"Kema Hafsat sekinyi hakuri da abubuwa da yawa yanzu, idan kika biyewa zafin bakyason Maheer kece zaki wahala, karki kuskura kiyi tunanin yin zawarci da k'uruciyarki kada kuma ki bari amiki k'wacen miji sabida wlhy ke zaki wahala, k'awarki 'yar duniya ce kuma ta fahimci wani abu yasa take miki hakan, karki bari a fahimci akwai aure tsakaninki da Maheer dan idan Aunty Nasara ta sani yanzu kuna london kece zaki wahala, Anty Nasara yayatace amma koni ina tsoron mugun halinta, wannan ya sanya nace ki rike adu'a da azhkhar, ki kuma hakura da kalmar baso a aranki ki rungumi mijinki, koba komai ke baki san komai ba akan tarayrayar maza ita kishiyraki fa? Meye bata saniba meye bata iyaba? Ki kama kanki ki kama mijinki ki cire wannan zancen na yayi amfani da kud'i wurin aurenmi kinjini ba" D'an turo baki tayi
"Anty Fareedah agabana yake wani kakkama matarshi, yana mak'ale mata amma ni ko oho, su dinga bani wahala sekace jaka shimafa basona yake ba, so kike yace ninake binshi ina zubar da ajina, ko jiya Allah banso nayi abinda kikace ba banaso ne kurun ranki ya b'aci" Dariya Antyn tayi
"Hafsatuwalle kenan, kina bani dariya wlhy ninasan wannan k'unk'unin da kikeyi duk kishine ba komai ba, kina so kina kaiwa kasuwa" Tabare fuskarnnan tayi tamkar suna tare
"Haba mana anty wane irin kishi kuma niba wani kishi wlhy, yanzu fa dazasu wuce konemana beyiba se fitowa nayi babusu a gidan kuma ko waya be nemeniba, ni ai sanda mamana ke sokoto tana auren Baba iro naga raba kwana akeyi ko" Sosai anty Reedah tagano Nancy cike take fam da uban kishi da soyayyar da batama san tanayiba.......murmusawa tayi
"Kece zaki kirashi da kanki kimai shagwab'a akan be nemekiba, da k'afarsa ze dawo, haba mana k'anwata ni rgimar nan dukni akewa alhalin kuma bani nakar zomon ba"
"Ni se anjima anty" Dariya tayi
"To anjima zaki kirani koni na kira"
"Duk yanda akayi anty, nafa gaya miki sun tafi abunsu kuma ke dariya ma kike ni wlhy kowama ya tsaneni, ace wai yaa Maheer yafison islam dani, ya dauke matarsa har yana ce mata wai bayaso ake bata ranta shisa ze dauketa" Rigiman hafsat na baiwa fareeda mamaki, idan ka ganta kamar bazatayi ba
"Kinga kiyi hakuri gaskiya be kyautaba, zanmq yi masa fad'a akan hakan kinji"
"Ni bance amar fad'a ba, kurun dai kice dani be kyautaba shikenan" murmushi ta qarayi.
"Be kyautaba gaskia kiyi hakuri kinji"
"To Anty nagode bye bye" kashe waya fareeda tayi tanata kwasan dariya, k'uruciya masiface kana kishi bakama san kanayi ba Allah shi kyauta.
****************
Be ragewa ummul komai ba gameda yanda sukayi da Alhaj Baba, ya qara da cewar
" Ni nasan Allah dole ya jarabeni da masifu iri iri ummul, seda k'arfin gwiwarki nake nema ki bani, gwarin gwiwa ki kasance tare dani komai rintsi, ina cikin ibtila'in rayuwa, nasha auren mace in kuma barta da wasu k'artin banzan suna yanda sukaso da ita, abun yana masifar damuna sosai yanzu, gashi kema anaso a tattab'amun ke, wlhy tallahi ummul zan iya kashe duk wani namiji daze tab'amun iyalina, bama keba babu mace koba matata ba dazan zura ido ayi fasikanci da ita, nasan halin Alhaj Baba idan yayi niyyan yin abu, kuma nasan kema kinajin tsoro sabida haka tunda kunada en uwa Niger inaso ki koma cen keda Naja da Ummami" tausayi ya bata ta shafi kanshi
"Zan koma duk inda kace mijina, ina fatan zaka kula da kanka, kuma kana yawan yin istigfari dan Allah, kasan Allah yana yafewa bawa zunubinsa komai girmansa indai ya tuba ya dena gaba d'aya" Rungumarta yayi
"Zannayi Ummul inshaa Allah, karki damu kedai kawai ku kularmun da kanki......Had'e bakinsa da nata yayi, basu suka sararawa junaba seda suka tabbatar sun gama gamsar da junansu sosai da sosai, sannan suka wanka atare suka kwanta, dama a guess house na gidan su Ummul yake kwana tun zuwansu...
Du Baba iro badu musantawa Ameen ba, se adu'a da duka masa, seda ya cika mata acc nata da kudi masu yawan gaske sannan da kanshi yakaisu Niger gun mahaifiyar Hafsat, kwanansa bakwai tare dasu sannan ya juyo ya d'auri anniyar yin yak'i da Alhaj Baba koda ze rasa ransa ne wurin yak'in neman enci.....
***********
Yau dai kosu Sophie sun gano yanda Hafsat ke k'unci tun tafiyar su Islam da yaa maheer, ko magana ka mata se fad'a se tsokanar ta suke suna k'ara tunzurar da ita akan sun kasa gane kuncin me takeyi, har kuka seda tayi ta rasa dalilin kukanta....su islam kuwa anacen ana iyayi a sabon gida, an kasa an kuma tsare se shagwab'a ake mannawa Maheer shi kuma ya biye mata se yanda tayi dashi, ta mantardashi duk wata damuwa se soyewa sukeyi, gata da ciki watanni bakwai amma se jarabar tsiya, shi har mamaki take bashi wasu lokutan..... Yau tunda sukazo ko skul batajeba se soyayya aketayi dukta gama tatsewa Maheer ruwan jikinsa, yayi lagwaf, bacci yayi se magrib yanayin sallah sukaci abinci sukayi isha se suka kara adana kansu acikin lallausan duvet bacci ne me nauyi yayi awon gaba dasu basu suka farka ba se asuba, anan ake rigimar kuwa cox a b'angaren Hafsat kwana tayi tana zuba uban kuka babu k'akk'autawa, shikenan ita an aureta an mayar da ita banza, an hanata auren Mahal sannan kuma anzo ana cutar da ita wlhy zata rama ne, Anty Fareedah ma wayau take mata tafison d'an uwanta akanta, ta mayar da ita jaka banza anzo duk anbi an tsaneta, meye amfanin wannan auren? Tayi bakin ciki sosai, kan daga bisani ta baiwa kanta magana akan tahak'ura kurun.
************
Maheer bashi yazo gidan ba se bayan kwana biyu, gaba d'aya islam ta hanashi fita ko company bejeba so biyu yana cancelling meeting nashi, Allah ne shaidarsa Nancy tana cikin ransa, har kunyan ganinta yakeji, Da sallamar sa ya shiga gidan, suna zaune susu uku, ko wacce sanye da riga iya cinya suna shan fresh milk, dukkansu wasanninsu suke suna raha amma banda Hafsat tayi shiru tana dannan wayanta, da Ummul take chat, su sophie atare suka had'a baki wurin gayar da maheer amma sam Nancy ko d'ago kanta batayi ba bare ya saka ran zata gayar dashi, ganin haka ya sanya yace dasu
"Ku barni da Nanuwa, zamuyi magana ne" Mik'ewa sukayi amma sophie sarakan gulma ajikin k'ofar d'akinsu ta mak'ale....ko kallon sa batayiba ya zauna kusa da ita ya rik'o hannunta tana zaune akan kujerar ko motsi batayi ba, gashin gemunsa ya sanya a bayan wuyanta yana gogawa a hankali, tsikan jikin ta ya miqe, lokaci d'aya taji saukar wata muguwar kasala lumshe idanta tayi ta bud'esu a hankali, d'ayan hannunshi ya sanya ya shafi k'irjinta zuwa wuyanta, sannan ya d'ago fuskarta suka fuskanci juna, Idanuwan su suka gauraya dana juna, idanta harya soma ja yana shirin kawo ruwa, mekenan batada zarafin ramawa ? Meke sanyata kasala? Mesa bata iya yi masa rashin m, mesa yazo mata ta wannan sigar dabazata iya hanawa ba, suna kallon juna kowa da abinda yake sak'awa a ranshi yace Nanuwa lagonki kenan, kina cika bakine kurun amma kinfi kowa bukatana......muryanshi kaman baya iya magana yace
"Kiyi hakuri Nanuwa, zazzab'i nake tunda mukaje cen, ko nemana bakiyi ba, kema kinsan bayanda zanyi in kasa koda kiranki ina lapiya, kyau ace ai kinemeni da kanki" har yanzu cikin idanshi take kallo ta kasa gaskata zancen sa takuma kasa k'arya tashi, shikuwa bakinta ya d'auke masa hankali kasa hakuri yayi seda ya manna bakinsa da nata wuri d'aya, ta kasa katab'us batada k'arfin hanasa, bazatace tana manta wancen ranar ba, harshenta ya lalubo ya soma tsotsa a hankali, har yana mata wani numfarfashi wanda shine yake k'ara kashe mata jiki, yanayin qshin da numfashin ke fitarwa yana k'ara kasheta gaba d'aya batada yanda zatayi daya wuce ta rike masa waist d'inshi sabida tasoma kasa iya rik'e kanta, janye bakinta tasoma k'ok'arin yi amma ya hanata, sake harshen yayi ya sanya nashi harshen ya lashi lips nata, ya dawo ya sumbaci wuyanta, saketa yayi suka k'ara manna idanuwansu acikin na juna, sam bata iya d'auke idanta a nasa, k'wallan idanta ya sakko tace dashi da k'yar
"Ka dena kallona dan Allah" murmushi yayi
"Kema ki dena kallona" yau kawai ta d'auke idanta a nashi da k'yar, amma ta kasa nutsuwa ji take idan yana kallonta tamkar yana jona musu wani magnet ne da dole seta kalleshi, d'ago idanta ta k'arayi a hankali ta gauraya a nasa, har yanzu ita yake kallo, kanta ya janyo ya sanya harshe ya lashe mata wannan hawayen dake ambaliya a idanta,ya k'ara manna bakinsa a nata, kuka tasoma yi masa yanzu kam, abinda bata saniba wannan kukan ne yake jinshi wani irin daya sanya ya kasa d'auke bakinsa anata ya soma shafa cinyar ta, da k'yar ta kwace idan nan dukya sauya tace
"Kayi hakuri karfa ka manta su safiyya suna nan fa" Dafe kanshi yayi ya saisaita nutsuwar sa, besan yanda za'ayi ya yadena kai hannunshi jikinta ba, bashi bane yake wannan shaukin akanta, gangar jikinsa ne ke masa izgilan cin nan, harga Allah yashiga tsoron yanayin zamansa da islam, kiss kurun dayawa Nancy ranar idan yana tarawa da islam seya sanyo tunaninta a zuci tukunna yake samun gamsuwa
"Kiyi hakuri bankiraki ko a wayaba, bazan k'araba banji dad'i bane shisa kinji" lumshe idanta tae ta qara budesu akansa kasala ya dirar mata, batasan meye feelings ba Allah be d'oro mata se yanzu
"Babu komai, Allah ya baka lapiya nizan shiga ciki bacci nakeji" D'an yatsanshi ya sanya yana mata yawo a cinya
"Kiyi baccinki asaman jikina Nanuwa kinji" ta kasa koda qwaqwaran motsi se kallonshi kurun datake yanameci gaba da yi mata yawo a cinya!!!! Sophie mamaki ya kamata taje d'aki tanawa sha'awa gulma, aikuwa suka had'a rai sunsan brother su bashida neman mata, shine kenan ya sanya taketa bakin rai, ashe iskanci take koya masa?....
Ya dade tare da ita a parlor sedaga bayane ma yawuce, tana shiga dakin sha'awa tamata kwal, wai ita er iskace zata iskanta musu yayansu kowa yasan shi mutumin kirki ne waye waye...... Tayi kuka tamkar zata mutu amma ta rasa kalmar yi musu magana.......bayanin mema zata musu su fahimceta? Ai babushi wlhy, ga abinda yaja mata nan, wannan muqun muqun ya isheta, zuwa tayi ta kira anty Fareedah ta fayyace mata komai...
Mom Nu'aiym
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
37
"Kinga Sis ki kwantar da hankalinki zan kira sha'awa na musu bayani zuwa anjima kad'an nanda ma 1 hour yanzu inada patient ne" tana kuka tace
."To anty nagode sosai" tanata faman kukanta a parlor Sophie tazo ta zasemta ta zauna kusa da ita
"Kiyi hakuri Hafsat banji dad'i bane dana ganki keda yaa Maheer kuna wannan abun, kinsan fa ba kyau kuma Abba yamana nasiha akan tsare mutuncin mu, mesa zakiyi hakan?" D'agowa tayi ta kalleta
"Haba sophie tunda muke dake kin tab'a ganin koda saurayi nayi? Kyau ace yanda muka shak'u da juna kifi kowa sanin halina" langwab'e kai tayi cikeda damuwa
"Kamar miji da mata amma Hafsat, kofa hanashi bakiyi ba kalli yanda kuke kallon juna mesa zaki biye masa?" Ranta a b'ace cikin d'acin murya ta furta
"Amma Sophie idan ma hakanne shi dayake yayanku bazeyi laifi ba seni, shiba d'an iska bane ba, shi bakwa zarginsa da lalatani seni ce zan lalatashi" riqo hannunta fiyya tayi
"To kiyi hakuri, amma kin san bakyau ko? Bedace koda shi ya nemeki ba ki bashi kanki, kinsan fa ko kadan babu kyau irin wannan, dan Allah karki k'ara bari yakai hannunsa jikinki, dama akn wannan ne kurun ya d'auke matar sa" k'ura mata ido tayi
"Kinsan amma yafi zama haramun ka hanawa mijinka kanka ko? Allah yana tsinewa duk macen datake hanawa mijinta kanta alhali yana cikin bukatar ta" Mamakin kalamanta ne ya sanya tayi mintuna kusan biyu bata samu abun cewa ba, da k'yar tace "ban gane ba, toke mujinki ne" wasu yawu ta had'iya kantayi magana ma Shauty ce tafito da gudu ta fad'a jikin Hafsat
"Dan Allah hafsat kiyi hak'uri, wlhy rashin sanine, karki d'auki kalaman mu har zuci, bamusan an d'aura aurenku da yaa maheer ba, dabamuyi wannan haukan ba" kukanta ta tsananta ta rungume shauty basu hanata ba seda tayi ya isheta tukunna ta tsagaita
"Banso ko kad'an ace ko 'yan uwana su gagara shaidan halina ba, nayi tsammanin koda fin haka kuka gani kumun uzuri da magana me dadi, amma se kuka gaggasamun maganganu da zeyi wahala na mantasu da wuri" shauty ce tace
"Dukda bamu kyautaba amma kinsan bazaki hanamu yin dogon zargi akan kuba, kema duk yanda muke dake ace wai ki gagara gaya mana aurenki dayaa maheer " kallonta takeyi kaman bazatayi magana se cen tace
"To Amma shauty Abba ne fa yace karmu fad'a"
"Dukda idan kika fad'a mana wazamu gayawa? Daduk abin bekai ga haka ba" sophie ce ta nemi qarin bayani awurin shauty kai tsaye ta gaya mata tub zuwan yaa Mahii Nigeria aka daura auren, murnarsu ne ya mantar da Nanuwa damuwar datake ciki dole ta hakura suka ware sunada jin dadi, amma ance karsu nunawa yaa Maheer sun sani ko umma karsu gayawa.
***********
Maheer ranar da yamma ya dawo gidan, su Sophie kuwa en iska suna ganinsa suka tsiri zuwa group discussion, be kawo komai a ransa ba, kurin dai suna fita ya rufe gidan da nufin wanawa Hafsat kai, dan ita batasan yazoba, shisa ma dasukace zasuje group discussion tace bazatayi ba ita ba course dinsu daya ba....... Kwance take asaman gadon tayi ashe ashe tanashan iska daga ita se vest da boxers irin na mazan nan, amma vest irin ta matace b'ingilalliya ce me fad'i, cotton bod ne a kunnen ta tana sosa kunnenta a hankali tana lumshe ido, jin anshigo d'akin be sanya ta bud'e idanta ba cox tama zata en shiriritar ne suka dawo, k'amshin turaren datajine ya ankarar da ita, bud'e idanta tayi a hankali ta saukesu akansa, batasan sanda tayi murmushi ba, lokaci d'aya ta miqe zaune
"Sannu yaa Maheer ina wuni" zama yayi kusa da ita abakin gadon ya rik'o hannunta
"Dakin sani dabaki tashi daga wannan kwanciyar da kikayiba, dazaki shekara dubu kwance a hakanan, dana shekara dubu a tsaye ina kallonki" Rausayar da kanta tayi tana murmushi, hannunshi yakai ya shafi mararta seda cikinta ya k'ara lafewa ciki da sauri
"My princes wurinki nazo muyi hira" Kallonshi tayi cikin idonshi shima ita yake kallo, takai hannunta d'aya saman nasa dake kan mararta ta murxa a hankali kantace
"Nagode yaa maheer, me kakeso na kawo maka" kanne idanshi d'aya yayi yace
"Fresh milk zaki bani" murmushi tayi, bata fahimcesa ba
"Babu agidan d'azu muka shanye, sedai ko yoghurt" hannunshi yakai akan dukiyan dukiyan fulaninta
"Ga fresh milk ina gani zakice wai babu, sedai ko idan rowa zakimun" yau kad'ai wata irin kunyarsa ta lullub'e ta, ta dukar da kanta ta gaza furta kalma koda d'aya ce....gogan jikinsa harya soma rawa tunda yake be tab'ajin laushin dukiyar fulani kamar wannan ba.....shi bama wannan ma ji yakeyi tamkar ya mata shigar sauri amma yana tsoron abinda zeje yazo, rungumota yayi gaba d'aya jikinsa yana kyarma
"Princess yau kawai ki barni in huta da jikin kinnan ko yayane, roqon alfarma nake dan Allah badan halina ba" hannunta takai ta shafi sumar kansa sannan tace
"Mesa kake mun irin wannan ne yaa Maheer, kodama cen ni bance dakai jikinka yanada wani shamaki da nawa ba, kaine kake nisantar da kanka daga gareni" Lumshe idanshi yayi, bashida wani taimako daze iya yiwa kanshi, Abba yabashi wani azababben punishment dayake ganin babu me zafinsa a duk fad'in duniyar nan, yana tsananin buk'atar matarsa, ada yana shareta ne sabida babu yanda zeyi yasani idan yaci gaba da kusantar ta wani lokacin seyayi b'arnar daba shiri, idan daddy yaga Hafsat da ciki shi yaya zeyi da ransa? Kuma tabbas baya samun nutsuwa da islam tunda ya k'wallafa ranshi akan hafsat, yana samun cikakkiyar gamsuwa da ita, tana iyakar k'ok'arin ta dukda kasancewar tanada juna biyu, zuciya ce da rai dakeda buri.....
A d'aya b'angaren kuwa,Nanuwa jikinta da zuciyarta duk lugude suke mata, batasan mezeje yazo ba, gashi sam bata shiryawa hakan ba, ta shirya nunawa Maheer cewar ba'awa mutum yanda yayi, kayi amfani da ikon ka ka auri yarinya batare da izinintaba, bazatace batasan k'awarta islam ba, amma ta sani zumuncin su ya tafi kenan har abada....ada tasani taso Maheer amma wlhy yanzu babushi a ranta dasunan so, abubuwan datakeji game dasu ta alak'an tasu akan burgewa kurun, idan kuma ya rab'i jikinta bata iya hanashi wannan b'angaren ma wa'azin anty fareedah take tunawa datace mata duk macen data hana mijinta kanta, Allah da mala'ikunsa sun tsine mata, tsinuwar Allah kuwa yana nufin nesanta daga rahamar sa idan hakane bazakawa kanka tunanin aljanna ba idan ka mutu baka tuba ba tunda yake har Allah yasa ka mutu baka tubaba!!! Ina zataje da wannan nauyin? Da wani tunanin yin ramuwar gayya gwara ka hakura ka fawwalawa Allah lamuranka, watak'ila ma zab'in iyaye zab'ine na Allah....... Saukar hannunshi tajiyo asaman mararta ba zato ta shanye marar ciki har cikinta, d'age rigarta yayi ya sanya hannunsa yaci gaba da shafar wurin a hankali, amaimakon jikin Hafsat ya mutu se jikinsu ya mace a tare suka kwanta saman gadon ya gagara aikata komai agareta, se shafar marar da yakeyi kanshi yana saman k'irjinta....sunyi tsit se numfashi suke saukewa dukkansu a hankali, besan meya kashe masa jiki ba....shafa k'asan cikinta dayakeyi ne ya haifar mata wata k'atotuwar sha'awa dabata tab'a shiga cikin irin yanayin ba, tana kwance batasan sanda hannunta yakai saman kanshi ba, tasoma shafa sumar dabatada yawa tasha gyara se shek'i takeyi, a hankali take yawo da hannunta asaman sumar tana shafawa, a tare suke d'aukar numfashi sukuma sauke a tare a haka dukkansu sukayi bacci batare da shirin yinshi ba, yasha mamakin sanda ya farka yaga anyi isha sunata bacci, cike da kwanciyar hankali take baccin ta, gashi dukta mak'alk'ale masa, sumar kanta har saman k'irjinsa bekosan sanda suka dawo hakan ba.....kwantar da sumar kan nata yayi yaci gaba da shafawa seda ta bud'e idanta a hankali, tamkar a mafarki taga komai, sauke idanta tayi akan dukiyar fulaninta dake waje da sauri taja vest d'inta zuwa k'asa kunya me tsanani ya kamata, murnushi yayi aranshi yace yarinya kin makaro naga komai.
"Ki tashi muyi sallah princess" Mik'ewa tayi zaune seta tsinci kanta dajin nauyin mik'ewa ya ganta da wannan wandon, tasaba zama da ire iren wannan kayan acikin gidan amma wannan yamata guntu, bashida maraba da pant, kallonshi tayi ta sauke kwayar idanta a qasa da sauri...mik'ewa yae ya mik'a mata hannunshi a hankali ta zura nata aciki yajata tamike kai tsaye a k'irjinsa ya mata masauki yana me k'ura mata, yau kawai duk yanda yaso ta kalleshi tak'i, sumba ya manna mata a goshi ya tallafo fuskarta da tafukan hannayenshi
"Hafsat ina sonki kinji?" Murmushi tayi batasan ta furta masa
"Nagode sosai yaa maheer" D'an bata fuska yayi seta kwace jikinta ta juya da sauri ya k'ara rik'ota, hannunsa ya sauka akan mazaunan ta, wani yamutsewa tunanin sa yayi, wannan wane irin laushi yakeji ajikin wannan baiwar Allah jikinsa ne da hannunsa ke neman bashi kunya, yayin da ya k'urawa cikin idanta ido, itama shi take kallo se zare ido takeyi, kaita yayi k'irjinsa gaba d'aya ya rumgumeta tsam ajikinsa....k'wacewa jikinta tayi
"Anyi salla fa, ko magrib bamuyiba" saketa yayi idanshi har yayi ja jajir, ban d'akin ta shige gaba d'aya tayi fitsari tayi alwala tafito. ..baya dakin yabata damar yin sallan ta cikin nutsuwa ta nutse sosai cikin tunanin Maheer indai zasu keb'e seya kai hannunsa jikinta, meke saka jikinsa rawa idan yana tab'a ta? Meye ma ya sanya yake tab'atan tana fatan ba sha'awace ya sanya ya aureta ba, idan ma hakanne zata gwadashi ta gani inshaa Allahu idan sha'awartace baze tab'a cimma burinshi akan taba.
Koda ta idar da sallolin anan yadawo ya sameta
"Tashi muje yawo princess" murmushi ta masa sannan ta mike, tilastata yayi seda ta sanya kaya agabanshi sannan suka fita restaurants.
***************
*Bayan wata Uku*
Har wannan lokacin irin wannan ce ke shiga tsakanin Hafsat da maheer, zezo ya kakkamata suyi wasanninsu amma baze taba kaiwa ko a breast dinta ba, yayi wuta ya laluba da hannunshi, ko tsiraicinta be tab'a buk'atar ganiba, ita kuwa hajiyar cikinta ya tsufa tanama asibiti sabidata wuce EDD d'inta da sati biyu, suna tsammanin yi mata aiki idan bata fara labour ba zuwa gobe....
***************
A b'angaren Ummul kuwa tanacen da cikinta watannj biyar a Niger, batada wata damuwa tana samun kulawa sosai ba er kad'an ba awurin Naja da maman Hafsat, ga Ameen kuma duk k'arshen wata seyazo yamata sati d'aya hotel suke tarewa abinsu.....Alhj Baba kuwa yaci kud'irin cin uban Ameen sabida yaji labarin matarsa tana Niger, lafe masa yayi sabida so yakeyi ya shammmace sa, bedai takai maimai inda take ba amma tabbas an sanar masa cewan taje Niger....
**********
Yauma kamar kullum, da sassafe Maheer yazo duba Hafsat, haka yakeyi da sassafe yake zuwa, a parlor suka had'u, Dama ya sabar mata suna had'uwa zata rungumeshi harda guzurin sumba shima kuma haka, suka Sophie suna parlor d'in kai tsaye wurinta ya nufa ita ma kuma tazo suka rungume juna da kanta ta sumbace sa a kunce tana murmushi tace
"Good morn my charming prince"
"Morn princess how was ur night?" Waigawa tayi ta kalli su Sophie da tunda suka gaidashi suke kallon tv basu ko kulasuba tace
"Bayan jiyan baka sakani bacci ba, to beyi dad'i ba" Mazaunanta yad'an daka
"Kin ganki, to kiyi hak'uri, baby ne tana asibiti bazan iya barinta ita kad'ai ba" kallonshi tayi ta cab'e fuska ta juya d'aki kurin, murmushi yayi yagama dasawa Hafsat soyayyarshi me tsanani ga kishi daya kula tanada shi yanata dariya sanda ya juya yabita d'akin, yajima da sanin kannensa sunsan da auren harya k'ara ja musu kunne akan su kama bakinsu kar islam taji......tana tsaye jikin mirro ta sanya atamfa ja me zanen fari ajiki, tayi kyau sosai, turare take fesawa ya k'araso ya rumgumeta ta bayanta
"Princess menene kuma yau kika barni a tsaye?" Juyowa tayi gaba d'aya ta fuskancesa
"Nazata ka koma wurin jinjirarka ka bata nono tasha" murmushi yayi yauce ranar farko data masa bak'ar magana shima d'in a fakaice
"Bazan k'araba" ya furta yana me marairaicewa" d'auke kanta tayi daga dubanshi
"Me kayi ne?"
"Cewa islam baby agabanki bazan k'araba kiyi hakuri kinji my princess" shiru tayi bata ansa ba, seda ya kara cewa
"Kinji?" Sannan tace
"Ba komai fa, ka fad'a kawai aina saba ji" Be kulataba
"Ina zakije ne?" Kallonshi tayi
"School mana" jinjina kanshi yayi
"Dama nasone muje asibiti dukanmu gun Baby" da sauri ta kalleshi jin ya k'ara ambatar babyn shima dai dukse yaji wani iri amma seya wayance tamkar bece komai ba.....k'walla ne ya taso mata bataso ta bada kanta agabanshi da sauri ta juya zuwa toilet......seda tayi hawayen batasan wane irin kishine da ita ba, wanke fuskar tayi tazo dakin harya fice ta k'ara gyarawa ta fito, suma duka shirya sukawuce asibitin gaba d'aya......labour ne ya tasowa islam amma sune sukayi indusing nata, dayake cen turai har mijinka yana shiga d'akin haihuwa dan haka yana ciki haihuwar ya taso bilhaq amma service yayi thick da yawa, se rirrik'eshi takeyi tana ihu sekace wata arniya shine ma yake mata adu'a, ganin haka ya sanya ya fito bemasan sanda yake hawaye ba, da sauri Hafsat taje gunshi ta lalubo masa hannu ta rungumeshi
"Menene Yaa maher, Babba dakai kake kuka?" D'agowa yayi ya share kwallan dake idanshi
"Hafsat islam fa kaman mutuwa zatayi zatayi, har yanzu fa bata haihu ba" runtse idanta tayi sannan ta bude su a kansa ahankali
"Noo inshaa Allahu lapiya qalau zata haihu, karka damu, kadena kuka kurun adu'a zaka mata kaji" bece komai ba, k'annensa ma sunyi cirko cirko, zaunar dashi tayi ta d'aura masa kansa saman kafad'arta, turai ne ina ruwan wani dasu....hankalinsa atashe yake tsoro yakeji, wannan azabar dayaga islam nasha anya maza sunawa mata adalci kuwa? Ka dinga cutar da mace alhalin itace ke baka dukkanin farin cikin daya dace? Kamar an tsikareshi sekuma ya mik'e zuwa labour room d'in....
Islam tasha wuya daga bisani cikin ikon Allah ta suntulo yarinya me asalin kyau, me matuk'ar kama da ita bako tantama.....murna awurin Maheer ba'a magana se sannu yake mata ansha wuya islam.
Mom Nu'aiym
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
*Assalamu Alaikum...'yan uwa da abokanan arzik'i nagode sosai da adu'anku nasamu sauqi Alhamdulillah...mutanen wattpad yakamata ace kuna yimun uzuri, kusani danku nakeyin rubutu idan har kukaga ban muku posting ba to kuwa halin yine ban samu ba, amma haka dai kurun ana zaune k'alau bazan kasa yi ba ina fatan zaku fahimceni*
38
D'akin hutawa aka mayarda ita, inda Taketa wani iyayi ganin su Nancy
"Honey pls karkamun nisa bakaji yanda bayana yakemun zafi ba sosai" Rik'e hannunta yayi
"Sorry my baby, zakiji sauk'i kinji, zanwa Dr. Magana ma su kula dake da gaggawa, kinyi kokari sannu kinji babyna" murmushi tayi idanta nakan Hafsat, yamutsa fuska ta k'arayi
"Honey kasan me?" Kallonta yayi still hannunsu yana had'e wuri d'aya
"Naso ace Baby boi na haifa me matuk'ar kamanni dakai" girgiza mata kansa yayi
"Noo ki godewa Allah ma daya baki wannan me kamar ke d'in, ni Alhamdulillah dama bana gajiyawa da kallon kyakyawar fuskarki kinga yanzu kin samamun farin ciki, kin haifamun me kamar ke swt hrt, kin haifawa kanki kishiya" Tabare fuska tayi
"Aa ni banason kishiya honey, Allah ya kiyayeni da kishiyar gaske" murmushi kurun yayi
"Yanzu kinsha ruwan sanyi daga haihuwanki, saura tea ko?"
"Noo nina k'oshi" Tabashi amsa tana wani yamutsa fuska
"Bazamuyi haka ba Babyna, ki daure kisha tea d'in ko yaya ne"
"Honey nika sanya amun tuwo, yaushe rabon danaci? Kuma kaga gidansu Nanuwa sun iya miyan me jego da kunun ma, sabida kaga ko mak'otansu aka haihu susukeyi ka sanya tamun mana" yasan da biyu tayi maganar
"Tunda Mamanki tana kan hanya ki hak'ura mana setazo, Hafsat dan anayi a gidansu be zama lallai ta iya ba" Tab'e baki tayi
"Menene amfanin ace setazo? Kenan idanda bazata zoba banida wani gata kenan anan garin, alfarmar daka nema aka wuto da kayan ta kenan yazama abanza"
"Noo ba haka bane Babyna kide bari tazo"
"Allah ni idan ba wannan tuwo da miyan da kunun ba bazanci komai ba in zata shekara bata zoba, so akeyi in lalace mijina ya gujeni anamun bak'in ciki ne kurun" murmushi yayi
"Islam rigima, naji bari muje gidan a had'a komai kinji" Se sannan tayi murmushi..ya kalli Nanuwa
"Ke nanuwa wuce muje na direki a gida sena wuce yin wasu sabgogi kanna dawo ki tabbatar kin had'a mata komai datake buk'ata har kunun" Wani k'ululun bak'in ciki ta had'iya kantace
"To Yaa mahii" ya miyar da dubanshi zuwaga su Sophie
"Ku kularmun da ita kanna dawo kunji" suma dai to sukace kurun basuyi magana ba,shida hafsat suka juya zuwa harabar asibitin suka shiga motar bamewa wani magana...seda ya daidaita kan motar sosai akan titin sannan ya kalleta,tayi wani kici kicin da fuska ta b'ata rai...hannunta ya kama
"Princess yadai,anmun haihuwa ko barka bazakimun ba" Waigowa tayi sukayi ido biyu idan nan yayi jajir kamar zata runtuma ihu haka takeji
"Matar yayana ta haihu ainima 'yatace ko, nima bakamun barka ba" murnushi yayi bece komai ba har suka isa gidan na islam inda ta koma......suna shiga ya rufe k'ofar ya kamota ya rungumeta jikinsa....dama kuka takejin yi wanda ze kama mata kurun take nema ta sanya kukan, lafewa tayi ta saka masa kuka sosai ya gane ta shak'a sosai ya sanya be hanata kukan ba seda yaga tsayuwar bazata haifa musu 'ya me idoba sannan ya d'agata cak zuwa bed room nashi, se a kan gado ya direta sannan ya manna mata kiss a goshi..idanta har lokacin a rufe dukda ta dena zubar da hawaye, Kayan jikinta ya zare mata tas ko motsi batayi ba seda ta dawo iya pant da bra ne ajikinta sannan ya sarara mata, idanta a rufe har lokacin ragewa kanshi nauyi yayi shima yadawo dagashi se boxers ya rungumota acikinsa, wani k'wak'waran numfashi taja ta fesar bazatace bataji saukar wata ni'ima ba, tabbas akwai wani al'amari na daban dan ganeda keb'ewa da mijin ka......tureshi tayi gefe
"Abinda ya kawomu kenan? Abinda kurun kake buk'ata a wurina kenan? Bakada wani abu dakake so a wurina se sha'awa yaa maheer, ni ban cancan ci soba ba matar so bace se zallan sha'awa, bazan barka ka b'atamun rayuwa ba a banza, bazan zura ido ka cutar dani kayiwa Allah wanda ya halicceka karka tara dani seka tabbatar kanka kana sona karka k'ara kusantana seka hak'ik'ancewa zuciyarka sone aranka nawa ba sha'awa ba, idan na hanaka kaina inhau tsinuwar Allah idan kuma na baka kaina alhalin baka sona wlhy na cutar da rayuwata!! Bakada labarin cewa idan ka gama biyan buk'atar ka dani cillar dani zakayi, kasani koba komai nk k'anwar kace mayar dani k'aramar zawara ba daidai bane awurinka!! Ka sauwak'amun aurenka indai har kasan zallan sha'awa nane a ranka" Mik'ewa yayi yana nodding kansa a hankali cikin jimami yace bayan ya matso kusa da ita sosai har suna jiyo bugun zuciyar junansu.....
"HAFSAT sha'awa ni Maheer tawaye? Badai wannan abun ba" yakai hannunsa saman dukiyar fulaninta, zagaye ta yae da hannunsa ya b'alle ma b'allin bra d'inta ya zare "Akan me zanyi sha'awar ki? Mata nawa na gani a tsirara ? Basu burgeniba seke zanyi sha'awarki? Sabida wannan abun? Islam batadashi ne? Ko naki yafi nata ne?" Idanshi ya sauke akan kunkurunta ya sanya hannu ya zare d'an kanfan dake jikinta ko motsi batayiba bare ta d'age k'afafuwanta ya zare shi kuma yabar shi anan k'ara matseta yayi kanya zare singlet d'in jikinsa
"Wannan girman kunkurun dakike tak'amar kinadashi be tab'a rud'ar dani ba, nakuma zata ko wannan abun naki yanada wani banbancine da sauran mata dahar zaki bani sha'awar dazan b'atawa kaina lokacin aurenki, ashe duk kanwar ja ce!!! Ban saniba se yanzu dana ganki tsirara! Ke kuma ki kalleni da kyau zaki tabbatar wa kanki cewar ni nakeda abun sha'awa bake ba, kalli k'irar jikina namiki kamada ragon namiji? A halaye nafa kinga alamun soko ne ni? Yanayina fa ya nuna miki irina zeyi sha'awar mace me kalar ki? Bari kiji tunkan adena saka miki wando nake ganin mata, k'asashen duniya babu inda ban zagaba ko karnai k'arya nace d'aif'aikune ban jeba,Naga mata iri iri wanda suka fiki komai! Naga na hutawa naga na aure naga wanda zan iya biyansu inyi amfani dasu in kawar da sha'awata, a london kurun inada dukiyar dazan iya kama hayar dukkanin karuwan garin nan, nida nakeda damar yin hakan duk banyiba sena b'uge dayin auren sha'awa? Sokon ina neni dazan auri mace ko wacce tafiki ma bare ke dan sha'awa, tunda nake ba'a tab'a jifana da muggan kalamai ba irin wannan.....Bakida abinda zanyi sha'awarki dominshi wlhy hafsat kuma ki sani sena banbance miki tsakanin so da sha'awa zan nuna miki banbanci tsakanin auren so dana sha'awa zan nuna miki inda ake aure badan sex ba!" Yakai hannunsa ya damqi nonuwan ta.... Bana bukatar wannan abun na rayu dubuna sun rayu babu, zan nuna miki yanda so ke tafiya batare da sha'awa ba ki fitar mun a d'aki!!! Ya fad'a cikin k'arajin daya firgita duniyar ta......
*******
Gid'imewa tae ta kasa mema zatayi, ta soma tattare jikinta da mayafinta,tsaki yaja yabar dakin...seda tayi kukanta me isanta tukunna ta shirya ta fito...A parlor ta sameshi....muryanta harya disashe tace
"Bansan kan gidanba,me dame zan dafa mata?" Ga mamakinta beyi fushiba
"Dama ke nake jira,na ciro komai,dayije saqon ya iso tun last week muje na tayaki" ta kasa sakin jikinta dashi taji kunyar sa da tunanin data masa dama yanda ta masa magana, taso ma ace fushi ya mata dayafi wannan wayancewar da yayi....Bayanshi tabi sukaje ktchn cikin k'ank'anin lokaci suka kammala tuwon semo miyan wake da ganyr suka kuma dama kunun atare se hira yake mata ta kasa sakin jikinta.
Islam nacen tana shirya k'azafin dazatawa Hfsat akan ta barta da yunwa tak'i ta dawo....kiran Maheer tayi a waya yana d'agawa ta soma kuka
"Haba mana Honey, se yaushe yarinyar zata kammala kaikuma ko oho, baka ma kirata bare kaji kota kammala, kaida ma kakeda yawan sabgogi agabanka yaushe zaka wani bi ka d'auketa ka taho abunka ita tazo a taxi kuma gaskia kamata fad'a idan ta wuce 30 mns bazanci abuncin ba" gyaran murya yae
"Muna hanya" ya bata amsa a tak'aice bataso hakan ba amma babu yanda ta iya da maheer, wani zubun a baud'e yake tafiyar al'amuransa!!!!
*************
Innan salaha ce tazo london abunka ga 'yar k'auye se kalle kalle takeyi, ita d'inma bata tunanin akwai sanda zataga haske matukar hafsat tana london ko rayuwa gidansu Maheer, gani take babu me niyyan hanasu cin duniya se Hafsat, tunda taga yanda hafsa tayi fresh take wani ciccin magani, haushi duk ya isheta, koda aka sallami Islam suka koma gida se wani yatsina take yi, har kitchen ta sameta inda take had'awa islam pepper soup na fish me yaji ta kalleta a wulak'ance tace
"Ke tunda kika shigo rayuwar su islam kin hanawa yarinyata rayuwar aure me dad'i wace iriyar me mugun kwad'ayi ceke da bazaki fita a rayuwar taba wlhy kinji na rantse zan iya kasheki akan farin cikin islam! Da sauri ta d'ago ta kalleta jinta ambaci kalmar kisa bakinta se motsi yake amma ta gagara furta kalma ko d'aya
" mamaki kikeyi ko, ki gwada shiga rayuwar yarinyata ki gani, shekaru aru aru muna cikin talauci Allah ya rufa mana asiri yanzu kizo kina lab'ewa kina lalata da mijin 'yarinya sabida kwad'ayin abun duniya waike ga er iska" Idanta ne ya kwo ruwa ta kasa cewa komai, juyawa tayi tayi hanyar waje, ta bude kofar ta rufota da sauri tana me toshe bakinta da hannunta akan kukan dayazo mata ba shiri da k'arfi!!!! Gidan sama yake tunda haya ne, karo tayi da mutum tana d'agowa sukayi ido biyu dashi, rike mata hannyaenta yayi yana tambayarta dalilin kukanta amma bata ce masa komai ba, Kaita acikin k'irjinsa yayi ya manna adaidai saitin kunnensa ya rad'a mata
"Idan kikace bazaki jajirce ki nuna kema macece ba zakisha wahala, idan kika nunawa tsoho mara tunani kema bakida tunani to akwai tulin matsala, ina kallon su karki zata bana gani, abu d'aya zan gayamiki wlhy zafin mutuwa ne kurun yafiyemun zafin ganin hawayenki, kimun adalci ki zama jaruma kidena nuna gazawarki dan Allah"
D'ago kanta tayi ta kalleshi ido cikin ido kantace
"Yaa Maheer tsoro nakeji wlhy, kasan me Maman islam tace,cewa fa tamun kasheni zatayi" kallonta yaqarayi
"Karkiji tsoro bazata wuce sati biyu anan garin ba, kan nan kuma zamuje yawo ma bazata ganki ba kinji" gyad'a masa kanta tayi amma har lokacin bata bar jikinsa ba...
*************
Tuna ya kira Abban sa akan sunan baby Abban yace ya bashi dama ya sanya wanda yakeso yayi shawara da Umma ma itama haka tace ya sanya wanda yakeso, lastly kuwa da fareedah yayi shawara inda ya sanar mata sunan yarinyar sa Hafsat goyon baya ta basa akan ra'ayinsa kai tsaye kuwa yaje ya sanar da islam sunan baby hafsat!!!!!!!😳😳😳😳
Mom Nu'aiym
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
39
"Kutmar ***** nan kai!! wlhy tallahi baka isaba, kai Maheer kamasan me kake cewa kuwa to ita Hafsat d'in k'anwar uwatace kona ubana dazan gama shan wahalar nak'uda sannan kuma in dawo ina bibiyar kiran 'yata da sunanta" koshingid'a yayi daga zaman dayake da ya lumshe kyawawan idanuwan shi, shisam Maheer becika san hayaniya ba,kamar bazeyi magana ba yace
"Abba ne ya zab'a sunan k'anwar mamarshine ko shima be isaba? Hafsat ita kad'aice me suna hafsat dakika sani a duniya mesane wasu lokutan bakida tunani me kyau? Inamaso na sani tukunna ita Nanuwa meta miki banaso in zamo silar komawar soyayyarku k'iyayya danni tare na ganku cikin so da kuma aminci, bansan dalilin ubangjiji matsarin komai na wurgo dukkan ku biyu a rayuwata ba, amma ki sani bazan lamunci k'iyayya akai naba, idan kina tsoron yau in dawo ince Hafsat nakeso ita zan aura tokuwa ki sani idan hakane tsarin Allah ni,ke ita dunuya ma kaf bamu isa mun hana ba, kuma tunran gini ingaya miki, abu na k'arshe dazan gaya miki, kinyi kuskuren danno Ashar agabana, a kunnen jinjirar yarinyata idan abinda kike shirin koya mata kenan sena k'waceta a hannunki wlhy ki kama kanki...zancen suna kuma wlhy ke d'in nan kinyi k'ad'an ki sauya umarnin ubana, albarkacin aure ya sanya kika tab'a ganinsa ma ido da ido bare kuma kice zaki sab'a umarnin sa, dabadan aureba kinyi kad'an ku had'u dashi wlhy.....wanda be masan mafarin suba ya basu umarni sunbi koba dan sunaso ba bare ni dakuma ke...koda ma ace nid'in ne nakeson sunan na hafsat ke wacece dazaki hanani sanyawa? Har kina kumfar baki kina zabgo Ashar, wannan ya zamar miki na farko nakuma k'arshe dazan fad'a miki karki k'ara koda wasa gigin d'agamun murya idan ina miki magana keba kowa bace dazaki kalleni kina mun ihu aka" mik'ewa yayi a hankali yau 'yan mazan ikon da mulkin sun motsa matsa, halin dabata tab'a sanin yanadashi ba ya motsa masa, tun zamansu dashi batasan halin ba, yaji zafin uwarta akan maganar datawa hafsat akan kisa, dalilan sa biyu ne na baiwa yarinya wannan sunan, na farko dai Hafsat yawa takwara badan gataba sedan Yana matuk'ar san halin 'yar tasa yayi kalan na wacce taci sunanta na biyu kuma yana jin dad'in kiran sunan a bakinsa, be shirya bata wani lak'ani ba se dai kiranta da zallan hafsat d'in ta.......Hanyar waje ya nufa yana takun k'asaita sam sryaji yarinyar ta sire masa, shi zata kalla take gayawa magana hadda danno ashar ita waye? Ko sanda yake k'arami babu me zaginsa wato ma shi take zagi, anya yawa litle hafsat adalci kuwa? Na baiwa islam matsayin zamtowa uwarta? Lumshe idanshi yayi ya k'urawa k'asan ido dayike suna sama, tunani me zurfi yakeyi akan halayen islam tabbas ze taka mata k'atoton burki!!! Baze lamun taba bari ya dawo mata Maheer d'insa na usul sam baze iyaba baze lamunci raini, harshi mace zatawa ihu da zagi, sophie ce tazo ta tsaya kusa dashi
"Yaa Maheer zamuje gidan mu" Waigowa yayi a hankali amma sebe kalleta ya kalli k'asan k'afafun ta
"Mesa?" Ya tambaya,Ta jima bata ganshi cikin irin wannan yanayin ba amma seta cije da tsoratan datayi tace
"Pardon?" Lumshe idanshi yayi
"Mesa zaku tafi?" Dan sosa kanta tayi
"Dama maman Anty islam ne taketa zagin Nanuwa tun d'azu har tana cewa da ita mayya, shine fa taketa kuka tun d'azu to kuma shine yanzu take ce mana kanta yana mata ciwo, shine kurun sha'awa tace mu tafi abunmu" A hankali ya sauke idanshi akan nata
"Laifin me tamata ne?" Sophie sarakan gulma gyaran tsayuwar ta tayi
"Toh nidai inaga tamkar akan zamanta gidan mu, maman take cewa ta nanuke mana waikai takeso ta aura shisa ita me kwad'ayi ita mayya" Ranshi yayi matuk'ar b'aci amma seyayi wani murmushi yace
"Ku jirani zamu tafi tare" Juyawa tayi sabida tasan halinsa sarai se sunci ubansu.
*************
Cikin Ummul kam tubarkalla ya fito sosai se shek'i takeyi abunta, tana samun kulawa mara iyaka agun Maman Nancy, tana samun kulawar so da k'auna awurin mijinta, bashida burin daya shallake ya faranta mata, tausayi take bashi akanshi tazamto sekaje wacce tai kisa tana b'oye b'oye......Naja ma hankalinta a kwance take al'amuranta amma tanaso taga iyayenta sedai ya bata hakuri akn yana kan dubasu.
**************
Tunda Mahal yace zezo shida ummanshi basu samu zuwa ba se wannan karon da akayi wannan haihuwar, shima zuwan ne yayi daidai da lokacin, har sunyi waya ma da Maheer sedai a hotel zasu sauka yaso su sauka gida amma mahal ya kafe, amma dai sunyi da yamma zezo musu kodan yaga sophie da aketa cewa suna kama sosai, yarinyar dayake fatan ya aura.......
***********
Yana shan k'amshi ya shiga d'akkn na islam tana zaune ta rafka tagumi tana hawaye ga innan tanan tana fad'ar wasu maganganu daya jiyowa kunnensa tunka yashiga d'akin, seya basar tamkar beji ba, yau har uwar ko kallonta beyi ba yace da islam
"Zanyi magana dake salaha" Kallon shi tayi ta marairaice fuska se uwar ce ta basu wuri yace
"Zan bar kwana anan gidan har se sanda inna ta tafi, koba komai jego kikeyi, yanzu zan tafi se kuma da safe sabida a kwanakin nan biyu na gaji idan kina buk'atar wani abu ki gayamun" Bakin cikine ya qara taso mata amma tasoma jin tsoron sa cikin ruwan sanyi yake ciwa mutane mutunci
"Babu abinda nake buk'ata" tabashi amsa a tak'aice be kara cewa komai ba ya juya abunshi itama se kunci takeyi takira anty Nasara take gaya mata sunan baby da komai daya faru, ashar ta danna ta soma kumfan baki, Abba tasoma kira tana zayyane masa abinda ya faru akan sunan da maheer ya danya murmushi yayi yace
"Haba Babba! " dayike haka yake kiranta wani zubin
"Ina sunan k'anwata ya sanya? Aiya kyauta ma yayi hikima Allah ya masa albarka" Haushi ya kamata tace
"Abba sunan wannan tsintacciyar magen nefa hafsat ya sanya" murmushi yayi ya gano sosai Babba batada kai har yanzu
"Babba sunan k'anwar sane waini tukunna ma ina ruwanki? Kinga karna k'araji bake kika masa aure ba, bake kika haifa masa yarinyar saba dan Allah babu ruwanki da iyalansa kinjini ba" Hakuri ta bashi sukayi sallama.
************
A gidan su Hafsat kuwa yau se kumburi takeyi kanta sarawa yakeyi, tarasa wace irin rayuwace wannan Allah ya jefeta dashi, Kiran sophie Maheer yayi
"Ki gayawa Hafsat zamu koma d'akina da ita, yau acen zata kwana" Murmushi sophie tayi taje ta gayawa Hafsat, turo baki taki
"Allah ni bazan jeba" tafad'a tamkar tayi kuka kallonta sha'awa tayi
"Akwai wani hali na yaa Maheer da baki saniba Hafsat, rufin asirinki d'aya ki tashi kiyi wanka ki kwashi tsummo karanki kije, ke matar sace bakida wani wulakancin dazaki masa, kuma wlhy karki bari yau ya sauke wannan halin a kanki kinmaji na gaya miki" Mik'ewa tayi jikinta a sake ta watsa ruwan ta kimtsa kanta cikin kayan bacci masu laushi hijab ta d'aura akai ta dauki zani ta musu sallama da wayanta a hannu zuwa d'akin nasa.....Da sallama ta tura k'ofar d'akin tashiga yana kwance yana danna wayarshi sanye da boxers da singlet yana wasa da alawar dake bakinsa......ya amsa mata sallama ta sannan ya mik'e ya tarbota ta hanyar sanyata a k'irjinsa...hannunsa ya sanya ya shafi kanta
"Ance kanki yana ciwo kinsha magani" Yanayin muryanshi taji ya sauya mata gaba d'aya, d'agowa tayi suka had'a ido sannan tace masa
"Ea amma naji sauqi sosai Alhamdulillah" jinjina kansa yayi ya juya zuwa gadon kana yace
"Kizo ki kwanta anan, ki rage wannan kayan nauyin" batai musu ba ta zare hijabin ta ninke da zanin ta daura akan resting chair ta d'are saman gadon a hankali ta zauna tsakiyar sa, akwai hula akanta data cuccura sumar kanta aciki.......ta lumshi ido ta had'e hannayenta tana rero adu'o in bacci a sarari....seda ta hura iska hannunta na dama dana hagu sannan tayi k'asa da sama tukunna ta shafewa jikinta, se kallonta yakeyi matsawa tayi ta kamo hannayensa duka biyu ta rufe idanta ta masa adu'oin sosai shima ta hura masa iska tako ina sannan ta shafe masa jiki se kallon ta yakeyi, yama kula kaman muryanta ya canja sannan kuma yaji zafi a hannunta bedai katseta baneba sabida yaga alamar wannan tarbiyar sabintace, ita kuwa ummul ta tunano kullum ita ke mata adu'a dabida batasanyi se baccin wuri...... Kwantawa tayi a gefen sa ta matse kusa dashi sosai, fuskarta adaidai k'irjinsa ta rufe idanta iskar datake shak'a tana fesarwa yaji zafinta a k'irjinsa, hannun sa yakai saman kanta
"Innalillahi, ke Hafsat zazzab'i kikeyi haka kikayi shiru?" Bud'e idanta tayi tana murmushi
"Nasha magani zakaga ya sauka yanzu, kayi baccinka kaji" hannunta ya rik'o taga duk ya rud'e
"Sannu wane maganin kikasha, ko asibiti zamuje?" Lumshe idanta tayi
"Nasha maganin zazzab'i karka damu" daganan ta rufe idan bata kara magana ba, harsema tayi tamkar bacci take alhali kuma idanta biyu zazzab'in ma da ciwon kai sun k'ara yi mata yawa....shikuwa yayi tsita yana kallonta yanda numfar fashi a wahalce wayar sace yayi k'ara ya d'akko ya ansa tare da daurawa a kunne....
"Anty Nasara Barka da war haka"
"Yauwa kana lapiya?"
"Lapiya lau sedai kinyi kiran dare" tsaki taja..
"Kaita shafa dama kiranka nayi ince inaso a baiwa baby sunana Binta Fatima kenan" murmushi yayi
"Kiyi hakuri anty, inshaa Allah idan aka qaramun haiguwa indai macece Fatima zan saka, yanzu har anwa yarinya hud'uba da Hafsat" k'irjin Hafsa ne yayi mugun dokawa ta kid'ime tashiga uku
"To saime, aiba suna akayiba dan haka a canja" murmushi yayi ya jima da gani ita ke juyawa islam kai tunda a farko ai basa shiri
"Kiyi hakuri anty, Se wani lokacin wannan dai hafsat ce" Masifa ta fara masa ya sanya ya kashe wayan gaba daya ya ajiye a gefe jin wannan sunan ya k'ara haukatar da hafsat zazzafan zazzab'i ya k'ara dabaibayeta. ...har rawar sanyi tadoma yi lura da hakan ne ya sanya ya kashe wutar d'akin dake atakan gadon, ya rage sanyi ta hanyar rufa musu bargo, anan ya soma cire kayan baccin dake jikinta, zuwa lokacin bazata iya komai ba se rawa da jikinta keyi, yayi mata zafi sosai
"Sannu Hafsatu, idan kika saki jikinki zan rage miki wannan zafin da jikinki yayi" Batace masa komai ba ita kad'ai tasan me takeji, seda ya kawo towel ma da ruwa ya soma gasata tukunna ya shiga lalubar jikinta, runguma me kyau yamata ya dinga smooshing nata nata tako ina seda tayi bacci jikinta ya sauka sosai ta dena wannan zafin jikin....Ta shiga bacci sosai cikeda nutsuwa, tabashi tausayi matuk'a, a haka suka kwanta sunata bacci se asuba tukunna ta farka, ba laifi ta samu sauki amma sam jikin nan bashida k'wari, jiya komai bata ciba ga alama har yunwa ma yana d'awai niya da ita sosai.... A daddafe tayi salla ta koma ta kwanta, fita yae ya bincikesu batashan magani shine amsar da aka bashi, ko bak'on wata zatayi setayi murd'an ciki amma batashan magani wai baya wucewa a mak'oshinta take cewa, tabashi haushi ai sanda ta kwanta asibiti yana bata magani da kanshi iskancine kawai, da kanshi ya nemi magani da tea yakai mata dakyar tasha seda ya mata jan ido, seda ta samu sassauci tukunna yace tazo yau bacci zasu koma, batai musu sukayi brush da wanka suka k'ara kwantawa, alawa ya wurga abakinsa itama setayi sha'awan shansa
"Yaa Maheer nima ka bani alawar mana zansha" murmushi yayi, ya matso sosai da ita ya had'e bakinsa da nata ya tura mata alawar dake bakinsa, taso wayancewa amma yata iya maheer d'an duniya ne, haka ya tsata agaba
"Tonima ki dawo mun da kayana mana muyi sharing, murmushi ta sakar masa ta rufe idanuwanta, haka suka dinga shan swt din seda ya k'are tas abakinta mintsilinta yayi
" kin gama mun wayo kin shaye kin hanani" murmushi tayi
"Kayi hakuri inasan wannan swt d'inne" ta bashi amsa murya cen mak'ale da mak'oshi...kwaikwayon maganarta yayi sannan yace
"Kizo zan sakaki bacci jiya kinsha wuya" Hannunshi ta kamo
"Nagode da kulawa yaa Maheer" lumshe idanshi yayi...ya matseta ya sanya gashin gemunsa ya soma yi mata susa dashi awuya mak'ewa tadomayi yak'i yadena daganan tasoma dariya aikam dama ahaka yakeso, ya matseta seyi mata yakeyi tana dariya tamkar zata shid'e har cakulkuli yadinga mata tana kwasar dariya seda ta gudu tukunna ya saurara mata...
Mom Nu'aiym
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
40
"Inna kina kallon kuwa Maheer ya soma sauyawa? Bakya kula da yanayinsa tun zuwanki dabashi yace kizoba dase nace wataqil beso kika zoba" Tab'e baki tayi
"Waccen mayyar ce dai keso ta zuzuta masa tunani, na mata gargad'i akanshi, bazan lamunci wata banza ta hanamu cin duniyar mu da tsinke ba, gidan talakawa ake kishiya idan ka shiga gidan masu dashi wlhy baka bari wata tashigo maka, Allah ya rufa mana asiri bazamu bari ta tona mana asiri ba, Allah ya sani bazan lamun taba" Gyaran zama Islam tayi
"Inna to meye abin yi? Nifa ina ganin kamar dan itama yaje cen gidan da zama, nasan ba'a zama gun me jego amma ina kwana biyunnan duk tare muka yisu, kuma se yanzu ya koma cen" kallonta innar tayi
"To wai meye dalilin sa na barin gidan ma dahar kika barsa ya tafi"
"To inna kinga cewa fa yayi dani wai tunda kizo yanajin kunya dole ya koma cen" Goron hannunta ta gutsura
"Tunda haka yace ki d'auka haka d'inne kuma kinga ai baze yiyu ma ace wai yaje guntaba ga qanninsa agidan, kedai kurin mu sanya ido muna ganin abinda be mana ba, mu tashi tsaye mu nemi mafita"
"Hakane Inna dolene ma wannan ai".
***************
Ummul se mugwayen mafarkai takeyi da matsafa wai sun farka cikin ta sun ciro mata baby sun kashe babyn itama sun kasheta, mutanen dabatasan ko waye ba amma a mafarkin tana ganin su kamar matsafa da jajayen kaya, abin ya dameta sabida kusan sati d'aya kullum setayi, ta rasa wa zata gayawa wannan maganar, Naja take gayawa tanata kuka
" wlhy kinsan Allah hankalina a tashe yake, musamman da mafarkin ke nunamun suna yawan cin galaba akaina, nasani hakk'ine wlhy hakk'in Nanuwa ne yake d'awainiya dani, duk wata masifa danake gani Baba Azumice ta janyomun, sabida tun asali ni. Ameen bani yace yanaso ba yar uwata yakeso k'anwata, amma Babar mu ta dage seda ta juye abun a kaina, watak'il kuma ajalina ta gayyato da hannunta, dan wlhy ina cikin damuwa da firgici....." Nisawa Naja tayi
"Anty kiyi hakuri kuma ki dinga adu'a inshaa Allahu lapiya lau zaki sauka kamar yanda yanzu Nana ta girma ta zama big girl haka zaki haife cikin ki lapiya lapiya da yardar Allah" Shiru tayi tana nazarin rayuwar duniya ko banda k'addara akwai hakk'in cin amana kenan haka wani yake da Allah, da zaran ka masa cuta tun a duniya zaka soma fanshewa...
Zuwa yanzu Baba Azumi ta soma rikicewa da rashin Ummul, tana cikin tsananin damuwar rashin ta, abubuwa sun soma yi mata yawa gashi dai Ameenu yana iyakar k'ok'arin sa akansu amma ita hankalinta yafi kwanciya akan taga yarinyar ta a kusa da ita.....
***************
Duk juyin dazatayi shi take gani take kuma tunawa, ya tsaya a ranta yanayin wasan daya mata jiya, har Allah Allah takeyi daren yau yayi su koma kwanciya wuri d'aya yafita tun safe be dawo ba amma bazatace ga second d'aya daya shud'e batare da tunanin sa aranta ba, a jiyan ya mata abubuwan dasuka tsaya a ranta matuk'a, Ashe dama haka yaa Maheer yake, dama Ashe akwai irin wannan fain cikin da ake cewa yana saka mutum kuka? Ita harga Allah jiya seda tayi k'wallah dayake mata wasan nin dako sanda take k'arama bazata ce ga sanda tayi irin suba, daren jiya har doki ya mata, seda ya tabbatar ya sanyata bacci ma tukunna shiya kwanta nashi baccin tana......... Wuraren k'arfe bakwai ta gota ya dawo gidan, kai tsaye d'akinsa ya nufa, harya shiga ya fito yayi kiran sophie ta kira masa Nancy, cikin mintuna k'alilan segata a d'akin, sanye acikin shigar ta ta alfarma doguwar rigan material me laushi, da akwai aljihu aduka gefen na rigar tayi kyau sosai babu kallabi a kanta, se sumar kanta data zube a k'asa batare data tufe shiba, wanda tsayinsa ya kusa zuwa kan mazaunanta
"Assalamu Alaikum" shine abinda ta furta a hankali, cikeda rangwad'a ta k'arisa a gabansa sanye take da k'ayataccen murmushi akan fuskarta alamomi sun nuna koda ba bacci take ba to kuwa a kwance take tuni
"Barka da dawowa yaa Mahii, kayi hakuri banji shigowar kaba" D'an murmushi ya saka shima ya shagala da kallon ta
"Ba komai, dama na dawo a gajiye shine zaki had'amun ruwan wanka a bath tube, ki tayani rage kayan jikina" D'an rintse idanta tayi cikeda jin nauyinsa kanta ce
"Babu damuwa" Toilet d'in ta wuce ta had'a masa komai tasha mamakin k'amshin turaren wankan dayake amfani dashi, zataso danin kud'insa tasan koyayane seyayi tsada...tajima a toilet d'in tana gyare gyare kanta fito da towel a hannun tana tinkaro inda yake zaune ko takalmi be cire ba, bata ganewa kansa ba yau ko fara'ar nan babu a fuskar sa ya tsuke fuskar nan tamau dukse ya mata kwarjini sosai ba kad'an ba, tsugunawa tayi ta kwance igiyar takalmin sa ta zare masa su ta cire masa sock's sannan ta d'ago, kasa yin komai tayi bata saba ba bata kuma iyaba, bece komai ba ya mik'e itama seta bisa ta zare rigar dake saman ta kasa,dayike suit ne ajikinsa ta ware masa neck tie cikeda nutsuwa sannan ta soma b'alle masa botiran rigar sa.......... Seda ta cire su tas sannan ta cire na hannun rigar ta zare masa rigar, shidai bece komai ba babu kuma alamun se kulata koya dakatar da ita, nauyi ita kuma takeji jitake tamkar k'asa ta tsage ta shige, singlet d'in jikinsa ta zaro daga kasan wandonsa ta zare masa, se wani kallo yake binta dashi yana lumshe ido alamar gajiya......kallon shi tayi gargasan girjinsa daya wani kwanta luff har zuwa tsagun marar sa yayi k'asa ga packs d'innan guda shida sunsha zane,batada dabaranyi dan bazata iyaba
"Kayi hakuri" Da d'an mamaki ya kalleta
"Menene?" Shine tambaya daya mata
"Bazan iya cirewa ba" lumshe idanshi yayi ya juya
"Kibar d'akin kawai" tsaye tayi taga kaman yayi fushi
"Kayi Hak'uri yaa mahii, wlhy ba raini bane ban iya bane" hannu ya d'aga mata alamar ya isa sannan ya mata alamar barin d'akin da hannun shi, Jiki a sanyaye ta juya kome ya sameshi oho, dukya sauya tana isowa d'akinsu sophie ta rik'eta
"Ke yau kinga idon yaa Maheer, wlhy halin yakeji ni seda ma ya tsoratani da yanda yake magana kodai waccen kojajjiyar ce ta hautsino mana shi" Tabare fuska tayi tamkar zatayi kuka
"Wataqil kam, dan cewa yayi na had'a masa ruwan wanka na rage masa kayan jikinsa to kuma sophie tsakani da Allah ni kunya nakeji, fisabilillah wai sena kama na cirewa babba kaya" Dariya tayi
"To Amarsu ya kukayi da angon?" K'wallan datake tarewa ya subo mata
"Ni nacire sauran wandone bazan iya cirewa ba, nikam nace yayi hakuri shine yayi fushi ya koroni har yana juyamun bayaðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜" Dariya tabaiwa sophie ta somayi har tana rik'e ciki
"Wlhy kinada wawta Nancy, ina mijinki ne? Kin fasan wacece kishiyarki wlhy ki rage wawta da kunyan kin nan, ni wlhy aka auramun Mahal nizanna riqa yi masa wanka ma ba cire kayaba, mujin kine fa, tukunna ma tsaya ina tare kuka kwana jiya mesa bakiqi kwana da shiba?" Kallonta tayi
"Sekinyi auren ki gane wlhy da kunya matsananciya sophie, tayaya zan kalli yaa Maheer na cire masa....kai dama bashi bane wani na aura, yayana fa" Dariya tayi
"To ki ringa daurewa kina masa abinda yakeso, yaa maheer seku shekara dari tare baki san halinsaba bayasan gadda shi sam, kuma shi ai yaga ke matar sace bakomai bane wannan ai" shiru bata kulata ta qara cewa
"Ki tashi kije gunsa ki bashi hak'uri" Ba musu ta mike tana kokarin k'ulle sumar kanta kamar yanda takeyi idan ya dameta seta masa kullin bakar leda.....
A bakin gado ta sameshi ya zauna dafe da kanshi dagashi se towel d'ure a qugu, zama tayi kusa dashi tace
"Yaa maheer kozan tayaka da shafa oil d'inne ?" D'ago kansa yayi ya kalleta tasha mamakin ganin idanshi yayi jajir, da sauri ta rik'o hannun sa
"Subhanallah yaa Maheer meke damunka" bece mata komai ba se kallonta yakeyi ana haka wayanshi ya soma ringing banza yayi har kiran ya yanke,cen kuma kiran ya k'ara shigowa wannan karon janyota yayi yana lumshe jajayen rinannun idanuwan sa...ya d'auka tare furta
"Assalamu Alaikum" A d'ayan b'angaren kuma Umma ce
"Alaikassalam Mahii"
"Na'am Umma ina jinki"
"Cewa na maka ka sauyawa yarinya suna daga Hafsat zuwa wani sunan daban karka kasance namiji me haddasa fitina a gidansa, matarka takirani a waya tanata kuka, sanin kankane ba macen dazataji dad'i ace anmata kishiya bata saniba kuma da k'awarta, har kullum ina maka gargad'i akan yin adalci a tsakanin matayenka, Abbanka yanada dalilinsa na cewa kar a gaya mata yanzu, gudun fitina yakeyi kuma yasan halin mata su tashi hankulansu agarin daba nasuba basuda kowa"
"Umma kiyi hak'uri ai nace zan sauya sunan inshaa Allah"
"Sannan takirani yanzu ma akan wai kabar gidan zuwa gidan su Sophie, meye dalilinka nayin hakan? Baka gudun tayi zargin wani abu kota gano wane abun" Ranshi ya matuk'ar b'aci dandai Umma ce
"Umma bazan iya kwana gida d'aya da sirikata ba wlhy, kana bazan iya zama awani wurin ni kad'ai ba, ki k'yalesu kurun suna kuma da kikace a sauya mata seki zab'a danni harga Allah bansan wani suna dazan baiwa babyn ba" Nisawa Umman tayi tasani sosai Maheer yanason sunan daya zab'a d'in nan takuma sani bazeji dad'in haban ba amma matar safa? Suna zaman lafiya idan ta gano sunan kishiyara aka sakawa babyn ta yaya zataji? Ai suma seta d'aukesu mutanen banza ...
"Autan maza kayi Hakuri, ka baiwa yarinyar nan suna Aisha kaga itace mahaifiyar Abban ku semu sakala mata sunan daya dace ana kiranta dash shida kanshi zeji dad'in hakan, inshaa Allahu"
"Babu damuwa Umma zanna rik'a kiranta Mamaa Allah yasanya albarka"
"Ameen autan maza, Allah yamaka albarka, kayi hakuri nasan halinka da zuciya dakuma yawan ciwon kai idan ranka ya b'aci dan Allah kayi hakuri, kakuma nemi hanya me sauk'i ta gayawa matarka aurenka da Hafsatun idan kun dawo, naji ance nanda kwana 30 zasu kammala jarabawa suyi hutu seka tarkatasu ku dawo gida anan semu sanarwa matar taka" Nisawa yayi "babu komai Ummana yanda duk kikeso haka zanyi,albarkanki kurun nake nema" Albarkan ta sanya masa ta masa godiya sosai sannan sukayi sallama, kanshi dake sara masa ya danne da duka hannayenshi guda biyu jikinsa harya soma rawa tsabar macin rai, baze iya yiwa ummansa musu ba, kisane kurun zata sakashi yace bazeyi ba, amma Islam ta gama rainashi wlhy, shi zatawa iskanci da wulak'anci takai k'ararsa gun iyayensa abinda yafi tsana, bazata masa magana bama setaje ta gayashi da iyayenshi lallai ma Salaha....... Duk se Nancy taji wani iri batajin me umma ke cewa amma ta fahimci akan sunan baby ne...... Rintse idanta tayi ta kai hannunta sama waits nashi ta zagaye
"Meyake damunka Zauji?"
"Ba komai ki kawomun coffee" zuwa tai ta had'o ta kawo masa,da kanta ta bashi coffee din me zafi yasha sosai, sannan ya nemi gadon ya kwanta luff dashi, kasa barinsa tayi shi kadai taje ta rage kayan nauyin jikinta zuwa nashan iska, tadawo d'akin da wayarta a hannu, kai tsaye gadon ta d'are ta soma daddan na masa bayanshi da kafad'un shi yana jinta amma ko motsawa beyi ba, sabida harga Allah yanajin dad'in tausar seda taji ya soma minshari sannan ta rufe shi da duvet, tana shirin kwanciya ta huta wayanta yayi k'ara, lambar London ce amma batada lambar, a sukwane ta d'ag kiran
"Bak'ar ashana k'ona gari, kina ganin kamar kinci galabane da kika sanya aka sanyawa 'yata sunanki? To na nuna isata na kira sirikata for ur information yanzu sunan yarinyata Aisha, banza karuwa mebin mazan mutane er tasha, uwarki ta k'are a karuwanci kema acen zaki k'are wlhy keda mijina har abada er dandi er dadiro yar kwararo haihuwar kan titi kawai" Ba kad'anba kalaman islam suna k'ona ran Hafsat tace
"Yanzu islam ni kike jifa da muggan kalamai irin wannan mena miki? In isheni akan mijinki, wai idan har inason auren na mijinki ne ke kin isa ki hanani auren nashine? Wlhy so dubu yafi ganin k'ima na dake, ke kin manta inda aka fito ne dazaki rik'a kirana karuwa, kijimun iskancin banza wai bayarbe keceda inyamuri kafiri, bari kiji islam wlhy kika k'ara kirana kina zagina sena nuna miki baki sanni bq tukunna, halacci ne kurun nakeyi ina qyaleki bawai don ina tsoron kiba,k'wacen miji kuma zakiga yanda akeyinshi wlhy banza shasha....
" Uwarkice banza, nace matsiyaciyar uwarkice banza, mugayen buzaye masu bak'ar aniya, wlhy sena sanya an lahanta miki rayuwa akan maheer mayya kawai, ko a lahira idan ana aure bazaki tab'a aurar maheer ba bare kuma a duniya ana zaune, shegiya er tasha" tsaki nancy taja ta katse kiran.......kai tsaye Anty Fareeda ta kira, tana d'agawa ta saka mata kuka
"Anty Fareedah ni dan Allah kicewa Abba a miyar dani school a kano, wlhy na tsani zaman garin nan islam ta sakoni agaba Anty Reedah bata bari inashan iska, yanzu ta kirawoni har ummana seda ta zaga tana cemun karuwa waye waye" Nisawa Fareedah tayi
Aiki kuwa yagano islam tabbas, amma ke Hafsat ki dena damuwa, umma tamun magana ma akan sunan baby nina qara bayarda goyon bayan a sauya, yarinyar sekin tashi tsaye makissaciya ce,ki dena kuka ina kan aiki yanzu anjima zan kiraki" sallama sukayi ta zauna tanata kukanta seda ta gaji bacci ya kwasheta a wurin...
Mom Nu'aiym
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
42
Batai aune ba taji hannunsa a saman nata, yace Ehm Princess? Bakya buk'ata ne? Bakyaso ki kasance tare da mijinki? Idan hankalinki be kwanta ba karkiji shayin komai ki fad'a namiki alk'awarin zan barki harse sanda kika buk'ata, abu d'aya nakeso ki saka a ranki ina cikin tsananin buk'atar ki a yanzu" Har lokacin batace komai ba, bata kuma kalleshi ba se murmushi datakeyi matsowa yae daf da ita
"Princess hafsy sarautar ya motsane ko azumun magana ne kikeyi?, Nace inaso in kasance tare da matana ko rowa za'a mun" wannan kalmar daya fad'a kansa tsaye daf da kunnenta ne ya sanya ta shige a k'irjinsa tana b'oye fuskarta aciki, ya kula sosai takejin kunyar sa yana son mace me kunya, tana daga cikin matayen dayake daraja darajarsu akoda yaushe, yasha fad'awa Kabeer baze auri mace wacce batada kunya ba se gashi yanzu Allah ya bashi....rungume abarsa yayi gaba'aya ya sanya hannu d'aya yana patting bayan ta a hankali
"Princess kunya na kikeji? Ehm? Bani amsa mana kunya na kikeji?" K'ara cura kanta tayi a k'irjinsa, d'agota yayi ya zare mata hijabinta, lumshe idansa yayi yana godewa mak'agin wannan halittar, se k'ara shige masa takeyi in d name of kunya😂😂😂... Nan kuwa bata saniba kashe wa gogan jiki take k'arayi, numfashinsa se hauhawa yake sakamakon dadd'an k'amshin turaren ta me sanyi da sanyaya zuciya, a b'angarenta kuwa itama hakance kwanciyar hankali tare da nutsuwa me tarin yawa take samu a wannan k'amshin na jikin Maheer ko kad'an bata so ta rabu da jikinsa, sunyi shiru dukkansu na kusan mintuna uku kowanne da abinda yake sak'awa a ranshi, shine yai jarumtar furta
"Ki d'agani mana muje kan gado" Kotak'i kotaso zamanta ajikinsa yayi matuk'ar tasiri agareta, bata shirya fitar kalmomin ba seji tayi sun fito a bakinta, a ranta take sak'a hakan batada labarin kalaman zuci sun fito
"Inajin dad'in k'amshin dake fita ajikinka yaa Maheer, dan Allah ka barni" murmushi yayi
"Tozan barki ajikina harse sanda kikace kin gaji, amma dukda haka muje kan gado nand'in gajiya zakiyi" seda ya bata amsa ta ankare da abinda tace, kasa motsi tai seda da kanshi ya mik'e ya d'agata chak zuwa kan gadon, zare jallabiyar jikinsa yae kana yawa kansa masauki a akan gadon tallafota yayi jikin ta rufe idanta tai yaja dogon hancinta ya sauke idanshi akan black lips d'inta asalin na buzaye shisa koda wane lokaci koda bata shafa lipstick ba yake kyau sosai yayi brown seyayiwa farar fatarta kyau matuk'a, Murmushin dayake kan fuskarsane ya fad'ad'a ganin yanda take rufe ido yanzu, ashe dama rainin na k'aryane dacen har mamakinta yake yanda take cire ma ta daddage ta k'ura masa na mujiya ido cikin ido
"Ki kalleni mana Princess" murmushi tayi
"Idan na kuskura na sanya idona anaka bana iya janye nawa, wani magnet ne inaga dakai a ido, idan ina kallonka bana iya janye idona sedai ko idan ka soma janyewa....idanma ba kallon ka nake ba idan idona yana a bud'e se magnet na idanka ya janyo nawa zuwa kanka nika barni a haka" Wasu lokutan setayi kaman bata surutu wani zubin kuma se kaga tana zuba tamkar ba ita ba
"Naji nine me magnet d'in,amma kefa meye naki? Nifa dazaran kina wuri to bana shakka ko waye a wurin sena biki dana mujiya nake jin sauqi, nutsuwa ta gaba d'aya tattarewa take ta nemawa kanta mazauni a gunki, ke kuma wannene magnet naki?" Murmushi tayi kantace wani abin wayanshi ya soma ringing....janyota yai ya kara a kunne bayan ya d'aga kiran yana me k'ara matseta ajikinsa
"Maheer wlhy ina cikin tashin hankali, Anzo har hotel an sumar dani an sace mun Ummul da tsohon ciki, Alhj Baba bashida imani Maheer, ko kasheta ze iyayi ayanda yakejin haushina, bansan me zanyiba, idan ma da hukuma nace zan had'ashi banida hujjan cewa shine kuma kaga asirinmu nida shi duk ze tonu tunda banida wata madafa, sefa ta wurin rabbu sabida nina me laifi ne" Zabura Maheer cikin tashin hankali
"Subhanallah Ameenu, kagani ko kaga abunda nakewa gudu ko, yanzu da tun farko ka turo ta nan da babu abinda ze sameta, Niger ai ba garin b'uya bane ba, beside kanata zarya sati biyu kazo ka koma dole na gaya maka su sanya maka ido, yanzu kaga amaimakon kaika cutu 'yar mutane ce aciki bakasan halin datake ciki ba" Kuka ya saka masa
"Wlhy na yarda maraici bala'i ne da inada iyaye na a raye meze sanya wannan azzalumin ya d'aurani akan gurb'atacciyar hanya irin wannan? Yanzu gashi banida mafita, ka taimakamun da mafita Maheer banida wani danasan ze fad'amun Gaskiya sekai Maheer, wlhy ummul tausayi take bai matuk'a, ga Nana Ummimi ma ita ba wani girma ba gashi tasha ciki, gaba uwarta a tare da ita, bansan ko itama yazo kanta ba"
"Ka kwantar da hankalinka Ameenu, babu abinda ze sameta itama jinjirin kurun yake so ta haifa masa, yanzu shawara biyu zan baka idan ma babu kud'i a hannunka nizanyi komai na visa ka had'o wannan Najar da Jinjirar suzo mun nan London dough dai ba jimawa zan dawo amma gwara basa k'asar, kai kuma ka lafe akan maganar Ummul, karma ka nuna masa kadamu da d'aukewan daya mata, hikima kurin zata iya dawo maka da matarka amma rigima sam bazatayi ba, ina kacemun kadena kuje masa yanzu ka kanje gunsa har kuna gudanar da kasuwancin ku shima yadena maka maganar laifin daka masa, to kaima lafe masa ci gaba da binsa kamar ba'ayiba harmu gano bakin zaren" Nisawa yayi
"To Maheer inshaa Allah zanyi yanda kace, amma Naja da Ummimi har ma na kaisu wurin wani abokina dake Ghana yanada kud'i sosai kuma akwai security sosai a gidansa, munyi magana akan ba inda zasuje Matsalar su d'aya Ummimi dake yawan tambayar mamanta, ta dinga kuka akan Ammy Ammy" Nisawa Maheer yai
"Ka rik'a yawaita adu'a kana sadaka ana maka, inshaa Allah komai ze daidaita, ka kuma sanarwa iyayenta" A raunane yace
"Na sanar dasu, yanzu haka Babarta tana kwance a asibiti hawan jini ya kwashe ta, se ciwo take akan 'yar wlhy duk na damu" ban baki yashiga yi seda ya kwantar da hankalinsa had'e da shawarwari sunfi 40mns a waya, Nancy dukta rud'e kan sui sallama
"Yaa maheer meya samu Ummul na ne, jiyan ma seda na kirawo wayanta amma bejeba meya sameta ne?" Tausayinta yaji ya janyo hannunta yace
"Hafsat ki saurareni kiji mezan gaya miki, dama na sanar akan matsalar da Ummul da Ameenu ke ciki to shine shekaranjiya se aka.........ya kwashe komai ya gaya mata, aikam kuka ta sanya masa wiwi wai ita 'yar uwata.....janyota yai jikknsa ya dinga rarrashi da ban baki, a haka hartayi bacci a jikinsa se sauke numfashi takeyi da k'yar alamun baccin ma ba a dad'in rai take yinsa ba sosai ya shiga damuwa.
********
Washe gari kuwa koda ya tashi harta bar d'akin, da tsananin ciwon kai ta farka akan damuwa, tanata mafarkin 'yar uwarta, last call nasu ma video call ne har aka bata mamanta taga k'aton cikin ummul se dariya take mata tana cewa tayi k'aton hanci ta zama k'atuwa....tana buk'atar kad'aicewa sabida ta samu yin nazari, be takurata ba ya shirya ya wuce abunshi gun islam, sallamar farko da fad'a suka fara wai jiya ya tafi da wuri kuma ko waya me yake nufi da ita, ya mata ciki ta haihu ze wulak'antata aiko laplfiyan baby ya kira yaji, Hakuri ya bata had'e da yi mata 'yan wasanni kan ya shawo kanta suci gaba da hirarrakinsu na soyayya tsakanin miji da mata se Allah kankace kwabo sun gama daidaitawa kamar ba'ayiba....
Mom Nu'aiym
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
43
Ranar maheer bashi yabar gidan Islam ba se washe gari, se zuba love akeyi ta bashi hak'uri kuma yaji dad'in hakan, yana son mutum yayi kuskure ya kuma bada hak'uri, yanda aka nanuk'ewa juna tamkar ba jego akeyi ba, shinshina da shafe shafe yashashi a wurin islam seda ta tabbatar ta gamsar dashi da wasanni tukunna ta tsiri kukan ya kwana mata, Bayason rigimar islam sukai sharad'i akan daga ranar baze k'ara kwana mata ba se Inna ta wuce, haka tace ta yarda sabida ta shrya shagaltar dashi kullum idan yazo.....wannan ma yana daga cikin shirin Anty Nasara na ganin bayan auren islam wanda ita a zatonta sone.......
*********
Tun wuraren k'arfe tara na dare Hafsat tawa su Sophie sallama ta wuce d'akin yaa Maheer, dayike sunada Exams setaje da takardunta tana dubawa, tun tana saka ran ze dawo har bacci ya d'auketa be dawo ba, ba ita ta farka ba se asuba, tasha mamakin inda yaje ya kwana be gaya mata ba, gata acikin damuwar abinda ya samu ummul har Baba iro sunyi waya akan Jikin Baba azumi ba kanta, gashi kuma yazo ya tafi ya barta ba sallama ba waya har yanzu baya kiranta a waya, tarasa dalilinsa nayin hakan......tamkar wacce k'wai ya fashewa a ciki haka tamik'e zuwa d'akinsu acen tayi wanka ta shirya ta wuce school tanada exams by 10:am......tana cikin school bus wayanta yai k'ara
"Yaa Maheer" shine sunan data gani rad'au ya aiko mata message, a hankali ta bud'e message d'in
"Good morning princess, hope kin tashi lapiya, jiyan na kwana wurin su islam ne, dafatan bakida matsalan komai?" Wani abu dabatasan ko meye shiba ya taso mata ya tokare mata k'ahon zuci, wani d'aci taji a yawun bakinta kanta ya sara mata, kashe wayanta gaba d'aya tayi aka huta, ta jingina da sit na kujerar datake kai, a hargitse tayi Exams din ta fito, amaimakon taje gidama library taje tanata karatu har yamma kuma bata bud'e wayanta ba, se bayan isha ta koma gida da azababben ciwon kan data rasa dalilin sa a rayuwa......sophie ta had'u da ita a parlor tana shan ruwa a cup
"Ke Hafsat yau ina kika shiga anata nemanki, ko wayanki baya tafiya" a wahalce ta d'ago ta kalleta
"Ina library karatu nayi ko gobe inada exams morning" jinjina kai tayi
"To ai dakin gaya, yaa Maheer se masifa yake mana akan ina kikaje har yamma mukace school mudai mukasan kin tafi" guntun tsaki taja a hankali kan tace
"Shima dai yasan ba b'ata zanyi ba a garin nan" ta wuce d'aki abunta, dama sunyi gulmansu da shauty akan be kyautaba jiya ya kwana cen gidan sun gano fushi tayi......
Yauma haka islam ta mantar da Maheer komai arayuwa, kissa da kisisna da iyayi, daga k'arshe ta bashi maganin bacci, bashi ya farka ba se washe gari karfe goma na safe, yasha mamakin wannan baccin, da girman sa baya iya tuna sanda ya rasa sallah asuba da sunan wai bacci ya sure shi, Amma kuskuren datayi sega tablet a gabanshi bata daukeba ta manta, ya shak'a sosai da ita har meeting yakeda ta hanashi ya halarta yanzu.....da fad'a suka rabu yau kam.
*************
Yauma Nancy dukda daren suna ne amma bata koma gidan ba se bayan isha, bayan an sanar mata yaa maheer yace taje gidan islam su dafa abinci ze gayyato mak'insa by 12:noon sabida suma suga yanda suke nasu shagalin biki, yaji haushi dabata jeba duk bayan mintuna seya yiwa Sophie waya tace batazoba har dare, dama ta k'are da school seta wuce abinta gida, interval nata da exams kusan 2 weeks ne amma haka ta mak'ale a library da waya a rufe..........se wuraren sha d'ayan dare suka dawo dukkansu lokacin tana parlor zaune maid d'insu ta kawo mata snacks da drink tana sha....se yamutsa fuska takeyi kamar an mata dole, yau a cike take fam da Maheer tamkar zata fashe haka takeji, kai tsaye wurinta yanufo, tana sanye da gajeren boxer irin na maza, da guntuwar farar vest ta baje sumar kanta har tana sakkowa tana rufe mata fuska lokaci zuwa lokaci takan kai yatsunta ta sak'aje wacce ta zubo a bayan kunnenta, Tsaye yayi a kanta ya murtuk'e fuskar nan itama kuwa ko kallonshi batayi ba ta had'e wannan fuskar tata abinda kake fin shekara baka ganiba a fuskar ta fushi ba.......ko Gayar dashi batayi ba shima bece mata komai ba, sophie sarakan iyayi ne tazo wurinta
"Ke Hafsat kwana biyun nan lafiyan ki kuwa, ki kama waya kin gark'ame ba inda banje nemanki ba a school dana kammala exams, kuma kinsan dai koma menene baki kyauta ba ko yaa Maheer zeyi bak'i gobe suna kink'i kizo mu masa girkin dayace alhali ya sanar mana dukkanmu" D'agowa tai ta kalli sophie, ita kanta ta tsorata da yanayin Hafsat idan nan tamkar ba nata ba, hadda bak'in ciki ya soma komawa brown akan jan dayayi, alamu ma sun nuna kuka tayi da sauri sophie ta sunkuya
"Dama bakida lapiya bamu sani ba? Mesa baki fad'a ba" ga jikinta da zafi sabida wahalan data baiwa kanta ga rashin cin abinci amma haka ta daddage
"Ni lafiyana k'alau yawan duba takadda ne kurun ya sanya idona yai haka" kallon tuhuma sophie ta bita dashi
"To amma duk duba takaddan ne ya sanya jikinki ya soma zafi, gudun magani ko? Umma zan kirawo a waya yanzu kuwa" rik'e hanunta tayi tana yunk'urin mik'ewa
"Karmuyi haka dake, wlhy lafiyana k'alau yanzu se umma tamun fushi kinsan halinta, kaina ke ciwo kuma ki tambayi catrina nasha magani ciwon kai" jinjina kanta tayi alamar gamsuwa
"Yakamata kije ki kwanta ki huta, yafi wannan zaman anan kinji swt hrt" gyad'a mata kanta tayi da murmushin yak'e a fuskarta wanda akace yafi kuka ciwo a tare suka bar wurin, shi kuwa yana nan tsaye tamkar wani statue, kai tsaye d'akinsu na usul ta wuce tai kwanciyarta, kallon ta sha'awa tayi
"Ke Hafsat ina yaa Maheer yana gidan me zakizo nan ki kwanta kuma, kefa Hafsat wlhy zan gayaki da anty Fareeda, ji yanda ya damu dake d'azu yakira yakai so goma komafi wlhy akan kinzo gida amma shine yanzu zaki k'yaleshi" Lumshi idan ta tae kanta yana ci gaba da sara mata, amma kanzil bata ceba, Catrine ce tashigo akan wai yaa Maheer yace Hafsat taje d'akinsa yanzu, bata kulataba kuma tafi 25 mns bata tashiba, harya cire rai da zuwanta ta mik'e tana ganin jiri taje d'akin nasa....... Mik'ewa tsaye yai cikeda masifa
"Hafsat ni kika raina ko? Ni zaki rainawa wayau? Tun yaushe na aika akiramun ke? Tukunna ma ubanme ya hanaki zuwa kiyi aikin dana sakaku?" Wannan fad'an dayake hadda zugar islam akan wai tana bak'in cikine an fasa sanya sunanta yasanya tak'i zuwa har tana cewa wai tunda takira ta zageta karta shigo mata gida kuji sharri!!!! Da k'yar ta iya d'aga idanta ta kalleshi
"Kayi Hakuri" shine abinda ta furta kanta zauna ragwaf akan gadon kasa zaman tayi taje luu ta kwanta kanta yana meci gaba da tsananin sarawa tamkar ze tsage gida biyu, ita da kanta tasan hadda yunwa bawai ciwo ba amma yanda takeji bazata iya cin komai ba.....binta yai da kallo yana nazarinta, jikinsa ne yai sanyi yabita zuwa gadon ya tallafo kanta sosai ya tsorata da zafin dayaji ajikinta, yakula dazaran ranta yana a b'ace se zazzab'in nan ya tashi mata seya kaita asibiti tukunna zeji meke sanya ta yin hakan, kar azo memory ya k'ara guduwa ya shiga uku
"Hafsat bakida lafiya sosai ne haka wai?" Cikin rashin sanin me tace da k'unan rai tace
"Da inada miji aida yasan banida lafiya, dayike ni gauruwa ce aidole inyi hak'uri na zama wacce ta rako mata duniya, ko albarkan kiran waya bana samu, kaje kaji da kanka gun Mowar gidan mana tunda yake albarka sanin zaka kwana a guntama ban samu ba sedai na nemeka na raba dare ina jiranka baka zoba, kai kuma wuni d'aya kacal daka nemeni dannaje nawa mowar gidan baka samu ba har ka rufe idanka kanacin mutun cina, babu ruwanka dani ko yanzu kana iya tashi ka koma gunta ai" Ya k'ara tabbatar wa kanshi fushin dai na kishine kuma yasan be kyauta ba
"Kiyi hak'uri Hafsat wlhy bada sona bane"
"Ni dason nawa ai ya Maheer, wannan ce soyayyar dakake cewa zaka nunamun kanamun tunkan ayi sati harka soma nuna mun rako mata duniya kurin nayi, mesa acikin kwanaki uku kacal zaka dasamun so da k'aunarka azuci sannan ka soma azabtar dani, wlhy seka ciremu " wowta take zazzaga masa meze cire ya tambayi kansa? Ba amsa
"Kiyi hakuri abun dukba haka bane ba, kuka ta saka masa, lokaci s'aya kanta ya k'ara hargitse mata da ciwo me tsanani, dafe goshi tayi tana sauke numfarfashi a hankali, daga haka kuma seyaji shiru bugun zuciyarta ya tsaya cak!!!! Kamar yanda numfashin ta ya d'auke cak!!! Lalubar hannunta yayi ya cira shi ya sako yaga yazo lagwaf....
" suma tayi" ya furta a sarari....tunawa yayi da maganar likitan ta tun a Nigeria....
"Idan kukayi sa'a zata warke na har abada, amma sekun kula idan damuwa ta mata yawa zata rik'a suma kuma ba'ason irin wannan suman sabida wani zubin dagashi basa tashi se k'abari" wata mahaukaciyar k'ara ya sake had'eda kiran sunanta, su sophie duk hankalinsu yadawo kanshi suka fito a guje har catrine ma suka nufi d'akin....
Mom Nu'aiym
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
45
Harara Fareedah ta wurgawa Anty Nasara
"Haba Anty, waime ya sanya arayuwa ke bakya k'aunar kiga an rabu lafiya ne?" Huci ta somayi
"Wlhy se umma taga wannan iskancin,dama zaman kenan da kukeyi a london, shisa mana matarka taga abinda ta gani ta tashi hankalinta...... Shidai kan Hafsat yai yaci gaba da jijjigata, anan ne mommy tashigo hankalinta bekaita wurinba seda Nasara ta nuna mata
" kalli Hafsat Umma, Maheer yayi zina da ita yau Allah ya toni asirin su" wanka mata lafiyayyen mari umma tai kai tsaye
"Maza Fareeda kauce mun zan duba ta, ke kuma Nasara karki fita tsaya a wurin" tafad'a tana tunkarar Hafsat d'in da kanta, Dubawa tayi sannan tace
" ki suturta mata jikinta mijinta ya dauketa kukaita mota kije asibitin ku da ita, lallai a dubata da kyau, kinsan matsalarta akuma duba wannan raunin dataji ajikinta" To fareeda tace aka daura mata zani da hijab Maheer ya kinkimeta, har lokacin Anty Nasara se sauke numfarfashin wahala takeyi, bayan sun fito umma ta kalleta
"Muje d'akina" ta furta, sannan batare data jira cewarta ba ta juya, seda Umma tajima da fita sannan tabi bayanta bayan ta zaro wayarta ta danna lambar islam
"Ke wlhy, wawiya ce toki sani wlhy yaudai da idona na kama Maheer da Hafsat sunyi zina, in tak'aice miki ma jini ya b'alle mata inaga dama sun saba yau akazoyi kila cikin shege ne da ita ya b'are, an kwasheta a sume kije tana asibitin su Fareedah ki ganewa idanki" zabura islam tayi tana salallami, lokaci d'aya ta soma kuka, ta rasa wanda zata gayawa tunda innan ta ta wuce!!!!!! Zarar Hijabi tai ta zura ta barwa yarinyar da aka kawo mata me reno mamaa ta fita da sauri, driver na ganinta ya taso da escort biyu, ta shige mota suka cira!
**********
Ba wani abu bane ciwon daine ya tashiwa hafsat, amma da sauk'i bekai wancen ba, an samu ta farfad'o sedai ta gagara bari a mata d'inkin wurin se kuka takeyi tana cewa tsoro takeji, Dr. Samha aka k'ara baiwa damar dubata inda kai tsaye tace za'a iya barin wurin hakan yankuwar bekai ace se anmata d'inki ba, sabida ba wani sosai bane daze gagara warkewa da ruwan d'imi, a cikin satima idan jikinta yanada kyau zeyi healing da kanshi, da wannan aka barta akan baza'a mata d'inkinba.....Anty Fareeda ta kalli Maheer sunbar hafsat tana bacci sun koma office d'in fareeda tace dashi
"Maheer meya kaika? Wane haukan ya kaika hayayyak'ewa mace haka, bazamuce baka saba ba tunda yake kanada mata harda arziqin 'ya, meye na yuwa mace wannan hawan k'awarar?...." Lokaci d'aya kunya ta dabaibaye Maheer yace
"Anty Reedah ba haka bane ba wlhy bansan ma anyi ba, bani acikin hayyacina sedaga baya" D'an murmushi tayi bataso ta k'ureshi ta kula kalaman suna masa nauyin fad'a
"Babu damuwa, amma kanada aiki, dan yarinyar seta dinga gudunka yanzu kam...kuma ka sani seka barta ta huta koda na one month ne, and nxt time plss kamata a hankali, hanyar budurwa komai yawan shekarunta se'a hankali ake mata wannan dakayi yanzu, a hankali zakabi da ita idanma tanada k'arancin ni'ima seka nemi wata hanyar ta sauk'ak'a mata, barema ina zancen saukar ni'ima ga yarinyar datake a tsananin tsorace, Dr. Samha tace ko suman datayi tsorone, dan Allah ka rik'a yin komai a hankali, lastly kuma kaida Anty Nasara kasan dai seta gayawa matar ka ko?"
*************
"Ke Nasara waime sa koda wane lokaci kikeyin abu kamar wata k'ank'anuwar yarinya ne? Tayaya zaki kalli idon k'aninki kice masa yana zina?" Cikin takaici ta furta
"Yaro da matarsa dan rashin tarbiya seya kawo mace cikin gidan ubansa ya hayayyak'e mata har haka, inada yak'inin cikine da ita Allah ya toni asirinsu"
"Waike bakida hankaline? Toki sani Hafsat Matar Maheer ce, ubanku da kanshi ya d'aura auren su, yace kar a gayawa kowa, ban gaya kiki bane ba sabida nasab halinki sarai, kuma ko yanzu akul d'inki kika gayawa matarsa wannan maganar kotajin wai matar sace Hafsatun" wara idonta tai
"Matarsa kaman yaya?" Dak'uwa ta mata da hannunta
"Kamar yanda nake mata a wurin ubanki, ki sani aurensu yafi watanni shida, watak'in yaune ya samu keb'ancewa da matarsa harya mata aika aika haka" tana tab'e baki na bak'in ciki tace
"An nunamun umma banida muhimmanci a gidan nan, ace anwa k'anina aure na biyu banida labari, to narigada na gayawa islam komai a waya wlhy....." Zaro ido waje Umma tayi😳😳😳 kantace wani abun wayanta ya soma ringing, a hankali ta d'aga ganin Fareeda ce ta kara a kunne
"Umma mun shiga uku, wlhy islam tazi har asibiti anwa Hafsat Allurar bacci ta shak'eta gatanan yanzu ba kanta, sanda tazoma bama nan nida Maheer yanzu bamusan abinyiba, ga jikinta cen ya rikice da k'yar aka k'waceta a hannunta" Allah umma tasoma kira kanta ce
"Ganin zuwa wurinku" ta mik'e ta sab'a hijab, Nasara ma ta biyota....
"Karki biyoni wlhy, karma ki sake zuwa inda nake!!!!
Mom Nu'aiym
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
44
Se jijjigata yakeyi amma ko motsi suma cirko cirko sukai a kanta babu me magana, ganin haka bazata haufa masa d'a me idoba ya bashi damar kwasarta zuwa asibiti, jalkabiya kurun ya zura, a tsaye ya kwana ranar dankuwa likitoci suna kanta....Allah sarki k'addara ta riga fata bincike ya nuna kan natane har lokacin da 'yar matsala wanda inhar ba'a dena b'ata ranta ba bazata tab'a dena suman ba, kuma idan anyi nasarar samun rayuwarta yanzu ba lallai a samu rayuwar tata wata rana ba, sabida haka suna shawarta su akan su dena yin duk wani abu daze jawo b'acin ranta ko yayane, amata abinda takeso, Dr. Ya k'ara da cewa akwai ulcer a tattare da ita wanda yanada yak'inin rashin yin breakfast ne da wuri ya janyo mata shi, anan ma yabada shawar wari sosai, hankalin Maheer ya tashi akan wannan ciwon da haka akayi sunan a tsaitsaye babu me kwanciyar hankali se su islam da a yanzu fatanta befi ace Nanuwa ta shek'a lahira ba.....wuni d'aya cur tana kwance an mata alluran bacci, maheer zaune a bakin gadon datake ya kifa kanshi akan gadon, a yau har Abba ya kira yake gaya masa matsalan Nancy cikeda damuwa Abba ya mata adu'a, yayi fad'a sosai akan akula da ita......
Hannunta dayake rik'e dashi ta matsa a hankali, da sauri ya d'ago kanshi ya kalleta, mik'ewa yai har lokacin hannunsu yana had'e da juna, su sophie ma suka taso dukkansu suka sunkuyo suna kallonta, murmushi ta sakarwa Maheer ta lumshe idanta, shima yana murmushi yace
"Swthrt sannu, sannu kinji kin tashi, yanzu inane yake miki ciwo?" Matse hannunshi ta k'arayi
"Ba komai amma inajin yunwa sosai, da kaman kuma tea nakeso nasha" Kanajin muryanta kasan tanajin jiki, daurewa kurun takeyi, kallon shauty yae
"Shauty dan Allah ki had'o mata tea da sauri, ki had'o kinji" Shagwab'e fuska tae
"Yaa maheer ka d'agani in tashi zaune naji duk jikina ciwo na gaji da kwanciya" A hankali ya d'agata zaune ya zauna a bayanta ya d'aura bayanta a saman faffad'an k'irjinsa, ya zagaye ta da hannunsa d'aya a haka har aka kawo tea d'in da kanshi ya bata tasha, sekuma ya bata magani kai tsaye tayi bacci ajikinsa, wani sanyine ya ziyar cesa har ransa sabida ta bashi tausayi.....
*****************
*Bayan sati uku*
Shirin dawowa sukeyi sabida su Nancy sun gama exams, tun daga ranar da aka sallamota asibiti bata k'ara zuwa kwana d'akin Maheer ba, sedai takan masa dukkanin abinda yakeso, gudun b'acin ranta ya sanya be tashi mata da maganar kwanan ba, a cikin hikima suke gudanar da soyayyar su dukkaninsu sunyi na'am da cewar k'aunar dasukewa juna ta samo asalaine daga indalla..
A hanyar shiga d'akinsa tayi mantuwa da caja wayarta gashi anata cewa sui sauri, shikuwa saurin yake ya fito sukai karo, kanta dake kallon k'asa ya daki k'irjinsa da sauri ta d'ago ta kallesa, se kuma ta shagwab'e fuska tawa kanta masauki a k'irjinsa had'e da dunk'ule hannunta takai masa naushi cikin wasa a k'irjinsa
"Shine kuma baraka kalla gabanka kana tafiya, so kake ka fasan goshi Hero?" Murmushi yayi ya zagayeta da hannayensa
"Am so sorry Swt hrt kinji, bansan kinzo ba kiyi hakuri" Tsalle ta daka ta sumbace sa a kuncinsa
"Karka damu Hero, sannu nima ban kula kana zuwa ba" Bata jira amsawar saba ta rab'a shi da bow legs d'inta tanata sauri ta zaro caja d'in ta ta fito......
***************
A b'angaren Ummul kuwa, kullum cikin sallan dare take da adu'o inta na neman tsari ta fauwalawa Allah lamuranta kuma da tsohon cikin ta take azumin nafila, tunanin Nana khadija ne yake neman illata mata rayuwarta, sabida akan Nanan ko abinci seta gagara ci, ta kasa cire tunanin 'yar akanta sabida batasan halin dasuke ciki ba, tadai Mayarda komai awurin Allah.
Ameenu ma yana cikin wani yanayi, ya tashi hankalinsa sosai, ya gagara d'aukar wani mataki, amma a yau yayi niyya da shirin tunkarar alhaj baba akan maganar matarshi.
*****************
A jirgi kowa yayi shiru tamkar ba tafiyar mutane da yawa ba, Islam, innan ta, sophie, shauty se kuma Maheer da Nancy, kujerar dake kusa data maheer itace ta islam, gefensu kuma sophie da Nancy ne, sophie ke gun window cen mak'ale se Nancy dake farkon kamar yanda maheer ma a farkon yake, jefi jefi sukan watsowa juna kallo dasu kad'ai suka san ma'anar sa a haka ahaka har suka sauka lafiya, inda suka kai mak'ura wurin k'ure islam dan kuwa tana kula da yawan murmushin dasuke sakarwa juna wanda bata gane kan saba....
****************
Gidan umma dukkansu suka sauka, acen akaci aka sha aka kuma wataya da hirar yaushe rabo, kowa yasha mamakin sakewar Nasara da islam, ga yaranta en mata harsu biyu ma sunzo, anty Fareedah da Nancy tamkar zasu cinye juna, Allah kuma ya had'a jinin Nancy da yarinyar Anty Nasara ta biyu da Nancy me suna Haneepha, se dare kowa ya fashe......su Nancy Umma se shagwab'ata takeyi wanda wannan ma bewa inno da islam dad'iba, har kanta ta d'aura akan cinyar ta tana mata shagwab'a, ita kuwa lokaci d'aya ta nemi kunyarta ta rasa, setake gani tamkar ta samu wata uwar ta cikinta.
****************
D'akin datake mallakinta ta zauna dama a gyare yake, ita kamma ta soma mantawa da nik'afi, kwana biyu da dawowar su, Bayan la'asar lokacin Umma batanan sunfita da anty Nasara da Fareeda, Maheer ya dira agidan, kai tsaye d'akin Hafsat ya shige ya sameta kwance tana bacci, sosai ta bashi sha'awa a yanayin shigarta wannan ne ya bashi damar d'are gadon ya kwanta a bayanta ya shiga shashafa jikinta, acikin bacci dabe jima da d'ibar taba taji alamun ana mata wannan abun, wannan ya sanya ta zabura ta ta mik'e zaune, juyowa tae ta fuskance sa lokaci d'aya ta sakar masa lallausan murmushi, kana tamik'e zuwa toilet, sanye ajikinta under skirt ne kurun sabida zafi sosai takeji an saba da sanyin london had'arine a garin shisa zafin sosai ya taso gadan gadan......kunna ac tai ta cire komai na jikinta ta ja under skirt d'inta sama ta kwanta kasancewar itada masu aikin sukai girki yau ta gaji....bakinta ta wanko sannan tazo ta d'auki cingom na kampanin orbit amma na waje ta sanya abakinta, zama tayi ta kwantar da kanta saman cinyoyinsa, ta zagaye waist d'insa da hannayenta
"Yaa Maheer nayi kewarka, jiya ban gankaba" shafa sumar kanta yayi
"Kiyi hakuri My princess, jiyan ina tare da Ameenu ne akan naganar yayarki, so bansamu kainaba se dare, sabida seda muka dangana abun ga Abba kuma kinsan ganin Abba wahala,appointment ma daya bamu wlhy kusan sati uku yace, gashi mune ma zamu sameshi mascow" jinjina kanta tayi
"To Allah ya shige mana gaba Hero" sunan dayake cewa seta gaya masa kenan shisa harta soma sabawa......." Shafa kanta ya somayi har wuyanta, cikin kunnenta yake tura yatsansa a hankali, tayi shiru tana jiyoshi yana mata wasanni ta lumshe idanta dai kawai, tako ina shafarta yakeyi shida kanshi ya soma fita hannaya cin sa, gashi sam be shiryawa yin komai da itaba seya jira umarnin Abba, Amma ya kasa hakura ita da kanta ya kula yau d'in son abun takeyi, besha wahalar kwanta da ita ya cire kayan jikinsaba, ya k'arawa Ac karfi ya kashe fitilar d'akin, sosai yake mata wasanni naji da fad'i Sanda yakai bakinsa kan manya manyan nipple d'inta kuka ma tasaka masa dabatasan na meye shikuwa a wannan lokacin bayaji akwai abinda ze dakatar dashi daga neman halalinsa ayau, Rarrashi da ban baki yasomayi mata yanata kissing nata dayi mata abubuwan daya tabbatar cewar zasu gigita masa duniyar ta, a hankali yakai harshensa kan cibiyarta me zurfi ya soma lasa yana zagayewa hannunsa d'aya yana kan mararta yana shafawa a hankali, se wani shigewa marar keyi tana masa wasu numfarfashi abun harya kai ga tasoma shafe masa kansa itama, soyayya aka gudanar me tsafta, sunkusa one hour suna wasanninsu seda yakai hannunsa gun manajanta ya tura acikin pant d'inta sannan ne ta tsorata ta soma rawar jiki, daban hak'uri
"Kayi Hakuri yaa Maheer kaji, wannan ma isa wlhy" shibemasan tanayiba, dan iya k'arfinsa ya zage wandon, Be b'ata lokaci ba wurin kai mata hari iya k'arfinsa sabida harga Allah a matse sosai yake, tunda joy stick d'insa ta isa a me martabanta yaji wani sanyin dad'i da ni'ima dabe tab'a jinsaba, se kuka take shi kuwa wannan dad'in ya sanya gaba d'aya ya rikice ya mata shigar sauri, hanyar daya samu ita ya daddage ya fatattake hafsatu baiwar Allah, tun tana kuka tana ban hak'uri daban baki hardai tayi shiru yadenajin motsinta, hafsat ta tsorata sosai a ranar tashiga firgiji mara iyaka, ga zabar rad'ad'in datakeji, maheer seda ya samu nutsuwa sosai sannan ya kwanta, surutu yake mata dabema san yanayiba harna tsawon 15 mns jin shirun yayi yawa ya sanyashi tarwatse idanuwanshi akanta, lallai ya aikata b'arna dan kuwa da sauri ya zabura, babu wadatar haske a d'akin amma hakan be hanashi hango bed sheet d'inta na cinderella da jini ba sosai dama ya wuce na kecewar verginity....mik'ewa yayi yaje ya kunna fitilar d'akin......."Innalillahi wa inna ilaihiraji'un" itace kalmar daya furta, da sauri yayo kan Hafsat, sam bata Numfashi ko kad'an ta sheqe, ga uban jini ga alama ya gama yanka er mutane, indai ba ciwon ta bane ya motsa, seda ya soma suturta kanshi cikin gaggawa sannan yai kanta, har ruwa ya saka mata masu sanyi amma ko motsi, kuka kawai ya somayi, ya kira anty Fareeda akan tazo cikin gaggawa yana d'akin Hafsat, kuma karta gayawa kowa, koda ya kira suna gate na gidan kuma Nasara sarakan muna furci tajiyoshi sarai, seta lafe seda Fareeda ta haye sannan tabi bayanta da sand'a, Ko Anty Fareeda ta tsorata da abinda ta gani ta kalleshi a hargitse
"Mahii meka aikatawa 'yar mutane?"
Jikinsa har b'ari yakeyi
"Ba abinda na mata Fareeda, dama kwanciyar aure ne bamu tab'a yiba kuma wlhy ko yanzu k'addarane ban zata ko kad'an haka zata faruba, Fareedah kofa numfashi batayi?" Kanta ta juya ta kunna fitilar wayarta ta haska k'asanta
"Innalillahi wa inna ilaihiraji'un, haba maheer, wane abu kayi haka sekace jahili, kaga yarinya a haka bazaka lallab'a ba, ka sumar da ita dan akwai sauranta amma wlhy se am mata d'inki, wannan ai haukane, haka aka gaya maka anayi?" Yana share kwallah
"Ki taimakeni anty Fareeda kar ummay taji, muje asibiti seta farfad'o hankalina ze kwanta" wani beyi maganaba acikinsu Anty nasara ta fad'o, Tafa hannu ta somayi ta juya tana kiran Umma itama umman da sauri tazo.....
Mom Nu'aiym
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
49
Anwa Ummul aiki susscesfully an cire mahaifan gaba d'aya ta huta, sedai bata farfad'oba dayike an mata alluran bacci....'yan biyu se cancara qarar yunwa sukeyi dole aka soma musu da madara karsu jigata......
********------********
Dukkansu sun kasa yin komai se kallonsu dasukeyi, hankalin Umman ya tashi ganin su a haka, tana zargi ko fad'a ne sukayi harya kai suka fad'a daga saman,sophie dake bacci acikin baccin tajiyo kururwan su wanda yasanya tai hanzarin tashi ta sakko itama, itane tai jarumtar zuwa ta d'aga hafsat amma t kasa, tadai kula tana numfashi amma sam bata cikin hayyacinta, ita kuwa islam jini ta hanci da baki...hankalin kowa ya mugun tashi da taimakon securities na gidan aka wuce dasu asibitin su Fareedah inda umman da kanta ta mata waya, cikin gaggawa aka karb'esu aka shiga duddubasu.....
Hafsat kam ciwon tame yai mugun tashi se kuma islam data samu targad'e a kafad'anta da kuma k'afanta se buguwa datai ba laifi tad'anji ciwo sedai ba masu hawalan warkewa bane...kowa yarigada ya gama cewan islam ce taja tajata fad'a suka fad'o a tare se tsine mata ake, har aka kwana biyu suna asibitin ga kuma babu wanda aka sallama, amma ita islam da magana da komai tanayi har tashima dukda raunin k'afarta yayinda Hafsat ke cikin tsananin rad'ad'i da azabar ciwo sabida har yanzu batamasan inda take se dogon bincike akeyi akanta kasancewar tanada matsalan da ake neman ciwo kanta tun farko.
*Bayan kwanaki biyu*
Kwanansu hud'u aka sallami islam, inda hafsat har lokacin shiru ko motsi, abincinma ta NG tube ake bata, sosai take shan wuya abubuwa sun mata nauyi a zuci........ Yau su maheer suka dira Niger ta jirgi suka zo a kano suka sauka, kai tsaye gidan islam suka nufa har ummul da Ameen, a d'ayan part d'in suka sauka gidan akwai tight security ya sanya suka sauka acen, beko lek'a wurin islam d'inba dama ya sanya kuku ya dafa abinci da komai ya fice, yana matuk'ar so yaga Hafsat, yana sani ya shareta be sanar mata zancen tafiya ba sabida yasan condition nata tabbas zata shiga damuwa.
A sukwane ya shiga cikin gidan, yaje d'akin umma batanan, ya duduuba parlor na sama dana k'asa bata ban. Kai tsaye ya juya d'akin Hafsat, ya d'anyi knocking shiru kanya tura k'ofar d'akin ya shige da sallama d'auke a labb'ansa, ganin ba kowa ya sanya shi juyawa yana tunanin ko tasamu sauk'ine sun soma fita, a k'ofar d'akin yaci karo da Gimbiya me aikin gidan, zubewa tai tana kwasar gaisuwa cikin k'aguwa ya d'aga mata hannu ya kuma ce
"Ummana da Hafsat fa?" Kallon shi tai.... Tana rik'e baki "Yallab'ai dama baka san abinda ya faru ba?" Gyaran tsayuwar sa yae cikeda mamaki, ko kan su taso yai waya da ummansa amma bata sanar masa komai ba, anty fareedah ma bayan ya iso sunyi waya amma komai batace masa ba
"Meyene ya faru kuma?" D'an jim tai batai magana ba seda ya daka mata tsawa
"Danla malama dake ake magan nace gayamun dalla dalla meya faru ne?" Cikin rawan jiki ga tulin munafurci na cinta, dan sarai taji uwar na gayawa k'awayen ta besan miyan da ake shaba tace
"Yallaba'i dama fa umman kane naji tana rok'an Anty hafsat akan wai su had'e kai acewa me gida bata sanka araba auren, injin umman wai bazasu barka ka nutsu ka samu kwanciyar hankali ba, kuma sannan islam ita takeda tsatso dakai dan haka ita ta hak'ura kawai dakai karka tsufa da wuri akan tashin hankalinsu, to daga sannan dai ban kuma jin d'uriyan anty Hafsan ba, sedai naji umman tanata dukan k'ofar d'akin ta tak'i ta bud'e se da yamma sosai Anty islam tazo tanemi ganin hafsat d'in akace tana sama, to dagacen dai dambe ya kaure a tsakaninsu suka gangaro daga saman nan har k'asa bame motsi, Alhamdulillah ita anty islam an sallameta jiya daga asibiti dan ta samu sauk'i ita anty Hafsan dai ko d'azu danaje asibiti kai abinci da driver gwanin tausayi ta hanci ake bata abinci" ta k'arashe maganar cikin share k'walla alamun tausayi" yama rasa mezaice mata ko kuma wane tunanin zeyi be tsaya cewa da ita komai ba ya sakko daga matattakalar benen da gudun fanfalak'i zuwa mota, body guard d'insa naganin sa suka bankad'e masa murfin mota kai tsaye convey suka rufa masa baya da kusan mota biyar tasace a tsakiya suka bar harabar gidan me k'atoton gate har round about ne aciki, tafiyan kusan mintuna uku kansuje gate nan take ha wangale kansa sukai waje...dama yanada guards nashi baya buk'atar yawon dasune sam yanzu ma akan Alhj Baba ne basusan ta ina ze bullo musu ba...kai tsaye office d'in farida ya wuce, beko wani tsaya knocking ba ya bankad'e k'ofar, ita da umma ne da mijinta suna tattaunawa, dukkansu mik'ewa sukayi tsaye ganinsa yace cikin sauri
"Fareeda Hafsat fa? Tana inane yanzu" labb'anta sun gagara sanar masa tana ICH (Intensive care Unit) tana kwatanto hankalin sabyanda ze tashi inhar itama d'azu da akai refering nata can tasha kuka shifa dake tsananin san matar sa? Ta gaza furta masa kalma d'aya kowa se kallonsa yake, tunkan tai Magana yaji zuciyar sa ta tsinke ya gagara tsayuwa zubewa a wurin gaba d'aya seda mijin fareeda ya rik'esa
"Ka kwantar da hankalinka matar ka tana nan, amma bazamuji k'warin gwiwar sanar maka ba harseka bamu nutsuwarka ka kwantar da hankalinka gaba d'aya....kallon sa kurun yakeyi baya ko k'iftawa tamkar ze cinyesa haka yakeji
" inajinka tana ina yanzu?" Seda Dr. Ya g'yara tsayuwarsa sannan yace "ICH" Mik'ewa yai tamkar wanda aka tsikara ya nanata kalmar ICH a bakinsa sekace me koyon magana, da riverse ya juya da gudu zuwa wurin baya ko ganin gabansa, dukkansu da gudu suka rufa masa baya, har suka isa an hanashi shiga se cizge cirge yaje yanda yaganta daure da ox da glass ita kad'ai batasan inda kanta yake ba, ya kalli umman sa
"Umma keda islam ne ko, kina kallo islam ta wurgo mun ita daga saman ita tanacen tana hutawa amma Hafsat na na nan tanashan bak'ar hawala ko, ummana nine fa mahee d'inki yaushe kika dena san farin cikina? Naji komai daya faru a wurin Gimbiya, yaya yarinya batada lafiya kuma kin sani, da aurenta kaman daga sama kice araba? Wlhy ni idan babu hafsat arayuwa ta banga amfanin taba ma, ita kuwa islam kinsan tayi attempting kisa daga farko yanzu kuma kin dawo kin bata damar ke b'ancewa itada Hafsat again, ga sauran abinda kuka ragemun nan a kwance, wlhy umma ban tab'a zata zakimun haka ba, amma shikenan" kowa yai shiru yana sake sak'e a xuci yayinda ya juya kurun zuwa gidan islam cikin rashin kuzari, har aka isa bema sani ba seda tukunna suka ankarar dashi k'arasowar tasu ya fito, kai tsaye ciki ya nufa yaci karo da 'yarsa a hannun maid ya karb'eta yanata masa wasa tamkar ba komai a ransa yayi missing d'inta sosai, islam dataji sallamar sa ta fito seta tsaya kurun ta kasa ce masa komai, bed room nashi ya shige ya kwantar da 'yar ya rubutawa islam takarsar sakinta ya fito da babyn ya baiwa maid d'in ya bita d'akinta, mik'a mata takardan yai ta gagara karb'a a gefen ta ya ajiye ya juya mata baya
"Ga takardar sakinki nan, ban sakeki dan bana sankiba, Allah ya sani akanki nasan meye so kuma har gobe ina sanki, sedai bazan zauna da macen dake iya yin kisa ba, 'yata kije da ita sekin yaye ta tukunna ,zan k'arb'o abata, dummanin abubuwan dake ciki Gidannan danke na siya ki tattare ki tafi dashi har motoci dake mallakinki, zan turo miliyan biyar a acc naki kimun renon 'yata, ki shirya da safe za'a maidaki sokoto" Wata uwar k'ara ta k'walla tahau magiya har waje ta bishi amma be saurare taba!!!
....\ko saki nawane akawa baiwar Allah, ko zaman ze k'ara dawowa oho.....muje zuwa
Pheey gobe da safe akwai wani inshaa Allah,inayinki tawan kina k'aunar littafinnan fiye da kowa dame rubutun gaba d'aya😀😀😀
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
50
Jikin islam har rawa yakeyi sanda ta dawo cikin gidan, takardan data barshi akan gado ta d'auka amma ta gagara bud'ewa, tunawan datai da umma me ya bata damar juyawa tana d'ingishi da k'afarta ko 'yarta bata tsaya karb'a ba ta juya a sittin, da kanta tai tuk'i zuwa asibitin da takardan a hannunta, bata tsammanin ganin kowa a ICH wannan ya bata daman zuwa office na fareedah dan kuwa anan ta barsu, koda taje kuwa tai sa'a suna nan, wurin umma taje ta durk'usa da k'afufuwan ta tana kuka
"Umma dan Allah ki tallafeni ki ceceni ki kuma agajeni, Maheer ya sakeni umma kinga takardan daya bani wai inaso zan yi kisa harso biyu, wlhy umma k'addarane ya fad'o damu nida Hafsat amma wlhy garin ceton tane ma nima na fad'o, ki cewa maheer ya taimakeni ya miyar dani d'akina wlhy shine farin cikina dan Allah kimun tallafi" Tunda Islam ta soma magana umman ke kallonta ta gagara koda motsi, ko ba komai ta tsorata da yanayin yaronta d'azu be tab'a mata kwatankwacin yanda yae ba d'azu hankalinta yakai k'ololuwar b'aci tama rasa me zatace, yanzu mezata cewa Abba idan yaji? Farida ce tai k'arfin halin karb'ar takardan ta bud'e ta soma karantawa da sauri wata wawiyar ajiyan zuciya ta sauke ta zauna dafe da kai kantace
"Saki d'aya ne Umma, dan Allah awa tufkar hanci, dan gaskia wannan ya zama hauka, daga faruwar abu bakada ilimi akanshi blindly kurin ka sako saki, an gayawa Maheer aure abun wasa ne wai? Ko kuma muya mayar shashashai? Ubanwaye ma yace dashi islam ta wurgo Hafsat d'in? Ita ta wurgo ta kuma suka fad'o a tare? Gaskia umma bakwa duba lamarin rayuwar maheer yanda ya dace abubuwa yakeyi gaba gad'i, ko zancen auren nan na hafsat haka yae iskancin nan yazo ya narke kuka amince masa batare dakoda jin ra'ayin yarinyar ba, wannan kurin ya isa ya haddasa fitina, tun wuri gwara a kirashi wlhy a nuna masa kuskurensa" Nisawa Umman tai kanta rik'o hannun islam
"Baze k'ara aikata wannan kuskuren ba inhar dai nice na haifesa, sannan ki koma gidan ki yanzu karnaji zancen kin tafi gidanku, karma ki gaya musu wannan mugun labarin, zanga maheer d'in ai" Godiya islam tayi sannan ta nemi komawa hanyar gida....
****------****
Maheer kai tsaye asibiti ya koma, Wurin da Hafsat take yaje ya tsaya wurin glass daze rik'a hangota, se k'wallan dake wanko masa ziyarar ba zata yake zubarwa, yayinda sakin dayawa islam ya masa tsaye a wuya, yana wa islam wani irin so dabaya tunanin amma tab'a halittar irin sa, tafiyar da yai yabar nata gida yasha wahalan rashin ta, har mamakin kansa yakeyi ya daurene kurun sabida yanuna mata iya karta, yanaji ajikinsa idan yaje gidan zuwa anjima ze dakatar da ita akan tafiyar da tai niyan yi....ya kasa barin hafsat ne tausayinta yakeji kamar me, baiwar Allah tun tasowar ta a wahala take har yanzu...yana tsaye a wurin ya kusa da sauyawar yanayin kwanciyarta alamun ta motsa, be b'ata lokaci me tsawo ba ya juya zuwa officr na Fareedah don sanar mata acen ya tarar dasu rai a b'ace, umman ma ta had'a fuska be damuba ya gayawa Fareedah a gaggauce suka fita zuwa ICH d'in..
Dr. Sam yarigasu isa wurin sabida shi dama yana aikin yamma ne, taimakon gaggawa ya bata ganin tayi regaining conciousnes nata, dama sun bada 24 hours ne idan bata farfad'o bama suna ganin se wani ikon Allah, idan kuma ta farfad'o Alhamdulillah....to 1 hour ya rage 24 hours din ya cika shisa ma yazo dubata, yaji dad'i sosai ganin ta farfad'o sedai batai masa magana ba, se binsa da kallo takeyi haka aka hana musu shiga su Maheer Fareeda ne kurun ta samu damar shigowa inda taketa murna dan suna shirin fidda rai da ita ne..
****----***
Alhj Baba ba k'aramun tashin hankali yake cikiba, ganin babban mutum ya matsa lamba akan anemo masa shi, Abban Maheer ya matsa matuk'a akan neman sa, wannan ne ya sanya ya gudu daga Nigeria gaba d'aya zuwa Ghana tafiyan dabesan ran dawowa ba sabida da asirinsa ya tonu gwara a tsinta gawar sa......Ga cutar dayawa d'an uwansa (Mahaifin Ameenu") sabida rikon amanar aminun ya bashi amma yaketa hallaka masa 'ya'ya yasan hakki kadai seyaci qaniyar sa.
Su ummul kuwa ita da Ameen kamar su cinye junansu, jin kansu sukeyi tamkar sababbin had'uwa duk motsi idanshi yana kanta, Neman iyayen Naja ya sanya a gaba kuma inshaa Allah ze gansu ne sedai bashi da kanshi ke neman nasuba ya sanya ne amasa bincike.
****-----***
Maheer yasha fad'a sosai a wurin Umma, kuma Hafsat da bakinta ta fad'i yanda komai ya kasance tsakaninta da islam, hasalima islam ta fad'one garin ceton ta daga fad'owa ita, yaji haushin kanshi na yanke hukunci cikin fushi kuma batare da buncike ba ya baiwa islam hak'uri inda yai shirin ganin ya had'e kan matan sa da yardar Allah kuma baze k'ara baiwa wani damar daze shiga tsakanin suba...
Hafsat dai ana asibiti har lokacin jiki se adu'a yak'i dad'i an kasa gano bakin zaren... Maheer duk a rikice yake, yasha mamakin islm ma dabata masa fushi ba, dan kuwa dayaji musababbin faruwar abun duk seyaji kunya da nauyinta ya matuk'ar kamashi...
Dafe kai Maheer yai, lamarin na Hafsat yana d'aure kanshi, se tayi kaman taji sauqi da rana se kuma dare nayi zazzab'i ya kuma lullub'eta, ga komai taci amai take kelamawa, bata masan ganin abinci, tayi wani mugun fari ta rame sosai sumar kanta kurin ke k'ara tsayi se uban goshi, islam ce keta kaikawo a wurinta tunda yake Ummul ba lafiya ne da itaba, ita kanta Baba Azumi da Naja ke kulawa da ita
"Yanzh Anty Fareeda meye mafita, kodai zan kwashe tane mu tafi london a dubamun ita yanda ya dace, naga anan komai nata sekuce normal amma ciwo yak'ici yak'i cinyewa yarinya dukta rame, nida akace mamanta zatazo ma dukse naji kunya wlhy, kartazo taga 'yarta kaman ana d'ebanta ana miya" D'an murmushi Fareedah tai dabekai zuciba ta kalleshi sosai
"Maheer Hafsat fa cikine da ita, alamomi da yawa sun nuna mana hakan, bana tunanin wanin ciwon ne daya wuce haka, yanzu haka d'azu da kaina nakai jinin ta lab, za'a mata syrum pregnancy test" kallonta yai da murmushin yake shima
"Kai Anty Reedah ni se kika bani dariya wlhy, ciki dai sekace almara, nifa tunda taji wannan ciwon rabona da ita, abu so d'aya kurin" kan tai magana an soma knocking na k'ofar office d'in izinin shigowa ta bayar aka shigo, Lawal ne me aiki a lab datace idan result ya kammala ya kawo mata...karba kurun tai ya juya tana dubawa ta soma dariya
"Lallai k'anina ka iya aika aika, yanzu yarinya ko amarci batasan dad'in saba zaka mata haka, cikin ma me wahala irin hakan nan, to kadai gani cikin satinsa shida da kwana hud'u" wara idanshi yae wato wannan sati ukun datai a asibiti duk azaban cikine, amma be tab'a kawowa kanshi hakan ba ciki da wuri haka...shi d'inma dariya yai
"Anty gaskia wasane" Dariyan taci gaba dayi
"Wlhy ba wasa bane ba, ni dariya ma kake bani wlhy, koda yake tsarin Allah ya zarce na kowa, Allah ya bata lafiya yanzu kam se a duba cikin, sabida tayita shan magungunan dabe dace da itaba" haka suka zanta sosai akan hakan,yamma aka kaita hoto ciki lafiyan sa qalau, gogar tamu dama ashe ta fahimci hakan sabida al'adanta daya dena zuwa tun bayan da suka sadu da Maheer batai magana bane sabida kunya, ranar taga tarairaya kuwa, umma ma da abin yabata kunya ai barin d'akin tai gaba d'aya..
********---********
*Bayan wata d'aya*
Tsakanin Islam da Maheer babu wata damuwa, hafsat kuwa tana gidan umma gashi kuma hutu ya kusa k'arewa, umma ta hanashi matarsa wai batada lafiya koda yake hakanne, ganin ummul ba k'aramun dad'i yawa Hafsat ba, har kukan dad'i tai mara iyaka.....dukda yake ummul tabi hasken *WATA FUSKAR* ne dake k'ark'ashin fuskar Ameen me tsananin duhu ada ta cuci kanta da kanta, hakan baze hanaka tausayin taba ainun, ga k'uruciya ga rashin mahaifa, dama Allah yasota da idan Rahama tanada yara har uku sedai fatan Allah ya raya mata su.....
*Bayan wasu en kwanaki*
Har lokacin babu alamar umma zata sakowa maheer matarsa, wannan ne dalilin dayisa sam ya kasa dukuni, zuwa yai gidan Anty Fareedah ya sanar mata shifa yanason matarsa ta tare agidanta kan su koma, hutu ya k'are tawa umman magana, tasha dariya kanta kora masa bayanin damuwarta akan hukuncin Abba akan Anty Nasara, nan suka yanke shawarar baiwa Abban hakuri, hakan kuwa akayi yace ya wuce su kuma suka d'unguma zuwa gidan ta, acen kana ganinta kasan taji dad'in ganin su sun jima sosai suna magana har shawarwari suka bata da kuma Nasiha taji dad'in hakan ta sakko daga mugun dokin data hau na cewan setaga bayan auren maheer da 'yayan talakawa, ta bashi hak'uri sosai inda tace da safe da kanta zatawa Umman maganar Hafsat har gidan zataje.....
*************
Umman tacene bazata baiwa Maheer Hafsat ba seya mata kayan lefe, shikuma shap ya manta da hakan aikam shida yayyinsa mata suka zage suka nunawa dala rashin mutunci mara k'arewa ciki kuwa hadda kyautar motoci k'waya biyu.......gidansu na sokoto suka kai kayan gaba d'aya inda Baba iro se washe bakinsa yake inda Baba azumi da ummul ma tazo da en tagwayenta, Ameen da Maheer ana cewa Ameen Ameer, Maheer kuma Babul kasancewan yafisa jiki, haka nan Ameen yaji sakawa yaran sunayen nan nasa dana abokinsa awani bangaren kuma aminin sa😀😀.....
Koda akace za'a kaita gidanta ranar wata juma'a tasha kuka, k'arara ta nunawa Anty Fareedah tsananin tsoron datakewa maheer, rarrashi sosai tasha daga gunsu itada Anty Nasara kan daga bisani a kaita gidan ta, cikeda mugun tsoro take zaune agidan, sanda ya shigo ma sosai ya mata kamada yanda take ganin mazan littafi na zuwar ma matayensu, jikinta se karkawa yakeyi sanda ya zauna a kusa da ita, be b'ata lokacin saba wurin aika mata kyakyawar ajiyan zuciya lokaci d'aya kuma ya sauke kyakyawan ajiyan zuciya, batace masa komai ba harya kai hannunsa saman mararta, d'an cikinta ya soma danno kai yana murmushi yace
"Amarya inaso zan gaisa da babyna, yaya kenan" Bata gane me yake nufi ba, amma seta tsinci kalamansa da sanya fad'uwar gaba!!!!
"Kafasan ina ciwo ko, kasan banida lafiya ya maheer, yaya kakeso jik.......bata k'arisa fad'an maganar taba ya manne bakinsu wuri d'aya, tun tana tattureshi har yae nasaran kashe mata jikinta, aikuwa lafiya lau yabi da abarsa yau dukda yasha kuka kam sabida a tsorace take amma bata wani ji zafi bama. Seda komai ya lafa ya bita da kallo, mata ko wacce da baiwarta a rayuwa, idan yace islam rake ce sarkin ruwa da zak'i mexe cewa hafsat? Yama rasa wacce ce acikin matansa zece tafi wata abu d'aya ya sani dukkaninsu suna matuk'ar gamsar dashi, kuma alfahari dasu, acikin mazaje bakowane yakeyin tsantsar sa'ar da yae ba......" Sannu Beautiful yau dai ba zafi ko?" fuskarta da rufe da tafukan hannayenta duka biyu alamun jin kunya matuk'a.....
************
Rayuwar girmama juna akeyi tsakanin dukkanin ahalin na Maheer, tubdaga kan gidansu har kowa ma, Sophie da Mahal auren su ya kusa ga cikin hafsat ya tsufa, shauty ma tasamu wani saurayin daze aureta yaron aminin mahaifinsu cikin kwanciyar hankali suke zuba love wanda atare gaba d'aya za'a ha'da ai bikin, su dama daga wannan hutun sun kammala karatun su.
Lafiya lau Hafsat ta haifi yaronta namiji me kyau, da tsananin kamanni da maheer ko kadan be dakko taba... Murna awurin maheer ba'a magana sam...yaro yaci sunan Abba ana kiran shi da Abbi..
*Bayan shakaru biyu*
Babu shakka zaman lafiya yafi zama d'an sarki, yanzu kam islam da Hafsat amintarsu ta k'ara ta ninka ta dawo fiyr ma da da, bazaka tab'a cewa sud'in kishiyoyi bane, a london duk sun kusa kammala karatu islam dai ciki har yau shiru ga babu an girma haka Hafsat ma, maheer anyi k'iba sosai sejinsa yakeyi wasai sabida ya had'e kan matansa ababen sansa.
Alhj Baba dai Anyi neman duniya babu labarinsa, har yanzu Allah shikad'ai ya baiwa kansa sanin inda yake kai jariran dayake garkuwa dasu an hakura ma an shareshi tunda yake yanzu ummul dame gidanta suna zaune kalau.
Naja kam babu labarin iyayenta, da wannan Ameen ya aureta tazo ata biyu, dole ummul ta hakura tunda kuwa batama haihuwar yanzu, wannan shine aminta da *WATA FUSKAR* dukda yake k'addara tarigayi fata dama.
*Tammat bi hamdillah*