Ya rada mata yana kara rumgume ta, sai ranar ya samu wuni da ita tun safe har dare domin babu wanda ya ziyarce su a ranar, wunin ranar duk a jikinsa ta wuni, be ya yarda ta zama nesa da shi yana mata haka ne saboda ta saba. Da sannu kuma abun ya fara bin jikinta within a week ya kai idan zata zauna sai dai a saman jikinsa ko kusa da shi, haka a gurin bachi sai ya rumgumeta ya mata kira'a sannan take bachi, 3 days after ya sake taba ta a nan ma ta masa kuka sai dai ba irin na wacan karon ba domin ta ji zafin ya ragu sama da na farkon da ta ji kamar zai cire mata rai, haka ya rika binta after 3 days yake taba ta saboda ya samu ta sake da shi.
The first gift da ya fara mata a gidan shine ya siya mata waya da sabon line ya saka mata number Bappa da Inna da ita na take da waya a yanzu tana gaisawa da su, ya saka mata number Nana da Ammy da duk wani wanda yake ganin ya dace tai hula da shi, sannan yai mata downloading games kala kala da littafan musulunci yana koya mata abubuwan da bata sani ba, a dole yake cilasta yin azkar da safe har ya soma zame mata jiki idan tai ta gama sai ta kwanta a cinyarsa tana sauraren karatunsa.
Sai da tai month a gidan ko ruwan tea bata taba dafawa ba komai yi mata ake, hadimai ke zuwa suna wanke komai su gyara gidan a saka turare, abinci kuma kullum daga masarauta ake kawo musu, two da cika wata daya Shattima ya dauke ta suka tafi Masarautar ta gaishe da Ammy da Mai Martaba, Nasiha sosai Ammy tai mata haka ma Mai Martaba, a nan Ammy ta sanar da ita cewar daga gobe ba za a sake aika musu da abinci daga nasarautar ba.
鈥淜e zaki rika yi da kanki, na san zaki ji wuya amman ki daure a haka har ki saba, karki taba yarda mai aiki ko hadimai su zama su ne za su rika dafa abincin mijinki, kuma karki yarda Mijinki ya rika cin abinci a waje sai idan ta kama dole babu yadda zaki yi, kuma ladabi da biyayya rike su, ki rike aure da kyau domin Annabi yace macen da ta tsare farjinta ta bautawa ubangijinta kuma ta bi mijinta to wannan matar ta ma shiga aljanna, ai kina son aljanna ko?鈥�
Ta daga kai tana jin nauyin Ammy sosai.
鈥淪annan ki rike kamshi, ki samu turare kaloli ki hade a guri daya ta yadda zai zama kamshi zai fito wani kala na dabam da ba kowa zai gane wani kalar turare kika saka ba, ki rika amfani da shi ya zama da shi mijinki zai gane ki, ko wane guri ya tafi idan ya ji kamshin turaren ke zaki fado masa a rai, turare yana da fa'ida sosai a gurin ma'aurata, ko da yaushe ki kasance a cikin tsafta da kamshi鈥�
鈥淭o Ammy鈥�
Ammy ta hada wasu turarunka ta bata tace tai amfanin da su, sai goma suka baro gidan a mota yake mata albishir din cewa jibi za su tafi su gaishe da su Bappa, tsabar murna bata san lokacin da ta rumgume shi ba.
Washe gari suka shiga katuwar super maket suka si ma Inna da Bappa siyayya kala kala, ita ya siya mata chocolate domin ta gaji da kazar da yake siyo mata kullum da dare bayan wanda ake kawowa a soye daga masarauta, a yanzu bata ma son jin warin nama duk ya fita ranta. Siyaya sukai mai yawa suka dawo da ita gida, hadiman da aka aje mata a gidan Shattima ya saka suka gyara komai suka saka a jaka, ita kuma ta shiga ciki tai wanka, ta fito ta shirya cikin wando da riga English wears, kayan su karbe ta sosai dan man leben da ta shafa ya kara mata kyau ta saka ma gashinta ribbom sai ta fito kamar wata balaraba.
鈥淲oooo wow look at my girl鈥�
Ta yi murmushi tana kallonsa ta cikin madubi har ya karaso kusa da ita ya rumgumeta ta baya yai kissing dinta.
鈥淜in yi kyau鈥�
鈥淣a gode鈥�
Ta fada tana dariya.
鈥淭wo days din nan jikinki da dan zafi鈥�
鈥淓h nima ina ji, amman bana jin zazzabin komai鈥�
鈥淵eah canjin yanayi ne?鈥�
鈥淪aboda ana sanyi yanzu?鈥�
鈥淣o saboda na yi ajiya a cikinki鈥�
Ta dan wara ido domin bata fahimta ba.
鈥淎jiya kuma? Mayu fa suke haka?鈥�
Yayi dariya ya sumbanci kumatunta tare da kai hannu ya shafa cikin.
鈥淚 mean you're I'm pregnant....鈥�
Ta ji wani shock da sauri ta juyo ta kalleshi.
鈥淏a da gaske ba? Miyasa ban yi amai ba ban yi ciwo ba ban yi komai ba鈥�
鈥淶aki yi soon, ai ko wane ciki da yadda yake zuwa鈥�
鈥淵a kai ka sani?鈥�
Ya kai goshinta kan nata yana goga mata hancinsa.
鈥淣i fa likita ne, ke ba ki ji canji a jikinki ba? Ba ki daina son wasu abubuwan da kike so ba? Tun da kika zo gidan nan kin yi period? Kuma ga girarki nan ta layin kasa yayi fari sosai ko dai haila ko ciki, ni kuma a san ciki ne hannunki da halshenkin ma sun nuna, kuma ke ai baki son cin abinci amman yanzu kina ci sosai鈥�
Ya fada mata cikin rada sannan ya mikar da ita tsaye ya duka ya bude cikin yai sumbance a cikin.
鈥淚dan kin gama ki sauko mu ci abinci鈥�
Ya fada mata sautin kunnenta sannan ya murza yatsun hannunta ya fice yana mata murmushi, juyawa tai ta kalli madubin dake bayanta ta bude cikin tana kallo ta madubi.
鈥淜enan yanzu dandan yana ciki?鈥�
Ta shafa cikin tana ta mamaki, sai kuma tai murmushi tana jin mugun dadi. Tana tsaye a gaban madubin tana kallon cikin har ya sake dawowa dakin, zuwa yai bayanta ya tsaya yana kallonta ta cikin madubin ya saka hannunsa yana zirya da shi a fuskarta.
鈥淢atata ta kusa zama uwa鈥�
Sai ra rufe ido tana dariya ta juyo ta saka kanta cikin kirjinsa.
鈥淚 can't wait...! To be a father again Allah yasa twins ne ko triple鈥�
Ta dago ta kalleshi.
鈥淜ai har uku? Akwai wuya ai鈥�
鈥淎i sauki Allah yake sakawa bawayinsa鈥�
Ya sumbance ta sannan ya kama hannunta suka fito, da kansa ya ja kujera ya zauna sannan ya zaunar da ita samansa ya shiga zuba abinci yana bata tana ci idan zata hade sai tai a hankali wai kar ta ji ma cikin ciwo.
Washe gari ta farka da wuri ta shiga kitchen tana kokarin kunna gas din da ya nuna mata yadda zata yi amfani da shi tun kwana uku da suka wuce, ta kunna lafiya lafiya gurin dora ruwan ya zama rigima wai tana jin tsoro saboda ya fada mata a wasa da gas zai iya illata mutum, tana haka ya shigo ya same ta sai ya karba ya dora ya sa ta fasa kwai ta kwada shi kuma ya hada komai ya karyarwa.
Da rana ma haka ya girka musu jalof yana nuna mata yadda zata yi, duk da ya san idan tai ba lallai ne yai dadi ba domin bata saba girki a gida ba sai dai yana da kyau ta fara koya tun a yanzu, da dare ma haka ya nuna mata yadda zata dafa indomie. Washe gari misalin 11 jirginsu ya daga zuwa Katsina, suna sauka Ra'ees ya iso ya dauke su, zuwa gidan Shattima dake cikin garin Katsina. A gidan suka huta sai yamma suka shiga Bandalo, zo ka ga kauna Inna kamar zata hade Fadime, sai mamakin yadda Fadime ta soma canjawa take cikin kankan lokaci, Fadime ma tana ta murna ganin an gyara gidansu kamar a birni. Bappa kam dukawa Shattima ne kawai be yi ba tsabar murna da farincikin ganinsu, duj yadda Fadime ta so ta kwana a gidan Shattima be barta wai saboda matsalar tsaro duk da kasancewar zuwan na su ma ba kowa ya san da shi ba. Da za su tafi ne yake shawartar Bappa cewar zai sama masa wani gidan a cikin garin Katsina ya koma domin a ganinsa zai fi samun tsaro a can fiye da nan.
Ba dan ya fada mata gobe zai kawo ta ta sake ganinsu ba da ba zata yarda ta be shi ba su kwana a Katsina ba, hakan kuma be hana ta yi masa kuka ba. Washe garin da za ta koma ta tashi da zazzabi mai tsanani, ko kanta bata iya dagawa sai da Shattima ya bata magani ta sha, bayan siyayyar da sukai musu ta Yola Shattima ya aika yaronsa aka siyo musu kayan abinci masu yawa ya aika direba tare da kayan aka kai musu sannan ya kara ya sanar musu ba zata samu zuwa ba saboda bata jindadi. Kwananta uku a Katsina tana jinya sai da ta fara samun sauki sannan Shattima ya saka ta mota da police aka kaita ta wuni ta kwana a can ta sake wuni ta kwana sannan tai musu bankwana tana ta kuka ta dawo Katsina, washe garin ranar suka bar Katsina zuwa Yola, kar ku so ganin yadda ta labe masa a jiki cikin girjin daman tana jin jikinta babu kwari tun rashin lafiyar da tai.
ZAINAB POV.
Yayi murmushi ya dauki karan dake gabansa ya saka a wuta.
鈥淢iye alakar addini da soyayya?鈥�
Kallonsa tai a zatonta idan ta fada masa haka zai janye kudinsa ne akanta, hakan yasa tun a lokacin da yai mata wacan maganar ta daina sakewa da shi.
鈥淵ana da alaka mai karfi, a iya abun da na sani addinina be yarda mace ta auri mijin da bashi da addinin musulunci ba, amman an yarda miji ya auri mace ko bata irin addininsa鈥�
鈥淜ina fada min wannan ne da gaske ko kuma kina neman nisanta kanki da ni ne?鈥�
鈥淢a zai saka mace ta nisanta kanta da kyakkyawan namiji irinka? Kana da kyau Wasim, kyau na halitta da na zuciya, duk da kasancewarka ba musulmi ba kana da tausayi kuma baka cutar da kowa, baka wasu halaye na banza, babu macen da za ka taya wa kaunarka ta ki karba, sai idan da wani dalilin kamar wanda na fada ko makamancinsa鈥�
Yayi murmushi a yanzu ya gamsu Zainab tana sonsa kenan ba kamar yadda zuciyarsa take raya masa ba.
鈥淢e zai hana mu aje addini a gafe?鈥�
鈥淏abu wannan damar a gareni domin rayuwata tana tafiya a tare da addnina ne, addinin musulunci addini ne mai sauki da kuma mai dadi, idan har na bar addinina to wuta ce zata zama makwancina ranar gobe kiyama鈥�
鈥淏an gane ba鈥�
鈥淩anar da za a tashe mu, ayi mana tambayoyi kan abun da muka aikata, kuma ayi mana hisabi daidai gwargwadon abun da muka aikata, daga nan wanda ya aikata zubuni za a yafe masa idan Allah ya ga dama, idan kuma tsakaninsa da bawa ne dan'uwansa kamar ni da kai, sai a cire wani abu daga aikinsa a biya wacan idan kuma ba shi da komai sai a ciro zunubin wacan a tafta masa, idan dan wuta ne zai dauwama a wutar idan kuma dan aljanna ne zai shiga aljanna bayan an gama kona shi, wanda yai aiki na gari kuma sai a saka shi aljanna daidai gwargwadon aikinsa gwargwadon matsayinsa a aljanna鈥�
Wani kallon mamaki yai mata.
鈥淲ai kina nufin bayan wannan rayuwar da muka yi zamu sake yin wata? Bayan mun mutu kenan鈥�
鈥淪osai kuwa, za a sake wata rayuwar da za a bi hakkin wanda aka zalunta, kuma azabtar da wadanda sukai zaluncin, tabbas bayan wannan rayuwar akwai wata rayuwa, wata rayuwa mai ban tsoro mai tsananin firgitarwa, musamman ga mutanen da ba su bi Allah ba鈥�
鈥淎mman miyasa abubuwa bauta suke da yawa ne?鈥�
鈥淎bun bauta daya ne Allah Subhanahu wata'ala, shi ne dauwamammen kuma rayayye, shi kadai ya cancanci bauta kuma shi kadai za a bautawa a rabauta, shaidan ne yake raya ma mutane cewar akwai wasu abunuwa da suka cancanci bauta bayan ubangijina, ban taba burge ka idan ina sallah ko alwala ba?鈥�
Ta tambaya tana kallonsa.
鈥淭un kamin ke akwai wanda nake ganin suna sallah da yawa, abun yana burge ni, amman ina ganin kamar akwai wahala ayin hakan鈥�
鈥淏abu wata wahala idan ka saba, kuma zaka samu natsuwa sosai a cikin ibadar鈥�
Kadan ta labarta masa daga ibadar sannan ta jadda masa.
鈥淚dan har kana son na kuma ka shirya zama da ni, dole na ka aje addininka ka bi nawa, bin addinina kuma yana nufin watsi da al'adunka ka zama mutum kamar ni, ka aje tsafinka da komai鈥�
Yayi murmushi.
鈥淜ina da tsada kenan?鈥�
Sai ta kai hannunta ta taba fuskarsa.
鈥淪osai鈥�
Yayi murmushi ya sake deban wasu karan ya saka a wuta, sai ta kwanta jikinta tana kallon wutar.
鈥淎ddinina be bani damar taba jikin namijin da ba muharramina ba鈥�
鈥淢inene haka?鈥�
Ta fada masa da gamsasshen bayani.
鈥淭o miyasa kike yi?鈥�
鈥淶an daina duk ranar da na samu wanda ya zama mijina halal malak鈥�
Yayi murmushi.
鈥淏arin addinina ba abu ne mai wahala ba, haka na al'adata domin ina jindadi idan nai shigar mutanen kirki masu saka tufafi irin naki, ina jin na cika cikanken mutum, ina jin natsuwa idan an saka tufafin da suka rufe min jiki gaba daya, sai dai barin tsafi ina jin kamar zan cutu鈥�
Ta dago da sauri ta kalleshi.
鈥淏a zaka cutu ba, ina tunanin saboda ni zaka yi, inda zamu je babu wanda zai mana sheri ko ya jefe mu da wani abu, zamu yi rayuwa ne cikin farinciki da kaunar juna, kuma saboda ni zaka yi ba kace kana son farincikina ba? Ba kace zaka zama min komai ba? Ashe ba so kake na jidadi ba?鈥�
Ya karasa hawaye na sauko mata tana kallonsa, shi ma kallonta yake yana jin kamar ba zai iya ba, barin tsafin da ya zame masa jiki? Ba dan kalubalen da zai fuskanta ba sai dan sabon da yai da shi. Kawar da fuska tai tana cigaba da hawayen.
鈥淎she ban cancanta ba, ashe ba da gaske kake ba, amman na sani wata rana zan samu wanda yake so na da gaske, wanda zan iya yin komai saboda farinciki鈥�
Ta mike tsaye sai shi ma ya mike tsaye ya riko hannunta.
鈥淏an taba yin karya ba, zuciyata bata raya min na fadi abun da ba shi ne ba, idan nace idan son ki to ina sonki ne da gaske Zainab har cikin raina...鈥�
Yayi shiru yana kallonta kamin ya cigaba.
鈥淚dan har hakan zai faranta miki rai, kuma zai sa na rabauta, zan aikata na miki alkawari sai kin samu farinciki saboda ni...鈥�
Murmushi da kuka ne ya zo mata a lokaci daya sai ta lumshe ido tana maida numfashi a hankali.
FALMATA POV.
鈥淜enan ke yanzu cigaba zaki yi da karatun?鈥�
鈥淓h ai sai da muka yi magana da shi yace ya yarda zan cigaba da karatuna bayan aure鈥�
鈥淕askiya haka yafi, ni ma yace idan na haihu zai saka ni a makaranta, a gida yake dan koya min su gaisuwa da kuma yadda zan iya karatun hausa, gashi har ina iya hada hausa na karanta鈥�
鈥淗akan yayi gaskiya, ai kin samu miji mai sonki da gaskiya Falmata, daman hausawa sun ce mai hakuri mawadaci鈥�
Falmata ta yi murmushi tana kallon kawarta Khadija.
鈥淜omai ya wuce, ni kaina ban tsammaci zan samu rayuwata a haka ba, Baba ma ya dawo kamar ba shi ba ko shekaranjiya sai da ya aiko Inna A'i ta kawo min daddawa da kayan yaji mai yawa, ita ma tana da kirki sosai, ko kanen na tana kula da su sosai kamar yayanta, dawo da su da Baba yai a hannunsa ba karamin dadi n ji ba Wallahi鈥�
鈥淎i yanzu kowa kirki zai miki Falmata, saboda anga kina auren mai arziki, da dai a dane za ki fi gane mai son ki da gaske da mai miki sheri, ita kanta Tumba da zata samu damar rabarki soyayya zata nuna miki鈥�
鈥淗aka ne, ko tana ina yanzu? Wannan matar ta cutar da ni sosai鈥�
鈥淲allahi ni a yadda na ji wai tana cikin garin nan gidan wani kawunta鈥�
鈥淒a gaske ashe bata koma kauye ba? 鈥�
Khadija ta mere baki.
鈥淗mm ina zata iya zaman kauye ta saba da birni, ba shiyasa tai yadda tai ta aure Babanku bayan mijinta ta mutu鈥�
鈥淪u ma ai yau da gobe gajiya za su yi鈥�
鈥淲allahi kuwa ai ni idan ban ga Tumba a titi tana bara ba, burina ba zai cika ba鈥�
Cewar Khadija tana mikewa tsaye ta dauki atamfar ankonta, sai Falmata ma ta mike tsaye da cikinta tana fadin.
鈥淣i dai idan akwai babbar ki siyo min鈥�
Khadija ta mata wani kallo.
鈥淚yyyyy yayi matar manya wato kin bar bangarenmu ko? To dole sai kin saka irin ta mu Malama鈥�
Falmata ta yi dariya.
鈥淭o ai ina son kalar atamfar ne, ko bayan bikin ne na rika sakawa鈥�
鈥淓h na ji dai, sai kin saka kalar ta mu, ko kuma na kawo kayan lefena duk mijinki ya siya min masu tsada sai mu zama daidai鈥�
Falmata ta yi dariya.
鈥淎i zai siya miki indai mijina ne ba shi da matsala, Amaryar ba kya laifi, zan miki order kaya na musamman gurin yar gidan Mai Fata, kayanta na da kyau sosai鈥�
鈥淵auwa kawata haka nake so dai, a gyara ni鈥�
Falmata ta kai mata duka.
鈥淜hadija ba ki da kunya鈥�
鈥淜e kina da kunya kika yi ciki ne? Ana ganinki ai an san me kenan鈥�
Dariya sukai dukansu sannan ta raka kawarta har gurin gate, sannan ta dawo ta kwashe plates din da suka ci abinci ta kai cikin ta gyara ko'ina na falon, sannan ta haye sama tai alwala tai sallah ta azahar tai addu'a tai ma mijinta sannan ta mike tsaye ta nade carpet din ta aje a muhallinsa, ta sauko downstairs ta shiga kitchen ta soma dora girki, sai biyar ta gama komai tuwon shinkafa tai miyar taushe sannan ta dauko komai ta kawo dinning da jera duk da ta san mijinta ba mutum ne mai son cin abinci a dinning ba, musamman da cikinta ya girma din nan ya fi son su zauna kasa su ci abinci a tare.
Bayan ta gama komai ta shiga tai wanka ta shirya cikin jar abaya ta saka hula ta zauna saman gadonta tana kallon tv, after like 30 minutes wayarta tai ringing sai ta mika hannunta ta dauka ganin number Sirleem yasa ta murmushi.
鈥淗ello鈥�
鈥淏abyn Baby?鈥�
鈥淣a'am ya aikin?鈥�
鈥淒a godiya i miss you鈥�
鈥淚 miss you too鈥�
鈥淔ada min me zan siyo miki?鈥�
鈥淏ana son komai kuma karka mana takeaway na dafa tuwo鈥�
鈥淥h baby ke da kanki?鈥�
鈥淵es鈥�
鈥淜in saba alkawari鈥�
鈥淣a ji zan iya ne, kuma ai likita yace na rika motsa jiki鈥�
鈥淚 love you, kuma ina big surprise da zan miki ina tafe da shi?鈥�
鈥淢inene?鈥�
鈥淚dan na fada miki ai ta zama ba surprise ba, ina tafe da shi ke dai ki shirya kawai鈥�
Kamin tace komai ya yanke wayar yana murmushi, mamaki ne ya cika ta jin yace yana tafe da surprised na minene, tana ta tunani kala kala amman ta kasa cankar ko minene, tana zaune a dakin har ta ji karar bude gate, wanda hakan yai daidai da kiransa a wayarta.
鈥淏an yarda ki leko ni ba, kuma ban yarda ki fito ba鈥�
Shine abun da ya fada mata a wayar sai gai shiru tana sauraren wayar da be yanke ba har ya fita motar ya rufe, sannan ya nufo falo manne da wayar a kunnesa ya bude ya shigo sannan ya ce.
鈥淶a ki iya fitowa yanzu鈥�
Aje wayar tai ta sauko saman gadon tana jin gabanta na faduwa for no reason, tafiya ta fara yi kadan kadan kamar wanda bata son fita daga dakin, kamin ta kai hannunta ta bude kofar dakin ma wani aiki ne, a hankali ta bude kofar dakin ta fito ta janyo kofar ta rufe ta fara saukowa a hankali, da Sirleem ta fara arba ya sauko mata da sakon murmushi, sai ta mayar masa kamin idonta ya sauka gurin Ameer da ya mike tsaye daga zaunen da yake yana kallonta, idonsa cike da hawaye tsayawa tai cak tana kallonsa hawaye na sauko mata, sai kuma ta sauko da gudunta har sai da Sirleem ya tsorota ganin cikin dake jikinta, sanin zata iya rumgumar Ameer ko kuma shi ya rumgume ta yasa Sirleem yai saurin riketa ya rumgume sai ta fashe da kuka.
_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number聽 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
03/12/2021, 18:59 - 馃馃馃馃: *Khadeeja Candy*
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
Kuka tai sosai kamin ta samu natsuwa, sannan Sirleem ya rikata suka zauna saman kujera daya, Ameer kuma yana zaune a dayar kujerar yana kallonta idonsa cike da kwalla.
鈥淢omy ta fada min komai, na fahimci komai a kuraren lokaci...鈥�
Ya fada hawaye na sauko masa, Falmata kan kuka take tana kallon dan'uwanta tana jin wani irin shaukin kaunarsa na ratsata, bayan kanen da take da su yanzu ma tana da wani yaya. Sirleem ya sake ta ya nufi kitchen ya dauko musu ruwa da cup ta zuba ma Ameer ita kuma ya dauka ya bata da kansa ta sha.
After ya sha ya aje cup din yana murmushin takaici.
鈥淚 wonder how ban gane cewar ke jina ce ba, na tafi na bar gida ina da dan wayo na, amman sai komai ya soma shafe min a kai, and the most painful thing鈥�
鈥淎n shafe maka komai ne saboda barin gidan da kai ba a banza ba ne, na san kana som Mama a yadda ka lake sai ka dawo kusa da ita kadai ya isa ya sanar da kowa ba da son ranka ya bar gidan ba, amman na san shirrin na Umma ne鈥�
Ya daga kai.
鈥淗aka ne ni kaina ina ji a jikina kamar ba a banza ba, saboda na saka zuwa neman mahaifiyata, bayan kuma tana cikin rai a kullum, na yi sa'a a lokacin da na bar gida, na yi nisan zango ban san inda zan je ba kawai dai na ji ina bukatar nisa da gidan ne, Allah yasa na hadu da abokin Daddy shi ya dauke ni ya kai ni gida gurin Daddy, tun daga lokacin sai na fara fuskantar wata wahalar daga gurin Inna Kulu (Uwargidan Daddy) a kullum ina mafarkin Mama ina ji kamar zata nemi inda nake amman shiru, na sha wahala kamin Allah ya budewa Daddy ya zama babban mutum kamar haka, sai kuma na kara samun wata sa'ar na aurin Momy da yai mace mai hakuri da sanin ya kamata, ganin irin wahalar da nake sha a can yasa Daddy ya maida mi hannun Momy saboda bata da yara kuma tana nuna tausayi da kulawa a gareni sosai, Matar nan ta rike ni kamar ita ta haife ni, ban san zafin rashin uwa ba saboda ita, sai dai hakan ina fatar wata rana zan ga mahaifiyata, ashe lokaci ya kure min鈥�
Ya fashe da kuka.
鈥淒a Mama tana raye, ta ga yadda ka zama da ta yi farinciki鈥�
Sirleem ya rumgume matarsa dake ta kuka yana lallashinta.
鈥淵adda Allah ya tsara abu haka yake kasancewa, kin ga da Allah ya so sai yayi ki a gidan masu hali inda ko ciwon kai kika yi sai an shiga damuwa, Allah yana da iko da power da zai iya haka amman be yi ba, sai ki fahimci akwai hikima a cikin lamarin, ku yarda da kaddara ku gode Allah da yai muku tsawon rai har kuka gane junanku鈥�
Sirleem ya fada sai Ameer ya girgiza kai yana murmushin da yafi kuka ciwo.
鈥淗aka ne, ni kaina na san Allah ne ya tsara min haka, sai kuma ya kawo min Momy kalar yadda ya kawo miki dauki a yanzu bayan abubuwa da yawa sun faru鈥�
Ita ma kan ta daga masa tana cigaba da kuka da yaki ya tsaya mata. Sai da Sirleem ya tabbatar ta daina kukan sannan ya tashi ya basu guri sun yu maganganu da yawa masu taba zuciya da tuna baya, Falmata tana fadar yadda Mama take yawan maganarsa. A gidan ya ci abincin tare da Sirleem da Falmata abincin da kanwasar Falmata ta girka, duk da kasancewar baya cikin walwala saboda abun da ya faru sai dai kana ganin fuskarsa kasan yana cike da son yar'uwarsa ko'ina tai binta yake da kallo irin na kauna da mamakin yadda ta zama jininsa lokaci daya, sai a yanzu yake ganin yanayinta yana yin kama da na Mamarsa.
***
Rayuwa da ciki a gurin mace ba abu ne mai sauki ba, musamman cikin fari kuma ga mai kananan shekaru kamar Falmata, sai dai kasancewar mai juriya da hakuri ya bata damar iya daukar nauyin cikinta cikin ma Sirleem yana hana ta yin abubuwa da dama gudun kar ta wahala, domin har ya fita kula da rawar kafa dan abu kadan zai yace zata gajiyar masa da baby ko tana son ta ja masa babynsa ya wahala. Sai da tai da gaske sannan ya barta ta tafi bikin kawarta Khadija domin ko fita baya son tana yi wai ciki ya tsofa tana ta wahalar da abun ke cikin, idan ya fita komai ya gani sai ya siyo mata idan kuma yana gida kullum tana jikinsa shi kuma hannunsa ko kansa na kan cikinta, har mamakin yadda yake ta zumudin cikin take wata kila. Saboda be taba yi ba ko kuma saboda an kawo gunsa ne, domin wani rawar kafar dai bata taba gani ko jin irinsa ba sai da aka kawo gunsa, haka dai akai ta fama Allah ya kai ta shiga watan haihuwarta, a nan ta gane ashe abun ba sauki sai ga wanda Allah ya kawo wa, asibiti ta haihu tana dakin haihuwa tana nakuda Sirleem ya waje cikinsa na murdawa kamar shi zai haihuwa daman tun kamin nakuda ta kama ta ya fara nashi zazzabin da ciwon kai.
聽 Sai yamma ta haihuwa cikin nasarar Allah, take Sirleem ya fadi yai ma Allah sujuda yai godiya. Kamin dare hotunan baby sun cika Media kasancewar mijinta sanannen mutum ne.
FADIME POV.
Zuwa tai ta tsaya gabansa ta mika masa hannu.
鈥淢iko min kofin can鈥�
Ya dauke kai daga laptop din dake gabansa ya kalleta.
鈥淪hi kofin?鈥�
Ta turo baki gaba.
鈥淓h鈥�
Sai yai murmushi ya kai hannu ya dauka ya mika mata, haka take masa ita ala dole tana da ciki ba zata duka ba, musamman idan ta san yana cikin gidan ko wanka za tai sai dai ta rage tsawo a hankali har ta kai kasa saboda cikinta kamar wata mai tsohon ciki, babu ranar da bata bude cikin tai ta kallo tana shafawa, har tana cewa wai bata ji motsinsa ba wai ko ba shi da lafiya ne ko kuma dan tana yawan cin abinci mai yawa ne, hakan yasa ta rage cin abinci mai nauyi kuma da yawa wai kar ta cutar da ciki, wani abun idan tana yi Shattima sai yai ta dariyarta yana mamakin yadda take wauta sosai. Ya fada ciki sai ya kai wata hudu yake fara motsi amman bata yarda ba, kullum sai ta masa complain.
Haka akai ta shan rainon cikin kamar akanta aka fara ciki a duniya ko numfashi ba ta yi da karfi, sai dai duk abun da take tana yi idan tana ita kadai ko kuma ita da Shattima, bata yi a gaban mutane musamman idan suka leka masarauta hakan yasa Shattima ya gane shagwabar har da shi ake yi ma. Daman kuma shi dan nema ne domin shi ya fara nuna mata tun farko ita kuma sai ta samu guri, haka zata tashe shi cikin dare ta ce zata ci abu, idan be nemo mata ba sai kuka kamar karamar yarinya, wani lokacin lallabata yake da sunan zai nemo mata sai ya samu tai shiru har bachi ya dauke ta, wani lokacin kuma fitowa yake da sunan zai fita ya nemo mata sai ya dawo falo ko dakinsa ya zauna sai ta yi bachi sannan ya koma ciki.
Ba ma kamar da cikin ya tsofa a lokacin ne yake son ta motsa jikin sai ta tsaya kai ta fata ta ce ba zata yi komai ba, sai fadar take cikin ya mata nauyi wani lokacin idan ta shiga bandaki fitsarin ma a tsaye take sakinsa, sai dai ta saka ruwa, domin idan ta duka zata ji kamar cikin zai fito mata ko kuma ta gagara tashi, hakan kuma baya hana ta fita cikin mutane da cikin saboda shegen son yawo, idan yace zai hana ta wata rigimar ce zai takalowa kansa. Yau ma ta kama weekend Shattima na gida amman hakan be hana ta shiryawa da sunan zuwa Walimar wata cousin dinsa da ake ba. Yana zaune falo ta sauko da shirinta karfin hali har su jaka. Shi dai kallonta kawai yake har ta sauko.
鈥淒a gaske zuwa zaki yi?鈥�
鈥淓h ni dai ina son zuwa鈥�
Ta fada tana dan turo baki gaba, so kawai take yace mata ba zata je ba ta fara masa kuka tana cewa ba zata ji abinci ba saboda ta san yadda yake shiga damuwa idan bata ci ba. Murmushi yai ya mike tsaye ya nufi dakinsa, be dade ba ya fito ya shiga dakinta ya sauko inda take tsaye tana jiransa ya cire gyalen dake jikinta ya mika mata Hijab.
鈥淜i saka wannan zaki fi rufe jikinki鈥�
鈥淣i nauyi yake min鈥�
鈥淒aure ki saka haka nan haba baby na dan Allah鈥�
Ba dan ta so ba ta saka Hijab din sannan ya aje gyalen akan kujera ya rika hannunta suka fita daga falon, ya riga isa gurin motar ya bude mata ta shiga ta zauna sannan ya zagaya mazauninsa yai ma motar key.
鈥淎llah ya taimake ni karki min raki gurin haihuwa鈥�
鈥淲allahi sai na yi haka kawai waya ce kai ciki waya ce? Mutum cikin mutum kuma zai fito a ciki mutum ace ba zai yi raki ba? Lallai fa鈥�
Yayi dariya.
鈥淜ina da gaskiya fa, mutum cikin mutum ko?鈥�
鈥淓h mana, kuma ni zan sake haihuwa ba ma daga wannan idan na haihu yar mace mai kyau鈥�
鈥淜amar ni?鈥�
Ta yi dariya.
鈥淜e da kika ce twins kike so? Ai mutum biyu ne zai fito a jikinki yarinya鈥�
鈥淣i dai da na ji wani abu ka kaini asibiti鈥�
鈥淎a asibiti? Ga asibiti a gida? Wa zai kula da ke kamar mijinki?鈥�
鈥淎i kai ta yaranka za kai鈥�
Ya kai hannu ya taba kumatunta.
鈥淜amin na ga yaran waye na fara gani?鈥�
Ta mika masa bakinta sai ya maso da nasa tai masa kiss.
鈥淣i ka fara gani鈥�
鈥淚 love you鈥�
Ya dora hannunsa a kan katon cikinta yana murmushi.
鈥淜in san dai kina saurin jin yunwa ko? Ki daina zama baki ci ba yunwa tana damunki鈥�
鈥淭o zo ka bude min鈥�
Ya fita daga side dinsa ya zagaya dayan side din ya bude mata ta fito sannan ya rufe ya fita da kallo har ta shige cikin falon shi kuma ya shigo motarsa ya dawo gida, bayan yayi sallah azahar ya kwanta be farka ba sai 4 shi ma alarm din wayarsa ne ya vmuslim app ya farkar da shi,聽 bathroom ya shiga yai alwala ya fito ya sauko yana hamma ga mamakinsa sai ya ganta zaune saman kujera tana kallon plasma dake falon.
鈥淗ajiya yaushe kika dawo?鈥�
Juyowa tai ta kalleshi da idanuwanta da suka mata ja tsabar kuka.
鈥淭un dazun, kaje kana ta bachi wai ni kuma ina ta daukar nauyi, kai ba ruwanka tun da ba a jikinka ne ba鈥�
Zaunawa yai kusa da ita, ya san kullum abun kuka take nema, but abun mamakin kar dai ace dan yana bachi take kuka, ya hana ta bachin ne ita?
鈥淪hi ne kike kuka?鈥�
鈥淓h mana, kuma mutane sai cewa suke a a ashe ciki ya tsufa mai ciki mai ciki suna ta ce min haka....鈥�
Ta kara fashewa da kuka domin a yanzu babu abun da ta tsana kamar ace mata mai ciki, daman tana ta daurewa a can amman a gida dole ne tai kuka saboda abun ya mata ciwo, gashi kuma tana zuwa ta tararda Shattima yana bachi abun shi. At first dariya ce ta zo masa sai yai saurin gintseta ya ja jikinsa ya rumgume.
鈥淣a san kina fama da abu, shiyasa na ce ki daina shiga mutane amman kin ki, da kina nan ai ni ma ba zan fara yi bachi ba, balle har su rika ce miki Mai ciki Mai ciki Mai ciki Mai ciki... 鈥�
Dagowa tai ta kalleshi.
鈥淐ewa kake yi kai ma?鈥�
鈥淎a ni ai ba zan fara ba, ina fadar yadda suke fada ne, Allah ya ba ni hakuri?鈥�
鈥淵a baka?鈥�
鈥淵a baki鈥�
Yayi saurin gyarawa yana maidata kirjinsa sai dariya yake amman yaki bari ta gani.
鈥淔ada min waya kawo ki?鈥�
鈥淒ireban gidan鈥�
鈥淵a kyauta, tashi ki yi sallah ni zan tafi masallaci鈥�
鈥淭o鈥�
Ta daga jikinsa shi kuma ya mike tsaye yana sumbantarta.
鈥淪e na dawo鈥�
Ta bishi da kallo tana jin haushinsa daman tun da cikin ya tsofa take ta jin haushin mutane, ko ido aka kura mata sai ya zama laifi, sai kuma takalar cikin take idan bata ji motsinsa ba sai ta hannu ta rika laguda tana takalarsa, idan kuma ya motsa mata da karfi sai tace ya taba mata hanji ta fara kuka tana cewa ciwo.
Haka dai Shattima yai ta fama har ta wuce kwanakin haihuwarta da kwana biyu sannan ta fara nakuda, a nan ta gane ashe wacan ciwon duk sharar fage tai yanzu ne na gaske yake tafe, idan marar ta murda mata sai ta ji kamar ba a duniya take ba, tun kamin ta shiga watan haihuwarta Shattima ya shirya mata komai na haihuwa a gida, har sai idan abun ya garara tukuna ya tafi da ita asibiti, sai dai baya barinta ita kadai idan zai fita hadimai za su zauna da ita saboda bukatu na yau da gobe da kuma gudun wata matsalar.
Ihu babu kalar wanda batai ba tun tana da kuzarin ihun har ta koma ta na ambaton Allah, tana fadin ba zata sake haihuwa ba.
鈥淏a zan sake haihuwa ba har abada, har abada ba zan sake haihuwa ba鈥�
Shattima ya zo kusa da ita ya kwanto yana shafa kanta
鈥淧ushhhhh鈥�
Sai ta buge masa kai.
鈥淏a zan yi ba, pushing din ba, ai duk kai ne kai yi kai ka ja min, wayyo uwata wayyo ubana, Wallahi ba zan sake haihuwa ba鈥�
Ya tsorata sosai a lokacin da ya ga ta daina unkurin yin nishin gudun kar ta kashe masa abun da ke cikin cikinta. Sai da yai da gaske sannan ta ni wani karfi ya zo mata daga gurin Allah yai nishi dai yunkuri sai ga kai ya fara fitowa, tanayin na biyu sai Shattima ya saka hannunsa ya janyo baby yana murmushi da hawaye a lokaci daya, ya saka alkamshi ya yanke cibiyar, ita ma a lokacin ne ta samu damar yin kuka mai hawaye domin a can da kukan kawai take ba hawaye, sai ta ji wani shauki yana ratsata babyn dake hannun Shattima sai kuka take tana jin kuka har cikin ranta, Shattima ya lullube ta da zane sannan ya sumbance ta ya kwantar mata da ita a jikinta.
鈥淚 love you so much鈥�
Ya fada yana kissing din Fadime, hawaye na sauko masa, ita ma hawayen take tana murmushin da bata san ta ina yake zuwa mata ba, saboda joyful na uwa.
鈥淲a ta biyo? Mace ce ko Namiji?鈥�
鈥淢ace鈥�
Ya fada yana shafa fuskarta, a tunaninta shikenan tun da ta haihu duk zancen da Shattima yake mata cewar yan biyu ne bata yarda ba a tunaninta yana mata wasa ne saboda ya san tana son yan biyu, sai da ta ji wata nakudar ta taso mata ta musamman, sannan Shattima ya fita ya bada Babyn wa mutanen da suke falo aka fara karba karba ana yabawa, shi kuma ya shiga wani sabon aikin, da taimakon Allah ta sake santalo danta yana kuka kamar yadda mace take. Za ku ga murna gurin Shattima kamar yanzu ne ya fara samun haihuwa.
Sai da ya gyara matarsa ya kwashe komai sannan ya shiga bandakin da ita ta gyara jikinsa ya fito ita kuma Jekadiya ta shiga yi mata nata aikin na kula da jikinta.
Da kansa ya buga ya fadawa Ammy da Inna cewar Fadime ta sauka, Inna sai ta ji kamar tai tsalle ta tafi, tana ta mamakin yadda akai Fadime tai iya karfin halin haihuwa domin ta san yarta da raki, gashi bata da halin zuwa domin Fadime kamar yar fari take a gurinta kuma kunya da al'adarsu ta fulani ba zata bari ta tafi ba, sai dai kenanta aka tura da wata yar uwar Bappa.
聽聽 Hankalinta be kwanta ba har sai da ta ji muryar yarta a waya tana labarta yadda akai ta haihu.
鈥淚nna da kaina na haihu Wallahi, amman akwai wuya ba zan sake ba, Inna haka kika ji kema鈥�
Inna ta yi murmushi idonta na cika da kwalla. Sai kuma Fadime ta fashe da kuka farinciki.
鈥淚nna na zama uwa... Nima na zama uwa....鈥�
Inna ta lumshe ido hawaye na sauko mata.
鈥淎llah ya baki ikon tarbiyantarwa, ya raya miki su yasa masu jinkanki ne鈥�
鈥淎min Inna, ke ma Allah ya saka miki da alheri dawainiyar da kika yi da ni da rashin da na yi miki Allah ya biyaki da aljanna鈥�
鈥淎meen鈥�
Shattima ya shafa fuskar matarsa yana jin kamar ya hadeye ta tsabar kaunarta da yake. Gurin ba da nono sai ido ya raina fata ashe a nan ma akwai wani zafin ba haka nan kurun ake bawa yaro nono ba, sai an yi da gaske sannan take shayar da yaran.
聽 Wani irin kula da tarairaiya ake bata kamar akanta kadai aka fara samun jika a masarautar, domin kwananta daya aka rabota da gidan Shattima aka dawo da ita masarautar, duk yadda Inna ta so ta ki zuwa bata samu hakan ba domin Ammy ta matsa mata kuma ta aika musu da komai na zuwa, ganin Ammy an wuce wannan karnin da ake cewa uwa tana kunya sosai da har zai hanata zuwa bikin yarta, bayan kuma babu abun da ya tafi so a wannan lokacin kamar gatan mahaifiyarta.
聽 Irin wulakancin da akai ma nera a ranar suna sai ka rantse da Allah daga sama ake jefo musu kudi, domin bidi'ar da kai a gurin sunan ba ayi irinta ba a gurin aurensu, namijin aka saka masa sunan Mai Martaba Abdallah, mace kuma ta ci sunan Inna Aisha, sai dai dukansu ana musu lakani da Ameer da Ameera.
ZAINAB POV.
bata dauka da gaske Wasim yake ba har sai da ya fada kuma suka amince masa cikin sauki, ganin cewar ba tafiya zai yi gaba daya ya bar garin ba, zai tafi a inda zai fi jindadin rayuwa ne fiye da nan, kuma ya karbi addinin da zai fi samun natsuwa da shi fiye da wacan na kakanni da iyaye.
聽 A lokacin da za su bar garin ita ta rika jin kewar garin da mutanen cikinsa, shi kan be ji komai ba domin ya saba yin nisa da garin dama kuma ya san ba wai tafiya ce ta har abada ba. Sai da be nuna musu zai aje tsafinsa ba wannan ya bar shi a zuciyarsa ne kuma a tsakaninsa da Zainab sanin cewar Familynsa za su iya kin yarda domin sun fi girmama tsafinsu fiye da addininsu.
聽 Garin Sokoto shine gari na farko da ya fadowa Zainab tun a lokacin da take tunanin garin da ya kamata ta zauna, bata san kowa a garin ba, amman hakan be hana ta zuwa ba, sai suka sauka a Hotel, iya kar kokari ta yi na ganin ta kare mutuncin addininta hakan yasa ta kama musu daki biyu ko wanne daban dabam. The following day after ta samu ma'aikatan hotel din tana tambayar ko akwai inda zata samu wata kungiya mai taimakawa musulmai haka a garin sokoto? Wasu suka fada mata hukumar zakka dawakafi sai dai yadda aka labarta mata Famwan da irin ayukansu sai ta ji hankalinta ya fi kwanaciya ta da ita, sai da tai magana da Wasim ta fada masa zata je ta dawo sannan ta karbi addiress din inda cibiyar kungiyar take, ta yi sa'a a lokacin shugabar na nan, da ta fadi dalilinta na zuwa sai sukai mata maraba suka karbeta hannu biyu suka gabatar mata da komai cikin har da yadda zata agabarta komai kamar yadda shari'a ta tanada, kana suka jinjina mata, sai dai ta nuna musu bata son kowa ya san abun kasancewar sananniya ce a media.
聽聽 Duk wani abu da ya kamata kungiyar ta yi mata, aka hada Wasim da manyan malamai da suka gabatar masa da komai na musulunci ya karbi kalmar shahada kuma suka karanta masa cewa ba a hada Allah da wani abu gurim bauta kamar tsafi ko kuma wani ubangijin na dabam. Shi kansa a lokacin sai da yaji wata rahama da natsuwa ta lullube shi da be taba jin irinta ba, natsuwar ruhi da jiki da kamala ta addinin musulunci.
聽 Ita da kanta ta bukaci mutanen da za a hada ta da su ta siya makanta gida a cikin garin albarka garin sokoto, sai suka hada ta da adalilan dillalai akai ta nuna mata gidaje har ta samu wanda ya kwanta mata a unguwar Clapperto road, ta siya gida mai kyau kusan 50million.
聽 Kungiyar ta dauki kudi mai kauri ta bata, da shi Zainab ta kara ta saka duk wani abu da zata bukata a gidan daidai karfinta, washe garin ranar aka daura musu aure a babban masallacin jumma'a na isa talatar mafara. Tun daga lokacin sai Zainab ta koma da zama a gurin daya daga cikin matan da suke fanwan din saboda kula da ita, sun yi mata duk wani hallaci da ya kamata, ciki har da alkawarin samawa Wasim sana'a kasancewar be yi karatu ba.
聽聽 After a month sa tarewarta ta koma Yola ta saida gidanta ta dauko motarta ta dawo sokoto ta bude shagon kasuwanci na siyarda tufafi da duk wani abu na sakawa kama daga na zama har na mata, katuwar plaza ce ta kama haya ta cika ta da komai na kawa, kuma ta cigaba da sana'arta ta daukar hoto da karbar tallar kamfanona har tai nasara kamfanin Glo suka bata ambassador.
聽 Sannu a hankali Wasim yake koyon komai na addinin, tun yana jin wuyar wasu abubuwan har ya soma sabawa, sunansa ma da ake kiran da shi Muhammad tun a lokacin da ya musulunta sai daga baya ya soma sabawa da shi, da fari idan an kirashi haka baya amsawa sai ya ji kamar ba shi aka kira ba. Sai dai yawan zama da yake a shagon Zainab da ke gawon Nama yasa ya soma sabawa da sunan da kuma mutanen dake kula da shagon, shi kuma yana a matsayin manager ta.
聽 Ba shi kadai rayuwarsa ta canja ba, har da Zainab domin a yanzu ta daina shigar banza da take da magana any how, ga sa'ido akan Wasim da take sosai saboda yadda yan mata suke kawo masa hari idan ya fita, kasancewarsa mai jini a jika gashi kyakkyawa kamar shi yai kansa fari kamar a zaga jini ya fito, sai wani kara fresh yake saboda yana samun hutu da jindadi a yanzu ga safiyayyen gurin bachi da abinci mai kyau ga sutura idan ya saka ya fito sai yai kamar wani balarabe.
聽 Shi kansa yana kishinta kuma yana tayata kare mutumcinta, musamman a yanzu da take kokarin zama uwa, wani abun har shi zai tuna mata cewar addinin musulunci ya hana, domin yana yawan sauraren wa'azi an every night sai ta tafi masallacin dake can kusa da gidan sidi mamman gurin karatu, yana koyar komai a hankali duk da kasancewar ba komai yake ganewa ba, musamman idam yace zai hada harufan arabi ya karanta sai ya ji abu ya masa nauyi but Alhamdulillah tun da yana fahimtar addinsa.
*AFTER FIVE YEARS...*
Hakika rayuwar dan'adam tana cike da kalubale na rayuwa kala kala, wala'alan kana cikin jindadi ne ko akasin haka, dole ne akwai daci akwai bakinciki a wata rana, sai dai idan an yi hakuri da sannu komai yake wucewa, kuma duk abun da yai farko dole ne cilas tai karshe, sai dai be zama lallai karshen yai dadi ba, kuma ba dole ne karshen ya kasance marar dadi ba. Waya tsammaci rayuwa zata kawo Zainab da Wasim a haka? Balle Falmata da Sirleem? Haka ma Shattima da Fadime? Ba su kadai ba har Aliyu da Ataa Muhseem da matarsa suna gurin, Mama Fulani ma tana cikin yan'uwanta.
聽 聽 Babu wanda yai tsammanin wata rana zata zo da sukansu za su hadu akan abu daya, ita kanta Zainab ta cire rai daga waiwayar rayuwar Shattima da Ammy, sai dai yadda suka samu labarinta suka kira a waya suka nuna mata nuna tare da ita har yanzu sai ya sa ta ji sanyi ta wani bangaren, shi kansa Wasim be tsammaci wata rana biki zai hada shi har ya ga Fadime da yaranta ba, ita ta ganshi da yayansa har biyu, kamar yadda bata tsammaci wata rana zata zauna a kujera kusa da kusa ba ita da Falmata. Dukamsu sun ci ado kamar ba a mutuwa, kallo daya za ka musu ka san suna cikin farinciki da kaunar junansu, gaba dayansu hankalinsu ya tafi gurin tafin da ake sakamakon fitowar amarya da ango cikin takun kasaita, Nana ce tana sanye da doguwar riga da farin mayafi dan karami kamar yadda rigar jikimta ma take fara sol. Sardauna kuma na sanye da tsadaddiyar shadda sky blue wanda ta karbe shi ta fito da kyaunsa, tsakanin shi da Nana sai ka rasa waya fi wani kyau da murmushi. Tafiya suke kamar wadanda basa son taka kasa, har suka isa gurin da aka tanadar musu suka zauna. Sannan kowa ya mike tsaye har su akai national anthem, kana Mai Martaba ya fara zaunawa Ammy na gefensa, gefenta kuma matar gobna ce, sai Governor da kansa a gefen matarsa, sai kuma manyan mutane da wakilansu.
聽 Mc ya mike tsaye yana ta gabatar da komai, ba ayi wata riya ba, sai dai bikin ya kayatar domin ayi gayyato masu nishadantar kala kala suka kayatar da bikin. Sai kusan 11 aka rufe taron da addu'a sannan kowa ya nufi gida wadanda aka tanadarwa masarauki kuma suka sauka a masaraukansu.
Washe garin ranar ya kama Sunday ranar za a kai Amarya Nana dakin angonta Sardauna, daman sun Friday aka daura auren Saturday akai Walimar dare bayan ayi sauran bukuwan da mata suke yi kuma bukukuwan al'ada.
聽 A hankali take saukowa da shirinta tana kallon mijinta dake dafe da waya a kunne yana dariya, kana gani kasan yana cikin nishadi.
鈥淒a wa kake waya?鈥�
Ta tambaya bayan ta zauna kusa da shi, a lokacin da ya gama wayar.
鈥淢ansura..鈥�
Dassss ta ji gabanta ya fadi.
鈥淢ansura fa ka ce?鈥�
鈥淵es鈥�
Ya fada try to kiss her neck sai ta ture shi.
鈥淢iye hadinka da ita?鈥�
鈥淓asy easy Mom Nu'ayn ta fa yi aure har ta haihuwa鈥�
鈥淵aushe?鈥�
鈥淎n dade tun a lokacin da na haihu ta ce ta fahimci da gaske ba zan aureta ba, maybe ta yi duk abun da zata yi ta kasa ne, yanzu haka tana garinsu ma鈥�
鈥淎mman kake waya da ita kasan matar wani ce? Amman ni nan har fada min kake ko malamai na baka yarda nai musu magana ba sai da babban dalili, ashe ba dadi鈥�
Yayi dariya yana rungumota.
鈥淓h kuma kika wasa sai na hana karatun gaba daya, dan ba zan yarda ana kalle min mata ba ana magana da ita ana jin zakin muryarta鈥�
鈥淎mman kai kake yi da matar wani?鈥�
鈥淲allahi ban taba kiranta ba ita take kirana, kuma zan daina dauka daga yau inshallahu鈥�
鈥淒a dai yafi maka鈥�
Ta fada a fusace tana jin wani bakin kishi na turniketa. Sai ya riketa yana dariya ya rumgume.
鈥淜in yi kyau, jiya kin ga yadda ake kallonki wai? Gaskiya idan za'ayi bikin su Kausar Hijabi za ki saka鈥�
Ta watsa masa harara.
鈥淎mman kai da akai bikin Rima da yan mata suna kallonka ai zuwa kai ka fada min wai yan mata sai kallonka suke鈥�
Ya saka dariya yana kara rike a kokarin da take na ta zame daga jikinsa.
鈥淭o ai ni namiji ne, hudu aka ce na yi, ke kuma kin auru鈥�
鈥淎u haka ma zaka ce? Shikenan bari Allah ya kai mu bikin kaga yadda zan yi ado, ai yanzu Aymana da Nu'ayn suna gurin Momy ba mi case ko gyale ba zan saka ba, kuma duk wanda ya tare ni tsayawa zan yi鈥�
鈥淎iko da da an yi bu**uba... Ni din za a tari matata a kwana lafiya a Yola?鈥�
Ta yi dariya tana Kwantowa jikinsa kamar yadda shi ma yake dariyar.
END....!
Ni kuma na yi murmushi na ce Alhamdulillah da Allah ya nuna min farkon da kuma karshen littafin Fulani lafiya, Allah ya yafe min kuraren da nai darasin dake ciki Allah ya ba mu ikon amfana da shi.
Na sadaukar da littafin nan ga mutane uku masu daraja.
Safiyya Dan Jumma (Ummul Falsak)
Asma'u Badamasi (My Asmee)
Salma Gidado (Salwees)
聽 Ina sonku ina kaunarku har cikina raina, Allah bar mu tare har aljanna, kada Allah ya ba shaidan damar shiga tsakaninmu.
Ba zan manta da ku ba, Mama Aisha Samaru uwata ta kaina uwata maganin kukana i love you. Mamana
Maman Hafiz, Mama Hajiya Zainab Kano, Aisha Maccido, Hadiza Mai Fata.聽 Rahama Kabir, Mrs J Moon (Mu ne yan uku lol).
Godiya ta musamman gare ku wadanda suka siya littafin nan, har muka kawo yanzu i love you irin sosai din nan idan babu ku babu ni.
Sai kuma idan mun sake tarayya da ku a littafi na gaba, idan mai komai mai kowa ya yarje mana mai suna BA茦AR WASI茦A. ina rokon yafiyar wanda na batawa rai cikin ganganci ko rashin sani, ayi hakuri a yafewa Candy dan'adam ajizi ne.
*** *** ***
*BA茦AR WASI茦A...!*
_Mai farin rubutu_
Ban ce tafiyar mai sauki ba ce.
Ban muku alkawarin zallar soyayya ba.
Ban ce babu farincikin ba.
Kunci, bakinciki da damuwa, sune abubuwan da suka taru suka tare farincikin AMINATU, kalubalen rayuwa bayan wata rayuwar, tabbas akwai kuka akwai damuwa da bakinciki.
聽
Labarin Tafida, Rafi'a, Laila Sudais da kuma Aminatu. Labarin BAKAR WASIKA, labari ne da zai tabo wani bangare na rayuwar mace, kuma wani bangare na rayuwar al'ummarta da iyayenta...
Ina fatar zaku karbe shi kamar sauran, duk na san ba lallai ne yai muku dadi ba domin ba soyayya ce zalla ba, kalubalen rayuwa ne da fadi tashin yar gudun hijira!
A ina zata kwana? Wa zai bata masauki? Taya za a fahimce ta har a nade mata damuwarta? Wa zata kaiwa kukanta iyeyenta ko al'ummarta? Ta ina mafarkinta ke tabbatuwa? Ashe bayan wuya akwai wata wuyar, bayan dadi ma akwai wata wuyar, bayan wuya kuma akwai dadi.
Tabbas akwai ciwo a rayuwar da baka san karshenta ba, akwai tsoro a mafarkin da ka gagara farkawa! Ta ina lamarin ya fara? Ina tsakiyarsa da聽 karshe? Yaushe damuwar zata wuce? yaushe bakincikin zai gushe? Sai yaushe hawayen zasu tsaya? Zuwa yaushe ne kuncin zai yanke?
Ashe a cikin rayuwa akwai wata rayuwa? A cikin rayuwar ma akwai mutuwa?
聽 聽聽 BAKAR WASIKA...
1ST JUANURY 2022
聽 In-Sha-Allah
BEST REGARDS 鉂も潳鉂�
Khadeeja Candy ce馃憣馃挒da