*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
__________________________
*_Naga idi🙆🏻, Galadima fa ba tsamin baki bane dashi, Ku fahimta😂, bashida (R) ne, amma gashinan nayi gyara, ina fatan yanzu zakuna fahimtarsa🤣._*
_______________________________
👉🏻1⃣1⃣
.........Ba manager kawaiba, hatta da sauran jama'ar dake gidan jaridar saida suka tsorata da tsawar Galadima, su Muftahu ma tsorone ya kamasu, sunsan irin wannan matsanancin fushin gareshi babbar matsala ce ga lafiyarsa.
Aikam sai gashi ya dafe kansa, saboda yay wani mugun sara masa, da sauri Harun yajawo kujera ya kamashi ya zaunar, har yanzu dafe yake da kan nasa.
Muftahu ya furzar da hucin, matsalar da suke gudun ta d'akko hanyar faruwa kenan. kallon manaja dake durk'ushe har yanzun yayi,
yace “tashi ka zauna”.
Mik'ewa manaja yayi jiki Na rawa yakoma saman kujera, Muftahu da Harun ma suka zazzauna.
Cikin tsare gida Harun yace, “manager ka nutsu, kabamu had'inkai wajan fad'ar gaskiya, inba hakaba wlhy zakayi nadama ne, ba kaiba hatta da ahalinka saisunyi nadamar kasancewarka acikinsu”.
Manaja yashare guntun kwallar dasuka taru masa a idanu, a nutse yafara fad'in “ai tunkan jaridar jiya tafita nake acikin nadama, nayi dana Sanin kasancewata ma'aikacin jaridar da aka ci zarafin d'an Wanda yay tushen kasan cewata a wannan matsayin danake, da ace remote d'in rayuwata a hannuna yake, dana tariyo bayana jiya bata shigo rayuwata ba, amma Na.....”
Muftahu ya katseshi cikin d'aga masa hannu “kaga manager, ba rayuwarka mukazo saniba, munason ka fad'a mana waye yasaka wannan aikin? nawa suka biyaka kamusu shi?”.
“wlhy tallahi yalla6ai basu biyani komaiba, kaga wacan jakar sune suka ajiye min ita, amma ko bud'eta banyiba. kuma babu wani ma'aikaci daya buga labarinan agidan jaridar nan da hannunsa. sune da Kansu adaren jiya sukayi komai, bayan sun had'emu waje guda da bindugu, kuma sunzo nannane dukansu fuska arufe, wlhy ko fuskar mutum d'aya bamu ganiba, yanzu haka sun kwashe muhimman documents dake ma'aikatar nan sun tafi dasu. kuma sunsan da zuwan yalla6ai gurinnan yau, Dan komai sunyishine a tsare kamar yanda mukaji suna hira a tsakaninsu” manaja ya fashe da kuka, sannan yacigaba da fad'in “saboda sunsan zakuzo nan yau, sunje gidana tun adaren jiya, sun kwashemin iyali da mahaifiyata, yanzu haka suna wajensu, sun tabbatar min inhar wani magana yafito abakina abakin ran matata da yarana hud'u da mahaifiyata sai k'anwata. wlhy ina cikin masifa, yau anan Na kwana, nakasa fita waje saboda banason jin 6atancin da jama'a suka gani a wannan safiyar akan yalla6ai. Wlhy Na rantse muku bansan komaiba”.
Tunda manaja yafara magana kowa yay tsit, Galadima bai d'agoba saida yaji manaja ya ambaci iyalansa Na wajen wad'anda suka aikata aika-aikar. Idonsa yakad'a yayi jazur, sosai manaja ya tsorata da idanun Galadima, haryana tunani a zuciyarsa anya Galadima shi kad'aine, bashida aljanu kuwa?.
Komai Galadima bai ceba, ya tashi dafe dakai yafice daga office d'in, ma'aikatan wajen sai zubewa suke suna kwasar gaisuwa, amma kallon kowa baiyiba yafice.
Dogaransa suna ganinsa suka mik'e da Sauri, Mota suka bud'e masa yashiga, suma su Muftahu suka fito da hanzari.
★.★.★.★.★.★.★.★.★.★.★.★
Tun daga fitar innaro sai gidan yay tsit, kowa ya kama gabansa zuwa d'akinsa, a can suka cigaba da gulmace-gulmacensu suda bak'insu.
Niko da Munubiya muka shiga raira sabon kuka, munubiya ta kamo hannuna ta rik'e anata.
“Munaya dan girman ALLAH kibarni Na kar6i hukuncin laifina, nice Na aikata bakeba, miyasa zaki cema iyayenmu kece? kibari nafad'a musu gaskiya please ”.
“A'a Munubiya, wannan laifin nawane, karki manta ta sanadina abinnan yafaru, da ace Fu'aad bai kaimu plaza d'innanba da hakan bata faruba wlhy, munubiya farincikina fansane agareki, har abada bazan iya juriyar ganinki cikin k'unciba, Dan Girman ALLAH koda da wasa kar wani agidannan yaji banice Na aikata abunnanba koda kuwa innarmu Ce, namiki alk'awarin zan jure duk wata fitina dazata taso, zankira Fu'aad yafito muyi aure, duk da naso ace rana d'aya aurenmu zai kasance, amma haka ALLAH ya k'addara mana”.
rungume juna mukayi muka kuma fashewa da kuka, cikin shashshekar kuka Munubiya ke fad'in “mi mukaima Wanda ya k'ulla mana wannan sharrin? mi muka tare masa agidan duniyarnan Munaya?”.
“ban saniba Munubiya, bansan waneneba? Amma nafi zargin gidan wannan jaridar, aganinsu sun sami babban labari, bara su buga suyi suna, Sun zaluncemu Munubiya, sun yad'a labarin abinda ba haka faruwarsa ta kasanceba, Galadima ko ta6aki baiyiba amma suka saka har yana kissing d'inki, wane irin zaluncine wannan? wlhy nima bai ta6a niba da mukayi karo a filin idi, amma ki duba hannunsa rik'e da nawa ajaridar, Munubiya banga laifin iyayenmu ba, kowanne mahaifa bazasu so ganin wannan mummunan abinba, kuma ko zamu kwana rantsuwa bakowa zai amince damu ba, INA tausayama innarmu, ada Yaya muka k'are ma a gidannan bare yanzu?, munubiya innarmu innarmu, banason innarmu tashiga mummunan hali akanmu, yazamuyi innarmu ta fahimcemu, koda ace kowa bai yarda damu ba inason innarmu fahimcemu munubiya.....”
“Na fahimceku 'ya'yana, tabbas nashiga tashin hankali da ganin hotonku a jarida, kuma a yanayin da kowace uwa ba zataso ganin 'ya'yanta a wanna halinba, kuma ace bazata shiga fiyeda yanayin Dana fad'aba, sai dai ni ba abinda naganine yasakani cikin rud'ani irin haka ba harna yanke jiki na fad'i, cin zarafin innaro ne.
'ya'yana nasan bazaku aikata koda makamancin hakanba, dan naji ajikina sharri akai muku.....”
Da gudu suka sakko a gadon sukazo suka fad'a jikin innarsu suka cigaba da raira kuka harda ita kanta innar, saida sukayi mai isarsu sannan sukayi shiru.
Duk suka nutsu suka mata bayanin komai, har Munaya ta d'akko wayar da Galadima ya barta da ita a filin idi ta nuna musu.
Nanna INA ta kuma fahimtar akwai 6oyayyen al'amarin abinda basu saniba akan lamarin, kuma tafi zargin k'ullin Anma Galadima ne kawai, 'ya'yanta k'addara Ce ta sakasu cikin sark'ak'iyar, itadai Addu'arta ALLAH ya fiddashi da 'ya'yanta baki d'aya, saitaji yabata matuk'ar tausayima.
Suna cikin haka saiga mama Rabi'a dasu Ayusher, nanma aka kuma zaman warware zance, mama Rabi'a da inna suka kuma fahimtar komai yanda yake.
Nasiha suka Shiga yima 'ya'yan Nasu mai ratsa jiki, sannan suka nuna musu illar biyema samari batareda wani dogon tunaniba, duk sai jikin su Munaya yayi sanyi, sun fahimci bin Fu'aad dasukayi plaza shine yazama babban kuskurensu.
Sun nemi gafarar iyayen nasu akan hakan dasuka aikata, daganan suka Shiga tattauna maganar Auren munaya da Abba yakafe akan nanda sati biyu.
Sun Yanke shawara akan akira Fu'aad, inhar da gaske yakeyi to saiya fito kawai.
Akan wannan shawarrar suka zauna gaba d'aya.
★★.★★.★★.★★.★★
Har suka Isa cikin masarautar Galadima baiko motsaba, yana tangad'i da layi yashige 6angarensa, daga Muftahu har Harun babu Wanda yayi yunk'urin binsa.
Tunda yaje yazube saman 3seater bai sake sanin inda kansa yakeba saboda matsanancin ciwon kai dake damunsa, da k'yar ya iya gabatar da sallar magrib da isha'i a lokaci d'aya, a saman abin sallar ya kwanta rigingine dafe da goshi, yana kwance shiba mai barciba shiba ido biyuba.
8:30pm dukkan mai ruwa da tsaki a meeting d'in ya hallara, hatta da sarki gaba d'aya, sai dai kuma babu Galadima babu dalilinsa har mama Fulani tafito.
(Babbar magana 😨) na fad'a a raina, saboda ganin tsantsar mulki da isa ajikin hamshak'iyar tsohuwa dazata iya kaiwa shekaru 77 a duniya, sai dai tsantsar hutu da gayu ya 6oye ziryan d'in tsufan nata, gata da k'aramin jiki kuma, daka ganta haka bafulatanar asali.
Tunda ta fito kowa a falon yamik'e tsaye saboda girmamawa a gareta, amma banda sarki, ya risinar da kansane kawai alamun girmamawa ga mahaifiyar tasa.
Saman kujera 2seater ta zauna cikeda izzar mulki, (saikace itace sarkin🤦🏻♀) sai da ta gamaima kowa dake falon kallon tsaf sannan takuma kamewa, cikeda k'asaita tace, “Shi yana ina? Ko raini. Hankalin nasane ya hanashi zuwa?”.
Kowa dake wajen yasan galadima take nufi, babu wanda ya iya cewa komai sai wani matashin saurayi dazasu iya zama sa'annin juna da galadima, ya gyara zamansa yana wani 6ata rai shima, “Granny kinsan halinsa aii, ba ganin kowa da gashi yakeba a masarautar nan mtsoww”.
Mama Fulani ta turo hanci ga bada, cikeda fushi ta bada umarnin a kira mata jakadiya.
babu dad'ewa saiga jakadiya tashigo, k'asa ta zube tamkar zatayi mata sujuda tafara fad'in “ALLAH yaja zamaninki ranki ya dad'e, kinga taki kinga tawasu, fatanmu kiga tawasun wasuma, Sarautar gagara badau a hannunki take, domin kaida kaya ai duk mallakar wuyane, duk mai shirin ganin barcinki ya tabbata shima bazaiyi nasaba, kece k'i gudu samaza gudu, jaruma mai dad'and'en tarihi, kin ajiye tarihin da babu wanda yake dashi a masarautar nan, koda kuwa mai martaba gagara badaune, ALLAH ya tsare gabanki ya tsare bayanki, mace mai kamar maza, mazanma a tafin k'afafunki suke ya uwar gijiyata”.
Sosai kirarin jakadiya yayima mama Fulani dad'i, takuma kishingid'a a kujerar, cikeda izza tace, “inason ganin Galadima yanzunan”.
Angama damusa k'i sabo, cika umarninki wajabtaccene a gareni 'Yar sarki, matar sairi kuma mamar sarki, wata ran kakar sarki, ki huta lafiya babbar giwa”.
Fita jakadiya tayi.
Ta isa 6angaren galadima, inda sarkin k'ofa yashiga domin yimata iso, halin daya isake shugaban nasa ya razanashi, amma haka yadake ya isar da sak'on jakadiya.
Da k'yar galadima yay masa nuni akan yabarta tashigo.
Babu dad'ewa saiga jakadiya, ta rusina cikin girmamawa ta gaisheshi, bata damu da rashin amsawar tashiba ta isar da sak'on mama Fulani. hannu kawai ya iya d'aga mata.
Kusan mintuna 7 da fitar jakadiya yamik'e dafe da kansa dayakejin tamkar zai fad'o k'asa, jiyay falon na juya masa, ya dafe bango da gyar kusan 2munute sannan yad'an lafa, haka yafito yana d'an tangad'i, wajen mota yanufa, dan bazai iya zuwa sashen mama Fulani da k'afaba, saboda akwai tazara sosai a tsakaninsu.
Da sauri sarkin mota yataso ya bud'e masa, shima shiga yayi mazaunin driver, sauran dogaranma suka shishshiga mota.
Da k'yar galadima yafurta “sashen mama Fulani zamuje, sauran su zauna”.
cikin girmamawa sarkin mota ya amsa, sannan ya sanarma sauran dogaran.
dukkan jama'ar dake falon idanu suka zuboma Galadima daya shigo dafe da kansa, baima kowa magana ba yasamu can gefe ya zauna, har yanzu hanunsa na saman kansa, muryarsa a shak'e yace, “barkanku da dare”.
Hakan yayi masifar k'ona ran mama Fulani, saboda ma ya rainata tare zai gaidata da kowa? kuma bazaizo gaban taba ma yabata girmanta?.
A falonma wasu sun amsa wasu basu amsa mishiba, shi baima San sunayiba, ta kansa kawai yakeyi.
Cikeda izza mama Fulani tace, “to isashe, gaisuwar ma saina rok'a ko yaya”.
Dukda halin dayake ciki bai hanashi sakin guntun murmushiba, ya janye hannunsa daga goshinsa, idanunsa dasuke matuk'ar jajur yad'ago ya kalleta, ba mama Fulani niba kowama a falon ya firgita daganin idanunsa, hakan ya tabbatar musu da bashida lfy kenan.
Ahankali Yakuma furta “bagykanki da hutawa”.
“ALLAH yarabamu da bak'in hali” . ‘mama Fulani tafad'a batareda ta amsa gaisuwar ba’.
Baice uffanba ya maida kansa ya duk'ar, tareda kuma tallafe goshin yana ta6e baki.
Idanun Ummu Hasheem yacika da kwalla saboda tausayin Galadima, ko kad'an batasan bashida lafiya ba, dukda d'azun ta aika bayinta su duba matashi suka tarar yafita.
Mama Fulani kam baki ta k'ya6e tareda kuma hard'ewa a kujera, takai dubanta ga wani dake gefenta, Matawalle! ahad'amin video call da Zeenah yanzunan”.
“angama ranki ya dad'e” Dan danan yahad'a video call bayan yakira wata number, wata kamilalliyar matace ta bayyana ajikin System d'in, tana sanye cikin shigar kamala, kallo d'aya namata Na hango kamannin Galadima tartare da ita, dukda kamar tafisa haske, hakkane ya tabbatar min da Momma ce.
Cikin girmamawa ta gaida mama Fulani, ita kuma ta amsa cikeda k'asaita sannan tafara magana kamar haka.
“nasan kowa yasan miya taramu anan wajen?, bana buk'atar maimaita wannan shed'ancin a harshena, wanda kuma ya aikata yasan kansa, Dan haka hukunci biyune, yanada za6i aciki. Na farko tozarcin da yayama masarautarnan da zubar mana mutunci mun haramta masa auren kowacce yarinya data fito daga kowacce masarauta, na biyu ya gaggauta fidda matar aure acikin shekararnan kafin yaje yayma wata ciki a waje akawo mana d'an tsakar gida a masarauta, kokuma mu muza6a masa acikin bayin gidannan, hukunci na farko babu sasauci acikinsa kuma babu canji, Na biyu yanada za6i nemowa komu nema masa. Wannan shine tabbataccen hukuncin kotun fulani. Idan akwai mai abun fad'a sainaji?”.
Kowa ya girgiza kai alamun a'a, wasu hukuncin bai musu dad'iba, wasuko yamusu fiye da zaton mai karatu.
A hankali Galadima ya yunk'ura yatashi batareda yacema kowa uffanba yanufi hanyar fita.
“to fand'ararre, daka tafi ba'a gama magana ba ai uwarka zataji, mara mutunci mai bak'in hali”.
Juyowa Galadima yayi ya kalli mama Fulani, wani k'asaitaccen murmushi ya sakar mata sannan yay salute nata yafice abinsa”.
Mafi yawansu saida suka zaro idanun mamakinsa, dama Kowa yasan galadima baya tsoron mama Fulani a masarautar, duk masifarta saima yagadama yake amsata, gaisheta kam saiya zo k'asar yatafi ma bata ganshiba. Iya kacinta tayi masifarta da sababi ta hak'ura, babu yanda ta iya dashi.
Murmushi kawai shima sarki yayi baice komaiba.
Mama Fulani kam kasa koda motsi tayi a kujerar saboda abin kunyar da galadima yayi mata gaban kowa, ta tsani shed'anin yaronnan mai ido a tsaitsaye dabaya shakkar kowa. Kwafa tayi sannan tatashi tabar falon tana tafiya cikeda mulki da izza.
Gaba d'aya suke fad'in ALLAH ya huci zuciyar sarauniyar sarakuna.
Duk abinda ke faruwa Momma naji kuma tana gani, amma dayake Galadima yana bayan laptop d'in bataga miyayiba, hasalima bataji ko sau d'aya yayi magana ba, hakanne ya tada hankalinta, mama Fulani Na barin wajen ta katse call d'in, waya ta d'auka takira number Galadima, amma harta tainke bai d'agaba.
Kira Na biyu ta sakeyi, hakan yay dai-dai da shigowar Galadima falon dafe da kansa.
Da k'yar ya iya d'aga wayar, muryarsa a shak'e yace, “Momma zan kigyaki anjima” bai jira cewarta ba ya yanke wayar.
Hankalin Momma yakuma tashi, tasan ransa yakai k'ololuwar 6aci, da sauri ta danna kiran Harun, yana d'agawa ko gaisuwar dayake mata bata amsaba tace, “Harun maza jeka duba min Moh'd yanzunan”.
Yanda yaji Momma Na magana shima kansa saiya kid'ime.....
★.★.★.★.★.★.★.★.★.★
Ayusher tafita tasiyo min credit domin kiran Fu'aad.
Jikina a sanyaye nagama loda katin, tunani nakeyi shin Fu'aad zai kar6eni bayan yaji abinda yafaru a jiya zuwa yau? tunda komai akan idonsa yafaru. Na dad'e ina juya wayar a hannu kafin Nayi dialing d'in Number d'insa d'in, harta tsinke bai d'agaba, ban damuba Na sake kiransa da tunanin ko baya kusa da wayarne.
Bugun farko kuwa ya d'aga wayar...........✍🏼
Humm masu karatu, mi kuke tunanin zai faru tsakanin Munaya da Fu'aad a waya, zai kar6eta kokuwa sa6anin haka?.
Yaya zata kasance ga Galadima kuma?.
Wannan amsar tana a page 12 da zaizo muku ranar Monday😃👌🏻.
Barkanku da juma'a.
Musha weekend lafiya🤝🏻🥰🥰.
Team *_INNARO & MAMA FULANI_*🥴🥴⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀.
*_ALLAH ka gafartama mahaifanmu._*😭👏🏻
*_Typing📲_*
*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
👉1⃣2⃣
.......Murya a sanyaye Munaya tace, “Assalamu alaika”.
“wa'alaikissalam”. ‘wata murya ta amsa sa6anin Fu'aad’.
“Uhhm 'yar uwa please, ko ina mai wayar dan ALLAH?”.
“Mai wayar kuma? ai nice mai wayar”.
Wani iri munaya taji a zuciyarta, suka kalli juna itada Munubiya dan a Hans free tasaka wayar. alama munubiya tamata akan tayi magana. kai Munaya ta jinjina mata, sannan tace, “ayya 'yar uwa sorry dan ALLAH, wlhy wanine yabani number d'innan mai suna Fu'aad”.
“Fu'aad!”. ‘yarinyar ta maimaita daga can’, saikuma tace “to gaskiya 'yar uwa yabaki wrong Number, ni sunana Afnan, ina Katsina state ne”.
Wasu hawaye masu zafi suka zubo a kumatun Munaya, “shikenan ngd sis..., kiyi hak'uri”.
“no babu damuwa”.
Bayan Munaya ta katse wayar ta dafe kai tana hawaye, daga Ayusher har Munubiya basa Neman k'arin bayani, tunda sunji komai, Munubiya ta share hawayenta tana murmushin takaici, “kibarshi karki sake kiranshi, nasan shine yabama yarinyar nan wayar akan tace wrong number ne, ya ALLAH ka kawo mana sauk'i a wannan lamari dai”.
Tsaki Ayusher taja, ta kamo hannun Munaya “sweet sis..., please wannan karya zama abinda zai ta6a zuciyarki, ki d'auki hakan matsayin ba komaiba, kuma hakan da Fu'aad yayi yasani kuma tabbatar da zargin danake a kansa, ku duba yanda yazage saimunje birnin gayu plaza aranar”.
Gaba d'ayansu zuba mata ido sukayi cikin wani yanayi.
Feena dake kwance tatashi zaune, “humm aini wlhy tunda zancen jaridar nan yafito zargina yana kan Fu'aad ne, Na barine akirashi dama danna sake tabbatarwa”.
Munubiya tace, “sisters nifa duk Na kasan fahimtar zancennan naku fa, zargi babu k'yau ai, miye ribarsa idan ya aikata hakan? dukama yaushe muka San juna dazai yi hakan a garemu? yarasa kuma dawa zai mana hakan sai galadima?”.
Zama Ayusher ta gyara, tafara musu bayani dalla-dalla. “tad'ora da fad'in kinsani ko saboda galadiman yayi?”.
“to amma Dan zaima Galadima mu miye Na had'awa damu kuma?”.
“wannan amasar tana wajen Fu'aad sister ”.
Hankalin Munaya yatashi ainun, itafa ko kad'an bata ta6a kawo Fu'aad acikin wad'anda take zargiba, amma maganar Ayusher tasata dogon nazari yanzu, duk da dai bawai tama yarda baneba kwata-kwata..
★★★★★★★★★★
Lokacin da harun ya iso sashen Galadima bai wani jira isoba yashiga, kwance ya iskeshi bisa 3seaters sam6al, hannunsa d'aya dafe da k'irji, d'aya dafe da kansa.
Da sassarfa ya k'arasa gabansa “Sameer lafiya kuwa?”.
Da hannu Galadima yamasa nuni da k'irjinsa da Kansa.
“ya salam, Sameer! Shiyyasa naketa cemaka kacire abunnan a ranka, kafasan matsalarka batason yawan takura da tunani”. Wayarsa dake ringing ya Ciro a aljihu, Momma Ce ke kiransa.
Cikeda girmamawa ya amsa sallamar data masa, sannan naji yace, “wlhy Momma bashida lfy, kuma k'irjinsa yake complain akai”.
“ok Momma ”.
Yana yanke wayar sai yayi kiran Dr Jalal.
“Jaalal please kana gida kuwa?”.
Bansan wace amsa ya bashi ba daga can, naji dai yace, “please kazo kaduba Galadima”.
Babu dad'ewa saiga Dr Jaalal, damuwa sosai Nagano a fuskarshi saboda ganin halin da Galadima yake ciki.
Harun ya taimaka masa suka kaishi bedroom, sannan yamasa allurar barci.
Babu dad'ewa kuwa barcin ya kwasheshi.
Su duka ajiyar zuciya suka sauke, Dr jaalal yama harun sallama yatafi.
Yana fita Muftahu Na shigowa, gaisawa sukayi da Harun, sannan ya tambayi jikin Galadima d'in.
Harun ya amsa masa Cesar da sauk'i.
Anan sashen Galadima suka kwana, sai dai kowanne acikinsu da dalilin kwannan nasa.
*_Washe gari_*
Alhmdllh Galadima yatashi jikinsa da d'an sauk'i, yakuma ji dad'in ganin Harun da Muftahu a tare dashi. bai iya zuwa masallaciba sai a d'aki yayi salla.
Yana zaune akan sallayar yana azkar su Muftahu suka shigo, zama sukayi bisa Sofa suna jiran yak'arasa azkar d'in nasa.
Bayan ya k'arasa ya juyo garesu, hannu ya mik'a musu sukayi musabaha, suka tamyashi jikinsa.
Yace da sauk'i Alhmddlh, sannan yace, “Muftahu inason ticket, dan yau zan wuce India, ina buk'atar ganin doctor d'ina”.
“ok babu damuwa, bara na bincika idan akwai jirgi mai zuwa India daret”.
Harun yamik'e yana fad'in “bara ahad'a maka ruwan wanka to”.
Kai ya d'agama harun, ya maida idonsa ya lumshe tareda jingina da Waldrop.
Muftahu dake latsa waya yad'ago ya kallesa, “babu jirgin dazai tashi a yau, sai gobe 1:30pm”.
Batareda ya bud'e idonsa ba yace, “bincika min ta Abuja ko legos. dan bazan iya kuma kwana a k'asar nanba yau, ina buk'atar ganin lilita”.
Kai Muftahu ya jinjina ya cigaba da latse-latsensa a wayar, kusan mintuna 4 sannan yad'ago, “an samu, amma zai biya Abu-Dhabi ya sauke Passenger's, daga nan zasuyi hutun kamar na 1hour”.
Idomsa a lumshen yace “yaushe zai tashi daga Nan?”.
“12pm, yanzu na saya maka ticket d'in zuwa Abuja, jirgin zai tashi 8am ne”.
“Ok bara na shirya to”.
Harun dake tsaye yana saurarensu yace “bara naje Na watsa ruwa nima”.
Shima Muftahu mik'ewa yayi suka fita tare.
Galadima yashiga bathroom, kusan mintunansa 40 sannan ya fito, dauriya kawai yakeyi, amma shi kad'ai yasan irin suyar da zuciyarsa ke masa. tsaf ya shirya cikin Suit blue, rigarshi ta ciki Orange, yayi k'yau sosai, yana zaune bakin gado yana saka takalminsa Muftahu yashigo da sallama.
d'ago idanunsa yayi akan Muftahu, sannan yatashi tsaye yana gyara belt nashi, “ya maganar binciko yarinyar nan?”.
“Nagama komai, inason kasami nutsuwane sai muyi maganar daman”.
Galadima dake gyara 'yar sumarsa da bawani yatarata da uban yawa bane yace “ok, katura min komai zan duba, sannan inason kaje kuyi magana da commisshiner of police akan iyalan Manager d'innan”.
“ok yalla6ai angama insha ALLAH”.
Sallamar Harun suka amsa gaba d'aya, ya zauna kan sofa sannan yace “amma yakamata ma'aikatan plaza su koma aikinsu, naga jama'a kamar suna fassara abin dawani Abu daban kuma”.
Murmushin gefen baki galadima yayi, ya ajiye Cumb d'in hannunsa yajiyo yana kallonsa “aini yanzun kuma babu kuma ta sigar dabaza'a fassara ni ba, inaga akan mace kawai yarage jaridu su buga duniya ta ganni, so sukoma aikin su kawai”.
Daga Harun har Muftahu kallonsa suke cike da tausayawa. Muftahu yace wannan d'inma kansu sukai mawa, kuma ALLAH bazai barsuba”.
“insha ALLAHU”. ‘cewar Harun’.
Galadima baice komaiba, sai d'an kimtse kimtsen da ba'a rasabane ya k'arasa, su Harun kam suka fice suka bashi waje.
Baifi mintuna 10 ba yafito suka fice, bayan yatsaya da bayinsa na mintuna biyar, bansan miya fad'a musuba, naga dai sunata faman godiya damasa addu'a.
Aka bud'e masa mota yashiga, duk wanda yake k'ark'ashimsa saikaga fuskarsa ta canja alamun baya son tafiyar tasa.
Kai tsaye fada suka nufa, bayan motocin sun tsaya aka bud'e masa yafito.
Shi kad'ai yashiga fadan, cike take da dukkan masu ruwa da tsaki anata fadanci.
Saida ya gaida sarki, sannan ya zauna mazauninsa kusada sarkin, sauran fadawan suka gaidashi cikin girmamawa, shima ya amsa cikeda mutuntawa.
“ya adalin sarkinmu yau zan koma inda na fito, saboda inason ganin likitana”.
Murmushi sarki yayi, sannan ya gyad'a kai bare da yayi maganaba.
Da sauri Dogarawa suka d'auka da fad'in Sarki yajika Galadima, Yakuma amsa, yana maka addu'ar sauka lfy kuma.
“ina godiya da wannan alfarma”. ‘galadima yafad'a cikin rissinar da kai alamun girmamawa”.
Sarki yad'an gyara zamansa, ahankali ya furta “ka gaidamin da d'an uwana da gimbiya Zeenah, insha ALLAH nima nextweek ina nan zuwa”.
“ina godiya ranka shi dad'e, insha ALLAH d'an uwanka zaiji”.
“gyad'a kai kawai sarki yayi”.
“An gaisheka galasima, ALLAH ya tsare gabanka da bayanka, ALLAH ya kaika lafiya yabama adalin tsohon sarki lafiya, Alkairin ALLAH da ni'ima sukai a garesa, gaba dai gaba dai Galadima mai jiran gado, d'an sarki jikan sarakuna k.....”.
Hannu ya d'aga musu alamar ya Isa.
Ya risinar da Kansa domin girmamawa ga fada sannan yamik'e suna jera masa addu'oi, yayinda shikuma yake amsawa asaman la66ansa.
Bai shiga sashen kowaba yay tafiyarsa, suna isa filin jirgi ko 20 minutes basuyiba jirgin su yatashi zuwa Abuja.
Muftahu da Harun da dogaransa suka dawo cikeda kewarsa.
Koda ya isa Abuja hotel yanufa kai tsaye, yakama d'aki danya huta, akwai kusan 3hours nan gaba kafin jirginsu ya tashi. Rigar suit d'insa yacire tareda tie d'in, sannan ya zame wandon da rigar cikin ya kwanta dagashi sai boxer da vest.
Juyi kawai yakeyi agadon, Dan barci yakasa d'aukarsa, abinda yafaru a kwanaki biyunnan yakasa barin zuciyarsa, yarasa wane irin hasashe zaiyi ga masu aikata masa hakan... Ringing d'in da phone nasa tayine yasakashi bud'e idanunsa, wayar yajawo yana kallon mai kiran. *_Sweet papi_* yagani ajikin wayar, yay saurin d'agawa kafin ta tsike.
Cikeda girmamawa tamkar yana a gabansa ya rissinar da kansa bayan yatashi zaune, “Barka da hantsi ranka ya dad'e”.
Daga can aka amsa “da yauwa Muhammad, ina fata kana lfy?”.
“Alhmdllh ranka ya dad'e”.
“To masha ALLAH, dama mamanka Ce takirani takemin wasu bayani, duk da kafin kiran nata dama naga zantukan dake yawo a jaridu da yanar gizo, zuciyata bata yarda zaka aikata hakanba Muhammad, amma inason sanin gaskiyar zancen?”.
“wlhy ranka ya dad'e sunyi hakanne kawai domin 6atamin suna, amma ainahin abunda yafaru shine.............”
Nan Galadima ya zayyane masa komai.
Murmushi mai sauti tsohon yayi, har Galadima Na jiyosa, sannan yace, “hummm! to yanzu kai kana wace nahiya ne?”.
“Ina Abuja zan koma India, saboda jikina yana Neman motsawa”.
“to to, hakanma dakayi dai-daine, amma a kwantar da hankali, komai mai wucewane, komai kaga yafaru da d'an Adam rubutaccene a littafinsa, dama ita rayuwa tana tafiyane da k'addara, yanzu zan isa fada, bayan kasamu nutsuwa idan kaje zamuyi magana, duk da watak'ilma nashigo ganin mahaifin naka k'arshen watannan”.
“to shikenan, ngd sosai, ALLAH yak'ara tsahon rai da lafiya mai amfani”.
“amin ya rabbi Muhammad” cikin tsokana tsohon yace “kaga d'annema, duk kabi ka susuce akan k'aramin Abu, kazo Na sanmaka jarumtata mana”.
Dariya Galadima yayai (karon farko danaga yayi dariya🙊😂) cikin tausasa harshe yace “haba dai, ai sai dai Na sammaka tawa, nifa sabon jinine, ta ina mai shekaru 80+ zai fi mai 29 jarumta?”.
Daga canma Sarki dariya yayi, cikeda k'aunar jikan nasa, “uhmyim tunda kace haka idan kazo saimu gwada kwanji ai”.
“hhh tom kafad'ama inno ta tsumaka sosai, inba hakaba zatayi takaba”.
“ja'irin gora zan kamakane ai, ALLAH ya tsare hanya, ka gaida iyayen naka”.
“zasuji ranka ya dad'e, a gaidamin inno, tayi hak'uri wannan karon ban shigo naci tuwon taba, nazo k'asarne da uzurori dayawa, gashima banyi ko d'ayaba”.
“zataji insha ALLAHU, babu komai, adage dai da addu'a watarana sai labari, *zakaran da ALLAH ya nufa da cara, ko ana mazuru ana shaho sai yayi jikana kaji*.
Murmushi Galadima yayi dan jin maganar kakan nasa, sukayi sallama cikeda k'aunar juna”.
Ajiye wayar yayi yakoma ya kwanta fuskarsa d'auke da murmushi, yana k'aunar kakansa (mahaifin Momma) saboda shima yana nuna masa k'auna da kulawa, akan la66ansa ya furata “ALLAH ya k'aramaka tsawon rai my sweet papi”.
Amin Galadima.
⛹🏻♀bara nalek'o su munaya.
★★★★*★★★*★★★★
Bansan yanda zan musalta muku irin bak'in cikin danakeba a yau, tundaga kiran Fu'aad zuwa yanzu zuciyata sai suya takemin, banida wata walwala, sai dai ina dannewa kodan kwanciyar hankalin innarmu da 'Yar uwata Munubiya, dama tun randa abunnan ya faru bamu sake fita koda tsakar gidaba dagani har 'yar uwata, abinci sai dai innarmu kosu Aryaan su kar6o mana.
Habaici dai da gugar zana muna shanshi acikin gidanmu, innarmu bata cemusu uffan, nikuma mai maida murtanin damuwa ta hanani iya cewa komai, 'yan biki dai zuwa yau kowa yakama gabansa, yanzu dagamu sai mune agidan.
Sauk'inmu d'aya tun ranar innaro bata sake shigowa gidanba, inaga baba mai kanwa yahanata.
Babu Wanda yay mana maganar komawa makaranta, muma kuma bamuyi yunk'urin zuwanba, kullum dai innarmu NATA k'ok'arin ganin munkwantar da hankalinmu, a koda yaushe cikin mana nasiha take dayimana kwatance da rayuwarta itada mama Rabi'a, takan Nuna mana muhimmancin hak'uri da amfanin yinsa, koda baka ci ribarsa anan gidan duniyaba zakaci ribarsa a lahira inda kowa ke rububin tara ayyukan alkairi.
Alhmdllh muma mun fara rage damuwar kodan ganin farin cikinta, Abu d'ayane kecin zukatanmu shine maganar fidda miji da Abbamu yace nayi acikin sati biyu kacal, gashi kuma babu wani tsayayye a hannu.
Duk mun rame mun zuge nida munubiya, dama gamunan bawani aukin kirkiba, ahaka muka cinye satin da abin yafaru.
Yau ta kasance lahadi, wasu a yaran gidanmu sunata shirin ziyartar gidajen amare, kaf sa'aninmu 'yan matan gidan sunyi shirinsu, Fauziyya, Fiddausi, Safara'u, Haleematu, amma ban da mu, Dan kogaya mana mu shirya ba'ayiba, saima Fauziyya Ce data tashigo da safe gaida innarmu take sanar damu wai mushirya zamuje gidajen amare.
Dagani har Munubiya bamuce da ita komaiba, sai 'yar dariya damukayi.
Koda suka gama shirinsu basu nememu ba, sai Fauziyya Ce tashigo danta mana magana akan mufito.
Turus tayi Dan ganinmu babu wani shiri, hasalima muna falo zaunene, Munubiya ta kwantar da kanta bisa cinyata ina kwance mata kai, innarmu kuma Na zaune gefe suna waya da mama Rabi'a, sai Aiyaan da Aryaan daketa faman buga game.
Hira mukeyi da Munubiya akan wasu write-ups datake dubawa a Instagram da akayi akan maganarmu da galadima, cikin damuwa take karanta writeup d'in, shiyyasa bamuga shigiwar Fauziyya ba saida tayi magana...
“wai sisters kuna nufin ma ko shiryawa bakuyiba?”.
Gaba d'aya muka kalleta, nayi murmushi ina fad'i “kiyi hak'uri Fauziyya, kutafi kawai, har yanzu fita bata kamacemu ba, dan abubuwa basu gama daidaitaba tukunna”.
Cikeda damuwa ta gyad'a kai, jiki a sanyaye tace “shikenan saimun dawo”.
“ok to Ku gaida mana amare”.
Kanta ta jinjina nanama tana ficewa.
Munubiya tace, “ALLAH Sarki Fauziyya, itadai tana sonmu”.
Nad'an murmusa ina taje mata Wanda Na tsefe, “Munu.... nima ina k'aunar Fauziyya wlhy itada mamansu, sune kad'ai suke sonmu agidannan, Na tabbata wannan fitar dama ba'a sota damuba, itace kawai taketa k'ok'arin taga munje d'in”.
“wlhy hakane sweetheart ”. ‘cewar Munubiya’.
Innarmu dai tanata waya, Dan haka batace mana komaiba.....
★★★★★★★★★
Lokaci na gabatowa yay shiri yabar hotel d'in, zuwansa airport babu dad'ewa jirginsu yad'aga, sun tsaya a Dubai Abu-dhabi sukayi hutun 1hour sannan suka nufi India.
Tunkan jirginsu ya sauka Sauban da Samha sukazo d'aukarsa.
Dan haka yana fara taka matakalar jirgin suka hangosa, cikeda jin dad'i suka nufo gareshi.
Duk da fuskarsa babu walwala hakan bai hanasu nuna farincikin ganinsa ba, shima dai yayi farin cikin ganinsu, duk da kwanaki 4 kacal kenan da barinsa k'asar.
Sauban ya kar6i bag d'in hannunsa yana fad'in yaya welcome”.
Kansa ya shafa yana lumshe ido alamun amsawa.
Samha ma tace “Wellcom back Uncle Sam”.
Ahankali ya furta Thanks you dear, ya school?”.
“Alhmdllh Uncle, ya kabaro Nigeria? ”.
Murmushi kawai yayi batareda ya amsa mata ba, yasan surutun Samha bamai k'arewa bane, yana amsa wannan wata zata jeho masa.
Sauban ya bud'e masa back seat ya zauna, sannan yarufe shi yakoma mazaunin driver, Samha Na gefensa.
Idonsa ya lumshe ya maida Kansa ya jingina da kujera.
Wani madaidaici Gida suka isa, Wanda baza'a kirashi k'aramiba, sannan ba k'ato baneba, sai dai muce tsaka tsaki.
Samha ce tafita da kanta tabud'e gate d'in, Wanda ana ganin komai dake farfajiyar gidan ta jikinsa daga waje. Sauban ya ida shiga da motar, kusada wasu motoci uku yay parking, Samha data k'araso tabud'ema Galadima yafita.
Kusan atare suka shiga falon gidan, yana gaba suna baya.
Masha ALLAH nafad'a saboda ganin tsaruwar falon, sai dai shiru gidan alamun babu kowa a ciki.
Ya zube bisa rukunin kujerun farko dasuka kasance golden color and white. Isaka yad'an turo daga bakinsa sannan ya kalli Sauban dake shirin zama shima.
“yanaji gidan shiru? inasu Momma ne?”.
“duk suna hospital, har jakadiya ma, zamu tafi d'akko kanema Aunty Mimi tatafi itama, dama ita kad'aice agidan saboda mu muna school ”.
“Ok, ya jikin Abie?”.
“hummm da sauk'i yaya”.
“mik'ewa yayi yana guntun murmushi, tunda yafara girma yafahimci mahaifinsa Na kwance yakejin idan antanbaya Momma jikin Abie tana cewa da sauk'i, amma shi shekaru kusan 25 Abie Na kwance amma shifa baiga wannan sauk'inba, kawai suna dai fad'ane, sauk'i d'ayane zai iya cewa yagani shine magana da idanu da Abie keyi kawai.
Da wannan tunanin ya haye steps d'in benen, yana tafiya yana sasaauta tied d'in wuyansa. ahaka harya k'arasa d'akinsa.
Komai needs kamar yanda ya barsa, (kullum ne babu fashi sai Samha ta gyara d'akin) Komai a d'akin fari ne, sai golden dasuka kasance d'ai-d'ai. d'akin yayi k'yau sosai, sai tashin k'amshin turarensa daya manne yakeyi, gakuma na air fresheners, saiya had'u yana bada wani ni'im taccen k'amshi. kayansa yashiga cirewa d'ai-d'ai yana sagewa jikin hanger. wanka yashiga sannan ya gabatar da sallan data riskeshi a hanya .........
★★*★★*★★*★★*★★
Da daddare muna zaune munacin tuwo saiga kiran Abba yashigo wayar innarmu, tana d'agawa yace ta turo masa mu.
To kawai tace ya yanke wayar.
Kallonmu tayi ad'an sanyaye, tace “idan kun gama cin abincin kuje abbanku Na kira”.
Daga ni har Munubiya sai da gabanmu yafad'i, jiki a sanyaye muka amsa da “to innamu”.
Kasa cigaba Dacin abincin mukayi, dole muka ajiye kawai mukaje muka wanko hannu..................✍🏼
🤔ko wane kira kuma Abba yakema su Munaya😕?.
Barkanmu da dawowa✋🏻, ina fata duk kuna cikin k'oshin lafiya?😄🤝🏻.
To gashinan Na k'ara yawan page Masu k'orafi😄⛹🏻♀⛹🏻♀
*_ya ALLAH ka gafartama iyayenmu_*👏🏻😭
*_Typing📲_*
*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
👉🏻1⃣3⃣
.......Mun d'anji sanyi a ranmu, ganin kiran bamu kad'ai baneba, hardasu Safara'u Ashe, waje muka samu muka zauna, sannan muka gaidasu.
Fiddausi kad'ai ake jira, itama babu jimawa sai gata ta shigo da sallama, duk muka amsa, ta gaida su Abba.
Falon yay tsit Na mintuna biyu, sannan Abbanmu yay gyaran murya, kallonmu yake mu duka cikin nazari, ganin muduka mun hallara yace “mun kiraku nan ne saboda dalilin abinda yafaru kwanan nan, hankalina yakasa kwanciya da zamanku a gabanmu, mun yanke shawara nida 'yan uwana zamu aurar daku duka kawai, kowace saita cigaba da karatunta a d'akinta, muma hakan zai sama mana kwanciyar hankali. dan haka kowacce saita sami mai zuwa wajenta ta sanar masa munason ganin magabatansa inhar da gaske yakeyi”.
gaba d'aya muka amsa da to abba kanmu ak'asa.
Wasunmu murna suke da hakan, amma banda ni da Munubiya, dan bamuda wasu tsayayyu a hannu, bawai samarinne bamu dasuba, a'a wad'anda zamu kawo amatsayin Na aurene matsalarmu.
Maganar Dady ce ta katsemin tunani, danaji yana fad'in su sutashi suje, amma ni Na tsaya.
Haka suka fice suka barni, duk tsoro yakuma cika zuciyata. bayan fitarsu baba k'arami yanuna min gabansu alamar Na matso.
Tamkar kazar da kwai ya fashema a ciki haka natashi Na isa gabansu, na zauna kaina ak'asa.
Baba k'arami yace “Munaya!”.
Muryata Na rawa Na amsa da “na'am baba”.
Ya gyara zamansa sosai, “Munaya na sanki bak'ya k'arya, kifad'a min tsakaninki da ALLAH miye had'inki da Galadima?”.
Gabanane yafad'i daaam!, nai k'ok'arin had'iye kukan daya taho mini “wlhy Baba banida had'in komai dashi, hasalima ban ta6a saninsaba sai awajen hawan sallah, shima ba ganin fuskarsa na ta6a yiba, sai kuma randa mukai karo dashi a filin idi ina neman su kamal, kuma wlhy aranar hak'uri kawai nabashi, koma amsamin baiyiba yatafi, ni banma san shibane alokacin”.
“amma miyasa aka buga hotonku kuna cikin plaza d'insa?”.
“Dady kuyi hak'uri, tabbas nasan munyi laifi anan, amma Ku yafemin, dan nasan da bamuje plaza d'inba a daren da k'ila hakan bai faruba, amma wlhy abinda yafaru shine...................., cikin nutsuwa ta zayyane musu komai, saidai batace Munubiya ce zata fad'inba, tace itace.
Koda basuga ainahin abin da idonsu ba sai zukatansu sukayi sanyi, baba k'arami yace “to ALLAH ya k'yauta, wannan akwai wani Abu daban dabamu saniba acikin lamarin, ALLAH ya warware komai cikin sauk'i”.
Duk mukace amin.
Dady yace, “Munaya! bisa hak'uri damukaita bama yaya kin sami sassauci akan sati 2 daya ce ki fidda miji, yanzu saiki nutsu ki kawo kamar sauran 'yan uwanki, insha ALLAH bayan babbar salla zamu aurar daku gaba d'aya kawai, ALLAH yayi muku albarka kinji, kucigaba da kare mutuncinku, sannan Ku koma zuwa makaranta tunda abin ya lafa”.
Kai na gyad'a sannan nayi godiya.
Na iske innarmu da Munubiya jigum-jigum a falo suna jiran dawowata, nasami waje na zauna jikina a sanyaye.
Innarmu tace, “miya faru kuma?”.
Guntun murmushi nayi INA share kwallar data zubomin, “babu komai innarmu, sun tanbayeni gaskiyar abinda yafaru ne, sannan since sun janye maganar sati biyu nafiddo miji da sukace nayi. nima za'a had'a danawa zuwa bayan salla kamar su Munubiya, kuma since mukoma makaranta”..
Daga Munubiya har innarmu ajiyar zuciya suka sauke, “to Alhmdllhi, ALLAH yabaku mazaje na gari”. ‘cewar innarmu’.
A zukatanmu muka amsa mata da amin.
Washe gari.
Mukayi shirin zuwa makaranta, gudun abinda zaije yadawo sai muka saka nik'af dagani har Munubiya kamar yanda innarmu tabamu shawara muyi.
Alhmdllh tunda muka fita bamuci karo da abinda ya Sosa zuciyarmu ba, saboda fuskokinmu arufe suke.
A ajima babu Wanda ya shaidamu sai Bilkeesu, nanma dai munyi mun fito lafiya babu wata damuwa. amma saboda a d'ar-d'ar Muke bamu wani sakeba, ana fitowa lectures muka nufi gida.
Haka muka cigaba da zuwa makaranta kulum fuska arufe, ko cikin anguwa za'a aikemu saimun saka nik'af, dan yanzu fuskokinmu sunrigada sun zama sannanun fuskoki....
★★★★★★★★★★
Yana gama kimtsawa yafice, ko abincin da Samha ta shirya nasa bai sauraraba, kai tsaye yanufi Hospital d'i. da Abie ke jinya.
da jakadiya yafara cin karo tana rik'e da Khaleel a hannu, khaleel yakwace yataho da gudu yana fad'in “Uncle oyoyo”.
Hannayensa ya bud'e masa yafad'a jikinsa, ya shafa kan yaron yana fad'in “my boy ykk?”.
“lafiya Uncle Sam... yaushe kadawo?”.
Murmushi Galadima yayi, yad'an ja kumatun khaleel “to maganatu yau na dawo”.
Dariya yaron yayi, zai sake joho wata maganar Galadima ya d'ora yatsansa akan bakin yaron alamun yayi shiru. Shirun kuwa khaleel yayi dan yasan halin Uncle Sam.. saraii.
Jakadiya ta rissina tana gaidashi, amsawa yayi fuskarsa da 'Yar fara'a, ya tambayeta ya jikin Abie.
“jiki Alhmdllh ranka ya dad'e”.
Kansa kawai ya jinjina mata yay gaba rik'e da hannun Khalel.
Da sallama ya shigo d'akin da Abie ke jinya, d'akine babba kamar Bana asibitiba, daka gani Kasan anyisane saboda manyan mutane irinsu, Momma na zauna akujerar gaban gadon da Abie ke kwance, gadon Kansa bawai ainahin gado bane na asibiti, duk wasu na'urori ne ajikinsa, da alama sune suke taimakama jikin Abie d'in, k'umba Momma ke yanke masa.
Aunty Mimi na zaune bisa kujerun da aka shirya a gefe tamkar falo, System Ce agabanta tana danne-danne.
Sallamar Galadima yasata d'agowa tana murmushi, “My k'ani oyoyo” tafad'a tana ture system d'in daga cinyarta.
Murmushi yamata shima, cikin maganarnan tasa ta k'asaita maikama da anmasa tilas yace “my dear aunty barkanki”.
Hannu tasa tad'an bigi damtsen hannunsa, cikin wasa tace barka zakace ba bagyka ba”.
Shafa Inda tad'an bigesan yakeyi yanda 6ata fuska kamar wani k'aramin yaro, “ALLAH akwai zafi aunty Mimi, wai har yanzu ban girma da buguba awajenki?”.
“tab ai da sauranka, sai randa kayi aure zan daina”.
Bakinsa ya ta6e yak'arasa inda Momma take yana fad'in, “aiko k'yadad'e baki barinba kenan”.
Momma dake murmushi saboda drama d'in tasu ta kalli Abie da shima fuskarsa take a washe alamun yayi farinciki da ganin d'an nasa.
Gabansa yaje ya durk'usa, saitin Face d'insa, ya saka hannunsa cikin NASA fuskarsa d'auke da murmushi yace, “my Abie barka da rana”.
Da idanu Abie ya amsa masa, dan sune bakin maganar yanzu.
Yakuma masa magana da ido alamar yaka barosu?.
Murmushi Galadima yayi na takaici, sannan yace, “mai martaba na gaidaka, shima zaizo nextweek”.
Farin cikine Yakuma fad'ad'a a fuskar Abie, dasu sukasan yanayinsa, sukad'ai zasu iya fahimtar farin cikinsa ko damuwarsa, musamman ma Momma.
Momma dake kallonsu tayi murmushi, Galadima ya maida kallonsa gareta, “Momma na yana sameku?”.
“Alhmdllh Muh'd, yaka barosu?”.
Baki yad'an ta6e sannan yace “lfy lau, ya jikin Abie?”.
“jiki Alhmdllhi, dan randa ka tafi yatsun hannun damarsa sund'an motsa”.
Da Sauri Galadima yace “da gaske Momma?” yay maganarne yana kallon hannun Abie d'in, sannan cikeda farin cikin ya sumbaci hannun yana fad'in Alhmdllh ala kulli halin, ALLAH yabaka lafiya my sweet Abie”.
Lumshe idanu Abie yayi farinciki na k'ara fad'ad'a a face nashi, aunty Mimi da momma da jakadiya suna kallonsu cikeda tausayi suka amsa da amin. khalel yata6a kafad'arsa, juyowa yayi yana kallonsa. yaron yakai hannu yana sharema Galadima hawayen dasuke kwance a kumatunsa. galadima yajawosa ya rungume yana sumbatar kan yaron, fuskarsa d'auke da murmushi.
★★★
Yau mune k'arshen tafiya school, saboda lectures d'in yamma ne damu, Fauziyya kuma batada lafiya bazatajeba.
Kasancewar abubuwa sun kuma lafawa yau sai bamu saka nik'af ba, amma yana rik'e a hannunmu idan mun shiga cshool zamu saka.
Mun fito bakin titi muna jiran taxi ko napep saiga wata bak'ar mota wulik ta faka agabanmu, dagani har Munubiya d'auke kanmu mukayi gefe.
Mai motar ya sauke glass d'in yana kallonmu, sallama yayi mana, Munubiya ta amsa, nikam koma kallo bai isheniba.
Ganin haka saiya bud'e motar yafito, matashin saurayine bak'i k'yak'yk'yawa mai yawan fara'a. Yace, “haba 'yan mata, babu fad'a miya kawo gaba”.
Cikeda tsiwa nace “sai aka cemaka mu 'yan matane? to matan aurene”.
Murmushi yayi, sannan ya gyara tsayuwarsa, “dear hakan ma dakikayi yakuma tabbatar min da Bahaka baneba”.
d'an hararsa nayi na d'auke kaina, danni yanzu maza duk haushi suke bani wlhy.
Dariya yayi, “oh sweety karkisa na sume mikifa a titinnan”.
Ganin yana neman shiga hancinmu yasani jan hannun Munubiya muka bar wajen, k'yalemu yayi Yakoma mota ya zauna. har muka sami abin hawa yana kallonmu. haka yayta bin mai napep d'in har k'ofar makaranta, daga nan kuma bamusan ya akayiba mudai muka shige.
Kwana biyu da faruwar haka muna wanki a tsakar gida saiga ya Anas yashigo, ya kallemu yana murmushi, twins cikinku waye mai saurayi mai bak'ar mota?”.
Mu duka kallonsa mukayi, gwaggon Haleema da maman safara'u dake aiki a tsakar gidan suma duk suka kallemu.
Da sauri Munubiya tace “munaya Ce yaa Anas”.
“kije to yana jiranki a k'ofar gida”.
harara na dallama Munubiya “wlhy Munubiya k'arya dai babu k'yau”.
Dariya tayi tacigaba da wankinta, “kitashi kije kina 6ata masa lokaci”.
Hijjab na d'auka nafita danufin zuwa na sauke masa masifa na dawo.
Gwaggon Haleematu da maman Safara'u suka bini da kallo cikin wani yanayi. oho ni bammasan sunayiba.
Jingine da motarsa na gansa, sanye yake da shadda ruwan zuma, harda hula, sa6anin ranar damuka gansa da k'ananun kaya, kwarjini yamin nakasa masa masifar danayi niyya, namasa sallama sannan nace “miya kawoka k'ofar gidanmu? waya nuna maka ma?”.
Yad'an murmusa, “miyake kawo saurayi gidansu budurwa?”.
“oho maka” Nafad'a cikin kauda kai gefe.
“kimga baby sorry, mu ajiye wannan drama d'in, ni bada wasa Nazo nanba, tun randa na ganku keda 'yar uwarki kuka rikatani, nasa a raina duk wadda ALLAH yabani cikinku tamin, bansami kwanciyar hankaliba saida na binciko gidanku, sunana Haidar Mustapha”.
Shiru nayi ban tanka masaba.
Yay murmushi yana matsowa kusa dani, “please mana baby, kimin magana?”.
Da k'yar ya sami na amsashi sannan nima nafad'a masa nawa sunan. abinda na fuskanta da haidar shi mutumne mai sauk'in kai, sannan ko kad'an banga alamun yaudara ba tattare dashi.
Cikin kwanaki kad'an mungama sabawa da haidar, sabawa maiban mamaki, wadda nikaina har mamakin kaina nakeyi wlhy.
Alokacinne kuma yaa Marwan shima ya nuna yanason Munubiya, wayyo zokuga farin ciki wajen iyayenmu, tamkar su zuba ruwa a k'asa susha dan dad'i.
Wannan Abu fa ya bak'anta ran 'yan gidanmu, sunso ace munyi kwantai, har agama sakama 'ya'yansu rana mu babu mazaje a hannu, amma ALLAH ya fisu ai.
Kud'in Munubiya aka fara kawowa gidanmu, daga nan saina Safara'u. nima saiga iyayen Haidar sunzo, ranar har kukan dad'i mukayi muda innarmu, duk wani masoyinmu zai tayamu murna akan wannan al'amari, dan ba'a ta6a tunanin zamu iya samun mazaje da wuri ba saboda abinda yafaru.
Sauran 'yan uwanmu ma duk ankawo kud'ad'en aurensu, dandanan aka tsaida ranar aure, watanni uku kacal, bayan salla babba da wata biyu.
Zuwa yanzu kam hankalinmu ya kwanta, sai dai matsaloli na gidanmu da basa k'arewa, saikuma abinda yafaru tsakaninmu da Galadima, wani lokacin mukan fuskanci tozarci daga wasu jama'a idan mun fita, tunma muna zama muyi kuka har zukatanmu suka fara dakewa.
Galadima kam bamu sake koda jin d'uriyar saba, hakama Fu'aad, tunima Haidar ya mantar dani wani Fu'aad gaba d'aya.
Ahaka babbar Salla tafara gabatowa. Masu shiri natayi, nikam dai babu mu aciki, dagani har Munubiya munyi alk'awarin babu inda zamuje sai gidan mama Rabi'a........
Munshiga bikin salla lafiya, inda iyayenmu sukayi layya kamar yanda kowacce shekara suka saba, itama innaro anmata, babu inda mukaje wannan karon, su Safara'u dai ansha yawo, ranar suyar nama kuma saiga dukkanin amare sunzo yawon salla, abin tamkar had'in baki, kowaccensu tayi 6ul-6ul da ita, harma damasu tsarabar ciki.
Kowacce jinta take a sama, mijinta yafi na kowa, iyayensu kam anata baza hak'wara da tink'aho ana zuba mana habaici.
Babu Wanda ya tanka musu acikinmu, dan innarmu ta hana.
wajen Ayusher mukejin wai babu Galadima a hawan salla wannan karon, hakan bai dameniba, danni baya gabana, nama manta dawani Galadima can.
Bayan gama bikin salla da kwanaki uku saiga wani tashin hankali.
Iyayen Haidar sunzo wai abasu kayansu sun fasa, ance musu ni 'Yar iskace.
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un. Yau munga tashin hankali muda innarmu, kuka da hawaye innarmu keyi itada mama Rabi'a, haka aka had'a kayansu aka basu.
Innaro tashigo tafara tata tsiya babuji babu gani, sai zuba cin mutunci takeyi ga innarmu, 'yan gidanmu natajin dad'i, jisuke kamar anmusu gafara da fasa aurennan nawa, aganinsu yaza'ayi 'ya'yansu suna auren masu kud'i nima na auri mai kud'i, ai bazai yuwuba..
Cikin kuka nakira Haidar ina tanbayarsa miyasa zaimin haka, yasan tun farko ba sona yakeba miyasa yazo gidanmu har iyayensa suka shiga.
“k dalla malama yimin shiru, ni mahaukacine zan auri yarinyar da aka buga hotonta jikin jarida wani na kissing d'inta, ok da an 6oyemin za'a bani sauran wani Ashe ked'in karuwar Galadima ce, to ALLAH ya toni asirinku dagake har iyayen naki, ko a hanya muka had'u karki kuma nuna kin sanni ma”.
Baki na bud'e da nufin maida masa murtani ya yanke wayar, nayi saurin kuma kira amma sai najita arufe.
Kuka na fashe dashi, bansan miya faruba sai dai najini ak'asa kawai.
Cikeda tashin hankali Munubiya tayo kaina tana kuka da girgizani.
Dandanan d'akin yacika dasu Dady, babu alamar rai atare dani, hakan yasa aka d'aukeni da gaggawa sai asibiti.........
★★★★★
A 6angaren Galadima kuwa wasu ayyukane suka d'auke hankalinsa, gaba d'aya yayi busy saboda kamfaninsu na k'ok'arin fidda wata waya sabuwar k'ira.
Abinda ya faru kuwa a Nigeria ya watsar dashi gefe, saboda gargad'in da doctor d'insa yamasa akan yarage yawan damuwa, saboda ciwonsa yana k'ok'arin tashi.
Haka yadage yacire komai d'in, amma har yanzu yasaka amasa aikin bincike ta k'ark'ashin k'asa, sannan iyalan manager sun ku6uta suma, yabar Nigeria da sati biyu suka sakosu.
Gaba d'aya ya ajiye duk wani abinda yashafi Nigeria a gefe, ko bikin salla bai hakarta ba, sannan zuwan dayankan yi duk karshen wata ma ya daina, Momma batace dashi komaiba akan k'in zuwan nasa.
Dan lokacin da mai martaba (mahaifin momma) yazo sun tattauna sosai akan abinda yafaru, shine yace Galadima yad'an tsahirta da zuwa Nigeria nawani lokaci, idan komai ya lafa sai acigaba da bincike, dan wad'anda suka aikata sumafa baza suyi barciba, yanzu idonsu abud'e yake akan komai, amma idan anyi burus dasu komai ya lafa sai a d'auki mataki. Wannan yasa bai sake zuwaba, gameda business d'insa nacan kuwa Harun yana tsaye akan komai.
Fitowarsa kenan daga office zaije gida yad'an kimtsa sannan yaje asibi, wayarsa tashi ruri, zarota yayi daga aljihu ya duba, ganin Muftahu a kan layi saiya maida wayar cikin aljihu kawai batare da ya amsaba.
Hannu yabama beejay abokin aikinsa sukayi sallama akan saikuma gobe. yana k'ok'arin shiga motar kiran yakuma shigowa, shiga yayi ya zauna sannan ya d'aga, suka gaisa da Muftahu, ya tambayesa jikin Abie.
Shikuma ya amsa da Alhmdllh.
Muftahu yace, “ALLAH yasa ban takuraka ba? Inason muyi magana ne dama”.
Kwantar da kansa yayi jikin kujera ya lumshe idanunsa, cikeda k'asaita ya furta “ina saurarenka”.
Daga can Muftahu yay murmushi, sannan yace “dama akan yarannan ne, d'aya daga cikinsu an fasa aurenta, wai Wanda zai auretan yace yafasa sabo...da sa... sa.... yakasa fad'a saboda maganar tamasa nauyi abaki”
Galadina yace “kafad'a mana, kasanfa bana son kwana-kwana a magana ni”.
“wlhy maganarce babu dad'in ji, ca yayfa wai ita karuwarka ce, yanzu haka yarinyar tana asibitima”.
Da k'arfi ya cije lips d'insa, zuciyarsa na suya, saikuma ya saki guntun murmushin takaci, yatashi zaune yana bud'e idonsa, “humm Muftahu waye shi yaron dazata aura d'in?”.
“wlhy ban saniba nima”.
“o right karka damu, zanyi tunani akan lamarin, ni bamma duba bayanai daka turomin akan yarinyarba fa, abubuwa sunmun yawane wlhy. amma masu bibiyar tata basuga wani abunda ya shafi waccan maganarba?”.
“Gaskiya basuga wani abuba sa6anin tunaninmu, ammafa bama yarinya d'aya bace ba, twins ne, kaduba bayanan kagani”.
“ok sai munyi magana kenan”.
Bayan sunyi sallama yay shiru yana tunani a ransa, da gani kasan ransa a6ace yake, ya furzar da huci daga bakinsa sannan ya tada motar yatafi. idonsa yayi jajir saboda bak'in ciki, yanzun har takai wani yafasa auren wata akansa? waye yamasa wannan abin? miya masa ne da zafi haka ya tozartashi? wlhy yayi alk'awarin duk Wanda keda hannu akan wannan tozarcin da akai masa bazai d'aga masa k'afaba, dolene yayi dana sanin saninsa.
Da wannan tunanin ya k'arasa gida.
Babu kowa a gidan sai jakadiya, su Sauban suna makaranta, Aunty Mimi da Momma kuma suna asibiti, jakadiya ta rissina tana gaidashi, hannu kawai ya iya d'aga mata ya haye sama.
Binsa tayi da kallon tausayi, hakan da yayi mata ya nuna ransa a 6ace yake, danshi mutum ne mai girmama nagaba dashi, dukda tana a k'ark'ashinsu bai ta6a wulak'antata ba, wannan tarbiyar mahaifiyarsu ce kuma.
Koda yashiga rigarsa kawai yacire ya zauna a bakin gado, medical glasses d'insa yasaka sannan yajawo System yabud'e, Emailil na Muftahu ya shiga.
Dukkan bayanai da tarihin su Munaya ne awajen.
Gaba d'aya ya nutsu ga abinda yake karantawar, shi mamakima abin yabashi, sukuma wane irin gida wad'annan yaran suka fito haka? Wani abun yakan bashi dariya (sai dai yakanyi dariyar ne a zuciyarsa), wani kuma haushi, tsaf yagama karanta tarihin yaran masu kama da juna.
Ya mik'e yana zagaye d'akin da tunanin miye mafita, har yanzu zuciyarsa bata bar karanta masa da hannun wad'an yaran aka masa wannan abunba, sai dai shi kansa yana tambayar kanasa mizaisa su aikata? miye kuma ribarsu bayan suma hardasu aka tozarta?. yanzu kuma zuciyarsa na masa wani tunani daban bayan yaji tarihinsu.
Zuciyarsa na cigaba da tunzurashi akan yayi amfani da damar k'arshe wajen bincikensa, tunda yabi dukkanin sauran bai samu wani bakin zareba.
To amma kuma wannan ai ba tarbiyyar Malam bahaushe baceba, daga baya kuma idan komai yafitofa? wane kallo kuma za'a masa?, shinma zata iya fahimtarsa kuwa? dan irin wannan abun yakan farune a labaran films ko Novels, to amma wannan ce damarsa ta k'arshe ai kawai, dolene ya jefi tsuntsu biyu da dutsi d'aya kenan?.............✍🏼
Tirk'ashi, Nikam dai nakasa fahimtar wannan cirkud'ad'd'en tunanin na Galadima☹, fan's koku kun fahimta Ku fassara mana🤔?.
*_Ya ALLAH ka gafartama iyayenmu😭👏🏻_*

Qanwata don Allah ki karo min irin wa'innan hotunan,Tare kuma da na twins maza daban mata daban amman manya da kuma wanda duk suke a hade
*_Typing📲_*
*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
👉🏻1⃣5⃣
.......Tunda yafara tafiya bai tsaya ko inaba sai a wata sabuwar anguwa, shiru anguwar take babu yawan hayaniya, dan gidajenma tsilli-tsilli suke tamkar rugar Fulani, wani gida dakecan nesa da sauran gidajen yanufa, gidane babba mai k'aton bak'in gate, yay horn sau biyu akazo aka bud'e masa. a babbar harabar gidan yay parking, yana cikin motar bai fitoba har kusan 10 minutes bayan yagama waya yace ya iso.
Idanu na zaro waje saboda ganin Muftahu yafito daga wata k'ofa yanufo motar, gaba d'aya mamaki yahanani kwakwkwaran motsi harya k'araso.
Mai taxi yafito ya risina ya gaidashi, sannan yace nagama aikina Oga.
Murmushi Muftahu yayi, sannan ya lek'a Munaya dake barci kashir6an ta glass, janye kansa yayi sannan ya zaro wayarsa daga aljihu yay kiran wani.
“Umh yalla6ai akwai 'Yar matsala fa, dan barci takeyi sosai, kona d'akkota”.
Da sauri yace “No ina zuwa, amma wannan driver dayay aikin yabar wajen, dan bana buk'atar ya ganni”.
Murmuahi Muftahu yayi, tare da fad'in “angama ranka ya dad'e”.
Muftahu ya sallami drivern daya kawo Munaya, yace zai kirashi ya maidata zuwa anjima, yaje yabar motar anan.
“babu damuwa Oga, saina jika”.
Bayan tafiyar driver Galadima yafito, dama duk yana kallon abinda ke faruwa ta window.
Taku yake cikin tsantsar nuna jinin mulki dake yawo ajikinsa, ga wata izza ta zamowarsa cikakken namiji mai isashshiyar lafiya. fusakarnan babu walwala kamar kullum, ahaka ya k'araso wajen motar, Muftahu ya bud'e masa murfin inda Munaya ke kwance tana kwasar barcinta.
Kallonta yayi na tsayin mintuna uku, sannan ya janye idonsa ya rankwafo da kansa cikin motar, saida yad'an cije lips d'insa sannan yasaka hannayensa biyu ya tallafota ahankali ya fito da ita, tamkar 'Yar baby haka ya d'akkota acikin hannayensa, sai wani kuma d'aure fuska yakeyi yana kauda kai, kaikace anmasa dolene ya d'auketa.
Hannu Muftahu yasaka yatoshe bakinsa saboda dariyar dake Neman kwace masa.
Wai yau Galadima gudane d'auke da mace a hannu, mutumin da ko kallon mata bai cika yiba, inkaga yana walwala ko dariya wa mace to Momma ce ko aunty Mimi.
Jakarta ya d'auka shima yabi bayansa.
Ya iske harya shinfid'eta a doguwar kujerar dake falon, yana gyara hannun rigarsa daya nannad'e yana jan k'aramin tsaki, ganin Muftahu na murmushi saiya kuma had'e fuska, Muftahu ya ajiye bag d'in yana had'iye dariyar da k'yar saboda gudun yin laifi.
Hannu yamik'ama Muftahu.
Muftahu yabashi handkerchief d'in daya zaro a aljihu, rankwafowa yayi kanta ya d'ora Handkerchief d'in bisa hancinta, tsayin minti 2 ya janye.
Tari tafarayi, saikuma ta fara k'ok'arin bud'e idanunta tana lumshewa, Muftahu ya mik'o masa gorar ruwa mai d'an sanyi.
Cikin hannunsa ya tsiyaya kad'an ya shafa mata a fuska, ahankali ta fara bud'e idanun ta, shikuma yaja da baya yakoma ya zauna bisa kujerar mai zaman mutum d'aya.
d'ora k'afa yayi d'aya kan d'aya ya jingina kansa jikin kujerar ya lumshe idanu, saika rantse idonsa arufe suke, amma ya zubasune akan Munaya dake ta mutsu-mutsun tashi zaune.
Da k'yar ta iya tashi ta samu ta jingina da kujerar tana k'arema falon kallo, yayinda hawaye ke zirara a kumatunta.
Ruwa Muftahu ya mik'a mata, babu musu ta kar6a dan wata kishirwa takeji, tunda tafara shan ruwan bata ajiyeba saida ta shanye tas, nan wata zufa tafara karyo mata kuma.
Mik'ewa Muftahu yayi yak'ara gudun AC n.
Ahankali zufar tafara tsanewa, saikuma tad'anji k'arfin jikinta, Muryarta na rawa alamun kuka tace, “Please Ku suwaye? miyasa kuka kawoni nan? dan ALLAH kuyi hak'uri karku cutar dani, karku lalatamin rayuwa dan girman ALLAH, Ku tausayama mahaifiyata, damuwar damuke ciki kad'ai ta ishemu, wlhy daku keta mutuncina gwamma Ku kasheni yafimin sauk'i”.
Daga Muftahu har uban gayyar kallonta kawai sukeyi, ita ko kad'anma bata gane Galadima ba, saboda yayi sama da fuskarsa.
Muftahu ne yace “ki kwantar da hankalinki, kuma ba abinda yasa muka d'akkokiba kenan”.
“to miyasa kuka d'akkoni? bawan ALLAH, mina muku?”.
Muftahu ya juya ya kalli Galadima, amma saiyaga ko motsawa baiyiba, bashima da niyyar tanka musu.
Itama Munaya saita maida kallon nata ga Galadima, a kuma lokacinne yad'ago kansa zai gyara zama.
Wata razananniyar k'ara Munaya tasaki saboda tsorata, da Sauri Galadima ya toshe kunnensa, shima tsawar ya Daka mata wadda tasakata nutsuwar dole.
“k!!! Dalla karki ciremana dodon kunni!!!!”.
Dole Munaya tayi shiru jikinta na 6ari da k'yarma.
Yaja wani wawan tsaki, tare da janye hannayensa daga kunnensa yana harara Munaya. “k wace irin shashashace ne?”.
Sukda halin da take ciki saida ta watsa masa harara, amma bata iya cewa komaiba.
Hannu yakai tamkar zai maketa saikuma ya FASA, komi yatuna oho.
Komawa yayi inda yataso ya zauna, ya maida k'afafunsa yay crossing d'insu.
Shi dai Muftahu yana kallonsu yakasa cewa komai, bakajin motsin komai saina shashshekar kukan Munaya Dana k'arar AC.
Cikin kuka tace “minamaka kasa aka kawoni nanan? ko sokake kakuma jamin wani sabon 6atancin bayan Wanda yafaru abaya? wane Abu na tare maka waishin aduniyarnan dan ALLAH bawan ALLAH?”. takuma rushewa da kuka mai tsuma rai.
Bakinsa ya ta6e a zuciyarsa yake fad'in daganin yarinyarnan akwai tsiwa dai, saikuma uban tsoro kamar farar kura. banza yamata, azahiri idonsa a lumshe suke, amma kuma abad'ini yana kallon Munaya ne, kukanta Neman saka masa ciwon kai yakeyi, dan haka yay maganar cikeda izza da mulki.
“kinutsu muyi abinda ya kawomu, inba hakaba zaki kwana anan gidan ne”.
Da Sauri Munaya ta share hawayenta, “indai kukane na daina wlhy, kayi hak'uri ka sanarmin, dan ALLAH ka maidani gida kafin hankalin innarmu ya tashi”. tak'are maganar da share hawaye.
Dariya taso bashi amma saiya gimtse, saikace ba itace tagama tsiwa ba yanzun.
Muftahu dai kasa hak'uri yayi saida yad'an dara, Galadima ya balla masa harara, hakanne yasashi yin shiru ya had'iye dariyar.
“kin shirya tafiya kenan?”. ‘galadima yafad'a tamkar an masa dole sai yayi maganar’.
Munaya tace, “wlhy na shirya ranka ya dad'e”.
Yace “good girl” yana ta6e baki.
“ki fad'amin waye yasaki aikin nan?”.
Cikeda rashin fahimta Munaya tace, “wane aikin?”.
Shiru Galadima yayi bai tanka ba, sai Muftahu ne yaymata bayani dalla-dalla akan abinda yafaru a plaza kwanakin baya”.
Cikeda k'unar zuciya Munaya tace “ni babu Wanda yasakani, saima tozarci da hakan ya jawo mana muda mahaifiyarmu, bansan komaiba, amma tunda al amarinan yafaru muka kuma tsintar kanmu a k'unci, kullum da irin abin kuka dazamu gani agidanmu, yanzu haka akan waccan abin maganar aurena sau biyu tana lalacewa, yanzu haka satina guda kenan da baro asibiti saboda tashin hankalin dana shiga a dalilin fasa aurena da cin zarafi dana fuskanta daga Wanda yafasa aurena nawa, wlhy Ku yarda dani bansan komaiba”.
Muftahu ya juya yana kallon Galadima da idonsa ke a rufe, amma yana sauraren Munayar.
Kusan mintuna 3 sannan ya bud'e idonsa, akan Munaya ya zubasu, bazata iya jurar kallon kwayar idonsa ba dan haka tayi azamar janye nata, shima janye nasa yayi ya gyara zamansa. “kince babu hannunki? amma miya kaiki plaza a wannan time d'in daya kamata duk yarinyar kwarai tana gidansu?”.
“Muna bikine, bayan munkai amare mun dawo sai fu'aad yamatsa akan saimun shiga, ba dan nasoba nayarda, kuma bani kad'ai baceba, harda 'yan uwana su uku”.
“waye shi Fu'aad d'in?”.
“Saurayinane, awajen bikin muka had'u dashi”.
da sauri Galadima yace “miye kamaninsa? kuma ya kukayi dashi bayan abin ya faru?”.
A nutse Munaya tabasu labarin komai, sannan ta zano musu kamannin Fu'aad dalla-dalla, danma bawani kallon tsaf tamasa ba a cikin kwana biyun.
Muftahu yace “kozamu iya samun Horton shi Fu'aad d'in?”.
“banida hotonsa, dan bai yarda munyi ko photo d'aya ba awajen bikin, amma zamu iya samu a video d'in da akayi maybe awajen dinner? ”.
“galadima yace “a ina zamu CD d'in yanzu?”.
“gaskiya wannan shine mai wahala, dan bansan taka maimai cikin angunan waye yasaka ayiba”.
Galadima ya cije lips d'insa da k'arfi, sai kace zai hudasune.
Kusan mintuna 3 kowa baice komaiba, sai can munaya tace “kunji na fad'a muku gaskiya, Ku maidani kafin afara nemana”.
“zamu maidaki bisa sharad'i guda d'aya”. ‘cewar Muftahu ’.
“wane sharad'ine?”. ‘Munaya ta tambaya’.
“Sharad'in shine zakuyi auren 1year keda Galadima”.
Cikin zaro idanu waje munaya tace “kamar ya? ban fahim cekaba fa?”.
“ina nufin Auren yarjejeniya zakuyi na shekara 1 ko 2, ta wannan hanyarne kawai zamu iya kamo bakin zaren, sannan kekuma zaki sama ma iyayenki kwanciyar hankali, nanda kafin adadin da aka d'ibama auren yacika kinga komai ya wuce, saiya sakeki kiyi idda ki sami Wanda kikeso sannan kuje gida a d'aura miki aure dashi, Galadima ma zai iya sawa har auren a d'aura muku, daga baya sai kuje ya warwarema iyayenki komai, yakika gani?”.
“tabd'i, wannan wace irin maganace saikace labarin Novels ko films? to tayayama za'ayi hakan yafaru? bayan nama sanarma iyayena banida wata alak'a dashi”.
Murmuahi Muftahu yayi, yace “dan wannan duk mai sauk'ine, kedai amincewarki kawai muke nema”.
“amma dai kun maidani wawuya wlhy, to ban aminceba, gara na dawwama banyi aureba ai”.
Baki Muftahu ya bud'e zai k'ara magana Galadima ya d'aga masa hannu alamar yayi shiru ya barta.
“kinga tashi kije kawai, amma wannan maganar tazama iyamu ukunnan, idan najita awani waje saina zubar miki da hanjin ciki waje, duk shawarar dakika Yanke da zuciyarki zaki iya nemanmu daga nan zuwa kwana biyu kawai”.
Da sauri Munaya tazaro idanu waje tana kallon Galadima.
Harara ya zuba mata yace “karki cinyeni”.
Baki ta zun6ura gaba tana k'unk'uni, bayajin mitake fad'a, sai motsin la66anta kawai yake gani.
Sai da aka rufemin iso sannan aka baro gidan dani, bankuma kwanceba saida motar ta tsaya, Wanda yake tare dani yacire k'yallen sannan yace na fita.
Ko kallonsa banyiba saboda tsoro nafice amotar da sassarfa.
Gudu-gudu sauri-sauri na Isa gidanmu, mutane sai kallona sukeyi, ALLAH ma yasoni babu kowa a tsakar gida, inaga matan gidan duk sun shige sallar magriba yaran kuma basu dawo daga islamiyya ba.
A 6angarenmu ma innarmu na d'akinta, hakanne yabani damar shigewa d'akinmu wuff, na iske Munubiya na barci itama, na sauke ajiyar zuciya mai k'arfi ganin ALLAH ya tsareni babu Wanda ya ganni, kayana nacire daketa kamshin turaren Galadima, bayi nashige nida kayan, nayi wanka sannan suma na wankesu na shanya a bathroom d'in.
Harna fito Munubiya bata tashiba, nayi sallar magriba sannan nafito wajen innarmu.
Da mamaki take kallona, “yoni har ina shirin kiranki naji lfy baki dawoba had dare yarufa?”.
Zama nayi ina murmushin yak'e, dan abinda yafaru tsakanina dasu Galadima d'anzu ya min kane-kane a zuciya. ganin abin nakeyi kamar a mafarki. “ayya innarmu ai tun d'azun nashigo, lokacin kina salla, harfa nayi wanka ma nad'an huta. tace tana gidaki, yaya jikin Munubiya?”.
Jikinta Alhmdllh, tad'an watsa ruwa takoma ta kwanta bayan taci d'an abinci”.
To Almdllh, ALLAH yak'ara afuwa.
Amin innarmu ta amsamin, daganan muka koma hirar gidan Inna lami.
Munkai tsawon lokaci afalon muna hira da innarmu, sai dai nifa bama fahimtar hirar nakeba, dan fili kawai nakeson samu nayin tunanin maganar su galadima.
★★★★
Tun bayan tafiyar Munaya Galadima yakoma kan doguwar kujerar yay kwanciyarsa tamkar mai barci.
Muftahu dake kallonsa yace, “Amma miyasa kace ta tafi? batareda ta bamu gamsashshiyar amsa ba kuma?”.
Shiru Galadima bai amsaba tsawon mintuna uku, sai zuwa can yabud'e idonsa yana kallon Muftahu, baki yad'an ta6e “karka damu kanka, tama yarda, amsa ce kawai bata bamuba, itama kuma zata bayarne, tuni naga yardarta cikin kwayar idonta, akwai abinda take shakku akansa shiyyasa tak'i amsa mana”.
Kai Muftahu ya jinjina kawai, yasan tunda Galadima yafad'i haka to hakanne kuwa, amma sai yace “to amma bamu bata koda number ba, tayaya zata sanar damu amincewar tata kenan?”.
Murmushi kawai Galadima yayi baice komaiba.
Hakanne ya tabbatarma Muftahu murmushin Galadima shine amsar tambayarsa. Daga nan bai sake cemasa komaiba shima.
Falon yay tsit.
★★★★
Gaba d'aya a kwanaki biyunan banida wani sukuni, tunanin maganar yak'i barin zuciyata, a kowacce dak'ik'a zuciyata tunzurani takeyi akan Na amince kawai, dan banida wata mafita sai wannan, ni kaina inason sanin Wanda ya aikata mana wannan abun, sannan bana fata sauran 'yan uwana suyi aure su barni a gidannan, hakan ba k'aramin tozarci zai zamarminba, ga Munubiya tadage akan innarmu ta sanarma Abba itama ad'aga bikinta har saina samu miji nima ahad'a ni da ita, na nuna mata 6acin raina akan maganar amma abanza, tanuna Sam ita tana a kan bakanta, nikuma harga ALLAH ba zanso hakan ta kasanceba.
Ita kanta innarmu nakula danne zuciyata kawai takeyi akan fasa aurena, amma tana cikin matsananciyar damuwa.
Yanzu yazanyi kenan? Na amince ko karna amince? gashi ya gargad'eni akan kadda Na nemi shawarar kowa, ni kaina nama kasa sanarma koda Munubiya, kuma kullum cikin tanbayata take mike damuna? duk da ita zatonta akan maganar Haidar ne har yanzu nake cikin damuwar.
Yau dai kwanaki biyu kenan da faruwar abin, har yanzu kuma nakasa tsayawa a matsaya d'aya.
Kusan tashin hantsi muna tsakar gida a baranda muduka 'yan matan gidan, kowa da hidimar dayakeyi, sai wasu daga cikin k'annenmu dake wasa agefenmu, iyayenmu kuma Na daga can k'arshen barandar suma kowa da hidimarta, innarmu ce kawai babu tana gidan mama Rabi'a taje duba feena da jikinta yad'an motsa.
Tsayuwar mota mukaji a k'ofar gida, yara suka tafi da gudu dansuga wanene? azatonsu cikin su Dady ne.
Mintuna baifi 10 ba saigasu suna shigowa da ledoji, saikuma ga Zarah tashigo cikin kwalliyar kece raini, tana taku d'ai-d'ai, daka ganta kaga mai yaron ciki, cikeda muran muka hau mata sannu dazuwa, itako saiwani ciccijewa take tana kuma Jan kai, ita adole matar manya.
Abin kallo bai k'areba saida mamansu yaa Hameed ta iso da d'an gudu ta rungume Zarah a jikinta, duk mukai galala muna kallon wannan sabon salo.
“masha ALLAHU Zarah sarkin haske, kinganki kuwa, da anganki anga matar manya yarinyata, kai ai aure Ni'ima ce babba, duk wacce ALLAH yabama 'yarta miji matan gidannan ta godema ALLAH, Dan wlhy yana sonta”.
Caraf Momy Hadiza ta kar6e da fad'in “wlhy kuwa Yaya, ai babu babban bak'inciki irin kanada gandamemiyar budurwa a d'aki tayi kwantai takasa auruwa, aimu sai godiyar ubangiji wlhy, babu ta inda ni'ima bata saukar manaba, Zarah zoki zauna ki huta kinji 'yar albarka”.
Maman safara'u da gwaggon haleema da maman su Fiddausi suka kwashe da dariya.
Kowa yasan damu ake wannan gugar zanar, amma sai mukayi murmushi kawai bamuce komaiba, maman fauziyya ma batace komaiba, nama godema ALLAH da innarmu bata nan balle ranta ya 6aci.
Tsam namik'e nabar wajen zuciyata Na suya, Na danne kukan dake shirin tahomin...
Maman Safara'u tace, “to yanzu ke bazaki iya danne zuciyarki ba saikin nuna hasaadarki a filin ALLAH?, to Ashe ranar auren 'yan uwanki mutuwa kuwa zakiyi?, dan kina gani za'a d'auke kowacce abarki agidan.
Wani k'arfine yazomin a zuciyata, Na had'iye kukana, najuyo ina kallonta ido cikin ido, wani murmushin takaici nasaki, sannan nace “maman Safara'u ke uwace agareni, sannan innarmu takoya mana tarbiyyar girmama kowacce mace agidannan, badan hakaba dana fad'a miki maganar dabazaki ta6a mantawaba, kuma ba hassadar tasani tashiba kamar yanda tunaninki yabaki, natashine Na d'aukama Zarah ruwansha, naga tashawo rana kuma babu Wanda yayi yink'urin bata”.
Ina gama fad'ar haka nabar wajen. tsit banji kowa yasake maganar ba, bansan miyasa ba, maganar tawace tasakasu yin shiru kokuwa oho.
Ina shiga falonmu Na fashe da kuka, anzo ga6ar da kawai zan amince da buk'atar Galadima, insha ALLAHU aranar datake fad'ar za'a tafi abarni, aranar nima zanbar gidan, Na gwammace nayi auren shekara d'ayan nafito.
Tunanin tawace hanya zanbi Na fad'ar musu Na amince na farayi, dan basu bani number ko wata hanyaba dazan iya nemansu, gashi kuma bazan iya gane gidan dasuka kainiba.
Tunawa dawata farar takarda nayi, wadda nagani a bag d'in dana fita da ita a ranar, kuma nasan ni bani Na ajiyeba.
Da Sauri Na d'auki bag d'in na zazage, saiga takardar tafad'o, na d'auka na bud'e, Number wayace ajiki kawai.
Jikina har rawa takeyi na d'auki wayata na kwafe number, sai kuma nakasa kira, na fara zagaye d'akin.
Motsi naji kamar na tafiya, da Sauri na shige bathroom d'inmu dan nasan Munubiya ce.
fanfo na kunna yanda zata d'auka wanka nakeyi.
Sha warar tura massage kawai na yanke. dan haka na rubuta
*_“na amince inhar bazai zama ka wulak'anta rayuwa taba”._*
Haka kawai natura masa na cire kayana nafara wankan gaskiya...........✍🏼
⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀time d'in wasa yafara.🤸🏻♀
*_Ya ALLAH ka gafartama iyayenmu_*👏🏻😭*_Typing📲_*

*_Ya ALLAH ka gafartama iyayenmu_*👏🏻😭
*_Typing📲_*
*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
👉🏻1⃣7⃣
.........Cikeda girmamawa yace, “Ranka ya dad'e barka da dare?”.
“barkan ka dai Muhammad. dama kashigo k'asar kenan?”.
Gabansa yad'an fad'i, danshifa yama manta mai martaba baisan yazo k'asarba, dakiyar dole ya aro yace, “wlhy kuwa nashigo d'azun yin wani aiki, amma gobema idan ALLAH ya kaimu zan koma”.
“tofa, gobe gobe? kuma gashi inason ganinka a goben”.
d'an jimm yayi, irin tamkar baisan komaiba, cikeda shakku yace, “ranka ya dad'e lafiya dai ko?”.
“lafiya k'alau, wata muhimmiyar magana nakeson muyine”.
“to shikenan, zanshigo insha ALLAH ”.
“to madalla saina ganka”.
Dafe kai Galadima yayi yana mamakin kansa, anya kuwa baima kansa d'aurin gorobo? koda yake idanfa yayi hak'uri shekara 1 ne ko 2 kacal, inma komai yafito kafin cikar shekarar zai sawwak'a matane, yad'an murmusa sannan yakoma ya kwanta abinsa cikeda tunani barkatai.
★★★★★
Rashin reply d'in Galadima ya dameni, haka dai naita danne zuciyata dankar innarmu da Munubiya su fahimta, nacigaba da harkokina tamkar banida wata damuwa a zuciya, saima sallar dare damuka fara dagewa da tashi nida Munubiya, gakuma azumin damuka tashi dashi yau litinin.
Duk da innarmu ta fahimci inada damuwa batacemin uffanba, saidai tausayina na damun zuciyarta, tana dannewane kawai.
Munubiya kam tsaf tagama fahimta ta, amma itama saita nuna bata fahimci komaiba, taje tasamu innarmu da maganar son a d'aga bikinta again.
“munubiya ba wannan yakamata muyiba, addu'a yakamata muyima 'Yar uwarki, idan da rabo saikiga ALLAH ya kawo mata miji a cikin watanni 2nan dasuka rage kinji. nima nasan tana acikin damuwa, amma tana dannewa a zuciyarta saboda farin cikinmu. addu'ar dazamu mata itace tsantsar k'aunarta a garemu”.
“shikenan innarmu, insha ALLAH zamu kuma dagewa da fad'ama ALLAH, itama ALLAH ya kawo mata ta hanyar da batayi zatoba, ya sakanka mata fiyeda sadaukarwar datayi, innarmu nasan sadaukarwar da 'Yar uwata tayine yasakata a wannan halin, ta sadaukar da farincikinta saboda ni, mizanyi na biyata nikam”.
Murmushi innarmu tayi, tace, “addu'a”.
★★★★★
Washe gari yatashi ya shirin tafiya masarautar su Momma, Harun yakira yace ya nema masa ticket.
Cikeda mamaki Harun yace, “yaushe kashigo k'asar Galadima?”.
K'aramin tsaki yaja, dan shifa yama manta Harun baisan da zuwansa ba, Link d'in hannun rigar milk d'in shaddarsa yake k'okarin sakawa, cikeda dakiya yace, “jiya nazo da daddare, kuma inagama yau zan koma”.
“tofa, amma baka cikin masarauta?”.
“no a hotel Na sauka”.
“ok barato a nema ticket d'in, sai muzo mu d'aukeka”.
“karka damu harun, banason kowa yasan nazoma, muhad'u dakai kawai a airport ”.
Koda suka yanke wayar sai yaja tsaki, gaba d'aya yakoma mak'aryaci, abinda yatsana arayuwarsa fiye da komai kenan (k'arya) amma sai gashi shi yana zundumata, “Astagafurullh” yashiga maimaitawa a zuciyarsa.
Tsaf yafito cikin shadda milk color (nakula yana k'aunar milk) d'inkin rigar 3quarter, harda su hula, yayi k'yau sosai, yafito ainahin sa na cikakken bahaushe kuma basarake, ya fesa turaraensa Na kullum, komai nasa dayazo dashi ya had'a a waje d'aya. sannan yakashe kayan wutar bedroom d'in.
Afalo ya iske Muftahu zaune yana jiransa, yad'anyi mamaki amma sai bai nunaba, yabashi hannu suka gaisa.
Muftahu yace, “zaka dawo ta nan kenan?”..
Kai Galadima yad'aga alamar a'a, sannan yanufi kayan wutar falon yafara kashewa. saida yagama komai sannan ya kalli Muftahu alamar suje.
Murmushi kawai Muftahu yayi, danya lura yau miskilawanne aka.
Sun isa airport, lokacin shima harun harya je, mamakine ya kama harun Dan ganin Galadima tare da Muftahu, shima yanzu yana mamakin yanda Muftahu ke kuma kusanta kanshi da Galadima, baice komaiba yabashi hannu suka gaisa kamar yanda yabama Galadima.
Harun yanason suyi magana da Galadima amma ga Muftahu a wajen, sai kawai yashare akan sayi a waya kawai.
Basu wani dad'e a airport d'inba jirgin su Galadima yatashi.
★★★★
Yau hankalin kowa a tashe yake agidanmu saboda gwaggo Safiyya da aka kawo batada lafiya, dayake ba'anan kusa damu take aureba, tanacan wani gari daban, tun lokacin bikinsu yaa Hameed tamasu Abba complain akan batajin dad'i, amma kunsan maza darashin d'aukar Abu serious, sai basu maida hankalinsuba.
Ita kuma kunya tahanata kuma musu maganar, har aka gama biki ta tafi, ashe baiwar ALLAH ciwo nata cin jikinta babu Wanda yasani, tun tanayi a tsitsaye har takai ga kwanciya, yaranta sun kaita asibiti amma basuga wani canjiba, hakanne yasa suka maidota gida, Dan aganinsu dai su Abba sunfi mahaifinsu k'arfi.
Aiko suna isowa babu 6ata lokaci aka wuce da ita asibiti.
Dan danan aka fara bata taimakon gaggawa.
Muda innarmu ne kawai da innaro a asibitin, amma matan gidanmu babu wace tabimu, kusan mudasu baba k'arami muketa shiga da fita a asibitin dan ganin komai ya dai-daita.
Kusan yamma saigasu Safara'u lokacin ma gwaggo Safiyya tana barci, yaranta duksunyi jigum-jigum da innaro saboda tashin hankalin dasuke ciki.
Har dare ba'abar kowa yashiga wajen taba, sai su Dady kawai, ganin dare yayi akace mu muje gida kawai.
Haka muka tafi akabar innaro da aunty habiba d'iyar gwaggo safiyyar ta uku, itama tayi aure amma tafito, yanzu zawarci takeyi. saikuma yaa Anas da aka barmusu saboda ko wani Abu zai taso.
★★★
Tunda yafito daga jirgi ya hango tawagar masarautar kakannin nasa, yasan tarbarsa sukazoyi, inhar zaishigo haka sukeyo gayyar tarbarsa, saikace wani bak'o daban, gefe yayi da fuskarsa dankarsu gansa, sashen motocin da akan d'auka drop ya nufa, duk manyan motocine da aka tanada dama domin irinsu, d'aya yabud'e da Kansa yashige da sauri, alamar yayma driver d'in suje.
Tacikin glass yake kallonsu yana murmushi, yanda suketa d'aga kai nason hangosa, suna fita daga airport d'in ya kwantar da kansa ajikin seat ya lumshe idanunsa yana tunanin wane hukunci mai martaba zai yanke akan maganar, shin ya amincene? Kokuwa?.
Driver yace, “oga ina muka nufa?”.
Bai bud'e idonsaba kuma bai d'agoba, yace “gidan sarki”.
Ta madubi driver n ya kallesa, “yalla6ai ko kaine ma dai akazo tarba daga masarauta?”.
Murmushi kawai yayi batareda yace komaiba.
Jin bai amsaba sai driver yakama bakinsa ya tauke shima.
Ganin shine yasa dogarai suka bari aka shigar dashi har cikin masarauta, tunda yafito bayi da hadimai keta zubewa suna kwasar gaisuwa, hannu kawai yake d'aga musu, fuskarsa ad'an sake take, bai d'aureba baikumayi murmushi ko dariya ba kai tsaye.
Tuni an kar6i kayansa an nufi sashin inno dasu, shikuma yanufi fada, Dan yasan yanzu Sarki suna fadanci.
Cike fadar take da 'yan majalissar Sarki anata fadanci, bayan an masa iso yashiga da sallama, nanfa dogarai suka fara zuba masa kirari.
Hannu kawai ya d'aga musu ya rissina yana mik'a gaisuwa ga Sarki.
Sarki da fuskarsa tacika da fara'ar ganin jikan nasa ya amsa cikin lumshe idanu.
Nan dogarai suka d'au da fad'in “sarki ya amsa maka sarkin gagara badau na gobe, an gaida magajin sarki, galadiman gagara badau, ALLAH yabaka zamani irinna sarki gagara badau.
Galadima Yakuma rissinawa ya mik'a gaisuwa ga 'yan majissar sarki, suma cikeda fara'a suka amsa, kowa yasan irin tsantsar k'aunar da sarki kema jikan nasa a masarautar.
Atake anan sarki ya sallami kowa, fadanci yatashi saikuma gobe idan ALLAH ya kaimu, yau yanada ganawa ta musamman da jikansa.
Haka kowa yatashi yana musu addu'ar kasancewa cikin aminci.
Tareda Galadima sarki yashiga cikin gidansa, hannunsa Na rik'e da Na Galadima, ba sabon Abu bane hakan a masarautar, duk Wanda yakwana yatashi acikinta yasan matsayin Galadima azukatan masu masarautar.
Akatafaren falon sarki suka yada zango, babu dad'ewa da shigowarsu saiga jakadiya da kuyangi uku, kowanne d'aukeda babban tire, bayan sun dire komai suka zube suna kwasar gaisuwa wa sarki, sannan suka gaida Galadima.
Jakadiya ma ta rissina ta gaida Galadima damasa barka da zuwa masarautarsu.
Bayan fitarsu Galadima yakuma risainawa a girmame ya gaida sarki kakansa.
Cike da murmushi sarki ya amsa yana kamo hannunsa, “Muhammad Sameer! kana lafiya”.
“Alhmdllh ranka ya dad'e”.
“Masha ALLAH, ya kabaromin Zeenah ta da jikin babanka da 'yan uwanka kuma su Haneefa?”.
“Momma lafiyarta lau, hakama jikin Abie Alhmdllh, suma su aunty mimin haka”.
“to Alhmdllhi, ALLAH yacigaba da jagorantar lamuranku ya albarkaci rayuwarku ta gobe da jibin jibima”.
Murmushi Galadima yayi yana amsawa da amin.
Sarki da Galadima tare sukaci abinci, (tun yana k'arami dama idan yazo gidan hakance ke faruwa tsakaninsu) Sunci sun k'oshi sukayi hamdala ga ALLAH.
babu wani 6ata lokaci sarki yashiga masa bayanin kiran nasa akan maganar da Fateema (mom) tazo masa da itane jiya, shima ya zauna yayi nazari yagane hakan shine dai-dai, Galadima ya auri Munaya.
tur6une fuska Galadima yayi tamkar baisan komaiba, yace “ranka yadad'e ka gafarceni, ammafa ni bata minba ai”.
Sarki yay murmushinsu Na manyan k'asaitattun masu ji da mulki, “basai tayi makaba Muhammad, domin sanda Na aurama babanka Zeenah itama bai mataba, amma saboda biyayya dakuma tausayin d'iyar 'Yar uwarta ta amince tamin biyayya, to kaima hakan nakeso gareka, ka amsamin da to kawai saimu zauna lafiya, kasan magana biyu ba halina baceba ko”.
Jinjina kai Galadima yayi yana kuma tankwashe k'afarsa, cikeda girmamawa yace “ALLAH ya huci zuciyarka ranka ya dad'e, Na amince da za6inka, ALLAH yabani ikon rik'ewa”.
Cike da tsantsar farinciki Mai martaba ya rik'o hannun Galadima, “Muhammad ALLAH shiyi maka albarka, ya tsareka dadukkan sharri, ALLAH yabama mahaifinka lafiya kaji”.
“amin ranka ya dad'e, ngd sosai ”.
Daga nan hira suka cigaba dayi cikin tsantsar soyayya da k'aunar juna, kowanne yanajin d'an uwansa sosaih a ransa.
Kusan atare suka yini, inno tun tana zuba idon shigowar Galadima harta hak'ura. Galadima bai shigo wajenta ba sai bayan sallar magriba.
Tundaga k'ofar sashenta hadimai keta kwasar gaisuwa, tuni labarin tahowarsa ta iske inno, hakan yasa ta k'imtsa da k'yau, ta sallami bayinta masu mata hidima.
Fuskarsa d'auke da k'ayataccen murmushi ya k'araso falon, bai zauna ko inaba sai jikin kakarsa, oh my sweet inno I miss you so much wlhy”.
Kunnensa tad'anja kad'an, cikeda tsokana tace “miskili kafi mahaukaci ban haushi, aini harna fara shirin yo bikonka daga turakar mai martaba”.
Yayi 'Yar dariya yana fad'in “tuba nake ginbiyar papi”.
“ja'irin kaya, bazaka canjaba dai? ya kabaro iyayen naka da 'yan uwanka?”.
“kowa lafiya lau ranki ya dad'e”.
“to Alhmdllhi ”.
Nanma hirarce ta 6alle tsakanin kaka da jikanta, kan mace me nanma an cika masa gaba da kayan itatuwa, shikuma yana zubama inno shagwa6ar daya saba tana biye masa.
Masu jiran Galadima kuwa a airport saida sukaga kowa yagama fita ajirgi babushi sannan wani dogari yakira sarkin fada yake sanar dashi sufa basuga Galadima ba.
Sarkin fada yace “yo kunacan kuna shashanci yaza'ayi Ku gansa, shi harma sun shige cikin gida da sarki ”.
'yan uwansa ya sanarmawa suka tattaro suka dawo masarautar.🤣
Dole a nan masarautar ya kwana, washe gari ya zagaya duka sashen sauran matan sarki ya gaidasu a mutunce. suma dai sunmasa tarbar mutunci kamar yanda suka saba, duk da dai taciki Na ciki. Sannan sai sassan iyayensa yayun momma da k'annenta, dukda dai bako ina yashigaba.
Yanzunma tare sukayi karin kumallo da maimartaba, sannan suka fita fada tare, da Galadima akayi fadanci yau, yana gefen adalin kakansa.
Washe gari da safe ya tattara inasa-inasa ya cane India, yabar tsofin da kewarsa, shima yatafi yana kewarsu.
********
Gwaggo Safiyya tacigaba da samun kulawa sosai, dukda dai tanad'an jin jiki, kullum matan gidanmu sukanzo sau d'aya, muma dai makaranta tasa bama yini a asibitin, amma kullum da safe mukanzo mu kuma dawo da yamma.
Matan gidanmu kam jarabar innaro tasakasu k'ok'arin zuwa kullum, dan tace wlhy duk Wanda bata zuwa saitayi Dana sanin saninta.
Wannan furuci ya d'an tsoratasu, dan kowa agidan yasan wacece innaro, idan kaga mutuncinku ya d'ore to kana cinna mata 'yan canji ta k'ark'ashin k'asane🙊, amma kana hanata gobe bazai hana ta karta maka rashin m ba🤣. (Ho innaro mu ta mutunci🤸🏻♀, ina yinki over ginbiyar Malam faruku😜🙊)
⛹🏻♀
Abin yafara tsoratani ganin har sati 1 dayin maganarmu dasu Galadima amma babuko labarinsu, tun ina saran yau gobe har na daina lissafin ma, ganin zan saka kaina a damuwa nacirema zancen a raina gaba d'aya, domin Na gama fahimtar maganar Galadima da abokinsa k'aryace, maybe ma mafarki nayi naketa shirmena kawai.
A tsaitsaye damuwa tafara ramar dani a tsaye, sai idanuwa da dogon hanci.
Tun ina daurewa har Abu yaso yaci tura, ciwon kai Dana k'irji suka fara zama abokaina.
Ranar data kama sati biyu cif saiga bak'i su Abba sunyi, babu Wanda yasan daga ina suke, kuma su Abba basuma kowa bayanin komaiba dangane da bak'in. saida sukayi kwanaki uku da zuwa sannan naji wai wanine yakawo kud'in aurena yana son abama d'ansa.
Lamarin yabama kowa mamaki, nanfa 'yan gidanmu suka hau dariyar mugunta wai kwantai dai ya tabbata kenan.
Gugar zanar dasuke tayine ya fusata innarmu, tasakama Abba kuka akan bata aminceba, yaza'ayi su d'auki aurena subama mutumin dabasu saniba, idan su sun gaji dani itafa tanason kayarta.
Lallashi duniya Abba yayi dan innarmu ta fahimta amma Sam tak'i saurararsa, wannan ne karon farko da yaga tsantsar fushinta.
Yarasa yazai mata, dan shima lamarin Na damunsa, yarasa minene yasakashi amincewa yabada auren d'iyartasa ga mutanen?, shi dai kawai tsohon yamasa kwarjinine wlhy, dan jiyay ko kad'an bazai iya musa masaba. dukda talakawane kamarsa, harma yana ganin yafisu abubuwa da yawa.
Lamarifa yayi tsamari a d'an tsakaninnan a gidanmu, dan innarmu takasa kwantar da hankalinta, hakama abbanmu, yayinda 'yan gidanmu sukejin Dad'i kamar su had'a fati.
Nikuwa uwar gayya ai ba'a magana ma, nakira number Galadima yafi sau 200 amma tak'i shiga ko sau d'aya, lokaci guda nagama fita hayyacina, 'Yar uwata kanta dukta lalace kamar itace cikin matsalar.
Innaro kam ciwon gwaggo Safiyya ne ya d'auke hankalinta, duk da dai su Abba sun mata bayanin kawo kud'in nawa, amma cikin halin ko in kula tace su basu kawai, idan sun barni agidan kuwa najawo musu abin kunyar dayafi nabaya, harma tashafi sauran kannena suk'i auruwa tamkar ni.
Wannan furuci ya Sosa zuciyar abbanmu, amma saiya danne saboda girman mahaifiya.
An sallamo gwaggo Safiyya da kwana biyu jikina ya birkice nima, dole aka kwasheni aka kai asibiti.....
*********
A 6angaren sarki kuwa bayan tafiyar Galadima da kansa yazo masarautar gagara badau, an masa tarba ta girmamawa domin shid'in babban abokine ga kakansu Galadima wato (marigayi sarki Abubakar na lll).
Mama Fulani kanta in kunga yanda take girmama sarki (Abdul'fatah idris) saikusha mamaki Ku d'auka ba itace mai ji da kanta d'innanba da tsantsar nuna sarauta(gaba da gabanta yo🥴).
Sarki bai 6ata lokaciba ya sanar musu abinda yazo dashi, ganin tsantsar farinciki nayi ga mafi yawan jama'ar gidan, dan hukuncin sarki Abdul'fatah yamusu dai-dai, koba komai an k'ask'antar da Galadima d'in, Wanda yadace ace an sama masa d'iyar wani mashahurin sarki ya aura, kodan sarautar da ake da yak'inin shine yakama ta ya gada.
Murmushi papi yayi, saboda ganin farinciki zancensa a fuskokin wasunsu, yasan tabbas dawata manufa suke wannan farinciki, amma hakan bai damesa ba, domin shi da k'yak'yk'yawar niyya yayi. maganar sarauta kuwa sune suke ganin bazai iyaba saida wata d'iyar babban sarki, amma shi yanada yak'inin ko d'iyar shugaban talakawan duniya koda baiwace agidan Galadima ya aura sarauta ta ALLAH Ce.
Daga baya ya tsara musu yanda yakeso Neman auren ya kasance, bawai zasuje musu da rigar mulki baneba, yanason suje amatsayin talakawa domin ganin tarbar dazasu samu daga iyayen yarinyar, daganan zai gwada yak'inin tarbiyar gidan da mutuncin iyayenta.
A masarautar sarki ya kwana, washe gari sukayi shigar talakawa shida sarki jalaludden k'anin mahaifin Galadima, sai wazirin papi dana sarki, saikuma k'annen mahaifin Galadima biyu sannan aka sami tsohuwar mota suka tafi aciki bisa jagorancin wani dogari da sarki yasa yamasa binciken gidansu munaya.
Abinda basuyi zatoba shi suka samu, domin tarba ta mutunci da girmamawa suka samu dagasu Abba, duk da suna kallonsu talakawa fitik harma da yak'inin sun fisu komai.
Hakan ya burge sarki Absul'fatah (papi) shi kansa sarki jalaludden lamarin ya masa dad'i. Sun bada kud'in gaisuwar farko data biyu naira subu 30 kacal.
Sai bayan tafiyarsu sannan su Abba sukaita mamakin kansu anya mutanen bada wani siddabaru sukazo musuba? Yazama ayi basu sansuba amma suzo su kar6i auren 'yarsu? sukuma su basu babu musu kamar sun gaji da ita. (Niko nace kwarjinin sarauta suka muku abba😜😂).
Can kuma dasu sarki suka tafi sunata yabawa suma, sarki Absul'fatah dad'i dukya gama cikasa, lallai Galadima yasamu tsatson daya dad'e yana masa fata da addu'ar samu.
Momma koda papi yakira yamata bayanin bataji komaiba, saima addu'a data masa da kuma nuna farin cikinta akan lamarin, koba komai zataga auren Galadiman ta, amma saida tayi hawaye data tuna za ayi auren Galadima babu mahaifinsa, kamar yanda akayi na Haneefa (Aunty Mimi).
Data sanarma Abie saiya fad'ad'a murmuahinsa, yayinda hawaye ke zirara ta gefen idanunsa, ALLAH sarki iko da falala, tun yaronsa na shekara 5 a duniya yake a wannan halin, gashi har zaiyi aure, yagodema ALLAH da wannan jarabawa shikam.
A satin papi yaje India ma da kansa, yaduba jikin Abie dakuma maganar auren Galadima dayayi musu, nanma saida Abie yay hawaye, amma sarki Absul'fatah yayta masa nasihar yawan hak'uri da kar6ar k'addara, ya nuna masa sunada yak'inin zaici ribar can.
Abie yana son surukinsa kuma aminin mahaifinsa sosai, dan duk lokacin dazaizo dubashi da irin salon nasihar dazai masa wadda zai k'ara tasirantar da imani a zuciyarsa.
Galadima kuwa sai wani basarwa yakeyi irin shifa abin bai d'ad'ashi da k'asaba, kuma bayason abin, aurenma dole za ai masa, haka yaytaima Abie korafi yana shagwa6a.
Murmushi Abie yay tayi yana lallaahinsa da idanun.
Cikin tsokana sauban dake d'ayan gefen Abie shima yace “yaa Sam to kawai ni abani kana, kaga na huta da zuwa tad'i k'ofar gidan kowa”.
Wata uwar harara Galadima ya maka masa, wadda tasaka Momma da auty Mimi da samha da jakadiya dariya, shi kansa Abie murmushine ya fad'ad'a afuskarsa.............✍🏼
Wannan shine yafaru 6angaren Galadima munaya bata saniba.
Guys kuje zuwa kawai, k'ila zuwa dare kujini da bonus⛹🏻♀⛹🏻♀
ALLAH yabama munaya lafiya.
Barka da juma'a.😄✋🏻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭👏🏻

👉🏻1⃣8⃣
..........A Asibiti gado suka bani, sunata fad'an yanda jinina ya hau sama, su mamakima suke yi 'yar k'aramar yarinya dani amma inada hawanjini, shin miyayi zafi haka?.
Su Abba dai kasa cewa komai sukayi, dan su kansu abin na yata6a zuciyarsu.
Wannan karonma Mama Rabi'a da Munubiya ne suka kwana a wajena, washe gari da yamma saiga 'yan gidanmu wai sunzo dubani, bamuyi mamakiba Dan munsan ba domin ALLAH sukazoba, kawai sunzo ganin kwafne.
Duk suncika d'akin da surutu akan wai suna mamakin miya samin hawan jini?. daga mama Rabi'a har Munubiya babu wanda yabasu amsa.
Doctor ne yashigo yace sud'an ragu wasu su fita baranda dan ALLAH, duk fita sukayi harda mama Rabi'a aka barmu iya mu yaran kawai, dansu Fiddausi duk hadasu akazo.
Ina daga kwance kan gado ina sauraren hirar dasukeyi, wai safara'u da Halimatu ne sukaje gidan su Siyama tai tamusu yatsina da d'aukar kai, saikace ba 'yan uwanta ba, mijinta yadawo sukayi shigewarsu suka barsu afalo har yamma sannan suka fito, mai makon tabasu hak'uri sai cewa tayi wai dama basu tafiba🤣.
Wannan abun daya faru shine yajawo rigima a gidanmu jiya da daddare, har saida su Abba suka tsawatar.
Murmushi kawai nayi Na gyara kwanciyata, a zuciyata ina fad'in maganinku ai, baku masu dangiba..........gabana yafad'i, saboda jin tamkar k'amshin turarensa. da sauri Na d'ago kai saboda jin su Fauziyya ma sunyi tsit daga surutun dasukeyi suna kallon bayanmu.
Wani yaam naji a raina domin ganin Galadima da tawagar dogaransa, sai wani dake gefensa amma ba muftahu bane, (Harun ne). Sanye cikin k'ananun kaya wad'anda suka fidda ainahin k'irarsa ta cikakken namiji, fuskarnan kamar kullum babu walwala.
Mu 4 ne kawai a d'akin, dan haka yana tsaye a gadon farko da alama tanbayoyi yakema matar dake jiyya a gadon. gani nai yasaki wani guntun murmushin gefen baki sannan ya kalli harun, bansan miya cemasaba nagadai yabaro wajen yana tunkaro gado Na biyu.
A hankali Na lumshe idanuna wani Abu Na tsikarar zuciyata mai kama da tsoro da rud'ani.
Sauran 'yan uwana kam sun zuba masa idanu tamkar zasu cinyesa, kowacce takasa furta komai a fili saida a zuciyarta take tattaunawa da yaba Galadima d'in.
Annanma yayi kusan mintuna hud'u sannan ya tunkaro gadon takusa damu, dan nice ta k'arshe. duk da akusa damu yake banajin miyake fad'a, saidai motsin la66ansa kawai nake gani, tabbas Galadima naji da Girman kai da mulki, kallo d'aya zaka masa ka tabbatar da tsantsar sarauta da mulki dake yawo a jinin jikinsa....... tunda naga yanufo inda nake sai kawai narufe idanuna gaba d'aya.
Su Munubiya duk suka risina suna gaidashi.
Hannu kawai ya d'aga musu yamatso jikin gadon danake.
Tsantsar mamakine ya bayyana a fuskarsa, yad'anyi kamar zai nunani da hannu saiya kuma fasa, su safara'u kam duk sun zubo mana idanu suga yanda za'a kwashe.
Munubiya ce cikin k'arfin hali tace “Munaya ki tashi ana miki magana fa”. daka ganta kasan a tsorace take maganar.
Shima juyowa yayi ya kalli Munubiyar domin jin kuma Muryata, maganar Muftahu ta fad'o masa arai dayace yaran twins ne, kuma ba'a iya banbancesu.
Suma Kansu dogaran NASA da Harun duk sunyi tsuru suna kallonmu, domin babu wanda baiga jaridarba a wancan lokacin.
Maganar sace tasaka kowa maida hankali a kansa, nidai har yanzun idona arufe suke, cikin basarwa da nuna halin ko in kula yace, “ya jiki?”. tamkar bayaso haka yayi maganar.
Nima cikin dakiya da shariyar kamar yanda yamin nabud'e idona nace “Alhmdllh”.
Kamar yanda yake tambayar kowa nima haka ya tambayeni miye matsalata?.
Na d'a6e baki sannan nace “masassara”.
Harun ya kalla, danshi baima fahimci minake nufiba.
Murmushi harun yayi, danya fahimci bai ganeba, cikin gyara tsayuwa yace “tana nufin fever”.
Caraf fiddausi tace, “ranka yadad'e k'arya take hawan jinine”.
Juyowa yayi ya kalli fiddausin da fararen idanunsa wad'anda suka nemi zautata, bai Ce komaiba ya janye ya maida kan Munubiya, “Sister naga drugs d'innan?”. yafad'a kamar anmasa dole.
Ko kad'an Munubiya bataji maiya fad'aba, dan a saman la66ansa yayi maganar, tana shirin sake tambayarsa d'aya daga cikin dogaran ya maimaita mata a tsawace.
Nikaina saida Na bud'e ido saboda tsawar, Na bankama dogarin harara ina magana k'asa-k'asa yan da babu mai jina, kajimin shegen dogari, dan tace batajiba zakawani daka mata tsawa?, shi mizaisa bazai bud'e baki yayi magana yanda kowa zaijiba? Mutum sai azabar Girman kai mtsoww, koma R bai iyaba.
Duk maganar danake la66ana ne kawai ke motsawa, shikuma idon nasa nakan la66ana, dukda duba kwalin drugs dayakeyi, tsaf ya karanci duk maganar danakeyi. yayi wani munafukin guntun murmushi yana mik'ama Munubiya magungunan.
Juyawa yayi yama Harun magana, sannan ya juyo ya kalleni yana fad'in “ALLAH yak'ara lafiya”.
Harara Na zuba masa batare da tunanin zai ganiba, amma sai caraf muka had'a idanu.
Janye idanunsa yayi a kaina yajuya yabar wajen yana cije lips d'insa da mamakin yarinyar nan da batada tsoro.
su Safara'u Na zuba masa godiya, duk da zukatansu Na mamakin yanda yanuna tamkarma bai sanmu ba.
Ko kallonsu baiyiba ya d'aga musu hannu, sukuma sunyine dama danya tanka musu.
Harun ya tambayi Munubiya wane doctor ne ke dubani?.
Ta Sanar masa.
Addu'a yaymin sannan yabar wajen shima.
Lumshe idanuna nayi zuciyata Na kaikawo, yanda Galadima yayi, saiya kuma tabbatar min da mafarki dai nayi kenan, bawai gaba da gaba ba yace muyi Auren Contract ba kenan.
Innalillhi, mike shirin faruwa danine ni Hussaina, hawayen dasuke neman zubomin nai k'ok'arin had'iyewa, Munubiya kanta tashiga kogin mamakin yanda Galadima yay tamkar ma komai baita6a faruwaba, shin kodai shi baiga abinda yafaru a jaridar baneba?....
Batada mai bata amsa, su safara'u ma magana suketayi k'asa-k'asa a tsakaninsu, alokacinne kuma matan gidanmu suka shigo.
Mamansu yaa hameed take tambayar wai wananan bashine Galadima ba na jikin jaridar nan?.
“wlhy shine kuwa mama”. cewar Fiddausi.
Haleematu ta kar6e da fad'in “mama kinga yanda ya nuna kuwa? tamkar ma bai gane su twins ba balle ya nuna yama San abinda yafaru a bayabaya tsakaninsu”.
Murmushin mugunta mamansu ya hameed tayi, “yo ai dama saboda irin haka ake cewa Ku kare mutuncin kanku, danshi namiji komi yayi adone, sannan shi d'an manyan mutanene, ko kallonsa da abin babu mai sakeyi, amma Ku gashi har ana fasa aure, kamun kai dai dad'i gareshi ai dama, kum.......”
Shigowar doctor tasaka maman su yaa hameed yin shiru, korarsu yayi gaba d'aya, yace subarni Na huta.
Basuso hakanba, dan shirya cin zarafinmu maman yaa hameed tayi.
Daganan gida suka wuce suna 'yan gulmace-gumacensu da dariyar mugunta.
★★★★★
Galadima kuwa yana gama zagaye-zagayensa a asibitin na duba marasa lafiya gida suka wuce.
Bayanin doctor yabashi mamaki, wai wannan 'yar yarinyar keda hawan jini, itako miyayi zafi haka a rayuwarta”. wani sashi na zuciyarsa yabasa amsa da (6atancin da akai muku).
Lips d'insa ya cije yana jan dogon tsaki, shikad'ai yasan burin daya d'auka akan dukkan Wanda yasamu da hannu a wannan lamarin.
Sun biya birnin gayu plaza yaga komai yana tafiya dai-dai, daga nan suka koma masarauta.
★★★★
Nima a ranar da daddare aka sallamoni, nadawo gida nacigaba da shan Magani, yayinda biki keta gaba towa kuma.
Har yanzu innarmu tana cikin damuwa dani kaina akan zancen aurena daba asan taka maimai angoba.
Zancen galadima kuwa ai tini na shareshi, dan nabarsa amatsayin mafarki nayi, musamman kuma dana bincika banga number wayan daya baniba, a wayata kuma tun randa na tura masa massege na gogeta dama gudun kar wani yagani.
Yanda 'yan gidanmu suketa rawar kai akan bikin saran 'yan uwanmu innarmu batayi, bazama ka ta6a d'auka itama zata aurar da 'ya'ya har biyu baneba.
Mama Rabi'a ce ke tsaye akan komai, sai aunty salamah datazo da magunguna ta d'id'd'irka mana, mu bamusan namiye ba, takumace mudinga sha, saikuma had'ad'd'en sabulun wanka da mai data had'a mana, ga wasu turare masu sirrin k'amshi, takuma gargad'emu daga yanzu muna saka hijjab duk inda zamuje da nik'af, domin fatarmu tasami nutsuwa kar rana ta maidamu gidan jiya.
Ni dai dagani har munubiya da to kawai muke binta, kuma duk abinda tace muyi munayinsa.
Abbanmu yakira mama Rabi'a yabata wasu kud'i akan tak'ara amana siyayyar kayan kitchen da 'yan uwa keyi, tunda ita innarmu bawasu dangi ne da itaba dazasu tara mata.
Sosai tamasa godiya, sanan tasanarma innarmu, ko babu komai taji dad'i, harma tamasa godiya itama.
Tafiya mama Rabi'a tayi da k'ud'in, washe gari suka Shiga kasuwa itada inna lami, kaya masu k'yau suka sissiya mana dai-dai gwargwadon k'arfinmu. aka adanasu gidan inna lami duka.
*_kwanci tashi_*
Babu wahala wajen ubangiji, yau gashi abinda kowa yake jira yazo, domin kuwa ankawo lefen Haleematu, gaskiya angonta yayi k'ok'ari, akwati 5 abinta, kuma kaya masha ALLAH, sai-dai hakan bai hana 'yan gidanmu gulmaba, washe gari kuma aka kawo kayan Safara'u da Fiddausi.
Suma dai kam saidai mak'iyi, amma jikin maman safara'u yayi sanyi, dan gaskiya kayan sauran duk sunfi nata. Itama dai akwati biyarne, amma kayan cikine basukai na sauranba.
Again washe gari saiga na Fauziyya da Munubiya, mama Rabi'a tasan komai dake wakana a gidanmu, dan haka suka dage sukaima Munubiya lefe na 'Yar gata, wlhy ba fariyaba lefenta yafi na kowa, ranar har kukan dad'i nayi, domin banyi zaton hakanba. itama dai fauziyya angonta yayi k'ok'ari gaskiya.
Tuni hassadar matan gidanmu tafito fili suka fara yada habaici wai an aro kaya anzo ana musu burga, da anyi aure sai ake maidawa d'ai-d'ai.
Dagamu har innarmu babu Wanda ya tanka musu, dan munsan yau dai mune aciki sune a kwana🤣🥴.
Rashin kawo nawa lefen kuwa ko a kwalar rigata bai dameniba, dan bama sanin mijin nayiba balle nadamu dawani lefen banza. saima Munubiya ce harda kukanta rurus akan wai saidai araba mana kayanta mu biyu.
Nifa dariyama tabani wlhy.
Ganin ni babu lefe yasaka su baba k'arami siyomin kaya masu k'yau na fitar biki har kala 10, aka d'inka min, sai takalma da bags da veils masu k'yau suma.
Habaici dai kam munshashi wa su innaro da matan gidanmu, danma ita innaro gwaggo Safiyya na hanata ne, da bamu san tijarar dazata zubarba a ranar kam.
A haka aka shiga satin biki, mu bamu wani gayyaci k'awayeba, daga Bilkisu sai su Ayusher, ashe Ayusher ta buga invitation na k'awaye suka raba itada Bilkisu bamu saniba.
Abin mamaki ranar kamu sai ganin k'awayenmu mukayi harna secondary.
munji dad'in hakan sosai kuwa.
A ranar kamun saiga wasu mata hud'u sunzo wai dangin miji nane, su mama Rabi'a sukayi musu tarba ta mutunci, ba a nuna musu komaiba kuma, dukda a yanayin shigar talauci da sukazo, saidai zund'e da gulma irinta 'yan biki. Matan gidanmu kam komai ya kaimusu dai-dai, sai dariya da yada magana a kaikaice sukeyi. Da aka kaisu su gaisa da innaro taita musu yatsine-yatsine, harda tanbayarsu waisu garinsu ba'a lefene? dabasu kawoma jikartaba?.
Basuce komaiba sai murmushi kawai da sukayi.
Washe gari kuma akayi k'unshi, mudai namu aunty Salamah ce tamana, tana tsaye akan komai namu tamkar yayarmu ciki d'aya.
A ranar kuma akaje a kaima sauran amaren jere, harda Munubiya, amma ni banda ni, tunda ba'asan ina za'aje ayiba.
Aranarma Munubiya tayi kuka, nidai ina k'ok'arin danne zuciyata, saboda nabama innarmu kwarin gwuywa karta tada hankalinta.
Aiko Alhmdllh ta dake tamkar komai baya damunta, tashige cikin abokan arzik'inta sunata harkoki. kowanne 6angare yacika da dangin matan gidanmu, abin tamkar fariya, namu 6angarenne kawai keda sauk'in jama'a, hakama gidan innaro yacika da danginta da dangin kakanmu.
Tunda aunty Salamah tagama yimana k'unshi da gyaran kai dana jiki sai muka nufo hanyar gida, saboda yaa marwan yazo neman Munubiya harsau biyu, sai kiran wayarta yake yana masifa saboda tare yake da abokansa. hakan yasa muka taho gida.
Gashi Yau zamuyi sister's and brother's day, duk da dai saima da yamma.
★★★★★
Galadima dake zaune a makeken falon Ummu hasheem, yanata bin jerin akwatinan da kallo, ga wasu daga 'yan uwansa zazzaune sunata kuma kimtsa kayan, aunty Mimi ta kalleshi, “kunga zanma mantafa, my k'ani ina kayan dana baka kayo gaba dasune?”.
Yatsine fusaka yad'anyi yana gyara zamansa, “nifa nama manta inda suke, shiyyasa nace bazan d'akkoba ai”.
Wata uwar harara ta watsa masa tace, “lallai bakada kai yaro, bar ganin matarka za'a kaimawa, suka 6ata biyana zakayi ehe”
Murmushin gefen baki yasaki yana lumshe idanu, cikeda k'asaitarsa yace, “Samha! jeki bedroom d'ina ki duba, maybe suna can“.
“bama kada tabbas kenan?” cewar mom.
Bud'e idanunsa yayi yana murmushi, “no mom insha ALLAH sunama can. ni yanzu kam kun sallameni natashi natafi? dan zansa aje a d'auko su Akash a airport ”.
Ummu Hasheem tace “kaje kawai, dama dan kaga kayanne, tunda kuma kace komai yayi ai shikenan”.
Mik'ewa yayi yana fad'in “thanks you Ummu, nabarku lafiya”.
Tunda yasamu yay escape sai ya sauke ajiyar zuciya, shi dariyama suke bashi dagasu har su papi, su Dan basu san auren shekara d'aya bane dabasu dinga wannan rawar k'afarba, sun wani zauna sun had'a uban kayan lefe, yad'an ta6e bakinsa kawai yana nufar sashensa.
Komai na gidan sarauta mai tsarine, dan haka kai lefen MUNAYA da suke shirin yima a tsare akayisa, (papi ne yace Subari sai yau ana gobe d'aurin aure sai akai, tunda gidan su munaya basusan kosu su wayeba).
An tsara iya wad'anda zasu kai lefenne.
Bayan an gama zuba akwatunan a wata farar mota mai k'yau sabuwa dal aka rufe, driver ne kawai zai shiga cikin motar.
Sai kuma motoci 6 da aka zaba wad'an da zasu kai lefen.
Motar farko dogaraine, ta biyu kuma kuyangi ne, sai guda biyu 'yan cikin gidansu Galadima ne su hud'u, ko wacce mota mutum biyu, sauran biyun kuma 'yan 6angaren masarautar su Momma, suma su hud'u, kowacce mota biyu. sai Samha datasa kuka saitaje taga matar Uncle Sam.
Aunty mimi harta korata da zare mata idanu saiga Galadima motocin na niyar tashi.
Da kansa yabud'e mata gaban motar da aka saka akwatinan yace tashiga nan, idan taje ta gaida masa matarsa.
Cikeda d'oki tace zataji Uncle Sam, bazaka bada komai akai mataba.
Kansa yad'an dafe dan yakula Samha na neman k'uresa, shikuma yafad'a mata maganarne domin yanason agaban jama'a yadinga yana tsantsar k'aunar Munaya, a bad'ini kuma suna zaman aurensu na contract, shiyyasa ko lefennan baiji tsadar kud'in saba yabud'e bakin aljihu aka zuba kaya masu azabar k'yau, gakuma kud'in da Mai martaba yabada shima, dakuma sauran k'annen mahaifinsa.
Hannu yasaka a aljihunsa yana duba kozai samu wani Abu, amma babu komai sai wata chocolates guda biyu, wadda ya d'akkota ne zaiba khaleel d'azun yama manta, mik'ama Samha yayi yace “gashi kibata”.
Da dariya samha ta kar6a tace “Uncle ta gode to”.
Kansa kawai ya jinjina mata ya shirin barin wajen.
motocin suna fita daga masarautar saiya sauke ajiyar zuciya kawai.
★★★★
Gidanmu ya cakud'e da hayaniyar da akasan gidan kowanne biki da ita, bare mu daya kasance har auren mutum 6, dukda sai gobene d'aurin aure kuwa, yara sunata wasansu da tsalle-tsalle.
A jere motocin suka shigo cikin anguwar, jama'a sai binsu da kallo sukeyi, dai-dai k'ofar gidanmu driver daya san gidan yay parking.
Babu Wanda yay mamaki a 'yan kawo lefe, domin kuwa dama labari ya karad'e masarautar cewar Galadima'yar talakawa zai aura.
Dogarawa da kuyangi suka fara fitowa, sannan suka bud'e motor da akwatina suka suka fara fitarwa. Nanfa jama'ar anguwa sukayi cirko-cirko suna kallon ikon ALLAH dan ganin akwatinan da aketa fitarwa daga mota.
Batare da neman isoba Kuyangin suka fara kwasar akwatinan suna shiga dasu gidanmu..............✍🏼
😂😂😂
Team innaro kufito mu caskale yau🙊🤸🏻♀
⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀
Asha weekend lafiya😅✋🏻
*_ALLAH ka gafartama mahaifanmu👏🏻😭_*

*
_*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
1⃣9⃣
Khulud ta kuma zaro idonta waje tace " kai my Sanah,
cikin dariya Sanah tace " eh mana,
" ni dai please kiyi man alk'awarin baki kuma ramawa please,
tayi maganar cikin sanyinta,
Sanah ta kuma yin dariya had'i da dafa kafad'ar Khulud tana kallanta ido cikin ido,
cikin marairaicewa Khulud tace " please tana langwab'ar da kanta gefe,
Sanah ta d'an k'ura mata ido kana ta sauke ajiyar zuciya had'i da cewa " nayi miki alk'awarin daga yau har abada duk abinda zai man ban kuma ramawa,
cikin jin dad'i Khulud ta rungume ta tana cewa " yawwa my Sanah thank you so much,
murmushi Sanah tayi kawai batare datace komai ba,
ta rok'o hannun suka nufi part d'in kakannin su.
Fitowa Hanash yayi zuwa harabar gidan,
su Wajnah na biye dashi a baya,
Papu yace " au kinga na manta Hanash zai fita batare dana aike shi bank d'in bako?
Yayi maganar yana kallan Mimmee,
tace " kaga kuma yau Friday ba,
da idan ya aje su sai ya biya bank d'in,
kafin su gama walimar shi yaje yayi abinda zayyi,
Mimmee ta fad'a idanta kan Papu,
" kuma daga yau ba bank har sai Monday,
ga time na tafiya naga yanzu wajen 4:30pm,
yayi maganar yana mikewa had'i da kallan agogon hannunsa,
da sauri ya fita daga parlor'n yabi bayan su Hanash,
Hanash na niyyar yiwa mota key,
yaga Papu ya nufo su da sauri,
a hankali Hanash ya fita ya nufi Papu,
check Papu ya mik'ewa Hanash yana cewa " idan ka aje su a gidan walimar ka biya banki ka amshi wad'annan kud'in,
sai ka saka su a account d'ina ko naka,
Hanash yayi murmushi yana kallan Papu zayyi magana drivers biyu suka shigo gidan a lokaci d'aya,
Papu yace " yauwa ga drivers nan sun dawo,
bari na saka d'aya daga cikin su ya kai su gidan walimar,
kai kuma sai ga je bank d'in,
Papu yayi maganar yana nufar wajen drivers d'in,
cikin taushi Papu ya fad'a musu,
sannan ya sanar dasu Zohal su fito su shiga motar driver shi zai kai su,
kana ya koma wajen Hanash dake tsaye inda ya barshi,
Papu ya lura da yadda yanayin Hanash ya canja sosai,
sannan walwalarsa da sakin fuskarsa ba kamar da ba,
kallan Papu Hanash yayi kana yace " Papu wannan kallan fa?
Ya fad'a yana dariya,
shima Papun dariya yayi yana dafa kad'afar Hanash yace " bakomai kawai ina kallan d'ana ne,
in kuma za'a hana ni ne to,
yayi maganar cikin barkwanci,
Hanash yayi dariya batare dayace komai ba,
Papu yace " kaje maza ka dawo zamuyi magana da kai,
Hanash yayi dariya kana yace " hala Papu ya manta yau Saturday?
Papu ya zaro ido had'i da cewa " what! haba dai?
Hanash yayi murmushi yace " Allah kuwa Papu yau Saturday,
hala ka shafa'a ne?
" Ka manta jiya mukaje sallar juma'a?
Papu yace " na manta,
kasan tsufa ya fara kamamu ,
abinka da tsoho, Hanash kuma yin dariya yace " kai Papu wanne irin tsufa kuma?
"Bayan gaka nan kamar matashin sauryi kamar mu,,
Hanash ya fad'a cikin tsokana,
dayake sun saba wasa da dariya sosai da Papu,
dan wani lokacin idan ka gansu sai ka rantse abokanai ne,
Papu yace " kayya wanne matashin sauriya,
muda samartaka ai sai dai a lahira a aljanna,
jiya ai ba yau ba ,
tunda na haifi k'aton saurayi kamarka ai na tsufa,
ko yanzu Alhamdulillah dan na mori k'uriciya ta,
kai ma sai kayi k'ok'ari ka mori taka k'uruciyar,
sanda nake kamar shekarunka na haifeka,
amma kai gaka nan har yanzu 30yrs baka da ko budurwar,
ko rowa kake man dan karna ga 'ya'yanka oho,
inaga sai na mutu sannan zakayi aure ka haihu,
Jadda dake jiyo su ta window ta,
suka jiyo muryarta tana cewa " kyale ja'iri wallahi idan na gaji sai dai ya shigo gidan ya iske matarsa a b'angarensa,
imma bak'in ciki kake man dan kar naga yaranka ehe,
daga Papu har Hanash duk suka sanya dariya,
Hanash ya shafa kansa yana kallan Jadda,
Papu dake tsaye a wajen shiya hana shi ce mata komai,
sai murmushi da yayi tayi shi kad'ai yana shafa kai,
kallansa Papu yayi yana nazarin yanayinsa ya tabbatar akwai abinda yake damunsa,
amma sai ya sabar yace " ka rik'e check d'in a hannunka,
ranar Monday sai kayi kamar yadda na saka ka,
"tom Papu ba damuwa Allah ya kai mu Monday,
Papu ya amsa da " amin yana komawa part d'in Mimmee,
iske ta yayi tana k'ok'arin shigewa bedroom d'inta,
ganinsa yasa ta jiyowa tana kallan shi,
yace " wai meke damunsa ne?
Tace " wa?
Yace " Hanash mana,
naga kwana biyu yanayinsa duk ya canja,
Mimmee tace " nima dai haka nagani kwana biyun nan,
kamar yana cikin damuwa,
Papu yace " kin tambaye shi ne?
Tace " eh,
"Ok meya ce maki?
" Wai bai jin dad'in jikin sa ne,
Papu yace " ok mu barshi zuwa nan da kwana biyu mu gani,
Mimmee tace " Allah ya kai mu,
muje ciki kayi wanka ko?
Bayanta yabi yana cewa " kamar ko kinsan zafi nake ji,
Hanash na komawa b'angarensa ya kuma zubewa kan sofa,
had'i da runtse idannuwansa,
shi har yanzu bai san so da soyayyar Khulud ke d'awainiya dashi ba,
ta hana shi sakat, ta hana shi walwala da farin ciki,
haka nan kullum yake jin damuwarsa na k'aruwa,
babban burinsa a rayuwa yanzu bai wuce na sake ganinta ko sau d'aya ne a rayuwarsa ba.
part d'in Ganez suka fara shiga suka iske Nisah zaune kusa dashi,
Sanah tace " oh! ashe dai har yanzu ana tsinkar korawayen fure?
Duk sukayi dariya kana Ganez yace " a'a aini idan bada ku zan tsinki korayan fure ba,
ai a banza, Khulud tace " kinji shi zayyi mana wayo kullum yayi ta cewa idan ba mu ba sai rijiya,
Sanah tace " kuma yana tsoran matarsa ba,
Nisah tayi dariya kana tace " oh! kuji man yara,
wato kun saka mana ido, ai irin haka ake so,
Khulud tace " mijin ya rink'a jin tsoran matarsa?
Nisah tace " eh mana,
Sanah tace " ina fa dad'i miji ya zama mijin tace,
an dai mayar mana da kakanmu tace kawai,
Nisah tace " wannan ai kan tace ne ma,
duk sukayi dariya kana suka fita suka nufi part d'in Danish,
ganin Erum tayi kwalliya yasa su yin dariya,
Khulud tace " wato ke har yanzu baki dai na kwalliyya bako?
Erum tace " ina ni ina daina kwalliya,
Sanah tace " kici zamaninki kici na wasu ko?
"Sosai ma kuwa cewar Erum,
" a'a kace yau amare nane a gidan,
cewar Danish dake fitowa daga bedroom d'insa,
Sanah tace " mune, munzo a bamu abinda akaci aka rage,,
Danish yace " ku da kuke amare ina ku ina raguwa,
ai sai dai sabuwar dahuwa,
Khulud tace " ai dama kun saba yi mana wayo,
bayan duk tsoron matan ku kukeji,
Erum tace " ai irin wannan k'arshen ake so ayi yara,
ku ma kuyi addu'ar Allah ya baku ita mu,
Sanah tace " wai ma duk ba wannan ba,
ina zaku na ganku duk kunyi kwalliya?
" Mu da muke da walima yau har a tambaye mu inda zamu dan munyi kwalliya,
Erum tayi maganar tana dariya,
Khulud tace " a she walima ce daku,
a ina kuma?
Erum tace " sosai ma, kuma a nan gidan,
Sanah tace " tab wai wacce walimar kuke nufi?
Badai tamu ba ko?
Tayi maganar a lokaci d'aya,
Erum tace " walimar ku ko tamu?
"Ai muke da walima kuwa,
tunda mune manyan k'awaye,
tayi maganar tana dariya,
Khulud tace " mu dai bamu gayyace ku ba,
kuma bamu san gayyar sod'i ehe,
duk sukayi dariya kana suka fita,
part d'in Juju sukayi,
da sallama suka shiga,
Didi ya amsa musu cikin fara'a,
kana yace " 'yan candy ne yau a gidan namu?
Sanah tace " mu ne,
Didi ya kalli Juju yace " ina kika b'oye mana su ne?
Juju tace " wacce ni?
" Ai sai dai ka tambaye Mamun su,
ni tunda sukayi candy ban sa su ido na ba,
sai yau, ko irin kayan kayan candy nan ba'a kawo mana ba,
balle muce mu shaida anyi candy,
muce Allah ya sanya alkhairi,
Khulud tace " kai Juju Allah bamu zauna bane,
mu ta yawan zuwa saloon da k'unshi,
Sanah tayi dariya kana tace " Juju ku da zaku bawa wasu ma,
kayan candy kuma ga walima nan kun shirya ku da kanku,
sai ku shaida anyi candy kuyi addu'ar Allah ya sanya alk'airi,
Didi yayi dariya yace " wai Sanah baki abin magana,
ke dai ba'a tab'a k'ure ki ta wajen magana,
Juju tayi dariya tace " ai ni nayi shiru tunda an fini baki,,,
dama hausawa sunce dokin mai baki yafi gudu,
Didi ya kuma yin murmushi kana yace " Sanah yaushe jamb d'inku zata fito?
Sanah tace " naji ance this coming Monday,
Juju tace " wacce university kika cike?
"First choice BUK second kuma ABU Zaria,
Didi yace " masha Allah Ubangiji ya taimaka, Allah ya bada sa'a,
duk suka amsa da Amin,
har Khulud dabata zana jamb d'inba,
dan cewa tayi ita ta gama karatun boko har abada,
Juju ta kalli Khulud kana ta mayar da kallan ta ga Didi tace " 'yar Abbu da Mamu ita aure take so,
Khulud ta d'ago kanta da sauri suka had'a ido Juju tayi saurin sadda kanta k'asa tace " Allah Juju ba haka bane,
tayi maganar a shagwab'e,
Juju tace " idan ba haka bane to yaya ne?
Khulud tace " Allah ni ban san cigaba da karatun ne kawai,
ni kwata-kwata ban tab'a sha'awar yin karatun boko mai zurfi ba,
Juju zata kuma yin magana,
Didi yayi saurin cewa " haka ne ai kowanne mutum yana da nashi ra'ayin,
hakan ma da kikayi dai-dai ne dabaki yaudare iyayenki kin shiga jami'ar ba,
kana kik'i yin karatun ko wata matsala ta faru,
so ni ina ganin kinyiwa kanki da Abbunki adalci,
Allah ya zab'a maku abinda yafi alkhairi a rayuwarku,
ya haskaka rayuwarku ya sanya albarka acikinta,
duk suka amsa da Amin,
fita sukayi suka nufi wajen da aka tanada dan yin walimar da tuni k'awayensu sun fara zuwa,
sosai walima ta kankama haik'an,
aka ci aka sha sosai dan sosai Abbu ya saki bakin aljihunsa dan nuna tsantsar farin cikinsa na kammala karatun yaransa lafiya,
sosai aka rarraba kyaututtuka,
kana kowa ya watse cikin farin ciki aka gama walimar lafiya.
Sannu a hankali matsanannaciyar soyayyar Khulud tayi mugun kama Hanash,
ta addabi ruhi da gangar jikinsa,
kwata-kwata ya rasa sukuni da walwalarsa,
ya rame sosai dan raban dayaci ishashshen abinci ko ya samun bacci har ya manta,
kullum yana cikin bedroom ko parlor'nsa,
dan ko fituwa sosai ya dainayi sai dai ya fito ya gaida iyayshi ya koma,
yauma kamar kullum kwance yake a d'akinsa ya tsunduma duniyar tunaninta,
idanshi rufe babu abinda yake gani sai ita tsaye a gabansa,
tana sakar mishi k'ayataccen murmushinta,
jin knocking yasa shi bud'e shu'uman idanuwansa,
k'ofar ya zubawa ido na tsayin lokaci,
batare da yayi wani yunk'uri ba,
sake knocking akayi a karo na biyu,
dakyar ya iya cewa " waye?
Muryar Papu yaji yace " mu ne,
dan sun kasa jurewa ganinsa cikin wannan mawuyacin yanayin,
da sauri ya mik'e ya bud'e musu k'ofar suka shigo,
akan sofa duk suka zauna, a hankali Mimmee ta d'ora hannunta akan kafad'arsa,
had'i da zubawa d'an nata ido,
Papu ma ya zauna kusa dashi ya zuba masa ido,
kansa ya duk'ar dan ya san kwanan zancen,
muddin akace bashi da lafiya ko yana cikin damuwa to gaba d'aya gidan babu mai yin walwala,
a hankali Papu ma ya d'ora hannunsa akansa kana ya kira sunansa,
" Hanash,
"na'am, Hanash ya amsa cikin ladabi,
" meke damunka?
Cewar Papu a tak'aice,
murmushin k'arfin hali Hanash yayi kana yace " babu abinda ke damuna Papu,
yayi maganar while kanshi k'asa,
Mimmee ta shafa kansa kana tace " Hanash please karka b'oye mana abinda yake damunka,
ka daure ka sanar damu koda babu wani abu da zamu iya yi akai,
sai mu tayaka da addu'a,
ta fad'a cikin damuwa,
murmushi Hanash ya kuma yi kana yace " ba ni da lafiya ne,
Mimmee zazzab'i da ciwon kai ke damuna,
ido Mimmee ta zuba mishi tana nazarinsa dan ita kwata-kwata bata yarda da abinda yace ba,
Papu yace " kaje hospital?
Hanash yace " eh Papu,
"me sukace yana damunka?
Papu ya kuma tambayarsa,
d'an shiru Hanash yayi kafin yace " Malaria,
" to ikon Allah kai ko ina kaga sauron daya cije ka?
Mimmee ta fad'a tana kallan kwayar idansa,
murmushi yayi kana yace " Mimmee, cikin shagwab'a,
Papu yace " shi ciwo ai daga Allah ne, ba ta inda baya shiga jikin mutum ko son?
Yayi maganar cikin tsokana,
dan shima yadai ji Hanash ne kawai,
amma bai yarda da abinda ya fad'a ba,
babu yadda Papu da Mimmee basu yi akan Hanash ya sanar da su damuwarshi ba, amma yak'i yace babu abinda yake damunsa,
Papu yace " Allah ya sauwak'e,
ya amsa da " Amin, kana suka fita,
suna fita Hanash ya koma ya kwanta,
had'i da rufe idansa.
Ranar Monday jamb ta fito,
Sanah cikin murna da d'oki suka je ita da Aarib & Khulud suka duba,
a cafe, aiko taci sosai dan ta samu 251,
tsalle ta buga ta rumgume Khulud da Aarib cikin matsananciyar murna,
motar su nayin parking a harabar gidan ta fito,
ta shiga kwalawa Halan kira,
da gudu ta shiga part d'in Halan,
ta iske ta parlor zaune ita da Ziyad,
cikin murna ta fad'a kanta, ta ma manta da tsohon cikin dake jikin Halan,
Ziyad ya daka mata tsawa had'i da cewa " ke baki da hankali ne ko baki ganin abinda ke jikinta?
Bata kula da tsawar daya daka mata ba,
sai ma kiss datayi mishi a kumatu,
cikin murna tace " Yaya naci jamb,
ta fad'a tana tsalle,
dariya Halan tayi tace " kai masha Allah gaskiya nima nayi murna,
badan kayan dake gaba na ba,
da har dani za'ayi tsallan,
Ziyad yayi dariya yace " bani abu na inyaso sai kije kiyi tsallanki,
Halan ta kalleshi had'i da zumb'uro baki tace " Allah da ana bayarwa ai bama sai ka tambaya ba,
Sanah da Khulud suka fita da gudu suka nufi part d'in Mamu,
suna zuwa Sanah ta fad'a kan Abbu,
yace " kai Sanah ke dai baki girma,
naga alamar so kike ki karya ni tunda baki ganin na tsufa yanzu,
Sanah tayi mishi kiss tace " Abbu albishirinka,
yana dariya yace " goro,
tace " fari ko ja?
Yace " fari tass,
tace " Abbu na ci jamb,
Abbu yace " wai dole ayi murna,
Mamu tace " masha Allah,
saura waec & neco,
Abbu yace " suma duka za'a cinye su,
in sha Allah,
fita sukayi suka nufi part d'in Juju,
nan ma aka sanar mata anci jamb,
murna kam ba'a magana,
a week d'in waec ta fito,
Sanah ta samu result mai kyau,
result d'inta yayi mugun kyau,
bayan two weeks BUK ta kira su first UME,
bayan week nan ma result ya fito,
ta samu taci, suka bata Admission letter na BSC COMPUTER SCIENCE.
Kullum Hanash bashi da wani aiki sai mafarkin Khulud,
da tunaninta ko idansa ya rufe ita yake gani,
koyaya ya rufe idansa ita yake ya gani,
abun duniya duk ya dame shi,
ba shi da wani burin daya ce na sake ganinta a yanzu,
ko da sau d'aya ne a rayuwarsa.
Yau itace rana ta farko da Sanah zata fara hallartar BUK,
ta gama shirinta tsaf cikin riga da siket na material red color d'inkin yayi masifar yi mata kyau,
ya amshi jikinta sosai, ta saka high hill shoe ta yafa mayafinta mai kyau kalar flowers dake jikin material d'in black,
sosai Sanah tayi shegen kyau,
duk da ba wani make up tayi ba,
ta dayyi simple make up abinta,
wanda ya bayyanar da tsantsar kyauta,
har cikin makarantar Aarib ya kaita,
sai da yayi mata fad'a sosai kana ya tafi,
sannu a hankali take tafiya harta isa department d'insu,
tambaya tayi,
aka nuna mata, inda zasuyi lectures yau,
dayake tana da time table na duka courses & time d'in su,
a hannunta tasan Computer lectures zata fara attending,
zama tayi a inda taga students na zama,
zamanta ke da wuya ta fara jiyo hirar students,
" yau fa Sir Aryan ne damu,
kasan ko ba sauk'i, d'ayan yace " wallahi ko ni gaba na ma sai fad'uwa yake yi,
tun jiya dana duba naga shine damu hankali na yake a mugun tashe,
wani daga gefe yace " kai ai Malamin nan bai da kyau,
d'ayan yace " kaga fito sak a mutum kai tsaye kace bai da mutunci,
d'ayan yace " ni fa yana mugun ban mamaki shi ko irin na sauran lectures d'in nan bayyi,
d'aya yace " me?
" San mata mana,
d'ayan yace " kai tanan wajen ai Sir Aryan yayi wallahi,
ba ruwanshi da mata, duk kyanki yanzu zai yarfa ki,
ba kamar sauran lectures d'in ba,
shegu da sunga mata sai suyi ta rawar jiki,
idan mune 'yan uwansu maza tsakanimu dasu ba mutunci,
sai su rufe ido su karta mana,
amma shi kwata-kwata mace bata isheshi kallo ba,
naga 'yan mata dayawa sunyi mugun matuwa akansa,
d'ayan yace " aiya had'u ne ga kyau ga kud'i, kaga kuwa ai dole mata su matu,
tunda ready mate ne,
d'ayan yayi dariya yace " aiko suna shan dizgi da wulak'anci a wajensa ba,
dan yanzu zai kartawa mutum rashin m,
idan ta kama ma ya yarfa maka mari ba ruwanshi,
shege ga girman kai da d'agawa da jan aji dan sai kayi mishi magana goma amma dakyar idan yaga dama zai amsa maka d'aya ,
d'ayan yace " kai ai ya iya d'aukar wanka dacin uwar sutura,
yana zagin gizna ta asalimma,
ni na rasa uban me yake yi a makarantar wallahi,
"hmmmm ga babu ruwanshi da ke wai mace ce,
shi hukunci d'aya yake yi tsakanin mace da namiji,
idan ya riga ka shiga class ko waye ubanka kuma ko uban ya tsaya maka ya d'aure maka gindi baka shiga,
d'ayan ya duba agogo yace " sauran just 5 minutes ya shiga fa,
kusan kuma baya African time,
d'an tsaki Sanah tayi a hankali kana ta mik'e tabar gurin,
saboda duk gurin wajen mutum 100,
maganar mutum d'aya suke tayi Sir Aryan,
duk inda students sukayi d'an group,
maganar shi kawai sukeyi mata da maza,
daga maganar had'uwarsa kyansa, gayu, ajinsa,
sai ta wulak'anci da dizginsa da kuma girman kansa,
da yadda mata suka mato akansa yake wulak'antasu,
shiyasa duk randa yake da lectures dasu suke kaffa-kaffa.
Can gefe ta koma ita kad'ai ta zauna,
ita kad'ai kasancewar yaune farkon zuwanta bata san kowa ba,
tana daga zaune taga wata matsiyaciyar had'add'iyar mota ta danno kai cikin makarantar,
students na ganin motar suka kai duba zuwa number motar dan su tabbatar idan shi,
saboda baya hawa motar d'aya,
duk nacinka baka isa kace ga yawan motocinsa ba,
ta number motarsa kad'ai suke gane shi ne,
saboda sunan family d'in su ne a duka number motacinsa,,
ai students na tabbatarwa shine,
suka fara gudu maza da mata ana rige-rigen shiga class.
Yana yin parking, ya zare key d'in tare da komawa ya kishink'id'a jikin kujerar, ido ya lumshe tare da fesar da numfashi mai sanyi, a hankali ya kuma bud'e idon tare da sauk'e ajiyan zuciya, yana mai shak'ar k'amshin jikinsa dana mortar, a hankali ya sa hannun damanshi ya dafe saitin k'ahon zuciyarshi dan jin gabansa yana muguwar fad'uwa da k'arfi,
bugun zuciyarsa ya k'aru sosai,
zuciyarsa ta rink'a bugawa so past,
idansa ya kuma lumshe yana k'ara d'an kishingid'a akan kujerar motar,
a hankali ya furta " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,
saboda yadda yake jin
duk ilahirin jikinsa ya mutu, gabansa na mugun fad'uwa zuciyarsa na bugawa da tsananin k'arfi, addu'ar yayi ta maimaitawa dan baya son ayi mishi African time shiyasa shima baya son yayiwa d'alibanshi, bere daga inda yayi parking yana iya hango yadda suke sassarfan shiga class, sharshesa ya fitar tare da d'an laso lips nashi, hadi da d'an cizawa dan kauda kasalar dake saukar mai a jiki,
a hankali ya b'alle marfin motar tare da zuro k'afarshi d'aya woje, baki ya d'an tab'e ganin yadda wasu matasa suka wuceshi da sassarfa, gudun karya rigasu shiga class, ya hanasu shiga, fitowa daga cikin motar tare da jawo laptop nashi, ya bud'eta tare da dorata kan hannunshi daya mik'ar, yana kuma d'an lallatsashi cikin k'orewa, ajiyan zuciya ya sauk'e tare da fara takawa zuwa class d'in yana mai jin dad'in iskar dake busawa sirrai da fawowi suna shawagi tsuntsaye na kai komo ga k'amshin furanni dake ratsashi.
Cikin takunsa na isassun maza masu haiba da kamala ga tarin nagarta yake tafiya cap-cap sautin takalminshi ke ratsa wurin in dalibai sun hangoshi sai suna rusunawa tare da ratse mishi.
Ganin yadda students ke gudu yasa Sanah kai idanta kan motar dataga kamar an saka MOLI'S 15,
amma data duba so sai taga kamar ba haka bane,
baki tad'an tab'e kana ta mik'e cikin takunta mai daukar hankali tabi bayanshi,
ta nufi class itama,
daga bayansa ya rink'a jin kamar takun mutum a bayansa k'at-k'at,
Fuska ya kuma had'ewa dan ya gane mace ce, daga k'asa ya kalli k'afarta data sha kunshi mai ja da bak'in lalle yayi masifar yi mata kyau,
gabansa ne yayi muguwar fad'uwa lokacin daya d'ora idansa akan k'afarta, sake had'e rai yayi , kana ya cigaba da tafiya,
yana tafiya tana binsa a baya,
har suka zo gaf da isa class d'in,
Kai ya d'an jinjina tabbatarwa da yayi class d'in sa zata shiga , hankalin shi na kan laptop d'inshi, hannunshi mai yin typing d'in ya d'an d'aga shi saman kafadarshi ta yadda zata gani, sanan ya had'e doguwar yatsarsa ta tsakiya da babbar yatsarsa ya kettasu sau d'aya ta yadda ya bada sauti, sannan ya had'e yatsunsa biyu ya kad'asu kamar mai buga fiyano ya mata nuni data tsaya inda take karta biyoshi,
batare daya juyo ya kalle ta ba bai kuma tsayaba yaci gaba da takunshi zuwa cikin class,
Itako Sanah bata gane abinda yake nufi ba,
dan haka taci gaba da binsa a baya,
Kai ya jinjina tare da yin gutun murmushi, mai dauke da alamar zaki gane kurenki,
kana ya cigaba da tafiya har suka k'arasa cikin class d'in,
Sanah tazo zata wuce mazaunin d'aliban, *"Keeh"* kamar daga sama sautin muryarsa ya ratsa shirun daya ratsa ajin,sai sautin takalminta dake amsakuwa, shirune ya sake ratsa ajin duk sunsha jinin jikin su, ita kuwa Sanah kai ta d'ago ta kalleshi ,Amman bata ga fuskarsa ba dan baya ya bata, sai gashin k'eyarsa da ta tsurawa ido ganin shi a kwance lub sai wani lauyewa a yayi ya bi k'eyan nashi yana Shek'i, tana cikin nazarin da me tayi mishi ta kuma jiyo muryarshi na ratsa ajin baki d'aya taji tajiyo muryarsa nacewa yana cewa, *"kneeling down,"*
ya fad'a still bai jiyo ya kalle ta ba,
juyawa tayi bayanta taga babu kowa sai ita kad'ai,
cikin mamaki ta kalli bayansa dan ita a iya saninta tasan ba'a saka Patick a jami'a.
Cikin mamaki ta kuma kallan bayansa,
batare daya jiyo ba taji yace *"ko bazaki kiyi bane?"*
Muryar dataji ta daki dodon kunnenta,
tasa gabanta mugun fad'uwa a razane ta kuma kallan bayansa,
babu damar taga fuskarsa saboda ya juya mata baya,
a hankali Sanah ta d'an zumb'uri baki kana tayi kneeling down d'in,
gaba d'aya students mamaki ya gama cika su,
duk da sun san halinsa, sun tabbatar zai iyin abinda ma yafi hakan,
dan sun san mari ko dizgi abu ne mai matuk'ar sauk'i a wajensa,
amma basu tab'a ganin yasa wata ko wani kneeling down ba,
sai yau kuma daganinta new comer ce,
students suka rink'a yin dogon wuya suna l'eka ta,
jin muryarsa ta fara explanations yasa duk suka shiga hankalinsu.
Sanah na nan har ya gama lecture tana ta zumb'ure-zumb'uren baki,
Cikin k'asaita ya fito zai tafi , ganin ya wuce ta gabanta amma bashi da niyyar ce mata komai,
yasa ta cewa *"Sir to ni wuni zanyi a nan ne? "*
Tsayawa yayi cak a inda yake,
kana ya juyo da fuskarsa a hankali ya zuba mata ido,
had'i da hard'e hannayensa a k'irji,
mik'ewa Sanah tayi batare daya bata umarnin tashi daga kneeling d'in ba,
kanta durk'ushe tana kakkab'e siket d'inta,
tana yin magana k'asa-k'asa, "eh wato kai zaka fece gidanku ni kuwa in zauna a nan, sai kace baiwar gidan ku ko, hegen k'eya! da nad'edd'en gashi."
dan ita a tunaninta ya tafi shiyasa ta d'anyi halin, baki ta murgud'a tare da mik'ewa tsaye,
d'ago kan da zatayi, keda wuya sexy eyes d'inta,
suka sark'e cikin na *SIR MOLI* dayake tsaye hard'e da hannuwa yana kallan ta..................
_Aunty AISHA ALIYU GARKUWA_
_kina tambayar inda nakai miki Sir Molinki to gashi nan na maido miki abinki_
~To fans masu tambayar ina nakai Sir Moli na b'oye har tsayin six years, gashi nan ya dawo~
~sai a cigaba da gashi a d'ora daga inda aka tsaya~
*_Typing📲_*
*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
👉🏻1⃣9⃣
.......Kallone ya koma sama yayinda kuyangin suka shigo cikin gidanmu, na d'akima tuni sun fara rige-rigen fitowa, baba k'arami da fitowarsa kenan daga sashensa yak'araso ga kuyangin, domin tambayarsu daga ina haka?.
Baiwa d'ayace tabashi amsa da fad'in basu kad'ai bane, masuyin bayanin suna waje.
Fita yayi sukuma suka ajiye kayan gefe suka kuma fitowa domin kwaso sauran.
Muna falo a zaune inna lami ta tsaremu sai mun sha romon wani nama da aka dafa k'anana, sai yatsine fuska mukeyi saboda rashin dad'in naman. shigowar Ahmad da Aryaan da gudu yasa mama Rabi'a tambayarsu lafiya?.
Ahmad yace “mama wlhy bak'ine da akwatina da yawa suka shigo”.
Gaba d'aya muka zuba masa idanu, kafin wani yay masa tambaya a cikinmu mukajiyo sallamar baba k'arami.
Innarmu ce tamik'e domin fitowa, ganinsa da manyan mutane cikin alk'yabbu yasata fad'in “baba k'arami bak'i mukayi?”.
Cikin washe baki yace, “wlhy kuwa maman biyu ”.
Itama murmushine shinfid'e a face nata, tabasu hanya suka shigo falon, duk suka zazzauna.
Muduka muka durk'usa muka gaisasu, yayinda suka kuma gaisa dasu innarmu cikin mutunci.
Fita baba k'arami yayi yasa yaa Anas ya kunna Gen..... dayake babu nepa. Shikuma yakuma fita da hanzari domin nemawa wad'annan bak'i masu bazata kayan tarba, bayan yakira Dady da Abba ya Sanar musu.
Kaf matan gidanmu suka shigo, kowa yanason jin daga ina kuma.
Mukam d'akinmu muka koma muda su Ayusher muna hasashen bak'i daga ina haka? da gani dai kasan jinin sarautane, ko kad'an ban kawo Galadima a rainaba ma, dan narigada Na shafe labarinsa ni.
Suna cikin gaggaisawa da matan gidanmu saiga innaro tashigo, kai kace an wurgotane. baki tarik'e tana fad'in “o ni Marwanatu, manyan bak'i irin wad'annan surasa gurin sauka sai 6angaren Ai'sha? kuko bayin ALLAH daga ina haka? ”.
Su aunty Mimi basu fahimci zancen taba, dan haka duk sai sukayi d'an murmushi, matan gidanmu kuwa kowacce tayi k'asa da kai dariyar mugunta Na cinta, Innarmu dai bata tankaba, hakama mama Rabi'a, sai inna lami ce tace, “yo inna in banda abinki waka hana rana fita idan lokacin fitar tata yayi?”.
Kallonta innaro tayi zatayi magana baba k'arami yashigo da sallama, su Yaa Anas na biye dashi da kayan ciye-ciye nik'i-nik'i, bayan sun ajiye suka gaishesu cikeda girmamawa suka fita.
Zama baba k'arami yayi suka sake gaisawa, sannan yace, “kufayi hak'uri, mukam duk kun sakamu a duhu wlhy”.
K'asaitaccen murmushi aunty Mimi tayi, domin dama papi yamata bayani akan komai na 6oye musu dasukayi. ta gyara zamanta sosai “Alhaji daga masarauta muke, munkuma zo kawo kayan k'anwatane Gimbiya munaya”.
Kusan kowa dake falon saida ya waro idanu waje, domin jin furicin aunty Mimi, wasuma zuciyar tasu kad'an tarage tayo tsalle waje.
Aunty Mimi bata damu da yanayin nasuba tacigaba da fad'in “kuyi hak'uri fa, nasan nakuma sanyaku a wani duhun, mai martaba sarki Abdul'fatah da maimartaba sarki Jalaludden Abubakar, sune sukazo Neman auren yarinyar Ku Munaya wa d'ansu Galadima Muhammad Sameer Saifuddeen Abubakar, sun 6oye muku kansune saboda wani dalili, amma sun aikomu da sak'on ban hak'uri a gareku, yanzu dai mun kawo kayan lefen Munaya ne gasunan”.
Jin jina kai kawai baba k'arami ke iyayi, bakinsa yakasa rufuwa saboda d'unbin farinciki da al'ajabin dake dank'are a zuciyarsa, yanzu nan daman manyan sarakunane agabansu a wancan karon sukazo Neman auren d'iyansu, lallai sun godema ALLAH dabasu aikata wani Abu Mara k'yauba agaresu, lallai ya yarda kwarjinin mulkine yasakasu mik'a Auren d'iyarsu ga mutanen dabasu saniba.
Ai su madam innaro sai aka zauna k'asa babu nauyi, muryarta har zuga take tace “ranki ya dad'e wai gaskene saboda ALLAH?, kokuwa wasa kikeyi?”.
Murmushi aunty Mimi tayi, sannan ta kalli su Ummu hasheem da suma suketa murmushi, kallonta ta maido akan innaro, “hajiya kaka mizaisa muzo muyi muku wasa irin wannan akan magana mai muhimmanci irin ta aure, tabbas maganar nan gaskiyace, munama fata gobe idan ALLAH ya kaimu iyanzu Munaya tazama d'aya daga cikin zuri'ar masarautar gagara badau”.
Innarmu da mama Rabi'a juna suka rungume suka fashe da kuka, yayinda innaro tamik'e ta callara gud'ar data jawo hankalin tawagar jama'ar 'yan biki, sai kawai tashiga taka rawa.
Dariya sosai tamaba su aunty Mimi, shi Kansa baba k'arami dariyar yayi yana girgiza Kansa da mamakin innar tasu mai kayan arzik'i Dana tsiya.
Matan gidanmu kam ba'a magana, kowacce tayi d'if takasa koda kwakwkwaran motsi, kowaccensu jitake tamkarma tafasa ihu take a nan.
Muryar gwaggon halimatu na rawa tace “wai da gasken dai Munayar gidan sarauta zatayi aure?”.
“kwarai kuwa”. ‘innaro tafad'a tana mata wani kallo, “jikata sai gidan sarauta, masu bak'in cikin kuma sai a mace”.
Lallai maganar innaro tadaki zukatan dukkan matan gidanmu, Sanin halin innaro da baba k'arami yayi saiyace duk afita abama bak'i waje susha koda ruwane.
Jiki babu kwari sukaita Jan k'afa suna fita Su da danginsu 'yan biki da gud'ar innaro tajawosu shigowa. bak'in cikin kuwa k'arara a fuskokin wasunsu, maman su yaa hameed tayi taga-taga zata fad'i saida aka taryota.
Gwaggo Safiyya tace “lallai jama'ar gidannan yau ake *RAINA KAMA KAGA GAYYAFA* duk Wanda kake Kallon bai kaiba to tabbas watan watarana shine zai kereka, babu ruwan arzik'i da mugun gashi, Wanda yace shine to tabbas bashi baneba”.
Su Ayusher suka shigo suna gumtsa mana, kallonsu kawai nakeyi amma badan na gaskataba, munubiya ta rungumeni ta fashe da kukan dad'i, kallonta kawai nakeyi nakasa koda motsi, to murnar Auren shekara d'aya zanyi? Kokuwa murnar Ashe galadimane mijin nawa? bawani can da ban ba kamar yanda muketa hasashe?.
Ban iya ta6uka komaiba wata k'yak'yk'yawar budurwa tashigo, daka ganta kaga wadda Hutu yagama ratsawa, babu shakka zamu iya zama sa'anin juna da ita, fuskarta d'auke da murmushi tace, “to ina amaryar Uncle Sam d'in?”.
Feena ta nuna ni da hannu itama tana murmushi.
Gadon ta hayo batareda jiran abata iziniba, ta mik'amin Chocolates guda biyu tana kuma fad'ad'a murmushin nata.
Cikin mamaki muryata a sanyaye na girgiza mata kai nace “yar uwa namiye?”.
Hannuna takamo tasakamin tana 'yar dariya, “inji Uncle Sam yace nabama matarsa, sunana Samha, d'iyar yayar Uncle Sam ”.
Duk da mamakin daya cika zuciyata, hakan bai hani mata murmushiba, nace “nagode Samha”.
Tad'an langa6e kai alamar itad'in shagwa66iyace tace , “zan dai fad'ama Uncle Sam kin gode, lallai Uncle ya iya za6en k'yak'yk'yawar sarauniyar gagara badau mai jiran gado insha ALLAHU”.
dariya su Bilkisu sukayi, nidai nakasa cewa komai, sai d'an murmushi danayi.
Ta dafa munubiya takuma fad'in inason twins sisters arayuwata, dan ALLAH nima kuna sona?”.
Yanzun kam kasa daurewa nayi, nima saida na dara kamar yanda su munubiya ke dariyar, nakula ko kad'an Samha batada girman kai irinna 'ya'yan sarauta, sannan tanada surutu gaskiya”.
Cikin shagwa6a ta langa6e kai gefe, “ALLAH da gaske nake kubarmin dariya, ina addu'ar ALLAH yasa nanda wata 9 aunty ki Haifa mana twins muma”.
Amin su Ayusher suka amsa atare.
Matsowa tayi kusa dani tafara mana hotuna, nidai nakasa ma magana, lallai Samha akwai rawar kai, ta tubure da shagwa6a wai sainayi murmushi kamar yanda munubiya tayi, tanason taje tabama Galadima tagani kozai iya banbancemu. Babu yanda na iya dole na murmusa akayi, sannan mukayi gaba d'aya.
Bata bar d'akinba saida mama Rabi'a tashigo kiranta zasu tafi, aikam kamar tayi kuka, dan bataso tafiyarba, sai dai tace anjima zasuzo wajen brothers and sister's event.
Har k'ofar gida su Ayusher suka mata rakkiya, dan lokacin su aunty Mimi harsun fita, sunso ganina amma sukayi shiru kar aga kamar dawata manufa sukayi hakan, sun hak'ura tunda dai insha ALLAH gobe ina cikinsu.
Basuci komaiba dai a kayan da'aka jibge musu sai ruwa, dan haka baba k'arami yasaka aka bisu dashi mota, yace inhar ba wai bazasu iya cin cimar tamu bane to dan ALLAH suje dashi koda bazasuci ba su bada.
Godiya sukayi, suna mai yaba halaccin wannan gida mai cikeda karamci, dukda dai sunkula akwai lauje cikin nad'i gameda wannan family d'in, musamman yanda wasu suka kasa 6oye hassadarsu, aunty Mimi ta murmusa a zuciyarta tana fad'in Ashe ba masarautar mu kawai baceba keda irin wannan kitimurmurar ta family.
Mukulin farar motar da aka zubo akwatinan suka dank'ama baba k'arami sukace ta amaryace.
ai yanzu kam rasa abin fad'a baba k'arami yayi, yak'agara 'yan uwansa su dawo suga wad'annan tarin baiwa da hikimar ubangiji da yayma d'iyarsu, wadda akulum ake ganin mahaifiyar yaran a k'ask'ance acikin gidan, sai gashi tazama *RAINA KAMA.....*
Bak'i na tafiya gwaggo Safiyya tasaka aka baje manyan tabarmi a tsakar gida, aka fiddo akwatinan domin kowa yagani, makwafta duk sun shigo suma kam dan kar ayi babusu.
Gaba d'aya gidan yacike da shewa da hayaniya, tun anama irga kayan har aka bari, saibi da idanu, 'yan bak'in ciki kam sun kume waje guda, sai kukan zuci, wasuma kasa daurewa sukayi suka bar wajen.
Kasancewar su Ayusher duk suna can nashige toilet d'inmu nashiga raira kuka, nifa bammasan yanda zan fasalta muku yanda nakejiba wlhy.
★★★★
A 6angaren sister's d'ina kam su Safara'u harda kukansu, fauziyya ce kawai ta nuna farincikinta, dan har d'aki tashigo ta rungumeni tana ALLAH ya sanya alkairi.
maganar tashin hankali ga jama'ar gidanmu ba'a magana, sunma rasa yanda zasu masalta lamarinma, maman yaa hameed data kasa hak'uri saita saka masifa da zage-zage wai ai munafurcine su abbanmu suka shirya, wannan zancen k'aryane akwai magana a k'asa, 'yan koranta ma irinsu momy Hadiza suna tayata.
Nanfa gidan ya hargitse da hayaniya, kowa da abinda yake tofawa, innaro dai Abu biyune ya dameta, farinciki dakuma damuwar abinda tayita ma innarmu shekara da shekaru, yau kuma gashi ALLAH ya d'aga darajarta, ita dawanne ido kuma zata kalli Ai'sha.
Babu Wanda ya tanka a 6angaren innarmu, saima farinciki dasu mama Rabi'a ketayi abinsu, inna lami kuwa da aunty salamah sunata callara gud'a dawasu acikin matan anguwarmu, hakanne yakuma harzuk'a su maman Safada'u, suka murje idanu sunata zuba tsiya, danginsu na tayasu.
Innarmu dai tana daga cikin d'aki abinta, sai zuba murmushi take tana sharar hawayen dad'i, yau kokad'an rashin mutuncin 'yan gidanmu bai 6ata rantaba, saima wani farin ciki dasuke sakata.
🤣🤣
Maganar sisters and brothers event kam ai bai yuwuba yau, dan gidanmu gaba d'aya a harmutse yake, ga 'yan anguwa sunata turuwar zuwa ganin kaya harda mota.
Nikam ma zazza6ine yagama rufeni tunda nagama kukan, duk wannan kacaniya da akeyi ina cikin bargo k'udundune, su munubiya kam sunacan tsakar gida sun kasa sun tsare akan kayan gudun masu suruf bahana😜🤣.
Da k'yar aka tartare kayan aka kaisu falon baba k'arami kasancewar magriba ta gabato, sai bayan isha'i su Abba da Dady suka gani, ranar Abbanmu shima saida yayi kukan dad'i, ALLAH Sarki Ai'sha, nagodema ALLAH da wannan babban al'amari yashigomin ta 6angaren tsatsonki, kema yanzu k'ya samu 'yancin kanki agidan mijinki, 'ya'yanki zasu samu 'yanci a gidan mahaifinsu, dama akance ka yarda da k'addara kakuma godema ALLAH a yayin da ya jarabceka, Ashe sharrin da akama d'iyarsa zai zame mata alkairine, sun had'ata da babban mutum domin 6atanci agareta dashi kansa Ashe zai zama sanadin alkairi a rayuwar yaranne, dan yasan inba dan wannan abin yafaruba ina Galadima zai ga munaya har iyayensa sunema masa aurrenta? hikimar ubangiji yawane da ita, yakan jarabeka domin kankare zunibinka, kokuma danya d'aga darajarka ta inda bakayi zato ko tsammaniba.
★★★★★★
Labarin tarbar mutunci dasuka samu tuni ya karad'e masarautar, wasu kam dariyama abin yabasu, ina wata tarba dazasu samu ga talakawa fak'irai. suna dai fad'ane dan kar amusu dariya.
Mama Fulani koda labarin yaje kunnenta saita ta6e baki tana murmushi k'asaita, Wanda ita kad'ai tasan fassarar kayanta.
Tsaf yagama shiryawa zaije sashen da aka sauke abokansa a cikin masarautar, dan babu damar saukesu a 6angarensa, saboda angama masa gyara tsaf amarya kawai ake jira, su aunty Mimi ma dasuka kai lefe sun Sanar da amaryarsu kawai suke buk'ata, basai su Abba sun wahalar da kansuba wajen kaita da komai. Wannan dalilin yasaka aka yanke shawarar k'arama munubiya kayan munayar kawai, da safe za'aje a kuma jera mata su a gidanta😄.
Cikin takunsa na kasancewar cikakken namiji mai tashen k'uruciya ga jinin mulki dake yawo ajikinsa yafito, waya ce manne a kunnensa, yayinda d'ayan hannunsa ke cikin aljihun jeans d'insa, bayi da hadiman gidan sai zubewa sukeyi suna kwasar gaisuwa, kansa kawai yake d'aga musu yayinda yake cigaba da wayarsa da Momma wadda tana India ita batazoba.
Samha tak'araso gareshi a hanzarce, “Uncle ka tsaya mana please ”. ‘tayi maganar a shagwa6e saboda ganin ya basar da ita tamkar baima gantaba’.
d'an juyowa yayi ya kalleta sannan ya d'auke idonsa yana cigaba da Murmushin sa na k'asaita saboda addu'ar da Momma ke jero musu ta zaman lafiya da samun albarka ta har abada acikin auren daza'a d'aura a gobe. jiyake tamkar yace Momma ta dainama auren shekara d'ayannan addu'a irin haka, shifa harma tausayi suke bashi yanda suke nuna farin ciki da zumud'insu akan auren, musamman idan ya kalli yanda masarautar tagama cika tab da dangi takowanne 6angare, ga tawagar wasu masarautu dasukayo gaba tun yau, hakama 'yan siyasa ba'a magana, dan ba k'aramar gayya papi da Sarki sukaima wannan aurenba, kasancewar shine jika namiji na farko dazaiyi aure a masarautar, Wanda kuma kowa ke saka ran shine magajin sarautar masarautar.
Ita dai Samha tana tsaye tana kallonsa harya kammala wayar da Momma ya kashe.
Had'e fuskarsa yayi yana hararta, “to maganatu miya faru kuma? kike kwalan kira tundaga wata uwa duniya?, wai sai yaushene zakiyi hankali Samha?”.
Baki ta tunziro gaba, idonta harya cika da gwalla “amma dai Uncle aina fara yin hankalin ko, kumafa wani Abu Nazo na nuna maka, naje Sashenka wannan sarkin k'ofar yawanice kana wajen mai martaba”.
Kansa kawai ya girgiza yana kallonta, saida takai aya sannan yace “to aini inada abunyi, yanzuma ba wai sauraren naki zan zauna yiba, dan nan ba India bane, ba'a ganina available ko yaushe OK?”.
Harya juya zai tafi tarik'o hannunsa tana daddaga k'afafu idonta na zubar da hawaye.
Kansa ya dafe domin sanin fitinar Samha, tace,
“please Uncle Sam 2munutes to”.
Juyowa yayi tamkar zai maketa, saikuma komi ya tuna ya fasa, d'an cije lips d'insa yayi yana hararta, “ke wai wace irin fitinanniyace ne?, Uwarmi to zaki fad'amin?”.
Dariya tayi tana share hawayenta dan ganin tasami nasara, wayarta ta daddana sannan ta mik'a masa.
Nanma Harar tata yayi kafin ya kar6a, itace yagani a photo da 'yammata biyu masu kama d'aya, kamarma yarinyar dasuke shirin auren contract, harya yatsina fusaka zaice suwaye? saikuma yatuna. d'an murmushi basarwa ya saki kafin ya kalli Samha da ta tsaresa da idanu. “Uncle ina aunty Munaya anan? ”.
Wayar yamik'a mata yay gaba abinsa yana fad'in titsiye zakimin ma kenan? an fad'a miki bazan ganeta baneba?”.
Baki ta turo tana k'unk'uni, “waikai Uncle Sam bazaka ta6a canjawa baneba? kai kenan kullum sai jan ajin tsiya, shiyya sama ALLAH yayoka jinin sarauta wlhy, Aunty Munaya kin bani da wannan mijin naki mai k'asaitar tsiya, aiko wlhy tunda kace haka saina had'a maka mugunta gobe a wajen dinner ”.
Ta tuntsire da dariya saboda tuno mizata shirya masa.
★★★★★
*Rana bata k'arya........*⛹🏻♀
Yau mun wayi gari safiyar d'aurin aure, gida yakuma d'inkewa da jama'ar dukda d'aurin Auren na Azhar ne bayan sakkowa masallacin juma'a.
Tun jiya banida lafiya, amma na hana su Ayusher fad'ama kowa, sai Magani suka samo min nasha, itama dai Munubiya duk sukuku take, babu abinda ke damummu sai jimamin rabuwa da juna, dan itama kusan zazza6inne ma ta kwana dashi, sai dai dayake nawa ya had'a da damuwa saina fita nuna jin jiki.
Jama'ar gidanmu dai a harmutse suka kwana, wasuma ko barcin basu sami damar yiba saboda ciwon hasada dake cin zukatansu, gashi gida d'inke da jama'ar babu damar matsawa koda nan da canne sai an gane, bare sufita neman mafitar tarwatsa Auren, waddama suke d'an samin tallafinta kwad'ayinta yasaka canja shek'a (innaro🤣), dan jiya da suke zuba tijara shigowa tayi tamisu tas, harma tana Neman tone musu asiri gaban tawagar 'yan biki, badan gwaggo Safiyya ta lalla6a taba ba'asan inda jarabar innaro zata tsayaba kam.
Ko karyawa ban iya tashi nayiba bare aje maganar wanka, ina kwance cikin bargo sai shar6ar kuka nakeyi babu wanda yasani.
Ahaka gwaggo Safiyya tashigo kiranmu nida Munubiya, da k'yar su Ameera suka samu natashi zaune ina tangad'i, gaba d'aya nayi wujiga-wujiga dani, da taimakon Munubiya dake rik'e da hannuna muka iso gidan innaro inda su Abba suke jiranmu.
Gaba d'ayanmu ne amaren aka had'a, abin mamaki saiga innaro ta kamani ta zaunar tanamin sannu, harda lallashina wai na kwantar da hankalina.
Kowa zuba mana idanu kuwa yayi, su Fiddausi sai jan tsaki suke a zukatansu sunajin wata tsanar innaro aransu.
Itakam bama tasan sunayiba, sai nannan takeyi damu nida Munubiya.
Nasiha mai ratsa jiki da 6argo sukai mana sosai, muhimmancin aure da hak'uri, biyya da tsoron ALLAH, kare hak'in miji da k'yautatama danginsa da iyayensa, k'arfafa zaman lafiya a tsakani da rik'e sirrin miji, banda biyema k'awayen banza sukaika su baroka, musamman ma da dukanmu zamu cigaba da zuwa makaranta.
Gaba d'ayanmu kowa hawaye yakeyi, musamman mani danakejin tausayin kaina dana iyayena dabasu San auren shekara d'aya nake shirin yiba nadawo garesu.
Munci kuka sannan aka sallamomu, tunda muka dawo sai aunty salamah ta saka mu agaba dole mukayi wanka, da k'yar muka amince aka mana simple kwalliya, muka saka dakakken leshin da mama Rabi'a tasa aka d'inka mana cikin kayan biki dasuka mana itada innarmu, less d'in blue ne da fararen bet ajikinsa, sai aka nad'a mana d'an kwalima blue, munyi k'yau harma bansan yazan musalta ba, nan su Ayusher suka hau zuba mana pictures. lokacin 12 tama wuce, masallacin anguwarmu daza'a d'aura auren yagama cika dank'am da jama'a, dayake bashida nisa da k'ofar gidanmu.
Cikin gidanmu kam ai ba'a magana, dan babu masaka tsinke, sai hayaniya kakeji wani bayajin zancen wani, rabin hirar jama'a kuwa duk akan zancen lefe nane da Wanda zan aura, wad'anda suka gani suna bama wad'anda basu ganiba labari.
Su siyama dai koma ganinsu ba ayi, dan suna taya iyayensu kishi da hassada, aunty Ramla da aunty Raihana sai aunty Hauwa'u ne kawai suka shigo sukaima innarmu murna har d'akinmu, amma aunty khaleesa ko k'eyarta bamu ganiba, kuma tunda safe tazo gidan daga ita har zarah, matar yaa hameed ma mama hanata zuwa tayi, dukda tanaso tazo tama innarmu murna amma surukarta takasa ta tsare, gashi bama dad'in zaman 6angaren takejiba, saboda 'yan ubanci na dangin miji da aketa nuna mata, itama matar yaa Naseer tashigo, dan har picture mukayi da ita, amma matar yaa Shafi'u ma bata shigoba.
Hakan duk bai dameniba, dan ni yanzu basune agabana ba, damuwata tarkon dana saka kaina na auren contract shike cazan tunani a halin yanzun, Wanda ko munubiya nakasa sanarma gaskiya lamarin.
*_1:30pm_*
Masallacin yagama cika taban mamaki, tuni tawagar gidan Sarki sun iso tun bayan gama sallar juma'a, d'aurin aurene daya tara manyan mutane ta dalilin gidan sarauta, manyan sarakunan k'asarnan da 'yan siyasa, governors senators attajirai na gida dana k'etare, talakawan gari da tawagar iyaye da dangin sauran angunan, abokan su abbanmu danasu yayunmu, abokan anguna da abokan arzik'i, dangin iyayenmu mata danasu abbanmu, kowa ya hallara, bakajin komai sai kad'e-kad'e da bushe bushe irinna gidan sarauta. president da Kansa ya iso wannan waje bisa gayyatar papi, bansan yanda zan musalta muku irin cikarda anguwarmu tayiba aranar, bama zaka iya gane taka maimai inane ake d'aurin aurenba. Su Kansu masarautar su Galadima sunsha mamaki, basuyi zaton auren Na Galadima zai tara jama'a manyan mutane hakaba, dubi da yanda ba d'iyar wata hamshak'iyar masarautar zai auraba. basu San abin ba anan yakeba wai *d'uwawu yafi fuska k'yawun gani*🙊🤥😜😂 inji masu iya magana......................✍🏼
Amin afuwa, mu had'u tomorrow danjin yanda d'aurin aurenba zai kaya⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀.
Barkanmu da dawowa😄✋🏻🤝🏻
*_ya ALLAH ma gafartama iyayenmu_*😭👏🏻
*_Typing📲_*
*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
👉🏻2⃣0⃣
.........A cikinmu Fauziyya ce babba, dan haka aka fara d'aura auren ta, daga nan sai ni da Munubiya, an fara d'aura na Hassana Auwal fharuk (munubiya) da yaa marwan Ibraheem, sannan ni Hussaina Auwal fharuk (Munaya) da Muhammad Sameer Saifudden Abubakar (Galadima), saikuma Safara'u, sai Haleematu, Fiddausice k'arshe.
Ana gama d'aurin auren busar algaitu suka fara tashi, sarkin marok'a yafara zuba kirari wa Ango Galadima sarkin gobe a masarautar gagara badau.
Maganar k'yawun da Anguna sukayi ma 6ata lokacine, kowanne yafito angonsa sak abin kallo da birgewar kowa, duk miskilancin yaa Marwan saigashi yana washe hakwara tamkar gonar audiga😁.
🤥ance anguna basa kuka ranar aurensu, to kuwa yau saiga Galadima na share hawaye, dukda auren contract yayi nakuma shekara 1 kacal, saiyajisa wani iri daban, ya kuma zama babban mutum, tuno Abie dayayi yasaka hawaye fitowa daga idanunsa, bazai iya tuna tsawon lokacin dayayi kuka na k'arsheba, amma saigashi yau yanayi acikin d'umbin jama'a, akuma ranar d'aurin auren da ya rad'ama suna na (wucin gadi).
Papi ne yad'an bugi kafad'arsa yana murmushin jin dad'i shima, dajin wata k'aunar jikan nasa ta musamman.
Aikam masu videos da photuna ansamu abinyi, hakama masu d'auka awaya ba'a magana.
Kafin kace mi social media ta d'auka, lungu da sak'o hotunan d'auren aurenne suketa yawo, musamman da jama'a ketajin wai wadda aka bugasu a jarida yana kissing ce ya aura, wayyo ALLAH abin magana yasamu a yanar gizo, kowane polder na charts ka shiga zancen kenan dai.
Daga wajen d'aurin aure tawagar gidan su Galadima k'aton hall d'in da aka tanada domin cin abincin bak'i suka nufa, duk wani maiji da kansa zaka sameshi awajenne, Galadima har kansa yafara ciwo saboda yawan magana ta amsa gaisuwar jama'a da murna da yakeyi.
Ana tsaka da cin abincin Momma ta kirashi, dama shi ba ma abincin yakeciba, zaune kawai yake yana juya spoon a plate, wayarsa yaciro daga aljuhun gaban rigar milk d'in shaddarsa, dan tuni yacire malum-malun d'in tana hannun Harun.
Ganin Momma yasashi mik'ewa yafice daga hall d'in gaba d'aya, can waje yasamu wasu kujeru ya zauna sannan yakirata ta video call, tana d'agawa sai kawai ya fashe mata da kuka ganinta zaune kusada Abie.
daga Momma har Abie d'in sagade sukayi suna kallonsa, saida yayi mai isarsa yasaka handkerchief d'insa ya goge fuska sannan Momma tace “ho d'an nema duk murnar aurence kokuwa shagwa6a ce ta motsa?”.
Tur6une fusaka yayi zai sake wani kukan Momma ta kwashe da dariya irin wadda yadad'e baiga tayiba, Abie ma murmushin sane ya fad'ad'a sosai. saida Momma tayi dariyar mai isarta sannan tace, “Muh'd kafa girma, kai yanzu babban mutumne, nan kuma da wata shekarar kazama baba, amma katasamu gaba kana kuka?”.
Handkerchief yasaka yakuma goge hawayen dasuka taho masa, sannan yace “momma na barka da rana”.
“Barkan ka dai angon d'iyata Munaya, ALLAH ya sanya alkairi yabada zaman lafiya yasa bad'i iyanzu munan muna shagalin sunan jikan mai martaba”. tayi maganar tana kallon Abie daketa zuba murmushi, gira d'aya ta d'aga masa, shikuma ya k'yafta mata idanu.
Dariya Galadima yasaka musu, irin wannan soyayya haka summa manta dashi.
Gyaran murya yayi sannan Momma ta d'ago tana kallonsa, suka saki dariya lokaci d'aya. yayinda Abie ke tayasu da Murmushi.
Galadima ya tsagaita dariyar yana fad'in “my Abie ya jiki?”.
Da idanu Abie ya amsa masa da Alhmdllh, sannan yamasa nuni da ALLAH ya Santa alkairi.
Hannu yasa yarufe fuskarsa alamar jin kunya.
Har aka kammala liyafar cin abincin yana a waje suna hira da parent d'insa, saida papi ya aiko akirasa saboda yanason nunashi wa jama'arsa da basu sanshiba, hakan yabama wasu daga cikin 'yan masarautar su haushi, sai dai basuda yanda zasuyi da wannan tsohon mai k'arfa-k'arfar tsiya da Nuna Isa.
Bayan ya Yanke call d'in yamik'e yabi bayan d'an Aiken, ya iske a hall d'in kuma papi ya had'a wani video call d'in dasu Momma, domin Abie yaga d'umbin jama'ar dasuka halarci d'aurin auren gudan jininsa.
Aiko yaji dad'i sosai harma Momma, harda hawayen farin ciki Abie yayi.
Nandai a kaita zuba masa addu'ar Neman lafiya ga mummunar addu'a ga dukkan masu hannu na shigarsa wannan halin tsawon shekaru, da idanu yake fad'ama Momma magana itakuma tana fad'a musu. Daga nan Galadima yayi jawabin daya ta6a zukatan jama'ar wajen, wasu harda share hawaye, wasu daga cikinsu dasuka San wasu abubuwan daya faru wa tsohon sarki Saifudeen kam duk sai zukatansu suka karye, musamman masu hannu aciki dasuka bada gusunmawa, jin addu'a da alwashin d'ansa Muhammad Sameer dake tabbatar da bazai bar duk mai hannu acikiba, sai dai shima amasa irin na mahaifinsa, hakanne kawai zai iya dakatar dashi.
Abie da Momma Kansu kuka sukeyi daga can suma.
Taron yatashi zukatan wasu cikeda tausayin Galadima da k'udirin taimakonsa, yayinda yasamu k'yaututtuka daga manyan k'asar.
Masu hannu aciki kuwa suntafi da nufin sake shiri akan Galadima d'in, domin aganinsu sunyi sake d'an zaki ya girma, kuma Galadima na neman zame musu *RAINA KAMA......*
★★★.★.★.★★★
Gidanmu kam tunda aka kammala d'aurin aure labari ya shigo gabana yashiga luguden daka, rungume juna mukayi ni da Munubiya muka fashe da kuka mai ban tausayi, Wanda muka saka jama'a dayawa kukan, ciki kuwa harda Innarmu da mama Rabi'a. babu wanda yace mu bari, aka barmu mukayi mai isarmu, dan kowa yasan dolene muyi irin wannan kukan na rabuwa, dan yau babu fashi dolene mu Rabun, abinda baita6a faruwa agaremuba, kullum a gado d'aya muke kwana muke tashi, kowanne aiki tare mukeyin sa, komai namu iri d'ayane, daidai da pants & bra iri d'aya muke sakawa, idan d'aya bashida lafiya saika d'auka muduka bamuda lafiyar, babu abinda ke banbantamu sai hali, amma yau gashi aure zai banbantamu, jinai inama muma mazane tamkar su Aiyaan, yanda babu mai rabamu d'in.
Haka dai wannan yinin biki akayishi a wani iri, mu cikin damuwar rabuwa, matan gidanmu cikin hassada da bak'in cikin mun fisu.
danma Su Abba sunyi dogon gargad'i akan wlhy duk wacce tasake tada finina a gidan sai dai ta k'arasa bikin a gidan su.
Wannan furucinne yasaka kowa yin likimo, sai dai fa ta ciki na ciki🙊😂.
Hotunama da akayi na family wasu fuskar tasu tamkar kashin farar safiya😖🥴, Innaro kam ai mune nagaban girarta a yau, sai dama-dama takeyi damu, dama komai akayi saitace an kaima Ai'sha dai ko, (😂su innaro anga banza).
Wannan abun datakeyine keta kuma hasala matan gidanmu da 'ya'yansu, itakam ko a ha6ar kallabinta, warkajaminta kawai takeyi na murnar auren jikoki.
Yayinmu mazane kawai babu ruwansu, duk suna cikin farin cikin wannan aure.
Bayan la'asar sakaliya saiga sak'o daga masarata mutane biyu d'auke da akwatina biyu wai sun kawo kayan da zansa awajen dinner ni da Munubiya, sun shirya dinner d'inne mu biyu kawai banda sauran amaren.
Wannan lamari kam ya sosa zukatan mutane da yawa, ni kaina banji dad'in hakanba gaskiya, dan banason su d'auka kamar mun banbanta da sune yanzun, gaskiya da ace inada Number Galadima dana kirashi nace a fasa wlhy, saboda muma anan gidanmu yayunmu sun shirya mana dinner d'in gaba d'ayanmu, duk da ni dama ban saka ran zuwan Galadima ba a wajen.
Gashi kuma gate pass guda 30 kacal suka kawo, alamun basa buk'atar mutane dayawa a wajen kenan, ikuma na nace inhar bada sauran 'yan uwana ba ban zuwa nima d'in.
Lallashin duniya anyi nak'i sauraren kowa, nakafe akan bazan jeba.
Matan gidanmu kam cewa sukayi munafurcine kawai.
Zancensu bai dameniba, nidai ina akan bakana bazanjeba. su Ayusher sun rasa yanda zasuyi dani, dama akwai number Galadima saisu kirasa su sanar masa halin da ake ciki.
Innarmu kam ko k'ala batace daniba, yitaima tamkar batasan mi akeyiba, mama Rabi'a da Aunty Salamah sai fad'a sukemin kamar zasu dokeni, hakama innaro, sai jaraba takemin harda dungure min kai.
cikin ikon ALLAH kuwa ana cikin haka saiga kiran Samha yashigo wayata, Ayusher ta d'auka suka gaisa, azaton Samha nice, saboda muryar Ayusher ma tana kama da tamu. Tace, “Aunty gimbiya ya hidima?”.
Murmushi Ayusher tayi danjin sunan nawa harya canja, tace “ba ita baceba Ayusher ce”.
Cikin jimami tace Aunty gimbiyar fa?”.
Labarin komai Ayusher tabata, sannan tace “dan ALLAH ko zaki had'ani da Galadima?”.
Samha tace “babu damuwa bara na dubashi, duk da nasan yana tare da abokansa yanzun”.
Godiya Ayusher Tamata sannan suka yanke wayar akan idan tagansa zata kira”.
Masifa nahau yima Ayusher akan miyasa zatace saita fad'a masa, nidai koma miye babu inda zanje.
Banza Ayusher tamin tamkar batasan inayi da itaba ma.
Kusan muntuna 7 saiga kiran Samha yasake shigowa, Ayusher ta d'aga, maimakon taji muryar Samha saitaji ta Galadima cikin k'asaitar nan tasa da izza.
Nutsuwa Ayusher tayi sosai ta gaisheshi, sannan ta masa bayanin komai.
uffan bai ceba saida ta kai ayar zancenta, lips d'insa yad'an cija kafin yace “had'ani da ita”.
A kunne Ayusher ta sakamin wayar, yayinda kowa yafice daga d'akin aka barni ni kad'ai saikace wata mayya.
Dagani har shi kowa yayi shiru, shi yanajin kansa nima hakance, kusan minti 4 yaji banida niyyar tankawa saiya yi guntun tsoki, “shin ke baki iya gaisuwa bane?”.
Dukda naji ban k'yautaba saina ta6e baki, cikeda dakiya nace, “ina yini”. muryata a dishe take saboda kukan danaketa sha tun jiya.
Bai amsa gaisuwarba yace “wane sak'o kika bada a bani?”.
Saida na tunzuro baki sannan nace “yoni minace abaka?”.
Lips d'insa ya lasa yana fad'in “nikikema wannan abun?”.
Banza namasa danni bansan mina masaba kuma.
Yaja guntun tsoki, “ki kama kanki fa, karkiga auren contract mukayi, akwai sharid'd'a acikinsa, bana buk'atar ganin kowa awajen inba keda sister d'inki ba, haka na tsara, kuma babu mai canjamin ra'ayina, zuwa anjima wadda zata shiryaku zatazo, idan kin gadama karki bari a shiryaki, nikuma zakiga mi zan yi akai..”.
d'if ya katse wayar, cirota nayi daga kunnina ina dubawa tamkar zan ganoshi acikinta. naja tsaki ina fad'in “aikin banza kaje ka koyo R sannan kamin wannan ikon, nifa baka isa takani ba acikin auren contract...... ”
Sauran maganar ta mak'ale a mak'oshina saboda shigowar munubiya.
Zama tayi akusa dani, “sweetheart zan iya neman alfarma a wajenki?”.
Kai na d'aga mata.
Ta gyara zamanta sosai tareda kamo hannayena duka acikin nata. “inason kima mijinki biyyay kiyi yanda yakeso, yanzu hakkin bin dokarsa tarataya a kanki dole inhar bata sa6ama addini ba, kina kaucewa kuwa zaki had'u da fushin ALLAH, tunda yace haka yakeso ayi kiyarda kawai, awa nawane anyi an tashi kowa yakama gabansa”.
Alk'awarin Dana mata yasani amincewa zanje tilas amma badan raina yasoba.
An tsara wad'anda zasuje, dan haka aka damk'ama kowa gate pass d'insa a hannu ya Adana. dukda wasu gani kwaf zasuje kuwa.
Bayan sallar isha'i saiga masu mana shiri sun iso, babbar magana wai d'an sanda yaga gawar soja.
Jama'a ni kaina bamma gaskata cewar nibace ballan tana Ku 'yan kallo, saika rantse kace dama can mud'in jinin sarauta ne, munyi k'yau har mun gaji, gashi dandanan akayi aka gama, har kusan 9pm muna jiransu, gidan yayi tsitt duk wad'anda zasuje dinner sun tafi, wad'anda zasu bimune kawai tare damu muna jiransu Galadima, dan shima yaa marwan d'in baikai ga isowaba.
Sai around 9:15pm sannan mukaji dirar mitoci a k'ofar gidan.
Aunty Mimi ce da kanta tashigo itada wasu bayi guda hud'u, saida ta gaisa dasu innarmu sannan aka mata iso d'akinmu, wani dad'ine ya ratsa zuciyarta, dukda batasan wacece matar k'anin nataba acikinmu, amma muntafi da imaninta, jitai inama natane wad'an nan twins, ALLAH yasa haihuwar farko na haifo musu irinmu.
Daga ni har munubiya rissinawa mukayi muka gaidata cikeda girmamawa, dan munsan a haife ta haifemu, dukda bawai sa'ar innarmu bace, ko mama Rabi'a ma ta girme mata.
Hakan damukayi yamata dad'i kuma mun birgeta, ta kama hannayenmu tana yaba k'yawun damukayi, wasu turarurruka ta fidso kala uku a bag d'inta tashiga feshemu dasu, dukda uban turaren da aunty salamah tamana wanka dasu zance, dan itama haka taita zazaga mana su d'azun, ni saima hawarmin kai sukeyi wlhy.
Wasu alk'yabbu masu azabar k'yau iri d'aya aka saka mana, takalman dake k'afarmu kansu abin kallone.
Aikam bamu fitaba saida tamana hotuna, afaloma saida aka mana muda su innarmu.
A waje muka iske motoci guda uku masu k'yau, da alama sauran motocin sun d'auki jama'a sun tafi.
Saida mukaje jikin motocin sannan aunty Mimi tayi murmushi tana kallonmu, to karnayi abin kunya, wacce ta my k'ani? wacce ta Marwan?.
K'asa mukayi da kanmu saboda kunya, saida ta kuma maimaita tambayar sannan munubiya tayi k'arfin halin nunani, kunyarmu takuma birgeta sosai, hannun munubiya ta kama tana fad'in kece babba ai, zoki fara shiga”. a motar farko ta sakata, sannan tadawo takama hannuna ta sakani a ta biyu.
Rufe k'ofar tayi takoma motar bayanmu tashiga. yayinda kuyangin nan hud'u suma suka shiga motar k'arshe.
Tunda nashigo k'amshin turarensa yadaki hancina, ta gefen ido na saci kallonsa, kishin gid'e yake a kan kujerar motar tamkar yasamu gado (dan bansan yama zan musalta muku tsarin motarba nikam, ammafa komai abin kallone) k'afarsa d'aya a k'asa d'aya akan kujerar, kansa na gab dani, dan dazai zame ko motsawa dolene saiya ta6a jikina, sanye yake cikin wasu Fararen suit masu azabar k'yau, sunyi mugun fidda ainahinsa matsayin cikakken namiji mai aji da gayu, aikin danna wayarsa kawai yakeyi tamkarma baisan na shigo motarba, dan ko sau d'aya bai d'ago ya dubeniba.
Nima basarwa nayi nayi tamkar bansan dawata halitta acikin motarba bayan driver.
Shikuwa tun shigowa ta k'amshin turarena yabigi hancinsa tareda shiga magudanar jininsa, a rayuwa yana matuk'ar k'aunar k'amshi, lumshe idanunsa yayi yana lasar lips, amma jinkai da k'asaita ta hanashi d'agowa yako dubeni.
Itakam munubiya tana shiga bayan aunty Mimi tarufe k'ofar yaa marwan jawota yayi jikinsa, tareda sumbatar gefen kumatunta. ta matse jikinta waje guda saboda tsorata, muryata na rawa ta gaidashi.
Ya amsa yana wani kuma shinshina wuyanta da bata wasu kisses d'in.
Mamaki da al'ajabine suka kamata, anya kuwa wannan yaa marwan d'in nanne mai shegen muskilanci da share mutane?, kanta bai ida kwancewa ba saida taji hannunsa indama batayi zatoba, tamkar zatayi kuka tace “please yaa marwan kayi hak'uri dan ALLAH, cikin motane fa”.
Rungumeta kawai yayi batareda yayi maganaba.
A wannan yanayin mukaji motocin sun tsaya.
Bayan an bud'e mana duk muka firfito, tsakanina da Galadima kuwa babu Wanda yacema wani kanzil har muka fito.
Yaa marwan da Munubiya ne agaba rik'eda hannun juna, saini da nawa d'an hayak'in Mr k'asaita abaya, harmun fara tafiya Aunty Mimi tamasa magana. banji mitace ba saboda da Indianci tayi maganar😜.
Jinai kawai wani lallausan hannu cikin nawa, dagani harshi babu shiri muka kalli juna saboda shock d'in daya jamu a time d'aya.
Shine yay azamar janye nasa idanun yana cije lips, kafin nima na janye nawa cikeda kasala da luguden zuciya.
Mamakine ya kamani lokacin da muka shigo hall d'in, inda sauran 'yan uwanmu sukene Ashe, sainaji dad'i sosai wlhy.
Nandanan mc yashiga sanar da isowarmu, tunda muka shigo kallo gaba d'aya yadawo kanmu, musamman mutane dake son ganin Galadima a yau.
Can saman hii table muka isa muma, mazaunin daya kasance namu, su Safara'u tamkar su saka ihu saboda ganin yanda muka had'u tamkar bamuba, duk sai suka raina nasu kwalliyan dukda suma sunyi matuk'ar k'yawu kuwa..
Bayan mun zauna angunan suka taso suna kawo gaisuwa wajen Galadima, fuskarsa d'auke da murmushi yake amsa musu tareda mik'a musu hannu suyi musabaha, koda sun nok'e saiya kamo hannun nasu da kansa.
Bak'in ciki tamkar yakarsu Halimatu, ganin angunansu suna kai gaisuwa wa Galadima, basusan hakan dole bane agaresu kodan kasan cewarsa d'an masarauta wandama ake da yak'inin zama sarkin gobe idan da rai, idanma badan hakan ta kasanceba ta ina suka Isa ganinsa balle ma har suyi gaisuwar Baki da baki harda musabaha. Aishi adaline ma tunda harya iya halartar taron nasu.
Yayunama duk saida sukazo suka gaisa dashi, mazan da matan, sannan mukayi hotuna, su Zarah da siyama matan 'ya'yan senator kam ai yau saikikaji tsit babu felek'e, dan mazajen nasuma ko zuwa basuyi wajenba, kamar yanda basu halarci tasu dinner d'inba lokacin aurensu.
Aunty Mimi dakanta ta kar6i microphone tabada hak'uri da neman alfarmar tafiyarmu, saboda suma mutanensu nacan suna jiran isowarmu, dama munzone domin kar6ar excuse.
Hakkane yad'an rage fushin wasu, sannan mun tafi dawasu acikin yayunmu maza.
Mun tafi kowa yana yaba tsarin namu.
Yanzuma haka muka tafi tamkar wasu kurame, saidai yanzu a zaune yake, yajingina kansa da kujera ya lumshe idanu.
Nikam gefe na maida kaina ina kallon titi.
Yanzun kam koda motocin suka tsaya bamu fitaba, sai kusan mintuna 10, Ashe lokacin harsu munubiya da yaa marwan sun shiga, saura mu kuma.
Bamu fitoba saida akayi knocking glass d'in gefensa, ahankali ya sauke glass d'in batareda ya bud'e idonsa ba, wanine yalek'o yana fad'a masa mu fito, duk bud'e mana motar akayi dagani har shi sannan muka fita.
Zagayowa yayi inda nake tsaye, a mamakina da al'ajabi sai kawai naji ya sak'alo Hannunsa a k'uguna, cikeda firgici nad'ago na kallesa, saiya sakar min harara dawani munafikin murmushi, saika rantse da ALLAH kallon soyayya yamin, nikam dukda kwarjini dayamin saida na turo baki gaba da hararsa a kaikaice, ALLAH ma yasoni baiga hararba.
Ahankali muke tafiya saboda Alk'yabbata, yayinda kuyangin ke watsa wasu flowers masu k'amshi a inda zamu taka, aunty Mimi kam da wata daban santaba suna feso mana Abu mai k'amshi.
Kai jama'a wajen taronnan fa ya had'u, k'arshen had'uwa kuwa, an k'awata wajen da kwalliyar white and Golden colors, yayinda kwalliyar jama'ar wajenma white and Golden colors ne, (suma mutanemu dasukazo wajen dama ankawo musu kaya irin kalar).
Mazan sunsha wankan white suit, takalmansu da agoguna zuwa tie duk golden, matan kuma white gown ta material sai d'ankwali golden.
Yayinda tamu shigar ta kasance golden gaba d'aya, su Galadima kuma sun saka white suit, komai nasu white ne shida yaa marwan.
Tunda muka shigo wajen ya d'auki tafi, yayinda aka saki wak'ar da aka raira domin mu. (Bara nad'an raira muku kad'an🤥😜).
*_Alk'awari yacika munubiya alk'awari yacika.... yacika yacika munaya alk'awari yacika amarya...._*
🙄iya nan na iya to🥴⛹🏻♀
Gaba d'aya sai wani tsoro da kunya ya kamani, nafara tafiya ahankali tamkar kazar da kwai ya fashema aciki.
Bansan lokacin da Galadima ya rankwafo kainaba, dan tunanina yatafi wajen mamakin yanda suketa shiryama auren shekara 1 wad'annan bidi'oin.
Jinai kawai an d'aukeni cak, ihu kawai aka sanya awajen da uban tafi, yayinda aka kuma sakin sabon kid'a na musamman.
Runtse idanuna nayi kawai zuciyata na kai kawo tamkar zata fito waje saboda mamakin munafuncin Galadima. (Yo inba munafuci ba miye na d'aukata agaban jama'a, bayan ni da shi ko magana bata had'amuba😏).
Bai direniba sai a kujerar da aka tanada domin mu.
Anan d'inma zama yayi yasakani jikinsa, kunya da haushi duk sun cikani, wlhy badan karna kunyatashi ba dayasha mamaki. Gashi sai wani magana yakemin k'asa-k'asa kai kace ta arzik'ice, nanko duk gargad'ine wai na kama kaina karnayi abinda wani zai fahimci ba auren soyayya bane a tsakaninmu.
Baki na tunzuro gaba dan haushi, yasaka d'an yatsa ya d'alli bak'in nawa.
Naji zafi wlhy kuma.😏
Abun ALLAH wadai bai k'areba saida akazo yanka cake, bayan su munubiya sun gama nasu cikin mutunci da yaa marwan saimuma muka yanka namu, maimakon yabani kamar yanda na bashi sai kawai yasa Wanda yaciro a bakinsa, bayan yayi tamkar zai bani, harna bud'e baki zan kar6a saiya lunk'uma a baki, nanma mutane suka Sanya dariya da tafi.
Wai kawai ina hararsa saboda haushin abinda yayi sai kawai naji fuskata cikin tafin hannunsa, kafin nayi wani yink'uri ya had'e bakina danashi waje d'aya yajuyemin cake d'in daya gama narkewa da yawunsa a bakinsa.
Bai cire bakinsaba saida ya tabbatar na had'iyeshi sannan.
Ai wlhy ihun yanzun yafi na ko yaushe, abokansa harwani kirari suke masa, yayinda wasu keta d'auka a hotuna, Munubiya kanta kunshe fuska tayi a alk'yabba tana dariya, duk miskilancin yaa marwan saida ya dara shima.
Aikam saida nayi hawayen bak'in ciki, mugu kawai yabani k'azantar yaunsa nasha, wlhy badan mutaneba saina k'ak'aro amai kuwa.
Daya bani drink ko k'insha nayi, ya rankwafo kaina bakinsa saitin kunnene yace, “bakiji sharad'inaba kenan? ALLAH shima zan zuba abaki na juye miki shi a bakinki yanzunan. Ai babu shiri na kar6a kuwa.
Daga nanne Samha taje wajen mc ta kar6i microphone wai tanason saka gasa tsakanin Uncle Sam da Uncle marwan, za'a shigar damu wani d'aki, bayan mintuna biyu mu fito, kowa ya nuna matarsa, duk wanda ya canka dai-dai shine yaci gasar, shikuma zata bama k'yautar.
Galadima jiyay tamkar ya mangare Samha, sai antaya mata harara yakeyi itada Sauban, dan yasan wannan munafurcin sune suka kulloshi.
Ai kam k'in kallonsa sukayi sunata k'unshe dariya.
Dole yanda sukace d'in haka akayi, muna shiga aka gyaramin janbakina da Galadima ya tsotse, sannan aka kuma feshemu da turararurruka saboda kowance k'amshin turaren mijinta daya manne mata yabar jikinta.
Kujeru aka ajiye mana muka zauna, kowacce taci serious.
Da Galadima aka fara, gabansa sai dukan sittin-sittin yakeyi, danshi da gske ba iya gane ni zaiyiba, inba na nuna halin nawa bane.
Aiko ya nuna d'aya acikinmu, mik'ewa tayi takoma gefensa ta tsaya, amma bai ta6a ta ba, dan ba'asan wacecenba acikinmu.
Shima yaa marwan rikicewa yayi, dama mafi yawan lokuta ta halayya yake ganemu, shima dai wadda Galadima yabari ya nuna.
Bayan suma sun koma gefe aka koma kan za6in Galadima, mc yace “zamu iya Sanin wacece?”.
Murmushi munubiya tayi, cikin sanyinta tace “Munubiya ce”.
Juyowa Galadima yayi ya kalleta, sanyinta ma kawai ya isa tabbatar da gaskiyarta.
Nima aka tambayeni cikeda Jan aji nace “Munaya ce”.
Nanama ihun akayi, cikinsu babu Wanda ya canka dai-dai, dan haka ni da Munubiya su samha suka bamu wata k'yauta dabamusan ko miye a cikiba, wai mune mukayi wining.
Daga nan aka rufe taro da addu'a aka tashi.
Har gida suka maidamu muda tawagarmu, lokacin 1:15pm.
Muna zuwa kowa makwanci kawai ya nema...............✍🏼
Irin wannan dogon page haka😨🙆🏻, shikenan harda na gobe na had'a muku kenan🙄.
⛹🏻♀⛹🏻♀
,
0 comments:
Post a Comment