""'Da daddare Mu"azzam nadawowa Ummi ta rufeshi da fadan meyasa yana zaune ciwonsa ya tashi ammh yayi shuru yaki fada,yana jin hakan yasan dalili wani dirty look yayima Lubna domin yasan adalilinta Ummi tasan halin dayake ciki,Ummi tayi ta mai fada daga karshe ta fashamai da kuka ganin yadda take kukane yasa yayi Saurin isa kusa da ita ya rikota yana fadin
"Plz Ummi nah Stop craying..In kina min kuka,tayaya kikeso na samu rahamar Ubangiji ranar gobe kiyama.."yafada yana sharemata hawaye lokaci daya yake fadin"Naji na yarda Lubna tazo ta dubani shikenan..'"Yafada yana matse hannunta.
Dago kanta tayi idanunta na zubar da kwallah tasaka hannunsa dake rike danata tana sharewa hawyen idanunta na kallon idanunsa tace"Why son?meyasa zaka dauki wannan matakin,matakin kashe kanka,kana Tunanin in kamutu saboda zahirah zata jidadi aranta,ko kuwa ya"yanka in suka girma aka basu lbrin mahaifinsu ya kashe kansa saboda mahaifiyarsu kana tsammanin zasu yafemaka?kokuwa ni danake matsayin mahaifiyarka zan gafartama kaina in har ka mutu ta dalilin Tursasawata,kokuwa ita lubna zata dauwama cikin Farincikine indan, muka rasaka,to kagani ka taimakemu son katashi kada katafi ka barmu,ina bukatarka,ya"yanka na bukatar ita kanta Zahirah na bukatarka araye,matarkama tana bukatarka araye,akwai hakkoki dadama dasuke wuyanka suke bukatar ka saukesu..,Don Allah Son kadinga kula da kanka da lafiyanka ba don niba,kodon ya'yanka da matarka don Allah..."tafada tana hada hannuwanta alamar roko.
Kawai Rumgume yayi yana fadin"Rasa zahirah ciwo ne yaki ci yaki cinyewa Ummi na,ammh wlh rasaki Numfashina ne zai dauke gabadaya..I love u so much Ammi na,"Yake fada yana kamkameta,itama kamkameshi take tana fadin"love u Too...My Son."Lubna dake gefe sai da ta share kwallah Iya burgewa Mu"azzam da Ummi suna burgeta hartake ji aranta inama itama inta haihu ta samu da"n dazai mata so tare da tsananin biyayyah irin na Mu"azzam da Ummi.
Dole Mu"azzam badan yaso ba ya kwanta Lubna ta dubasa ta rubuta magunguna da allurai Ummi tabawa Ushe yace wani babban phamarcy ya siyo,tayimai allurai har guda uku masu karfi,su suka taimakamai ya samu hutu sosai,tun da ya kama barci bai farka ba sai washegari da Safe koda ya tashi Ummi da lubna basu nan Karime ke fadamai Ummi tace Suntafi zaria su dawo,magungunar da zai sha da safe da rana duk lubna tabarmai Rubuce,yayi matukar mamaki yadda Tafiyan tatashi ba shiri kuma,ko albri Ummi batamai zencen ba,ganin bawani waje bane sabo,zaria ai gidane yasa ya share batun ya shiga tiolet yayi wanka yazo ya karya kana ya sha mgani Waya ya dauka yayi Taking Excuse wajen aiki,kafin mganin yafara mai aiki nan ya haye kan gado yaja blanket barci mai nauyi ya kwashesa mai cike da Natsuwa.
____________
*BAYAN SATI BIYU*
""Zahirah ce zaune cikin dakinta ta zabga Tagumi tana jin Baruntun da little ita moodu suke mata adaki,domin yaran suna da karkaza da kama jiki har sunfara rarrafe,suna dafa abu su taka,kamar hadin baki,da little tayi abu sai moodu yayi,suna gasa da juna,yanzu haka sunacikin wata na takwas ne,sun ma kusa wata tara,daga gani zasuyi Saurin takawa saboda suna da karambani..
Kallo daya zakamata ka fahimci ta rame,saboda yadda idanunta suka zurma sosai,Tunanin makomar rayuwarta take ammh haryanzu takasa samun mafita,Tuni ta fawwalama Allah dukan Lamarinta ta rumgumi Alhaji amtsayin miji,kamar yadda yagana ta raba musu kwana,hakan ta kasance yana kwana bibbiyu ako wani daki,duka duka ne,Sau biyu ne ranar girkinta ya zagayo Alhaji ya kwana adakinta,ammh yau tsawon kwana goma sha biyu baya shigowa dakinta ranar girkinta,baya cin abinta kuma baya mata mgana,boyewa ganinta ma yakeyi,ko sun hadu afalo sai yayi Saurin shigewa daki ya rufe kofa,ko Abinci tayimai inyadawo kafin ta fito daga daki ya saka Yagana takaimai daki,duk da ba son Alhaji takeyi ba Shariyarsa gareta tamata ciwo,ko Su moodo sai dai ya aiko a karbesu tun abu bai bata mamaki haryakoma yanzu yana bata,intace bata damu ba tayi karya domin har Damuwar ta bayyana afuskarta.
Yau din ta kuduri niyyar mai mgana taji wani laifi ta aikatamai da zafi haka,kuma in Alissafinta daidai ne,yau din ita kedashi,bata wani tsaya bata lokaci ba,ta mike ta sungumi little Ummi dayan hannun ta riko moodu tana nishi saboda yaran ba laifi sunada girma,falo ta fita ta kwalama Zulai kira,bayan ta zo ta mikamata little tace ta goyamata ita zata goya moodu,zasu shiga kichen ne,amsa tayi ta goyamata ita kuma ta goya moodu suka fada kichen Tuwan Shinkafai tayimai miyar zogale,lokacin dasuka kammalla komai ake kiran sallar mangariba,Zulai tabarma Daukan Wammers din zuwa saman Diining,itakuma ta karbi Little ta shiga dasu daki zata yi musu wanka.
Agurguje tayi musu wanka itama tayi,ko shirin nasu agurguje,tayi musu itama ta shirya cikin wata doguwar rigan da mu"azzam ya aikomata dashi,Sallah tayi kafin ta dauki little Ummi ta goya ta riko moodu ahannunta tafito daga dakin dukkansu suna baza kamshi cikin sha"awa..
Abunda tagani ne afalon yasata jan burki ta tsaya,yagana ce Zaune gaban Alhaji sun baje abinci atsakiyar falon sunaci suna dariya Ranta yayi mummunar baci batasan sanda ta karisa cikin falon ba tana fadin"ammh Allah ya hana zalunci baiwar Allah,meye naki namin katsaladan ranar girki na,naga dai ni na girka abu na,ko ba"a jira ni nazo munci tare ba,ajira nazo nabawa mijina Tunda yau hakkina ne.."Tafada tana huci wanda nikaina bansan cewa haka Zahirah take Intayi Fushi ba.
Dawani salon rainin wayau Yagana ta dago tana kallon zahirah kan tasaki wata siririyar dariya tace"Hmm su miji manya,yo ai mijin naki da kansa yakirani ya Umarceni dana zubamai abinci,kuma na tsaya kusa dashi harsai ya koshi,shiyakamata kima wannan tambayan bani ba hajiya.."Tafada da rainin wayau,tuni idanun zahirah suka kawo ruwa cikin bakin ciki ta juya kan Alhaji tana fadin"Alhaji menayi maka,baka cin abincina,kadaina kulani? baka shiga dakina?in wani laifi nayi maka bazaka iya samu na kafadamun na baka hakuri ba.."tafada hawaye suna kwaranyomata.
Alhaji da jikinsa yayi Sanyi ya dago yana kallon zahirah yace"Ko daya Zahirah babu abunda kika tabamin na sabawa duk iya zama dake.."yafada yana kallonta cikin kuka zahirah tace"To menene,ban maka laifi ba,duk meya jawo wulakancin..?tafada tana ratseshi da ido,kallonta yayi kafin yace"Ki koma daki zan zo na sameki muyi mgana.."yafada cikin kulawa.
Yagana ko dariya take kasa kasa daga,gani abun nayimata dadi matuka,zahirah takara gyara tsayuwa tana fadin"wlh babu inda zani sai ka fadamin dalilinka na yankemin wannan danyen hukuncin alhalin kace ban maka komai ba.."Alhaji ya dago yana kallonta yadda ta kafeshi da ido tana kallonsa cikin zubar kwallah,ajiyar zuciya ya sauke kan yace.
'" *SABODA KE BA MATATA BACE YANZU..,YAU KIMANIN KWANA GOMA KENAN KINA CIKIN IDDARKI NE..*
Da wani rawan jiki da firgici,Zahirah ta dafe kirji lokaci daya Tace" Ina..Ci..Ki..n..Idda..Ta ku..ma.. me k..a..Ke...Nu..fi.."? tafada bakinta da muryanta na rawa lokaci daya hawaye na wankemata fuska,kallonta yayi kafin yayi wani mirmishin yake yace"Ma"ana na SAKEKI KWANA GOMA DA SUKA WUCE,SAKI DAYA.."
Saboda razana zahirah batasan sadda ta aza duka gwiwoyinta akasa ba tana fadin"ka sakeni Alhaji,na shiga uku menayi maka..? tafada tana zubar kwallah daidai lokacin da moodu dake hannunta ya subuce ya fadi akasa yana kuka,guda yagana ta saki kafin tace"gaskiya wannan karon kayi abunda ya dace,kama saki tunkan asaka ka,kai gaskiya aiki yayi kyau.."take fada tana shekewa da dariya.
Da kallo Alhaji ya bita yana dan mirmishi domin azahirin gaskiya yafara dawowa hayyacinsa da taimakon Mahaifiyarsa data sanya akemai Saukan qur"ani da Sadaka,dauke idonsa yayi akanta yamaida kan zahirah wacce ke kuka wurjanjan dakyar ya iya bude baki yana fadin"Ki yi hakuri.."dagowa kanta zahirah tayi idanunta sunkada sunyi jawur tana so tayi mgana ammh bakinta yamata nauyi,kawai sai ta yunkura tatashi,ta dauki moodu dake tsandara kuka,itama Tuni little dake bayanta ta fara nata kukan,ta shige daki da gudu tana kuka,tana shiga daga ita har yaran suka zube bisa gado suna kuka,zahirah fadi take"Shikenan nakara zama bazawara akaro na biyu.."take fada ranta na kuna,tasani batason Alhaji ammh sanda ya furta ya saketa sai da komai nata ya tsaya cak,dama haka Abun yake duk takamar mace,da izzarta kalmar saki na matukar girgiza ya"ya mata.
Alhaji baima yagana mgana ba,ya tashi yabi bayan Zahirah da kallo yagana tabishi tana maijin dadi aranta lalle aikin boka yayi,tashi tayi ta shige daki ta dauki wayarta ta kira kawarta zinatu,tana bata lbrin komai,itama ihu ta saka tana fadin"Dole sujema boka godiya domin aikinsa ba irin na sauran bane.."Sunata murna awaya,su azatonsu Asirinsu yaci Alhaji har ya saki zahirah basusan kwanan zencen ba.
Yana shigowa cikin daki zahirah tamike tana mai wani kallo,ajiyar zuciya ya sauke kafin yafara mgana"Zahirah ko alama ban sakeki don na bata miki ba""..To don ka maidani bazawara akaro na biyu ka aikata hakan..."Zahirah ta katseshi da cewa haka,Hannu ya daga mata kafin yace"Ba burina kenan ba zahirah,.."yafada yana juyamata baya kafin yacigaba da cewa"Nasani cewa koda na Aureki bawai don ina sonki bane,na aureki ne,domin kwadayin samun zuru"a daga gareki,kema kuma na san cewa ba sona kikeyi ba,biyayyah ce da kuma hakuri yasa kike zaune dani,na yanke shawaran Sakin ki ne saboda akwai wanda yafinin bukatarki wanda yake chan kwance cikin halin ciwo tunda ya rasaki,kema kuma nasani kullum cikin begenshi kike,domin gangar jikinki kawai ke tare dani ammh hakikanin gaskiya Ruhinki da zuciyarki tana tare dashi.."yafada cikin Raunin murya.
Daskarewa Zahirah tayi tana bin bayan Alhaji da kallo cikin mamaki da zubar hawaye tace"waya fa..da..Maka.."tafada tana rawar murya juyowa yayi yana fadin"kowaye ya fadamin ba sai kin ji ba,zaki rantse min da Allah cewa kullum baki cikin Tunani Tsohon mijinki kuma uban ya"yanki? zaki iya rantse cewa abunda na fada karya ne.."yafada yana kuramata ido.
Ja da baya zahirah tayi tana wani kuka,lokaci daya tana kamkame jiknta take fadin"a..a...."kiyi Shuru kawai Zahirah basai kince komai ba, narigaya dana yanke hukunci Nayi SADAUKARWA..,Zaki zauna anan gidan kici gaba da iddarki har zuwa jini uku,in inada rabon samun zuru"a Atsakani dake,zanyi murna da hakan,in kuma harkika gama jininki uku,ma"ana lokacin kingama iddarki zan maidake gaban iyayyanki,nayi musu godiya bisa hallarcin dasukayi min,kiyi Hakuri Zahirah nayi hakan ne,domin Farincikinki,farincikin kowa naki tare daFarincikin su Little Ummi,Allah yaga zuciyata,ammh inaji ajikina kila ban da rabon ganin kwai na aduniya ne..."yafada lokaci daya hawaye suna kwaranyomai kafin kawai yajuya yafice yana share kwallah.
Yana fita Zahirah takoma bisa gado tafada tana kuka,lokaci daya taja moodu da little ta rumgume tana fadin"Zamu koma gidan Abbanku,zamu koma gidan Abbanku.."take fada tana kuka da dariya lokaci daya hawaye suna zubomata,kamar ko yaran sun sani sai sukayi tsit,suna kallonta kawai,rumgume tayi kamkam tana dariya hade da kuka lokaci daya,Tarasa kukan me takeyi,na mutuwar aurenta ko na murnar ta hallarta ga mu"azzam,tama rasa wani yanayi take ciki,jikinta na rawa ta rarumi wayarta talalubo nombar mahgana tadokamata kira.
Lokacin mahgana na falo tare da bukar suna cin abinci kiran zahirah ya shigo ta daga tana fadin"Zahirah ce,maman yan biyu.."Tafada tana kallon bukar daidai lokacin data dauka,sallama tayi ammh sai zahirah ta katseta da cewa.."Mahgana Alhaji ya sakeni.."Tafada hawaye na ziraromata,saurin mikewa mahgana tayi,hannunta na dafe da kirji tace"Alhaji ya sakeki? mekikayimai Zahirah..? tafada hankalinta tashe goge kwallah zahirah tayi kan tace"Babu abunda nayinai mahgana,da kanshi ya sakeni,sai yau yake fadamin kwana na goma ina cikin idda.."
Dafe kai mahgana tayi tana sallallami,Bukar dake zaune ya mike yana fadin"Ita wa aka saka.?.'Mahgana ta yanke wayar tana fadi asanyaye"Zahirah..."Zaro ido Bukar yayi kafin yace"Shi Alhaji kabirun ya sakarmin ya'.."Yafada yana bayyanar da bacin ransa kai mahgana ta daga tana fadin"eh..,Tama ce yace yau kimanin kwana goma duk tana cikin iddarta ne.."Hulan kansa ya cire yana fadin"Innalillahi wa"inna Alaihirraju"un..."Yake fada yana share zufan dake ketomai,Mahgana ko dakinta takoma farinciki ya isheta tarasa wazata kira tafadamawa bata da nombar Ummi,kawai sai ta kira yagana.
Yagana na zaune tana bama shettima Abinci abaki kiran mahgana ya shigo wayarta hartaji tsoro ta dauka tana fadin"mahgana lafiya kuwa..? naga kira da daddare..? Mahgana na dariya tace"Albishirinki..."Tafada tana dariya,gyara zama yagana tayi tana fadin"Goro fari kal dashi mahgana,domin daga jin dariyarnan taki abun Farinciki ne ya samu.."Da hanzari mahgana tace"kwarai ma kuwa,yanzu zahirah takirani tana fadamin Alhaji dai ya saketa tun kwana goma da suka wuce.."zaro ido yagana tayi tana fadin'Kibari don Allah.."Dariya mahgana ta sakamata tana fadin"wlh Tallahi da gaske nake fada miki.."
Ai yagana batasan sadda ta saki guda ba,tana fadin",Masha Allahu matarmu ta dawo.."take fada harda hawayen murna kashe wayar mahgana tayi aranta tana kara godema Allah dayaba Alhaji ikon sakin zahirah hankali kwance batare da an kaucema hanya ba.
Shettima dake zaune yabi yagana da kallo kafin yayi mgana ta rigashi da cewa"Allah yayi da rabon zama tsakanin masoyan guda biyu,mijin zahirah ne ya saketa,tun kwana goma dayawuce,kaga kenan ma yanzu haka tana cikin iddarta ne.."Tafada tana bayyanar da murnanta,Washe baki Shettima yayi yana fadin"Alhamdulillah..Allah yasa karshen wahalarsu kenan.."yafada yana jinjina kai.
Yagana ta amsa da Amin daidai lokacin datake kiran Ummi a waya,takira ta shiga ammh har ta yanke ba"a daga ba,sai takara kira,Lubna dake bedroom din Ummi tana shiryamata kaya awardrope taji wayar Ummi na ringing ta dauko ta kawomata kafin ta sauko kasa wayar ta yanke,Tamikama Ummi wayar kenan kiran ya sake shigowa Lubna tace"Yauwa gashi Ummi ana kiranki.."
Ummi dake zaune Afalo ta amsan wayan tana kallon Screen din wayar take fadin"Mutan maiduguri ne,Yagana ce,Allah yasa lafiya.."tafada tana daga kiran daga chan bangaren Yagana tace"Uwar ango akaro na biyu.."Dariya Ummi tayi tana fadin"yagana yau kuma sabon suna na samu,me aka samu ne,naji muryanki tayi chakwai ne,kamar wata yar budurwa yar sha takwas.."Tafada cikin zolaya.
Gyara zama yagana tayi kafin tace"Dole kiji muryata haka,Zamu sake kawo miki zahirah akaro na biyu..'Da hanzari Ummi ta mike tana fadin" Ban...ga..ne..Me..Ki..ke Nu..Fi ba.."?Tafada cikin rawan murya yagana tana dariya tace"Auren ya mutu,yanzu mahgana ke fadamin Zahirah ta kirata take fadamata wai ma kwana goma da sakin nata.."Da wani hanzari Ummi tace"Bani son zolaya yagana,wlh zuciyata zata buga.."da Sauri yagana tace"Wlh da gaske nake Suhaima,Mu"azzam da Zahirah Allah ya dubesu ya sake hallarta musu juna akaro na biyu."
Ai da wani hanzari Ummi ta sulale kasa tana yima Allah Sujudda ta dade tana kwararo godiya ga Allah kafin tadago Fuskarta shabe shabe da hawaye Lubna dake gefe takalli Ummi tace"Ummi,lafiya kuwa daga gama waya kina kuka kuma? da hanzari Ummi ta mike ta rumgume Lubna tana fadin"Ya saketa Lubna,wlh ya saketa..."Da mamaki lubna ke fadin"Ya saki wa..?
Ummi tace"Zahirah mana.."Ido Lubna ta zaro ta rike Ummi tace"Da gaske Ummi..? batama bari Ummi tayi mgana ba ta saki Ummi ta rumtuma dakin Mu"azzam tana kwalamai kira,shiko yana zaune bisa gado yana aiki bisa system dinsa jin irin kiran da lubna kemai da karfi ne yasashi saurin durowa daga gadon hankalinsa tashe Daidai ta shigo sukaci karo da juna.
Cikin hanzari yace mata"Ke lafiyanki kuwa..?"Haki takama kafin tace tana dariya'"An saketa..."Harara ya zabgamata kan yace"ke natsu an saki wa kuma,yanzu daddare nan..?"yafada yana jijjiga kafadunta.,Hannunsa ta riko tana fadin"Zahirah aka saka yanzu aka kira Ummi ana fadamata daga maiduguri.."Zaro ido yayi yana kallonta kafin ya damki kafadunta da karfi yana fadin"wai wasa ko gaske..? yafada yana neman Fita daga hayyacinsa.
Lubna na dariya tace"Wlh da gaske ya mu"azzam Zahirah ta sake zama naka akaro na biyu.."Ai batama karisa ba ya sabeta ya fara juyawa da ita, acikin dakin yana dariya gefe daya kuma hawaye yake,Lubna tana kallonsa tana dariya hawaye na zubomata,sai da yagaji da kansa ya sauketa kafin ya Rumgumeta kamkam yana fadin"Tanque So much..Tanque Lubna Tanque for been their for me..'yake fada yana hawaye.
Hannuwanta Lubna tasaka ta rumgumesa back bayan ta kwantar da kanta abayansa hawaye suna kwaranyomata,lalle Tayi gaskiya data hasaso dawowar Zahirah Rayuwar Mu"azzam ne kadai zai sa tasamu mtsayin Kallo mai daraja A idanun Mu"azzam,Hawayen tsausayin kanta suka cigaba da zubomata lokaci daya tana kara kamkame Mu"azzam din.
_Zakujini Shuru Cuz ina Katsina na tafi biki,buh in,na samu lokaci zaku jini..,One Luv#Janaf fans#_
*Kakata wacce tahaifi mamata hadiza,Bata da lafiya har anyi addmitting dinta a hospt,plz include her in ur Prayers*
*Comment,share and vote.*
*Janafty*
*UWAR MIJINA...!*
_(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)_
*Mallakar:JANAF*
*Wattpad:Janafnancy12*
*Dedicated to my blood Sisters JANAF*
*GIFT TO:Hussain80k*
*Intelligent writer's Asso*✏
_*Today D Whole Chapter Is Dedicated to u,my Childhood Best Friend, FADILAT FALALU MASKA,D BRIDE💑,May Allah(SWA)Albarkate ur Marriage Wit full happiness,Baraka,taqwa,love and Childreen..,HML*_💑💕💓❣💝💞🌹😘
*NOT EDITED*💥
*NO 41*
"""Sundade Rumgume da juna kafin Mu"azzam yarabata da jikinsa ya dagota yana kallonta,itama shi take kallo cikin wani yanayi na shauki da soyayya ta har abada,Mu"azzam kwayan idon Lubna yake kallo,yana ganin tsantsan soyayyaarsa,Lumshe ido tayi hawaye suka kwaranyo ta gashin idonta.
Tattausan Hannunsa Mu"azzam ya sanya yana Sharemata hawaye yana fadin"Stop crayiing kinji yanzu ba lokacin Kuka bane.."Ya fada yana sakin mata mirmishi jin abunda yafadane yasata Saka hannu ta karasa share hawayen da suka zubomata tana dan mirmishi itama tana gyada mai kai,Sakin hannunta yayi yana fadin"Ina Ummi na..?
'"Tana Chan Falo.."Tabashi amsa ,bai tsaya wani mgana ya wuce ya fice daga dakin Fuskarsa da jikinsa suna muna tsananin Farincikin dayake ciki da kallo ta bisa kafin tazame bisa gado tana share hawayen daya zubomata na tsausayin kanta tare da Tunanin makomarta in Zahirah ta dawo tasan cewa matukar Zahirah na tare da mu"azzam Wata mace agunshi ba mace bace,saboda baya ganin kowa amtsayin Mace sai ita.
Mu'azzam yana fita ya fito Falo yana kwalama Ummi kira,da hanzari ta mike tana dariya ta taroshi,tana fadin"Son.."take Fada tana hawayen Farinciki yana zuwa baiyi wata wata ba itama ya chabeta sama yana juyi da ita yana fadin"Ummi na,zahirahta zata dawo gareni Allah Abun godiya.."yake fada yana juyi da Ummi,dariya Ummi keyi tana shafa kansa cikin Farinciki kafin tace"To Saukeni Son,Kada ka kadani.."take fada tana dariya Sauketa yayi kafin itama yajata ya rumgume cikin Tsananin Farinciki Kamkamesa Tayi tana shafa kansa harzuwa bayanshi tana hawaye mai cike da murna da Farinciki,lalle Rayuwa juyi juyi,wai yau Ummi ce ke kukan Murna saboda Zahirah diyar Fadi zata dawo garesu..Dama Hausawa sunce Abunda yasaka Dariya watarana ba shakka shi zai saka kuka.
Dago da kansa tayi tana sharemai kwallah take fadin"Bari kuka,ango da kuka,to amarya kuma mezatayi? tafada da sigar zolaya shagwabemata yayi yana fadin"Ummi nidai yanzu ba wannan ba,tashi zakiyi muje mu Taho da zahirah don Allah.."Sororo Ummi ke kallonsa kafin tace"bazai yuyu ba Son,don yanzu muka kara mgana da yagana take fadamin Shi mijin yace ta zauna chan tayi idda kafin ya maidata ga mahaifinta,.."zaro ido Mu'azzam yayi yana fadin"What..?haba Ummi in Tazauna Ubansa zatayi masa,nidai wlh da sake bazata zauna chan zanje dakaina na dawo da ita gidan nan adakinta tazauna in tagama idda amaidamana Aurenmu.."yafada Fuskarsa na Chanzawa zuwa bacin rai.
Juyawa kawai Ummi tayi ta isa ga Kujera ta zauna tana fadin"Son kacika rigima,ai kowa yasan Zahirah takace,so karka damu kabarsu suyi yadda sukeso bani so kayi sonkai aciki.."binta yayi shima yaje ya zauna kusa da ita yana fadin"Haba Ummi don Allah karki ce A"a nifa tsoro nakeji kada ya maidata matarsa.."yafada idanunsa na nuna tsoron.
Hannunsa ta riko tana fadin"Nasan manufarka,abunda nakeso dakai kabari aji ta bakin mahafinta,domin ance haryanzu baice komai ba,ammh bana Tunanin bukar zai barta achan tayi iddata,kadai jira muji koma miye sai muje ayi mganar,kaji.."Tafada tana kallonsa,zuramata ido yayi zuciyarsa na gudu kafin ya maida kansa bisa kafadanta yana fadin"Shikenan.."cikin karaya,hannu tasaka tana shafa kansa tana fadin"karka damu Son,i promise u Zahirah takace insha Allahu..gyada mata kai yayi kafin ya gyara kwanciyarsa bisa cinyarta yana wani lumshe ido Farinciki tare da fargabane suka tarunmai waje daya.
Ko Kafin wayewar gari duk wanda yakamata yaji lbrin mutuwar Auren zahirah,Lubna da kanta ta kira su Abbie tana fadamusu,bayyana irin murnan da Abbie yayi bata lokaci ne,Shikanshi mooh yataya mu"azzam Murna saboda dawowar Farincikinsa,shima Shureim Da mu"azzam din kefadamai kin yarda yayi Saida ya dawo gida Hajiya kefadamai yanzu suka gama waya da Ummi take fadamata,baki ya rike yana mamakin wannan al"amarin Lokaci daya Farinciki ya mamayesa Abokinsa zai dawo Mutum kamar da,saboda dawowar Uwar ya"yansa,kuma bugun zuciyarsa.
Ranar mu"azzam dakyar yayi barci saboda murna,salallo kuwa na godiya ga Allah ya jerasu ba adadi,tunkan ma zahirah tadawomai akaro na biyu,itako lubna kwana tayi kukan,kukan Tsausayinta kanta da rayuwarta domin daga Ummi har ya mu"azzam bata ta kanta sukeyi ba,suna ta murna da wannan al"amarin ne,gwara ma Ummi dataji ta Shuru ta leka tana tambayanta ko lafiya? ammh mu"azzam ko nemanta baiyi banda buge bugen waya babu abunda yakeyi ya kasa ya tsare sai Ummi takira Maiduguri taji ya ake ciki shifa,ko yau ne sai yakama hanya,Tun Ummi na ganin Abun wasa harta Fahimci Mu"azzam din da gaske yake,Waya ta dauka takira hajiya tana fadamata rigimar mu"azzam din,dariya kawai hajiya tayi kafin tace abasa wayar,magana tayi mai cikin sanyi da fahimta,tafadamai cewa yanzu ya jira yaji abunda mahaifinta zaice,kuma mganar yadawo da ita nan Abuja ya barta domin bazata yuyuba yadai tsaya iya mganar dawo da ita gaban mahaifinta tayi iddarta,ko Shidin ma kada suyi mgana Sujira suga Abunda Shi bukar din zai zartar.
Dole Mu"azzam ya Sauka daga kan dogin naki,ya bar mganar zuwa maiduguri dauko zahirah,saboda Rudewa ne da murna yakasa ganewa Gaskiyan Abunda Ummi take fadamai,dole ya hakura,ammh shima ya share kafa ya zauna yana jiran tsammanin ammh ji yake kamar yayi Tsuntsu ya ganshi gaban Zahirah,wannan Jiran zai iya sa Zuciyarsa bugawa saboda doki,dama awajen aiki ansan baida lafiya,ai sai ya sake Sabon zama,Ummi sai da takalleshi tayi dariya tana tsokanarsa da Sabon Ango,datace haka sai yabata rai yace"Bawani Sabon ango Ummi bayan kunki dawomin da matata nan..",yake fada yana wani Tura baki kamar yaro dariya takemai Domin Ta lura yau mu"azzam din nata rigimarsa ce tatashi.
_______________
*MAID*
""Bukar kwana yayi aransa abace gari na wayewa baima mahgana mgana ba,ya dauki mota sai gidan Auren zahirah Awaje ya tsaya yakira Alhaji kabirun yace ya fito yana kofar gida,Alhajin baiwani yi mamaki ba,domin yasan za"a Rina,shima jiyan bawani barci yayi ba,jallabiyansa ya zura ya fito haraban gidan,bai ga Motar Bukar din ba,sai ya fita waje,ya gansa jingine jikin motarsa karisawa yayi yana fadin"A!a ya haka Alhaji ka tsaya daga waje,kamar wani bako? Yafada yana mikamasa hannu.
Bukar yace"haba abokina,babu damuwa,nam din ma duk gidane aie."yafada yana mikamasa hannu sukayi musabaha,Damke hannun juna sukayi Suna gaisawa kafin Bukar yace"Gunka nazo Alhaji,.."Alhaji yace"To mu karisa daga ciki Alhaji sai muyi mganaer.."Saurin girgiza kai yayi yana fadin"Basai na shiga ba,nan ma ya wadatar,mganar bawata mai tsawo bace..",yafada kafin yace"Jiya da daddare zahirah takira mai dakina tana fadamata wata mgana data girgizani,wai ka saketa tun ma kwana goma daya wuce,shine nazo naji duk meya jawo wannan Abun Alhaji.."yafada yana kallonsa
Mirmishin karfin hali Alhaji yayi kafin yace"Tabbas hakane,duk abunda tafada gaskiyane,na sauwakemata kwana goma da suka wuce Alhaji."yafada yana son jadaddamai,Kallonsa bukar yayi kan yace"to miye dalili,?wani laifi tayi maka koko ita ta bukaci daka saketa,yanzu na shiga na cimata mutumci.."Saurin girgiza kai Alhaji yayi kafin yace"Ko daya batama san Abunda yafaru ba sai jiya dana fadamata,wlh Alhaji in nace gawani laifi da zahirah ta aikatamin da bayan tarewarta to nayi mata karya,sai dai cikin Rashin sani,ko ajizanci na dan adam.."bukar ya numfasawa yana fadin"To meya sa Ka saketa,kagaji da ita,koko baka sontane,ai da kafadamin Tuntuni da Wlh Tu fari ma ban yarda na auramaka ita ba,indai kasan sakinta zakayi."yafada cikin bacin rai.
Saurin Riko hannunsa yayi yana fadi "Wlh ban Auri zahirah da niyyar na saketa ba,bani da buri illa na zauna da ita har karshen rayuwata,inada babban dalilina na sakinta,nasani inda zata koma,zata samu Farinciki fiye da yadda zata samu agidana,kayi hakuri Alhaji bada gayyah nayi ba,inada dalilina,ammh kuma kayi hakuri kada ka tursasani sai na fadamaka dalilina nayinka."yafada Muryansa ta fara rawa.
Kallonsa kawai Bukar keyi yana jinjina kai,kafin yace",to Shikenan Allah yasa haka shiyafi zama alheri,ammh mgnar zamanta agidanka tayi idda Gaskiya Alhaji ban amince ba,Tafito mutafi gida Tunda Aure ya kare to mekuma za"a jira.."Alhaji kabiru yace"Alhaji badai Fushi kayi ba ko?girgiza kai Bukar yayi kafin yace"Ko daya,kawai naga kyautuwa ne takoma gida tayi iddarta,ada dai na kullace ammh bayanin dakamin wlh ka wanke laifinka awajena."jinjina kai Alhaji yayi kafin yace"Hakane,Kana da gaskiya bari na shiga nayimata mgana.."
. Sake musabaha sukayi, kafin Alhajin yakoma ciki,direct dakin Zahirah ya shiga ya kwankwansa kafin ya tura ya shiga,tana zaune kan sallaya da hijabi ajikinta Little Ummi da moodu suna kwance basu tashi ba,da sallama yashiga dakin,juyowa tayi tana kallonsa kafin ta amsa sallaman tana mikewa,Gaisheshi,tashigayi Shiko ya amsa yana isa kusa dasu little yake fadin"Kai yau Sunsha barci,naga sundade basu tashi ba"amsamai tayi da cewa"eh wlh dayake Jiya basuyi wani barci ba rigima sukayi tayi sai wajen asuba suka kwanta"
Zama yayi gefen gadon yana fadin"Subhannallah..Badai wani abu ke damunsu ba ko? yafada yana kallonsu,kauda kai tayi kafin tace"Babu abunda ke damunsu rigimace sukeji jiyanan.."tafada tana tsaye abayansa,bai waigo ba ya mike yana fadin"ok,kishirya yanzu Abbanki na waje yana jiranki,zaki bishi ki koma gida.."yana gama fadar haka ya fice da Sauri,da kallo tabisa kafin ta daka tsalle tace"wayyo Dadi,dama wlh nagaji da zaman gidan nan"Tafada tana isa wardrope dinta ta hau jido kaya sai da ta kwashe fin rabi,kafin ta barshi haka,takoma tana zubasu cikin akwati,nata dana yaran sai da tacika akwati Biyu kafin tabarshi haka,da hanzari,da Dauki little ta goya kafin ta fito falo tana kwalama zulai kira da hanzari ta fito da hannu ta yafito ta suka shiga daki Moodu ta mikamata tana daukan akwatin guda daya tace"Taimakamin zulai,waje zamu Abbana na jirana.."da mamaki zulai ke bin akwatunan da kallo kafin tace"Anty ina zaki haka.."mirmishi zahirah tayi kafin tace"Gidanmu zan koma zulai Aurena yakare tsakani na da Alhaji"Ido zulai ta zaro kafin tace"wayyo Allah.."Tafada idonta sun ciko da kwallah,dafata zahirah tayi kafin tace,"Kar ki damu zulai,haka Allah ya kaddara zama na,bamai tsawo bane agidanan.."
zulai sai da tashare kwallah domin ta saba da zahirah uba uwa su moodu zatayi kewarsu ita ta daukan mata moodu har waje inda Motar Abban ke jiranta suna fitowa da sauri ya karisa yakarbi moodu hannu zulai yana kallon zahirah wacce ke janye da akwati,booth ya budemata ta saka kafin takoma ta dauko Sauran zata fito kenan taga yagana afalo tana kwasan dariya ta kalleta,batace komai ba tasakai zata fita,sai yagana tace"dama ai na fadamiki bamai Auren mijin yagana,dole ne ko an aura a barmin miji akara gaba.."take fada tana jifanta da wani banzan kallo.
Da baya Zahirah Tadawo tana kallon Yagana kafin tace"Kai ammah naji dadi,ni wlh kin ma taimakeni,domin ko azamin jahiliya banyi kama da kalar wacce zatayi zaman kishi dake ba,nagde miki sosai bisa asirin dakikayi Alhaji ya sakeni dama burina kenan,kinsan Allah aiki yayi kyau,da badon bani na bada aikin nan ba,ai da nabaki kudi kin kara ma mallam din."tafada tana zagbamata harara kafin tayi tsaki tawuce abunta,Da kallon mamaki Yagana tabi zahirah aranta tana fadin dama tana mgana,kada kai tayi tana fadin"koma miye daga baya kenan,aje dai gaba,abi wani Sarkin.."
Tana Zuwa tasanya Dayan akwatin abooth Bukar ya rufe booth tazagaya ta shiga gaba tana kallon Zulai tace"To Zulai nagd Allah kaddara saduwa.."zulai takasa mgana sai kwallah,Bukar ya tada mota suka fara tafiya kafin lokaci daya zahirah taji kwallah na ziraronata tasa hannu ta share kafin tadagama Zulai hannu wacce ke dagamata itama tana share kwallah.
Sai da Suka dau hanya kana Zahirah tadago tana fadin"ina kwana bahna.."kallonta yayi kafin yace"lafiya kalau yahna,kiyi hakuri da jarabawar Ubangiji Abunda Allah ya tsarama bawa bai isa ya kaucemasa ba"yafada cikin tsausayi da soyayyar mai dorewa,moodu ne dake kan cinyarsa yafara kuka,sai ta sanya hannu ta daukeshi tadorasa kan jikinta tana share kwallah tace"A iya tarbiyan daka bani bahna,ka gayamin cewa kaddara da jarabawa Musulmin kwarai ake yawan jarabta dasu,ko ahaka na tsaya zan godema Allah,domin yamin ni"ima,ta haihuwa ya"ya har biyu,ko banjin dadin zaman Aure ba,ina fata agaba in Sun tashi sunji lbrina suji kaina bahna.."tafada tana zubar kwallah
Hawayen Farinciki,ya kwaranyoma bahna bai damu da sharewa ba yace"Hakika ke ya"ce mafi soyuwa awajena,Kankatar shekarunkin sunyi kadan da hangen nesanki,Ina rokon Allah ya cigaba dayima rayuwarki albarka tundaga yanzu har karshen Rayuwarki,kuma inaji ajikina Lokacin Farincikinki damu kanmu yazo,Allah yayi miki albarka"Zahirah na mirmishi tana sharan kwallah take amawa da Amin,haka dai yayi ta mata nasiha har suka iso,sai da mahgana taga zahirah kwatsam Bukar na shigowa da akwatuna tsalle tadaka ta rumgumeta lokaci daya tana sakin guda.
Da kallon mamaki Bahna ya bita kafin yace"ke miye haka,mutuwar auren kikema guda.."dariya mahgana tayi kafin tace"eh wlh,Allah ya rabata da wannan kaddaran gidan,da bakar kishiya mai bakar aniya,sai taci kanta.."da mamaki Bukar yace"To in kina murna ta rabu da nan din,gaba kinsan inda zata"mahgana tace tana riko hannun Zahirah"Ai ba bakon waje bane,Mu"azzamu ne Uban ya"yanta kuma na tabbata kasan abunda yake jira kenan,Ai mu kan muna murna da wannan Sakin.."
Zama bukar yayi yana fadin"Hmm,mata mata Sha"aninku sai dai abarku,yanzu shi Sakin Auren ne,kuke ma murna,kun manta Allah da kanshi ya halarta saki,ammh in akayi sai al"arshin Allah ya girgiza ammh ke dadi kikeji"Yafada yana kallonta,Mahgana tace"hakane ammh wannan Sakin dabam ne.."
zahirah dake gefe ta tura baki tace"Ni fa mahgana babu inda zan koma,Ai ya mu"azzam din yayi aure ya manta dani saboda haka,nima bazan koma ba,Zama zanyi agida na kula da ya"yana.."Tafada tana wani zakuda kafada,baki mahgana ta saki kafin tace"Allah,karya kikye yarinya bazaki iya rayuwa babu Mu"azzam ba,kamar yadda shima bazai iya rayuwa baki ba.."
Mahgana Tabude baki zata karayin mgana,Bukar ya dagamata hannu da fadin"plz mahgana kirabu da ita haka,taje ta tayi wanka,tayima yaran,kibata abinci taji takwanta ta huta,nayi alqawarin bazan kara takuramata ba,abunda ta zaba shi zan bi,koda kuwa na zama har abada ne batayi Aure ba."Da kallo mahgana tabishi na mamaki,dole tayi Shuru ta bakinta saboda yadda bukar ya kauda kai itako Zahirah Dakinta ta fada dauke da little Ummi,moodu na hannunta,dukkansu babu wanda yakara bi takan Mahgana balle maganarta,itama dole ta fice zuwa kichen Ammh matakin da bukar keson Dauka bamai bullewa bane.
_Srry ooo..,Ba yawa,yau dinma, don Typing din na amarsune shiyasa kuka Samu,via wit me Janaf Freeking Fans Luvs u Wujiga wujiga😘Lodi lodi😍mazga mazga💕Bhahoot Bhahoot ya Habibaties_
*Comment,share and vote*
*Janafty*
*UWAR MIJINA...!*
_(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)_
*Mallakar:JANAF*
*Wattpad:Janafnancy12*
*Dedicated to my blood Sisters JANAF*
*GIFT TO:Hussain80k*
*Intelligent writer's Asso*✏
_Dis Page iz Dedicated To u my MOMMA..,HAUWA S ZARIA(mmn Uswan)My mommah Ina matukar Kaunarki har cikin Raina,Zuciyata tana dabbaka alherinki,bakina baya gazawa wajen ambatan kirkin ki,Idanunawa Suna darajaki,gangar jikina tana matukar girmamaki Mommah,Allah nake roko Ya iya miki Abunda kika gaza,bayan ya dafa miki gaba da baya,Ya Allah ya raya miki Zuru"a cikin Tafarkin Addinin musulunci ya karemin ke daga Sharrin mahassada da makiya,Allah yayima Rayauwarki Albarka datamu gabadaya Ameen...,UR DOTA LUVS U MORE MORE UWA TAGARI_😘💕✌🌹
*NOT EDITED*💥
*NO 42*
""Mahgana Abunda zahirah tace da yadda mahaifinta ya goyamata baya,ya tsayamata arai,dakanta ta zuboma Zahirah abinci taje ta dibo Ruwan zafi tazo tayi masu little wanka,zahirah sai dataci takoshi kana tayi wanka tabi lafiyan gado tana barcin data dade batayi Irinshi ba,moodu ne yayi barci,little ko tana hannu Ummi afalo,bukar kuwa tuni yayi wanka ya fice Abunsa.
Mahgana ita takira yakura tana fadamata Abunda zahirah tace,kuma ga yadda bukar yace"Mirmishin gefen baki yakura tayi kafin tace"Ah wasa takeyi mahgana,Zahirah ce tace da bakinta bata komawa gidan mu"azzam din?mahgana Tace"Wlh kuwa,wai ai shima yayi Aurensa ya manta da ita,kuma inajin Tsoron bukar,kan kafiya,in yace eh to hakane bamai sashi ya chanza ra"ayi"tsaki yakura tayi kafin tace"Duk wasa suke,ita zahirah kishi ne ke damunta Shikuma bukar abunda ya Faru ne,yasa bayason kara mata dole,kimanta dasu don Allah,tadai gama iddar tukunnah"dahaka suka rabu da yakura,koda zahirah tatashi daga barci mahgana bata kara mata mgna,Ko bukar din daya dawo,batakara tadamai mganar ba,tabi Shawaran yakura,ta kyalesu har Zahirah tagama iddah,komai ke akwao ayi daga baya.
_______________
*BAYAN KWANA BIYU*
""""Mu"azzam cikin kwanakin jiyake,kamar yayi Tsuntsuwa daga Abuja zuwa maduguri,kullum ya kwanta barci mafarkin Zahirah yake da yaransa,ammh haryanzu Ummi batace komai ba,gaskiya ya gaji yau Tun safe yayima Ummi dirar makiya adakinta ko Tashi batayi ba,Tana cikin bedroom dinta akwance,ya shigo,mikewa zaune tayi tana yaye blanket dinta,lokaci daya take fadin"Son,wht happen naganka ealry in d mrning haka? Kariswa yayi kusa da ita yayi yana hawa bisa cinyarta ya yada kansa yana fadin!"Haba Ummi ,yanzu shikenan sai kiyi banza dani,tun yaushe akayi sakin nan,ammh haryanzu baki kara cemin komai ba.."yafada yana lumshe ido.
Hannu tasanya bisa kansa tana shafawa lokaci daya tana murmusawa kafin tace"Ho,Son kana da rigima Wlh,bana ce kayi hakuri muji ta bakin mahaifinta ba,kuma ko zata dawo gareka basai tagama idda ba,kuma kana sane da Sai ankara daura Muku aure,so Sauri bana ka bane,kaji son.."Tafada tana kai hannunta kan Fuskarsa tana shafawa,runtse ido yayi kafin ya riko hannunta yana fadin"i know Umm,buh i want to see her,Wlh in banganta ba yadda zuciyata keyi mutuwa zanyi.."ido Ummi ta zaro kafin tace,"Mutuwa Son..? tafada cikin Tsoro.
Lumshe ido yayi kafin ya dagamata kai,Wayarta dake kan Side drower ta mika hannu ta jawo tana fadin"Bazan bari saboda son ganin zahirah ka mutu ba Son,insha Allahu Zahirah takace let me Talk to yakura.."Tafada tana kara wayan akunne gyara zaman kansa yayi bisa cinyarta bayan ya kamkame hannunta yana sakin mirmishi,Da sallama yakura tadaga kiran Suna gaisawa,Ummi tace"Amrm yakura nace ba"yakura ta gyara zama tana fadn"Inajinki Suhaima..'Ummi tace,,"kan mganar Zahirah ce,ya ake ciki ne,ga mu"azzam ne wlh ya damu wai Shi sai yazo ya ganta.."yakura tace"Tama kwana gidan Sauki Suhaima yataho kawai,Tunda ma Bukar yaje ya daukota ya maidota gida Tun ranar,Ni banje ba,mahgana ce takirani tana fadamin wai Zahirah tace bata komawa mu"azzam,zama zatayi ta rike ya"yanta,Shikuma bukar yace duk yadda ta zaba,bazai Takura mata ba.."Cikin mamaki Ummi tace"Ita Zahirah tace bazata koma gidan Son ba.."Tafada Tana mamaki.
Dariya yakura tayi kafin tace"Eh wai tace yayi Aure ya manta da ita,kishin danki ne,ke damunta da da zarar yaje Shikenan"Tafada cikin zolaya yar dariya Ummi tayi tana fadin"Umhmm yaran zamani,to Shikenan yataho din babu mtsala"yakura tace"Eh yataho babu mtsala.."da haka sukayi sallama da Ummi daidai lokacin da Mu"azzam ya tashi daga kan ciyar Ummi yana kallonta.
Ijiye wayar tayi,ta zuramai ido kafin tace"Is ok,ka shirya sai Ushe yakai ka chan maidugurin Tunda ka matsa,zaka kwana ne,ko yau zaka dawo.."? Saukowa yayi daga kan gadon yana fadin"Wai Ummi ita zahirah ce,tace bazata koma wuri na ba ko?yafada yana nuna kanshi.
Yar dariya Ummi tayi kafin tace"Eh Tace Tunda kayi Aure,ita bazata dawo ba.."bai kara cewa komai ba,ya juya ya fara tafiya yana fadin"Lalle Zahirah ta raina ni I will deal Wit her.."yafada cikin dakewa,Da kallo Ummi tabishi hannunta bisa habanta tana fadin"kwaji dashi dai,katafi kuje chan ku karata"Tafada taba komawa ta kwanta lokaci daya tana jan blanket.
Da Sassarfa ya sauko daga Saman ya nufi dakinsa yana Shiga Ya iske lubna,kwance bisa gado,gabadaya jikinta na cikin blanket,kanta ne kadai awaje,bai wani tsaya ba ya fada,Tiolet yayo wanka sanda ya fito sanye da rigan wanka kansa karamin Towel yana tsane ruwan kansa dashi,lubna ta bude ido tana kallonsa baibi ta kanta ba,ya isa ga dressing mirrior,ya shafa lotion kafin yayi Cumbing din kansa,Ga wardrope dinsa ya isa ya bude,ya ciro wata Shadda Wagambari, Navy blue,tana yarari tana maiko da kallonta zaka san tabama Dubbai baya,hula ya dauko zannah bukar ya saka bayan ya hau Feshe jikinsa da Turarensa na MAN,Takalminsa yadauko Sau ciki ya sanya yana dagowa suka hada 4eyes da Lubna wacce ke kwance tana kallonsa da duk Abunda yakeyi.
Kuramai ido tayi kafin tadan muskuta tace"yaya,ina zaka da safe haka kaketa Shiri ahanzarce..? yana gyara zaman Hulansa kansa yace"Maiduguri..."zaro ido tayi kafin tace"Wajen wa..? wani banzan kallo ya watsamata kafin yace"wajen wa kike tambayana,? ban tsammaci wannan Tambayan Daga gareki ba,domin kinfi kowa sanin muhimmanci garin awajena.."yafada cikin bacin rai.
Mirmishin dayafi kuka ciwo tayi kafin ta yaye bargon ta sauko tana fadin"Am Srry yaya,wlh bansan sadda tambayan Ta fito min bane,kayi hakuri baran kara ba"Better...."ya fada yana juyamata baya,Bayansa tabi da kallo,kafin ta gyada kai ta share kwallar data zubomata ta dago kenan Suka hada ido da mu"azzam yana kallonta,Saurin Wucewa tayi Tana fadin"Allah kiyaye hanya,ka gaida Antyna da yarana.."tafada cikin sanyin murya"da kallo ya bita lokaci daya yaji Tsausayinta ya tsirgamai Baki ya sa yakirata"Lubna..."yafada yana takowa gabanta.
Cak ta tsaya bayan Ta waigo Shikuma daidai lokacin ya kariso idanunta yakeso ya kallah ammh taki bashi dama,saboda kada kwallar datake tarawa su zubomata,bata son ya Fahimci ta fara gazawa,Hannunta ya Riko duka biyu yana Matsawa kara kiran Sunanta yayi da cewa"Lubna,dago ki kalleni.."ya fada yana kallonta,Dagowa tayi ahankali tana kallonsa,Kuri yayi mata,itako jikinta ne yafara rawa lokaci daya tana jin kamar ta fashe da kuka,hawayen datake boyewane Suka zubo basu Shiryaba,Runtse ido tayi hawayen suka zubo sharr,hannu mu"azzam ya sanya yana sharemata lokaci daya yake fadin"Am Srry..I know wht i did,is hurt u..Banda zabi ne,Kiyi hakuri don Allah.."yafada jikinsa nayin Sanyi,Kara volume din kukanta tayi,Saboda tsausayinta baisan sadda ya jawota jikinsa ba ya rumgumeta,jinta akirjinsa yasata kara lafewa,hannu yasa yaana Shafa bayanta har zuwa kanta yana fadin"Srry kinji bazan kara ba,wlh ba da gangan nake miiki wani abun ba,Zahirah ta riga ta mamaye ko"ina a zuciyata,in har bata dawo rayuwata ba,Rayuwa ta bazata daidai ta ba."ya fada yana shafa kanta.
Dagowa tayi tana kallonsa Lumshe ido yayi kafin ya bude baya taja tana fadin"i know,ammh Don Allah kadaina kokarin Batama zuciyar datake Tsananin Sonka da girmamaka,na yarda ka cigaba da Son zahirah har karshen Rayuwarka,nikuma na cigaba da Sonka har karshen nawa rayuwa,haka kaddarata take.."Tafada hawaye na ziraromata.
Tsam yayi yana kallonta kafin yamika mata hannu takama ,matso da ita yayi yana kallon kwayan idonta yace,"Plz kibar kuka,insha Allahu da zarar Zahirah ta dawo zanyi kokarin kamanta adalci atskaninku,sai dai Abunda na gaza don Allah kiyafemin kada Allah yakamani da laifin take miki hakki.."Sadda kai tayi kasa kafin tadago ta sanya hannu ta share kwallah tace"babu komai Yaya,Ni bazaka taba laifi awajena ba,Ai nina na shiga rayuwarku So,karka damu ina bayanka Allah yasa Antyna ta dawo.."tafada tana sakin mirmishi.
Mirmishi shima yayi yana bata kiss akumatu yana fadin"Tanque my lil Sis u ar d Best,sai na dawo kinji,kuma bani son kukan nan,plz ki bari kada Ummi ta zargi ko nayi miki Wani abu ne.."Sandarewa tayi Tun sanda yabata Sumba abaki,saboda yadda taji abun abazata,bai jira cewarta ba ko Fahimtar halin data Ciki ba,ya fice daga bedroom din Cikin Takun isa,bayansa ta raka da kallo,kafin ta sanya hannu ta shafo inda yayi mata kiss takai bakinta tana shinshinawa kafin Ta rumgume hannu tana fadin"yes zan iya,nasamu cigaba,tunda har zai batamin yakuma bani hakuri,zan cigaba da hakuri nasan watarana nike da riba"Tana gama fadin haka tafada Tiolet ta wanke Fuskarta da hanzari Ta fito da bedroom din tayi falo,nan ta tarar da Mu"azzam afalo Ummi ta rakosa,tare suka rakasa har wajen mota,Ummi na jaddadamai cewa in Sunyi dare su tsaya su kwana,Amsamata yayi da toh,Ushe yaja suka fice daga gidan Suna dagamai hannu,kafin sukoma cikin gida.
__________________
*MAID*
Zaune take afalo Tana kallon tashar Arewa,Ana Shirin Akushi da Rufi,Little da moodu suna ta zagayen Falon da kafarsu bayan su saka hannayensu sun dafa kujera,batabi da kansu ba hankalinta naga kallo,domin gidan babu kowa mahgana batanan Tatafi anguwa ita dasu Alee Bukar kuma bayanan Ya fita wajen aiki,ita kadai aka bari agidan,sanye ta da riga da zani na wani golden less,Rigar Fitted ce ta kamata,Sosai tayi Daurin maryam babangida,gashinta ya fito ta kasa cikin Band dinta.
Bataji Sallamarsa ba sai dai kamshin Turaransa daya cika falo,ko mutuwa tayi ta dawo bazata kasa tantance kamshin yaya mu"azzam ba,Cikin wani yanayi Ta dago kanta karaf ko idanunta sukayi kyakyawn gani Mu"azzam tagani Tsaye a tsakiyar Falon Yana kallonta bayan ya saka duka hannunuwansa cikin aljihun wandonsa ya zubamata duka idanunsa.
Mikewa tayi afirgice Hannunta bisa kirjinta tace"Ya..ya..Mu..az...zam.."Tafada kamar bata yadda da Shidin take gani ba,saboda yadda ya ramemata a ido,sai dai yakara fari da tsawo,kallonta yake yana cije lips dinsa,lokaci daya yafara takowa zuwa gabanta Fuskarsa babu fara"a ko kadan Ja da baya Zahirah ta hauyi tana kallon yadda mu"azzam yawani hade rai Sai da yakaita bango kafin taja ta tsaya kuramata ido yayi yana kallonta,Itama Shi take kallo ammh jikinta na rawa,Hannunsa yasa ya dafa bangon wajen yana kara kusantota har jikinsu na gogan juna,Fuskarsa ya ja zuwa gareta Saurin Runtse ido tayi saboda yadda taji gabanta na fadi Fat...Fat..Fat.
Jira take taji saukan mari,ammh sai mai sai taji Shuru Bude ido tayi tana kallonsa yadda ya kuramata ido lokaci daya idonsa yajanza kala,,tuni jikinta Yayi sanyi takuramai ido hawaye suna taruwa a idanunta,Bai mata mgana ba,sai kallonta kawai yake yana cije baki,Hawayen da zahirah ke Rikewa su suka zubomata,hannunsa na rawa ya saka ya dalle mata baki yana fadin"wannan bakin ne yace bazai koma gida na ba,shine yace baya bukatata alhalin ni ina chan,kullum ina fama da cuta,ko tari nayi sai jini ya zubo,why My hirah,kina so zuciyata ta bugane.."yafada Idanunsa sunyi Raurau,Kuka kawai Zahirah ta fashe dashi tama kasa mgana,kallonta yayi kafin yace"Ni banyi kuka ba,sai kece zaki wani Fashemin da kuka,Allah kimin Shuru ko na matse miki baki yanzu nan."Jin haka yasata karama Volume din kukanta,baiyi wata wata ba,ya rumgumota kam ajikinsa,lokaci daya suka saki ajiyar zuciya,Kamkameta yayi yana Shinshinar wuyanta Cikin wani kasala yace"I miss u .."yafada yana dora kansa bisa kanta wasu zafafan hawaye na ziraromai
Jin hawayensa na diga abayanta ya sata kara kara kamkamesa tana fadin cikin kuka"Mi...ss..U...Tooooo..."tafada tana kara tusa kanta akirjinsa,kamkam suka damke juna tamkar wani zai rabasu,Dukkansu hawayen Farinciki suke na murna sake ganin juna arayuwa,Sun manta da kowa da komai,kawai duniyar ne ke juyawa dasu Saboda farinciki Suna cikin halin Rumgume da juna,Sukaji kukan Little wacce tatako ita zatayi Tafiya sai tafadi ta buga kanta,tako kwala ihu,moodu najin kukanta Shima ya tako sai Shima ya kifa,kukansu ya ruda iyayyan nasu suka saki juna da Sauri kowanne na rige rigen zuwa garesu.
*Comment*
*Share*
*Vote*
*UWAR MIJINA...!*
_(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)_
*Mallakar:JANAF*
*Wattpad:Janafnancy12*
*Dedicated to my blood Sisters JANAF*
*GIFT TO:Hussain80k*
*Intelligent writer's Asso*✏
*NOT EDITED*💥
*NO 43*
"""Shiya samu Nasaran Daukan little Ummi ita kuma ta dauki moodu,atare suka rumgumesu suna lallashinsu lokaci daya suna kallon juna,mirmishi zahirah Ta sakarma mu"azzam shiko ya ballamata harara kamar zai daketa,Kauda kai tayi tana yar dariya kafin ta koma kan kujera ta zauna tana Cigaba da lallashin moodu,ganin sunyi ki yin Shuru yasa mu"azzam takawa zuwa inda Zahirah take yana kallonta yace,"Malama ki bude riga ki basu abincnsu yunwa sukeji.."yafada Yana wani cin mgani.
Dagowa tayi tana kallonsa kafin itama tace"yanzu fa suka gama sha,babu yunwar dasuke ji Faduwar dasukayi ne Rigimarsu tatashi.."Kuramata ido yayi kafin yawani zaro ido yana fadin"ke ina wasa dake ne? yarinyarnan fa wlh kin fara rainani zaki basu kokuwa sai na danneki na basu dakaina.."yafada Yana danne dariyansa,Tura baki tayi tana fadin"to..To agabanka ne zan bude riga,sai dai ka fita waje,ko ka juya baya.."Tafada tana kifkifta ido.
Dariya Taso kwacemai bai san Sadda ya rike baki yana fadin"kaji min yarinya da sanabe,yo Allah na tuba Shi abunda bakison naganin inace ba agabana ya ida girma ba,kinga wlh ki bashi nono yasha ko na saba miki"yafada adole Shi miji kuma babba😂Zahirah tayi nakwa nakwa da Fuska kafin ta zage zif din Rigarta tabaya ta ciro nononta guda daya kamar tayi kuka ta turama Moodu abaki tana fadin"Ai daman kadaina sona,kuma ma haushi na kakeji tunda yanzu kasamu wacce tafini balarabiya niko baka dani.."Tafada hawaye na digomata bisa Fuskarta.
Kuramata ido yayi yana kallon yadda take goge kwallah tana bama Moodu nono,Zama yayi akusa da ita yana kallonta yakasa cemata komai ba,illah kuramata ido dayayi yana kallonta ransa na kuna,Tana gama ba moodu ya mikamata little Shikuma ya rike moodu,sai da tabasu suka koshi kana tamaida rigarta harta gama,tana share kwallah kuma taki kallonsa,suna jikinsa yaran Sukayi barci Shimfidesu yayi kan 3siter,din kujeran dake kallonsu ya mike yazo gabanta ya tsaya yana kallonta kafin yasa baki ya kirata cikin wata irin murya.
"ZAHIRAH...."Yafada Numfashinsa na sama da kasa,jin muryan dayasa yakirata yasata dago kai Tana kallonsa,Idonsa sun kala sunyi jawur ya nuna kansa yana fadin"Tunda kikabar rayuwata,Na tagyara rayuwata ta durkushe,na rasa walwalata,dariyata,Annurina,komai nawa ciki harda aikina,saboda ke na bar mahaifiyata da kasata baki daya,na bar dukiyata da yan"uwa natafi inda bani da kowa nayi rayuwa duk don saboda ke!Saboda ke naki zama lafiya kullum cikin allurai nake da shan magunguna,Saboda ke nakasa kallon Lubna Amtsayim mace awajena,Saboda ke banta kallonta da Sunan soyayyah ba,Saboda ke nadaina barci Saboda son da nake miki naki zama lafiya,adalilin sonki na saka rayuka dadama cikin kunci Saboda ke nashiga gararin rayuwa,Saboda ke na aikata komai,wlh Tallahi,..inda bana sonki Bazaki Auri wani yaketa inda naketaba,kuma nasake marmarin Kusantoki gareni domin sake komawa gonar dawani yayi nomarsa aciki ba,Dabana sonki bazaki taba gani na anan ba...."
Ya fada yana juyamata baya daidai lokacin da wasu zafafan kwallah suka zubomai,Jikin zahirah daya gama yin sanyi ta dukar dakai tana kuka,ta mike tana danne bakinta da hannunta kafin ta durkusa bisa gwiyoyinta kafin Tace"Don Allah ya mu"azzam kayi hakuri nasan nayi kuskuran fadan cewa baka sona,wlh bada gangan bane,nikaina Banson dalilin dayasa nakejin wani zafi ba duk sanda na tuna kana da mata ba.."Tafada ciikin kuka kafin tacigaba da fadin"Wlh duk karyace nake fada,tunda muka rabu,bantaba jin nadaina sonka ko na minti daya ba,na yarda na amince don kai kadai akayi ne,zan koma gidanka akaro na biyu na bautamaka na kuma sakaka farinciki har karshen rayuwata..."Tafada kuka yaci karfinta.
Saurin juyowa yayi yana rikota Lokaci daya ya sakata ajikinsa yana fadin"kibar kuka don Allah my hirah,kukanki daidai yake da barazanar daukewar Numfashina.,na hakura dama ni baki batamin ba am sryy kinji na sakaki kuka.."yafada yana dagota lokaci daya yana sharemata kwallah,Lafewa kawai takarayi tana sakin ajiyar zuciya,sun dade ahaka,Zahirah ce ta tuna da cewa idda takeyi Shiyasa tayi zumbur ta kwace jikinta tana kallonsa shima kallonta yake kafin yace"meya faru?
baya taja kafin tace"Idda nakeyi fa,Haramun ne Kama junan da mukeyi..,"Tafada tana sadda kai ,Tamke Fuska Mu"azzam yayi kafin yace"Jini nawa kika gani..?dagowa tayi tana kallonsa kan tace"Ko daya baizo ba tukunnah.."zaro ido mu"azzam yayi kafin yace"wht?na shiga uku, kardai knje kin sakin mai jiki ya dura miki ciki.."jin haka yasa gaban zahirah faduwa,dagowa tayi lokaci daya idonta ya ciko da kwallah,girgiza kai tayi kafin tace"a"a insha Allahu ma ba haka bane.."
ajiyar zuciya ya Sauke kafin ya koma ya zauna Jingina kansa yayi da cussion din kujeran kafin ya lumshe ido,ganin haka yasata fadawa kichen,Katon tire ta samu ta zubomai fankasau din datayi da safe da miyar ganda,sai lemon kwali,da Ruwan Faro,takawomai Center table din dake tsakar falon ta ja zuwa gabanshi ta ijiye Tana fadin"ga abinci da Ruwa yaya.."bai dago ba,kuma baiyi mata mgana ba,ganin haka yasa takoma kujeran dake kallon nasa ta zauna ta rafka tagumi tana kallonsa,Sai da yagaji da kansa ya dago ya gyara zama ya tsiyaya ruwan ya sha,abincin ma kadan yaci,kuma tundaga sannan bai Kara yimata mgana ba,daga karshe wayarsa ya fito dashi yakira Shureim suna mgana,bayan sun gama dashi ya kira mooh daga Sudan sukayi mgana kafin Suyi sallama.
Mahgana ce ta fara dawowa,Tayi murna da ganin mu"azzam har hakan yakasa boyuwa aranta,ta furtamai tana mai barka da arziki,ya amsamata Shima cikin sakin Fuska da girmamawa,Dawowartane yasa Zahirah komawa daki tayi wanka,tazo ta amshi su little daga hannusa Domin Sun tashi tun dazu,taje tayi musu wanka ta sauya musu kaya,sai gabda mangariba,Kana bukar ya dawo Shima yayi mamakin ganin mu"azzam din ammh sai ya shanye mamakinsa sukayi musabaha bayan sun gaisa,nan yake fadamai Tun safe yazo gidan babu kowa sai Zahirah,Jinjina kai bukar yayi ko Afuska bai nunama Mu"azzam din komai ba,shima baimai wata mgana data dankanci zahirahn ba,dama shikanshi bukar yasan Fade kawai take,ammh ai dukkansu bamai iya gujema dan"uwansa.
Tare sukatafi mallaci Sukayi sallar mangarib da Bukar,suna dawowa Mu"azzam yayi musu sallama ya tafi gidan Baffa shettima,ammh kafin ya tafi sai da ya amshi wayar zahirah ya sakamata sabon layinsa,bayan ya cikata da kudi,suka rabu cikin kewa da son juna,tayi tayi da safe ya dawo kan ya wuce,ammh yaki yacemata bazai dawo ba,saboda kada su shiga hakkin Allah,haramun ne mace na idda ta dinga kebewa dawani namiji,ko yanzu ma dayazo don takamane,shiyasa dole ta hakura ammh Zahirah Harda dan hawayenta tace agaida mata da Ummi da lubna yace zasuji.
Baffa da yakura suka ga mu"azzam da daddare,nan yake shaida musu Tun safe yazo,yana gidansu zahirah,dariya kawai baffa da yakura sukayi basu ce komai ba,Nan gidan ya kwana sai washegari tun safe suka dau hanya,bayan ya cikasu da kudi,dayake tun bayan dawowarsa ya dauki nauyin wani likita dayake zuwa gida duk sati yana duba Baffan,babu laifi jikin da sauki Tunda yanzu ana mai gashin kashi,yanzu yana iya motsa hannuwansa da kafafunsa kuma bakinsa ya bude,jiki dai yayi kyau domin mu"azzam ya saki kudi sosai game da ciwon baffa,bangaren kudi da abinci basu da wata mtsala sukan Domin mu"azzam baya barinsu haka,koda bayanan Shureim yamaye gurbinsa,balle yanzu daya dawo bai gaza ba ko kadan.
Koda yakoma gida Baifadama Ummi komai ba,ammh afuskarshi ta fahimci ya samu kwanciyar hankali,bata tambayeshi ba,shima bai cemata komai ba sakon gaisuwan da zahirah tabashi yafada,dakuma sakon su yakura na agaishesu sosai,washegari kuwa yakoma wajen aiki domin kaso mafi yawa daga cikin damuwarsa ta gushe,yana kiran zahirah ammh sai bayan kwana bibbiyu saboda yaji lafiyarta data yaransa,basa wani dogom hira sai ya yanke,domin bayaso ya zura jiki,domin Shine zai sha wuya.
Kwana ashirin da biyar da Sakin zahirah ammh Shuru bata ga period dinta ba,hankalinta yatashi sosai tana fargaban kada ace ta samu cikin Alhaji da shikenan an gama da ita,tashiga tashin hankali da zullumi sosai saboda tasa abun aranta,Jinin farko baizo mata ba Sai da ta kwana talatin Cif cif kafin ta gansa da yammah,ai data da gansa batasan sadda ta daka tsalle daga bandaki ba tana ihun murna,har sai da mahgana ta shigo tana tambayan lafiya,rumgumeta tayi tana fadin"period dina ne yazo,wayyo na godema Allah"
Rumgumeta mahgana tayi tana fadin"murna banaki bane kedai hardamu Allah mun godemaka da baki samu ciki ba.."Dariya zahirah Tayi kafin mahgana ta fice ta barta da hanzari ta rarumi wayarta ta Kira yaya mu"azzam,shiko lokacin yana falo suna hira da Ummi,lubna na gefe kiran na zahirah ya shigo wayarsa yadaga tunkafin yayi magana ta daka tsalle tana fadin"Albishirinka yaya mu"azzam..."tafada cikin murna gyara zama yayi yana fadin"Makullin mota yar yayi,fadamin naji meya faru ne..,?"dariya tayi kafin tace"Yanzu naga Period dina yazo.."Ware ido yayi kafin yadanyi ihu yana fadin"Yes...Alhamdulillah nagodemaka Allah na sonah.."yafada yana bayyanar da murnansa,ganin yadda Lubna da Ummi suka zuramai ido ya sa ya mike yakama hanyar shashensa yana fadin"ammh Shine kike wannan tsalle,bani so karki ji ciwo kiman Asara.."yafada yana mata dariya.
Bata fuska tayi kamar yana ganinta tace"to kar nayi murna zan dawo wajen my miji,ok wato abunda nayi rashin hankali ne ko"?Saurin cewa yayi"Waneni da cewa gimbiya guda bata da hankali,tabdijam ai ba wanda yakai ki hankali,kinma Fini inaga.."yafada yana danne dariyansa don kartaji jin abunda yace ne,yasa ta tsintsire da dariya harda rike ciki,kansa ya hau shafawa yana fadin"muguwa kawai..."Yafada cikin kasala,gwalo tamai tanamai dariya kafin ta yanke kiran tana cigaba da murnanta saboda ganin zuwan jinin domin ko bakomai ta hango kamshin komawa gidan yaya mu"azzam dinta.
Tana yanke kiran,ya shiga cikin bedroom din ya fada bisa gado yanajin wata kasala na rufeshi,Runtse ido yayi yana shafa habansa,haka kurum in ya tuna da hiransu sai mirmishi ya kwacemai shi kadai ransa fes,domin yanzu Tuni ciwo yakama gabansa Tunda ya samu kwanciyar hankali,Abunda yakema ciwo yadawo mallakinsa,da wannan Tunanin daganan barci ya kwasheshi,ko awajen aikinsu anga cigaba domin walwalrsa ta dawo kamar da,yakoma aiki tukuri,brr mu"azzam ya dawo da Kasaitansa,da izzansa da komai nasa saboda rayuwarsa tafara daidaita,Lubna kuma tana iya bakin kokarinta wajen bashi dukkan kulawa koda bazai godemata,ita ta yarda ta amince haka kaddaranta yake,ita yanzu fatanta zahirah ta dawo kila abubuwa zasuyi sauki.
Zahirah takira Asma"u tana shaida mata dukkan Abunda ya faru,saboda tsausayin Zahirah da Farinciki sai da tayimata kwallah,tabata hakuri tace taso zuwa lokacin da suka kammallah Jarabawa bata samu dama ba,gashi yanzu tana Sokoto Usman dan Fodiyo Universty Tana karanta Medicine,ammh tayi mata alqawarin in lokacin maida auran yayi don Allah ta shaidamata zatazo,sun sha hira sosai kafin suyi sallama,duk da yanzu Asma"u ta lura kawarta ta takara gogewa aharkan rayuwa,duk yar kunyanan da Rashin sakin jiki duk ta ragesu,taji dadin hakan sosai kuma ta kudiri niyyar kara taimakon Zahirahn akaro na biyu.
_______________
""Rayuwa tana tafiya tare da Ababen mamaki,Kowani bawa yana kwana yana tashi da buri ne,aransa Kwanci tashi kuma batabar komai ba,gashi har Yau ne zahirah take kammallah iddanta bayan tayi jini uku,Alhamdulillah duka zukata na cike da Farincikin barin ma Zahirah da mu"azzam ji suke kamar sunyi aikin hajji Saboda yadda suka samu natsuwar zuciya.
Mu"azzam yaso amaida musu Auren a washegari Ammh bukar yabashi hakuri,da cewa yabari sai sati ya zagayo jumma"a bayan an sauko daga sallar jumma"an sai amaida auren,duk da Ransa baiso ba yaji dadin haka saboda yasamu damar gudanar da duk wani Shirye shiryensa,domin Duk abunda basuyi ba a auren farko to wannan karan za"ayi bidi"a sosai domin wanchan karan ba"ayi murna sosai ba.
Shureim da Dr,Abduljabar sukace hakan nada kyau,nan da suka hada musu wata kasaitattaciyar dinner wacce za"a gudanar ranar Asabar da daddare,kuma zasuyi lunching achan bayan an daura aure,itako Ummi da lubna kasaitattaciyar walima suka shirya Suma Ranar asabar din,da safe,Abun ba ba"a cewa komai,domin mooh ma zaizo da shida mom daga Sudan Abbie dai bazai samu daman zuwa ba yace,Hajiya ma da zulaika sun shiryama Abun sosai don wannan karan Ummi ta wasa wukarta zata shiga ta fita domin bayyana murnarta,kayan auren kuwa ita da lubna suka tafi Dubai suka kwana biyu Suka hado Saitin akwatuna guda ashirin da biyu shake da kaya,Sha biyu na Zahirah Sha biyu na Lubna ne,mu"azzam fa yayi barin naira,ita Ummi ita kuma ta hadama Su little nasu akwatin shake da kayan alfarma domin suma ba"ayi musu na suna ba,Itama Zahirah Mu"azzam ya turamata da kudi Dubu dari biyu yace tayi hidimar gabanta,to suma su mahgana dasu ashe sunce baza"a barsu abaya suma sun shirya wata hadaddiyan Sister day dinsu ranar Alhamis,gyara kuwa Zahirah ta zare ba kama hannun yaro,tasha tayi wanka tayi Tsugunne,Ashe da mahgana basu barta ba,sun dage wajen gyarata ciki da bai,Itama kuma tana taimakon kanta da shan kayan Fruit babu wasa domin so take ta zautar da yayan nata abun ba Sauki fa,takowani bangare shirye shirye kawai keta kamkama tako"ina Saboda Abun ya karato.
Ranar laraba,Ummi da hajiya da zulaika da lubna suka kai kayan Akwatina Maiduguri,sunga kara da karramawa da Mutumci wajen yan"uwan Bukar,an manta komai an zama yan"uwa sai wasa ake ana dariya,kayan sunyi domin an bata dukiya,sosai Kamar ba bazawara ba,Domin Shifa mu"azzam yace Shi budurwa zai Aura,basu kwana ba suka juyo gida suma da kayan arziki sosai na kayan toye toye da lashe lashe..Abun sai wanda yagani.
Gabadaya gidan Mu"azzam ya gayyaci kamfani nan na MAKARI tazo ta sauya komai na gidan,hatta su kayan Na"ura saida aka chanza,dakin Zahirah ma komai sabo aka chanzamata tundaga bedroom har zuwa falonta,itako Lubna dakin kusa da zahirah itama aka Zubamata kayan alfarma iri daya dana zahirah sai dai bambamcin colour,Ita zahirah Black and ash ne,sai lubna black and red ne,Ranar alhamis da safe mooh da Mom Suka iso gida ya kaure da murna domin su hajiya tun ranar talata suke,Ummi ta fahimci haryanzu Mu"azzam bai kusanci Lubna ba,yasata itama ta shiga gyarata,domin har ga Allah bazata fifita zahirah akanta ba,itama gyarata tashiga yi domin kallon yarta ta cikinta take mata,su karime ko suma shagalinsu kawai suke da murna zahirah zata dawo akaro na biyu kowani ma"akacin 10th mu"azzam yaba kowannesu domin ya siya Abunda yakeso na biki,suka amsa suna murna tare dasa albarka,su uche ma ba"a barsu abaya ba,suma sunata shirinsu domin kowa fa ya shaida da yallabai yana cikin Farinciki.
Ana gobe Daurin Auren Abokan suka kammallah,Shureim da Dr,Abduljabar,da Mooh da ango mai gayyah mai aiki mu"azzam sun rigaya da sungama tsara komai,Wannan karon Tafiyan mota zasuyi,da yammah suka tashi mota hudu daya Ushe ke tukata empty benz din mu"azzam ne,sai 4matic motar Shureim,sai Corollah sai wata bakar jeep,da direban Shureim din shima ke tukata empty babu kowa aciki suka dauki hanyan maiduguri,basu isa ba sai dare wani kayatattacen Hotel suka kama suka sauka sukayi wanka suka huta kafin su isa gidan baffa shettima suka gaishesa basu samu Yakura ba tana gidansu zahirah,koda suka isa chan sun iske haraban gidan cike da al"ummah an gama Sister day din ba dadewa suka iso,Zahirah na dakinta cikin Shigar dogowar rigar abaya baka an mara rollin da bakin gyalen abayan,An mata make up tayi matukar kyau kamar ba ita ba, hannunta da kafanta yaji kunshi ja da baki yayi kyau sosai,Sai kawarta Asma"u datazo tun jiya daga mkranta wanda Mami ma ta iso yau domin ita ta kirata ta fadamata ba,sai ko gashi tazo domin tace ai zahirah yace awajenta,koda mu"azzam yanemi ganin zahirah Ashe ta hanata Ita da kanta tafita dauke da su little dakai musu tacema mu"azzam yayi hakuri sai gobe bayan Daure Aure zai ga zahirah babu yadda ya iya sai hakuri buh ammh an batamai bajet dinsa wlh,yaso yasa zahirah a ido saboda yadda tunaninta yahanasa sukuni cikin kwanakin nan data kashesa da wani salo in suna waya,wanda karatun Asma"u ne domin kwata kwata yar kunyar nan babu ita wajen zahirah domin yaga alamar wannan dawowar zata ida zauta shi ne gabadaya.
Asma'u ce tayi hidima dasu wajen abinci da abun sha,tana ma mu"azzam tsiya Shureim na tayata shida Dr,Abduljabar mooh ne yace yana bayan dan"uwansa,yana karemai ammh idonsa na kan Asma"un tunda ta shigo falon saboda yadda tatafi dashi,ko"ina tabi yana binta da kallo,tana lura dashi duk sai ta tsargu domin ba karya gayen itama ya tafi da ita basarwa kawai takeyi,goma daidai suka yi sallama Suka koma masauki, bayan Mu"azzam yabata an maidama zahirah su little Ummi yaran da sukafara tafiya da kafafunsu gwanin ban"sha'awa suma sun dau wanka cikin kayan kanti duk inda suka wulga sai an kara waigowa saboda Sha"awa.,.
*RANAR DAURIN AURE*
Rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya,Gashi tarihi yakara maimata kansa,amsallacin kusa da gidan baffa aka kara maida auren zahirah dana mu"azzam bayan asallaci sallar jumma"a dubban mutane suka shaida Daurin Auren nasu kan sadaki naira dubu dari,lakadan ba ajalan ba,Allahu akabar baffa da kanshi yakara yima dansa mu"azzam walicci akaro na biyu ,Awheelchair aka daukosa yazo wajen yakara nemamasa Auren zahirah akaro na biyu,Shikuma wan bukar ya basu shima akaro na biyu,ana gama tabbatar da Daurin Auren Baffa ya shiga share kwallah,wanchan karon bayan daurin Auren yayi kuka mai cike da fargaban,ammh na yau kukane mai cike da farinciki da Annuwasha tare Murna ya cika burinsa ko yau ya bar duniya.
Shiko mu"azzam Rumgume Shureim yayi yana hawayen Farinciki domin ada ya fidda rai da samun zahirah akaro na biyu sai gashi Allah ya sake bashi ita,bayan yakusa fidda rai,Allah sarki Alhaji kabiru yazo Daurin Auren na zahirah,kuma har gaisawa yayi da mu"azzam yana tayasa murna,Domin Bukar da kansa yakirasa yafadamasa maida auren zahirah dazaya gudana,Alhaji kabiru yaji takaichin rashin dacen da bai yi ba na samun Zuru"a daga zahirah ba ammh yabarma,Allah komai,yana tunanin kila baida rabon haihuwa ne aduniya,yagana Kuwa tuni alkadarinta ya fara karyewa domin yanzu Alhaji baya wasa da ibada,inna ma daga chan ta dage dayimai addu"a kuma ta sanya anamai,cikin lokaci yafara dawowa hayyacinsa itakuma yagana bata gane bane,domin baya nunamata komai,ko umarnin data saba bashi baya mata musu binta yake,ahaka lokaci kadai yake jira tagane bata da wayau domin kamar an farkar dashi daga barcin daya kwasheshi.
*Comment,share,and vote*
"Janafty"
*UWAR MIJINA...!*
_(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)_
*Mallakar:JANAF*
*Wattpad:Janafnancy12*
*Dedicated to my blood Sisters JANAF*
*GIFT TO:Hussain80k*
*Intelligent writer's Asso*✏
*NOT EDITED*💥
*NO 44*
"""Daganan wajen Daurin Auren bayan sungama gaggaisawa da mutane,suka dumguma zuwa gidansu zahirah domin daukansu zuwa wajen Lonching din,koda suka zo,tuni amarya ta cakare cikin wani dakakken Codde less,Light brown Colour,ammata dinki ciki da alaku,riga da zani,sai head dintama milk colur haka pos din dake hannunta,da mayafinta takalmin kafanta ma milk colour ne,halfcover ne mai wasu Stones ta sama,su little Ummi kuwa wata gown aka samata fara Kal da ita mai wani baza daga kasa,angyaramata gashinta an rabashu gida biyu,ansa wasu band masu kyau an daure,kafarta itama sanye da wani bakin takalmi itama din cover ne wanda ya hadu har yagaji da haduwa.
Moodu kuwa shima an shiryasa cikin shigan wani riga da wando yan kanti black and white,wandon baki rigar fara,ansaka Tambarin ARMY da babban baki ajiki,yaci ko zanzaro abunshi,shima kan nan ya sha gyara,kafarsa shima sanye da takalmi sawu ciki bakake na fatar damusa,hannunsa harda wani bakin Royal Din agogo mai tsada da yarari,kai Abun fa sai wanda ya gani,in kaga little da moodu saboda sha"awa sai kaji kamar ka sacesu balle zahirah wacce Teema makeup tazo ta fitomata da aininhin Sirrin kyanta sai wanda ya ganta,duk da basuyi anko ba,Asma"u tayi shigar less ne itama Ammh nata riga da Sikat ne dinki halfjamfa ce ta dauketa matuka Sikat din pencil ne yakamata sosai ya fitomata da Suranta da Allah ya badata,Less din nata milk colour ne,shima yana da wasu Stone ajiki suna kyalli suna daukan ido gwanin ban sha"awa,head din kanta brow colour ne,haka Takalmin kafarta itama Halfcover ne,mai kyau dashi tare da pos din dake hannunta harda ita akama kwalliya abunka ga farar mace sai ta haska cikin kayan da kwalliyan gabadaya,su Alee ma sun sha gayunsu cikin Riga da wando abun sai wanda yagani,Su Ashe kuwa anci doguwar riga cikin wani boyel less,an saka gwaggwaro an bazo gashi ta baya,tace bamai barinta abaya dole ta hallarcin wannan wajen,hakama mahgana da Sauran yan"uwa da abokan arzuka suma sun chakare sunce baza"a barsu abaya ba Suma..
Suna isowa suka shiga har cikin gida Suna fadin afito musu da amarya Su wuce da ita,ga ango chan na jiranta amota,Dr.Abduljabar kenan da Shureim suke ke wannan mganar,kin ko basu amarya Ashe kuwa tayi tace sai Sun gama diban mutane kana,dolensu suka fara daukan mutane suna kaisu kayatattacen Hall din daza"ayi Lonching din wanda kenan cikin GRA din,Su Asma"u ne karshen Tafiya ita da zahirah domin ko su Little Ummi da moodu Ashe tatafi dasu,Lokacin da aka sanya Zahirah cikin motan dayake ciki sai da yakusa zaucewa da ganin kyan da zahirah tayi,Shima din yana sanye da Shadda Milk colour aikin jikinta kuma brown colour ne,sai hular kansa ma haka,hatta Rufaffan Takalmin kafanshi ma hakane,sai agogon hannunsa ma na wani fatane Shima brown colour ne,Kallonta kawai yakeyi,itakuma tana mai Fari da ido,hanunta ya riko yana matswa lokaci daya,yana kurama Kunshinta ido yadda ya tsaru kuma ya dace da hannun nata,dayake Shureim da Dr.Abduljabar na gaban motan baya da halin mgana,Asma"u kuwa motar Mooh ta shiga don yana ganinta yajata yace tazo ta shiga motanshi Tunda Tasu zahirah tacika ba waje,to ya zataki balaraba daga sama,ai sai tatafi tana yanga ta fad motar yaja suka bi bayan Su mu"azzam.
Koda sukaje wajen sun iske su Little bakin hall din don dama dasu zasu shiga,mu"azzam na fitowa ya damke hannun zahirah su moodu kuwa suka ruga wajen iyayansu Zahirah ta rikema little hannu ayayinda Mu"azzam ya rikema moodu ammh dayan hannun nasu suna damke juna su Asma"u da mooh suka biyo baya kana,Su Shureim da Dr Abduljabar suka takamusu baya har zuwa cikin hall
Suna Shiga wajen yadau sowa da ihu da tafi lokaci daya wata waka tana tashi ahankali na U ARE MY LIFE.."Sukuma suna taku cikin isa da Shauki hannunsu rike da juna,gefe daya kuma,suna damke da yan"diyansu duk wanda yagansu indan akace ya"yansu ne, sai sunyi mamaki matuka,Abun ya burge kowa fa,sun isa wajen dazasu zauna suka zauna suka sanya ya"yan nasu atsakiya kowanne ya rike hannu daya cikin burgewa,nan da nan waje yadau Sowa,kafin mc ya fito yafara gabatar da Abunda ya tara mutane,nan da nan aka zagaye kowani tebur da abinci bayan anci ansha aka sanya kida mata Suka shiga fili Sunata rawa cikin harda Ashe da mahgana,Su Shureim da Dr Abduljabar suma sun shiga fili sun chase sosai mu"azzam dai ko da akace su taso ki yaki,yakuma hana zahirah tasowa Asma"u ne tazo ta dauki su little ta shiga fili tadan taka rawa mooh ya fito yana mata barin yan dubu na liki,su Shureim namai tsiya suna bazasu basu ba,Saboda shi balarabe ne,dariya kawai yake musu baya mgana saboda murna,sai wajen la"asar aka tashi bayan anyi hotuna da Sauransu,kafin kowa ya watse amaida amarya akafara Shirin Tafiya Abuja da ita don mu"azzam yace yau zasu wuce babu tsayawa,suna dawowa aka shiryamata kayanta da nata dana yaran sai akwatunanta aka fita dasu aka sanya amota,Wanka aka sakata ta sakeyi ta sanya wata atamfa da Farin hijabi kafin akaita wajen bahna dinta,albarka kadai yaketa sakamata domin yace in da zata ba bakonta bane kuma ita ba yarinya bace yanzu ta san Abunda ya kamaceta,Hardashi mu"azzam ya aika yazo ya hadasu yayi musu nasiha,daganan gidan Famfari suka nufa da ita wajen baffa da Yakura suma sukayi musu nasiha tareda fatan alheri,Wannan karon tafiyan babu yakura saboda ba mai kula da da Shettima shiyasa ta zauna Ashe ce da mahgana da wacce Ashe ke bima wa,Wacce suke cema yafindo,Sai mami mahaifiyar Asma"u,Wacce dama da direbanta Tazo shi ya dauketa,Shureim Shiya dauki amarya da yan"uwanta ayayinda Dr.Abduljabar ya dauki Mooh da Asma"u da mu"azzam wadanda Su little ke hannunsa,sun makalemai Ushe,kuma motar daya tuko ta dauko kayan abinci ne na gara,da kayan toye toye na al"ada,shikuma direban Shureim kayan sawan zahirah ya dauko da akwatunanta da kayan bukatuwanta danata dana yara,Sai mami ita kadai ita da direbanta karfe 5:30pm na yammah Suka bar garin suka dau hanyar maiduguri zuwa Abuja..
_________________
Basu isa Abuja ba,sai after 9 na dare kana motocin suka shiga maitama,abakin get din suka tsaya suka fara malamala hon da gudu sani mai gadi yazo ya budemusu motocin suka fara Sulalawa zuwa cikin gidan,Ummi da hajiya da mom sune ke falon sanda motocin suka shigo gidan,Lubna da zulaika ko ciki,suna hira.
Dama Tun tasowarsu Mu"azzam yakira Ummi ya fadamata gasu bisa,hanya shiyasa duk wani abu daza"ayi na tararsu an kammallahshi kama daga kan girke girke zuwa kan kayan lashe baki,suna jin Diran mota suka mike,Ummi dake sanye da wani Ubansu less,Doguwar riga less din daga kallon Farko zaka gane bakaramin dukiya aka mikaba kafin a daukosa ba,Kunnanta da hannuwanta Zinarene, ke kyal kyali yana haskawa,da hanzari suka fice Ummi ce kan gaba,ita ta bude motar da zahirah take ta fito da ita babu kunya Ummi ta rike hanci ta rangada kuda akunnan zahirah aifa sai waje yadau sowa,mahgana da Ashe ma suka soma guda,harda juyawa da rawa,Mu"azzam dayaji Ummi na guda sai dayayi mamaki,dama haka Ummi take,ita ta riko zahirah da kanta harzuwa cikin gida,itakuma hajiya da mom suma ma sauran jama"a sannu da zuwa,haka aka sassauke kaya su karime na jida suna kaiwa cikin gida,gabadaya suka dumguma zuwa falon hardasu mu"azzam din,Wanda yayansa ke makale dashi sunki yarda da kowa sai shi,jin guda daga falo shi ya fito da zulaika da lubna daga saman Ummi itama Lubnan tayi shigarta ta alfarma cikin Shaddart Navy blue,riga da zani tayi kyau sosai abunka da farar mace,da hanzari suka sauko suma masu sannu da zuwa,ita ta kariso ga Ummi tana riko zahirah tana fadin"oyoyo Antyna barka da zuwa..."Zahirah bata amsa ba domin tana cikin mayafi ne,daganan dakinta nada wanda ta barshi aka nufa da ita da kafar dama Ummi ta umarce zahirah ta shiga saiga Ummi har kan makeken gadon zahirah tayima mata masauki tana sakin guda da kanta,su ashe na tayata,lubna ce ta zauna agefenta tana rike da hannuwanta nan da nan Ummi ta fice tabada umarnin kawo kololin abinci kafin kice kwabo ancika gabansu da Nau"ikan Abunci kala kala da drinks suma su mu"azzam an kai musu shashensu Abun sai wanda yagani,Lubna bata nuna kishi ba ko kadan ita ta samo pilet ta zuboma Zahirah sinasir da miyar alayyahu,tazo har kan gado tayaye mayafin nata ta mikamata abincin,zahirah batayi musu ba,ta karba da mirmishi tana fadin"Ta gode.."
Batawani ci dayawaba ta ture Lubna ta dauke bayan ta tsiyayamata ruwa okofi,tasha ta koshi,yanmatan ne kadai a bedroom din Su ashe da mahgana da Sauran suna falo suma Sun baje suna diban arziki,Lubna ce aciki da Zulaika sai zahirah da kawarta Asma"u,maminta tana falo wajen su hajiya Suna hira,Sai da suka kusa raba dare kana kowa ya kwanta saboda gajiyan hanya,zulaika da Lubna dakinta suka koma suka kwana,Su little ko wajen Ummi suka kwana Abunsu suma murna suke kamar sunsan sun dawo gida ne.
Washegari da hadahadar walimar dasu Ummi suka hada aka tashi ko kafin karfe goma tuni an kayata haraban gidan da kujeru farare da tanti,Karfe shadaya na safe aka fara gudanar da walima,Ummi ta gayyaci wata malama takanas daga zaria wato MALAMA SAFIYYA MUHD BA"ARE.,Ita tazo ta dagargaji wa"azin zama da miji da kwatanta adalci awajen maigida,dama ko awajen zama zahirah da Lubna suna sawun gaba hannunsu sarke da juna,hakikanin gaskiya wa"azin ya tsuma musu jiki matuka mussaman ma zahirah wacce taji duk kishin lubnar ya ficemata aka,in tayi duba da yadda bata kishi da ita,duk inda take tana tare da ita,tana nuna mata kauna mai tsanani,haka kurum taji ta burgeta,kuma itama tayi alkawarin taimakama mijinta wajen sauke nauyun dake wuyansa ko ya rabauta ranar gobe kiyama,Sai wajen uku na yammah aka tashi daga walimar bayan anci ansha,kuma anyi rabe raben su karamin alqur"ani da casbaha,da azakar da dabino,dauke cikin wata karamar jaka da"aka rubuta sunanye su Zahirah da mu"azzam din bayan ansaka Cut cee,Childreen SUHAIMA AND MUHMMED MOODU,abun sai wanda yagani,antashi cikin Farinciki da Annushuwa,bayan an cikama malama kayan arziki direbanta ya dauketa suka koma zaria.
Dare nayi aka fara shirin zuwa Dinner,wanda dukkansu matan ne Wato Lubna da zahirah wanda kowacce ta dau ado,kaya iri daya suka sa wani blue din material ne mai Stones fari suka sanya matukar kyau sunyi daya baka daya fara,ba"ayi african Time ba,Karfe 8:00pm aka fara dinner saboda ana so atashi da wuri,Guri ya cika da al"ummah Tundaga kan likitoci da lauyoyi domin kunsan yau ranar tasu ce,wannan karon hatta da Ummi da hajiya ba"a barsu abaya ba,sun hallarci wajen dinner din yan janaf novellah 1,2,hafnan novellah,Uwar mijina fans1,23 Zumunta novellah Taskar littafan hausa Aisha Alto Novels,Taskar marubuta da Sauransu suma sun sha anko sun hallarcin wajen dinner nan,sahibata kuwa barayin abinci ta nufa kowani kala sai taci dakuma ta fakaici indon mutane da diba ta zuba cikin wata burgamar jakarta,😂😛hakama Sisinah Aisha Alto ita tebura ta dinga bi duk wanda ya rage nama,sai tayi sauri ta dauke tana waige waige data ga ba"aganinta sai ta bude wani buhu da tazo dashi ta zuba aciiki...😂😂😜, mu"azzam na tsakiyar matansa,wanda suka sha kyau Suka koshi,anci ansha anyi rawa,kuma anyi barin naira,koda za"a yanka cake,mu"azzam sai da yafara bama Zahirah kana ya juya yabama Lubna,ita kuma Lubna ta yanka tafara bawa zahirah kana ta juya tabama mu"azzam,haka itama Zahirah tayi Tako sha harara wajen Mu"azzam din wanda daga karshe suka bawa ya"yansu dukansu su ukun,Asma"u ko tana tare da Saurayinta wanda yagama sacemata zuciya mooh,suna chan suna zencensu na soyayyay,karfe 11:00pm aka tashi daga wajen dinner,kowa yakoma gidansa ya kwanta saboda gajiya yan maidugurima da Wuri Suka kwanta saboda gobe sammako zasuyi na tafiya gida.
Gari na wayewa Su Ashe suka fara shirin komawa gida karfe takwas na safe Ushe ya daukesu zuwa maiduguru cike da kayan alheri daga mu"azzam da Ummi,hajiya da zulaika da shureim ma sha biyu nayi suma suka dau hanya bayan Hajiya tatarasu tana musu nasiha,Su Asma"u ne karshen Tafiya domin maminta tabi zuwa gida,domin sai an kwana biyu kozata koma mkranta,bayan sun karbi nombar juna ita da mooh,wanda ya jaddadamata kafin yakoma sudan zaizo suyi mgana,to haka dai aka rabu cikin kewa Dr.Abduljabar ma aranar yakoma gida,gida ya rage daga Ummi sai mom,sai Lubna da zahirah da mu"azzam da ya"yansu little Ummi da moodu wadanda suka samu sabon waje sai guje guje suke,antafi da cikinsu an dawo dasu da kafarsu Allah kenan..
*Kai yasin nagaji*
janafty