Sai yamma lis ta fito suka hadu da Imran din suka nufi sassan Anneti sbd sosai yake girmamata itama duk cikin familyn lailah shine yaron datafi ganin hankalinsa fiyeda kowa har iyayensa shiyasa akwai mutuntawa a tsakaninsu ba laifi tana yaba Masa.
A palon Anneti din na farko suke zaune suna gaisawa tana sake tambayarsa family tareda jajanta Masa abin daya farun na lailah Yana jajanta Mata itama.
Duk maraice NURU na zuwa gurin Anneti din hakama yau Kai tsaye ta nufo sassan cikin sanyi da nutsuwa tareda jekadi tana sanye da doguwa riga dark purple suka qaraso sashen da sallama dauke abakinta tashigo
Dukkaninsu suka dago kowa na zuba Mata ido da nasa tunanin.
Ganin Imran datai shine abu na qarshe da Bata tsammanaba ta sunkuyar dakai tana kokarin juyar da hankalinta daga kansa ta nufi Anneti ta zauna kusada ita tana gaisheta cikin biyayya Kamar ko yaushe
Cikeda kulawa Anneti ta amsa tana miqewa Dan amsa wayar da ake Mata ta shige ciki tana cewa"
Ina zuwa.
Murmushin qarfin hali NURU tasaki tareda Dan waiwayowa ta kalli su afia din a natse tacewa imran"
barka da zuwa.
Boyayyar ajiyar zuciya ya sauke tareda dagowa ya 'dan kalleta ya dauke Kai Yana cewa"
Thank you.
Yi afia tayi Kamar batasan meya taba faruwa tsakaninsuba ta gyara zama tana fuskantar kowannensu tayi musu godiya tana cewa"
Anjima zata karbo takardun daga hannun Mr Omar yabawa imran.
Qala NURU Bata samu cewaba sai Dan yaqen murmushi datayi ta miqe tana cewa"
Zan koma.
Tashi sukayi dukkaninsu suka fito tare afia na kokarin Jan kowannensu da zance sbd su samu sakewa kada itadai asamu matsala agurin fitar mum dinta.
Suna fitowa kofar sashen gabaki daya daidai isowar MALEEK Mr Omar na gefensa Yana Masa wani zancen Wanda kullum baya rasa zance tsakaninsa da MALEEK.
Kwarjininsa da cika musu idon yayi yasa dukkaninsu sauke Kai Banda NURU data dago ta kallesa zuciyarta na narkewa saidai dukkaninsu Babu Wanda yasamu ko kallo daga garesa ya wucesu ya shige saidai abin mamaki Yana shiga din saiga dukkaninsu sun dawo Banda NURU wadda ta nufi sashenta zuciyarta ba dadi.
Ba wani fargaba ko tunanin komai afia ta sanarda dad dinta gameda zuwan Imran da aikin dasuyi din shida NURU tareda amincewar NURUn sai daidai lokacin ya dago ya kalleta da idanuwansa dasuka sata Jin tana neman fara rawar murya.
Ya maida kallonsa kan Imran ahankali kafin ya juyarda kallonsa kan Mr Omar ba wani zance Mr Omar ya kalli Imran yana cewa"
Bismillah muje abaka takardun.
Dan kallon maleek Imran yayi Dan Dole cikin girmamawa yace"
Ka huta lafiya" ya juya yabi kofa da Mr Omar yake nuna Masa suka fice.
Kasa sukuni afia tayi ta juya ta fice da sauri itama tana cewa"
Kafito lafiya dad.
Tana fitowa ta wuce sashen NURU Kai tsaye saidai Koda ta isa NURUn Bata wani cikin walwala sbd cewa tayi kanta na ciwo sai tabarta Dan tasamu ta huta sbd goben.
Juyar da Kai NURU tayi tana Dan rufe idanuwanta kallo daya maleek ya Aiko Mata Yana dawo Mata sbd itakai ta lurada kallon Wanda yasa duk taji Kamar zazzabi na neman kamata ta sauke qaramin numfashi ahankali tareda tashi zaune sbd sallar magriba datayi ta nufi toilet tashiga tayo alwala tana fitowa farhat na shigowa a Sanyaye tace"
Jeki kiyo alwala sweetie muyi sallah ko.
Zaune yake cikin palonsa bayan sallar magriba Yana kallon sketches din guda biyu dasuka nuna mutum dayane da Wanda yakaiwa Yan jaridar da Wanda yabada meriz ya sake kallon idanuwansa
Cikin nutsuwa Mr Omar yace"
Yakoob ne.
Dan waiwayosa maleek yayi cikin kamewa yace"
Ya aika sketches din gurin hukuma tareda bayanin komai da aka hada akan case din gobe ko jibi Inshallah za'a Kai karshen matsalar Ina buqatan komawa Paris.
Dan shiru Mr Omar yayi Yana Dan Sosa tsakiyar kansa kadan cikin Dan tausasa harshe yace"
Maganar shigar mushrah cikin maganar MSS LAILAH akwai hadari sbd abune na sirri dakuma hadari sbd neges nada mutane ko Ina
Akwai hadari zuwanta is too risky Kuma tareda umnn ummn Imran din ma is....
Wani Abu maleek din ya Dan hadiye batareda ya kalli mr Omar din ba yace"
Yaushe ne tafiyar daukan lailan??
Gobe ne Inshallah da karfe Tara na safe yace sbd jirginsu zai tashi karfe goma na safe.
Shiru yayi na wani lokaci kafin ya miqe tsaye ya fuskanci kofar shigewa palonsa na kurya cikin kamewarsa da muryar asalin MALEEK dinsa yace"
Kaji da aikin fitarsu lailan daga qasar ita wannan ko haske waje gobe bazata gani ba zanji wannan.
Dan sunkuyar da Kai mr Omar yayi Yace"
Maleek tariga ta amince da cewar zataje ko Zan sanarda jekadi dokar kada abarta fitowa din sbd kada taje din batareda ankarewar muba....
Kallo daya maleek yayi masa yayi saurin Dan soke Kai Yana cewa"
Nagane zanji da fitarsu lailan gobe
Saida safe ahuta lafiya.
Sidadewa yayi ya fice daga sashen gabaki daya Yana murmushin dayasan na menene shikadai sbd duk duniya ko motsi maleek yayi yasan me yake nufi bare kallonsa wannan wata baiwace da Allah ya hadasu akanta shiyasa Babu me iya sanin sirrin tsakaninsu cikin ransu Allah yasaka musu qaunar junansu Dan dai shi Yana qarqashin maleek din ne yasa maleek nasa kulawan yake a boye shikuwa dama ko ransa zai iya badawa akan maleek.
Yana fitowa gabaki daya daga sashen na maleek ya ciro wayarsa ya Nemo numbern jekadi ya Danna Mata Kira Yana kokarin daidaita kansa Dan cika aikin ubangidansa tana dauka Kai tsaye yace"
Zuwa anjima maleek na buqatan ganinta a rakata sbd tsaro.
Yanayin yanda yayi maganar yasa jekadin amsawa tana satar kallon NURU wadda ke zaune Palo farhat na jikinta suna kallon cartoon din da hankalinta baya wani kai duk da dai tana Dan murmusawa kadan idan akai abin dariya.
Sai da akayi sallar ishai suka tashi sukai sallah suna idarwa tasa aka jera abinci sbd farhat Dan ita Bata wani Jin yunwa tadaisha sabuwar madarar raqumi me dumi wadda kullum ake kawowa safe da dare daga sashen Anneti.
Suna gamawa suka nufi daki farhat ma dakinta ta nufa tayi wanka Da kanta ta shirya cikin kayan bacci tazo dakin NURUn ta haye gado ta kwanta.
Wanka NURUn tayo itama ta fito ta shafa Dan neu oil kadan ajikinta tareda shafa body mist da sprays masu sanyin qamshi ta daure gashinta da band qarami ta dauko rigar bacci me tsantsi tasaka ta nufi gadon zata hau taji knocking din kofar dakin ta juya ahankali tana kallon agogo kafin ta qarasa jikin kofar Dan tasan jekadice ta bude Kai tsaye.
Ajiyar zuciya jekadi ta sauke tareda kallon NURUn tace"
Maleek na buqatan ganinki yanzu.
Shiru tayi tareda kallon jekadin cikin mamaki a natse zatai magana saita fasa ta juya Takoma ta dauko sabuwar free jallabiya ta saka akan rigar baccinta dako bra batada ajiki ta zari qaramin gyalen rigar ta rufe kanta ta kalli farhat tana Dan shafa kanta yace"
Ina zuwa sweetie kinji.
zuro slippers tayi ta fito jekadi na gefenta suka nufi sashen nasa.
Suna Isa har kofar palon kuya jekadi ta rakata ta dakata daganan tareda kallonta cikin nutsuwa tace"
Afito lafiya" ta juya ta fice daga sashen gabaki daya masu tsaron gurin suka sake rufe sashen duka.
Bude kofar tayi a natse tashiga da siririyar sallama bakinta.
Sanyi da qamshin turarensa ne suka cika palon ba motsin komai sai tv dake aiki itama murya can qasa kaman Koda yaushe.
Baya palon Dan Haka ta daga Kai ta kalli kofar shiga bedroom dinsa sai taji shakkar qarasawa ciki Kai tsaye
Ta dauke Kai tana Dan sauke numfashi bugun zuciyarta na sauyawa ta daure ta taka ahankali ta Isa kofar dakin ta Dora hannu ahankali kan handle din kofar daidai ya bude kofar shima.
Tsayawa tayi cak tareda dagowa tana kallon fuskarsa dake fidda sirrin zallar kyawunsa.
Fararen idanuwansa ya zuba Mata Yana kallon fuskarta Batareda kowannensu ya motsaba.
Wani yawu ta hadiye tana sauke kanta qasa sbd Jin yanda suka matse sosai gashi qamshinsa direct yake shiga hancinta kamar yanda nata ahankali yake tashi Yana shigarsa.
Motsawa tayi ahankali zata kauce matsa daga kofar ya riqo hannunta ahankali tareda janta zuwa cikin dakin suka koma tareda rufo kofar ya saki hannunta ya nufi kujerar dake dakin ya zauna tareda daukan wayoyinsa Yana kashewa daya bayan daya batareda ya dagoba ya bude Baki cikin kamewa zaiyi magana ta qaraso gabansa cikin nutsuwa ahankali ta rigasa da cewa"
I'm sorry.
Dagowa yayi ahankali ya kalleta da fararen idanuwansa batareda yace komaiba ta dauke nata idon daga nashi tareda sake bude Baki zatayi magana ya miqe tsaye ya tsaya gabanta har suna Jin dumin numfashin juna ahankali can qasan maqoshi yace"
Uhum Ina sauraronki.
Shiru tayi sbd zuwa lokacin bugun zuciyarta yagama sauyawa ta rintse idanuwa ahankali ta bude tana sake motsowa cikinsa take wani yawu ya wuce Masa da sauri ta maqoshi ya kalleta zaiyi magana ta dago idanuwanta ta kallesa sai ya kasa maganar Ya kalli idanuwanta dake neman cikowa da hawaye ya lumshe ido yanajin mamakin saurin hawayenta dasuka bashi matsala aduk lokacinda yagansu
Ahankali ya daga hannunsa ya kamo qugunta ya qarasa mannota da jikinsa gabaki daya
Ta lumshe idanuwanta hawayen dasuka cikasu suka gangaro kan kumatunta yabisu da kallo yana zura hannuwansa cikin jallabiyarta ya zage zip din dake gaban rigar ta zame gabaki daya ta zube aqasa rigar baccinta ta bayyana ya kalli wuyanta zuwa qirjinta dake sama Yana qasa sbd numfashin datake fitarwa na bugun zuciyarta daya sauya
Kafin ya dago ahankali Ya kalli cikin idonta tasake rufe idanuwan sbd Jin hannuwansa cikin rigarta Yana zamewa
Rigarta na zamewa kasa ta shige jikinsa tareda qanqamesa sbd kunya da mutuwa da jikinta keyi ahankali.
Qanqamesa datayi shiya haifar Masa da tonuwar asirin zuciya da gangar jikinsa ya dago da fuskarta Yana kallonta idanuwanta a rufe taji bakinsa kan kunnenta Saida ya sakar Mata wani numfashi me dumin dayasa kafafunta sarewa ta zube gabaki daya ajikinsa ya riqeta dakyau Yana sauke numfashin kirjinta dake gugarsa dakyau can qasan maqoshi da wata irin murya taji yace"
*_Befik'iri wisit'i nenyi_*
sumewa takusa Yi ajikinsa lokacinda kalmomin suka shiga kunnuwanta
Dukkanin jikinta ya dauki rawa ta bude fararen idanuwanta dasuka sauya take hawaye suka ciko cikinsu ta dago amatuqar sanyi ta kallesa tana kasa yadda da abinda yace saiga hawayenta na gangarowa
Ya Dora hannunsa a inda yasata rinte ido da sauri Yana dauke numfashin kafin tajin saukan bakinsa cikin nata tareda dagata sama gabaki dayanta ya Dora kan gadonsa har lokacin bakinsa na cikin nata wannan karon tun daga Nan tasan yau labarin dabam ne musamman dataji Yana sauyawa bakinsa gurin zuwa nishinsa na daukan sauti ahankali ahankali.
Karfe bakwai na safe afia ta qaraso sashen NURUn cikin shirinta tsaf duk da bada ita za'a ba ita airport zataje ta jirasu acan zatai bankwana da mum dinta.
Kallon farhat dake bacci ita kadai kan makeken gadon NURUn tayi cikin mamaki kafin ta waiwaya kofar toilet da bataji motsin komaiba ta nufa kofar toilet din tai knocking tareda budewa tana leqawa da Alama ma toilet din Babu Wanda yashiga Dan babi digon ruwa a kasa
Ta dawo ta zauna bakin gadon ahankali tareda Dan taba farhat tana tada ita ciki kulawa tana cewa"
Baby tashi lokacin sallah yayi kiyi sallah.
Bude idanuwa farhat tayi cikin bacci tana cewa"
Zanyi tareda Aunt NURU idan tadawo daga gurin daddy.
##MAMUH#
****************
'Dan shiru afia tayi Dan Kamar Bata fahimci abinda farhat din tafada ba ta sake Kiran sunanta tana tadota gabaki daya ta zaunar da ita tana cewa"
Ina aunt dinki tashiga bangantaba.
Mutsitsika idanuwa farhat tayi tareda budewa tana 'yar guntuwar hamma ta baccin yasaketa ta kalli afia din tace"
Bata Nan jiya jekadi tace Daddy na Kiranta tatafi.
Shiru afia tayi tana neman dauke wuta sbd wani dumm dataji kunnuwanta na dauka saidai har lokacin takasa fahimta gwari gwari takeson ayi Mata Dan Haka tasake kallon farhat din tace"
Dad ya Aiko Kiran jiya da dare?
Data tafine haryanxu Bata dawoba kokuwa tadawo yanzu tasake fita??
Saukowa gadon farhat tayi tana cewa"
Bata dawoba."toilet ta nufa ta shigewarta tabar afia daskare agurin tana dulmiya cikin wani irin dogon nazarin tunanin
Shin lafiya dai??kokuma tace menene zaisa NURU kwana gurin dad?kodai wani abin yakuma faruwane Dan ita Sam Bata kawo wani alaqar aure a tsakaninsu sbd sanin yanda auren ya wakana da sanin Koda dad dinta da mum sun rabu har abada NURU sa'ar'yarsace ko kallon Mata baya Mata bare har wani Abu da Mata ke iya yiwa Miji Dan Haka Bata kawo wani tunaninba bayan na wani abun yafaru ita babbar damuwarta yanzu lokaci na tafiyar Mata.
Dagowa tayi tana kallon agogo kafin ta miqe tsaye ta fita zuwa Palo tana duba wayarta cikeda takaicin yanzu ko waya NURUn batada bare ta kirata.
Da jekadi dazata kitchen da Akira gefenta daukeda wani qaton tray da abubuwa akai saidai rufe da wani farin kyalle me adon zaiba ta kallesu ta kalli tray din ta maida kallonta kan jekadi tace"
NURU fa???
Kallonta jekadi tayi cikin Dan Bata nata girman tace"
Batanan saidai ko Zaki dawo zuwa anjima ko gobe.
Anjima ko gobe???"tafada cikin mamaki da Dan daga sauti kafin ta Dora da cewa"
Yanzu nake buqatan ganinta uzurine me girma.
Murmushin manya jekadi tayi cikin ranta kafin ta kalli afian tace"
Uzurin gabanta ya zarce kowane uzuri idan Kuma a matse kike da magana da ita ki Fadi sakonki Zan isar mata.
Da kaina nakeson isarda saqon tana Ina?
Kai tsaye jekadi tace"
Ki nemi maleek zai sadaki da ita.
Wucewa jekadi tayi Akira tabi bayanta suka wuce kitchen Dan fara hadin kayan dasuka zo dasu Wanda musamman na NURUn ne.
Kamar wawuya Haka afia ta tsaya agurin harsuka bace Mata
Take taji tashin hankali na neman shigarta sbd Bata fatar abin dazai kawo matsala akan fitar mum dinta hakama takasa yadda Sam da cewa Wai NURU gurin dad dinta takwana
Shin dama tana zuwane itace Bata saniba kokuwa yaune zuwan na farko?
Sashenta Takoma ta zauna tana sake duba agogo saura AWA daya da mintuna atafi can din
Bata tsaya tunanin komaiba ta daga wayarta ta Nemo numbern dad dinta Kai tsaye ta Danna kiransa.
Kiran duniya tayiwa wayoyinsa Babu me Shiga karshe ta Nemo numbern Mr Omar ta saka Kira tana fatan shi tasamu tasa wayar.
Ringing din dataji wayar tafara yasata sauke ajiyar zuciya tana fatan Yana tareda dad dinta duk da tasan da wuya idan takalli lokacin.
Cikin nutsuwa ya dauka Yana cewa"
Good morning princess.
Morning Mr Omar
Inason magana da dad ga wayoyinsa duka akashe.
Shiru Mr Omar yayi kafin ya Dan gyara murya cikin nutsuwa da basarda zancen yace"
Wayoyinsa suna kashe ne sbd ayyukan da suka Dan Sha kansa kwanakin Nan musamman akan wannan case din kiyi hkr zuwa anjima idan yasamu kansa zai kunna wayoyin Zaki samesa Inshallah.
Cikin damuwa da Dan daga murya tace"
Maganar mum dinace ta Yaya Zan iya Bari zuwa anjima lokaci na tafiya Ina buqatan mgn dashi Akan NURU ne.
Ajiyar zuciya Mr Omar yasaki Yana sake daidaita murya Kai tsaye yace"
Maganar dayan lawyern miss lailah cikin dare anrigada an Samar muku wani lawyern sbd dayar lawyern da kuka dauka banajin zata samu damar zuwan Dan Haka ki nemi Imran jalal Kai tsaye Dan nahadashi da lawyern
Ki huta lafiya princess.
Kashe wayar yayi yabarta zaune tana fadawa cikin sabon tunanin abinda yake faruwa data kasa fahimtar komai amma dai babban abin dayafi Mata komai yanzu maganar mum dintace tunda anbasu lawyer abin yazo Mata da sauqi sauran zancen sayishi daga baya tsakaninta da NURU taji inda tashige.
Ahankali ta Dan motsa tana bude idanuwanta dasukai Mata nauyi sosai sbd rashin bacci da mutuwar da dukkanin jikinta yayi
Akan fuskarsa dake daf da tata idanuwanta suka sauka ta lumshe ido tana budewa ahankali kan bakinsa zuwa dogon hancinsa da idanuwansa dasukafi komai narkar da kuzarinta
Da Alama baccin yakeyi har lokacin be tashiba ta sake motsawa ahankali daidai fararen idanuwansa da gabaki daya suka sauya zuwa wani sabon yanayi na budewa ya zubasu akanta
Ta rufe Bata ahankali tana shigar da kanta jikinsa dake manne da nata
Ya motsa ahankali tareda matso da fuskarsa ya hade hancinsa da nata yana sakar Mata numfashinsa me dumi ya bude Baki yace"
Good morning.
Bude idanuwanta tayi tana kallonsa a kasalance da kunyar gaisuwar saidai gabaki daya bakinta ya mutu murus batada qarfin iya magana
Ganin kallon datake masa kwayar idanuwanta na bayyana sirrin zuciyarta akansa ya riqo hannuwanta Yana sarqewa da nasa suka sauke ajiyar zuciya atare
Ya matso da fuskarsa Yana zura kansa cikin wuyanta dake bayyane ba Kaya ajikinta har lokacin sbd bayan tasamu tayi sallar asuba daqyar ya sake rabata da komai ya qarasa bude hanyarsa dabai Gama budewaba Dan Haka baccin wuya da muguwar kasala ya dauketa sai yanxu data farka
Tanajin dumin lips dinsa cikin wuyanta Yana saukar Mata da wasu irin kisses tareda numfashinsa me dumi da sauti ta lumshe ido tana sake Rena kanta Dan kuwa ita kadai tasan irin tsananin wuyar datasha tsakanin Daren zuwa safiyar sbd ko qafarta daqyar take iya motsata
Tanajin hannuwansa na yawo tsakanin wuyanta zuwa kirjinta zuwa cikinta da bayanta ta qanqamesa cikin tausayin kanta Dan kuwa Babu inda baya ciwo ajikinta musamman kirjinta daganan numfashinsu ya sarke Yana daukan sauti musamman nashi dayake fita sosai Yana fada Mata wasu kalmomi cikin yarensu acikin kunnuwanta wainda suke Bata qwarin jure Masa.
Baccin wahalane yakuma daukanta wannan karon wuyar dataci a bayyane take qarara sbd ko numfashinta ahankali yake fita cikin sanyi datake baccin
Ya kalleta Yana gyara Mata kwanciya ajikinsa tareda shafa fuskarta Yana lumshe ido.
Qarfe goma Sha daya harda mintuna ya farka ya zare jikinsa ahankali daga nata ya gyara Mata rufa Yana shafa lips dinta dasukai kaman sun bushe alamar tsutsan dasuka kwana suna Sha ya saki guntun numfashi tareda Dan rankwafowa yai kissing dinsu ya juya ya shige toilet.
Bayan fitowarsa shiryawa yayi cikin wasu fararen Armani kaftan dasukai matuqar daukan fatarsa dake glowing fuskarsa a kame yafito Yana kunna wayoyinsa Kai tsaye ya nufi palonsa na farko daya ganawa da Mr Omar Yana Isa Mr Omar na palon tsaye Yana waya da commissioner daya tabbatar musu da ankama yakoob Wanda yaqi fadar komai sai cewa komai duk azabar da ake bada.
Kashe wayar Mr Omar yayi ya waiwayo yayiwa MALEEK kallo daya ya Dan sauke kansa cikin 'yar sakewar murya yace"
Barka da fitowa MALEEK.
Zama yayi Yana amsawa tsananin kwarjininsa da qamshinsa na cika palon da idanuwan Mr Omar din
Ya matso ya zuba Masa lemon tea me zafi ya ajiye gabansa Yana Dan fara Masa wasu bayanin sama sama shikuma Yana sauraronsa batareda yace komaiba.
Shigowar jekadi ne daukeda tray na silver me Dan girma daukeda dafaffiyar Nonon raqumi da wani ruwan madaran na musamman sai Dan breakfast Mara nauyi
Sai wata kyakkyawar qaramar jaka dake hannunta na akayan NURUn dake ciki wainda ayau din akai odarsu aka kawosu
Cikin girmamawa tace"
Allah ya qarawa maleek lafiya da walwala
Barka da tashi.
Da Kai ya amsa Yana daukan wayarsa dake ringing ta sudada ta wuce cikin palonsa na gaba ta ajiye komai akan dining ta koma palondasu maleek din suke shima ta zuba Masa breakfast kadan yafara ci Mr Omar naci gaba da koro Masa bayanai.
Sai Sha biyu ta farka ta bude idanuwanta dasukai mugun nauyi fuskarta harta Dan kumbura kadan ta dafa ta tashi zaune tana sauke ajiyar zuciya ahankali tareda rufe ido ta bude tana zuro qafafunta qasa saidai abinda takeji batajin zata iya tashi tsaye.
Shiru tayi agurin zaune tana kokarin miqewa cikin dauriya taji anbude kofar dakin
Bata buqatar dagowa sbd tasan shine yashigo
Jin shiru yasata dagowa daidai isowarsa dab da ita ya rankwafo baice komaiba ya dauketa gaba daya
Tayi qasa da Kai tana rufe idanuwanta yakaita har cikin toilet ya kwantar cikin ruwan dumi ya kalleta tareda shafa gefen fuskarta ya matso da tashi fuskar yakai bakinsa kunnenta ahankali ya furta"
Sorry.
Zamewa tayi ta kallesa ya sake shafa fuskarta ya juya ya fice yabarta da mamakinsa Bata fito daga mamakinba sai ganin jekadi tayi cikin toilet din da sauri ta zame cikin ruwan tana shigarda jikinta ruwan tana rufe ido
Kenan shine yake cewa tayi hkr.
Cikin nutsuwa jekadi ta qaraso gurinta tana cewa"
Ni tamkar uwace karki ji komai magani kawai zanbaki wannan sirrinkine da mijinki Nima sbd baisan yazaiyi mikin bane kisamu kyakkyawar kulawa.
Ruwan zafi ta kunna ruwan da NURUn take ciki suka dauki zafi Sosai
Ta bude wata babbar kwalba cikin kayan data shigo dasu ta zuba cikin ruwan take toilet din yadauki wani qamshi NURU kuwa tanajin ruwan na shigarta ta koina jikinta yafara Dan sakewa Yana Mata wani iri
Jekadi taqara zuba Mata wani abun daban kafin ta dibi ruwan zafin ta zuba cikin wata roba tayi hade hadenta ta ajiye Mata tace"
idan kingama wankan kiyi tsarki da wannan.
Juyawa tayi ta fice sbd tausayin NURUn takeji sbd alamun dasuka nuna tana cikin mawuyacin hali.
Wanka tayi sosai taji dadin jikinta tayi tsarki da ruwan da jekadin ta jiye Mata tun alokacin taji wani irin sauyi Sosai agurin ta Gama tafito ahankali daureda towel ta nufi gaban mirror dinsa ta shafa mansa tareda spray ta dauki kayan data gani an ajiye Mata Wanda da Alama jekadi takawo ta daga kayan tana kallo dukkaninsu Babu me nauyi duk na Shan iska ne
Bata wani damuba sbd jirin datake gani ta saka wata doguwar qaramar riga Mara nauyi tayi drying gashinta daqyar ta 'daure da sabon band fito palon tana tafiya ahankali jekadi dake tsaye dining tana jiranta tai Mata sannu tareda ja Mata kujera ta zauna tana gabatar Mata da abubuwan dazata fara Sha kafin komai.
Daqyar ta daure Tasha duka ko abincin Bata iya tsayawa taci ba Takoma daki ta kwanta
Jekadi ta tattare kayan ta fice dasu
tana fita Mr Omar ya sulale yabi bayanta Dan bawa maleek lokacin hutawa
Ya miqe ya koma ciki Yana duba lokacin sallah da yayi.
##MAMUH#
*_Mamuhgee 47_*
Bacci takeyi har lokacinda ya Shigo din,ya kalleta tareda sauke boyayyar ajiyar zuciya ya juya ya nufi toilet yayo alwala yazo ya fice batareda ya tada ita ba Dan baccin Yana Bata nutsuwa da damar yanayinda takeji.
Yana fita bada jimawaba ta farka ahankali ta tashi zaune itama tayo alwala tazo tayi sallar Takoma ta kwanta tanajin zazzabin datake ji na qara shigarta ta lumshe ido tana sake shigewa bargo idanuwanta a rufe.
Qarfe goma aka Isa da lailah airport acikin wata sirrantacciyar mota
Lokacin afia tafi mintuna ashirin agurin tana jiran isowarsu Dan Haka tana ganinsu ta fiddo doguwar jallabiya da Dan qaramin mayafi da goggles datazowa da mum din Tata dashi ta nufi motarsu itama tata fuskar Bata bayyanataba yanda za'a gane itace ta bude motarsu ta shiga baya inda mum dinta ke zaune tana kakkama jikinta tayi wani duhu cikin kwana biyu ga wani irin tsamin dauda da wahala na tashi ajikinta
Cikin tsananin baqin cikin ganinta Haka da kaunar mahaifiyarta me qarfi afia ta rungumeta gabaki daya tana cewa"
Mum.
Zarewa Lailah tayi ta kurawa afia ido idanuwanta na cikowa da hawayen tsananin baqin ciki da dumuwa tarema da tsoron halinda rayuwarta tashiga kokuma ma Wanda tariga tashiga,
Ahankali ta bude Bakinta dake rawa wani tsamin Baki ya feso yacika motar Amma afia ita Sam batama jisa sbd Babu abinda uwarta zata zama ta gujeta da rawar murya tana hawaye tace"
Afia,afia my baby,afia my little princess I'm sorry baby ki yafewa mum dinki Amma ki yarda Dani bantaba aikata kisa ba Kuma bazan taba aikatawaba...ban aikata ba...bazan taba iya aikatawaba...ban aikataba...banyiba...
Riqota afia keyi tana cewa"
Mum mum na yarda Baki aikataba
Mum na yarda
Na yarda mum".ganin mum din takasa daina fadar Bata aikataba cikin firgici Kamar lokacin abin ke faruwa yasa afia rikicewa tana korarin kwantar Mata da hankali cikin kulawa hankalinta na neman tashi sbd ganin alamun kaman mum din har lokacin tana cikin shock saidai Kuma....
Imran ne cikin hali na damuwa daya shiga akan lailan tun lokacinda Mr Omar yayi Masa bayanin komai gameda Dan tabuwa da kan lailan yayi sbd Shiga hali na shock lafiya zata ringa komai Kamar yanda take sai dai idan ta tuno abindaya faru na kisan abin zai dawo Mata zata fara fizgewa tana fadar ba ita tayiba cikin tsananin tsoro da firgici,
Shi kansa bazaiso afia tasaniba sbd hankalinta zai tashi yakoma kan kula da neman lafiyar mum dinta bazata taba maida hankali kan karatuntaba Kuma Dan Haka shima ya shirya kula da al'amarin bazai Bari tasaniba yanzu sai tagama kammala karatunta tsaf yanama fatan zuwa lokacin lailan tasamu lafiya Dan Haka shima ya yanke shawaran komawa Vegas gabaki daya zai zauna da lailah Dan nema Mata lafiya ta dawo daidai ta gyara rayuwarta ta ingantata yanzu kan tunani da hanyar dazata bullar da ita sbd Lailah tamkar uwa ya dauketa Dan kuwa itace wadda tafi sonsa aduniya bayan iyayensa sbd itanema yake Paris baibi iyayensaba Koda tabar maleek dasu afia Basu rabu ba shida ita Kuma sbd itane yake tareda maleek Yana aiki a qarqashinsa farko sbd ya kula dasu farhat dasuka shaqu.
Ajiyar zuciya ya sauke ahankali tareda fitowa ya zagayo yashigo bayan ya zauna dayan gefen lailan suka sanyata tsakiyansu ya dago ya kalli afia data fara shiga firgici cikin kulawa da kwantar Mata da hankali yace"
Tana cikin damuwar abin daya faru sbd case na zargin kisa wani abune da bakowa ne zai iya daukaba
Dole zata shiga wannan halin musamman yanzu data fito Kuma taganta agabanki Dole zataji wannan damuwar da shauqin son sanar dake ba halinta bane.
Hawayene suka gangarowa afia ta rungumeta tana sakin siririn kukan tausayin mum dinta ta dago tana kallonta tace"
Mum Inshallah komai yariga ya wuce bazai sake dawowaba
Ki yarda da wannan wata jarabawace Allah yayi Miki danki gyara Kuma Inshallah nasan kin gyara mum kimin alqawarin bazaki sake zuwa gizah ba sbd bakida abinda yarage Miki anan sai tarihi.
Kallon afia kawai lailah keyi da idanuwanta dasukai jajir tanajin radadin abubuwa da dama data rasa arayuwarta sanadin son zuciya da son Rai,
Ta rasa MALEEK namijin da bazata taba samun kamarsa ba a fagen komai Dan kuwa ya nuna Mata so da kauna da gata da kulawa da komaima Amma duk ta watsar ta tsallake a tunaninta zai zauna dakon jiranta,
Ta rasa Farhat dinta yarinyar da Bata morewa komai na soyayya ko kulawar mahaifiyaba da shaquwa Dan kuwa tasan NURU tariga tashiga ran farhat ta yanda bazata iya rabuwa da itaba ko yiwa wani kallon uwa idan ba NURUn ba,
Ta rasa darajarta,sunanta,mulkinta, dukiya da career dintama gabaki daya
Afia ce kawai abindake gareta yanzu sai Imran datasan har abada shima bazai gujetaba adaidai yanzu datafi buqatan masoyanta atareda ita.
Kama hannun afia tayi ahankali hawayenta suka gangaro kan fuskarta ta kalli afian tareda gyada Mata Kai tace"
Nayi alqawarin Inshallah bazan qara zuwa gizah ba sbd Nima na tabbatarda banida sauran komai anan sai tarihi Wanda bana alkhairi ba Dan kowa zai ringa tunoni amatsayin wadda tayi kisa labarinta ya Bata.
Sake karyewa zuciyar afia tayi da tausayin mum dinta ta yanda lokaci daya ta rasa komai Kuma tana fatan zatai tawakalli ta karbi hakan.
Kayan data shigo Mata dasu ta Sanya Mata tareda rufe Mata fuska ta Sanya Mata goggles din ta bude motar suka fito dukkaninsu ta sake damke hannun mum din cikin kulawa da qauna ta tsakanin 'da da mahaifi tace"
Mum ki kula da kanki Zan ringa kawo Miki ziyara lokaci lokaci kinji¿
Ajiyar zuciya lailah tayi tareda kallon afian akaro na farko rayuwarta tace"
Allah yayiwa rayuwarki albarka afia
Allah yabaki 'yayan dazasu San darajarki irin Haka da Miki biyayya.
Amin tace ahankali tana dagowa ta kalli Imran tace"
Mum na hannunka.
Guntun murmushi ya saki Yana gyada Kai yace"
tana hannu mekyau.
Murmushin yaqe tayi tana cewa"
Thank you.
Kama hannun lailan dake waiwayen afia tana daga Mata hannu yayi suka wuce itama afian tana musu har suka bace Mata ta saki numfashi a hankali tanajin nutsuwa ta juya ta fada motar da kanta ta jawo ta tada taja tabar airport din.
Ko data koma sashenta ta nufa sai alokacin tasamu nutsuwar cin abincin data manta rabon dataci
Taci ta koshi ta miqe ta wuce bedroom dinta tayi sallar azahar ta kwanta Dan tasamu baccin dazai qarasa wargaza damuwarta Dan kuwa dukkanin damuwarta ta yaye takeji.
NURU zazzabi yakamata sosai Wanda ya Hana musu bacci da daddare daga ita har maleek din sbd sosai jikinta yayi zafi tana kwance cikin jikinsa Yana rage Mata zafin jikin da nasa Dan kuwa yanajin yanda dumin jikin nata ke shigarsa Yana saukan Masa da kasalar sake shigar da ita jikin nasa itakuma tana lafe tana sauke numfashi ahankali cikin sanyi.
Kallonta yayi cikin Dan qaramin hasken dakin Ya shafa bayanta ahankali Yana sake ce mata"
_Azinalehu_ (Sorry) cikin kunnenta da wata sirrantacciyar muryarsa da tsakanin jiya zuwa yau tasanta.
Ahaka yayita lallabata suka samu bayan sallar asuba tasamu bacci ya dauketa me nauyi sai alokacin yasamu nutsuwar kansa ya gyara Mata kwanciya tareda fitowa Palo sanyeda milk jallabiya me taushi ya zauna Yana daukan wayoyinsa ya kunna sbd yau yakeson Kai qarshen matsalar komai tunda sungama hada dukkanin shedodinsu dasuka tabbatar musu da zarginsu Akan Wanda suke zargi
Yana buqatan komawa Paris kodan rashin lafiyan Nan daya sameta.
Mr Omar yakira Kai tsaye yace"
A bayyanarda duka shedu akan yakoob a cikin kotu yau.
Cikin girmamawa Mr Omar yace"
Maleek haryanxu Yana maganar son ganin 'dansa Kuma idan aka bayyanar a kotu cewan 'dansa ne ya mutu zai iya bayyana komai a gaban kotu Wanda zai taba gizah da Kuma Anneti sbd al'amarin zaizo Mata da tashin hankali tunda Bata taba tsammanin hakan ba daga Wanda take aure
Kana ganin yakamata mu fitar da zancen duka a kotu?
Yan media zasu yada abin fiyeda komai ta yanda zai Yi Muni.
Shiru maleek yayi na wasu mintuna kafin yace"
Yanada damar yasan mutuwar dansa saidai baida damar fadar komai bayan abubuwan daya aikata da wannan za'a yanke Masa hukunci basai anbari yafada komaiba bayan wannan.....
Shiru yayi Yana kokarin daure abin dayake ji a zuciyarsa dasuka bayyana a idanuwansa yaci gaba da cewa"
Neges Kuma sbd daraja ta auren Anneti zanji da matsalarsa ta cikin gida batareda duniya tasan abin daya aikataba sauran haqqin Rai dake kansa Kuma tsakaninsa da ubangijinsane.
Cikin yanayi na sanyi shima Mr Omar yace"
Allah ya kyauta ya sake tsare imaninmu
Allah Kuma yaqara maka tsarkin zuciya.
Ba Haka suka so ba duk su dukan Amma Kuma wani lokacin kanayin abinda shine zaman lafiyar kowa da Hana fitina.
Lokacinda aka tafi da yakoob har mortuary aka jawo gawa tareda yaye Masa yaga gawar 'dansa amed datai fari tas sbd ajiya da sanyi.
Sarewa qafafuwansa sukai sbd firgicin ba zata daya fizgesa lokaci daya da wannan mugun ganin dayayi
Cikin tashin hankali ya zube gaban gawar Yana ihun Kiran sunan"
Amed Amed Inidēti ibakíhìni¿
Yaushe wannan mummunan Abu yasameka batareda nasaniba?
Amed katafi kabarni Banda kowa sai kai.
Dagowa yayi cikin ficewa hayyaci da tashin hankali ya kalli Mr Omar Yana cewa"
Meyasa???meyasa??
Ta yaya?
Yaushe kuka kashesa?
Meya muku?
A Daren ranar daya tafi aikin neges yamun saqon cewa Yana lafiya tafiyan gaggawa yayi.....ko shekaran jiya yamun sakon Yana lafiya Dana kira..yaushe kuka kashesa.....
Kukan tashin hankalin masifa yakeyi sbd sanin tsaf wannan umarnin maleek ne ya sake gangaro da hawayen baqin ciki jikinsa na daukan rawar Shiga tashin hankalin rashin tsammani na wannan afkuwar dabai taba kawowa aransaba ya rasa dansa kwalli kwal Wanda duk suke wannan fafutukar rayuwar dansu tsira su Tara abin kansu su gudu wani gurin su Gina rayuwa.
##MAMUH#
KUYI MANAGE YAU INADA UZURI DAN ALLAH.
*_Mamuhgee 48_*
Kallon yakoob Mr Omar yayi Yana gyara tsayuwa yace"
Allah ya yafe Masa kurakurensa tareda Kai mahaifinsa daka dorasa akan irin wannan rayuwar da batada hanyar bullewa ko a duniya ko agurin ubanginka,
Son Rai da bin zuciya qarshensa baida Dadi yakoob Amma tunda kune kuka zabi hakan hakan shine daidanku,
Babban kuskuren daka aikata yakoob shine sako 'danka da baida kwarewa acikin wannan harkar dakai ka Jima da dadewa acikinta Dan kuwa gashi kuskurensa yakaisa ga Haka kaima yakaika ga hakan.
Allurar meriz ce ta kashesa kaman yanda kukai amfani da ita Dan kashe tsohon NEGES mahaifin maleek Kuma kukaso kashesa da ita,
Kun aikashi kashe padima saidai kun manta cewan a sashen maleek ne take
Kuma a sashen Babu wani lungu da Babu camera a maqale Wanda idonku da zuciyarku sun rufe da aikata hakan kuka saka Amed disconnecting dinsu Wanda ko karatun addini bayadashi bare na zamani Dan Haka ta Yaya kuke tunanin zainiya ciresu.
Ranarda muka samu labarin zuwan lailah gizah muka tabbatarda akwai dalilin zuwan nata Wanda anyi kirantane Dan ayi amfani da ita hakan yasa muka sauya tunani ta hanyar Dena shayarda padima meriz sbd ga hanyar sauki tazo Mana,
Tunda neges yayi magana da lailah tafara bibiyar jekadi Wanda jekadi tagane hakan ta sanar Mana daga lokacin mukasan meyake faruwa har lokacinda muka tabbatarda amed na bibiyar lailah itama bamui wani motsiba muka barku Dan ku aiwatar da naku Shirin dazai bamu tamu damar.
Kaf gizah Babu Wanda yasan da padima na cikin masarautar shiyasa muka kyaleku Dan munsan Dole bazaku barta ba duk da batasan ainihin waye yasakata aikin daya sakata ba ahaka rashin nasararku yakaiku aika amed kashe padima wadda taji sauki da kanta zata iya Kare komai kuma a Daren ranar jekadi ta miqa Mata allurar meriz a hannunta ta sanarda ita duk Wanda ya shigo kawo Mata farmaki ta tabbatarda ta kwaci kanta da allurar Wanda hakan zai fidda ita daga wannan rigimar gabaki daya har abada.
Padima na son ranta fiyeda masoyinta amed Wanda shima yakeson dukiya fiyeda rayuwarta Dan Haka a Daren ranar abindaya faru shine bayan yaja lailah da dubara zuwa gurin Dan kisan ya hau kanta mun gani Kuma mun sanarda jekadi komai kafin isowarsu gurin Dan Haka jekadi tasake nanatawa padima tana sane ya fito lailah ta doketa saidai bamuyi tsammanin amed yaqara doke jekadin ba yasamu ya qarasa dakin ya bige lailah ta hanyar kwada Mata katako akai Wanda ganinsa yasa padima shiga tashin hankali saidai Bata Bari tsoronta yabarta barin amed yasamu sa'ar kashetaba tayi amfani da matsayinta na mace ta nuna Masa kanta amatsayin su Raya darensu na qarshe kwadayin Zina yajasa ga rasa ransa batareda yasamu abinda yake kwadayinba.
Babu Wanda yasan padima na kasar tayaya Yan jaridar suka San waye aka kashe bayan Babu Wanda yaga gawar da idanuwansa wannan shine babban kuskurenku na biyu daya kawo karshenki batareda ansha wuyar hakan ba,
Padima ta kashe amed sbd Kare Kai itama Allah yabata nata sakamakon ta hanyar rasa cikakken hankalinta kamar lailah Da Haka kowa zai girbi nasa aikin.
Allah ya tsare Mana imaninmu yabamu kariya daga mutane kamarku Wanda suka Tara arziki ta hanyar kisa da miyagun ayyuka gashinan dukiyar Zaki tafi ku barta abawa mutane suna Kuma tsine muku.
Juyawa yayi ya fice yabar yakoob din tsaye cikin rashin sanin makamar tunanin Yi sbd dukkanin gangar jikinsa da jininsa sun tsaya cak Babu abinda yake motsi ajikinsa bayan zuciyarsa dake bugawa ahaka aka jasa Yana tangadi aka fice dashi
Take 'yan jarida aka sakar musu labarin suka fara yadawa cewan
Yakoob amintaccen bawan neges ne ya kashe tsohon NEGES na gizah
Take aka bayyanarda shedu dasuka hada da garin meriz dake ciki sarkar da padima ta taba boyewa da aka samu a sashensa gurin bincike.
Hankalin jama'ar gizah ya tashi tareda girgiza matuqa sbd kishin kishin fara zargin NEGES da akai Wanda yasa akai gaggawar yankewa yakoob hukuncin kisa ta hanyar cire kansa sbd kada ragewa fitinar tsayi
Amma duk da hakan ba a daina bayyanarda zargin NEGES ba Wanda yasashi kasa fitowa sbd tsananin kunyar kansa da baqin ciki me nauyi daya lullubesa sbd Kai tsaye ko an boye laifinsa saidai yasa jama'a yin shiru Amma wannan zargin da laifinma gabaki daya bazai rufu ba musamman da kaleeb da maleek sukai shiru sunki saka Baki a maganar sai hakan yasake bawa jama'a kwarin gwiwa aka fara kishin kishin sauke neges jama'a da jinin sarautar gizah da 'yan delah gabaki daya kowa yafito ya nuna sha'awarsa ta sauyin neges sbd kobabu saka hannunsa zamtowar bawansane ya aikata hakan to tabbas hakan ya shafesa Dan Haka gabaki daya kusan ya rasa girmansa da mutuncinsa a idon jama'a
Musamman Anneti da yakejin Kamar bazai iya hada idanuwa da itaba sbd girman kunyar abindaya aikata Wanda yasan itama yagama fahimtar komai saidai kawai tayi shiru sbd wani abin basai kafadaba Allah ya kyauta kawai yafi maka saukin fada
Da wannan ya kebe kansa da kansa a sashe dabam bayan ya fitar da wasiqar sauka mulki da kansa ya aika har delah gurin kaleeb Wanda har lokacin yaqi cewa komai bare maleek daya fara Shirin barin qasar bayan ya bayarda sunan Mohan YONAS (autan kaleeb) amatsayin Wanda za'a nada sabon NEGES na riqon kwarya kafin lokacinda zai karba Dan haryanzu Yana buqatan wani Dan lokaci kadan kafin yadawo gabaki daya ya karba gizah din.
******
Zazzabinta yayi sauki sosai ba laifi Dan kuwa Daren tasamu tayi bacci sosai sbd wani magani da jekadi ta kawo Mata Dan Haka gari na wayewa tun karfe shida da mintuna ta fito cikin doguwar jallabiya data rufeta koina ta nufi sashenta tana Isa ta wuce bedroom dinta tashige tana sauke numfashi ahankali kafin ta dago ta kalli farhat dake kwance kan gadonta tana bacci cikin nutsuwa
Ta qarasa gadon ta zauna tana kallonta tasaki murmushi ahankali tace"
Sweetie nayi missing naki da surutunki sosai.
Miqewa tayi ta zare rigar jikinta ta jefa cikin wardrobe ta nufi toilet ta shige.
Kodata fito komawa gadon tayi ta haye ta kwanta gefen farhat ta gyara musu rufa Takoma bacci sbd baigama isartaba.
Qarfe tara ta farka lokacin har farhat ta Jima da farkawa ta bude idanuwanta ahankali tana kallon farhat dake Kiran sunanta cikin murna da farin ciki tace"
Aunt NURU yaushe kika dawo?
Tashi zaune tayi tana gyara gashinta da murmushi akan fuskarta tace"
Sweetie na barci nadawo
Ya kike?
Fadawa jikinta tayi ta rungumeta tana cewa"
Next time idan zakije tare Dani Zaki Zan biki kinji Aunt NURU.
Wani irin Murmushi ne ya saukowa NURUn ta kalli hancin farhat din zuwa bakinta dasuke Zak Zak Dana dadynta saita sake sakin murmushi tana saukowa gadon tace"
Kinyi brush?
Biyota tayi tana cewa"
Eh nayi nace next time zakije Dani??
Tsayawa tayi tareda juyowa ta kalli farhat din ta kamo fuskarta taja hancinta ahankali tana murmushi tace"
Wannan hancin Ina sonsa sosai kaman yanda nake son sweetie dan haka kidainama tambayan idan zanje wani guri ba dakeba ok¿.
Cikin murna tace"
I love you too lewa.
Knocking kofa akai ahankali tareda bude kofar aka shigo
NURU ta dago tana waiwayowa kofar sukai ido biyu da afia dake kallonta da dukkanin hankalinta tana nazarin NURUn da akace batada lafiya saidai bataga alamar ciwo atareda NURUn ba jikinta ba inda ya nuna alamar akwai ciwo tareda ita ta karaso ahankali cikin 'yar kulawa da alamar tambayarta tace"
Jekadi tace bakida lafiya da fatan dai ba wani serious ciwo bane ko??
Murmushi NURU tasake tana matsowa gaban afia din tace"
Naji sauki kawai gajiya ce da rashin isashen bacci Amma yanzu lafiyana kalau.
Kallon cikin idanuwanta afia tayi tana kokarin karanto idan da akwai ciwon atareda NURUn tace"
Mezaisa ki kasa samun isashen bacci bayan kina samin hutu sosai bakida aikin komai a gabanki....
Aiki dad dinku yabani Wanda duk ya kawo hakan yanzu dai inason Baki hakuri akan rashin samun damar zuwana gurin mum dinki I am really really sorry for that Kuma Ina fatan komai yatafi yanda ake fata?
Ajiyar zuciya afia ta sauke tana qarasawa bakin gadon dakin ta zauna tana cewa"
Komai yatafi yanda akeso mum Dina tana Las Vegas tareda Imran Wanda yakoma can yanzu da zama da aiki sbd su manta rayuwarsu ta baya su fara sabuwar rayuwa Mara damuwa da Danasani.
Numfashi NURU ta sauke cikin ahankali tareda ajiyar zuciya tana kallon Afia da taushin murya tace"
Ina musu fatan kyakkyawar rayuwa me Dadi da amfani.
Thank you afia tace tana kallon fuskar NURUn data sauya Mata gabaki daya.
Wanka NURU tashiga ta fito cikin nutsuwa ta shirya cikin doguwar riga golden me sequence ajiki suka zauna dukkaninsu su ukun anan sashenta sukai breakfast tare suna gamawa suka dawo Palo suka zauna NURU na Shirin zuwa gurin Anneti afia ta kalleta tareda dawowa gefenta ta zauna cikin nutsuwa ta kalleta tana tattaro abinda zata fada Mata tace"
Shin kinsan case din kisan da mum take ciki padima ce wadda ake cewa ta kashe......
Wani irin kallo NURUn juyo tanayiwa afia din da dukkanin fararen idanuwanta.
Wata ajiyar zuciyar afia takuma saki tana dafa hannun NURUn tace"
Padima ce wadda dukkanin labarai da duniya ta shedarda an kashe....
Hawayen dasuka ciko fararen idanuwanta dasuka koma ja Nan take suka gangaro kan fuskarta ta sake kallon afian da kyau tana kasa gasgata zancen sbd bazai yiyuba babban zance irin wannan a boye Mata
'yar uwarta jininta aka kashe ace Bata saniba sai yanzu bayan wadda tayi kisan har ansaketa ta tafi Kuma maleek na sane da hakan,wane hali iyayenta suke ciki gameda wannan mummunan al'amarin na rasa padima itakuma Bata tareda dasu a lokaci irin wannan miqewa tayi zuciyarta da idanuwanta na rufewa da wani irin yanayi Mara Dadi da damuwa
Afia tayi saurin riqota tana Miqewa tsaye cikin nutsuwa da kulawa tace"
NURU ki kwantar da hankalinki anyi bincike angano komai da cewan ba padima bace kawai yan media ne suka juya zancen sbd basusan ainihin wayeba aka kashe angano komai yanxu tareda gano Wanda sukeda hannu a komai har kisan tsohon NEGES wato mahaifin dad dinmu komai ya wuce yanzu Inshallah...
Girgiza Kai tafarayi ahankali hawayenta na tsananta gudu cikin wani irin yanayi na toshewar Kai tace"
Bani wayanki inason Kiran abal Dina Ina buqatan Jin halinda suke ciki,
Ina buqatan magana da padima
Mezaisa padima ta zauna Nan har irin wannan Abu yasameta,
Ni gabaki daya ban fahimta ba,abal nakeson magana dashi yanzun Nan......
Cikin sanyi da son kwantar Mata da hankali afia ta miqa Mata wayarta tana cewa"
Dan Allah ki nutsu kada ki dagawa su abal din naki hankali idan har Basu saniba, ki tambayeshi ta yanda bazaki daga hankalinsu ba muji idan padiman na taredasu.
Bata tsaya sauraren sauran bayanin afia ba ta hau saka numbobin abal dinta ta Danna Masa Kira zuciyarta na rawa.
Kamar zata tsinke saigashi ya daga cikin nutsuwa da kwanciyar hankali yayi sallamar data Sanya NURU saurin riqe numfashinta tana seta muryarta tace"
Abal.
Jin muryar NURU yasa abal din tashi zaune daga kishin giden dayake Yana kallo a tv cikeda kewarta da kaunar 'yarsa yace"
NURU kece?
Kina lafiya?
Ya kike?
Yaya maleek da yaransa?
Shiru tayi zuciyarta na sake bugawa ahankali muryarta na rawa tace"
Abal Ina padima?
##MAMUH#
*_Mamuhgee 49_*
Shiru yayi Yana kallon padima data lallabo ta tsaya gefensa Jin sunan NURUn daya ambata tana kallonsa da idanuwanta dasukai wasu iri kaman me jiran sammaci ya Dan gyara zama Yana sake murya cikin farin cikin Jin NURUn yace"
NURU me padima zatai Miki??
Shiru tayi sbd jikinta daya fara sanyaya ta bude Baki da qyar tace"
Abal labarin rasuwarta nake samu yanzu duk tsawon lokacin Nan bansan meyake faruwaba Ina matsayin 'yar uwa Kuma 'ya acikinku
Dan Allah abal ka sanar Dani komai Kuma idan padima na Nan inason jinta ko yayane..
Wasu hawayen takaicine da sanyin jiki suka gangarowa ammynsu Jin abinda NURU ke fada
Abal kuwa nutsar da murya yayi cikin kwantarwa da NURUn hankali da murya Kai tsaye ta matsayinsa na mahaifinsu su duka yace"
NURU dagani har ammynku da meryam munanan lafiya cikin kwanciyar hankali da nutsuwa sakamakon Miji na gari me adalci da Allah yabaki,
Muna cikin masarautar delah a kebe cikin walwala da wadata tareda ni'imar duniya,
Saidai har gobe da kullum zuciyata takasa samun kwanciyar hankali na uban daya haifi 'yar da Babu Allah ko miskala zarratin acikin ranta face zuciya irinta kafiran farko da qyashi da hassada tareda taurin Rai yagama cikata,
Padima na nan da ranta saidai banajin tanada sauran qimar da Zaki cigaba da kiranta 'yar uwarki sbd ta nunawa duniya cewan Babu qauna ta jini a tsakninku har abada
Muda muka haifeta Dole zamu zauna da ita Amma ke Kam ba Dole sbd ta wuce iyakarta....
Tsananin sanyi jikinta yayi da kalaman abal dinsu ta sulale ta zauna bakin kujera ta zauna cikin sanyi da sagewa tace"
Abal meya faru?
Me padima tayi wannan karon?
Kai tsaye yace"
Padima taje gidanki da niyar rusa kyakkyawar rayuwar da Allah yabaki ta hanyar niyarta ta kashe mijinki Wanda tabawa gubar meriz yasha wadda Allah ne kawai yayi da kwanansa agaba da babushi Kuma niyarta shine su maqala Miki wannan sharrin da ita da mahaifin amed dama amed din....
Innalillahi wainna ilaihirrajiun
Innalillahi wainna ilaihirrajiun"
Shine kawai abinda tasamu bakinta yake iya furtawa ahankali idanuwanta na bushewa sbd tsananin firgici da tsoron maganar da abal din yafada cikin rawar murya tace"
Abal abawa padiman wayan Dan Allah...
Shiru yayi Yana shakkar hakan sbd har cikin ransa baya buqatan alaqar NURU da padiman yanzu ya dago ya kalli padiman datai tsamo tsamo da idanuwanta dasuka Gama jemewa ya miqa Mata wayar.
Karba tayi ta Dora akan kunnenta cikin sanyi tace"
NURU
Dakakkiyar ajiyar zuciyar karfin hali NURU tasake cikin kasa gasgatawa tace"
Padima menene abindaya faru???
Numfashi padiman ta sauke cikin muzantuwa da wata irin kunya da wulaqanta saidai Babu yanda zatayi bayan fadan gaskia ta bude Baki ahankali tace"
Dukkanin abinda abal yafada hakane,
Banida ciwon komai nai Miki karya naje gurinki da burina na dabam Wanda yakaini ga sawa maleek garin meriz Wanda zai kawo karshen rayuwarsa saidai hakan be faruba suka gane nice na aikata hakan
Sukaso hukuntani saidai Kuma Basu kaiga yin hakanba amed sukaso kasheni Dan boye tonuwar asirin dayasa na kashesa batareda nasan Yaya zanyiba
Maleek ya zabi da a boye Miki komaine sbd gudun shigarki damuwa....
Zubewa qasa tayi duk da NURUn Bata gabanta cikin tsananin damuwa da kanta daya fara juyawa alamar zata birkice tace"
NURU ki yafemun kinji
Kisa maleek ya yafemun kinji
Kisa abal ma ya yafemun kinji
Kisa ammy ma ta yafemun kinji
Bani nakashe amed ba shine ya kasheni na gudu na boye bayan maleek kinji,
NURU kisa mutanen gizah ma kowa ya yafemun kinji
Nima kisa na yafewa padima kinji,
Padima Tama lalata rayuwarta gashi yanzu takoma Kamar Mara hankali nake gani
NURU kinyafemun ko???.......
Shiru NURU tayi dukkanin jikinta na sake yin sanyi sbd daga maganganun padiman tagama gane kanta ya juye wannan rayuwar dame tayi Kama?
Wannan wace irin masiface me mummunan karshe Wanda zaikai bawa ga irin wannan makomar gashi padima da kyanta da cikar zatinta Takoma kayan kwankwani saika kwankwasa kaji sauti.
Cikin sanyin jiki da muryarta data toshe tace"
Na yafe Miki padima Allah ma ya yafe Miki yabaki lafiya idan kinada rabon warkewa.
Karban wayar abal yayi Yana cewa amin dukkaninsu jikinsu a Sanyaye sbd idan abin ya juyo padiman nada tausayi wani lokacin sbd lafiyayyan budurwa takoma saidai zaman gida sbd Babu Wanda zai iya aurenta ahaka saina Allah musamman abubuwan nata sunyi yawa,
Ga rashin budurci,ga mummunan zuciya data kaita ga hakan ga na karshe rashin hankali daya shigo.
Kallon meryam ammy tayi tana cewa"
Rakata daki ki zaunar da ita har abin ya lafa ta 'dan dawo daidai.
Kallonta Meryam tayi tana kamo hannunta ta jata itakuma tabita tana 'yan maganganunta qasa qasa batareda kowa yamaji me take fadaba sbd sanin batada zance saina a yafe Mata ba ita takashe amed ba amed ne ya kasheta.
NURU najinsu tayi shiru tana sake Jin al'amarin har cikin ranta dukkanin gabobinta sun saki takasa cewa komai
Abal cikin sanyi shima yace"
Maleek da kansa yasa aka kawomu Nan Dan mu samu sauyin rayuwa tareda boyewa duniya abinda padiman tayi Wanda bazamu taba daina gode Masa akan hakan ba
Ya allah yakara rufa Masa asiri duniya da lahira yayiwa rayuwarki taredashi albarka da zuriar dazaku samu agaba.
Amin ta furta daqyar sbd toshewar da muryarta tayi da mamaki da firgicin dukkanin abin dataji yanzun.
Miqawa ammy wayar abal yayi ammyn najin muryan NURU taji hankalinta ya kwanta sbd Koba komai sunada sauran 'yaya biyu dasuke fatan su zamo tafarki na gari agaresu Wanda zasuyi alfahari dasu duniya da qiyama.
Meryam ce ta sake sosai tayi magana da NURUn Wanda har lokacin Bata dawo hankalinta duka ba da Haka ta ajiye wayar tanajin sauran bayanin da afia ke koro Mata na NEGES da sauran labarin.
Sai alokacin hawayen tsananin son mijinta Da kaunar iyayenta suka gangaro Mata ta miqe ta nufi dakinta ta turo kofa ta zauna bakin gado tareda fashewa da wani irin kuka Mara sauri sosai tana rufe fuskarta da tafin hannuwanta sbd tabbas idan tace batajin tausayi da kaunar Yar uwarta tayi qarya saidai Kuma bazata iya cigaba da rabartaba Dan kuwa wannan wani al'amarine me girma daya rusa rayuwar farin cikin gidansu dasuka taso dashi Dan kuwa iyayenta har abada bazasu daina Jin damuwa da baqin cikin ganin padima acikin wannan halinba Dan haka tasan farin cikinsu Yi zai ringayi Yana daukewa Dan 'da duk lalacewarsa acikin Rai yake.
Sai yamma lis tasamu damar fitowa bayan ta sauya wanka da Kaya idanuwanta da fuskarta a 'dan kumbure
A shirye ta fito Dan zuwa gurin Anneti farhat da afia ma dake sashen har lokacin sbd takasa tafiya tabar NURUn cikin wannan halin suka miqe tareda jekadi da Akira suka nufi sashen Annetin wadda itama tana Dan daurewane sbd ita qaddara ba'a canzata Amma tana cikin hali na damuwa da baqin cikin wannan al'amari daya faru na NEGES Wanda a safiyar ranar ya tattara yakoma delah gabaki daya da zama sbd shirye shiryen Nadi da aketayi Wanda ake qara la'antarsa akan wasu abubuwan da dama
Anneti kuwa maleek ya hanata zuwa koina yace tayi zamanta a gizah sbd dama auren kawai sukedashi a tsakaninsu babu wani kebewa irinta ma'aurata dasukeyi sbd tsufa da manyanci daya Kama.
Ganinsu yasanyaya ranta musamman NURU wadda tagama samun tabbaci daga gurin jekadi cewar tazama cikakkiyar macen UBAYD MALEEK wadda a fili ya nuna hakan Kuma ko agurin kwanciya da ita ya nuna hakan sbd alamu dasuka nuna ba so daya ya sadu da itaba acikin daren wannan shine cikakkiyar alamar tasace ta har abada tasamu guri me girma a zuciyarsa da rayuwarsa da yardar Allah.
Kayan marmari aka kakkawo aka jere musu Anneti tasa aka kawowa NURU nata hadin wani sirrin daban suna 'yar Hira sama sama jekadi na miqo Mata tana Sha a Dan kunyace harsuka Gama sukai sallar magriba Basu barota ba sai bayan ishai
Suna fitowa afia ta kalli NURU cikin sakewa tace"
Meye sirrin wanna maganin da Anneti ke Baki?
Kodai na......
Kallonta da NURU tayi yasata dakatawa da zancen tana 'yar dariya.
Murmushi NURU tayi tana tafiya a natse tana cewa"
Idan nafada Miki sirrin bazaki iya bacci ba nikuma inason ki ringa samun bacci yanzu sbd ki koma AFIA UBAYD MALEEK dinki ta asali duk wannan 'yar ramar ta fice.
Murmushi afia tayi tana cewa"
Thank you Ms NURU YONAS.
Suna Isa ko zama basuyiba saqon mr Omar ya samesu na cewa gobe zasu koma Inshallah Dan Haka su shirya.
Wanka kawai tayi tayi Shirin bacci ta haye gado ta kwanta da wuri sbd ciwo ciwon Kai datake ji.
Washe gari da safen kayanta ta hada acikin qaramar akwati saina farhat data saka Akira ta hada Mata ta shirya tsaf ta nufi sashen Anneti tareda jekadi dake gefenta tana sake nanata Mata wasu maganganun akan zama na aure.
Koda suka Isa ga mamakinta kusan kayayyaki ta tarar jere a tray Ana jiranta Kai tsaye Anneti ta nuna Mata kujera tana cewa"
Zauna jekadi ki nuna Mata komai yanda yake ta shanye shekara daya zasuyi ajikinta suna aikinsu.
Miqewa tayi ta shige sbd ganin yanda NURUn kejin kunyar Sha din
Tana shigewa jekadi ta zage tana zuzzuba matasu tana Bata tana shanyewa a wahalce sbd sunyi Mata qarfi sosai a Baki daqyar ta shanye kusan duka sauran daya rage ganin tana neman yin amai yasa Dole jekadi ta qyaleta.
Koda Anneti ta fito daukeda kyautar Dan qaramin akwatin turarukansu na asalin hadin Ethiopia masu wani irin kamshi kamar na turarukan oud ko itacen turaren wuta qamshinsu dai me sanyi da Sanya nutsuwa ta miqawa NURUn tana cewa"
NURU Allah yayiwa aure albarka.
Amin jekadi tace tana karbanwa NURUn wadda take godiya cikin girmamawa da ladabi kafin sukai bankwana suka fito.
Qarfe goma Sha daya suka fito zuwa airport har lokacin Babu Wanda yaga MALEEK acikinsu har suka Isa airport suka shiga jirgi jirginsu ya daga Saida suka Isa Paris suka sauka tukuna suka San bataredashi suka dawo ba shi sai bayan nadin sarauta zai dawo.
Ajiyar zuciya dukkaninsu suka sauke lokacinda suka fito daga cikin motar data ajesu daidai kofar shiga palon gidan
NURU ta lumshe ido tareda karanto adduar samun zaman lafiya da ingantacciyar rayuwa a gidan auren nata tayi bismallah ta jefa kafarta ciki da sallama tana kallonsu mum Sarah dasuka jera suna Mata sannu da zuwa cikin farin ciki da murnar dawowarsu.
Afia ma kusan adduar samun nasarar rayuwa da qarfin gwiwan cigaba da rayuwa kaman da tashigo tana murmushi wa su mum Sarah dasune kusan suke taredasu tun suna yaransu haryanzu Dan Haka yanzu ta yarda da cewa basai Wanda ya haifeka yake iya zama uwa agarekaba hakama basai jininka ne kawai zai amsa sunan 'dan uwa agareka.
Da wannan kowaccensu ta nufi dakinta sukai wanka da salloli suka fito cin abinci,
Sanyeda wasu riga da wando marasa nauyi ta fito gashinta a daure kyakkyawar fuskarta tayi fayau ta nufo dining din afia tabita da kallon burgewa sbd ita akoda yaushe tana yiwa NURU kallon kyakkyawar halitta me sanyin kyau da shiga zuciya saidai takasa ganewa ko ta yadda dad dinta da NURUn zasu iya rayuwar aure a tsakaninsu.
Ganin kallon da afia ke Mata yasata sakin murmushi Tana zama kan dining tace"
Thank you.
'yar dariya afia tayi tana cewa"
Kinma riga kinsan Ina yabawane kenan.
Wani murmushin takuma saki tana cewa"
Nariga nasan ko kallonki me yake nufi ai.
Suna Gama cin abincin kowaccensu ta nufi daki sbd gajiya da baccin dasuke buqata musamman gobe kowaccensu tayi niyar fara fita makaranta sbd satin zasu fara exams dinsu na karshe Inshallah kafin sukama ayyukansu na Gina career dinsu.
Rashin waya a hannunta yasa washe gari kafin su Isa makaranta tasa aka tsaya wani qaton shagon waya ta siya waya tasaka layinta suka wuce tana gani sakon baquwar number na shigowa wayarta batareda ta duba ba ta saka wayar jaka ta shige class.
Sai yamma suka dawo wanka tafara yi kafin ta Dan kwanta tayi hutun AWA daya da rabi kafin lokacin sallar magriba yayi ta tashi tayo alwala tazo tayi sallar ta Dan dauko takardunta zatai karatu sai alokacin ta duba wayarta ta bude sakon daya shigo dazun taga ansaka"
_Inidemìní āderíki kwēn of GIZAH_
(Gud morning Queen of gizah)
Wani irin Murmushi ne ya sauka kan kyakkyawar fuskarta har tana Dan dafe goshinta sbd wani yanayi data tsinci kanta bayan karanta sakon tasake kallon numbern ta Dan sunkuyar dakai tana murmushin sbd sanin tabbas MALEEK ne yayo sakon ta daga wayar ahankali tanason yimasa reply Amma takasa sanin me zata rubuta saita ajiye wayar tareda daukan takardunta tana karatu Wanda fiyeda Rabin hankalinta baya Kai Yana kan tunaninsa.
Kwana shida sukai da dawowa suna zuwa school aka fara exams Dan Haka kansu yadauki zafi Sosai musamman afia dasuke likitoci gabaki daya basuda lokacin kansu bare na gida shiyasa farhat ta daga musu kafa Dan itama nata karatun Yana daukan zafi yanzu sbd tashiga secondary yanzu.
Daga NURUn har afia gabaki daya kashe wayoyinsu sukai suka ajiye Saida suka kammala Kuma har lokacin maleek be dawoba sbd abubuwan dayakeson saisun daidaita a gizah kafin yabarota shiyasa shima ayyaukansa na Nan Paris suka taru ga hutu dayake buqata na duk wainnan gwagwarmayar da akai Yana buqatan samun nutsuwa.
NURU ce tafara gamawa da kwana biyu kafin afia Nan hankalinsu ya kwanta suka hau Taya juna murna tareda farin ciki har wani Dan party suka hada acikin gida na tsananisu su uku da farhat saisu mum Sarah da 'yan aikin gidan NURU da kanta tayi musu katoton cake suka yayyaknka abinsu aka bawa kowa sunata farin ciki dayake ciki Palo ne sukai abinsu Babu me wasu kayan nauyi ajikinsu
Ita afia jeans ne three quarter da blue da purple riga Mara dogon hannu
Itama NURUn pencil jeans ne dogo dayafi na afia tsayi ajikinta Ash daya kwanta jikin dogayen sirarun cinyoyinta da fadin hips dinta sai farar riga me hannun shimi ta nufi kitchen ta wanko hannunta daya Dan baci da cake ta fito duba massages dinta saiga Kiran abal dinta ta daga cikin farin ciki suna tayata murna da Dan mamaki tace"
Abal waye yafada muku?
Murmushi abal dinta yayi kawai ya bawa amminta ta tayata murna itama tareda Sanya Mata albarka aka bawa meryam Nan tahau ihun tayata murna tabawa afia itama sukai Mata adduoi da Taya murna ta karba wayan kenan ta Dora a kunnenta taji qamshinsa daf da ita sosai Yana Shiga hancinta tayi saurin juyowa ahankali tana sauke wayar daga kunnenta
Sukai ido biyu dashi Yana tsaye daf da ita a bayanta fararen idanuwansa nakanta Yana Mata kallon daya sata juyawa ta kalli gefen Afia ahankali wadda itama gabaki daya Bata lura da shigowar dad din nata ba
Ahankali ya bude bakinsa daya motsa kadan ba sauti yace"
Congrats lewa.
Wani irin Murmushin farin cikine me tsanani ya lullubeta ta matso ahankali ta matsu dashi sosai ta lakaci tsakiyan cake din dake gefenta kadan da babban yatsanta takai bakinsa ya bude bakin ahankali ta zura Masa yatsan ya kame ya kasa hannun da harshensa ta lumshe ido ta bude tana zare yatsan sbd Jin yanda yake tsotsa ya Kai hannu ahankali zai kamota
Farhat data lura dashi alokacin cikin tsallen murna tace"
Yeeeehhh daddy yadawo.
Matsawa baya NURU tayi ahankali tana dauke idonta daga kallon dayake Mata ta juyar da Kai tana boye kyakkyawan murmushin dake kan fuskarta
Afia ta juyo da sauri cikin farin ciki tana cewa"
Barka da dawowa dad.
Thank you and congratulations to you Dr AFIA UBAYD MALEEK.
Wani qayataccen murmushin farin ciki tasaki sbd ganin alfari da ita a fuskar dad din nata ta matso ta 'dan rungumesa tana cewa"
Thank you dad.
Dafa kanta yayi Yana cewa"
Ina Miki fatan nasara da albarkatacciyar rayuwa agaba.
Amin ya furta tana kallon NURU dake tsaye gefe tare dasu mum Sarah ta miqa Mata hannu tana cewa"
Dad ka Taya NURU murna itama.
Kallon NURUn yayi Yana dauke Kai ahankali yace"
Allah yayi Mata albarka yabata sa'ar rayuwa.
Amin afia da farhat sukace suna kallon NURUn data ki dagowa ta kallesa sbd Jin idanuwansa dake yawo ajikinta wainda tun anan tanajin kaifi da Dafin son dasuke dauke dashi.
##MAMUH#
*_Mamuhgee 50_*
Zame jikinsa yayi daga 'yayan nasa ya nufi hanyar shigewa palonsa Yana amsa gaisuwar su mum Sarah dake Masa barka da dawowa
Dama shi mr Omar Yana sako Kai yaga shigar dake jikinsu NURUn da shagalin dasuke yaci ribas ya juya Yana bawa MALEEK hanya Yana shigowa daga cikin palon inda su NURUn suke taredasu mum Sarah dasu Fana.
Ahankali ta Dan dago tabi bayansa da kallo harya shige ta qaraso gurinsu afia suna cigaba da Yan hotunansu da videos ta kalli farhat da hankalinta yafi tafiya sosai agurin hotunan da cake ta maida kallonta akan afia da itakuma Imran yakirata video call da mum dinta suna tayata murna cikin tsananin farin cikin tareda fatan Allah yabata nasara
Ta ajiye qaramin plate din hannunta na cake ta juya tabar gurin batareda kowa ya lura da Barinta gurinba ta nufi palon tashiga cikin nutsuwa tana gyara rigarta data lafe ajikinta gashi ko bra Bata sakaba sbd rigar data kamata sbd robace me taushi da rashin damuwa tana shiga palon ta nufi dakinta ta sake wanke hannunta tafito ta sake shafa turare tana gyara daurin gashinta daya fara warwarewa ta nufi fridge din dake can gefe cikin palon ta dauko ruwa marasa sanyi sosai da power horse energy drink dinsa dake jere acikin fridge din ta dauki qaramin tray ta dorasu akai ta nufi bedroom dinsa Kai tsaye tana sake sakawa kanta nutsuwa ta murda kofar dakin Kai tsaye ahankali ta shiga ta rufo kofar tana kallon dakin sbd Bata taba shigoshi ba ta ajiye tray din sbd MALEEK din baya dakin da Alama Yana cikin toilet
Saita nufo kofa zata fice tana bude kofar Yana fitowa daga toilet daureda towel Brown a qugunsa ta sauke boyayyar ajiyar zuciya kafin ta waiwayo ahankali ta kallesa ganin yanayin dayake saita sauke kanta daga kallonsa cikin nutsuwa da laushin murya tace"
Barka da dawowa.
Hannu ya daga ya miqa Mata batareda yace komaiba Yana kallonta da idanuwansa dasuka Sha kewar ganinta acikinsu,
Ta dago fararen idanuwanta ahankali ta zuba Masa tana kallonsa kafin tafara takowa ahankali ta Isa ta Kama hannunsa ya jawota jikinsa Yana lumshe ido suka sauke ajiyar zuciya ahankali atare ya shigar da ita cikin jikinsa Yana zura hannayensa bayanta ya mannota da jikinsa da Babu Kaya ajiki ruwan wankan jikinsa suna taba fatarta me tsanani laushi wadda take haduwa da tasa fatar me laushin shima sukai shiru ahaka kowa na sauraren bugun zuciyar 'daya idanuwanta a lumshe suke shikuma ya zuba Mata nashi kafin ya dago hannuwansa ahankali ya kamo fuskarta ya hade da tasa Yana goga Mata ruwan fuskarsa a tata fuskar wainda suke kashe jikinta ta 'dan qanqamesa tana sake rintse idanuwa ya sake rankwafowa Ya Bata light kiss abaki Wanda yasata bude idanuwan ta kallesa ya hura Mata iska kadan acikin idanuwan Yana sake Bata kiss wannan karon me tsayi Dan sai dataji kafafunta suna gazawa ta qanqamesa tana zamewa tareda shigewa jikinsa ta rungumesa dakyau tana sauke Dan boyayyan numfashinta daya sauya.
Murmushi yasake ahankali tareda Kama hannunta suka nufi gaban mirror ya zauna yana nuna Mata gaban mirror din da ido ta kallesa ta kalli gaban madubin tasaki 'kayataccen murmushi tana Kai hannunta ta dauki oil na Neu ta zuba a hannunta kadan ta kallesa ya daga Mata gira daya Yana murmushin daya kusa rikitata takai hannuwanta ahankali ta Dora kan qirjinsa tafara shafawa ahankali ahankali take ya riqe hannunta Yana kallonta da idanuwansa dasukai wani iri ahankali ya bude Baki yace"
Zakiyi kisane?????
Wata irin mummunan kunya tasata zare hannunta da sauri ta juya ta nufi kofa ta bude da gudunta ta fice tabarsa zaune Yana duba kansa Dan kuwa data cigaba numfashinsane zai tsaya cak sai ya hada da inhaler kafin ya fizgoshi.
Dakinta ta nufa ta zauna gaban madubi itama tana kallon kanta kunyar zancensa har lokacin tana jinta ta miqe ta fada toilet ta wanke hannuwan tareda yowar alwala ta fito daidai shigowan Afia data shigo fuskarta da 'yar damuwa ta qaraso tsakiyar dakin tana kallon afian tace"
Lafiya dai ko?Naga kin canza.
Zama tayi kan kujera Yana ajiye wayarta gefenta tace"
Mum nason naje ne kafin nafara aiki na zama Banda lokacin zuwa
Nima inason zuwa ganinta sbd yanzune nakeda duka wannan lokacin Amma dad bazai barni ba
Inama ganin rashin dacewar fada Masa Dan Haka Zan hakura har gaba Inshallah.
Dan murmushi NURU tayi tana cewa"
Ki gwada tambayan Inshallah zai barki tunda dama akan karatunki ne Kuma yanzu kingama Dan haka inaga kaman bazai hanaki zuwa ganin mum dinkiba tunda abune dayazama kaman tilas.
Sauke numfashi tayi tana cewa"
Zangwada tambayan Inshallah.
Tana Gama sallar magriba din ta fito ta nufi kitchen tasaka hannu sharp sharp akan abincin Daren da Saida akaga maleek din aka Dora da niyarsu ciki cake da drinks su koshi suyi kwanciyarsu dama su mum Sarah sunsaba da irin wannan kwalamar dake Hana aci abincinma ko anyi.
Suna gamawa da kanta ta jere komai ta fito kitchen din tabar Fana na gyarawa itama tana Gama gyarawan ta fice daga sashen gabaki daya ta koma sashensu na masu aiki.
Wanka tayi tana fitowa ta shafa Mai kadan ajikinta sai turarukan da Anneti taba data shafawa jikinta ta Sanya doguwar straight riga ta roba wadda ta kwanta jikinta duk daga sama har qasa ko bra kin sakawa tayi sbd lafewar da rigar tayi ajikinta saidai ba'a gane Bata saka bra din ba ta daure gashinta batareda ta shafawa fuskarta komaiba ta fito zuwa dining lokacin duk su afia da dad dinsu nakan dining din ta nufosu tana qarasowa
Cikin hancinsa ya jiyo sabon qamshinta tareda takunta na nutsuwa data Saba.
'dan dagowa yayi a natse ya kalli inda take tahowa ya zuba Mata ido fitar numfashinsa na 'dan sauyawa
Kallo daya yayi Mata ya gano Bata saka bra ba wani kyakkyawan murmushi yaso sauka kan fuskarsa ya dauke Kai Yana Dan kamewa sbd kame Kai kada ya fita control.
Yanaji ta iso dining ta 'dan kallesa cikin lallausan muryanta tace"
Barka da fitowa.
Juyawa gurinsu afia tayi da dama duk yanxu suka zauna Basu kaiga fara cin abincin ba
Afia ta miqe tayi serving dad dinta kafin tayi nata NURU Kuma ta zubawa farhat kafin ta zuba Bata suka fara cin abincin cikin nutsuwa.
Suna gamawa kafin ya miqe yabar dining din afia ta kallesa cikin nutsuwa da kwantar da Kai tace"
Dad Ina roqon alfarmar zuwa Las Vegas kafin takarduna su fito.
Sunkuyar dakai tayi cikin Dan sanyin jiki tana jiran Jin abinda zai fada.
Shiru yana kallon afian datake jiran amsarshi ya juyarda idanuwansa kan NURU datake cin abinci ahankali har lokacin Bata gamaba yasake maida kallonsa kan Afia din ya miqe tsaye yace"
Mr Omar zai shirya muku komai zakije tareda farhat itama ta duba mahaifiyarta nabaki sati biyu.
Da mamakin bazatar amincewarsa da har sati biyun daya Bata suka dago dukkaninsu suka kallesa
Kafin NURU ta sauke kallonta ahankali tana daukan ruwa ahankali Tasha Jin ta koshi suka bi bayansa da kallo.
Cikin tsananin farin ciki Afia tace"
Thank you, thank you dad.
Rungume NURU tayi da sauri tana cewa"
Zanyi missing naki sweetie.
Murmushi NURUn tasake tana kallon afian a 'dan shagwabe tace"
Nice zanyi missing naku nida zaku Bari Ni kadai I will miss you guys like crazy musamman my sweetheart farhat darling please kudawo da wuri.
Yar Dariya Afia tasake tana cewa"
Karki damu su mum Sarah zasu dauke Miki kewa.
Sake shagwabe fuska tayi tace"
Nima inason zanje gida Nagano su abal da ammyna Zaki tayani tambaya Nima Allah yasa abarni.
Amin Afia tace tana Miqewa suka bar dining din suka nufo palonsa afia ce Agaba sai ita NURUn na gefenta suka shigo cikin sa'a Yana zaune palon Yana amsa waya be Shiga na kurya ba
Ya Dan waiwayo ya kallesu ya dauke Kai Yana cigaba da amsa wayar kafin ya taqaita ya kashe batareda ya sake kallonsu ba yace"
Unhum????
NURU lafewa tayi tayi shiru sai afia ce ta bude baki tace"
Dad NURU ma tanason zuwa dubo su ammynta sbd zaman kadaici kafin mudawo tare.
Sai alokacin ya Dan waiwayo ya kalli NURUn data sake lafewa ya dawo da kallonsa kan Afia da muryarsa me Dadi da nutsuwa yace"
Wayene yace zatayi zaman kadaicin????
Tsit sukayi musamman NURU dataji wani iri sbd zancen nasa kamar da ma'ana ta sauke Kai daga irin kallon dayake Mata gaban afia din taji kunya na neman kamata ta Kama hannun afia zasu juya afia tace"
Dad Dan Allah ka duba zancen.
Batareda ya kalli afian ba Kai tsaye yace"
Itama mr Omar zai Shirin tafiyarta.
Miqewa yayi ya shige ciki yabarsu tsaye suna farin ciki kafin afia ta fita ta wuce dakinta NURU ma kallon kofar dakinsa tayi tana Jin farin cikin zuwa gida na shigarta ta nufi dakinta tayi sallar ishai ta zauna tana Dan duba chats har zuwa karfe Tara kafin ta aje wayar ta tashi ta nufi toilet ta wanko fuskarta da hannuwanta ta fito ta shafa Dan Mai tasake shafa turaruka ta cire rigarta ta dauko wata fingilalliyar rigar bacci tasaka ta kalli kanta cikin madubi taga bazata iyaba sbd rigar tayi lalata da yawa ta daure gashinta ta dauko wasu riga da wandon baccin masu qaramin guntun wando tafara zame rigar taji anbude kofar dakin tayi saurin juyowa sbd yanayin rigar jikinta Bata fatan ko afia taganta da ita ajiki.
Dan fiddo da fararen idanuwanta tayi ganin Wanda Bata taba tsammani ba ya tsaya daga bakin kofar Yana kallon jikinta ta cikin rigar baisan lokacinda kafafunsa suka kawosa gabanta ba saijin ya jawota jikinsa ahankali tayi
Ta dago tana kallon fuskarsa data koma kamar ta sabon tashen saurayi sbd tsimuwa acikin soyayya ya lumshe ido Yana sake matseta jikinsa takai hannu ahankali ya zare daurin gashinta
Gashin ya sake yakai hancinsa ya shaqa qamshin dake fita cikin gashin ya lumshe ido Yana sake zagayeta da hannuwansa.
Sake dagowa tayi ta kallesa ya dage Mata gira daya tareda daukanta gabaki dayanta cak ya fita daga dakin da ita tana sake lafewa jikinsa.
Suna shiga dakinsa ya kwantar da ita kan makeken gadonsa Yana kallon fuskarta zuwa wuyanta kafin ya gangara da idanuwan zuwa kirjinta Yana tuno rigar data saka dazun gurin cin abinci take ya lumshe ido Yana zura hannuwansa cikin rigar baccinda da ita da Babu duk daya ya shafo lafaffen cikinta daya kusa saka numfashinta barin jikinta ta qamqame wuyansa Wanda ya matso dashi ahankali ya kamo bakinta da nashi Yana zura harshensa ciki ahankali Yana qarasa hade kirjinsu Wanda yake mugun kashesa.
Jin irin Nishin dayake fitarwa cikin Jin Dadi da samun nutsuwar abinda yake yasata sake shigewa jikinsa tana goga Masa nata jikin tana qarasa kunnashi gabaki dayansa.
Qarfe tara ta fito zuwa kitchen a matuqar gajiye take ga baccin dabai ishetaba Dole ta girgije tafara aikin breakfast tareda Fana
Suna cikin Yi afia ta shigo itama suka hau aikin tare
Suna kammalawa kowaccensu tayi daki Dan yin qanka.
Wanka tayi tareda Yar simple kwalliyarta ta sako doguwar turkian gown me shape daga sama kawai ta fito tana fidda sanyin kamshi ta nufi dakinsa tana shiga Yana Gama shirinsa tsaf cikin black Armani's kaf ta kallesa shima ita ya kalla ta qarasa gabansa cikin 'yar yanga da taushin murya tace"
Good morning.
Jawota yayi yayi kissing bakinta da hot red waterproof lipstick dinta ya zaunu 'daram a bakin ya Kai bakinsa kunnenta ahankali yace"
Wannan kwalliyan nawane right???
Wani lafiyayyan murmushi tasaki Saida haqoranta suka bayyana ta dago ta kallesa murmushin na kashe jikinsa yace"
Unhum right??
Ahankali ta juya tana sake sakin murmushi ta nufi kofa zata fita
Ya riqota Yana dawo da ita ya rungumeta ta baya Yana cewa"
Ok nagane basai kin fada.
Fitowa sukayi tare hannunta na sarqe cikin nasa suna kawowa hanyar fitowa main Palo ta dakata tareda zare hannunta ahankali tafara wucewa yabiyo bayanta zuwa dining daidai fitowar afia sai farhat data riga kowa fitowa
Afia ta gaida dad din cikin kulawa da girma afin farhat ta qaraso ta riqe hannunsa tana cewa"
Good morning Daddy.
Morning princess"yace Yana kallon fuskarta.
Basu wani jimaba gurin cin abincin maleek din yagama ya fice tareda Mr Omar zuwa office.
Shirye shiryen tafiya sukai ranar
NURU ma qaramin akwati daya ta hada sai handbag data saka su id cards dinta da sauran abubuwan buqatan.
Sai dare maleek ya dawo sbd tarin ayyukansu dasuka taru Dan haka tea kawai yasha baya buqatar abinci suka kwanta.
Washe gari da yamma su afia suka wuce suka barta da tsananin kewarsu musamman farhat ma daqyar ta yadda tabi afia din da tace ita NURU zatabi delah Amma NURU tayi Mata dubara da 'yan nasihu akan mum dinsu kafin ta amince tabi afia suka tafi.
Sai washe gari nata jirgin ya tashi saidai tareda maleek zasuyi tafiyar ta cikin ticket dinta taga inda sukai ba delah ba wato _Maui Hawaii_
Murmushi kawai tasake tareda Dan dagowa ta kallesa kafin ta kwantarda kanta jikinsa tana lumshe ido.
Sai cikin dare suka Isa Kai tsaye driver yazo daukansu ya nufi masaukinsu dasu Wanda mamaken 5star hotel din yake kusada ruwa Wanda yaqara gurin ni'ima da nutsuwa ga tight security dake kewaye dako Ina gurin Sam gurin ba hayaniya akwai tsaro sbd gurin manyane kawai aciki.
A gajiyen datake sallah kawai tasamu tayi daqyar ta bayan tayi wanka da ruwan zafi Sosai ta saka kayan bacci ta haye gado ta shige bargo take bacci yayi gaba da ita me Dadi ko abinci Bata tsaya nemaba.
Saida yagama komai shima ciki hadda waya da Mr Omar kafin ya hawo gadon ya kwanta tana shigewa jikinsa
Shima baccin yayi me nutsuwa.
Sai qarfe bakwai na washe gari suka tashi har sunyi lattin sallah
Sukai sallar sai alokacin yunwa ta taso Mata
Yayi Mata odar abinci lafiyayye baa dauki mintuna da yawaba aka kawo ta tashi taje kan table tafara ci yazo ya zauna kusada ita suna ci tare duk da Bai saka hannuba da hannunta sukeci.
Bayan sungama wanka sukai suka sake komawa bacci sai Rana sosai suka tashi sukai sallah suka Kara cin abinci
Gabaki daya ranar dai a kwance suka yini sallah da cin abinci kawai ke tadasu ko washe gari ma Haka Saida sukai kwana biyu kafin suka fara fita da qafa yawon Shan iska cikin qananun Kaya Wanda ta mutu da mamakin duniyanci da iya zallar soyayyar da maleek din ya iya musamman dayake yazaba Nan dinne sbd Ana rayuwane anan ta couples sbd yawanci Yan honeymoon ne.
Kwanaki sukai suna fita wani irin shaquwa da sabuwar soyayya me qarfin gaske tasake shiga tsakaninsu musamman da yariga yagama busar Mata da idanu akan soyayyarsa ko Ina Babu ruwansu kissing juna sukeyi musamman shi ko magana take Masa wani lokacin Haka zaibi bakin Yana kissing sbd komai nata kashesa yakeyi.
Yau ba awani gajiye suka dawoba Dan Haka suna dawowa yaqarasa gajiyar dasu akan gadansu aikuwa taqarasa gajiyar gaske kafin sukai wanka suka kwanta bacci.
Wata irin sabuwar rayuwa suke a qasar ta zararrin masoyan da basa ganin kowa sai junansu
Dan kuwa yanzu ko irin kayan datake saka Masa cikin daki sun gama makantar da idanuwansa da ganin kowa bayan ita musamman da yanzu ya koya Mata batada gurin zama sai kan cinyoyinsa da jikinsa.
Tana waya dasu afia sosai saidai har lokacin takasa fada mata inda take tadai sanar da ita Bata tafi delah ba tana gida sbd cewa abata su abal su gaisa afian datai.
Su abal ma dadin duniya da farin ciki ya ishesu duk lokacinda sukai waya da 'yarsu
Itakuma padima kullum akai waya da NURU sai kaman ciwon ya tashi sbd ta ringa Kiran sunan NURU kenan yinin tana cewa ta yafe Mata.
Satinsu uku cif suka dawo gida har lokacin su afia Basu dawoba sbd afia data gane mahaifiyarta tana samun 'yar matsalar juyewar Kai wani lokaci shiyasa takira dad din tasake rokon yaqara Mata sati daya yakuma qara musu din.
Koda suka dawo kallo daya mum Sarah tayiwa NURUn ta dauke Kai tana yaba zallar kyau da cikar data Karo shi kansa oga kwata kwatan Mr Omar dinga satar kallonsa yayi Yana Masa barka barka akai akai har Saida maleek din ya kallesa yace"
Yaushe ka zama me saka ido Mr Omar?
Murmushi yayi Yana shafa Kai yace"
Allah dai yaqara maleek lafiya da kwanciyar hankali.
Dan guntun murmushi shima yasaki Yana share Mr Omar din sbd dama yasanshi da 'yar Karan saka Masa ido musamman daga baya bayan Nan.
Kwanansu biyu da dawowa yayi tafiya tareda Mr Omar bayan yagama aikin bada Baki sbd kedaicin dazata shiga basu afia babushi
A ranar kafin ya wuce yakira afia yace su biyo jirgin washe gari su dawo gida
Afia tace to.
Washe gari da yamma saigasu sun dawo cikin tsananin farin ciki da murna tarbesu ta rungume farhat kafin ta rungume afia din tana cewa"
Oh my God I missed you guys so much
Musamman wannan beautiful sabuwan likitan tamu" taqarasa fada tana kallon farhat data tsuke fuska zatai mgn ta tareda da Bata kiss a goshi tana cewa"
My sweetie kinsan kece farko a zuciyana basai kince komaiba kinji.
Har dakin afia din suke duk su dukansu suka zauna afia na sauke ajiyar zuciya tana lumshe ido tace"
Alhmdlh Ya Allah
Gida me Dadi.
Murmushi NURU tayi tana tayata janye akwatin ta gefe tace"
Keda Zakiyi aure wata Ran kitafi
Amma nidai har banason tuna ranar
I don't wnt you to leave us" taqarasa fada tana kallon afian cikin kwabe fuska.
Dariya Afia tayi tana miqewa ta dauko wayarta cikin Jakarta tadawo kusada NURUn ta zauna tana cewa"
Hmmm ki shirya to babe sbd nakusa tafiya idan kina maganar aure ne sbd....
Wani tsananin farin ciki NURU tace"
Yaushe kika fara soyayya Banda labari¿
Wane me sa'ar ne wannan?
Dan wani blushing afia tayi tana kallon NURUn kafin ta miqe ta nufi toilet tana cewa"
Zanfada Miki komai kinsani Amma saina hutu yau da daddare akwai fira.
Murmushi kawai tayi tana cewa"
To ahuta lafiya Bari naje na saka hannu a abincin yau abincin dakukafi so za'ayi.
##MAMUH#
*_Mamuhgee 51_*
Sai dare suka samu kansu a dakin afia din ma suka kwana bayan sun kwanta
Afia ta fuskanci NURUn ta sauke ajiyar zuciya da numfashi ahankali tafara cewa"
NURU mum Dina tasamu matsalar juyewar Rabin Kai dayake Dan tashi wasu lokutan idan tana tuno abinda daya faru na wannan al'amarin.
'dan shiru tayi tana sake juya al'amarin cikin ranta ta bude Baki tacigaba da cewa"
NURU mum ta rokeni alfarmar na amince na auri Imran sbd nuna sha'awarsa da yayi ga aure Dan samun cikakkiyar nutsuwar Bata kulawa shine ta nuna sha'awarta nason auren Hadi a tsakaninmu idan har dad Dina ya amince,
Na zauna nayi nazarin maganarta NURU Nima inason kasancewa tareda ita Dan samun lafiyarta Dan Haka na amince da maganar auren saidai bansaniba ko hakan danayi nayi daidai kokuwa?....
Ajiyar zuciya ahankali NURU tasaki tana kallon afian cikin tsananin tausayinta da qaunarta sbd a rayuwa tasamu gata da dukiya da kyakkyawan asali da ilimi da komaima na rayuwa Allah yabata Amma ta bangaren mahaifiyarta ta hadu da jarabawa me qarfi wadda gashi dai daga karshe tayi sacrificing rayuwarta kacokan akan auren Hadi sbd neman lafiya da kawo sauyi a rayuwar uwarta Wanda hakan yaqarawa NURUn ganin girman afian fiyeda koyaushe sbd tabbas tsakaninta da Allah takeso da kaunar mahaifiyarta komai halayenta kuwa.
Cikowa idanuwansu duk su biyun sukai da hawaye NURU tace"
Ina Miki fatan kyakkyawar nasara arayuwa fiyeda kowa afia,
Allah ya dasa Jin Dadi da kwanciyar hankali tareda soyayya me girma acikin wannan auren Kuma Inshallah dad dinku ma bazaiqi hakan ba sbd burinsa dama akanki karatunki ne Kuma kin kammala Dan Haka burinsa na gaba akanki bazai wuce aurenki ba.
Ahankali ta furta"
Thank you NURU.
Murmushi tasaki tana dafa hannunta ta girgiza Mata Kai.
Washe gari a washe suka tashi kowa da nasa farin cikin sbd takardunsu dasuka fito Kai tsaye tare data aikinsu
Murna da farin ciki a ranar ma Saida sukai partynsu cikin Palo wannan karon afia harda rawa Tasha
Farhat da itama farin cikin ganinsu cikin farin ciki duk ya lullubeta itama tasha rawarta duk da Bata iyaba
Saiga Imran yakira afia din vcall ta zauna sunayi tana gyara gashinta data sauyawa kala daga baqi zuwa dark brown suka fara fira sama sama wadda yawanci idone yake kafe dasu sbd wasu halayenta da kyakkyawar kamilalliyar fuskarta dasuka fara saka Masa Sonta.
Mum dinta yafita yakaiwa wayar suka hau murna mum dinta na cewa"
My baby I love Allah ya albarkaci rayuwarku duka.
Amin ta amsa tareda janyo NURU dake can gefe tana waya da Alama duk wanda take wayar dashi yanada mahimmanci a rayuwarta ta kara Mata wayar tana cewa"
Mum ki gaisa da NURU ki tayata murna itama.
Kallon kallo sukayiwa junansu tareda yin tsit na wasu sakanni kafin NURU ta Dan ago tana kakalo murmushi cikin nutsuwa tace"
Ina wuni?
Ya gida?
Ajiyar zuciya tareda numfashi lailah tasaki kafin ta kalli NURUn cikin nutsuwa tace"
Congrats to you.
Thank you.
Sake kallonta lailah tayi tace"
Kiyi hkr da duk abinda yafaru abaya Ina fatan Zaki yafemun komai ya wuce?
Murmushi NURU tasaki tana girgiza Kai a natse tace"
Yariga yawuce na Dade da yafe Miki sbd girma da darajarda afia take dashi a zuciyata.
Nagode sosai" lailan tafada tana sake murmushin daya qarawa kyakkyawar fuskarta kyau ta Dora da cewa"
Ina gaida farhat.
Jawo farhat NURUn tayi tana cewa"
Sweetie zo ga mum dinki ki gaisheta.
Zama farhat tayi tana karban wayan fuskarta daukeda farin ciki sbd yanzu tafara sakewa da mum din tasu sbd ta sauya sosai yanzu har cikin ranta takeson yayan nata ita Kuma farhat dama tsorone yasata take shakkar kusantar lailan.
Har Imran suka gaisa dashi kafin NURU ta miqe Takoma ga tata wayar datakeyi da Bata oga kwata kwatan Wanda duk wayar datayi da lailah da gaisawa datai da Imran duk yanaji Kuma shima hakan yasashi farin ciki ganin atlast dai afia tasamu soyayyar mahaifiyarta dataketa kwadayi tun tasowarta.
Da daddare sbd gajiya tunda suka kwanta Basu farka ba sai qarfe takwas na safe suka miqe cikin sauri sukai sallah kowa yafara Shirin fita aiki musamman afia datafi NURU buqatan fita da wuri sbd yanayin aikin nasu ba daya ba.
Cikin ikon Allah kowaccensu tafara aikinta cikin aminci da kwanciyar hankali har sun Dan fara sabawa cikin kwanaki kadan.
Yau NURU ce tajasu suka fita tare suka biya ta ajiye afia asibiti kafin ta wuce gurin aikinta tana sake trying numbern MALEEK dabata shiga tun safe rabonta dashi tun jiya cikin Daren dasukai vcall.
Tunanin rashin samunsa yasakar Mata ciwon Kai da damuwa qarshe Bata Bari yamma tayi sosaiba ta tattara ta baro office din harta Kama hanyar zuwa gida ta fasa ta nufi asibiti gurin afia sbd tayita kiranta tafada Mata zata wuce gida idan tagama takira zata Aiko Edward yazo ya dauketa Amma afian Kuma Bata dauki wayarba shiyasa Mata biyawa asibitin Dole tana sakin Dan qaramin tsaki sbd kanta dake tsananin sarawa
Tana yin parking cikin asibitin saidata dakata cikin motar ta sauke ajiyar zuciya da numfashi sbd yanzu Kam kaman hadda jiri tana gani Haka ta daure ta fito sanyeda shades sbd Rana ta nufi ciki.
Direct hanyar office din dazata samu afia wato office din Dr Damien ta nufa saidai kafin ta qarasa tana daf da Isa ta dakata sbd wani jiri daya dibeta tayi gefe zata Fadi afia data hangota zuwa ta taso tana kawowa ta tareta cikeda mamaki da 'yar damuwa tana kallonta tace"
Lafiyanki kuwa???
Gyara tsayuwa NURUn ke kokarin Yi tana Dan dafe goshinta ahankali tace"
Bansaniba kawai ciwon Kaine yake damuna yanzu Kuma Kamar karna baro office jiri yafara kamani Ina ganin stress ne da rashin bacci.
Kallonta afia keyi da kyau kafin ta gangaro da idanuwanta zuwa kirjin NURUn ta kalla tasake maida idanuwanta kan fatar hannuwan NURUn saitaga kaman Bata gani sosai ta kalli NURUn tana cewa"
Bana tunanin stress ne kadai muje nadubaki mugani sbd jiri matsala ne zai iya jefar dakai inda zaka halaka kanka.
Suna Shiga office din Dr Damien ta zaunar da NURUn tana juyawa ta dauko ruwa takawo Mata ta Bata Tasha ta durqusa gabanta tana cewa"
Muji pulse dinki.
Bata hannunta tayi ta riqe tana Jin pulse din NURUn tayi shiru zuciyarta na bugawa
Duk Bata yarda ba ta juya da ita kan gadon scanning din dake office din Dr Damien din NURU ta kwanta tana gyara Mata kafafunta.
Tana Dora Mata abin scanning din take cikin jikin NURUn ya bayyana baro baro ta ajiye abin tana kallon NURU da cikakken mamaki da tsoro harma da shakku da firgici duka
Bakinta na rawa Kai tsaye ta fuxgo kalmar cikin tsananin mamaki tace"
NURU you are 7weeks pregnant.
Da sauri NURU ta kalleta tana saukowa daga gadon tana goge jikinta da tissue ta Dora hannunta kan cikinta cikin son tabbatarwa tace"
Pregnant???
Ni¿
Wani irin Murmushin farin cikin da Bata taba tsammanin yiba ta sake dafe cikin tana dagowa ta kalli afia datai mutuwar tsaye tana kallonta cikin mugun mamakin da batasan lokacinda bakinta ya furta"
Dad ne???
Sai alokacin kunyar afia din takama NURU ta Dan takaita farin cikinta tana kallonta ta daga Mata Kai ahankali tana cewa"
Yes wannan qaninki ne afia.
Wani yawun sabon mamaki afia ta hadiye tana sake dulmiya cikin tunani da tsananin mamaki alokaci daya Kuma hadda kunya tana kamata
Daga ita har NURUn sai suka samu kansu da kunyar juna afian tayi saurin juyawa tana zaro takardar scanning din da batama Gama dubawa ta miqawa NURUn ba shiri bakinta na furta"
Congratulations.
Kallonta NURU tayi ahankali tace"
Thank you tana sakin murmushi.
Bakin afia mutuwa yayi murus da mamakin al'amarin dakuma kunyar dad dinta Haka ta raka NURUn har mota Dan Dole itace taja motar tabar gurin aikin ranar saidai Kuma gobe suka nufo gida tana satar kallon NURU wadda farin cikine fal cikin ranta Allah zai Bata 'da ko 'yar kanta.
Suna shigowa gidan tun daga motocin maleek dake harabar gidan taga alamun an sauya musu parking wanda hakan ke nuni da yadawo kenan
Cikeda murna ta fito motar tana mantawa da komai ta nufi hanyar office dinsa na cikin gidan dayake aikin office aciki sbd hango Mr Omar agurin tasan Yana can Dan Haka ta nufi gurin cikin tsananin farin ciki da murna.
Tsaye suke daga bakin kofa tareda baqinsu 'yan China dasukazo wani aiki harsun Gama magana sun fito kenan zasu wuce ya hangota tana tahowa
Sanin sabon daya koya Mata da yanayin yanda take tahowar ya tabbatarda abinda zai faru ya hadiye wani 'dan yawu ya waiwaya ya kalli Mr Omar Wanda take yagane kallon ya matso Yana washewa bakin Baki Yana nuna musu hanya da cewa"
chairman Zhou let me see off please?
Gyada Kai sukai suna sake bawa maleek hannu suka tareda Mr Omar zuwa gurin motocinsu da securities ke zagaye suna jiran fitowarsu.
Da gudu ta qarasa qarasowa ta fada jikinsa tana Dora bakinta kan nasa ta bashi wani lafiyayyan kiss daya sanyashi dagota ya kalli fuskarta kafin yasake maida fuskarsa yayi kissing din lips dinta Yana fidda wani lafiyayyan murmushin dayasa afia kusan suman tsaye sbd Bata taba ganinsa akan fuskar dad dintaba
Ita gabaki daya daburcewa tayi ganin abinda idanuwanta suka ganar Mata wato dai ba yanzu bane al'amarin ke faruwa sbd komai data gani ya nuna dad dinta ya dade da tsunduma wata sabuwar daddadar rayuwa hakama NURUn.
Wayyo Allahna" tace tana juyawa da sauri zata bar gurin sbd ita duk kunyar komaiba ya rufeta Jin take Kamar ta nutse a qasa
Tana juyowa saura kadan suyi Karo da Mr Omar da shima yake tsaye agurin Yana jiran sugama soyewar ya qarasa.
Kallon kallo sukai itada Mr Omar dake sakin murmushin Haka yakeson ganin megidansa ya sake kallon gefen su maleek din ya juyo ya kalleta da ido yayi Mata alamar tasake waiwayawa tagani
Ta juya ahankali daidai lokacin NURU ta Dan daga duga duganta takai bakinta kan kunnensa daya rankwafo yana riqeda qugunta cikin rada tace Masa"
_Nenyì Irìguzí_ (Am pregnant).
Wani irin Abu yashigesa ya dagota ahankali yana kallon cikin idanuwanta da ido yake tambayar" da gaske??
Kai ta gyada tana zagayo da hannuwanta qugunsa tana cewa"
And I missed you yau duka bani muryanka ba.
Dago fuskarta yayi ya hade bakinsu yabata wani irin lafiyayyan kiss daya sata kallonsa a kasale tace"
Are you this happy??
Kamar yaro haka ya daga Mata Kai Yana kamo hannunta suka nufo ciki
Afia da Mr Omar sukai saurin barin gurin har suna ture juna tayi saurin fadawa Palo ta nufi dakinta da gudu tana cewa"
Heyyyy
NURU kin wuce tunanina
Dad kuma bazan iya cewa komaiba sbd yau Naga asalin MALEEK da bakowa zai taba samun damar ganiba sai su Mr Omar 'yan kullum da kullum din MALEEK.
Suna shigowa dakinsa suka wuce Kai tsaye acan aka qarasa sauran murnar da farin cikin cikin Wanda yasata mamakinsa Dan Bata dauka yanada sauran son haihuwa har hakaba.
Sai dare gurin cin abinci Afia tasamu ganinsu lokacin ba kunya NURU tayi wanka tana sanye da wata lalatacciyar riga Mara tsayi Sosai gashinta daure tsakiyar Kai kaman baby shikuwa akai akai idanuwansa na kanta
Duk sai taji abin wani iri saidai Kuma farin cikin data gani taredasu din ya tabbatar Mata da ba qaramin so sukewa juna ba
Ta ajiye spoon dinta ahankali ta dago ta kallesu cikin farin ciki tana murmushi tace"
Congratulations dad you are having another child Allah yakawo manashi lafiya.
Murmushi yasake Ya kalli afian yace"
Thank you princess Afia.
Da ihu farhat tayi kan NURUn tana cewa"
My aunt zata haifamuna baby me kyau kamanta.
Murmushi NURU tasake tana kissing kumatun farhat din.
Tun daga dining din Babu Wanda yakuma ganin NURU sai washe gari da safe dasuka fito cin abinci sai alokacin afia tabada shawaran NURUn tafara ganin likita musamman akan jirin aikuwa ba Bata lokaci Mr Omar dakejin kaman ya taka kan jariri yakira Dr Damien yazo har gida ya duba NURUn daganan yafara zuwa dubata akai akai.
Lokacinda su abal dinta suka samu labarin cikin hadda sadaka ammynta tayi meryam kuwa tuni tafara takura tanason zuwa gurin NURUn saigashi kuwa maleek da kansa yasa jekadi taje har Delah ta daukota dama Kuma itama jekadin tana Shirin zuwa ne harsai NURUn ta haihu.
Zuwan jekadi da meryam da sati biyu maleek ya dauketa suka tafi _Maldives_ inda sukai zamansu acan suna hutawa Saida cikin yashiga wata na budu kafin suka dawo lokacin anfara maganar auren afia Imran Wanda tun kafin suyi tafiya dad din Imran din ya nemesa yayi magana da afia tace da amincewarta take yace ya Basu aka tsaida Rana.
Imran yadawo Paris gabaki daya da lailah sbd gidansa a Nan Paris yake bazai zauna gidan mahaifin matarsa ba ba girma bane Dan Haka murna kan murna agurinsu NURUn da afian sbd bazasuyi nesa da juna ba take aka hau Shirin biki gadan gadan musamman uwar amarya lailah da ba laifi yanzu ta warke harta fara komawa ayyukanta zata fara daga farko Dan ma a qarqashin kamfanin dad din Imran din take aiki.
Sosai akai shagali a gizah na auren afia din Wanda hatta iyayen NURU sun halarto tareda kaleeb sosai tayi farin cikin ganin iyayenta Suma sunyi farin cikin ganinta musamman cikinta daya fara tsufa a gizah kowa yasan MALEEK na gaf da samun magaji kila suke fata.
Padima dai ba laifi tananan sama sama wani lokacin kalau wani lokacin Kuma abin ya Dan juye ahaka aka gama bikin suka tattara suka dawo Paris afia ta tare a babban gidan mijinta Wanda mum dinta take sashe guda na musamman da Imran din ya ware Mata.
Ranarda afia tacika wata hudu cif da aure ranar nakuda ta tasowa NURU
Maleek ya tattara mulkin da sarautar ya ajiye suka dunguma zuwa asibiti sbd ganin gidan zata wahala bazai iya jure ganin hakan ba
Saigashi cikin ikon Allah suna Isa ta haifi qatoton jaririnta me Kama da farhat sak.
Koda maleek ya karbi Dan wata hamdala yasaki Yana godewa ubangiji yayi Masa huduba da sunan Mr Omar tareda yiwa Mr Omar wata gagarumar kyautar datasaka Mr Omar din rungumesa Yana hawayen godiya duk dai yatara tarin dukiya me yawa a qarqashin maleek din Amma sai bazai iya dainawa maleek din aiki ba sbd sunzama kaman jini.
Acikin motarsu ta dawowa gida duk yabita ya lashe da kisses itada baby Omar Wanda hotonsa tuni yafara yaduwa a duniya Matar UBAYD MALEEK me gizah ta haifar Masa baby boy.
Daqyar ya suka iya raba gurin kwanciya sbd jekadi data Dan sako NURUn agaba har aka samu sukai 50days daga Nan delah suka tafi tayi sati biyu gurin iyayenta daganan suka dawo gizah tayi kwana biyar kafin tadawo Paris su afia sukazo aka wuni gidan suna Yan kus kus dinsu na kayan datazo dasu suka raba
Washe garin ranar maleek ya dauketa suka tafiyarsu _Santorini_ sbd wata sabuwar duniyar da NURUn ta jefasa a Daren jiyan inda sukai wata daya kafin suka dawo
Saidai Koda ta dawo da sabon ciki ajikinta wanda yazo Mata da Dan laulayi da son jiki Haka shima duk ya shirirce gurin tattalinta da jinya sbd koyaushe tana lafe ajikinsa karshe dai Mr Omar Dole ya rungumi wasu ayyukan da kansa yakeyi a office.
##MAMUH#
*ALHAMDULILLAH YA ALLAH*
*MUNZO QARSHEN WANNAN LABARIN ME SUNA UBAYD MALEEK WANDA NAKE FATAN KURA KUREN CIKI DA ABUBUWAN DANAYI BA DAIDAIBA ACIKI ALLAH YA YAFEMABA GABAKI DAYA HAKAMA KURAKURAI IRIN NA MANTUWA DA TYPING ERROR DUK INA FATAN ZAKUMIN UZURI HAKAMA WAINDA ZASUGA BAI KAI MUSU INDA SUKESO BA SUYI HAKURI AMMA DAI KYAN L
LABARI AGAMASHI ANA MARMARINSA BASAI MUNKAI INDA ZAKUJI YA GUNDUREKU BA NIMA BASAI NAKAI INDA RUBUTASABA ZAI GUNDURENI DAN HAKA INA FATAN NUSHANDIN YAYI DAIDAI YANDA ZA'A DADE ANA TUNAWA*
*NAGODE SOSAI SOSAI DA KAUNA DA KUKA NUNAWA LABARIN KUMA INSHALLAH INA MANA FATAN HADEWA A GABA DA LABARIN DAZAIFI UBAYD DA NURU DADI* 😜😜
*NAGODE*
*_MAMUHGEE_* 💋