Sassauta rik'on yayi, ya sauke ajiyar zuciya, muryarshi a sanyaye yace, “Miyasa kikeson 6oyemin abinda kika Sani? shin bak'ya tausayinane? kullum cikin aiki kwakwalwa ta take, aikin Neman kud'in da zan taimaki kaina da ahalina, aiki akan mak'iyana, ya kike tunani a kaina? yanzu haka ji nake tamkar kwalwar kaina zata tarwatse saboda damuwa da abubuwan da suka sakata matuk'ar nauyi, ta6a kiji yanda zuciyata takoma bugawa a slowly”. ya kamo hannuna ya d'ora a k'irjinsa, saitin zuciyarsa. da gaskiyarsa kad'an-kad'an zuciyarsa ke aiki, ba kamar kowanne bugun zuciya dake tafiya normal ba. Sai naji tausayinsa ya kamani, cikin sanyin murya nima nace,
“yalla6ai kayi hak'uri da abinda zan fad'a maka, inhar ka kawoni gidanka ne domin muyi aiki tare a matsayin Friend bai kamata ace ka gaza yarda daniba akan sirrinka. kasan minene yake saka kwalwarka da zuciyarka wannan nauyin kuwa?”.
Kansa ya girgiza mini.
Na gyara kwanciyata ina kallon p.o.p, “Matsalarka d'ayace baka yarda da kowa ba sai kanka, mu cire Momma da papi, dansu aiyukansu sunkai amusu uzuri, Momma hankalinta akan jiyya yake, dan haka kana k'ara mata damuwa, papi kuma babbane shawara da dabarun manya kawai kake buk'ata daga garesa. Sai kuma Muftahu da Harun nakula suma kakan d'an saki jiki dasu akan wasu abubuwan, to amma fa.........”.
Saitayi shiru bata k'arasaba.
Ya matso jikinta sosai, tare da d'ora hannunsa saman cikinta, murya k'asa-k'asa yace, “Harun da Muftahu amma fa mi? Please ki k'arasa mana”.
Kad'an Na juyo nad'an kallesa, Na d'ora hannuna nima akan nasa daya d'ora akan cikina. Janye fuskata nayi Na koma kallon p.o.p d'in. “kayi hak'uri da abinda nake fad'a, badan ina zarginsu bane zan fad'a d'in, dama zancene Harun da Muftahu kuma kamar bai kamata 100% susan komaiba, dan za'a iya sayensu ko tursasasu suci dunduniyarka. domin koba komai har yanzu bakada tabbas d'in cewar babu hannun wasu a cikin masarautar nan. amma kayi hak'uri idan na shiga hurumin daba nawaba”.
Shiru yay baice komaiba tsawon lokaci, har nayi zaton nayi laifi ko yayi barci, a sanyaye nakuma fad'in “please & please kamin afuwa yalla6ai”.
“is okay”. ‘kawai ya fad'a yana kuma sakani a jikinsa, tareda d'ora ha6arsa saman kaina.
Babu Wanda yasake magana a tsakaninmu, kowa yay shiru yana k'ullawa da kwancewa, har dai barci yafara fisgata.
“Kina ganin su Aiyaan bazasuyi kuka ba idan suka farka sukaga su kad'aine?”.
Naji maganarsa cikin kunnena.
“a'a” na fad'a ina girgiza masa kai, “ko'a gida sukad'ai suke kwana dama”.
“okay”.
Saikuma muka kuma yin shiru, har barci yakuma fara d'aukata yakuma fad'in “kozaki sha Magani ne?”. ‘yay maganar yana ta6a gefen wuyana’.
Kaina Na girgiza masa batareda nace uffanba. shima bai sake cewa komaiba..
Yanda numfashina ke sauka a hankali sai ya fahimci nayi barci, shiko gaba d'aya yakasa nasa barcin, tunanin wani Abu daya ta6a faruwa a baya ya fad'o masa, dukda shi ba yayi imani da hakan baneba.
👇🏻
*_Wata ranar juma'a a India, sai suka tashi da matsananciyar damuwar motsawar ciwon Abie, a time d'in ma sun zata rai zaiyi halinsa, hankalin Galadima ya tashi har ciwonsa shima yakai ga motsawa, amma yak'i yarda doctors su dubashi, yace abarsa kawai gara ya mutu ya huta, hankalinsu momma ya tashi, amma Galadima yak'i sauraren kowa, daga k'arshema saiya sulale daga asibitin ya fice abinsa, haka yayta tafiya rik'e da k'irjinsa saboda azabar ciwon da zuciyarsa ke masa, mutane sai kallonsa sukeyi, shiko baimasan sunayiba, yayi tafiya mai nisan gaske batareda yasaniba. k'arfinsa da kuzarinsa sukai gazawar da bazai iya cigaba da tafiyanba, shine yazube a wajen ya fad'i._*
*_bai tashi farkawa ba sai awani d'aki mai kama dana bunu, ya yunk'ura zai mik'e amma saiya kasa, wani tsoho ba indiye, a cikin indiyawan ma irin masu k'yawunnan sosai, ya dafa kafad'arsa, cikin harshensu yace ma Galadima “koma ka kwanta d'an saurayi, bakada lafiyane”. Galadima yace “kayi hak'uri baba gida zanje nasamu sauk'i, zamana annan bak'aramin tashin hankali bane ga ahalina”. tsohon yay murmushinsu Na manya, yace “zakaje gida d'ana, ni da kainama zan kaika, amma lallai kai acikin al'amuranka akwai abubuwan ban mamaki da al'ajabi, gakuma tsantsar rud'ani, saidai komai yanada lokacinsa, kuma lokaci zai tabbatar maka hakan, albishir d'aya zanmaka, nanda wasu shekaru dabasu Gaza 7 ba mai taimakonka zatazo, kwarai zatazo gareka, ba lallaine ka fahimci abinda nake fad'aba ko yarda dani, Dan Na lura kaid'in musulmine, kuma bad'an wannan k'asarba, amma wannan mai taimakon naka itace zata zama fitilar haska maka hanya kakai ga cinmma burinka, domin taurarinta da naka sunada matuk'ar k'arfi, harma suna gogayya da juna, zaku zama sh........”. Saikuma yayi shiru yana murmushi, ya shafa kan Galadima yana fad'in “tarin Albarka sucigaba da baibaye rayuwarka data zuri'arka”._*
*_daga wannan maganar sai barci mai nauyi ya kwashe Galadima, koda ya farka saiya gansa a asibiti tareda su Momma, yata tambayarsu INA tsohon yake sukace su basu San wani tsohoba, wasu samarine su biyu suka kawoshi asibitin, wai sungansa yafad'i a gefen hanya, zancen tsohon yata damun Galadima a time d'in har yayta bincike kozai gansa amma ko alamun mai kamarsa bai ta6a ganiba, daga hakama saiya cire abin a ransa yacigaba da harkokinsa._*
Ajiyar zuciya ya sauke, tareda kuma rungume Munaya, a kan la66ansa ya furta “ALLAH kaine mafi sani”. daga haka yay shiru tareda lumshe idanunsa, barcine yayta fusgarsa harya samu nasarar sacesa.
Can gabannin asuba yay wani mafarkin daya sakashi farkawa a firgice, har itama Munaya ta farka tana tambayarsa lafiya?.
Kansa ya dafe, da hannu yaymin nuni na bashi ruwa.
Sauka nayi daga gadon dan zazzza6inna ya fara hucewa nima, freight na bud'e na d'akko masa ruwa, na had'o da Kofi, zama nayi kusa dashi a gefen gadon na tsiyaya ruwan a Kofi na mik'a masa. kar6a yayi ya shanye, ya mik'o min kofin, zan kar6a ya girgiza min kai tare da min nuni da in k'ara masa.
Kuma tsiyaya masa nayi, yakai rabi ya d'aga min hannu alamar ya Isa, bayan yakuma shanyewa ya mik'a min kofin yana fad'in “Thanks”.
Kar6ar kofin nayi, ba tareda na tashiba nace “Yalla6ai lafiya kuwa”..
“Mafarki”. ‘yafad'a yana komawa ya kwanta’.
Idanu kawai Na zuba masa, kusan 4minutes ya juyo da kansa ya kalleni, “kizo ki kwanta mana”.
K'aramar ajiyar zuciya kawai Na sauke Na mik'e, Na d'ora ruwan da Kofi a dirowan gefen gadon na koma inda nake na kwanta.
Ganin ya sauya hannun da yay mafarkin kuma yana addu'a sai ban sake cewa komaiba, na kwanta shiru ina sak'e-sak'e a raina mafarkin mi yayi to? da har yasakashi firgita irin haka?. banida mai bani amsa dan haka nayi shiru.
Saiya zamto da asuba na rigashi tashi, harma saida nayi alwala sannan na tadashi, da k'yar ya iya tashi yana dafe kai, binsa nayi da kallo kawai harya shige toilet.
Lokacin daya fito na fara salla, dan haka saiya fice kawai. A mamakinsa saiya iske Aiyaan da Aryaan sun tashi suna alwala, hakan ya Burgesa sosai. Sai kawai ya kama hannunsu suka tafi massalaci.
Bayan an idar da salla bai yarda sun had'u da Sarki ba, ya gudo. Sai dai abinda bai saniba shi Sarki ya gansa, dan yau ya makara salla shima.
Wajen Around 9am nagama gyaran d'aki nayi wanka, saina d'an fito falon domin duba dubawa, natarar sabbin kuyangina suma komai sun gyarashi k'al, harma da mana break fast, banyi yunk'urin bud'ewa ba ma balle tunanin son ci, dukda kuwa natashi da yunwa, to amma Momma ta gargad'eni sosai akan cin abinci wani a masarautar, dan haka na fito daga kitchen d'in kawai.
Tunkan na shigo nake jiyo maganarsu Aryaan, zaune na iske Galadima su Aiyaan na kusa dashi suna bashi labari, anmusu wanka tsaf, sunsha sabbin kaya iri d'aya.
Har yanzu Galadima bayada walwala, na zauna ina gaisheshi, batareda yabar latsa wayarba ya amsa min, su Aiyaan suka dawo kusa dani suna gaisheni, kumatunsu naja ina murmushi, “oh my guys kunsha k'yau, waya muku wanka haka?”..
Atare suka amsa min da fad'in “Uncle ne, kuma ya saka mana tirare yanda kuke mana”.
Murmushi nayi, na saci kallon Galadima da yay biris damu kamar baya d'akin, alhalin sanda na shigo na iske suna hira shidasu 'yan 2.
Sallamar da wata baiwa keta kwad'awa na amsa, sannan na mik'e na fita dannaji minene? A k'ofar falona na isketa, nace, “miya farune?”.
Duk'ewa tayi ta gaisheni, sannan ta mik'omin ledojin hannunta tana sanarmin Sarkin motane yace “na kawo wannan ranki ya dad'e”.
Kar6a nayi, na koma ciki.
Ajiye ledojin nayi a gabansa, “gashi wai inji sarkin mota”.
Idanunsa ya d'ago ya kalleni, yace, “breakfast d'inku ne”.
Tashi yay ya fita yana fad'in na shirya zaije ya dawo mu shiga cikin gida gaida mutane.
Na amsa masa da to.
___________________
Tun a daren jiya wasu bayi sukaga Muftahu, dan haka suka shiga ihu, dandanan sauran bayin dake kusa da wajan suka firfito, manyan bayin cikinsu ne suka kai maganar cikin gida, shine akasakasu d'aukar Muftahu su shiga dashi.
Lamarin yabama kowa mamaki, babu wani mummunan rauni a jikinsa, inbanda d'an jini dake gefen bakinsa, saidai sun sami kwanciyar hankali ganin yana numfashi.
Maganar dawowar Muftahu bata baje masarautar ba sai washe gari.
Bayan Galadima ya fito daga sashensa zaije fada yaji anata k'ananun magana akan dawowar Muftahu, saidai kuma miskilancinsa bai barsa ya tambayi kowaba ya nufi Fada.
Ya isa mai martaba baikai ga isowa ba, dan haka suka gaisa da 'yan majilissar Sarki dake fadar, sannan ya nemi mazauninsa dake gefen Sarki Na dama ya zauna.
Zamansa baifi da mintuna 10 ba Mai martaba ya iso, gaba d'aya suka mik'e tsaye, dogaran Sarki sunata kirari da fad'in gyara kintsi da k'yau, duksun baza riguna ba'a gani mai martaba, basu bar kowa ya gansa ba har saida ya zauna a kujerarsa.
Baya suka mammatsa mai martaba ya bayyana, atare su Galadima suka rissinar dakai alamun girmamawa, sannan kowa yafito tsakkiyar fada ya mik'a gaisuwarsa ga Sarki, yayinda fadawa ke faman amsawa, tsakanin Sarki dasu kuwa shine d'aga hannu.
Mai martaba yayi mamakin ganin Galadima yau azaman fada, bawai baya zaman bane, sai dai yakan dad'e bai zaunaba, an masa uzurine kasancewar ansan ba zaune yake dindin dinba, kuma idan yazo akwai harkokinsa Na kasuwanci da yakeyi, sai dai dolene yakan shigo yayi gaisuwa.
Bayan fada ta nutsu aka fara fadanci.
K'a idane fadar gagara badau takanyi fadancine a sati sau hud'u kawai, litinin ba'a zaman fada, domin ranace da ake tunawa da abinda ya faru ga tsohon Sarki mahaifin Galadima, talata, laraba, alhamis, asabar, sune ranakun da ake fadanci, ranar juma'a ma ba'ayi saboda muhimmancin ranar ga al'ummar musulmi. A wad'annan ranakun akanyi zamanne daga 10am zuwa 12:30pm, da an tafi sallar zuhur ba'a dawowa, idan kaga anwuce wannan time d'in a fada to tabbas akwai abinda ya farune.
A wannan zaman fadancine maganar dawowar Muftahu ta fito, sun tattauna akai harda shirin kuma d'aukar matakai Na tsaro a masarautar.
Bayan anyi sallar zuhur ne Sarki ya shige gida, sauran fadawa ma kowa ya kama gabansa, Galadima bai shiga gidaba saiya nufi sashen su Muftahu domin dubashi.
Bayan an masa iso ya shiga, ya iske mahaifiyar Muftahu da 'yan uwansa zagaye dashi, har yanzu kuma yana cikin yanayin barci.
Ya jajanta musu, Yakuma kwantarma da mamansu Muftahu hankali, kusan mintunsa talatin ya fito ya koma sashensa.
Ya iske su Aiyaan kawai a falon Munaya suna kallo, suka taso da gudunsu suka rungumesa, fuskarsa cikeda fara'a ya tarbesu, ya tambayesu ina Auntynsu?.
A tare suka bashi amsa, “Uncle tana d'aki ta kwanta kuma tace karmu tadata, inba hakaba jiki magayi”.
Murmushi yayi yaja kumatunsu, “kuce zatayi zana kenan idan aka tada ita?”.
Nanma atare suka amsa da “eh Uncle, kasanfa Aunty Munaya tacika fad'a, gidanmu tsoron masifarta akeyi, amma ita Aunty Munubiya babu ruwanta”.
Galadima yace, “da gaske?”.
“ALLAH kuwa Uncle, idanfa mukayi rashinji ita ke zanemu ba innarmu ba, kuma dukanta da zafi, gashi taita hararmu da katun-k'atun idanunta nan”.
Sosai abin yabama galadima dariya, dan haka ya dara sosai abinsa yana fad'in, “kubari tajiku to, idan ta zaneku babu ruwana nidai, kunga bara naje naga kota tashi, karfa Ku shigo, dan zata iya zaneku”.
Sukace “ai bazamu shigoba Uncle”.
Yace, “good boys”.
Da sallama ya shigo, amma saiya isketa baje a gado tana shak'ar barcinta, yad'an murmusa kafin ya k'arasa ya zauna a bakin gadon saitin fuskarta, yatsunsa biyu yasaka a gefen wuyanta dan yasan da wahala wannan barcin ya kasance na lafiya, aikam jikinta ringim yake da zazza6i, tausayinta ya kamashi, lallai uwa dabance acikin al'umma, Ashe haka sukeshan wala, tundaga d'aukar cikinma zuwa rainonsa, akoma rainon yaro, daganan tarbiyarsa, lallai masu raina mata ko kallonsu masu k'arancin tunani sune masu k'arancin tunanin ai, ya d'an lumshe idanunsa yana cije lips, ganin ta dunk'ule a waje d'aya saiya ja bargo ya lullu6a mata, harya mik'e ya koma ya zauna, risinowa yay kanta a hankali ya mannama goshinta kiss, sannan yamik'e ya fice.
Koda ya dawo saiya wuce d'akinsa, yabar su Aiyaan suna kallonsu.
Kayan jikinsa ya cire ya kwanta shima, dan yana buk'atar hutawa kona 2hours ne, kwanciyarsa kuwa babu dad'ewa barci ya saceshi.
Kiran sallar la'asarne ya tashesu kusan lokaci d'aya, Galadima yatashi da k'yar, a mamakinsa sai yaga Aiyaan da Aryaan kwance a gefensa suma suna barci, murmushi kawai yayi yasako, saida ya watsa ruwa sannan yay shirin tafiya massalaci cikin k'ananun kaya.
Harzai fita saiya dawo yashiga wajen Munaya. tana tsaye gaban wardrobe tana neman kaya, da alama wanka tayi, dan daga ita sai towel.
Banji sallamarsa ba, saboda shi idan zaiyi magana bayason bud'e baki, ganin batajishiba saiyayi gyaran murya, a tsorace na waigoshi, ganin shine nai saurin saka kayan dana d'akko ina kare k'irjinna da tura baki, bakinsa ya d'an ta6e, sai kuma ya shiga takowa inda nake, duk takun da yayi sai gabanna ya fad'i, na waiga kozan samu nabar wajen ko abinda zan suturta jikinta sosai, amma sainaga babu a kusa, kuma ina jikin wardrobe d'inne sosai ai. ban gama yanke shawara ba ya k'araso daf da ni, kuma matsawa nayi na matse jikinna sosai a drowa d'in, shikuma yawani had'e gabas da yamma, wannan ne yakuma sakamin tsoronsa a raina, na zata kowata tsiyarce ta kawoshi.
Hannu yasaka ya d'ago da ha6arta muka kalli juna, ya tsareni da idanu yanda nakasa janye nawa cikin nashin, munkai kusan 2minutes a haka, kafin yakumamatsoni sosai, ya kai fuskarsa gab da tawa tamkar zai had'e bakinmu, dan haka saina lumshe idanu, murmushi yayi ya hura mata iska akan idanun, ta rumtse idon sosai, ya d'an ja baya yana ta6e baki, kafin yasaka hannu ya cire nata dataketa faman kare k'irji da kayanta, still ya kuma matsawar saitin kunnenta yana fad'in “wane darene jemage bai ganiba yalla6iya”. ‘ya k'are maganar da shafa kirjina ya fice abinsa.
Kad'an yarage namasa ihu wlhy, aiko yana fita na durk'ushe a wajen ina sauke numfashi, sometimes nakan rasa yazan fassara Galadima da ayyukansa.
Da k'yar Na iya tashi nayi sallar nakoma kan gado Na kwanta.
Galadima kam daya fita dariya ce taita cinsa, ya kula Munaya akwai tsoro, kuma haryanzu a tsorace take dashi, cikinnan ne kawai kanci galaba akanta yake samunta cikin sauk'i, ya girgiza kansa kawai yana murmushi.
Bayan ya dawo massalaci d'akin nata ya dawo, dan yanason suje su gaida jama'ar gidan, maybe gobe suje masarautar papi ma.
A kwance ya iskeni, nak'i kallonsa, jingina yay da mirror yana fad'in “yaya jikin naki?”.
Ban kalleshinba nace, “da sauk'i”.
“ALLAH ya k'ara sauki, idan zaki iya tashi ki shirya muje cikin gida, kafin waccan tsohuwar tafarama mutane surutu”.
“to” nafad'a ina mik'ewa, Na sakko a gadon, harna nufi wardrobe zan d'auki alk'yabba saina tsaya, batareda Na kalleshi ba nace, “toka fita Na shirya”.
Hard'e hannayensa yayi a k'irji yana fad'in “ashe bazaki shirya d'inba, dan bazanje ko inaba”.
“karkaje d'in, ai akwai bayi” nayi maganar a zuciyata.
Kayan Na d'auka na shiga toilet, shikuma ya ta6e baki.
Babu dad'ewa na fito tsaf, nayi k'yau, nazo ta gefensa na d'auki turare nasaka kad'an sannan na kallesa nace, “na shirya”.
Baice komaiba ya nunamin hanya, gaba nayi yana bina a baya muka fice.
Kasancewar tazarar dake d'an tsakaninmu da sassan nasu muka shiga mota, dan banajin dad'in jikinna, bama zan iya tafiyarba.
6angaren Abba hayatudden muka fara zuwa, daga nan sai sashen matan mai martaba, soyayyar da uwargidansa ke nunamin yasani k'ara k'aunarta, sai addu'a take zabgamin akan ALLAH ya saukeni lafiya. Galadima kad'ai ke amsawa, amma ni saidai a zuciya kawai. daga nan muka d'an shishshiga wasu sassa, 6angaren mama fulani shine k'arshen zuwanmu.
Kunsan dai mutuniyar taku akan mulki, tana kishingid'e kuyanginta nata bauta, mai matsa kafa daban mai firfita daban, ga masu bata labarai, tufa takeci cikeda k'asaita da izza.
Amintacciyar baiwarta data mana iso tana gaba muna biye, mama Fulani ta d'agama kuyanginta hannu alamar subata waje.
Rige-rigen ficewa suka, yayinda mukuma muka k'arasa gareta, idonta a kammu ko k'yaftawa batayi, nidai tsarin ALLAH na nema daga sharrinta, ina dalili wannan kallon k'urilla haka?.
Galadima yace, “barka da yammaci”. nima saurin fad'a nayi.
A yatsine ta amsa mana, ta d'ora da fad'in “Saraki kayi wuyar gani?”.
Galadima ya murmusa yana kallona, “Ranki ya dad'e kinsan mai amarya ai yafi dubu wahalar gani dama”.
“Humm” kawai tace batareda ta amsaba.
Sai zuwa can tace “nafa manta, ina tayaku murnar samun k'aruwa”.
“mun gode ranki ya dad'e, amma taki murnar itace tazo a latti, gashi kuma idonkine yafara hango abin cikin kwan tun a india”.
Mama Fulani ta tsatstsare Galadima da idanu, shikuma yay salute nata yana murmushi.
Jitai kamar zata makesa dan haushi.
Ya lura da haushin da taji, dan haka ya kama hannuna muka mik'e tsaye yana fad'in, “bara mukoma inda muka fito ranki ya dad'e, a huta lafiya”.
Bai jira amsartaba mukayi fitowarmu.
Da kallo kawai ta bimu, takasa koda motsawa, tarasa miyyasa yau Galadima da matarsa suka mata wani mugun kwarjini? batada mai bata amsar tambayar tata...
Yini guda yau Galadima a gida yayishi, baije ko inaba, sai da daddare Nuren yazo sukayi magana, daga nan yace ya nema mana tickets d'in zuwa masarautarsu.
Washe gari muka tashi da shirin tafiya masarautar su papi, mukad'ai muka tafi, babu kuyangi babu dogarai, dagani sai shi dasu Aiyaan, sai Nuren..................✍🏼
*_ALLAH ka gafartama mahaifanmu_*😭🙏🏻
*_typing📲_*
💡 *_HASKE WRITERS. ASSO....._*
*_♦RAINA KAMA.....!!♦_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
~Book 2~ 👉🏻1⃣5⃣
...................Abin yabani mamaki ganin yanda akazo tarbarmu, yo saikace wani Sarki, hakan yakuma tabbatarmin da Galadima d'an gatane a wannan masarautar.
A masarautar ma gungun mutane muka iske wai masu tarbarmu, ni dukma sai kunya ta kamani wlhy, musamman da Mom ta rungumeni tana fad'in “ga maman twins d'inmu ga Maman twins d'inmu”.
Galadima dai murmushi yayi, Nuren kam dariya ya kemin.
Lallai naga tsantsar soyayya a wannan masarauta, sai nan nan ake dani kamar wata sarauniya, duk wani Motsina Inno tace minakeso? hakama mom.
Aiyaan da Aryaan kam ai suna tare da Galadima, duk inda yasaka k'afa suna biye.
Nikam dai a kwana biyun da mukayi babu abinda zance da wad'annan bayin ALLAH sai godiya, naga karamci naga hallaci sosai, hakama k'annena.
Sosai Galadima yasamu tattaunawa da papi a tsakaninnan, sunyi maganganu masu muhimmancin gaske. Musamman akan ciwon Abie da cikin jikin Munaya, harma da Abbanta. sosai kuma Galadima yakuma samun haske akan lamuran.
Kwannamu biyu muka dawo cikeda kewarsu, tare da tarin alkairi ga wad'annan mutane masu tsayawa a rai.
Mun dawo da kwana 1 yaran gidanmu na ma'auri suka kawomin ziyara.
Aunty khaleesa, aunty Hauwa'u, aunty Ramlah, aunty Raheenat, matansu ya hameed, Fiddausi, Siyama, Zarah, Safara'u, Fauziyya, Haleematu,Munubiya, Ayusher, Feena. Wayyo dad'i wlhy saika d'auka biki akeyi, rasa inda zansaka kaina nayi saboda dad'i, shi kansa Galadima ya fahimci ina tare da tsantsar farinciki, nima dagewa nayi namusu hidima iya hidima, dan hardani aka shiga kitchen.
Sukam duksun rikice da mamaki, dama haka gidan sarautar yake, dan saidama Galadima yaje da kansa ya shigo dasu. Su Aiyaan anata murna anga 'yan gida.
Ranar dai anan suka yini zir, dazasu tafi Galadima yay muzu alkairi mai yawa tareda godiya ta musamman. Sunji dad'i sosai kuma sunyi farinciki, sunata masa godiya nima ina tayasu.
Da zasu tafi jinai tamkar na rik'esu, aiko harda 'yan kwallana, sauk'inama kawai su Aryaan tare dani.
Kowaccensu tatafi da labarin data gumtsawa uwarta a bayan fage, dansu Zarah dai sun Shiga taitayinsu, sun gane ruwa ba sa'an kwando bane, nanfa hassada da bak'inciki tamkar ta babbake zukatansu, mamansu Yaa hameed hardama Abba ALLAH ya Isa tana sharar kwalla, wai yasan da gidan sarautar amma ya yarda Zarah ta auri d'an sanata, ga aunty khaleesa nanma kullum cikin matsala da miji, dan kishiyarta akwai kissa.
*_ALLAH yarabamu da ciwon hassada fans_*😏
Sati d'aya da zuwansu muka koma India, saboda Company suna Neman Galadima da gaggawa. harda innaro iya bala'i muka tafi🤣.
A jirgi taita kudundune fuska a gyale wai batason ganin tashin jirgi, duk tsare gidan Galadima saida yayi dariya, Aryaan da Aryaan kam sukaita tsokanarta. Yau babu masifarnan dan bata kulasuba, saima Galadima ne ya hanasu. nikam banza na musu dan tawama ta isheni nikam. Jikina sai ciwo yakeyi, ga cikina na mun ciwo shima kad'an-kad'an.
Khumar da Sauban da Samha sukazo d'aukarmu, muka rungume juna da samha muna farinciki.
Daga nan muka wuce gida, yaukam munashan k'auyancin innaro, ni harma tabani haushi, komai tagani saita tambaya, Kodai su Aiyaan basa abinda takeyi.
Mun iske jakadiyane kawai sai bayi, Su Momma da innarmu suna asibiti, Mudai sama muka haye ni da shi, 'yan biyu kuwa suna wajen Samha ta kasa ta tsare, innaro kuma aka barta da jakadiya.
Ko ina tsaf yasha gyara tamkar mai d'akin na nan, Muna shiga kwanciya nayi bisa kujera, naja bargon saman gadon na lullu6e, kallona yayi da mamaki “k lafiyarki kuwa?”.
“zazza6i”. kawai nace masa na k'udundune har kaina.
Zama kawai yayi ya zubamin idanu cike da tausayi, ganin zaman bazai masaba yatashi ya shiga toilet, saida ya gama dukkan uzirinsa sannan nima ya had'amin ruwan wanka, tadani yayi, na tashi da k'yar tamkar zan masa kuka.
Yace, “tashi kije kiyi wanka kozakiji dad'i”.
Baki na tura masa gaba.
“idan bazaki iyaba tashi muje na miki”. ‘yay maganar cike da basarwa’.
Harara na zuba masa sannan na mik'e na nufi bayin. shikuma ya ta6e baki yana wani mikilin Murmushi.
Abincima sai nan ya saka aka kawomin, dan nakasa sauka.
Innaro sai catake wai nacika langyare, dan naga yana shagwa6anine shiyyasa nake ta6ara, ai badaga kaina aka fara cikiba.
Galadima dai murmushi kawai yayi danshi lamarin innaro abin dariya ya d'aukesa, tana buk'atar uzuri.
Bayan nasamu naci abinci daya bani nasha magani, harzan kwanta a sofa yace na koma saman gadon, kamar zanyi magana saina fasa, na tashi kawai na koma.
Yana kammala duk abinda ya dace yafice asibiti domin duba Abie da Abba.
Yaji dad'in yanda yaga canji sosai a jikin nasu su duka, dan raunuka da yawa sun warke a jikin Abba, da bakinshi ma ya amsa masa gaisuwa yana masa godiya, inna da baba k'arami sunata saka masa albarka. maganar da abie ya fara kuwa rungumesa yayi yana kuka Abie nayi, hakama su Momma, a hankali Abie yace “ina d'iyata Muh'd”.
Murmushi Galadima yayi, yace, “zuwa anjima zaka ganta Abie, yanzu na barta tana barci zazza6i ya rufeta”.
Momma da Aunty Mimi sukace “ALLAH dai ya sauketa lafiya to”.
Babu kunya Galadima ya amsa da amin.
Aunty Mimi dake kusan dashi ta doki gefen hannunsa, “kai mara kunya, shine zaka amsa”.
Hannu ya saka ya rufe bakinsa yana fad'in “ni jikan Abdul'fatah da Abubakar”.
Dak'uwa Momma tamasa tana kai masa duka, ya matsa da sauri yana dariya.
Abie ma murmushi yakeyi, lallai yau yakuma ganin canji tare da d'ansa sanyin idaniyarsa, sukam yaushe rabon da suga irin wannan nutsuwar tare dashi haka, lallai dolene su godema ALLAH da shigowar Munaya cikin rayuwarsa, basu da wani abinda zasu iya biyanta har abadan, saidai suyita mata fatan alkairi da k'yautata rayuwarta.
Saida na tashi sannan muka tafi asibitin muma, wajen su momma muka fara zuwa, Momma da aunty Mimi sukazo suka rungumeni tamkar zasu had'iyeni dan dad'i, nikam duk kunyarsu ta gallabeni, sai 6oye fuska nakeyi, koda zan gaida Abie ban yarda na kalleshiba.
Sauban da Samha sai dariya sukemin.
Duk bak'in halin innaro saida tayi kuka ganin halinda Abie yake ciki, taita kwarara masa addu'a kuwa.
Su momma sunji dad'i, kuma sunata girmamata.
Samha sai dama-dama takeyi dasu Aiyaan, motsi kad'an tace, “ALLAH yasa Aunty gimbiya muma ta Haifa mana irinku”. Su Momma sunata amsa mata da amin. Nidai kaina na k'asa saboda kunya, ina lura da Galadima kuwa duk sanda tafad'a saiya murmusa kuma bakinsa ya motsa alamar yana amsawa da amin.
Sosai naji dad'in ganin jikin Abbanmu shima, dan har magana mukayi, jikinsa yayi k'yau sosai, karayunne ma kawai suka rage nakula, amma k'ananun ciwukan duksun warke, to wajene dayake samun kulawa ta musamman. Munaya harda rungume inna, itako ta tureta tana hararta, su Aiyaan kam duk sun d'are bisa cinyarta suna d'okin ganinta da kewarta. Itama tayi kewarsu over, tsakanin uwa da d'a kenan (iyaye mata ga naku fa🥰🥰🥰❤👍🏻).
Haka muka dawo gida ina farinciki, koba komai nasamu nutsuwa mai yawa a yau d'innan, aiko ban yarda mun kwantaba saida nayi nafilfili domin mik'a godiya ta ga ubangijin sammai sannan na kwanta.
Galadima kuwa muna shigowa d'akin sirrinsa ya shiga yanata aiki.
___________________________
Hankalin Minister ya kai k'ololuwar tashi shida families nasa akan 6atan 'yarsa, farhat, duk wata hanya daya kamata subi sunbita amma babu koda labarin Wanda ya ganta, tun lamarin nabasu mamaki harya koma basu tsoro, ga wani text massage da akama minister d'in d'in kwana 10 daya wuce.
_Idan kana buk'atar 'yarka kana iya mik'a wuya._
Wannan massage ya tsaya masa a rai, har police sun kar6a amma sun gaza gane komai gameda massage d'in ko wannada ya turo shi.
Mahaifiyar Farhat harda kwanciya asibiti, dan ita kad'aice mace a gidan, dan haka suke masifar son yarinyar da mata gata, dudu shekarunta 16 ne kawai, tana wata private boarding school ne a abuja. a binciken da Galadima yakeyine ya gano hakan, kuma yayta bibiyar yarinyar har saida yasamu nasarar saka Nuren ya kwamuso masa ita.
___________________________
Tunda muka dawo India bani da lafiya, kullum innaro cikin min gorin ni ragguwace take, bana wani kulata dan tawa ta isheni, koma uwarmi zata fad'a ta shekara fad'i, bazan yarda mu Raba hali a gidan surukai naba, nakan bar lamarinta a wasan jika da kaka agabansu, amma ni nasan badan hakan takeyimin ba, ita kanta innarmu bata kulata ko kad'an, idan tanayi shiru take mata ma.
Kulawa kam bazanyi butulciba ina samu wajen Galadima dasu Momma, musamman ma jakadiya da Aunty Mimi. Saukina ma cikin bamai tsurfa baneba, komai inaci hankali kwance, kuma ban ta6a amaiba ko wani zubda yawu, saidai zazza6i da ciwon jiki.
Yaudai dole Akash yazo har gida ya sakamin k'arin ruwa, kozan sami sasaauci.
Yini guda yau a gida Galadima yayisa, duk wani motsina akan idonsane.
**************************
*_5 months ago_*🙆🏻🙄😆
A kwana atashi babu wahala wajen ubangiji, rayuwa ta shud'a, kwanaki nata sauri, a wanni da mintuna kam ai ba'a cewa komai, abubuwa masu yawan gaske sun faru a watanni biyar d'innan, ciki harda warkewar Abbanmu sarai, tamkarma baiyiba, saidai k'afarsa da yakan d'an tizgid'a saboda matsala data samu, shima saika k'uramasa I done zaka fahimci hakan.
Innaro dai dasu Aiyaan tuni suka koma saboda makaranta, sai dai duk Hutu Galadima yakansa azo dasu Aiyaan d'in, hakama Munubiya da yaa marwan sunzo sun mana sati biyu sukaga jikin Abba da Abie.
A wattani biyar d'inna Galadima yaje Nigeria kusan sau hud'u, dukda bai ta6a fad'amin wani abuba ina samun bayanai ga Saleem da sarkin Mota. har yanzu kuma Farhan d'iyar minister tana hannunsa, hakama Malam Saminu driver Alhaji Balala.
Yaran gidanmu masu cikkuna duksun haihu, su Siyama an zama iyaye, naji haushin rashin halartar taron suna ko d'aya, dan dana fad'ama Galadima inason zuwa banza yamin, naci kukana kuwa na hak'ura, sai turomin abubuwan da akayi sukaitayi ina gani.
Cikina ya fito kwarai da gaske, dan yanzu yana cikin wattani 7 da wasi kwanaki, yamin d'as yakuma sakani k'iba, duk kamannina sun canja, kumatuna sunyi manya, dukdai wanda ya ganni zaisan na canja, hakama Munubiya, idan ta turomin hotonta nata dariya kenan.
Tsakanina da Galadima kuwa har yanzu muna a yanda kowa ya sammu, canji d'aya zance ansamu shine nuna yawan tausayinsa akan cikin jikina, dan dukkan wani motsina cikin nuna damuwarsa yake. Idan yana wajen aiki kam yakan kirani sau uku sau hud'u dan yaji lafiyata kawai.
A 6angaren iyayensa da danginsa kam banida abin fad'a sai godiyar ALLAH, dan tamkar a kainane aka fara ciki haka suke nunamin kulawa.
Hakan nama Innarmu da Abba dad'i, hankalinsu na kuma kwanciya sosai akan aurenmu. baba k'arami yakanyi wata d'aya ya tafi Dady kuma yazo, haka suka dingayi har ALLAH yabama Abba lafiya.
Jikin Abie ma said dai muyitama ALLAH godiya, dan bayan magana an kuma samun cigaba 6angaren motsa hannunsa, yanzu kuma maganarsa takan d'an fito yanda akeji, saidai duk wannan cigaban da ake samu babu Wanda yasan dashi, har mai martaba k'aninsa, kaf masarautar gagara badau da dukkan wani makusanci bai San komaiba a kai, dan papi yahana fidda maganar, ko zuwa akai dubashi yakan komane tamkar yanda ya saba kamar da, daga mama Fulani har mai martaba sunzo kusan sau uku dubashi, hakama Muftahu da Harun, 'ya'yan Sarki ma dama suna k'ok'arinzuwa lokaci-lokaci suma. Hakama Hayatuddin Autan mama Fulani. amma babu Wanda aka bama damar sanin wani sirri akan jikin Abie d'in. dagamu sai mu kawai muka Sani.
Dukda fama danake da kaina haka na dage muka cigaba da addu'oin nan, zuwan innarmu ma yakuma sakamu ho66asa saboda taimakon da take bamu, sannan muka raba addu'oin ga wasu musulmai malamai dake nan suma suka cigaba da tayamu, aka cigaba da bama Abie yanasha da wanka, doctors d'in sunyi surutunsu harsun gaji sun barmu, dan munk'i fasa masa amfani dasu, tunda muna ganin haske a lamarin sosai.
A wata ranar talatar da su Abba suke shirin tafiya k'arshen satinne ina zaune a falo ni kad'ai, dan Galadima ya fita aiki tun safe, zafine ya isheni na dawo falon na k'ure AC, dan Galadima ya saka ma na bedroom d'in key saboda k'urewa da nakeyi, gashi inata fama da mura, shi kansa abin cikina ance tana Neman shafarsa. nikam bana iya hak'uri da Abu mai sanyi konasha ko AC.
Sosai na baje ina kwasar dad'ina, sai faman lumshe idanu nake a cikin kujera, gama wayarmu kenan da Munubiya itama tana bani labarin halin son Abu mai sanyin datake a ciki, kullum Yaa marwan fad'a shida mama Rabi'a amma bata d'aga k'afa, data faki ido saita sha, Ayusher da dole ta dawo gidan tayata wasu abubuwan saita gani ta sanarma Yaa marwan, shikuma yay ta jarabar masifa, amma hakan bazai hana gobe tagani ta shaba........
Jinai kawai iskar dake ratsani ta daina shigata, na bud'e ido sai naga Galadima tsaye jikin k'arfen bene daya shigo ta falon ya hard'e hannayensa a k'irji ya zubamin ido ransa a 6ace, hannunsa rik'e da remote d'in ACn.
Tsorone ya kama ni, na tashi zaune ina wani marmar da idanu, da hura kumatu danaketa yi, takowa yayi inda nake, idonsa tamkar zai fad'o dan hararata “k kin rainani ko? bazan hanaki Abu sau d'aya ki daina ba, ki duba muran dake damunki tun cikinnan nada wata 3, shin ke bazaki tausayama kanki baneba?”.
Shiru nayi bance masa Uffanba, sai faman kumbura baki dai nake yi.
“kinsan ALLAH idan baki maida wannan bakinba na kamashi saiyayi jini”.
Da Sauri na maida bakina, dan ban manta muguntar da yaminba kwana biyu daya wuce, ba k'aramin morata yakeba yanzu, saboda ALLAH yabani ciki mai sakani yawan buk'ata, sai komai ya lafa nayita masa kuka, shikam ya shareni saboda shegen miskilanci da k'asaita, idan na ishesa yace zai makeni, aibashi yace na kawo kaina ba, dan haka nabar cika masa kunne da ihu, anjima ma nazo yi zaiyi tunda ba fyad'e yaminba ninake kawo kaina.
Sometimes nakanji haushin furucinnan nasa, nakuma yi alk'awarin nisantarsa, amma bana iyawa, kona d'auki alwashin saina karya, da yazo yara6u jikina nake mik'a wuya, mugun tunda ya gano lagona saiya dunga bina ta wannan hanyar, duk sanda yaji buk'atata yasan yanda zaiyi ya ra6u da jikina harta kai ga wani abinda nikuma zan mik'a wuya batareda na saniba, saidaga baya nake gane kuskurena.
Ganin namasa banza nak'i tankawa saiya shige bedroom yana tsaki, komawa nayi na kwanta ina share hawaye. ga zafi ya fara addabata.
Kusan mintuna 19 sannan ya fito, ya canja kayansa zuwa k'ananu, da Alama wanka ma yayi, k'in kallon inda yake nayi harya samu kujera ya zauna, remote ya d'auka ya kunna TV.
Haka mukaita zama tamkar wasu kurame, kusan 30minutes, kiran da Nuren yamasane yasakashi d'agawa, bansan miyake fad'a masaba naga dai ya mik'e ya shiga d'akin sirrinsa.
Na dad'e ina kallon k'ofar, zuwa can nima na yanke shawarar binsa kawai.
Doguwar rigace yellow a jikina, batada hannu, sannan bata kaimin k'asa ba, kad'an ta wuce guywata👗, banason kaya masu nauyi saboda jin zafi, sai silifas d'in k'afata jaa mai taushi. cikinan ya kaimin ko ina, jinake kamar na jawo haihuwar na juyeshi na huta.
Ciki-ciki nayi sallama, bai jiniba, hankalinsa nakan Computers d'in d'akin dayake k'ok'arin dai-daitawa, duksun kawo wuta, har k'aton glass d'in dake jikin bango guda na d'akin, ban ta6a d'aukar shima Computer baceba sai yau, dukna d'auka saboda ado aka sakashi a wajen.
Sallamar na k'ara yi, ya juyo yana kallona, idonsa na cikin medical glasses mai haske, dan har kwayoyin idanunsa ina hangowa.
Kamar zai shareni saikuma ya amsa mini, juyawa yayi yacigaba da abinda yakeyi, mikuma yagani saiya juyo, ya jawo kujera ya gyaramin, yay min alamar da ido na zauna.
Babu musu na zauna, ya d'auki remote ya rage gudun AC d'in d'akin, sannan ya juya ga abinda yakeyi.
Yanda yake sarrafa Computers d'in saiya tafi da imanina, kai guy d'innan yasan Computer over.
Bansan lokacinda bakina ya su6uce nace, “yalla6ai ALLAH ya baka”.
Juyowa yayi yana kallona da mamakin furucina, ya saka pen d'in hannunsa a baki yana wasa da shi, kafin ya shiga takowa gareni, k'asa nayi da idanuna nabar kallonsa, yaja kujera ya zauna kusa dani, idonsa a kan cikina, ban Ankara ba naji hannun nasa a saman cikin, idanu Na d'ago Na kallesa, ya d'agamin gira d'aya yana fad'in “ALLAH ya bani k'yautar magaji?”.
Murmusawa nayi ina girgiza masa kai, “niba haka nake nufiba fa”.
“mikike nufi to?”. ‘yay maganar yana janye hannunsa daga cikin nawa’.
Fuska nad'an ya mutse, cikin salon yanga nace, “ina nufin ALLAH yabaka nasibin sarrafa Computer's ”.
Yanda nayi maganar cikin salo saiya sakashi murmusawa yana ta6e baki, “toni miye namin yanga yalla6iya? saikace kina tare da masoyinki?”.
Haushi ya kamani Na dalla masa harara.
Bai kulaniba ya mik'e yana fad'in, “masu cikifa saida uzuri”.
Harna yunk'ura zan mik'e yace, “oh haushi kikaji? to sorry zauna kiga wani abu”.
Komawa nayi Na zauna INA k'unk'uni.
Hotunane da yawa ya nunomin daga cikin Computer, ya danna hoton farko ya fito sosai. Batareda ya kalleni ba yace,
“wannan sunansa *Kabiru Ibrahim*, nasanshi shekaru kusan 9 da suka shige a dalilin neman bayanan sirrina tacikin Computer, nabashi dama yashiga sosai saboda a time d'in yaci k'arfina, inada yak'inin wanine yabashi wani yanki sirri daga abinda nake da shi, ganin ya zuk'i bayanai 90 a cikin 100, saina tura masa goman gaba d'aya, saida ya zamana 99 duk sun shige ga Computers d'insa sannan Na nuna masa banbancina da shi, Na lalata abinda yake da shi da Wanda ya samu agareni, tundaga wannan ranar kuma nafara bibiyar rayuwarsa. Abin mamaki saina gano yanada Ubangida, shine wannan, *Timothy yoha*, dukkan abinda ya aikata agareni Umarnin uban gidansane Timothy, Na maida akalar tunanina ga Timo, saina iske shima aiki yakema wani, ba kowa bane face tsohon shugaban k'asarmu *Labaran Ahmad kachia*. shine wannan, nasan kuma k'ila kisansa dukda dai lokacin dayayi shugabanci bana tunanin an haifeki ma gaskiya, ta silar *Former p... Labaran Ahmad Kachia* nasamu wani kundin bayanai akan tsantsar abotar dake tsakaninsu su a k'alla 15, babu maijin sirrinsu saboda Kansu a matuk'ar had'e yake, ALLAH yayima 4 daga cikinsu rasuwa shekarun baya kad'an, saisu 11 suka rage”.
Ya kumayin wasu 'yan danne-danne nidai duk ina kallonsa da mamaki, hotunan mutane 15 suka bayyana, sai dai an lik'e fuskar mutum 4 alamun wad'anda suka mutu kenan.
Gaban frigate d'in d'akin yaje ya had'a Coffee a mug, sannan ya tako zuwa gareni ya mik'amin, kaina Na girgiza masa alamar a'a, ya d'aga kafad'a sannan ya juya zuwaga Computers d'insa.
“wannan mutane hud'un sune jiga-jigan wannan abota, d'aya ya rasu a cikinsu saura uku, *Josaya Bamma* shine mataimakin *Alhaji Lawan tanderu*, bayan mutuwar tanderu shugabancin wannan abota ya dawo hannunsa, dukkan wani shigi da fici na man fetur dake faruwa a Nigeria josaya Bamma yasanta, dan sune masu yinsa, yanda ake fita da mai a k'asar da yanda suka mallaki rijiyoyin mai ba bisa k'a ida ba, gwamnati kuma batada damar magana domin sune masu fad'a aji, sune tsoffin shugabanni da suka San dukkan sirrin k'asar, sai *Bana baba gana*, dukkan wasu magunguna dake shiga Nigeria saida saka hannunsu, akwai wad'anda batareda k'a idaba suke kaita shi da *Alhaji balala* da *William Solomon*, domin manyan likitocine masana sosai, *Hajia A'i Barnawa*, babbar d'iya ga tsohon soja *Garba mai dala sokoto*, tashiga wannan group d'in sanadin k'awarta *Victoria*, dukkan wani cin zarafi mata ko cin dunduniya suke saka ido, kullum suna ik'irarin sune masu Kare hak'in mata a zahiri, amma a bad'ini ba aikin da sukeba kenan, suna aikin gyara aljihunansu ne. wannan shine *Mansur Habibu Abu*, wannan kuma *Abdul-Naseer Nafi'u*, da *Miracle Asun*, wad'annan dukkansu manyan 'yan kasuwa ne, amma a bayyane, amma a 6oye su sukasan tsiyatakun dasuke shiryawa a k'ark'ashin k'asa *Sagir sulaiman Sulaiman* minister mai mulki a yanzu, sai wannan da wannan duk sun mutu banida matsala a yanzu tsakanina dasu, Munaya inason sanin alak'arsu da Mahaifina, wad'annan mutanen, domin sune mahaifina yay zama dasu ana gobe wannan ciwon zai sameshi, a daren ranar kuma Abie yashiga wajen mama Fulani domin gaisheta, jakadiya data masa rakkiya ta tabbatarmin da lallai yafito ransa a 6ace daga wajenta. Sannan a wannan ranar matarsa ta uku ce ta kawana a turakarsa, alhalin kuma kwannan matarsa ta biyuce, amma saboda kud'in data bama jakadiya da dad'in bakinta saita kaita turakar Abie a wannan daren, takuma sanarma matarsa ta biyu cewa takawa bashida lafiya yana fama da mura. kwana biyu kuma kafin faruwar dukkan wad'annan abubuwan Abie yayi zama Na musamman da Hakimansa saboda kama Wazirinsa da yayi Dacin amanar Masarauta wajen d'aukar sirrin cikinta ya bama wasu bak'in turawa da ba'asan dalilinsu na yin hakanba, a bincikena d'aya a cikin turawan ya Mutu, amma d'ayan yana nan da ransa. Abie ya kwanta jiyya da sati biyu aka kashe babban malaminsa, limamin masallacin sarki maikuma bama Abie shawara akan addini. dukkan wad'annan dana ambata miki sunayensu a kwai hotunansu anan d'akin, akwai abokin mahaifinki da kika fad'amin, shine Alhaji Mamman k'afur Wannan babban yaron Alhaji Lawan tanderu ne, dan wannan group sunema suka tsaya masa ya fito takarar shugaban k'asa, babbar matarsa k'anwar matar tanderu ce, wadda a gidan tanderun ta taso tun tana k'arama. Senetor halluru garba abokin Alhaji Mamman k'afur Ne sosai, akwai wani 6oyayyen sirrin dake tsakaninsu kuma, sai dai ban saniba ko Abbanki yasan wani Abu a ciki. Idan nace zan cigaba damiki bayanin sirrikan dake cikin d'akinnan kanki bazai iya d'auka ba Munaya, amma nabaki damar kimin kowace tambaya ni kuma zan baki amsarta batareda shamakiba”.
Ajiyar zuciya Na sauke, Dan tabbasa kaina bazai iya d'aukar wannan bayanan nashiba inhar suka wuce zurfin haka, Na yink'ura zan mik'e, saiya matso ya taimaka min da kansa, zaman silifas d'ina Na gyara a k'afata, sannan Na taka ga wasu hotuna, hotona na nuna masa dana muftahu, yad'an murmusa yana ta6e baki, kafin ya ajiye cofin hannunsa ya hard'e hannayensa a k'irji, “Ba manufar wannan hoton ke d'inba, dan haka manta da wannan kawai, sai nan gaba watak'il zaki iya sanin wani abu”.
Zanyi magana ya girgizamin kansa, alamar karnace komai.
Idona na janye daga garesa kawai, na maida kan hoton Muftahu tareda nunashi da yatsa.
Takowa yay har inda nake, ya kama hoton yana kallo tamkar yau ya fara saninsa, “Muftahu d'an uwa nane, kuma abokina, sai dai bakomai ne nake sakin jiki da Shiba, domin lokacin muna yara mutumne shi mai yawan k'arya, hakanne yasaka ko yaushe muke fad'a, babu abinda na tsana ga hallayar d'an Adam irin k'arya dacin amana, wannan halayyar tasa saita gaza barin zuciyata har girmanmu, kullum kallonsa nake bai canjaba, wannan yasakani fin yarda da harun fiye dashi, saikuma yake gwadamin wasu halaye na rashin gaskiya a lokuta da dama, ban k'ara tsinkewa da lamarinsa ba sai a time d'in da abinnan yafaru tsakanina da ke a birnin gayu, Muftahu shine Wanda yakawomin shawarar mizai hana na aureki ko ta wannan hanyar zansan wani Abu, da farko na d'ana masa tarkone, na yarda da auranki na shekara d'aya, yanda yacigaba da rawar jiki sai lamarinsa yacigaba da tsoratani, randa ya saka mana pill's a fresh milk daga ranar na yarda 100% shi maicin dunduniya tane, kuma akwai wani 6oyayyan al'amarin da yake son cimma buri, wannan yasakani kauda idanu a kansa, nabashi dukkan dama, dukda kullum Harun kan nusar dani illar hakan, amma na share komai tamkar bana gani, sai dai wannan zuwan danayi maganar da kika ta6amin a wani dare ya sakani cikin dogon nazari, daga time d'in kuma na saka idanuna akan Muftahu da Harun, zuwannan da nayi na k'arshe Nigeria, naga wani abin mamaki da ban al'ajabi. akwai wani d'aurin Aure da mai martaba yace mu wakilcesa ni da Hakeem (Wambai) amma sai Harun da Muftahu sukace zasumin rakiya, ba rakkiyarce ta sani Ankara a kansuba, yanayinsu ya nusar dani kowanne akwai manufarsa, ban kulaba mukaje muka halacci d'aurin auren, anatashi Hakeem yace shi zai wuce, Dan yanada wajen zuwa, banbi ta kansaba Dan bana d'aukar raini, karramawar da aka shirya yima mai martaba sai ta juye kaina, aka karramamu sosai, ni bammaci abincinba, sai Harun da Muftahu ne sukaci, suna tsaka da cin abincin sai aka kira Harun, bai d'aga wayar a gabanmu ba ya tashi ya fice, ko alama ban kawo komai a rainaba, muka cigaba da hira ni da Muftahu, abinda na lura da shi rabin hankalin Muftahu akan Harun yake, dan yanayinshi ya nuna, zuwa can sai shima ya mik'e ya fice, yacemin yana zuwa, fitarsa babu dad'ewa d'ayar wayar Harun tayi ring, ni mutumne dabai damu da shiga abinda babu ruwansa ba, amma a ranar saina tsinci kaina da duba wayar, bansan Number d'inba, amma nasan fuskar wadda take jikin hoton da Number ta bayyana, ba kowa bace face d'aya daga cikin matan Abie na”.
“Matan Abie kuma?”.
“kwarai kuwa, wannan shine abinda na gani, Wanda ya zaunamin a rai, koda Harun ya dawo yaga wayarsa kusa dani sainaga kamar baiji dad'iba, na bashi ina fad'in hajia ta kiraka, kinga kuwa yanda yanemi zubewa? humm saida Muftahu ya taimaka masa, dana tambayesa se cewa yayi wai tunkan mu taho dama kansa na ciwo, nasan ba haka baneba amma na sharesa. tunda muka taho na lura ana kallon kallo tsakanina Muftahu da Harun, kuma duk sanda hakan tafaru, Muftahu kanyi wani murmushi mai tattare da ma'anoni masu yawa, Wanda har yanzu nakasa fasarasu”.
Huci na fidda daga bakina, na koma Inda na taso na kuma zama, shima saiya tako zuwa inda nake, ya durk'usa a gabana tare da d'ora hannayensa bisa Gwiwoyina, idanu na d'ago a hankali na sakasu cikin nashi, k'ok'arin janyewa na farayi, saboda wasu abubuwa danake hangowa cikin idanunsa. Amma saiya hanani wannan damar, yay wani sassanyan murmushi yana fad'in.............🤫✍🏼
Barkanmu da dawowa sister's😄🤝🏻🥰🥰🥰.
*_ALLAH k'a gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
*_typing📲_*
💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._*
*_♦RAINA KAMA.....!!♦_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
~Book 2~ 👉🏻1⃣6⃣
.................“Kin shirya taimakon Mijinkine Munaya?”.
A salon da yay maganar saida tsigar jikina ta tashi, nad'an lumshe idanu sannan na bud'e a kansa, muryata na rawa nace, “ni bansan komaiba. kuma ina ganin a wajen Abie yakamata ka k'ara samun haske ai, tunda yanzu yana magana”.
Murmushin takaici yayi, sannan ya kamo hannuna cikin nashi, “Kinsan miyasa nabaki dukkan wannan labarin daba kowanne mahaluki ya sansu baki d'aya ba?”.
Kaina na girgiza masa a sanyaye.
Ya murmusa, tareda d'ora hannunsa saman cikina, hannun nasa na kalla, shima idonsa na a wajen, yace, “saboda kece wadda zata zama uwar d'ana ko 'yata, ina fatan koda nabar duniya ban cimma burina ba kibama duk abinda kika haifa labarinnan domin ya ida cimma manufata, wannan wasiyyace ga abinda zaki haifamin, dan inaji a jikina komi zaki haifamin insha ALLAH ba zai zama ragoba, sannan kuma tabbas kin cancanta, domin kece mutum ta farko dana ta6a yarda bazataci amanata ba bayan Mahaifiyata da kakannina da yayata da k'anina. daga k'arshe ina rok'onki girman ALLAH ki sanarmin da abinda kika Sani game dani, dan tabbas nasan kinsan wani Abu, nasha auna fik'irarki a ma'auni kuma ina samunta dai-dai, dan haka batun 6oyemin ma kibarsa zuwa yanzu, kinga Abba jibine zasu koma, to lallai rayukansu tana cikin had'ari kuma komai zai iya faruwa, saboda a yanzu mak'iyansa sunyi shirin dayafi na farko ma, a zatonsu Abbanki yasanar dani komai ne. ni kuma ban ta6a wannan maganar dashiba, sannan Abie da kike magana likitoci sunyi gargad'in kar'a tuna masa da abinda ya wuce yanzun, saboda gudun dawo da hannun agogo baya, kuma kodama na tambayesa zai iya dakatar dani yace ya yafe, ni kuma nariga nataso da BURIN 'DAUKAR FANSA, a cikin zuciyata da kwanjina, Ni nasan Yaya nayi jiyana, yau d'ina ma a wahale take kasantuwa, dan haka nakeson gyara gobena da goben 'ya'yana da dukkan ahalina, inason sanin dalilinsu nama mahaifina hakan, inba hakaba bazan ta6a samun kwanciyar hankaliba”.
Nad'an muskuta domin gyara zamana, ina fad'in “shikenan, amma kabani lokacin please”.
“Nabaki”. yafad'a yana mik'ewa tsaye.
Binsa kawai nayi da kallo, saiya kuma bani tausayi, dukda kasantuwar rayuwarsa cikin Rud'ani, hakan bai habashi zama kamilin mutum mai tarin Nutsuwa ba, gashi da sauk'in kai, saidai idan baka fahimceshi baneba, kamar yanda na kasa fahimtarsa a farko, saika masa kallon mai girman kai.
A gaba d'aya yinin wannan ranar cikin nazarin maganganun galadima na yisu, tabbas abotar Alhaji Mamman kurfe da Senator Halluru da Abbana abin dubawace, na shiga tunano wasu abubuwa danaita karo dasu a d'akin Abbana ni da Munubiya, a wani time d'in da Innarmu ta sakamu masa wani gyaran d'aki, Wanda shine sanadin shigowarmu wannan cakwakiyar kuma, na dafe kaina saboda saramin d'in da yakeyi, motsin da d'an cikina yayine ya sakani dafe cikin ina lumshe idanu, gaba d'aya kaina yana Neman kullewa, har a washe garin ranar haka naita fama da tunani, danma yana hanani, amma danaga ya matsa zan d'ora daga inda na tsaya, yanzu ma dazai fita aiki saida yamin gargad'i, yace na sauka k'asa wajensu innarmu nayi hira, to kawai nace masa, amma yana fita ban fasaba, ganin lokaci na k'ara k'urewa saina d'auki waya na shiga rubuta massage mai tsawo dazan turama Munubiya.
Duk abinda takeyi a idon Galadima ne, tun d'azun yana lura da dukkan motsita ta camera d'in daya ajiye a d'akin wadda koda wasa Munaya batasan da zamanta ba, ya murmusa tareda godema ALLAH, dan yasamu damar kamata a hannu, ta wannan hanyarce kawai zaiyi amfani da ita wajen samun abinda yake buk'ata ga Abbanta, dan Abba yak'i bashi kowacce k'ofa dazai san wani abinda ya sakashi shiga wannan halin, alhalin yaga tarin damuwoyi a idanunsa, masu kuma matuk'ar muhimmanci a aikinsa.
Wayarsa tai 'Yar k'ara alamar Munaya na sarrafa wayarta, saurin saita abinda ya saka mata a wayarta bata saniba yayi, harta gama typing ta tura sak'on akan idonsa, shiga yayi ya duba, saiyaga Munubiya ta turama sak'on, yay hanzarin bud'ewa. (Galadima ya had'a wani tarko a wayar Munaya batareda ta saniba, dukkan wani Abu dazai shiga wayarta ko fita saiya gansa a wayarsa, ta wannan hanyarne yaga na yanzu, saimu bishi muga abinda Munayar ta rubuta to).
_“ ‘Yar uwata, tabbas Allurafa na shirin to no galma, anzo ga6ar da lallai yakamata mu sanarma Galadima komai akan abinda muka Sani, danna fahimci lallai zatonmu yazama gaskiya, wannan sunedai ahalinnan da mukaga bayanai a Kansu, dukda nakula Abbanmu nasan basarwa, saidai bansan manufarsa tayin hakanba, bayan wannan itace damarsa ta k'arshe dazai yadda kwallon mangwaro ya huta da k'uda, sweetheart minene shawararki? dan burina dana haife cikinnan auren contract ya k'are a tsakaninmu, domin babu alak'a kuma kenan, kinga nima na samu 'yancin kaina, nayin auren din din din kamar kowacce mace”._
Babu shiri Galadima ya mik'e tsaye, jikinsa har wani tsuma yakeyi, lallai anzo ga6ar Ashe, hasashensa yazama gaskiya kenan kokuma zai zama, tomi wad'annan yaran suka sani? kenan Munaya Nada dalilinta na yarda da auren su na Contract? Mi Muftahu ya Sani gameda Munaya dahar ya d'anata a gareshi a matsayin tarko?, bayan shi yana nan yana ik'irarin yima Muftahu tarko da auren Munayar. Lallai kan yakula itama Munaya da 'Yar uwarta da Muftahu suna Neman zame masa RAINA KAMA.
Baifi mintuna 15 ba da tura sak'on da Munaya tayi, saiga Munubiya ta kirata, duk Galadima yana kallo daga camera d'insa da kuma saitin wayarsa, dukda kuwa yana office ne, Munaya bata d'aga kiranba, saida ya katse sannan ita ta kirata, munubiya na d'agawa Munaya race, “Sweetheart kinga sak'ona kuwa?”.
“Na gansa sweetheart, amma fa ni duk kin rikitani, kinga wata alamace data tabbatar miki ahalin Galadima ne?”.
“Munu, tabbas alamomi da yawa sun nunamin hakan, sannanfa shima yasan Alhaji Mamman k'afur fa, kuma kinga ai a takardarnan munga sunan Alhaji Mamman k'fur d'in, gashi abokin Abbanmu sosai, nifa yau wlhy abubuwa masu yawa ya fad'amin game da sirrinsa, dukda kasancewarsa mutum mara yarda, duk dai da inaji a raina kamar ya fad'amin wani yankin sirrinsane danya bigi cikina be, amma ni wlhy tausayi guy d'innan yake bani da gaske”.
Munubiya tayi murmushi daga can, cikin tsokana tace, “to ALLAH yabar k'auna dai, sweetheart”.
“ban ganeba, k'aunar mi zai bari?”.
“keda Galadima mana, ai soyayya kan fara da tausayine”.
“Mtsoow dan ALLAH muyi magana mai amfani Munu, yanzu ya kika gani, danya rok'eni ALLAH akan nafad'a masa mina Sani, nikuma ina tsoron koba akansa d'in baneba Abbanmu yake cikin damuwar, karmuzo kuma muyi aikin Baban giwa”.
Ajiyar zuciya Munubiya ta sauke, ta gyara kwanciyarta tana fad'in Munaya kodai mu sanar da innarmu ne kozata bamu shawara?”.
“kai amma bakida hankali yasin, sokike innarmu taci k'aniyarmu Ashe, zatace miyasa tun a farkon lamarin bamu sanar mataba, k'ilama tayi fushi, Dan nima wlhy ayanzu ina ganin munyi wauta fa”.
“to komadai miye munrigada mun aikata. Yanzu mafita zamu nema, mizai hana ki rok'eshi inhar bashi bane kokin fad'a Dan girman ALLAH karya tada zancen kawai, yakuma rik'e mana sirrinmu, idan kuma zai taimakemune akan Wanda kema Abbanmu barazana da mutuwa ai kingani munsamu madafa muma, kinga dai yanda sukaso cin galaba wajen kashesa, wlhy Munaya jinake kamar kar Abbanmu su dawo k'asarnan”.
“Ni kaina tsoron dawowar tasa nakeji, musamman da jiya Yakuma maimaitamin, shiyyasa kawai na Yanke shawarar mu fad'a masa, idanma ba shi bane saiya taimakemu wajen gano wanene”.
“to shikenan, sai naji yanda kukayi kenan, Yaya unborn d'inmu?”.
“gashi nan ya isheni da motse-motse wlhy, na k'agara ma ya fito na huta, kema Yaya namu da lafiyarki?”.
Cikin tsokana Munubiya tayi dariya, “aikoya fito nanda wata shekarar Munafata wani ya Shiga sweetheart”.
“wlhy na kula bakida man kai Munubiya, sai anjima”. Munaya tafad'a tana yanke wayar.
Galadima daga can yay wani k'asaitaccen murmushi yana shafa Kansa da cije lips, ya koma jikin kujera ya lafe yanamai lumshe idanu.
👭
🤣Galadima Kodai-kodai🤫
************
Muna gama waya da Munubiya na sakko k'asa, babu kowa gidan dagani sai su innarmu sai jakadiya, a falon k'asa na iskesu suna hira.
Jakadiya tace, “ranki ya dad'e kin fito?”.
Murmushi namata, ina fad'in “na fito jakadiya, ya k'ok'ari?”.
Tai 'yar dariya tana cewa “kuke fama da k'ok'ari ai, ALLAH dai ya raba lafiya”.
Bance komaiba na zauna ina gaida Innarmu ta amsa tana tambayata ya jikin.
“da sauk'i” na fad'a kaina a k'asa, nace, “innarmu Abba fa? ko barci yakeyi?”.
“A'a sun fita ai shida Sauban tunda safe, zasuga likitansa daga nan sud'an zaga gari”.
“Oh ALLAH ya dawo dasu lafiya to, zaisha yawo kam indai fita da Yaa Sauban ne”.
Dariya jakadiya tayi, tace, “ai mai sunan manya sai a hankaki, shibama ya gajiya”.
Inna tace, “a baya gajiya kam, ni ai birgeni yakeyi, babu ruwansa, sai tsokana da barkwanci”.
“Ai tamkar gadone abin nasu, dan mai martaba lokacin yanada lafiya, dukda kasancewarsa shugaba hakan baya hanashi barkwanci da mutane lokaci-lokaci, to hakama magajin gari yake, daga bayane shi sai nasa halayyar suka canja, yazama shiru-shiru, amma shi mai sunan manya saibai canjaba kuma”.
Ina jinsu nidai bance komaiba, sai murmushi danake tayasu dashi kawai.
Mun dad'e a falon har su Abba suka dawo, masaukinsu ya wuce, Sauban kuma ya zauna muka cigaba da hira, tashi innarmu tayi tabi bayan Abba.
Sauban ya mik'e yana cewa zaije ya watsa ruwa, itama sai jakadiya tashiga domin nunawa kuku abinda zai dafa, ganin haka natashi na nufi masaukin su innarmu.
Nakama handle d'in k'ofar zan murd'a tareda yunk'urin sallana sainaji muryar innarmu kamar tana kuka, “Haba Abbansu dan ALLAH ka sanarmin damuwarka, Yaya kana cikin matsala amma ka gaza fad'ama kowa?, tunda tafiyarnan tamu ta gabato ina lura dakai baka ko barcin kirki, sannan inajinka kana sambatu cikin mafarki jiya da asuba akan kozasu kasheka bazaka bayarba, shin wai minene? kuma su waye?, nidai tun bayan haihuwar su Munubiya na fuskanci kana cikin wata damuwa, amma kullum cikin k'ok'arin 6oyewa kake, bansan minene kake 6oyewarba, haba Auwal, a tunanina yanzu munzama irin d'ayan da bazaka 6oyemin matsalaba kowacce irice, a nawa tunanin munkai bigiren raba farinciki ko sa6aninsa, ko kasan ranar da muka fita da dasu Samha naga lokacin da wani bak'in mutum yazo kuka ke6e gefe, kana kuma magana tsakaninka dashi cikin fushi”......
A rikice naji Abba ya katseta da fad'in Ai'sha kenan ido kike sakamin ban saniba?, dan kawai kin ganni da mutum saiki fassara da wani Abu, Toni banma sanshiba, dan kawai ya ganni bak'in fatane shine yake tambayata, amma daga hakan babu komai, tunba yanzuba kikemin tambayar mike faruwa ina baki amsa babu komai, miyasa bazaki yarda babu komai d'inba, ni nama matso da tafiyar tamu baya, dan doctor yakuma tabbatarmin da babu wata sauran matsala, ki sanarma Munaya ta sanar da mijinta gobe zamu koma kawai”.
“gobe kuma Abbansu?”..
A fusace yace “eh!”.
Ni kaina saida na razana da tsawarsa naja baya daga jikin k'ofar, da sauri nabar wajen jin alamun za'a bud'e k'ofar, tabbas akwai abinda Abbanmu ke 6oyewa da gaske, to wanene bak'in fatar da innarmu tagani tare da Abba ranar? a ranar tare dasu muka fita, saidai sun rigamu tafiya, saboda ni da Galadima mun biya asibiti wajen awo, saida akamin sannan mukabi bayansu, kenan kafin muje abin ya faru? dan tabbas na tarar Abba baya cikin walwalarsa, harna tanbayesa ko jikinsa ne? Amma yacemin a'a kansane kawai ked'an ciwo.
Bansan na iso bedroom d'inmu ba saboda zirfi danayi a tunani, ko hawan benen ma bansan nayoba, juyowa nayi da sauri saboda jin an kama hannuna. ganin Galadima saina rajaza zanyi baya, da sauri ya rik'oni da k'yau yana fad'in “Nutsu mana”.
Da k'yar na tattaro nitsuwa ta, shikuma ya zaunar dani gefensa, hawayrne suka shiga ziraromin a kumatu, Abbana yana cikin matsala, amma wani dalili ya hanashi fad'a, takai har inda yake jiyya ana bibiyar rayuwarsa kenan?.
Ido Galadima shidai ya zubamin, bai hanani kukanba baikuma tambayeni dalilin yinsa ba, kusan 5minutes sannan ya kwanto da kaina jikinsa, jina a k'irjinsa saina fashe da sabon kuka, nanma k'ala bai ceminba, yadai cigaba da bubbuga bayana alamar lallashi, saida nayi mai isata nayi shiru sannan ya d'agomin kaina, dukkan kumatuna ya rik'e cikin tafin hannunsa, Kafin yay k'ok'arin saka idanunsa cikin nawa, cikin k'asaitacciyar muryarnan tasa mai kama da anmasa dole yace, “Haba yalla6iya, sokike ki haifamin abin cikin kwan mai saurin kuka irinkine wai shin?”.
Bansan Sanda murmushi ya su6ucema fuskata ba, na lumshe idanuna saboda bana da jimirin jure kallon da yakemin, shima murmusawa yayi, sannan yakai fuskarsa dab da tawa yana huramin iskar bakinsa a saman ido.
Ban iya hanashiba kusan mintuna 2 sannan ya daina, bud'e idona nayi nad'an kallesa, ya d'agamin gira yana fad'in, “ya dai?”.
Cikin tunzuro baki nace, “babu komai”.
“To miye abin jin haushi daga tambaya”. ‘yay maganar yana sakin kumatuna’.
Binsa nayi da kallo, ganin zai fara k'ok'arin cire kaya, na mik'e zan fice, dan yanzu na lura lamarinsa kullum k'ara girmama yakeyi, baya shakkar cire kaya a gabana ko sakawa, sai dai ni na fita na bashi waje.
Hannuna ya rik'o, na waro ido waje cikin mamaki.
“ina zaki?”. ya fad'a cikin tsare gida.
“ba wanka zakayi ba?, idan kagama zan dawo ai”.
“toni dodone?”.
“A'a na fad'a ina ta6e baki”.
“to koma ki zauna ki kalli sadakinki”.
Idanu na waro masa waje da hangame baki.
Yiyai kamar bai ganniba ya basar. bai sakeniba yakuma cigaba da cire kayansa da hannu d'aya. Ni daifa k'in kallonsa nayi, dan wlhy kunya nakeji sosai, dukda 'yar shak'uwa ta shiga tsakaninmu hakan bai sa mun saki jiki da junaba, garama shi idan rashin kunyarsa ta motsa yakanyi abinda ya gadama yana basarwa a dole kar'a kawo masa raini. Yakan bani dariya sometimes, amma nima saina Basar saboda Jan aji.
Iska kawai naji a cikin kunnena, da sauri na waigoshi, ganin sa dagashi sai boxer sai na juya fuskata.
Bayana ya koma ya zagayo da hanayensa duka akan cikina, yayinda kansa ke a kafad'ata, muryarsa can k'asan mak'oshi yace, “miya sakaki kuka?”.
Salon da yay maganar ya sakani lumshe idanu saboda tsigar jikina data tashi.
Nace “kabari ka gama zan fad'a maka”.
“miyasa ba yanzu ba?”.
“ka saka riga to”.
Murmushi yayi yana shafa cikina, “my friend sarkin tsiwa sarkin kuma Kunya, akwaiki da abubuwan bi........”
Saikuma yay shiru yak'i k'arasawa, hannuna na saka na rik'e hannunsa da ke yawo saman cikina, nace, “ka k'arasa mana, akwaini da mi?”.
“Humm” kawai ya fad'a yana sakina, yaja bathrobe d'insa dake jikin hangar ya sanya, saida naga ya fara k'ok'arin d'aure igiyar sannan na d'ago na kalleshi.
“To mikuma kike kallo?”. Ya fad'a cikin tsare gida.
Baki na ta6e ina fad'in, “miye abin kallon to?”.
Ya d'an fiddo ido sannan ya matsoni, “zona nuna miki”.
Nasan ko guduwa nayi saiya kamoni dan haka na duk'e ina fad'in “wash ALLAH cikina”.
Tsayawa yay cak, saikuma ya tako da hanzari yana tambayar lafiya?.
cikin marairaice face nace “Motsi yakeyi ALLAH”.
rankwashina yayi aka yana cewa “ke d'inan ko”.
Dafe wajen nayi, bai kulani ba ya shige bathroom, na harari bayansa ina masa gwalo, nasan inda banyi hakaba bakina ne zaisha wahala.
Ina zaune ya fito, na d'auke kaina tamkar ban ganshiba, shima hakan yayi, ya wuce wajen frigate ya d'akko ruwa da Kofi, kujerar dake wajen karatunsa ya jawo ya zauna yana fuskantata, batareda yayi yunk'urin cire bathrobe d'in jikinsa ba, yanzun kam babu wasa a fuskarsa, ban damuba dan nasan halin kayana yanzu, yanzu zakiga yasaki jiki yana magana kamar ba shiba, anjima kad'an saiya koma Asalin Galadimansa dana fara gani a Hospital, Mara dariya mara later r😏.
K'afarsa d'aya ya d'ora kan d'aya yana shan ruwa, yasha kusan rabi sannan ya cire, batareda ya ajiye kofinba ya maido dukkan hankalinsa kaina, “A kwana biyunnan kokin lura Abba yana cikin damuwa?”.
d'ago idanuna nai na kallesa, a sanyaye nace, “abinda naji innarmu na masa Complain kenan yanzu, amma saiya nuna fusata”.
“shine kika shigo kina kuka?”.
Na jinjina masa kai batareda nace komaiba.
Shima bai sake cewa komanba ya kauda idonsa daga kaina yana kur6ar ruwansa. kusan 2minutes sannan yakuma kallona, “Munaayaa mukawo k'arshen 6oye-6oye mana”.
Kallonsa nima nayi, nace, “kamar ya?”.
“humm” yafad'a yana cije lips, mik'ewa yayi tsaye ya ajiye cup d'in hannunsa a gabana, sannan ya shiga zagaye d'akin hannunsa goye a baya, nikam dai binsa kawai nakeyi da kallo kamar na samu television, maganarsa ta katsemin tunanina.
“Munaaya! Mikuka ta6a gani a d'akin Abba ke da 'Yar uwarki?”.
Zumbur na mik'e dan mamaki, “yalla6ai a ina kasan wannan?”.
batareda ya kalleni ba yace “Munaya Sameer ya wuce dukkan tunaninki, dan haka fad'amin?”.
Ajiyar zuciya na sauke, wadda ta tilasta masa juyowa ya kalleni, nace, “yalla6ai ba fad'a maka bane matsalar, kuskuren muhallin fad'arne da kuma makomata”.
“bakida dukkan Matsala da wad'annan, idan bai danganceni ba zan d'auki matakin taimakon sirikina, makoma kuwa inada yak'inin kare martabar matata uwar d'ana ta kowanne hali”.
Furicinsa yaban mamaki, dan haka nace, “matar Contract ko?”.
“Well Duk yanda kika fassara dai-daine, abinda na Sani kawai wannan maganar batada nasaba da waccan, dan haka kibar kowanne a muhallinsa sai lokacin yinsa yayi”.
“humm” kawai na fad'a na koma na zauna inda na tashi.
Idonsa a kaina ko k'yaftawa bayayi.
Na nisa sannan nafara fad'in,
_“Na tabbata tunkan ka k'ulla alak'a dani saida kasan koni wacece, dan babban mutum irinka bazaiyi Abu babu wani tanadiba, banida matsala wajen maimaita maka sunana ko tarihin ahalin dana fito, kamar yanda kasani mu 'yan biyune hakan yasaka ba'a banbancemu ni da 'yar uwata, sai dai hallaya takan banbantamu ga Wanda ya sanmu, Munubiya mutumce mai hak'uri da yawan kawaici, a wajen gadon hali tabbas ta biyo mahaifiyarmu ne, sa6anin ni Munaya mai zafi da yawan tsokana, a lamarina babu ragi ko d'aga k'afa, inhar kaga nayi dogon zama da mutum babu sa6ani to ka tabbata ya tanaji matakan iya zama danine, basai amfad'a ba nima kaina nasan halayena na kamanceceniya dana Mahaifina da kuma kakata innaro, a wata litinin d'in da bazan ta6a mantawa ba sai mahaifinmu yayi wani bak'o, matsalar da aka samu shine yazo bai iske Abba a gidaba, a wannan ranar innarmuce da aiki, dan haka hak'in tarbar wannan bak'o saiya rataya a wuyanta, maimakon tayi da kanta saita saka cikinmu ni da Munubiya wani yayi”._.......................✍🏼
Mu had'u a page na gaba🤫
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu🙏🏻😭_*
*_typing📲_*
💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._*
*_♦RAINA KAMA.....!!♦_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
~Book 2~ 👉1⃣7⃣
_..................“Da haushi na d'auki ruwan da innarmu ta bani na fita, saboda muna tsaka da kallon wani film daneke masifar sone, Munubiya dan kartaje kaiwa saita hau barcin k'arya. Tunda na shigo shegen mutumin nan ya tsura min idanu yana lasar baki, kai kace tsohon mayene yaga nama, a zafafe na dire tiren agabansa ko k'ararsa zatasa ya dawo hayyacinsa, amma wawannan yayi nisa, na buga tsaki a zuciyata zan fice, caraf ya kamo hannuna, ban dubi girmansa ba na dage na watsa masa mari, hakan kuma yayi dai-dai da shigowar Abbanmu falon. Amma d'an iskan ganin Abbanmu da marin danai masa baisashi sakin hannunaba, saida Abba ya daka masa tsawa da fad'in “SD! wane irin iskancine wannan? a cikin gidana ka kama hannun 'yata?!”. Abba na rufe baki ina kuma bashi mari na biyu, tunda naga alamar shi bunsurune. a wannan karon ya saki hannun nawa, saboda janyeni da Abba yazo yayi, Abba ya nunamin k'ofar fita, koda na fita saina la6e a corridor d'in shiga falon bak'in._
_A zafafe Abbanmu naji yana fad'in “SD ubanwa yabaka damar shigomin gida ne?”. sautin tafin bak'on na jiyo dan haka nai saurin lek'awa ta kafar labule, gani nai yana zagaye Abba yana dariya da tafi, cikin shak'iyanci yake cewa “Alhaji Auwal, Alhaji Auwal! dama kanada k'yawawan 'yammata haka? Woow nice babie, idan na samu wannan ai ko rana bazata sake ganina ba, wlhy nasan zan kwashi rom........., mari Abba ya zuba masa a kumatu, yana nunashi da yatsa, a matuk'ar fusace yace, “wlhy idan ka kuma furtawa saina datse kazamin harshenka a falonnan, wawa kawai”. SD ya shafa kumatunsa sannan ya sumbaci hannun yana hurama Abba, “Kafa birgeni Alhaji Auwal, kai jarumi, 'yarkama jaruma, kai inason irin haka mutumina uhhhhhhm mutccch”. ya k'are maganar da kuma kissing hannunsa. Banza Abba yamasa ya d'auke kai daga kallonsa yana fad'in “miya kawoka gidana?”._
_Alhaji Auwal kenan, kaima kasan dakaga SD kasan zancen, a wannan karon da albishir d'in k'arin farashi akan tayin baya nazo maka, sannan kuma damace a gareka ta k'arshe hakan, mun yanke shawarar baka naira milyan 500”. Abba yaja tsaki yana hararsa, “ka koma ka sanar ma iyayen gidan naka ina kan bakana, sannan Ku farka daga barcin da kukeyi, dan bazan ta6a badawa ba, kamar yanda ban ba da jiya ba, bazan bayar yauba, sannan gobe ma bazaku samuba, wannan kuma yazama first and last dazaka shigomin gida, inba haka ba ina mai tabbatar maka zaka aikata kuskuren da bayan bayanka ma saisunyi takaicin jin yanda zaka k'are”. “kwantar da hankalinka sarkin jarumai, tabbas zan tafi, bakuma zan sake dawowa ba balle nayi nadama Oga, ammafa bazan 6oye makaba, kana bani mamaki, kak'i bama Wanda akace ka bamawa, sannan kak'i saida mana mu masu buk'ata, shikuma wannan Abu ba tuwoba balle muyi tunanin zakacine, waikai mike damun kankane haka? ka zauna kanata rik'ema Wanda yarigada ya mutum amana, shikuma Wanda kakema tanadin bashida maraba da gawa, koda yake ashefa ga Galadiman Ku nan, koshi kakema tanadi?”. “wannan ba matsalarka bace”. Abba yafad'a cikin karsashi. “kumafa gaskiyarka wannan ba matsalata baceba, amma tabbas inada yak'inin kai zata zama taka matsalar maybe ma harda santaleliyar budurwar 'yarka, lallai labarin k'yak'yk'yawa da ahalinta zai Shiga duniya kwanannan, nabarka lafiya, ka huta”._
Da sauri nabar wajen gudun karya fito ya ganni, nakoma cikin gida ina juya wad'annan zantuka na abbamu da bak'onsa, masu tsananin wahalar fassara, mi bak'on yake nema a wajen Abba dahar yake ik'irarin sun basa zunzurutun kud'i naira na gugar naira, d'ai-d'ai har miliyan d'ari biyar? Amma dukda yawansu Abba bai firgitaba balle mik'a wuya?, sannan wanene Galadima kuma? Miyake nufi da labarina zai shiga duniya? Na shiga uku ALLAH karka bama bawannan damar cutar da rayuwata ko ahalina gaba d'aya.
Munubiya data lura da halin danake cikin ta sakani gaba da tambayar, tun ina k'ok'arin 6oye mata Dan kar hankalinta itama ya tashi, harna fito fili na sanar da ita gaskiyar abinda naji da kuma gani, harma Wanda na aikata.
Hankalin Munubiya ya tashi sosai itama, nanfa muka Shiga kullawa da kwancewa Munason gani gaskiyar lamarin, amma mun kasa kama bak'in zaren, fita kuwa mun koma yintane a d'arare saboda tsoron furucin mutuminnan.
a wata ranar talata da Abba zai dawo daga tafiya sai innarmu ta sakamu gyaran d'akinsa saboda kanta namata ciwo. muna tsaka da aikin sai muka tsinci wani file da yasha k'yak'yk'yawar adana a awani akwati dake cikin wardrobe d'in Abba, to dama da biyu muke aikin, harda bincike akan Neman hasken maganganun da mukaji ranar, jikinmu har rawa yake muka bud'e wannan file, a shafin farko mukaci karo da wani Abun daya kuma rikita tunaninmu”.
👇🏻
*_Tabbataciyar wasiyya ga ahalina, koda ace na kwanta dama kafin cimma burina ko mik'a wannan sak'on amana ga Wanda ya cancanta, to na shaida muku da cika umarnina na ida nufina a garesu 'ya'yana ko 'yan uwana, inason Ku isar da wannan amana da aka bani ga ahalin wannan masarauta............”._*
“iya nan rubutun ya tsaya, muka bud'e shafin na biyu kozamuga sunan masaurar da Abba ke magana da k'arashen zancensa, amma sai sunayen mutane muka gani a k'alla sunkai goma. Wucewa mukayi shafi na uku, a dai-dai wannan lokacin Abbanmu ya shigo d'akin batare da mun Ankara ba, wata hargitsatstsiyar tsawa mai tsinka hanji ciki da zukata ya daka mana yana fad'in “ku harkunkai girman da zakumin bincike a d'aki a matsayina na mahaifinku? mi kuka sani akan wannan takardar dahar kuke binciken abinda ke cikinta? Yaushe kuka koma la6e?”. haka Abba ya rikice gaba d'aya muma ya rikita mu, ya dinga zabga masifar dahar tajawo hankalin jama'ar gidanmu, indai tak'aice maka bayani har innarmu saida fushin Abba ya shafa ranar, hakanne yasani fahimtar Abba ya gane naji komai a ranar. munshiga damuwa a time d'in matuk'a, dukda hak'urin da muka bashi yak'i saurarenmu, ya d'au tsawon lokaci yana fushi damu kafin ya daina. bayan komai ya daidaitane kuma wani yammaci mun fito daga school saiga motocika a jere suna tsula uban gudu a titi, wucewarsu tamkar iska yasakani fad'ar bak'ar magana ga manyan k'asarnan har 'yan uwana na tayani. Sai kuma mukaji sunanka a bakin wani saurayi da 'yammata biyu. Wannan ganinaka ne yasakani dawoma Munubiya da abinda ya wuce, saboda sunan Galadima da mukaji saurayinnan ya ambata, sai muka dinga tunanin kokaine Wanda muka ta6aji a furucin bak'on Abba?. ga kuma sunan masarauta da muka gani a rubutunsa, dukda bamuji sunan ainahin masarautarba kuma, balle mu tabbatar da kaid'inne.. Ganinmu dakai na biyu kuma saika bani haushi, dan ganinka mutum mai yawan izza, sainaga bebekin Abba daya saka kansa had'ari akan Wanda shi baima damu da damuwar kowaba sai tasa gakuma tarin girman kai Dana hango tartare dakai”. (Kafayi hak'uri, gaskiyata nake fad'a, guntun murmushi kawai Galadima yamata baice uffanba) taci gaba da fad'in “Wannan ne dalilin yimaka tsak'i a asibiti, idan har baka mantaba, har dogarinka d'aya yataho da zummar d'aukar mataki amma ka dakatar dashi da fad'in ya barni”.
Galadima ya murmusa alamar bai mantaba.
Nace, “ka tuna kenan?”.
“Na tuna kwarai da gaske, dan bancika manta abuba saidai idan na d'aukeshi mara muhimmanci, amma a time d'in ai banga face nakiba, shiyyasa banida tabbacin kece, saidai na muku kallo d'aya a lab da muka iskeku keda sisters d'inki, ni nama zata Ku 'yan uku ne ai”.
“Umyim, amma a time d'in babuma Wanda zai d'auka Kasan da zamanmu a lab d'in, dan gaisuwar da ake maka ma, kamak'i amsawa sai d'aga hannu, hakanne ya tunzurani na fito daga lab d'in, dasu munu sukace kainema kabada jinin da za'a sakama feena ban yardaba”.
Baki Galadima ya d'an ta6e yana shafa kwantaccen sajensa, ya d'agamin gira d'aya yana fad'in “bazaki fahimta bane yalla6iya. yanzu labarin da kika bani ya farune duk a wace shekara?”.
Na d'an ya mutsa fuska ina fad'in bamai nisa bace, dan ko 2years cikakku baza'a k'ulla ba, Muna Exam d'in NECO nema, dan har results d'inmu suka fito aka fara biyan JAM Abbanmu ya biyama sauran 'yan uwanmu amma banda ni da Munubiya, sai baba k'aramine ya biya namu, so munfara karatu dai babu dad'ewa muka shirya da Abbanmu saboda magana da dad d'insu Ayusher yamasa Yakuma sake bashi hak'uri. tundaga nan komai yazama Normal. Amma kaikanka yakamata kayi mamakin yanda a kwanaki kad'an na amince da tayin auren Contract d'in da kukaimin, dukda ba waccan binciken namu kawaine keda alak'a da amintar tawaba, akwai wani dalili daya shafi ahalina”.
Mik'ewa Galadima yayi yana salute d'ina, yace, “kin cancanci yabo my friend, dukda tabbas a farkon aurenmu kema kina cikin zargina akan turoki akai gareni tun farko, amma yanda kike halayyarki da d'abi'unki sai kika kauda hankalina, a tunani na dukkan mutum dazai kwantarmin dakai yaringa nuna tsorona to tabbas wannan mutumin sunamsa *MAGE MAI KWANCIYAR 'DAUKAR RAI* a wajena, amma kece mutum ta farko kuma mace data iya mayarmin murtanin magana kai tsaye, batare da shakka ba, sai dai inason Sanin minene alak'arku da Muftahu to?”.
“muftahu kuma? babu wata alak'a bayan wadda kasani, dan tare Na fara ganinku ai”.
Takowa yay zuwa inda yake zaune a da, ya koma saman kujerar ya zauna, “kin tabbatar babu alak'a ta kowane fanni?”.
“miyasa kake kokwanto? inhar zaka kasa gaskatani a nan bai kamata ka aminta da zancena Na farkoba kenan?”.
Ya murmusa yana fad'in “kozaki gaji Abba ne?”.
Nace, “akan me?”.
“jaridanci mana, naga kin shahara wajen iya bincike”.
Mik'ewa nayi saboda k'afata tafara yaamm alamar jinina yana buk'atar motsawa, nafara d'an takawa. hannaye kawai ya hard'e a k'irji yana bina da kallo, saida nad'an zagaya d'akin kafin nabashi amsa da fad'in “yalla6ai kasan wani Abu kuwa?”.
Kansa ya girgizamin kawai.
Nace, “humm nifa nan daka gani, kwakwalwata tana aiki fiyeda yanda kake aiki da agogo”.
“really?”.
“baka buk'atar jayayya”.
Ya d'aga kafad'a yana ta6e baki, “hakane kuma”.
Sharesa nayi na zauna a bakin gadon danna d'an mik'e, a haka najawo filo na kwanta k'afafuna a k'asa.
Tasowa yayi ya dawo ya zauna saman k'aramin table d'in gaban sofa, jinai kawai ya kama k'afata ya d'ora saman cinyarsa yana matsamin a hankali.
Da mamaki na d'ago kai na kallesa.
Ido d'aya ya kannemin yana d'an ta6e gefen bakinsa, ya maida kallonsa ga k'afar.
Sabon salo, na fad'a a raina. a fili kuma nace, “yalla6ai kaine......”
Bai bari na k'arasa ba yay saurin fad'in, “ba dole na taimaki lafiyar abin cikin kwan ba”.
Harara na dalla masa ina janye k'afata, ya kalleni da mamaki, “ya haka? ko haushi kikajine?”.
“miye zai Sani jin haushin? saika bari idan yafito duniya ka matsa tashi k'afar”.
“oh ni Sameer naga ta kaina”.
“zama kaga ta k'afa bata kaiba, Sunan nakama bazaka iya fad'arshi da r ba”.
“oh nan kuma kika dawo?”.
Matsawa nayi baya saman gadon sosai batareda na bashi amsaba. shima saiya taso ya hawo gadon, hakan yasani yunk'urawa zan sauka na bar masa, fan nasan hawan nasa bazai haifar da d'a mai ido ba, yasa hannu ya rik'eni, “yalla6iya ai saikin maimaita mikika fad'a dalla-dalla”.
“lah wasafa nake maka, kaga rigar wankace a jikinka kaje ka cire kar mura ta kama ka”.
“Ai kinga dai-dai kenan”. Yay maganar yana k'ok'arin kwance igiyar rigar.
Hannunsa nayi azamar rik'ewa ina marairaice face alamar yaji tausayina.
Baki ya ta6e yana ture hannuna, na kuma k'ank'ame nasa nak'i bari. Murmusawa yayi, ya kwanto gefena tareda sakani jikinsa ya rungume.
“Nace please wankama zanyifa, zafi nakeji”.
Maidani yayi ya kwantar, cikin kunnena yace, “kedai fad'i gaskiya, ko kina son a.......”.
Rufe bakinsa nayi da tafin hannuna ina kukan shagwa6a, ya shiga k'ok'arin cirewa amma nak'i bari, shi dariyama na bashi, irin wannan hak'ilo haka. duk yanda yaso na barsa k'i nayi, saida barci yafara fisgata hannun ya zame.
Kansa ya girgiza kawai yana murmushi, a fili ya furta “mai bakin tsiwa”. Ya k'are maganar da sumbatar goshinta yana gyaramata kwanciya a jikinsa.
Ya tsira mata idanu yana kallon yanda take fidda numfashi a hankali, a zahiri idonsa a kanta, amma zuciyarsa maganganunta taketa cud'awa, shi baima ta6a ganin mace yarinya k'arama mara tsoro da shiga rikita-rikita irinta ba, bata gudunma shiga had'ari? ya sauke ajiyar zuciya yana tashi zaune, k'afafunta yashiga mammatsa mata a hankali, aikam harda gyara kwanciya su madam munaya, yad'an murmusa, yasan ko'a d'azun tanaso fa, amma iyayi yasata hanashi ya mata. Ya d'auki tsawon lokaci yana mammatsa mata jikinma gaba d'aya, yayinda zuciyarsa kuma ke tattance bayananta dalla-dalla, daga k'arshe sauka yay daga gadon ya fice zuwa d'akin sirrinsa, duk abinda tafad'a yasamu sabon file ya bud'e masa, baya wasa da evidence komai k'ank'artarsa, balle ma nata ya wuce Na wasa, ya dad'e yana rubuce-rubucensa kafin ya koma kan Computers, sunan SD kawai ta ambata masa, dan haka yafara searching gameda SD d'in kawai, babu abinda ya fahimta akan hakan, dama baiyi tunanin fahimtarba, waya ya d'auka ya kira Nuren, bayan sun gaisa yace, “Nureddin acikin yaransu Tanderu kasan SD?”.
“SD! SD! kai anya kuwa? amma dai ina zuwa bani mintuna 30”.
“ok saina jika”.
Galadima Na yanke wayar ya nemo number d'in Abba da bakowa ya sani d'innanba yafara aiki a kansa, dukkan Contact d'in ciki suka bayyana, d'aya bayan d'aya ya dinga binsu yana nazarin adadin kiran da aka ta6ayi, sau nawa aka kira Abba sau nawa ya kira shima? Mafi yawa ma kiransu yafi yawa, yad'an murmusa yana wasa da tsinken hannunsa a kan la66a da nazarin yanda zai 6ullo musu, dan duk hanyar daya kamata yayi bincike an d'auki mataki a kanta, tsawon lokaci bai fahimci komaiba, sai zuwacan wata dabara tafad'o masa, nutsuwa yay yana sarrafa Computer's d'in cikin tsantsar kwarewa da gwaninta, ya kafa musu tarko ne a wayar innarsu Munaya, dan ya tabbata watan watarana zasu iya kira ko sak'o, amma abinma haushin saiya iske wayar inna a kashe, ya dafe kansa, saifa da yacema dady aringa barin wayar a kunne.
Babu shiri ya d'auki waya ya kira daddy, bayan sun gaisa yaymasa maganar kunna wayar innar. cikin mamaki Dady yace, “ai a kunne take koda yaushe, Change ma baya k'arewa nake kuma sakata, idankuma zan zo nan nakan sanarma Jafar shima ya kula, amma ina zuwa dai”.
Galadima ya amsa da to, amma k'asan zuciyarsa tana mamaki. babu dad'ewa Abba ya sake kiransa, “Ashe Change ne ya k'are babu dad'ewarnan ban lura ba, amma gashinan Na sakata”.
“to Dady, Na gode sosai”.
Sunayin sallama da Dady Kiran Nuren Na shigowa, d'agawa yayi, Nuren yace, “inagafa brother hanya d'ayace dazata saka musan shi wanene SD d'in, dan abinda Na lura dashi baya amfani da hakan ta kowanne fanin yanar gizo, maybe da full name yake amfani. yanzu zan sayi ticket insha ALLAH zanje domin bincika a wajen Malam Saminu, nasan ya magantu yanzu, zai amsa mana dukkan tambayarmu”.
“ok hakan yayi, idan ka fahimci bai saniba karka takurashi, ka binciki yarinyarnan itama, koma ka fara bincikarta dan ita bama wayo ta cikaba sosai, k'ila kafi samu cikin sauk'i a wajenta, abinda yasa Malam saminu baison fad'ar komai, babbar 'yarsa cikin 'ya'yan Alhaji balala wani ya mata ciki, kuma sun dai-daita akan idan ta haihu za'ama yaran aure, wannanne yasakashi tsoron fad'ar komai, dan karya lalata waccan alak'ar, dan tabbas yasan yana fad'a auren bazai yuwuba, to nima banason shiga hak'in kowanne ahali akan aikina, shiyyasa nabashi dama kaga bankuma waiwayarsa ba, yanzu haka yarinyar ta haihu kwana hud'u kenan, amma shi yaron ya kawota nan Dubai ta haihu ne, a nufinsu bayan haihuwar da sati d'aya zasu dawo Nigeria a d'aura musu aure sannan su dawo Dubai d'in, dan Alhaji balala baya son abinda zai 6ata record d'insa, kuma mamar yaronce ta Dage sai anyi auren dan ita mutuniyar kirkice, dan haka mu bama Malam Saminu wannan damar”.
Ajiyar zuciya Nuren ya sauke, cikin mamaki yace, “duk ya akayi kasan wannan brother? ”.
galadima ya murmusa, yana fadin “Nuren kenan, to bara nayi copy d'in my mata, kwakwalwata tana aiki fiyeda yanda kake aiki da agogo, nasha fad'a maka bada kwanji kawai ake yak'i ba, sai anhad'a da dabarun tunani dana nazari, so kad'an nafad'a maka daga abinda ya shafi Malam Saminu, kaidai saina jika kawai, a time d'in da zakuyi maganar ka tabbatar ka had'a Communication dani ok?”.
“babu damuwa aljanin munaya”.
Dariya sosai Galadima ya shiga tuntsurawa da iskancin Nuren, wato shima ya maida Aljani yau, wlhy yaronnan yagama rainashi, wai Aljanin Munaya, d'an iska zan kamaka ai.
Kashe komai yayi ya fito daga d'akin, bai koma cikiba saiya sakko k'asa, ya iske Sauban kad'ai a falo, shima shigowarsa kenan daga asibiti yake.
Galadima ya zauna yana fad'in “jirgi sarkin tashi daga ina?”.
Dariya sauban yayi, yace, “kai Yaya, nine kuma jirgin?”.
“Kamafi jirgi ai. Wane shiri kakeyi gameda zuwa bautar k'asarka Nigeria”.
Sauban ya 6ata fuska kamar zai fasa ihu “yaya yanzu fa ca za'ayi saina koma 9ja har zaman 1year?”.
Hararsa Galadima yayi, “to zakayi anan k'asar ne?”.
“Ni Yaya ALLAH da anayi da nayi, a manta da bautar k'asar kawai mana, nayi joining masters d'ina”.
K'aramin tsaki Galadima yayi, yay crossing k'afarsa yanama Sauban wani kallon bammasan amsar dazan bakaba, saida ya d'auki wasu mintuna sannan yace, “rashin yin ai bazai zama matsalar kowaba sai taka, bakuma zaka gane hakanba sai nan gaba idan ALLAH ya kaika inda bakayi zatoba, idan kace bazakayiba it's better, nidai ai nayi nawa ko. tashi kabani waje”.
Ganin ransa ya 6aci Sauban ya marairaice fuska zaiyi magana, amma sai Galadima ya d'aga masa hannu, sannan yamasa nuni da k'ofa alamar ya fice masa.
Fita Sauban yayi yabarsa, shifa tsakani da ALLAH zaman masarautar ne baya son yi shi kad'ai.
Galadima ya girgiza kai kawai yana fad'in “ALLAH ya shiryeka, gata kasamu tunda katashi kaga komai basai ka nema ba”.
Jakadiya data fito ta rissina tana fad'in “Ashe ka shigo magajin gari, barka da dawowa”.
Murmushi Galadima yayi, yanason matarnan saboda halaccin datake wa rayuwarsu, “yauwa jakadiya, ya gidan?”.
“lafiya lau Ranka ya dad'e, a shirya abinci ko?”.
Agogon dake tsintsiyar hannunsa ya kalla, sai kuma ya maida ga jakadiya, “bar abincinan jakadiya, akwai Inda zanje”.
“to ALLAH ya dawo dakai lafiya”.
Hannu ya d'aga mata kawai sannan ya tashi ya fice. mashin ya hau yafita.
Abba dake can gefe a harabar gidan tsakanin wasu flowers yana hutawa ya sauke ajiyar zuciya, tundaga fitowar Galadima har hawansa mashin da fitarsa akan idonsane, rufe idanunsa yayi yacigaba da tunaninsa da tun d'azun yake zaune a wajen yanayi.
Asibiti Galadima ya nufa, yay kici6us da Aunty Mimi Na shirin tahowa gida ta huta, ta kalleshi da mamaki, “my k'ani dawowa kayi?”.
Gefen girarsa yad'an shafa da d'an yatsa d'aya, “eh , ina zakije k?”.
“gida zanje nad'anyi wasu abubuwa”.
“ok sai kin dawo”. yafad'a yana ida shigewa, ita kuma ta fice.
Momma Na zaune tana waya da papi, ya zauna d'aya a kujerun yana kallonta cikeda sha'awa, uba da 'Yar sun birgeshi, juyawa yay ya kalli gadon Abie, barci yakeyi, har Momma ta gama wayar ison Galadima Na kan Abiensa ko k'yaftawa bayayi, shi kad'ai yasan mi zuciyarsa take sak'awa.
“Muh'd daga ina haka?”. Maganar Momma ta katse masa tunani.
Janye idonsa yayi daga kan abie ya maido ga Momma, “Daga gida Momma, har yanzu barcin Abie yakeyi?”.
“eh tunda ka Fita bai farkaba, mike faruwa naganka cikin damuwa?”.
Huci ya furzo daga bakinsa, zaiyi magana sai kuma yayi shiru.
“Nifa tsiyata dakai kenan Muh'd, Yaya Abu nacin ran mutum bazai iya fad'ama kowa a taimakeshi da shawara ko addu'a ba, kaga yanda jijiyar kanka ta tashi kuwa? Haba Muh'd Sameer d'ina, kaifa yanzu ubane, girmanka ya k'aru, aringa rage damuwarnan da miskilanci mana, ni ALLAH ma yasa ba haka kakema d'iyar tawaba?”.
“kai Momma”. ya fad'a amarairaice cikin 'Yar shagwa6a.
Murmushi tayi tace “to fad'amin mike faruwa?”.
Yay d'an tsaki, “Ni ai Momma bammasan ta ina zan fara baneba”.
“kafara ta sama kawai”. Momma ta fad'a tana dariya.
Shima dariyar yayi kad'an sannan ya gyara zama, kuma maida muryarsa k'asa-k'asa yayi yana maganar ahankali, tsaf ya zayyanema Momma yanda sukayi da Munaya, ya d'ora da fad'in “Amma kinsan wani Abu kuwa Momma?”.
“a'a saina fad'a dear”.
“uhm gani nake kamar bakomai ta fad'a minba, ta 6oye wasu abubuwan dai kamar, saidai bansan dalilinta ba.
Momma ta jinjina kai tana murmushi, “To Muh'd mizai hana kacigaba da binta a hankali, nasan zata fad'ama sauranma, ni aganina kamar tana ganin kaima ka kasa yarda da itane shiyyasa tafad'i wasu tak'i fad'in wani, idan har ka yaba da hankalin matarka yakamata ka fara sakin jiki da ita wajen Neman shawararta da sakata cikin wasu al'amura naka Na tabbata itama zata fara fad'a maka nata”.
“gaskiya kika fad'a Momma, dan naga fa'idar hakan kwarai da gaske, zan kula insha ALLAH. ya addu'oin Abie akwai saura?”.
“saura kad'an, gashi bakuyi wasuba”.
“mai k'arfin yince tazama sai a hankali, daga barci sai barci take yini”.
“ALLAH Sarki d'iyata, ai tanama k'ok'ari, dama idan ciki ya fara tsufa hakane, ALLAH dai ya sauketa lafiya”.
“To amin Momma”.
Sun cigaba da 'yan hirarrakinsu har zuwa lokacin da Abie ya farka..................✍🏻
*_inata gaisheku da yawa da yawa, comments naku Na sakani nishad'i over🥰🥰🥰🥰🥰😍😍😍😘😘😘_*.
I love you wijiga-wijiga sister's🥰🥰🥰🥰
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭🤚🏻✋🏻
*_typing📲_*
💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._*
*_♦RAINA KAMA.....!!♦_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
~Book 2~ 👉🏻1⃣8⃣➖1⃣9⃣
.................Na dad'e ina barci kafin Na tashi, nayi mamakin ganina ni kad'ai, bansan time d'in da Galadima ya ficeba, sakkowa nayi daga gadon Na nufi Na watsa ruwa.
Ina tsaka da shafa mai Samha ta shigo, saida tayi sallama nabata izinin shigowa sannan, ledar hannunta Na kalla ina fad'in “mikika samo mana 'Yar Uncle?”.
Cikin dariya ta zauna kan sofa tana cewa “kayan dad'i ne Aunty gimbiyarmu, alfarma nazo nema wajenki keda Uncle”.
Hankalina gaba d'aya Na maido kanta, “Alfarmar mi kuma?”.
“Aunty gimbiya please ki lalla6a Uncle ya barki muje birthday d'in k'awata Dhibya, ALLAH yarinyarnan tana sonki sosai, kullum hirarki”.
Nad'an zaro ido “kai Samha yaza ai naje wani birthday da wannan cikin? kuma kema kinsan bazai bariba tunda Na 'yammatane”.
“kai aunty, cikin saikace Wanda yayi wani k'ato, kumafa a cikin gida za'ayi wlhy, iyamu goma ne kawai”.
“to naji, ALLAH yasa ya bari, mikika kawo mana a ledar?”.
“yes my sweet aunty, wannan wani sari ne yamin k'yau a wani shagon da muke zuwa siyan kaya, shine nayi alk'awarin siya miki, Uncle Sauban ya cikamin na siya, yanzu Na kar6o please ki gwada muga”.
Dariya nayi, nace, “inye kaga 'Yar Uncle Anfara jink'an iyaye, to amma ni ina na iya saka sari?”.
“kowama koya yayi nidai ki saka muga dan ALLAH”.
“to shike nan bara na gwada, ALLAH ya saka da alkairi, ina alfahari da d'iyata”.
Samha ta fita tana dariya, nikuma na warware kayan, masha ALLAH sarin ya had'u gaskiya, farine anmasa kwalliya da pink and silver kad'an-kad'an. Na saka rigar, sai dariya ta kamani, saikace wata bafulatana🤭🤣.
Warware zanin nayi, tofa anan akeyinta, dan ban iya nad'awaba, na tsaya gaban mirror inata gwadawa amma na kasa, dariya ta kamani, yau naga takaina, Samha ta had'ani da aiki.
Tunda ta fara k'ok'arin d'aura zanin sarin yana tsaye a k'ofa, ya hard'e hannayensa ak'irji kawai yana kallonta, kamar zaiyi dariya saboda yanda taketa murd'e-murd'en d'aurawa.
A hankali ya taka zuwa inda take, jinai kawai andafa min kafad'u ta baya, na d'ago a tsorace muka had'a ido ta cikin mirror, fuskarsa babu walwala, ya d'agamin gira d'aya, maida idona k'asa nayi, yayinda shikuma ya juyo dani ina fuskantarsa.
Gwiwarsa d'aya ya saka a k'asa ya dogare d'aya, nidai kallonsa nake mizaiyi?. Batareda ya kalleni ko min magana ba ya zare zanin dake tattare a hannuna, nikam kamar wata sokuwa saina sakar masa.
Yiyay kamar zai warware zanin, nayi saurin rik'ewa, ya d'ago fararen idanunsa yanamin alamar na saki, ban iya musa masaba na sakar masa.
Shima sai bai yaye dukaba ya dai-daitashi, ammakina sainaga yana nad'amin, babbar magana Galadima da nad'a sari.
Dazai saka wanda a ke sokewa a gefen kugu sai yayi dawani salon daya sakani zabira saboda sak'onsa yajemin har kwalwar kai, ya d'ago ya kalleni yana wani miskilin murmushi da d'agamin gira. Sai kawai na lumshe ido dan naji kunya wlhy. Ya mik'e tsaye yana daidaitamin na kafad'ar shima, nidai harya gama ban bud'e idoba. baiyi magana ba ya warware reborn d'in kaina, da sauri na bud'e idon, yanda yawani tsareni da idanu sai nakasa jurewa na maida na rufe.
Cumb ya d'auka yahau gyaran kai, to nikma naga abinda yafi k'arfina yau d'innan, wai dama guy d'innan ya iya abin mata ne?. Bai barni ba saida ya gama yanda yakeso dani, ya zubamin ido kawai batareda yace komai ba. nikuma nakasa bud'e idona na kallesa, ahankali yafara busamin iskar bakinsa saman idona, dole nafara marmar da idanu, dainawa yayi, na bud'e idon ahankali a kansa, kuma matsoni yayi muka Zuba juna ido ko k'yaftawa bamayi, gashin dake neman shigarmin ido ya saka d'an yatsa ya matsar, na maida idanun na lumshe ina sauke k'aramar ajiyar zuciya.
Shima nannauyan numfashi ya sauke kafin yaja da baya, wardrobe d'insa ya nufa, jin yabar wajen saina bud'e idona, duk jikina ya saki, kallo d'aya namasa na d'auke kaina na juya ga mirror Dan naga yanda ya maidani, murmushi nayi ina saka hannu na gyara gashina, nima na yarda da gaske nayi kyau.
Nakuma d'ago ido da nufin sake kallon kaina sainaganshi a bayana, sark'a ya ziro a ya sakamin tareda gyara zamanta ta zauna sosai a k'irjina, ya janye gashina ta baya yana sak'ala sark'ar, nidai nawa idone, ya gama ya cire d'an kunen dake kunnena ya sakamin na sark'ar, sannan ya mannani da jikinsa yana zagayo hannunsa duk biyu saman matashin cikina, hannuna ya kama yana sakamin bangles, cikin k'asaitacciyar muryarnan tasa yake magana cikin kunnena, “haka dama sari kema Afirikawa k'yau?”.
Murmushi nayi, na d'ago idona muna kallon juna ta cikin mirror, haryanzu hannayena na cikin nasa yana saka bangles d'in da guda d'ai-d'ai.
Ya lumshe idanu yana shanshanar wuyana, jikina yafara rawa, babu shiri na saka hannuna d'aya daya gama saka bangles d'in na shafo gefen kumatunsa, cikin rawar murya nace “please kabari yalla6ai”.
Batareda ya dainaba cikin sark'ewar harshe yace “mizaisa na daina? yalla6iya”.
Yanda yake min akan dokin wiya da yanda hannunsa d'aya ke canja salo a jikina sainayi k'ok'arin juyowa garesa, ko hakan zaisa yabari d'in. Ashe dama ma na sake bashi, gaba d'aya yawani rikice kamar ba Galadiman Dana saniba. Hannunsa ya sak'alo kuguna yana kuma matsoni jikinsa sosai, yasaka d'ayan hannun ya tallafo kaina tareda d'ora la66ansa akan nawa.
Kasa jurewa nayi, na mik'a masa wuya kawai, harda bada gunmawa nima........
Tofa munga idi, daga gyaran sari🙆🏽😹.
Samha tataho da karsashinta dantaga ko Munaya ta saka, daga nan ta nuna mata yanda zata nad'a zanin sarin, tunda tasan bata iyaba, ko kad'an babu Wanda yaga shigowar Galadima, Dan babu kowa a falon, jakadiya ta tafi asibiti itada Sauban da innarsu munaya, aunty Mimi kuma barci takeyi, Dady kam yanacan baya inda ya maida lambun tunaninsa, itako Samha tana bama Munaya sari takoma d'aki danta bata lokaci ta shirya a tsanake. Sallama d'aya kawai tayi ta turo k'ofar tana kwala kiran “Aunty gimbiyarmu kin saka?”.
Galadima dayake Neman fara zirmawa yay hanzarin sakin Munaya, da sauri naja baya nima, dan kamar a sama mukaji muryar Samha.
Itama Samha baya ta koma da sauri gabanta na fad'uwa, Dan ganin Wanda batayi zatoba a d'akin. ALLAH ma yaso bataga komaiba, lokacin datake sako k'afarta a d'akin Galadima ya janye bakinsa yana k'ok'arin matsawane baya.
Wata uwar harara mai kad'a hanji da hanta ya zubama Samha, hakanne yasakata yin baya da sauri ta koma.
Nikam kasama d'aga ido nayi balle na kalleshi dagashi har Samhar, saima wani yaam nakejin jikina tamkar zan fad'i.
Lura da hakan da yayine yasakashi azamar rik'o hannuna, na shige jikinsa ina sauke tagwayen ajiyar zuciya, dagani harshi idanu kowa ya lumshe, tsawon lokaci muna a haka munkasa sakin juna, ahankali na shiga k'ok'arin janye jikina, bai hananiba yabani damar barin jikinsa, ra6awa nayi ta gefensa na wuce, na koma saman sofa na zauna ina dafe kai, juyowa yayi yana kallona, kafin yatako shima zuwa bakin gado ya kwanta, k'afafunsa na k'asa duka, yayinda yay filo da hannayensa yana lumshe idanu.
Duk munyi shiru d'akin tamkar babu wata halitta mai numfashi a cikinsa, kowannenmu shiyasan mi yake sak'ama zuciyarsa.
K'arar wayarsace ta sakamu d'an firgita mu duka, duk sai muka zubama wayar ido tamkar wani ojuju. harta tsinke bai d'aukaba, saida aka sake kira sannan ya cirota daga aljihun wandonsa yay picking.
Muryarsa vary low yace, “Nuren Yaya dai?”.
Mamaki da al'ajabi ya cika Nuren, yakuma Ciro wayar daga kunnensa ya duba Dan tabbatar da Galadima ne kuwa?, lallai shine, maida wayar yayi a kunne yana fad'in “brother lafiyarka kuwa?”.
Taune lips nashi yayi, ya yanke wayar, dan indai ahaka zasuyi wayarnan bazai fahimci komaiba, ajiye wayar yayi yatashi ya shige bathroom.
Da kallo k'asa-k'asa kawai na iya binsa, amma nakasa ko kwakwkwaran numfashi.
Daga can kuwa Nuren kwashewa yayi da dariya saboda tuno wani Abu, (to su Nuren dai dama bariki sune manyanta🤣), dariya yakeyi iya iyawa yana dukan kansa, daya fara tsagaitawa saiya kuma saka wata, saida yayi ta ishesa sannan ya daina, ya rik'e ha6a yana fad'in “oh ni su brother ansan takan tsiya, ina ganinsa lab-lab Ashe d'anba sauk'ine, toma uwar miye na d'agamin wayar tunda yasan yafara sauka a network🤣, yakuma saka dariya saikace wani sabon kamu.😬
Galadima kam ruwa ya sakarma kansa kawai, ya dafe bango da hannu biyu ruwan na kwarara saman kansa, sai faman taune lips yakeyi shi kad'ai, yayi da zuciyarsa ke sak'awa da kwancewa, saida ya ji k'arfi-k'arfi sannan ya kashe shower d'in yaja bathrobe d'in ya saka yana faman sauke 6oyayyar ajiyar zuciya.
Inda yabarta anan ya fito ya isketa, kallo d'aya yamata ya d'aukekai, bakin gadon ya zauna yana goge kansa da k'aramin towel, yajawo wayar da d'ayan hannun ya danna kiran Nuren.
Bugu d'aya Nuren d'in ya d'aga, da k'yar yasamu ya danne dariyarsa, “brother wai miya farune naji muryarka haka? nifa ka tadamin hankali”.
“Ba komai, shin kajene?”.
Nuren ya toshe bakinsa gudun kar dariya ta kufce masa, Sameer d'an rainin wayone ALLAH, wai babu komai, to naji babu komai aje a haka.
“wai kana jina kuwa?”. Galadima yafad'a.
“Oh sorry brother network nayin wasa, gani a gidan, amma bankai ga shiga inda takebane”.
“ok tom kaje, amma kabar wayar a kunne, inason naji komai”.
Nuren yace “to”.
Da sallama ya shiga d'akin, sai wani ciccin magani yake.
Farhat dake zaune bakin gadon d'akin ta zabga tagumi ta d'ago kai tana kallonsa, yayin da wasu hawaye ke shirin zubo mata.
Kujera guda d'aya dake d'akin ya jawo ya zauna.
Farhat ta share hawayen kumatunta, murya a sanyaye tace, “yayana dan ALLAH kayi hak'uri, wlhy ina missing d'in families d'ina da karatuna, dan ALLAH idan kasheni zakayi ka kasheni kawai na hutama rayuwa ma ni gaba d'aya”.
Murmushi Nuren yayi, idonsa a kanta yace, “bazan kashekiba Farhat, dan bakimin komaiba, kamar yanda na sanarmiki mahaifinkine yaja miki, ki kwantar da hankalinki, insha ALLAH zaki koma gidanku kwana kusa, yanzuma dukba wannanba, wata tambaya nazo yimiki, ALLAH yasa zaki bani had'in kai?”.
Kanta ta jinjina masa tana kuma share sauran hawayen, “insha ALLAH inhar nasani zan fad'a maka”.
“good girl ”. ‘cewar Nuren yana gyara zama’.
“Farhat nasan kinsan duk yaran Abbanki ko?, ina nufin masu masa hidima a office ko a gida?”.
“Eh nasan mafi yawansu, dan ina zuwa wajensa a Office, kuma wasu acikinsu sukanzo gidanma”.
“Masha ALLAH, kokin san SD?”.
“SD!?”.
“eh shi”.
“gaskiya a yaran Abbana dana sani babu wani mai suna SD”.
“okay, amma ko wani mai Something sunan dazai iya kasancewa full name bazaki iya hasasowa ba?”.
Shiru tayi ta lula duniyar nazari, shidai Nuren ya zauna mata idanu yana kuma jinjina ma ubangiji akan yin k'yak'yk'yawar hallita, dan Farhat black beauty ce masha ALLAH.
A jiyar zuciya ta sauke, “yaya inaga kamar dai akwai wani Sagir dauda dana Sani, amma bansan aikin da yake a k'ark'ashin Abbanmu ba, sai kuma ya Shareffudden k'anin Aunty Umma, sai Steven Daniel”.
“shi Steven d'in wanene shi a gidanku, itama Aunty Umman haka?”.
“Driver d'insu Mom ne, shike kaisu anguwa, ita kuma Aunty Umma matar Abbanmu ce ai, itace amaryarsa”.
“Uhyim”. Nuren yafad'a yana jinjina kai.
“Dan ALLAH yayana in tambayeka mana?”.
“ina saurarenki”.
“laifin mi Abbana yamuku hakane?”.
murmushi Nuren yayi, “karki damu nangaba kad'an komai zai wuce, kuma bashi yay laifinba, wanine yayi na kusa dashi”.
“to ALLAH yasa Ku kamashi, amma dan ALLAH karkuma Abbana komai”.
“insha ALLAH babie”.
Murmushi Farhat tayi, Nuren kuma ya mik'e tsaye idonsa a kanta. “babu dai wata Matsala ko?”.
Cikin shagwa6ar data saba tace, “please ko TV ka samin, banajin dad'in zaman hakanan”.
“Am sorry to say dear, har kibar gidannan dokace, babu television, babu phones, amma way not nakawo miki irin Hausa novels d'innan danaga mata na karantawa?”.
Idonta ya cika da kwalla, “ayya yayana wlhy ban iya karatun hausaba sosai, yana bani wahala”.
Ido yad'an zaro waje, yace, “saboda mi? Keba bahaushiya bacene?”.
“bahausa mana”. ‘tafad'a cikin turo bani irinnan ta6ararru’.
Baki ya ta6e yana kama hanyar fita, “zaki cigaba da kad'aicinki ashe kuwa”.
Ganin zai fice da sauri tace, “please ka siyo zan fara koya to”.
“it's better”. ‘yafad'a yana ficewarsa’.
Saman gadon ta fad'a ta fashe da kuma mai ban tausayi.
Duk abinda ke faruwa Galadima najin komai ta waya, Munaya ma na zauna a sofa har yanzu tana satar kallonsa, amma batajin miyake saurare da ya nutsu haka.
Cire wayar yafara k'ok'arin yi ya jiyo muryar Nuren na fad'in “hello brother kana jina?”.
Galadima yace, “eh”.
“okay duk kaji aimi ta fad'a ko?”.
“duk najiku, saika samin ido akan duk d'unsu, a bincikomin komai daya shafesu”.
“indai wannanne insha ALLAH angama, amma ni a ganina banda wannan Shareffuden d'in datace, domin babu wani kamanni a cikin nashi sunan, ballema tace k'anin step mom natane”.
“Humm Nuredeen kenan, shifa mak'iyi ba'a rainashi, mutane da yawa sukan d'auki cinnaka ba komaiba, amma idan yacijesu sukan ji cizon har a ransu, dan haka karka ta6a d'aukar mage mafi sauk'i akan kare, itama idan taga nama citakeyi”.
“wannan gaskiyane brother, ALLAH yabamu sa'a”.
“amin ya rabbi, naji kuna maganar buks da ita, kaje ka samo mata dukkan Wanda take buk'ata, har English novels d'in, sannan ak'ara tanadar mata dukkan abinci mai k'yau datake so”.
“insha ALLAH angon Munaya”.
Girgiza kai kawai Galadima yayi ya yanke wayar.
Kallon Munaya yayi suka had'a ido, saita janye cikeda basarwa. Shima tashi yayi ya koma gaban mirror, duk uzirinsa yayi ya gama sannan yamatsa ga wardrobe ya ciro kayan dayake buk'ata.
Ganin haka Munaya tazame ta kwanta cikin kujerar yandama bazata gansaba.
Baki kawai ya ta6e yacigaba da saka kayansa.
Bayan yagama yamatsa kusada ita, “tashi ki canja kaya ki rakani wani waje”.
Fuska Munaya tad'an yatsina, kamar zatace wani Abu saikuma ta yunk'ura zata tashi kawai, hannunta ya kama ya taimaka mata ta tashi zaune. fita yayi abinsa. Hakan yasata fahimtar zai jirata a falo kenan.
Bata 6ata lokaciba ta canja kayanta da atanfa skt da riga, takawo after dress ta saka sannan ta nad'a Vail d'in rigar, d'as ta fito itada cikinta, kamar ka saceta ka gudu abinka.
Tunda ta fito ya zuba mata idanu, ko k'yaftawa bayayi, saida yaga tana gabda k'arasowa garesa ya basar yana mik'ewa. Gaba yayi tabisa abaya, yandama yake taka steps d'in benen dolene ya birgeka, duk takunsa nakan idonta, yayinda itama take binsa daki-daki a hankali.
Babu kowa a falon, dan haka suka fice basu nemi kowanba.
A mota yana tuk'i da sauraren karatu itakuma tana latsa waya suna charts a families group d'insu. Sai murmushi take zubawa, duk abinda take yana kallonta ta gefen ido. Sun isa wani k'aton shagon saida kayan babies, duk abinda kake buk'ata zaka sameshi indai na yarane daga 1year zuwa 15. Itadai mamaki ya ishi Munaya, miye nawani kawota nan? yabari a haihun mana ma.
Tarba ta musamman aka musu, hakan ya tabbatar ma Munaya yasan mai shagon kenan, dan yanda aketa girmamasu sai abin ke bata mamaki. gashi indiyanci sukeyi bata fahimtar maganganunsu. Itadai tana zaune hankalinta ya rabu gida biyu, wajensu Galadima da kuma wasu mata biyu da yaransu uku dabazasu wuce 7-7years ba, yaran k'yawawa masha ALLAH, ga wayo.
Galadima ya juyo zai mata magana saiya lura da inda ta zubama idanu, shima shagala yay a kallon yaran, iyayensu na za6ar kaya amma su suna tibirewa sai Wanda sukeso za'a d'auka. Munaya sai zuba murmushi takeyi, dan suntafi da imaninta, shima murmusawa yayi yana lasar lips, kafin ya d'auke kansa ya maida ga Wanda suke maganar.
Zuwa can gardama ta hark'ume tsakanin yaran akan wani game da iyayen ke dubawa maybe zasu saya musu ne. Kuma games d'in suna kusada Munaya ne, d'aya a cikin yaran ya d'akko yazo wajen Munaya yana tambayarta wai “Aunty wannan yafi dad'i aidai ko?”.
Munaya bata fahimceshiba, dan yayi maganane da yaren dabata ji, dan haka saitayi murmushi ta tambayesa yanajin English?.
Yaron ya d'aga mata kai alamar eh.
Ta kuma murmusawa, duk abinda ke faruwa a idon Galadima ne.
Da turanci munaya tace, “yarona kai kata6a irin wannan game d'inne?”.
Murmushi yamata shima, yace “aunty akwai dad'i ma sosai, ranar saida na cinye kharan a gidansu ma”.
“da gaske?”. munaya tafad'a tana dafa kafad'arsa.
Kansa ya d'aga mata, cike da d'oki yace, “Aunty na koya miki?”.
Munaya ta d'aga masa kai.
Game d'in ya d'ora a cinyarta, ya danna wasu Number, sai kuma ya zubasu cikin d'aya, duk suka shige. Cikin mamaki munaya tace “mikenan to?”.
Shima dariyarsu ta yara yayi, yace “Aunty ai wayo na miki, Abu guda d'ayane, amma sainayi ammafani da numbers daban-daban, kuma kowanne a cikinsu aiki d'aya yayi na canja da wani, kekuma zakiga kamar na had'a daban-dabanne, kuma kowanne da aikinsa, amma aiki d'aya ne na had'aka kuma akan Abu guda d'aya kacal”.
Sosai abun ya birge munaya, tayi dariya har hak'oranta na bayyana, jawo yaron tayi a jikinta ta rungume.
Iyayensa dake tsaye suna kallonsu tun d'azun duk sukayi dariya suma, sannan suka matsa kusada munaya suna bata hannu alamar gaisuwa. itama ta mik'a musu suka gaisa, d'aya tace sunanta Radha, d'ayar kuma tace Anjali, munaya ta fad'a musu nata suna itama, sannan takamo hannun saran yaran tana tambayarsu suma, d'aya yace vanish, d'ayan kuma Anjun, duk kumatunsu ta sumbata tana sakama rayuwarsu albarka.
Wadda tace sunanta Radha tace “kiyi hak'uri da surutun Vishnu shi baya gajiyane ko kad'an”.
Munaya tace babu komai.
Daganan sukai gaba, munaya tana binsu da kallo tana murmushi, yaran sai waigenta suke suna d'aga mata hannu.
Sunje wajen biyan kud'i akace subar kud'insu inji mai shagon, da mamaki suka tambayi wanene? Mikuma yasa ya barmusu.
Mai kar6ar kud'i ya murmusawa yana fad'in mijin matarcan da kuka gaisane mai shagon ai.
Munaya batasan mike faruwaba taga sun dawo, godiya suka shiga yimata, ta tambayesu akan me?.
Suka bata amsa da cewar mijinta bai kar6i kud'in kayansu ba. Murmushi tayi, k'asan ranta tana mamakin dama shagon na Galadima ne?.
Sun katse mata tunani da tambayar kozasu samu number ta, babu musu tabasu sukayi sallama suka tafi.
Maida kallonta tayi ga Galadima dake zaune yanata latse-latsen laptop tamkar baisan mike faruwaba, da alama yana duba kayane ko wani Abu, dan time to time Wanda yake gefensa yakan nuna masa wani yanki na kayan dake shagon, shikuma ya waiga ya kalla, idan bai hango sosaiba saiya kalla ta cikin Computer d'in dake tareda cctv cameras d'in shagon.
Munaya tace kai mutuminnan akwai son kud'in tsiya, kai komai kana saidawa, wata zuciya tace idan bai nemi kud'iba dame zai kula da mahaifinsa?. “hakane kuma”. ta fad'a a fili tana sauke ajiyar zuciya.
Kusan mintuna 15 saitaga ya taso ya nufota. Zama yay kujerar kusa da ita yana fad'in “sorry friend na barki ke kad'ai. kin gaji mu tafi ko?”.
Munaya tad'an yamutsa fuska tace “ba sosaiba”.
Ya d'an murmusa, “ok tunda baki gajiba kozaki d'an mana taimako ni da abin cikin kwan?”.
Hararsa tad'anyi, itafa haushin wannan abin cikin kwan dayake fad'a takeji.
Hannu yasa ya dafe bakinsa yana fad'in “maida wuk'ar”.
A tare suka dinga zagayawa cikin shagon, dayake babbane sosai, kayan yarane kuma zalla a wajen, komai bibbiyu take d'auka, baice komaiba, dan yasan dai bai wuce tana had'awa da cikin 'Yar uwarta Munubiya bane. Sund'an d'iba kaya babu laifi, yabada ATM d'insa aka d'auka harda na wad'ancan matan, yaran shagonne suka kai musu har cikin mota.
Yanzuma haka suka taho tamkar kurame.
Kowa da abinda yake sak'awa....
Danja data tsayar damune yasakashi juyowa yad'an kalleni, ganin hankalina nakan wasu yara 'yan makaranta dake mota yace, “dama haka kike da son yara?”.
Juyowa nayi Na kalleshi, amma saiya d'auke kai tamkar bashine yay maganarba ma.
Nima maida kaina nayi ga yaran, a kuma time d'inne muka sami damar barin wajen.
Saida muka fara tafiya nabashi amsa da “yalla6ai kenan, waye zaice baison yaro, a duniya babu abinda yafi k'uruciya dad'i”.
Kad'an ya juyo yad'an kalleni yana fad'in “really?”.
Nima kallon nasa nayi ina fad'in “na tabbata amsarnan kowama zai baka idan ka tambayesa”.
Bai kalleniba yanzun kam, hankalinsa naga tuk'insa, yace, “ALLAH ya kawoka duniya lafiya abin cikin kwan”.
“shiru namasa bance uffanba”.
Har muka isa gida kuma babu Wanda ya sake magana a cikinmu. Saida yay parking motar a harabar gidan sannan ya juyo gareni, ina niyyar bud'ewa Na fita ya ruk'o hannuna. kallonsa nayi da mamaki, yawani ci magani irin babu raininnan, kamar zanyi magana saikuma nayi shiru muka zubama juna ido, kowannenmu zuciyarsa Na bugawa da sauri-sauri. Cikin k'asaitarnan tasa yace, “Addu'a nayi amma jan aji yahanaki amsamin da amin”.
Ni dariyama ya bani wai jan aji, hakanne yasakani murmusawa kad'an ina k'ok'arin janye idona daga cikin nasa, amma saiya hanani hakan, nace, “na amsa ai, bakaji bane kawai”.
“aiba kurma kika auraba”.
Uhm wannan aure ana tak'ama dashi, Na fad'a a raina, a fili kuma nace, “a zuciya Na amsa”.
“k'arya haramun, banji wannan sak'onba a tawa zuciyar”.
Da mamaki Na waro idanu waje ina fad'in “ban fahimceka ba”.
Lips d'insa yad'an ciza da hak'ora yana matsoda fuskarsa dab da tawa, gashi ya sark'eni da idanu nakasa matsawa, d'an yatsansa ya d'ora saitin zuciyata, muryarsa k'asa-k'asa tamkar mai rad'a yace, “zuciyoyi aminan juna sukan kar6i sak'on juna alokacinda d'aya ya aikashi ga d'aya, karki jahilci kanki har yanzu akwai sauran dama”.....
Yana gama fad'a ya saki hannuna, tareda bud'e motar ya fice.
Galala nabisa da kallo tamkar wata sokuwa, nakasa motsi nakasa fassara zantukansa da ma'anarsu.
Tsawon mintunan dahar bayin gidan sungama kwashe kayan da mukazo dasu ban fitoba, bud'ewa naji anyi, hannunsa kawai ya mik'omin alamar nakama Na fito. tamkar sokuwa haka Na d'ora hannun cikin nasa, ya kamoni ahankali Na fito, maimakon ya sakeni saiya jawoni Na shige jikinsa, ya d'ora kansa a dokin wuyana, cikin kunnena yace “wasu bayanan basa buk'atar fassara, ayanda sukazo ahaka ake barinsu, karki zurfafa tunani, dan yana kawo ciwon kai da hana Hutu”.
Ya d'ago kaina tareda janye jikinsa yana d'agamin gira da salute d'ina, ya juya zuwa cikin gida.
Binsa kawai nakeyi a baya tamkar kazar da kwai ya fashema a ciki.
A falo muka iske duka ahalin gidan, har Momma dazata kwana yau a gida, Abba ne kawai babu, muduka sun birgemu, Dan hira suke ta nishad'i da girmama juna.
Dagani harshi gaishesu mukayi, Sauban da Samha dasuka k'arasa da kayanda da bayi suka shigo dasu suka sakko daga samanmu suna mana sannu da zuwa.
Ni kad'ai Na amsa, Galadima hannu kawai ya d'aga musu.
Momma tace, “kuje ku huta mana”.
mik'ewa mukayi duk a kunyace, ina gaba a yanzu yana baya, suduka da kallon sha'awa suka bimu, dad'i da farinciki Na ratsa zukatansu, innarmu harda kwalla suka cika idonta, Wanda ita kad'ai tasan fasaarar kayanta.
★★★★★★★
Da daddare Galadima Na zaune akan sofa ya d'aura k'afafunsa saman teble yana latsa laptop, yayinda Munaya ke zaune a tsakkiyar gado tana karatun wani English novel na Galadima, buk d'in love story ne dan haka taketa faman zabga murmushi, lokaci-lokaci yakan d'ago ido ya kalleta, saboda idan tayi murmushi yakan jiyo sautinsa.
Maida kansa yayi, yacigaba da aikinsa dayakeyi akan numbers d'in layin Abba na sirri, kwatsam sai maganar yaron d'azu na shago mai suna Vishnu ta fad'o masa a rai.
*_Aunty ai wayo na miki, Abu guda d'aya ne, amma sainayi amfani da numbers daban-daban, kuma kowanne a cikinsu aiki d'aya yayi na canja da wani, kekuma zakiga kamar na had'a daban-dabanne, kuma kowanne da aikinsa, amma aiki d'aya ne na had'aka kuma akan Abu guda d'aya kacal._*
Saida yakuma maimaita maganar kusan sau uku a ransa, kafin ya kalli Munaya da dukkan hankalinta ke kan Novel,
“Friend!”.
Ya kirata a nutse.
Da “na'am” Na amsa ina kallonsa, saikuma Na janye saboda wandon jikinsa baiko rufe masa cinyaba, sai k'aramar riga mara hannu.
Yace, “mikika fahimta ga zancen abokinki na shago?”.
“abokina? waye abokina?”.
Tasowa yayi dagashi har laptop d'in da coffee d'insa ya hawo gadon, nima saina tashi zaune sosai.
Ya zauna ta gefe tareda ajiye mug d'in hannunsa a drowa d'in gefen gadon, laptop d'in kuma a saman gadon d'ayan gefensa. hannu ya mik'amin alamar nazo.
Ban musa masaba Na matso, ya kamoni ya sakani a jikinsa, dan tsakkiyar k'afafunsa ya sakani, saina zame Na kwanta na d'ora kaina a cinyarsa, (dama wajen lak'ewa nake nema🤪).
Ya kar6i buk d'in hannuna ya ajiye gefe, ya d'ora hannunsa a saman cikina.
Kuma maimaita masa tambayar nayi.
Ya shafa sajensa yana cije lips, “miyasa wataran kike da basarwa”..
“ni d'in?”. ‘nafad'a ina nuna kaina da kallonsa’.
Bai bani amsaba yace “ina nufin yaron d'azun”.
“Oh sorry”. nafad'a ina gyara kwanciyat.
Nace, “wai Vishnu? ”.
Kansa ya d'aga min
“to amma wace maganace tasa? tazama abin nazari yalla6ai?”.
“game”.
“game! game!” nashiga fad'a ina k'ok'arin tunanowa.
“okay, wai yanda yafad'i yaci game d'in?”.
“Uhhm”. ya fad'a a tak'aice..
Nikuma saina murmusa, “to dukda dai bansan ma'anar d'aukar maganar da muhimmanciba amma anawa tunanin yana nufin _abinnan mabanbantane, amma saiyayi amfani dasu cikin Abu d'aya, kuma sukai masa aiki iri d'aya, sannan duk shi kad'ai ya sarrafasu akan Abu d'aya bawai yayi tarayyar da wasu mutane da yawa bane ko aikinsa had'aka,_ wannan itace fahimta ta ga zancen nasa”.
Lumshe ido Galadima yayi, ya duk'o a hankali ya mannamin Sumba mai k'au a goshi. Sannan ya d'akko novel d'in ya damk'amin a hannu, yajawo laptop d'insa yacigaba da aikinsa.
Kallon mamaki kawai na zuba masa, kokad'an ban fahimci muhallin maganar tasaba da son fashin bak'i.
Batareda ya kalleni ba, idonsa akan system d'insa yace, “kallonfa?”.
Janye idona nayi ina ta6e baki.
Shima saiya ta6e nasa alamar yaganni kenan. karatuna nacigaba shima yacigaba da aikinsa yana shan coffee time to time.
Yayi aiki mai tsawo kafin yasaki wani murmushi da ajiyar zuciya, ya kalli munaya da barci ya kwashe, fuskarta ya shafa yana kuma sakin wani murmushin, “tabbas gaskiya Vishnu ya fad'a, mutum d'ayane ke amfani da Numbers daban-daban wajen kiran Abba munaya, duk wadda yagama da ita bazai sakeba, tagama aikinta, a wannan karon lallai kunyi aiki da basira, wadda harta birkita tunanin Sameer, kuna kiran Abba da mabanbanta Numbers wad'anda kunrigada kun gama shirya matakan da kowacce number bazata sake aikiba, shima kansa ya d'auka mutane daban-dabanne ke kiransa. O ALLAH wannan shine bada k'afa, to ai inkunsan wata bakusan wataba kuma, Muhammad Sameer ruwane, idan bakasha yanzuba zakasha anjima, idan kak'i kuma k'ishirwa ta kasheka. Inhar tarkon dazan d'ana zai d'annu dai-dai, tabbas zan cafke kurayen daji mai duhuwa a wannan karon”. ‘Ya k'are maganar da jan hancin munaya yana kuma sumbatar goshinta’.
Kwanciya ya gyara mata sosai, ya ja bargo ya lullu6a mata sannan yaje bayi ya d'auro alwala, kamar yanda ya saba ya raya wannan dare da nafilfili da godiyar ALLAH, kafin yazo ya kwanta gefen munaya zuciyarsa na cike da annashuwa da farinciki, kaikace komai yayi done ne.
Addu'a ya musu sannan yasakata jikinsa barci ya Lula dashi shima.
Nima mai d'aukar rahoto bara nad'an rintsa my sweet sisters😉🤩......................✍🏻
Duk Wanda yaga ban amsa massage nashiba yamin afuwa, nayi up date WhatsApp d'inane🥰🥰🥰🤝🏻
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu👏🏻😭_**_typing📲_*
💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._*
0 comments:
Post a Comment