Tace yadiko ce fa da inna talatu burleey yace to me zaki musu ?kinga wuce mutafi nan tadinga magiya da kyar burleey ya kira waya yace azo atafi dasu asibity
Shuhada taje gaban yadikko tace yadiko nice fa nice shuhada ce kin ganeni?
Yadiko ta kyalkyale da dry tana qwaqular idonta daya mai ciwon tace karya ne shuhada ta mutu nima na mutu talatu ta mutu nuratuna ta mutu sale ma ya mutu nan tadinga lissafin jama'a tana cewa sun mutu har akazo aka tattare su
Adeel ya kama shuhada yasata amota suka tafi
Ko da suka isa cikin garn azare gidan su gwaggo mairo suka nufa nan adeel ke basu lbr gwaggo mairo tace dan ma kina da tausayi da karfin imani da watace wlh bazata kalli laure ba Allah yasa muyi kyakkyawar karshe suka amsa da ameen
""""""""""""
Da washe gari suka koma kaduna
Nan wata sabuwar soyayya da tattali ke tashi tsakanin *shuhada* da *Adeel* da kyar yabarta take zuwa aiki amma ba kullum ba
Bangare su raeena raeeesa zeeyadat shukra mihik suma soyayyarsu suke bajewa kamar baza amutu ba
******** *AFTER 5YRS*
Zaune take aparlor ta zama cikekkiyar mace sanye take da wata tsadaddiyar less baqi da dan yellow yellow ajiki tayi matukâr kyau tasha makeup yara ne su kusan goma sha daya suna wasa sai zagaye parlorn sukeyi da guje guje
Sallama akayi da sauri ta tashi tace tuntuni sai yanzu raeesa tace wlh ke kam bari my horror ne yabatamin lkc suka kwashe da dry ,shuhada tace wato bazaki daina cemasa horror ba ko ?zeeyadat tace duk acikin love ne wata yar yarinya ce acikin yaran da suke wasa tazo da gudu tayi tsalle tace oyoyo momyna raeesa tace sai yanzu kika ganni ?
Zeeyadat tace ba gwanda ma ita tazo ba amma mukam ai ga yaran namu can kamar basu ganmu ba
Mihik ta juyo ta kalli irfan da aryan suna zaune sun wani hade rai sai kace wasu manya ,,,tace wai shuhada raeeesa wannan yaran naku saiku shuhada tayi dry tace waima fa ahakan gwanda aryan akan irfan
Raeesa tace gwanda irfan dai ,,shuhada tace humm wlh gwanda aryan kinga irfan sainayi da gske yake min mgn nida nake uwarsa amma yafi mgn da dadynsa
Shukra tace idan ana neman rashan ji kuwa idan aka samu bittin kin nan angam bitti dake kwance ajikin mom dinta raeesa ta hau turo baki ta tashi ta koma wajen wasa
Raeena tace haba idan har bitti batayi rashin jiba ai sai a tambayeta uwarta tayi fa ko kun manta rashin jin raeesa ne ?
Raeesa tace kaiii jama'u karku takurawa yarana nagafa kuma kuna dasu kowa da rashin jinsa gasu can sai tsalle tsalle sukeyi kubar nawa su hutu suka kwashe da dry dukkansu
Su yaya burleey an kara cika anzama babban magidanci ga yaransa uku irfan da twins dinsa husna da husni
Ranar a family house suka wuni kawu baba da hajiya kaka shekaru sun sake ja jikin yaja tsumma ahakan ma wai familyn sun mori jiki
Su abba abbu abbi ammy momma mamy duk sun manyanta
Sunje har niger sukayi wata daya da yaransu binayya ma ta haihu ko da suka hadu da shuhada ta dinga kakkauda kai shuhada ce tafara yimata mgn harta bata hakuri tace shuhada kiyi hkr ki yafemin shuhada tace ba komai anty binayya Allah ya yafe mn baki daya ni dama ban riqeki ba wlh ,,,tun daga lkc ba laifi suna dan shiri da binayya har suka gama zagaye dangi suka koma kaduna
Lkc zuwa lkc kuma suna zuwa azare har su wuce kauyen tanko suyi kwana biyu su duba marasa lpy
"""""""""
Tsaye take ajikin mirror tana shirin bacci yayi sallama ta kallesa tayi murmushi ta amsa ya rungumeta ta baya yace momyn irfan ina sonki sosai ,juyowa tayi ta rungumesa tace dadyn irfan momyn irfan tana sonka sosai yayi dry ya ɗauketa cak yayi gado da ita yace yawwa dama su husna da husni sukace suna son kanne dan suma adinga ce musu antys dan haka yau zan sama musu kannan ta hau dry ta janyosa ta rungumeta tace *SHUHADA MATAR BURLEEY* dry yake ya hade bakinsu waje daya
____________________
Daga nan nima nce bari na ajiye alqalami na anan domin na huta
__________________
*ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH MASHA ALLAH DUKA DUKA ANAN NA KAWO KARSHEN WANNAN LITTAFI TAWA NA SHUHADA ALLAH YASA ABINDA NA RUBUTA YA ZAMOMIN SHAIDA RANAR GOBE QIYAMA KUSKURENA KUMA ALLAH UBANGIJI YA YAFEMIN*
_Allah yasa mu amfana da darasin dake cknta_
*_SAI KUN SAKE JINI A LITTAFINA NA GABA KARKU MANTA DAI NICE TAKU HAR KULLUM ZAHRA ABDUL MOMYN AHLAN_*
*_WANDA NABATA MASA ACIKIN LITTAFIN NAN DAN ALLAH YA YAFEMIN DOMIN DAN ADAM AJIZINE NIMA NA YAFE MA KOWA ALLAH KUMA YA YAFE MANA BAKI DAYA AMEEEN NGD MUKU SOSAI MASOYANA INA QAUNARKU ADUK INDA KUKE INA MIKO MUKU GAISHEWA TARE DA FATAN ALKHAIRI_*
_NAGODE NAGODE NAGODE DA BIBIYAR LITTAFINA DA KUKAYI_
*_sai Allah yasake sadamu kuma_*
Comments
And
Share
*momyn ahlan ce*✍🏻