Tsayawa yayi ya sayar masu abinci sannan suka tafi ,koda suka iso gidan cewa tayi bara ta fito ba wallahi ……
Cikin lallashi yace "kiyi hakuri ki fito kinji Twee kinga dare yayi har 10 fa ……wallahi banyi dan na sakaki kuka ba i want to examine wther you love me or not……"
Banza ta mashi tana kallon gefe guda ……
Wata mota da yaga anyi yayi parking nesa dasu…… yasa ya waiga yana kallon motar na yan mintuna wadda dama ya lura tunda suka taho ake binsu……
Kallonta yayi sannan ya fita ya bude gate din ya shigar da motar yayi parking……
"Ki zauna anan karki Fito kinji ko?……idan ba ni nazo na bude ba……"ya fada yana kokarin fita daga motar ……
Tabe baki tayi ba tare da tace komae ba……
juyowa yayi yana kallonta sannan yayi Kissing dinta a kumatu tare da bude motar ya fita yana kallonta ……
Binshi tayi da kallo har ya bude kofae falon gidan ya shiga……Sannan ta lumshe ido a hankali ta kwantar da kanta baya
Mutane suka fara dirowa cikin gidan su kusan 12 Ko wane rike da makami……
Tana dagowa gidan ya gauraye da haske A rude ta fara binsu da kallo daya bayan daya……
JB ta hango rike da katuwar bindiga yana nuna masu kofar gidan ……Ganin sun shige cikin falon yasa ta fara kokarin balle kofar ta fito……
Duk iya kokarinta ta kasa ashe ya rigaya ya rufeta ta waje ……Wani irin ihu ta saki da karfi tana dukan glass din motar tare da kwala Abdul maleek kira……
Abdul maleek da tunda ya shiga gidan ya zauna falon hankalinshi bai kwanta da motar da ya gani ba ……Yana jin lokacin da suka diro ya kira wani police officer yana fada mashi……
Uban bugun da aka kai mashi da kasan bindiga ya sashi sakin wayar kasa ……kallo ya bisu dashi har ya tsayar da idonshi kan JB dake harde saman kujera tun zuwansu……
"Ina take ……?JB ya fada da idanunshi kamar garwashi……
"Wacece ……? ya tambaya yana watsa mashi wani fitinanen kallo
"Ku fada mashi ko wacece……"Ya fada tare da kallon yaran da suka zo tare……
Su duka suka rufeshi da duka…… duk da yana kokarin ramawa amma sae da suka mashi laga laga ……
"Where's she……?JB ya fada cikin tsawa
"Yanzu na tabbatar Kai ba namijii bane Jabir !macece cikin kayan maza…… tun da har ka dauka wadannan karnuka aka mace ……"Ya fada a galabaice
Yar dariya yayi yana fadin "Kae da kake namiji yanzu sae ka gwada taka jamurtar……"
Kafin su ankara ya saka kafa ya farde jabir din har sae da kanshi ya daki tiles da karfi ……Bugu sauran yaran suka rufeshi dashi wasu kuma na yankarshi har sae da suka barshi kwance ……
Sannan yasa Yaranshi suka bincike kaf gidan amma babu ita……Har karkashin bed da cikin drawers suka bincika amma babu ita duk wani lungu da sako na gidan sae da suka bincike amma babu ita……Suka dawo suka fada mashi ……
Bakin bindiga ya buga mashi yana fadin "Tana Ina……?
"Ban sani ba……"ya fada yana dafe da inda aka dakeshi……
Safeena kam wayarta ta lalubo cikin kuka ta fara kiranshi……
Ganin haske ya sa JB ya kai hannu ya dauki wayar "TWEE……" Ya gani bisa screen din ……
"Tana kiranka……"JB ya fada yana murmushin mugunta……
Da sauri Abdul maleek ya kai kafarshi ya hankade wayar ta fadi kasa ta tarwatse……
Wani daga cikinsu ya kai mashi yanka a gefen hannunshi na dama ……Dafe gurin yayi tare da sakin karamar kara ya duke don har bone dinshi sae da ya fito ……jini kam kamar an bude famfo ……
Wayar JB ya dauka tare da hadewa ya kunna ……tana kawo haske Safeena ta sake kira ……dauka yayi tare da sakata speaker……
"Ki fito daga inda kika boye…"
Cikin kuka ta ke kiran sunan Abdul maleek ……
Tsawa JB ya daka mata yana fadin "Kina ina nace wallahi idan baki fito ba na zo na nemoki da kaina sae na kasheki sannan na kashe Abdul maleek idan kunso ya RAYU DAKE a lahira……"
Kamar ana fizgar lumfashinta take fadin "Kar ka mashi komae Jabir zan fada maka inda nake yanzu ……"
Da karfi Abdul maleek yace "No Safeena karki sake ki fada masu……"
Yana jin lokacin da ta saki kuka tana fadin "Ina cikin……"
Kukan kura yayi ya warce wayar tare da bugata a jikin bango ta yarda barata sake amfani ba ……
"Mu tafi dashi oga Zata kawo kanta ……"Wani daga cikinsu ya fada
Mikar dashi sukayi da tsiya suka fito dashi harabar gidan jini na fita sosae daga jikinshi……
Tana kokarin kiran wayar JB taga sun janyoshi kayan dake jikinshi kansu sun canza kala ……
Uwar kara ta saki tana buga glass din motar da karfi ta yarda zasuji……
Su duka hankalinsu ya dawo gurin tare da sakin Abdulmaleek din sukayo kanta ……
Tambayarshi keys din sukayi yace bara ya bayar ba ……Kara yankarshi sukayi……ya tafi kamar zai fadi yayi saurin dafe kofar ……
Buga kofar take cikin kuka take fadin "Ka basu Abdul maleek dan Allah……"
Girgiza mata kai yayi yana fadin "I Wld'nt Safeena……"
"Kuyi ta dukanshi har ya fito dashi ……"JB ya fada tare da juya baya ……
Kamar ranta zai fita take fadin "Ka daina Jabir…… na roke dan Allah ka daina dukanshi it griefs JB ……"
Jin yarda take kukan ya sa Jabir din juyo wa yana masu alamar dasu dakata sannan yace "Kina sonshi ne?
Bata san lokacin da ta dinga daga mashi kai ba tana fadin "Ina Sonshi jabir…… dan Allah karka cutar dashi……"
Da sauri Abdul maleek din ya daga kai yana kallonta ……
Kallonta JB d yayi da idanuwanshi kamar garwashi sannan ya kalli Abdul maleek din tare da gyara bindigarshi yana fadin "KO WA YA RASA……" Tare da saita Safeenar ya harba……ta cikin glass bullet ya huda tare da nutsewa a kafadarta ta haggu……
Kara ta saki da karfi tayi baya ta daki dayan glass din motar ……zaya kara harbinta Abdulmaleek din ya saka kafa tare da tadiyeshi ya fadi yana dukanshi da karfi ……
A hankali yake fadin "You'll pay for this JB ……"
Karan motar yan sanda ta su suka bi ta katanga suka dire su dukansu ……
Da gudu ya fara laluben flowers din dake gefen motar har ya fito da keys din ya bude ya shiga tare da rungumota yana girgiza fuskarta ……cikin kuka yake fadin "Dan Allah ki tashi Safeena despite the fact you're the light that brighter my heart,you're are everything to me i'm lost without you……"
Shigowar yan sandan ya sashi kwantar da ita cikin motar tare da fitowa ya koma driver sit ……
Da sauri police ya matso yana fadin "Sorry……Bamu da petrol lokacin da ka kira……"
Tsawa ya daka masu yana fadin "If any one of you step one hnds here I'll chop his legs wallahi ……Me zaka man yanzu ?meye amfanin ku?baku da wani amfani a rayuwar yan adam ……aikin kawae sae criminals sun tafi sannan ku zo da uzurinku na banza……Kar wanda ya matso kusa damu bama bukatar komae daga gareku……"
Kunna motar yayi ya fita daga gidan ya barsu tsaye cirko cirko……
Tuki yake amma hankalinshi naga Safeenar ……duk bayan seconds sae ya juyo ya kalleta ,har yayi parking cikin asibitin sannan ya fito da sauri tare da balle marfin motar ya daukota ……Sae da ya shiga asibitin sannan ya lura da police din da ya biyoshi ……kallon daya ya mashi ya watsar tare da sakin tsaki da karfi……
Nurses suka karbeta aka shiga da adjoin ……
Kamashi wani nurse yayi don ganin ciwon dake cikinji ……da sauri ya dakatar dashi yana fadin "Karka damu dani kaje ku dubata……"
Sae da wata nurse ta fito tace mashi an cire bullet din sannan ya yarda sukayi treating dinshi ……
Ana fitowa da ita ya bi bayansu har aka shigar da ita wani daki da ke da duhu ……Cewa akayi kar ya shiga amma bai kula kowa ba ya shige tare da zama gefen gadon yana shafa fuskarta ……
Kamar karamin yaro ya dinga kuka yana surutai……
《》《》《》《》
Su JB kam suna barin gidan guest house na babanshi suka nufa ……Kudinsu ya basu suka tafi sannan ya zauna dafe da kai kamar zuciyarshi zata fito saboda masifar bugawa……
Fitilon dakin suka dauke lokaci guda Sannan lalubayen dakin suka fara yayewa yayin da kara ta cika dukka dakin ……Ko gizau baiyi ba ya mayar da kai ya kwantar yana dafe da gefen zuciyarshi ……
Wani farin abu kamar gawa yaga ya fara nufo inda yake ……
Wayarshi ya fara laluba yana kokarin kunna flash din ……kifar da wayar akayi kasa tare da kifa mashi mari ……dafe gurin yayi yana fadin "Yanzune zaa sha banban don bana daukar duka daga ko wane shege……"
"Ko zaka rama yanzu ma……" Yaji maganar na fitowa daga bayanshi ……
Murya na sarkewa yace "Fito idan kai babban shege ne kaga idan ban rama ba ,don wallahi bana daukar rainin duka ninan namijin dan iska ne wallahi……"
Haske ya gauraye dakin ta ko'ina ……tare da kida kamar ana dukan ganga……
Ta bayanshi aka taboshi……
A hankali ya fara waigowa yana fadin "Yanzu kau zan gwada maku nima shegen kaina ne ……"
Dafe wandonshi yayi yana fadin "RABBANA ATINA FID DUNIYA……"Ganin wata mummunar bakar halitta sanye da korayen kaya ……duk hakorinta daya yafi karfin bakin mutun daya ……idanuwanta na fitar da wani irin jini yayin da gashin kanta ke jan kasa……
Cikin wata hargitsartsar murya take fadin "Gani ka rama namijin dan iska……"
Jan numfashi yake da karfi ya kasa furta ko da kalma daya har lokacin yana rike da wandonshi da ke kama da an wankeshi……
Matsowa ta fara yi jikinshi yana jan baya har ya kai jikin bango ……
Cikin tsawa tace "Ka rama babban shege ko sae na kara maka wani zaka hada ka rama……"
Lokaci guda tayi girgiza ta dawo sak Raliya da suka hadu india ……kafin ta sake juyewa ta zama raliyar da yakai Fadama ……sannan ta zame masa yarinyar da ya kora shekaranjiya……
Kallonta kawae yake yana fitar da numfashi yayin da zufa ta wanke mashi jikinshi ,fitsari kam yayi ya kai sau biyar nan take ……
Dariyar ta saki da karfi sannan ta kai hannunta zata sake marinshi ……
"QUL HUWALLAHU……"Ya fada tare da sulalewa jikin bango yana fizge fizge kamar mai farfadiya……
Dariya ta saki tana fadin "Ka dade kana wa yaudarar yan mata ta hanyar yi masu alkawarin aure amma da zaran bukatarka ta biya sae ka wulakanta ……nima na maka alkawarin aure kuma bama sabawa Jabir……"
Wani abu ta hura mashi sannan ta bace bat kamar walkiya……
《》《》《》《》
Kwana Abdul maleek yayi kusa da Safeena ko nan da can bai je ba ……Haka ya hana idonshi bacci gudun kada ta farka yana bacci ……
Bai kuma kira kowa ba har garin Allah ya waye ……haka ya wuni ko abinci baici ba ……yan sanda kuwa sunyi shigowa yafi 10 wae sunzo investigation ne……ko kallon inda suke bayayi don baiga amfanin yan sandan nigeria ba da sae an gama mugun abu sannan ka gansu……
Wajen karfe 6 na marece sannan ta fara bude idonta a hankali,……
A rude yasa hannun ya ida bude mata su yana kiran sunanta "Safeena ……
"Kalleni dan Allah kinji Safeena Abdul maleek ……"ya fada lokacin da ya gama bude mata idanun da hannunshi ……
*FEEDOHM💞*
[2:31PM, 11/17/2017] Feedohm💞: *💧💧 ZAN RAYU DAKE🌹*
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
© *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM💞_*
*Devoted to Ummi A'isha👌🏻*
*Bestowed to Aunty Sis💕*
,
*51 to 52*
"Bude idonki ki Kalleni kinji Safeena Abdul maleek ……"ya fada lokacin da ya gama bude mata idanun da hannunshi ……
Sae da ta maida idon ta rufe da sauri sannan ya tuna abunda yayi bai dace ba "Sorry ……"ya fada a hankali
Bude idon tayi tana kallon gefen hannunshi dake nannade da bandage sannan ta saki kuka a hankali tana fadin "JB ne Abdul maleek……Shine ya yankeka ,bayya da imani sae da nace mashi karka yayi amma yayi Allah bara ya barsa ba wallahi mugune……"
Lumshe idonshi yayi yana jin kukan nata har cikin ranshi ……Rungumeta yayi sossae yana fadin "Ki bar kuka kin ji Insha Allahu muna cikin kariyar Allah kuma,nima bazan kyalesa ba ……"
A Hankali tace "Yana so na mutune Abdul maleek……?
Da sauri yace "Ko yana so ko bayya so nothing will happen to you ……"
Sae da kalleshi sannan tace "Zai sake zuwa nan Abdul maleek ……Mun tafi gurin Abbana……"
"Bara ya zo ba kinji ko……"ya fada cikin sigar lallashi tare da kara rungumeta sossae……
Sun dade a haka sannan ta dago idonta tana kallonshi ……Shima kallon nata yake kafin ya sa hannun ya rufe idonta yana murmushi ……
"Menene……?ya fada cikin kunnenta har lokacin hannunsa na saman idonta ……
A Hankali ta sa hannunta saman nashi tare da cirewa tana aika mashi da wani irin tsadadden kallo na musamman ……
Sannan ta Lumshe ido a hankali tana fadin "Last tima i asked you Abdulmaleek How did you bear when i insulted you so badly without understand you amma baka bani amsa ba am appolozed……"
Rungumeta yayi yana fadin "I see your love on me behind every word you say……I love you"
Shiru tayi tare da zagaye hannunta da baya da ciwo a jikinshi ……likitan ya shigo yana fadin "Patient dinka ta tashi amma bakayi reporting ba kana nan cikin lovers trcts ko?Ga magunguna nan ya kamata ku samu abu liquit kuci sannan ku sha ku duka sannan kaima ka kwanta ka huta saboda yanayin jikinka……"
Langwabe kai yayi yana fadin "Help,me doctor ga kudi ka bada a sawo mata ni bana bukata ……"
Sannan ya maida hankalinshi kanta yana fadin "Da na tashi kuka zakiyi ko Twee……?ya karashe maganar yana kallon fuskarta
Kadan ta murmusa cike da kunyar likitan ……
"Ba wani kai dae ne zakayi kukan idan ka tashi……ya kamata ka kwanta ka huta tunda ta tashi ko……"likitan ya fada tare yin gaba yana fadin "zaa kawo,maku abinci ka tabbata ta ci kaima ka ci dan Allah sannan kusha magani……"
"Okey……"ya fada a hankali tare da bin likitan da kallo har ya bar dakin……
Wani Police ya shigo ya zauna yana fadin "Sir ya mai jikin……"
Kallon zanci gidanku ya mashi sannan yace "lafiya……"
"Zaka iya fada mana cikakken sunan wadda aka harba……"
"A'a ……"ya fada kai tsaye
"Me yasa?ya kamata ka bamu hadin kai domin gano wadanda suka maka wannan aikin……"ya fada yana kallonshi
Wani kallo ya watsa mashi yana fadin " Bana tunanin nan da Shekara goma zaku iya gano su ……please Get out……!
"Amma……"
Katse shi yayi yana fadin "Baka san kofar da ka shigo bane?alright ka juya lefthand side dinka zaka ga door akwae dan karfe a jiki sae kayi clicking ,idan ya bude sae ka fita ka bani guri……"
"Kayi hakuri lokacin da ka kiramu motar mu babu petrol sae da aka kira commissioner ya aiko da kudin sannan……"
"Shi yasa nace baku da amfani yanzu……Dan Allah ka fita……"
A sanyaye ya fita…… bai damu da abunda Abdul maleek ya mashi ba tunda yasan laifinsu ne da basu zuwa cikin gaggawa ……
Nurse ta shigo rike da katon flask dauke da ruwan zafi sae kamar Cler a hannunta da Plates……
"Thank you……"Abdul maleek ya fada bayan ya karba sannan ta juya ta fita ……
Chips ne a cikin Cler din ……ya juye yana cije bakinshi saboda hannunshi da ya rike yanzu ……
Kallonshi tayi tare da karban Plate din da hannunta mai lafiya ta aje gefe guda ……
Zaiyi magana ta daura hannunta saman lips dinshi tana jefa mashi wani fitinannen kallon da yasa shi dauke idonshi da sauri ……
"Go nd brush……"ta fada ba tare da ta kalleshi ba ……
A Hankali ya mike yana tafiya har ya isa toilet din ……
Brush yayo ya dawo yana mika mata hannu alamun ta taso itama tayi ……
Hannun nata mai lafiya ta bashi ,ya jata har toilet din tayo brush tare da alwala sannan suka dawo ,suka zauna saman gadon……
Tea din ta ta hada a cup sannan ta kai bakinta ta sha kadan tare da janyewa ta daura saman nashi ……
Lumshe ido yayi a hankali sannan ya bude yana kallonta ,cikin sanyin murya tace "Ko da zafi ne……?
Murmushi yayi ya hade cup din da hannunta ya rike yana kallon kyakykyawar Fuskarta ……
" Kullun kai ke Feeding dina Abdulmaleek……don Allah yau ka barni nayi naka……"ta fada muryarta rawa
Sakin hannun yayi a hankali yana kallonta tare da lumshe ido ……
Chips din ta debo ta saka mashi a baki ……sae da ya hadiye sannan ya bude ido tare da kama hannunta ya debo wani ya kai bakinta ……Janye idonta tayi daga kanshi tare da bude bakin ta saka tana murmushi mai fitar da ainahin kyawunta……
A haka suka ci abincin har suka koshi sannan ta janyo magani suka sha tare da kwantar da kanshi saman cinyarta tana fadin "Sleep……"kusa da kunnenshi ……
Lumshe ido yayi yana shakar kamshinta farinciki na ratsa dukkan zuciyarshi ……Bai san lokaci da bacci yayi gaba dashi ba ……
Murmushi tayi lokacin da ta fahimci yayi baccin tare da saka hannunta tana zagaye dukkan fuskarshi a hankali ……Sannan ta cusa yatsunta cikin sumar shi……
"I Love you……"ta fada tare da pecking goshin shi……
Wayarta ta janyo tayi dialing number Abbanta cikin saa ya dauka ,bata fada mashi abunda ya faru ba sae dae tambayarshi da tayi yaushe zai dawo……
"Nan da sati daya Safeena……"ya fada kai tsaye
Daga haka suka cigaba da firansu ……
Sunfi awa daya sannan ta aje wayar tana kallon Abdul maleek da har lokacin bacci take cikin natsuwa ……
Hannu ta kai ta Shafi wuyanshi ,da Sauri ta janye jin jikin nashi kamar wuta ……haka nan taji kwalla na neman zubo mata ……
Kwanto da kanta tayi bisa kanshi tana fadin ……
"Sorry……Allah sae ya saka maka wallahi……"
【】
Tun suna Asibitin Hajiya tace a zubar da cikin amma likitan yace idan aka kuskura aka zubar dashi to wallahi zata iya mutuwa saboda ciwon dake tare da ita ……
Duk da hakan bata yarda ba Aunty Fatee ta aika wani asibitin ta karbo mata wasu taps ta dawo ……
Ranar da ta shasu kamar zata mutu amma cikin yaki fita ……
Satinsu biyu asibiti sannan aka sallamesu wanda har lokacin barin jikin hajiyar baya amfani……
Aunty Zuby kam keken guragu aka bata ta dinga amfani dashi idan taji sauki ……kuka sosaae tayi da ta tabbata da ta riga ta zama gurguwa……Babban tashin hankalinta da akace hajiya nada HIV ita ma ta san bata rasata tunda kamar yarda boka ke kusantar hajiyar ita ma haka yake kusantarta ……tayi kuka kamar ranta zai fita tare da nadamar rayuwarta ta baya……
Gashi tunda aka kawota asibitin sau daya dadyn su Fadila ya leko ……yanzuma da Aunty fatee ta kirashi tana tambayarshi ko gidanshi zaa maido Aunty zubyn cewa yayi aa ta zauna gidan hajiyar ba sae ta dawo ba……
Fadila ma jini sae abunda ya cigaba tun tana sa ran daukewarshi har ta fitar da rai domin har kananan Tsutsa ke fita wani sani ……
Set na gold din Aunty fatee ta sace taje ta sayar dashi dubu dari da hamsin ba tare da kowa ya sani ba taje asibitin zaria aka hado mata magunguna ta dawo ……
Sauran kudin kuwa taci gaba da kashewa abunta……
Uncle Abbah ma duk da magungunan da yake sha amma abun yaki sauki ……wani irin jini ke fita daga cikin kurajen sossae ta yarda baya da damar saka wando sae ya baci ga tsutsa da yanzu sae uku ta fito lokaci guda……
Kullun yana zaune da yar shara sae ya daura zani a ciki ta yarda rigar barata baci ba ……
Tunda suka koma gida Aunty Fatee ke hidima dasu don dawowa tayi gaba daya gidan da zama kwanansu biyu ta fara gajiya da hidimarsu komae ita ke masu hatta kashi nan hajiyar ke yinshi sae dae ita zata wanke mata ……
Saukinta ma da Mijin,Aunty bilki ya saketa wai tana mashi sata
Sai ta dawo gida tana taimaka mata …
Shima ba komae take iyayi ba sae ta ga dama……
【】
Ganin har an kwana amma JB bai dawo ba yasa hankalin mum dinshi ya tashi ta sami Dad dinshi ta fada mashi ……
A fusace yace "Wae taya zaki takurawa yaro da girmanshi ,Jabir bai isa ya kwana bane a waje ?koko yarone da zaa matsa mashi dole sae ya kwana gida……"
Kwantar da murya tayi tana fadin "Ba haka nake nufi ba ,naga bai taba kwana ba har ya yini bai dawo gida ba ……"
A Zafafe yace "To yau ya kwana har ma zai kara kwanan sae muga wanda ya isa ya takurawa yarona……"
Tabe baki tayi zata juya taji yana fadin "Ki sa ahada abinci sossae zanyi baki daga abuja yanzu ma zan fita na daukosu don a guest house dina zasu sauka……"
Banza ta mashi tana gunguni ta fita……
Ko da yaje ya dauko bakin nashi daga airport guest house dinshi ya nufa dasu ……
Da yake duhu ya fara ya bude masu falon suka shiga suka zauna ba tare da sun lura da Jabir dake sandare gefen falon ba ……
Sai da aka kunno Gen sannan suka ga mutun kamar gunki tsakiyar falon ……
Su duka suka mike tana kiran "Ekilisiya……"abunka da ba musulmai ba……
Dad dinne ya isa gurinshi tare da dagoshi a rude yana kiran sunanshi ……Shirun da sukaji ne yasa wani mai karfin hali ya dauko robar ruwa suka watsa mashi ……
A firgice ya bude ido yana fadin "Muga dan iska a cikinmu……"yana yi yana karkada kai ……
Dad din ya rungumoshi yana fadin "Jabir me ke faruwa……?
"Muga dan iska a cikinmu ……"Abunda ya fada kenan tare da angaje Dad din ya ruga da gudu zaya fita daga falon ……
Bakin Dad din sukayi namijin kokari gurin kamoshi sannan suka turashi mota aka nufi asibiti dashi ……
A Can dinma sai da aka daureshi ya tsaya duk wanda yayi magana ko ba dashi yake ba to shi zai bashi amsa da "Muga dan iska a cikin mu……"
Duk abunda zaa mashi akayi sannan aka mashi allurar bacci likitan yacewa Dad din ba maganin asibiti bane ya dace dashi ……
A Maidashi gida a nemi wani malami ya mashi addu'a……
Wulakantaccen kallo Dad din ya aikawa likitan yana fadin "Kawae kace bara ku iya ba amma babu abunda yafi karfin asibiti……"
Cikin natsuwa likitan yace "Wallahi alhaji ba maganin asibiti ya dace dashi ba……"
Dariya dad din yayi ta izgilanci sannan yace "Kamar yarda ubanka ya kashe maka kudi aka baka kwalin wannan aikin haka nima zan kashe kudi ko wane asibiti ne na samama dana lafiya……"
Shima kallon Dad din yayi a wulakance sannan yace "Kamata yayi ka kashe kudi a bawa dan naka irin kwalina sae ya nemawa kanshi magani ……asibiti kuma daga nan har Sin ka kai danka dole ku dawo a nemi wanda nace ……marasa mutunci"
Daukar Jb din akayi suka tafi gida dashi ……Mum din na ganinshi ta hau ihu da kururuwa kamar diyar arna har sae da Dad din ya taka mata birki sannan ta zagaita tana fadin "Waya maka haka Jabir……?
"Muga dan iska a cikinmu……"abunda ya fada yana kokarin bude da idonshi dake rufe ……da yake bata san abunda ke faruwa ba sae cewa tayi ……
"Haba Jabir nice mum dinka me ke faruwa haka ?waya maka haka?
"Muga dan iska a cikinmu ……"
Zata sake magana Dad din ya taka mata birki dole tayi shiru……
*FEEDOHM💞*
[3:07AM, 11/19/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
© *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM💞_*
*Devoted to Ummi A'isha👌🏻*
*Bestowed to Aunty Sis💕*
*53 to 54*
Satinsu daya a asibiti aka sallamesu ……
Ishaq abokinshi ya kira ya mayar dasu gida ……
A Bayan motar suka zauna babu wanda yace kala a cikinsu sae dae kanta na saman kafadarshi……
Tana ganin sun doshi hanyar gidan ta masa wata irin cakuma tana kallonshi ……
"A'a……"take fada da karfi tare da girgiza mashi kai ……
Matse ta yayi a kirjinshi ba tare da yace komae ba ……har cikin gidan ya shigar dasu sannan ya fita daga motar jin Safeena na kuka ……
Ishaq na barin motar ta saki sabon kuka tana fadin "Kar mu zauna anan dan Allah……"
Riketa yayi sossae yana fadin "Me yasa Safeena?
"Gidan JB ne Abdul maleek dan Allah ko gidan Baffanka ne muje mu kwana amma baa nan ba ……"ta fada tana kuka a hankali……
Shafa kanta yayi tare da kara rungumeta yana fadin "Ba gidansa bane Safeena ……dan Allah kiyi shiru wallahi,bana kaunar kukanki……"
"Ban yarda ba dan Allah mu tafi ni dae wallahi dawowa zasuyi……"
"Akwae sojojin da aka kawo Safeena babu abunda zai faru da yardar Allah……"
Lekawa tayi tana kallon sojan dake tsaye bakin gate din da katuwar bindiga ……
Ihu ta sake tare da kara makalkaleshi ……
Dakyar ya samu ta yarda da ba gidan jabir bane na Ishaq ne ……Sannan suka fito har lokacin tana rungume jikinshi tana zare ido kamar karamar yarinya……
Bankwana sukayi da ishaq din ya mika masu ledar hannunshi sannan ya fita ……
Koda suka shiga falon da sauri ta rufe kofar tare da jingina da ita tana kallonshi ……
"Common ……"ya fada yare da janyota ta fado jikinshi……
"Ki saki jikinki kinjo Twee……"
"Idan suka zo fa……"ta fada a,hankali…
Daukarta yayi ya daga sama yana fadin "Bama zasu zo ba……"
Shiru tayi har lokacin tana mazurai ……da wayau ya samu ta shiga dakin tayi wanka sannan suka fito ya jasu sallah ……
Ledar Da ishaq ya basu ya bude ya fito da Potato'n chicken bundt dake ciki ya juye masu a plate yana kallonta ……
Yatsina fuska tayi tana kallon gefe guda har lokacin jikinta bai koma dae dae ba……
"Eat……"ya fada tare da janyo hannunta ya daura saman,spoon din yana kallon blming face dinta……
Girgiza kai tayi tana lumshe idanunta a hankali tare da jingina da kujera……
"Eat kinji Twee……"
"Bana ci……"ta fada a takaice……
"Me yasa?ko bakya sonshi ne……?ya tambaya cikin sigar lallashi
Gyada mashi kai tayi alamun Eh ……
"To me kike so……?Ya fada a hankali
Cikin Salo tace "Awara……"
Dariya ya saki mai sauti yana kallonta tare da sake maimata Awaran a fili ……
Turo baki tayi tana kallonshi ta kasa kasa ……
Still murmushi yayi yana shafa sajenshi sannan yace "Ina zan samo awara yanzu Twee……"
Ware Hannayenta tayi tare da bude manyan idanunta tana kallonshi ……
Murmushi ya kuma yi sannan ya mike yana fadin "Bara naje na bayar a sawo maki ……"
Bata ce mashi komae ba har ya fita sae dae gabanta dake faduwa da karfi ……
Har ya bar falon ta bishi da gudu tare da rungumeshi ta baya tana fadin "Na fasa ……bana son Awaran dan Allah ka dawo……"
Hannunshi ya sanya ya zagayota tare da rungumeta jikinshi yana kiran sojan dake tsaye bakin gate din ……
Lamo tayi jin hannunshi na yawo tsakiyar bayanta ……
Sojan ya baiwa kudin ya sawo mata sannan ya dauketa cak ya shigar da ita falom tare da zaunar da ita saman kujera ……
"Me kike tsoro……?ya fada tare da tsareta da manyan idanuwanshi ……
Dukar da kai tayi tana fadin "JB……" Kai tsaye
Kallonta yayi na yan mintina sannan yace "Baya lafiya ai……"
Da sauri ta kalleshi tana girgiza mashi kai alamun bata yarda ba……
Hannunta duka biyun ya riko yana kokarin saka idanunshi cikin nata amma taki yarda ……Yar dariya yayi mai sauti yana fadin "Da gaske baya lafiya jiya Ishaq ke fada man yanzu haka kamar ciwon hauka yake fama dashi ……"
Da sauri tace "Allah ya kara ……"
Hannunshi yasa tare da buge bakinta yana hararanta ……
Turo baki tayi tare da dafe inda ya buga tana shefa mashi hararan kasan ido……
"Allah ya baki hakuri……amma komae mutun ya maka idan kaji baya lafiya addu'a kake mashi kinji Safeena……"
Turo baki tayi tana fadin "Shine fa……"
Da sauri ya katseta yana fadin "Ko da Aunty Fatee ce Safeena……"
Da sauri tace "Allah ya kyauta wallahi ……"
Kanne mata ido yayi yana fadin "Ko……?
"Uhm……"ta fada a takaice ……
Sallama akayi tare da bashi ledan awaran sannan ya dawo ya juye ……
Zata saka hannu ya janye plate din yana hararanta ……"Ki barni nayi aikina……"
Shiru tayi tare da kallon kasa fuskarta dauke da murmushi ……
Sae da ya gama bata awaran sannan suka,mike ya rufe kofar falon suka shiga dakin dake kallonshi ……
Katon gadone a ciki an gyarashi kamar wata sabuwar amarya ……
Brush sukayo sannan ya sata tayo alwala sukayi nafila tare da kwanciya ……
Janyota yayi ya rungume kamar zaa kwace ta har sae da yaji bacci ya dauketa sannan ya mike ya kunna fitilan wayanshi yana kare mata kallo……
Ya dade yana kallonta tare da kyalla mata photo kala kala sannan ya,kashe wayar ya janyota ya rungume tare da rufesu da bargo……
【】
JB kam iyayen kudi dad dinshi ya kashe aka fitar dashi india ……
Cewa sukayi wai kwalwarshi ce ta samu matsala don haka suka dinga banka mashi allurai kala kala na kwalwa……
Amma ba wani cigaba da aka samu sae dae ci baya tunda alluran da suke mashi sun fara effecting brain dinshi ……
Hakanan sai dae aga yana fizge fizge kamar mai farfadiya baya ga surutun da hat lokacin bai daina ba……
《》《》《》
Abba kam tun da Safe ya hawo motar haya ya dawo katsina ……
Abdul maleek ya kira lokacin da suka iso yace yazo ya daukeshi……
Safeena na wanka ya zame ya fita ba tare da ta sani ba ……Sae da ta fito ta nemeshi bata ganshi ba sannan ta shiga zagaye gidan tana dubawa ……
Don tsaruwa ya tsaru Sae dae bai shigar mata rai ba tunda ta san ba nasu bane ……
Ita tama fi son su bar gidan su nemi nasu koma ko da daki dayane da toilet su zauna don bata tunanin Abdul maleek din zai koma Cikin gidajen Abbanta ya zauna……
Ko da ya dauko Abban nan gidan ya wuto dashi ……
Lokacin da suka shiga falon tana kitchen tana dube dube har ta bude wata yar kofar da ta gani a gefe ashe tulun kayan abincine a ciki ……
Maidawa tayi ta rufe tunda ta san ba nasu bane ta fito tana kakkabe hannu ……
Tsalle daya tayi ta iso gaban Abban tare da rungumeshi ……
Kafin su gama gaisawa Abdul maleek ya shiga kitchen din ya daura masu ruwan zafi sannan ya soya kwai……
Tana jin kamshi ta mike ta shiga kitchen din tana waro ido
"Waya sa ka taba masu kaya……"ta fada tare da jan kunnenshi……
Kashe mata ido yayi yana fadin "Allah ya basu hakuri……Zan biyasu idan na samu kudi……"
Cikin sanyin murya tace "To dole sae mun ci abunda bamu dashi……"
Ganin yanayinta yasa shi janyota jikinshi yana fadin "Sorry ……Sun ce nayi amfani da komae ne fa……"
Shiru ta masa tana kallonshi ……
Janyeta yayi daga jikinshi ya bata ta kaiwa Abban……
Sai da suka koshi sannan Abban yace su taso su tafi ……
Da "To……"Abdulmaleek ya amsa ……
Safeena kam waro ido tayi tana fadin "Ina?
"Gidansu Fateema……"Abban ya fada kai tsaye……
*FEEDOHM💞*
[5:26AM, 11/19/2017] Feedohm💞: *💧💧 ZAN RAYU DAKE🌹*
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
© *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM💞_*
*Devoted to Ummi A'isha👌🏻*
*Bestowed to Aunty Sis💕*
*55 to 56*
Daga Safeena har Abdulmaleek suka kalleshi lokaci guda a sanyaye sannan Abdul maleek din ya shiga daki ya fito da hijab din Safeenar a hannu suka fito……
Babu wanda yace ma wani komae har suka bar gidan sannan suka dauki hanyar zuwa gidansu Aunty Fatee ……
A bakin gate din gidan sukayi Parking kusa da inda wasu masu aikin kawo yashi suke juyewa……
Kai tsaye Abban ya kutsa kai cikin gidan ba tare da fargabar komae ba ……Daga harabar gidan suke jiyo muryar Aunty Fatee tana bala'in an dauke mata set na gold dinta kuma sae an biyata ……
Murya Fadila suka jiyo tana fadin "To Uban Wa zai maki sata a gidan Aunty Fatee……"
Kai tsaye tace "Ubanki ……"sannan ta cigaba da hargowarta……
Sallamar Abban ya sata juyowa a sukwane tana kallonshi tare da nuno shi da hannu tana fadin "Khaleed kai ne ……"
Murmushi yayi wanda yafi kuka ciwo sannan yace "Nine Fateema kinyi mamakine……?
Uban ihu ta saki tare da dafe kai tana fadin "Wallahi karya ne ba kai bane ……Hajiyarmu fito ki ga Khaleed wae shine bayan nasan karyane ya mace…… Kece Shaida ya mutu Ni ce Shaida, Zuby ma shaida ce Abbah ma Shaidane ka mutu……"
Babu mai iya fitowa cikinsu sae Uncle Abbah da ya fito daure zanin atampha yana kallon Abban ……Sannan ya koma da gudu tare da garkame kofar dakin yana fadin "Fatalwa ……wallahi fatalwace hajiya bani hijabi na shige Hajiyarmu……"da karfi……
"Shine Aunty Fatee Abbana ne ,ko kin dauka ya mutu ne da gaske……?cewar Safeena dake tsaye tana kallonsu ……
Dariya Aunty Fateen ta saki tana fadin "Ni ce Shaida ……kai wallahi malan habu ma shaidane kuma Malan bala ma shaidane ya mutu……a'a a'a ya mace nace maku ya mace ……"ta karashe maganar cikin sautin waka tare da fara soshe soshe tana wurga idanu……
Salati Abban ya dauka tare da binta da kallon ……Zuwa tayi gabanshi ta kai hannu zata kamoshi ……yayi baya da sauri yana nunata da yatsa yace "Akul fateema karki kuskura ki tabani……"
Itama baya tayi tana wurgawa Safeena kallon da ta fara tsorata da ita ……tayi bayan Abdul maleek ta boye tana ware idanu……
Daga falon ta fita tana fadin "Malan habu shaidane Khaleedu ya mace ……haka liman ma shaidane ka mace ……"Bin ta sukayi a baya Abban na salati amma kafin ta fita gidan ta gama cire kayan jikinta tsab tana fadin ……
"Nace maku ya mace tunda sae da na barbada mashi a abinci daga baya ma na juye mashi duka don yayi saurin mutuwa……Kai har Nafeesa na kashe, nace maku ta mace……"
Motar dake kwaso yashin ce tayi gaba da ita tare da bi ta samanta ta wuce ……
Ihu Safeena ta saki ganin kwalwar Aunty Fatee a tayar motar tare da kankame Abdulmaleek kamar numfashinta zai fice ……
Cikin Sauri ya kaita mota sannan ya dawo yana fadawa Abban zaije ya maidata gida ya dawo……
Mutanen gurin kam salati suka dauka bayan motar ta daki bango ta tsaya……na ciki ya fito amma ko kwarzane babu a jikinshi ……
Yan hanjin cikinta yashe saman hanya ……haka hannuwanta ko wane ya kama gabanshi ……haka a ka tattarata aka shigar da ita gidan don babu maganar zuwa asibiti……
Cikin Yan mintina labarin mutuwar Aunty Fatee ya karade ko'ina a lungun ……
Hajiya kam suna cikin gida babu kafafuwa, banda ihu babu abunda sukeyi……
Liman aka aika yazo amma ba'a sameshi ba wai yaje kauyensu ……
haka ladanin unguwar shima baya jin dadi ……
Abban ne ya taimaka aka mata wanka tare da sallah ,shima dukka mutanen basu cika sahu daya ba ……
Da yan k'warorin mutane aka tafi da ita makabarta ……
Bayan anyi kabarin da za'a sakata ne aka ga kananan kunamu jawur kwance a cikin kabarin……
Hankalin mutanen yayi bala'in tashi har ma wasu suka fara sabewa suna barin makabarta……
Abban ne ya jajirce yace su taimaka a sake wani kabarin……
Haka aka sake gina wani kabarin amma the same abunda aka gani ana farkon shi aka gani ana biyu……
Sai da aka gina kabari kusa biyar amma duk wanda aka gama ginawa kunamu za'a gani a ciki ……
Wani dan dattijo yace a saka a haka saboda idan zasu gine dukkan makabartar to da alama abunda zasu gani kenan……
Haka aka kamata aka saka cikin kunamun ……Sannan suka juya a sanyaye cikin tashin hankali suka tafi ……
Basu fita makabartar ba kabarin Aunty ya kama da wuta……
Cikin kidima suka juya suna kallon tashin hankali ……
Abban bai san sadda kuka ya kwace mashi ba yana fadin "Wallahi indae Alhaki na ne Fateema na yafe maki duniya da lahira ……Allah ka tausayawa wannan baiwar taka dan darajar Fiyayyen halitta……"
Ruwa Aka fara kawowa da kasa ana kokarin kashe wutar amma ko alamun mutuwa batayi ba ……
Lokaci guda wutar ta tsallake kabari biyu dake kusa da na Aunty fateen ta kama ana uku sannan ta kara tsallake kabari Biyar ta kama ana shiddah ……Duk da makabartar zagaye take da ciyawu busassu hakan bai shafi sauran kabarurrukan dake zagaye da makabartar ba ……
Kusan Awa uku wutar naci yayin da mutane ke zagaye da makabartar har saman gini……ruwa kan har firefighter sun zo amma a banza sae da suka gaji suka zubawa sarautar Allah ido……Wasu hotuna suke dauka wasu kuma video sukeyi wasu kam kuka suke cike da tashin hankalin da basu taba gani ba……
A hankali kuma wutar ta dinga baya har ta mutu kurmus dan kanta……sannan mutanen suka fara tafiya cike da al'ajabin tare da tambayar wace mata aka kawo me take aikatawa haka?
《Wa iya zubillah……Wallahi tallahi baku bina bashin rantsuwa abunda ya faru kenan akabarin wata baiwar Allah kuma ni,ganau ce ba jiyau ba ……Muji tsoron Allah mu gyara aiyukanmu domin karshenmu……》
Cikin mintina dukkan unguwar da kewayanta an dauka cewa an kai wata mata kabari amma kafin a fito kabarinta ya kama da wuta……
Da labari ya isa gurin su Hajiya karku so kuga tashin hankalin da suka shiga har dasu Fadila da Uncle Abbah ……
Lokacin ne Hajiya tayi kukan da ake kira kuka tare da nadama mai tarin yawa ……haka Aunty Zuby wadda dama ta rigaya ta yi nadama amma ranar sae da ta gwammace da ba'a haifeta ba har ta ga wannan bala'in ……
Abban ma kuka yayi cike da tausayinta tare da kwarara mata addu'a ……Dan zaman makokin da akeyi ma mutanen kin zama sukayi wadanda suka zauna ma suna jin abunda ya faru suka mike suna fadin ko an zauna ma babu abunda zaman zai mata ……
Haka duk suka watse suka bar Uncle Abbah da Abban Safeena durkushe ……
【】
Abdul maleek kam yayi niyar da ya aje Safeenar ya dawo amma ta kankameshi tare da sakin kuka tana dafe kai ……
Tambayar duniya ya mata ta fada mashi meke damunta amma taki magana sae zabura take tana kara kankameshi ……
Ya tabbata tsoro taji don ko ba'a fada mashi ba yasan bata taba ganin mutun a haka ba ……
Addu'a ya fara tofa mata a hankali yana rungume da ita har sae da ta fara dawowa natsuwarta sannan ya dinga maimaita mata Inna illahi wa inna ilaihir raju'un a hankali tana maimaitawa……
Kin barinshi tayi ko nan da can ya tafi tana jikinshi har dare ……sannan ya kira Abban ya fada mashi ……
Abban cewa yayi kar ya damu shi har ya wuce gida ma……
Haka suka kwana ko magana ta kasa yi sae zare idanu take kamar mage,……
Kwanansu biyu a haka sannan ya samu ta saki jikinta dashi……
【】
Tana kwance jikinshi ya zagayeta da hannunshi yana karanta mata wani english novel mai suna tears drops at the sun set……
Dukkan hankalinta ta maida akan littafin tana saurarenshi cikin natsuwa har da su lumshe ido……
A je littafin yayi yana fadin "Meye date yau……?
Dan turo baki tayi tana fadin "19 Nov 2017 mana……"
Lumshe ido yayi tare da matseta a jikinshi ……
Dagowa tayi tana kallonshi tare da shafar sajenshi tana murmushi ……
"Menene……?ta fada a hankali
Waro ido yayi ya tabe baki sannan ya janyeta ya mike ba tare da yace komae ba ……yatsina fuska tayi tana Spreading arms dinta a hankali tace "Kai ka sani ……"a hankali
Juyowa yayi yana kashe mata ido yace "Ko……?
Tsuke baki tayi ta gyada kai sannan ta mike ta dauki littafin ta koma saman one siter ta zauna tana fadin "Thank God nima na iya karatun……"
Dariya yayi mai sauti sannan ya shige daki yana girgiza kai……
*FEEDOHM*💞
[9:21AM, 11/19/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
© *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM💞_*
*Devoted to Ummi A'isha👌🏻*
*Bestowed to Aunty Sis💕*
*56 to 57*
Sae da yayi wanka sannan ya fito sanye da kananan kaya sai kamshi yake zabgawa yana waka a hankali " *ZAN RAYU DAKE* Zan mutu dake *ABADAN* Dani dake zamu zauna……"
Kallo daya ta mashi ta yatsina fuska tana turo baki sannan ta cigaba da kallon littafin don ba karantawa take ba ……
Kusa da ita ya matso tare da dukowa ya mata kiss a fuska yana kashe mata idanu ……"Twee zanta fita……"
Turo baki ta kuma yi tare da dagowa tana kallonshi sannan tace "Zan je ……"
Ido ya waro yana fadin "Ina……?
"Inda zaka ……"ta fada a hankali
Murmushi yayi mai sauti yana kallonta sannan yace "Alright bara na dauko maki hijab ,dama JB zan gano kema ya dace kije ki ganshi……" Ya karashe maganar tare da kafe ta da ido ……
Da sauri ta dago ido tana kallonshi tare da fadin "Sae ka dawo Allah ya kiyaye ka yo man tsaraba……"
Dariyar mugunta yayi yana fadin "A'a Twee ki taso muje ……"
Turo baki tayi sannan ta cigaba da duba littafin ba tare da tace komae ba ……
Lakuce mata hanci yayi tare da kissing kumatunta sannan ya fita yana waigenta……
Mintina kadan ya dawo shida wata yar kyakykyawar budurwa a bayanshi ……
Cikin Fara'a ta tari matar tare da bata ruwa ……
Sannan ta dawo saman hannun kujeran da yake ta zauna ta kashe murya tana fadin "Wannan fa?ban santa ba……"
Kallonta yayi suna hada ido ya kashe mata ido "Zata maki kunshi ta wanke maki kai ta maki kitso……"ya fada tare da kamo hannunta
Waro ido tayi tana fadin "Kitso fa kace?
Gyada mata kai yayi yana tsuke bakinshi
"Bana so gaskia……"ta fada a shagwabe……Saboda har ga Allah bata kaunar kitso
Cikin wata irin murya yace "Ni kuma ina so ……Dan Allah kiyi danni kin ji ……?
Gyada kai tayi tana mashi murmurshi na musamman tare da komawa gurin budurwa suka fara fira ……
Mikewa yayi ya fita ya basu guri……
Kunshin zallah bakin lalle yarinyar ta mata mai shegen kyau kamar an daura zanen……
Sannan ta wanke mata kanta tare da yaryara mata kitso two step kanana kanana ……wanda suka sauko har tsakiyar bayanta ……
Wani masifar kyau tayi kamar ba ita ba ……
Kusan magrib sannan aka gama ta shiga daki ta kirashi tace yarinyar zata tafi ……
Cewa yayi ta tafi kawae ya rigaya ya sallameta ……ko da ta dawo yarinyar tana tsaye bakin kofa zata tafi ……tace ta jirata ta fito……
Yan kayan kwalliya ta kara mata dasu banda 5k da ta bata sannan budurwar ta tafi kamar ta sude dob murna……don Abdulmaleek din 20k ya bata……
【】
Sai bayan isha'i ya dawo tana zaune falon sae kamshi take ……
Sae dae da ganin fuskarta kasan fushi take ……
Dariya yayi bai ce mata komae ba ya dauketa cak ya nufi da ita upstair din gidan wanda tunda suka zo bata taba gigin hawa ba……
Lamo tayi har ya bude wani daki mai duhu ya shigar da ita tare da dagata sama yana juyi da ita ……
"Ka sake ni……"
Cak ya direta kasa ……kai hannu tayi tana lalubarshi ganin dakin babu haske ko kadan tare da kiran sunanshi a hankali ……
"Dan Allah ka kunna haske ……"ta fada kamar zatayi kuka
Jinshi tayi bayanta yana kokarin zage zip din rigarta tayi saurin rikewa tana fadin "Meye kake yi haka ……"
Shiru ya mata tare da kamo duka hannunta ya matse a arms dinshi sannan ya sabule mata rigar ta kasa ……
Bai ankara ba yaji hannunshi na yawo a dukka gabobin jikinta ……
Wuyanta ya fara kissing a hankali har ya gangaro shoulders dinta ……yayin da hannunshi ya kasa zama guri guda ……
Kukan da ta sakine ya sashi lumshe ido tare da matseta a jikinshi ya bar duk abunda yake sannan ya saka mata wata doguwar riga da iyakarta guiwa……Sannan ya daura mata crown dake salki sossae……
A jiyar zuciya ta saki tana fadin "Meye kake yi haka Abdu ……"kasa fadin sunan tayi saboda nauyin da taji ya mata ……
Hasken da ya gaurayen dakin ne ya sata waro ido tana bin bangon dakin dake blming da *Happy Birthday to my Princess……*
Kallon jikinta tayi tare da kankame hannunta a hankali ta ware hannunta tana juyi a hankali tare da fadin *I Love you* da karfin karfe……
Fitowa yayi daga cikin labule ya dagata sama yana juyi da ita sae dariya take ……Sannan ya shige da ita wani dakin dake ciki wanda ke dauke da katon gado kadae……Sae katon cake din dake gefe guda shima an rubuta sunanta a jiki……
Kallonshi take irin kallon da bata taba mashi ba sannan ta ware hannayenta tana lumshe mashi ido……
Cikin Zarra ya,tako har ya iso ya shige jikinta ta mayar da hannun ta rufe tare da daura bakinta saman wuyanshi ……
Tsawon mintinsu goma a haka sannan ta jiyo kara da karfi kamar fashewar wani abu ……
"JB ……"ta fada tare da fadawa saman gado ta janyoshi ta makale ……
A kunnenta ya rada mata "Baloon ……"tare da cije kunnen a hankali……
Duka ta kai mashi tana niyar tureshi ……Duka nauyinshi ya sakar mata tare da kafeta da ido cikin salon soyayya……
Lumshe ido tayi a hankali har sae da ya gangare daga jikinta sannan ta bude tana kallonshi a hankali ……
"Ki shiga kiyi alwala ……"ya fada ido a lumshe ……
Bata san lokacin da tace "Bana sal……"
Da sauri ya bude idonshi yana kallonta tare da janyota ta fado jikinshi……
Hannu yake niyyar sakawa a pant dinta tayi saurin rike hannun……
"Cire man hannunki daga jikina……"ya fada ido a lumshe ……
Turo baki tayi kamar tayi kuka tace "Zan fa yi alwalan dan Allah karka saka ……"
"Uhum ……"Ya fada tare da hade hannunta guri guda ……
Kukan da ta sakine ya sashi yin dariya tare da sakinta ta mike……
Mintina kadan ta fito Sannan shima ya mike yayo wanka tare da alwalan ……
Prayer mat ya shinfida sannan ya mika mata sabuwar hijab har kasa ya jasu Isha'i Daga nan sukayi raka'a biyu ……
Sannan ya juyo ya dafa kanta tare da jero,mata addu'o'i……
Ita kam sai zare idanu take kamar mage har ya gama ya dauko wani katon tray ya aje gabanta……
Kajine ciki masu rai da lafiya sae kamshi suke sae Fresh milk gefe guda tare da dabino da inibi……
Ganin babu wasa ya sata karban abunda yake bata tana yatsina fuska ……kadan taci ta kauda kai shima dabinon kawae yaci ya mike ya kauda komae ya dawo ya mikar da ita yana fadin "Good ……naga yau bara ki iya komae ba sae na maki ……"
Shiru tayi har lokacin tana zare idanuwa ……
Toilet ya kaita tayo brush sannan suka dawo…
Takurewa tayi sossae tana raba idanu
Sai da ya canza kaya sannan ya miko,mata wani Glom night Pink riga da wando ……bata dauki kayan ba sae kara takurewa da tayi tana kallonshi……
Kwanciya yayi tare da janyota yana fadin "Haba Twee ki saki jikinki mana ba abunda zan maki fa……"…
*FEEDOHM💞*
[9:26AM, 11/19/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
© *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM💞_*
*Devoted to Ummi A'isha👌🏻*
*Bestowed to Aunty Sis💕*
*58*
A sanyaye ta dago tana fadin "Da gaske……"
Hararan wasa ya sakar mata yana fadin "Da da muke tare na taba maki wani abu ……?
Girgiza mashi kai tayi da sauri tana murmushi sannan ta mike ……
"To kin gani ……tashi ki sa kayanki ki taho muyi baccin mu ko?ya karashe maganar yana kashe mata ido……
Murmushi tayi ta mike ta koma toilet zata canzo kayan ……dariya yayi a hankali yana mamakin Safeena……Ta canza kamar ba ita ba ta koma wata yarinya ……
Tabe baki yayi yana fadin "Dama yarinyarce tunda yaune ta cike 20years dan dai Allah ya mata bakine……"
"Me ka ce……?ta fada lokacin da ta fito
Murmushi yayi yana fadin "Cewa nayi bacci zanyi tunda kinki fitowa hakanan ……"
Yatsina fuska tayi sannan ta hawo gadon tare da kwanciya saman jikinshi ……
Kashe hasken yayi ya mayar da ita kasanshi yana kallon yarda take wurga idanu cikin duhu ……
"Ba fa haka muke kwanciya ba……"ta fada kamar zatayi kuka
A Wahale yace "Ya mu ke to?yana shafa skin dinta
"Ni ce ke kwanciya a sama……"ta fada a hankali
Dariya ta bashi amma ya danne ya hade bakinsu guri guda yana tsotsa a hankali cikin kwarewa ta yarda bara ta ji zafi ba ……
Tun tana mutsu mutsu har tayi lagwas tana karbar sakonshi ……
Ba tare da ta sani ba ya rabata da duk wata sutura dake jikinta……hannunshi kam kyarma suke sun kasa tsayawa guri guda……
【】
Duk yarda Dad din JB ke tunanin abun ya wuce haka dole ya tattaroshi ya maidoshi gida …
Babban malami ya saka aka nemo mashi yazo ……
Rukiyya ya fara mashi cikin Saa Raliyar tayi magana da kakkausar murya tana fadin irin yan matan da ya yaudara yana lalata masu rayuwa har ya kawo kanta ……
Hakuri malamin ya bata,……
amma sae cewa tayi barata hakura ba ta riga ta aureshi……
Da kyar da addu'o'i aka samu ta fita daga jikinshi ……
Sae dae alluran da aka dinga mashi sun taba mashi kwalwa ta yarda ya koma kamar wani Dolo…
Saboda har miyau yake fita daga bakinshi……
【】
Sae da asuba sannan Abdulmaleek ya dawo hayyacinshi ……Safeena ya kallah dake gefe tana baccin wahala da kananan hawayen kwance a fuskarta sannan lokaci lokaci takan saki ajiyar zuciya……
Janyota yayi ya rungume yana kwarara mata albarka ,don har ga Allah baiyi tunanin zai sameta budurwa ba idan yayi la'akari da jinyar da tayi ……
Sai dae masha Allah cikakkiyar budurwa ya sameta,mai dumbin ni'ima……Godiya yayiwa Allah sannan ya kwantar da ita gefe guda zaya tashi ……
Kankameshi tayi sosae tana kuka cikin bacci tana fadin "Bana So Ka Daena dan Allah ……"
Lumshe ido yayi tare da hura mata iska a fuskarta ,ai kuwa tayi shiru kamar ruwa ya cita……
A hankali ya zame jikinshi daga rikon da ta mashi ya shiga wanka sannan yayo alwala yazo yayi sallah tare da komawa ya hada mata ruwan wanka ya dawo……
Kunnenta ya dinga tsotsa a hankali har ta bude idanunta ……ganinshi da tayi ya sata saurin mayar da idon ta kulle tare da juya baya ……
"Sorry na amshi laifina……"ya fada a hankalin
Banza ta mashi kuma dama yasan barata kulashi ba ……
Daukarta yayi ya kaita toilet din ya sakata cikin ruwan dumi …… hannunshi ta rike da sauri zata mike ya mayar da ita yana fadin "Sorry……"
Tun tana jin Zafin har ta koma jin dadin ruwan……
Sannan ya fita ya barta ……kusan minti talatin ta gasa kanta sannan tayi wankan tsarki tare da alwala da brush ta fito ……
Ko kallon inda yake batayi ba……
Murmushi yayi mai sauti yana fadin "Morning Twee ya jiki ……"
"Oho……"ta fada a takaice tare da canza kaya tayi sallah…… anan ta kwanta bacci ya kwashe ……
Zuwa yayi ya mayar da ita saman gado sannan ya rufeta ya fita ya nema masu abun kalaci……
Ko da ta tashi da kuka ta tashi kamar yarinya haka dinga mashi shagwaba yinin ranar ,gashi duk inda zata sae dae ya goyata…… sannan taki yarda su koma upstair din tunda suka sauko ………
Ya koma kamar wani yaronta nan da can ma bai isa yaje ba sae lallabata yake kamar kwae ……
Ranar ya sake tabbatar da wacece Safeena gurin rigima ……
Da daddare ma cewa tayi barata kwana a daki ba a falo zata kwanta saman one siter ……
"To ……"ya ce mata yana murmushi
Sae da tayi bacci sannan ya mayar da ita daki suka kwanta
A haka suka cigaba da rayuwarsu gwanin ban sha'awa lallaba yake kamar kwae ya katange mata duk wani bakin ciki ya maye mata da Haske……
sae dae har lokacin bai fada mata aikinshi ba sae dae da safe idan zaije office yaje ya tafi wani guri
【】
Hajiya kam ana can ana renon cikin da ko yaushe take sa ran haihuwarshi ……
Aunty Zuby ma an koma ga Allah kullun ana rike da carbi haka Uncle Abbah tunda Aunty Fatee ta rasu ya tattara duk wani iskanci ya aje gefe……
Fadila ma ba laifi tana kokarin kwatantawa sae dae matsalan bata da damar ta rabi mutane sae su dinga kyamarta tare da hatararta wae wari take ……
Sae ma ta daina shiga cikin mutanen kwata kwata
OGA JB ma an samu lafiya sae dae har lokacin kamar wani dolo zaka ganshi saboda aluran da aka dinga mashi a india ……
Duk da an mayar dashi amma a banza saboda kwalwar ta rigaya ta tabu da yawa saboda alluran da aka mashi babu cutar a kwalwarshi……
*8 MONTH……*
Girgiza kai yayi kamar ya mata kuka yana fadin "Idan haka masu ciki suke da bala'i ko wallahi mu bani maza……"
Kwace wayarshi tayi daga hannunshi tana hararanshi tare da tura mashi abinci tana fadin "Allah sae ka cinyeshi tunda ban aikeka ka ciyo abinci gidan granny ba……"
Langwabe kai yayi tare da kwantar da murya yana fadin "Haba Twee dan Allah ki rufa man asiri in ba so kike cikina ya fashe ba……"
Karar wayarta ya katse mata maganar da tayi niyar yi ta dauka tana fadin "Besty jiya fa nan kika bar IV din zaki bawa su Hauwa'u da Aisha Sada Raddah ba……"
Tabe baki maryam din tayi tana fadin "Ke dallah share wadannan tsamayen me suka iya inba suzo su cinyewa mutane abinci ba……wallahi ko jiya naji ana gulmar zainab din gidansu wae ta kusa takaita Abbansu da shegen ci……"
Dariya Safeena tayi tana kallom Abdulmaleek daya aje spoon din ya tallabe kai yana kallonta ta ta watsa mashi harara ……Zatayi magana maryam tace"Kinga kin cikani da magana ban fada maki dalilin kiranki ba ……"
"To fada man Bestie……"
Kai tsaye tace "Kinyi Sabuwar Uwa ……"
"Ban gane ba……"
Dariya maryam tayi tana fadin "To hajiya ta haihu gobe ma suna babu wanda suka fada mawa nima makwabtansu na jiyo……"
Abdul maleek ta kalla taga har lokacin ita yake kallo ta sakar mashi murmushi tana fadin "Zan kiraki anjima bestie……"
Katse wayar tayi sannan ta tallabe kumatunta tana kashe mashi ido ……Shima idon ya kashe mata tare da kanne daya ……
Tasowa tayi ta dawo saman cinyarshi tare da sagalo hannayenta a kafadarshi ……
"Kace na rufa maka asiri ka koshi ko?ta fada cikin kunnenshi
"a'a bara na cinye kawae……"ya fada tare da janyo plate din don ya fahimci akwae abunda suke shiryawa da Maryam din ……
Janye plate din tayi tana fadin "Tunda ka koshi kuma ai shikenan tashi mu tafi na baka labari……"ta fada tare da mikewa ta kama hannunshi ……
Daki ta ja shi ta kwantar dashi saman gado sannan ta daura kanta saman cikinshi ta kwanta ……
"Kasan me ke faruwa?ta fada a shagwabe
"Uhumm"shima ya fada yana wasa da kalabarta data sauko……
"Dazu maryam ta kirani wae Hajiya ta haihu……"ta karashe maganar tana dariya
"Allah ya raya……"ya fada a hankali
"Kuma har gobe suna ……sae ka kaini goben ko?
"Uhumm"ya fada
Turo baki tayi tana fadin "Bangane Uhumm ba……"
"Allah ya baki hakuri me kike so ayi……"ya fada yana fitar da lumfashi a hankali
"Ka fada man da yaushe zamu je ……"
"Wae Gidan hajiyar……?
"Eh mana……"
"Daga nan ma kina iya mata addu'a Allah ya raya……"
Turo baki tayi kafin tayi magana ya mirginota tare da hade bakinsu guri daya ……
Bata ja lokaci ba ta cigaba da mayar mashi da martani cikin kankanin lokaci suka lula duniyar masoya……
*FEEDOHM💞*
[8:59PM, 11/19/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
© *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM💞_*
*Devoted to Ummi A'isha👌🏻*
*Bestowed to Aunty Sis💕*
*59*
Sanye take da doguwar riga blue ta shadda wadda taji aikin hannu na pink din zare,rigar ta karbeta sosae ta yarda sai kayi tunanin a jikinta aka dinka ……Cikinta ya fito tsam dashi sae ya kara mata wani kyau na musamman……Wayarta ta dauki ringing a hankali ta kalli gurin ,ganin number Maryam ya sata saurin dagawa tare da sallama
"Haba bestie ya tun dazu nake jira naga kin kirani mu tafi suna amma har yanzu shiru ko bara kiyiwa su Aunty Zuby kara bane ……"ta fada tana dariya
Dafe kai tayi tana dariya "Oh Bestie bara naje na sameshi naga yana falo kila ya barni don jiya cewa yayi wai gulma zai kaini……"
"Ya dai kamata gaskia don ku ya dace ace tun safe kuna gidan ……"ta fada tana dariyar mugunta
"Bana son iskanci maryam……"
"Allah ya baki hakuri Bestie amma naga matsayinku na jikoki ya akai ace tun safe kuka je……"
Dariya ta kwashe tare da yanke wayar ,sannan ta dauki dankwalinta tare da zura plat shoes dinta pink ta fita ,Zaune ta sameshi sanye da jallabiyya fara yana duba wani karamin littafi da taga zane abun shari'a a jiki ……
Tabe baki tayi ta isa gurin tana fadin "Mutun sae janye janye……,Ni gaskia na gaji……"ta karashe maganar hade da turo baki……
Dagowa yayi ya na sakar mata wani fitannanen kallo bai taba sanin ciki yana wa mata kyau ba sae a kan Safeenarshi… mika hannu ya janyota ya zaunar da ita bisa cinyarshi ,Hannu ya kai yana shafa gefen wuyanta a hankali sannan ya fara goga hancinshi a bisa wuyanta a hankali yana shakar sanyayyan kamshim dake fitowa daga dukka gabobin jikinta ……Hannun nashi ta rike idonta a lumshe "Yaune fa ake sunan hajiya ……"ta fada kamar an fizgo maganar daga bakinta ,ita kanta dariya ta saki bayan ta fadi maganar ……
Manyan idanuwanshi ya zuba mata ba tare da ya kyafta ba kafin ya lumshesu a hankali ……
"Kayi shiru ,Dan Allah ka kaini……" ta fadi maganar a shagwabe……
Bude idon yayi tare da sakin murmushi mai sauti "Yeah hakane,kinga ni na manta wallahi kara da kika tuna man amma idan kinje me zakiyo……? Ya karasa maganar tare da kissing wuyanta
Dan murmushi tayi wanda iyakarshi a lips dinta ,amma a zuciyarta ba haka bane……
"Zan gano baby……"ta fada tare da kare lafewa jikinshi
"To kiyi hakuri idan naki yazo ba sae ki gani ba Twee……?ya fada cikin sigar lallashi
"Dan Allah……"ta fada kamar zatayi kuka
"Nima dan Allah kiyi hakuri Twee ki zauna gida kin ji ko ……"ya fada cikin sigar lallashi
Harara ta balla mashi tare da sakin kukan shagwaba lokaci guda ta mike daga jikinshi tana fadin "Wallahi nima baran sake zuwa asibiti ba………"
Hannuwanshi ya hade guri guda ya zuba mata ido tun lokacin da ta fara maganarta har ta kai aya sannan ya saki ja'irin murmushi yana fadin "Allah ya baki hakuri Madam……"
Banza ta mashi ta koma ta zauna saman rug tana kallonshi tare da hade kai da guiwa tana kuka a hankali ……
Murmushi yayi ya mike ya shiga dakinta ya dauko mata hijab sannan ya dawo ya tsugunna gabanta tare da dago habbarta "Sorry tashi mu je……"ya fada cikin kunnenta……
Juyar da kai tayi tana turo baki tace "Na fasa……"
Dariya yayi yana fadin "Yauwa Twee Allah ya maki albarka kinga sae muyi zamammu gida na goyaki ko……"
Duka ta kai mashi tana goge hawayenta sannan ta mike ta fizgi hijab din ta saka taje bakin kofa ta tsaya tana hararanshi ……
"Kuma kin ce kin fasa Twee……"ya fada cike da zolaya
Murguda mashi baki tayi tana fadin "Zan je fa……"
Dariya yayi mai sauti tare da dagata sama yana juyawa ……bai ajeta ko ina ba sae cikin mota ……Sannan ya zagaya shima ya shiga ya zauna suka fita……
Maryam ta kira tana fadin "Na fito ki shirya yanzu mu biyo mu daukeki ……amma wallahi bara ki bini hannu biyu ba dole ki nemi Rigar da atampha ki baiwa Kakata……"
Kwashewa da dariya sukayi sannan ta kashe wayar tare da kallonshi ta marairaice tana kafta ido tana fadin "Dan Allah muje a sayar wa Mamata riga……"
Dariya ta bashi sossae ya tabbata ba hakanan zata gidan ba ……
Juyawa sukayi suka siyo kayan yarinya masu kyau set 5 sae atampha Exclusive guda daya tare da swiss shima daya……
Gidansu maryam sukaje ya daukota ……a mota yana jin sai iya shege suke amma yayi banza dasu ……sae dae idan yaji abun nasu yayi yawa ya dago ya sakewa Safeenar harara ……
Kuma hakan bara ya sa tayi shiru ba sae dae ta dan turo baki tana hararanshi ta kasa kasa sannan ta cigaba da maganarta……
Yana parking kofar gidan ta juyo tana washe baki tare da pecking kutamunshi tace "Sae dare zaka zo ka daukemu ko ……ko kuma kayi zamanka idan mun tashi ga maryam nan sae mu samu napep ya kaimu ko ……"
"Ki shiga ku fito ina jiranku……"Ya fada yana kallon wayarshi……
Zaro ido tayi tana kallonshi sannan tace "Amma ai……"
Kallon da ya mata ne ya sata yin shiru tare da saddar da kai kasa……
"Ki je ku gaisa ki fito nace……"ya fada a hankali tare da kallonta……
Idonta ya ciko da kwallah tace "Dan Allah ka barni sae anjima……"
Dauke kai yayi daga fuskarta ganin hawayen ya gangaro sannan ya bude baki a hankali yana fadin "Tana jiranki Safeena……"
Juyawa tayi ta fita ba tare da ta dauki kayan ba ta fita ……
Ta iske maryam har ta shige gidan ta barta ……
Wani kululu ya tsaya mata wuya duk shirin da sukayi da maryam ya rushe kenan hawaye taji sun kwace mata ta sa hannu ta share tare da juyowa ta kalleshi tayi gaba ……
Kwala mata kira yayi amma ko ta juyo,dauko kayan yayi ya biyota dasu ……
Kafin ta shiga gidan ya tareta tare da janyota jikinshi ……Kuka ta saki da karfi tana kokarin janye jikinta……Lallashinta ya fara amma ta ki yin shirun ……
Zuciyarshi ta karya ya dubeta a sanyaye yace
"Sae daren zaki tafi Safeena……?
Gyada mashi kai tayi tana kukan……
"To kiyi hakuri kinji ko……Zuwa daren zan dawo na daukeki amma dan Allah ki kula Safeena bana son wani abu ya taba lafiyarki……"
Wani yaro ya kira ya bashi kayan yace ya shiga dasu ……
"Take care Twee……"ya fada a hankali tare da pecking goshinta sannan ya juya ……
Hakanan ta ji ya bata tausayi ……tayi saurin kamo hannunshi tare da zagayeshi da hannunta ……
"Sorry yanzu zan fito mu tafi kaji ko……"ta fada a hankali
Dan murmushi yayi yana kallon fadila da ta fito ta tsaya tana kallonsu ……
Kusa da kunnenta ya fada mata "Kiyi zamanki kinji ko……babu komae amma ki kula……"ya karashe maganar tare da janyewa daga rikon da ta mashi ……
Kallonshi tayi tare da kallon inda taga ya kalla sannan ta juyo tana dan murmushi ……
"Mu shiga sae mu fito tare ka ji ……wallahi na fasa zaman tunda bakka so……"ta fada cike da shagwaba tare da zare takalmata ta dage kafar da sauri ta daura saman tashi ……
Da sauri ya kalli kafar yana fadin "Menene?me ya samu kafar……?
Jujjuyar da kai tayi tana fadin "Kamar an tsireni naji fa……"
Dukawa yayi ya daura kafar saman cinyarshi yana dubawa sannan ya dago cike da tausayawa yace "Sorry twee nayi maki addu'a amma banga komae ba……"
*FEEDOHM💞*
[12:32AM, 11/20/2017] Feedohm💞: : 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
© *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM💞_*
*Devoted to Ummi A'isha👌🏻*
*Bestowed to Aunty Sis💕*
*END……*
GODIYA TA MUSAMMAN
*Haske writer's Asso💡*
*Feedohm novella*
*Taskar billy galadanci*
*Zauren biebie isa*
*Duniyar makaranta*
*Home of novels*
*Pherty novels*
*Hajjace novel group*
*Ladies worlds*
*Exclusive angels*
*Novels lgdes*
*Asy khaleel novels*
*Khadija candy novels*
🤝🤝🤝🤝
*The page is Whisticall to*
*Aunty Ummi A'isha😘 Aunty Sis😘My Swt Mum Mizz Zozo😘 Bestie Firdaws😘 Aisha Sada 😘Hauwa'u Sada😘 Salima Sada😘 Jeeddah Aliyu😘Asiya Usman😘 Meela Adeel😘 Meenarh parrot😘 Hajja ce😘 Pherty😘 Nucy luv😘 Faxy fashion😘 Safiya huguma😘 Billy Ladan😘Queen mermue😘Muneera😘Sawwama😘Hafsat mai sherrif😘Slendid😘 Maman khady😘Aunty maijiddah😘Billy galadanci😘 Sofie Galadanci💧Wadanda ban ambata ba matsayinku na dabanne😘*
Murmushi ta masa tare da janye kafar tata daga saman jikinshi "Yanzu zan fito……"ta fada a hankali
"Allah ya maki albarka to……"shima ya fada yana murmushi
Da Ameen ta amsa sannan ta juya gurin Fadeela da har lokacin ta kasa wucewa ……
Kallo daya ta mata ta tausaya mata barema da taje kusa da ita taji kalar warin da take fitarwa ……
"Ki Sameni gida ki karbi magani ……"ta fada Hankali
Bayanta fadilan ta juya taga ko da wata take amma taga ba kowa…… ,sam batayi tunanin Safeenar zata kalleta da idon rahama ba bare har ta mata magana……
A Sanyaye tace "Nagode Safeena dan Allah kuyi hakuri abun……"
Katseta tayi tana fadin "Ya rigaya ya wuce……"Sannan tayi gaba abunta ……
A Tsakiyar gadon hajiya ta hango Maryam dauke da jaririyar tana ta dariya wadda su biyu suka san fassaranta ……
Kallon Aunty Zuby tayi tana fadin "Ya jikin?
Aunty Zubyn ta sunkuyar da kai cike da nadama ta kasa amsa gaisuwar Safeena ……
Tabe baki tayi tana fadin "Allah ya kawo sauki……"sannan ta juya tana fadin "Meye sunan babyn ?
" *Fateema* ……"Maryam ta fada tana dariya ……
Itama dariyar Safeena tayi cike da shakiyanci sannan tace"Duba man da wa take kama……"
"Wannan Aunty Zubaida ce ……"cewar Maryam tare da daure fuska ……
Haka suka karaci shakiyancinsu babu wanda ya kulasu a ciki ko wane kunya da tsoro ya hanashi tankawa Hajiya ma sadda kai tayi tana kuka sannan suka mike suka fita suka iske Abdulmaleek din……
【】
Tun da daddare take jin ciwon amma bata fadawa kowa ba har sun fara bacci ta mike zumbur tana kuka ……
Maida ita yayi ya danne ya dauka rigima ce kawae ……Sae da yaga abun nata nayine sannan ya mike yana lallashinta ……
Ganin kamar zata mutune ya sashi kiran Dr bala wanda ke duba ta ya tambayeshi ko yana asibitinshi ……
Dr Balan yace wallahi yana nan General hospital wani aiki yake amma su zo nan sae a dubata ……
Ba dan yaso ba ya kaita General din saboda ko kadan bai taba zuwa asibitin ba kuma yana ji, yarda mutane ke kukan ana wulakanta mutane acan don tana ta government ……
Suna zuwa Dr Balan yace a shigar da ita labour Room sannan yaja Abdulmaleek din saboda maza basa shiga cikin ……
A rude Abdulmaleek din ke tambayarshi ko za'a kula da ita sosaae ……
Ce mashi yayi wallahi ba matsala za'a kula da ita bara ya kira Sister Aisha zata fi kula da ita sosaae tunda tana da sauki kai ……
Number Sister Aisha a rufe ……Sae yace mashi kar ya damu ……
Labour Room……
Tunda aka kai Safeena aka jibe babu wanda ya tabata sae ma nurses din komawa da sukayi suka zauna suna firansu ……
Macen dake kusa da gadon Safeenar ce ta zabura ta fado tana ihun neman taimako……Cikin Sisters din wata ta taso a harzuke tana fadim "Ke dallah jakar banxa zaki dingawa mutane ihu kamar diyar arna baki kije islamiyya ba kike son gwada mana ……!
Matar cikin magagin nakuda tace "Dan Allah ki taimaka man Sister……"
Tsawa ta daka mata "In taimaka makin ubanki kin san baki iya jure azabar haihuwar wane shege ya kaiki ga mijin…Ka gane man yan iskan mata marasa da'a kauyawa dasu zasu ishemu da ihu kamar mu muka masu cikin,Wallahi na fara gajiya da iskancin masu haihuwar na Sister meelah…"
Sister meela ta tabe bakinta tana fadin "Keni wallahi shiyasa bana taba ko wace shegiya idan ta haihu don kanta idan ma ta rasu ita ta sani……Haka kawae akwaso maka kazanta kazo kana saka hannunka?ko wane shege da ya tashi haihuwa sae ya kwaso jiki yazo nan don sunga ba'a kashe kudi……"
Wani ihu Safeena tayi jin yaron na fitowa tare da silalowa daga saman gadon ta fado kasa …
Ai kuwa nurse din ta iso a fusace tare da kifa mata, mari tana fadin "Ji beki banza zaki kashe yaronki a banza a wuhi ……"
Yaron ne ya fado kasa tare da mahaifa amma sae da nurse dinnan tayi kusan minti talatin tana zaginta sannan ta yanke mata cibin aka gyara yaron ……
Wae kuma saboda masifar rainin wayau sae zuzuta kyawun yaron suke……
Safeena na jinsu har ta samu ta dawo dae dae ……sannan ta kalli ta kusa da ita da har yanzu take yashe a kasan tiles tana birgima babu wanda ya kulata cikin nurse din……
Abdulmaleek aka mikawa yaron bayan an gyara shi……
Huduba ya mashi tare da rungumeshi kamar wani zai kwace mashi yana tambayar Safeena ……
Har ta kawo bakin kofa ta wa Nurse din magana ……matsowa Sister tayi tana fadin "Yaronki mai kyau gaskia da alama ke ya biyo……"
Dariyar takaici safeenar tayi tana fadin "Ko……?
Kafin nurse din ta bata amsa ta dauketa da lafiyayyen mari tana fadin "Marin da kika man ne ina cikin labour Saboda tsabar jahilci da rashi tausayi ……"
Baki nurse din ta bude zata yi magana ……Safeena ta sake sauke mata wani marin tana fadin "Wannan kuma na zagin da kika man ne ……Rashin iya aiki kuma ki jira karshen ki banza wawiya……"
Ta wuce ta barta sake da baki ……
Da hannu daya ya dinga driving yana rike da yaron da hannun daya sannan duk bayan yan seconds zai juya ya kalli Safeena da wani irin fitinannen kallo……
Sae dae kawae ta mashi murmushi tare da kawar da kai……
Suna Isa Gida ya fara kiran mutane yana fada masu ……
Cikin yan mintina gida ya cika da yan uwa da abokan arziki……
Shi kanshi sae da yayi nadamar kiran mutanen domin gidan gagaran shi shiga yayi daga baya Safeena ma gaisuwa kadae ke hadasu……
, Ita kanta ranar Suna sae da tayi mamakin kudin da aka kashe tare da tambayar kanta ina Abdulmaleek ya samesu……
Cikin wani hadadden Less Coffee ta hade tayi masifar kyau ta nufi dakinshi jin shigowarshi gidan don tun jiya da safe rabon da ganshi……kuma tana so ta gwado mashi kudin Da Abba ya aiko ayi hidimar suna……
Tun kafin ta shigo yaji kamshin turarenta dan haka ya tsaya bakin kofa ……
Dasallama ta shiga yayi saurin janyota tare da rufe kofar yana kissing dinta ……janye jikinta tayi tana hararanshi tare da fadin "Meye haka Abdulmaleek ……?
"Love ……"ya fada tare da kashe mata ido
Zama tayi bakin gefen gadon ya bita ya tsugunna tare da dafa guiwata yana leken yaron "Kin bani abunda banyi tunani ba Safeena kin mayar da Abba Safeena…kin kawo man wani sauyi na musamman a rayuwa Ina matukar Kaunarki ,Bana jin zanyi amfani indae bana tare da ke safeena ……kece duk Silar wani farincika tunda lokacin da fara ganinki na tabbatar da *ZAN RAYU DAKE* cikin salama…,bana da bakin gode maki sae dae Na maki addu'a ……Ina karama Allah godiya da ya bani ke Safeena samun mace kamarki ba abune mai sauki ba na maki alkawarin *ZAN RAYU DAKE* Cikin ko wane hali don Allah duk runtsi karki barni Safeena……You brighten my day Safeena with the sound of your voice, you bring so much laughter and love, you are everything to me and I was so blessed when Allah sent you here for me I Really Love you……."
Lumshe ido tayi tana fadin " Nima *ZAN RAYU DAKAI……* Komai wuya Abdulmaleek kaine ka haska man rayuwata ka soni lokacin da kowa ke guduna ka Rayu dani duk da cutar da nake dauke dani ……bana fatan na butulce maka Abdulmaleek kaine Zuciyar Safeena ko bayan raina zan tafi da zuciya……"
Shiru yayi suna kallon juna sannan yace "Sunan dan mu *ABDULMALEEK……*
Waro ido tayi tana kallonshi dauke da murmushi sannan ta lumshe su a hakali……
"Kin yi farin ciki……"ya fada tare da kashe mata ido…
Gyada kai tayi a hankali tana lumshe idonta……
Mikewa yayi a gabanta tare da daukar yaron ya maidashi saman bed……
Dagota yayi tsaye ya rungumeta sossae jikinshi cikin kunnenta yace "Proove……"
Kallon fuskarshi tayi sannan ta saka tongue dinta a bakinshi tana juyawa a hankali cikin salo da kwarewa……
A hankali ta dago idanun su duk sun canza tana kallonshi
Murmushi tayi tare da zagaye hannunta jikinshi tana fadin "Abdulmaleek ka kashe kudi da yawa ina ka samoshi……"
"Allah ya bani……"
"Ba haka ba Dan Allah kar kayi abunda yafi kar……"
Katse tayayi "Bai fi karfina ba safeena karki damu ……"
ID card dinshi ya fito ya aje mata tare da mata bayani sossae a kanshi ……
Dukan wasa ta kai mashi ya kauce yana dariya tare da janyo kunnenta yana rada mata kalamai masu dadin gaske ……
*Alhamdulillah*
*Alhamdulillah*
*Alhamdulillah*
Nagode wa Allah da ya bani ikon kamalla wannan littafin kura kuren dake ciki Allah ya yafe mana ……
Masoya nagode da dumbin soyayyarku Allah ya albarkaci Rayuwarku gaba daya ……💞💞
Sai kun jini a sabon littafina *ABUN DA KE BOYE……*
Sadaukarwa ga mai rabo😹😹
08066598868
*FEEDOHM💞*