Rai bakon Duniya..!
Misalin karfe 7:00am..!
Gabadaya gidan Baba Sa"idu haka suka tashi zuciya ba sukuni,Wasu sun samu barci da yar natsuwa ammh akwai wadanda basu runtsa ba ciki har da Amina domin yadda taga Rana haka taga Dare ita ba kuka take ba Domin zuciyarta ta kekashe bata ma jin yin kukan abu daya ta sani bata son tuna inda kaddaranta ta jata ta kaita domin in tana tuna yau ita ta haramta ga Aminu sai taji gabadaya Duniyar na juya mata,Abu daya yake mata nauyi acikin kirjinta Aminu shi take so ta san wani hali yake ciki ammh babu dama sannan sai Aba da Yaya wanda bata taba tsammamin Fushinsu zai dameta ba abu daya ke damunta Shedar iskanci da suka Zargeta dashi sauran bata damu ba Domin ta aikata ammh abu daya ke sata bakinciki yadda aka kasa Fahimtar abubuwan da suka faru kan yadda suke..!
Tun bayan data idar da sallar asuba bata jirga daga inda take zaune ba ta kalli gabas da katon hijabin haddarsu bangon Dakinsu ta kurama ido ita ba kuka take ba ammh kana ganinta kasan bata cikin natsuwarta cikin kwanakin nan gabadaya Amina ta Zafge sai idanuwa fuskarta tayi wani iri tayi zuru zuru Hamida da Hanne ne ke tare da ita acikin Dakin Domin Ya zeenatu ta fita Kitchen ita bata koma barci ba.
Hanne ce ta gaji da ganin Amina ahaka yasa tatashi tsam ta koma kusa da ita tadafata tana fadin"Amina don Allah kiyi hakuri..Ki yi hakuri..Haka Allah ya kaddara miki!
Kamar bazata tankata ba tama yi Tunanin bata jinta yasa ta kara Girgiza kafadanta tana Fadin"Ameena kina jina kuwa..?
Sai alokacin Amina tayi motsi da bakinta Cikin wani irin Sautin da Hamida da Hanne zasu iya Rantsewa da Allah basu taba jin Amina cikin wannan Sautin ba..!
Asaman lebenta mganar ta fito cikin karyewan zuciya da Rayuwa tace"Ina jinki Hanne..Tun jiya keda Hamida kuke maimaita kalmar nayi hakuri..Tawa kaddaran kenan baku Tunanin na Haddace wannan..?
Tafada Lokaci Daya tana sakarma Hanne manyan Idanuwanta cikin wanu yanayi na neman ma tallafi Dayasa Hanne saurin kauda kanta Tana fadin"Na sani..Ammh ki sani mai hakuri shi ke da riba watarana..Ko Hamida..!?
Hamida da duk jikinta ba Dadi tace"Sosai ma Hanne..!
Tana jinsu gani take su din suna cikin Farinciki tunda rayuwarsu bata yi musu juyin waina kamar yadda tayi mata ba..!
Kara murmusawa tayi wanda kana ganinsa zakasan ba Annuri ko jin Dadi acikinsa tace"Hakane..Nagode bazaku je hadda bane..?
Ta fada tana son kauda mganar domin tasan bazasu taba gane wani Hali take ciki ba..!
Hanne ce tace"Bazamu ji dadin zuwa baki ba Amina ki saki jikinki..Sati mai zuwa sai mu koma tare..!
Amina taji kamar tayi kuka alokacin Dama dama ace baya zata dawo Da tafi kowa jin dadi bata samu zarafin mgana ba Hamida tace"Ni kaina bazan ji dadin zuwa ko"ina ba baki ba Amina..Tare muka tashi muke komai tare..Wh damuwarki tamu ce Amina don Allah kiyi hakuri..!
Tana Fada sai kuka hakama Hanne sai ta rumgume Amina tana kuka hamida ma tazo suka hadu suka Rumgumeta suna Fadin"Amina wlh mu zamu shaidarki..mun sani Fahimtar hakane basu yi ba..!
Amina cikin wani irin kuncin zuciya tace"Wlh ban taba iskanci ba..Bantaba kadaicewa da Wani Namiji ba da sunam alfasha ba..Abunda ya faru ranar Tsausayi ne..Wannan itace kaddaran daman datake jiran bawa koda yaushe..?
Itace kaddarata sannan kuma natabbata na Fita zakkan da ake yawan Fadi akaina Tunda gsshi ni Tawa Rayuwar ta kare ba yadda ta kowa take karewa ba..Hanne da Hamida kun ji dadinku bakinciki bai gauraye jin dadinku ba..Wlh ayadda nake ji dama ace Ban hadu da Aminu ba dama komai kamar mafarki ne..!
Take fada sai kuma ta fashe da kukan da ba Hawaye daga gani abun yana Fitowa ne daga kasan ranta ne
Haka suka hadu suna ta kuka kamar wasu yara bame lallashinsu cikin wannan yanayin sukaji muryan Ya Zeenatu tana Fadin"Jawaad wai lafiyan ka kuwa..?
Me yayan zatayi maka Dakake ta mata wannan uban kiran..!
Muryan Jawaad sukaji a Tsakar gida yana Fadin"Ya zeenatu tun dazu nake tashinta taki tashi..!
Tana daga kofar kitchen ta Hararesa yana Sanye da zani da alamu wanka yayi Cikin dan fada tace"Bazaka je ka shirya ba sai Idi ya tafi ya barka ko..?
Cikin Tura baki yace"To ai ban ga Jallabiyata ba shine nake ta tashin Mama ta Daukomin taki tashi..!
Domin kaf gidan nam Jawaad kadai ke kiran Yaya Mama shi har alokacin sunan Yaya bai kama bakinsa ba..!.
Ya zeenatu da mamaki ya kamata tasan yaya bata barcin safe In ta idar da Sallar asuba sai gari ya waye tana Lazimi koda bata ga fitowarta ba Tasan tana da Bayi adaki kila ciki tayi Hidimarta ammh cikin son kwantar da Hankalin Jawaad yasa tace"Kila barci ne ya Dauketa bayan tayi sallah jeka ka Duba cikin Dirowa kila ka gani kayi sauri fa..!
Har ya juya sai ya juyo yana Fadin"Batayi sallah ba fa ya Zeenatu..!
Dam gabanta ya fadi cikin Fitan hayyaci tace"Bangane ba..!?
Cikin yarintarsa yace"kuma fa bata motsi..!
Karaf Sai a kunnen Mamanmu Dake zaman jiran wannan sakon ya isketa Mikewa tayi bakinta kamar ya Tsage Cikin Yar dariya tace"Komai ya kamallah..!
Daga haka ta gyara yanayinta Lokaci Daya tana fitowa alamun barci a idonta tace"Zeenatu me ya faru nake jin hayaniya..!
Zeenatu da Hankalinta ke tashe tace"Mamanmu jawaad fadi yake yaya bata motsi fa..?
Ido ta zaro tana fadin"Bata motsi kamar yaya..?
Tafada cikin bayanna Firginta Wanda ya fito dasu Hamida Daga daki har da Amina Da suke jin meke faruwa gabanta ke fadi jikinta ke rawa tana Fatan ba wani abu bane zai kara kutse Cikin Rayuwarta ba..!
Ya zeenatu ce kan gaba wajen shiga Dakin Yaya har bedroom dinta jawaad suka kara samu akanta yana jijjigata yana faman fadin"Mama ki tashina ina jallabiyata..?
Yake fada ammh ko gizau dukkansu kamar an dasasu sun kasa karisawa gareta tana kwance sambal Cikin Hijabinta,fuskarta tar ta kara wani Haske sai dai abu daya ya Sandarar dasu shine ganin Idanuwanta suna kallon Saman Dakin ammh kuma bata Motsi gabadayansu kamar an Sassake jikinsu haka suka kasa karisawa..!
Jawaad daya gansu ya sauko yana jan Hannun Mamanmu yana fadin"Mamanmu taho ki gani..!
Haka yake fada kamar rakumi da akala haka ya jata har gaban gadon yaya inda take kwamce daidai Lokacin da sukaji sallaman Ya Jafar Ya zeenatu kamar walkiya ta fice da Sauri kamar ta kifa a tsakar gida taga ya Jafar Bayansa Aba ne,Kaya ne ahannun Ya Jafar da bargo da Filo sai Kwandon abinci,Bata Tsaya ko Gaida Aba ba tace"Aba ya jafar kuzo ku gani Yaya bata NUMFASHI..!
Dukkansu haka mganar ta shigesu Aba kuwa dakyar ya iya Tsayuwa da Kafarsa Meke faruwa ne..?,Tabbas wanu abu ya faru ko kuma zai faru Domin Tun jiya yake fama da Faduwar gaba da yanayi mara Dadi sai ya Danganta haka da Kila abunda ya faru ne na Amina ammh kalaman Zeenatu sun saka gabbansa kara Saki Cikin wani yanayi.
Ya jafar ne ya tsaya yana fadin"Bangane bata Numfashi ba..?
Aba bai Tsaya sauraransu ba ya taka ya shiga Dakin yaya jafar na ganin haka ya watsar da kayan Hannunsa yabi bayansa Zeenatu sai ta kasa Binsu kafafunta sun kasa Daukanta koda batasan Mutuwa ba Ta tabbata yaya MUTUWA tayi..!
Ba wanda yasan da shigowar su Aba sai dai ganinsu kawai akayi Kamar Daga sama Hamida da Hanne da Amina sun rirrike hannun juna cikin wani yanayi Mamanmu tana ganin Aba sai ta fara sauya yanayinta Taga yadda take kallon yaya tana Sakin Mirmishin jin dadin.
Kan jikinta ta fada lokaci Daya tana Fashewa da kuka sai kuma ta Mike ta Nufi Aba tana nunamai yaya Lokaci Daya tana fadin"Sa"idu duba ka gani..Kamar yaya ta MUTU fa bata motsi..!
Kalmar ta Mutu shi ya shiga kunnen Amina da wani yanayin da har Abada bazata manta dashi ba..!
Aba kuma sai ya Ture Mamanmu ya karisa gaban Yaya ya jafar na bayansa Cikin wani yanayi Kallonta yake yi yana kokuwa da Numfashinsa Allahu akbar ashe ashe mganar da sukayi jiya itace ta bankwanansu Allah ya jikanki Hadiza ya fada acikin ransa kafin ya Dago hannunta da yayi sanyi karau har ya fara sandarewa na dan Lokaci kafin ya saketa Mamanmu ta Dora hannu aka tana fadin"Ta Mutu ko..?mun shiga uku mun Lalace wayyo ni Balaraba..!
Kan Yaya tayo da Sauri Aba ya Riketa yana fadin"Natsu mana Balaraba..Wa ya ce miki ta mutu..?
Cikin dan Daburcewa tace"Bata Mutu ba..?
Kallonta yake da dukkan zuciyarsa yana Faman karanto duk addu"an da tazo bakinsa shima natsuwarsa ke neman kwacemai yasa ya Saketa yana Fadin"Jafar je kazo da Mallam..!
Da haka ya koma jikin Wardrope din Dakin ya jingina kansa yana jin kamar zai fadi Jawaad da ya fara kuka ya isa garesa ya Rumgumesa yana Fadin"Aba kace mama tatashi..!
Sai Sa"idu yaji kamar ya Sulale kasa Ya sume saboda yanayin Dayake ciki rumgume Jawwad yayi kawai yana fadin"Kayi hakuri jawaad..!
Haka kawai yake fadi zuwa Lokacin Kukan Mamanmu ya cika Dakin su hamida ma sun fara ita da Hanne banda Amina da ta kasa Fassara yanayinta ji take kamar ta Bude ido Taga komai ya koma mafarki ne..!
Sai dai ina abunda take gani gaskiya ne domin ba Dadewa sai ga Ya Jafar da Baba Mallam sun sake shigowa Cikin Tsashin hankali Aba na ganinsa yace"Dubata Mallam ta rasu ko..?
Baba Mallam bai Sauraresa ba sai da ya isa kusa da yaya ya kalleta na wani Lokaci ko bakasan mutuwa ba in ka kalli yaya zakasan ta amsa kiran Mahallicinta Cikin Fargaba yake da Tashin hankali Tun zuwan jafar dama ga Damuwar abunda ya faru gabadaya shi kanshi Baba Mallan fata yake yaya bata rasu ba baisan da wani ido zai kalli Sa"idu ya Fadamai Hadiza ta rasu ba..!
Hannunta ya rike na wani Lokaci kafin ya saka kunnensa Saitin zuciyarta na wani Lokaci cikin Sanyin Jiki ya Dago yana kallonta kafin ya Juya yana kallon Aba da kaifaffun idamuwansa da na ya jafar suke kallonsa da su Hamida Mamanmu kuma Sai kuka take rusawa..!
Aba ya kalli Baba Mallam yana Fadin"Ta rasu ko..?Don Allah in ta rasu ka fadamin..Na yarda da Allah ke kashewa kuma shi ke rayawa..!
Baba mallam yayi mamakin Kalaman Aba aransa yaji salama Cikin Dattakomsa yace"Kayi hakuri Sa"idu..Allah yayi ma Hadiza RASUWA..!
yafada Lokaci Daya yana Dafa kafadarsa alamun Lallashi abun mamaki bai ce komai ba illah matsawa da yayi ya shafe idonta sannan ya Dagata ya cire mata Hijabin jikinta ya Lullube kanta dashi Lokaci Daya yana Fadin"Allah ya jikan ki Hadiza..Allah ya kyautata zuwanki...Allah ya Sadaki da Mala"ikun Rahma hakika ke yar aljannah ce Laifin da kika aikatamin da ganga da wanda kika sani da wanda baki sani na yafe miki Duniya da Lahira Allah ya yafe miki kema yasa ki kwanta Cikin kabarinki Cikin Salama ke da kika tafi baki Gaggawa ba..Muma da muke duniyan Jiranta muke Allah yayi miki Rahama Hadiza..!
Sai alokacin Muryansa ta fara rawa yasa ya Dakata Baba Mallam da ya Jafar dake kuka Suka amsa da Ameen Mamanmu ce ta fasa wani ihu ta Fadi kasa sumammiya shi ya shigo da ya Zeenatu Dake kuka itama ganin Yaya Lullube yasa itama ta fasa kuka tabi ayarin su Hamida Dake durkushe gaban Mamanmu suna kuka ya jafar ne yayi jarumtar fita ya Debo ruwa suka shafa mata sai gata ta farfado tana kuka tana mganganun Rudewa da yadda Mutuwar ta Daketa matuka..!
Baba Mallam ne yace"Balaraba ba kuka Hadiza ke bukata ba sai addu"a ayi hakuri..kinji ko Allah ya jikanta..!
Mamanmu fadi take"Yaya ta rasu..?Innalillahi..Wayyo Allah na..!
Haka take fada tana kuka jikin ya Zeenatu dake ta kuka itama su sun samu Damar kuka ita Amina ta nan Tsaye kukan ma yaki zuwa mata maimaitawa kawai take yi wai yaya ta rasu..?ina wannan ai ba gaskiya ne yayan da jiyanan lafiyanta kalau..!
Baba Mallan ne ya Dago Aba Dake duke gaban Yaya yana kokarin Daidaita Numfashinsa cikin lallashi yace"Sa"idu tashi.kayi hakuri ka nuna Jarumta..In ka rushe suma iyalanka zasu rushe..!
Ba Musu ya Mike yana Rike Jawaad da Zuwa Lokacin ya Fahimci abunda ya Faru shekarunsa goma sha Daya yasan Mutuwa rumgumesa yayi yana kallon Baba Mallam Lokaci daya yace"Asanar ma da Mutane Baba..Jafaru kuma sai yazo da mai awon Likkafani domin ashiryata mu sallaceta zuwa gidanta na gaskiya..!
Baba Mallam ya jinjina kai kafin yace"Shine abunda zamu mata mu nuna mata soyayyarmu.muje waje..Bazaku iya zama da gawa,kuna wannan koken koken ba..Bari naje na Turo Hajiya..!
Ya jafar gaban yaya ya karasa ya Bude Fuskarta kafin yace"Allah yayi miki Rahma yaya..
Kuka ke neman kwacemai yasa ya fice da Sauri Su ya zeebatu suka kama Mamanmu dake kuka Sai alokacin Baba Mallam ya Lura da Amina cikin wani yanayi yace"Mamana sai hakuri kin ji..?Hadiza addu"an ku take Bukata kawai..!
Abun mamaki kallonsa tayi da idanuwanta cikin wani yanayi tace"DA gaske yaya ta rasu..!
Kai ya gyada mata kafin ya samu Zarafin mgana tace"Ba sai ka kira Hajiya ba..Ni zam zauma da ita har ku dawo..!
Gabadayansu suka kalleta Har Aba da su Mamanmu Cikin Sautin Amon muryan data Sadaukar dakomai tace"Eh zan zauna da ita..Don Allah kada ku hanani..Ku barni na zauna da ita na wani Lokaci na karshe a Rayuwata..!
Sai kuma taji kamar Rauni zai bayyanan mata sai ta Dake domin ji tayi kamar zuciyarta ta kara Bushewa ba wanda bai ji Tsausayinta ba Baba Mallan ya dafa kanta yana Fadin"Shikenan Mamana ki zauna da ita banda kuka kiyi ta mata addu"a..!
Da kai ta amsa mai kafin ta Nufi gaban Yaya ta tsaya sai kuma ta Sulale ta Zauna da katon Hijabinta Cikin wani irin Sauti tace"Nan zan zauna..har Ku dawo baba Mallam..Ko bata ji Dumina ba..Zan tuna watarana na zauna da ita alokacin da Numfashinta ya bar jikinta..!
Ba wanda ya tankata har suka fice Baba Mallam da Aba suka fita daga gidan su Zeenatu kuma tsakar gida suka koma suna ta kuka kafin kace me Mutuwar yaya ta Zaga ko"ina duk wanda ya kamata yaji wannan Mutuwar data girgiza mutane da Dama kowa akace yaya ta rasu sai yace Daman tayi ciwo ne..?Mutuwa ko babu ciwo ana tafiya..!
Hajiya babba Mutuwar Yaya ta Daketa Matuka duka matan Baba Mallam suna gidan Baba sa"idu tare da Mamanmu da Yaran,Amina taki Fitowa Daga Dakin yaya tana zaune gaban gawan ba kuka take ba sai dai da ka ganta bata cikin natsuwarta Fata take taga komai ya koma ba yadda take gani ba Hajiya tayi tayi Amina tatashi ta koma Falo in da su Mamanmu ke zaune dasu Anty Amarya su hanne suna Dakin mamanmu sanye da Hijabai su da matan su ya jafar sun saka hijabai suna ta karatun Qur"ani suna Hawaye tunda Hajiya ta hana su kuka..!
Ammh Amina taki tashi fadi take"Hajiya ki kyaleni..Wlh Lokacin Yaya na Raye ban taba zama da ita ko na minti biyar ba..?Bazaki barni na zauna da gawanta ba ko naji Dadi..!
Daganan Hajiya tasan Amina ba kalau take ba,Sai ta kyaleta sai itane tazo suka zauna anan tare tana mamakin ko Kwallah Daya Amina batayi ba..!
Tana fatan kada abunda suka faru da su saka zuciyarta ta Harbu da wani matsala..
Alokacin bataasan me Amina ke Tunani ba..Mganar Aminu ta Tuna da taba cemai ta fison Mamanmu akan yaya alokacin Dariya yayi yana mata kallon yarinta kafin yace"Meenata ke yarinya ce har yanzu shiyasa baki san girman uwa ba..Ammh Har Abada Uwa uwace bamai kwace wannan Matsayin Allah ne ya basu..Bazaki Fahimce matsayin Uwa ba sai Ranar da kika rasata ina mai Tabbatar miki ko muna tare ko bana Tare sai kin fi kowa kukan rasa yaya..Ga Mamanmu din da kike fada ammh Bazata iya kare miki wannan Jinin ba Amina..Bazata iya shafe miki makwafin UWA BA har Abada..!
Sai ayanzu mganarsa take Dawo mata Domin abaya in ya fada bata Damuwa da mganarsa ashe ashe ranar ma tanan nan kusa abu Daya ke damunta Yaya ta bar duniya tana Fushi da ita da ZArginta sannan Tunda ta haifeta bata taba Hutawa da Jidalinta ba Abun yana Sakata jin kamar ta Mutu in ta Tuna bata taba zaman minti Biyar da yaya ba da sunan Hira ba..Anya bata zama asararriya ba kuwa..?Kaiconta ita Amina in akwai wacce Mutuwar Yaya zata kasassara to itace domin su ya Jafar har ta bar Duniya bata taba Daga baki akansu ba sai ita kadai da ta fita Zakka cikin ya"yanta..!
Karfe Daya na rana aka saka za"ayi Jana"izarta zuwa Lokacin harta kannen iyayenta da suka rage na nan Gumel din sun zo sai wata goggonta goggo Jumai Sun zo suna gidan Sai su ya Zulaihat da suna Jigawa Labarin Rasuwar ya isketa sai ya Ikram da ke kusa duk suna nan gidan suna ta kuka Goggo Husai Mallam da kansa ya Kirata ya Fadamata,Ita ta shaidama Jadwa wanda akace sai da ta suma Mijinta na chan na nema musu Visar tahowa sai Mutanen gusai da Aba ya Kirasu ya shaida musu..!
Jaleela kuma ya kira mijinta ya Fadamai shi ya Fadamata sai kuka Domin mutuwar farar Daya tafi shiga Jiki sosai ance sun samu Jirgi sun taho Ita da megidanta da ya"yanta da Ya Nazir da matarsa tafiyar su daya..!
Sai ya Jamila Dake gombe ita din ma Mijinta aka kira aka Fadawa yace suna Tafe suma,Jawahir kuma da yan Gusai zata taho Allahu akbar rai bakon Duniya..!
Zulfa ma an gayamata tana Hanyan Tahowa ita da Nazeem Uzairu na Exam,sai Zahra Dake parthercourt Itama Tafiyar Jirgi tace zatayi sauran Iyalan Baba Mallam na kusa duk sun ce suna Hanyar Tahowa..tunda Rasuwar ta Safe ce..!
Dan mallam Dake chan Madina abakin Ya Nasir yaji Rasuwar Yaya Mutuwar data sanyayamai jiki matuka yana cikin makaranta sanda yaji Rasuwar ko kafin ya koma gida Sakina taji Labari itama cikin Tashin hankali ya fita nema musu Visar tafiya shi da Sakina Sarood nan zai barta Saboda kada Zirga zirgan tayi yawa..!
Ko kafin karfe Dayan an gama Hada yaya,Hajiya Babba da Wata Tsohuwa daga Gusai da suka iso suka hadu suka mata wanka suka shirya har alokacin Amina bata bar dakin ba kuma ko Hawaye Daya batayi ba..!
Kofar gida kuma ya cika Damkam da Jama"a tunda har agidan Radio an Sanar da Rasuwar zuwa Lokacin yan gusai sun iso sannan Ya Fati dake Dutse ta iso ita da Ya akila da Jidda ko"ina ya cika ba matsaka tsinke domin Yaya ta jama"a ce uwa uba kuma Aba dasu ya Jafar da abokan aikinsu sun cika wajen Allah sarki Aliyu abokin Danmallan yazo Jana"iza Tunda Umar ya fadamai yace sai yazo ya samu Janaza..!
Gida bai kara Daukan Kuka ba sai da aka zo fita da gawa bayan an kira duka Ya"yan Aba domin su mata addu"a wadanda suka iso kenan Ya Jawahir da ya Jafar sune manya sai su Amina da su hamida addu"a suka mata da Fatan dacewa Har Hamida da Hanne sun duka gaban gawanta sun mata addu"a Amina kuma sai da Hajiya ta Dukar da ita gaban gawan tana Fadin"Mamah yi ma mahaifiyarki addu"a..!
Sai ta zama out of Control yan"uwanta nata basu damu da Rashin kukanta ba susan bata Damu da yayan ba sai dai abunda basu sani ba awannan gabar Amina ta fisu bukatar uwa a raye domin ita ke cikin Tsaka mai wuyar da Uwace kadai zata Tsaya akanta da addu"a ammh kuma addu"a uwa ga ya"yanta har gaban Abada bata yankewa..!
Tana gaban gawan Kanta sara mata yake yi gabadaya yan Dakin sun koma masu fararan kaya haka take ganinsu kuka take so tayi ammh ta kasa kawai sai ta Sulale ta Rumgume gawan Yaya tana Fadin"Ki yafemin Ki yafemin..MAMA..!
Haka take ta fada cikin ihu Saboda tana so tayi kuka ta kasa sai Tsausayinta ya kamasu Da jawaad suke Tsausayamawa ammh Halin da suka ga Amina sai Rauni ya Tarun musu mamanmu na wajen tana ta kuka Hajiya Babba ke fadan ba kyau wannan kukan da suke mata..!
Ya Jafar ne ya jawo Amina Jikinsa ya Rumgume su ya Nasir suka kama gawa zasu fice tana ganin haka ta fara Fizge fizge tana Fadin"Ku bar min gawanta..Don Allah ku bar min ita..!
MAAMA...!
MAAAAMMAA..!!!!
Hake take fada cikin karyen Sautin da duka kowa yasan ba Sautin Amina bane Ana fita da gawan ta fara Bige Bigen da sai da tafi karfin Jafar su Hajiya suka taso suka sakamata karfi. Da Karfi take fadin"Ku dawomin da ita..Mamatace..!
Haj Nasara na sharan Hawaye tace"Allah sarki..akace Uwa uwace Ko da akan Bola take kwana..!ba wanda yayi Tunanin Amina zata damu don Yaya ta bar gidan Duniya..!
Ana gama Fita da gawan sai ta Daina ihu da Fizga ta koma kuma ta Sume musu kamar yadda aka kwashi mamanmu da ya Jawahir suma sun Zube kai anga Tashin hankali gida ya Rude da koke ba wanda akayi mamakinsa sai Aba ya nuna Jarumta ko Daya ba wanda yaga kukansa Dashi aka sallaci gawan Yaya aka kuma kaita makabarta yana rike da Hannun Jawaad da yaci kuka ya koshi..Aba bai yi kuka ba sai da Mallam yace ya matso shi da Ya Jafar da Ya Nasir da yan"uwanta suka sakata Cikin Kabarinta su ka kuma Debo kasa suka Rufe dashi sai alokacin yaji kuka ya taho masa Baba Mallam na bashi baki kan kabarinta ya Duka har su ya jafar suka gama mata addu"a bai tashi ba Fadi kaawai yake,"Tun zamana da ita bata taba Sabanin da gangan ba..Allah ya jikanki Hadiza har abada bazan samu makwafinki ba..!
Dakyar Baba Mallam ya rikosa suka bar makabarta suka Dawo nan Haraban gidan Mallam aka Saka Dardumai da Tabarmu ana karban gaisuwan maza, mata kuma suna cikin gidan Aba ko"ina Kaje sai yabon yaya ake yi ba wamda zai Bude baki bai Fadi Alherinta ba an samu su Amina sun Farfado sai dai ita Tunda ta Farfado bata kara mgana ba kuma bata kuka tana kusa da Hajiya kogaisuwa akazo sai dai tabi mutane da kallo..!
Sai Dare gidan ya kara Rudewa isowar sauran baki su ya Zahra da ya Zulfa da su ya Jaleela da yaya Jameela sai ya Nazir da Matarsa su ya Aisha duk sunzo karon farko zuwansu gida ba cikin Dadin rai ba,ya Sadiya ce bata zo ba suna Ameriaca inda Mijinta ke aiki tadai kira tayi gaisuwa..!
Ita Mutuwa daman ai bata da Sabo..ko abinci ba wanda ya Nema duk da ana ta kawowa Sadaqa,haka wadanda Mutuwar ta shafa sukayi kwanan zaune suna kuka da addu"an Allah ya jikan Yaya su ya jafar kuma suna waje suna karban gaisuwa sai dai in Mazan sun nemi shigowa sai suyi musu Jagora..!
Ko su saka su shamsu su shiga dasu hatta yan makarantar Islamiyansu da Hadda sun zo gaisuwa su da Malamanau da Dalibansu Sai alokacin akaji Amina tayi mgana data amsa gaisuwan mariya yar ajinsu Sa"adatu duk suna nan gidan suna tare dasu Hanne duk wani mai imani in yaga Amina sai ya tsausaya mata ta Fyade ta rame bata ci bata sha sai an matsa mata..!
Ranar da akayi sadakar uku Goggo Husai ta iso da ita da Jadwa sai mutuwar ta Dawo sabo aka fara koke koken Zuwa yammah sai ga Yaya Danmallam da Sakina sun iso suma..!
*AKWAI SOFTY COPY DA HARDCOPY NA LITTAFIN GIDANMU MAI BUKATA SAI YAMIN MGANA SANNAN LITTAFIN ZAMAN GIDANMU MAI CIKE DA KUNCI SHIMA ZA"A SAMESA A SOFTY COPY DA HARDCOPY KAN FARASHI MAI SAUKI A TUNTUBE NI TA WANNAN LAMBAR DOMIN KARIN BAYANI 09069067488*
*Janafty*
*TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*
*🅿️24*
Aranar dai Danmallam bai shigo cikin gida ba yana kofar gida wajensu Aba da Baba Mallam,Sakinar dai ta shigo nan cikin gida ana ta yi musu barka da sauka Daki daki ta shiga tayi gaisuwan kafin ta koma Dakin su Amina inda su Ya Jidda ke zaune..!
Sai washegari da Misalin karfe shaDaya na safe suka shigo shi da ya jafar da ya Nasir da abokinsa Aliyu..!
Dakin yaya suka fara shiga tunda nan su Hajiya Babba ke zaune ita da Haj.Nasara da goggo jumai sai jama"ar gusai,sai Amina da Tun da akayi Rasuwar tana Dakin Bata yarda ta kwana ako"ina ba Sai gefen hajiya wacce ke Tsausayinta tana kula da ita Su Hamida da Hanne da zafira da suka zo Dakinsu suke kwana su da su ya Abida sai dai wasu na Ragewa in Dare yayi su koma gidan Baba Mallan su kwana ammh hajiya Babba da Haj.uwani nan suke kwana Anty Amarya ce da Hj.Nasara ke komawa gida su da ya"yansu su kwana..!
Sanda suka shigo Amina na Tsakanin Hajiya Babba da Mamata mahaifiyar Zafira sanye da Hijabin nan nata na Makaranta Tun da akayi rasuwar ko wanka batayi ba ballatana tayi Tunanin Sauya kaya gabadaya ta sauya kamar ba Amina ba mgana ba Tsiwa ba Hayaniya ashe ashe akwai Watarana da Bakin Amina zai mutu..?
Daga Ciki suka shiga suka Durkusa suna gaida iyayan nasu Danmallam ya Dago kansa yana kallon Hajiya cikin Tausasawar Sautinsa yace"Hajiya ya karin hakuri kuma..?Allah ya jikan yaya Allah yasa ta huta..!
Hajiya ta amsa da"Ameen ya Allah Hakurin duka namu ne Danmallan Fata kun zo lafiya..?Naga sakina ban ga Saratu ba..?
Kansa na kasa yace"Tafiyar ba Shiri Shyasa ban taho da ita ba..Ammh tace ayi muku gaisuwa Haka ma Abu kattab yace yana muku gaisuwa shi da Mami Sara..!
Hajiya tace"Mungode kwarai Allah ya bar zumunci..!Aliyu ma ya gaisheta ta amsa tana tambayan iyalansa yace suna Lafiya sai godiya Hajiya take yi tana Fadama Danmallam da Aliyu akayi Janaza in ji mallam..!
Nan ya juya suka gaisa da Haj.Nasara da goggo Husai da mamata da sauran yan gusai ana ta Nunasa ana kuskus din fadin shine babban yaron Mallam dake madina..!
Amina na jinsu tun sanda suka shigo Gabanta yake faduwa bata son ma ta Dago kanta ta ganshi Domin zuciyarta har alokacin ta kasa karban gaskiyan ta Auri wanda bai dace da Rayuwarta ba,Shiyasa tun sadda suka shigo kanta na kasa bata yarda ta Dago kanta ba ballatana ta ganshi..!
Sai dai duk Gudun hakan da tayi bata Tsira ba,Saboda Ya Jawahir ta shigo da kulan abinci tana Fadin"Hajiya ga Alale an kawo daga gidan Mallam Sidi..iyalan nasa sun fara shiga Dakin mamanmu ne..!
Hajiya tace"Angode Allah ya bada Lada..!
Sai kuma ta kalli Amina Dake gefen hajiya Lokaci daya tana fadin"Amina ko zaki Daure kici abinci ne ga Alale an kawo nasan kina so..?
Tafada Cikin Tsausayinta da ganin yadda Mutuwar ta daketa Fiye da Tunanisu kiran sunanta da Hajiya Tayi shi ya jawo hankalin Danmallan gareta Wanda kansa ke kasa har Lokacin Duke kan kafafunsa Daga chan gefe shi da Abokinsa Aliyu,Su ya Jafar sun fita tsakar gidan suna mgana da Ya Jadwa ne..!
Daidai Lokacin itama Amina ta Dago Manyan idanuwanta da suka zama sune kadai afuskan nata ayanzu karaf kuwa suka Hada ido Hudu atare gabansu ya fadi ras..!
Ambaton sunanta yasa abunda ya faru kwanaki hudu kafin wannan Rasuwar ya fadomai Alokacin abun na ransa yana Damunsa sai dai wannan Rasuwar ne ta shafemai wannan Tunanin,Kamar yadda yake kallonta haka itama take kallonsa Cikin wani yanayin da bai gane ba Shidai kallonta yake yi yana auna Mallam bai kamata ya aura masa wannan yar Cikinsa ba,Ba shi ya Dace ba ga Nazeem ko Nasir sune zasu yi Daidai da yarinyar bashi ba da bai hango da inda suka yi dacen da Mallam zai zabosa ya aura masa ita ba Bayan haka baya shiri da mara kunya ko Fitsarrre sannan yasan yarinyar nan Gangararriya ce gata kazama ga Rashin Natsuwa ga yarinta ayadda yake jin kansa Sakina da Sarood ma Nauyi suke mai ballatana an aura masa wannan yarinyar kamar an gayattomai Jidali ne da Rashin Sukuni acikin Rayuwarsa..!
Ita kuwa ba kare masa kallo take yi ba Zuciyarta ta Kuntake waje Dayan data kasa gane komai ita dai tasan Sanye yake da Farin Boyel Riga da wando da Hula zanna Bukar,sannan ya kara Fari Gemunsa kuma kamar ya kara Tsawo sai dai kallo Daya zakayi mai ka san Jin Dadi da Hutu sun zauna mai Saboda yanayin Fatarsa da yanayin Murjewan jikinsa zaka Fahimci Hutu da jin Dadin Rayuwa sun samu kyakyawan zama awajensa..!
Tana kallonsa ne tana jin kamar ta yanka Ihu acikin ranta ta kasa dora Mizanin komai domin tana ji kamar bata da Hankali Domin yin wani nazari kan Rayuwarta sai Hankalinta ya Dawo Jikinta kamar yadda ta kafe shi da ido shima a fakaicen yake kallonta sai dai abunda bai sani ba azahiri ne take kallonsa abidini kuma ta shiga wani yanayi ne yanayin da bawan da Allah ya Jarabta yake ciki..!
Haj.Uwa ce ta sako baki tana Fadin"Ai da ruwan zafi ta fara sha Hajiya sai hanjinta su sake..!
Wannan mganar ta Haj.Uwa shi yasa Danmllam Saurin Dauke kallonsa Daga gareta itama sai alokacin ta maida idanuwanta kasa tana Faman kokuwa da Numfashimta..!
Hajiya tace"Eh kuma na sha"afa Domin tun Rasuwar nan banga Amina taci abinci ba sai ruwa..Sai Hakuri Allah daya fimu sonta ya Dauketa Mamah addu"an ku kadai take Bukata yanzu..!
Mamata na gefe tace"Wlh sai hakuri ni Aminar ce ta bani mamaki..Yadda Mutuwar yaya ta Daketa na Dauka Ko zai Daki kowa banda ita Tunda Balaraba ta Kore mata Kishir ruwan uwa. !
Haj.Uwa ce tace"Uhm bari mamata..Kinsan Girman Daraja da Kaunar dake tsakanin uwa da abunda ta Haifa..?Mutum bai isa ya Fada ko ya kwantata ba..Allah Kadai yasan iyakarta..!
Sai Dakin ya dau mgana kowa na Fadin albarkacin bakinsu yawanci mgana suke kan yaran bazasu maraici ba ga Balaraba wacce take Tsaye kan yaran Tun yaya nada rai bata san wahalan ya"ya ba komai Mamanmu ce..!
Danmallam ganin mganar ta koma wani bangare yasa suka yi ma su Hajiya Sallama suka fice Amina ta Bisu da kallo gani tayi ma kamar ya kara Tsawo da zai fita sai da yadan Rankwafa duk Tsawon kofar yaya..!
Dakin Mamanmu suka shiga inda take karban gaisuwa ita da Anty Amarya da Haj.Nasara sai sauran yan"uwanta ,Sai su Sakina Dake dakinta ita da Jidda da Su Zulfa,nan suka yi musu gaisuwa yaran kuma na Rawan jiki gaishesu basu jima ba suka fito suka shiga Dakin yaran Lokacin Jawahir da Jadwa sun shigo Dakin Suka gaishesu suka amsa kafin suyi musu gaisuwa basu jima ba suka Fice Daga gidan zuwa kofar gida inda ake zaman gaisuwa..!
Sai da suka zauna chan Nesa da Tabarman su Baba mallam inda manyan Mutane ke zaune abokan aikin Aba da kuma Amintattun malamai abokan Da"awan Baba mallam,Sannan Danmallam ya kalli Aliyu yana Fadin"A cikin dakin da yaya da muka shiga kaga wata yarinya da Hajiya ta Kira da Amina..?
Bai bama mganar Muhimmanci ba yace"Eh wacce ake cewa bata ci abinci ba Tun bayan rasuwar..?
Da kai ya amsa masa kafin ya Cije baki yace"Wai ita Mallam ya aura min kwana Hudu da suka gabata..!
Sai Aliyu yaji kamar bai ji da kyau ba ya kallesa yana Fadin"Bangane ba..?
Dammallam yayi mirmishin Takaici kafin yace"Am serious abunda kaji gaskiya ne Aliyu..!
Aliyu ya Dafa kafadan Danmallam yana fadin"Kai..Abu haka kwatsam Shehi.Oh wlh yarinyar Sweet Sisty ce Abokina kace kaima kabi shawarata kafara yin gaba kafin ni..!
Kalamam Aliyu sun kara batamai rai Cikin Takaicinsa yace"Kai yanzu in nace maka da son raina na auri yarinyar chan sai ka yarda..?
Tsiyana Dakai wauta..Wlh tallahi bazan iya da mata uku ba Aliyu.bama haka ba yarinyar tamin kankanta sa"ar autan Hajiya ce fa Hanne tare suke fa ina zan kai yar cikina Aliyu..?bana son jidali Allah ma ya taimakeni Sakina ta kwantar da Hankalinta Sarrod kuma bata da Hayaniya ammh ina Tabbatar maka auran yarinyar nan sai ya Rusani Aliyu kasanni bana son Hayaniya da Damuwa ya kake gani na Hada yarinyar nan da sauran matana..?
Ba ka hangomin tashin hankali azama na dasu..!?
Ya karishe fada cikin Rauni Aliyu ya jinjina kai yana fadin"Eh kaima kayi mgana..To ya abubuwan suka faru..Ai nasani Mallam baya aurar dasu sai sun yi candy..!
Danmallam yace"Abubuwan da suka faru suna da yawa...Aliyu Abu Daya na sani Mallam ne ya Kirani ya Tambayeni yardata ba kuma neman izini ba Aliyu tayaya zan watsama Mallam kasa a ido..?
Bazan iya ba..Yana da Kima da Darajan da ko Wuta yace na Fada zan fada Uwa uba kuma Diyar Baba Sa"idu ce har Abada jininsa nada Daraja awajena sannan Diyar yaya ce Allah ya jikanta ko kasa sun shafe idonta bazan ki karban Abunda ta haifa ba Aliyu Yaya Mutum ce Hajiya ta Fadamin bayan ita data Haifeni yaya tayi wahala dani Wahalan da ko ya"yan data Haifa bata musu ba kana ganin in naki karban abunda suka Haifa Allah zai yafemin Aliyu..?
Yafada yana saka yakininsa da Kallonsa kan Aliyu da yayi Kasake yana kallon Umar din..!
Bai basa zarafin mgana ba yacigaba da Fadin"Sai dai abu daya na sani..Meyasa Mallam ya Zabeni..?
Bayan ni akwai Nazir,Ga Nasir ga Nazeem ayadda nake gani akwai kwaruwa yarinyace karama da batasan komai ba sai Shirme an cutar dani An cutar da ita Dukkanmu Rayuwar batayi mana Daidai ba Aliyu..!
Awannan gabar ji yake kamar ya saka kuka sai dai ina Jarumtarsa bazata barsa ba..!
Aliyu ne ke Bubbuga Kafadansa yana Fadin"Easy mana Shehi..Biyayya kayi kuma insha Allahu bazaka tabe ba..Komai da kaga ya faru tsarin Allah ne..Sannan da kake fadin gasu Nasir ai mallam din ya san dasu ko..?kuma ya Zabeka na Tabbata kamar yadda ya Zabeka cikin ya"yansa yana da kyakyawan yakinin bazaka basa kunya ba..Sannan kai din kafi su chanchanta kabar mganar yarinya ce Annabi ma ya auri Nana Aisha As tana da Shekara Tara ne kaga kuwa sunna ce sannan yarinyar nan ba karama bace yadda kake tsammani zata kai 16 to 17 fa Shehi ai kuwa batayi kankanta ba wadanda ma basu kaita ba anayi musu aure kuma su zauna Lafiya kuma mganar yar cikin ka yaushe ta zama yar cikinka..?Just 39yrs fa gareka Shehi ta ina zaka iya Haifanta banda Tsabar son girma da Sharri irin naka..!
Sai da ya Murmusa jin kalaman Aliyu kafin yace"Ammh dai kasan da auran wuri nayi..Da yanzu ko ban haifi kamar ta ba na kusa..!?
Aliyu na Dariya yace"Uhmm.Naji Ka dai kafin naji watarana yar cikin naka ta baka Wahala..!
Ya karishe fada yana kallon sa kasa kasa karamin Tsaki yaja kafin yace"kasha kwaya ne..?ko ka fara Hauka inaga..Ni fa duk ba wannan ba Ina cikin Tashin hamkali ko su Sakina ban yi mgana dasu ba fa..!
Aliyu yace"Tab..Ai sai kayi hakuri..Domin tama ji ta gama Tunda dai kuka zo nan..!
Dammallam ya Sauke Numfashi bai yi mgana ba Diramar da zasu kwasa Kadai yake hangowa in Sakina taji Labari ganin haka yasa Aliyu yake ta Kwantar mai da Hankali tare da bashi Shawarwarin da zasu mai amfani kuma ya natsu yana jinsu aransa yana godema Allah Daya Hadasa da aboki nagari kamar Aliyu.
Hakika an ga jama"a Domin kungoyin Matam malamai duk sun zo gaisuwa,Kowacce cikin masu auran nan Dangin mazajensu sun zo gaisuwa,Mutane ne suke ta Zuwa har abun yaso bama Mutane mamaki,sai dai kuma ba abun mamaki bane sanin Wacece Yaya shaidar duniya itace ta Lahira Tabbas yaya ta dace
Kowa sai mamakin Aba akeyi ganinsa Cikin natsuwarsa ba wanda yayi Tunanin Mutuwar bazata Gigitasa ba..Sai dai ina wadanda suke son ganin gazawar tasa basu gani ba Tabbas Mutuwar ta tabasa sai dai ya Riga ya yarda da Allah ke kashewa kuma ya raya alokacin Daya ga Dama sannan kuma Ga Baba Mallam agefensa Koda yaushe cikin mai Nasiha yake yi da karamai karfin Gwiwa Kuma cikin ikon Allah komai yazo da sauki yana Tsaye kan kafafunsa Cikin Jarumta da Takwalli..!
Sai da akayi addu"ar bakwai kana aka Rufe zaman gaisuwa akuma ranar Baki suka fara tafiya hatta yan gusai da yan bazanga maza da wasu daga cikin matan sun koma da Rana yaran dai duka suna nan,sun samu zama Tunda Mallam bai ce komai ba shi kuma so yake sai ya Hadasu yayi musu Nasiha sannan ya Umarci kowacce ta koma Gidan Mijinta
Haka kuwa akayi ranar da yaya ta cika kwana Takwas da Rasuwa da Daddare a Falon Baba Mallam ya tarasu kowa da kowa banda ya Nazir da ya koma Tun ranar uku saboda aiko ko Umar da yazo basu hadu ba..!
Yara da manya Harda Jawaad dake jikin Aba wanda tunda akayi rasuwar Aba ne komai nashi yanzu..!
Mazan gabadaya suna zaune akasa ne gaban Baba Mallan hatta Aba yana zaune akasa ne sai su Hajiya Babba,da su Hajiya Nasara da Anty Amarya da Anty Uwa sai gefe Mamanmu ita ke zaune ita da yaran gabadaya Amina na can karshe kusa da Hanne kanta na kasa Tun bayan rasuwar sai yau tayi wanka shima sai da Hajiya ta nuna bacin ranta..!
Bayan Bude taro da addu"a da Ya Nasir yayi Baba Mallam ya fi Minti Talatin yana musu Nasiha da jan hankulansu gabadaya harda Aba Daga karshe yayi musu Fatan suyi hakuri su Rumgumi wannan Rashin da fatan Allah ya haskaka kabarin Hadiza aka amsa da Ameen..!
Ba zato ba Tsammani Mallam ya Fadi auran dayq daura Tsakanin Umar da Amina,Kowa daman ya sani wannan Mutuwar ne tasa ba wanda ya Tada mganar Sakina na wajen sai dai ta Riga ta samu Labari bakin Sa"adatu data tambayi Anty Amarya ta tabbatar mata,Bata wani damu ba Domin Anty Amarya ta mata alkawarin ba inda auran zai je ayadda aka Kullashi hakaza"a warware shi ne..!
Danmallan Sakina yake kallo yaga yanayinta sai dai bai Fahimci komai ba Illah Mirmishin Fatan baki data Saki aranta Tana Tunanin kishi da wanchan mara kunyar yarinya ai bata Lokaci ne ta tabbata ko a kafa aka Daurama Umar ita sai ya kwanceta yayi ta kansa to me zai Dameta..!
Dukkansu yaran sunyi Fatan Alheri batare da sun ji musabbin abunda ya Faru har Lamarin ya koma haka ba Sai dai sun san da abunda ya Faru haka kurum Baba Mallam bazai Sauya Tsarinsa na aurar dasu in sun yi Candy ba,sai dai tunda bai sanar dasu ba sai suka bar mganar hakanan..!
Daganan addu"an tashi akayi ya sallamesu da Umarni goben goben nan kowacce ta shirya komawa gidan Mijinta Angode hakanan da Toh suka amsa suna ma godiya domim sun ga ma kokarim sa daya barsu suka yi kwanakin nan bai yi mgana ba..!
Ya sallami kowa illah Hajiya Babba Dayace ta Tsaya ita da goggo Husai da Ya Danmallam sai Aba kadai yace yana son mgana dasu..!
Amina ta mike zata fita Baba Maallam Dake Lura da ita ya Dago yana Fadin"Mamana kariso nan ina son mgana Dake..!
Hannunta na cikin na Hanne ta zame ta fara tafiya zuwa wajensa tana jin yadda Ido ya koma kanta abunda bata sani ba Uban gayyar kansa na kasa ko Dagowa bai yi ba Duk da yasan itace Mallam yake kira da Mamarsa..!
Har gabansa taje ta Duka kanta na kasa Lokaci daya tace"Gani Baba Mallam..!
Tattausan Mirmishi yayi kafin yace"Na ganki Mamana..shin ko yima Babanki gaisuwa..?Gashi nan Sa"idu nake nufi..?
Yafada yana Nunasa sai Alokacin ta Dago tana kallon Aba Rabonta da ganinsa gani mai kyau Tun ranar da aka kaisa asibiti sai yau dataga ya Rame yayi baki yana cewa ya Tsufa sai yau taga Tsufansa ta bayyana yana Sanye dajallabiya Mai ruwan madara da Bakin wando kansa ba Hula Furfuransa duk ta bayyana Idanuwansa sun Zurma ciki alamun akwai rashin Barci da kwamciyar hankali..!
Batasan sadda tace"Aba ka rame..Ka dade kana cemin ka fara Tsufa ban taba ganin tsufanka ba sai yau..Sai yau bayan kasa ta Rufe idon yaya..!
Take fada cikin raunin Raunin da Tun da akayi rasuwar bata saukan mata ba sai yau datake ganin Aba agabanta da yanayin daya koma..!
Kowa afalon sai da jikinsa yayi sanyi Aba kwalla ta kawo masa yana kaunar Amina kaunar Hadiza ne ta shafeta ba saboda komai ba sai Saboda kammaninta da Hadiza!
Cikin Dauriya yace"Na Dade da Tsufa Amina..Sai yanzu ne tsufan ya bayyana..bayan na rasa Hadiza..!
Akaron farko Amina ta fashe da kukan daya rike mata zuciya in Tana ganinsu ya Jadwa na kuka sai taji su gwara su yaya bata bar duniya tana Fushi dasu ba gwara su sun samu kyakyawan Mu"amala ita fa bata da wani abu da zata Dorar Tsakaninsu in yaya ta saka baki a lamarinta to na Bacin rai ne ba na Dadin rai ba..!
Kuka take kamar ranta zai fita cikin kukan ta Rarrafa gaban Aba ta kama kafarsa tana fadin"Aba ka yafemin..Don Allah ka yafemin kada kai ma ka rasu ka barni baka yafemin ba kamar yadda yaya tatafi ta barni tana Fushi dani..!
Haka take fada tana wani irin gunjin kuka,wanda duk mai Tsausayi da Imani sai ya Tsausaya mata hatta kuwa da Danmallam Dake gefe sai da ya Dago ya kalleta cikin wani yanayi..!
Hajiya baya ta juya tana sharan kwallah Baba Mallam ne mai Dakiya yana Binsu da kallon Tsausayi..!
Jawaad yayi barci shi yasa Aba ya kwantar dashi kan kujera sannan ya saka Hannu ya Dago Amina yana Fadin"Hadiza bata rasu da Haushinki ba Amina..Komai kikayi sai dai tace Allah ya shiryaki..Bata taba aibataki b .....Addu"ata gareki mai kyau ne Amina..!
Hajiya babba ta amsa da cewa"Kuma addu"anta baza ta taba fadi abanza ba.Da yardan Allah zaku yi alfahari da Amina Hadiza zatayi alfahari da Amina ko bayan kasa ta shafe idanuwanta ne..!
Yanayin falon ya koma na Jimami Barin ma yadda Amina ke kuka Data Rumgume Aba tanayi kuka mai Cin rai Baba Mallam ne yaga kukan yayi yasa yace"Mamana tashi nan bar kukan nan hakanan kina tadama Babanki Hankali..!
Sai Lokacin ta bar jikin Aba ta sulale kasa tana Fadin"Ka yafemin Aba..!
Yana kokarin Dauke Hawayen idonsa yace"Ban taba rike ki ba Amina..Komai kikayi min na bacin rai ina yi miki uzuri Wlh..Hadiza koda yaushe fadi take mu yi mata Fatan Shiriya mu yi fatan Allah yasa in ta Girma ta sauya..Na yafe miki Duniya da Lahira Amina Allah yayi miki albarka..!
Tana kuka take amsawa da Ameen kafin ta Rarrafa gaban Baba Mallan rikota yayi ya Tadata ya zaunar da ita gefensa ya saka Gefen rawaninsa ya Share mata Hawaye yana fadin"Bar kuka..Addu"a zaki rika mata in kin Tunata kinji ko..?
Kai ta gyada mai tana sharan majina Hajiya Babba tace"Kabarta tayi kuka Mallan tun fa rasuwar nan banga tayi kuka ba..!
Sai Alokacin goggo Husai ta tanka"To zainabu sai kuma abarta ta tadama Mutane da Hankali..?
Tana Raye bata huta da Jidalin Amina ba bayan ta rasu bazata barta ta Huta Cikin Salama ba..!
Da sauri Baba Mallan yace"Husai kibar wannan mganar..Hadiza zata Huta cikin kabarinta da yardan Allah Shaidar duniya itace ta Kiyama..!
Dole ta koma tayi shuru domin ita bata da wannan Sakewan da yara shiyasa Tuni taso Sa"idu ya bata Amina tatafi da ita da Tuni duk wannan Tabaran ta daina shi
Ita gani take harda da Laifin Sa"idun da su Mallam din..!
Nan Baba Mallam ya cigaba da Lallashin Amina har sai da ta bar kuka sannan ya kalleta yace"nima zan baki Hakuri Mamana..Nayi miki laifi nayi sonkai..Na rabaki da wanda kike so na aura miki Da"a na..!
Sai kunya ta kama Amina ta kalli Baba Mallam da manyan Idanuwanta kafin tayi mgana Ya saka baki ya Kira Umar Dake gefen Aba kansa na kasa kamar baya Falon
Gaban Baba Mallam yazo ya Durkusa Cikin Sanyin sa yace"Gani Mallam!
Ba zato kawai yaji ya Damki hannunsa ya Hada cikin na Amina cikin Dattakonsa yace"Ga Amanar Hannun Mamana nan Umaru..Ko bayan raina ban yarda ka saki ba..Ko Laifin me ta maka ka Duba girmana ka mata afuwa ka yi juriya kan Hallayarta ka zama mai mata Nasiha yayinda ta bata maka Sannan Daga karshe ina fatan zaka riketa Bisa gaskiya da Amana sannan ka kwantatanta adalci Tsakanin matanka..,!
Gabadaya sai jikinsa ya Mutu hannuwan nasu yabi da kallo kamar yadda Amina itama take bin Karamin hannunta Sarke cikim Tattaausan hannun yaya Danmallam mai cike da gargasa da kallo..!
Bakinsa yayi nauyi da wannan Abunda Mallam yayi shiyasa ya jinjina kai kafin yace"Insha Allahu Mallam..Allah ya kara girma..!
Ya amsa da Ameen har Lokacin hannayensu na Sarke da juna Hajiya Babba ta kallesu farimciki ya cikata Cikin wani yanayi tace"Yadda kuke rike hannun juna..Allah yasa ko a Lahira tare zaku tashi rike da hannun juna..Allah ya Hada zuciyoyinku Waje daya..!
Gabadaya aka amsa da Ameen Aba na gefe yama kasa mgana Alherin Baba Mallan garesa ai mai girma ce..!
Goggo hussai tace"Sai faman bashi Amana kuke yi kun manta Amina..?Kai Umaru kalleni nan..Kada ka damu da mganar Mallam ko ta Hajiya..Amina sai da wuta..In tayi maka ba Daidai ba kaci Zarafinta kada kayi mata da Sauki Domin kai zaka sha Wahalanta Ahtto..!
Tafada bilhakki da gaskiyanta Dayasa Hajiya ta Murmusa tana fadin"Ke fa Goggo ce Husai..!
Tace"Ai na sani shiyasa nake Fadamai gaskiya..jidalin Amina ai Allah kadai yasan shi Har Hadiza ta bar Duniya bacin ranta Daya kan Amina..Allah yasa ta samu ma uwar goyo ta gari ai da ba Domin Balaraba ba da Amina kuma sai Allah..!
Amina na jinta ita yanzu komai ma ya zama mai Sanyi awajenta in da abayane ta Tabbata Sai ta Tura mata baki tayi gunaguni kamar baya ammh yanzu sai taji ta kasa bata cikin Hayyacinta har yanzu Aminene bata Dawo ba Amina ce da kanta yanzu..!
Ta manta da Hannunsu dake Waje Daya sai da taji ya Sabule hannunta Sannan ta Dago suka hada ido Saurin Dauke kansa yayi saboda wani irin abu yaji acikin ransa kamar na Tsausayi itama kanta ta Dukar tana wasa da Hannunta gabadaya kalaman Baba Mallam sun gama riketa ita kuwa me ta aikata ne..?
!Da Alherin Baba Mallam da Hajiya ya Lullbe Rayuwarta haka..? Har Abada bazata manta dasu ba kamar yadda bazata manta da kaddaran data Hadata da Masoyinta Aminu ba..!
Baba Mallam yayi gyaran Murya yana Fadin"Umaru me ka yanke kan Mamana..?Ina Nufin kana da wani Tsari ne..?
Kansa na kasa har Lokacin yace"Tsari na na Ubangiji ne Mallam..ba ni da wani Tsari..!
Sai dai bazan ki duk abunda ka Zartar ba..!
Baba mallan yaji Dadi Cikin Fara"a yace"Naji Dadin haka shiyasa na Tambayeka..Zan yi ma Mamana adalcin da nake yi ma kowa..Bazata Tare ba sai ta gama makaranta Umar..Nan da shekara Daya da wani abu kenan tunda Hajiya tace suna aji Daya na Babbar makaranta sun kusa shiga Aji Biyu..!
Zata kamallah makaranta da Walimar sauka zan hadata da sauran yan"uwanta Hamida da Hannatu da Sa"aadatu na aurar dasu ita kuma sai ayi Bikin Tarewarta alokacin bazan karbi Uzurinka ba na baka Lokaci ka Tsara komai inda zaka ijiyeta da yadda zaka zauna da iyalanka..!
Goggo Husai tace"Mallam me zai hana tunda anriga an Daura ayi Tarewan ba Nisa?
Kai ya Girgiza kafin yace"A lokacin Auransu nayi gaggawa Husai..ban kuma bama yaran nan dama ba Husai..Bana so na kara maimaita irin haka Shiyasa na Dibi wannan Lokacin bana Fatan wani Daga cikin su yaji aransa ban mai adalci ba..!
Ba wanda bai gamsu da mganarsa ba Ya Danmallam kamar ya goya Mallam haka yaji dama Fargabansa ace ya tafi da ita ko kuma mganar Tarewa Amina kuwa acikin ranta itama Hamdala Take yi Domin bata shirya ba..Bata Shirya karban wannan Kaddaran ba Har yanzu..!
Goggo Husai tace"Shikenan..Ni na Dauka zaka hadata dasu Zeenatu ne.?
Kai ya girgiza kafin yace"A"a ai ba Sa"aninta bane..So mganar su ma tana nan Rasuwar nan ne ta hanani nayi mgana yaushe ne zasu fara Jarabawar Fita ma kikace Hajiya..?
Hajiya tace"Sati na sama Abida tacemin Mallam.!
Cikin Dattakonsa yace"Zan bama Mazajensu dama zasu fara zuwa su gana dasu..Mai son Zeenatu dan wajen Aminina Mallam Hamza ne Dake Gombe,Babbar D'ansa Ahmad Soja ne..Sai mai son Abida na gida ne Jikan kawuna Lawali na Bazanga Dake Jamus..? To yaron wajensa ne Yana Porthercourt yana aikin Zanen gidaje ko wannan Gaisuwan da suka zo shi kawu Lawalin ya karamin mgana..!
Goggo Husai ta fara fadin"Masha Allah..Allah yasa a kulle alheri..!
Aba ma yayi fatan Alheri shi da Hajiya
Baba mallan ya kalli Danmallam yana Fadin"Baka ce komai ba Umaru..?
Cikin Ladabinsa yace"Hakan yayi mallam..Allah ya saka da Alheri ya kuma kara girma..!
Cikin Fara"a yace"Ameen Allah yayi muku albarka..Tashi kaje ka Dauki iyalanka kuje gidanku ku huta..Ina fatan zaka kwana Biyu kafin ka koma..?
Cikin Kankantar dakai yace"Jibi zamu koma Mallam..Saboda aikina na iya adadin kwanakin da aka bani kenan..!
Baba Mallan ya Jinjina kai yana Fadin"Shikenan Allah ya kaimu..Mamana tashi ki bisa ka rakata har kofar gida ko wajen Hajiya zaki kwana..?
Kai ta girgiza kafin tace"Eh..!
Da sauri domin bata son ahadata dashi jin haka yasa Danmallan yayi musu sallama ya Fice daman shima Takuramai Mallam zai yi ko Cikin gida bai koma ba ya Kira Sakina awaya yace ta fito su tafi..!
Amina kuma sai da tattabatar da sun tafi Domin taga Budewar get da Fitan Mota ta kuma tabbatar da Shine sannan tayi musu sallama ta wuce shashen Hajiya..!
Koda taje har ya Abida tayi barci sai ya Aisha ce da ya Zulaihat ke zaune ashen nan sukayo Dadi taji Dataga su hanne da Hamida Zafira sun koma gida Tun jiya..!
Bata ma kowa mgana ba Kujearan falo mai zaman mutum uku ta Dungule akai tana Sauke ajiyar rai su kuma sai suka sauya hira daman Hirar Aminar Suke da Al"ajabin Auranta da Yaya Danmallam,Sai dai kuma ko su Hanne da sukasan Dalili basu ce komai ba Domin Sirrin Amina Wajensu bazai Taba Faduwa ba koda ba awaje bane na gida ne..!
Sai awannan ranar Amina ta samu barci Domin batasan Dawowar Hajiya ba
Washegari kuma su ya Jawahir suka fara tafiya,sun yi kuka Lokacin sallama kafin yammh gida ya Rage sai ya Jadwa da Goggo Husai da Goggo Jumai duka sun koma Gidajensu har su ya Zahra..!
Chan gidan Baba Mallam ma Duka sun koma gidan auransu gida yayi tsit dayan washegarin kuma Ya Danmallan suka koma shi da Sakina Basu hadu da Amina ba itama Goggo Husai taji Tana mganar Tafiyar tasa..!
Tun Ranar ashashen Hajiya suke kwana har Hamida sai da su goggo Husai suka samu Visa suka tafi gida ya zamana ba kowa yasa Hajiya tace su Amina su koma basoda Mamanmu kada kadaici ya Dameta..!
Kwana Goma sha daya da Rasuwar yaya suka koma gida ya rage daga Amina sai hanida sai zeenatu da Jawaad sai mamanmu da Aba. !
Sati biyu da rasuwar suka koma makaranta Boko da Islamiya,Saboda zasu fara jarabawa su ya Zeenatu har sun fara Neco..,!
Komai ya tafi kan tsari sai dai Abu Daya ne yayi ma mamanmu cikas Wannan Raunin data so gani awajen Sa"idu bata gansa ba sai ma wani Takwalli Daya shigesa..!
Ko sau daya bai zubar da Hawaye agabanta ba..!
Balle taga Rauninsa ko kananan kukan gulma take sai dai ya kalleta yace"Muma fa jiranta muke yi Balaraba..Hadiza batayi gaggawa ba..!
Fatanmu Allah ya rahamsheta..!
Bata gani ba har yau bata gani ba..Sannan Gurbin yaya har Abada Sa"idu bazai taba bata ba..bayan Mutuwar taso komai ya zama karkashinta abunda bata sani ba Allah ya riga ya Rubuta kaddaran kowa ciki harda nata in ta Kauda yaya to ba Lalle ta samu cikar Burinta ba zata samu wani wanin kuwa har ta koma ga Allah bazata taba samun sa ba..!
*Janafty*
*TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*
*🅿️25*
*BAYAN WATA DAYA..!*
Acikin Wata dayan daya gabata na rasuwar yaya komai ya fara dawowa daidai,Wadanda akayi ma rashi sun Dauki Dangana da Tawakkali,Mussaman Aba da su Amina da yanzu ta fara dawowa da Walwalarta sai kuma yanzu take matukar kulawa da Jawaad tana Taausayinsa gani take daga shi sai ita sukayi rashin yaya basu da wata matsala Domin mamanmu tana Tsaye kansu da Fuskar da suka santa da ita,ya taimaka wajen dawowa da walwalar yaran har wadanda ke gidan auran nasu,Uwa uba ga Hajiya babba da bata bari sun yi kukan maraici ba Duk da ga Mamanmu tare dasu tana zaryan zuwa Dubasa barin ma in Taga Amina ta kwana Biyu bata leko ba
Acikin kamshin Nasaran da Mamanmu take gani ta Samu bayan kasa ta Shafe Idon yaya abu Daya ne zuwa Biyu na Farko ta samu yardan yan"uwa da Duka Dangin Baba Sa"idu sannan Aminci Data gina shekaru masu yawa da yaran bai gurbace ba yayi mata amfani sosai gabadaya su ya jafar da komai nasu yana Tafin Hannunta ne tun yaya nada rai yaran da ita Suke shawara sai dai yayan taji Daga bakinta to har yanzu bata Sauya Zani ba ballatana yanzu da ba Uwarsu sai Duka yardan da Amanan ya koma kanta Harta kuwa Jafar da Abaya yake da Kulafunci nuna yaya ce uwarsa ba Ita ba shima yanzu wani girma yake bata kamar me yana ganin ta tamkar makwafin yaya..!
Gida ya zama nata ita kadai Yaran suna Tafin Hannunta sai dai Abu Daya ya Gagareta Samun SA"IDU yadda take so,Sannan kuma wannan Raunin da taso gani atare da Sa"idun bata gansa ba,Sai ma wani Jarumta da Takwalli bata so ta gansa Tsaye kan kafafunsa ba taso ace yana kwance ne yana Fama da wannan Babban rashin sai Taga akasin haka sai dai bata Sare ba ai ta Rabasu Wannan kallon kauna da Tausayin Sai dai in ya Bita chan Lahira ya nuna mata anan Duniya dai ta gama Shiga Tsakaninsu..!
Bayan Bakwai da rasuwar yaya ta kasa gane kansa ya daina cin abinci baya Fara"a baya Hira da ita ballatana mgana mai Dadi haka zasu kwana su tashi in ba ita tayimai mgana ba shi bazai ce mata ba tasan wani Lokacin bai da Hayaniya ammh tasan Rashin mganarsa yafi Faruwa akanta In yaya ce keda Turaka kusan Raba Dare suke suna Hira cikin Nishadi bata san Darare nawa ta bata cikin bakincikinsu ba Domin tana Daga Dakinta in Dare yayi tana jin tashin muryoyinsu In kuma ranar itace keda shi Daya gama cin abinci yayi wanka Sai ya fara Hamman barci tana mai Hira sai ya fara barci ma"ana baya son Hirarta ta Dade tana kunsan bakincikin Sa"idu shiyasa bayan Rasuwar yaya ganin zai bata wahala yasa ta sa madina ta kai ma malaminsu korafi aka Samo mata kansa shine har ta Fara Tunanin Burinta ya fara cika Sa"idu da komai nasa yana Hannunta..
Tunda yanzu In ya dawo aiki yaci abinci yayi wanka ya kan zauna su yi hira koda bazai amsata yadda take so ba ammh cikin kaso goma tana da Nasaran kaso Takwas aciki Abunda ya Rage mata shine ta fara sanin komai nasa kamar yadda yaya ta sani sai dai har zuwa yanzu yaki bata Damar haka!
Yau ma kamar kullum safiya ranar asabar ce ta hutun karshen mako,Ba kowa agidan duk sun tafi Hadda,Sai ita kadai da Aba bai fita yau da wuri ba,Kamar yadda ta tsiro dashi yanzu Gari na wayewa kafin Aba ya fita sai ta Chaba kwalliya Kamar wata yarinya bayan makircin karkashin kasa har da na Kissa Madina tace ta Dinga Hadawa duk a Kokarinta na sai taja Hankalin Sa"idu akanta gabadaya..!
Abunda bata sani ba ita zuciya ba"ayi mata Dole kan abunda tagani kuma tasan dashi ammh ta nuna bata so..Sannan duk da tana son mai kyautata mata bata cika bashi matsayin daya Zarta wanda ta zabe ta da kanta ba koda bai taba mata wani abu na Alheri ba..!
Zaune suke afalonsa yana karyawa ita kuma tana gabansa kamar mai kirga yawan Numfashinsa Hira take yi mai yana jinta yawancin Labaranta ba wasu masu amfani bane,Shiyasa yake mata Shuru kawai batare daya tanka ta ba,Har kuma gobe bazai daina kukan Rashin Hadiza bai jin zAi iya mantawa da ita.
Jin tayi shuru yasa ya Dago Daga cin Soyayyan Dankalin data soyamai ya ganta tayi Tagumi tana kallonsa Cikin dan mamakinta yace"Lafiya..?Me kike Tunani..?
Alokacin bakincikin Tambayarsa taji Saboda tafi kama data rainin wayau ta Zauna tanayimai Hira yayi mata banza sannan ya Dago yana ce mata Lafiya..?Saurin Daidaita kanta tayi ammj bacin rai yasa Kiris ya Rage Dayan Fuskar tata ta bayyana.
Cikin sosa ido da hanci ta fara fadin"Yaya na tuna..Bana iya kwana na Wuni ban yi kukan rashinta ba..Ballatana in na gifta Dakinta sai naji gabadaya Duniyar ta Juyamin baya..!
Tana Fade tana matso hawaye kamar gaske ya Dade yana kallonta kafin ya maida kansa ya cigaba da cin Dankalinsa yana jinta tana Fadin"Wlh nima sai naji Duniyar duk ta isheni Abbansu..Dama nima na mutu kamar yadda yau ba yaya adaron Duniya..!
Sai da ya Kurbi Tea din Dake hannusa sannan ya Dago yana kallonta Cikin Sanyinsa na koda yaushe yace"Zo nan Balaraba..!
Baki ta bude tana kallonsa Ganin haka yasa ya gyada mata kai alaman tazo ba musu ta mike ta isa kusa dashi ta zauna Juyowa yayi suna kallon juna Hannayenta ya kama Duka ya Rike yana Tuna Nasihan Baba Mallam aranar da Hadiza tayi arba"in da Rasuwa ya Horar dashi Kada rashin Hadiza yasa ya cutar da Balaraba ya sani Ko sau Daya ya Danne mata Hakki Allah zai tambayesa..!
Cikin Idanuwanta ya kallah kafin ya fara fadin"ki daina Fadin haka Balaraba..Mutuwa ta Allah ce..Hadiza batayi gaggawa ba sannan muma da muke Duniyar jiranta muke..Ko yau ko Gobe zamu mutu..Saboda haka ki Sani Hadiza tatafi ba domin tana son Tafiya ba..Addu"rmu take Bukata ba kuka ba..Don Allah in kin Tunata,ki Dinga mata addu"a don Allah..!
Kai ta gyada tana kara Jan hanci Lokaci Daya tana fadin"Wlh Abbansu na kasa ne..Kullum in na tunata sai nayi kuka..Barin ma in na Juya naga gidanan yanzu Dagani sai kai yau babu Yaya..Sai naji kamar nayi ta kuka har Abada..!
Sharr sai hawaye suka Zubo mata Taausayinta ya kamasa yasan ita mai Hidima ce agaresa shi da ya"yansa har Abada wannan kyautatawar nata yana cikin ransa kuma yana gode mata.
Hannu ya Sanya ya share mata Hawaye cikin Tattausan murya ya cigaba da fadin"Haka Allah ya Tsaara..Daman chan ita din bamai Tsawon rai bane..In kina wannan kukan zaki tadamin da hankali naga kamar na gaza ne balaraba..Sannan in kuka ya Haifar miki da Damuwa ina zan saka raina ni da ya"yana da kike zama mana tamkar wata inuwar gingiya mu Rabe ki mu ji Dadi..!
Wlh tallahi nayi rashin Hadiza sai dai nasani da yau baki cikin Rayuwarmu da Raunin mu ya fi bayyana..Allah ya Dauketa ne saboda yasan ina Dake..Na tabbata ko ni yau Allah ya Dau raina ke zaki zama madadina da madadin Hadiza..Girmanki a idona mai girma ne Balaraba..Yau zan gode miki bisa Hidimarki gareni da ya"yan Hadiza da baki bari sun yi maraici ba..!
Tunda ya fara mgana take kallonsa Zuciyarta ta cika da Farincikin da shekaru aruru basu sa tayi shi ba sai yau..Daman haka take so ta zama Komai na Sa"idu da ya"yansa wanda basu da wata Dama sai ita ta Kasance itace jinsu da ganinsu kuma tayi nasara bayan Shekaru ashirin da wani abu akallah yau ta fara Hango kamshin nasara cikin Wahalar data Dade tanayi..!
Ammh sai bata nuna ba sai ta Sadda kanta tana fadin"Basai kamin godiya ba..Aikina ne nayi maka Biyayya da Hidima mganar yara kuma ka bari bana so..Tun yaya nada rai yaran suke ya"yana Har ga Allah ina masu kaunar da banayi ma ya"yan cikina..!
Cikin Farinciki yace"Nayi kuskure..bazan kara Fadin haka ba Allah ya jikan Hadiza ke kuma Allah yayi miki albarka..!
Ta amsa cikin Farinciki acikin ranta da Ameen Ameen..!
Tare suka karisa karyawan cikin Farimciki ranakun da Balaraba bazata manta dasu ba acikin Rayuwarta..!
Ita ta kwashe kayan da suka bata zuwa Kitchen sannan ta Dawo Dakin nasa.
Sai ganinsa tayi Tsaye yana saka agogon Hannunsa na fata cikin Mamaki tace"Fita zakayi..?
Bai kalleta ba yace"Ina so na fita saboda akwai wadanda zasu zo Diban kwai yau..Sannan masu aikin gonar mallam ta bazanga sun kirani Suna bukatar taki nasu yaja baya gaskiya shine nake so na fita na leka Mallam muyi mgana sai na Kira Jafaru naji ya zamu yi..!
Farinciki ya cikata abaya fa sai dai Ya fadama yaya irin wannan batun ammh yau babu yaya Dole dai kanwar nakin itace komai cikin Alhini tace"Na Dauka yau zaka tayani zama..Tunda yaran duk suna makaranta..!
Ta karishe Fada cikin Shagwaba kamar wata yarinya Mirmishi kawai yayi yana Fadin"Bazan dade ba zan dawo..Daukomin Hula in saka..!
Ba musu ta shiga ciki Ranta Fes ta Zabomai hula kadan shaddan Jikinsa kalan Sararin samaniya ita da kanta ta sakamai ta feshesa da Turare ta Daukomai Bakin Takalminsa Budadde ta Gogemai ta bashi ya saka ta Dauko Wayarsa da key din Motarsa ta mikamai ya karba yaana yaba Kokarinta akansa cikin yabamanta yace"Allah yayi miki albarka..!
Kanta na kasa ta amsa da Ameen
Fita yayi tabi bayansa sai da suka zo Tsakar gidan sannan ya Tsaya Dakin yaya ya kalla na wani Lokaci kamar ita zai gani tana zaune kofar Dakinta Cikin baranda kamar yadda ta saba Sai dai ina mai Rabawa da Riga ta raba..!
Mamanmu kuma Tuni Farincikinta ya Gudu ganin inda yake kallo cikin Kissa ta kalli wajen kafin ta Sauke Numfashi Tana fadin"Kaima sai kaji kamar zka ganta ko..!Nima haka nake ji Koda yaushe..Su kansu yaran sun kasa sakewa Wuni suke cikin Dakin musamman ma Amina gani take kamar yayan zata Dawo watarana..!
Kai ya jinjina yana kokarin Daidaita kansa yace"Nayi tunanin ko na Dauko Goggo Jumai ce tazo ta zauna Dakin yayan..tunda chan gidan nasu fa ba kowa ko ya kika gani..?
Mamanmu taji kamar ta saka kuka Yaya ta rasu ammh bazata Huta ba..!
Cikin Danne abunda ke ranta ta kallesa kafin tace"Ka raina kulawar da nake basu ne..?
Cikon Daburcewa yace"Me ya kawo wannan maganar kuma..?
Sai ta fara kuka tana fadin"Eh mana ka raina ne..In ba haka ba meyasa zakaje ka Dauko goggo Jumai Salon mutane suju suce bana rike su Amina Tsakani ga Allah in ko ka jamin wannan Shedar bazan taba yafe maka ba Sa"idu..!
Sai ya Rude ya Rikota yana Fadin"A"a fa ba Haka nake nufi ba..Kada kimin mumman Fassara..!
Cikin Jan hanci tace"sai dai in ka janye mganar Dawo da goggo Jumai sannan zan yarda ba haka kake nufi ba..!
Da sauri yace"Na janye..Daman Dake kadai nayi mgana ko Mallam ban yi mgana dashi ba..Itama goggon da wuya ta yarda tunda wajen jikanta Take zaune dake Hadeja..!
Sai alokacin ta saki ranta da Fuskarta tana Fadin"Bana son abunda zai min Shamaki da yarana..Ina matukar kaunarsu kamar ni na Haifesu mussaman Diyata Amina..!
Mirmishi yayi bai ce komai ba ya Fara Tafiya tabi bayansa ganin har sun fita Koridi yasa ya Juyo yana fadin"Na zama dan gata kenan..Rakiya za"ayin har waje kenan..?
Sunkuyar dakai tayi tana Dariya sai kawai ya kalleta yana fatan kada ya Dannen hakkinta domin karfi hali kawai yake yi.
Har bakin get ta rakasa Motarsa tana Gidan Baba mallan sukayi sallama har zai fita ya juyo yana fadin"Kin Duba Cefanan kayan abincin da Jafaru ya kawo jiya kuwa..?
Tace"Na duba komai yayi..!
Yace"Ba abunda za"a karo..!
Kai tsaye tace"Sai dai goldenmorn saboda yaran nan..Sai Cornfkles naga Kwali Daya ne .!
Kai ya gyada kafin yace"Shikenan zan fadama Jafar zai kawo anjuma..!
Daga haka sukayi sallama ta Bishi da Allah ya Kiyaye hanya.
Yana wucewa ta koma cikin gidan Tana takun Daidai kamar wata Sarauniya sai da tazo Tsakar gidan ta Juya ta kara juyawa kafin ta kyalkyace da Dariya tana Fadin"Burina ya cika..Abunda na Dade ina neman ya Kusa Tabbata..Sa"idu ya zama nawa Dashi da komai nasa..Ni Dayyaba duniya Sabuwa..!
Sai kuma ta fara Dariyan kamar tayi hauka Karan wayarta Dataji shi ya Sa ta Ruga zuwa Dakinta sunan wanda ke kira yasa gabanta ya fadi ta Dauka da Sauri tana Fadin"Gabana ya fadi madina..Kada ki cemin min kuskure ma wannan karon..?
Tsaki Anty Amarya taja Dagachan bangaran kafin tace"Kice zaki kuskuremin Dayyaba..!
Da mamaki tace"Ni kuma..?
Kai Tsaye tace"Eh mana..Tayaya zaki shanyani ina jiranki ban ji wata mgana Daga bakin ki ba..?
Ko Saboda na taimaaka miki kin samu cikar Burinki ni kuma sai ki ki bani Damar da zan cika nawa..?Auto kin samu Sa"idu atafin hannunki Dayyaba zaki juyamin baya..To baki isa ba..In kikace zaki haka na Rantse har ga Allah zan sakaki a Tara ba uku bama..
Cikin Tashin Hankali da Sigan Lallashi Mamanmu ta fara fadin"Haba Madina taya zaki min wannan Fahimtar..?Sa"idun ai bai gama zuwa Hannuna ba ke kinsani kuma komai zan yi yanzu sai da Lura kada ki mamta Fuskarmu ta Balaraba da Marliya akasani ba"asan Fuskar Madina da Dayyaba..Ina sane da aikin mu kan Amina Dayyaba..ina sane so nake nabi komai Daki Daki yadda in komai ya Lalace baza"a taba zarginmu ba..!
Sai alokacin ta sauke Numfashi tana Fadin"Kinsan abunda yasa Sakina bata Damu ba..Saboda nace mata zan Lalata wannan auran zai zama mara amfani Dayyaba..Kuma ke zaki mun wannan kokarin bana shiri da yarinyar..Ke kin jata ajikinki tana ganin girmanki Fiye data uwarta..Bana son na gaza..Sakina ce kadai Tauraruwa agidan Umar Dayyaba..kina saka Amina ta samu Baba Mallan tace mai bata son wannan auran zai rabashi,Sannan shi kanshi Sa"idun ki hillacesa ya Furta ma Mallam kinsa akan auran Daganan Mallam zai kullacesa Burina Zai cika ma ganin baraka Tsakanin Mallam da Sa"idu sannan Wannan yarinyar ta fita Daga Tsarina..!
Mamanmu tace"Kada ki damu yau zan fara aikin mu..nayi miki alkwarin yau zan Turata gobe zaki ji Labari mai Dadi..!
Cikin Farinciki tace"Dakyau..Nasan zaki iya..In hakan ta faru ki Sani Sa"idu zai kara zama naki ke kadai har gaban Abada..!
Atare suka saki Dariyan Nishadi da Tunanin Duniya ta Bude musu sabuwa abunda basu sani ba Alkwarin Allah bazai taba tashi ba sannan Dan Hakin Daka raina watarana shi zai tsole maka ido..!
*****
Sai shidda da wani abu na yammah suka dawo daga makaaranta Karfe hudu suka tashi Hadda suka shiga Islamiya,Amina da Hamida sai da suka Biya suka gaida Hajiya babba da ke Fama da kafa.
Sun fito Daga Dakin Hajiya Babba suka iske har ya Abida ta baje afalo da passQ tana Faman dubawa Daga Dawowarta dayake sun yi nisa a jarabawarsu sun kusa gama Neco zasu fara Weac,su kuma su Amina sun gama Exam hutu suke yi sai in sun koma zasu shiga SS2..!
Amina ta kalleta tana fadin"Ubanki Boko..Boko..Bokoko..!
Abida ta Dago tana kallonta cikin Harara tace"Allah yasa dai ba ni kika Zaga ba Amina..?
Da sauri Amina tace"A"afa..Ni Ubanki Boko nace..!
Kai ta gyada kafin tayi kyaci tana Fadin"Da kin Daku na Rantse..!
Amina ta Murguda mata baki tana Fadi kasa kasa"Sai dai ki Daki wannan mai Dogon wuyan..!
Ta jita sai dai bataji karshen ba Hanne da Hamida ne sukaji suna kunshe Dariya Saboda tuna wanda zai auri ya Abidan da Mallam ya basu izini su zo su gana,Har na ya Zeenatu yazo shi dai bai da Muni sai bakin masifa kamar na Zunubi na ya Abida kuma Fari ne girman Lagos tunda hannun yayan babansa ya tashi Dake lagos Jikinsa na Hutu ne sai dai kamar mace har muryansa kamar ta mata yaa wani Lamgwabe kai sai Dogon Wuya rana Daya sukazo su Amina saboda Bala"i sai da suka Labe suka gansu haka suka dinga Dariya,sai kuma suna Tsokanar su kasa kasa suna Dariya..!
Yau ma ya Abida cewa tayi"Amina maimaita abunda naji kince..?
Amina tace"La cewa fa nayi ina Uncle Jalil..?
Wata uwar harara ta banka mata kafin tayi Tsaki ta cigaba da abunda take yi yasa su ka kwashe da Dariya ta Dago tana kallonsu Suna ganin haka suka Danne bakinsu suna zare ido ganin haka yasa. Ta mike tana fadin"Yaran nan kun ranani Wlh yau sai naji Ubanku..!
Ganin ta Nufosu yasa suka Rumtuma Hanne ta shiga Dakinsu su kuma su Hamida suka fice aguje ganin haka yasa ta Dawo tana fadin"Hanne sai dai in bazaki fito ba..Marasa,kunya ko naga wanda Baba mallam zai kawo muku..Gwara Amina ta ga nata ku ba"a sani ba ko wasu kala ne don mai garinku..!
Hajiya babba tana Daki tana jinsu Dariya takeyi ita kanta ranar da Jalil din yazo ya gaisheta sai da tayi Dariyan yadda yake karya wuya Gwarama Auwal din Zeenatu sai dai shi kato ne ga baki..!
Aguje suka shiga gidan Mamanmu na Alwala bakin Famfo ta gansu sun fado har ta tsorata ta zabura tana fadin"Lafiya..?
Hamida ce tace"Amina ce ta Tsokano ya Abida shine ta biyomu..!
Tsaki taja kafin tace"Shine zaku shigo da gudu wlh har kun tsoratani..!
Daga haka ta cigaba da alwalanta Hamida ce ta zube kan Tabarman da suke shimfidawa duk dare su zauna zaman hira kafin kowa ya nemi makwanci.
Amina kuwa Dakin yaya ta shige taga ya zeenatu na zaune tana karatu itama ganin yadda Amina ta shigo yasa ta Dago tana fadin"bana son hayaniya ki koma Dakin mamanmu..!
Amina ta kalleta da Hijabinta na Hadda bata cire ba cikin Danne Dariyanta tace"To..!
Ta kama Hanyar fita tana fadin"Baki baki..baki fentin Allah bana Mutum ba..!
Zeenatu ta bita da kallo Lokaci Daya ta bata rai gaskiya Amina ta fada Auwal akwai baki gashi kato Allah na Tuba ina zata kaishi..!
Hamida fashin Sallah take yi Amina ce kadai ke sallah ita tayi alwala tayi sallar mangariba,itama bata Dade da yin wankan tsarkin ba.
Suka fito waje suna Hira abinci suka Dibo ita da Hamida suna ci Shinkafa da wake da Miyar Jajjage suna ci suna Santi Mamanmu na cikin Daki tunda ta shiga sallah bata fito ba ita da ya Zeenatu..!
Da aka kira isha"i ma awaje Amina tayi Sallarta bayan ta idar suka cigaba da Hira da Hamida Amina mantawa take tana da aure in ba wani ya Tuna mata Ba Hamida da Hanne ce tunda sukasamu Amina ta Dawo yadda take basa Dauko mganar da zai Dagula mata Lissafi.
Mamanmu ce ta Leko tana Fadin"Ina Jawaad..?naga ban gansa bane..!
Hamida tace"Muna dawowa makaranta yaga Aba ya manne masa suna Falon Baba mallan yanzu..!
Kai ta gyada kafin tace"Amina zo ina son ganinki..!
Ba musu Amina ta mike ta Bita Ciki Hamida bata damu ba sanin Sirri Tsakanin mamanmu da Amina sun saba komawa tayi ta kwanta saman Tabarman.
Mamanmu ce kan gaba har cikin Bedroom dinta ta zauna gefen gado tana fadin"Taho ki zauna nan mgana nake som muyi..!
Ba musu Amina ta zauna tana fadin"Lafiya kuwa mamanmu..?
Mirmishi tayi lokaci Daya tana Dafa kafadan Amina kafin tace"Bakomai mgana zamu yi ki natsu ki Saurareni..
Amina ta natsun tana jinta Mamanmu sai ta gayyato damuwa afuskarta kafin tace"Amina kinsan ina kaunarki ko..?Kaunar da ko Hamida bata same shi ba..?
Amina tace"Bama ni ba Mamanmu kowa ya Shaida Amina ce kadai Diyarki..!
Cikin Fara"a tace"Yauwa Diyata shiyasa na damu da rayuwarki sosai..Abunda ya faru na rasuwar yaya shiyasa ban Daga mganar ba..Ammh abun na raina Amina ko barcin Kirki banayi..!
Amina ta kalleta da mamaki kafin tace"Menene yake hanaki barci mamanmu..?
Cikin Sauke murya tace"Kan auranki Da Danmallam ne Amina..Sam baku Dace ba..Kina karama dake ta ina zaki iya auran wanda ya kusa haifanki uwa uba kuma kishi da mata Biyu..Ni ban ma jin balarabiyar Sakinar dai Daman chan ita da uwarta ba kaunar mu suke yi ba inaga kuma aure ya Hada..!
Shuru Amina tayi jikinta yayi sanyi bata son tuna yau ita matar aure ce..Har yau bata karbi wannan kaddaran ba ta kuma kasa zama ta fuskanci da gaske ne abunda ya faru..!
Yasa ta kasa mgana har sai da mamanmu ta cigaba da bata mgana da kuma nuna mata illah auran kuma ta yarda da ita matuka ta kuma san gaskiya ta fada barin ma inda tace"Amina a kuruciyarki naso ki sami Saurayi kamarki ki aura..Ba Umar ba..Ba sonki yake yi ba wahala kadai zaki sha ahannunsa da matarsa..Me zai hana ki fito fili ki Fadama Baba Mallam bakya son auran nan..?na tabbata zai saka Danmallam ya sakeki ki auri wanda kike so yama sunan Surukin nawa..?
Amina ta Kalleta da Idanuwanta da suka fara ruwa cikin karyen Murya tace"Aminu..!
Mamanmu tace"Yauwa Aminu..Ashema Amina ce da Aminu.
kada ki damu da zarar ya sakeki zan san yadda nayi kika auri wanda kike so nayi miki alkwari kin san dai ban taba miki alkwari na gaza cikashi ba ko..?
Amina ta gyada kai tana Zubar kwallah kafin tace"Ina tsoro Mamanmu..In Aba yaji wlh zai Kasheeni..Kuma ni bazan iya kallon Baba mallam da Hajiya babba nace bana son jininsi ba kamar in nayi hakan ban kyauta ba..!
Kamar ta kwadaa mata mari haka taji ammh sai ta cije tana Sassauta murya tace"Kada ki damu da wannan Zan san yadda zan yi..Aba dinku ni zan bashi mgana shima ai ya Fahimci an kwareki wlh..Nasan Hajiya da Mallam zasu fahimceki nasani..!
Kidai kije kiyi mai mgana na Tabbata zaki ga abunda nake fadama miki..!
Amina na sharan kwallah tace"To me zan ma Mallam din..?
Mamanmu ta gyara zama tana Fadin"Yauwa ko kefa..?Kuka Zaki sakamai kina fadin baki son auran don Allah yasa Danmallan ya Sake ki shikenan..!
Amina ta jiku da Hawaye kafin tace"Kina ganin ba matsala mamanmu..?
Da sauri tace"Babu matsala nace miki zan tare komai nice fa
Ko Duniya zata juya miki baya ni ina Tare Dake..?ko na taba juya miki baya..?
Amina ta girgiza kai da Sauri tace"Yauwa to tashi kije..Ki bari sai Aba din ku ya shigo gida sai ki tafi Wajen Mallam din..!
Da kai ta amsa mata ta kasa mata Musu,Ammh tana ganin kamar abunda tasata tayin bamai kyau bane Tayaya zata Bijirema Aba da kuma Baba Maallam anya in tayi haka batayi Butulci ba..?
Sai dai kuma ta kasa yima mamanmu Musu har ta baro Dakin ta bar mamanmu na Hararanta cikin Takaichi kafin tace,"Shashasha..!
Amina kuma Dakinsu ta koma ta kwanta kan gadonta tana kukan yadda Rayuwa ta juya mata baya aduk ranar Duniya sai ta tuna da Aminu tayi kuka,da kuma kewarsa tare da Tunanin Halin Dayake ciki..!
Bata da mai gayamata kuma ita bazata nemi taji ba Tun bayan Mutuwar yaya tayi alkwarin daina Zame kowa Jidali so take ta wanke kanta wajen Aba kada ya kara ganin bakinta ammh kuma meyasa mamanmu zata ce sai tayi haka..?
Tana kwancen taji Shigowar Aba,chan kuma sai ga Mamanmu tazo Dakin tana tashinta yi tayi kamar mai barci tatashi tana sosa ido.
Mamanmu tace"Tashi kije Aba din ku ya shigo shi da jawad..!
Dole ta mike tana Tsaye kanta har ta saka Hijabi tare suka fita ta iske hamida na barci ma saman Tabarma har kofar gida ta rakata ta bude mata gida tana Fadin"In kin dawo ki shigo Sai ki Rufe..Ko kuma kiyi kwanciyar ki Bangaran Hajiya kada Aba din ku yaji Dawowarki..!
Hawaye ya cika idonta yasa ta kasa mgana,Haka ta wuce sum sum har Zuwa gidan Baba mallan megadi kansa yayi mamakin ganinta Tara na Dare har ya wuce,sai dai bai yi mgana ba.
Gabadaya kamar an cire mata wani karkashi Jiki a sukuku ta karisa har Falon Baba mallam data ga haske acikin Alamun bai kwanta ba.
Ta Dade tsaye ta kasa shiga tana saka tana warwara,Har sai da taji mganar Baba Mallam daga ciki yana Fadin"Waye anan..?
Jikinta sai ya fara rawa cikin Inda inda ta Daga Labulen falon ta shigo Tana fadin"Nine Baba mallam..!
Mamakin ganinta yayi da Daddaran nan zaune yake kan kujera mai zaman mutum Biyu sanye da Shigarsa kamar bai ma Sauya kaya ba Harda Rawaninsa da Farin gilashinsa yana Duba wani littafin Larabci..!
Cikin mamaki yace"UWATA..!
Jin sunan daya kirata yasa taji Rauninta ya fara bayyana kaawai sai ta Fashe da kuka kukan data ke rikewa Baba Mallam ya ijiye littafin hannunsa yana fadin"Ashh..Kari so naji waye ya tabanin Uwata..!
Dole ta karisa gabansa ta Zube tana kuka ya Dafa kanta yana fadin"daina kuka Fadamin damuwarki ni kuma nayi miki alkwarin Magance miki ita..!
Sai taji Wani irin kaunar da bata jinta ba kan Baba Mallam ya taso mata tayaya zata iya kallon wannan Dattajon mai Farin Alheri taki jininsa taki Alherin daya kulla da ita duk da Rashin Fahimtar dake Tattare da Rayuwarta gaskiya bazata iya ba..!
Kawai sai ta sulale kan kafar Baba Mallam tana Cigaba da raira kukanta..
Cikin Damuwa ya saka Hannu yana Shafa kanta zuwa bayanta Allah ne ya Hada wannan Kaunar kwatankwancin kaunar da yake ma Sa"idu..!
Cikin wata murya yace"Kiyi hakuri Mamana..Ki yi hakuri nasan ban kyauta miki ba..Na aura miki Umaru Jinina sai daga baya naji kamar nayi son kai..ban kyauta ba kamar na Zalunceki..!
Da sauri Amina ta Dago Idanuwanta Jajir cikin kuka tace"Har Abada bazaka Taba Zaluna ba..Na karbi wannan gatan da kayi min na yaba..Allah yafini yabawa Baabaa..!
Kawai sai yaji sukuni sukunin da bai Taba samu ba Tunda ya hada wannan auran cikin Tausasawa yake fadin"Allah yayi miki albarka..Nagode sosai .Allah ya jikan Hadiza da gafara..!
Da amin take amsawa ta na godema Allah da baisa ta tafka wannan abun kunyar ba watsama Wanda Alherinsa ya Lullube rayuwarta data iyayanta gabadaya..!
*Janafty*
*TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*
*Sadaukawa ga Halima yusuf gwarzo Besty Alherin Allah ya kai miki a dukkan inda kike Ameen*
*🅿️26*
Ranar Hajiya Uwani keda Shashen Mallam shiyasa ta chaba ado tana tashin kamshi ta ko"ina,Ta shigo da Fara"arta sai dai kuma ya mamaye hakan da bakincikin ganin Amina gaban Mallam suna hira saboda Takaici ji tayi kamar ta koma da baya sai dai sun riga sun ganta bata da yarda zatayi sai ta Saki Fuskarta ta Kakaro Dariya da Mirmishi ta Dora Saman Fuskarta..!
Baba Mallam ya dago kansa Daga kan Amina ya sauke kan Hajiya uwa data Tsaro kwalliyanta cikin Doguwar rigar shaddanta Nan da nan ya saki Fuska yana kallonta acikin matansa kaf ko Anty Amarya bzata gwadama Uwani Kwalliya da kamshi ba Duk da Ta kwana Biyu a duniya bata yarda ta zauna ba gyara ba ita din yar Kwalliya ce kowa ya sani.!
Cikin Fara"arsa da Sautinsa yace"Lale da zuwa Hajiya uwa..Uwanin Alheri uwanin Yunusa daman yanzu nake Fadi araina ko an tsaya yanga ne yanmatancin ne ya tashi!
Kanta sai ya kara girma ta kariso Cikin takun mata har ta kariso gefensa ta zauna sai Amina ta matsa gefe Tana gaisheta ta amsa Tana Fadin"Ka fahimci abunda ya Tsaidani ko Mallam..?
Yana kallon Fuskarta yace"Na fahimta..Uwani uwayen kwalliya da ado..!
Dariya tayi Tana kallon Amina da kanta ke kasa tana wasa da Gefen Hijabinta cikin Fara"a tace"Allah yasa ban katse Hirar surukanta ba. !
Sai da ya kalli Amina kafin yace"Ko da Sakina bana Surukanta Uwani..Ballatana Amina..Itadin Uwatace..Hira muke ta Tsakanin Uwa da abunda ta haifa kin kum san bamai iya raba wannan soyayyar..!
Tana Mirmishi tace"Ba shakka kam.Ko na koma sai kun gama ne Mallam..?
Kai ya girgiza kafin yace"A"a ai bazata kare ba..sai dai mu barsa zuwa gaba..Mamana tashi kije shashen Hajiya ki kwana zuwa safe Dare yayi su Akilu sun kwanta ballatana na Taso shi ya rakaki..!
Amina batayi gaddama ba ta mike tana musu sallama ta fice zuwa shashen Hajiya babba tana jin sukuni aranta da bata Furta abunda Mamanmu da tsarata mata da batasan ina zata kai kunya ba..!
Sai da Amina ta fice sannan Hajiya uwa ta gyara zama tana fadin"Mallan kayi mgana da shamsu kuwa..?
Kai Tsaye yace"bai kirani ba meya faru..?
Cikin kwantar dakai tace"Kudin hannunsa ne duk suka kare wajen Registration,yace min yana son aturamai wasu kudin..!
Dayake shamsu ya samu gurbin karatu a Federal Universty Dutse ne har ya tafi..!
Baba mallam kamar bazai yi mgana ba sai chan yace"Nayi mgana da Aliyu abokin Umaru yace min har Daki ya samu nan Kusa da makarantar bai ce Komai ba..Ammh zan kira shi Shamsu naji kinsan ba kasafai zaka rika sakarma yara kudi domin sun Tsallake gaban zuwa karatu ka rika saka ido kada watarana sakewarka ta saka su jawo maka wani abun mgana zan yi mgana dashi kuma zan saka shi Aliyun ya Bincikamin inda bukatar wani Abu zam ma Sa"idu mgana zai Turamai Insha Allahu..!
Hajiya uwani gabadaya takaici ya Rufeta,kamar ta saki kuka haka take ji sai dai bata nuna ba sai ma kai data Rausayar tace"Shikenan hakan yana da kyau Mallam ka bincika din..!
Daga haka ta tsuke bakinta tana wani Nazari har yaushe ne ya"yanta zasu zama na Farko wajen Mallam bayan ya"yan Hajiya Babba da Sa"idu Burinta na shekaru bazai cika da wuri ba kenan.
Shi ya katse mata tunani da Fadin"Ya jikin Umaima ina Fatan ta daina Ihun nan cikin Dare..?
Ya famo mata inda ke mata kaikayi Cikin Karin Damuwa tace"To yayi sauki za"a ce Mallam..Anya ba mganar malamin nan gaskiya bane..?
Cikin Kallon sama sama yace"Dayace mene..?
Sannan wajen wani malami kika kai min yata ban sani ba..?
Sai alokacin tasan tayi barambarama ai baisan sunje har Niger kan matsalan Umaima ita da Batula ba..!
Cikin Inda inda ta fara mgana da sauri ya katseta cikin Kaushinsa yace"Ina kika kaita kuma me malamin da kika bashi yarda Fiye da Ubangijinki yace..?in kikamin karya wlh zan ci Mutumcinki in nayi bincike na gano gaskiyan mgana..!
Sai Jikinta ya fara rawa tasan Halin Mallam in bata Fadamai ba bazaman Lafiya ita kuwa dake cikin Kishiyoyi har uku mezai sa ta dinga Fada da Miji..!
Da hanzari tace"Wlh ba da son raina naje ba labarinsa naji ance yana bada mganin Aljanu..k..
"Ki amsamin Tambayata..!
Katseta yayi cikin bacin rai bakinta na rawa tace"Niger ne..Mukaje kuma..kuma yace ne wai Ture ne akayimin bai sameni ba ya Fadama Umaima..!
Wani wawan Tsaki yaja kafin yace"Wa ya rakaki wajen..?
Kai Tsaye tace"Kanwata Batula ce..!
Yana kallonta cikin bacin rai yace"Ba tun yau ba na lura da Batula ta yarda da Bin malaman nan makaryata makiyan Allah kema shine ta jaki kikai min ya gaban wani mushuriki da sunan neman mgani akwai abunda zai baku wanda Allah bazai baku bane..?Meyasa wani Lokacin baku da Tunani ne Uwani..!
Da sauri ta tareshi ganin yadda Ransa ya baci tace"Wlh ni da batula muka je..Ban je da Umaima ba..!
Cikin bacin rai yace"Ko baki je da ita ba kin kai laluranta gabansa kin Tallatamai shi kuma ya cikaku da karyansa..Banda Hada fada da karya waye zai miki sihirin da har zai koma kanta..?To ban yarda da wannan ba Ni ya'ta Lalurarta daga Indalahi ne kuma garesa nake nema mata waraka in ta warke wannan ikonsa ne in bata warke bama wannan ikonsa ne..Kada na Sake ji koda wasa wata mgana irin wannan in haka ta sake faruwa komai ma zai yi faruwa zan dauki mataki mummana akanki kin ji na Fadamiki..!
Ya karishe faada cikin bayyana bacin ransa da sauri ta Sulale kan Gwiwoyinta tana fadin"Kayi hakuri mallam..Insha Allahu haka bazata kara faruwa ba..!
Bai kalleta ba yace"Bana son Rabuwar kai kan mata na da yara na..Nayi shekaru ina hada kan iyalaina Waje Daya..Nan duniya bayan ku da Iyalan Sa"idu bani da wani Ahali da zan kallah nace nawa ne sai ku..To ki sani in kina Biyema mganar malaman karyan nan zaki haifarmin da Gaba cikin Gidana kuma in hakan ta faru Uwani zaki sha mamakin hukuncin da zan yanke akanki Wlh..!
Gabanta ya fadi taya ya komai zai kwace mata Burinta bai cika ba yasa ta kwantar dakai tana ta basa Hakuri sai da taga ya Hakura sannan ta Sauke Numfashi ta koma ta zauna tana kokuwa da bacin ran dake taso mata..!
Ba domin ta kasa galaba akansa ba da Tuni Mama ta samo mata kan mallam ya zama sai yarda tayi dashi sai dai ina ta gaji da kashe kudi akansa ta Hakura Allah yana tare dashi kuma ya kare bawansa wani abu bai isa ya Cutar dashi ba sai dai ko in ya so..!
Ganin yadan sauko har suna Hira yasa ta Sako mganar dake cin ranta"Mallam ya mganar Amina da Danmallam ne..!?
Naji bakace komai ba haryanzu..?
Kai tsaye yace mata"Har gobe sunanan a matsayin miji da mata..wani abu kike son sani kuma..?!
Ya kalleta cikin son Tabbatar da abunda yake Tunanin take son ji game da lamarin.
Da sauri ta sauya mganarta da cewa"Maallam mganar tarewa fa..?ai tunda angama mai wahalar itama sai yayi mata Visa da Shedar zama achan kamar yadda yayi ma Sakina ya Tafi da matarsa ni aganina zai fi mallam..!
Ya dade bai yi mgana ba har ta Fidda rai kafin taji ya sauke numfashi Lokaci Daya yana fadin"Bazan yi haka ba..zan bama Mamana daman da bana ma kowacensu..Bazata tare a matsayin matar Umaru ba sai ta gama makaranta ma"ana in sunyi Candy in Hadata da yan"uwanta in aurar dasu..!
Hajiya uwani da Farimciki ya cika sai ta kanne cikin wani yanayi tace"Nan da shekara nawa kenan Mallam..?
Kai Tsaye yace"Hajiya tace alissafi Shekara Daya da wani abu in bai kai Biyu bama..!
Ranta Fari tas kafin Lokacin nata Burin ya cika wato ma ta kwantar da Hankalinta Amina bata cikin Tsarinta yanzu tunda mijin ma baisan da ita ba kuma tarewar ma ba yanzu ba hakan ya Bala"in yi mata Dadi har sai da Fuskarta ta Nuna cikin dan yanayinta tace"Gaskiya kuma fa hakane..Ko Sa"idu kada yaga anyi mata Rashin Adalci..!
Wani banzan kallo yayi mata Kafin yace"ko Sa"idu ina da iko da Kansa ballatana abunda ya Haifa..Ko cutar dashi zanyi bazai taba mgana ba..Ballatana ba wannan Tsakani na dashi.Kauna ce da Biyayya Tsakanin Uba da abunda ya Haifa..Kada ma na Sake jin wannan mganar Sa"idu namin Biyayyar da ko ya"yan dana Haifa basa min yana wahala dani da Dukiyata batare da na yankamai albashi ba gayamin cikin Tarin mazan da na Haifa akwai wanda ya zauna Dani yake wahala dani kamar Sa"idu..?
Kai ta girgiza ta kasa mgana Miyan bakinta ya kafe cikin Dattakonsa yace"To ki saka aranki Sa"idu Shakikana ne..Kafin na same su shi na Sama kuma ina masa kwatakwacin kaunar da Uba zai yima abunda ya Haifa..Ki saka wannan aranki..!
Daga haka bai jira cewarta ba ya mike Dauke da Littafinsa ya Nufi Cikin Bedroom dinsa yana Fadin"Ni na shiga ciki sai kin shigo..!
Da kallon Takaici ta bisa kamar tatashi ta Makesa haka take ji Sa"idu rai Daya ya hana Burinta cika agabanta Mallam ke fadin yafi yemai ya"yan daya haifa Dariya tayi acikin Ranta Saboda itace silar rashin zaman Umar da Nazir agaban Ubansu ballatana su taimakamai bata so su sha gaban ya"yanta Yanzu kuwa Burinta yana gabda cika Nazeem ya kusa gama makaranta sannan Tsumi da Tanadi ya karanta wato Economics sannan yayi Degrre dinsa na Biyu kan abunda ya shafi Kasuwanci yana Dawowa zata san yadda zatayi Sa"idu ya matsa ya bama mai waje wajensa ya kasance shine kan duka Dukiyar Mallam din Kafin Uzairu shima ya gama yazo su hada hannu hango kanta Take shekara Biyar masu zuwa ita Amtsayin Hajiya babba..Ya"yanta ne masu gidan ita ce mai Bada Umarni da mgana da yawun mallam wannan Tunanin yasa ta farinciki ta tashi Cikin Takunta ta nufi Bedroom din mallan tana cigaba da Tsara wasu abubuwan acikin ranta..!
Amina kuwa sai washegari Hajiya ta ganta saboda sanda ta shigo gabadayansu sun yi barci Ya Abida ce kadai idonta Biyu tana karatu hanne ma ta Dade da yin barci.
Da safe ko gida bata koma ba kayan Hanne ta saka da hijabinta na Hadda Tunda guda Biyu hannen gareta.
Suka tafi Hadda Hamida bata je ba bata da Lafiya ciwon mara Ya zeenatu ke fadama da Amina taga bata ga Hamidan ba..!
Sai da yammah da suka Dawo Amina ta Dawo gida ita Da hanne suka Duba Hamida taji sauki ma,Hanne bata jima ba tayi musu sallama ta wuce gida Mamanmu daman jiran Amina take yi taji ya ake ciki tun Safe Aanty Amarya ta Kirata taji Labari mai Dadi ba wani bayani shiyasa Hanne na Tafiya taja Amina kuryan Dakinta Tana Fadin"Ya kuka yi da Mallam din..?
Amina ta Sadda kanta kasa kafin tace"Mammanmu na kasa..Bazan iya kallon Baba mallam nace bana son jininsa ba..Bai kamata na rama Tarin Alherinsa da sharri ba..Sannan in Aba yaji Wlh sai ya kusa kasheni agidanan..!
Ta karishe kamar tayi kuka ba Domin mamanmu ta kai zuciyarta nesa ba da sai ta kaima Amina Duka yadda Wani Takaicinta ya kamata ammh duk da Haka sai da ta Tureta tana Fadin"To Shikenan tunda kin kasa..sai kije..Sakina ta gasaki don Ubanki..bakuma zaki taba Daraja ba Tunda baya Sonki..Kuma matar Cushe bata Daraja .!
Yadda ta Zageta ta kuma Tureta yasa tasan ranta ya baci da Sauri ta riko Hannayenta tana fadin"Ba haka bane mamanmu..Wlh na kasa ne bazan yi kallon Baba mallam nace mai bana son auran nan ba..!
Mamanmu da kanta har ya fara ciwo Saboda takaici tace"Shikenan na fita Acikin mganar nan..Ba ruwana daman yancinki zan kwatan miki..!
Amina taji kanar tayi kuka kafin tace"To ke kije mana ki fadamai mamanmu..!
Hararanta tayi kafin tace"Saboda ni ce nake son rabuwa da shi ko..?ba inda zani ke kika sani ni sakamar min hannu Ke ji chan ki karata Wlh Amarya da Sakina bazasu barki ki zauna Lafiya ba.!
Amina tace"Tab..Sai dai ni ce bazan bar su zauna Lafiya ba Mamanmu..!
Ta razana gabanta na Fadi tace"Bangane ba..?
Amina tayi dariya kafin tace"To ai ba Tsoronsu nake ji ba..mamanmu ai Amina nake kirarina badai ta Mutum ba sai ta Allah su din banza!
Basu isa suyimin Abunda Allah bai min ba..!
Ta dade tana kallon Amina sai taga kamar Shagube tayi mata shiyasa cikin son tabbatarwa tace"ko kin fara son Danmllan din ne..?
Ta fada cikin Hararanta Amina ta Zaro Ido kafin tace"Ni..?Allah ya kyauta..ni Aminu kadai nake so..!
Ta Karishe Fada cikin wani yanayi Mamanmu ta sauke Numfashi kafin tace"Na Dauka kin fara son shi ne nace Ke kika sani..Domin Danmallam dai ya fara Tsufa auran wuri ne bai yi da kuma Haihuwar da bai samu ba..Kadan ne Aba din ku fa ya Girmesa..
Amina ta zaro idanuwanta suna shekk tace"Kai Mamanmu ko Aba fa bai Tsufa ba ballatana ya Danmllam..!
Mamanmu tace"Eyee..Kina son shi kenan Tunda ke baki ga tsufansa ba..?
Tafada tana Dungure mata kai Amina ta Dafe wajen tana fadin"Allah ya Tsari Amina..wannan ne zan so..Ya taba fa cemin banda natsuwa kuma ni wai kazama ce..!
Ta fada kamar alokacin yake fada mata Takaicin abun na Dawo mata Mamanmu ta kwace hannunta tana Fadin"ni sakeni..Kekika sani..Ba ina neman hanyar kwatan miki yanci ba kina bani kunya ba..Na barki dashi..Kin dai ji kazama yake ce miki Allah kadai yasan kuma wata kalma zai kara Jifanki dashi in ya ganki agidansa an riga an Tusamai ke..!
Amina ta Tura baki kafin tace"Sai na rama wlh..!
Mamanmu ta kalleta cikin Tunanin mafita ko mgana batayi ba ta Tura Kofar Tiolet din Dakinta tana Fadin"An kira sallah..!
Amina fita tayi ranta yadan yi sanyi ganin kamar mamanmu ta Dauki Zafi da Farko ammh Taji Dadi taga Daga baya ta saki ranta ajiyar rai ta sauke Tana jin kaso mafi yawa daga cikin Damuwarta suna yayewa Samun uwa irin Mamannu is a Bleessing..!
Mamanmu kuwa har Aba ya Dawo ta kasa samun wata mafita tana ganin ta bangaran Amina ba nasara Dole zata Jaraba ta bangaran Sa"idu ta Latsa ta gani ko zata ga Jini..!
Shiyasa koda ya dawo tayi wanka ta Shirya cikin riga da zani na Atamfa Hamida ta saka ta gyara Shashen nasa Dazu dataji Saukin jikinta Kayan abincinsa kuma tun kafin ya Dawo akai kai komai ciki.
Sanda ta fito duk suna Tsakar gida kan Tabarma suna Hira an kunna Gen akwai haske shiyasa basu shiga sun kwanta ba..!
Ganin bata ga Jawad ba yasa ta kalli Zeenatu Dake fama da karatu tace"Ina Jawaad..?
Hamida ce tace"Aba na shigowa ya makale masa..!
Mamanmu kamar ta saki Tsaki yaron nan zai zame mata ciwon ido sai ta rabashi da Uban taga ya zai yi shege kawai..!
Mirmishi ta saki kafin tace"Ni ina Dakin Abban ku. Ku kwanta da wuri ke Zeenatu saboda makaranta Gobe..!
Da toh suka amsa mata har ta wuce suka cigaba da Hiransu Amina da Hamida suke ta uban gaddama sai da Zeenatu ta Daka musu Tsawa tace sun dameta.!
Koda ta shiga Shashen Aba ta iskesa zaune shi da Jawaad suna cin Tuwom Shimkafa Miyar shuwakan data Girka Dazu da yammah Saboda Aba din Ranta ya kara baci ganinsa Dare Dare kan cinyar sa yana bashi Tuwon abaki Dakyar ta iya shigowa cikin Dakin tana kokuwa da yanayinta..!
Kan kujera ta zauna Tana fadin"Sannu da zuwa..Ka shigo ina wanka..!
Da yauwa ya amsa mata yana fadin"Haka yaran suka ce..!
Kafin ya cigaba da cin Tuwonsa yana Tambayan ko Jawad ya koshi ya Dagamai kai alamun eh Mamanmu tace"Daman Gulma ce irinta Jawad..Bai dade da gama cin nasa ba .!
Aba yace"Kinsan yaro..Ballatana ko abaya Jawad dani yake cin abinci ko da riga yaci nasa ne..!
Takaici bai barta tayi mgana ba Tana kallonsa har ya gama cin abimcin tatashi ta Dauki Faranti ta Fito dashi Ta mikama Amina tana fadin"Saka shi a Kitchen Amina..!
Da Sauri ta zo ta karba ita kuma ta koma ciki ta ga Jawaad ya gyara zama kan cinyarsa yasa ranta ya kara baci ta kalli Jawad tana Fadin"Jawad tashi kaje dakina ka kwanta..!
Tunda tun bayan rasuwar yay wani Lokacin in ya saka Rigima wajen Aba yake kwana ita kuma bazata iya Daukan wannan ba ta gama da Uwarsa kuma shi yazo ya rika sakata Damuwa ba..!
Aikuwa make Kafada yayi alamun bazai je ba Aba ya kalleta yana Fadin"Kyalesa in yayi barci sai ki kaisa..!
Takaici bai kara sa tayi mgana ba ta koma kan Daya daga cikin kujerun falon ta lafe ta maida hankalinta kan Tibin Dake falon cikin tashan Larabawa tana ji Aba ya maida hankalinsa kan jawaad yana Biyamai karatun da sukayi yau a makaranta Tun tana jinsu tana Gumduma ma Jawaad zaki aranta har ta fara barci Sama sama taji Aba na Kiran sunanta ta Bude ido tana kallonsa cikin Mamaki yace"wai har kin yi barci..?
Har jawad yayi barci na mika shi wajen Zeenatu nace yayi Fitsari kafin ya kwanta..!
Mikewa zaune tayi Dakyau tana sosa idonta kafin tace"bansan sanda barcin ya kwasheni bane..!
Kai ya gyada kafin ya wuce ciki yana Fadin"Bari nayi wanka..!
Da toh ta Bisa kafin tatashi tabi bayansa Yana shiga wankan ta Fitomai da jallabiya da gajeran wando ta koma ta zauna tana jiran fitowarsa Daya fito ya ganta sai da yayi mamaki cikin mamakin yace"Baki kwanta ba..?
Kai Tsaye tace"Eh ina son mgana Dakai ne..!
Bai damu ba yace"Bari nayi shafa"i da wuturi ke kin yi ko.?
Da sauri tace"Eh saboda bata so yace sai tayi alhalin ba Damunta yayi ba Khamsul salatin ma dole take yinsu.
Sai da ya saka Jallabiyan ya Shimfida Darduma ya tada salla har ya idar tana zaune ganin haka yasa bai Tsawaita addu"a ba ya juyo yana kallonta kafin yace"Ina Sauraranki..!
Gyara zama tayi tana Tattaro Jarumta da wani Kalan Tsausayi tace"Abban Jawad daman kam mganar Amina ce..!
Cikin dan Fargaba yace"Amina..?me Aminan ta sake yi kuma..?
Da sauri tace"Kwantar da Hankalinka batayi komai ba..Kawai ni ke son mgana Dakai kam Auran da mallam ya hada Tsakaninta da Danmallam na wajem Hajiya..!
Kallonta yake yi ko Kiftawa bai yi ba cikin mamakinta yace"Ina jinki..Sai me ya faru kuma..?
Mamanmu ta gyara zama tana Fadin"Tsakani ga Allah Abbansu baka ganin an kwari yarinyar nan..?
Cikin kosawa yace"Ina jinki..jeki kai Tsaye kan mganarki..!
Mamanmu bata Lura da yanayin kallonta da yake yi ba ta cigaba da Fadin"To gani nayi shi ba sa"anta ba In fa aka duba ya kusa haihuwanta in da auran kauye yayi..Ina Amina zata kai shi..?Sannan ga tarin Kishiyoyi har Biyu Abbansu a shekarun Amina batasan Dubarun zama da Kishiya ba,Shiyasa naga bari nayi maka mgana gaskiya aduba wannan al"amarin..!
Kallonta yake yi yana kokuwa da bacin Ransa kafin cikin Kaushin Murya yace"Ita Aminar ne tace miki bata son Dubarun zama da kishiyoyi ba..?To don Ubanta agidan nan Tsakanin mata Biyu ta taso..Gidan Baba Mallam kuma Hudu garesa reras gayamin wani karatu ne ya Ragemata bayan na wadannan gidajen..?
Sai mamanmu ta Daburce cikin Inda inda ta fara fadin"Ai kasan yarinya ce..Allah na Tuba ko hamida girman jiki ne..Ammh sai wannan shekaran ne suka shiga sha shida fa..Ina zata kai Umar..?
Akwai zalunci gaskiya..!
Kai Tsaye yace"Naji an zalunceta..Yanzu me kike so ayi..!?
Ta zata ya yarda da mganarta ne yasa Cikin Fara"a tace"Yauwa..Mallam kawai zaka je ka fadamawa baka son wannan Hadin na tabbata zai saka Danmallam ya saketa..!
"KE BALARABA..!
Aba ya Daka mata Tsawa da sai da ta Tsorata cikin Bacin rai mai Tsanani yace"Ita Aminar ne ta aiko ki kizo ki Fadamin naje na samu Mallam na Fadamai bata son auran Umar..?Tana so ya saketa..?
Mamanmu Sai taji ta kasa mgana Mikewa yayi cikim bacin rai yana Fadin"Dake nake mgana..!
Cikin kwantar da Murya tace"ba yadda ka Dauka bane..Wlh basu dac..!
"daman waya ce sun dace..!
Ya katseta cikin Tsawa kafin ya Cigaba da fadin" A yanayin Rayuwar Umar Kwata kwata Amina bata Dace dashi ba..Ita din ba ajinsa bane..Kinsan waye Umar kuwa..?Kyakyawan Asali Ubansa Malami ne, da ba iya Nageria ba kasashen Duniya sun san da zamansa Umaru nada shaidar Degree guda Biyu akan abunda ya shafi Qur"ani da Hadisai Balaraba tashin Madina karatun Madina garin ma"aiiki Kinsan adadin iliminsa..?Koyarwa yake a Babbar Jami"ar Musulunci ta Madina Shine kike fadin an zalunci Amina domin an aura mata Mutum nagari mai kamala da nagarta..Mai Sanyi mai biyayya da gudun mgana Shine kike fadin an zalunceta..?To bari kiji ba ita aka cuta ba Shi aka Cuta..Shi aka Tauye Balaraba ammh bai Bude baki yayi mgana basai ku..!?to ni Ubanta banda Sanadin Ubansa da ko Filin jirgin sama bazan taba Tsallakewa ba..!
Ya karishe fada cikin bayyana bacin ransa har jijiyon kansa na mikewa.
Mamanmu kuma ta Daskare Rashin Sukuni ya shigeta tasan ba Nasara wannan gabar bata ci nasara ba sai dai bata sare ba cikin Lallashi tace"Kayi hakuri abun bai kai harda gori ba..!
Dakatar da ita yayi yana fadin"Ko ni Sa"idu ban isa Mallam yayi Umarni akaina na Tsallake ba ballatana abunda na Haifa ki Fadamin gaskiya Aminar ce ta aiko ki ko..?
Mamanmu ranta ya gama baci shiyasa tace"Yarinya ta fadi Ra"ayinta ne Abbansu kada kaga Laifinta..!
Bai jira cewarta ba Fuuu ya fice yana kwala Kiran Sunan Amina Tun daga Cikin Dakin har ya fito Tsakar gidan Mamanmu ta rufamai baya gabanta na Fadi.
Amina da suke hira da Hamida da taji kiran Aba sai da gabanta ya fadi kuma sai suka ganshi agabansu kwatsam cikin Tsoro ta mike tana fadin"Gani Aba..!
Yadda idanuwanta sukayi ne saboda Tsoro sai ya ganta kamar Hadiza Shiyasa sai ya Sauke Murya yana Fadin"Zo nan..!
Lokaci daya ya juya ya Raba gefen Mamanmu ya koma Falonsa Amina ta koma Daki gabanta na Fadi ta Dauko Hijabinta ta saka tabi bayansu Hamida da Zeenatu sukayi Tsuru Tsuru suna Tunanin me ya faru kuma..!
Dukkansu a tsaye ta gansu Aba da Mamanmu sai ta kara Rikicewa yasa ta Zube gabansa cikin Rawan baki tace"Gani Aba..!
Cikin rawan murya sai yaji Fushinsa ya Sauka sai yaji Tsausayinta komawa yayi ya zauna yana Sauke Numfashi kafin yace"Amina..Ni waye a wajenki..?
Sai da ta kallesa sannan tace"Kai Baba na ne..Mahaifina..!
Cikin Jinjina kai cikin wani irin Sauti yace"Indai ni mahaifinki ne Amina..Ki sani ko bayan raina kika bijirema Auran Jinin Baba Mallam ban yafe miki ba Amina..!
Ba Amina kadai ba hatta Mamanmu ta firgita cikin wani yanayi Amina ta Dago ta na kallon Aba cikin Taruwan Hawaye aidanuwanta.
Ganin haka yasa ya Daga mata kai yana Fadin"Eh haka nace..Ban yafe miki ba Amina..Sannan zan sallama ki acikin ya"yana..Bazan jure ganin Abunda na Haifa ya Bijirema Mutumin da ya zama gata na ba..Mutumin da ya Lullube Rayuwata da Duka Alheransa..ki Tuna da wannan..!
Da haka ya mike ya shige ciki ya bar su nan Amina ta kalli mamanmu sai hawaye sharr.
Mamanmu tayi saurin cewa"Tashi kije zamu yi mgana da safe..!
Ba musu ta mike ta fice bayan ta share hawayenta tana fita su hamida suka fara Tambayanta Lafiya Mirmishin Daya fi kuka ciwo tayi kafin tace"Bakomai..!
Daga haka ta shige daki kokarin Daidaita kanta take yi domin tayi alkwarin daina bayyana rauninta kan wasu abubuwan..!
Ko washegari kasa ce mata komai tayi mamanmu ta tuna yadda suka kwana Aba bai kalleta ba tasan kwabarta tayi Ruwa da Safe ta Fadama Madina komai ita kuma tace bama zai sabu ba auran nan bazai Daure ba koda ya Tabbata din.!
Amina kuma ko hanne bata fadamata abunda Aba ya fadamata ba,sai dai ta Dauki nauyin mganar acikin ranta tana jin kamar abu ne mai wahala.!
Haka Rayuwar ta cigaba da Tafiya su Zeenatu suna cigaba da Jarabawarsu sun gama Weac sun fara Neco gefe Daya kuma ana cigaba ana cigaba da Shirin Bikinsu wanda Baba mallam yace nan da wani Lokaci za"ayi Auran nasu kamar yadda Tsarin yake..!
*Janafty*
*TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*