Wani abu mai kama da mashi Lateefa taji ya soke ta a kirji,ga wani d'aci daya taso mata Wanda bata san ta ina yazo ba saiji tayi ya cika mata mak'ok'oro.
Da k'yar ta saita kanta gudun kada Rabi ta fahimci halin da take ciki tace..."naji tashi ki tafi ki k'arasa aikinki"
Mik'ewa Rabi tayi tana dariya a cikin ranta tace..."duk *UKUBAR* da zaki gana mata baki isa ki canza abinda Allah ya tsara ba.
Rabi tana b'ace mata ta fad'a kan kujera ta baya dab'as ta zauna dan dama jiri take gani daurewa kawai take..
Ta rasa wani irin tunani zatayi,wani sashi na zuciyarta yace kije ki gani da idonki kamin ki yanke hukunci.
A zabure ta mik'e kaman wacce aka tsikarawa allura tayi part d'in Ameera.
Tana shiga ta samesu sun saka kayan breakfast da Rabi ta kawo musu a gaba Umma tana yiwa Ameera fad'an ta shanye tea d'in da ta had'a mata.
Zama tayi kusa da Ameera tana dariya wanda yayi kama da mai nishin kashi.
Gaida Umma ta farayi sannan ta juyo tana duban Ameera tace... "Haba k'anwata muna cikin gidan nan amma ki haihu ke kad'ai ba k'ya tsoron wani abu ya faru dake?"
"Yanzu na gama yi mata fad'a kada ta sake irin wannan koda a gaba ne"Umma tace mata.
Lateefa ji yayi kaman an watsa mata tafashasshen ruwa ajiki.
Tana yiwa Umma wani irin kallo ta k'asan ido kuma tana magana a zucoyarta tace kaji min munafukar tsohuwar nan har wani haihuwa 'yar taki zata k'arayi a gidan nan wannan ma sakaci nane but zan baku mamaki a gaba.
K'ara had'iye damuwarta tayi tace..." Ina jinjiran ko jinjiri muka samu?"
Umma ce ta bata amsa da.."gasu can kan gadi"
Cike da fargaban me Umma take nufi gasu can ta juyo ta dubi kan gadon.
Idanunta kusan zazzagowa suka yi ganin twins a kan gado,zuciyarta kuma kaman ya fashe take ji.
Da k'yar ta daure ta rarrashi kanta ta mik'e ta iso bakin gadon tana lek'ensu.
Wannan karan da k'yar ta hana bakin ta kurma ihun da yazo mata ba shiri.
Umma da Fateema suna cin abinci basu lura da yanayinta ba amma Ameera tana kallonta ta k'asan ido.
Ko d'aukansu batayi ba tace..." Ina zuwa ta fice cikin sauri saboda ta tabbata tana k'ara minti 2 a gaban yaran nan zata iya aikata abinda bashine ba a gaban mutane.
Tana fita yayi daidai da sauk'owar Al'ameen daga part d'inshi.
Ya lura da yanda ta birkice amma ya basar yace.." Ya naga kan table bakomai ko masu aikin basa nan ne?"
Da gudu Lateefa tayi kanshi tare cin k'walan rigan shi tana jijiga shi ta fara bala'i.."Al'ameen wallahi kayi kad'an ka wulakantani a gidan nan daga kai har ita baku isa komai a wajena ba,munafuki kawai in banda munafurci kaida nayi maka iyaka da wannan yarinyan ta yaya ka ka tsallake kaje kayi mata ciki? Iye tambayarka nakeyi"
Murmushi kawai Al'ameen yake yana kallonta,a haka Aina'u ta shigo ta same su.
Da k'yar Aina'u taja ta zuwa part d'inta.
Gyara zaman rigan shi yayi ya shige part d'in Ameera hankalin shi k'wance.
A parkour ya iske Umma da Fateema suna kintsa mata.
Durk'usawa yayi har k'asa ya gaida Umma,Fateema ma ta gaishe shi sannan ya wuce ciki bedroom inada Ameera da twins d'inta suke.
Ameera tasa twins a gaba tana ta kallo tana mamakin wai a jikinta suka fito.
A haka Al'ameen ya shigo ya same ta.
Zama yayi a bakin gado suka sakarwa juna murumushi ya shafa gefen fuskarta yace..." Maman twins kinyi kokari ya jiki ?"
"Da sauki" ta bashi ansa.
D'aukan Baby boy d'in yayi yayi mishi hud'uba yayi pecking goshi shi sannan ya rungume shi yana k'ara jin k'aunar yaron yana ratsa ko'ina a jikin shi.
Da k'yar ya ajiye shi sannan ya d'auko Baby girl itama yayi mata d same thing ya ajiye ta.
Yana juyowa yaga Ameera ta zuba musu ido tana murmushi,gira d'aya ya d'aga mata yace..." Ya dai?"
"Bakomai kallo nake" ta bashi amsa tana murmushi.
Dungure mata kai yayi yana dariya yace ..." 'Yar sa ido kawai".
Dariya itama tayi batayi magana ba.
Nan yake tambayarta abinda ya kamata ya sayo musu.
Cewa tayi ya tambayi Umma ta gaya mishi.
"OK ke bazaki gaya min ba?"ya tambayeta.
Amsa mishi tayi da..."kasan tafini sanin abinda ya dace".
" hakane,na tafi saina dawo"yace tare bata Peck sannan ya fito parlour wajansu Umma.
Dukawa yayi ya tambayi Umma abinda ya dace ya sayo,nan tayi mishi bayanin abubuwan da ya dace ya sayo irinsu madaran da zasu sha towels,kayan sawa,kayan sanyi da sauransu.
Ya mik'e da niyan fita Hajiyar shi tayi sallama ta shigo.
Komawa yayi ya zauna suka gaisa ya mata jagora zuwa d'akin mai jego sannan ya fita siyan abinda aka lissafa mishi.
Lateefa tana zaune sai cika take tana batsewa tana ciccize leb'e.
Aina'u tace" wai meya faru na ganki haka,ki tashi tunda ya fita mu kai shegiya ayi mata alluran mu huta".
"Komai ya lalace Aina'u komai ya wargaje"
Cikun rashin fahimta Aina'u take kollonta tace..."bangane komai ya lalace ya wargace ba".
Murmushin takaici Lateefa tayi tana kallonta k'awarta tace.."ta haihu,ta haifi 'ya'ya har 2".
D'ora hannayenta duka 2 Aina'u tayi tana salati tace..."2? Lateefa bama d'aya ba?"
"Saima kin gansu zuciyarki zata iya bugawa" Lateefa tace tana goge hawayen daya zubo mata.
"Haba dole in ganki cikin tashin hankali,kuttt ya akayi kika bari ta haihu baki kashe shegiya ba?" Aina'u ta tambaya cikin tashin hankali.
"Cikin dare ta haihu kawai ganinta nayi yara da safen nan,ita kuma munafukar uwarta harda cewa nayi mata fad'a haihuwa ita kad'ai koda gaba ta nemi mutum kusa da ita" ta karasa maganan cikin k'waikwayon muryan Umma.
"Kaji 'yar abu kazan uba,kinsan abinda zamuyi wajan boka zamu koma ya kashe yaran shima munafikin mijin naki muyi maganin shi ya kasance naki ke kad'ai".
Ajiyar zuciya Lateefa tayi tace..." King Aina'u na fara tsinkewa da al'amarin nan kuma...."
Pls kuyi manage da wannan.
đđđđđđ
*UKUBAR KISHIYATA*
đđđđđđ
(Its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman Yusuf)
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*đŤđŤđŤ
❄ *~we bearer's of golden writer's assiduously percieven No pain so Magical our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u no pain~*❄
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*Part forty one*
"Ke dallah dakata" Aina'u ta katse ta tana huci.
"Karki bani kunya mana sai kace ba Lateefa 'yar k'walisa ba,ta yaya zaki basu chance suyi winning akanki.just ki bani wuka da nama kiga abinda zai faru but for now dole ki daure zuciyarki karki sake ki nuna musu ba k'ya farinciki da haihuwan nan yanda koda daga baya wani abu ya faru ba wanda zai zarge ki.bayan suna sai mu koma wajan boka"....
Lafuza da shawarwarin Aina'u sunyi tasiri wajan k'wantarwa Lateefa hankali tare da d'aukan alkawari zata daure ayi komai da ita.
Al'ameen yana fita wani babban shopping mall da ake saida kayan babies suka je shida driver.
Kaya Al'ameen yake ta k'wasa kaman ba gobe,yawanci bala ke nuna mishi abinda ya dace ya saya kasancewar shi yana da yara har 3.
Saida suka cika trolley 3 da kayan babies sannan suka dawo gida.
A lokacin gidan a cike yake tap da 'yan barka,kama daga matan brother's d'in Al'ameen da 'yan uwan Ameera duk sun iso gani.
Haka gidan ya kasance kullum cike da 'yan barka.
Lateefa ta daure zuciyarta akayi ta hidima da ita mutane sai yabon k'yan halinta suke.
Ranan suna yara suka cika sunan parents d'insu wato Mudassir mai sunan Alhajin Al'ameen sai Hadiza wacce taci sunan Umma Ameera.
Anyi shagali kaman ba gobe an bawa naira kashi sosai kowa da yazo sunan sai ya tafi da katuwar jaka cike da gifts.
Ameera da twins suma sun samu gifts daga 'yan uwa kala-kala.tun daga kan uban gayya wato Al'ameen,iyayen shi da 'yan uwanshi wanda ya kara hura wutan tsana su a zuciyar Lateefa..
Bayan suna da k'wana 2 Umma tace zata tafi da Ameera gida wanka.
Bori Sosai Lateefa ta tayar wai za'a rabata da 'ya'yanta harda kukan munafurci.
Ganin yanda ta dage yasa Umma tace toh su zauna ita da Fateema kuma zata turo da Gwaggonsu ta cigaba da yi nata wanka.
Lateefa ba haka taso ba,taso ace ita kad'ai aka barwa Ameera da yaranta yanda zataji dad'in b'atar dasu ba tare da wani ya ankara ba.
Ta wani side kuma taji dad'i tunda komai zasuyi a gabanta za'ayi.
Kusan kullum a part d'in Ameera take wuni ana hira da kula da twins tare da ita.
Sosai Gwaggo take jin dad'in zama da ita kuma take yabonta harta kai tana yiwa Ameera fad'a tabi ta su zauna lafiya dan a wannan zamani kamin ka samu mace kamar Lateefa sai an tona.
Shiru kawai Ameera take in taji Gwaggo tana irin wannan magana saboda ko tayi niyyan fad'awa Gwaggo halin da take ciki a sanadin Lateefa sai taji kaman ansa super glue an like mata baki.
Satin ta 2 da haihuwa babban jikan Gwaggo ya rasu ta tattara zata tafi zaman makoki Fateema ta rakata suka tafi tare.
Gida Fateema ta wuce daga gidan rasuwan wai tayi missing Ummanta.
Wuni tayi a gida suna hira da Umma sai bayan 5 tayi shirin komawa gidan Ameera nan Umma ta had'a mata kayan gyara tare da jadddawa Fateema ta fad'awa Ameera ta kula da kanta.
Da zata tafi Abba ya kawo ruwan Addu'a ya bata yace ta kaiwa Ameera su sha ita da yaranta kullum da safe kamin taci komai kuma in zasu k'wanta su shafa jikinsu dashi harna tsawon k'wana 7.
Fateema tana zuwa tayi mata bayanin kayan da Umma ta bata dalla-dalla sanna tayi mata bayanin ruwan addu'an.
A ranan suka fara amfani dashi har zuwa k'wana 7 kaman yanda aka umarce ta.
Kuma a ranan Fateema ta had'a kayanta zata koma gida soboda zasuyi resuming school.
Da daddare Al'ameen ya maida ta gida bayan sun cika ta da sha tara na arziki harda Lateefa wacce farinciki ya cika mata ciki sun watse sun bar Ameera zata cika burinta cikin sauki.
Da washe gari da safe Ameera tana shirin yiwa Fadeel da Fadeela wanka( sunan da Fateema ta zab'awa twins a rinka kiransu dashi kenan)su Fa'iza da Shamsiyya sukayi sallama suka shigo.
Amsawa tayi tana mamakin wai yau ita su Fa'iza kewa sallama.
Gaisheta sukayi ta amsa still a mamakince.
Fa'iza ta tambaya "ina twins ne?"
"Gasu can a cikin gadonsu yanzu nake shirin yi musu wanka".
Shamsiyya tace ..." Dama Aunty ce tace ki kawo su tayi musu wanka".
"Wanka kuma" ta tambaye su.
"Eh saboda ta tayaki ne yau taga bakowa Fateema ta tafi". Fa'iza ta amsa mata.
Kaman zata kara cewa wani abu kuma sai tayi shiru.
Wani k'aramin basket d'insu ta d'auko tasa kayansu kala 2-2 dasu diapper,su mai,powder da sauran kayan amfaninsu ta mik'a musu .
Shamsiyya ta d'auki Fadeel,Fa'iza kuma ta d'auki Fadeela suka fita.
Suna fita direct part d'in Lateefa suka wuce dasu,dama tana zaune tana jiransu.
Da sananin murna ta karb'i yaran tayi ciki, su kuma suka fita zasu tafi gidan binta tare da mamakin canzawar Auntyn nasu.
Ruwan sanyi Lateefa ta tara a bathtub sannan ta saka yaran aciki ta barsu suna ta tsala kuka kaman ransu ya fita.
Tana dariya ta fito parlour ta kira Aina'u tace..." Gasu can na saka su a cikin ruwan sanyin kaman yanda kika ce".
Dariya Aina'u tayi tace..." Kai Besty baki da wasa wallahi yanzu kukan sune nake ji haka?"
Dariyan itama ta shek'e dashi tana..." Ta ina zanyi wasa da wannan babban dama da na samu".
" gaskiyane yanzu saura step 2" inji Aina'u,suka sa dariya a tare.
Tana gama wayan ta koma wajansu duk sun galabaita ba bakin kukan sai idonsu da yake a lumshe.
Fito dasu tayi a cikin ruwan ta dawo d'aki ta k'wantar dasu a kan tiles babu kaya a jikinsu balle ta lullub'e su da towel.
Kara karfin a.c d'akin tayi ta fito parlour ta k'wanta bayan ta kulle k'ofan harda murza key.
Ameera tunda aka fita da yaranta taji sam hankalinta bai k'wanta ba.
Bayan tayi wanka ta shirya ta d'an kishingid'a akan 3 seater tace bari ta bada 10 to 15 mis in basu dawo dasu ba zuwa zatayi ta karb'o kayanta.
Tana k'wanciya wani bacci mai nauyi yayi gaba da ita sakamakon jiya daddare Al'ameen ya hanata bacci da wuri da fitinan shi dama kaman jira yake Fateema ta tafi.
Bayan good 2 hrs Lateefa ta tashi cike da d'aukin ganin halin da suke ciki ta bud'e k'ofan ta shigo.
Farinciki fal zuciyar Lateefa ganin basa motsi.
Turus tayi tana kallon yanda suke fitar da numfashi a hankali da alama baccin su yayi nisa.
Cike da takaici take tsaye akansu tana tunanin abinyi wata zuciyar tana bata shawaran ta shake su kawai su mutu ta huta amma wata zuciyar ta hanata.
Basket d'in kayan su ta jawo tasa musu diaper da kaya ko mai bata shafa musu ba ta fito tana k'walawa Ameera kira.
A nan parlour sukayi clashing da Ameera da farkawarta kenan kuma ta fito neman yaranta .
Mik'a mata su tayi tace ..."wuce kije ki basu nono yunwa suke ji".
Ameera tana karb'ansu taji jikinsu sanyi kalau kaman kankara.
A razane ta d'ago tana kallon Lateefa wanda har saida itama Lateefan ta firgita jin tambayar da Ameera tayi mata.
" meye ya faru dasu naji jikinsu sanyi kalau haka"Ameera ta tambaya tana kallonta.
Wani yawu Lateefa ta hadiye na mamaki had'e da tsoron me yake shirin faruwa a gidanta.
Cikin inda-inda tace..." Ke ni kikewa tambayan rainin wayon nan?"
Murmushi Ameera tayi tace..." Ki sani ni Ameera ba zan tab'a zuba miki ido ki cutar min da yara ba,amma in kina ganin zaki ita toh bismillah kuma ina tabbatar miki in har wani abu ya samu yarana hmmm" tana gama fad'an haka ta juya tayi part d'in ta da yaranta ko d'ar babu a zuciyarta bata san dalilin da yasa ta rage tsoron Lateefa ba Dan cikin 100℅ 70℅ ya ragu.
Lateefa kam daskarewa tayi a wajan ko yatsanta ta kasa motsawa dan bata gama yarda wai Ameera ce ta gaya mata wa'yan nan magagganun ba.
đđđđđđ
*UKUBAR KISHIYATA*
đđđđđđ
(Its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman Yusuf)
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*đŤđŤđŤ
❄~*we bearer's of golden writer's assiduously percieven No pain so Magical our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u no pain~*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*forty two*
Lateefa da k'yar ta dawo hayyacinta tana tambayar kanta meke faruwa ne?
Juyawa tayi cikin sauri ta koma part d'inta tare da dannawa Aina'u k'ira.
Bai dad'e yana ringing ba ta d'aga tana cewa..." Nasan kin kira ne dan bani good news,yah sun shek'a?"
Lateefa a hasale tace..." Ke yi min shiru wani good news zan baki yara da shegen taurin rai,ba abinda ya same su lafiyarsu k'alau.ni ba wannan ba yarinyan nan wai yau har ita take kallon tsakiyan idona ta gaya min magana".
" wacce yarinya kuma kika samu?"Aina'u ta tambaya.
A zuciye Lateefa ta amsa mata da..." Wace yarinya kuwa banda wannan 'yar iskan gidan nan,akan way'an nan b'erayen nata ta dubi cikin idona tace in wani abu ya same su in kuka da kaina".
" wai Ameeran ce tace miki haka?"Aina'u tace cike da mamaki.
Kwafa kawai Lateefa tayi ba tare da tace komai ba.
Aina'u ta cigaba cewa..."lalle akwai matsala dole mu koma wajan boka but before then ya kamata ki koyawa shegiya hankali kamin in dawo muje dan yanzu haka ina hanyan zuwa Kano nida Alhaji nura amma k'wana 2 kawai zanyi,ki nuna mata ko ba boka kinfi karfinta".
Cike da k'warin guiwa Lateefa tace..." Off course wallahi ubanta zanci a gidan nan dole tasan ni Lateefa nafi karfin uwarta bare ita useless da ita".
Shawara sosai Aina'u ta bawa Lateefa wanda yasa mata natsuwa da courage akan gallazawa Ameera sannan suka rabu akan sai tazo jibin.
Ameera tana shiga part d'inta ta hada ruwa mai zafi sosai tayi musu wanka dashi tare da shafa musu baby oil jikin su sosai sannan ta saka musu kayan sanyinsu,ta had'a musu madara ta basu suka sha suka koma bacci.
Saka su tayi agaba tana kallon yanda suke had'a gumi a goshinsu,sai a lokacin hankalinta ya k'wanta.
Tana zaune tana accusing kanta meye dalilinta na basu yaranta bayan tasan ba k'aunarta suke ba bare abinda ta haifa.
A yanda take jin yaranta a cikin ranta zata iya yin komai kuma da kowa da yayi niyar cutar mata dasu.
Har dare basu had'u da Lateefa ba ko wacce tana part d'inta.
Al'ameen yauma ya shigo da daddare duk suka isheta da fitina da shida twins,bata samu bacci ba sai kusan asuba.
Koda tayi sallahn asuba komawa baccinta tayi tare da tura Fadeel da Fadeela wajan Rabi dan tayi musu wanka.
Tana tsakiyan baccinta kaman daga sama taji saukan ruwan sanyi a jikinta Wanda yayi sanadin farkawarta agigice.
Lateefa ta gani tsaye a kanta rik'e da k'ugu tana girgiza cike da masifa.
Tashi Ameera tayi tana gyara zaman Rigan bacci ta.
Lateefa ta fara zuba mata ruwa bala'i.
"Samun guri da k'wanciyar hankali,iyyeh har baccin safe kika samu yanzu Dan kinga k'wana 2 ina d'aga miki k'afa kina jin kanki kamar wata toh bari in gaya miki as from now hutun da na baki ya kara daga yau zaki dawo bakin aikin kamar yanda kike da.ki wuce yanzu ki had'a min breakfast kuma 5 mins na baki just 5mins ko minti d'aya kika k'ara akai kema kinsan sauran".
Tunda ta fara magana Ameera take kallonta tana mamaki .
Ganin ta ida masifarta yasa itama ta shanye nata mamakin ta fara maida mata martani.
" na farko ke wacece wama ya baki izinin shigo min har bedroom saboda rashin tarbiya,maganan ina d'aukan kaina ni wata ce kinyi kuskure anan ni ba wata bace amma ina da matsayin da wasu suna nema da milliyoyin kudi amma basu samu ba,ni UWACE nayi miki gya..."
Lateefa al'ajabi ya gama daskar da ita ta NASA cewa komai sai ido da ta zuba mata amma kalamanta na karshe su suka harzuk'ata har ta d'aga hannu da niyan marinta amma Ameera tayi caraf ta rik'e hannun.
Tana murmushi tare da girgiza mata kai tace..." Don't ever make this mistake in ur life saboda in har baki rik'e girmanki ba ni kuwa zansa k'afa in taka ta"tana gama fad'an haka tayi jifa da hannun abinka da mai kib'a tayi tangal-tangal ta fad'a kan stool din gaban mirror Ameera har ta na buge goshinta.
Ameera ko kallonta bata k'arayi ba ta fad'a bathroom tare da bango mata k'ofa da karfi.
Lateefa jiki duk jiki yayi yayi tsami more especially goshinta har ya taso haka taja jiki ta fice mata a daki.
Al'ameen mamaki fal a ranshi wai Ameera ce tayiwa Lateefa haka,tayaya hakan ta faru?amma can k'asan zuciyar shi kuma dad'ine fal.
Basarwa yayi yana wani yamutsa fuska yace.."wacece haka sabuwar 'yar aiki kika samu?"
Farinciki ne ya lullub'eta ganin har yanzu asirin bai bar jikin shi ba.
" ka kirata yanzu ka korata gidansu dan nagaji da ganinta cikin gidan nan".ta fad'a in a commanding way.
Mik'ewa yayi ya nufi hanyan part d'inshi yace..."tunda a karkashin ki take ke ya kamata ki Kore ta bani ba dama me kike d'ebo 'yan aikinki".
Takaici duk ya cikata ta rasa ya zatayi can wata zuciyar yace ta k'ira k'annenta su dawo mana tasan su zasu iya maganinta.
Nan take ta k'ira Shamsiyya tana d'auka ta fara sauke mata bala'i da take dannewa a ranta.
"Bansan wani irin hankali gare Ku ba,in banda shashanci daga yiwa k'awarku aure sai kuje Ku tare mata a gida haka akeyi?toh ina gaya muku duk abinda kuke Ku bari Ku dawo gobe ina nemanku kuzo Ku min maganin k'aramar 'yar iskan gidan nan".
" Aunty wa kike nufi wai kuma meya faru?"
Nan ta basu labarin abinda ya faru tsakaninta da Ameera.
Fa'iza sai huci take har ji take kaman ta faso ta cikin wayan .
Hakuri suka bata suka ce gobe da sassafe zasu shigo su gyara mata zama.
Al'ameen daya sauk'o k'asa yaga Lateefa ta tashi bata parlour,bai tsaya bata lokaci ba ya fad'a part Ameera ya same ta tanawa babies d'inta wasa hankali k'wance .
K'arasowa yayi ya zauna tare da sa hannu ya d'auki Fadeela ya fara mata wasa yace...."Maman twins kin ganki kuwa kullum k'afa k'yau kike meye sirrin ne?"
Ajiye Fadeel tayi ta juyo gare shi haba d'aya tana fuskantan shi..." Kaine sirrin Yayana".
Kanne mata ido d'aya yayi yace..."kin tabbata?"
Dariya tayi tana gyad'a mishi kai.
Zama yayi sunsa yaransu a tsakiya suna ta hira,anan yaci abincin shi na dare.
Shi bai koma part d'inshi ba sai bayan sallahn asuba.
Wanka yayi ya shirya ya fita office.
Ameera zama cikin d'aki ita kad'ai ya isheta,yau suka fito ita da yaranta main parlour dan shan iska.
Canza channel tayi daga MBC Bollywood zuwa saudi2 tana sauraron karatun alqur'ani.
Bata dad'e da zama ba Lateefa ta fito tana yamutsa fuska.
Daram zuciyarta ya buga da karfin gaske ganin Ameera ta baje tana kallo.
Tana son tanka mata amma wata zuciyar ta hana ta ,kar ta gama zubar da ajinta bari ta hira zuwan su Fa'iza.
Kan dinning ta wuce ta fara breakfast tanayi tana satan kallon Ameera da take harkokinta ta d'auke kai kaman bata san da ita ba a parlour.
Tana mamakin yanda abin ya juye lokaci 1 haka kaman ba Ameerar da bata iya mata magana sai a duke ba kamar ba Ameerar da in ba cewa tayi tashi anan ba bata isa ta motsa ba kaman ba Ameerar da...shigiwar su Shamsiyya shi ya katse mata zancen zuci da take.
Suka wuce Ameera suna mata kallon banza ita ko ta bawa banza ajiyarsu.
Bayan kus-kus da sukayi da Auntynsu suka nufo ta gadan-gadan dai-dai lokacin kuma Fateema tayi sallama ta shigo.
đđđđđđ
*UKUBAR KISHIYATA*
đđđđđđ
(Its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman Yusuf)
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*đŤđŤđŤ
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONđŤđŤđŤ~*
*_~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~_*
*part forty three*
Shigowan Fateema bai hana su Fa'iza k'arasowa gaban Ameera ba kowacce tana k'okarin kai mata bugu.
Da gudu Fateema tazo ta shiga tsakaninsu tana..."me zan gani haka wani irin dabbobi ne ku?"
Ameera ko k'ala bata ce musu ba saida ta k'washe yaranta ta kaisu safe place sannan ta dawo ta samu har sun fara gabazawa da Fateema,Lateefa tana gefe tana suyi kasa-kasa da ita sannan su bi Ameera data gudu.
Ameera tana zuwa batayi wata-wata ba ta finciko Fa'iza ta gashin kanta da yasha Brazil.
Ihu Fa'iza tasa tana neman k'watan kanta amma ta kasa ga bakinta yaki mutuwa sai zagi take aikawa Ameera.
Buge bakin zagin Ameera tayi da iya karfinta sai ga bakin yana tsiyayan jini,wancalar da ita gefe ta fad'a kan glass center table.
Kasa tashi Fa'iza tayi illa dafe goshinta tayi da yake ta zubar da jini tana kula.
Tana juyowa d'ayan side sai ganin Fateema tayi ta haye ruwan cikin Shamsiyya sai bugu take kai mata kota ina.
Murmushi Ameera tayi ta juyo arean dining inda Lateefa take zaune.
Suna had'a ido Lateefa ta mik'e jiki na b'ari tayi hanyan part d'inta dama a tsorace take tana mamakin wani irin karfine dasu duk sun raunata mata k'anne.
"Ina zaki je?ki tsaya ki nuna min jarumtar ki,ki tsaya nace".Ameera ce ke fad'an haka lokacacin da ta bin bayan Lateefa da gudu.
Tsantsin tiles ne ya k'washi Lateefa sai gata tayi zaman 'yan bori a kasa.
Dakewa tayi ta juyo ga Ameera duk da a tsorace take hakan bai hana ta fara cika baki ba harda zagi..."Dan ubanki karki ga ina kyale ki ina nan a Lateefa ta da kika sani ba zan tab'a canzawa ba Kuma dole ki kasance a karkashin iko na in mulke Ki dan Abu Kazan ubanki.."
Ameera batayi niyyana tab'ata ba amma jin zagin da take antayo mata yasa ta jawo wire receiver da yake gefen kayan kallonsu ta shiga lafta mata ta ko ina.
Lateefa duk iya kokarinta na ganin ta kare kanta kasawa tayi.
Ganin in batyi da gaske ba zata sha wiya,hankad'a Ameera tayi da duka karfinta tayi hanyan part d'inta da gudu.
Tsayawa Ameera tayi tana dariya har da fad'uwa kan kujera ganin yanda Lateefa take k'wasan gudu jiki na rawa.
Da k'yar ta d'aga Fateema akan Shamsiyya da tasha mazga.
Zama Fateema tayi tana huci tace..." Wallahi Aunty ke kike sake musu har suke k'okarin tab'a lafiyarki,wallahi kun ci sa'a yau ina cikin mutunci if not hmmm mayu duk kunsa min 'yar uwa a gaba ganin ba abinda 'yar uwarku ta iya sai katon kashi."
Ameera dai dariya take tayi mata tace..." Haba Fateema duk suburbud'an da kika yi mata kike cewa haka?"
Fa'iza da Shamsiyya da k'yar suka ja jikinsu suka fece daga gidan gaba d'aya ba tare da kowa ya lura dasu ba.
Lateefa tana cikin d'aki sai kaiwa da komowa take ta rasa me yake mata dad'i a rayuwa jikinta duk yayi rud'u-rud'u da shatin wire.
Waya ta d'aga ta k'ira Aina'u tasa mata kuka.
Hankali tashe Aina'u take take tambayar ta me yake faruwa?
Da'kayar ta tsagaita kukan ta bata labarin abinda ya faru dasu yanzu.
Ashar Aina'u ta fara d'urawa tana kunfan baki tace yau d'in nan zata taso wallahi sai sun koya mata hankali sannan su koma wajan boka yayi maganinta.
Da washe gari da sassafe Lateefa ta fita sannan ta k'ira Aina'u tace ta fito tazo su wuce.
Bata wani dad'e ba tazo ta same ta suka tafi.
******************
Dariya boka ya bushe da ita yana kallon yanda Lateefa da Aina'u sukayi tsuru-suru suna sauraron shi.
" dukansu 2 kike son akashe?"
Da sauri ta amsa da..."eh boka dan rayuwar yaran nan tashin hankaline a gare ni".
"Za'a kashe su duka amma ba yanzu ba sai mun tura bak'ak'en aljanu suyi ta azabtar dasu zuwa shekara d'aya sai a kashe su,kin amince da wannan shawaran?"
Cikin jin dad'i ta amsa.." Na amince boka dan ni hakan ya min dad'i sosai kuma boka ina son a mantar da Al'ameen yaran nan da ita uwarsu gaba d'aya".
Wani d'an k'aramin sanda da aka laulaye shi da guraye ya mik'o mata yace...bansan ya akayi kikayi sake har tasha abinda ya karya kusan duka sihirin da yake jikinta ba kuma a halin yanzu ba wani aljani da zai iya tunkarta saboda haka ki samu dama ki ajiye mata wannan sandan a karkashin gadonta kuma ki tabbatar a k'wance kika ajiye shi".
D'an dakatawa yayi sannan ya cigaba..."ina gaya miki koda yayi satan k'afa ya shiga d'akinta toh ba abinda zai iya tsinana mata balle harta k'ara haihuwa a gidan".
Farinciki mara misali ne ya lullub'e Lateefa jin abinda boka yace mata.
Godiya suka mishi tare da tula mishi mak'udan kud'i suka fito.
Lateefa bata samu tangard'a wajan aiwatar da duk wani sharad'i da boka ya bata ba komai ya tafi dai-dai yanda take so.
Aikin boka yayi k'yau as usual dan yanzu Al'ameen ya manta hanyan part d'in Ameera balle ita da yaranta..
Haka Ameera take rayuwarta da yaranta duk da rashin kula da Al'ameen yake musu yana damunta amma ta daure tana sha'aninta.
Lateefa tunda tasha suburbud'a a hannun Ameera bata k'ara shiga harkanta ba,hankali k'wance take jiran time d'in da boka ya bata yayi taje a gama mata dasu.
Fadeel da Fadeela yau kusan suna da 6 months amma in ka gansu zasu baka tsoro saboda kamanninsu gaba d'aya ya canza ko zama basu iya ba sai mugun cin abinci.
Ranan wata talata Fateema ta kawo musu ziyara tare da fad'a mata auren 'yar k'anwar Umma da za'ayi nan da 3 weeks.
Fateema tunda ta shigo take kallon yaran da damuwa a fuskanta tace..." Ameera ya nake ganin kaman abin nasu gaba yake dan last time da nazo kaman bai kai haka ba".
Sauke ajiyar zuciya Ameera tayi da matuk'ar damuwa akan fusksnta tace.." Bansan ya zanyi ba Fateema hakan ma da kike gani da sauki dan d'azu nayi musu addu'a na shafa musu ajiki".
"In na je gida zan fad'awa Umma ta fad'awa Abba yayi musu addu'a". Fateema tace haka tana d'aukan Fadeela.
Girgiza kai Ameera tayi tace..." Karki fad'a musu ki tayar musu da hankali nafi son inje da kaina ya gansu".
" shikenan ba zan fad'a ba Allah ya kaimu lokacin kije da kanji"inji Fateema.
Haka Fateema ta wuni mata sai yamma lis ta koma gida.
Ameera tana son fita zuwa bikin amma ta rasa ya zatayi taga Al'ameen ta tambaye izinin fita.
Ana gobe zata je bikin ta fito ta zauna a main parlor ko zata gan shi.
Tana nan zaune har bayan sallahn isha'i sannan tagan shi ya shigo dawowar shi daga masallaci kenan.
Suna had'a ido dukkansu saida zuciyar su ya buga a tare.
Ameera ganin duk ya lalace ya rame yayi baki kaman bashi ba shiyasa zuciyarta bugawa tana tunanin me yake damun shi ya lalace haka?.
Shi kuma ganinta da yayi yau shiya tuna mishi da ita a rayuwar shi.
Yana son sake kallonta amma yaji wani haushinta yake ji dan haka ya d'auke kai yayi hanyan part d'in shi.
Da sauri tace..." Yayana..." Tsayawa yayi can ba tare da ya juyo ba.
Ganin ya tsaya yasa ta taso da sauri tazo ta tsaya a bayan shi tace..."yayana meya faru ko ince me nayi maka ne ka yanke yi mana wannan babban hukuncin nida yaranka?"
Tafiyan shi ya cigaba dayi ba tare da ya tanka mata ba.
Hawayen idonta ta share tace.." Ina Neman izininka zanje gida gobe saboda muna da biki zanyi k'wana 2 kamin in dawo".
Ware hannayen shi yayi irin who cares d'in nan ya k'arasa bakin stairs inda Lateefa take jiran shi da murmushin farnciki a fuskanta tace..." My Ameen meya had'aka da wannan idiot d'in?"
"Pls ki daina b'ata bakin ki akan useless thing my Lateefa".
Dariya tayi suka haura sama suka barta nan tsaye tana hawaye.
Ranta bai tab'a b'aci akan halin ko in kula da Al'ameen yake musu kaman yau ba,toh me yake nufi da ita? In har ya daina sonta ne ya sauwaka mata ta koma gidan iyayenta ko zataji sauki.
Saida tasha kuka sosqi a wannan daren da k'yar ta samu bacci ya d'auke .
Da washe gari da sassafe ta tashi ta had'a musu kayansu a d'an k'aramin trolley.
9am sun gama shiri tafiya tsab.
d'aukin yau zata je gidansu yasa ko breakfast bata tsaya yiba su Rabi suka rakota da kayanta har wajan mota.
Bala driver yana ganinsu ya taso da sauri ya fito da mota sannan ya karb'i trolley a hannun Rabi ya saka a boot sanna yaja mota suka fita su Rabi suna ta d'aga mata hannu cike da kewanta.
Bala yana parking a k'ofar gidansu ta fito tana mamakin yaushe aka gyara musu gidan ya koma haka.
Kota kan kayansu bata bi ba ta Shiga gida da matuk'ar sauri kaman ta kifa tare da k'walawa Umma k'ira.
Fateema ce ta fito da gudu suka rungume juna a zaure tasa hannu ta karb'i Fadeel suka karasa shigowa cikin gida.
Umma ta fito cikin farinciki daga kitchen inda take aikinta tana musu lalle marhabin.
Tabarma Fateema ta shinfid'a musu a bakin sabon parloursu suka zauna ana gaisawa.
Bala yayi sallama ya shigo da trolley su tare da gaishe da Umma sannan yayi musu sallama ya tafi.
Nan Ameera take tambaya ina Abbanta?Umma ta amsa mata daya tafi duba wani abokin shi da bashida lafiya.
Ajiye mata yaran sukayi suka shige d'akin Fateema data sha gyara tana bata labarin Ai Al'ameen ne yayi musu gyra nan.
Tunda suka shiga Umma take kallon yanda yaran suka canza kaman basu ba,ga Ameera itama duk ta canza kana ganinta zaka San tana cikin matsala ba sai an fad'a maka ba.
Cike da damuwa Umma ta k'wantar dasu ta koma kitchen ta cigaba da aikinta zuciyarta a cunkushe.
Ameera suna d'aki Umma ta gama jefa d'an waken da take ta k'ira Fateema ta kai musu d'aki suka faraci.
Sun kusa gamawa suka ji muryan Abba yayi sallama ya shigo.
Da matukar Murna Ameera ta fito da gudu tana yi mishi sannu da zuwa baki har kunne..
Abba cike da farinciki yake amsawa yana tambayarta yaranta.
Fateema ta shigo dasu tana "Abba ga takwaran Umma nan ita zaka fara d'auka".
Suna had'a ido Fadeela ta callara ihu,yariyan da ko zama bata yi yau sai gata tana rarrafe tana Neman hanyan fita daga parlour.
Tsoro,figici da mamaki ya hana kowa tab'a ta illa zuba mata ido da sukayi.
Murmushi Abba yayi yana kallon Ameera da take hawaye yace..."mesa yaran nan basu da lafiya baki kawo min su ba?"
Cike da rashin fahimta Umma tace" wani irin rashin lafiya kuma Mallam?"
đđđđđđ
*UKUBAR KISHIYATA*
đđđđđđ
(Its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman Yusuf)
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*đŤđŤđŤ
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONđŤđŤđŤ~*
*_~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~_*
*part forty four*
"K'warai kuwa amma ba haka aka haife su ba ko?" Abba ya tambaya yana kallon Ameera da take kuka.
Umma ce ta mishi bayanin yanda suke lokacin da aka haife su,nan Abba ya bukaci a shigo da Fadeel da yake bacci a waje.
Fateema ce ta shigo da shi a hannu,aiko shima suna had'a ido da Abba ya fara ihu amma shi baiyi yunkunrin guduwa ba.
Gyara zama Abba yace..."duk yanda akayi yaran nan da aljanu a jikinsu.
Jin haka duk suka kid'ime musamman Ameera da tasa kuka da karfi.
" Ku k'wantar da hankalinku zanyi musu ruquyya ba abinda yafi karfin ayar Allah".
Cirko-cirko sukayi suna sauraron Abba.
"Fateema ki shiga d'akina ki d'auko min ruwan zam-zam,man zaitun dana habba ki kawo min".
Fateema har tuntub'e take saboda sauri, cikin lokaci sai gata ta dawo dasu a hannun.
Abba cewa yayi duk su fita su bashi waje su jira zai fara.
Mik'ewa sukayi suka fita dukansu suna ta waiwayen su.
Suna fita Abba ya shafe su da man zaitun dana habba sannan ya fara karanto ayoyin alqur'ani mai tsarki da ake ruquyya dasu.
Wanda yake jikin Fadeela shiya fara wani irin ihu da murya mai rikitarwa yana rokon Abba da yayi hak'uri ya barshi ba laifin shi bane boka ne ya turo su.
Abba yace..." Akan wani dalili bokan ya turo ku kuke wahalar da jinjiraye?"
" Hajiya Lateefa matar babansu ita tasa aka turo mu muyi ta azabtar dasu har zuwa shekara 1 sannan mu kashe su".
Abba ya jinjina kai ya kara tambayan shi yace...."iya abinda aka saka ku kenan koda saura?"
Murya a galabaice ya bawa Abba labarin irin tuggu da Lateefa ta shirya shekara da shekaru har zuwa yau,sannan ya roki Abba da ya yafe mishi karya kona shi zai fita kuma yayi alkawari ba zai sake zuwa ba.
Atishawa Fadeela tayi ta jerawa har 3 sannan ta bingire da baccin wuya.
Abba ganin Fadeela ta samu lafiya yasa ya maida hankalin shi gabaki 1 zuwa kan Fadeel daya zuba mishi ido ya mishi wani kallo kaman ya shake shi.
Irin kallon da yake mishi yasa Abba sanin cewa wannan yana da taurin kai,dan haka ruwan zam-zam daya sha addu'oi ya d'auko yana watsa mishi a jiki yana cigaba da karatu.
A tsawace yaji wacce take jikin Fadeel d'in tace..." Wai kai wani irin mutum ne mai nacin tsiya?gara ka rabu dani saboda ni duk nacinka sai dai kayi ka gama dan bazan fita ba sai na aiwatar da abinda aka sakani".
Abba yace..."shikenan kada ki fita ni kuma zan kona ki da ayoyin Allah".
Wani dariyan rainin hankali tayi irin na kayi kad'an d'in nan.
Karatu Abba yake yana zuba mishi ruwn zam-zam d'in,tun tana ganin Abba yayi kad'an ya k'ona shi har ta fara k'onewan.
Nan itama ta shiga magiyan Abba ya daina k'ona ta zata fita amma Abba yace shi bai yarda ba dan zata iya dawowa.
Alkawari tayi mishi in ta tafi ta tafi har abada kenan sannan Abba ya tsagaita da karatun da yake.
Atishawa masu karfi shima yayi ta jerawa sannan ya kama bacci kaman na 'yar uwar shi.
"Alhamdulillah!!" Abba yake ta jerawa.
D'aga murya yayi yace suna iya shigowa.
Fuska shame-shame da hawaye suka shigo dama suna tsaye sun kasa zama suna jira.
Umma ta d'auki tak'warta tana share hawayen fuskanta da gefen zaninta tace..." Wannan mata me zamuyi mata ne muji sauki a cikin ranmu?"
" kul kar in kara jin haka daga bakin ki,mutum duk abinda zaiyi maka ka barshi da Allah dan baki ji sauran abubuwa da tayi bama".
A hargitse Umma ta d'ago tana kallonshi tace..." Me kuma tayi bayan wannan?"
Nan Abba ya maimaita mata abinda d'ayan ya fad'a.
Kuma wiwi Umma take tana"Ashe wannan faram-faram da take mana na munafurcine? Oh mutum abin tsoro amma wannan mata Allah ya isa tsakanin mu da ita".
Fateema ita ta fad'i abinda ta sani ciki harda dambe da sukayi Ameera ta hana ta fad'a.
Umma ta jawota jikinta ta rungume tana rarrashinta tace..." Ki yafe mana Ameera duk laifin mu da bama ziyartan ki kuma muka hana kowa namu zuwa gudun kada mutane suce an zuba k'afa a gidanki dan k'wad'ayi ashe kanmu muka cuta da matar nan batayi nasaran wukanta min ke haka ba."
Abba ya katse ta yace..."ya isa haka nan komai da kuke gani muk'addarine na ubangiji,in Allah ya hukunta faruwan abu to dole ne sai ya faru.yanzu abinda nake so ku tashi ke Ameera ku koma gidanki keda Fateema ku rusa kayan d'akin duk abinda kuka gani kada ku tab'a ku Kira ni awaya".
"Toh " suka ce tare da mik'ewa nan Umma ma ta mik'e tace lalle tare zasu tafi kar wani abu ya samu 'yan matan ta.
Abba yace ta zauna ba abinda zai faru tunda su aljanun da aka turo su dan aikin ma sun gudu toh komai ya k'are tayi hak'uri suje.
Haka Umma ta hak'ura ta zauna ba dan taso ba,Ameera ta goyi Fadeel Fateema kuma ta goyi Fadeela suka fita.
Har sun kusa bakin titi Ameera tace..." Dame zamu tafi dan ni ko naira banida shi".
Fateema batayi magana ba ta juya ta koma gida can sai gata ta fito da d'ari 5 a hannunta suka karasa bakin titi tare da tsaida mai adaidaita suka shiga suka tafi.
Pls kuyi manage da wannan.
đđđđđđ
*UKUBAR KISHIYATA*
đđđđđđ
(Its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman Yusuf)
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*đŤđŤđŤ
❄~*we bearer's of golden writer's assiduously percieven No pain so Magical our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u no pain~*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*part forty five*
A bakin gate mai a daidaita ya sauke su,Fateema ta bashi kud'i ya karb'a tare da maida mata change sannan suka nufi cikin gidan.
Bala driver suna zaune da Baba mai gqdi suna hira suka shigo.
Da sauri Bala ya mik'e ya tare su yana.." Haba Hajiya da kinyi waya naje na dawo dake,in Alhaji yaji ba zaiji dad'i ba".
Murmushi kawai tayi tace mishi..."bakomai Bala".
Cikin suka shiga ba kowa a main parlour hakan ya basu daman shigewa part d'in Ameerar ba tare da kowa ya gansu ba.
A parlour Ameera suka k'wantar da Fadeel da Fadeela sannan suka wuce bedroom.
Cikin abinda baifi 20 mins ba suka warware gadon.
Mamaki da tsoro su suka daskar dasu waje d'aya ba wacce ta iya motsi cikinsu.
Can Fateema tayi karfin hali tace..." Bani wayarki in kira Abba in fad'a mishi abinda muka gani"
"Ba kud'i a wayan Fateema".
" nima babu a nawa amma bari in fita in sayo yanzu ina zuwa"
Fateema tans fad'an haka ta d'auki change da mai a daidaita ya basu ta fita.
Bata jima ba kuwa ta dawo da recharge card na m.t.n.
Ameera tana nan tsaye a inda ta barta bata matsa ba.
K'iran Abba tayi bayan ta loda katin a wayarta.
Wayar tana shiga Abba ya d'aga da sauri dama yana zaune shida Umma ya kasa fita ko bakin k'ofa suna jiran k'iran daga gare su.
" Fateema kun samu me kuka gani?"Abba yake jerowa Fateema tambayar nan.
"Eh Abba abubuwa da yawa muka ga..."
"Kaman su me? Gaya min inaji" Abba ya katse ta.
Nan ta shiga lissafo mishi abinda suka gani tace..." Akwai layu guraye sanda harda rigar Ameera dana mijinta da wasu k'ulle-k'ullen magani".
Abba yace..."kada ku tab'a komai ku fara yin alwala sannan ku karanta suratul Iklas,Falaq,Nasi da Ayatul qursiyyu ku shafe jikinku dashi,kusa tsintsiya da abin k'washe shara ku k'washe da shi ku fitar waje".
Kashe wayan Fateema tayi ta ajiye a gefe bayan ta amsa mishi.
Parker da dustbin suka d'auko suka fara k'washewa kenan wayar Fateema ya fara ringing.
Tsaida aiki sukayi Fateema ta amsa wayan taji muryan Abba yana cewa..." Ku kona duk abinda kuka fitar Fateema karku bar komai".
"Insha Allah Abba " tace sannan suka cigaba aikinsu.
Ta bayan gidan suka fita da kayan can arean su Rabi,wuta suka cinnawa dustbin d'in ba tare da sun juye surkullen a k'asa ba.
Wuta ya kama yana ci bal-bal ga wani irin hayaki bak'i kirin na tashi wanda ya k'ara firgita su Fateema da suka koma gefe d'aya suna kallo.
Wutan yana k'asa Ameera ta yanki jiki ta fad'i a wajan.
A rud'e Fateema tayi wajan Rabi tana cewa tazo ta taimaka mata.
Rabi tana tambayarta me ya faru amma Fateema bata tsaya bata amsa ba ta fita da gudu,ganin haka Rabi bata tsaya b'ata lokaci ba ta rufa mata baya.
Salati Rabi ta fara har tana tafa hannu tare da tambayar meya same ta amma ba amsa.
Haka suka ciccib'e ta sai cikin bedroom d'inta suka k'wantar da ita suna aikin fifita.
Ruwan sanyi Rabi ta shafa mata a fuska.
Ajiyar zuciya tayi ta bud'e ido a hankali tana binsu da kallo suna yi mata sannu.
Tashi tayi ta zauna tana tambayar Fateema meya faru?
"Bakomai just tiles ne ya k'washe ki kika fad'i" Fateema ta bata amsa tana b'oye hawayenta.
Kukansu Fadeela suka ji a parlour Fateema ta tashi ta d'auko su ta shigo dasu.
Ameera wasu abubuwa take ji kaman sun faru amma sai take gani kaman a mafarki ya faru.
K'iran Abba ne ya kara shigowa wayar Fateema,parlour ta fita sannan ta d'aga yake tambayar ta ya sukayi.
Abinda ya faru tun daga kan k'ona kayan tsafin harda fad'uwar Ameera duk ta bashi labari.
Godiya ga Allah Abba ya fara yi na Allah ya bawa 'yar shi lafiya,nan yace mata ta kaiwa Ameera wayan zaiyi magana da ita.
Komawa cikin d'akin tayi ta bata wayan tace Abba ne zaiyi magana da ita.
Karb'a tayi taxa a kunne bayan tayi mishi sallama ya amsa ya shiga yi mata nasiha da fada akan rike addu'a da yin azkar saboda addu'a itace makamin mumini sai mutum yayi sake da azkar Sannan duk wani mugun abu zai iya shafar shi amma da mutum zai kiyaye kaman yanda manzon Allah (s.a.w) ya umarta toh bi izininllahi ya tsira sai sai wani ikon Allah.
Ameera sai amsawa take da toh sabida ita tasan bata wasa da azkar bata san tunda tasha juice d'in da su Fa'iza suka bata ta daina duk wani Abu mai suna addu'a ba.
Bayan sun gama waya da Abba ta dubi Fateema tace..." Fati Dan Allah ki gaya min me yake faruwa kaina ya kulle".
Tiriyan-tiriyan Fateema ta maimaita mata iya abinda ta sani.
Rungume twins d'inta tayi tana kuka sai yanzu take gani ashe abinda take gani kaman a mafarki da gaske ya faru da ita.
Rabi ta dafa kafad'arta tace... " Hajiya yanzu ba lokacin kuka bane godiya ya kamata kiyiwa Allah da ya warware wannan kulle mai wuyar warwara".
Bayan sun natsu suka had'a gadon yanda yake suna hira da 'yar uwarta tana jinta kaman wata sabuwar halitta.
Kitchen ta fito tana cewa Fateema ta kula dasu Fadeel zata sama musu abinda zasu ci.
Abinci mai sauki ta girka musu tayi musu pepper soup na kaza ta shirya a d'an madai-daicin tray ta d'auka zata fita Rabi ta shigo tana..."haba Hajiya ai da kinyi min magana zan girka muku duk abinda kuke so".
Murmushi Ameera tayi tace..." Bakomai Rabi taimakon da kike min a baya ba abinda zance sai sai ince Allah ya saka mini da alkhairi".
Tana gama fad'an haka ta d'auki trayn ta fita daga kitchen d'in Rabi ta rakata da murmushi.
******************
Al'ameen yana zaune a office aiki yasha mishi kai,Shu'aib sectaryn shi yana nuna mishi files yana signing.
Wani matsanacin ciwon kai had'e da jiri yaji ya ziyarce shi lokaci d'aya har wani duhu-duhu yake gani.
Dafe kan shi yayi da hannun dama har pen d'in hannun shi yana fad'uwa.
Tambayar shi Shu'aib ya farayi ko lafiya,maimakon ya bashi amsa sai gani yayi ya yanki jiki ya zube a wajan.
A rud'e ya fara k'walawa Massinger kira Wanda yayi sanadin Jan hankalin sauran mutane dake kusa da office d'in.
Mota suka saka shi suka nufi hospital d'in Yayan shi.
A hanyan su ta tafiya Shu'aib ya kira sauran 'yan uwan da iyayen shi ya sanar dasu halin da ake ciki.
Innalillahi wa inna ilahi rajiun Alhaji yake ta maimaitawa yana sharce gumin da suka tsastsafo mishi a goshi.
Hajiya ce ta fito daga kitchen hannunta rik'e da ludayin miya tace..." Alhaji lafiya kuwa,me yake faruwa?"
"Al'ameen ne wai ya yanki jiki ya fad'i a office yanzu haka suna kan hanyan zuwa hospital dashi".Alhaji yace yana saka hula alamun fita zaiyi.
Nan Hajiya ta bukaci ya jira ta su tafi, bai ki ba ya tsaya jiranta.
Ita kuma ta kira Altine tace ta karasa mata aiki ta d'auki hijabi tabi bayan mijinta cike da tashin hankali.
Su Shu'aib suna isa hospital suka Tatar da Ya Sa'ad da wasu doctors 3 suna jiran zuwan su.
Nan da nan aka d'ora shi a wheel bed suka tura shi emergency.
Basu dad'e da shiga ba iyayen shi suka karaso cikin tashin hankali.
Ganin doctors basu fito ba,ba wanda zai basu gamshashiyat bayani dan haka waje suka samu suka zauna suna jiran fitowarsu.
Sun kai good 1 hr a kanshi amma sun kasa gane me yake faruwa,gashi baya numfashi sai zuciyar shi da take bugawa kad'an-kad'an.
Fitowa sukayi jiki a sanyaye.
Wani doctor da ake kira da Abubakar shi yayi karfin halin yi musu bayanin abinda suka gani dan Ya Sa'ad kuka yake wiwi.
" Alhaji kuyi hak'uri ba abinda Al'ameen yake bukata daga gare Ku kaman addu'a saboda a yanayin binciken da mukayi in numfashin shi bai dai-daita ba cikin 30 mins masu zuwa ba toh gaskiya ba abinda zamu iya yi sai hak'uri"yana fad'an haka shima ya wuce office d'in shi.
Hajiya kuka take kaman ranta ya fita Alhaji yana bata baki duk da shima ta maza yake.
Haka sauran yaransu suma sun taru ana rarrashin Hajiya.
Da'kyar suka samu tayi shiru kowa ya nemi wake ya zauna da add'ua a bakinsu sunayi suna kallon agogo wanda ko wani mint da zai buga da zuciyarsu yake bugawa.
Zaman forty mins sukayi suna add'ua amma shiru ba labari hakan yasa Alhaji yace su tashi su yafi dashi ayi mishi wanka akai shi gidan shi na gaskiya.
Dole kowanne su ya daure zuciya tare da rungumar kaddara suka shiga d'akin da aka k'wantar dashi.
Sun shigo suna kokarin d'aga shi su d'aura kan wheel bed
Kaman daga sama suka ga yayi mik'a tare da salati a bakin shi ya bud'e ido.
Nasan wasu sun kusan samun heart attack saboda sun dauka Al'ameen ya shekađđđ
đđđđđđ
*UKUBAR KISHIYATA*
đđđđđđ
(Its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman Yusuf)
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONđŤđŤđŤ~*
*_~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~_*
*part forty six*
Da ido yake bin mutane da suke zagaye dashi suna mishi sannu.
Mik'ewa yayi cikin hanzari ya zauna tare da tambayan meya faru,me suke yi a asibiti?
Amsa mishi suke da bakomai ya k'wantar da hankalin shi,Ya Sa'ad yazo ya k'ara duba shi ya tabbatar musu komai normal yanzu.
Tashi yayi yana cewa shi zai wuce gida dan a lokacin ba abinda yake bukata kaman ya saka Ameera a idon shi.
Alhajin shi yace ba inda zaije sai dai driver ya kaishi.
Dagewa yayi shi zai iya driving da kanshi saboda baya jin komai a jikin shi,nan Alhaji yace toh suje Shu'aib ya ajiye shi a gida dan ba zai yarda yaja mota da kanshi ba.
A mota Al'ameen ya tsare sectaryn shi Shu'aib akan ya fad'a mishi meya faru dashi har aka kawo shi asibiti?
Dolen shi ya bashi labarin abinda ya faru tun daga lokacin da ya yanki jiki ya fad'i har zuwa bayanin da doctors sukayi musu.
Mamaki ya hana shi cewa komai haka Shu'aib ya sauke shi ya wuce office dan kimtsawa saboda a wargaje suka bar komai.
Cike da nishad'i ya nufi cikin gidan yana jin shi kaman wani sabon halitta.
Ameera suna main parlour ita Fateema harda Rabi suna hirar su hankali k'wance ga twins suna zaune a gefe da kayan wasan su .
Rabi tana basu labarin wani yaro mara ji a kauyen su suna k'yalk'yalar dariya Al'ameen yayi sallama ya shigo.
Dukkan su suka amsa mishi amma banda Ameera da ta tsura mishi ido ko kiftawa batayi.
Shima idon ya zuba mata dukkan su ji suke kaman sun d'ebi shekaru basu ga juna ba.
Rabi ta mik'e da sauri tare da kama hannun Fateema sukayi ciki suka basu waje.
Karasowa yayi gabanta ya durkusa ba tare da sun d'auke idon su a cikin na juna ba.
Kamo hannayen ta yayi ya sumbata yace..." Babyna ina kika shiga kika bar zuciyata cikin kuncin rashin ki? Kece farincikin rayuwata I can't live without u".
Kasa magana tayi ta sunkuyar da kanta k'asa tana kuka mara sauti.
Hannu yasa ya d'ago da fuskarta suna kallon juna,girgiza mata kai yake alamun baya son kukan da take.yasa hannu yana share mata hawaye.
Fad'awa tayi jikin shi ta k'ank'ame shi tana kuka sosai.
Shafa bayanta yake a hankali yana aikin rarrashi.
Kaman daga sama suka ji muryan Lateefa ta danno wata muguwar ashar.
A razane suka juyo suna kallonta ba tare da sun rabu ba.
"Al'ameen me zan gani haka,kana cikin hankalin ka kuwa?meya had'a ka da wannan k'azamar karuwar da..."
Lafiyayyar mari da taji a kuncinta shiya katse mata bala'in da take.
A rud'e ta juyo tana kallon shi rike da kuncinta tace..." Al'ameen ni ka mara?"
Ido a rine yana huci yace..."u re lucky marin ki kad'ai nayi a yau,but am warning u in kika k'ara attempting k'iran mata ta uwar 'ya'yana da mugayen suna makamancin wannan wallahi zan baki mamaki shasha kawai".
Kasa gaskanta abinda yake faruwa tayi ta tsaya tana binsu da ido kaman wata doluwa,sai da ta d'auki some seconds sannan ta dawo hayyacinta.
Hannayenta duka 2 ta d'aura a kai tare da fasa wani ihun da sauran mutanen gidan suka fito.
" na shiga 3 na lalace ni Lateefa".
Da gudu tayi kan Ameera tana..." Wallahi baki isa ba yau zan nuna miki kinyi kad'an kija dani".
Ameera tana tsaye tana kallonta ko motsi batayi daga inda take ba har Lateefa ta kusan karasowa gabanta wanda takun da yake tsakanin su baifi 3 ta goce gefe Lateefa kuma ta taho da karfinta hakan yasa ta fad'a kan center table ta fasa goshi.
Ko zugin da goshinta yake bata ji ta mik'e da gudu tayi kan Al'ameen taci k'walar shi tana... "Wallahi baka isa ba duk nafi karfinku wallahi karya ne..."
Ameera ce tazo a zuciye ganin abinda take kuma Al'ameen yayi shiru yana kallonta ba tare da ya d'auki mataki ba.
Finciko Lateefa tayi ta jefata kan kujera tana nuna ta da yatsa tace..."wani irin dabbanci kike mana a cikin gida haka?ki sani komai kika min zan d'auka amma ba zan tab'a zuba miki ido kina abinda kika dama akan mijina ba ".
Mik'ewa tayi bakin nan nata bai mutu ba sai zage-zage da tsine-tsine take ta wuce part d'inta.
Ameera kamo su Fadeel tayi tana rarashi saboda razana da suka yi.
Al'ameen shima yazo joining yana tayata rarrashinsu.
Lateefa tana shiga d'akinta sabon kuka ta saka tana..." Shiken nan asirina ya tonu komai ya lalace min".
Wayarta ta d'auka ta nemi number Aina'u ,ringin 2 yayi ta d'aga tana..." Sarauniya a gida Al'ameen ya aka yine?"
"Aina'u na shiga 3 duk asirin da mukayi duk sun warware yau ni Al'ameen ya mara a gaban tsinanniyar matarshi" tace cikin tashin hankali da matsacin kuka.
Aina'u cikin tashin hankali tace..." Ya akayi haka ta faru ko dai kinyi kuskure wajan aiwatar da abinda boka ya saka ki?"
"Ba tambayoyi nake nema ba Aina'u mafita nake nema". Lateefa ta amsa mata tana face hanci.
Nan Aina'u tace mata mafita 1 ce shine su koma wajan boka.
Babu musu Lateefa ta yarda kan gobe da safe zata same ta sai su wuce.
Tana gama waya da Aina'u ta kira number Maman ta taji switch off,ta gwada nasu Fa'iza suma still a kashe.
Haka ta k'wana a cikin part d'inta ita kad'ai dan koda wasa bata yi yunkurin fitowa ba kuma suma 'yan gidan babu wanda ya lek'a ta.
Da washe gari da sassafe Lateefa ta tashi ta shirya tare da tattara 'yan kud'ad'e da suka rage mata ta fito dan tafiya wajan boka.
A parlour ta had'u da Ameera tana shirya kan table ta d'ago suka had'a ido,harara ta Watso mata tare da cewa..." Kiyi abinda kike so in just 2 hrs dan kika bar wannan precious time d'in ya wuce it means a lot,dafatan kin gane"tana gama fad'an haka tasa kai ta fice daga gidan.
Murmushi Ameera tayi tana girgiza kai a zuciyarta tana cewa ba abinda zan gani sai alkhairi saboda da Allah na dogara.
******************
Suna saka kai d'akin boka ya daka musu tsawa tare da dakatar dasu yace...." Ku tsaya daga nan kada Ku kuskura Ku shigo min cikin dan abinda kuka zo dashi ba mai yiwuwa bane saboda mutanen nan yanzu sunfi karfina gashi kinsa tsiburitu da manaru sunyi matukar fushi dani sakamakon k'ona musu 'yar auta da sukayi.Ku fita nace kamin kusa in huce a kan Ku".
Lateefa dama tun jiya ranta yake a jagule kuma boka ya k'ara mata da nashi saboda ta gama imanin tana zuwa wajan shi zata samu solution amma ya kore ta,nan da nan taji zuciyarta ya mugun b'aci bata San lokacin da itama ta daka mishi tsawa ba tace...
"Dallah dakata Mallam in ka kasane kawai kace mana ka kasa ba wai ka samu a gaba kana mana ihu kaman wasu 'ya'yanka ba kuma wallahi..."
Bata samu daman k'arasa maganan ba sakamakon rufe mata baki da Aina'u tayi tana wuri-wuri da ido tace..." Lateefa bakida hankaline kike musu da boka,ko kin manta abinda na gaya mini a baya ne?"
"Ke dallah sake min baki " tace tana ture hannun Aina'u a kan bakinta ta cigaba da magana..." Anyi mishi musun sai me?yayi duk abinda zaiyi in ya isa".tace tana huci.
Aina'u zubewa tayi a kasa tana tuba a gaban boka .
Wata mahaukaciyar dariya ya kece dashi yana nuna Aina'u yace..." Ke tashi kiyi tafiyarki,ke kuma kije zaki ga abinda zanyi da wanda ba zanyi ba" ya karasa yana zarowa Lateefa manyan idanun shi kaman na 'ya'yan boris.
Tsaki Lateefa taja ta fice abinta ko d'ar bata ji a zuciyar ta ba.
Suna shiga mota Aina'u tace..."gaskiya Lateefa kinyi kuskure ko ince kinyi ganganci but dont worry akwai wani shahararren boka da yafi wannan in kina so yanzu zan je wajan shi ya gama mana dasu dan shi ba abinda yake gagaran shi,shiyasa ake mishi lak'abi da boka gagara badau.amma yana da matsala 1 bata karban kudi kad'an kaman wannan bokan sai masu yawa".
Ba tare da ta kalle ta ba Lateefa tace..." Har nawa yake karb'a?"
"Millions of naira ake bashi" Aina'u ta bata amsa.
Wani mugun kallo Lateefa ta watso mata tare da cewa..."wat millions of naira kika ce?amma daga ke har shi baku da hankali".
"Da hankali na mana Besty ganin situation da kike ciki shi yasa nace muje wajan shi and am assuring u zai miki aikin da nan da wani lokaci kad'an ba mai yawa ba zaki maida abinda yafi wanda kika kashe,ko ya kika gani?" Aina'u tace haka tana kallon fuskan Lateefa.
Ajiyar zuciya Lateefa tayi tace..." Na yarda dake Ainau,bud'e hand bag na ki d'auko min check book inyi miki singing duka abinda ya bukata just ki cire ki bashi".
Da haka suka iso inda zata sauke Aina'u ta sauke ta da sharad'in kada ta koma gidan har sai ta k'ira ta sanar da ita aiki yayi k'yau.
Direct hotel da take permanent room ta wuce akan a can zata zauna ta saurari k'iran Aina'u,dan baza ta iya jure ganin Ameera da 'ya'yanta cikin walwala ba.
Salees ta k'ira a waya kan yazo suyi zaman su tare amma yace mata yana Dubai yaje saro musu kaya sai nan da sati maybe zai shigo.
Haka ta cigaba da zama a hotel ita kad'ai ba abinda take sai shan wine sai bacci.
A ranan da ta cika 3days ne da daddare har ta fara bacci ta fara jin motsi cikin baccin.
A d'an tsorace ta bud'e idonta.
Tsoron ta ne ya k'aru ganin d'akin duhu ya mamaye alhalin bata kashe wutane d'akin ba.
Kamin tayi yunkurin yin wani abu taga haske a tsakiyan d'akin kaman an kunna candle.
Boka ta gani yana mata dariya d'akin yana amsawa,hannayenta tasa ta toshe kunnuwanta da shi sakamakon Dodon kunnen ta da taji suna barazanan fashewa.
Ganin shi tayi akan gadon da take tsirara da wata k'warya a hannun shi ga warin da yake fitowa daga cikin kwarayan shima yana yana barazanan sata amai.
Hannu yasa ya ciro abin ya d'aura mata a kan cikinta tare da karanto wasu kalamai da shi kad'ai ya san ma'anar su.
Tun da Ya fara Lateefa ta kasa motsa koda yatsanta balle tayi yunkurin guduwa.
Saida ya shafe minti 2 yana yi sannan abinda ya d'aura mata a kan cikin ya b'ace bat.
Abin yana b'acewa boka ma ya b'ace kuma wutan d'akin ya dawo, kuma sai a lokacin taji zata iya motsi.
đđđđđđ
*UKUBAR KISHIYATA*
đđđđđđ
(Its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman Yusuf)
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONđŤđŤđŤ~*
*_~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~_*
*part forty seven*
A razane ta tashi zaune tana dube-dube ko zata ga wani Abu amma bata ga kowa ba.
Barin gadon tayi ta koma kan kujera ta takure cike da matukar tsoro.
Kamin wayewar gari duk kamannin ta sun canza,baya ga haka ga cikinta inda boka ya d'aura mata abu ya zama gyambo yana fitar da wani irin ruwa mai warin gaske da ita kanta tana cutuwa da wsrin balle kuma ta kaiga mutum ya zauna kusa da ita.
Gari yana wayewa ta k'ira Aina'u amma wayarta a kashe.
Wuni tayi tana trying but amsa d'aya take samu shine is switch off.
Ganin yamma ta karato yasa tsoro ya karu a zuciyarta tana ganin in ta sake k'wana a d'akin nan maybe abinda zai same ta sai yafi na jiya worst.
Had'a 'yan kayanta tayi ta fito da niyan komawa gidanta.
Tana fitowa reception,duk mutanen da suke wajan suka fara toshe hanci suna mata kallon kyama wasu har guduwa suke daga wajan.
Sauri-sauri gudu-ggudu ta fice daga reception d'in ta fad'a motan ta.
Direct gida ta nufa,ta shigo bugum- buzugum kaman wata mahaukaciya.
Ameera ta gani k'wance a kan cinyar Al'ameen ta d'aura Fadeel kan cikinta,Al'ameen yana rik'e da Fadeela yana sai ta sauk'e Fadeel ta d'auki Fadeela da take kuka ita kuma tana bata so.
Tsayawa tayi a bakin k'ofan parlour tana kallon yanda suka kaure da kokuwan wasa suna ta dariya.
Lokaci d'aya suka ji wani irin wari mai kama da mushen jaki ya cika musu parlour.
Lokaci d'aya suka toshe hanci tare da dubu-dube ko zasu ga me yake musu wari haka.
Lateefa suka gani tsaye a bakin k'ofa fuska duk hawaye ga kamannin ta da yanayin ta duk sun canza.
Ganin duk sun zuba mata ido yasa tayi hanyan part d'inta ba tare da tace musu komai ba,suma ba Wanda ya iya ce mata komai illa rakata da ido suka harta shige.
Tafi 5 mins da wucewa sannan suka samu daman sake hancin su.
Ameera turaren wuta ta saka a parlour harda room fresher sannan warin yayi dama-dama.
Tsaki Al'ameen yaja yana cewa ..." Gaskiyan Hajiya da tace zata dawo da kanta ni ko shekara zata yi a gidan nasu ba zan tab'a binta ,ji yanda ta dawowa mutane kaman wata mahaukaciy".saboda Al'ameen duk a tunanun shi yaji tayi dan ya mare ta akan ta zagi Ameera.
Ameera ta rasa bakin magana jin abinda Al'ameen yace,saboda tabbas tasan ba yaji tayi ba bisa la'akari da magananun da ta fad'a mata kafin ta fita.
Allah ya musu tsari daga sharrinta tace a zuciyarta
dan Al'ameen baisan komai game da zaman da suka yi a baya ba.
Lateefa taci kuka a d'aki kaman ranta zai fita ta rasa tudun dafawa ga number Aina'u tayi ta gwadawa harta gaji.
Alert da tagani ya shigo mata waya shiyasa ta tsayar da kukanta ba shiri ganin an k'washe mata kud'in da suke account d'inta dama 12.5 Millon ne a ciki.
Tunawa tayi da Aina'u da kuma blank check da ta bata.
Sumbatu ta fara tana zagaye d'akin ita kad'ai kamar wata zararriya,ya za'ayi Aina'u ta k'washe mata kud'i tas kuma ta kashe waya me take nufi da hakan?
Kaman wacce ta tuna wani abu a zabure tayi wajan wani drower da take ajiye muhimman abubuwanta ciki harda documents na Al'ameen da ta k'washe a wajanshi.
Tana bud'e drowern shima wayam tagani ba ko d'aya duk ya k'wshe kayan shi sai 'yan kud'ad'e a cikin.
Ta baya-baya ta fara tafiya tana girgiza kai harta kai jikin bango.
Zaman 'yan bori tayi a wajan ta rasa wani irin tunani zatayi dan hawayen ma kafewa suka yi.
Lokaci d'aya komai na rayuwa ya tsaya mata Iowa ya juya mata baya ga wannan gyambon k'ara girma yake yana mata ciwon da ba zata ya misalta shi dana ciwon ajali.
Wayarta ta d'auka ta k'ara gwada number Aina'un hoping zai ko shia but still a kashe.
Number su Shamsiyya ta gwada suma a kashe dan haka sai ta k'ira na Mama bugu 2 ta d'auka tana..."Lateefa 'yar k'walisa ".
Da ba sunan da take jin dad'in shi kaman shi amma yau wani bakin ciki taji ya rufe ta.
Daurewa tayi tace..." Mama su Fa'iza sun zo gida wajanki?"
"Yaushe rabona dasu,sun dad'e basu zo.basa gidan ne?"
"Nima rabo na dasu yafi sati 2 bansan ina suka je ba" Lateefa ta amsa mata.
Mama tace..." Kin san su da zuwa gidan k'awaye kila yanzu suna gidan wata k'awar su".
Amsawa tayi da haka ne,suka yi sallama suka ajiye waya.
Yini tayi a d'aki ko parlourn ta bata leka ba har zuwa dare.
Karfe goma da rabi na dare tana kwance ta kasa bacci saboda azababben yunwa da yake k'wakularta tun tana daurewa har dauriyan nata ya kare taga ba zata iya jurewa ba.
Cikin tsand'a ta fito dan nemawa cikinta wani abu, Allah ya bata sa'a babu kowa a main parlour bata tsaya b'ata lokaci ba ta fad'a kitchen.
Warmers da akayi dinner dasu ta fara bubbud'ewa ko zata samu amma duk babu komai a ciki.
Wata daban tagani a can kusa da sink tana bud'e shi taga guntun tuwon shinkafa ce da akaci aka rage ga pepper soup na kifi da akaci sauran shima aka zuba akai.
Jiki na rawa ta jawo shi tare da zama dirshan akan tiles ta ciccire k'ayan ciki sannnan ta fara sambad'a loma hannu baka hannu k'warya.
Cikin abinda baifi kiftawar ido ba harta cinye abincin tas .
Bata tashi a wajan ba saida ta sid'e cooler tas kaman an wanke ta sannan ta hakura ta koma d'akinta ta kwanta da niyan gobe da sassafe zata tafi hospital taga doc ko zata samu maganin wannan bala'in da boka ya had'ata da shi.
Da washe gari da sassfe ta saka kai ta fice daga gidan dan zuwa hospital ba tare da kowa ya ganta ba.
Wani private hospital taje cikin sauki ta samu ganin doctor saboda warin jikinta duk inda taje bata hanya ake.
Tana yi mishi bayanin matsalarta amma ji yake kaman ya fita ya bar mata office d'in.
Daurewa yayi ya nuna mata gado da yake cikin office d'in yace ta hau ta k'wanta ya duba ciwon.
Hand gloves ya saka tare da rufe hancin shi da abin rufe hanci sannan yaje kanta ya tsaya a k'yamace ya mata nuni da ta d'aga rigarta ya gani.
Da gudu doctor ya fita a office d'in yana kwara amai kaman ranshi ya fita sakamakon ganin ciwon Lateefa da yayi.
Da ido tabi shi zuciyarta na suya lalle boka ya gama cutarta yasa ta zama dodo a cikin mutane.
A sanyaye ta tashi zaune tana gyara rigarta wasu securities 3 suka shigo suka tasa keyarta gaba har bakin motarta..
Shiga tayi ta tayar da motarta ta fita a asibitin ga hawaye sai tsere suke a idonta.
Tunani take a zuciyarta na ta tafi wani asibitin ne kota ta fita abroad?
Zuciyarta yafi amincewa da ta fita abroad d'in dan haka ta juya kan Motan ta tayi hanyan gida.
Tana tafe tana zancen zuci,tana gwara da tayi dabara ta bawa Salees kud'inta yana juya mata su gashi yanzu sai ta karb'i abinta taje ayi mata maganin fitinan da boka ya had'ata dashi.
Tsaki taja ganin yanda hold up yayi yawa yawanci 'yan zuwa aiki da makaranta sunfi yawa.
Juyawar da zatayi kaman daga sama taga Aina'u cikin wata luxurious car sabo dal sai sheki take.
Murza idonta tayi Dan tabbatar da gaskiya idonta yake nuna mata ko dai Aina'un da ta sani ne?
Sauke glass na window motarta tayi tana k'wala mata amma bata jiba saboda ita glasses nata a rufe suke.
Har tana shirin bud'e kofar mota ta fita taga taja motarta tayi gaba.
Da sauri ta fad'a nata tabi bayanta.
Tana bin bayanta taga Aina'u ta tsaya a wata lafiyyar gida madaidaici mai d'an karan k'yau.
Tun kamin tayi horn mai gadi ya bud'e mata gate ta shiga ciki.
Tana shiga ya mayar da gate ya rufe.
Da gudu Lateefa ta fito a nata mota ko kashewa bata tsaya yi ba tabi bayan Aina'u ta shiga ta karamin k'ofa tana kwala mata kira.
Juyowa kawai tayi tana kallonta fuska a had'e kaman an aiko mata da sakon mutuwa,ba tare da ta amsa ba har ta karaso kusa da ita tana haki da fara'a akan fuskarta.
Hanci Aina'u ta toshe tana komawa baya tana mata kallon wulakanci da kyama tace..." Lafiya kike kwala min kira haka?"
Hawaye ta fara tana..."Aina'u kin ga abinda boka ya min kin ga yanda ya maida ni na zama abin kyama a cikin mutane kowa ya ganni sai ya toshe hanci,kema kulum ina ta trying number ki bata shiga. Nayi ta jiran kiranki kaman yanda kikayi alkawari shiru sai daima alert d'in kwashe min kud'in account da kikayi gaba d'aya".
Tunda ta fara magana take binta da kallon wulakanci harta karasa kana tace..." Maganan boka ke kika jawowa kanki dama na gargad'e ki tun farko ba'a mishi musu kikayi harda cacan baki,maganar kud'i kuma nice na kwashe su kuma banje wajan wani boka ba face rabona dana kwada dan bazan tashi a tutar babu ba,saboda haka fita ki bar min gida tun kafin ranking ya b'aci ko insa yanzu ayi min waje dake".
Da gudu Lateefa tayi kanta tana..." Wallahi baki isa ba ni zaki yiwa haka?na rantse da Allah sai kin fito min da kud'i na".
Hankad'ata Aina'u tayi sai gata ta zube a kasa kaman kayan wanki.
"Isa isa!!" Aina'u ke kwalawa masu gadinta k'ira tun karfinta.
Da gudu suka zo gabanta suka zube.
Cike da masifa tace..."Ku fitar min da matan nan a gidana kuma wallahi in kuka k'ara barin irin wa'yan nan suna shiga min gida a bakin aikin Ku"tana gama fad'an haka tayi cikin gida abinta.
Ciccib'ar Lateefa da take ta faman zage-zage da tsine-tsine harda fizge-fizge amma hakan baisa sun sarara mata ba saida suka fito da ita da karfin tsiya suka jefar tare da maida gate suka rufe.
Ta dad'e zaune a bakin gate d'in gidan tana cigaba da masifa har tana bubbuga gate ba wanda ya kulata saima jama'a da suka fara taruwa suna mata kallon sabuwar mahaukaciya.
Gajiya tayi da masifar ga zafin rana da ya ishe ta yasa taja tsuman jikinta ta shiga motarta ta bar anguwan.
đđđđđđ
*UKUBAR KISHIYATA*
đđđđđđ
(Its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman Yusuf)
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONđŤđŤđŤ~*
*_~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~_*
*part forty eight*
Kuka take kaman ranta ya fita wai yau ita Aina'u zata yiwa haka?duk abinda tayi mata a baya bata gani ba?
Cak kukan nata ya tsaya kaman d'aukewar ruwan sama sakamakon abinda idonta ya gane mata.
Fa'iza da Shamsiyya ta gani a bayan moton sojoji fuska duk a kumbure.
Bata san lokacin da ta juya kan motan ta ba ta fara binsu a baya har zuwa jaji.
Zata shiga wasu manyan sojoji masu kama da samudawa suka dakatar da ita.
Rokonsu ta farayi kan suyi hak'uri su barta ta wuce kannenta ta gani an shiga dasu ciki.
D'ayan yace.." wa'yan nan ne k'annenki?"
Amsawa tayi tana k'ara kusanto su.
Tsawa suka daka mata kan ta tsaya inda take.
Duk baya sukayi suna toshe hanci tare dayi mata kallon k'yama.
D'ayan cikin su yace...
"Hey chidimma make u call oga and tell him".
Wani k'aramin d'aki ya shiga ya d'auki waya irin lane line d'in nan yayi k'ira.
Bayan sun gama magana ya fito yace..." Joseph escort her in".
Mota ta shiga tace shima ya shigo su tafi.
Kallon banza ya fara aika mata sannan yace..." Ban shirya mutuwa ba ji yanda kike wari kaman mushe in na shiga motarki suna na marigayi".
Bata ce k'ala ba ta fara Jan motanta a hankali take bin bayan shi har zuwa wani area mai ban tsoro wajan tsit baka jin motsin komai sai wani k'aton soja mai manyan idanu gasu jawur dasu kaman barkono da suka gani a wajan da alamu shi yake tsoron wajan.
Tambayar Joseph yayi daga ina?
Nan Joseph yayi mishi bayanin komai.
Ido ya tsura mata na wani lokaci sannan ya tambaya..." K'annin ka ne?
"Eh dan Allah kuyi hak'uri ku sake su" tace tana mai zubda hawaye.
Girgiza kai yayi yace..." Kasan menene sunyi kana cewa a sake su? "
Da sauri ta girgiza kai dan gaba d'aya ta gama tsurewa ganin wasu d'ika-d'ikan sojoji sun zo wajan da manyan bindigogi a hannun su.
"Those bloody bitches an kama su a gidan oga kuma a cikin bedroom na oga wit his wife suna yin iskanci,or I think u re among them abi?" Yace yana zaro mata manyan idanu shi.
Jiki na karkarwa ta fara basu hak'uri tace..." Wallahi ban san suna aikata irin wannan mummunar d'abi'a ba dan Allah ku rufa min asiri ku bar ni in tafi".
"Then get out before oga come and sees u here" yace mata cikin tsawa.
Da gudu ta fad'a motarta ta fita daga barack d'in tana kukan bakin ciki na ba yanda zata yi ta fita dasu daga wannan bala'in,koda yake su suka jefa kansu a ciki.
Toh ya akayi suna cikin irin mutanen nan amma bata tab'a sani ba .
Sai yanzu idonta yake hasko mata yanda suke rayuwarsu su 2 kaman wasu masoya ta d'auka zallan shak'uwa ce ashe su abinda suke aikatawa kenan.
Da haka ta k'araso gida cikin tashin hankali.
Addu'a take Allah yasa ba kowa a parlour.
Cikin sa'a kuwa babu kowa ta samu parlour sai t.v da yake ta aiki shi kad'ai.
Ba b'ata lokaci ta fad'a part d'inta tare da murza key.
Zama tayi dirshan a k'asa ta rushe da kukan nadama,wai yau su duniya ta juyawa baya haka? Daga ita har k'annenta suna cikin *UKUBAR* rayuwa.
*UKUBAR* da suka jefa wasu a ciki yau gashi suna cikin wanda yafi karfin tunaninsu.
Ga wacce suke wulakanwa a baya yau gata cikin k'wanciyar hankali.
Dama haka duniya take?.
Har karfe 2 tana zaune a wajan ta kasa tashi.
Dama ba damuwa tayi da sallah ba,amma yau ganin azabar rayuwa yasa ta tashi tayi sallahn azahar.
Komawa tayi ta zauna kuma a lokacin ne ta tuna ashe ba taci komai ba tun safe.
Tunanin ya zatayi ta fita ta samu abinda zata ci take,can ta tuna ashe tana ajiye kayan tea a cikin d'aki.
Jiki na rawa na nufi drower ta bud'e taga kayan tean suna nan harda su snacks.
Bata damu da ta nemi ruwan zafi ba.
Bathroom ta shiga ta taro ruwa a cup tazo ta had'a tea tasha da snacks ta koshi.
Gado ta hau ta k'wanta tana tariyo tarihin rayuwarta.
Ta dad'e a k'wance sannan ta tashi ta d'auki wayarta ta k'ira number Salees.
Saida ya kusan tsinkewa ya d'aga yace..."yah ne Babyna?"
"Ba lafiya Salees i na cikin wani yanayi na tashin hankali ga rashin lafiya ya sani gaba" tace muryanta na shaking alamun tana kuka.
"Subhanallah!! Babyna meya faru,meke damunki?" Salees ya tambaya cikin tashin hankali.
Saida ta face hanci sannan tace ..." Labari ne mai tsawo honey amma ina bukatan kud'ad'ena na wajanka saboda in samu daman fita abroad neman lafiya".
Cike da tashin hankali yace.."abun har ya kai haka Baby na?kada ki damu gobe mu had'u a hotel sai in zo miki dasu ko?"
Wani sanyi taji ya ratsa ta na jin ya rik'e mata alkawari tace..."nagode Salees daz y I love u".
" I love u 2 my Lateefa".yace mata tare da katse wayan.
Tana k'wance a part d'inta taji Al'ameen yazo yana knocking amma tayi biris dashi kaman bata jiba.
Shima bai damu ba ya juya yayi kowan shi dama Ameera ce ta takura mishi lalle sai yazo ya duba lafiyarta duk da abinda Lateefa tayi mata bata rik'e ta a zuciya ba illa damuwa da tayi da ita.
Gari na wayewa tayi sammakon ficewa daga gidan ta tafi hotel inda sukayi alkawari da Salees kan zai kawo mata kud'i.
Anan tayi ordern kayan breakfast tayi ta zauna har zuwa 9am sannan tayi mishi waya.
Shi kuma ya tabbatar mata da ba matsala yana nan zuwa.
Zuwa thirty minutes sai gashi nan ya shigo jaye da wata katuwar trolly da wata madaidaiciyar jaka a kafada.
Tana ganin shi ta mik'e cike da murna dan ta tare shi.
Warin daya ji ya tare shi,shiya hana shi shigowa ya tsaya a bakin k'ofa yana yatsina fuska.
Ganin haka yasa itama tayi turus ta tsaya ba tare da ta k'arasa wajan shi ba.
"Kaga babban dalilin da yasa nake neman kud'in kenan Salees"ta fad'i haka tana duban shi tare da marairaicewa.
Ta cigaba da cewa..." Banyi zaton kaima kana cikin masu guduna ba,saboda kai kad'aine hope d'ina Salees".
"No don't say so Lateefa" ya fad'i haka yana k'arasowa ciki.
Sannan ya cigaba..."kema kinsan bazan tab'a gudunki ba no matter how, saima in k'ara tausaya miki".
Sauke jakunan da yazo dasu yayi tare da zuge zip d'insu duka.
Dollars ne tab a cikin babban trollyn,sai k'aramar kuma dubu Dubu ne a ciki.
D'ago kai yayi yana murmushi yace..."ga dukiyar ki nan na dawo miki dasu kaman yanda kika bani amana".
Durkushewa tayi a wajan tana hawaye tace..."da za'a samu irinka a duniyan nan da duniya bata lalace haka ba dan rik'on amana yayi k'aranci a wannan zamanin .ban san da wani baki zan gode maka ba Salees sai dai ince Allah ya barmu tare.insha Allah in na sami lafiya na dawo zan baka sharen ka".
Murmushi yayi yace..."don't worry Baby just buri na ki samu lafiya.let's go in kinsan nayi missing d'inki sosai".
Cikin murmushi tayi ciki yana binta a baya ta hau gado ta k'wanta.
"Oh gosh " yace yana dafa goshin shi sannan ya cigaba ..."na manta ban rufe kofa ba ,bari in rufe in dawo kuma nazo miki da surprise sai dai ina so ki rufe idonki har sai nace ki bud'e sannan ki bud'e kinji Babyna?"
Cikin zumud'i ta saka tafin hannayenta ta rufe fuskanta.
Tana ji ya fita zuwa parlour har ya rufe k'ofan ya dawo ya tarar har yanzu fuskarta a rufe yake.
"Babyna bud'e idonki...." Yace cikin romantic voice.
A hankali ta bud'e idonta tana murmushi.
A zabure ta mik'e tana nuna su da yatsa bakinta yana motsi amma sauti yaki fitowa saboda kid'ima.
Salees ya k'ara rugumo Aina'u suna mata dariya yace... " haba Babyna meye na kid'imewa haka?wannan shine first surprise saura na 2 kenan".
Kukan kura tayi tayo Kansu da gudu.
Tun kamin ta k'araso Salees yasa mata k'afa ta fad'i.
Kamota sukayi suka fito parlour da ita Salees ya zaunar da ita akan kujera, Aina'u ta bud'e hand bag da tazo dashi ta fito da igiya ta bashi.
Karb'a yayi tare da d'aure ta a jikin kujeran.
Hannu yasa a aljihun wandon shi ya fito da gum ya manne mata baki dashi.
Durkusawa yayi daidai fuskarta yana murmushi yace..."ni bawan ki ne da zaki ce kin bani ajiyar irin wannan kud'in kuma kice in dawo miki dasu?harda wai sai kin dawo zaki bani rabona?hmmmm gaskiya kin raina min wayo ke da baki kare amanan mijinki ba har kike zaton wani zai kare miki amana?kinyi kuskure babba Lateefa cos tunda muke dake ban taba sonki ba koda na second 1 ba.look at this"yace yana nuna mata kud'in da ido.
Ya cigaba..."sune dalilin da yasa muke tare,na da kuma sabida Kore sha'awata nake tare dake.but I regret every second I spent with u"ya k'arasa yana huci.
Dariya Aina'u ta sheke dashi harda rike ciki tace..."kasan me?wai ni ta bawa blank check akan in cire kud'i,dakikiya kawai saboda duk zaman da mukayi dake Lateefa ban tab'a sonki da alkhairi ba ,wajan boka da shawarwari da nake taimaka mini dasu Salees ne yake tilasta min inyi dan Mu cimma burin mu,but Lateefa i terribly hate u".
Tayi kaki ta tofa mata a fuska.
Rintse idonta tayi da karfi saboda wani rad'adi da take ji a k'asan zuciyarta da take ji kaman ya fashe.
Meye zata iya yi musu balle taji sauki a ranta?
Babu shine amsar da ta bawa kan ta sabida tasan sun gama cutarta a rayuwa kuma gata a d'aure.
Saukar lafiyayyar mari taji shiya dawo da ita hayyacinta.
Salees tagani yana nunata da yatsa yace...ni zaki rainawa hankali INA magana kina jina?"
K'aramar jakan ya jawo gabanta yace..."ga rabonki sweetheart sai dai nake ganin kaman d'aukan zaizo miki da matsala,let me call wanda zai taya ki d'auka kin san bana son inga kina wahala".
Wayar ta ya dauka ya fara scrolling yana neman Wanda zai kira.
Yana zuwa kan sunan da yake nema ya kece da dariyar mugunta tare da nuna mata screen d'in wayar.
Sunan da ta gani ne ya k'ara jefata cikin tashin hankali da ya d'ara na yanzu.
Kai ta fara girgiza mishi hawayenta na k'ara k'aruwa.
Shafa gefen fuskanta yayi yana murmushi yace..." Haba Babyna kar ki d'aga hankalinki just dakon kud'inki zai mini kin gane?"
Tana gani ya danna k'iran number.
Fizge-fizge ta fara ko zata iya kunce d'aurin da yayi mata amma ko motsin kirki ta kasa yi.
đđđđđđ
*UKUBAR KISHIYATA*
đđđđđđ
(Its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman Yusuf)
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONđŤđŤđŤ~*
*_~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~_*
*part forty nine*
Al'ameen yana rik'e da Ameera da take ta k'wara amai kaman ranta ya fita.
Sannu yake ta jero mata kuma at d same time yana ta masifan shi..." Dama saida na hana ki zuwa d'akin nan amma kika nace ke sai kin kai mata breakfast, ita yarinya ce da sai an kai mata?gashi kin jawowa kanki aman dole.wannan warin jikinta dana d'akin nata zai iya kisa,kinyi sa'a da kika tsaya a amai".
Ameera dai tana jinshi ba tace komai ba saboda aman yaci karfinta .
Da k'yar ta samu ya tsaya ta kuskure bakinta tare da wanke fuskarta ta dawo kan kujera ta zauna tana maida numfashi.
Shima zama yayi a kusa da ita yana yi mata sannu.
Ringing d'in wayar shi da yaji yasa ya tashi zuwa kan center table inda ya ajiye wayoyin shi.
Sunan Lateefa da ya gani yana yawo akan screen d'in wayan yasa yaji kamar kar yayi receiving saboda yanzu babu wanda ya tsana kaman ita ga sabon al'ada da ta samu na fita da shiga a duk lokacin da taga dama ba tare da izinin shi ba.
Saida k'iran ya kusan tsinkewa sannan ya daure ya d'aga.
Maimakon yaji muryarta sai yaji murya wani namiji yace.... "Alhaji Al'ameen mudassir mijin Lateefa ko?"
Da k'yar ya bud'i baki ya amsa da..."eh nine meye ya kawo wayar mata ta hannunka?"
Dariya ya kece dashi sai da yayi mai isar sa sannan yace....matarka ko matar mu?"
Tsawa Al'ameen ya daka mishi wanda yaja hankalin Ameera gare shi yace..."bana son zancen banza waye ne kai?"
Salees yace..." Easy man stop shouting yanzu zaka ce baka sanni ba?sau nawa kake zuwa ka same ni a gidanka koda yake raina maka hankali take tace maka no d'an uwanta ne,ga files da kake saka hannu ana kawo min.no need of explanation tunda kasan wannan wayar matar kace yanzu haka tana (prince hotel)room number 35 wannan d'akin matarka tana rik'e da shi fiye da 15years.u can come and see for urself saboda ka tabbatar da abinda na fad'a maka in kaki kuma kayi zamanka,maybe zakayi mamakin dalilin da yasa nake fad'a maka haka ko?ta gama yi min amfani shiyasa".yana gama fad'an abinda yayi niyya ya katse wayan yana kallon Lateefa fuskar shi d'auke da murmushi yace....
" mijinki yana nan zuwa ya d'auke ki,mu zamu tafi sai wata rana.
Juyowa yayi wajan Aina'u yace mik'o min abin muyi mata suprice na 3.
Wata sharb'eb'iyar wuk'a Aina'u ta ciro a cikin hand bag d'inta ta mik'awa salees.
Karb'a yayi yana jujjuyawa daidai fuskan Lateefa wacce tuni tayi suman zaune dan hawayen ma bata san lokacin da suka kafe ba.
Kan wuyanta ya d'ora yana dariya yace..."am sorry Babyna".
Rude idonta tayi tana jiran mutuwarta .
Hannunta na dama ya kama daidai wajan yatsunta 5 yace..."bazan kashe ki ba amma zan miki abinda zaki rinka tunawa dani always ".
Sare hannun yaji wanda nan da nan hannun ya guntule ya fara tsalle a cikin parlour ga jini yana ta tarwatsuwa a parlour.
Kafa yasa ya danne gutun hannun daya guntule har ran ya fita.
Ya juya yana kallon Aina'u yace..." muje sweetheart".
K'wasan duka tarkacen su sukayi gaba suka bar mata k'aramar jakan kud'in.
Ita kuwa Lateefa tun daga nan bata san inda take ba sakaman yawan jini dake ta zuba a jikinta.
Ameera ce durkushe a gaban mijinta tana kallon da ya rine yayi ja kamar gauta..
Hankalinta ne ya tashi saboda bata tab'a ganin shi cikin irin wannan yanayin ba.
Cikin Sanyin murya ta fara tambayan shi meya faru?
Ya dafe goshin shi da hannayen shi duka 2 yana kallon kasa.
Ya d'ago yana kallonta,itama idonta taf da hawaye yace..."wani ne ya k'irani yake min maganan banza akan Lateefa har yake cewa in ban yarda ba inje in gani da idona".
"Maganan banza?wani irin maganan ne haka?" Ameera ta tambaya da alamun tsoro akan fuskarta.
Mik'ewa yayi zumbur ba tare da ya bata amsan tambayarta ba yasa kai ya fita da saurinsa.
Da kallo ta bishi tana addu'an Allah yasa lafiya.
Yana fitowa compound gidan Bala driver ya taso yana mishi magana ko kallan shi baiyi ba balle ya tanka.
Mota ya shiga ya fige ta da karfin tsiya ya fita a gidan.
Driving yake kaman zai tashi sama zuciyar shi kuwa a cunkushe take duk da yana shakkar abinda yaji a Waya amma wani bangare na zuciyar shi kuma ta yarda bisa la'akari da rashin kulawa da yake samu daga gare ta.
Cikin lokaci k'ankani ya iso hotel d'in ya fito a motan bayan yayi parking a parking space na hotel d'in.
Bugun zuciyar shi sai k'aruwa take a lokacin da yake duba numbers na d'akunan har ya kawo room number 35.
Cak ya tsaya yana fargaban bud'ewa dan bai San abinda idon shi zai gane mishi ba.
Haka ya daure ya kai hannu kan murfin k'ofan ya murd'a ya jiya a bud'e.
Turawa yayi ya shiga ciki tare da dube-dube.
Lateefa ya gani d'aure kan kujera cikin jini male-male bata cikin haiyacin ta.
Da gudu ya k'arasa wajanta yana ambaton sunanta tare da girgiza ta amma bata san ma yanayi ba.
Waya ya fito dashi ya k'ira Ya Sa'ad da shi,shi kuma yace ya fara k'iran police tukunna suna zuwa.
yana nan tsaye cikin tashin hankali dan ya rasa dame zai fasaara wannan al'anari.
Within 15 mins ambulance da police suka zo at d same time.
Bayan 'yan geaje-gwaje da bincike da police suka yi aka saka ta a ambulance akayi Hospital da ita.
Al'ameen shima motan shi ya fad'a ya bisu a baya.
Suna isa asibitin aka wuce da ita emergency,doctors kusan su hud'u harda Ya Sa'ad suka taru a kanta wanda a dole suke aikin saboda warin da jikinta yake fitarwa.
Mamanta ya k'ira ya sanar da ita abinda yake faruwa.
Cikin rud'u da gigita tace gata nan zuwa.
Iyayen shi ya k'ira suma ya sanar dasu,nan suka taya shi jimami tare da cewa suna zuwa .
Haka yayi ta sanar da duk wanda ya dace ya sanar,bayan ya gama wayar doctors suka fito da nasaran cewa an samu dakatar da jinin kuma anyi sa'a blood group d'inta A ne dan haka har an k'ara mata zuwa nan da 1 hr zata iya farkawa.
Godiya ya musu sannan yace zai je gida ya dawo.
Ameera tana zaune ita kad'ai a parlour ta rafka tagumi da hannayenta duka 2 .
Tana ganin shi ta mik'e da sauri ganin ya dawo kaman ba yanda ya fita ba.
A tare suka zauna akan kujera 2 seater yace ..." Ki shirya muje hospital "
"Hospital kuma meya faru waye ba lafiya?"Ameera ta katse shi da tambaya.
" Lateefa ce"ya bata amsa a gajarce tare da bata labarin abinda ya gani .
Salati ta rinka maimaitawa tare da mamakin waye yayi mata wannan aikin.
A gurguje ta gama shiryawa harda twins d'inta cikin kaya masu k'yau suka nufi hospital gaba d'ayansu.
A can suka tarar dasu Alhaji da sauran 'yan uwa duk sunyi jugum dasu .
Bayan sun samu waje sun zauna Hajiyar shi take tambayar shi ya akayi hakan ta faru?
Nan itama ya maimaita musu abinda ya gani.kowa ya rink'a tofa albarkacin bakin shi,sun d'an jima zaune suka hango Maman Lateefa wujiga-wujiga tana tahowa.
Idonta ya riga da ya rufe dan haka bata ma lura dasu ba har zata wuce Al'ameen yayi mata magana ta tsaya ta dawo wajansu .
Hajiyar Al'ameen ta sauke Fadeela dake kan cinyarta ta kamo hannunta suka zauna tare da tambsyar ya jikin'yarta?
Hajiya tace..."gamu nan dai muna jiran farfad'owarta dan sunce nan da awa 1 zata farka amma gashi har awa 2 ta wuce".
Kuka tasa tana..."dan Allah ku gaya min ko ta mutu ne?"
Hajiya ta bud'i baki da niyan bata amsa wata nurse tazo tana tambayar INA Al'ameen da Ameera?
A tare suka mi'ke suna kallonta.
"Ta farka kuma tace tana son ganin ku"
Gaba d'ayan su suka d'uru cikin d'akin.
A take sauran suka koma baya suna toshe hanci sakamakon warin da suka ji ya tare su.
Kuka take kaman ranta ya fita tana duban su d'aya bayan d'aya .
Cikin kuka tace..."Al'ameen,Ameera ku yafe min nasan alhakin kune yake bibiyata na cuci kaina na cutar daku a bata ta fanni da yawa".
Nan ta fara zaiyane musu abubuwan da ta shuka tun kamin auren ta da Al'ameen har zuwa yanda Al'ameen yazo ya same ta a hotel.
Tunda ta fara jawabin Al'ameen yake ji kaman ba shi ba kuma sai a lokacin ya fara tuno abubuwan da suka faru wanda da yake ganin kaman a mafarki ya faru ashe da gaske ne.
Wani irin tsanan ta ya rinka ji wanda baya tsammanin akwai wani halitta da ya tab'a tsanan abu kaman yanda ya tsani Lateefa ba a yanzu.
Rokonsu ta farayi tana magiya harda hawaye kan su yafe mata wanda Al'ameen yake ji kaman ruwan dalma take zuba mishi.
A zuciye Al'ameen yayi kanta ya shake mata wuya yanda ko numfashi bata iya shak'a nan da nan idonta suka firfito waje tare da firfitowa.
đđđđđđ
*UKUBAR KISHIYATA*
đđđđđđ
(Its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman Yusuf)
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONđŤđŤđŤ~*
*_~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~_*
*part fiffty*
*last page*
Da gudu yayun shi sukayi kanshi suna kokarin b'anbare hannun shi daga wuyanta amma suka kasa.
Alhaji ne yazo ya k'washe shi da mari tare da hankad'a shi gefe.
Bango ya nausa da duka karfin shi na haushin bai samu nasaran halakata ba inama ace Alhaji baya wajan da sai ya raba ta da duniyan inyaso duk abinda zai faru ya faru.
Lateefa sai tari take Mamarta tana rik'e da ita gaba d'aya ta fita haiyyacinta.
Ameera tana gefe sarkin tausayi sai sharar hawaye take tace...Anty kiyi shiru ni kam na yafe m....".
Tsawan da Al'ameen ya daka mata yasa ta katse maganarta tana kallon shi a tsoro ce saboda a iya zamansu hakan bai tab'a faruwa ba.
"Baki da hankali ne?kina jin abinda tace ta aikata miki harda yaran mu da bakinta amma ki wani ce zaki yafe mata?" Ya k'arasa maganan cike da takaici yana huci.
Ta bud'i baki da niyar magana kenan police duka shigoda hakan kud'in da Sslees ya bar mata.
Gaishe da mutanen d'akin sukayi sannan d.p.o ya fara bayani kan cewa basu samu evidence d'in komai ba,da alama mutanen sunyi da gloves amma dai zasu cigaba da bincike har sai sun gano wanda yayi wannan d'anyen aikin.
Juyowa Al'ameen yayi wanda tunda suka shigo ya juya musu baya yace..."kaga d.p.kuyi tafiyarku ba sai kun wahala ba na yafe binciken Ku bar shi kawai".
"Amma yallabai aiko kace mu bari ba zaiyu ba saboda dole hukuma ta nemo mai laifi a duk inda yake a hukunta shi and ga kud'in da muka samu a d'akin" ya k'arasa gaban Al'ameen ya ajiye jakan.
"Ku d'auka bana bukata " yace Yana juya musu baya.
Matsowa d.o.p yayi yana..." A gaskiya yallabai ba zamu iya d'auka ba saboda...."
A harzuke ya juyo yace...." Nace ku d'auka in bakwa so ku jefar a hanya is not my problem but pls leave me alone ".
Alhaji ne yasa baki yace su tafi kawai tunda yace baya so.
D.p.o yace..." Shikenan Alhaji mun gode zamu tafi mu cigaba da bincike".nan suka juya suka fice,constable sai murna suke kaman suyi tsalle ganin makud'an kud'in nan ance ya zama nasu.
Suna fita Al'ameen ya dawo da duban shi kan Lateefa da ta gama shan jinin jikinta yace..." Kina wani cewa kin cuce mu toh ki sani bamu kika cuta ba face kanki kuma ba wajan Mu zaki nemi gafara ba sai wajan mahaliccinki Dan shi sab'awa ba wani ba,anan kuma a gaban kowa zan fad'a in Al'ameen na saki Lateefa saki 3...."
"Kai!!! Haka da hankali ne" Alhaji ya katse shi a tsawace.
Hajiya ce tayi saurin cewa..."haba ya zaka hana shi?wannan shine dai-dai da ita sai taje can ta samu irinta ta aura ba dai d'ana ba wallahi kuma tsakanin Mu dake Allah ya isa macuciya kawai".
Tana gama fad'anta ta fice a zuciye,alokacin ita da Alhaji ne kawai suka saura Dan Al'ameen da yayun shi sun dad'e da barin d'akin.
Alhaji ma fita yayi ba tare da yace komai ba saboda shima hukuncin yayi mishi dai-dai ya dai yi magana ne kawai a matsayin shi na babba a wajan.
Mama kanta a k'asa tayi shiru ba tace komai ba har suka gama ficewa a d'akin suka bata daga ita sai 'yar ta.
Ita kanta abin ya bata mamaki da takaici dan duo shekarun nan bata tab'a sanin wannan mummunan halin 'yarta ba,ta d'auka tunda tayi aure ta watsar da komai a titi ashe abin ba haka yake ba.
Jiki a mace Mama tace..."ina su Fa'iza ban gansu ko basu san abinda ya faru dake ba?"
Murmushin takaici tayi sannan ta bawa Mama labarin abinda ya faru dasu.
Kuka Mama take sosai irin kukan nadama nan.
Lateefa tana kallonta tace..."lokacin kuka ya wuce Mama tunda kece sila na duk wani rayuwa da muka tsinci kan mu a ciki,run farko me kika lalata mana rayuwa Dan muddin zamu kawo miki kud'i ba ruwanki komai ma muyi gashi yau wa gari ya wayewa? 'Yan Mayan ki 2 sun halaka ni da nake rayen ma gwara mutuwata kan rayuwar da zanyi a gaba".
Mama kass cewa komai tayi sai kuka da take rizga saboda ita tasanmaganar da Lateefa ta fad'a gaskiya ce da hannunta ta watsar da yaran ta gashi yau duniya da rayuwar sun juya musu baya.
******************
Driving yake cike da nishad'i sun taso daga night club ya d'an kalli inda take yace..." Swthrt yau jina nake wani fresh dani".
Dariya tayi tare da k'wantar da kan ta akan kafad'an shi tace..." Nima haka nake ji my love yanzu said Mu bud'e sabon rayuwa da zunzurutun kud'i naira million 150".
Dariyan mugunta ya k'washe da ita yace..."kuma a banza muka same ta ba?"
Hirar su suke sosai cikin jin dad'e har suka zo gidan su.
Masu gadi har 2 sukayi rige-rigen bud'e musu gate suka wuce ciki.
Wanka suka fara yi sannan Aina'u ta jera musu abinci akan table.
Bayan tayi serving d'in shi yace..." Me ba zaki ci ba?"
Girgiza kai tayi tace..." Zuciyar ta tashi take ba zata iya cin abinci ba ruwan Lipton zata sha tasa ruwa a kettle.
Salees ya fara cin abinci suna hira yanda gobe zasu kai kud'ad'en su bank.
Aina'u tace..." My love dole Mu raba k'afa in ba haka ba akwai matsala.
D'an dariya Salees yayi sannan ya d'auki ruwan dake gaban shi ya shanye tare da ture gutun abincin da yake gaban shi ya dube ta yace..." Me meye tabbacinki na zan sure ki da har kikayi saurin amincewa haka?Ku mata k'wak'walwan Kifi ne daku,ita da taci amanar mijikin ta ta fifitani akanshi bai hana ni ci mata mutunci da wulakanta ta ba sai ke?kema kin San banida mutunci ko kad'an more especially akan money"
Murmushi Aina'u tayi tana kallon shi ko d'ar babu azuciyar ta tace..." Na sani ba sai ka tuna min ba kai kare ne mara mutuncti how can I trust u? But tunda kaci abincin nan plan na ya taxi dai-dai saboda ko 10mins ba zakayi a raye ba balle evil plans d'inka suyi aiki a kaina" ta k'arasa tana yi mishi dariyan mugunta.
Dariyan shima ya cigaba da taya ta dashi yace...." Wow!!! Kin birge ni sosai but u re too late ".
Had'e rai yayi kaman ba shine yake dariya yanzu ba
Pistol ya zaro daga aljihun wandon shi kamin Aina'u ta ankara ya d'auke goshin ta dashi.
Nan Aina'u ta fad'i ko shurawa ba tayi ba.
Tashi yayi yazo gaban trolleyn kud'in ya bud'e ya durkusa a gaban yana dariya yana shafa kud'in yana aiyana yanda plan d'in shi ya tafi kaman yanda ya tsara saboda yayi imanin Aina'u a yanda take matukar son shi ba zata iya Sa mishi wani abu a abinci ba.
Tari ya fara yi babu kakkautawa jini ya fara fitowa daga baki da hancin shi.
Nan ya fad'i yana shure-shure mutuwa ko minti 2bayi ba ya sandare a wajan .
Parlour ne ya fara tururin hayaki ,ruwan zafin da Aina'u ta saka a kettle ya kone adalilin haka wuta ya kama gadan.-gadan.
Kamin masu gadi su ankara had wutan yaci karfin gidan.
Fire fighters sunyi nasaran kasbe wutan amma Aina'u da Salees sun zama toka.
Lateefa da Mamar ta sun koma zariya sakamakon Koran kre da akayi musu daga asbitin Ya Sa'ad.
Lateefa taga rayuwa kasancewar ta zama mai larura ga rashin hannu ga gyabonta da kullum k'ara gaba yake dan haka a waje tske k'wana Mama taki yarda su k'wana d'aki 1a Cesar ta zata iya mutuwa in suka zauna wake 1.
Ko tana nema taimako ba mai taimaka mata duk sanyi da iska hard a damina akan ta suke k'arewa,in mutum ya ganta sai ya rantse da Allah ba Lateefa bace 'yar k'walisa tayi kuka har ta saddakar.
Yanzu sosai abin nata yayi gaba saboda har kayan cikinta ya tab'a bata iya ci balle sha.
Tana jefe a cikin gidan sauro ba mai kula ta had tsutsosi saida suka fara cinyeta.
Kwana 2Mama bata ji motsinta ba tazo ta duba ta taga ashe rai yayi halin shi da dad'ewa dan harta fara kumburi.sakamakon in da gyambon ta yake fitarwa shiyasa basu lura da mutuwar ta balle suji warin gawa.
Allahu Akbar!!! Shiyasa ake so mutum ya shuka khairi in kayi akasinta kuma tun a duniya zaka fara gani kamin muje kiyama.duk abunda mutum zaiyi ya tuna akwai Allah yana ganin mu kuma mu kuma mutuwa dole zata riske Mu ko kana so kp baka so.Dan haka Mu koyi rungumar kaddara a rayuwa mai dad'i ko akasinta Mu kai zuciya nesa.*ALLAH KA SHIRYA MANA ZUKATAN MU AMEEN.
Al'ameen sabuwar rayuwa mai tsabta suke shida Ameerar shi da k'yawawan twins d'in su hankali k'wance.
Duk Wanda ya gan shi zai San ya canza daga Al'ameen d'in baya.
Iyayen shi sunfi kowa farinciki saboda kullum said yaje ya gaishe su ga 'yan uwan shisuna zumunci sosai bakaman da sai sunyi kusan shekara basu ganshi a gidajen su ba.
Katafaren Gida Nagani na fad'a ya ginawa iyayen Ameera suka koma, aciki akayi auren Fateema,ta samu miji na gari a can garin gombe ba laifi shima yana da rufin asiri rayuwar suke gwanin sha'awa.
Matan Yayun Al'ameen su duka 3 suka kawo musu ziyara da yaransu suka wuni har dare mazajen su suka zo d'aukansu .
Nan ma suka dasa Sabon hira sannan suka raka su har bakin mota,basu bar wajan ba har saida suka ga tafiyarsu.
Shigowa parlour sukayi tare da twins d'insu da suka k'ara girma da wayo nan suka zube kan kujera Ameera tace..."wash na gaji".
Hararan wasa ya aika mata yana..."gaya min aikin da kikayi harna gajiya"?
Cike da shagwab'a tace" haba Yayana ai wayan nan ma sun isa su gajiyar da mutum" ta k'arasa rana nuna twins da hannu.
"Kuma fa hakane amma kin san me? Ya kamata ace suna dak'ani". Yace yana d'aga mata gira 1.
" kani!!! Haba wallahi saina huta".
"Wani Hutu kuma yara sun kai 3 years?" Yace yana tsare ta da ido.
Cunno baki tayi ta juya mishi bata tana..." Ni kam ban shirya ba".
Dariya yayi yana.." zaki ga shiryawa yarinya".
K'iran twins yayi yace suje wajan Rabi ta basu ice cream su sha.
Da gudu sukayipart d'in masu aiki suna tsallen murna.
Tana ganin haka tasan nufin shi dan haka da gudu ta tashi tayi hanyan part d'inta tana dariya
Shima mara mata bata yayi yana dariya yana "baki isa ba yarinya" kamin ta kai har ya kamo ta ya daga ta sama yana juyi da da ita suna dariya.
*tammat bi hamdullilah*
Alhamdulillah INA mika godiya ga rabbi da ya nuna min karshen novel d'ina lafiya kaman yanda na fara shi lafiya.
Ina godiya gare Ku my fans na yanda kuka rinka bibiyar novel nan tun daga farko har karshen ta.INA mai Baku hakuri akan masu msg both fb and watsapp in kuka ga banyi reply ba toh abinne yafi karfina amma ina son Ku Sani INA kaunar Ku sosai fiye da tunanin saboda in babu Ku babu ni luv u all.
My special thanks goes to big brother *UMAR DALHA*
Godiya da jinjina zuwa ga *SIS NABEELERT* golden pen tana matukar alfahari daku without u guys things seems to b difficult..
Ban manta daku ba yan *GOLDEN PEN* kun amsa sunan Ku golden saboda yanda kuke haskawa a ko INA kun fita daban Allah ya kara baseera da karfin ido.
At d end INA rokon Allah daya nuna mana azumi lafiya tare da wadata Ameeen.