TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑃𝑎𝑔𝑒 𝑜𝑛𝑒_
_Free page_
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan ALLAH, Mai rahama, Mai jin ƙai._
.........Humm wato Bilyn Abdull atawa fahimtar da abinda shekaran jiyata da jiyata har zuwa yau ɗina tazo min dashi zan iya cewa JARUMTA itace asalin RAYUWA. HAƘURI shike jagorantar numfashi da samun tsahon rai ga kowanne halitta a cikin salama. A duk sanda wasunmu suka tambayemu minene adonmu? Amsa ɗaya muke fara kallo a zukatanmu da furuci (TARBIYYA). Sai dai a gareni ni nace sam ba haka bane. Zan kuma iya faɗa a hankali ko da amsa kuwwa harma da shelantawa. Kada kai mamaki ko fahimtata a bisa tsatstsauran ra'ayina ko zama mai bahagon hasashe. Bance tarbiyya bazata amsa suna ADO ba, sai dai magana ta gaskiya ADDINI shine mafi girman zama ƙololuwar ADO a waje na. Sannan akai kanka da ku kanku duk shine. Ina tsaye bisa wannan ra'ayine saboda ina girmama ADDINI NA bisa koman dake amsa komai na a rayuwa. DUNIYA itace MAKARANTAR farko ga kowanne ma'abocin numfashi, domin a cikinta ake fafutuka da hanƙoron neman SAKAMAKON zuwa MATABBATA. Sobada a yanda ka tafi da ita a haka take baka daraja da kima a wajen komai da kowanka. Kowanne mai numfashi yana tsoron MUTUWA, amma hakan baya hanamu buƙatar RAYUWA da fatan shiga ALJANNA, saboda a canne ake iya samun komai da komai da zukata basa iya hasasowa koda da tsayin motocin hange. Haka zalika ƙarewar kwanakin numfashinmu a kowanne wayewar gari baya hanamu sake tanadin BURIKANMU koda kuwa yaƙininmu na nufin baza muga GOBENMU BA. Duk wani ɗan adam zakiga RAYUWA na taka masa iya rawar abinda littafin ƙaddararsa tazo da shi ne kawai, duk kuma iya hanƙoronka da faɗi tashi akan neman DUNIYA ko guje mata baka isa zartama wannan ƙaddarar taka ba.
Kar na kaiku da nisa bara na baku komai a buɗe a yanda zaku fi fahimtar abinda nake son faɗa ga Bilyn Abdull da ku baki ɗaya. Sunana shine *_SAMRAAH ABDUL-WAHAB GWARZO_*. A zahirin rayuwa ni ɗin ba kowa bace face ɗiyar Malam Abdul-wahab Gwarzo. Domin kuwa mahaifina bai kasance mutum mai mulki ba, haka ba attajiri bane, ba kuma babban malami ba. Shi ɗin driver ne dake aikin tuƙi a wani gidan attajirai. Sai dai ALLAH yay masa rasuwa sakamakon haɗarin mota tun inada shekara bakwai a duniya. Mu uku kacal ya haifa shi da mahaifiyarmu da itama dai ALLAH yay mata rasuwa bayan haihuwar ƙanina tun bamma cika shekara uku a duniya ba. Yaya Musaddiq shine babban yayanmu, sai ni Samraah da autanmu Hafizzullah. Tun bayan rasuwar mahaifiyarmu riƙona ni da Hafizzullah ya koma hannun ƙanen mahaifiyarmu Uncle Imam. Matarsa ita ta ƙarasa shayar da Hafizzullah tare da yaronsu data haifa itama kusan lokaci ɗaya da mamanmu, sai dai bamu da tabbacin ma kota shayar da shi ɗin ko batayi ba. Dan haka suka tashi tamkar tagwaye. Bayan rasuwar mahaifinmu riƙon Yaya Musaddiq ma ya dawo hannun Uncle Imam. Duk da mahaifinmu bamai arziki ko mai mulki bane ya tafi ya barmu da gonakin gado harma da gidan zama. Sai wasu ƴan kuɗaɗe a account. Itama mahaifiyarmu tabar mana gonaki data gada a wajen nata iyayen tare da Uncle Imam dan su biyu kacal iyayensu suka haifa suma. Kasancewar duka iyayenmu a cikin garin Gwarzo suke waɗan nan dukiya tamu duk tana acan ne. Sai gida da muka rayu kawai anan cikin birnin Kano. Karancin shekarunmu yasa duka abinda iyayenmu suka bar mana bayan an raba mana shi ba'a bamu ba, acewar Uncle Imam sai mun girma dan duk shi ya ɗauki komai ya ajiye, gonaki ya cigaba da nomasu, gida ya saka ƴan haya. Uncle Imam shine ya cigaba da ɗaukar nauyin karatunmu dama dukkan al'amura na rayuwarmu har sanda muka kawo girma. Duk da dai rayuwa a gidan Uncle Imam bata taɓa kasancewa mai sauƙi a garemu ba saboda mugun halin matarsa duk mun shanye wannan a ranmu. Amma tabbas mun ɗanɗana kuɗarmu a hannunta akan abubuwa daban-daban. Mun fuskanci ƙalubalen maraici kala daban-daban. Dan komai da zasuyi ma ƴaƴansu yanada bambanci da wanda mu za'a mana. Hatta da abinci takan fifita ƴaƴanta akan mu. Hakama a makaranta suna private school muna government school. Sutura akoda yaushe tasu nada banbanci da namu. Hatta da ɗakin kwana na yaransu nada banbanci da namu. Abin zai baka mamaki idan nace duk wannan wariyar launin fatar muna ganine har daga Uncle Imam bawai ita kawai ba. Kafin mu san kammu mukanyi kuka mu share hawayenmu, bayan mun mallaki hankalinmu musamman ma ni sai na fara maida murtani. Nakan shanye daga ƙyara da hantarar Mom da Abba. Amma bana iya kauda kai daga al'amuran ƴaƴansu. Dan hatta waɗanda suka girmeni idan suka nuna min yatsa saina karya shi nake samun nutsuwa koda za'a rama musu ne. Amma ga Yaya Musaddiq ba haka bane ba, dan shi mutum ne mai shiru-shiru, hakama Hafizzullah baida yawan hayaniya. To nima ɗin dai a zahirance bazakace ina magana ba, dan banda yawan surutu, sannan inada yanayin fuskar salihan mutane. Shiyyasa sometimes nakan aikata abu Mom ta faɗa ace ba'a yarda ba, ni ɗin nan dako yatsa aka saka min a baki bana ciza ba. Wannan halayya tawa na ƙona mata zuciya da ruhi, dan haka nafi sauran ƴan uwana cin wahala da azaba a hannunta harma da hannun Abba ɗin. A haka dai muka rayu cikin haƙuri da juriyar rayuwa har ALLAH yasa muka kammala secondary. Daga nan Abba yace baida kuɗin biya mana mu cigaba da karatun jami'a. Raina ya ɓaci matuƙa domin ganin yanata cuku-cukun biyama Abbas ɗansa dake sa'a da Yaya Musaddiq, da Baby mai sa'a dani. Dan haka na sameshi da batun tunda hakane ya biya mana da gadonmu. A saida gona guda a biya mana. Maruka nasha lafiyayyu masu gigitarwa a wajensa, daga ƙarshe ya koroni da zagi daga falonsa. Duk da ran Yaya Musaddiq ya ɓaci shima baice komai ba, saima faɗa daya shiga min akan abinda nayi. Acewarsa baikamata nayi magana ba, dan koba komai Abba ƙanin mahaifiyarmu ne, ya kumayi wahalar riƙemu kafin yau. Komai bance masa ba, face hawaye kawai da nake zirararwa. Shima bai sake cewa dani komai ba ya fice a gidan.
Kwanaki biyu da faruwar hakan Yaya Musaddiq yazo min da labarin ya samu wajen aikin koyon kanikancin motoci. Duk da ni ba haka nake buƙata ba karatu nake son muyi sai na tayashi murna kawai da fatan alkairi. Daga lokacin Yaya Musaddiq ya fara zuwa gareji, dan koda ya faɗama Abba sai bai wani maida hankali ba face cemasa ALLAH ya bada sa'a a daƙile. Su Baby sun fara zuwa makaranta, yayinda ni kuma na koma mai aikin gidan. Dan dukkan wani aiki na cikin gidan a yanzu ya koma kaina ne gaba ɗaya har wanda banayi a da. Sai idan Hafizzullah ya dawo yake kama min da wasu ayyuka. Ina matuƙar jigatuwa, amma hakan bai hanani shiryawa na tafi islamiyya duk rintsi kuma koda za'a dakeni ne. Tun ma idan na sulale naje na dawo Mom kan dake ni har ta haƙura ta tattarani ta watsar, sai dai dolene bazan fita ba sai na kammala duka aikin data bani, samun wannan damar ya sakani jajircewa na gama komai akan lokaci dan na wuce. A wannan yanayin shekara ɗaya ta shuɗe da kammala sakandare ɗinmu, na samu nasarar yin saukar Alkur'ani, sai dai babu abinda akaimin na walima sai wanda Yaya ya ɗan mun, ban kuma damu ba. Yayinda su Baby keta zuwa makaranta, Yaya Musaddiq na jelen zuwa gareji. Dan in ya fita tun safe sai yamma yake dawowa. Da farko Abba bai damu da aikin Yaya Musaddiq ba balle abinda yake samu, sai daga baya da Mom ta zugashi wai yana samun kuɗi tunda yamun ɗinkin walima sai ya sharɗanta masa yo cefane kullum a gidan. Duk da hakan ya zafi Yaya Musaddiq saboda shi yanada burinsa akan shiga aikin bai nuna ba ko'a fuska, sai ya koma raba kuɗin da yake samu biyu yana ajiye rabi kamar yanda ya saba rabin yana cefanen. A wata ranar da tai dai-dai da cikar shekarar mu ɗaya da watanni biyar da gama sakandire sai ga wani malamin mu yazo neman Abba. Bayan sun ɗan gana na wasu mintuna akai kirana. Ranar da bazan taɓa mantawaba kenan a rayuwata, ranar data zama komai daga cikin TSIRON da yazama shine TUSHEN LABARINA. Ranar da ta zama MAFARIN da har yau ba'a kai ga zuwa ƘARSHE ba tunda numfashi bai rabu da gangar jiki ba.......✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒐_
.......Mal Saminu yazo da daddaɗan labari garemu cewar na samu scholarship na cigaba da karatuna. Misalta muku yanda na shiga ɗunbin farin ciki a wannan ranar ni da ƴan uwana guda biyu ɓata lokaci ne. Yayinda Abba da Mom da su Baby suka nuna baƙin ciki da hassadarsu a fili akan hakan. Dan da farko ma Mom catai ƙarya ne babu inda zanje, Abba kuma ya goya mata baya, sai da Malam Saminu ya tabbatar musu da in har aka hanani akwai matsala. Dan kuwa gwamnati zata iya bibiyar al'amarin ta kuma hukunta duk wanda yay uwa yay maɗaukiya akan hakan. Jin wannan bayani ya sakasu barina dole nima a wannan shekarar aka shiga damawa dani a harkar karatu a B.U.K. inda Baby da yayanta Abbas suke nasu karatun suma.
*_MATAKON FARKO_*
Uhm dole a kira wannan ajin da matakin farko. Domin kuwa akansa ne komai ya fara, farawar da kamar itace farkon buɗe shafin rayuwata ta hankali, domin kuwa ko babu komai shekarata goma sha bakwai a yanzu. Zan iya cewa na shiga jami'a a sa'a. Domin kuwa course ɗin da nafi so da buri shina samu. A shekarar farko dana fara karatuna na fahimci halin da Baby ke ciki a school ɗin. Dan kuwa tuni ta ajiye karatu gefe sune shegun makaranta. Iyaka su shiga ofisoshin malamai su ɓata lokaci wani lokacin ma harda gidajensu ko a ɗaukesu a mota a fita da su, batun karatu kuwa sam babu shi tare da su, sunada group kuma. Amma abin mamaki sunansu na gaba-gaba a allon kafe jarabawa matsayin wanda suka cinye komai sai ɗan abinda ba'a rasa ba. Ga Yaya Abbas ɗin ma bata sauya zani ba. Dan shima ɗin dai yafi maida hankali ga siyasar makaranta da bin abokai masu motoci fiye da karatun. Bayan Yaya Musaddiq ban taɓa sanarma kowa a gidanmu ba, shima kuma tunda ya kwaɓeni akan hakan ban sake kawo masa zancen ba na maida hankali ga karatu na. Ina a wata na biyar da zuwa mukai karan batta da Mansoor. Mansoor Khalil Musa matashin yaro ɗan ƙwalisa. Ƙyaƙyƙyawan gaske mai tarin ilimi. Yana shekararsa ta uku a cikin b.u.k. A yanda Mansoor ke shigar suturu na alfarma da mota zai tabbatar maka da shi ɗin ɗan masu hannu da shuni ne. Sai kuma ƙwazonsa da ƙyawunsa ya sake jan hankalin ƴammata na cikin makarantar da yawa a kansa. Sai dai sam bai ɗaga ido ya kalli kowaccensu balle ya yarda magana ta haɗasu. Hakan yasa ake masa laƙabi da mutum mai girman kai. Domin kuwa bayan abokansa biyu babu wanda yake kallo da gashin arziƙi a ɗaliban dake ƙasa da shi harma wanda ke sama da shi. Amma sai me rana ɗaya ALLAH ya haɗamu a cafeteria. Muna tsaka da cin abinci ni da ƙawata ɗaya tilo Joy muna hirarmu cikin nishaɗi ya shigo tare da abokansa. Duk da yanda naji cafeteria ɗin ta ɗauki gunaguni a kansa banko kalla sashin da suke ba. Sai kawai jin abokinsa mukai kammu cikin gadara yace wai mu tashi zasu zauna. Cikin tsoro Joy tai niyyar miƙewa, amma sai na balla mata harara batare da nace komai ba. Zungurina tayi cikin roƙo da magana ƙasa-ƙasa ta ce, “Please Sam Gee mu tashi, ni sam bana son fitina. Kin san kuma halin guys ɗin nan ba mutunci ne da su ba”.
Kai tsaye na buge hannunta a fusace da faɗin, “Idan kinga na tashi a wajen nan na gama abinda nake yi ne Joy”. Daga haka na cigaba da cin abinci na. Zaram Joy ta miƙe, amma a mamakinmu dama duk mutanen dake wajen sai muka tsinkayi Mansoor na faɗin ta zauna abinta, cikin rashin damuwa yaja kujerar kusa dani ya zauna shima. Hakan da yay ya bama kowa mamaki, duk da dama bawai an taɓa ganinsa yana faɗa da wani bane ba, kawai dai an sanshi shi mutum ne mai girman kai da rashin shiga shirgin kowa, abokansa ne masu zuba rashin mutuncin ga kowa. Dan ko magana ma sai yaso yayita da mutum. Suma abokan nasa zama sukayi bayan sun musu order ɗin abinda zasu ci, ko gezau banji ba, ban kuma kalli kowannensu ba harna kammala cin abincina na miƙe bayan na saki niƙab ɗin fuskata. Dan kullum nakan shigo makarantar ne cikin hijjabi har ƙasa da niƙab, ko kuma nurse mask da eyeglasses, dan haka ba kowa ne zai iya shaida maka fuskata ba hatta ƴan department ɗinmu ma. Hasalima sunan Hijjab girl na neman bina, dan kowa idan zai kwatance da sunana yakan kwatantani da hakan ne. Idan ka cire Joy da ke kirana da *_Sam Gee_*. Mun bar wajen yayinda mutane keta ɗan ƙusƙus ɗin magana, kun san dai ɗalibai da rashin raina abin kace nace, yayinda Mansoor ya bini da kallo tamkar ya samu television. Tun daga wannan ranar al'amarin kamar wasa, sai ya zam a duk sanda mukaje cafeteria cin abinci Mansoor da abokansa zasu zo. Kuma koda tare muke da wasu a tebiri sai sun tashesu sun zauna. Ban taɓa tanka musu ba balle nuna nasan sunayi har muka shafe kusan sati biyu a haka, kafin shi Mansoor ɗin da kansa ya fara biyan kuɗin abincin da duk muka amsa a kullum. Anyi na farko anyi na biyu a ran ta uku na taka masa birki dayin hakan cikin masifa da kowa bai san na iya ba, amma maimakon yaji haushi sai yay murmushi kawai ya tashi ma ya bar cafeteria ɗin abinsa. Naji haushi amma sai na dake, na kumayi alƙawarin saboda shi bazan fasa zuwa cafeteria ɗin cin abinci ba, yayinda shi kuma bai fasa biya mana ba, kuma koda mun biya ba'a amsar kuɗinmu sai ace ai anbiya mana. Abin na ƙona min rai, na kuma rasa yanda zanyi, ina kuma akan bakana na bazan daina zuwa cafeteria ba. Tun ina jin zan sharesa har na fara magana, nan ma a banza, sai kawai na daina dan na fahimci maganar tawa ke tunzurashi kamar. A haka muka cinye wata guda. Abu dai kamar wasa sai ƙaramar magana ta zama babba. Dan kuwa dai shaƙuwa ta fara shiga tsakaninmu da Mansoor da abokansa. Takai idan ma basu zo cafeteria ɗin ba nakanji babu daɗi, kamar yanda shima yakanji idan bai ganni ba. Abinda zai baki mamaki kuma har lokacin ba wata doguwar magana ke shiga tsakaninmu ba, gaisuwa ce kawai sai zaman cin abinci.........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
......Tun dai muna shashshare juna har abinda ke cikin zuciya ya bayyana, domin kuwa Mansoor ya fito fili ya nuna min shifa sona yake. Tom kun san dai halin mutuniyar taku, ban gusa ba na balbalesa da masifar da zuwa yanzu wasu sun fara kallona da sumumu kasau macijin sari ka noƙe. Maimakon yaji haushi sai ya dinga sakar min murmushi, wannan shine karo na farko da nabar zuwa cafeteria da tunanin ai Mansoor zai ƙyaleni na huta, dan ni kam burina karatu ba soyayya ba. Sai dai kuma ba hakan bane ba, dan kuwa dai shima salo ya canja ta hanyar nuna ba soyayyar za'aiba yanzu karatu ne gaba, idan komai ya daidaita nan gaba sai soyayyar ta koma gaba. Tun ina shashsha masa ƙamshi harna miƙa wuya. Kafin wani dogon lokaci kowa yasan soyayyar mu da Mansoor kasancewar sa mutum popular a cikin makarantar, duk da dai kamar yanda ta faɗa karatune gaba ba soyayya muke ba, dan da wahala ma kaji ya saka min batun soyayya, sai yayta amfani da hakan shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tdakaninmu. Komai ya cigaba da tafiya yanda ya kamata, Mansoor na taimaka min matuƙa a ɓangaren karatu ni da ƙawata Joy. Hakan kuma ya sake fiddo ƙwazona. Sannan soyayyarsa na bani kariya sosai daga tsagerun ɗalibai harma da malamai ƴan bani gishiri na baka manda. Tun sauran ɗalibai na ɗaukar soyayyar yaudara ko wata manufa har suka yarda ɗari bisa ɗari da gaske muke, saboda komai muna gudanar da shi a tsaftace.
Tafiya tai tafiya, shekaru sunja abubuwa sun canja. Su Mansoor sun kammala karatunsu, sai dai kuma muna nane da juna ta waya. Yana kuma zuwa gida duk da ban taɓa yarda kowa yasan da batunsa ba bayan Yaya Musaddiq. Koda yake su Baby sun sani, dan nasha jin ma wai ai Baby ta jima tana son shi, sai dai bansan minene ya faru koya katangeta da sanarwa a gida ina soyayya da wani ba, sannan ita bata taɓa tarata da batun Mansoor ba kai tsaye, sai dai tai habaici a wasu lokutan ko shaguɓe, ni kuma sai ban taɓa kulata ba ko nuna na fahimta. Ina zangon ƙarshe na kammala karatuna na fahimci ashe Yaya Musaddiq shike biyamin kuɗin makaranta babu wani scholarship dama. Ya haɗa baki da malamin namune kawai, dan a yanzu haka shima Hafizzullah yana a level 100 a jami'ar Umaru Musa ƴar-aduwa dake Katsina. Shima kuma dai da batun scholarship ɗin nan aka rufe bakunan su Uncle Imam duk da an kwashi tashin hankali sosai fiye da nawa lokacin kasancewar shi Nabil bai samu ya tafi ba har yanzu. Ranar da nasan wannan sirrin nasha kuka a gaban Yaya Musaddiq. Shiko ya dinga lallashina yana murmushi, a ranar ya sanar min da komai bai ɓoye min ba. Dan yace bazai taɓa iya zama bamuyi karatu ba, dan haka ya zaɓi bi ta wannan hanyar domin gina gobenmu. Shiko aikin kanikancinsa ya ishesa in sha ALLAHU. Na nuna masa ban yarda ba, shima dole ne musam yanda zamuyi ya koma karatu, dan kuwa zuwa yanzu yana samun kuɗi sosai, sai dai duk a hidimar gidanmu da karatunmu suke tafiya, dan har yanzu bai tsinanama kansa komai na rayuwa ba irin burin matasa na son gina gida da sauransu, hatta budurwa ma baida ita shi sam. Ya min alƙawarin idan lokacin komawar yayi zai koma in sha ALLAHU.
Alhmdllh na kammala karatu cikin nasara, yayinda na riga Abbas da Baby da suka rigani farawa kammalawa saboda su sun saka wasa a karatun nasu. Bakuma su da niyyar gama school ɗin da alama, maybe sai an korosu su shiga hankalinsu oho, dan gasu nan koda yaushe cikin maimaita shekara suke. Bayan kammala karatuna da wasu watanni Mansoor yay uwa yay maɗaukiya ya sama min aiki a wani gidan tv da rediyo dake tashe a wannan lokacin. Hakan ya saka Yaya Musaddiq farin ciki, yayinda ran su Abba yay baƙi har suka kasa ɓoye hassadarsu a fili musamman ma Mom, dan da farko ma tuburewa tai akan tunda na gama karatu aure kawai ya kamata Abba yay min, wai akwai wani ɗan yayarta ya jima da cewa yana so na. Abba har ya ɗauki zancenta da muhimmanci niko na tibire nace wlhy idan aka aura min shi kashesa zanyi, dan ni ban shirya aure ba sai na fara aiki na. Ganin fa da gaske nake kuma sun san tsurin idona dan randa yaron yazo hira wajena zagin ƙare dangi na masa, hakan yasa Abba ya kashe maganar, sai dai ban san yaya sukai da matar tashi ba a ɓoye, a zahiri dai yace ya kashe wannan batu naje nai aiki na. Amma ya bani nan da ƙarshen shekarar nan na kawo miji. Oho ban wani damu dasu ba na fara aiki na, dan nasan dai inada Mansoor ɗina a hannu. Cikin nasara kafin kace mi na samu karɓuwa, albashina na farko dana biyu dana uku na haɗa da shi na sayama Yaya Musaddiq fili da taimakon Mansoor. Lokacin dana damƙa masa takardun sai kawai ya fashe da kuka. Nima kukan na fashe da shi tare riƙe hannunsa ina roƙonsa dan ALLAH ya daina, shifa uba ne a garemu yanzu, idan bamu masa hidima da abinda ALLAH ya azurtamu da shi b