"Hankali tashe aka kwashi Alh Kasim akai dashi asibiti, kuka Hajiya Farha keyi shar shar da idanun ta ga uban zogin da wuyar ta ke mata yanda Alh Kasim ya shak'e ta, for second Mamy bata bar side d'inta ba...
"Suna isa Asibiti Dr ya tabbatar masu Alh Kasim ya sami Heart attack he's in critical condition komai ka iya faruwa dashi..
"Wani sabon tashin hankali ya ziyar ce su, uwa uba hospital bills da za'a caje su domin kuwa basu da komai komai nasu ya k'are, harta gwala gwalan Mummy ya d'iba ya biya bashi dasu. Sosai hankulan su ya tashi, abu kaman wasa The Dasuki's well known family masu kud'i masu fad'i aji in a flash sun rasa komai na rayuwa, wanda da a da ne cikin awanni za'a shirya fita k'asar waje... .. Tabbas Allah Ya wuce gaban wasa.
"Babu hali su shiga wajen sa, yana nan a intensive care unit, ta glass suke hango sa yanda yake kwance saman gado cikin tsananin ciwo, na'uran bature ne ta ko ta ina a jikin sa.....
**********
"Idan kaga Salim bazaka shaida shi ba, gaba d'aya ya d'aid'aice ya fita hayyacin sa, he couldn't believe what he's going through, yau shine haka, no place to stay, no luxury, Kai abincin da zai saka a bakin sa ya zame masa masifa, kayan sakawan sa an sace su balle ya sayar ko zai d'an sami na cin abinci koda kuwa ruwan kunu ne...
"Rakub'e yake zaune k'asar gadan yana hangen mutane yanda suke wucewa suna shawagin su, ya kai duban sa ga paratan hannun sa yanda duk suka guggutsure sukayi datti sabida rashin wanka, ina ma zai sami wajen wanka yana neman na abinci, ko jiya ma satan buredi yayi a guje ya samu ya d'an ci... "Hawaye masu d'umin gaske suka shiga gangaro masa sanda ya tuno rayuwar su a baya, when everything was perfect, ... "Ina Kai bazai iya wann rayuwar ba, he needs to call his parents at least ko kud'i ne su turo masa yasan yanda zai yi,...
"Da wann tunani ya mik'e ya nufi bakin beach yanda mutane ke shawagin su, 'Yammata da samari masu ji da kansu suna ganin sa zaka ga sun soma b'oye wayoyin su don kuwa shakka babu irin su ne masu satan waya..
"Girgiza kai kurum Salim yake idan ya tuna yau shine a wann yanayi na rayuwa, wanda a da zai iya kyutan iPhones sama da hamsin a rana yau shine ake b'oye waya sabida an gansa, ya tuna shine Salim Dasuki masu had'a party da 'yammata a cikin jirgin sama arararin samaniya sabida gata yau shine shiga jirgi ta gagare sa kai mota ma ta gagare sa balle aje ga maganar jirgi.... Ya kuma sa bayan hannun sa ya share hawayen sa.....
"Yana ganin wasu 'yammata sun mik'e zasu shiga ruwa sun sha swimming trunks d'insu ya nufi yanda suka baro yana bin sauran snacks d'in da suka bari yana ci hannu baka hannu k'warya..
"D'aya daga cikin 'yan matan ne ta dawo d'aukan cream d'inta..... Nan ta hangi mutum sai masu bincike yake yana cinye sauran abincin su.... Zata yi ihu kenan ya d'ago idanun sa suna kallon juna...
"Da mugun mamaki take binsa da kallo kafin tace " Salim Dasuki, is that really you..??
"Salim Ya mik'e yana k'ok'arin k'ak'aro murmushi kafin yace " Miemie Turaki kina nan...
"K'arasowa Miemie tayi tana kallon sa cike da mamaki kafin tace " Kai what's wrong ya na ganka haka, ina su Labib Tariq and that my crush the most handsome among you... Jalal,..?? Ta k'arashe tana murmushi kafin ta rik'o hannun Salim suka zauna tace " Kwanaki naji batun auren ka, lokacin na koma Scotland shiya sa baku ganni ba, Jiya jiya muka zo k'asar nan kuma... Fasali ta d'an ja ganin Salim yayi sakare yana kallon ta kafin ta soma fad'in cike da mamaki ...."But Salim wai kaine ma kuwa, kaman ba kai ba.
"Salim ya murmusa kafin yace " I've to go Miemie, someone's waiting for me... Daga haka ya mik'e yana tafiya, saurin rik'o hannun sa Miemie tayi kafin tace " From your looks abubuwa da dama suna faruwa da kai and you don't want to share it... Anyway take this ta mik'o masa kud'i masu d'an yawa wanda zai kai dubu ashirin....
"Kallan kud'in yayi kafin ya d'ago yana duban ta, murmushi ta masa kafin tace " Ka karb'a Salim koma meye ke damun ka nasan it will help...
"Salim yasa hannu ya karb'a don ko bashida zab'in da ya wuce ya karb'an... Godiya ya mata kafin yasa kai ya fice daga wajen da saurin gaske...
"Nan Miemie ta daskare a wajen tana kallon sa har ya wuce, a haka friends d'inta suka k'araso suka same ta don sunji shirun nata yayi yawa...
"Babe meye ne kike tsaye a nan staring at nothing...?? K'awarta guda ta tambaya..
"Girgiza kai Miemie tayi kafin ta juyo ta dubi k'awatar tace " Amal I just saw something that terrifies me, Amal I'm afraid of this world, kinsan wa na gani yanzu..
"Amal ta girgiza kai tana yatsina fuska, Miemie tace " It was Salim, Salim Dasuki,, he was right here.... I... I don't know, bansan meke faruwa dashi ba but koma meye Salim yana cikin wani hali na canjin rayuwa, mahaifin sa mai kud'in gaske ne, shi ne guy d'in da na fad'a maki da yana had'a mana Party a jirgin ruwa ko a jirgin sama, ..... Na ganshi cikin wani irin yanayi, I asked him but ya ma kasa tsayuwa yayi min magana,..... Amal koma meye ne ke damun sa na tabbata baya cikin gata da jin dad'in da yake ji a da... Amal wllhi wllhi na tuba daga irin wann rayuwar wllhi na daina ta daga yau, duk kud'i irin na mahaifi na bai kai mahaifin Salim kud'i ba although mun bar k'asar gaba d'aya bansan me ya sami family d'insu ba, amma tabbas Allah zai iya juya Al'amran sa likacin da ya so, Na tuba Amal gida zan koma daga nan, naga ishara akan Salim.. kuma kema idan zaki tuba fine, idan bazaki tuba ba sai mu raba hanya....
"Cikin sauri Miemie ta kwashi suturun ta ta saka ta nufi mota, fuskar ta cike da nadama da tsoron mahaliccin ta...
"Wani wajen waya Salim Ya samu ya biya kud'i kafin ya shiga neman layin Dad dinsa shiru baya shiga, haka na Mummy ma karshe ya yanke shawarin kiran Barr Munir,
"Barr na waje ta d'an k'ofar baya domin kuwa basu isa fita ta gate ba sabida yanda journalist sukayi chaa suna d'aukan labarai... Nan yaga kira da bak'uwar lamba... Cikin sauri ya d'aga yana mai ciccije fuska...
"Kuka Salim Ya fashe masa dashi yana fad'in" Uncle I couldn't reach any of them, Uncle meyasa zasuyi neglecting d'ina, I'm suffering Uncle....
_Daga can NCC kuwa tuni anyi connecting kiran da Barr Munir yake tare da jami'an tsaro, gaba d'aya suna sauraren su.._
"Barr ya fuzar da iska kafin yaci gaba da fad'in" Things are not easy here either, you better stay where you are, if you show up here, police will have you arrested, so gwarama kayi zaman ka a can...
"Cikin muryar kuka Salim yaci gaba da fad'in" But I can't uncle, I just can't, banida kud'i banida wajen kwana, ko kasan cewa k'asan bridge shine wajen kwana na, do I have to hide my whole life...... " Okay naji bazan dawo ba, but where is My Dad, I wanna talk to him, ka had'ani dashi pls...
"Barr ya fuzar da iska, hawayen da baisan dalilin zuban su ba suka shiga fito masa kafin ya soma fad'in" Salim I'll be honest with you, we are ruined, completely, we lost the company, we lost the mansion, in short mun rasa komai, your Mum and your Aunt, mahaifiyar Labib had to move in with Jane, Salim Hajiya Farha da mahaifiyar Labib dole suka koma gidan Jane, cook d'inku mai dafa maku abinci coz they have no where to stay..... And your Dad..... He's....
"Salim da hawayen sa suka kasa daina zuba cike da shock yake fad'in" My Dad what happened to him, how's he..??
"Munir ya cija leb'en sa kafin yace " He's in a hospital right now..... Ya sami heart attack, I'm afraid he's dying.....
"Kuka sosai Salim Ya fashe dashi yana girgiza kai yake fad'in" No, no, this can't be happening, ina mummy na, I'm quite sure she must be affected... Ina take..... Daidai lokacin da Mummy da mamy suka iso wajen...
"Journalists kuwa tuni suke aikin d'aukan su ta cikin flowers, Domin kuwa shakka babu sun san da Salim suke waya, gashi sunce basu san yanda yaje ba, hakan na nufin sun san yanda Salim Ya gudu ya b'oye kenan...
"Munir ya mik'a mata wayar yana fad'in" Farha... Here..
"Da sauri ta mik'o hannu tana fad'in" Is that Salim, oh my poor boy... Tana soma magana cikin wayar ya kuma fashe mata da kuka, kuka itama take, tana rok'on sa kar ya dawo koma a ina yake, don kuwa yana dawowa police zasu kama sa, already an kama Labib...
"Salim kuka yake yana fad'in" But mummy ina so naga Daddy na, mummy pls ki barni na dawo...
"D'aga kan da Barr zaiyi yaga journalists sai d'aukan su suke, ....Shittt, Dammit... Ya furta da k'arfin gaske kafin ya fincike wayan ya kashe, Mummy tana kuka haka Barr ya fizge wayan yace dasu su shige cikin asibiti idanun journalists na kansu ne gaba d'aya...
***************
"Ai kuwa bayan wasu awanni Police suka zo sukayi interrogating nasu sabida wayan da sukayi da Salim, fir suka ce basu san yanda Salim ya b'oye ba...
"Rayuwa fah ta kuma shiga cikin tsananin matsi da tak'ura, ta kai point d'in da basu da kud'in da za'ayi jinyar Alh Kasim, dole Barr ya soma bin k'afar tsofaffin abokan kasuwan cin Alh Kasim yana rok'o kud'ad'e da sunan jinyar Alh Kasim, idan sun basa sai ya raba kud'in kashi biyu ya d'au kashi guda ya bayar da kashi guda...
"A haka har Alh Kasim ya soma samun sauk'i saidai babu baki babu k'afafu, maganar nasa ba'a iya fahimta, ga shanyewar b'arin jiki, harta bakin sa ta karkace, ba don Drs sun so ba suka sallami Alh Kasim sai don rashin kud'in ci gaba da jinya a asibitin....
"Gaba d'aya gidan Jane suka tattara suka koma, Mummy da Mammy sai godiya suke ma Jane, Jane kuwa tace " Ai babu komai tunda harta gudan nata a dalilin masu aikatau ta samu,...
"Haka zasu zauna suyi jigum suna tuna rayuwa, Alh Kasim kuwa komai fitsari bayangida saman keken guragun sa yake yin s idan ba'ayi saurin ankara an kaisa ba sabida babu baki balle yace zaiyi, ba'a gane me yake fad'i.... Tau Jane ma fah ta soma k'osawa dasu, don duk ranar da Alh Kasim yayi bayan gari a jikin sa toh fah haka gidan gaba d'aya zai wuni yana wari... Ita kanta Mummy ta soma gajjiyawa...
"Shi kuwa Barr bai fasa bin k'afafun abokan kasuwancin Alh Kasim ba yana amso kud'ad'd'e da sunan Alh Kasim kafin yazo ya cika ma rigar sa iska kafin ranar shiga kotu tazo.....
******************
"Labib ya kalli d'an sandan cike da mamki kafin yace " Are you sure Alh Kasim ya sami heart attack, police officer ya shek'e da dariya kafin yace " Ba abin mamaki bane tunda Allah ne ya kawo k'arshen ku, ku saduda ku amsa laifin ku don kuwa baku da wajen gudu, Allah Ya karya ku gaba d'aya....
"Labib girgiza kai kurum yake hawaye na fita masa yake fad'in" No, no I can't go to jell, I just can't.....Get me out of here,..... Ya k'arashe cikin tsananin d'aga murya...
"Police kuwa yayi dariya kafin yace " Kai ka sani wann ba matsala ta bace, dad'in mutum ya shuka alkhairi kenan....
"Durk'ushewa yayi saman gwiwoyin sa yana kuka da duka zuciyar sa.....
***********
*Fadah*
*A week to the Trial*
"Hannunta ya rik'e cikin nasa kafin yace " Baby we would do everything possible mu fitar da Hadiza daga jell koda zamu kashe mak'udan kud'i ne, ki daina damuwa kinji, although bamu san dalilin da yasa Checks d'in Kasim Dasuki ya shiga hannun ta ba amma nasan yanzu zata fad'i koma meye, su kansu Dasukis yanzu ta kansu suke bata Hadiza ba na tabbata. Nima ina tausayin Hamma da Kamal, sosai it breaks my heart seeing them suffering while mu muna cikin jin dad'i, koma meye tayi she's still part of us, she's our family, nasan kin yafe mata tun tuni..... Ya k'arashe yana mai murmushi yana murza 'yan yatsun hannun ta...
"Mumrmushin itama tayi kafin ta gyad'a Masa kai tana share hawayen da suka Zubo mata... Daidai wayan Jalal tayi k'ara Shattima ne me kira....
"Jalal na d'agawa Shattima yace " Prince ka fito babban gwani right now, we've got the Doctor, ka fito yanzu....
"Ai bai gama ji ba ya mik'e ya mik'e yana fad'in" Really, gani nan zuwa... Cikin zuciyar sa kuwa tafarfasa kawai yake don yasan suna yin ido hud'u da likitan nan sai yayi smashing face d'in sa... Baiko ce ma Zubaidah komai ba ya fice cikin sauri yana zura takalmi,..
"Zubaidah ta bisa da kallo tana addu'an Allah yasa lafia...
*****
"Labib ya kuma kallon officer kafin yace " Officer pls ka taimaka min da abin rubutu takarda da pen..
"Officer ya kalle sa tsegege yayi dariya kafin yace " Wata k'aryar zaka rubuta, kar ka damu zan bake... Ya mik'e yana murmushi kafin ya kawo ma Labib doguwar takarda da pen..
"Labib yayi godiya kafin ya zauna ya soma rubutu kamar haka... "
_January 15th, I Confessed....._
"Hawaye suka ci gaba da kwaranya daga idanun sa....
*Sameena Aleeyou Mrs*
🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
*95*
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_*Dedicated To All Victims Of Rape...*_
_Wannan littafi kacaukam d'insa sadaukarwa ce ga dukk wata d'iya mace wacce tsautsayi da k'addara na fyad'e ya auka mata... Ina fatan wannan littafi nawa ya sanya murmushi a saman fuskar ki 'yar uwa 😊_
"Daidai k'ofar da zai sada ka da Babban gwani Jalal yaci karo dasu, burki yayi yana watsa wa Dr mugun kallo, yayinda fadawa tuni sun zube suna kwasan gaisuwa suna kod'a Jalal suna fad'in" D'an sarki jikan Sarki, Allah Ya baka gidan ku, d'an na gada, kafi d'an na koya, mai ado da tagulla da azirfa.... Allah Ya ja zamanin Yarima.... Wata naushin da Jalal yakai ma likitan nan yasa fadawan nan yin tsit suka shiga tsine ma Dr suna fad'in" Allah wadan ka D'an talakawa ka b'ata ran Yarima, ..Allah Ya wadan ka... Hattara d'an talkawa.... Allah Ya huci ran Yarima...
"Jalal huci kawai yake yana rik'e da kwalan rigar likitan nan yake fad'n" You shameless imbecile ka gama b'uyan naka, you such a coward, you should be ashamed of your self....
"Shattima ya shiga janye sa yana fad'in" Calm down Jalal, pls compose your self...
"Huci kawai Jalal yake yana watsa ma likitan nan mugun kallo ga jijiyoyin jikinsa dake tsahi idon sa da fatar sa sun koma jazir....
"Fadawa kuwa sai fad'i suke " Allah Ya taimake ka wann aikin mu ne, a barmu mu ladabta shi... Tsinannen Allah, ka sab'i ran Yarima.....
"A zuciye Shattima ya daka masu uban tsawa yace su watse a wajen baki d'aya.....
"Rik'o hannun Jalal yayi suka soma tafiya yayinda Detective Mudi ya janye hannun Dr suka nufi cikin fadah... Jalal sai faman huci yake....
***************
"Kasa ci gaba yayi da rubutun sai hawaye dake neman wanke masa fuska, ya d'aga kai sama yana kallon killataccen d'akin da aka ajiye sa, tabbas no way to escape, dole ne ma ya zauna a jail for many years, they lost everything, basu da komai balle yayi tunanin kud'in su can save them, Alh Kasim ta kansa yake bashida lafia babu kud'i babu company, snn ba'a kama Salim ba balle yayi tunanin koda ace yana da kud'in zai iya yin wani abu, yasan cewa uncle dinsa ya tsane sa , shima kuma bai son sa ko k'ank'ani.....
"Ya dafe kansa yana mai ci gaba da tunani hawaye na ci gaba da kwararo masa... He started it all, he was the one who first came up with the idea... But, ta yaya zai fara confessing, mai zai ce, daga ina zai fara...
"Take zuciyar sa ta rad'a masa start from that very night 🌘.... Sunkuyawa yayi yana mai ci gaba da rubutu lokaci guda kaman a mafarki kaman a tunani yake jiyo murya tamkar na mahaifin sa yana fad'in"
"If you are going to confess, write everything down, ka fad'a komai kar ka b'oye ko guda, kar ka mance musababbabin abinda kayi niya a wancan lokacin shine ka b'ata auren Salim, snn ka bak'anta Alh Kasim a idanun Alh Tahir, snn kar ka mance ka saka ma Jalal k'waya a abun shansa don hankalin sa ya gushe ka cimma burin ka, mai yuwa su sauran sun aikata laifin ne domin jin dad'in su, amma kai ba haka bane, ka aikata ne sabida ka destroying uncle d'inka da d'ansa, so my dear boy kar ka b'oye komai ka fad'i komai ma Alk'ali only then you'll have peace.......
"Labib ya toshe kunnuwan sa da k'arfin gaske shi kad'ai ya tak'ure waje guda cikin garu yake fad'in" No... No Dad, I hate my uncle so much...And Salim, that coward stole Kausar from me, ni na fara sanin Kausar ni yafi cancanta na aureta not him..... Dad I hate them, na tsane su....... Ya k'arashe yana mai ci gaba da toshe kunnuwan sa...
"Saida yayi kuka mai isan sa kafin ya d'ago yana waige waige yake fad'in" Dad.. Dad where are you, pls take me out of this place, I don't wanna end up behind bars... Ya k'arashe cikin tsananin kuka sai faman buge buge yake tamkar tababb'e...
**************
"Tsaye yake bayan wani restaurant yana faman sak'e sak'e, ya duba kud'ad'en hannun sa wanda suka rage, tabbas gwara yayi amfani dasu ya koma gida ko a sace ne yaga mahaifin sa kafin ya zama too late.. Saidai fah idan ya sai abinci kud'in bazai ishe sa ya isa Abuja ba .....
"D'aga kansa yayi ya hangi ma'aikatan restaurant d'in sai firfito da sauran abinci suke suna zubawa a dustbin alamun wanke wanke zasuyi...
"Salim yaga karnuka da kenwa suna shawagi a wajen.. Ya had'iyi miyau ga yunwa dake azalzalan sa..
"Cikin sand'a ya k'arasa ya kore kenwar nan ya suri parks d'in abincin ya koma gefe ya bud'e ya hau ci hannun sa har na rawa sabida yunwa, yana ci yana hawaye yana mai tuno rayuwar sa a baya, abincin sai kalan wanda ya zab'a gashi yau tafi k'arfin sa....
********
"Alh Kasim ya d'an sami sauk'i yana d'an iya magana saidai da k'yar ake fahimta snn yana d'an iya motsa hannun sa..
"Nan ya buk'aci Jane ta taimaka masa da laptop,. Email d'in sa ya shiga yana dubawa, shaye da mamaki yake bin laptop d'in da kallo tsugugun kud'ad'e Barr Munir yake karb'a da sunan sa.... Cike da tashin hankali ya soma k'ok'arin turo wheelchair d'insa yana gungurawa yake doka kira wa Mummy cikin muryar sa da ba'a fahimta sosai...
"Mummy ta fito daga cikin a guje tana tambayar sa lafia... "Cikin gwalamniyar muryar sa wacce ta yara ta fita fitowa da kyau yake fad'in" Mumnir Munir ya amshe kud'ad'en..... Farha take me him pls.... Ki kaini wajen sa..
"Mummy dai baki sake take kallon sa kafin ta d'an jinjina kai cike da tausayawa ta soma fad'in" Daddy don girman Allah ka cire maganar kud'i a ranka, kadai ji abinda likita yace, kuma ma how could you say such a thing, ta yaya d'an uwa na zai cuce ka bayan irin taimakon da yake maka da shari'an yaran ka, kaima kasan Munir bazai tab'a maka haka ba koda wani zai maka ....
"Girgiza kai kurum Alh Kasim yake yana fad'in" Da sunana yake amsan kud'ad'en gashi sak'onni sai shigo min suke, yanzu haka ma ga alert na gani daga Diamond Bank, nasan zai bi yaje ya amshe...... Ta.. Take me to the bank..... Ya k'arashe yana mai ci gaba da gungurawa...
"Cikin sauri Mummy ta k'arasa ta rik'e keken nasa tana mai k'walla ma Jane kira don tai masu rakiya....
"Taxi suka fita suna nema a bakin titi, saida suka wuya kafin suka sami taxi d'in da ya d'auke su don kud'in su ba wai yakai bane, ita kanta Jane duk savings d'inta sun k'are a ciyar dasu Alh Kasim da hidimar su...
"Suna isa k'ofar banki suka hangi Barr Munir yana sai gaisawa yake da mutane yana washe baki yana rungume da envelope na kud'i....
"Mummy sai salati take tana tafe hannaye, bata tab'a zaton Munir zai masu haka ba.... Cikin sauri Hajiya Farha ta fincike marfin mota a fusace ta nufe sa sanda yake tsaye bakin titi yana neman tasi sai faman mammatse idanu yake sabida zafin rana yana shafa tand'alellen k'eyar sa....
"Kaman daga sama ya jiyo muryar k'anwar sa Farha cikin karaji take fad'in" Amma Yaya Munir kaji kunya wllhi, Allah wadai butulu irin ka...
"Munir ya dube ta cike da mamaki kafin yace " Farha me kike yi a nan, me ya kawo ki nan snn wasu irin maganganu kike....
"A fusace ta kuma cewa " Don't act innocent ka d'auka bamu san abubuwan da kake shiryawa bane,...... Dai dai nan tasi d'in dasu Alh Kasim suke ciki ta k'araso, yasa hannu da k'yar ya bud'e marfin motar yana k'ok'arin kai kwakusa ma kud'in dake hannun Barr Munir yake fad'in" Kud'ad'e na ne, bani su,...ddu... Duka da sunana kake amso su...
"Barr yak'i mik'a kud'in tsam ya mak'e su a hammatar sa yana fad'in" Kasumu ka kama kanka, don't make a sin, wad'an nan kud'ad'e ba naka bane, snn ko an karb'o su ai sabida kare ka da 'ya'yan ka a kotu ne, ko kanada kud'in zaka biyani ne a shri'a mai zuwan.....
"Mummy sai salati take tana tafe hannuwa tana kallon Barr Munir cike da mamaki... Alh Kasim kuwa sai k'ok'arin wawusar kud'ad'en daga hannun Barr yake yak'i sakin su...
"Mummy ta shiga k'ok'arin taya mijin ta suka wawushe kud'ad'en daga hannun Barr Munir suna fad'in "Zai mana amfani , Mummy ta k'ara da mugu kawai mai bak'in zuciya...
"Munir ya zabura yana fad'in" Farha kin zab'i wann azzalumuin mijin naki akaina d'an uwan ki jinin ki.... Yayi kyau kuje, zaku gani wllhi duk sai kunyi nadama..
"Mugunta ya wuce wanda kayi, wllhi kaji kunya duk irin alherin da ka samu a jikin mu nida mijina abinda zaka saka mana dashi kenan, bari kaji saidai muga Alheri, ta k'arashe tana kulle bayan motar tasi d'in... Cikin sauri Alh Kasim yace da dreban tasi d'in su tafi, yana fad'i yana tura envelope d'in cikin hammatar sa... Jane dai sai kallon su take cike da mamaki, tabbas abin tausayi ne kaga wanda suka rik'e kud'i da madafan iko irin Dasuki family yau suna sa'insa kan kud'ad'en da basu taka kara sun karya ba, kud'ad'en da a da saidai suyi kyauta dasu basu san sunyi ba.....
"Munir ya fuzar da iska yana shafe kansa yana dukan kwalta da k'afafun sa, wllhi zai bama Alh Kasim mamaki, Allah Ya kaimu rananr shiga kotu, da wann tunanin ya k'arasa shagon mak'ocin su da ya rok'a yake d'an kwana don yanzu zaman apartment d'insa yafi k'arfin sa.....
**********
"Zaune yayi a parlor yana lissafin kud'ad'en kaman daga sama suka jiyo knocking..
"Cikin sauri Alh Kasim ya shiga tura kud'ad'en k'asan carpet, cikin dabo dabon maganar sa yake fad'in" Kar ku bud'e k'ofar nan, nasan Munir ne, kar ku barsa ya shigo.....
"Mamy da Mummy dake kitchen suka kalli juna suka girgiza kai kafin Mummy ta dubi Jane dake k'ok'arin zuba macaroni cikin ruwa tace " Jane pls get the door...
"Jane ta kalli Mummy kafin tace " But.. Mummy tayi saurin katse ta da fad'in" Don't mind him Jane, just get the door, who knows it might be somebody else....
"Jane ta gyad'a kai kafin ta isa k'ofa ta bud'e, cike da mamaki take kallon mai knocking d'in ba kowa bane illa Salim, ya toshe fuskar sa hood ..... Baki na rawa tace " Salim...???
"Jin an ambato Salim yasa Mummy da Mamy fitowa da sauri yayinda Alh Kasim yayi sakare yana sauraren su...
"Salim da Mummy suna had'a idanu sai rungume juna sukayi kuka na neman kufce masu, cikin muryar kuka Mummy take fad'in" Why Son, meyasa ka dawo? Zasu kama ka, zasu kama ka Son.....
"Cikin kuka shima yake fad'in" Mummy I just can't, Mummy ina so na dawo na san halin da Daddy yake ciki...... Kuka ya hanasa ci gaba da maganar da yake....
"Barr Munir dake lab'e ta can gefen gidan... Murmushi yayi kafin a fili ya furta, So you're back, zan d'auki fansa na akan d'anka Kasim Dasuki, murmushi ya kuma yi kafin ya ciro wayar sa ya shiga neman layin jami'an tsaro......
"Salim yana hango mahaifin sa yanda ya koma hawaye suka ciko idanun sa.... Cike da sanyin jiki yake k'arasowa cikin parlorn yana fad'in" Da... Daddy is that you, Daddy haka ka koma.....
"Lokaci guda hawayen na dama wanda bai tab'a yin irin su ba suka ciko idanun Alh Kasim.
"Kai gaba d'aya ma sai lokacin suka lura da rama da bak'in da Salim yayi...
"Cikin sauri Salim Ya k'araso ya tsuguna had'i da eungume mahaifin sa nan sukayi bursting cikin tsananin kuka gaba d'ayan su....
"Cikin kuka Alh Kasim yake fad'in" It's all my fault, I failed you all, I destroyed our family, na cuce ku gaba d'aya, If only I raised you well, idan da ace ban zamto mai son kaina ba duk da hakan bata faru ba.... "Son bazan iya d'aukan girman laifuka na ba.... Nasani ban gama ganin ishara ba bisa bak'ak'en laifukan da na aikata wanda bazan iya fad'i maku wasu daga cikin su ba..... Ba Salim kawai ba harta su Mummy kuka suke yi sharshar da hawayen su...
"Kaman daga sama sukaji k'aran motar police ga bugun k'ofa da ake da k'arfin gaske...
"Cikin su gaba d'aya ya d'uri ruwa, Salim cikin sauri ya mik'e yana girgiza kai ya nufi window ya dira da gudun gaske.... Lokaci guda police suka ci gaba da bugun k'ofa dole Jane ta k'arasa ta bud'e...
"Where is he??? Suka tambaya kai tsaye...
"Kuka Mummy take tana fad'in " Pls no, no, don't take my son away from me, pls I beg of you....
"Tuni 'yan sanda sun soma searching gidan...
"Cikin sauri inspector ya danna intercom d'insa ya sanar da 'yansandan dake waje kan su watsu a unguwar su duba Salim.... Cikin sauri suma suka fice...
"Har su Mummy suka fito sai faman kuka take kaman ranta zai fita...
"Haka polisawan nan suka bi Salim a guje suka capko sa, kuka yake kaman k'aramin yaro yana fad'in"Mummy pls I don't wanna go to jail, pls mummy, Aunty pls don't let them take me, Jane pls help me, I don't belong to jail.......
"Munir ya k'araso yana murmushi kafin yace " Don't you worry my dear nephew, I'll defend you in court.....
"Alh Kasim kallon Barr Munir kawai yake suna aika ma juna kallo, tabbas yasan shi yayi reporting Salim, idan ba haka ba waye zai san yazo....
"Suna ji suna gani aka tasa k'eyar Salim cikin motar 'yan sanda, Jane ta k'arasa da sauri ta taro masu tasi suka bi bayan motar police d'in, Alh Kasim sai watsa ma Barr Munir mugun kallo yake..
"Barr Munir kuwa ya murmusa harda d'aga masa gira ya d'aga masa hannu alamun 1/1 kafin shima ya tari acab'a ya cika ma rigar sa iska....
"Koda 'yan sanda suka soma interrogating Salim suka sanar dashi Uncle d'insa ne yayi reporting nasa Alh Kasim ko kad'an baiyi mamaki hakan ba yasan za'a rina.....
"Babu yanda 'yan sanda basuyi ba Salim Ya fad'i dalilin gudun da yake fir yak'i admitting, k'arshe haka suka jefa sa d'akin da Labib yake...
"Labib yana zaune yana karanta doguwar rubutun da sharara kaman daga sama ya hangi officer rik'e da katifa kafi tabarma, daga can gefensa ya hangi wani matashi hannun sa rufe cikin handcuffs, saida suka matso kusa sosai kafin ya gane Salim ne... Sabida tsaban ramar da yayi Sam bai gane sa ba....
"Officer ya bud'e cell d'in ya tura k'eyar Salim ciki had'i da sunce masa hannayen sa kafin ya wurga masa katifar kansa ya dubi Labib yace " I brought you company.... Enjoy your castle princes.... Ya k'arashe yana murmushi...
"Labib ya k'arasa ya d'an bugi kafad'un Salim kafin yace "Welcome bro... Ya karbi katifar yana gyara masa...
"Zama sukayi su duka biyu saman katifar Labib kafin Labib ya soma tambayar sa garin yaya aka kama sa, .
"Salim bai b'oye masa komai ba ya fad'i masa, ya k'ara da Munir ne yayi reporting nasa..
"Dariya Labib ya dinga yi har yana rik'e ciki kafin yace " Ai na d'auka Munir won't turn his back on his nephew, I was wrong ashe, kodayake nasan shida Alh Kasim yanzu are not in good terms, kowa a cikin su k'ok'arin ceton kansa yake....
"Salim Ya fuzar da iska kafin yace " It's all over, the Dasuki's are ruined, we have nothing left, naji ance Hajiya Raliya is now the owner if the company, ....???
"Labib ya murmusa kafin yace " K'warai kuwa, Inlaw d'inka da, wanda Kasim Dasuki ya tarwatsa masu rayuwar su a baya, da duk wani farin cikin da suke ciki.... But at the end Allah Ya nuna masa ishara, company d'in da yake tamkar rayuwar sa sai ya Mallaka masu....
"Salim yayi shiru kawai ba tareda ya iya furta komai ba.... "Labib ya jawo sa yana buga kafad'unsa yake fad'in" Hey just cheer up is not the end of the world.... This is exactly where we belong... Ya k'arashe yana dariya kafin yace " Ka tuna sanda na b'alle k'waya muka ba wa Jalal ya sha.... Ka tuna yanda ya ringa layi yana ce mana muyi shiru muyi shiru....
"Salim Ya kwashe da dariya ya d'aura yatsan sa saman d'an leb'en sa yana fad'in"Shiiiish" yana gwada yanda Jalal yayi wancan lokacin.... " Dariya suka kuma yi a tare, kafin Labib yace " Ka tuna Tariq yanda yake lashe baki sanda na keta mata riga.....
"Salim yayi dariya kafin yace " Duka basu nan, familyn Yusuf Maina ta tarwaste, that idiot, I mean Umar is in Jail, Tahir Marafah ya mutu, Asmah da DT Amir duk sun mutu, all because of Kasim Dasuki..... Dariya suka fashe dashi suna fad'in muguntar Alh Kasim lokaci guda dariyar su ta juya zuwa kuka... Kuka sosai suke cike da takaici da danasanin irin rayuwar da suka tsinci kansu ciki...
"Lokaci guda Salim Ya hangi doguwar takardan da Labib yayi rubutu a ciki...
"Hannu yasa ya d'aga yana goge hawayen idanun sa yake fad'in" What's this..... Cak ya tsaya yana karanta kallon takardan....
*Sameena Aleeyou Mrs*
🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
96
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
*_Dedicated To All Victims Of Rape..._*
_Our sweet Aunty Zee the chapter is yours, Allah raya mana zuri'a ya d'ayyiba 😍😘_
"Ya d'ago kansa cike da mamaki yana duban Labib, murya har na rawa Salim yake fad'in " What's this for...?? Are you backing down??
"Labib ya murmusa kafin yace " Toh me kake so nayi, yeah this is my confession, kana tunanin akwai miracle d'in da zai fitar da kai daga nan ne..? Tell me what else do you still have, me kake dashi, wani hope kake dashi..? Baka da zab'in da ya wuce ka fad'i gaskiya domin kuwa prison ne dole mu tafi ko muna so ko bamu so....
"Salim Ya shiga k'ok'arin girgiza kai yana fad'in" No, no Labib don't do this to us....
"Tsaki Labib ya buga had'i da fincike takardan don kuwa bai bari Salim Ya karanta ba, ya d'aga k'asar matashin sa ya tura ciki had'i da kwanciya ya bama Salim baya...
"Shiru kurum Salim yayi yayinda zuciyar sa ta shiga zullumin abinda ka iya zuwa yazo, sanyi ta d'an soma kad'asa ya soma shivering yana janyo hannun rigar sa... "K'arasawa bakin k'ofan k'arafunar yayi ya shiga k'walla ma 'yan sandan kira " Officer... Officer.
"D'an sanda d'aya ya k'araso yana watsa masa mugun kallo.
"Salim yana shivering yake fad'in" Officer it's cold in here ko zaka taimaka min da blanket....
"Officer ya kwashe da dariya kafin yace " You think this place is a hotel right,?? Toh ka jirani zan kawo maka abin rufuwa... Useless kawai... Ya k'arashe yana watsa masa mugun kallo kafin ya wuce...
"Labib dake kwance yana sauraren su fashewa yayi da mugun dariya har yana hawaye... For sure yaji dad'in kamo Salim da akayi..
"Salim Ya d'an juyo yana duban sa kafin yace " This is not funny you know...
"Labib ya juyo yana duban sa still dariya yake kafin yace " You're so stupid wllhi, okay ai nan yafi k'asar gada da kake rayuwa, ka gode ma harda mattress ka samu, zo kawai ka kwanta a haka and enjoy your hell..... Ya k'arashe yana kuma tuntsurewa da dariya..
"Fuzar da iska kawai Salim yayi kafin ya isa katifar sa ya kwanta had'i da tak'urewa waje guda...
***********
"Zahidah da Shattima ne zaune saman wata k'atuwar darduma dake shimfid'e cikin katafaren Lambun wanda yake Kore sharr ta ko ina, yayinda Jalal da Zubaidah suke zaune saman wasu 'yan duwatsu a bakin ruwan dake faman gangagara cikin duwatsun, daga ganin su zaka san zukatan su sun cika da nishad'i,.
"Hannu Jalal ya mik'a ya rungumo bayan ta had'i da kwantar da ita cikin jikin sa, yayinda Zubaidah taci gaba da jefa k'ananan duwatsu cikin ruwan,...
"Zahidah da Shattima dake zaune saman darduman su na picnic d'in sai faman murmushi suke suna kallon su, sosai suka burge su, .
"Zahidah tasa bayan hannun ta tana share hawayen da suka zubo mata sanda Shattima ya labarta mata irin hardships da challenges da su Jalal da Zubaidah suka fuskan ta a rayuwa... " Ganin tana share hawaye yasa sa saurin mik'o mata hanki, ta amsa tana murmushi ta goge hawayen kafin taci gaba da fad'in" Sun sha wahala, but still....despite everything they've been through they didn't give up on each other, they deserve to be happy..... Tana kallon su take murmushi take maganar, taci gaba da fad'in" Just look at them, they are happy now, I'm so happy for the both of them.... Kaman daga sama ta jiyo muryar Shattima yana fad'in" And soon ours will come....
"Ta d'an dube sa tayi murmushi kafin tace " You know what Ya Shattima, Zubaidah should write her Story and share it with the world....
"Shattima ya murmusa kafin yace " Yeah hakane, labarin ta akwai tarin jarabawa da k'alubale snn ya k'unshi labarin mutane da dama, ciki harda naki, and you know what...??
"Ta kafe sa da idanu ba tareda ta iya furta komai ba...
"Shattima yaci gaba da fad'in" You are the most beautiful part of the story..... Sabida had'uwa dake da family d'inki ya sanya Jalal and his entire family cikin sabon rayuwa mai cike da farin ciki....
"Zahidah ta murmusa kafin tasa hannu ta rufe fuskar ta, kaman daga sama sai ganin Jalal da Zubaidah sukayi zaune gefen su, fuskokin su cike da murmushi. Wani sabon kunya ya kuma lullub'e Zahidah...
"Shattima ya murmusa kafin ya dubi Jalal yace " Bro now that you saw everything I've to admit that I love your only sister..... She's my inspiration, I love her with all my heart, and I promise to cherish her , love her and take care of her till my very last breath......
"Zubaidah sai murmushi take don kuwa abin ya mata kyau, tamkar taurarin cikin film. Mai da duban ta tayi ga Jalal tana jiran ganin nasa reaction d'in, murmushi ta gani saman fuskar sa, yasa hannu ya dafa kafad'an Shattima kafin yace " Bro if my sister loves you as well, then you have my unconditional support, fatana shine ku kasance cikin farin ciki, Shattima you are my brother from another mother and Zahidah is my favorite and only sister, all I want for her is a happy ever marriage..... I know you'll take care of her.... Ya ci gaba da murmushi ya rik'e hannun Shattima da hannu guda sann Zahidah da hannu guda kafin yaci gaba da fad'in" You both have my blessings, Allah Ya wuce mana gaba ya tabbatar da abinda yafi zama alkhairi...
"Murmushi ya cika fuskokin su, tabbas yanzu ya sami k'warin gwiwan doke Khalifa, this time around bazaiyi wasa da DAMAR SA ba... Zahidah ta k'araso ta janye hannun Zubaidah suka matsa gefe Alkyabban su sai sharan k'asa suke....
"Jalal da Shattima suka bisu da kallo fuskokin su cike da murmushi...
"Khalifa dake saman dokin sa ya hango komai, hawaye masu d'umi suka gangaro masa, tabbas idan yana son Zahidah he should let her go, ya k'yaleta ta samu farin cikin ta da wanda take so, abubuwan da ya gani ya ishe sa ishara, na farko bai zama Yarima ba snn na biyu bazai tab'a samun soyayyar Zahidah ba koda ya aureta snn na uku mahaifin sa na cikin tsananin ciwo tabbas d'an Adam ya kasance mai godiyar Allah da duk abinda Allah Ya hore masa not everything you want you get..... Juyawa yayi ya soma tafiya cike da sanyin jiki da nadaman kasancewa d'an Adam mai ji da kai da ya kasance a baya.....
**************
"K'arfe 5:30pm daidai jirgin su tayi landing a babban filin jirgin saman Abuja,..
"Annah tana rik'e hannun Kamal cikin nata, gaba d'aya sun canza sunyi kyau bakace su bane,.
"Shattima da Zahidah sun jero suma gwanin sha'awa, wani dad'i take ji finally Abbah ya barta tayi tafiya sabida Zubaidah da Hamman ta Modibbo snn zataga k'awarta Kausar....
"Gogan shima ya jero da princess d'insa, tana sanye cikin bak'ar doguwar riga abaya tayi kyau sosai, har wani shek'i ta k'ara, hannu yasa ya sakale cikin nata... D'an d'ago kai tayi tana duban sa ya sakar mata murmushi kafin ya rage tsawon sa daidai kunnen ta yace " You so beautiful my wifey I love you....
"Murmushi kawai Zubaidah tayi had'i da d'an mintsilan hannun sa.... Matse 'yan yatsun hannun nata yayi da d'an k'arfi suka sakar ma juna murmushi su duka biyu....
"Tuni Guards sun iso da motoci na alfarma, nan suka shige gaba d'aya suka nufi gidan su dake Asorock..
"Jalal zai masu ordering abinci Annah tace " No zasuyi ta dubi Zubaidah da Zahidah tace girls kun sanni babu wani sayo abinci da za'a keyi, this is not Fadah, dukan ku aiki zakuyi, I want you all to be good housewives....
"Shattima yace " Yauwa Annah hakan ma yafi... Ya k'arashe yana kashe ma Zahidah ido..
"Zahidah ta d'an turo baki tana aika ma Shattima hararan wasa kafin tace " Annah pls mana yanzu fah muka iso...
"Annah ta galla mata harara kafin tace " Girls to the kitchen, no excuses...
"Zubaidah sai dariya take ma Zahidah duk da ba wai jin dad'in jikinta take ba, haka dole Annah ta turasu kitchen...
************
"Zaune suke saman wasu brown kujeru masu shape d'in shell, daga gani ba sai ance maka na shak'atawa bane, daga ganin su kaga masoya amma sam su d'in basu fahimci hakan ba...
"Kausar ta tsiyaya masa lemonade d'in cikin cup kafin ta mik'a masa fuskar ta d'auke da murmushi..
"Murmushi shima yayi kafin ya karb'a yace " Thank you lil sis,
"Kausar ta murmusa kafin tace " At your service big bro.... Ehen you were telling me Salim's been caught ....
"Ansar ya kurb'i lemonade d'in ya had'iya yaji wata sanyi cikin zuciyar sa kafin ya ajiye saman k'aramin table d'in dake wajen yace " Yeah police sun kama sa, and you know what, his uncle reported him..... Their lives became so miserable....
"Kausar da idanun ta ke kafe waje guda suna neman ciko k'walla don kuwa duk ranar data tuna Salim da family d'insa hakan ne yake faruwa da ita, ta d'an sa bayan hannun ta ta goge hawayen sabida tuno Asmahn ta mahaifin ta da kuma Amir d'inta da tayi kana tace " They got what they deserve , non of them is innocent.... Mutum d'aya nake tausayi Hajiya Nurah mamin Labib, don kuwa I'm pretty sure Alh Kasim shine sanadin mutuwar mijin ta, ya cuce su ya ruining masu ryuwan su.... Shine sandin duk abubuwan da suka faru ko nace suke faruwa..... Ta k'arashe hawaye na gangaro mata....
"Cike da tashin hankali Ansar ya d'an turo gaba daf da face d'inta yake fad'in" It's okay lil sis, dukan su yanzu basu da wajen gudu, basu da zab'in da ya wuce suyi surrender, they'll all pay for their damn crimes.... Ki daina kukan nan kinji, it hurts, it really hurts..... Ya k'arashe fuskar sa cike da damuwa sosai.....
"Kausar ta d'ago tana duban sa, sun jima suna duban juna cikin idanu....
"Mumsy dake tsaye saman balcony kallon su take cike da so da k'auna, fuskar ta Ya cika da annuri tana mai son fahimtar abubuwa da dama, idan hakan ta kasance zatafi kowa farin ciki.... A hankali ta furta Allah Ya maku albarka 'ya'ya na...
_Ni Sameena na amsa da Ameen Mumsy_
************
"Fitowar sa daga gidan su Kausar ya ga kiran Jalal na shigowa, saida ya rage speed kafin ya d'aga yasa a speaker... Da kirari ya soma masa bayan sallama..
"Ranka shi dad'e,... Allah Ya taimaki Yarima, Allah Ya baka gidanku...
"Jalal ya murmusa kafin yace "Would you stop being ridiculous Attorney...
"Ansar yace " Toh ba gaskiya na fad'i ba... Kai fah you must adopt sarauta things like it or not...
"Yaya su Abbah, ya Gombe. Where is my Annah, nayi missing nata da delicious foods d'inta sosai fah.
"Jalal ya murmusa sanda ya saka trafficator yana sharan kwana kafin yace" Duk suna lafia... Gombe kuma mun baro shi lafia,...
"Ansar ya b'alle orbbit cwing gum ya jefa a bakin sa yana mai ci gaba da driving kafin yace " Ban gane kun baro Gombe lafia ba, don't tell me kuna Abuja...
"Jalal ya murmusa kafin yace " D'azu muka iso....
"Ansar harda wani sauk'e deep breath kafin yace " Great news ever, kasan we don't have much time left, kwana biyu ya rage a shiga kotun, ya maganar Dr d'in...
"Jalal yace " That's precisely why I called... Ka gane yanzu haka na fito daga gida gidan ka na nufa, Dr d'in yana Gwarumpa tare da Detective Mudi, so I'll fetch you up sai muje mu same su ku samu kuyi magana... And daga can zamu wuce station issue na case d'in sister inlawn mata ta..
"Ansar yace " No ba sai kaje Apo ba mu had'u a Gwarumpan nima daga Asokoro na fito yanzu haka ina hanya ma..
"Jalal ya murusa kafin yace " Kai wai tarewa ne kayi gaba d'aya a Asokoro, anya kuwa wann lil sis din naka ba ita ke b'oyeka a Asokoro ba....
"Ansar ya dara kafin yace " Kai kam sai mun had'u... Dariya Jalal ma yayi kafin sukayi sallama, ko wannen su ya maida hankali ga tuk'in da yake.....
**********
"Daga gidan inspector Mudi station d'in da aka tsare Hadiza suka wuce. Nan suka tarar da inspector Bilal shi ya tsaya masu akan komai har releasing papers d'in suka zama ready, dole aka je aka zo da Hamma don akwai yanda zai saka hannu kafin a Saki Hadiza...
"Idan kaga Hadiza sai ka tausaya mata yanda halittar ta ta canza lokaci guda, gashin kanta duk ya tuge ta d'aid'aice tayi bak'i, jikinta kuwa ta ko ina tabo ne, bakinta har tsini ya k'ara sabida azaban bugu da yake sha...
"Daga can data hango Hamma hawaye ya ciko idanun ta... Tana k'arasowa ta zube saman gwiwoyin ta, tana rik'e da k'afafun sa take sharb'an kuka tana rok'on sa gafara....
"Habibu ka yafe mun, ku yafe mun kaida Zubaidah nasan na ha'ince ku na zalunce ku, wllhi ko yanzu naga ishara, ku yafe min don Allah...
"Allah sarki Hamma tuni shima ya fashe da kuka harda shesshek'a.
"Jalal da Ansar cike da tausayawa suke kallon su, k'arshe mota suka wuce saida suka gama koke koken su kafin suka nufo mota suka wuce, Hadiza sai jero godiya da addu'o'in alkhairi take ma Jalal da Ansar....
**********
"Suna isowa gida Hadiza sai rakub'e rakub'e take, Zahidah da Kamal dake jera plates a dinning ai da gudu suka nufi stirs ganin Hadiza don kuwa sun zaci mahaukaciya ce koma aljanah....
"A tamanin su Annah da Zubaidah suka fito daga kitchen suna tambayar su lafia....
"Cirko cirko suma suka tsaya don kuwa ba don sunyi ma Hadiza farin sani ba sai suce wann tsohuwar kamun hauka ce, Hamma ne ke biye da ita yana mai ci gaba da share hawayen sa...
"Har gaban Zubaidah ta k'arasa ta durk'usa tana kuka shar shar da hawayen ta take rok'on Zubaidah gafara... Daga Annah har Zubaidah kai harma Zahidah dake mak'ale saman staircase tausayi ne ya cika zukatan su...
""Kamal kuwa da gudu ya k'araso ya rungume ta yana fad'in" Umma na kin dawo ne, nayi kewarki meyasa kika tafi kika barmu....
"Hadiza ta rungume Kamal tana mai ci gaba da kuka...
"Ta d'ago hannayen ta sama tana duban Zubaidah taci gaba da fad'in" Ki yafe min Zubaidah, ki yafe min Don Allah, wllhi tallhi hakkin ki ne, hakkin ku ne gaba d'aya ya kamani.... Annah ku yafe min, na tuba na gane kuskure na, bak'in ciki da hassada shi ya kaini ga halin da na tsinci kaina ciki, don Allah Zubaidah kice kin yafe ni....
"Zubaidah tasa bayan hannun ta ta goge hawayen ta kafin ta kamo Hadiza ta d'ago ta kana ta soma fad'in" Ni ban rik'eki ba Yaya Hadiza, ki sani na yafe ki tuntuni, Allah Ya yafe mu gaba d'aya....
"Hadiza ta rungume ta tana kuka sosai, cikin zuciyar ta kuwa bata jin zata iya fad'a masu musababbin abinda tayi har checks d'in Kasim Dasuki suka shigo hannun ta, babban dad'in dataji shine yanda ko kad'an basu tada zancen ba.... Asirin ta Ya rufu babu wanda zai sani..
"Haba Hadiza fah, an sake, wani dad'i take ji kowa ya nuna mata komai ya wuce, nan nan take da Zubaidah kaman ta maidata ciki, Zahidah kuwa sosai abin ke bata dariya, sosai matar take bata dariya, daga ganin ta kasan anyi makira ja'ira a da.....
"Zahidah tayita neman layin Kausar bata samu k'arshe kawai ta hak'ura sai bayan an gama da court case ta neme ta....
*********
"Alh Kasim ya d'aga idanu ya dubi k'ofar gidan kafin ya dubi d'an tasi d'in yace Malam nan ne... Cikin maganar sa da bai fita sosai...
"Mai tasi ya tsaya a daidai k'ofan gidan Ansar yanda Alh Kasim ya umarce sa....
"Kallon Mai tasi d'in yayi kafin yace " Malam ka taimaka min Don Allah ka warware mun keke na ka fito dani ka d'aura ni akai....
"Tsaki mai tasi yayi kafin yace " Amma dai wann mutumi nacin tsiya ne da kai, bayan na maka k'ok'ari na d'auko ka shine zaka wani ce na fito da kai, kai wllhi bazan yi ba, idan ban watsar da kai a nan nayi tafiyata ba.... Or to make you even more cripple.... Get out dalla banza kawai.....
"Ya k'arashe maganar sanda ya fito ya wurgar dashi harda jefa masa keken sa akan sa, ya karkad'e hannu ya shige motar sa yana fad'in" Banza kawai ni banma san meyasa na d'auko ka ba....
"Alh Kasim yasa bayan hannu ya share hawayen da suka zubo masa.... Kaman daga sama yaji ana horn a bayan sa... Cikin sauri Jalal ya bud'e motar ya fito yana fad'in" Subhanallah wani tsoho ne a yashe kan titi...
"Zubaidah na zaune gaban motar yayinda Annah Hadiza da kuma Zahidah suke baya.....
"Carkeke Jalal yayi yana kallon Alh Kasim dake watse k'asa, ashe shine a zube a wajen, da mugun mamaki yake bin Alh Kasim da kallo, yanda lokaci guda Allah Ya canza sa....
"Ganin da sukayi ya tsaya yana bin mutumin da kallo ya kasa taimaka masa yasa su fitowa babu shiri suka nufo wajen...
"Ai suma cak suka tsaya suna kallon ikon Allah.... Hadiza ta shiga tafe hannaye tana salati...
"Alh Kasim ya rarrafo ya k'araso gaban Zubaidah yana mai ci gaba da fad'in" Ta yafe masa...
"Mamaki da Al'ajabi ya hanasu furta koda kalma guda, tsoron duniya ya kuma cika zukatan su...
"Harta Jalal kasa cewa komai yayi sai kallon buwayar Ubangiji da ya tsaya yi.....
"Ansar ne ya turo gate ya fito don dama mai gadin sa ya sanar dashi abinda ke faruwa a Gate.. Har gaban Alh Kasim ya k'araso kafin yace " Alh Kasim yau kaine a k'asa, k'arshen tikatiki tik, ka sani Allah bazai tab'a barin zalunci ya tabbata a doron k'asa ba...
"Snn da kazo kana rok'on mu gafara, idan mu munji tausayin ka mun yafe maka, ina Allahn sauran mutanen da ka zalunta, shin su sun yafe maka, shin matayen da ka maidasu zawrawan dole ka rabasu da mazajen su shin su sun yafe maka, 'ya'yayen da ka rabasu da iyayen su ka maidasu marayun dole shin su sun yafe maka, .... Snn Alh Kasim idan har da gaske kake kayi nadaman duk abubuwan da kayi a kotu zakayi wann bayanan a gaban Alk'ali, justice must be served.... Kaje gida sai mun had'u a kotu.. Allah Ya yafe mu gaba d'aya...
"Hawaye na bin idanun Alh Kasim ya juyo yana nuna Hadiza yana fad'in" Kece sila, kece kika soma cewa zaki iya rufe bakin Zubaidah idan an baki kud'i...... Ya k'arashe yana tari sosai...
"Hadiza cike da borin kunya take waige waige tana fad'in" Ni, ni, sharri zaka min, wato kaga k'arshen ka yazo shine bari ka bini da sharri bayan wanda ka mun... Wlhi k'aryar ka tasha k'arya....
"Kallon mamaki suka bita dashi had'i da girgiza kai kafin suka shige cikin gidan suka barta nan tsaye kan Alh Kasim sai banbami da masifa na borin kunya take masa... Taga abin bazai ficce ta ba ta ciro wayar ta cikin jaka, ta lasto lambar Hajiya Farha,..
"Su mummy suna nan gida hankali tashe don babu wanda yace yaga fitar Alh Kasim sai ganin wayar Hadiza tayi na shigo mata, har ta mance tanada layin Hadiza...
"Da masifa Hadiza ta soma mata tana fad'in toh wllhi tallhi ki rabani da wann shegen mijin naki, don munafunci bayan k'ulleliyar da ya k'ulla min shine zai kuma biyowa ya d'aura min laifi yaga bashida hanyar tsira, toh wllhi idan yayi gigin d'auran laifi wllhi har kuma bazaku tsira ba....
Tayi tsaki ta kashe wayar kafin ta nufi cikin gidan, facal facal, sai faman huci take ita ala dole an d'aura mata sharri...
"Hankali tashe su Hajiya Farha suka fito suka nemi tasi suka nufo k'ofar gidan Ansar suka kwashi Alh Kasim....
"Koda Hadiza ta shigo cikin gidan babu Wanda ya d'ago mata zancen...
"Kana ganin yanayin ta kasan dai babu gaskiya a tattare da ita...
"A haka kwanakin komawa kotu suka cika....
********
*January 21st,* rana ce da tayi daidai da ranar komawa kotu, jama'a ne ta ko ta ina sun cika haraban kotun... Jama'a ne cike a wajen musamman mata matasa kai harda wanda suka d'an data, ko wacce ta rik'e babban takarda a hannun ta mai d'auke da rubutun Justice for Zubaidah, rubutun anyi su ne da manyan haruffa, basu fasa nanata abinda ke rubuce jikin takardun su ba tamkar masu biya karatu.....
"Sanda aka zo wucewa dasu Salim sai k'ara sautin muryoyin su suke, .
"Hajiya Farha itace mai tura keken Alh Kasim yayinda Mamy ke tsaye gefen ta...
Sanda su Zubaidah suka iso kuwa gaba d'aya waje ya dad'a kacamewa, sai ka rantse Prinyanka Chopra ne ko kuma Salina Gomez ce ta shigo taro sabida yanda hankulan mutane yayi kansu gaba d'aya itada Jalal, sai kakkare ta yake sabida yanda mutane ke tururuwan zuwa kallon ta, tamkar wata celebrity haka ta koma, bai yi niyan Guard su zo kotun ba dole yayi waya ma Chief security d'insa yace ya turo masu guards, ...
"Journalist kuwa kaman anyi ruwan su....
"Bayan wasu mintoci aka hallara a d'akin gudanar da shari'a....
*Toh fah readers..... Here we are.. #FinalTrial let's see su waye zasuyi nasara... 😄**
*Sameena Aleeyou Mrs*
🌒🌒🌒🌒 *ZUBAIDAH*
97
*©Sameena Aleeyou... ✍🏾*
_*Dedicated To All Victims Of Rape...*_
_🌈Kainuwa Writers Association wannan Shafi naku NE, Allah k'ara hazak'a d'aukaka da baseera... Ana tare🤝 😍_
*Anty Batul Jattko*
*Aysha Sada Machika (Commander)*
*Aisha Machika*
*Fauxy MB*
*Anty Fauzah*
*Ummy Ontop*
*Ayshat Hamzat*
*Maryam Ahmad Paki (Inlaw)*
*Mrs Mansoor*
*Anty Napy Saulawa*
*Nafisa Isa*
*Beebhalo*
*Fadeela Talba*
*Maimouna Maradi*
*Jiddah*
*Jiddah cool*
*Ummy Abdoul*
*Meenat Yakasai*
*Ummu Nabil*
*Halima MK*
*Sa'adat Alk'ali*
*Maryam Ishaq*
*Maryam Gozaki*
*Miss Ayush*
*Jamila Isma'il*
*Aysha S Bayero*
*Memcy Ata*
"Zahida rik'e da hannun Kamal ta bud'e bayan BMW d'in Shattima wa Kamal ya shige yana mai cike da murnan za'a je Wonderland, ya cikata da surutu yana tambayanta Anty Zahidah pls nidai zan shiga Water splash pls kar ki hanani...
"No Kamal you might catch cold, and it's risk for kids like you kaji Champ.... D'an turo baki yayi kafin yace " Okay fine but zan sha ice-cream, pls don't say I'll catch cold..
"Murmushi tayi ta shafi kansa kafin tace " Of course zaka sha ice cream harma da Pizza.... D'an turo baki yayi kafin yace " I don't like pizza I prefer Shawarma...
"D'aga masa babban yatsa tayi tana murmushi kafin tace " Hey same team, Team Shawarma,.. Tsalle ya d'an yi yana murna harda mik'a mata hannu suka tafa yana fad'in yaji dadi team din su d'aya...
"Shattima ne ya k'araso yana danna wayar sa yake fad'in" Team pizza...
"Zahida ta juyo tana duban sa tana murmushi yayi kyau cikin shigar sa ta k'anan kaya kafin tace " Mun maka wayo mu biyu kai d'aya... Ehen kuma mutum dole yaci irin namu...
"Shattima ya k'araso yana saka phone d'insa cikin aljihu kafin yace " Aima dole na tunda Gimbiya tana so...
"Murmushi kurum tayi cike da so da k'aunar sa..
"Shattima ya k'ura mata idanu yana kallon ta yanda tayi kyau sosai kafin yace " My lady, you look spectacular...
"Murmushi tayi kafin ta d'an rausayar da idanu tace " Godiya nake My Champion... Murmushin shima yayi kafin ya bud'e mata frontseat yace " Shall we??... Gyad'a masa kai tayi kafin ta shige nan suka d'auki hanyar Wonderland.... Fuskokin su cike da murmushi
*********
*National High Court*
"Kotun ta cika mak'il harda mutanen da bakayi zato ba, hannun Zubaidah rik'e cikin na Jalal, tunda aka shigo dasu Labib take jin kanta na juyawa, lokaci guda kanta ya sara ya soma mata ciwo, daurewa kawai take amma kam tabbas bata jin dad'i wanda ta alak'anta hakan da cink'oson mutanen da ta shiga ne ya janyo mata hakan ko kuma ganin su Labib....
"Jalal ya d'an dad'a rungumota daidai lokacin da aka shigo da Umar, idonsa k'yam akansu..
"Jalal yace " Baby idan bazaki iya zama a nan ba Annah ta kaiki wancan parlorn ku zauna...
"Murmushi ta sakar masa kafin tace " No Hubby zan iya.... Murmushi ya kuma mata kafin ya mik'a hannun ta ma Annah suka zauna waje guda daidai lokacin da Alk'ali ya shigo gaba d'aya kotu ta mik'e, aka buk'aci su Jalal Labib da kuma Salim da su k'araso cikin akurkin tuhuma....
"Kotu fah tayi tsit k'irajai sai bugu suke yayinda idaniya suka sauya launi....
"Confession d'in Labib aka soma gabatarwa a gaban Judge....
"Tunda aka soma karanto confession d'in idaniya suka shiga zubda hawaye.... Babu kaman Mamy da Mummy, Alh Kasim kam jigum kawai yayi saman wheelchair d'insa yayinda Barr Munir ya kifa kansa kurum yana saurare...
"Idanun Jalal sukayi ja suka kad'a yayinda hawaye yaci gaba da zuba daga idanun Zubaidah, Annah na rik'e da yatsun hannun ta gam, itama hawayen ne ke zubo mata....
"Sanda Salim yaji musabbabin abinda yasa Labib ya kawo masu shawarin su bi Zubaidah su mata fyad'e tsalle yayi ya kai mai naushi a hanci yana kuka da idanun sa yake fad'in" I knew it, I knew you always loved her, you loved Kausar...... I knew you did it to ruin me...... I hate you Labib....
SILENCEEEEE... Don't speak without permission..
"Alk'ali ya fad'i had'i da buga benchi.....
"Mumsy tayi saurin rungumo Kausar dake faman k'unshe bakin ta hawaye na zubo mata,....
"Ansar ya sauk'e idanun sa akan Kausar yana mai jin zafin hawayen da take..
"Kotu tayi stit kafin Labib yaci gaba da fad'in" I'm not denying my guilt your Honor but I promise you, I didn't force any of them to rape her.... All I know.... All I know is that I got Jalal drunk.... Nasan na bawa Jalal k'waya ya sha hankalin sa ya gushe to fulfill my mission..... Bai kai aya ba Jalal dake faman huci yayi wata tsalle yakai mai naushi a hanci yana fad'in" You miserable coward... I knew it, nasan aikin ka ne bansha wani abu alcoholic ba a wancan daren... You'll rot behind bars and pay for your dirty crimes....
"A can mazaunin su Zubaidah kuwa runtse idanun ta kawai take sabida wani irin yunk'urin aman da take ji..... Sanda Jalal ya soma kai duka ma Labib daidai lokacin data shiga k'waza amai.... Hankalin Annah ya tashi sosai..... Lokaci guda hankalin Jalal yayi kansu yana rik'e da kwalan rigar Labib.... A daidai lokacin kuma ran Alk'ali yayi mugun b'aci....
"Cike da b'acin rai yake buga benchi kafin yace " All of you should get out of here... Get out, we breaking for 15minutes.....
"Gaba d'aya dole kowa ya fice...
"Annah ta rik'o hannun Zubaidah lokaci guda Jalal ya k'araso ya rik'eta sosai yana fad'in" Baby are you sick ne... " Ya rik'eta sosai kanta na k'asa bata iya furta masa komai ba... Duban Annah yayi kafin yace " I'll take her to the restroom....
"Annah ta gyad'a masa kai kurum tanai ma Zubaidah sannu...
"Har restroom d'in ya rakata ya wanke mata baki da fuska kafin yace " Zubaidah you can't go back in there... Ki zauna tareda Annah a wancan parlorn...
"Girgiza masa kai tayi tana goge goshinta lokaci guda yana taimaka mata kafin tace " No Ya Jay... Zan iya naji sauk'i, I just want to see them been sentenced to Jail even if I'll vomit again.... I wanna see them confessing their crimes... Ina so ihun su da dariyan su ya b'ace min daga cikin kunnuwa na da confession d'insu da zasuyi... Ta k'arashe tana kwantar da kai cikin k'irjin sa.
"Sauk'e ajiyan zuciya yayi kafin ya matse ta cikin jikinsa had'i da rungume ta gaba d'aya....
"Zulaihat ta hangi su Annah dasu Mumsy suna zazzaune waje guda kafin a koma ga shari'a ta d'an dubi Imam kafin tace " Bara naje mu gaisa.
"Murmushi ya sakar mata had'i da gyad'a kansa kafin yace " Kina so na maki rakiya..?
"D'an murmushi tayi kafin tace " A'a haba dai babu damuwa zan iya zuwa...
"Imam ya murmusa kafin yace " Kin san bakida lafiya kinyi insisting muzo ne shiyasa muka zo, but you supposed to be at home getting some rest.
"Murmushi ta kuma kafin tace " I promise you I'll be fine insha Allah... Snn Umar na tare da jami'an tsaro so he can't do anything insha Allah...
"Gyad'a mata kai yayi yana murmushi kafin ta wuce....
***********
*15minutes later*
"Shari'a taci gaba.....
"Labib yaci gaba da fad'in" Your Honor na bawa Jalal k'waya ne don hankalin sa ya gushe na cimma buri na, sabida nasan tabbas Jalal na cikin hankalin sa bazai bari mu aikata laifin ba.... Idonsa ya kawo ruwa sanda yaci gaba da fad'in" Jalal's innocent your Honor, bai aikata laifin ba bai aikata ba, on the contrary he was only trying to protect her from us, tun lokacin da muka d'aura idanun mu akanta, tunda naga abokai na suna da interest akanta nasan zan iya amfani da damar nayi ruining Salim da Uncle d'ina.....
"Alk'ali ya sunkuya yayi rubutu kafin ya d'ago ya dubi Salim yace " Salim kaji confession d'in da d'an uwan ka yayi... "Ka yarda ka amince ka aikata laifin...??
"Idanun Salim suka ci gaba da zuban hawaye... Jalal kallon sa kawai yake da idanun sa da suka kad'a sukayi jazir...
"Kai muke saurare Malam Salim" Alk'ali ya kuma fad'i...
"Salim Ya soma girgiza kai hawaye na bin k'uncin sa kafin yaci gaba da bayanin yanda mahaifin sa Kasim Dasuki da kuma Uncle d'insa Barr Munir suka shirya yanda zasu lak'aba ma Jalal laifin shi kad'ansa...... Yasa bayan hannu ya goge hawayen da suka zubo masa kafin yaci gaba da fad'in" But your Honor you heard him right, da bakin sa Labib ya fad'i sabida biyan buk'atar sa ya jamu yayi mana jagora snn shine mai laifi a nan, shi yafi cancan ta a hukunta sa, ciki harda mutuwan Tariq da kuma b'ata mana rayuwa da yayi.....
"Labib ya zabura yana kallon sa kafin yace " Shut your mouth you idiot.... Did I drag you by force,????
"Silence...!!!!!
"Don't speak without permission.... " Alk'ali ya fad'i had'i da buga benchi kafin yaci gaba da fad'in" Just answer the question did you commit the crime..??
"I don't care if you were forced or not, just go straight to the point and answer my question, ka aikata laifin...???
"Salim yana hawaye.... "Zubaidah kallon sa kawai take da idanun ta da suka jik'e tana jiran taji amsar sa, kotu tayi tsit gaba d'aya all eyes on Salim....
"Saida ya had'iyi wata miyau kafin ya soma gyad'a kansa yana mai ci gaba da hawaye yake fad'in" Yes yes your Honor, I admit..... I... I took all responsibilities of my actions and declared my self Guilty.....!!!!!.
"Sauk'e nannauyan ajiyan zuciya Zubaidah tayi lokaci guda suka had'a idanu ita da Jalal suna masu kallon juna, idanun ta sharkaf da hawaye yayinda Jalal ya k'ak'aro murmushi saman face d'insa ya sakar mata ....
"Alk'ali ya bawa Dr dama shima ya fad'i duk iyaka abinda ya sani har kud'i da Alh Kasim ya basa da kuma b'acewa da yayi aka neme sa aka rasa duk a dalilin Alh Kasim....
"Alk'ali yayi rubutu kafin ya buk'aci Alh Kasim da Barr Munir su fito gaban Kotu.....
"Barr Munir ya gyad'a kansa hawayen nadama suna k'ok'arin bin k'uncin sa sanda yaci gaba da fad'in" Yes your Honor, naci mutuncin shari'a I'm nothing but a miserable coward, an incompetent Attorney who deserve to rot in jail...... I was always there helping Alh Kasim with his evil missions.... Da taimako na yake gudanar da duk bak'ak'en mugayen laifukan da ya aikata...... Duk mutanen da Alh Kasim ya ha'inta ya salwantar da rayukan su da dukiyar su saida Barr Munir ya fad'i a gaban Judge....
"Kotu ta kacame da kuka... Sosai Kausar take kuka itada mahaifiyar ta sanda suka ji Alh Kasim shine sanadin mutuwar Alh Tahir Marafah da kuma Amir da Asmah....
"Ansar wani irin hawaye mai zafin gaske ne ke bin k'uncin sa ya yunk'ura ya cakamo wuyan Alh Kasim yana kuka sosai yake fad'in" I'll kill you.... You Animal..... Jalal yayi saurin rik'osa sanda Alk'ali ya buga benchi...
"Fizga Ansar yake yana fad'in" You'll spend the rest of your miserable life behind bars...
"Ai Jalal yana janye Ansar Labib yayi kan Alh Kasim yana fad'in" I knew it, I knew it was you.... You were behind my fathers death Kasim Dasuki I'll kill you with my bear hands... Ya mak'ure Alh Kasim yana k'ok'arin aika sa lahira.... Saida aka taru aka janye Labib....
"Kai jama'a gaba d'aya kotu ta rikice saida aka kuma breaking for some minutes...
"Gaba d'aya su Mummy da Mamy kuka suke kaman ransu zai fice, wann wani irin Al'amari ne haka.... Duk wanda yake cikin d'akin shari'an nan saida ya girgiza da jin irin laifukan da Alh Kasim ya tapka.....
"Bayan wasu mintoci bayan an dawo Alk'ali ya buk'aci Hadiza ta fito gaban kotu don kuwa Barr Munir ya fad'i komai yanda ta taimaka masu suka cimma burin su, duk wani shirin da su Ansar suke ita ke kai masu rahoto, har zoben Salim data tsinta ta kaimasu da kuma checks na bogi da suka bata, bai b'oye komai ba....
"Hadiza ta fito gaban kotu hannayen ta duka biyu aka ta durk'usa saman gwiwoyin ta tana kuka tana rok'on a yafe mata wllhi sharrin shed'an ne..... Bata musa laifukan ta ba tsaf tayi confessing itama tana mai cizgan kukan nadama...
"Mamaki da Al'ajabi ya cika zukatan su......
"Bayan Hadiza Umar ne aka fito dashi gaban kotu hannayen sa d'aure cikin cuffs....
"Shima confessing laifukan sa yayi yana mai kukan nadama da rasa iyayen sa duka biyu da yayi duk a dalilin son zuciya da rashin d'aukan k'addara irin nasa.... Har kisan Tariq da yayi bai musa ba....
"Cikin kuka yaci gaba da fad'in" The Dasuki's are to blame for everything.... Su suka destroying rayuwar kowa, su suka fara jefa kowa cikin k'uncin rayuwa....
"Mum d'in Tariq da Alh Maina dake gefe kuka suke su duka biyun, suna kaicon rayuwar da suka jefa d'ansu ciki kafin ya bar duniya, ko kad'an basu ga laifin Umar ba sai nasu....
"Umar ya d'ago kai yana kallon Zubaidah kafin yaci gaba da fad'in" Zubaidah ki sani I did it all because of you, duk abubuwan da nayi nayisu ne because I love you, snn da zan sami chance na kashe su gaba d'aya i'll kill them all, harda mijin naki wanda nafi tsana fiye da kowa cikin su.... .I loved You Zubaidah And until now I still does , and i'll die loving you.... You and only you.....
"Basu bamu chance mu kasance tare ba, sunyi destroying happy life d'in da muke ciki, sabida son zuciya irin nasu...
"Sosai Zubaidah ke kuka yayin da Jalal ya sadda kansa k'asa kurum hawaye na neman ciko idanun sa....
"Zulaihat ma kuka take kaman ranta zai fita tana mai shafa jaririn cikin ta dake k'unshe a jikin ta... Imam kallon ta kawai yake shima hawaye na neman ciko idanun sa...
"Kotu tayi tsit sai rubuce rubuce da Alk'ali yake...
"Tabbas yau ake yin ta, yaune ranar bankad'an asiri ranar tonan silili....
_'Yan uwa wann na duniya kenan inaga ranar mai gaba d'aya... Ranar da gabb'ai zasu bada shaida, shin mun shirya ma wann ranar....???? Kukan kurciya dai Jawabi ne Mai hankali shi ke ganewa.... Allah ka sa mufi k'arfin zukatan mu ka rabamu da sharrin shaid'an da Zuciya... Ameen_
******
"Alk'ali ya d'ago bayan ya gama rubuce rubucen da zaiyi snn ya furta " The Court Decide.....
"Gaba d'aya kotu ta mik'e kowa ya mik'e don jin hukuncin da za'a zartar....
*Sameena Aleeyou Mrs*
🌒🌒🌒🌒 *ZUBAIDAH*
98
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_*Dedicated To All Victims Of Rape...*_
*Gaisuwa ta musamman a gareku tareda fatan Alkhairi Momin Twins and Mum Ma'arouf... 😍🤝*
"Alk'ali yaci gaba da fad'in" Alh Kasim Dasuki an same ka da laifuka wanda ka amsa su sannan shaidu sun tabbatar da hakan..
"Na farko ha'intar abokan huld'arka na kasuwanci tareda tauye masu hakki da jawo nak'asu ma rayuwar su ciki sun had'a da Marigayi Alh Ma'aruf Kumo da k'anin ka wanda yake d'an uwanka ne na jini wato Alh Jamil Dasuki snn abokin kasuwancin ka kuma amini a gareka marigayi Alh Tahir Marafa..... "According to Nigerian Criminal Law you're sentenced to imprisonment for 45years..
"Still Kasim Dasuki an same ka da laifin b'oye gaskiya, ka tilasta ma Zubaidah yin shiru kayi amfani da k'arfin dukiyar ka da ikon ka, kayi threatening nata cewa zaka kashe yayan ta da d'ansa muddin ta bari magana ya fito fili.... For that, according to Nigerian Criminal Law you're sentenced to imprisonment for 6months
"Still Alh Kasim Dasuki, an kama da laifin blackmailing Umar Sanda kayi bribing nasa da kud'ad'e masu yawa domin asirin 'ya'yan ka ya rufu,..... According to Nigerian Criminal Law you're sentenced to imprisonment for 6months
"Still Kasim Dasuki, Kotu ta kama ka da sa hannu dumu dumu, kai kayi umarnin a kashe Attorney Kumo wanda aka sami akasin hakan, aka kashe DT Amir Kaita da kuma Barr Asma'u Marafah... According to Nigerian Criminal Law you're sentenced to imprisonment for 25years...
"Still Alh Kasim Dasuki " Kayi limiting right d'in Faisal Haris matashi d'aya daga cikin yaranka wanda ka salwantar dashi kayi amfani dashi wajen kashe mutane ka cimma burinka at the end ka harbe shi da hannun ka.... According to Nigerian Criminal Law you're sentenced to imprisonment for 23years..
"Alk'ali yaci gaba da fad'in" These are Kasim Dasuki's Sentences (Wad'an nan sune hukuncin Kasim Dasuki)...
"Mummy k'unshe bakinta kurum tayi sanda ta gama jiyo hukuncin mijinta wanda idan an had'a duka yawan shekarun da zaiyi a gidan Yari ya nin ka shekarun sa da yake dasu a duniya,... Tabbas bashida da ranar fita a gidan Yari...... Kuka take, hawaye na bin k'uncin ta, Mamy ma tana gefe tana nata musamman dataji Alh Kasim ne silan mutuwar mijin ta.....
"Alh Kasim kam zaune yake kurum saman keken sa na wheelchair baya ma fahimtar me ake yi domin kuwa gefen sa gaba d'aya a shanye take, sosai yake cikin ciwo ko magana bai iya yi....
"Alk'ali yaci gaba da fad'in" Attorney Munir Anka kotu ta kama ka da laifuka wanda ka amsa su snn k'wakk'waran shaidu da tabbacin kayi hakan sun gabata a Kotu...
"Na farko.. Kotu ta kama ka da laifin tauye gaskiya ka tsaya ka jajirce akan k'arya kayi shaida akan k'arya bayan kanada masaniyar hakan ba gaskiya bane, despite the fact kayi rantsuwa zaka tsare Al'umma da gaskiya zakayi shaida da hukunci da gaskiya a aikin ka, sai aka sami akasin hakan wanda kanada masaniyan hukuncin duk wanda ya aikata hakan a cikin aikin, kayi biris kabi kai ka take gaskiya, Ka wulak'an ta aikin Shari'a... According to Nigerian Criminal Law you're sentenced to imprisonment for 18years...
"Still Attorney Munir, Kotu ta kama ka da laifin taimaka wa Alh Kasim a duk wani shirin sa da yake yi na ha'intar mutane da cutar dasu, bakayi komai akai ba sai taimaka masa da kake yi.... According to Nigerian Criminal Law you're sentenced to imprisonment for 5years..
"Still Barr Munir, Kotu ta kama ka da laifin tauye hakkin Zubaidah, tilas ta mata tayi shiru, tsoratar da ita cewa idan tayi magana ta shigar da k'aran abin da aka mata zaku kashe Yayan ta da d'an sa.... According to Nigerian Criminal Law you're sentenced to imprisonment for 6months.....
"These are Attorney Munir Anka's sentences ( wad'an nan sune hukuncin Attorney Munir)... Alk'ali ya fad'i yana mai juya takardan dake gaban sa yana gyara zaman tabaraun dake manne idanun sa....
"Barr Munir hawaye masu d'umin gaske ne suke bin kumatun sa.....
"Alk'ali yaci gaba da fad'in" Dr Hashim Ajiya, Kotu ta same ka da laifin karb'an cin hanci da rashawa daga hannun Alh Kasim Dasuki, ya saye bakin ka don kar gaskiya ta bayyan snn ka gudu gaba d'aya an neme ka an rasa, bayan kasan hukuncin mai aikata hakan a aikin ka.... According to Nigerian Criminal Law you're sentenced to imprisonment for 1year.....
"Dr Hashim ya dafe kansa hawaye na zubo masa, yana nadama da kaico, shikenan ya rasa aikin sa, ga zaman gidan kaso har na tsawon shekara guda a gaban sa... Kai kaico irin wann rayuwa na son abin duniya.
"Alk'ali yaci gaba da fad'in" Malama Hadiza kotu ta kama ki da laifi kaman haka... Snn kin tabbatar da kin aikata hakan, shaidu masu k'wari sun tabbatar da hakan..
"Na farko " Tauye hakkin Zubaidah kika yi amfani da ikon da kike dashi akan ta a matsayin ki na uwar goyon ta, kika amshi kud'ad'e kika hanata karb'an 'yancin ta na 'yar Adam, kika tilas ta mata yin shiru... Na biyu tampering da evidence da kika yi, kika salwantar da k'wakk'waran shaida da kika samu a wajen kika kai ma Kasim Dasuki don ya baki kud'i... According to Nigerian Criminal Law you're sentenced to imprisonment for 1year.. Kotu ta yanke maki shekara guda a gidan kaso....
"Hadiza ta d'aura hannu aka hawaye na bin k'uncin ta, sam bata sami daman rafka ihu ba ma....
"Alk'ali yaci gaba da fad'in" Umar Sanda, Kotu ta same ka da laifuka kaman haka, snn ka amsa su, shaidu masu k'wari sun tabbatar da hakan..
"Na farko " Karb'an cin hanci da rashawa in exchange of your silence da kayi daga wajen Kasim Dasuki sabida sirrin laifin 'ya'yan su da ka riga ka sani.... According to Nigerian Criminal Law you're sentenced to imprisonment for 6months..
"Na biyu " Sace Zubaidah da kayi ta hanyar tilastawa da kuma tak'ura had'i da tsoratarwa... According to Nigerian Criminal Law you're sentenced to imprisonment for 2years...
"Na uku, Kisan Tariq Maina da kayi, ka d'auki doka a hannun ka sabida yana d'aya daga cikin wad'an da sukayi fyad'e wa maccen da kake so.... According to Nigerian Criminal Law you're sentenced to imprisonment for 25years.....
"These are your sentences.... Umar Sanda...
"Hawaye masu zafin gaske suka zubo ma Umar.....
"Zulaihat ta k'unshe bakinta hawaye masu d'umin gaske suna ci gaba da kwaranya a idanun ta, yayinda Hannun ta ke d'aure saman cikin ta, tausayin kanta da abinda ke cikin ta suka cika mata zuciya....
"Mai Shari'a yaci gaba da fad'in" Labib Dasuki kotu ta kama ka da laifi kaman haka, snn ka amsa laifin ka shaidu masu k'wari sun tabbatar ka aikata ....
"D'aura k'arfin ka na d'an adam physically and mentally akan Zubaidah, ka keta mata hakkin ta ba tareda amincewar ta da yardar ta ba.... Kayi amfani da k'arfin da Allah Ya maka a matsayin ka na jinsin namiji, snn kayi taking advantage d'inta na kasamcewar ta d'iya mace wanda ko kusa a halittar ku k'arfin ku ya banban ta, ka keta mata haddi ka taketa da k'arfin gaske.... According to Nigerian Criminal Law you're sentenced to imprisonment for 19years...
"Still Labib Dasuki, ka musa tuhumar da Malama Zubaidah ke maka daga farko, ka k'aryata a gaban Alk'ali kasa k'afa ka gudu don kar a kama ka, k'arshe da gaskiya ta fito fili kayi confessing cewa ka aikata laifin.... According to Nigerian Criminal Law you're sentenced to imprisonment for 1year.....
"These are sentences for Labib Dasuki....
"Mamy kuka take tamkar ranta zai fita...
"Koda aka zo kan Salim ma irin hukuncin Labib aka yanke masa..... Tariq Maina kuwa anyi dismissing nasa daga Case d'in sabida ya riga ya rigaye mu gidan gaskiya....
"Alk'ali ya ambato JALAL...
"Runtse idanun sa Jalal kawai yayi yana sauraren nasa kalan hukuncin da za'a yanke masa..
"Zubaidah ma runtse idanun ta masu zuban hawaye tayi suna masu sauraren Alk'ali.. Sanda yaci gaba da fad'in"
"Jalal Aliyu Lamid'o " Kaine wanda ka soma confessing wann laifi a ranar 15 ga watar satumba a babban ofishin 'yan sanda dake Wuse..... Kayi statement ma 'yan sanda cewa ka aikata laifin, alhali baka aikata ba, shaidu masu k'arfi sun bayyan cewa baka aikata ba saidai ka fad'i hakan ne to rescue the Victim sabida yunk'urin halaka kanta da take yi...... According to Nigerian Criminal Law you're...... --------
"Ba ni Sameena kawai ba harta su Fatima su Mum Mus'ab, su Aysha cool su Sis Rally su Phertyzara , su Anmunah da muke zaune tare dasu ta can bayan kotu saida suka mik'e k'irjin su na lugude suna son jin hukuncin da Alk'ali zai yanke ma Jalal..... Kaman daga sama sai jiyo muryar Alk'ali suka yi yana fad'in"
"You're set to be free"......
"Masha Allah.... Zubaidah bud'e idanun ta da suke jik'e da hawaye tayi, ta saki wani murmushi mai sauti wanda ya isa dodon kunnen Jalal dake zaune wajen tamkar an dasa sa..... A hankali ya bud'e idanun sa siririyar hawaye ta sauk'o made, ya sauk'e su tsaf kan fuskar Zubaidah..... A hankali ya karanto hamdala yana mai mik'a godiyar sa ga Ubangiji....
"Fuskokin masu gaskiya suka cika da annuri yayinda na azzalumai suka cika da akasin hakan...
"Jalal ya k'arasa ya rungume Zubaidah dake zuban hawaye, very tied ya rungume ta shima hawayen ne ke bin k'uncin sa, a hankali yake furta " It's Over, it's all over Baby.... This is the end.... We will finally have peace....
"Alhamdulillah, Annah tace sanda take binsu da kallo hawayen farin ciki na zubo mata..
"Jalal ya sake Zubaidah ya k'arasa yayi hugging Annah, yayinda Hamma ya k'araso suka had'a idanu da Zubaidah, kana ganin sa kasan murmushin k'arfin hali kawai yake,.... Cikin sauri ta rungume d'an uwanta hawaye naci gaba da kwaranya masu..
"Hamma yaci gaba da fad'in" Alhamdulillah k'anwa ta, Allah Ya kawo mu k'arshen shari'a snn ya tabbatar da gaskiya da adalci a doron k'asa... Kar ki damu kowa ya sami abinda ya dace dashine... Allah sa masu irin halayyan su su gane...
"Kar ki damu dani kinji 'yar uwata wann shine abinda ya kamaci mai hali irin na Hadiza na tabbata yanzu idan ta fito daga gidan yari babu wanda zai kaita tsoron duniya...
"Zubaidah dai kasa ce masa komai tayi sai hawaye dake kwarara daga idanun ta, ta yaya ma bazata tausayawa wa d'an uwan ta ba, bayan tasan kalan soyayyar da yake wa matar sa, gashi zata tafi kurkuku har na tsawon shekara, inama tanada iko data fitar da Hadiza, Allah sarki saidai babu halin hakan, wann shine abinda Alk'ali ya yanke mata... Allah yasa hakan ya zamto sanadin shiriyar ta ameen..
********
"Mutane kuwa mak'il, dam haka suka cika bakin kotun...
"Aka zo za'a wuce da Umar.... "Ya d'an dubi police d'in kafin yace masa minti d'aya pls...
"Police ya gyad'a kansa kafin Umar Ya tako har gaban Zulaihat da Imam...
"A hankali ya soma fad'in" Nasan na zalunce ki, nayi amfani dake da soyayyar da kike min, nasan ban cancanci yafiyar ki ba, amma bazan gushe ba zan rok'eki yafiya koda bazaki yafe min ba... "Siriryan hawaye tana sauk'o masa yaci gaba da fad'in" Zulaihat ki yafe min, nasan bazan tab'a fita daga gidan Yari ba, I'll rot there forever.... Jikina na bani I don't have much time left.... I lost everything including my child dake cikin ki...
"Cike da mamaki Zulaihat take kallon sa tana mamaki yaya akayi yasan she's pregnant.. Kallon Imam tayi taga ya sadda kai k'asa, shakka babu tasan shi ya fad'a ma Umar...
"Hawaye suka ci gaba da bin k'uncin ta.... Yayinda Umar yaci gaba da fad'in" Ki sani no one shouldn't act crazy in the name of love.... All that I did nayi su ne out of love, ina son Zubaidah da duka zuciya na.... Thank you for everything Zulaihat, tabbas kinada zuciya mai kyau..... Ya d'an dubi Imam kafin yace " Imam pls don't leave her side, take care of her and my child, pls don't tell him my story, tell him a different story...... Nasan zaka iya, don Allah ka kula dasu kar ka rabu dasu, ko bana raye nasan Family na suna good hand... You both deserve each other....
"Hawaye ne kurum ke bin fuskar Imam babu zato yaji hawayen na bin k'uncin sa... Hannun Umar Ya rik'e cikin muryan kuka yake fad'in" You have my word.... Bazan tab'a rabuwa dasu ba da izinin Allah.....
"Daidai lokacin da d'an sanda ya janye sa yana fad'in "Move.... Criminal...
"Kuka ya b'arke sosai ma Zulaihat, Imam ma d'an juyar da fuskar sa yayi yana matsan k'walla......
"Su Mummy suna ji suna gani aka fito dasu Alh Kasim su Barr da kuma su Labib, dukannin su hanayen su rufe cikin handcuffs...
"Mutane sai ele suke masu suna masu gwalo suna fad'in" Sunji kunya... Haka Mummy da Mamy suka safare can wani wajen don basu isa fita gaban mutane ba, journalists sai sun titsiye su da tambayoyi....
"Ansar dake tsaye yana amsa ma d'inbin Journalists tambayoyin su yana ganin an fito dasu Alh Kasim yayi excusing kansa kafin ya k'arasa gaban Alh Kasim...
"Durk'usawa yayi gaban sa suna kallon juna ido cikin ido kafin Ansar yace " I told you so Alh Kasim.... I told you won't get away with all the crimes you had committed..... Now look at you your self .... You'll rot behind bars for the rest of your miserable days....
"You took away everything from me, you took away my family my happiness, you took away the woman that I loved.... I don't feel sorry for you , yanzu ne zakaji zafin rashi, yanzu ne zakaji zafin a rabaka da wani naka.... Seeing your only Son spending his days in jail sai yafi komai maka ciwo.... And too bad you can't do anything to save him...... Kai da shi da sauran muk'arabban naka zaku tabbata a gidan yari domin kuwa baku da ranar fita..... "Ya d'an murmusa hawaye na bin k'uncin sa kafin yace " Alhamdulillah ko yau na ajiye aikin lawyer Allah Ya cika min buri na..... I wish you rot in hell Kasim Dasuki.... Goodbye..
"Daga haka Ansar mik'ewa yayi yana share hawayen sa yana mai tuno mutanen da Alh Kasim yayi sanadiyan rabuwar sa dasu.... Hango Kausar yayi tana sakar masa murmushi tana girgiza masa kai alamun ya daina kuka...
"Samun kansa yayi da mayar mata da martanin murmushin had'i da gyad'a mata kai alamun toh...
"Journalists suka kuma masa chaa suna masu son ci gaba da interviewing nasa...
"Zubaidah tana fitowa 'yan mata da manyan mata sai tafi suke mata, kowacce tana mai son gaisawa da Zubaidah,... Dukda kakkare ta da securities da kuma Jalal da Annah keyi hakan bai hana mutane tururwan nufowa wajen ta ba.... Kowa so yake yayi masabaha da ita... Bakin ta Ya kasa rufuwa kai batasan tanada masoya haka ba..... Mutane k'ungiya daban daban kowa so yake su gaisa da Zubaidah kama daga 'yan k'ungiyar rajin kare hakkin bil adama musamman mata da k'anan yara zuwa irin su Queen samy novels 'yan ZBI 'yan Musha karatu, 'yan Duniyar Novel kaii jama'a dai da dama haka suka ringa tururwa Zubaidah kuwa sai gaisawa take dasu suna masu jinjina mata itada Jalal.....
"'Yan jarida suka tsare ta da tambayoyi, ba don Jalal yaso ba don ganinyake kaman zata kifa a wajen, sam babu k'arfi a jikin ta... Jaka dai ta d'an amsa masu kad'an daga ciki..... All she says shine, fatan ta ga mata 'yan uwanta masu irin labarin ta, shine that they should never give up, they should be strong and put Allah first... Ta k'ara da I was never be alone.... I hope they will never be alone.... Ta k'arashe suna masu kallon juna itada Jalal... Ya matse hannun ta sosai cikin nasa kafin suka soma tafiya, suka nufi motocin su.....
*Sameena Aleeyou Mrs*
🌒🌒🌒🌒 *ZUBAIDAH*
99
*©Sameena Aleeyou... ✍🏾*
*_Dedicated To All Victims Of Rape..._*
"Hamma da Hadiza sukai sallama da juna, su Zubaidah ma har zasu shige mota suka k'araso yanda suke, kowa sai ya tausaya ma Hadiza da Hamma idan ya gansu, zaka fahimci shak'uwa da soyayyan juna a idanun su... Shakka babu Hadiza ta shiga taitayin ta, ta kuma yarda ita dai duniya budurwa ce amma ta wawa...
"Ta kuma share hawayen da suka zubo mata kafin tace " Nasan Kamal na hannun na gari, Habibu ka yafe mun duk abinda na maka kaida k'anwar ka...
"Hamma ya share hawayen sa kafin yace " Hadiza mun yafe ki tun tuni snn shekara guda kaman kwana guda ne a wajen mai sama, Allah yasan hakan ya zama sanadin shiriyar ki, snn ki sani ni Habibu zan zauna na jira ki har wa'adin fito dake ya cika......
"Suka rungume juna suna hawaye...
"Gaba d'aya jikkunan su Annah yayi sanyi haka Hadiza ta ringa sallama dasu one by one.... Annah ta rik'e hannun ta gam tana hawaye take fad'in insha Allah Kamal yana hannun na gari, ki kwantar da hankalin ki, Allah Ya wuce mana gaba baki d'aya...
"Zubaidah kam lamo tayi cikin jikin Jalal don gaba d'aya babu k'arfi a jikinta, snn sosai take jin zafin abinda ya samu Hadiza duk sai ji take tamkar laifin nata ne, Hamman ta doesn't deserve to go through any of this... Amma hakan Allah Ya k'addara HE is the best planner... Allah yasa hakan shine silan shiriyar Hadiza da masu hali irin nata....
"Sunaji suna gani wata ganduroba ta janye Hadiza aka wuce da ita.....
"Mum d'in Tariq ce ta k'araso wajen tana mai goge ragowar hawayen ta da hankacif, cikin muryar kuka take duban Zubaidah tana fad'in" Zubaidah ki yafe wa d'ana Tariq snn muma ki yafe mana, da ace tun farko bamu bi son zuciya ba da bata kawo mu ga haka ba.. Ki yafe mana don Allah.... Jalal kaima ka yafe mu...
"Zubaidah ta rik'e hannayen ta tana hawaye kafin tace " Wllhi na jima da yafe ma Tariq, na sani he wasn't like them, and he was about to confess... Ba laifin sa bane denying d'in da yayi, da ace beyi hakan ba na tabbata da tuni kuma Alh Kasim ya halak'a ku, yin hakan da yayi yayi daidai... Snn insha Allah yanzu zai fi samun kwanciyar hankali, Allah Ya gafarta masa da sauran musulmi da suka rigamu gidan gaskiya.... Tana kaiwa aya Mum ta rungume ta sosai tana hawaye...
"Jalal ya d'an murmusa kafin yace " Mum ina mai k'ara maki ta'aziyan aboki na... Allah yakai haske makwancin sa ya gafarta masa laifukan sa...
"Mum ta murmusa kafin tace " Ameen Jalal, Allah Ya albarkace ku ya azirta ku da zuri'a d'ayyiba... Gaba d'aya har su Annah suka amsa da Ameen....
************
"Yau dai duk gidan Talabijin d'in da ka kunna labarin kenan... Finally yau an gama da shari'ar da mutane suke ta son jin k'arshen sa...Allah Ya kawo k'arshen shari'an.
"Zahidah da Kausar kuwa tunda suka had'u haba nan fah Abuja ya kuma yi ma Zahidah dad'i... Kwata kwata batasan Kausar dasu Jalal sun san juna ba... Hakan yayi mata dad'i sosai tunda yanzu an zama tamkar 'yan uwa..
"Zahidah ta dube ta kafin tace " Babe kice kema you're part of the story..
"Kausar ta murmusa kafin tace " Ai labarin ZUBAIDAH ya had'a da mutane da dama... Ko wanne da irin nasa k'alubalen da ya fuskan ta...
"Zahidah ta gyad'a kai kafin tace "Wann hakane 'yar uwa... Allah Ya amfanar damu da darussan dake ciki..
"Kaman daga sama suka jiyo muryar Zubaidah tana fad'in "Ameen..
"Gaba d'aya suka juyo suna kallon ta suna masu sakar ma juna murmushi..
"Kausar tace " Zuby nifah zan rubuta labarin ki idan kin min izini...
"Zahidah tace " Kaman kin shiga raina friend..
"Zubaidah ta zauna cikin d'aya daga cikin kujerun kafin ta d'anyi Far da idanu tace " Bayan duk wanda Samyn mu ta rubuta kuma...
"Suka murmusa gaba d'aya kafin suka ce kuma fah haka ne.. Our Samy wrote everything, ba naki kawai ba ma harma da namu...
"Suka dara gaba d'aya kafin Zubaidah tace " Wann haka ne... Ubangiji yasa rubutun ta Ya amfani Al'ummah..
"Muryan Jalal, Ansar da kuma Shattima suka jiyo suna amsawa da "Ameen"...
"Suka juyo suna kallon su gaba d'aya kowa na kallon masoyin sa...
"Kausar tace " Ah ashe dai an kasa mana kunne ne anata sauraren mu..
"Ansar yace " Gulmar ta isa haka maza ki tashi mu tafi is getting late already, Mumsy might be worried...
"Kausar ta d'an turo baki tace " Kai Big bro, fah ba gulma muke ba tad'in mu ne na mata...
"Shattima dake danna wayar sa yace " Ai tad'in matan kenan real name d'insa gulma, kuyi addu'a kafin ku tashi...
"Sukayi dariya gaba d'aya.... Basu ankara dasu Zubaidah da Jalal ba tuni ya sure ta sun shige d'aki yanai mata rad'i a kunne da " Baby someone's in need of you....
"Kaman ta k'walla ihu haka taji amma bata so taja hankalin mutane wajen su snn tasan bazai ajiyetan ba, yin shirun shine rufin asirin ta...
"Ansar ya wani sha mur cike da umarni yake magana ma Kausar.... Haka ba don taso ba sukayi sallama da Zahidah da alk'awarin Zahidar zata je mata gobe kafin su wuce Gombe....
"Har waje Shattima da Zahidah sukai masu rakiya kafin suma suka jero suna hiran su ta masoya....
******
"Tunda aka shiga mota Kausar ta turo baki gaba ko yayi magana bata amsa sa...
"Murmushi yayi cikin ransa yana mai yaba komai nata na burge sa... Bai kuma ce mata komai ba har suka iso gida..
"Yana gama parking tasa hannu zata bud'e motar, yayi saurin sakata a lock...
"Cikin sassanyar muryar sa yace " Lil Sis are you mad at me..??
"Ba tareda ta kalle sa ba tace " Ba kaine ba, just k'arfe takwas ne fah, kuma this is our first time da muka had'u da Zahidah in person..... Kum....
"Karkatowa sosai yayi yana kallonta jin ta kasa ci gaba da maganar nata, ba komai ya hanata ba, illa k'warjinin da ya mata...
"Ansar ya fahimci hakan ya murmusa kafin yace " Toh I'm sorry, kinji lil Sis... Amma kinsan abinda yasa nayi hakan, ever since that tragedy happened Mumsy bata so muna kaiwa dare a waje... Idan kin tuna ko ni kad'ai na fita da dare tana damuwa balle harda ke.... Hakan ma bai dace bane Lil Sis amma dai kiyi hak'uri kinji I apologize..
"Murmushi ta d'an yi kafin yace " Kinyi hak'uri...
"Tana mai murmushi take gyad'a masa kai shima murmushin yayi kafin ya bud'e masu mota suka fito...
"Fitowarsu keda wuya security guda daga cikin masu tsaron gate ya k'araso yana gaidasu kafin yace " Ma'am dama wani aika aka kawo ya k'arasa parking lot yana yaye wata hamshak'iyar Lamborghini da aka rufeta da tampol..... Daga Kausar har Ansar kallo suka bisa dashi...
"Ansar yace " Wa ya kawo snn Hajiya ta sani..???
"Security ya girgiza kai kafin yace "Aikan daga Senator Ali Ali ne yace wai zai kira k'aramar Madam sabida aikan nata ne, snn Hajiya bata sani ba, don lokacin da aka kawo duk baku gida ni kuma ban sanar da ita ba...
"Ya k'arashe yana mai mik'a wani takarda da key ma Kausar kafin yace " Ma'am wai zakiyi signing a nan...
"Harara kawai Kausar take galla masa tama rasa me zata ce...
"Ansar kuwa sai huci yake fizge takardan yayi ya keta lokaci guda.... Kausar ta bisa da kallon mamaki bata tab'a ganin sa cikin yanyin ba...
"Wrathfully yake fad'in" You're very stupid, uba wa yace ka karb'a..... Kasan yanda zakayi ka fitar da wann motar daga gidan nan kaji na fad'a maka wllhi bazai kwana a gidan nan ba....
"Cike da tsoro security ke kallon Ansar, zaiyi magana yace " I'm done talking, get this whatever outta this house, if you don't want to get yourself fired.... Snn daga yau kar ka sake amsan wani abu nasa... ... Daga haka ya nufi cikin gidan yana huci..
"Kausar jiki a sanyaye ta bisa da kallo kafin tabi bayan sa....
"A k'ofar da zai sadaka da cikin gidan ta had'u dashi sai faman huci yake...
"Kaman wata munafuka haka ta k'araso wajen..... Cikin wani irin huci yake fad'in" Since when...?? Since when mutumin nan ke maki waya...??
"D'an jim tayi kafin tace " About a month...
"Ansar ya fuzar da iska kafin yace " Shine baki sanar dani ba, why why... Meyasa baki sanar dani ba...
"Ganin yanda ya hayayyak'ota yana mata masifa yasata saurin fad'in" And why must I tell you.... Sabida bana son shi banga dalilin da zaisa na sanar da kai ba...... Cikin sauri ta nufi cikin gida...
"A tamanin ya take mata baya.... Curus suka yi da Mumsy dake tsaye jikin window ta gama ganin komai....
"Ku k'araso ta fad'i tana mai k'arasawa cikin parlour...
"Kafin su soma mata bayani ta soma fad'in" Ansar kayi daidai da kace a maida masa motar sa.... And you Kausar ki sani Ansar is only trying to protect you ne, he's like a brother to you.... You shouldn't have disrespected him, ba hanaki zaurawa zamuyi ba amma dole musan su waye maneman ki ... Oya bashi hak'uri..
"D'an kallon juna sukai kafin ta basu hak'uri dukan su... Komai ya wuce... Mumsy tace tayi serving nasu dinner... Babu musu tayi yanda Mumsy ta sakata...
"Suna cin abinci yana satan kallon Kausar da har lokacin babu walwala a tattare da ita... Yayi murmushi a ransa kafin ya soma fad'in" Mumsy dama akwai d'an wani abin da nake so ki min...
"Mumsy tace " Me kenan d'ana..
"Ansar ya murmusa kafin yace " Mumsy dama aure nake so kije ki nema min since you're my only parent...
"Ai abincin da Kausar bata had'iye ba kenan, ta ajiye spoon tana duban sa cike da mamaki...
"Mumsy ta fad'ad'a murmushin ta kafin tace " Kai Son, naji dad'i sosai... In fact this is great news.... Ko ina ne kuwa nai maka alk'awarin zuwa koda yakai birnin sin ne....
"Ansar ya murmusa yace " Godiya nake Mumsy, you the best....... Basu ankara ba sai ganin Kausar sukayi ta mik'e zata bar table d'in...
"Ina zaki..? Mumsy ta tambaya...
"Baki a ture tace " Mumsy na k'oshi ne, I lost my appetite...
"Ansar yana d'an satan kallon ta yake murmushi kafin yace " Mumsy nasan matsalan ta, idan wancan Lamborghini d'in ne kar ki damu zan saya maki ko salary na na shekara ne zan tara na saya maki....
"Ni me zanyi da sport car motar maza kawai ni na k'oshi ne....
"Ansar ya ajiye spoon d'insa ya mik'e yana murmushi kafin yace " Lil Sis yaudai fushi kawai kike dani, kiyi hak'uri yau kam ma Apo zan tafi can zan kwana...
"Kukan da take matse wa ya soma zuba mata, ta juya da sauri ta rungume Mumsy tana fad'in" Mumsy kin gani wllhi yanzu Big bro bai damu damu ba, wai tafiya zai yi, tun kafin yayi auren ya soma barin mu, what if yayi aure... I'm sure matar rabamu zatayi dashi....
"Ansar sosai abin ya basa dariya, daga shi har Mumsy k'unshe dariyar su sukayi...
"K'arasowa yayi daf da ita kafin yace " Inace baki so nayi auren ne, toh ki kwantar da hankalin ki na fasa, duk abinda lil take so ayi shi za'ayi......
"Tura baki tayi ta wuce stirs da sauri.....
"Ya bita da kallo yana murmushi.... D'an juyowa yayi Ya dubi Mumsy gaba d'aya sai yaji kunyar ta Ya rufe sa...
"Mumsy ta k'arasa cikin parlour ta zauna.... Ansar ya tako a hankali Ya zauna a gaban ta saman carpet, yayi irin zaman rak'umi...
"Tattaro nutsuwar sa yayi gaba d'aya kafin ya soma fad'in " Mumsy thank you, thank you for everything...... Kin dawo min da soyayyar mahaifa da na rasa... Thank you for accepting me into your family... I know I owed you alot....
"Mumsy tana murmushi take kallon sa take giriza kai kafin tace " You don't owe me anything Son.... Ni yafi cancanta na mik'a gidiya ta ga Allah daya blessing d'ina with a Son like you Ansar ...... All I want shine na ganku kun sami abokan zama na gari... Both you and Kausar....
"Ansar ya d'an shafi k'eyar sa kafin yace " Thanks Mumsy...... Snann ya d'ora da.... Dama... Dama Mumsy there's something I want to ask of you.....
"Mumsy ta gyad'a kai kafin tace " Ina jinka Son go ahead...
"Idonsa naga Carpet yake fad'in" Mumsy if you may allow me... Ina son na nemi auren Kausar....
"Murmushin dake fuskar ta ya kasa gushewa, hawayen farin ciki suka ciko idanun ta....
"Jin tayi shiru yasa sa d'ago kai cike da tsoron amsar ta... Ya maida kansa k'asa k'irjinsa naci gaba da fad'uwa...
"Muryar Mumsy ya tsinkaro tana fad'in" Ansar da zanfi kowa farin cikin kasancewar hakan... But Son.... Kausar bazaura ce while on the other hand kai baka tab'a aure ba, shin kana ganin hakan yayi maka...
"Ansar cike da jin dad'i yake murmushi had'i da gode ma Allah kafin yace " Mumsy, I love her for who she' and I promise to take care of your Baby, cherish her and give her all the love that she deserves..... All I want is your blessings Mumsy.....
"Kausar dake lab'e saman Staircase... Wani farin ciki ne taji ya mamaye ta... Da gudu ta shige d'aki had'i da turo k'ofa, ta runtse idanun ta hawayen farin ciki na zubo mata....
"Sosai Mumsy ta sa masa Albarka had'i da masa fatan Alkhairi... kafin ta mik'e ta nufi d'akin Kausar don jin nata ra'ayin...
"Tun daga looks d'in da Mumsy ta gani tattare da Kausar tasan itama tana son Ansar, hakan yayi ma Mumsy dad'i.. Saidai tayi masu fatan kasancewa cikin farin ciki, ji take kaman tafi ko wata uwa sa'a....
"Mumsy da kanta ta shirya Kausar ta sauk'a downstairs wajen Ansar....
*************
"Bayan kwana biyu suka tattara suka koma Gombe... Har liyafa maiji da lafia aka had'a masu...
"A ranar kuma Baba Ciroma ya soma magana, tunda Ummi taji haka, jikinta ya sare, jin yau Baba Ciroma zai shigo fadah yasata sarewa gaba d'aya... Abu mafi mata sauk'i shine tayi confessing laifin ta...
"Cikin parlorn Abbah yayi tsit Ummi ake saurare...
"Sosai jikkunan su yayi sanyi.... Daskarewa kurum Jalal yayi yana sauraren Ummi, kai ba Jalal kawai ba gaba d'aya kasa gaskata abinda kunnuwar su ke jiye masu suke...
"Duk k'arfin hali irin na Abbah saida hawaye suka shiga gangara masa....
"Kuka Zahidah keyi kaman ranta zai fita...
"Cikin kuka ta k'araso gaban mahaifiyar ta tana jijjigata take fad'in" Ummi why, why Ummi..... Meyasa kika zama Monster, Ummi meyasa kika zama SANDIN K'UNCIN MU, why Ummi..... Ummi don Allah kice min abubuwan da kike fad'i ba gaskiya bane...
"Ummi ta rik'e Zahidah tana kuka sosai take fad'in" Daughter I was a monster, a betrayal.... I don't deserve any of you..... Amma ba yin kaina bane, shawarin Baba Ciroma ne da kuma sharrin shed'an snn wllhi tllhi babu hannu na a kisan Daada..... "Abu guda da nasan nayi shine salwantar da Lamid'o..
"Ku yafe min don Allah..... Modibbo ku yafe min, Abbah ku yafe min....
"Jijiyoyin jikin Jalal sukayi rud'u rud'u, hawaye masu zafi suka ci gaba da bin k'uncin sa....
"Ummi jiki a sanyaye ta matso kusa da Jalal yayi saurin matsawa baya...... Tana mai ci gaba da kuka take rok'on sa gafara...
"Kaman daga sama sai jiyo muryar Abbah tayi yana fad'in" Kilishi kin cuce ni, kin zalunce mu nida d'ana, kar kiyi gigin tab'a min d'a da wannan k'azantacciyar hannun naki..... "Keda Ciroma bansan me zan ce maku... Amma ku sani Allah yana nan kuma yafiku, da sannu zaku girbe abinda kuka shuka.... Ku sani Zakaran da Allah Ya nufa da cara ko ana muzuru ko ana shaho toh fah sai yayi.... Kun rabani da farin cikin rayuwata Suhaima.... Kilishi kin cika butulu.... Ki sani ni Aliyu na gama zaman aure dake.... Ki tattara ki koma masarautar ku..... Zan rubuta sak'o na tura, duk irin mugayen abubuwan da kika aikata..
"Ummi tasa hannu aka tana kuka.... Zubaidah da Annah ma sosai suke kuka..
"Annah ta rungumo Jalal tana fad'in" I'm here son, I'm here for you, let it out... Yi kukan ka... Ai Jalal kaman jira yake nan ya kwantar da kansa jikin Annah ya shiga kuka da duka zuciyar sa.... Tabbas an zalunce su... Zahidah ma k'arasawa tayi ga Zubaidah ta kwanta cikin jikinta tana kuka sosai...
"Jiki a sanyaye Khalifa ya shigo yana kuka sosai... K'arasawa yayi gaban Mai Martaba yayi irin zaman rak'umi, cikin tsananin kuka yake fad'in" Abbah, Baba Ciroma babu, he confessed everything before he died..... Abbah ya fad'i komai duk mugayen ayyukan da yayi kafin ya mutu, Abbah ka yafe wa mahaifi na ko zai sassaucin Ubangiji..... Khalifa ya kifa kansa yana kuka sosai....
"Tsit kake ji sai sautin kuka, ...
"Mai Martaba ya kifa kansa kurum hawaye na kwarara masa... Tabbas matar sa da d'an uwansa sun masa zalunci mafi muni a duniya...
"Shattima ne yayi k'arfin halin rik'o Khalifa ya fice dashi don yasan Abbah bazai iya koda kallon sa ba....
"Wann rana haka Fadah ta wuni babu walwala....
"Su Baba Waziri mahaifin Shattima da sauran masu sarautun gargajiya su suka tsaya akan komai har aka kai Baba Ciroma makwancin sa... Mai Martaba kam ranar haka ya wuni babu lafiya...
"Jalal ma bai gane yanda yake ba, for second Zubaidah bata bar side d'insa ba, dukda Zubaidan ma ba jin dad'in jikin ta take ba, but she needs to be very strong for her husband, he needs her now more than ever....
"Zahidah ma sosai abin yayi affecting nata, Annah ita ta tsaya sosai akan Zahidah, sosai take bata duk wani kulawa da d'a yake nema wajen iyaye...
"Zahidah ta rik'e hannun Annah kafin tace " Annah why my mother, why she??? I thought lokacin da aka sami Hamma Modibbo bak'in ciki ya k'are mana, but I was wrong Annah.... Why Annah..???
"Rungumeta Annah tayi kafin tace " Wannan shine rayuwar sweetheart, Allah yakan jarabce mu ta yanda bamuyi tsammani ba, the most important shine kar mu rasa imanin mu, Allah yafimu sanin meyasa Al'amra suke faruwa haka...
"Kiyi hak'uri sweetheart ki karb'i k'addaran ki hannu bibbiyu sai kiga Allah Ya sawwak'a maki... And if you need anything don't forget that I'll be right here okay.....
"Rungumeta Zahidah tayi tana matsan hawaye.....
"A haka Jalal ya shigo ya same su, cike da tausayawa yake kallon Zahidah... Ganin sa yasata mik'ewa da sauri... Da gudu ta tafi ta rungume sa tana kuka take fad'in " Brother...... "Sosai ya rungume ta yana fad'in" it's okay Sis we are here, we are all here for you kinji...
"Gyad'a masa kai tayi tana hawaye, Jalal ya kuma hugging d'inta tausayin ta na ratsa zuciyar sa.....
***********
"A haka har akayi kwana Uku, Ummi da Jakadiya b'ab'ewa sukayi, gashi Jakadiya ma an koreta daga masarautar.... Haka ta tagayyara a titi...
"Ummi kuwa sam masarautar Katagum suka k'i karb'an ta, dama Mai Martaba sarkin Katagum ne ya had'a auren....
"Haka ta koma gaban iyayen ta cikin k'unci... Gashi ba wani k'arfi bane dasu, ta saba rayuwa cikin daula da sarauta da jin dad'i... Abubuwa sun sauya ma Ummi, idan ka ganta sai ka tausaya mata... Dama mahaifin ta irin masu Almajiran zauren nan ne... Haka Ummi ta koma tuk'a tuwo tukunya lamba Arba'in... Duk d'an farin fatar ya tauye ta koma abin tausayi, ga tarin kunyar abunda ta aikata....
"Jalal da Zahidah sun tafi masarautar Zazzau sunyi kwanaki biyu, masarautar Mahaifiyar sa, sosai sukaji dad'in zuwan sa, dukda Kakan sa saekin Zazzau mai rasuwa baya nan, amma sosai 'yan uwan sa sukaji dad'in zuwan sa, tarban girma da karramawa akai masu.... Basu samu damar zuwa da Zubaidah ba sabida lalurar dake jikin ta... Inama zai bari tayi tafiya, bayan yanda yake ji da cikin jikin tan nan, wani rirtata yake kaman ya maidata ciki....
"Sosai ya dank'a amanarta hannun Annah...
"Kwana hud'u sukayi suka dawo Gombe... A hanya Zahidah ta kawo wani shawari wanda Jalal yaji dad'in hakan sosai wanda idan hakan ta kasance shi zaifi kowa farin ciki, sosai ya jinjina ma k'anwar tasa da wann dogon mazari da hange da tayi...
"Sanda suka proposing buk'atar su ma Annah da Mai Martaba sosai Annah taji kunya, Kai yaran nan basu kyauta mata ba, haka ta ringa fad'i cikin zuciyar ta.. Shi kuwa Abbah sosai yaji dad'in hakan.. Kaman yaran nasa sun shiga zuciyar sa don ya jima da k'yasa hakan lol....
"Abunku da manya kuma masu sarauta ba wani d'aukan lokaci za'ayi ba... Cikin lokuta k'ank'ani aka soma gudanar da komai, sanda Jalal yayi waya yake sanar da Ansar nan shima ya sanar dashi an saka auren su da Kausar sosai Jalal yaji dad'in hakan ya jero masu addu'o'i..
*Ranar Biki*
"Babban biki akayi a fadah abin sai wanda ya gani.. Su Unman Shattima ba'a sama ba'a k'asa, ji take kaman k'awarta Suhaima ce ta dawo masarautar... Fuskoki suka cika da annuri, Algaita da Tambura sun bugu a wann rana... Shi kansa Abbah abin saida ya tuno masa da Suhaimar sa... Wani dad'i yake ji cikin Zuciyar sa maras misaltuwa...
"Bayan biki da kad'an Annah ta nace saidai a dawo da Ummi tunda tayi nadama, snn wanda yayi sanadiyar mutuwar Suhaima shima tasa ta k'are... Ba don Abbah yaso ba saida rabin ransa Jalal ya saka baki snn ya amince...
"Annah da kanta ta tafi masarautar Katagum don yin bikon Ummi, wayyo zo kaga yanda ake bawa Annah tsaro... Ummi sosai tayi farin ciki, tabbas Jalal dasu Annah alkhairi ne a gare ta... Amma kam tanajin kunyar had'a idanu da Jalal musamman dataji shine musabbabin komawar ta...
"Annah ta rik'e Fadah kowa nata ne, Ummi kanta 'yar kallo ta zamto a masarautar.. Fadah tayi albarka tayi dad'i sai Allah son barka...
"Bayan wasu kwanaki Khalifa ya sami Shattima ya basa hak'urin duk wasu abubuwan da ya masa a baya snn ya k'arada, zai tafi wani k'asa k'arin karatu, tabbas kunyar abinda mahaifin sa yayi bazai barsa yaci gaba da zama a masarautar ba.... Shattima ka rik'e amanar Zahidah domin da kai tafi dacewa.. Allah yaso saduwar mu Bro... Rungume sa Shattima yayi cike da alhini... Haka sukayi sallama da Khaifah....
**********
*Prison*
Boris ya kalli Labib yana sosa hab'arsa yana wata kafiran murmushi kafin yace " What do we have here.... "Ina alk'awarin mu dakai cewa zaka fitar dani, baka fitar dani ba baka bani kud'i ba gashi ka dawo... Koda yake kun tsiyance gaba d'aya... And yanzu ni kuma zan amshi kud'i na... Boys get them... Ya fad'i yana duban muk'arraban sa.... "Salim na jada baya Labib ma na jada baya.... Basu ankara ba suka soma sauk'e masu na jaki, sauran 'yan prison sai tafi suke suna zuga su....
"Labib da yaji duka yayi duka yace " Ku dakata wllhi nabada kud'inku ma wancan mutumin ya cinye, ku tambaya kuji lawyer ne.... Ya k'arashe yana nuna Barr Munir...
"Ai kuwa nan suka yi kan Barr suka soma lakkad'a tamkar an turo su... Garin duka suka jefo sa daga saman bene....
"Kankace me sun gudu sun watse, k'ashin bayan Barr ya kareraye... Haka ya dinga ihu yana fad'in" I don't feel my legs, my don't feel my hands, what's happening to me.... Aka zo aka kwashe sa sai ihu yake... Babu hannu babu k'afafu sai kansa ne kurum mai motsawa.....
*Sameena Aleeyou Mrs*
🌒🌒🌒🌒 *ZUBAIDAH*
100
*🔚*
*©Sameena Aleeyou... ✍🏾*
_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_
*Gaisuwa a gareku Aysha Mrs Muhammad and Zeenert 😍🤝*
"Kwanci tashi babu wuya wajen mai sama, satuttuka sun shud'e hakan nan watanni sun shud'e, anyi bikin Ansar da Kasaur sannan Shattima da Zahidah....
"Rayuwa tayi das'i sai godiyan Allah... Da k'yar Madaki ta amince da dawowar Ummi, dukda haka bata wani sake da ita ba, komai Annah ce akan gaba, sosai Annah ta rik'e masarautar, wani sabon rayuwa mai dad'in gaske suka tsinci kawunan su ciki.
"Tsakanin Annah da Ummi an rasa waye yafi bawa Zubaidah da jaririn cikin ta kulawa.. Sosai suke kula da ita, harta Madaki ba'a barta a baya ba... Masha Allah Zubaidah ta zamto shalele, kowa burin sa ya kyautata mata, baga mijin ta ba baga siraka nan ta ba..
"Hamma da Kamal sosai ake basu kulawa, Hamma a kullum cikin lissafin kwanaki ko ince watannin da suka rage ma Hadiza yake... Allah sarki soyayya dai gamo ne na jini.....
*********
"Zaune take saman carpet cikin nata ya turo sosai, k'afafun ta sun d'an hahhau.... Nad'e hannayen rigar sulken sa yayi ya shiga matse mata k'afafun yanai mata sannu..
"A hankali ta bud'e idanun ta ta sauk'e su saman kyakkyawan fuskar sa...
"Murmushi ya sakar mata kafin yace " Sannu Baby wifey... Do you need anything....??
"D'an murmushi ta masa kafin tace " Of course my Hero...
"Da sauri ya mik'e yana tambayar ta me take so...
"Far da idanu tayi kafin tace " I love you, a hankali....
"Zama yayi gefen ta yana murmushi kafin yace " And I love you too Baby Wifey.... You and our unborn Champion or princess..... Murmushi ta sakar masa kafin ya had'e lips d'insu waje guda.....
**********
"Zaune take saman kujera a d'akin Goggo, gashesshiyar masara ne a hannun ta take kan faman ci, da alama ta shiga watar haihuwar ta.....
"Da sallama ya turo k'ofar d'akin ya shigo.... Murmushi ta sakar masa tanai masa sannu..
"Murmushin shima ya mata kafin ya zauna daga can gefe yanai mata sannu...
"Ledan hannun sa ya bud'e ya ciro d'an wani k'wali ya mik'a mata...
"Kallon sa tayi ta kalli kwalin kafin tace " What's this... Another gift... Hey it's not my birthday..
"Murmushi yayi baice komai ba... "
"Tana Bud'ewa taga kayan Baby ne unisex masu kyau da tsada... "Kallo take kan faman bin kayan dashi baki sake kafin tace " Hey this is way too expensive... Haba Imam...... "Shiiihhh yayi saurin katse ta kafin yace " It's not yours ai, na Baby ne... His first welcome gift....
"Murmushi tayi soyayyar Imam na dad'a shiga zuciyar ta... Kafin ta soma masa godiya yayi saurin mik'ewa ya ajiye mata sauran kayan ya fice wajen Goggo...
"Hawaye masu zafi suka shiga kwararo ma Zulaihat.... Murmushi tayi had'i da rungume kayan cikin jikin ta...
"Bayan kwana biyu labor ya tashi ma Zulaihat.... Goggo da Imam basu bar side d'inta ba har saida ta haifo d'anta k'ato namiji kyakkyawan gaske...
"Sanda Imam ya rungumi d'an cikin k'irjin sa a hankali ya furta "Welcome to the world Son had'i da sumbatar sa a goshi....
"Hawaye suka sauk'o mata... Kowa a asibitin mamakin yanda Imam ke son d'an sa da matar sa yake, duk a zaton su matar sa ne da d'an sa...
"Tana asibitin ta sami labarin harbin Umar da akayi sabida escape a prison da ya tashi yi... Sosai tayi kuka tana kallon jaririn ta... "Haka Imam yayita k'arfafa mata gwiwa yana rarrashin ta, amma kam kuka ya zama mata dole......
"Duk kulawan da ya kamata mai jego ta samu Imam da Goggo suna bata..... A haka har tayi wata guda da satittuka... Nan ne suka shirya suka nufi Yola gaba d'aya harda Goggo...
"Sun sha mamakin samun mahaifin Zulaihat cikin tsananin ciwo, haka ya ringa kuka yana bama Zulaihat hak'urin duk wani abinda ya mata a baya.. Anty ma haka tayita bata hak'uri suna neman yafiyar ta, don kuwa tabbas abubuwan da suka same su a rayuwa hakkin Zulaihat ne..
"Zulaihat ma ta basu labarin irin rayuwar da ta shiga tareda Umar, ta kuma nemi yafiyar mahaifin ta.. Anty ta karb'i jinjirin ta mai suna Muhammad tana gani... Sosai yaron ya shiga ransu.... Haka Dad da Anty sukayita godiya ma Goggo da Imam....
"Bayan tayi arba'in aka sha bikin su tareda Imam...Ba yanda Anty batayi ba a bar mata Muhammad sai ya kwana biyu a kawo sa... Dashike nono bai dami yaron sosai ba... Fir Imam yak'i ko kunya babu, wai zaiyi kewan d'an sa...
"Imam ya rik'e hannayen ta kafin yace " Alhamdulillah, yau burina ya cika, Allah Ya cika min burina, ya mallaka min matar da nake mafarkin kasancewa tareda ita....
"Ta d'an murmusa had'i da sunkuyar da kai idanunta suka kawo ruwa ... A hankali ta soma furta, Imam you don't deserve me, you deserve someone more than me.... You're Young and fresh blood, while on the other hand I... I'm... Saurin rungumo ta yayi kafin yace " Shiiish " Kar na sake jin wann maganar a bakin ki.... I don't care.... I love you for who you are.. Ni ke d'in nake so..... Murmushi suka sakar ma juna kafin ya jawo ta had'i da rufa masu bargo masu light off.....
*************
"Zubaidah ta haifi yarinyar ta k'atuwa kyakkyawa..... Ranar suna yarinya taci sunan Maman Jalal wato Suhaima.... Kai Masha Allah... Wann yarinya taga gata da soyayya wajen illahirin dangi baki d'aya... Kowa so yake ya burge uwar yarinya da jaririyar ta....
"Hawan daba mai ji da lafiya aka shirya a garin Gombe na murnan samun wann jaririya....
"Kai Masha Allah... Komai yayi sai Allah son barka...
"Jalal baya sama baya k'asa....
"Suna zazzaune a wargajejen bedroom d'in Zubaidah, Kausar Zahidah da kuma ita kanta Zubaidar sai tad'i ake irin ta k'awaye, Baby Suhaima kuwa tana can sashen Mai Martaba ana saka mata albarka.... Wata kuyanga d'aya ce ta shigo cike da rusunawa ta sanar dasu wata mata tana sallama.... " Zahidah tace maza ta tambayo sunan ta... Jim kad'an Kuyangar ta dawo ta rusuna kafin tace " Tace sunan ta Zulaihat...
"Zubaidah ta saki murmushi kafin tace " Bisimillah a shigo da ita....
"Kausar da Zubaidah ne suka santa.. Basuji mamakin ganin ta da Baby ba, saidai sun tausaya mata sanin Umar yana gidan Yari...
"Bayan sun gaggaisa ta nuna masu babyn ta sann tayi murna ma Zubaidah... Zubaidah ta mik'a hannu ta karb'i Muhammad tana kallon sa... Sosai take murmushi take kallon yaron had'i da yima addu'a da fatan zama d'a na gari... Zubaidah tayi introducing Zahidah ma Zulaihat , nan Zulaihat ma ta labarta masu abubuwan da suka faru da ita, ciki harda auren Imam da kuma mutuwar Umar.... Sosai suka tausaya mata suka kuma mata murnan auren Imam da tayi.....
************
"Mumsy ta saya ma Mummy da Mamy gida mai kyaun gaske har ma'aikata ta sama masu... Haka suka dinga mata godiya suna hawaye..... Nan kuma su Mummy suka sami labarin mutuwar Kasim Dasuki a gidan Yari... Allahu Akbar, shi kuwa Barr Kansa ne kawai ke aiki a jikin sa ko motsa jikin sa bai iya yi...
"Allah ka bamu jarabawan da zamu iya ci a rayuwa.....
"Wa'adin da aka d'ibar ma Hadiza sun cika, an fito da ita daga gidan Yari, Idan kaga Hadiza gaba prison ya canza ta, ta zama mutuniyar arziki, har karatun addini dana boko tayi a prison, sosai Hadiza ta nustu, tabbas gidan Yari, Alkhairi ne a gareta...
"Hamma da Kamal babu wanda yakaisu farin ciki, gida mai ji da lafia Jalal ya sai masu suka koma ciki cike da farin ciki
**************
*Some Years Later*
"Daddy pls let's go for a vacation..... Suhaima 'yar shekara takwas ta fad'i...
"Tura laptop d'in gaban sa yayi kafin ya jawota ya d'aura bisa laps d'insa yace "Angel where do you want us to go..??
"Suhaima ta d'anyi far da idanu ta d'aura d'an yatsan ta saman kumatun ta kafin tace " Let's see... Kaman tana tunani... Can kuma sai cewa tayi yesss.. " Daddy Malaysia pls, I wanna visit Ghenttin Island...
"Jalal ya murmusa kafin yace " Whatever Daddy's Angel want, Daddy will do it right away.... But you see Precious , Daddy is a very busy Man, I got alot of commitments to take care of.... Why not mu bari sai wani hutun...
"Suhaima ta d'an tab'e fuska tana son yin kuka, Jalal sai faman ririta ta yake yana rarrashin ta..... "Zubaidah dake sauk'owa daga stirs rik'e da yaro d'an shekara uku , wand yaci sunan mahaifin ta wato Ibrahim, suna kiran sa Khalil, sai faman mitan sakalta Suhaima da Jalal keyi take....
"Bud'e hannu yayi ma yaron kafin yace " Come here Champ..... Da gudu yaron ya tafi ya rungume sa Jalal ya d'aga sa sama yana fad'in" My Champ is really adding weight, I barely pick him up..... Sai wasa suke da yaran suna d'alewa kansa.....
"Murmushi tayi tana mai kallon su yanda suke cike da farin ciki..
"A hankali ta furta Alhamdulillah....
*Nima Sameena nace wann shine k'arshen labarin ZUBAIDAH..... ina rok'on Rabbi fad'akarwan dake cikin sa ya amfane mu dasu, kurakuran dake ciki ya gafarta mana... Ameen*
ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAJ!! ALHAMDULILLAH!!!
*Dukkan Yabo da godiya sun tabbata GA Ubangiji ALLAH wanda ya bani ikon rubuta littafin nan cikin kwanciyar hankali daga farko har zuwa k'arshe.*
*Ina mik'a godiya ta a gareku k'ungiya ta ta KAINUWA bisa jajircewan da kukayi da goyon bayan ku da shawarwarin ku a gareni har Allah yasa na kammala wannan littafi, Allah Ya saka maku da Alkhairi ya kuma k'ara d'aukaka da hazak'a.... Allah Ya barmu tare har a Aljannah..... Ameen😍*
*Queen Samy Novels Forum*
*Kainuwa Fans Groups 1to6*
*ZBI*
*Duniyar Novels*
*Aysha Sada Machika Novels*
*Fadila Talba Novels*
*Musha Karatu na Kausar luv*
*Novel da Zumunci #Maman Sadiq*
*My darling Sis Rally Garba*
*My darling Shawty*
*Na gode k'warai da goyon bayan ku a gareni... Sameena Aleeyou Aka Queen Samy ke maku fata na Alkhairi😍🤝*