A chan 6angaren memartaba koda yana a kwance ammah har a lokacin maganarsa d'ayace shidai yarima, ahaka yasa aka ware kud'i masu yawa yace agyara ma suhail d'insa part d'insa dan yana ji a jikinsa zai dawo garesa, kowa ya d'auka magagin ciwone har anshare maganar saida sukaga ran memartaba yana shirin 6aci sannan akasa akafara yi masa gyara.
Yanzu mulkin hannun waziri suka damk'asa dan bawani mai kwanciyar hankali a cikin 'ya'yansa, gabad'aya family d'in abubuwa goma da ishirin sun had'u sun cakud'e musu, kullum maganar d'ayace shine memartaba ya amince aje ayi scanning d'in ammah ya k'i saidai ruwan addu'o'i da malamai suke aiko masa da shi ake bashi yana sha, masallatai ko duk sallah sai sunyi ma sarkinsu addu'a dafatan Allah yatashi kafad'unsa.
Yau ma kamar kullum 'ya'yansa ne zagaye da shi daga gefensa dada ce, cike da damuwa sultan ahmad yaruk'o hannun mahaifin nasa yace ranka yadad'e kataimaka ka amince muje ayi scanning d'innan kaga gabad'aya hankalinmu atashe yake babu sauran mekwanciyar hankali dukkanmu nan a k'ark'ashinka muke burinmu d'aya shine muga kasamu sauk'i.
Murmushin k'arfin hali memartaba yayi sannan ahankali muryarsa tana fita dakyar yace Ahmad kucigaba da yi min addu'a in da rabon intashi toh zan tashi domin waraka ta ubangiji ce.
Dada fashewa tayi da kuka tace hakane ranka yadad'e ammah ai ubangiji bai safkar da cutaba saida yasafkar da maganinta dan Allah kataimaka aje asibitin kaga bamu kad'aiba hatta sauran mutane hankalinsu atashe yake.
Cikin dauriyar ciwo memartaba yace shikenan na amince muje ammah ubangiji ya gama tsara komai akan lamarinsa.
Cike da jin dad'i tare da neman gasgata kalmar da kunnuwansu suka jiye musu nan suka shiga kallon juna suna murmushi.
Sultan Abbas ne yace dagaske ya amince muje?
Shima sultan ahmad murmushi yayi yace nima kusan abinda kunnuwana suka juyo min kenan.
Dada share hawayen fuskarta tayi tace Alhmdllh yanzu kuje kusa ashirya motocin da zamu tafi da shi, asibitin suhail kawai zamuje.
Cikin jin dad'i sukaje sukasa aka shirya motoci nan aka fito da memartaba aka shigar da shi motar da aka tanada dominsa Dada kawai tashiga cikinta.
Su kuma cikin d'ayar motar suka shiga ahankali ake tuk'in duk inda aka wuce talakkawa d'aga masu hannu suke suna ma shugabansu fatan samun lafiya.
Koda suka isa Prince.S hospital, cikin gaugawa akazo aka tarbesu dan motocin kawai da suka gani yasa sukagane daga inda suke,
Dr khalil da sauran manyan likitocine tsaye akan memartaba a cikin wani k'ayataccen room suna ta bincike bayan anyi masa scanning d'in, inda shi kuma yake ta baccinsa.
Gabad'aya hankalinsu ya tashi saboda basusan yadda zasuyi sushawo kan matsalar ba nan sukayi 'yan maganganunsu.
Dr khalil ne yafito jiki ba k'wari yanufi inda su dada suke zaune, ganinsa yasa gabad'ayansu suka mik'e suna tambayarsa jikin memartaba.
Murmushin k'arfin hali yayi yace Alhmdllh dasauk'i sannan yasamu waje yazauna, ya umurcesu da suma suzauna bayan sun zauna, kallonsu Dr khalil yayi sannan yace Alhmdllh mun gano abinda yayi causing d'in ciwon cikin ba komai bane face 'yan hanjinsane da wasu suka nad'e,
Gabad'ayansu saida gabansu yafad'i sukace 'yan hanjinsa sun nad'e?
Ganin yadda hankalinsu yatashi yasa Dr khalil yad'anyi murmushi yace kar kudamu ba wata babbar matsala bace tunda daman ana samun masu shiga wannan condition d'in kuma suna rayuwa saidai ta hanya d'aya za'a bi.
Gabad'aya suka had'a baki wajen cewa ta wace hanya kenan?
Ajiyar zuciya yasafke sannan yace ta hanyar yin theatre.
Sultan abbas ne yace toh Dr indai ta hakan za'a samu sauk'i toh mu relatives d'insa mun amince ayi masa kawai.
Jinjina kai Dr khalil yayi yace abbah saidai wani hanzari ba guduba jinin memartaba ya hau sosai babu yadda zamuyi mu iya yin wannan aikin batare da jininsa ya d'an yi low ba.
Salati suka sanya cike da tashin hankali, dada kuka tasaka tace yanzu khalil babu yadda za'ayi a iya yin komai?
Cike da jin tausayinta yace ranki yadad'e kar kidamu zamu duba mugani.
Yauwa Dr dan Allah kubincika sosai.
Dr khalil yace kar kidamu ranki yadad'e zamuyi iya bakin k'ok'arinmu.
Yafuto sultan Ahmad yayi da ido sannan yamik'e yace ina zuwa.
Saida yafita sannan sultan Ahmad yamik'e yabi bayansa.
A office d'insa suka je, bayan sun zauna Dr khalil kallonsa yayi cike da damuwa yace daddy adai cigaba da yi masa addu'a dan jininsa ya hau over, kuma a wannan condition d'in da yake ciki baikamata ad'au lokaciba batare da anyi masa aikinba, ammah a yanzu zamu d'aurasa akan wasu drugs tsawon kwana ukku idan har jinin baiyi low ba toh saidai afitar da shi abroad.
Innalillahi wa'innah ilaihiraji'un daddy yashiga nanatawa cike da damuwa.
Dafe kai Dr khalil yayi kamar mai tunani sannan yace yauwa akwai wani mai irin wannan condition d'in da aka kawo mana bamuyi aikinba sai dagabaya akace mana ankaisa a wani gari wani likitane yayi masa aikin saidai ban tambayi wane gari bane ammah gaskiya ance yanzu haka mutumin yana nan lafiya lau ya warke.
Cike da damuwa sultan ahmad yace dan Allah khalil kataimaika kagano wane garine inyaso sai muje.
Murmushi Dr khalil yayi yace insha Allahu daddy zan bincika yanzu dai bari inje infara kawo drugs d'in da zai fara amfani da su mugani, Indai har akayi kwana ukkun bai safkaba sai kutafi chan.
Jinjina kai daddy yayi cike da gamsuwa da maganar Dr khalil yace Allah yashige mana gaba.
Ameen,,cewar Dr.
Sannan suka tashi suka fito tare inda sultan ahmad yakoma wajensu dada yai musu bayanin rik'esu da za'ayi tsawon kwana ukku ad'aurashi akan magani, ammah bai fad'a musu sauran bayaninba gudun kar hankalin tsohuwar tasu yatashi sosai.
Haka Dr khalil yaje yakawo drugs d'in, tun daga wajen d'akin dogarawane aka zuba suna gadinsa, sultan ahmad ne yace zai dinga kwana da mahaifin nasa ahaka su dada suka amince suka koma gida.
Kulawa sosai memartaba yake samu daga ma'aikatan asibitin ba a awa d'aya batare da anzo anduba lafiyarsaba, abinci dakyar ake samu yana d'an ci kad'an kafin yasha magani, su dada kullum suna hanyar asibitin sai dare suke komawa.
Mutanensa dadama sunzo dubasa dan ma ana hanasu shiga wajensa saboda ba aso ana damunsa dayawa.
*BAYAN KWANA UKKU*
Nan likitoci suka k'ara taruwa akan memartaba aka k'ara bincikawa ammah har a lokacin jinin nasa bai yi wani low ba saidai d'an ragewa da yayi kad'an.
Gabad'ayansu hankalinsu ya tashi, nan Dr khalil yakira sultan ahmad da sultan abbas cikin damuwa yasanar da su,
Su dukansu hankalinsu ya tashi, ganin haka yasa yace ammah Alhmdllh na binciko garin da kwararren doctor d'in yake ance min garin Abuja saidai sunce bazasu iya tuna sunansaba ammah yana aiki a babbar asibitin garin, insha Allahu inaji a jikina za'a dace idan akaje chan.
Cike da gamsuwa suka ce insha Allahu zuwa gobe zasusa ayi masu komai sukama hanya dan yanzu ma dare ne kuma sunaso suyi shirye-shirye saisa bazasujeba a lokacin.
Dr khalil yace Allah yasa adace.
Nan sukaje suka sanar ma dada akan batun zuwansu jihar abuja, saida ta jinjina ma lamarin sannan tace toh shikenan Allah yakaimu goben yanzu muzo mutafi gida muyi 'yan shirye-shiryenmu.
Koda suka koma gida kayansu suka shirya nan sultan abbas yaje yayankar musu ticket, su sultana bilkisu da sultana sadiya sunso subi aje dasu dada tace a'a subari sai daga baya sai suzo ammah yanzu in suma sunbi wa za'a barma gidan.
Haka suka hak'ura suka zauna tare da yin fatan Allah yasa adace.
Da dare koda waziri yashigo duba jikin memartaba, rik'o hannunsa memartaba yayi cikin muryarsa da bata fita sosai saboda zafin ciwo yace ga amanar gari da talakkawana nan na damk'a maka.
Rik'e hannunsa waziri yayi kwallah duk tacika masa ido yace na amsa ranka yadad'e Allah yabani ikon cikawa kaikuma Allah yabaka lafiya.
Cikin jin dad'i memartaba yayi murmushi tare da maida idanunsa yalumshe.
Wanshe kare tun dasafe motoci kusan guda goma sukayi layi suna jiran fitowar su memartaba, wajen k'arfe goma suka fito, inda su sultana bilkisu sukayi musu rakiya har airport, inda dandozon mutane suke tsaye ahaka suka shige jirgin mutane na d'ago musu hannu tare da addu'an Allah yaba shugaban nasu lafiya, saida sukaga tashinsu sannan kowa yakoma gida.
*GARIN ABUJA*
Suna isa garin nan sukatarar da motoci da shi kansa sarkin garin tsaye suna jiran isowarsu, kasancewar daman tun jiya sun sanar da shi akan zuwan da zasuyi.
Cikin karamci da jin dad'i suka tarbesu daga nan suka d'unguma wani k'ayataccen gida da aka tanadar masu dan suzauna a ciki, sunso sufara wucewa asibitin ammah sarkin garin yace sufara zuwa su huta sannan.
Haka suka hak'ura saida sukaje suka kimtsa suka ci abinci sannan sukafito suka shiga motocin da sarkin ya aje musu aka jasu zuwa asibitin.
Koda suka isa yanayinsu kawai aka gani da motocin da suke ciki yasa aka gane daga inda suka fito, koda daman sarki kabir ya kirasu ya sanar da su akan zuwan sarkin gazban.
Tarbarsu akayi sosai inda aka wuce da memartaba a amenity, nan suka duba history taken d'in da ke cikin folder d'insa na chan garin, saida suka k'ara yi masa scanning d'in dan tabbatarwa nan kowa yai shuru.
Sultan Ahmad ne yasanar da su abinda Dr Khalil yafad'a musu akan wani mai irin condition d'in da aka ta6a yi ma theatre kuma BP d'insa yayi high.
Jinjina kai MD Dr Muhammad bashir yayi sannan yace shikenan zanje intuntu6i Dr S domin nasan shine kawai zai iya hakan.
Cikin jin dad'i sukayi masa godia nan yatashi yanufi office d'in Dr suhail da baisan wainar da ake toyawaba.
Lokacin da M-D yashiga zaune yatarar da shi yana research a cikin system d'insa.
Nan yamik'a masa hannu suka gaisa, bayan sun gaisa nan yake sanar da shi akan zuwan wasu da irin condition d'in da patient d'in yake ciki.
Shuru Dr suhail yayi na d'an Lokaci sannan yace zan iya ganin file d'in patient d'in?
Nan Dr muhammad bashir yayi waya, ba a wani dad'eba saiga wani Dr hannunsa rik'e da file nan yabud'o yamik'a ma Dr suhail, saida gaban Dr suhail yafad'i ammah yadake yana karanta history taken batare da ya duba sunan me file d'inba.
Saida yagama karantawa nan gabansa yai wani irin fad'uwa lokacin da yaga sign d'in Dr khalil, cikin sauri yajuya bayan folder d'in, baisan lokacin da saki folder d'inba lokacin da yaga sunan da yake jikinsa, nan gabansa yacigaba da dukan ukku-ukku tashin hankali yabayyana k'arara a fuskarsa.
Bai san MD yana masa magana ba saida Dr muhammad bashir yata6osa tare da cewa Dr S lafiya.
Ajiyar zuciya suhail yasafke cike da damuwa yace ba zan iyaba kusami wani yayi.
Kallonsa Dr muhammad bashir yayi cike da damuwa yace ammah ai an tabbatar min da cewa kaine kata6a yi ma wani mai irin condition d'in.
Dafe kansa yarima yayi yace ni ba zan iyaba kakyaleni.
Cikin d'aga murya Dr muhammad bashir yace haba Dr suhail baidace kace haka ba bayan aikinka ne kuma inaji a jikina zaka iya.
Mik'ewa suhail yayi tare da kife system d'insa yace bazan iyaba nafad'a maka!.
Cikin jin haushi shima yamik'e yace zaka iya man, dan haka umurni nabaka a matsayina na shugabanka dole kacika umurni na.
Wani irin kallo suhail yawurga masa yace shugaba kuma?
Murmushi Dr muhammad bashir yayi yace eh shugaba kaga indai kanaso kacigaba da aiki a k'ark'ashina dole sai ka bi umurni na.
Cikin d'aga murya suhail yace ank'i abi umurnin naka, kai bari kaji baka isa kasanyani abinda banyi niyaba, kuma dayake kaga su masu haline saisa kake rawar k'afa a kansu, ammah talakkawa wane irin wulak'ancine bakayi musu?
Cike da k'ulewa yace suhail ni kake fad'a ma magana haka?
An fad'a maka, shin ko ka mance lokacin da me irin case d'in yazo wulak'ancin da kayi ma relatives d'insa kafin ka amince? Ko ka mance da yadda ka wulak'antasu a lokacin da kud'insu bai cikaba? Ko ka mance da nayi musu aikin yadda kadinga nuna hakan bai burgekaba.
Matsowa suhail yayi kusa da shi yace idan ka mance toh ni ban mance ba kuma ni wajena da talakka da mekud'i duk d'ayane, dan haka a yanzu idan kai zaka iya yi saikaje kayi.
Dafe goshinsa Dr muhammad bashir yayi yace wai kai suhail maganar me kakeyi haka, kuma kasan ni ba cadre ta bane, ni doctor ne iyaka induba marassa lafiya kawai, kaiko har theater kanayi.
Key d'in motarsa yad'auka yace sai kasan yadda zakayi,,,yana fad'in haka yajuya zai fita.
Cikin d'aga murya Dr muhammad bashir yace suhail kar kasaki kafita daga hospital d'innan inkuma ba hakaba zaka fuskanci hukunci daga gareni.
Juyowa suhail yayi yakallesa a wulak'ance yace indai kana tak'ama da matsayin medical director da aka bakane toh daga yau kakoreni kaga idan zan daina numfashi kuma idan kana tunanin ina cin kud'ine a wannan aikin da nake toh nabaka satar amsa kaje katambaya kaji nawa nake kar6a, inaso kasani babu abinda zaku bani kawai dai ina wannan aikin ne saboda Allah,,,yana fad'in haka yajuya yaficce yabar Dr muhammad bashir tsaye.
Cike da mamaki Dr muhammad yakebin k'ofar da kallo sannan daga k'arshe yaficce yanufi office d'in Dr mu'az.
Yarima koda yafita motarsa yashiga yai mata key dagudu yafita yabar asibitin cikin k'ank'anin lokaci ya isa gida, lokacin da ya isa zarah tana bedroom dan haka yai kwanciyarsa saman 3 seater, jin kansa yake yana wani irin sara masa, ahaka yamaida idanunsa yalumshe zuciyarsa tana masa wani irin zafi.
Zarah da tafito daga bedroom tsaye tayi da mamaki tana kallonsa dan batasan dawowarsaba, takowa tayi ta iso inda yake daga gefen da yake kwance tad'an zauna tace ashe ka dawo.
Shuru yayi yakyaleta,
Am ko bacci zakayi? Cewar zarah.
Batare da ya bud'e idanunsa ba ahankali yace please kibarni banason damu.
Marairaicewa tayi tace toh bakada lafiya ne?
Bud'e idanunsa yayi da suka canza launin ja yai mata wani irin kallo da yasa zarah tamik'e ba shiri dan sak yarima suhail d'insa yakoma mata, maida idanunsa yayi yalumshe.
Juyawa zarah tayi takoma bedroom tana mamakin canjin da yarima yayi mata cikin k'ank'anin lokaci tunani tashigayi toh ita me tayi masa? Ko dai wani ya6ata masa a wajen aiki? daga k'arshe sharewa tayi tacigaba da hidimunta.
Dr muhammad Bashir ba ko sallama yashiga office d'in Dr mu'az kujerar da take opposite d'insa ce yaja yazauna fuskarsa ba alamun fara'a yace Dr wane irin marar kunyane kakawo mana muka d'auka aiki har yake ik'irarin fad'amin magana.
Cike da mamaki Dr mu'az yace ranka yadad'e wa kenan nakawo muku?
Cikin d'aga murya yace akwai wani bayan wanchan Dr suhail d'in.
Cike da mamaki yace suhail kuma anya shine zai maka rashin kunya?
Toh wa kake tunani bayansa duk matsayina a hospital d'innan ammah har zansa shi yayi theater yak'i bayan kuma abinda yazoyi kenan aikin, toh wlh kafad'a masa idan baiyi wasaba zan sa akoresa, su daman 'ya'yan talakkawa basu iya samun wajeba daga ya samu ana biyansa albashi mai tsoka shine har yai bakin da zai fad'amin magana ko yana tunani daidai yake da ni? Daman tunda naga take-takensa nasan bazamu zauna lafiya da shi ba dan ya cika jin kai.
Dr mu'az baki yasaki yana kallonsa har yakai aya sannan yace Dr suhail d'in da kansa?
Tsaki yaja cike da k'ulewa yace kai wai ma shi d'an gidan uban wanene a garin nan? Wlh in dai har baizo yayi abinda nasa shiba toh zanyi sanadiyar barin aikinsa.
Mik'ewa Dr mu'az yayi yana murmushi tare da jinjina kai yace ranka yadad'e kayi hak'uri saidai ina tunanin bakasan waye prince suhail ba.
Da mamaki Dr muhammad Bashir yake kallonsa yace prince suhail kuma? Wanene kuma haka.
Murmushi Dr mu'az yayi a karo na biyu sannan yace prince suhail tun daga zubinsa da yanayinsa da komai nasa yaci ace ka gane babu talauci a tare da shi dan ko hanyar talauci bai saniba, d'an sarautane gaba da baya dan shine zai kasance magajin garinsu, saidai nasan kanka zai d'aure da kaga ya zo yana aiki a k'ark'ashinka.
shuru yayi nad'an lokaci sannan yace prince yana da babban hospital wanda yake mallakinsa ne, kuma kud'in da yake rik'ewa per month ko rabinsu ba a biyanka, ko salary d'in da ake biyansa a nan ba shi yake cinsuba yana raba ma talakkawa mabuk'ata, girgiza kai mu'az yayi yace idan prince yaso takarda kawai zai rubuta ba kai ba hatta ni zai iya yin silar barin aikinmu, dan de bai d'au kansa komai ba saisa bai bayyanar da kansaba ga sarkin garin nan.
Dr muhammad Bashir zare ido yake cike da tsoro dan gabad'aya maganganun Dr mu'az sun firgitasa, shi kansa ya yarda da maganar saboda yanayin yarima kawai zaka kallah kagane cewa kud'i sun zauna masa.
kuma nasan prince yana da dalilinsa da yasa yak'i yin aikin, ammah prince mutum ne mai tausayi.
Ajiyar zuciya Dr muhammad Bashir yayi tare da mik'ewa yashiga zagaye office d'in sai chan yace mu'az meyasa tun farko bakaimin bayani akansaba?
Murmushi Dr mu'az yayi yace ranka yadad'e ai shine bayaso ana bayyanasa yanzu ma nafad'a makane dan naga kana da buk'atar sani tun kan katafka babban kuskure.
Jinjina kai Dr muhammad yayi yace tabbas ka taimaka min kuma nagode, ammah akwai wani taimakon da yarage kayi dan Allah kataimaka kaje kalallashesa yazo yayi wannan aikin yaceci rai wlh wannan shima daga royal family yafito duk ga danginsa chan suna jirana kuma sarkin garin nan yakirani yafad'amin zuwansu.
ajiyar zuciya yasafke yace shikenan zan kwatanta yanzu bari inje office d'in nasamesa.
Ai baya office d'in ina tunani ya tafi.
ohk bari inje gida ina tunani yana chan.
Dr muhammad yace dan Allah kataimaka kashawo kansa.
kar kadamu Dr zanyi iya k'ok'arina.
jinjina kai yayi yace Allah yataimaka.
Ameen Dr mu'az yace,,,nan suka fita a tare.
Tunda yayi horn aka bud'e masa gate d'in gidan a chan parking space yahango motar yarima, murmushi yayi sannan yaje ya aje tashi koda yafito cikin sauri yashiga gida, bai ko je part d'insuba direct yawuce na su yarima.
Knocking yayi zarah da take cikin bedroom ita tafito da mamaki taga yarima yananan inda yake nan tawuce taje tabud'e, ganin Dr mu'az yasa tayi murmushi tare da gaishesa.
Amsa matayayi sannan yace prince fa?
Juyowa tayi takalli yarima da baida alamar motsawa sannan tace gashinan, bismillah kashigo.
Da sallamarsa yashigo nan zarah tashige bedroom tabasu waje.
Kujerar da take kusa da yarima yaje yazauna tare da fuskantarsa yace prince ba dai bacci kakeba ko?
Yarima batare da ya bud'e idanunsaba yace ya dai?
Murmushi Dr mu'az yayi yace ranka yadad'e da ka taimaka ka tashi sai muyi maganar
Banza yarima yayi yakyalesa
Ganin baida niyar tashi yasa yace prince dan Allah kayi hak'uri da abinda yafaru tsakaninku da MD kataima kayi ma patient d'innan theater d'in domin yana buk'atar taimakonka.
Ahankali yarima yabud'e idanunsa yasafkesu akan Dr mu'az murmushin k'arfin hali yace shikenan ka gama?
Girgiza kai Dr mu'az yayi yace kayi hak'uri ranka yadad'e ban gamaba kawai dai ina neman alfarma ne koda banga patient d'inba bansan irin condition d'in da yake cikiba shi kansa MD a yanzu ya yi nadama akan abinda yayi maka.
Ta6e baki yarima yayi yace wannan matsalarsa ce dan ni banda lokacinsa, kuma da kake maganar patient wannan ba matsalarku bace kuma ga surgeons nan mezai hana kunemi wani tunda bani kad'ai bane.
Haba prince bansanka da hakaba please kataimaka ka.....
'Daga masa hannu yarima yayi yace please mu'az kana cikani da surutu kabarni zanyi nazari akai.
Jinjina kai mu'az yayi yace angama ranka yadad'e Allah yasa muji alkhairi ahuta lafiya.
Yarima batare da yayi magana ba yamaida idanunsa yalumshe, ganin haka yasa Dr mu'az yamik'e yafita yabar d'akin.
koda yafita kiran Dr muhammad Bashir yayi yashaida masa yadda sukayi, ajiyar zuciya MD yayi yace toh Alhmdllh zamu sauraresa,,,,bayan sun gama wayar zuwa yayi yasamu su sultan ahmad da suke jiransa cike da girmamawa yace kuyi hak'uri na tsaidaku.
cikin zak'uwa sultan abbas yace ya kukayi da Dr d'in da zaiyi theatre d'in?
Ajiyar zuciya yasafke yace ranka yadad'e kuyi hak'uri yanzu haka shi muke jira muji daga garesa.
Dr ahmad ne cikin sanyin jiki yace toh ko zaka rakamu wajensa muje mu dakanmu murok'esa.
Kar kudamu kukwantar da hankalinku insha Allahu munasa ran zai zo yayi masa domin Dr d'in baida matsala.
jinjina kai sukayi cike da gamsuwa da maganarsa sannan sukace Allah yasa.
Bayan Dr mu'az ya fita yarima wayarsa yad'auko yakira wani doctor da yake k'ark'ashin yarima nan sukayi magana.
_Comment_
*nd*
_Share_
_Sis Nerja'art✍🏻_
[5/3, 9:53 PM] Sis Naj Atu: 👑👑👑
_*YARIMA SUHAIL*_
👑👑👑
_*Written By~Sis Nerja'art*_
_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔
_Sak'on gaisuwa agareku Mamar rumaissa nd khadija mekano ina ji da ku irin sosai d'innan😍_
❤❤❤
_*Mum chubad'o muhammad a kullum ina alfahari da ke har cikin zuciyata Allah yabarmu tare😘*_
*PAGE* 6⃣7⃣
Su sultan ahamad suna a tsaye nan wasu doctors guda ukku sukazo zasu shiga room d'in da memartaba yake a ciki,,Dr muhammad Bashir ne yace ku kuma ina zakuje?
'Daya daga cikinsune yace ranka yadad'e Dr S ne yabamu umurni akan muje muyi ma patient d'in injection sannan musanya masa drip, ya ce sai zuwa gobe by 10am zai shigo.
Gabad'ayansu murmushin jin dad'i sukayi tare da furta Alhmdllh.
Haka suka shiga sukayi abinda aka umurcesu sannan suka fito, su dada nan aka basu izini sushiga suzauna ammah kar sudinga yin hayaniya saboda patient d'in ba a so atashesa daga baccin da yake.
Haka suka dawo bayan drip d'in ya k'are suka cire sukace kar asaki abashi wani abu yaci, nan ma da dare suka dawo sukayi masa wata injection d'in tare da k'ara gargad'insu kar abashi komai.
Yarima ko a ranar kasa samun sukuni yayi dan tun baiga yanayin da memartaba yake cikiba ammah hankalinsa ya tashi sosai musamman ma da yaga case d'in da yake tare da shi, dafe kansa yayi yana jin k'unci a ransa nan hawaye yashiga kwarara cike da tausayin memartaba da baida kamarsa bayan iyayensa.
Zarah da take gefensa ganin halin da yake ciki yasa tafashe da kuka dan tun d'azu yarima bai kalli ko inda takeba bare tasa ran zaiyi mata magana.
Kukanta yasa yadawo cikin hayyacinsa ahankali yabud'e idanunsa tare da share hawayen fuskarsa sannan yakalleta yace Zarah meyake faruwa ne? Bakida lafiya ne?
Cigaba tayi da kukanta tare da juya masa baya, murmushin k'arfin hali yayi sannan yajanyota a jikinsa yarungume d'ago mata kanta yayi yakalli cikin idanunta yace kifad'amin abinda yake damunki.
Rage sautin kukanta tayi tace ba kai bane kake ta shareni inma wani abu nayi maka ai sai kafad'amin inbaka hak'uri, kuma tun d'azun kake cikin damuwa har fa kuka kayi yanzu.
Jan hancinta yayi yace injiwa yace miki kuka nayi? Kidaina damuwa kidinga yi min addu'a kinji ko baby?
Turo bakinta tayi tace toh, murmushi yayi yace fushin ya isa haka.
Murgud'a masa baki tayi tace ank'i d'in.
Kwantar da ita yayi a k'irjinsa yace baby please muyi bacci.
Nan Zarah talumshe idanunta saboda daman baccin takeji ganin yarima ne a wannan yanayin yahanata bacci,
Shafa bayanta yashiga yi ahankali ahaka bacci yai awon gaba da ita, nan yazameta daga jikinsa tare da tashi zaune yadafe kansa,,,,,ya dad'e a zaune sannan daga baya yakoma yakwanta yana ta juyi ahaka bacci yai awon gaba da shi.
Wajen 8am yagama shirinsa kallon zarah yayi da take baccinta hankali kwance, zuwa yayi yai mata peck a kumata tare da shafar cikinta sannan yaficce batare da yayi ko breakfast ba.
Koda ya isa direct office d'in MD yaje lokacin MD yana zaune yana cike wasu files, ganin yarima yasa saida gabansa yafad'i dan fuskarsa ba alamun fara'a kujera yarima yajanyo yazauna muryar MD tana rawa yace am Dr S sannu da shigowa.
Wani irin kallo yarima yawurga masa yace Dr muhammad kar kayi tunani na shigo hospital d'innan ko zanyi theater d'innan saboda kai ne, murmushi yarima yayi sannan lokaci guda yahad'e fuska yace na amince zanyine saboda amfanina da na dangina, jiya ka fad'a min magana son ranka ammah na yi maka uzuri saboda bakasan wanene ni ba, ammah inaso kasani ya zama dole kakiyaye kalamanka akaina inbahaka zansanyaka kayi nadamar da batada amfani.
K'ut dr muhammad yahad'e yawu sannan yace shikenan dr s nagode sosai da ka fahimtar da ni.
Ta6e baki yarima yayi tare da mik'ewa yace wannan ya rage ruwanka, har ya fara tafiya sai kuma yajuyo yace am ban yarda akar6i ko naira d'ayaba daga garesu domin duk abinda ake buk'ata na bada ansiyo min sannan kuma nasaka kud'i a account d'inku na hospital zaka iya zuwa wajen accountant for confirmation, ammah idan nasaki naji kun kar6i kud'insu, girgiza kai yayi tare da murmushin mugunta sannan yace a lokacin zani nuna muku kalata zakusan wanene ni,,,,yana fad'in haka yajuya yafita yabar office d'in.
Cike da takaici MD yabuga hannunsa a table d'in da yake gabansa yace suhail ka 6atamin duk wani budget nawa,, dan dama abu guda yasa yashige gaba a lamarin dan yasan ba k'aramar riba zai samuba cikin jin haushi yamik'e yashiga zagaye d'akin cikin ransa yashiga tunanin maganar yarima yace anya mutanen chan ba wajen Dr s suka zagaye sukaje ba suka bashi kud'i? toh inma ba hakaba taya zai iya biya musu mak'udan kud'i,, chan kuma yace kokuma ai yana da taimako,,,cikin d'aga murya yace inaaa hakan ba zai ta6a yuwuwaba akwai dai wata a k'asa, fuuu yawuce yafita daga office d'insa rai a 6ace.
Yarima koda yakoma office d'insa system d'insan yazuba ma ido yana wani nazari a cikinta, dr mu'az ne yaturo k'ofan yashigo tare da yin sallama bai jira aka amsa masaba yashigo tsaye yayi wajen kan yarima yace haba suhail ammah baka kyautaba ashe memartaba ne su daddy suka kawo bayada lafiya shine baka fad'aminba har kana ik'irarin cewa bazakayi masa operation ba, toh na je na gansu.
'Dago kai yarima yayi cikin sauri yace mu'az bakadai fad'a musu ina nan ba dai ko?
Cike da mamaki mu'az yake kallonsa yace toh menene dan sun sani? Kawai dai kaci sa'a basu ganeniba ammah da sai nai musu bayaninka.
Ajiyar zuciya yarima yasafke sannan yace ka taimaki kanka ammah please kar kasaki kafad'a musu cewa ina nan kuma kar kabari sugane cewa nine wanda zaiyi theater d'in.
Mamaki k'arara yabayyana a fuskar Dr mu'az yace saboda me Dr?
Saboda wani dalili nawa,,,yarima yafad'a a tak'aice.
Dr mu'az har ya bud'e baki zaiyi magana nan yarima yai sauri yatari numfashinsa yace saura 30minutes inshiga theatre room please kaje kakar6o min constant foam kawakilce ni kaje kuyi agreement da relatives d'insa inkuka gama sai kakawo min inyi sing.
Toh kai saboda me bazakaje da kankaba?
Yarima duba agogon hannunsa yayi sannan yace kana 6ata min lokaci kasan dai na yi maka duk wani bayani.
Murmushi Dr mu'az yayi sannan yajuya yafita yabar office d'in.
Zuwa yayi sukayi komai da su sultan ahmad sannan yazo yakawo ma yarima foam d'in yayi singing.
Bayan yarima ya gama singing d'in kallonsa yayi yace saura abu d'aya yanzu dai kaje kasasu subar wajen sannan kasa nurse sutura min shi a theater room ganinan zuwa.
Haushi ne yakama Dr mu'az yace wai kai prince ni zaka maida kamar wani yaronka.
Shuru yarima yayi yakyalesa, ganin haka yasa Dr mu'az yawuce yafita yana 'yan maganganu.
Sa nurses yayi suka tura memartaba zuwa theater room sannan yakalli su sultan abbas da sukayi jugudum yace ranku yadad'e zaku iya shiga daga cikin room kuzauna kujira yanzu doctor d'in zai shiga.
Dada ce tace a'a d'annan kabarmu Kawai a nan dan inmukaje wani wajen hankalinmu bazai ta6a kwanciyaba.
Murmushi Dr mu'az yayi yace ranki yadad'e hak'uri zakuyi kucigaba da yin addu'a akan Allah yasa adace, saidai doctor d'inne idan yafito yaganku a nan bazaiji dad'iba domin bayaso yaga ana tsayawa a nan ransa yake 6aci.
Cike da gamsuwa da maganarsa sultan abbas yace toh shikenan doctor bari mubar wajen fatanmu dai Allah yasa adace, Ameen sukace sannan suka wuce sukashige room.
Yana ganin sun shiga nan yajanyo wayarsa yakira Dr suhail yashaida masa, mik'ewa yarima yayi yacanza kayansa zuwa na theater sannan yafito yanufi room d'in, a bakin theater room d'in yatarar da doctors biyu da nurse d'aya suna jiransa, har ya wuce zai shiga doctor mu'az yakira sunansa.
tsayawa yayi batare da ya juyoba, cikin sanyin jiki Dr mu'az yace ina maka fatan sa'a.
'Daga masa hannu kawai yayi sannan yawuce yashige theater room d'in.
Tsaye yayi yana kallon memartaba da gabad'aya baisan inda hankalinsa yakeba saboda allurar da akayi masa, tausayinsane yakamasa,,,dafasa da akayine ta baya yasa yadawo cikin hayyacinsa nan yamatsa domin sufara aikin.
Su dada alwallah sukayi suka fara sallah tare da rok'on Allah sa'a acikin aikin nan da za'ayi wayoyinsu ko saidai suka kashesu saboda kiran da akeyi musu tun daga iyalansu zuwa mutanen garin gazban dan har gajiya sukayi da amsa wayoyi daga jiya zuwa yau.
dan su sultana bilkisu, sultana sadiya, rahama, sumayya, Aunty husna dukkansu suma sallah suka shigayi, hatta wasu daga cikin mutanen gari, fada ko liman yashige gaba aka dinga suburbud'a addu'o'i da karatun alk'ur'ani, gabad'aya garin wani irin shuru yayi mutane d'aid'ayane zaka gani suna raharsu sai kuma k'ananun yara da basusan abinda ake cikiba, hatta gidansu zarah.
Tun wajen k'arfe goma suka shiga theater room d'in ammah basu suka fitoba sai wajen 12 suka gama komai dan daga k'arshe baya sukaja sukayi cirko-cirko sukabar Dr suhail da aikin kasancewar shi yayi komai dama su kayan aikin ne kawai suke mik'a masa har yagama yamaida yad'inke, bayan ya gamane yajuyo yakallesu yai musu nuni da sunyi nasara ai nan sai suka shiga murna.
Zamewa yayi yaficce daga theater room d'in yakoma office d'insa yacire kayan yasaka nashi.
Nan nurses suka tura memartaba zuwa room d'in da aka admitting d'insa, su dada akayi ma albishir da anyi a sa'a nan suka hau godia ga ubangiji harda duk'awa yin sujjada, dasauri suka fito sukanufi room d'in zasu shiga nan nurses sukace a'a babu damar sushiga a yanzu saboda bacci yake, daganan suka bud'e wayoyinsu kamar jira ake suna kirawa kira na shigowa nan suka shiga yi ma mutane albishir da anyi a sa'a kowa yayi murna sosai.
Yarima kife kansa yayi a table d'in da yake gabansa shi kansa ya rasa shin murna yake ko me, dan ji yake hankalinsa ya d'an kwanta a yanzu ba kamar kafin ayi aikin ba, nan Dr mu'az yashigo yataya murna akan nasarar da aka samu.
Wajen k'arfe ukku badda kama yayi yaje yashiga room d'in yak'ara duba memartaba da har lokacin yake bacci nan daga gafe ya aje wata injection sannan yafito, bai d'ago yakalli su dada ba lokacin da zai wuce ta gabansu ammah saida gabansa yafad'i su kansu saida fad'uwar gaba ta ziyarcesu, haka yafito yawuce yashiga motarsa yanufi gida.
Koda aka kirasa akafad'a masa farkawar memartaba umurni yabada akayi masa injection d'in da ya aje sannan yace za'a iya barin iyalansa sushiga sugansa ammah kar a bari suyi hayaniya.
Zarah da take zaune gefensa ta kafesa da ido tana sauraren wayar da yake, bayan ya gama juyowa yayi yakalleta yace baby ya dai?
Murmushi tayi sannan tace ai tunda naga ka fita da wuri nasan theater ce zakayi.
Murmushi suhail yayi,,,kwantar da kanta tayi saman kafad'ansa nan ta marairaice kamar zatayi kuka tace please kadaina fita bakayi breakfast ba, indai ka san zaka fita da wuri toh tun dare kadinga fad'amin kaga sai intashi dawuri inhad'a maka breakfast.
Murmushi yayi yace toh ranki yadad'e angama.
'Dago kai tayi takallesa saida tad'aure fuska sannan tace duk ranar da kak'ara fita batare da kayi breakfast ba zamu had'e.
Dariya ce taci Yarima ammah yadanneta yace toh Aunty angama.
au nima ce Aunty?
Eh man tun kan inji safkar bulala,,,dariya sukasaka gabad'ayansu nan yad'age mata riga yana kallon cikinta da yake motsawa, d'ago kai yayi yakalleta, murmushi tasakar masa tare da lumshe idanunta,
shafa cikin yashiga yi yace kinga babyna shima ya k'agara yafito yaga daddynsa.
Uhm nima ai na k'agara yafito inhuta da wahalar nan, har ma rasa rigimar wa zanji da ita nake tsakanin babyn ko daddynsa.
Ido yazuba mata yace au nima rigimar nake?
Fari tayi masa da ido sannan tace wata ran ma k'ara na babyn dan taka rigimar har rasa yadda zanyi nake.
Haka kika ce?
Eh,
Tallabo fuskarta yayi tare da kallon cikin idanunta yayi ahankali kamar me rad'a yak'ara cewa haka kikace?
Gira tad'aga masa alamun eh, bata ankaraba sai jin bakinsa tayi cikin nata nan tabiye masa suka shiga nuna ma juna salon so, gabad'aya suka fita hayyacinsu a nan parlour suka baje, saida taga yana shirin wuce tunaninta sannan tasamu tazame jikinta tamik'e dak'yar tanufi bedroom dan gabad'aya ya kashe mata jiki.
Nan yarima yai pillow da hannunsa tare da maida idanuwansa yalumshe, ahankali yayi k'ayataccen murmushinsa cike da k'asaita.
Bayan kwana d'aya sultana bilkisu da sultana sadiya visarsu tafito nan suma suka kama hanyar garin Abuja sosai sukaji dad'i da sukaga memartaba dan a yanzu har 'yar magana yana d'anyi.
Yarima ko tun ranar da yayi masa aiki rabon da yak'ara sakasa a idonsa, saidai yatura wasu doctors domin sugano masa lafiyarsa ammah duk da haka duk wani abu da za'ayi masa shi yake bada umurni ahaka har memartaba yacika sati guda yawarke garas kamar bashiba dan har takawa yakeyi dakansa batare da anrik'esaba, dressing ko kusan kullum akeyi masa dan a yanzu d'inkin ma ya had'e har an warwaresa.
A ranar da yacika sati guda saida yarima yatabbatar da ba abinda yake damunsa sannan yasallami doctors d'in da suka taimaka masa wajen kula da memartaba dan burinsa ya cika nan shi kuma yafito yanufi gida.
A ranar bayan wani doctor yashigo yai masa injection nan dr muhammad bashir da Dr mu'az suka shigo, bayan sun gaisa da su memartaba, Dr muhammad Bashir kallon memartaba yayi yana murmushi yace ranka yadad'e ya kake jin jikin naka?
Shima memartaba murmushin yayi yace Alhmdllh discharge kawai nake jira dan najini daidai nake, ance min ma har yanzu baku fad'i kud'in da za'a biyaba ai yakamata ace zuwa yanzu kun fad'a anbiyaku.
Murmushi sukayi tare da kallon juna sannan Dr mu'az yace kar kudamu ai angama komai ranka yadad'e.
Memartaba kallon sultan ahmad yayi yace karubuta musu cheque kabasu tunda bazasu fad'i kud'inba hakama mungode da karamcin da akayi mana Allah yabiya.
Dada ce tace ai naso inga wannan d'an albarkan da yayi aikin inmasa godia ammah har yau doctor baku gwada mana shi ba.
Dr muhammad Bashir yaga samu yaga rashi haka aka basu cheque d'in ammah yak'i kar6a.
Sultan abbas ne yace kukar6a mana ai duk abinda zamuyi muku bamu biyakuba saidai addu'a,,,
girgiza kai Dr mu'az yayi yace ai doctor d'in da yayi theater d'in ya riga yabiya komai babu abinda baiyiba dan ya ma ce kar a kar6i komai naku.
Gabad'ayansu da mamaki suke binsa da kallo,,,sultan ahmad ne yayi k'arfin halin cewa ya biya komai fa kace? Saboda me zai biya?
Dr muhammad Bashir murmushi yayi yace wannan kad'anne daga cikin halin Dr S, mutum ne mai kyauta da karamci.
Girgiza kai sultan ahmad yayi yace duk da haka baidace yataimaki irin mu ba, taimakon da yayi mana na theater ma kawai ya isa mungode dan bamuda abinda zamu biyasa, yanzu kukar6i wannan kukaimasa.
Memartaba ne yace wai wanene wannan Dr S d'in? Miye full name d'insa? Dan Allah kuyi masa magana yazo mugaisa insaka masa da abinda yayi mani.
Shuru Dr mu'az yayi dan shi ya ma rasa abinda zaice musu,,,muryar Dr muhammad Bashir ce yajiyo yana cewa Dr suhail shine full name d'insa.
Gabad'ayansu saida gabansu yafad'i kusan a tare suka maimaita Dr suhail? Ummi da dada fashewa sukayi da kuka dan antuna musu da suhail d'insu.
Memartaba ne yace dan Allah wanene wannan Dr suhail d'in? daman d'an nan garin ne ko zuwa yayi? Kutaimaka kukaini ingansa ko jikanane.
Shuru sukayi sukarasa amsar da zasu bashi sai chan Dr muhammad yakalli Dr mu'az Girgiza masa kai Dr mu'az yayi alamun kar yafad'a.
Memartaba mik'ewa yayi ya isa inda suke yace dan Allah Kutaimaka min ingansa inaji a raina suhail d'ina ne da nake nema kusan wata ukku kenan yatafi yabarni.
Sultan abbas ne yazo yarik'osa yace ranka yadad'e anya suhail d'inmu ne? Kayi hak'uri kaga bakada lafiya, bana tunanin shine me zaizo yi a garin abuja alhali baida kowa a nan, kuma taya zai ganmu batare da yayi mana magana ba.
Girgiza kai memartaba yayi yace bazan ta6a gamsuwa da maganarkaba har sai nagane ma idona, nidai kukaini ingansa dan Allah.
Dr mu'az cike da jin tausayinsu yace tabbas suhail d'inku ne ranka yadad'e.
Arazane gabad'ayansu suke kallonsa ummi dasauri tamatso inda yake tsaye dada da sultana sadiya suka take mata baya, memartaba ko rik'o masa hannu yayi yace k'ara maimaita min abinda kace kamar kunnena bai jiye min daidaiba kasan inba sunan yarima ba babu abinda yake son ji.
Murmushi Dr mu'az yayi yace tabbas ranka yadad'e abinda kaji gaskiya ne, yarima ne yai maka komai shi yabuk'aci da kar abayyana muku kansa.
Alhmdllh, sultan abbas da sultan ahmad sukashiga furtawa.
Hawayene suka shiga zuba daga idanun memartaba yace dan Allah kataimaika kakaini inga suhail d'ina.
sultana bilkisu ma cikin kuka tace na rok'ek'a kataimaika kakaini inga d'ana.
Dada ma cikin kuka tace kakaini inga jikana ko nasamu sanyi a raina.
cike da tausayin family d'in Dr mu"az yace na amince zan kaiku kugansa a duk lokacin da kuka shirya.
Sultan abbas ne yayi karaf yace yanzu mukeso kataimaka kakaimu.
jinjina kai Dr mu'az yayi yace toh shikenan ranka yadad'e zamu iya tafiya.
Yarima yana komawa gida a bedroom yatarar da zarah tsaye tana shiryawa da alamu wanka tafito, kallonta yayi yace yisauri kishirya yanzu zamubar gidannan.
da mamaki zarah take kallonsa tace barin gida? Ina kuma zamuje daga nan?
Wata uwar harara yarima yawurga mata yace ba shawara nake nemaba umurni nabaki,,,,yana fad'in haka yawuce yaje yabud'e wardrobe yafara tsintar musu kayansu.
Zarah kasa ida sanya kayan tayi nan tai tsaye tana kallonsa cike da mamakin dalilin da zaisa subar gidan alhali mutanen suna da kirki, chan kuma sai tace ko dai gida zamu koma, har yagama shirya kayan tana tsaye ,,,juyowar da zaiyi ganinta tsaye yasa cikin fad'a yace bazakisa kayanba?
Nan cikin sauri Zarah tacigaba da saka kayan dan gabad'aya ya koma mata yarima suhail sak.
_Comment_
*Nd*
_Share_
_Sis Nerja'art✍🏻_[5/1, 7:01 PM] Sis Naj Atu: 👑👑👑

*PAGE* 6⃣8⃣
Tana gama sa kayan bayan yarima tabi suka fito, kallon part d'in jamila tayi taga a kulle yake kasancewar jamila taje anguwa, har cikin ranta bataji dad'iba dabasu samu sunyi sallama da jamila ba.
Suna janye da trolly d'insu sukafito zasu nufi wajen motar yarima, daidai lokacin aka hangame gate motoci hud'u a jere suka shigo, tsaye sukayi suka zuba ma motocin ido cike da mamaki dan basusan ko suwanene ba a ciki.
Tun kan a ida yin parking ummi tabud'e murfin mota tafito dagudu tanufi wajen yarima.
Mutuwar tsaye su yarima sukayi tana zuwa tafad'a jikinsa tarungumesa tare da fashewa da kuka tana cewa kaine my son, daman zan k'ara ganinka?
Tsaye yarima yayi yakasa ta6uka komai, d'ago kai tayi takallesa tare da shafa fuskarsa tace suhail d'ina kaine a gabana ko mafarkin da nasaba ne?
Muryar yarima tana rawa yace ummi na.
Rungumeta yayi sosai a jikinsa yace ba mafarki kikeba nine dai a zahiri ummina nayi missing d'inki.
K'ara shigewa tayi a jikinsa tace shine kuma katafi kabarni baka nemeniba? Meyasa? Meyasa kaimin haka suhail.
Ahankali yabud'e baki zaiyi magana hango su memartaba da yayi sun zuba masa ido yasa maganar ta lak'afe a bakinsa.
Takowa memartaba yayi yanufo inda suke,,,ganin haka yasa yarima yajanye ummi daga jikinsa tare da d'an ja baya kad'an.
Memartaba yana isowa wanka ma yarima mari yayi, gabad'aya wajen ido aka zuba masa cike da mamaki ganin yadda yake d'okin ganin suhail ammah daga had'uwa sai mari, zarah ko jikin sultana bilkisu tafad'a tana kuka,,
Duk'ar da kansa yarima yayi ammah ko kad'an bai gezaba,,,muryar memartaba tana rawa yace sake guduwa kake shirin yi a karo na biyu saboda kar muzo gareka? ka kyauta suhail yanzu har kayi tsawon wata ukku batare da kazo ka nemeniba? Hakan da kayi daidai ne?
Cike da mamaki yarima yad'ago yakallesa,,,,memartaba yacigaba da cewa eh suhail koda ni nakoreka ammah ai cikin fushine kaduba kaga yadda nakoma duk akan rashinka, ni kaina nasan na aikata babban kuskure da na iya korarka daga cikin danginka, suhail taya kake tunani zan iya yafema kaina bayan daga baya nagane kaine akan gaskiya, wlh sumayya ta cuci rayuwata, ya zanyi a yanzu inwanke wannan laifin da na aikata kaicona ina ma ace duk cikin mafarkine.
Girgiza kai suhail yashiga yi cikin sauri yafad'a jikin memartaba yace ranka yadad'e kayi hak'uri bahaka bane, ni ban rik'ekaba ko kad'an kawai dai umurninka nacika, kayi hakuri da bijire ma maganarka da nayi wlh nima bahakanan na rabu da ku ba kawai dan gudun abinda za'a aikata daga baya azo ana da nasani ne domin zarah kwata-kwata batada laifi acikin maganar, ina tsoron in cuceta domin na tabbata sai Allah ya bi mata hak'inta, tunda tana k'ok'arin kyautata min taya zan saketa batare da tayi min komai ba, kayi hak'uri ranka yadad'e,
Shafa bayansa memartaba yayi yace hakan da kayi shine daidai suhail nidai burina kabiyoni mukoma gida.
Janye jikinsa yayi daga na memartaba tare da yin murmushi ahankali yace zarah,,,sai a lokacin memartaba yakalli zarah da take a jikin ummi, murmushi yayi yace d'iyata zo mugaisa mana,
Ummi janye zarah tayi daga jikinta, nan zarah taduk'a cikin sauri tagaishe da memartaba.
Amsa mata yayi cikin sakin fuska sannan yace kiyi hak'uri da abinda yafaru zarah.
Girgiza kai zarah tayi cikin kuka tace bakuyi mana komai ba ranka yadad'e duk abinda kukayi akanmu daidaine tunda kune sama da mu, mune yafi dacewa mubaku hak'uri tunda mu mukayi laifi.
Jinjina kai memartaba yayi cike da jin dad'in lafazin zarah, yace Allah yai muku albarka.
Sultan abbas isowa yayi yarungume yarima, yace yarimana naji dad'in ganinka dafatan zaka yafe mana abinda yafaru.
Murmushi yarima yayi yace abbana akodayaushe bakwa laifi nine dai nayi muku laifi.
Yarima ma baya laifi hakan da yayi shine daidai,,,cewar sultan abbas.
K'ara shigewa jikinsa yarima yayi yace nagode sosai abbana.
Yarima janye jikinsa yayi daga na abbah yaje yarungume dadynsa cikin jin dad'i yace daddyna kayi hak'uri kayafe min nasan nayi muku laifi.
Shafa kansa yayi yace kar kadamu my son tuni laifinka yagogu daga garemu bare ma suhail d'ina baya laifi, Allah yaimuku albarka
Dariya Yarima yayi yace nagode sosai daddyna, ina alfahari da ku,,,kallonsa yakai ga su dada dasuke gefe d'aya tsaye ita da sultana sadiya, murmushi yayi sannan yawuce yanufi inda suke tsaye ganinsa yasa dada tahad'e hannunta biyu waje guda cikin kuka tace suhail,,,rungumeta yarima yayi cikin sanyin murya yace meyasa matata zatayi kuka bayan ga mijinta a tare da ita? Cikin kukan tayi dariya tare da rungume yarima tace suhail ina farin cikin ganinka, kayi hak'uri da abinda yafaru kayafemin wlh duk abinda nakeyi maka sumayya ce take kawomin zuga.
Murmushi yayi tare da d'ago kai yakalleta yace kakata duk abinda kikayi daidaine kuma kin cancanci kiyi fiye da haka saboda kin isa da jikanki.
Itama d'agowa tayi tace dagaske, d'aga mata gira yayi yace toh ya kikace.
Jan kumatunsa tayi tace suhail bakada dama ammah nagode da naganka.
Murmushi yayi yace nima haka matata,,, daganan yamatsa kusa da sultana sadiya da taduk'ar da kanta tana hawaye, gyaran murya yayi, kamar daman jira take cikin sauri tafad'a jikinsa tare da fashewa da kuka tace suhail kayafemin na cuceka na k'untata ma rayuwarka tun kana k'arami na d'aura maka karan tsana, dan Allah kayafemin akan abubuwan da nayi maka wlh nayi nadama insha Allahu yanzu zan gyara rayuwata.
Janyeta yayi daga jikinsa yace ummah kidaina tunawa da abinda yariga yawuce na yafe miki tun tuni.
Cikin kuka tace nagode sosai suhail Allah yabiyaka.
Ameen ummana.
Nan sultana sadiya da dada sukaje cikin jin kunya sukaba zarah hak'uri akan abinda sukayi mata.
Girgiza kai zarah tayi cikin kuka tace wlh bakuyi min komai ba inma kunyi toh na yafe.
Dr mu'az da yake tsaye chan baya yana kallonsu takowa yayi ya iso inda suke nan yaimusu jagora suka shiga cikin gida
Sultana bilkisu tana manne da yarima haka suka shiga kamar wani ya ce zai k'wace mata shi
A main parlour suka yada zango nan zarah taje tad'auko musu ruwa da lemu, memartaba yai gyaran murya yace Alhmdllh gaskiya naji dad'i sosai da naga yarima a yanzu ji nake duk wani ciwo da yake tare da ni ya warke, dan haka gida kawai zamu koma gabad'ayanmu gobe.
Girgiza kai yarima yayi yace kagafarceni ranka yadad'e a yanzu banaji zan iya komawa gida kubarni nan kawai inyaso zan dawo daga baya.
Gabad'ayansu ido suka zuba masa, memartaba ne yai k'arfin halin cewa saboda me suhail, me zaka zauna nan kayi? Kodai baka huceba?
Cike da girmamawa yace ba haka bane ranka yadad'e ina nufin zamu tafo daga baya.
Ina wlh bazaka k'ara kubce manaba k'afarka k'afarmu kayi hak'uri kawai mukoma gida,,,,cewar dada.
Sultana bilkisu ma rik'o hannunsa tayi tace suhail kar kace haka ka amince kawai mutafi 'yan uwanka suna chan suma suna burin ganinka.
Eh suhail ka amince kawai,,,,cewar sultan abbas.
Shuru yarima yayi nad'an lokaci sannan yakalli mu'az da yazuba masa ido, nan mu'az yad'aga masa kai alamun eh, murmushi yarima yayi sannan yace shikenan na amince zan biku.
Gabad'aya nan sukayi murna, haka sukayi ma mu'az godia sosai akan kulawar da yaba su yarima, murmushi mu'az yayi yace duk abinda nayima yarima ban biyasaba domin shi yamin fiye da haka addu'a ce kawai zanyi masa inbiyasa.
Nan memartaba yasa aka kira waya yace ayankar musu ticket.
Jamila ma koda tadawo nan tatarar da su memartaba cike da girmamawa tagaishesu nan mu'az yagabatar da ita.
Sai gab da magrib sannan memartaba yace sutashi sukoma masaukinsu dan su shirya, yaso su yarima subisu masaukinsu ammah yarima yace a'a sai dai goben zasu shigo, ummi rik'esa tayi dan gani take kamar zai k'ara kubce mata.
Murmushi yarima yayi yace kar kidamu ummina babu inda zanje ina tare da ke, kuje kawai gobe zan shigo dasafe.
Kwallah ce tacika mata ido tace kayi alk'awali?
Murmushi yayi a karo na biyu sannan yace eh ummi.
ajiyar zuciya tasafke nan sukayi musu rakiya har wajen motocinsu, saida sukaga tafiyarsu sannan suka dawo, mu'az zama yayi saman kujera tare da dafe kansa.
Ganin haka yasa yarima yazo gefensa yazauna tare da cewa abokina ya dai?
'Dago kansa yayi Cike da damuwa yace prince yanzu tafiya zakayi kabarni? Ya zamuyi idan kuka tafi wlh mun saba da ku bamuso kutafi.
murmushi yarima yayi yace mu'az wa yace maka zamu iya rabuwa? Ai ko muntafi zamu dinga kawo muku ziyara inma takama dakaina zan neman maka transfer kakoma hospital d'ina kacigaba da aiki tunda dama bakada kowa a garinnan aikine yakawoka.
Murmushin jin dad'i Dr mu'az yayi yace prince wlh da ka gama min komai, dan Allah idan kakoma kayi min wannan taimakon.
Murmushi yarima yayi yace kar kadamu kafi k'arfin haka wajena insha Allahu zanyi iya k'ok'arina.
Nagode sosai prince Allah yasaka da alkhairi.
Koda su yarima suka koma part d'insu kallon zarah yayi da takasa kulle baki saboda murna yace kina murna zaki tafi gida ko?
Eh man sosai ma, kaima kana murna?.
Shuru yarima yayi yakyaleta,,,matsowa tayi kusa da shi tare da tallabo fuskarsa saida takalli cikin idanunsa sannan tace kaima nasan zakaso mukoma garinmu dan zamanmu cikin family d'inka shine kwanciyar hankalinmu.
jan hancinta yayi yace kedai tunda kina murna shikenan ammah ni nafison zamanmu a nan.
Marairaicewa tayi tace saboda me kace haka,
Murmushi yayi har saida beauty point d'insa suka lotsa sannan yace saboda a nan babu mai takura mana, a chan ko baza a barni inhuta da matataba.
Murmushi itama zarah tayi tace kar kadamu hearty babu abinda zai hanamu kasancewa da juna dan a yanzu mun riga munzama d'aya.
Ajiyar zuciya yasafke yace hakane dear, ammah zanso kihaihu nan.
Langwa6e kai tayi tace kayi hak'uri mukoma chan garinmu tunda kaga haihuwar da sauran lokaci kuma zatafi dad'i muna cikin danginmu,,,kaga fa kungama magana da su memartaba cewa gobe tare zamu tafi
Shikenan dear tunda kinfi son mutafi toh nima na amince.
Rungumesa tayi a jikinsa tace Nagode sosai my heartbeat.
Su sultan abbas sunkira su waziri a waya sunce gobe zasu dawo nan cikin jin dad'i sukayi musu addu'a akan Allah yamaidosu lafiya.
Memartaba fadar sarkin garin yasa suka wuce suka gaisa tare da yi masa godia akan karamcin da yayi musu a nan suke shaida masa gobe sukeso suwuce garinsu.
baiji dad'iba da yaji sun ambaci tafiya nan yashiga rok'onsu akan suk'ara kwaana biyu.
ammah memartaba yace a'a nan suka shaida masa har ticket sun sa a yankar musu.
ba yadda ya iya kan dole yahak'ura a nan sukayi sallar magrib sannan suka wuce masaukinsu, tare da yi musu alk'awali gobe dashi za a je rakiyarsu.
Koda suka koma had'a kayansu suka shigayi cike da farin ciki biyu ga lafiyar da memartaba yasamu ga ta bayyanar yarima.
Daga chan 6angaren su yarima ma haka zarah tak'ara shirya musu kayansu, duk yadda yarima yaso tazo sukwanta k'iyawa tayi saida tagama shirya duk abinda tasan suna so sannan taje takwanta.
Washe gari tun k'arfe goma wayar da ummi tayo masane ta tashesu daga baccin da suke, bayan sun gaisa nan take shaida ma yarima flight d'in k'arfe biyu zasubi dan haka sugama komai dawuri kafin biyu.
Wajen k'arfe sha biyu suka gama shirinsu gwanin kyau, a parlour suka tarar da su Dr mu'az suna jiransu nan suka gaisa sannan suka wuce sukayi breakfast daga nan sukahau yin hira saboda gabad'ayansu basuson rabuwa da juna,
yarima key d'in motarsa yad'auko yadamk'a ma Dr mu'az yace gatanan ka k'ara, zaro ido Dr mu'az yayi yace ranka yadad'e kodai a ajiye maka ko inje dakaina inkai maka har gida?
Girgiza kai yarima yayi yace kod'aya na mallaka maka ita halak malak yanzu tazama taka.
Dr mu'az da matarsa godia sukayi ma yarima sosai cikin jin dad'i har da duk'awa k'asa saida sukaga ran yarima ya fara 6aci sannan suka daina godiar
Memartaba ne yadamesa da kira dan haka suka tashi gabad'aya suka nufi chan masaukinsu har da su Dr mu'az,
Rungume yarima Memartaba yayi cikin jin dad'i, sultana sadiya ko jan zarah tayi kusa da ita, duk yadda zarah take nok'ewa ammah duk motsi kad'an da zatayi sai sultana sadiya tayi mata sannu.
Bayan sunyi sallah sarkin garin dakansa yasa aka shirya motoci nan yazo dakansa masaukinsu, lunch ma daga masarautarsa yasa aka kawo musu, bayan sungaisa nan Memartaba yagabatar mashi da yarima da matarsa.
Sosai sarkin garin yanuna farin cikinsa akan ganin yarima da akayi.
Bayan sungama kimtsawa gabad'ayansu suka nufi airport nan suka zauna har saida flight d'in ya iso sannan sukayi bankwana da juna cikin rashin jin dad'in rabuwa da za'ayi.
Dr mu'az, matarsa da zarah har da 'yar kwallarsu yarima ma ne maik'arfin halin basu baki.
Basu sukabar wajenba har saida flight d'in yatashi sannan.
A cikin flight d'inma Memartaba yana tare da jikansa, inda zarah take gefen dada kad'an kad'an da tad'aga ido sai taga yarima idanunsa suna a kanta gabad'aya sai taji kunya saboda su Memartaba da su daddy dan hakama sai tadaina kallonsa.
A chan airport d'in garin gazban tun kan su iso ya cika da jama'a kowa yana farin cikin son ganin memartaba dan basusan tare suke da yarima ba.
Lokacin da flight d'insu yasafka gabad'aya wajen yarikice da murna musamman ma da Memartaba yazo fitowa tsaye yayi yana d'aga musu hannu cike da jin dad'in ganin jama'arsa yadda sukazo tarbarsa.
Ai suna ganin yarima sai wajen ya ida rikicewa nan aka cigaba da murna dan ma dogarawa sun hana kowa yamatso inda suke nan aka bud'e musu motocin da aka tanadar masu suka shiga dakyar suka samu hanya sai emir palace,
A chan d'inma mutanene dank'are suke jiran isowarsu, nan ma anyi murna sosai da ganin yarima, shaheed ko rugowa yayi yarungume abokin nasa cikin jin dad'i shima yarima yarungumesa.
Shaheed yace abokina ina katafi kabarni? shine katafi kabarmu muna ta nemanka.
murmushi yarima yayi yace kayi hak'uri shaheed yanzu gani nadawo ba inda zan k'ara tafiya inbarka.
cikin jin dad'i yace dagaske?
'Daga masa kai yarima yayi alamun eh.
nan shaheed yayi murmushi yace nagode sosai abokina ammah fa nayi kewarka.
Memartaba baishiga gidaba saida yatsaya suka gaisa da mutane tare da yi masu godia sannan suka rantaya a turakar su Memartaba, rahama da husna dasauri suka nufo dan tarbar iyayen nasu ganin yarima yasa suka rikice suka nufi wajensa har da kukansu, rungume 'yan uwannasa yayi cikin jin dad'i, rahama cikin kuka tace Bro meyasa katafi kabarmu? Baka tunanin halin da zamu shiga, kaduba kaga tun bayan tafiyarka gabad'ayanmu bamu cikin kwanciyar hankali.
shafa kanta yayi yace kiyi hak'uri Lil sis yanzu gani nadawo yayanki zai kasance da ke akowane lokaci,
murmushin jin dad'i tayi tace nagode sosai yayana, nan takoma wajen zarah tarungumeta cikin jin dad'i.
Kallon husna yayi da take ta kuka yace akan me babbar yaya zata dinga kuka bayan ga k'anenta a kusa da ita? 'Dago kai tayi takallesa nan yad'aga mata kai, cikin sauri tafad'a jikinsa tare da fashewa da sabon kuka.
rungumeta yarima yayi yace please sis kukan ya isa haka indai baso kike nima kisanyaniba.
Cikin sheshek'ar kuka tace meyasa katafi kabarni, kai kanacan hankalinka kwance bakasan halin da muka shigaba saboda rashinka.
Murmushin k'arfin hali yarima yayi yace big sis duk inda suhail yakasance toh shima tunaninsa yana a wajenku, daidai da kwana d'aya ban ta6ayiba batare da kuna a raina ba.
toh dan Allah kar kak'ara tafiya kabarmu.
Jan kumatunta yayi yace angama big sis, cikin jin dad'i takai mai peck a goshi sannan suka rantaya zuwa turakar su memartaba.
Gabad'ayansu a saman carpet d'in da yake shimfid'e tsakiyan d'akin suka zauna inda memartaba da dada suka zauna saman cushin.
gyaran murya memartaba yayi sannan yace Alhmdllh godiya ta tabbata ga Allah da yasa cikin ikonsa nasamu lafiya akan ciwon da ni kaina banyi tunanin zan tashiba saidai cikin ikon Allah ayanzu gani garas saidai d'an abinda ba a rasaba.
gabad'ayansu sukace Alhmdllh Allah yak'ara lafiya da nisan kwana.
Shuru yayi nad'an lokaci yacigaba da cewa yarima suhail munatayaka murnar dawowa cikin family d'inka tare da baka hak'uri akan abinda yafaru.
Murmushi yarima yayi yace bakomai ranka yadad'e.
masha Allah sannan magana tagaba itace......shuru memartaba yayi alokacin da yaga sumayya ta shigo d'akin, gabad'ayansu ido suka zuba mata.
daga nesa dasu kad'an tatsugunna tana kuka,,,abban sumayya ne yai k'arfin halin cewa ubanmi kikazo kiyi mana nan? Ko kitashi ko insa6a miki.
Cikin kuka sumayya tace dan Allah kuyi hak'uri kuyafemin abinda nayi maku wlh nayi nadama nadaina bazan sakeba.
Memartaba jinjina kai yayi yace zancen banza koda kikaga na k'yaleki bansa aka had'a da ke aka sa prison ba toh nabarkine yarima yadawo yayanke miki hukunci dakansa saboda shi yafi dacewa yayanke miki ba niba tunda kuma yanzu gashi ya dawo toh alhmdllh wuk'a da nama suna hannunsa dan haka suhail ga sumayya nan kayanke mata hukuncin da yadace da ita.
dada tace tabbas hakane suhail duk abinda kazartas daidaine.
Mik'ewa sumayya tayi tamatso kusa da yarima tatsugunna cikin kuka tace yarima ban damu da hukuncin da zaka zartas ba akaina nidai burina d'aya kataimaka kayafemin abubuwan da nayi maka wlh duk abinda nayi ba yin kaina bane zinat ce silar komai, tasha fad'amin cewa bazan iya rabuwa da itaba saboda akwai abinda tashirya min tun farkon had'uwarmu, indai zinat zatayi magana toh tatanake d'auka inbar ta kowa koda ace ta iyayenace, sannan nasha k'ullah makirci dan inga nashiga tsakaninku da zarah dan ina gani nice nadace da kai ba zarah ba ammah a yanzu nagane cewa zarah ita tafi dacewa da suhail,
Kallon zarah tayi tace zarah nai miki abubuwa dadama ammah baki ta6a d'aga ido kin kalleniba dan tsakani ga Allah kike zaune da ni.
Zarah da tunda sumayya tafara maganar kuka take dan ta bata tausayi sosai musamman ma da taga duk ta fita hayyacinta.
Yarima Kallon memartaba yayi yace ranka yadad'e dalilin da yasa ban fad'a mukuba tun farko saboda nafiso ku ma kugani da idanunku gudun kar kuk'i yarda musamman ma dada da ummah gabad'aya basuson laifin sumayya a lokacin.
Uhm kaidai bari d'annan ai yanzu dai mungane komai,,,cewar dada.
Jinjina kai yarima yayi sannan yace ashe saida k'awartata tak'ara dawowa gidannan,
Memartaba yace yanzu ma haka tana a prison bari insa atafo da ita, nan memartaba yayi waya.
bayan mintuna kad'an saiga wani barde yazo da zinat duk ta yi bak'i ta k'ok'e inba ka kalletaba sosai bazaka ta6a cewa ita bace hatta ita kanta sumayya da taganta saida tafirgita.
Daga nesa dasu kad'an taraku6e tana hawaye, kallonta sumayya tayi cikin kuka tace zinat dan Allah kiwanke ni wajensu susan banda laifi a ciki.
Zinat ma cikin kuka tace idan bakida laifi toh wa yake da laifi? wlh sumayya kin cuceni.
Duk mutanen da suke zaune wajen shuru sukayi sukarasa megaskiya tsakaninsu,,,yarima ne yace bari akira dogarawa suzo atambayesu.
Zinat a tsorace dan ta tsorata sosai da bulala tamanin d'in da akayi mata cikin kuka tace dan Allah kar kakira ni zan fad'i komai ammah kar kasa ak'ara dukana.
Indai har kika fad'amin gaskiya batare da kinmin k'aryaba toh babu wanda zai dakeki sannan zani sallameki kiyi tafiyarki.
Share hawayen fuskarta tayi sannan tace tabbas sumayya batada laifi a ciki nice silar fad'awarta wannan harkar dan tun muna school sumayya tana da wulak'anci bata yadda tayi abota da kowa sai 'ya'yan masu kud'i nikuma tun lokacin da nafara ganinta naji ta burgeni ganin nima d'iyar masu kud'i ce yasa nayi amfani da dadamata muka k'ullah abota nan mukacigaba da wulak'anci saida naga sumayya ta saba dani batada abokiya kamarni sannan nabijuro mata da buk'atata akanta ammah tak'i yadda ban nuna mata 6acin rainaba daga k'arshe naje wajen wani malami yaimin aiki akanta yazamana duk abinda nakeso shi takeyi bata iya tsallake maganata, a lokacin wani saurayina yanuna yana buk'atarta yabani kud'i masu yawa nikuma naimasa silar samun sumayya shima saida taga raina yana neman 6act sannan ta amince har yayi zina da ita.
gabad'aya d'akin suka saka salati cike da al'ajibin abun kowa yana Allah wadai.
memartabane yatsaidasu, nan zinat tacigaba da cewa tun daga lokacin nima nafara neman sumayya har nasaba mata da harkar itama tabi layi.
a lokacin da take fad'amin zatayi aure na nuna bak'in cikina sosai saboda inason sumayya banaso inga abinda zai rabani da ita, daga k'arshe koda tayi aure ni nadinga hure mata kunne akan kar tayi ma mijinta biyayya duk wani abu da sumayya takeyi da sa hannuna a ciki saboda bata iya tsallake maganata, hatta pills ni nasakata tana sha duk dan kar tahaihu saisa kukaga bata ta6a ko 6atan wataba,
ahaka nacigaba da bibiyarta gidan aurenta mukacigaba da harkarmu batare da tsoron komai ba sai gashi lokaci guda dubunmu tacika ankama mu muna aikatawa.
Dan Allah tunda na fad'a maka gaskiya kabarni intafi wlh bazaku k'ara ganin ko k'eyataba nima nadaina.
Gabad'aya matan da suke d'akin kuka suke, sultana sadiya cikin kuka tace Allah ya isa ashe kece kika 6atamin d'iya.
sumayya girgiza kai tayi tace zinat babu abinda zance miki saidai kawai kije munhad'e gobe k'iyama gaban ubangijinmu ammah hakanma nagode da kika wankeni a wajen dangina.
Sultan abbas murmushi yayi wanda yafi kuka ciwo sannan yace kema sumayya harda laifinki a ciki nasha kwatanta miki akan kibi rayuwa a sannu ammah rawan kanki ya hana daman ita rayuwa *DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA* shi ruwa kan doka dan haka kije gashinan duniya ta nuna miki hankali daman ita duniya ta ishi kowa riga da wando.
Sultan ahmad da memartaba shuru sukayi kamar ruwa ya cisu
Yarima kud'i yad'auko yamik'a ma zinat batare da ya k'irgasuba yace nabaki minti ukku kifita kibar gidannan ko k'eyarki kar kibari ink'ara ganinki.
cikin sauri zinat takar6i kud'in gudu-gudu sauri-sauri haka tafita.
Sai a lokacin yarima yakalli sumayya yace kije kawai sumayya duk abinda kikayi min dan kanki daman tuni nagano haka kawai dai gudun kar zargi yashiga tsakaninmu shiyasa ban ta6a magana ba ammah yanzu Alhmdllh da gaskiya tabayyana
Rik'o hannunsa tayi cikin kuka tace dan Allah suhail kataimaka kayafemin ba dan halinaba ko na sami sauk'in abinda nakeji.
Fizge hannunsa yayi, ganin haka yasa zarah cikin kuka tace dan Allah kataimaka kayafe mata tunda ta gane laifinta kuma kunji batada laifi a ciki.
murmushi yarima yayi yace shikenan dear ta ci albarkacinki nayafe mata.
Cikin jin dad'i tace nagode sosai Allah yasaka da alkhairi, koda taje wajen zarah tunkan tayi magana zarah tace kar kice komai sumayya ni tuni na yafemiki daman ban rik'ekiba.
haka sumayya tazagaya wajen kowa tanemi gafararsa kowa yace ya yafe mata cikin jin dad'i tayi musu godia.
memartaba sai a lokacin yayi magana yace toh Alhmdllh tunda anyafe ma juna, dan haka yanzu wannan ya kamata yazama darasi ga kowa, kekuma sumayya yanzu tunda kin nuna kin tuba kicigaba da neman gafarar ubangiji akan abinda kika aikata sannan kicigaba da zama har Allah yakawo miki miji kiyi aure.
Cikin jin dad'i sumayya tace toh nagode sosai ranka yadad'e.
Memartaba kallon yarima yayi yace suhail ga part d'inku chan nasa angyara maku zaku koma kucigaba da zamanku guards d'inka da ma'aikatanku duk suna nan.
Sosa k'eyarsa suhail yayi yace ranka yadad'e da gidana da nagina naso inkoma da zama idan ka amince.
Girgiza kai memartaba yayi yace a'a suhail kar kayi haka kayi hak'uri kucigaba da zama nan kusa da ni dan hankalina ya fi kwanciya da haka.
murmushi yarima yayi yace toh ranka yadad'e yadda kakeso haka za'ayi.
Toh masha Allah, Allah yasafke matarka lafiya, idan da me magana sai yayi.
gabad'aya shuru sukayi alamun babu memagana dan haka memartaba yasa sultan ahmad yarufe taron da addu'a aka sallami kowa yawatse cike da farin ciki da jin dad'i.
_Comment_
*Nd*
_Share_
_Sis Nerja'art✍🏻_
[5/2, 5:19 PM] Sis Naj Atu: 👑👑👑

*PAGE* 6⃣9⃣
Yarima koda sukaje 6angarensa da mamakinsa yabi ko'ina da kallo yaga angyara sosai duk anzuba masu sabbin ma'aikata da bayi, koda yaje part d'insa tsaye yatarar da guards d'insa nan suka zube suka kwashi gaisuwa, amsa musu yayi cikin sakin fuska sannan yawuce yashiga ciki komai a gyare yake fes, murmushin jin dad'i yayi dan shi kansa yasan memartaba yana sonsa sosai.
Zarah ma koda tashiga part d'inta nan kuyanginta suka kaure da murna da jin dad'in ganinta harda d'an kukansu.
Zama Zarah tayi suka gaisa cikin mutunta juna sannan tatashi tashiga bedroom d'inta ko'ina a gyare yake fes nan aka shigo mata da kayanta, saida tayi wanka tai sallah sannan tashirya nkayanta cikin watdrobe daganan tabi lafiyar gado takwanta nan bacci yai awon gaba da ita.
Sumayya ma wajen sultana bilkisu tacigaba da zama inda sultana bilkisu tacigaba da kula da ita cike da tausayinta.
Yarima bayan yagama shirinsa cikin shigarsa ta alfarma yafito a yarimansa sak fitowa yayi inda yatarar da shaheed yana jiransa saida suka k'ara gaisawa cike da jin dad'in ganin Juna sannan suka d'unguma zuwa fada.
Suna shiga nan duk mutanen da suke ciki suka zube Suna kwasar gaisuwa haka yacigaba da amsa musu cikin sakin fuska daga k'arshe da yagaji sai yakoma d'aga musu hannu ahaka suka isa har chan wajensu memartaba da waziri sai iyayensa da suke zaune, cikin girmamawa yaduk'a yagaishesu suka amsa masa sannan yaje yazauna kujerarsa da aka tanadar mashi sai kujera ta kusa da tashi shaheed yazauna.
Bayan jama'a sun nutsu memartaba lasifika yakar6a ahankali yai sallama sannan yafara yi musu godia akan addu'o'in da sukayi masa daga k'arshe yak'ara bayyanar masu da Yarima da yadawo sannan yak'ara shaida musu akan shine magajinsa ko bayan ransa.
Nan fada tarud'e da murna da kabbara cikin jin dad'i, bayan ya gama bayani yatambayi Yarima ko yana da magana nan Yarima yagirgiza kai.
Waziri ne yakar6i lasifikar yak'ara yi ma jama'a godia sannan yanuna farin cikinsa akan samun lafiyar memartaba yakuma yi murna akan bayyanar Yarima daganan yaba wasu fadawa umurni akan suje susa akawo abincin da yasa ashirya a gidansa saboda gaggarumar walima yahad'a yanaso kowa yaci yanuna farin cikinsa.
Haka akaje akazo da abincin me rai da lafiya aka zuba ma kowa na cikin fadar hatta su memartaba saida akasa masu nasu, bayan angama nan akaba kowa umurni yaci nan jama'a aka shiga ci ana jinjina ma karamcin wannan masarauta hatta su memartaba da shi kansa waziri sunci.
Shaheed ne ganin suhail baya ci yasa yata6osa yace kaci man.
Murmushi Yarima yayi yace na k'oshi, harararsa shaheed yayi yace ammah kasan bazasuji dad'iba idan sukaga bakaciba.
Jin haka yasa Yarima yad'ebo abincin cikin izza yaci, cokali biyar yayi yature abincin yajanyo wayarsa yashiga dannawa.
Bayan kowa ya gama nan sarki ya amshi lasifika yanuna godiarsa ga waziri sannan yad'auko wata alkyabba da rawani masu kyau yadamk'a ma Yarima.
Kar6a Yarima yayi cikin jindad'i sannan yanuna godiarsa, daga k'arshe yayi ma su memartaba sallama yaja shaheed suka fita, motarsa suka shiga suka nufi hospital d'insa.
Lokacin da ya isa sosai staffs d'insa suka nuna farin cikin dawowarsa, dr khalil ko rungumesa yayi cikin jin dad'i.
Yarima farin ciki yayi sosai alokacin da yaga komai yana tafiya daidai nan yanuna jin dad'insa tare da godia ga manyan staffs d'insa.
Bayan sallar isha'i bayan ya gama shirinsa na bacci saman gadonsa yahau yakwanta kad'an kad'an ya duba lokaci yayi tsaki ganin har wajen k'arfe tara ammah zarah batazo part d'insaba, daga k'arshe mik'ewa yayi yasaka alkyabbarsa sanan yafito yanufi part d'inta.
Koda yashiga babu kowa a parlour dan haka yawuce bedroom d'inta, kunna gloves yayi nan yahangota tsakiyan gado ta baje sai baccinta takeyi, murmushi yayi sannan yai light off yawuce yanufi saman gadon yahau yakwanta a gefenta.
Janyota yayi jikinsa yarungume ahankali tabud'e idanunta cikin muryar bacci tace bakayi bacci ba daman?
Uhm taya zanyi bacci bayan baki lek'aniba tunda muka dawo nifa ban yadda adinga nisa da niba dan ina buk'atar kulawa,
K'ara shigewa jikinsa tayi tace kayi hak'uri d'azun saida naje lokacin ka fita insha Allahu bazan dinga nisa da kaiba yanzu ma dan a gajiye nake saisa nakwanta.
Kina gudu kar inyi miki wani abu ko saisa bakijeba?
Marairaice murya tayi tace bahaka nake nufiba kawai dai baccine da gajiyar tafiya ammah nima naso inzo.
na k'i wayon naki yanzu dai kiyi baccinki babu abinda zanyi miki
K'ara tura kanta tayi cikin k'irjinsa tana murmushi.
Washe gari zarah part d'in yarima taje tagyara fes ko a gyare yake sannan tahad'a masu breakfast, bayan sun gama breakfast a part d'in yarima fitowa tayi tabarosa yana waya takoma part d'inta,
wardrobe d'inta tabud'e tad'auko wayanta takunna cikin jin dad'i tahau saman gadonta takwanta sannan tayi dialing d'in number d'in abbah ammah har ta k'arashi ringing baiyi picking ba dan haka talalubo ta mama, tana fara ringing mama tayi picking cikin Jin dad'i zarah tagaisheta nan mama ta amsa tace d'iyata ba dai kun dawoba.
Eh mama mundawo dafatan kuna lafiya? Ya su yaya rauda? Na kira wayan abbah ammah baiyi picking ba
Murmushi mama tayi tace duk muna lafiya nima sa'a kikayi wayartana hannuna kinsan yau ake d'aura auren Aisha.
zumbur zarah tayi tatashi zaune tace yau kuma mama? Shine baku fad'amana ba.
Haba zarah ke ai mun d'auke miki zuwa tunda kinyi nauyi yanzu, kuma shi suhail ai yana sane da maganar bikkin tunda kusan kullum muna gaisawa, kima tayamu godia a wajensa dan ya turo mana gudunmawa dasu mukayi ma Aisha siyayyar kayan d'aki kedai kinyi sa'ar miji mekirki saidai muce Allah yabiyasa.
Zarah kwallah ce tacika mata ido koda taji dad'in abinda yarima yaima iyayenta saidai abun yaimata ciwo da ba'asanar da ita yau ake bikkin Aisha ba, cikin fushi tace gaskiya mama ba'a kyauta minba ace ana bikkin 'yar uwata ammah ba wanda zai iya fad'amin.
Haba zarah kuda bakunan kiyi zamanki kawai kihuta, yanzu dai bari inje inji da bak'i munyi waya anjima,,,,mama batajira jin abinda zarah zataceba takashe wayarta.
Nan zarah takira yaya rauda waya, yaya rauda tana yin picking zarah cikin fushi tace haba yaya rauda yanzu saboda Allah kun kyauta min ace yau ake bikkin Aisha ammah banda masaniya.
dariya yaya rauda tayi tace toh sarkin tsogumi kuda baku gari taya zamu fad'a miki bayan babu waya a wajenki kuma mijinki ai ya sani tunda har gudunmawa yaturo, abbah ne yace kar yafad'a miki dan ya san halinki matsamasa zakiyi sai kunzo.
Hawaye suka fara fita daga idanun zarah cikin muryar kuka tace toh ai yanzu mundawo kuma sai nazo ko bakuso.
Dariya rauda tayi tace wannan tsakaninki da mijinki ne mudai babu ruwanmu.
Cikin jin haushi zarah takashe wayarta nan takife kanta tafara rera kuka.
Wajen k'arfe d'aya yarima yagama shirinsa yafito yanufi part d'in zarah a bedroom yasameta ta kife kanta, kallonta yayi yace baby bacci kike?
'Dagowa tayi takallesa sanye yake cikin galilarsa maroon colour ya yi gwanin kyau, fuskarta a d'aure tace ina zakaje?
Da mamaki yake kallonta yace ikon Allah yau kuma tambayata ake inda zanje saikace mace?
Shuru zarah tayi tare da janye idanunta daga kallonsa cikin muryar kuka tace gaskiya baku kyauta minba wai ana bikkin Aisha ammah banda masaniya alhali kai kana sane, koda ace ba barina zakiyi injeba indai kafad'amin ko addu'a nayi musu ai yayi,,,tak'arashe maganar cikin kuka.
Takowa yarima yayi yazo kusa da ita yazauna cikin sauri zarah tajuya mashi baya.
murmushi yayi cikin rashin damuwa yace zarah kinsan dai babu yadda za'ayi mudawo jiya sannan aganki yau kinfita kuma ga ciki.
Toh ai fitar kamawa take kuma ko yayane nad'an lek'a ai yafi banjeba.
Kibari bayan bikki sai inkaiki kiyi mata wuni.
mak'e kafad'a tayi tare da k'ara sautin kukanta.
Dafe kansa yayi da hannu biyu dan babu abinda yatsana sama da jin kukanta ahankali yace toh shikenan yanzu tashi muje kilek'a da an d'aura aure zan d'aukoki mu dawo.
Juyowa tayi tana share hawayen fuskarta tace dagaske kake?
Murmushi yayi yace toh ya zanyi.
Rungumesa tayi cikin jin dad'i tace nagode sosai hearty ka gama min komai.
Janyeta yayi daga jikinsa yace yanzu dai yisauri kishirya kinsan k'arfe biyu za'a d'aura auren mik'ewa zarah tayi tahau cire kaya tace please bari ind'an watsa ruwa ba zan dad'eba.
Yanzu har sai kinyi wanka ina nan?
Turo baki tayi tace duka fa minti ukku zanyi.
Hmm toh shikenan ammah indai kika dad'e saidai kifito kitarar baninan.
Bama zan dad'eba insha Allah,,,,cikin sauri taje tashiga wanka, bata wani dad'eba tafito d'aure da towel dan tasan halin kayanta zai iya tafiya yabarta,,,d'ago kai yayi yakalleta sannan yamaida idanunsa akan wayarsa da take hannunsa yana dannawa.
Gaban dressing mirror tazauna tayi simple makeup sannan tamik'e tanufi wajen wardrobe d'inta kallon kayan da suke jikin yarima tayi tai murmushi sannan tad'auko shadda marron gown wadda tasha aiki da pink d'in zare tasaka, gaban dressing mirror tazo tamurza d'aurin kallabi sannan tad'auko veil da hand bag da takalmi duk pink colour tasaka, k'ara feshe jikinta tayi da turare sannan tayi masa gyaran murya.
juyowa yayi yakalleta nan tasakar masa murmushi, zuba mata ido yayi yana kallonta bai ko k'yaftawa, kashe masa ido d'aya tayi tare da d'aga gira tace nayi kyau ko?
Janye idanunsa yayi daga kallonta tare da mik'ewa tsaye yace muje, rik'o hannunsa zarah tayi tare da langwa6e kai tace bakace nayi kyauba.
Cize le6e yayi sannan yace ba laifi ammah da hijab kika ssnya da zakifi yin kyau.
Jin haka yasa zarah tawuce gaba gudun kar yace sai tasa hijab, murmushi yarima yayi sannan yabiyo bayanta.
Cikin motarsa suka fita, suna cikin tafiya zarah kallonsa tayi tace sunfa tashi daga wanchan gidan na mance ban tambayesu inda suka komaba.
Batare da ya kalletaba yace ba sai kin tambayesuba na san gidan abbah yaimin kwatance.
Gaban wani madaidaicin gida yai parking ganin mutanen da suke shige da fice yasa yagane nan ne gidan.
K'ik'irin bud'e k'ofa zarah take cikin zumud'i, rik'ota yarima yayi yace zan fa dawo ind'aukeki da and'aura aure.
Langwa6e kai tayi tai kalan tausayi cikin kwantar da murya tace please kabari sai dare.
Ta6e baki yarima yayi yace na dai fad'a miki.
Toh naji,,cewar zarah tare da bud'e k'ofar tafita nan kallo yadawo wajenta daman jira ake aga wanda zai fito daga motar, ratsa mutane tayi tashiga cikin gidan nan suka gaisa da mutane, yanayin tsarin gidan ya burgeta koda flat house ne med'auke da d'akuna ukku, dakyar tagano mama nan tarungumeta tana murna itama mama murna tayi sosai nan tatambayeta jikinta da mutanen gida.
Alhmdllh duk suna lafiya cewar zarah, nan tagaishe da abokan mama daganan tawuce d'ayan room d'in da taga abokan amarya suna shiga rumgumeta su yaya rauda da Aysha sukayi cike da jin dad'in ganin 'yar uwartasu itama zarah rungumesu tayi cikin jin dad'i, nan suka baje suna hira, Aisha kamar ba ita bace amaryar dan sakin jikinta tayi sukai hira sosai da zarah saida taji ana gud'a ana shelar and'aura aure sannan tadawo hayyacinta harda d'an kukanta.
Bayan sallar la'asar akasa amarya tashirya nan zarah tazage taimata kwalliya tashiryata sosai tayi kyau sannan aka tafi da ita wajen su mama dan suyi mata nasiha, zarah komawa tayi takwanta saman gado sukacigaba da hira da yaya rauda.
wajen k'arfe biyar akace amarya tafito atafi da ita dan dama abbah ya ce dakansa zai kai d'iyarsa saisa ba wanda yasa ran tafiya.
zarah fita tayi suka gaisa da abbah nan tatarar da yarima wajensa, bayan sun gama gaisawa yarima yace tafito sutafi, ba dan ta so ba haka tashiga tayi sallama da su mama taja yaya rauda gefe tad'auko cheque d'in 1 million tabata tace taba su abbah gudunmawarta ne.
Koda suka kama hanyar gida fushi kawai take a mota dan taso yarima yabarta takai dare.
Dariya yarima yake ciki-ciki har suka isa, yana yin parking batajirasaba tashige gida.
Bayan sallar isha'i yarima kiranta yayi a waya, zarah tana kallon wayar kamar bazata d'aukaba saida takusan tsinkewa sannan tayi picking batare da tayi maganaba.
Baby please kikawo min coffee insha yunwa nakeji.
umhum kawai tace takashe wayarta.
Nan tatashi tashiga kitchen saida tasoya mashi kwai sannan tahad'a mai coffee tad'aura saman tray, komawa tayi bedroom d'inta tak'ara gyara jikinta sannan tad'aura alkyabba saman sleeping dress d'inta.
Kuyangarta d'aya taba tray d'in tad'auka nan suka nufi part d'in yarima.
Guards d'insa tun kan ta iso suka bud'e mata k'ofa nan suka russuna cikin girmamawa suka gaisheta, amsa musu zarah tayi takar6i tray d'in da yake hannun kuyangarta tashiga.
Ganin baya a parlour yasa tanufi bedroom d'insa tare da yin sallama ciki-ciki, yarima da yake zaune yana waya ganin yadda tahad'e fuska yasa yad'anyi murmushi sannan yacigaba da wayarsa.
Wucewa zarah tayi chan gefensa tad'aura saman bedside sannan tajuya zatabar d'akin.
Janyota yarima yayi tafad'o jikinsa nan yai sallama yakashe wayar tare da kallonta yace baby haka ake ba miji abu?
Fuskarta a d'aure tace toh me kakeso inyi maka bagashinan na aje makaba ni kabarni intafi.
Hmm ammah ai kinsan agajiye nake kuma ga yunwa ina ji indai kinaso insha saidai kibani dakanki,,,yak'arashe maganar tare da kashe mata ido d'aya.
Kallonsa zarah take cikin k'ulewa tace chab ashe ba yunwar kakejiba.
Shima yarima idanunsa a kan fuskarta yace indai ba zaki baniba kid'auki kayanki kiyi tafiyarki na k'oshi.
Jin haka yasa zarah tad'auko cup d'in takai masa a baki, yarima kallonta yake yadda take cika tana turo baki, hannunsa yad'aura saman cikinta yana shafa.
sharesa tayi tacigaba da bashi nan tad'ebo wainar kwai takaimasa a baki, ahankali yake ci, ta k'ule sosai ganin yadda yake ci kamar ba ya so kuma ahaka wai yunwa yakeji.
Bai wani yi cin kirkiba yajanye kansa alamun ya k'oshi.
harararsa tayi tace daman ba wata yunwa da kakeji dukafa rabin cup d'in kasha.
Toh baby naga kamar ba'aso insha saisa nahak'ura yanzu dai tashi muje toilet kiwanke hannunki.
Tashi zarah tayi sukaje toilet saida yai brush ita kuma tawanke hannunta sannan suka fito.
Suna fitowa yarima janyo zarah yayi jikinsa yace baby kayannan sunyi miki yawa bari inrage miki ko alkyabbarce.
Harararsa tayi tace ni kakyaleni tafiya zanyi.
Tallabo fuskarta yayi yace baby please yakamata fushin yak'are hakanan Indai gidane kibari insha Allahu idan kin haihu zan kaiki kinga fushin nan da kikeyi yana ta6amin zuciya nasan shima babynmu bayajin dad'in yadda mummynsa take ma dadynsa yakamata kitausayamin,,,yak'arashe maganar tare da cire mata alkyabba sannan yarik'o hannunta yace muje kiji wata magana.
Turo baki tayi tace ni nasan ba wata magana da zaka fad'amin wayau kakeson yi min, kwanciya yayi tsakiyan gadon sannan yamik'a mata hannu alamun tazo.
Rik'o hannun nasa tayi nan tahau yajanyota a jikinsa yakwantar da ita nan yashiga shafa mata baya, a kunnenta cikin wata irin murya merikitar da ita yace baby please fushin yak'are hakanan kinji?
'Daga masa kai tayi alamun toh, nan yacigaba da shafa mata baya yana lasar kunnenta cikin wata irin siga da yasa zarah tafara sakin layi, ahankali yasalu6e mata riga.
Sanin halinta yasa yadinga binta ahankali ammah duk da haka saida tayi masa raki.
washe gari koda suka tashi yarima tarairayata yayi sosai har saida yaga gabad'aya ta safka daga fushin da take.
Bayan sungama breakfast zarah d'aid'aya tayi bisa yarima tana ta zuba masa shagwa6a akan kar yafita, kan dole yahak'ura yazauna nan sukaita soyewarsu, sai wajen azuhur sannan memartaba yakirasa yafito fada nan zarah tasamu talalla6asa ya amince akan zataje tagaishe da su ummi, nan kuyanginta suka take matabaya zuwa wajensu ummi.
Saida tafara zuwa turakarsu dada sosai dada tanuna mata kulawa, daganan tawuce wajen sultana sadiya nan ma sultana sadiya tarasa inda zata sanyata saboda farin ciki, duk nok'e-nok'en zarah saida sultana sadiya tasamu tad'an saki jiki suka yi hira, kwad'on zogale sultana sadiya tasa akayi mata nan Zarah tazauna taci sosai, tarairaya tasamu sosai ita kanta zarah tajidad'in yadda tayi mata ta dad'e a nan sannan tayi mata sallama taje wajen ummi a chan parlour tagamu da sumayya tayi matashin kai da cinyar ummi suna hira dan gabad'aya sumayya tadawo wajen ummi ammah duk da haka tana lek'awa wajen iyayenta da dada koda a yanzu ba kamar da ba sun sake mata.
Ganinta yasa sumayya tatashi zaune cikin jin kunyarta.
Zarah cike da girmamawa tagaishe da sultana bilkisu, cike da so sultana ta amsa mata tare da tambayarta jikinta da gida.
cikin jin kunya tace Alhmdllh sannan tajuyo tace Aunty sumayya ina wuni?
Amsa mata sumayya tayi batare da ta d'ago ta kalletaba saboda kunyarta da takeji.
ummi ce tace Zarah kizauna saman kujera man kin zauna k'asa.
Ummi nan ma ya yi nafi jin dad'in k'asan...tafad'i hakan cikin jin nauyinta.
Murmushi sultana bilkisu tayi tace toh lafiya lau, ya gida da hidima? Ashe bikkin k'anwarki akayi wlh bamusaniba ai da mun lek'a.
Eh ummi daman saida mama tayi min magana tace lokacin taji ance memartaba baida lafiya saisa bata aiko maku da invitation card ba.
ayyyah Allah sarki toh Allah yabada zaman lafiya.
ameen ummi.
nan ummi tak'walama wata kuyangarta kira tace akawo ma Zarah kayan motsa baki.
Duk'ar da kanta zarah tayi tace ummi subarsa kawai ak'oshe nake.
a'a zarah baridai sukawo miki.
kafin kace mi nan aka cika gaban zarah da kayan marmari da abinci, mik'ewa sultana bilkisu tayi tace ina zuwa nan tawuce tashige bedroom d'inta.
sumayya kallon zarah tayi a karo na biyu ahankali tace zarah zan k'ara rok'onki akan abubuwan da nayi miki dan Allah kiyi hak'uri.
kallonta zarah tayi cike da tausanta tace wlh Aunty sumayya ko kad'an ban rik'ekiba kuma ai komai ya wuce please kidaina tunawa.
k'wallah ce tacika ma sumayya ido tace hmm zarah taya kike tunani zan iya mance cin mutuncin da nayi muku, wane irin makircine banyiba akanki ammah daga k'arshe kinga yadda rayuwa takoma min nayi wasa da damana ni kaina ina jin haushin wannan halin da najefa kaina.
girgiza kai zarah tayi tace Aunty sumayya kidaina cewa haka kema fa wasu abubuwan kowa yasan ba laifinki bane, kuma ko ba hakaba ni wlh tuni na yafe miki.
Share k'wallar idanunta tayi tace nagode sosai zarah Allah yasaka da alkhairi, Allah yasafkeki lafiya.
Nan suka d'an ta6a hira kad'an-kad'an ganin marece ya yi yasa taje tayi ma ummi sallama tafito sukai sallama da sumayya tawuce part d'inta.
cike da sha'awa sumayya tabita da kallo tanaji ina ma ace itace da cikin hawayene suka shiga gangaro mata alokacin da tatuno zuwa hospital d'in da sukayi da ummi aka tabbatar mata bazata ta6a haihuwaba saboda pills d'in da tasha da injections d'in da take na tsawon lokaci sun6ata mata mahaifa, kukane yaso yakubce mata cikin sauri tatashi tashige room d'inta tafad'a saman gado saida tasha kukanta me isarta sannan taje tawanke fuskarta tare da d'auro alwallah, nan tashimfid'a darduma tad'auko alk'ur'aninta takaranta.
Zarah koda takoma part d'inta a parlour tayada zango nan kuyanginta suka zagayeta suna mata hira, haka tabiye musu har aka kira sallah sannan tamik'e taje tayi alwallah tai sallah.
Haka rayuwa tacigaba da tafiya yarima yana tafiyar da aikinsa, a gefe guda kuma ga mulki dan memartaba yanzu bai cika bari yai nisa da shi ba dan a kullum cewa yake nan ba da dad'ewaba ko rai yayi halinsa kokuma insafka daga kan karagar kahau dan gabad'aya yanzu shekaru sunja sosai,,,a duk lokacin da yake maganar yarima yanaji babu dad'i a ransa, shi kansa waziri idan yaji memartaba yai furucin cewa yake a duk lokacin da mulkinka yak'are toh nima nawa ya k'are dan haka dole waziri mejiran gado shima yadinga yawan zaman fada, haka ake matsama yarima da shaheed suna zaman fada sosai.
Zarah sosai take samun kulawa daga wajen dangin yarima, dan sultana sadiya da sultana bilkisu kullum sai sun kirata a waya sun tambayi lafiyarta dan wani lokacinma sultana sadiya da kanta take zuwa tadubata takawo mata abubuwan da tasan meciki tana buk'atar ci dan Zarah kulawa take samu sosai a wajenta kamar yadda zata kula da sumayya.
A 6angaren Dada ma tana aikowa aduba mata lafiyar Zarah kuma tanayi mata aike da kwad'on ganye iri-iri.
su kansu su rahama yanzu wani irin kulawa sukeba zarah dan nan da nan zarah tasaba da rahama.
Yanzu sumayya danginta sun sake suna nuna mata kulawa sosai shima saida sultan ahmad yak'ara tunatar da su akan batada laifi fa sosai tunda da sa hannun zinat take wasu abubuwan, nan suka fara janta a jiki ammah duk da haka sumayya tayi sanyi sosai dan yanzu batada yawan magana.
*BAYAN WATA 'DAYA*
Sumayya ce tafito daga room d'inta dasafe da mamakinta taga su ummi suna ta zirga-zirga da shirye-shirye cike da girmamawa tagaishe da ummi, fuskar ummi a sake ta amsa mata.
murmushi sumayya tayi tace ummi bak'i zamuyine naga kuna ta shirye-shirye?
Kedai bari sumayya wlh wani d'an yayanane zaizo daga agadaz zaikawo min ziyara dan rabonsa da garin nan tun yana k'arami lokacin da nahaifi husna akazo da shi.
Murmushi sumayya tayi tace Allah sarki Allah yakawosa lafiya.
ameen daughter yanzu dai je kiyi breakfast muma ai mungama komai dan ina sa ran nan da awa biyu zai safka.
Bayan ta gama breakfast d'inta zaune take ita kad'ai a parlour hannunta rik'e da hisnul muslim tana dubawa, sallamar da akayine yasa tad'ago kai takallesa tare da amsa masa sallamar.
Wani matashi ne wanda ak'allah bazai gaza shekaru talatin da shidda ba sanye yake cikin manyan kaya yanayin kamaninsa yasa tagane shine wanda ummi tace mata zaizo, ido yazuba mata yana kallonta, ganin kallon ba mai k'arewa bane yasa tagaisheshi.
tattare nutsuwarsa yayi sannan ya amsa tare da tambayarta ya gida?
Lafiya lou sumayya tace sannan tamik'e zata wuce room d'inta.
Gyaran murya yayi yace am ummi fa tana nan?
Batare da ta juyoba tace eh bismillah kazauna bari inmata magana, tana fad'in haka tawuce tanufi part d'in ummi tasanar da ita zuwan bak'on sannan tafito tawuce room d'inta.
ummi koda tafito cikin jin dad'i tace oyoyo yau ga salim mutanen agadaz dakansa ya kawo mana ziyara.
Murmumushi wanda takira da salim yayi tare da d'an zamowa daga kujerar da yake zaune yace ummi ina wuni.
Lafiya lou salim ya gida da mutanen gidan dafatan kowa yana lafiya.
lafiya lou ummi.
masha Allah toh ya k'arin hak'uri? Ayi dai hak'uri ban samu nadawo ba bayan sadakar ukku, ni ina ji tun ma lokacin rabona da agadaz.
Alhmdllh ummi ai bakomai.
masha Allah toh Allah yajik'anta, Allah sarki khadija mutuniyar kirki Allah dai yasa ta huta, ina yaran naku ina fatan suna lafiya?
Duk suna lafiya.
toh masha Allah, Allah yaraya mana su,
Ummi kira tashiga k'walah ma sumayya, fitowa tayi sanye da hijabi a jikinta tace ummi gani.
murmushi ummi tayi tace sumayya wannan shine bak'on nawa matsayin yaya yake a wajen su yarima kije kisa su kuyanga zinnira sushurya masa abinci.
Kallon bak'on tayi da a yanzu ma yatsareta da ido ahankali tace sannu da zuwa ina wuni?
Murmushi yayi yace lafiya lou ya gida?
Batare da ta bashi amsaba tawuce taje tabada umurni akawo masa abinci daganan tawuce wajen dada.
Cika masa gabansa akayi da abinci iri-iri ci yake ammah gabad'aya hankalinsa yana ga k'ofa.
Bayan ya gama kallon ummi yayi yace ummi wai ina prince? Kinsan bana k'asar akayi bikkinsu shi da rahama.
Murmushi ummi tayi tace duk suna nan lafiya lou yanzu ma zaka ganshi dan na fad'a masa zakazo, ina fata dai ka dawo k'asarka ta haihuwa kenan bazaka koma india ba, haba salim mutuwa ai bata wuce kowaba yakamata ace zuwa yanzu ka cire khadija aranka tunda wanda yabaka ya kar6i kayansa shekara biyu da wani abu fa kenan yanzu, kadaure kayi aure karik'e 'ya'yanka ukku wajenka suma sutaso hannun iyayensu, dan su yaya munir hankalinsu ba a kwance yakeba basuda buri dayawuce suga ka saki ranka ka canza aure, d'azun koda yakirani a waya cewa yayi ink'ara kwatanta maka, kaifa salim ba yaro bane kai yakamata kakwatanta ma wasu.
Ajiyar zuciya salim yasafke yace insha Allahu ummi zanyi aure dan a lokaci guda wata ta fara canza min tunani.
Cikin jin dad'i ummi tace masha Allah wace me sa'a ce haka?
Dariya salim yayi yace ummi kuma a wannan garin naku daga zuwana yau d'innan.
Gyara zama ummi tayi tace salim fad'amin inda take insha Allahu zanje dakaina insami iyayenta.
Dariya salim yayi yace ummi kima kwantar da hankalinki ba wata bare bace nidai fatana Allah yasa ba matar aure bace.
Toh Alhmdllh tunda 'yar gida ce wacece ita?
Duk'ar da kansa yayi alamun jin kunya sannan yace ummi ba wata bace face wadda nagani nan wlh ummi tunda nashigo taburgeni Allah dai yasa batada aure.
Murmushin jin dad'i ummi tayi tace in na fahimceka sumayya kenan kake nufi?
Eh ummi ita indai zaku bani ita toh wlh na amince zanyi aure.
Cikin jin dad'i ummi tace toh sumayya dai ta ta6a aure ammah a yanzu basu tare sa mijin nata Indai har kana sonta tsakani ga Allah toh nikuma insha Allahu zan sameta muyi magana.
Shima Cikin jin dad'i yace wlh ummi ina sonta kuma zan kular muku da ita, da gobe naso inkoma ammah a yanzu na canza ra'ayi har sai ta amince sannan zan bar garin nan.
Jinjina kai ummi tayi alamun gamsuwa sannan tace toh Allah yashige mana gaba.
Salim yace Ameen.
Koda yarima yashigo zama yayi sukasha fira cikin jin dad'in ganin d'an uwannasa kuma babban yaya dan dama tun yana karatu a india ummi tahad'ashi da shi.
Yarima fita sukayi tare suka zagaya gari yanuna masa wurare sai dare suka dawo gida.
Bayan sallar isha'i sumayya zaune take ta gama shirin bacci tana duba wasu addu'o'i.
Ummice taturo k'ofan tashigo tare da yin sallama.
Murmushi sumayya tayi ta amsa mata tare da fad'in sannu da zuwa ummi.
Yauwa daughter nan tazauna bakin gadon tare da kallon sumayya tace daughter daman bakiyi bacci ba?
Eh ummi ammah yanzu nake shirin yi.
Ohk ya yi kyau ammah inaso kitaimaka kiban aron hankalinki zamu d'anyi magana, gyara zamanta sumayya tayi tace toh ummi.
Ummi ma fuskantarta tayi tace sumayya aganina yakamata ace wannan lokacin kinyi aure indai kina da wanda kikeso yake sonki saidai idan babune shine sai kizauna har sai Allah ya kawo.
Murmushi sumayya tayi cikin jin kunya sannan tace ummi ai har yanzu babu wanda mukeson juna.
Murmushi itama ummi tayi sannan tace toh sumayya Allah yakawo, sai kuma tayi shuru kamar metunani sai chan tace am yauwa sumayya d'azun salim ya tuntu6eni akan maganarki ya nuna min yana sonki sosai indai zaki bashi dama sai yagabatar miki da kansa.
Gaban sumayya saida yafad'i cikin damuwa tace ummi ya za'ayi in amince masa daga ganinsa ba irina bane ko kin mance abubuwan da na aikata kuma fa doctor ya ce ba zan ta6a haihuwa ba taya kike tunani zai iya aurena,,,,tak'arashe maganar hawaye suna zuba daga idanunta.
Ummi cike da tausayinta tarungumota jikinta tace sumayya kidaina cewa haka tunda kin tuba ai Allahu gafururrahim ne, sannan da kike maganar haihuwa kikwantar da hankalinki nasan salim Indai yana sonki toh zai iya aurenki ahaka dan shima yana da yara ukku marayu da mahaifiyarsu ta mutu tabari shekara biyu da wani abu kenan kizauna kiyi tunani ko ma ince zuwa gobe kibashi dama kuhad'u kuyi magana dan jibi yakeson barin garin, ammah Indai baiyi mikiba kar kiji komai kisanar da ni kinji ko?
'Daga kai sumayya tayi nan ummi tamik'e tace kikwanta kiyi bacci kar kisa damuwa a ranki kinji ko?
Ahankali tace toh ummi.
Murmushi ummi tayi tace sai dasafe dota.
Bayan ummi ta fita sumayya zama tayi taita tunani akan maganar ummi ta dad'e ahaka sannan dagabaya takwanta tai bacci.
Wanshe kare wajen 11am bayan ta gama breakfast fitowa tayi parlour dan tayi kallo, zaune ta tadda mutum shi kad'ai yana kallo, ganinta yasa salim yazuba mata ido, sumayya bataji dad'in had'uwarsuba ahankali tace ina kwana? Amsa mata yayi fuskarsa d'auke da fara'a.
Juyawa tayi zata koma room d'inta nan taji muryarsa ya ce please sumayya in ba damuwa kiban dama yanzu muyi magana.
Tsaye tayi tai shuru batare da ta juyoba, ahankali yak'ara cewa please.
Juyowa tayi batare da tayi magana ba tadawo tazauna bisa d'aya daga cikin kujerun da suke parlourn.
Salim tashi yayi yakoma bisa kujerar da take saitinta yazauna, kallonta yayi da take wasa da yatsun hannunta yai murmushi sannan yace hajiya sumayya ina fata dai ummi ta yi miki bayani akan komai.
Shuru sumayya tayi, ganin haka yasa yace toh ammah duk da haka bari ink'ara miki bayani da kaina agaskiya sumayya tunda naganki jiya naji k'aunarki ta shiga raina, ina sonki tsakani ga Allah idan kin amince sai kiban dama in nuna miki irin son da nake miki dan ni har ga Allah aurenki nakeson yi.
Batare da ta d'ago kantaba tace ummi bata fad'a maka na ta6a aureba?
Kar kidamu indai wannan ne toh ba matsala dan nima na ta6a aure shekara tara kenan rasuwa matata khadija tayi muna da yara ukku, Al-ameen shine babba shekararsa takwas sai Amina shekara shidda sai autansu Sadiq shekara ukku, indai har kin amince zaki zauna da marayu kikasance uwa agaresu toh insha Allahu bazaki ta6a samun matsala daga garemuba zamu zauna da ke tsakani ga Allah, dan ni tun mutuwar matata ban ta6a tunanin zan k'ara son wata maceba ammah sai gashi cikin k'anganin lokaci na fad'a tarkon sonki.
Cikin tausayi sumayya tace Allah sarki Allah yajik'anta su kuma Allah yaraya su,
Ameen nagode saura inji daga gareki.
Sai a lokacin tad'ago kai takallesa tace ammah fa ni bana haihuwa zaka iya zama da ni ahaka.
Murmushi yayi a karo na biyu sannan yace kar kidamu sumayya ni naji na amince ina sonki kuma muna da su Sadiq gasunan zan mallaka miki su sugama 'ya'yanki halak malak.
Sumayya har cikin ranta taji dad'in maganar da yayi ko bakomai itama yanzu zata fara sabuwar rayuwa....murmushi tayi masa a karo na farko sannan tace kabani lokaci zanyi tunani.
Marairaicewa yayi yace please kitaimaka kizartas da hukunci yau dan gobe nakeson barin garin saboda wani aiki da nabaro kinsan 'yan kasuwa.
Shuru tayi nad'an lokaci sannan tace shikenan zuwa anjima zaka ji ni.
Murmushin Jin dad'i yayi yace toh Allah yasa inji alkhairi.
Ameen tace tare da mik'ewa zata wuce d'akinta har ta fara tafiya yakira sunanta, a nutse tajuyo takallesa,
Marairaicewa yayi yace please ataimaka atausaya min kar ayanke min hukuncin da ba zan iya d'aukaba.
Yanayin yadda yai maganar ya bata dariya nan tajuya tashige d'akinta.
A ranar taje tasamu ummanta tafad'a mata maganar da sukayi da salim, sosai sultana sadiya tanuna farin cikinta tace na tabbata sultana bilkisu bazata ta6a za6a miki abinda zai cutar da keba koda salim d'an uwantane kuma jiya sun shigo tare da yarima mungaisa na yaba da hankalinsa, Indai ya yi miki toh ki amince ki auresa.
Cike da gamsuwa da maganar mahaifiyartata tace toh ummah nagode sosai Allah yaza6a abinda zaifi zama Alkhairi
Ameen sultana sadiya tace nan suka d'an ta6a hira da d'iyartata sai bayan azuhur sannan sumayya takoma part d'in ummi.
Bayan sallar la'asar sumayya ta shaida ma salim ta amince sosai yanuna farin cikinsa tare da yi mata godia, nan suka zauna sukasha hira sama-sama dan rabin hirar duk shi yakeyinta, musanyar number waya sukayi.
Koda akayi sallar isha'i haka yakirata sukasha hira saida yasan yadda yayi tad'an saki jikinta da shi har wajen k'arfe goma na dare suna tare.
Ummi taji dad'i sosai da taga sun amince ma juna.
Hatta memartaba, dada, sultan abbas, sultan ahmad aranar sukasan da maganar salim nan sukayi musu fatan alkhairi.
Washe gari saida suka k'ara gaisawa sosai da sumayya sannan yai musu sallama yakoma tare da yi mata alk'awali zai dawo ba da dad'ewaba, a mota koda yarima zai kaisa airport labarin sumayya kawai salim yake bashi shidai yarima saidai yayi murmushi nan yai musu fatan alkhairi shima.
Tun daga ranar soyayya mai k'arfi ta k'ullu tsakanin sumayya da salim dan ko da yakoma saida yasanar da danginsa nan suma sukayi murna tare da yi masa fatan alkhairi.
Kusan kullum sai ya bata yaransa a waya sunsha hira sosai da sumayya, ita kanta har mamakin kanta take dan bata ta6a tunani zata iya son waniba bayan yarima ammah sai gashi lokaci guda salim ya canzata.
_________________
A lokacin da cikin zarah yacika wata tara cif kulawa sosai take samu a kowane 6angare yarima ko bayaso yana nisa da ita ko da ace yana wajen aiki toh suna manne da juna a waya, bayan 30 minutes batare da ya kirata ya tambayi lafiyartaba.
Kuyanginta ma basu yin nisa da ita indai yarima baya nan dan idan yadawo yaganta ita kad'ai fad'a yake musu sosai, saidai idan bacci zatayi shine take sallamarsu takwanta.
_*BAYAN SATI BIYU*_
Zarah zaune take gefen yarima inda gabanta plate d'in apple ne aje ammah ba ci takeba kad'an-kad'an ta cije le6e, kallon yarima tayi da yake cike wasu files, rik'o file's d'in tayi nan yad'ago kai yakalleta, murmushi tasakar masa tace hearty ka aje hakanan kahuta man tun d'azun fa kaketa abu d'aya kaga dare ya yi kazo muje mukwanta zuwa gobe sai ka ida..
Shima murmushin yamaida mata sannan yace sorry baby ai na kusan gamawa gobe nakeso inje inyi submitting d'insu kiban minti goma kinji?
Kwantar da kanta tayi a kafad'ansa tace toh shikenan hearty ammah minti goma kawai nabaka,
Ohk angama ranki yadad'e.
Bayan ya gama kallonta yayi yace baby muje mukwanta.
Mak'e kafad'a tayi tace ni saidai kad'aukeni mutafi.
Hancinta yaja yace shikenan baby as you wish.
Koda sukaje bedroom Kwantar da ita yayi sannan shima yakwanta, juyawa tayi chan gefen tana murmushi bata ankaraba sai ji tayi ya rungumota ta baya, cikin kunnenta ahankali yarad'a mata baby yau guduna akeyi?
Juyowa tayi takallesa tare da marairaicewa tace bahaka bane hearty wlh ji na nake yau duk wata iri,
Kwantar da kansa yayi a k'irjinta yace baby daman tun d'azun da naga yanayinki nace bakida lafiya ammah kikace lafiyarki lau.
Shafa sumar kansa tayi tace ni lafiya ta lau hearty.
Toh bari ingani idan kina da lafiyar ganin ya d'age mata riga yasa tayi saurin cewa dan Allah kabarni kar kayimin komai.
Murmushi yayi yace toh sarkin tsoro ni ba abinda zanyi miki lafiyar babyna kawai zan duba.
Nan yashiga shafa cikinta tamaida idanunta talumshe tana jin sauk'in ciwon da takeji daman tana daurewane dan kar ta tayar mashi da hankali, ahaka bacci medad'i yai awon gaba da ita.
Yarima ma gefenta yadawo yakwanta tare da rungumota jikinsa.
Cikin baccin ne taji kamar wani abu yana tsikararta firgit tayi tafarka tana jin wani irin ciwo tun daga cikinta zuwa mararta, ahankali tazame jikinta tasafko k'asa tazauna tana murk'ususu nan da nan tafita hayacinta sai hawaye, jin ciwon ba mek'arewa bane yasa tafara kiran sunan Yarima da yake baccinsa.
Cikin bacci yaji ana kiransa ahankali yabud'e idanunsa ganin zarah yayi a k'asa tana ta murk'ususu cikin sauri yasafko daga saman gadon yazo inda take tare da rik'ota cike da tashin hankali yace zarah lafiya?
Hawaye suna fita daga idanunta tajawo hannunsa tad'aura saman mararta, dak'yar tabud'e baki tace ciwo.
Cikin tashin hankali yace bari inzo muje hospital ina tunani haihuwar ce,,,tashi yayi yacanza kaya sannan yad'auko mata zane da hijab yasaka mata, jakkar da suka tanada ta haihuwa yad'auko cikin sauri yax'auko key d'in motarsa sannan yad'auki zarah yafito.
Guards d'insa k'arfan jakkar da take hannunsa sukayi nan suka take masa baya har wajen mota, a back sit yasakata sannan yabud'e mazaunin driver yashiga, kallon guards d"insa yayi yace kar su biyosa, wuta yaba motar tun kan ya isa gate yafara horn cikin sauri megadi yazo yabud'e masa yafita daga masarautar.
Gudu yake sosai cike da tashin hankali ga zarah da take kwance baya tana ta kuka da salati, cikin k'ank'anin lokaci ya isa hospital d'insa, tun kan ya isa yakirasu yasanar da su zuwansa dan haka suna isa yatarar da su suna jiransa nan aka fito da zarah cikin sauri aka turata zuwa labour room.
Dr leemah ce tatsaya kanta, yarima ko gefenta yatsaya yana taimaka mata cike da tausayin matar tasa, zarah ta sha wahala dan gabad'aya gidansu babu sunan wanda bata kiraba, yarima waje biyu yaraba hankalinsa da wajen lallashin zarah sai wajen ceto babynsa, cikin ikon Allah batafi minti sha biyar tana nak'uda ba tahaifo shantalelen d'anta, Dr leemah ce tayi saurin d'aukesa tamik'a ma wata nurse dan tagyarasa, inda yarima yakoma wajen zarah yana mata sannu batare da ya ga abinda aka haifar masaba.
Hawaye suna fita daga idanunta tana maida numfashi sama-sama ahaka dr leemah tagyarata.
Koda nurse d'in tagyara yaron Dr leemah tafara kar6ansa tana yaba kyaunsa tana cewa wannan prince ne sak yabiyo.
Sai a lokacin yarima yamik'a hannu yakar6esa murmushin jin dad'i yayi tare da furta Alhmdllh, nan yai masa addu'a da kiran sallah, zuba ma yaron ido yayi cike da so, zarah ahankali talek'o yaron da yake hannun yarima saida gabanta yafad'i batasan lokacin da ta furta masha Allah ba dan yaron kyakkyawane kamar daddynsa, kallonta yarima yayi yana murmushi yace kinga kyautan da ubangiji yabamu ko?
Itama murmushin tayi tace masha Allah yanzu nan ni na haifesa?
Yanayin yadda tayi maganar ta ba yarima dariya, murmushi yayi yace eh man kece, ammah ai da ni yake kama.
Itama murmushin tayi cikin jin dad'i tace saidai kai d'in dai.
Nan su Dr leemah suka taimaka mata tatashi tayi wanka, a cikin daren yarima yakira sultana bilkisu yashaida mata, da har ta ce gasunan zuwa asibitin nan yashaida mata ai ta haihu cikin k'oshin lafiya yanzu dan dare yayi ammah tun da asuba zasu dawo.
Sosai ummi tanuna farin cikinta tare da addu'an Allah yaraya.
A nan hospital d'in su yarima suka kwana, tun asubar fari sultana bilkisu takira sultana sadiya tashaida mata sosai sultana sadiya tanuna farin cikinta inda tasa ma'aikatanta su d'aura ruwan wanka kafin su zarah su iso.
Dada ma koda taji labari murna tayi sosai har da hawayenta zataga jinin suhail d'inta shi kansa memartaba ya nuna farin cikinsa sosai,
Kan kacemi gabad'aya masarautar ta san da maganar haihuwar zarah.
gabad'aya su dada suka taru bayan sunyi sallar asuba suna jiran dawowarsu yarima cike da tsaguwa da son ganin babyn.
_Comments_
*Nd*
_Share_
_Sis Nerja'art✍🏻_
[5/3, 7:55 PM] Sis Naj Atu: 👑👑👑

_Sak'on gaisuwa da jinjinar bangirma agareku masoyana, nagode sosai da soyayyarku agareni, hak'ik'a kun nuna min kulawa sosai banda abinda zance maku saidai addu'a Allah yasaka da alkhairi Allah yabar k'auna.😍😘_
💝💝💝
_*Yayata ko ma ince Auntyna jiddah mumyn zarah bazan ta6a mancewa da keba a rayuwata ke d'in tadabance saidai ince Allah yabar wannan zumuncin namu💞*_
💓💓💓
_~M.B.A nd Mu'az banda abinda zance maku saida addu'an fatan alkhairi🤩~_
🧡🧡🧡
```My dala dole ingaisheki kuma in jinjina miki da namijin k'ok'arin da kike Allah yabar k'auna😍```
💕💕💕
_Intelligent Writer's ni kaina bansan abinda zan ce ba akan k'warin guiwar da kuke bani saidai ince Allah yak'ara d'aukaka mana k'ungiyarmu ya albarkaceta, Allah yak'ara had"a kanmu gabad'ayanku na gaisheku, Aunty maryam Allah yaraya mana newborn baby muhammad🥰_
💘💘💘
_*S.A.N 4EVER na jinjina maku tagwaye ukku ku d'in na daban ne acikin zuciyata😍👍*_
🔚🔚🔚🔚🔚🔚
*PAGE* 7⃣0⃣
Yarima saida yai sallar asuba sannan yad'auko zarah suka dawo gida, staffs d'insa wad'anda sukayi night duty zuwa suka dinga yi suna tayasa murna,, a mota zarah da take rungume da babyn ido tazuba masa tana kallo cike da sha'awa, yarima da yake tuk'i juyowa yayi yakalleta yai murmushi har zaiyi magana sai kuma yafasa.
Lokacin da suka isa gida suna fitowa daga mota su dada da suke tsaye suka iso inda suke, sultana sadiya ce tafara kar6an babyn cikin jin dad'i tadubasa tai masa addu'a sannan tamik'a ma dada nan dada har da hawayenta tace suhail ashe da rabon zanga d'an cikinka, cikin jin kunya yarima yasosa kansa, zarah ko rufe fuskarta tayi da hijab d'inta saboda kunya, nan su memartaba ma suka amshesa cikin farin ciki sukayi ma yaron addu'a, sultana bilkisu ko d'an kallonsa tayi ta gefen ido saboda kunya, nan sultana sadiya takar6esa taja zarah suka wuce 6angarenta, room guda tasa aka bud'e ma zarah, jakkadiya tazo takar6i jaririn dan tayi masa wanka.
Dada aikawa tayi da mota aka d'auko mata wata hajiya tsohuwa da tayi ma husnah wankan jego lokacin da tayi haihuwar farko, koda tsohuwar tazo nan tayi ma zarah wankan jego.
Bayan sun fito tea mekauri aka had'a mata tasha kafin agama tuwo, sultana sadiya tayi-tayi zarah tashayar da babyn ammah tak'i wai ita kunya saida taga tana niyar kiran dada sannan takar6esa tana nok'e-nok'e cikin jin kunya tabashi yasha, daurewa tayi duk zafin da takeji cije le6e takeyi, nan sultana sadiya tatsareta saida taga ya k'oshi sannan takar6esa tace zarah takwanta tahuta, nan zarah tayi kwanciyarta dan rama baccinta.
Sultan bilkisu sosai taji dad'i da sultana sadiya tawuce da zarah part d'inta dan ta san halin d'an nata.
Yarima koda yakoma part d'insu nan kuyangi da bayi suka dinga tayasa murna akan k'aruwar da aka samu, saida yakira su mama yafad'a musu haihuwar sannan yaje yai wanka yakwanta ammah yakasa bacci saboda farin ciki, daga k'arshe mik'ewa yayi yajanyo alkyabbarsa yasaka yafito yanufi part d'in sultana sadiya, cikin sa'a yatarar da bakowa parlour Dan haka yawuce room d'in da zarah take yana tura k'ofan yaji ta bud'e cikin jin dad'i yashiga, hangota yayi saman gado ta baje tana ta kwasar baccinta, ahankali yamaida k'ofan yarufe sannan yawuce yaje yahau gadon yakwanta daga gefen zarah kallonta yake cike da tausayinta baccinta take a nutse, hannu yakai yana shafa fuskarta cikin so da k'aunarta ganin ta motsa yasa yajanye hannunsa nan yarungumota jikinsa ahaka shima yasamu bacci yad'aukesa.
Wajen k'arfe goma knocking d'in k'ofar da akene yatashesu daga baccin da suke, zarah cike da mamaki takalli yarima tace nashiga ukku yaushe kashigo nan? Murmushi yayi yace kina tunani zan iya yin nesa da ke?
6ata fuska tayi kamar zatayi kuka tace haihuwa fa nayi kuma nan ai ba 6angarenmu bane yanzu ya kakeso inyi idan aka shigo aka ganmu a tare?
Kedai baby tsiyata da ke kin faye tsoro toh menene dan anganmu.
Har ta bud'e baki zatayi magana nan aka k'ara knocking d'in k'ofar, nuni yarima yai mata alamun taje tabud'e.
Mik'ewa tayi tanufi k'ofan ahankali tabud'e tad'an lek'a kanta ganin sultana sadiya ce rik'e da baby daga bayanta wata kuyangata d'auke da tray nan wata irin kunya takamata dakyar ta iya matsawa tabata hanya.
Ganin yarima zaune saman gado yasa sultana sadiya tace suhail ba dai zuwa kayi ka hanata bacci ba?
Murmushi yayi yace a'a ummah ni ban hanata bacci ba yanzu ma tafarka,
Toh hakan ya yi, nan taba kuyangar dama ta aje tray d'in tafita.
Yarima kar6an babyn yayi daga hannunta.
Sultana sadiya kallon zarah tayi tace ga tuwo nan kizauna kici dada ta aiko miki da shi ta ce kicinyesa sannan ga pepper nan shima kar kirage komai har romon.
Ahankali zarah tace toh ummah ammah ai ban iya cinye duka.
Kedai yanzu safko kifara ci, mik'ewa zarah tayi taje tawanke bakinta sannan tadawo tazauna tabud'e tuwon ahankali takeci.
Kallon yarima tayi da yake wasa da babynsa tace kasafko muci.
Sai a lokacin yakalli tuwon yamitsa fuska yayi kamar Wanda yaga wani kashi yace menene wannan kuma?
Harararsa zarah tayi tace ba kasan tuwo bane.
Ta6e baki yayi yace ni irin wannan tuwon ya fi k'arfina aci lafiya.
Dariya sultana sadiya tayi tace daman wannan na masu jegone, yanzu dai yi sauri kici kiba yaron nan yasha dan yunwa yakeji.
Haka sultana sadiya tatsareta saida taci tuwon sosai taci pep d'in da aka kawo romon dukansa tashanye.
Bayan ta gama zuwa tayi tawanke hannunta tafito, nan sultana sadiya takalli yarima tace suhail gatanan katsareta taba yaron nan yasha dan yunwa yakeji.
Kallon zarah yayi da take turo baki sannan yace toh ummah.
Bayan sultana sadiya ta fita ahankali yace sweetmee kizo kizauna man.
Daga nesa dashi kad'an tazauna nan yamatso yad'aura mata babyn saman cinyarta.
babu yadda ta iya haka tadaure tashayar da shi, suhail saida yaga ya k'oshi sannan yad'aukesa yace baby kikwanta kihuta bari inkai ma ummah shi inkama gabana tun kan jama'a sufara zuwa.
Komawa tayi takwanta nan yabata peck a goshi sannan yafita a parlor yatarar da ummah nan yamik'a mata yaron sannan yaficce.
Kafin azuhur mutane dayawa sun taru gidan, sultana sadiya dakanta taje tahad'o ma zarah kayanta da na baby a chan part d'insu.
Su Rahama da sumayya sosai suka nuna farin cikinsu da suka ga babyn nan sukaita santinsa.
Yarima kud'i yaba Aunty Husna sosai taje tahad'a ma baby da mejego kaya na azo agani masu kyau da tsada.
Yarima yaso amaida masa matarsa part d'insu ammah sultana bilkisu tace kar yakuskura yatunkari sultana sadiya da maganar yabari tazauna chan har tagama wanka ba dan ya so ba kan dole ya hak'ura yabarta saidai kusan kullum yana manne da ita da babynsu, tun sultana sadiya tana fad'a har tagaji tadaina.
Ita kanta dada koda talura da yadda yake shige ma zarah fad'a tayi masa sosai ammah yashareta baifasa abinda yakeba.
Sosai su dada suke nuna ma zarah kulawa inda hajiya tsohuwa tazage tana gyara mejego sosai.
Su yaya rauda ko kusan kullum sai sunzo gidan hatta ita kanta amarya Aisha.
Tun ana saura kwana ukku suna 'yan agadaz sukazo 6angare guda aka bud'e masu sosai masarautar tacika da bak'i.
Ranar suna yaro yaci suna Faruk Umar Faruk (Ameer Faruk) memartaba sosai yanuna farin cikinsa da karar da akayi masa shanuwa biyu da rago biyu yabada ayi hidimar suna, inda yaware shanu hud'u da garken tumaki sannan yakawo alkyabba yabada yace na takwaransa ne.
Su daddy da abbah ma ba'a barsu a bayaba dan filaye sukaba Ameer faruk sai cheque na mejego
Sultana sadiya da sultana bilkisu suma gudunmawa suka bada ta azo agani.
Dada kanta ba'a barta a bayaba kaya masu kyau da tsada tasa aka had'o ma mejegmejego da baby.
Shagali akayi sosai inda jama'a sukaci sukasha, zarah tasami kyautuka sosai a wajen 'yan uwa da abokan arzik'i hatta abokan suhail da matansu ba'a barsu a bayaba suma sun bada tasu kyautar.
Jamila da Dr mu'az ma tun ana saura kwana biyu suna suka dura garin dasu akayi komai.
Yarima raguna hud'u da shanu ukku yayanka ranar sunan aka had'a da Wanda memartaba yabayar, a ranar anyi shagalin da ba"a ta6a kamarsaba a garin anci ansha har aka bari.
Da dare sultana sadiya ce sai su sumayya suke duba kayan da zarah tasamu dan turame da kayan baby kamar za"a bud'e shago, ga mak'udan kud'i, bayan sungama dubawa nan sukai mata sallama suka fita.
Ido tazuba ma kayan tana kallo turo k'ofan da akayine yasa tad'ago kai takallesa murmushin jin dad'i tayi dan rabonta da mijin nata tun d'azu da safe.
Takowa yayi ya iso inda take daga gefenta yazauna nan yakai hannu yad'auki Ameer da yake bacci sannan yace baby ya gidan da hidima?
Kwantar da kanta tayi a kafad'ansa cikin shagwa6a tace shine ko kalek'o kadubamu kabarmu da kewarka.
Murmushi yayi yace sweetmee taya zan shigo bayan gidan cike yake da mutane, kuma ga su dada sun sanya min ido, ke ni nagaji zuwa zakiyi mukoma part d'inmu kawai dan zanfi samun kwanciyar hankali in kina kusa da ni.
Mik'ewa zarah tayi tace ina zuwa nan taje tad'auko hand bag d'inta tafiddo kud'ad'en da tasamu tamik'a masa batare da ya kar6aba yace na menene?
Murmushi tayi tace wanda nasamu ne na suna kad'auka na mallaka maka, sannan ga kayan da muka samu nan ni da Ameer.
Murmushi shima yayi yace my sweet wannan hak'in kine ki aje wajenki kawai nagode, idan ban k'ara mikiba ai bazan kar6aba.
Turo baki tayi tace nidai a'a toh me zanyi dasu ni?
Janyota yayi jikinsa yace bakisan abinda zakiyi da su ba?
'Daga masa kai tayi alamun eh.
Murmushi yayi yace toh kid'ibi wani abu kiba su baba sauran kuma sai kizuba a account d'inki inyaso daga baya sai kiyi tunanin abinda kikeso ayi miki.
Cike da gamsuwa da maganarsa ta jinjina kai.
Hannunsa yatura cikin rigarta tare da k'ara matsota jikinsa.
Zaro ido zarah tayi taturesa tace ban fa gama wanka ba.
Hmm toh wani abu nace zanyi miki? Na ma lura kamar dad'i kikeji da kikayi nesa da ni, ke nifa so nake kidawo hakanan.
Rungumesa tayi tare da marairaicewa tace wlh a'a kawai dai kunya nakeji kabari ingama wanka sai indawo nima ai nayi missing d'inka.
Janyeta yayi daga jikinsa yace nak'i wayon, in dagaskene kibini mukoma.
Dariya tayi tace wlh baza'ayi wannan abun kunyar da ni ba
Shuru yayi nan yasa hannunsa cikin aljihunsa yafiddo wani d'an k'aramin zoben azurfa mekyau da tsada yasa ma sultan a k'aramin hannunsa.
Zarah ma kallon hannun tayi tana murmushi tace yai kyau.
'Dago kai yayi yakalleta yace dagaske?
Fari tai masa da ido, Kwantar da sultan yayi sannan shima yakwanta tare da safke ajiyar zuciya.
Kallonsa zarah take cikin tsoro tace please katashi kaje kakwanta dare yayi fa.
Janyota yayi jikinsa yarungume tare da yin light off, k'ara shigewa tayi jikinsa ahaka sukayi bacci.
Washe gari tun da asuba yatashi yakoma 6angarensu.
Zarah turamen tad'auka tad'ibar ma su dada, babu wadda bataba ba k'in kar6a sukayi, sukace a'a kije kid'inka kayanki hak'in kine.
Hajiya tsohuwa tad'ibar mawa, koda taba su sumayya suma k'in kar6a sukayi saida tanuna bataji dad'iba sannan suka kar6a sukayi mata godia.
Koda yaya rauda tazo nan tad'ibar mata nasu da na mama sannan tabata kud'i dayawa tace na su baba ne, nan taware wasu tace natane ita da aisha.
Sosai sukanuna farin cikinsu sukai mata godia.
Hata tacigaba da zama wajen sultana sadiya tana samun kulawa sosai daga kowane 6angare ga gyara da takesha wajen hajiya tsohuwa, Ameer yaro me farin jini da shiga rai kulawa yake samu sosai dan baima cika wuni wajen Zarah ba indai ka gansa ankawo mata toh yunwa ce takeji.
Shi kansa suhail saida ummi taimasa dagaske sannan yarage shige ma Zarah.
Ranar da tayi arba'in kitso da k'unshi tasha, sannan bayan sallar magrib aka maidata part d'inta, mamakine yakamata ganin ancanza mata kayan d'akinta komai sabo.
Bayan tayi sallar isha'i wanka tayi tashirya cikin wasu sleeping dress masu kyau, feshe jikinta tayi da turaruka masu k'amshi sosai.
Lokacin da tafito har an shirya ma Ameer dan haka tasa wata kuyangarta tad'aukesa suka nufi part d'in yarima.
Gani tayi shima komai ancanza masa sabo room d'insa ya burgeta sosai.
Kar6an Ameer tayi daga wajen kuyangar tasallameta, ahankali tatura k'ofan bedroom d'in tashiga kwance tahangosa saman gado yai pillow da hannuwansa.
Ganinta yasa yatashi zaune tare da mik'a mata hannu cikin sauri ta iso inda yake, mik'a masa Ameer tayi sannan tazauna gefensa, murmushi suka sakar ma juna yace baby dafatan kin dawo lafiya? Tun d'azun nake ta jiranki ammah shuru, hmm Nasan dai ba wani missing d'ina kikayi ba, ni kad'ai nayi missing d'inki.
Rungumesa tayi tace hearty wlh nima nayi missing d'inka tsayawa nayi ind'an kimtsa sannan inzo wajen rabin raina.
Wani irin kallo yai mata mai d'auke da sak'onni wanda yasa saida taji wani yar a jikinta, cikin sauri tasadda kanta k'asa.
Kallon Ameer yayi da yake baccinsa sannan yamik'e yaje yakwantar da shi yadawo nan yakwanta saman gadon.
Biyosa zarah tayi takwanta k'irjinsa tace hearty kayi hak'uri nima kasan kunyarsu ummah ne da nakeji ammah ai da tuni na gudo wajen mijina abun alfaharina dan nayi missing d'insa sosai.
Rungumeta yayi yana shafar bayanta yace baby aike bakya laifi duk abinda princess tayi daidaine dan ta cancanta tunda har tasace zuciyar suhail ai ba abinda yai saura, dole yahak'ura yabita yadda duk takeso.
K'ara shigewa tayi jikinsa tace hearty kaima ka sani da ace ana bud'e zuciya aga sirrin da yake cikinta da tuni na bud'e maka kaga abinda yake cikinta.
Janyo hannunsa tayi tad'aura saman k'irjinta tace duk wani bugu da zuciyata zatayi tare da sonka takeyinsa.
Tsura mata juna ido sukayi suna karance duk wani sirri da yake cikin ransu, zarah ce cikin sauri tazame jikinta tazauna saman gadon tana jin wani iri.
Inda yarima yamaida idanunsa yalumshe yana jin sonta yana fizgarsa, cikin sauri hannunsa har k'yarma yake nan yajanyota yarungume tare da had'e bakinsu waje guda yafara kissing d'inta, cikin dabara yarabata da duk kayan da suke jikinta nan yacigaba da sarrafata son ransa gabad'aya yafita hayyacinsa nan yaita mata sumbatu.
Zarah tausayin mijinta yakamata ganin yadda gabad'aya yarikice mata ita kanta ta san ya yi missing d'inta sosai.
Ta wahala sosai a hannunsa ya sa mata albarka ya fi ak'irga.
Bayan komai ya lafa yarima d'aukanta yayi sukaje sukayi wanka bayan sun gama d'aukota yayi yamaidota saman gado yakwantar da ita sannan shima yakwanta yarungumeta a jikinsa cike da shauk'in sonta, wata irin runguma yayi mata kamar zai maidata cikin ciki har saida zarah tayi 'yar k'ara sannan yasafsafta rik'on,
Cikin dare koda Ameer yafarka saidai yarima ne yaje yad'aukosa daga cikin gadonsa dakyar yasamu zarah tatashi shima saida yataimaka mata sannan tabashi yasha.
Bayan ya k'oshi shi yaita riritashi inda zarah takoma baccinta har saida sultan yai bacci sannan yarima yakwanta.
Washe gari bayan sunyi breakfast zaune suke suna hira cikin nishad'i, mik'ewa yarima yayi tare da rik'o hannun zarah yace sweetmee taso muje kiga wani abu.
Mik'ewa tayi tabi bayansa koda suka shiga gaban dressing mirror yatsaya da ita sannan yatsaya a bayanta yace tarufe idanunta.
Koda tarufe sarka ce yasaka mata da zobe sannan yadamk'a mata keys a hannunta yace tabud'e.
Wuyanta tabi da kallo tana shafa sark'an da yasaka mata cikin jin dad'i sannan takalli keys d'in da suke hannunta juyowa tayi tafuskancesa tace hearty wannan sark'an kamar ta gold ce yanzu tawa ce?
Murmushi yayi tare da d'aga mata kai yace tabbas ta gold ce ga d'ankunnen nan, wannan keys d'in kuma d'aya na motar da nacanza miki ne d'ayan kuma na gidane na mallaka maki halak malak.
Zarah rasa me zatayi tai shin farin ciki ko me? Fashewa tayi da kuka tare da rungumesa tace nagode, nagode, nagode sosai hearty Allah yak'ara girma da d'aukaka Allah yarabaka da iyayenka lafiya, bansan me zanyi inbiyakaba dan Allah kafad'amin abinda zanyi wanda zaisa ko kad'anne kaji dad'i a ranka.
Rungumeta yayi yace kidaina yi min godia dear dan kin riga kin gama min komai dan akowane lokaci kina faranta min rai, saidai ince Allah yabaki masu yi miki kema, yanzu dai muje inbaki labari medad'i.
Haka yajata suka dawo parlour suka zauna nan sukacigaba da hira.
_______________
Kamar yadda yai ma Dr mu'az alk'awali hakan ko akayi dakansa yarubuta takardar neman masa transfer ya aika da ita, batare da 6ata lokaciba akayi requesting.
Gidan da zasu zauna ma shi yasiya masu nan mu'az yadawo hospital d'in yarima yacigaba da aiki.
Zumunci ake sosai tsakanin jamila da zarah.
A ranar da tayi arba'in ranar yad'auketa yakaita gidansu tayi wuni daga nan yawuce da ita gidan Aisha, saida yajera kwana ukku yana kaita gidajen 'yan uwa day abokai.
_*A gurguje please*_
Sumayya da salim sosai kawai ake zubawa daga k'arshe dangin salim sukazo suka neman masa auren Sumayya ba a wani sa bikkin dayawaba, ahaka har akayi bikkin aka kaita agadas, sukaita zuba soyayyarsu me tsafta ga yaransu atare da su, sosai sumayya takejin yaran a ranta dan jinsu take kamar ita tahaifesu.
Yaya rauda ma Alh munir zuwa yayi yanemi gafara a bisa abinda ya aikata mata, dakyar yasamu yashawo kanta ta yafe mashi nan yanemi yafiyar iyayenta, daga baya yanuna yanaso ya aureta da ta nuna ba zata aminceba saida yanuna shi dagaske tsakani ga Allah yake sonta sannan ta amince sukayi aure.
_*BAYAN SHEKARA UKKU*_
Yarima kud'i sun zauna ya k'ara kyau da cika, sarauta ta k'aru.
Wani d'an yarone kyakkyawa wanda bazai gaza shekaru ukku ba naga ya shigo dagudu cikin maganarsa da bata ida k'warewaba yana kiran daddy daddy daddy dagudu yafad'a jikin suhail da yake kwance saman cinyar zarah
d'aukansa suhail yayi yad'aura saman jikinsa yace little prince wa yata6a min kai?
Cikin gwarancinsa yace daddy wajen meenal zaka kaini.
Shafa kansa yayi yace yanzu ko zan kaika.
Zarah da take saurarensu 6ata fuska tayi tace haba hearty kasa akaisa kawai ko yaje wajen hinde takaishi magana fa nakeson muyi ganin kana waya yasa najira kagama.
'Dago kai yayi yakalleta yace sorry sweetmee me kikeso kice ina saurarenki, chocolate yamik'a ma Ameer nan yafara sha.
murmushi tayi sannan tace yauwa d'azun naji kana waya ka ce asa sunan su mama cikin wad'anda zasuje aikin hajji ka mance wanchan shekarar duk tare kabiya mana mukaje?
Murmushin shima yayi yace eh ina sane so nake sukoma, kema naso mukoma ammah hakan bazai yuwuba saidai muje umara tunda mefaruwa ta riga da ta faru.
Ido tazuba masa cikin rashin fahimtar maganarsa.
'Daukan sultan yayi yamik'e yace bari inje inshirya inzo inkaisa gidan shaheed wajen meenal daga chan zan wuce fada tunda gabad'aya yanzu memartaba ya daina shiga sha'anin mulkin ya sakar min komai....yana fad'in haka yawuce yashige bedroom d'insa.
Zarah da kallo tabisa cike da son mijin nata sai kuma chan tamik'e tabisa bedroom d'in ganin sultan tayi zaune saman gadon yarima yana shan chocolate yana game da wayar yarima, inda yarima yake cire kayansa zai shiga wanka, takawa tayi ta isa inda yariman yake nan tashiga tayasa fuskarta d'auke da murmushi, rungumeta yayi jikinsa yace sweetmee wannan murmushin fa?
Kwantar da kanta tayi saman k'irjinshi tace hearty baka bari muka ida magana ba zaka fita.
Shima k'ara rungumeta yayi yace kijirani da nadawo zamuyi magana kinsan a yanzu haka nasan waziri yana chan yana jirana dan shima so yake ya aje mulkin yadamk'a ma shaheed.
Cikin wata irin murya tace toh shikenan hearty muje intayaka yin wankan.
Nan suka shige toilet sukabar Ameer zaune yana shan chocolate yana game.
A tare suka fito kowa d'aure da towel suna dariya nan suka shirya, ido tazuba ma suhail lokacin da yake sa alkyabba, juyowar da zaiyi nan suka had'a ido murmushi yasakar mata yace sweetmee wannan kallo haka ai sai kija infasa fita.
Fari tayi mashi da ido sannan tace duk cikin sonkane hearty, rungumota yayi tare da had'a goshinsu waje guda suna aika ma junansu wani sihirtaccen kallo,
muryar Ameer sukaji ya ce daddy kazo kakaini wajen meenal,
Janye zarah yayi daga jikinsa yarik'e hannun Ameer sannan yace baby bari muje sai mundawo.
Duk'awa tayi tace Ameer so kake daddy yatafi yabar mummynka ko?
Girgiza kai yayi cikin maganarsa yace a'a mum kibari inmuka yi wasa da meenal zanzo inkaiki wajen granny sultana.
Shafa kansa tayi tare da bashi peck a goshi tace toh shikenan my boy ina jiranka.
Shima peck d'in yabata a kumatu sannan tad'ago takalli yarima tace please hearty kar ka dad'e.
Kar kidamu baby zan dawo dawuri, hannu tasa tarufe ma Ameer ido sannan tayi ma yarima kiss a baki.
Murmushi suka sakar ma juna tace adawo lafiya my heartbeat.
Allah yasa baby nan tad'aga masu hannu har suka fita.
Take masa baya guards d'insa sukayi nan yasa Ameer a mota yace akaishi gidan shaheed sannan yawuce yagaishe da su memartaba da yake fama da ciwon k'afa bayan sungaisa yaje yagaishe da su ummi da sultana sadiya daga chan yawuce fada.
Wajen k'arfe takwas koda yadawo yatarar da zarah har tayi bacci nan yai shirin baccinsa sannan yahau gadon kallon zarah yayi da tabaje tana ta kwasar bacci ahankali yad'age rigarta yakai hannu yana shafa cikinta daga k'arshe yad'aura kansa saman cikin.
Jin abu samanta yasa tafarka daga baccin da bata dad'e da fara yinsaba, kallon yarima tayi tashafa kansa sannan tace hearty me kakeyi nan?
Murmushi yayi batare da ya d'ago kansaba yace ina gaisawa da baby na ne.
Zaro ido tayi tace wane irin baby?
Sai a lokacin yad'ago yakalleta yace Wanda yake manne a cikinki.
Karufan asiri ni banda komai.
Murmushi yayi yace taya kike tunani zan k'ara bari kisamu ciki batare da nagane ba, wanchan karen ma dande ban maida kaiba ammah ai naga alamomi kawai jin kai ne yahana intabbatar da hakan.
Ajiyar zuciya tasafke tace toh taya akayi kagane ina da ciki bayan ni kaina bansan da shi ba.
Rungumota yayi jikinsa yace baby ko kin mance ni doctor ne? Insha Allahu nan da wata shidda zaki haifo min wani babyn.
Zaro ido tayi tace nashiga ukku yanzu har ina da ciki wata ukku batare da na saniba?
Jan hancinta yayi yace toh kidai shirya ni d'in kinsan ba ma wasa bane.
Marairaicewa tayi tace toh ammah duka fa Ameer shekararsa ukku.
Toh ai ya ma kwana biyu ai na gama wasa duk bayan shekara biyu zaki dinga haihuwa Insha Allahu k'ara ma kishirya dan mijin nan naki yana da son yara, wlh zarah indai kece bazan damuba dan inaso inga kin haifar min yara kodan susamu irin tarbiyanki, dan halayyarki ce ta kirki tacanza min rayuwa, tabbas na yarda kud'i basu bane rayuwa, rayuwa medad'i itace aginata akan ilimi na addinin musulunci, duk kud'in mutum indai baida ilimi toh bai cika mutum ba yana da tauwaya a rayuwarsa, a kodayaushe ina k'ara gode ma Allah da yamallaka min ke a matsin matata tagari wlh wani lokacin har ji nake kamar ba zan iya rayuwaba in babu ke, zarah kece komai nawa, ina fata zaki cigaba da haifamin yara masu irin tarbiya da hak'urinki wad'anda duniya zatayi alfahari da su.
Rungumesa tayi kamar zata maidasa cikin ciki hawaye suna fita daga idanunta tace nagode sosai mijina Allah yabarmu tare, duk abinda kakeso toh nima shi nakeso dan ka riga ka zama ni nima nazama kai fatana Allah yabarmu tare har k'arshen rayuwarmu, ka gama min komai a rayuwata kaine silar dawowar duk wani farin ciki nawa, a kodayaushe bakina cikin yi maka addu'a nake dan addu'a ce kawai zanyi maka inbiyaka abubuwan da kakemin, kaduba kaga gidan da su mama suke zaune yanzu babba ne sosai kuma kai kamallaka masu, sannan duk wata sai ansafke masu kayan abinci, hatta su yaya rauda baka barsuba kullum cikin kyautata masu kake sannan.......cikin sauri yarima yasa hannu yarufe mata baki yace baby ya isa haka duk abinda nayi ma su abba cancantace tasa haka ko da ace bana aurenki zan iya yi masu fiye da haka, kukan ya isa haka dear indai ba so kike nima inyiba, cikin sauri tagirgiza kai tace a'a kar kayi,,,harshensa yasa yashiga lashe mata hawayen fuskarta bayan ya gama nan yashiga yi mata rad'a a kunne chan sai suka saka dariya gabad'ayansu, turesa zarah tashiga yi tace nak'i wayon naka ni kak'yaleni.
Rik'o hannunta yayi yace please dear kitaimaka min.
Tallabo kansa tayi tatura bakinta cikin nasa nan suka shiga kissing d'in juna kowa yana nuna ma d'an uwansa k'warewarsa cikin salon so daga k'arshe yarima suhail yajanyo blanket yarufesu.
_Laifin dad'i k'arewa_
_*Alhamdulillah* anan muka kawo k'arshen wannan novel mesuna *YARIMA SUHAIL* abinda muka fad'a daidai Allah yabamu ladar kurakuren da suke ciki Allah yayafe mana_
_Fatan alkhairi agareku dukkan masoyana naji dad'i kuma nagode ma Allah akan yadda wannan novel d'in yasamu kar6uwa sosai a wajenku_
_Duk wani wanda nata6a 6atamawa ina fata zai yafemin domin duk d'an Adam ajizine tsakanin harshe da hak'ori ma ana sa6awa balle tsakanin mutane, Allah yayafe mana gabad'ayanmu al'ummar musulmai_
_Daga k'arshe ina taya dukkan d'aukacin al'ummar musulmi murna akan wannan wata mai albarka da zamu shiga, ina fata Allah yabamu ikon shiga watan ramadan lafiya sannan yabamu ikon azumtarsa, ya ubangiji kasa muna daga cikin bayinka wad'anda zaka 'yantar a cikin wannan watan me albarka_
_Sis Nerja'art takuce a duk inda kuka kasance masoya,😍👍_