Na dad'e ina barci kafin Na tashi, nayi mamakin ganina ni kad'ai, bansan time d'in da Galadima ya ficeba, sakkowa nayi daga gadon Na nufi Na watsa ruwa.
Ina tsaka da shafa mai Samha ta shigo, saida tayi sallama nabata izinin shigowa sannan, ledar hannunta Na kalla ina fad'in “mikika samo mana 'Yar Uncle?”.
Cikin dariya ta zauna kan sofa tana cewa “kayan dad'i ne Aunty gimbiyarmu, alfarma nazo nema wajenki keda Uncle”.
Hankalina gaba d'aya Na maido kanta, “Alfarmar mi kuma?”.
“Aunty gimbiya please ki lalla6a Uncle ya barki muje birthday d'in k'awata Dhibya, ALLAH yarinyarnan tana sonki sosai, kullum hirarki”.
Nad'an zaro ido “kai Samha yaza ai naje wani birthday da wannan cikin? kuma kema kinsan bazai bariba tunda Na 'yammatane”.
“kai aunty, cikin saikace Wanda yayi wani k'ato, kumafa a cikin gida za'ayi wlhy, iyamu goma ne kawai”.
“to naji, ALLAH yasa ya bari, mikika kawo mana a ledar?”.
“yes my sweet aunty, wannan wani sari ne yamin k'yau a wani shagon da muke zuwa siyan kaya, shine nayi alk'awarin siya miki, Uncle Sauban ya cikamin na siya, yanzu Na kar6o please ki gwada muga”.
Dariya nayi, nace, “inye kaga 'Yar Uncle Anfara jink'an iyaye, to amma ni ina na iya saka sari?”.
“kowama koya yayi nidai ki saka muga dan ALLAH”.
“to shike nan bara na gwada, ALLAH ya saka da alkairi, ina alfahari da d'iyata”.
Samha ta fita tana dariya, nikuma na warware kayan, masha ALLAH sarin ya had'u gaskiya, farine anmasa kwalliya da pink and silver kad'an-kad'an. Na saka rigar, sai dariya ta kamani, saikace wata bafulatana🤭🤣.
Warware zanin nayi, tofa anan akeyinta, dan ban iya nad'awaba, na tsaya gaban mirror inata gwadawa amma na kasa, dariya ta kamani, yau naga takaina, Samha ta had'ani da aiki.
Tunda ta fara k'ok'arin d'aura zanin sarin yana tsaye a k'ofa, ya hard'e hannayensa ak'irji kawai yana kallonta, kamar zaiyi dariya saboda yanda taketa murd'e-murd'en d'aurawa.
A hankali ya taka zuwa inda take, jinai kawai andafa min kafad'u ta baya, na d'ago a tsorace muka had'a ido ta cikin mirror, fuskarsa babu walwala, ya d'agamin gira d'aya, maida idona k'asa nayi, yayinda shikuma ya juyo dani ina fuskantarsa.
Gwiwarsa d'aya ya saka a k'asa ya dogare d'aya, nidai kallonsa nake mizaiyi?. Batareda ya kalleni ko min magana ba ya zare zanin dake tattare a hannuna, nikam kamar wata sokuwa saina sakar masa.
Yiyay kamar zai warware zanin, nayi saurin rik'ewa, ya d'ago fararen idanunsa yanamin alamar na saki, ban iya musa masaba na sakar masa.
Shima sai bai yaye dukaba ya dai-daitashi, ammakina sainaga yana nad'amin, babbar magana Galadima da nad'a sari.
Dazai saka wanda a ke sokewa a gefen kugu sai yayi dawani salon daya sakani zabira saboda sak'onsa yajemin har kwalwar kai, ya d'ago ya kalleni yana wani miskilin murmushi da d'agamin gira. Sai kawai na lumshe ido dan naji kunya wlhy. Ya mik'e tsaye yana daidaitamin na kafad'ar shima, nidai harya gama ban bud'e idoba. baiyi magana ba ya warware reborn d'in kaina, da sauri na bud'e idon, yanda yawani tsareni da idanu sai nakasa jurewa na maida na rufe.
Cumb ya d'auka yahau gyaran kai, to nikma naga abinda yafi k'arfina yau d'innan, wai dama guy d'innan ya iya abin mata ne?. Bai barni ba saida ya gama yanda yakeso dani, ya zubamin ido kawai batareda yace komai ba. nikuma nakasa bud'e idona na kallesa, ahankali yafara busamin iskar bakinsa saman idona, dole nafara marmar da idanu, dainawa yayi, na bud'e idon ahankali a kansa, kuma matsoni yayi muka Zuba juna ido ko k'yaftawa bamayi, gashin dake neman shigarmin ido ya saka d'an yatsa ya matsar, na maida idanun na lumshe ina sauke k'aramar ajiyar zuciya.
Shima nannauyan numfashi ya sauke kafin yaja da baya, wardrobe d'insa ya nufa, jin yabar wajen saina bud'e idona, duk jikina ya saki, kallo d'aya namasa na d'auke kaina na juya ga mirror Dan naga yanda ya maidani, murmushi nayi ina saka hannu na gyara gashina, nima na yarda da gaske nayi kyau.
Nakuma d'ago ido da nufin sake kallon kaina sainaganshi a bayana, sark'a ya ziro a ya sakamin tareda gyara zamanta ta zauna sosai a k'irjina, ya janye gashina ta baya yana sak'ala sark'ar, nidai nawa idone, ya gama ya cire d'an kunen dake kunnena ya sakamin na sark'ar, sannan ya mannani da jikinsa yana zagayo hannunsa duk biyu saman matashin cikina, hannuna ya kama yana sakamin bangles, cikin k'asaitacciyar muryarnan tasa yake magana cikin kunnena, “haka dama sari kema Afirikawa k'yau?”.
Murmushi nayi, na d'ago idona muna kallon juna ta cikin mirror, haryanzu hannayena na cikin nasa yana saka bangles d'in da guda d'ai-d'ai.
Ya lumshe idanu yana shanshanar wuyana, jikina yafara rawa, babu shiri na saka hannuna d'aya daya gama saka bangles d'in na shafo gefen kumatunsa, cikin rawar murya nace “please kabari yalla6ai”.
Batareda ya dainaba cikin sark'ewar harshe yace “mizaisa na daina? yalla6iya”.
Yanda yake min akan dokin wiya da yanda hannunsa d'aya ke canja salo a jikina sainayi k'ok'arin juyowa garesa, ko hakan zaisa yabari d'in. Ashe dama ma na sake bashi, gaba d'aya yawani rikice kamar ba Galadiman Dana saniba. Hannunsa ya sak'alo kuguna yana kuma matsoni jikinsa sosai, yasaka d'ayan hannun ya tallafo kaina tareda d'ora la66ansa akan nawa.
Kasa jurewa nayi, na mik'a masa wuya kawai, harda bada gunmawa nima........
Tofa munga idi, daga gyaran sari🙆🏽😹.
Samha tataho da karsashinta dantaga ko Munaya ta saka, daga nan ta nuna mata yanda zata nad'a zanin sarin, tunda tasan bata iyaba, ko kad'an babu Wanda yaga shigowar Galadima, Dan babu kowa a falon, jakadiya ta tafi asibiti itada Sauban da innarsu munaya, aunty Mimi kuma barci takeyi, Dady kam yanacan baya inda ya maida lambun tunaninsa, itako Samha tana bama Munaya sari takoma d'aki danta bata lokaci ta shirya a tsanake. Sallama d'aya kawai tayi ta turo k'ofar tana kwala kiran “Aunty gimbiyarmu kin saka?”.
Galadima dayake Neman fara zirmawa yay hanzarin sakin Munaya, da sauri naja baya nima, dan kamar a sama mukaji muryar Samha.
Itama Samha baya ta koma da sauri gabanta na fad'uwa, Dan ganin Wanda batayi zatoba a d'akin. ALLAH ma yaso bataga komaiba, lokacin datake sako k'afarta a d'akin Galadima ya janye bakinsa yana k'ok'arin matsawane baya.
Wata uwar harara mai kad'a hanji da hanta ya zubama Samha, hakanne yasakata yin baya da sauri ta koma.
Nikam kasama d'aga ido nayi balle na kalleshi dagashi har Samhar, saima wani yaam nakejin jikina tamkar zan fad'i.
Lura da hakan da yayine yasakashi azamar rik'o hannuna, na shige jikinsa ina sauke tagwayen ajiyar zuciya, dagani harshi idanu kowa ya lumshe, tsawon lokaci muna a haka munkasa sakin juna, ahankali na shiga k'ok'arin janye jikina, bai hananiba yabani damar barin jikinsa, ra6awa nayi ta gefensa na wuce, na koma saman sofa na zauna ina dafe kai, juyowa yayi yana kallona, kafin yatako shima zuwa bakin gado ya kwanta, k'afafunsa na k'asa duka, yayinda yay filo da hannayensa yana lumshe idanu.
Duk munyi shiru d'akin tamkar babu wata halitta mai numfashi a cikinsa, kowannenmu shiyasan mi yake sak'ama zuciyarsa.
K'arar wayarsace ta sakamu d'an firgita mu duka, duk sai muka zubama wayar ido tamkar wani ojuju. harta tsinke bai d'aukaba, saida aka sake kira sannan ya cirota daga aljihun wandonsa yay picking.
Muryarsa vary low yace, “Nuren Yaya dai?”.
Mamaki da al'ajabi ya cika Nuren, yakuma Ciro wayar daga kunnensa ya duba Dan tabbatar da Galadima ne kuwa?, lallai shine, maida wayar yayi a kunne yana fad'in “brother lafiyarka kuwa?”.
Taune lips nashi yayi, ya yanke wayar, dan indai ahaka zasuyi wayarnan bazai fahimci komaiba, ajiye wayar yayi yatashi ya shige bathroom.
Da kallo k'asa-k'asa kawai na iya binsa, amma nakasa ko kwakwkwaran numfashi.
Daga can kuwa Nuren kwashewa yayi da dariya saboda tuno wani Abu, (to su Nuren dai dama bariki sune manyanta🤣), dariya yakeyi iya iyawa yana dukan kansa, daya fara tsagaitawa saiya kuma saka wata, saida yayi ta ishesa sannan ya daina, ya rik'e ha6a yana fad'in “oh ni su brother ansan takan tsiya, ina ganinsa lab-lab Ashe d'anba sauk'ine, toma uwar miye na d'agamin wayar tunda yasan yafara sauka a network🤣, yakuma saka dariya saikace wani sabon kamu.😬
Galadima kam ruwa ya sakarma kansa kawai, ya dafe bango da hannu biyu ruwan na kwarara saman kansa, sai faman taune lips yakeyi shi kad'ai, yayi da zuciyarsa ke sak'awa da kwancewa, saida ya ji k'arfi-k'arfi sannan ya kashe shower d'in yaja bathrobe d'in ya saka yana faman sauke 6oyayyar ajiyar zuciya.
Inda yabarta anan ya fito ya isketa, kallo d'aya yamata ya d'aukekai, bakin gadon ya zauna yana goge kansa da k'aramin towel, yajawo wayar da d'ayan hannun ya danna kiran Nuren.
Bugu d'aya Nuren d'in ya d'aga, da k'yar yasamu ya danne dariyarsa, “brother wai miya farune naji muryarka haka? nifa ka tadamin hankali”.
“Ba komai, shin kajene?”.
Nuren ya toshe bakinsa gudun kar dariya ta kufce masa, Sameer d'an rainin wayone ALLAH, wai babu komai, to naji babu komai aje a haka.
“wai kana jina kuwa?”. Galadima yafad'a.
“Oh sorry brother network nayin wasa, gani a gidan, amma bankai ga shiga inda takebane”.
“ok tom kaje, amma kabar wayar a kunne, inason naji komai”.
Nuren yace “to”.
Da sallama ya shiga d'akin, sai wani ciccin magani yake.
Farhat dake zaune bakin gadon d'akin ta zabga tagumi ta d'ago kai tana kallonsa, yayin da wasu hawaye ke shirin zubo mata.
Kujera guda d'aya dake d'akin ya jawo ya zauna.
Farhat ta share hawayen kumatunta, murya a sanyaye tace, “yayana dan ALLAH kayi hak'uri, wlhy ina missing d'in families d'ina da karatuna, dan ALLAH idan kasheni zakayi ka kasheni kawai na hutama rayuwa ma ni gaba d'aya”.
Murmushi Nuren yayi, idonsa a kanta yace, “bazan kashekiba Farhat, dan bakimin komaiba, kamar yanda na sanarmiki mahaifinkine yaja miki, ki kwantar da hankalinki, insha ALLAH zaki koma gidanku kwana kusa, yanzuma dukba wannanba, wata tambaya nazo yimiki, ALLAH yasa zaki bani had'in kai?”.
Kanta ta jinjina masa tana kuma share sauran hawayen, “insha ALLAH inhar nasani zan fad'a maka”.
“good girl ”. ‘cewar Nuren yana gyara zama’.
“Farhat nasan kinsan duk yaran Abbanki ko?, ina nufin masu masa hidima a office ko a gida?”.
“Eh nasan mafi yawansu, dan ina zuwa wajensa a Office, kuma wasu acikinsu sukanzo gidanma”.
“Masha ALLAH, kokin san SD?”.
“SD!?”.
“eh shi”.
“gaskiya a yaran Abbana dana sani babu wani mai suna SD”.
“okay, amma ko wani mai Something sunan dazai iya kasancewa full name bazaki iya hasasowa ba?”.
Shiru tayi ta lula duniyar nazari, shidai Nuren ya zauna mata idanu yana kuma jinjina ma ubangiji akan yin k'yak'yk'yawar hallita, dan Farhat black beauty ce masha ALLAH.
A jiyar zuciya ta sauke, “yaya inaga kamar dai akwai wani Sagir dauda dana Sani, amma bansan aikin da yake a k'ark'ashin Abbanmu ba, sai kuma ya Shareffudden k'anin Aunty Umma, sai Steven Daniel”.
“shi Steven d'in wanene shi a gidanku, itama Aunty Umman haka?”.
“Driver d'insu Mom ne, shike kaisu anguwa, ita kuma Aunty Umma matar Abbanmu ce ai, itace amaryarsa”.
“Uhyim”. Nuren yafad'a yana jinjina kai.
“Dan ALLAH yayana in tambayeka mana?”.
“ina saurarenki”.
“laifin mi Abbana yamuku hakane?”.
murmushi Nuren yayi, “karki damu nangaba kad'an komai zai wuce, kuma bashi yay laifinba, wanine yayi na kusa dashi”.
“to ALLAH yasa Ku kamashi, amma dan ALLAH karkuma Abbana komai”.
“insha ALLAH babie”.
Murmushi Farhat tayi, Nuren kuma ya mik'e tsaye idonsa a kanta. “babu dai wata Matsala ko?”.
Cikin shagwa6ar data saba tace, “please ko TV ka samin, banajin dad'in zaman hakanan”.
“Am sorry to say dear, har kibar gidannan dokace, babu television, babu phones, amma way not nakawo miki irin Hausa novels d'innan danaga mata na karantawa?”.
Idonta ya cika da kwalla, “ayya yayana wlhy ban iya karatun hausaba sosai, yana bani wahala”.
Ido yad'an zaro waje, yace, “saboda mi? Keba bahaushiya bacene?”.
“bahausa mana”. ‘tafad'a cikin turo bani irinnan ta6ararru’.
Baki ya ta6e yana kama hanyar fita, “zaki cigaba da kad'aicinki ashe kuwa”.
Ganin zai fice da sauri tace, “please ka siyo zan fara koya to”.
“it's better”. ‘yafad'a yana ficewarsa’.
Saman gadon ta fad'a ta fashe da kuma mai ban tausayi.
Duk abinda ke faruwa Galadima najin komai ta waya, Munaya ma na zauna a sofa har yanzu tana satar kallonsa, amma batajin miyake saurare da ya nutsu haka.
Cire wayar yafara k'ok'arin yi ya jiyo muryar Nuren na fad'in “hello brother kana jina?”.
Galadima yace, “eh”.
“okay duk kaji aimi ta fad'a ko?”.
“duk najiku, saika samin ido akan duk d'unsu, a bincikomin komai daya shafesu”.
“indai wannanne insha ALLAH angama, amma ni a ganina banda wannan Shareffuden d'in datace, domin babu wani kamanni a cikin nashi sunan, ballema tace k'anin step mom natane”.
“Humm Nuredeen kenan, shifa mak'iyi ba'a rainashi, mutane da yawa sukan d'auki cinnaka ba komaiba, amma idan yacijesu sukan ji cizon har a ransu, dan haka karka ta6a d'aukar mage mafi sauk'i akan kare, itama idan taga nama citakeyi”.
“wannan gaskiyane brother, ALLAH yabamu sa'a”.
“amin ya rabbi, naji kuna maganar buks da ita, kaje ka samo mata dukkan Wanda take buk'ata, har English novels d'in, sannan ak'ara tanadar mata dukkan abinci mai k'yau datake so”.
“insha ALLAH angon Munaya”.
Girgiza kai kawai Galadima yayi ya yanke wayar.
Kallon Munaya yayi suka had'a ido, saita janye cikeda basarwa. Shima tashi yayi ya koma gaban mirror, duk uzirinsa yayi ya gama sannan yamatsa ga wardrobe ya ciro kayan dayake buk'ata.
Ganin haka Munaya tazame ta kwanta cikin kujerar yandama bazata gansaba.
Baki kawai ya ta6e yacigaba da saka kayansa.
Bayan yagama yamatsa kusada ita, “tashi ki canja kaya ki rakani wani waje”.
Fuska Munaya tad'an yatsina, kamar zatace wani Abu saikuma ta yunk'ura zata tashi kawai, hannunta ya kama ya taimaka mata ta tashi zaune. fita yayi abinsa. Hakan yasata fahimtar zai jirata a falo kenan.
Bata 6ata lokaciba ta canja kayanta da atanfa skt da riga, takawo after dress ta saka sannan ta nad'a Vail d'in rigar, d'as ta fito itada cikinta, kamar ka saceta ka gudu abinka.
Tunda ta fito ya zuba mata idanu, ko k'yaftawa bayayi, saida yaga tana gabda k'arasowa garesa ya basar yana mik'ewa. Gaba yayi tabisa abaya, yandama yake taka steps d'in benen dolene ya birgeka, duk takunsa nakan idonta, yayinda itama take binsa daki-daki a hankali.
Babu kowa a falon, dan haka suka fice basu nemi kowanba.
A mota yana tuk'i da sauraren karatu itakuma tana latsa waya suna charts a families group d'insu. Sai murmushi take zubawa, duk abinda take yana kallonta ta gefen ido. Sun isa wani k'aton shagon saida kayan babies, duk abinda kake buk'ata zaka sameshi indai na yarane daga 1year zuwa 15. Itadai mamaki ya ishi Munaya, miye nawani kawota nan? yabari a haihun mana ma.
Tarba ta musamman aka musu, hakan ya tabbatar ma Munaya yasan mai shagon kenan, dan yanda aketa girmamasu sai abin ke bata mamaki. gashi indiyanci sukeyi bata fahimtar maganganunsu. Itadai tana zaune hankalinta ya rabu gida biyu, wajensu Galadima da kuma wasu mata biyu da yaransu uku dabazasu wuce 7-7years ba, yaran k'yawawa masha ALLAH, ga wayo.
Galadima ya juyo zai mata magana saiya lura da inda ta zubama idanu, shima shagala yay a kallon yaran, iyayensu na za6ar kaya amma su suna tibirewa sai Wanda sukeso za'a d'auka. Munaya sai zuba murmushi takeyi, dan suntafi da imaninta, shima murmusawa yayi yana lasar lips, kafin ya d'auke kansa ya maida ga Wanda suke maganar.
Zuwa can gardama ta hark'ume tsakanin yaran akan wani game da iyayen ke dubawa maybe zasu saya musu ne. Kuma games d'in suna kusada Munaya ne, d'aya a cikin yaran ya d'akko yazo wajen Munaya yana tambayarta wai “Aunty wannan yafi dad'i aidai ko?”.
Munaya bata fahimceshiba, dan yayi maganane da yaren dabata ji, dan haka saitayi murmushi ta tambayesa yanajin English?.
Yaron ya d'aga mata kai alamar eh.
Ta kuma murmusawa, duk abinda ke faruwa a idon Galadima ne.
Da turanci munaya tace, “yarona kai kata6a irin wannan game d'inne?”.
Murmushi yamata shima, yace “aunty akwai dad'i ma sosai, ranar saida na cinye kharan a gidansu ma”.
“da gaske?”. munaya tafad'a tana dafa kafad'arsa.
Kansa ya d'aga mata, cike da d'oki yace, “Aunty na koya miki?”.
Munaya ta d'aga masa kai.
Game d'in ya d'ora a cinyarta, ya danna wasu Number, sai kuma ya zubasu cikin d'aya, duk suka shige. Cikin mamaki munaya tace “mikenan to?”.
Shima dariyarsu ta yara yayi, yace “Aunty ai wayo na miki, Abu guda d'ayane, amma sainayi ammafani da numbers daban-daban, kuma kowanne a cikinsu aiki d'aya yayi na canja da wani, kekuma zakiga kamar na had'a daban-dabanne, kuma kowanne da aikinsa, amma aiki d'aya ne na had'aka kuma akan Abu guda d'aya kacal”.
Sosai abun ya birge munaya, tayi dariya har hak'oranta na bayyana, jawo yaron tayi a jikinta ta rungume.
Iyayensa dake tsaye suna kallonsu tun d'azun duk sukayi dariya suma, sannan suka matsa kusada munaya suna bata hannu alamar gaisuwa. itama ta mik'a musu suka gaisa, d'aya tace sunanta Radha, d'ayar kuma tace Anjali, munaya ta fad'a musu nata suna itama, sannan takamo hannun saran yaran tana tambayarsu suma, d'aya yace vanish, d'ayan kuma Anjun, duk kumatunsu ta sumbata tana sakama rayuwarsu albarka.
Wadda tace sunanta Radha tace “kiyi hak'uri da surutun Vishnu shi baya gajiyane ko kad'an”.
Munaya tace babu komai.
Daganan sukai gaba, munaya tana binsu da kallo tana murmushi, yaran sai waigenta suke suna d'aga mata hannu.
Sunje wajen biyan kud'i akace subar kud'insu inji mai shagon, da mamaki suka tambayi wanene? Mikuma yasa ya barmusu.
Mai kar6ar kud'i ya murmusawa yana fad'in mijin matarcan da kuka gaisane mai shagon ai.
Munaya batasan mike faruwaba taga sun dawo, godiya suka shiga yimata, ta tambayesu akan me?.
Suka bata amsa da cewar mijinta bai kar6i kud'in kayansu ba. Murmushi tayi, k'asan ranta tana mamakin dama shagon na Galadima ne?.
Sun katse mata tunani da tambayar kozasu samu number ta, babu musu tabasu sukayi sallama suka tafi.
Maida kallonta tayi ga Galadima dake zaune yanata latse-latsen laptop tamkar baisan mike faruwaba, da alama yana duba kayane ko wani Abu, dan time to time Wanda yake gefensa yakan nuna masa wani yanki na kayan dake shagon, shikuma ya waiga ya kalla, idan bai hango sosaiba saiya kalla ta cikin Computer d'in dake tareda cctv cameras d'in shagon.
Munaya tace kai mutuminnan akwai son kud'in tsiya, kai komai kana saidawa, wata zuciya tace idan bai nemi kud'iba dame zai kula da mahaifinsa?. “hakane kuma”. ta fad'a a fili tana sauke ajiyar zuciya.
Kusan mintuna 15 saitaga ya taso ya nufota. Zama yay kujerar kusa da ita yana fad'in “sorry friend na barki ke kad'ai. kin gaji mu tafi ko?”.
Munaya tad'an yamutsa fuska tace “ba sosaiba”.
Ya d'an murmusa, “ok tunda baki gajiba kozaki d'an mana taimako ni da abin cikin kwan?”.
Hararsa tad'anyi, itafa haushin wannan abin cikin kwan dayake fad'a takeji.
Hannu yasa ya dafe bakinsa yana fad'in “maida wuk'ar”.
A tare suka dinga zagayawa cikin shagon, dayake babbane sosai, kayan yarane kuma zalla a wajen, komai bibbiyu take d'auka, baice komaiba, dan yasan dai bai wuce tana had'awa da cikin 'Yar uwarta Munubiya bane. Sund'an d'iba kaya babu laifi, yabada ATM d'insa aka d'auka harda na wad'ancan matan, yaran shagonne suka kai musu har cikin mota.
Yanzuma haka suka taho tamkar kurame.
Kowa da abinda yake sak'awa....
Danja data tsayar damune yasakashi juyowa yad'an kalleni, ganin hankalina nakan wasu yara 'yan makaranta dake mota yace, “dama haka kike da son yara?”.
Juyowa nayi Na kalleshi, amma saiya d'auke kai tamkar bashine yay maganarba ma.
Nima maida kaina nayi ga yaran, a kuma time d'inne muka sami damar barin wajen.
Saida muka fara tafiya nabashi amsa da “yalla6ai kenan, waye zaice baison yaro, a duniya babu abinda yafi k'uruciya dad'i”.
Kad'an ya juyo yad'an kalleni yana fad'in “really?”.
Nima kallon nasa nayi ina fad'in “na tabbata amsarnan kowama zai baka idan ka tambayesa”.
Bai kalleniba yanzun kam, hankalinsa naga tuk'insa, yace, “ALLAH ya kawoka duniya lafiya abin cikin kwan”.
“shiru namasa bance uffanba”.
Har muka isa gida kuma babu Wanda ya sake magana a cikinmu. Saida yay parking motar a harabar gidan sannan ya juyo gareni, ina niyyar bud'ewa Na fita ya ruk'o hannuna. kallonsa nayi da mamaki, yawani ci magani irin babu raininnan, kamar zanyi magana saikuma nayi shiru muka zubama juna ido, kowannenmu zuciyarsa Na bugawa da sauri-sauri. Cikin k'asaitarnan tasa yace, “Addu'a nayi amma jan aji yahanaki amsamin da amin”.
Ni dariyama ya bani wai jan aji, hakanne yasakani murmusawa kad'an ina k'ok'arin janye idona daga cikin nasa, amma saiya hanani hakan, nace, “na amsa ai, bakaji bane kawai”.
“aiba kurma kika auraba”.
Uhm wannan aure ana tak'ama dashi, Na fad'a a raina, a fili kuma nace, “a zuciya Na amsa”.
“k'arya haramun, banji wannan sak'onba a tawa zuciyar”.
Da mamaki Na waro idanu waje ina fad'in “ban fahimceka ba”.
Lips d'insa yad'an ciza da hak'ora yana matsoda fuskarsa dab da tawa, gashi ya sark'eni da idanu nakasa matsawa, d'an yatsansa ya d'ora saitin zuciyata, muryarsa k'asa-k'asa tamkar mai rad'a yace, “zuciyoyi aminan juna sukan kar6i sak'on juna alokacinda d'aya ya aikashi ga d'aya, karki jahilci kanki har yanzu akwai sauran dama”.....
Yana gama fad'a ya saki hannuna, tareda bud'e motar ya fice.
Galala nabisa da kallo tamkar wata sokuwa, nakasa motsi nakasa fassara zantukansa da ma'anarsu.
Tsawon mintunan dahar bayin gidan sungama kwashe kayan da mukazo dasu ban fitoba, bud'ewa naji anyi, hannunsa kawai ya mik'omin alamar nakama Na fito. tamkar sokuwa haka Na d'ora hannun cikin nasa, ya kamoni ahankali Na fito, maimakon ya sakeni saiya jawoni Na shige jikinsa, ya d'ora kansa a dokin wuyana, cikin kunnena yace “wasu bayanan basa buk'atar fassara, ayanda sukazo ahaka ake barinsu, karki zurfafa tunani, dan yana kawo ciwon kai da hana Hutu”.
Ya d'ago kaina tareda janye jikinsa yana d'agamin gira da salute d'ina, ya juya zuwa cikin gida.
Binsa kawai nakeyi a baya tamkar kazar da kwai ya fashema a ciki.
A falo muka iske duka ahalin gidan, har Momma dazata kwana yau a gida, Abba ne kawai babu, muduka sun birgemu, Dan hira suke ta nishad'i da girmama juna.
Dagani harshi gaishesu mukayi, Sauban da Samha dasuka k'arasa da kayanda da bayi suka shigo dasu suka sakko daga samanmu suna mana sannu da zuwa.
Ni kad'ai Na amsa, Galadima hannu kawai ya d'aga musu.
Momma tace, “kuje ku huta mana”.
mik'ewa mukayi duk a kunyace, ina gaba a yanzu yana baya, suduka da kallon sha'awa suka bimu, dad'i da farinciki Na ratsa zukatansu, innarmu harda kwalla suka cika idonta, Wanda ita kad'ai tasan fasaarar kayanta.
★★★★★★★
Da daddare Galadima Na zaune akan sofa ya d'aura k'afafunsa saman teble yana latsa laptop, yayinda Munaya ke zaune a tsakkiyar gado tana karatun wani English novel na Galadima, buk d'in love story ne dan haka taketa faman zabga murmushi, lokaci-lokaci yakan d'ago ido ya kalleta, saboda idan tayi murmushi yakan jiyo sautinsa.
Maida kansa yayi, yacigaba da aikinsa dayakeyi akan numbers d'in layin Abba na sirri, kwatsam sai maganar yaron d'azu na shago mai suna Vishnu ta fad'o masa a rai.
*_Aunty ai wayo na miki, Abu guda d'aya ne, amma sainayi amfani da numbers daban-daban, kuma kowanne a cikinsu aiki d'aya yayi na canja da wani, kekuma zakiga kamar na had'a daban-dabanne, kuma kowanne da aikinsa, amma aiki d'aya ne na had'aka kuma akan Abu guda d'aya kacal._*
Saida yakuma maimaita maganar kusan sau uku a ransa, kafin ya kalli Munaya da dukkan hankalinta ke kan Novel,
“Friend!”.
Ya kirata a nutse.
Da “na'am” Na amsa ina kallonsa, saikuma Na janye saboda wandon jikinsa baiko rufe masa cinyaba, sai k'aramar riga mara hannu.
Yace, “mikika fahimta ga zancen abokinki na shago?”.
“abokina? waye abokina?”.
Tasowa yayi dagashi har laptop d'in da coffee d'insa ya hawo gadon, nima saina tashi zaune sosai.
Ya zauna ta gefe tareda ajiye mug d'in hannunsa a drowa d'in gefen gadon, laptop d'in kuma a saman gadon d'ayan gefensa. hannu ya mik'amin alamar nazo.
Ban musa masaba Na matso, ya kamoni ya sakani a jikinsa, dan tsakkiyar k'afafunsa ya sakani, saina zame Na kwanta na d'ora kaina a cinyarsa, (dama wajen lak'ewa nake nema🤪).
Ya kar6i buk d'in hannuna ya ajiye gefe, ya d'ora hannunsa a saman cikina.
Kuma maimaita masa tambayar nayi.
Ya shafa sajensa yana cije lips, “miyasa wataran kike da basarwa”..
“ni d'in?”. ‘nafad'a ina nuna kaina da kallonsa’.
Bai bani amsaba yace “ina nufin yaron d'azun”.
“Oh sorry”. nafad'a ina gyara kwanciyat.
Nace, “wai Vishnu? ”.
Kansa ya d'aga min
“to amma wace maganace tasa? tazama abin nazari yalla6ai?”.
“game”.
“game! game!” nashiga fad'a ina k'ok'arin tunanowa.
“okay, wai yanda yafad'i yaci game d'in?”.
“Uhhm”. ya fad'a a tak'aice..
Nikuma saina murmusa, “to dukda dai bansan ma'anar d'aukar maganar da muhimmanciba amma anawa tunanin yana nufin _abinnan mabanbantane, amma saiyayi amfani dasu cikin Abu d'aya, kuma sukai masa aiki iri d'aya, sannan duk shi kad'ai ya sarrafasu akan Abu d'aya bawai yayi tarayyar da wasu mutane da yawa bane ko aikinsa had'aka,_ wannan itace fahimta ta ga zancen nasa”.
Lumshe ido Galadima yayi, ya duk'o a hankali ya mannamin Sumba mai k'au a goshi. Sannan ya d'akko novel d'in ya damk'amin a hannu, yajawo laptop d'insa yacigaba da aikinsa.
Kallon mamaki kawai na zuba masa, kokad'an ban fahimci muhallin maganar tasaba da son fashin bak'i.
Batareda ya kalleni ba, idonsa akan system d'insa yace, “kallonfa?”.
Janye idona nayi ina ta6e baki.
Shima saiya ta6e nasa alamar yaganni kenan. karatuna nacigaba shima yacigaba da aikinsa yana shan coffee time to time.
Yayi aiki mai tsawo kafin yasaki wani murmushi da ajiyar zuciya, ya kalli munaya da barci ya kwashe, fuskarta ya shafa yana kuma sakin wani murmushin, “tabbas gaskiya Vishnu ya fad'a, mutum d'ayane ke amfani da Numbers daban-daban wajen kiran Abba munaya, duk wadda yagama da ita bazai sakeba, tagama aikinta, a wannan karon lallai kunyi aiki da basira, wadda harta birkita tunanin Sameer, kuna kiran Abba da mabanbanta Numbers wad'anda kunrigada kun gama shirya matakan da kowacce number bazata sake aikiba, shima kansa ya d'auka mutane daban-dabanne ke kiransa. O ALLAH wannan shine bada k'afa, to ai inkunsan wata bakusan wataba kuma, Muhammad Sameer ruwane, idan bakasha yanzuba zakasha anjima, idan kak'i kuma k'ishirwa ta kasheka. Inhar tarkon dazan d'ana zai d'annu dai-dai, tabbas zan cafke kurayen daji mai duhuwa a wannan karon”. ‘Ya k'are maganar da jan hancin munaya yana kuma sumbatar goshinta’.
Kwanciya ya gyara mata sosai, ya ja bargo ya lullu6a mata sannan yaje bayi ya d'auro alwala, kamar yanda ya saba ya raya wannan dare da nafilfili da godiyar ALLAH, kafin yazo ya kwanta gefen munaya zuciyarsa na cike da annashuwa da farinciki, kaikace komai yayi done ne.
Addu'a ya musu sannan yasakata jikinsa barci ya Lula dashi shima.
Nima mai d'aukar rahoto bara nad'an rintsa my sweet sisters😉🤩......................✍🏻
Duk Wanda yaga ban amsa massage nashiba yamin afuwa, nayi up date WhatsApp d'inane🥰🥰🥰🤝🏻
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu👏🏻😭_*
*_typing📲_*
*_typing📲_*
💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._*
*_♦RAINA KAMA.....!!♦_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
___________________________
_jinjinar gaisuwa a gareku da fatan alkairi, Bilyn Abdull ta gaisheku, gaisuwa irin ta musamman d'innan my lovely sister's🥰🥰🥰🥰🥰🤝🏻_
*_Aysha Manshart (Ummu zunnur😍), Hafsa abdulaziz, mmn fukaihat, Hannah A Ali, marnona, Mmn Al'ameen, Sumee waziri, Ummu walid, Yar tulluwa, Khadija Aliyu Sa'id, Umm Abdul, Umm Yusuf, Mrs Ahmad, zubby abdullahi, Hajara Ismail shatu, Ummu barakat, maryam haruna, Ummu sulaym, Ummu Ahmad, Haizarana halliru._*
I love you mazga-mazga😂🤸🏻♀
____________________________
~Book 2~ 👉🏻2⃣0⃣➖2⃣1⃣
................Tafiyar su Abba dai ta kankama, dan Abba ya matsa ainun, dole Galadima ya musu dukkan shirin daya kamata, zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu jirginsu zai d'aga.
Da yake yau Saturday ce babu aiki, amma hakan bai hana zama gidan shiru ba, su Sauban da innarmu sun fitane, nikad'aice a gidan sai jakadiya, nima barci nake suka gudu suka barni a gidan.
Yunwar dana farka da ita ta tilastamin sakkowa k'asa neman abinci, dan a 'yan kwanakinnan nazama wata acici, danaci abinci danaji sabuwar yunwa, narasa wannan dalili.
Bannemi kukun gidanba ma ko cikin bayi, nahau dafa abinda zaimin saurin dahuwa, kafin ya dahunma saida na d'umama madara nad'ansha sannan 'yar nutsuwa tazomin. ina sauke abincin kuwa Na juyoshi a plate na koma sama. tun a hanya naji k'amshin turarensa, ban kawo yashigo gidan bane nidai na ida hawa. ban tsaya faloba na shige bedroom.
Galadima dake zaune a sofa yana kwance igiyar takalminsa ya d'ago ido yana kallona da amsamin sallamar danayi.
Sandunan wasan Golf d'insa daya shigo dasu ya zube a carpet d'in gaban gadon na janye gefe na zauna, dan nafijin dad'in xaman k'asan yanzu.
Shidai bai fasa kallona ba baikuma bar cire takalman ba, dan abincin dayaga ta zubo yakema kallon mamaki, kafinfa yafita harda kukanta ta farka wai yunwa takeji, haka dole yafita yasaka kuku dafa mata abinci, baibar gidanba saida taci takoma barci, da fitarsa kuwa baifi 3hours ba, amma jita yanzu dawani abincin.
Ya janye takalaman daya gama cirewa a gefe ya zubamin ido kawai, dukda abincin nada zafi haka nakecinsa da sauri-sauri.
Janye plate d'in yayi daga gabana, fuskarsa babu walwala yace, “waike mike damunki hakane?”.
Idona harya fara tara kwalla cikin marairaicewa nace, “dan ALLAH kabani, wlhy yunwa nakeji bata wasaba”.
Rasa ma mizaicemin yayi, ya zubamin ido kawai yana kallona. a mamakinsa saiyaga ma ina hawaye, abincin ya tura min yana fad'in “wannan cin naki yayi yawa, gama muje wajen Akash ya dubaki”.
Uffan bance masaba, shima bai sake tankawa ba yanufi bathroom, yaja wasu mintuna saigashi ya fito d'aure da towel, kallo d'aya namasa na janye idona, wannan abun nasa yafara damuna, yanzu baijin kunyar yafitomin a duk yanda yaso, ko yana mantawa bashi kad'ai bane a d'akin oho.
Shima dai kallonta kawai yakeyi, dan nacinye abincin plate d'in tas, a ransa yace shiyyasa taketa zama k'atuwa, irin wannan ci haka.
Oho bansan yanayiba, nidai mik'ewa nayi nashige bathroom abuna, nasamu nai wanka da ruwa mai sanyi dan naji dad'i. lokacin dana fito yagama shiryawa cikin ainahin kayan malam bahaushe, blue d'in shaddace akaima d'inkin wando da 'yar shara, saidai tasha aikin sarauta d'an asali da d'aukar hankali, ya kawo bak'ar hularsa ya d'ora, itama dai irin ta mutanen dace *dara* (irin wadda su ibro suke sawa), saidai wannan batakai waccan tsawoba, dai-dai take kamar sauran huluna. harga ALLAH kwalliyar tasa tamin k'yau, dan yafito a cikakken bahaushensa, turare yake fesawa amma nakasa d'auke idona daga kansa.
Duk kallon k'urillar datake masa yana kallonta ta gefen ido, wani miskilin murmushi yayi Na gefen baki, ya juyo muka had'a ido, saurin janyewa nayi cike da basarwa.
Shikuma ya ta6e baki yana takowa inda nake. tuni zuciyata harta fara tsitstsinkewa, dan ayanzu babu abinda nake gudu kuma irin yace zai ra6u jikina koya nunan buk'atar wani abu, shima inaga fahimtar hakanne yasa a kwanakinnan bai cika takurani kamar abaya danake kawo kaina ba.
Ganin yanda ta tsorata sai abin yabashi mamaki, waskewa yay yafasa zuwa gareta, ganin ya canja hanya Na sauke ajiyar zuciya wadda har fitar sautinta saida yaji.
Kansa kawai ya girgiza ya zauna a bakin gado yana fad'in “kishirya mana”.
Bance komaiba nawuce Na d'auki Arabian gown da zan saka, dan yanzu sune kawai kayan dakemin dad'in sakawa, bathroom nakoma Na saka, Na fito Na iskeshi yana waya da Akash dake fad'a masa inda zamu iskeshi. wucewa nayi nad'an gyara fuskata, inason shafa mai a k'afa amma ina tunanin yanda zan sunkuya.
Lura da yay da hakan yasashi mik'ewa, wajen takalmanmu yanufa ya d'aukamin masu taushi cikin wad'anda ya siyamin saboda naji sauk'in tafiya.
Kafad'una ya kama ya zaunar dani ga stool d'in mirror, sannan ya d'auki man ya duk'a k'asa a gabana yakamo k'afata yana shafamin, nidai kallonsa kawai nakeyi, harya gama yasakamin takalman ya d'auran igiyar yana fad'in “yakamata ma mufara fita kina motsa jiki, dan k'afarnan kamar tana d'anyi fushi a kwanakin nan”.
Nace, “ai bata ciwo”.
Baice komaiba yamik'e yana kama hannuna ya mik'ar dani.
A falo muka iske jakadiya tana kallo, tamin sannu sannan ta gaida Galadima.
yafad'a mata zamu fita, tabimu da addu'ar dawowa lafiya.
Tafiyar tamu takasance shiru kamar yanda muka saba inhar ta had'amu mu biyu, maimakon muje asibiti sai gamu awani gida mai k'yau da tsari, kafin nasamu damar tambayarsa saiga Akash yafito yana zabga murmushi, rungume juna sukayi da Galadima, kafin ya d'ago yanamin sannu da zuwa.
Fuskata da murmushi Na amsa masa tareda gaishesa.
A tsararren falon gidan muka yada zango, komai ya birgrni dan an tsarashi yanda ya kamata. dandanan Akash ya tara mana kaya a gaba, sannan ya zauna muka sake sabuwar gaisuwa. Suka d'ora da barkwancinsu irin Na abokan da suka shak'u. A firar tasune nakejin Auren Akash d'in ya matso, dan zasuyi baiko next week da wadda zai aura, Na tayashi murna da fatan kaiwa da rai. ya amsamin bakinsa har kunne.
Bayanin yawan cin abincina Galadima yamasa, Akash yay dariya, “to inbanda abinka Sameer ai dole taci abinci fiyeda da, karka manta yanzu ba ita kad'ai bace, kuma saitaci abin cikinta zai samu shima, kunk'i yarda ayi scanning muga adadin 'ya'yan namu ko jinsun su”.
galadima ya murmusa kawai, karka damu, miye Na zazzari, kwana nawane insha ALLAH zaizo ko zatazo duniya, yanzu dai tunda ba Matsala bane cin abincin ai Alhamdllh”.
“no babu wata Matsala, abindama yasa zakuga yanzu takanyi saurin jin yunwa cikinta ya tsufa, shima yak'ara girma abin cikin nata, dan zama ta dingajin idan bataciba ana motsi da harbe-harbe a cikin, idan da zaka kalli cikin a time d'in datakejin yunwar sosai har yanda yake wuntsilniya saika gani kaima, Madam ko hakan baya faruwa?”.
Nace, “yana faruwa sosai, amma da zaran naci abincin sai a nutsu”.
Akash yay dariya, “Alamun yana cikin k'oshin lafiya kenan, abincinne kawai buk'atarsa”.
Galadima ya juyo muka kalli juna, gira ya d'agamin nikuma nayi murmushi ina kauda idona gefe.
Daga nan wata hirar suka koma, wadda nake zargin akan Abba nane, dan naji Akash Na fad'in doctor Johnson yabama Abba glasses d'in amatsayin medical glasses, kuma ya gargad'esa karyayi wasa dashi saboda jijiyar idonsa nason samun Matsala, to sunason glasses d'in yazama riga kafine, dayake da turanci suke magana sai yazam inaji nima.
Murmushi Galadima yayi yana jinjina kai.
A raina nace mikuma Galadima ya shiryama Abban?. banida mai bani amsa, dan haka nayi gum.
Muna niyyar tashi Akash yace bamu isaba, bazamu tafi bamuci komai a gidansa ba, kodan munga bashida matane.
Badan munsoba mukad'anci abinda zamu iya, sannan yayo mana rakiya har wajen mota.
Saida munaya tashiga mota sannan Galadima ke fad'ama Akash yayi mantuwa.
Akash yace “tami?”.
Babu kunya Galadima yad'an ciza lips yana tambayar Akash wai miyasa yanzu take gudunsa?.
Akash yabashi amsa da maybe salon cikine, danshi babu yanda baya zuwa ma mace, wani yasata sha'awa wani kuma akasin hakan, amma idan na haihu zan iya komawa normal. Galadima ya basa hannu sukai musabaha sannan ya shigo mota yana masa godiya.
Tunda muka fara tafiya saina kasa jurewa, na jeho masa tambaya muryata a sanyaye.
Kad'an ya juyo ya kalleni ya maida kansa ga tuk'i, saida yaja wasu mintuna kafin yasaki ajiyar zuciya tareda cizar lips nashi, batareda Yakuma kallonna ba yace, “Friend! Wani karatun baya buk'atar fashin bak'i, akan karantashine a barsa a yanda yazo”.
Murmushi nayi ina maida hankalina gareshi, nace “yalla6ai koda shi wannan karatun zai iya fita a jarabawa?”.
“Humm” yafad'a yana rage gudun motar, yanzunma bai kalleniba, yad'an zakud'a jikin sitiyarin sosai, “sometimes akanyi burin cin jarabawane domin canjin aji ko gama makaranta ko shiga, saidai awannan karon ni nawa jarabawar da banbance-banbance tazo, dan bana buk'atar cin jarabawar kai tsaye, har sai harsashina ya isa ga zukatan malaman”.
“to amma yalla6ai karka manta Hasashefa ba shi bane yak'ini”.
“wannan gaskiyane yalla6iya. Saidai yak'ini kuma baya amsa sunan tabbaci, daga lokacinda kika shiga fili wasa kika saka aranki bazakiyi nasara ba, to da kamar wahala kiyi nasarar, duk abinda zanyi nakan rok'i ubangiji nasara Kafin yinsa, sannan na cika zuciyata da kwad'aituwar samun wannan abin, lokuta da dama mutane kan Gaza tsarkake zuciya kafin su cikata da buruka, shiyyasa kikaga duk gudun jirgi a samaniya wataran gaggawa nasakashi tarwatsa a filinda ba muhallin saukarsaba, kiringa zama mai yak'ini saikiga kin tabbata a jerin masu samu”.
Murmushi nayi har hak'orana na bayya, nace, “dakai kanarine danace kafi dukkan halittar kanari iya raira zance, dakuwa mawak'ine saina saka a jerin masu zak'ak'an murya, inkuwa a Marubuci kazo to tabbas kai Kanada yawan fik'ira, domin hikayarka zata yawaita saye zukatan mabiyanka ne”.
Gefen hanya ya gangara, ya kashe motarma baki d'aya ya maido hankalisa gareni.
“Munaaya!” yakirani cikin wani yanayi kuma murya ahankali.
nima saina amsa masa a sanyaye.
Hannuna ya kamo cikin nasa yana mirza yatsun a hankali, yaci gaba da fad'in “A shekarun baya ni mutumne mai ra'ayin Kansa, ma'ana murd'ad'd'e mai wahalar sha'ani, sannan mai zama a bisa tsarinsa, kece mutum ta farko dana fara doguwar magana da ita koda bana so, nakanyi mamaki a duk lokacin da kika taya nazamo mai sallama miki, anya kuwa bakizo da wani Siddabaru ba?”.
Idanu nad'an fiddo waje, nace “siddabaru kuma yalla6ai? to ai awajena ni har gobe kana akan wad'annan ra'ayoyin naka, dan banga canjin dakake hasashen kasamu ba, amma miyasa kace hakan?”.
Numfashi ya sauke ahankali, kafin ya ciji gefen lips nashi yana Sosa girarsa d'aya da d'an yatsa “wannan sak'on zuciyane, kibata dama, zata tabbatar miki da cewar wannan Muhammad Sameer d'in yasha banban dana shekarun baya”.
“sak'on zuciya kuma?”. nafad'a cikin hasashe, dan nikam Yakuma dilmiyar dani.
Mortar ya tada yana fad'in “well basai kin zurfafa ba, dan haryanzu akwai sauran dama”.
Baki na d'an ta6e ina gyara zama, “har walau zancen “dama! dama! dai again?, bana son saka baki a hurumin daba nawaba, amma abinda nasani dama dai duk damace, sannan mai ita yakan tanadar mata dukkan muhalin daya tadace da ita, damarmu ce mu damata takowane
hanya mukaso”.
Idanunsa ya lumshe yana sakin wani k'asaitaccen murmushi daba koyaushe yake irinsaba.
Jin Sautin murmushin ya sakani juyawa na kallesa, ya d'agamin gira yana maida hankalinsa ga tuk'insa.
Babu Wanda yasake yin magana har muka Isa gida. har yanzu babu Wanda ya dawo, dan haka muka haye sama kai tsaye. dama na k'agara na cire rigar jikina saboda azababbiyar zufar danakeji, danma ya tausaya min yad'an saka AC a mota, ban iya zama ba saida na watsa ruwa, nifa abubuwan sunmin yawa, nice jin zafi nice ci kamar gara, harda alwala nayo, Dan magriba tayi.
Ina fitowa shima yashiga yayo alwala. Koda yafito saiya wuce masallaci.
Ina jiyo hayaniyar su Samha dasuka dawo amma nakasa sauka, ina kwance abina, hawa da saukarnan bak'aramin wahal dani yakeba yanzu, ahaka Galadima yadawo ya iskeni, sallamarsa kawai na amsa, amma ban iya d'agowa na kalleshiba. Saida ya sauya kayan jikinsa zuwa marasa nauyi kafin yazo ya zauna kan sofa yana fad'in “lafiya dai?”.
d'ago ido nai namasa d'an murmushi, nace, “babu komai, gajiya ce kawai”.
Shima murmushin yamin, cikin lumshe ido yace, “Sorry friend, saura k'iris insha ALLAH”.
“Humm” kawai nafad'a batare da nace masa komaiba.
Daga nan muka d'anyi shiru, kusan mintuna 3 yanata latse-latsen wayarsa, batareda ya kalleni ba yace, “Abba kuwa yana saka zobe?”.
Kallonsa nayi, amma hakan baisa ya kalleniba, a d'arare nace, “eh yana sakawa amma miyasa kamin wannan tambayar?”.
Wayar ya ajiye yana sauke ajiyar zuciya, ya saka d'an yatsansa yana bubbuga la66ansa ahankali, yayinda idonsa yake a kaina tamkar mai nazari, “kina ganin idan kika bashi zai saka?”.
Yunk'urawa nai na tashi zaune sosai, “dan sakawa zai saka, amma kana ganin bazai zargi wani abuba kuwa?”.
“miyasa kikace haka?”.
Shiru nad'anyi, dan ganin ina neman zirma kaina, saina d'an murmusa kawai cikin basarwa, nace, “waynot abashi ba kai tsayeba”..
Murmushin gefen baki yayi, yace, “y'ar tsuntsuwata wai mikike tunanine? da har kiketa kwana-kwana haka?”.
Baki na tunzuro gaba, ina fad'in “nidai ba tsuntsuwa bace ba”.
Dariyace ta kufce masa babu shiri, yasaka hannu yana rufe bakinsa.
Haushi ya kamani na d'auki filon dana kwanta na jefa masa. da sauri ya cafe yana cigaba da dariyarsa, hakan yasa najawo na kujerar ina cigaba da kai masa duka yana karewa da wancan. daga k'arshe sakkowa yay yahad'a nida filon ya rik'e yana fad'in “sorry sorry na bari, ba 'yar tsuntsuwa ba giwar mata”.
Hararsa nayi nafara kukan shagwa6a kuma.
dariya Yakuma sakawa yana fad'in “toni bansan mikikeso nace mikiba kuma?”.
“ni banaso duka”.
“to shikenan nabari, yanzu dai yaza'ayi Ring yaje yatsan Abbanmu to?”. ‘yay maganar yana d'ora kaina jikin kafad'arsa’.
“saika fad'amin sirrin sannan zan fad'a nima”.
Ya murmusa yana jan hancina, “kin cika wayo yarinyarnan wlhy”.
K'aramar dariya nayi nace, “ai awajenka na koya”.
Murmushi kawai yay baice komaiba, ya jawo wata 'yar k'aramar bag mai k'yau fara ya mik'omin.
Kar6a nayi ina tashi zaune sosai na bud'e jakkar ina fiddo kayan ciki, agogone mai masifar k'yau da tsari, na azurfa 'yar asali mai tsada, sai wani d'an akwati da ring mai k'yau na azurfa shima, an masa ado da farin stone mai garai-garai tamkar diamond, na jujjuya zoben kafin na d'ago mu kalli juna ni da Galadima, ido d'aya ya kashemin😉.
Janye idanuna nayi nakuma maidawa ga zoben ina k'ok'arin sakashi a yatsana, saidai yamin yawa sosai, na cire ina fad'in “amma gaskiya zobenan ya had'u sosai yalla6ai”.
“duk haduwarsa bai kaikiba ai”. ‘yay maganar acikin kunnena’.
Kallonsa nayi, amma saiya basar tamkar bashi yay maganar ba.
Lips na cije na d'an hararesa.
Shikuma ya ta6e baki.
Na maida kayan duk a cikin bag d'in dad'an hanzari ina rik'e cikina dayay wata wuntsulawa.
“lafiya?”. ya fad'a yana rik'o hannuna.
'Dagowa nayi na kallesa da k'yar, da hannu na nuna masa cikina dake juyamin, jinake kamar numfashine zai bar jikina.
Babu shiri ya dire wayar hannunsa ya rik'oni jikinsa da k'yau.
Sosai na fara murk'ususu ina kuka da k'ank'amesa, dukya rikice, yama rasa mi zaiyi?.
Ana cikin haka saiga sallamar Aunty Mimi dataga shirun yayi yawa sun dawo ban sakkoba, saitai tunanin kobana jin dad'ine, sallama tayi Galadima ya amsa murya a rikice, hakanne yasakata shigowa batareda jiran isoba.
Da hanzarinta ta k'araso tana tambayar miya faru?. nidai kuka kawai nake ina kuma k'ank'ame Galadima.
Shine yasamu damar mata bayani sama-sama, yak'are maganar da fad'in “Aunty mutafi asibiti please, maybe haihuwa Ce?”.
Da sauri tace, “badai haihuwaba Sameer, cikin dake wata takwas, kaga ina zuwa”. Ta fita a hanzarce.
Babu dad'ewa sai gata tadawo da innarmu da jakadiya, dak'yar innarmu ta amince ta hawo, danma taga tsantsar rikicewar da aunty Mimi tayine. har yanzu dai kukan nake ina jikin Galadima dashima dukya koma kalar tausayi kamar zaiyi kukan.
Ganinsu a haka yasaka innarsu munaya k'ok'arin komawa da baya, dan saitaji kunya ta kamata, dukda tasan suma bada son ransuba ne. ita kanta jakadiya taji kunya. ganin innarsu munaya zata gudu Aunty Mimi tayi azamar rik'o hannunta. “please inna karki duba ta kunya, halen datake cikine abin dubawa, kowa yasan dai ba haihuwa baceba tunda da saura”.
Ajiyar zuciya inna ta sauke, batare da ta motsa daga inda takeba takuma musu kallo d'aya ta d'auke kanta, tace, “inaga juyine ai, zai lafa insha ALLAH”. ‘tana gama fad'a ta fice abinta’.
Jakadiya da aunty Mimi suka kalli juna, murmushi jakadiya tayi, tace, “gaskiya ta fad'a, juyine, amma nadad'e banga uwa mai kawaiciba irinta a wannan zamanin”.
Murmushin itama aunty Mimi tayi, ta maida kalonta kansu, yafara lafawa sosai, dan haka munaya tafara tsagaitawa da kukan.
Galadima yakuma k'ank'ameni a jikinsa sosai yana shafa kaina, nikam sai ajiyar zuciya nake saukewa tareda shashshekar kuka, ya manna min kisses a kaina idonsa a lumshe, danshi yama manta dasu Aunty Mimi a d'akin.
Jakadiya ma dai lalla6awa tai ta gudu, dan taga magajin gari yau sai a hankali.
Aunty Mimi ta tako inda suke ta zauna a sofa tana fad'in “sannu Munaya”.
Bud'e ido Galadima yayi, harsun kad'a zuwa launin jaa, yad'an furzar da iska yana lek'a fuskarta, barci ya d'auketa. ido ya d'ago yana kallon aunty Mimi dake kallonsu cike da sha'awa, tamasa murmushin kwantar da hankali, ajiyar zuciya ya sauke yana cije lips da jinjina mata kai.
Tace, “tayi barcine?”.
Nanma kansa ya jinjina mata, yana gyarama Munaya kwanciya a k'irjinsa yanda zataji dad'i, yace, “Aunty Mimi amma yakamata muje asibiti aga miye matsalar?”.
“karka damu my k'ani, juyine kawai, insha ALLAH babu wata damuwa. bara inje nima saida safe, idan kuma kaga dawata matsala saika kirani muje asibitin tunkan dare ya kumayi”.
Bayan fitar aunty Mimi kuma k'ank'ameta yayi yanamai jin tausayinta na ratsashi, ya sumbaci goshinta, kafin ya d'auketa dukda nauyin datayi ya maidata saman gadon, yanzunma a jikinsa ya sakata, yaja bargo ya lullu6esu tareda musu addu'ar kwanciya.
Cikin barci ta farka da wata matsananciyar yunwa, k'irjin Galadima na shiga girgizawa ina kuka.
Galadima ya farka a firgice yana rik'e hannunna, ya yunk'ura da k'yar ya tashi zaune, “miya faru?”. ‘yafad'a cikin muryar barci’.
“yunwa yalla6ai, abinci xanci, kafad'a masa magana yabar halbina”.
Dukda tabashi tausayi saida ya murmusa, sauka yay yafita, k'asa ya sauka zuwa kitchen, yau saiga Galadima a kitchen🤣, rasa mizaimayi yayi, ganin yana 6ata lokacine kawai dan ba iya uwar komai yayiba saiya fice, dole yaje ya tado kukunsu.
Mai aiki da aikinsa dannan saigashi ya had'a mata Abu mai sauk'i, Galadima ya kar6a da kansa Yakoma saman.
Isketa yayi zaune tsakkiyar gado tana kuma rurus, saita k'ara bashi tausayi, ya haye gadon da abincin, da kansa yabata yana lallashi. saida tayi nak sannan ya sauka da tiren yana sauke tagwayen ajiyar zuciya.
Nikam hankalinna kwance nazame na kwanta, barci ya sake kwasheni.
Mamaki yasakashi tasata gaba yana kallo, saikace wata mai aljanu, lallai duk namijin daya kasa tausayawa matarsa lokacin da ciki yake jikinta yacika mara tausayi number d'aya, babu abinda miji zai iya biyan matarsa dashi akan rainon cikinsa datayi da tarbiyyar 'ya'yansa, amma a wannan time d'in wani namijinma rashin tausayinsa ke tashi akan matar, ALLAH ya ganar dasu to.
Amin galadima🙁😔.
**********************
Washe gari
A safiyar yau su Abba suka tashi da shirin komawa Nigeria, gaba d'aya saina tashi duk babu dad'i, jinake kamar karsu tafi, dana tuna yaune zasu barmu sai hawaye ya zubomin, inama zai amince nidai nabisu mu tafi tare?.
Agogo da zoben jiya na d'auka nafita masaukin su Abba, dan Galadima ya fita tunda sasaafe, bansan ina yajeba.
Saida nayi sallama aka bani izinin Shiga sannan na shiga, Abba na zaune a bakin gado agogo rik'e a hannunsa suna magana da innarmu dake tsaye ita kuma tana zuba sauran kayansu a k'aramin akwati.
Abba yay murmushi yana fad'in “sannu munaya kinji”.
Murmushi nayi a kunyace, na dafa gadon zan durk'usa k'asa na gaidasu amma saiya dakatar dani ta hanyar rik'e hannuna, “kinga zauna, inake ina durk'uso yanzu”. da taimakon Abba na zauna a kujerar dake kusada gadon, sai faman jeran sannu yakeyi, nikuma ina amsawa cikeda jin kunya. gaishesu nayi, suka tambayeni yaya jikin? na amsa da “Alhmdllh”.
Jakar hannuna na mik'ama Abba, ya amsa yana fad'in “minene kuma?”.
“Abba ka bud'e to”. ‘nayi maganar a shagwa6e’.
Dariya yayi yana k'ok'arin bud'ewa, “yanzu dai fitinarki k'aruwa ma tayi Munaya”.
Innarmu dake ta6e baki tace, “ai bamaka san fitinarta ta zarce tadaba sai jiya, juyi kawai ta zauna tana rusama mutane kuka a gidannan, yo ke aibama asan abin fad'in dazaki bariba ranar haihuwar?”..
“babu abin fad'in dazata bari insha ALLAHU”. cewar Abba yana juya agogon fuskarsa d'auke da murmushi.
Nima sai ban kula zancen Innarmu ba nace, “Abba yayi k'yau?”.
“sosai kuwa Munaya”.
“Abba kawo na saka maka to”.
“to amma kekuwa ina kika samu kud'in sayen wannan agogon da zoben mai tsada haka?”.
Murmushin nayi, nace, “Abba awani shago mukaje sayen kaya tun kwanaki dashi, daga nace agogon yamin k'yau shinefa yace na d'auka to”.
“Amma munaya yayi tsada da yawa, karna sakejin irin haka, dan takurawace ai, idan kuma bashida k'arfin siyen abunfa? Karki sake kinji ko?”.
“inasha ALLAHU Abba bazan sakeba, amma dan ALLAH karkace bazaka kar6i wannanba, dan shima bazaiji dad'iba”.
Murmushin Abba yayi, yashiga sanya albarka a garemu da abinda ke cikina, hardama addu'ar d'orewar lafiya ga Abie shima. cikeda d'oki naita amsawa da amin, da kaina na saka masa agogon da zoben.
Daga nan muka d'an ta6a hira. Dan akwai sauran time sosai na tafiyarsu. Mun dad'e muna hira, dan ko break fast yau tare dasu na sakeyi, dama tun asuba ni yanzu nakeyin nawa🤭, sanda kowa zai k'ara sainayi na biyu.😂
Galadima ma daya dawo ya kimtsa nan yazo ya samemu, yanda suke sakin jiki da juna shida Abba abin na bani mamaki, Galadima yakuma yima Abba bayani sosai akan yanda zaicigaba da tattalin lafiyarsa da kulawa da dukkan dokokin da sukai masa, daga nan muka cigaba dad'an ta6a hira, itadai Innarmu duk adabaibaye take, danma taga yau zasu wuce da bazata zaunaba.
Wajen 12pm mukabar gidan zuwa asibiti, a asibitine akayi dogon zama, dan godiya ta musammance tashiga tsakanin surukan guda biyu, Abba kuma yay alk'awarin kuma tsayawa wajen dagewa da addu'oi na musaman ga jikin Abie da alk'awarin kawo wasu taimakon na tsarin jiki, dan sunga fa'idar addu'a sosai.
Kowa jiyake tamkar karsu tafi, saboda shak'uwace ta musamman tashiga tsakanin wad'annan families guda biyu, zaman mutunta juna ya gudana sosai a tsakani.
Kuka na shiga rairawa lokacin danaga tafiyarfa da gaske yinta za'ayi, sai alokacin muka san ashe wai harda Sauban, zai rakasu saudiyya suyi umrah ta kwana 10, daga nan saisu wuce shikuma yadawo. na kama hannun Abba na rik'e gam nak'i saki zai hau jirgi, su Sauban suka tasani da dariya kuwa, oho ban kulasu ba, Galadima ya girgiza kaiwai yana murmushi, yarinyarnan ta6ararta tayi yawa, yafad'a yana takowa inda muke da Abba yana lallashina.
A Kallonsa Abba yayi sukayi murmushi, Abba ya zame hannunsa a hankali yajuya zuwa ga jirgi, yunk'urin binsa nayi Galadima yay azamar rik'o min hannu batareda yayi magana ba, juyowa nayi na fad'a k'irjinsa ina kuma sakin sabon kuka.
Hannu biyu ya saka ya rungumoni yana guntun murmushi.
Innarmu dake hangenmu ta cikin jirgi ta share hawayenta itama tana murmushi, banda aure waya isa ya rabaka da 'ya'yanka. Abba daya zauna kusada ita ya saka hannunta cikin nasa yana murzawa, juyowa tayi ta kallesa, yamata murmushi yana share mata hawayen da har yanzu sun kasa tsayawa, jikin kafad'arsa ta d'ora kanta kawai.
Sauban dake kallonsu yay murmushi, lallai Aunty gimbiya 'yar gatace a gidansu.
Saida naji alamun jirgi zai tashi sannan na d'ago kaina, inaji ina gani jirgin yafara shawagi a samaniya harya shilla da iyayena.
A motama haka naita sharar hawaye, dayake dagani sai shi da Samha a motar, cankuma Aunty Mimi da Khaleel da jakadiya.
Samha tana ta bani hak'uri, amma tamkar tana zuganine, saida Galadima ya harareta yana mata alamar tamasa shiru sannan tayi shiru, shikam ko sau d'aya baicemin uffanba..
Asibiti muka koma, tunda muka shigo Momma ta taso ta rungumeni a jikinta tana lallashi.
Galadima ya jingina da bango ya hard'e hannayensa yana kallonmu, a haka sauran suka shigo suka iskemu, Abie ma kallonmu yakeyi cike da tausayina.
Saida nasamu na tsagaita da kukan sannan nacema Momma zanci abinci.
Galadima yaje kusada Abie ya zauna yana k'aramar dariya, “dama kice yunwa kikeji kika zauna kinama mutane ta6ara?”.
Hararsa Momma tayi tana masa dak'uwa, hakama Abie, aunty Mimi kam saida ta rankwasheshi akai.
Gurin ya dafe yana fad'in “a'a yazaku tararmin ne kuma?, gaskiyafa na fad'a ko Samha?”.
Samha tace, “Uncle nima dai ina bayan aunty gimbiya”.
Idanu ya kwalalo alamar tak'aremin.
Muka had'a ido na hararaesa.
Lips d'insa ya ciza yanamin alamar zan kamakine da ido.
Na ta6e bakina nikuma. Dolenesa yatashi yanemomin abinda zanci.
★★★★★★★★★★
Tunda su Abba suka tafi lafiya tamin k'aranci, bana iya tsinanama kaina komai sai kwanciya, dukna fita hayyacina na canja kamanni, ga cikifa sai kuma bud'ewa yake yana k'ara girma. Kai kace ba halitta d'aya bane a cikinsa.
Galadima dole ya d'auki hutu a office, idan abinda yazama dolene saiyaje Office kam yakanyi shine ta yanar gizo.
Gakuma nasarar jikin Abie daketa k'ara k'yau, dan wasu sassan jikinsa suna nuna alamun fara aiki kamar yanda doctors d'insa suka sanar mana.
A kwana na 8 da tafiyarsu Innarmu ranar a asibiti na kwana, saboda jiki dai yak'i dad'i, ga masifaffen cin abinci abin babu arzik'i.
★★★★★★★
Su Abba sun gudanar da ibadar Umrah cikin kwanciyar hankali da nutsuwa, ga Sauban dake nuna musu komai yanda bazasu wahala ba.
Suna cika kwanaki goma yasakasu a jirgi suka nufi k'asar haihuwa Nigeria kenan, sun rabu cikeda kewar juna suna saka masa albarka.
Sun isa Nigeria batareda sanin kowa namuba sai Yaa marwan da Galadima yakira ya sanarma yaje ya d'aukesu a airport.
Isowarsu gidanmu tazama a bazata, hakan yasaka gidan rikicewa da murna, dukda kishin daya cika matan gidan ganin innarsu munaya takoma wata d'anya shakaf saboda Hutu da canji wajen zama data samu, dandanan 'yan anguwa suka shiga shigowa taya murna dama Abba jajen ALLAH ya kiyaye gaba.
Innaro babu kunya taketa haba-haba da d'anta, kota innarsu munaya batayi, dan haushinta takeji taje ta zauna a India itako an maidota gida. (Babu mai iyama Innaro dai sai ALLAH🤦🏻♀🤣).
Su Ayusher da sukazo suka zage suka gyarama inna d'akinta, komai ya koma need, tamkar ba shineba ya had'a uban datti na tashin hankali.
Tafiyarsu Abba Nigeria da kwana 5 Sauban ma ya dawo India, ya iske ina asibiti, dan gado suka bani dole, babu ranar sallama ma, k'ila saina haihu.
Saidai randa mukayi waya da Munubiya nake fad'a mata tace ai gidama yakamata na dawo na haihu, itama batada lafiyar sosai.
Da to na amsa mata kawai, amma ina tunanin yanda Galadima da ahalinsa zasu amince da zuwana haihuwa Nigeria, kuma tunda 'Yar uwata ta ambata dolene hakan za'ayi, kona so koban soba kuwa.
___________________________
*_Two months ogo_*😬🤭
Watanni biyu kenan da tafiyarsu Abba, tunda sukatafi kuma babu wani Abu mara k'yau kona Sosa zuciya dayay gamo dashi, harma ya koma wajen aikinsa hankali kwance.
Jama'ar gidansu Munaya kuwa sunyi haushin da nuna hassadar ga inna harsun gaji sun bari, dan sudai san ba kulasu zatayiba, ita yanzu babbar damuwarta ma 'ya'yanta su sauka lafiya, dansu Safara'u duksun haihu sukam, kuma dab da dab sukaita kancamo 'ya'yan, ayanzu haka sunan d'an Fauziyyane kawai yarage gobe idan ALLAH ya kaimu, dan itace k'arshen haihuwa..
Su fiddausi duk suna gida sunzo wanka, iyayensu kowa ta zuba k'arya a hidimar sunan 'yarta, yanzu maman Fauziyya da innarsu munaya kawai aka zubama ido aga yanda zasuyi nasu.
Inna dai bata d'ad'ara kanta da k'asaba, iya abinda ALLAH ya hore mata iya shine tai k'udiri yi a hidamar sunansu Munubiya idan sun haihu. Fatantama su sauka lafiyar, dan gasu suna neman share watanni na goma haihuwa babu amo babu labari.
Mama Rabi'a cema kawai keta k'ok'arin ta na ganin sun tanadi dukkan abin fita kunya, sai Aunty Salamah dake taimaka musu, wadda a yanzu tazama 'Yar uwa agaresu makusanciya, dan komai nasu tana tsaye a akai tsakaninta ga ALLAH.
WASHE GARI akasha sunan d'an Fauziyya. Wanda mijinta da mamarta suka bada mamaki, masu shirin asha kunya sai aka barsu su dajin kunyar da shak'ar bak'inciki irinna masu hassada.
Itama tamkar su Haleematu gida ta taho wankan jego.
**************************
A wata ranar talata datai dai-dai da cikar cikunanmu wata goma da sati biyu natashi da matsanancin ciwo, Wanda ya rikita Galadima da ahalinsa, nan take doctors sukace haihuwace, aka fara shirin kar6arta amma ina, gadai haihuwar gadan-gadan da gaske amma kuma nagagara haihuwar har washe garin laraba.
Nayi masifar galabaita, Galadima yace sumin cs idan bazan iya haihuwa da kaina ba.
Amma sukace zan iya haihuwa.
Ranar laraba da daddare Galadima da Momma na kusadani suna ta tofamin addu'a saboda zufar danakeyi, nace su kiramin munubiya, babu musu Galadima ya kira Yaa marwan.
Shima dakaji muryarsa zakasan a rikice yake, hakan yasaka Galadima tambayarsa ko lafiya?.
Yaa Marwan yace, “dadai sauki ranka ya dad'e, tun daren jiya Munubiya ke nak'uda amma haihuwa shiru, sai sunan Munaya kawai taketa kira”.
Mik'ewa Galadima yayi tsaye, yace, “muma ai halin da ake ciki kenan, yanzuma itace tace akira mata ita, please kakai mata wayar”.
“ok”. Yaa marwan ya amsa yana nufar d'akinda Munubiya take...............✍🏻
Barkanmu da dawowa.🤩✋🏻
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭👏🏻
*_typing📲_*
💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._*
*_♦RAINA KAMA.....!!♦_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
_________________________
*_HASKE WRITERS...._*
_gaisuwarku ta musammance, alkairin ALLAH ya baibayeku aminan kwarai abokan tafiya👍🏻😽._
I love you manya-manya fa🥰🥰🥰🥰🤩🤸🏻♀
________________________
~book 2~👉🏻2⃣2⃣
................Cikin kuka Munubiya tace, “y'ar uwata ki taho gida please”.
Munaya dake saurarenta ta share nata hawayen itama, “insha ALLAH zan taho, ki kwantar da hankalinki, daga yau zuwa gobe ko yaushe zaki iya ganina sweetheart”.
Daga haka munaya ta mik'ama Galadima wayar tana cigaba da share hawaye.
Hankalinsa atashe yace, “miyasa zakimata alk'awarin zuwa? bayan kinsan ga halin da kike a ciki”.
“kayi hak'uri yalla6ai, gara ka barni Na tafi shine mafi a'ala, tun farko y'ar uwata bata 6oyeminba ta sanarmin naje gida Na haihu, idanma baka kainiba to wahala kawai zanta sha anan d'in tunda hakan take buk'ata”.
Galadima jiyay tamkar ya make Munaya, ya haukace mata da masifa kaikace zai cinyeta d'anya, “wannan ai canfin banzane da wofi, ALLAH shine kawai maiyi ai bawani alk'awarinku ba, shin Ku bazaku tausayama kanku baneba? yaufa kwannanki biyu kina wahalarnan, wane irin taurinkai ne wannan.......?”.
Dakatar dashi Momma tayi ta hanyar d'aga masa hannu, ta dafa k'afad'ar munaya dake kuka tana fad'in “y'ata dama kinmata alk'awarin zakije Nigeria ki haihu ne?”.
“Momma ba alk'awari namataba, amma kusan 2months kenan tacemin gida zanzo Na haihu ko? nikuma bance mata komaiba”.
Murmushi Momma tayi, ta kalli Galadima dake tsaye yanata kumbura dan haushi. “Muh'd anemi ticket d'in Nigeria yanzunnan”.
Da sauri yace “Momma amma......”
Hannu ta d'aga masa alamar bata buk'atar jin komai. ya had'iye wani k'ullutu daya tsaya masa a mak'oshi, shifa ba tafiyar tata bace matsalarsa, shima akwai tashi manufar da dalili, amma bashida ikon yin jayayya da Momma, waya ya zaro a aljihu. Ya lalubo wata number yay kira, ficewa yay daga d'akin.
Momma tacigaba da lallashin Munaya daketa hawaye, ga zufa Na cigaba da jik'eta dukda AC dake aiki a d'akin.
Kusan mintuna talatin Galadima yashigo shida doctor, dannan aka shirya Munaya, nurses biyu suka kaita mota.
Wannan karon harda Momma rakkiya Airport, tanata jerama Munaya addu'oi har suka isa.
Haka sukai wannan tafiya babu shiri, Galadima kayan tun safenema a jikinsa bai ko koma gida ya canjaba, hakama aunty Mimi.
A jirgi yana rungume da ita tanata murk'ususu idan abin ya motsa, wai danma waje Na musamman aka basu dankarta takura. idan nak'udar ta lafa sai barci mai dad'i ya kwasheta, da abin yamotsa kuma tata kuka kenan tana k'ank'amesa, dukta jimasa ciwo da farce, shikam tausayinta dukya cika zuciyarsa.
Yaa marwan ma cikin haushi yakira inna ya gaya mata abinda Munubiya tayi, inna taita fad'a tamkar zata ari baki, itada ta haifi su munaya ita tasan halin kowa acikinsu, tabbas a fili Munaya tafi Munubiya fad'a, amma a bad'ini Munubiya tanada ak'idar tsiya da tsatstsauran ra'ayi, lokuta da dama idan takafe akan Abu bata tankwaruwa, kuma dolene Munaya ta amince ayi kokuwa tasha wahala, dan idan Munubiya ta murd'e abin bazai ta6a ya yuwuba saidai idan Ubangiji ya juna mata ikonsa, to amma bata ta6a zaton shirmen nasu zai iya ta6a har lafiyarsu irin hakaba.
Dole inna tashirya zuwa asibitin da kanta, taita zubama Munubiya dake fama da kanta fad'a, su mama Rabi'a da Maman Fauziyya sunata bata hak'uri, tunda dai anrigada an aikata, saidai kuma a kiyaye nagaba.
Su Munaya sun iso Nigeria lokacin tsakkiyar ranane anan, dan irin 1pm d'innan ne, dayake yakira su sarkin mota ya sanar dasu time d'in dazasu iya isowa, tun wajen 11am ma suna airport d'in..
Tunda Galadima yafara sakkowa daga matakalar jirgin rungume da Munaya akan idonsune, hakanne yasaka sarkin mota matso da motar bisa alfarmar ma'aikatan wajen, suna gama sakkowa k'afarta ta rik'e, dole ya d'auketa daga ita har nauyin cikin ya k'arasa da ita motar, mutane duk tausayinta yakamasu.
Tunfa a mota labari yafara canjawa, dan Munaya tafita hayyacinta sosai, Galadima sai tsawa yakema sarkin mota, ALLAH daine kawai ya kaisu asibitin lafiya, aiko suna shiga dogarai suka shiga da gudu cikin asibitin kiran doctors.
Tunima Galadima ya kuma sunkutarta yayi ciki, a hanya yagamu da nurses da gadon d'aukar marasa lafiya, bai d'orataba, yawucesu abinsa, doctor Farida ta nuna masa d'akin da aka canjama Munubiya.
Gadon da aka tanada dan Munaya ya d'orata, Munubiya tashiga mik'o mata hannu tana kuka, itama a wahalce tamik'a mata nata, dan gadon kusa da kusa aka sakasu....
A tare suka dinga Neman yafiyar junansu suna kuka, sai tausayinsu ya kamasu Galadima.
Da k'yar doctor Farida tasamu Galadima ya fita suyi aikinsu, dama haka tasha dagama da Yaa marwan shima, saida ma Abbansu yamasa magana, Dan shima yana asibitin.
Munubiya da Munaya Haka suke rik'e hannun juna kowa nashan azabar nak'uda, (wannan k'auna dabance gaskiya, nak'uda ba abun wasaba amma suna son jin junansu a kusa, wato koma mutuwace tazo musu a tare?😽).
Haihuwar Munubiya ce tafara gadan-gadan, Dan haka Munaya ta k'ank'ame hannun y'ar uwarta tana kuka da kiran sunanta a galabaice, itama sai labarin yafara canjawa, Nurse da doctor Farida and doctor Zainab dake Kansu duk suka maida hankali ga Munubiya, cikin rahamar ubangiji saiga jinjiri yayi sallama duniya da kuka. tamkar jira itama Munaya ta kar6a, a time d'in Munubiya tayi shid'ewar wucin gadi, amma hannunta na cikin na Munaya datake shan azaba itama. Ba'a d'auki tsawon lokaciba itama tata mace tafito, saikuma sabuwar nak'uda ta tashi a tare suduka, yanzu Munubiya mace Munaya kuma namiji, na Munaya na fad'owa wani yakuma biyo baya😳.
Turk'ashi, ALLAH sarkin rahama da tausayi, maiyin yanda yaso kuma ga Wanda yaso, Munubiya ALLAH yabata k'autar tagwaye mace da namiji, yayinda Munaya keda uku, maza biyu mace d'aya.
Su doctor Farida duk sun kacame da murna da k'ok'arin gyara yaran, kaikace su akama haihuwar.
Dandanan aka shiga goge yara da zaitun, amma cikin hattarar kar a had'esu agaza ganewa..
Su Munaya ma dai kulawa ta musamman aka basu, amma Munubiya ta suma, kuma bata farfad'oba, hakanne ya tada hankalin su doctor Farida suka rufu akanta suna bata dukkan wani taimako, sama-sama Munaya ma kejin 'Yar uwarta tashid'a, hakanne yasata kuma k'ank'ame hannunta hawaye na zurara mata, itama bawani k'arfine da itaba, Dan ko idanu dak'yar take iya d'agawa, dishi-dishima take ganin komai.
Lamarin yana san zama babba, Dan saida wani babban doctor ya shigo dole, ganin shigi da ficinsu doctor Farida yayi yawa yafara ankarar dasu Galadima.
Nanfa suka fara turkesu da tambayar ko lafiya?, sukuma suna basu amsa da babu komai, kowa dai bai yardaba, dukda suna jiyo kukan jariran.
An d'auki wasu adadin mintuna kafin numfashin Munubiya ya dawo, ajiyar zuciyar da Munaya tasaki duk saida yasaka su doctor Farida kallon ta da tausayi, dukda tana cikin wani hali itama, amma hankalinta nakan 'Yar uwarta.
Sun kimtsasu tsaf, daganan aka musu allurar barci dansu sami Hutu, yara dai kam Alhmdllh, duk da sun lura d'aya daga cikin na Munaya bai cika kuzariba, kamar sauran mace da namijin sun fishi lafiya, amma basuda tabbas tunda basu bincikaba. Nurse d'aya tafito ta kar6i kayan haihuwar takoma, duk an saka musu, dukda basu zama iri d'aya ba tunda sunzo babu tabbacin miza'a haifa, musamman ma su Galadima, gara su Yaa Marwan sunsan ita Munubiya dama biyune.
Tunda su doctor Farida suka fito Galadima dake ta kaikawo shida Yaa marwan da Muftahu suka maido hankalinsu Kansu, Galadima bai iya matsawa ba, saisu aunty mimine suka k'arasa ga su doctor Faridan.
Kowa yana k'ok'arin tambayar abinda ke faruwa.
Doctor Farida tayi murmushi, tace, “to ai bakine bazai iya fad'a ba ma, inaga kawai angunan k'arnin su shiga daga ciki, idan sun fito kwaji komai”.
Yaa marwan da Galadima suka kalli juna, kowa yana fargabar abinda zai tarar d'in.
Aunty Mimi ce takama hannayensu tana fad'in “kuje mana, mi kuke tsorone wai?”.
Kowa tamkar an doke masa gwiwa haka suka nufi d'akin, Yaa marwan ne gaba Galadima a baya.. Duk sukayi sororo a k'ofar d'akin suna bin gadajen matan nasu da jariran kusa dasu da kallo.
Badan kowa yasan kayan jikin matarsa ba dabasu iya banbancewa ba (kunsanfa mu 9ja 'yan gargajiyane🤭, kod'an canja kayannan na asibiti bamayi🤣).
Galadima da Yaa marwan suka kuma kallon juna, kowa ya kasa cewa uffan, doctor Farida dake bayansu tamkar ta kwashe da dariya, tadai daure ta danne.
Ra6asu tayi ta shigo ciki sosai, ta tsaya tsakkiyar gadajen tana kallon hannun Munaya da Munubiya dake had'e da juna har yanzu, sunyi-sunyi su saki amma sunk'i, sai suka saka musu lokar asibiti a tsakkiyar aka d'ira hannayen Dan kar suyi sanyi.. Juyowa tayi ta kallesu da murmushi a fuskarta, tace, “wannan itace Munubiya ga babies d'inta nan 2 mace da namiji, wannan kuma Munaya ga nata 3 maza biyu mace d'aya. Ina muku fatan alkairi gaba d'aya, ALLAH ya rayasu akan sunna”. tana gama fad'a ta juya ta fita tabarsu.
Binta sukayi da kallo harta fice, sannan suka maido ga iyalan nasu, saikuma kowa ya k'arasa da hanzari ga matarsa.
Yaa marwan yasaki murmushi yana d'aukar macen, sanan ya d'auki namijin shima, dukya rungume.
Galadima kam durk'usawa yay gaban gadon yasa gwiywoyinsa a k'asa ko k'yank'yami bayayi, dukda angyara wajen tsaf tamkarma ba'a haihunba.
Hannunsa d'aya ya d'ora agoshin Munaya da duk yaga ta masifar rame masa yau, d'ayan kuma yafara tsafa kumatun yaran d'ai-d'ai, hawaye masu d'umi Wanda shikad'ai yasan ma'anarsu suka fara sauka a kumatunsa. Cikin lumshe ido ya matsa ya sumbaci goshin Munaya da hancinta, sannan ya dawo kan babies nashi yana sumbatarsu.
Yaa marwan ma yanacan ya duk'ufa kan matarsa yana mata kalamai masu dad'i acikin kunne k'asa-k'asa, kai kace idonta biyu tana jinsane😹.
Galadima ya share hawayen fuskarsa, cikin murmushi yace, *“UBANGIJINA ka gamamin komai, yau nine da k'yautar abin cikin kwan d'ai-d'ai har 3 a lokaci d'aya, badan k'arfina kabaniba, bakuma Dan nafi sauran bayinka ka baniba, suma y'ay'a jarabawace ga iyaye, ya Mahaliccinmu kabamu ikon bama yarannan tarbiyar da zasu zama cikin alfaharin MANZON ka da addininmu mu da mahaifansu mata, ka rayasu bisa turbar addinin islama, ALLAH yasa suzama masu tausayi da jink'ai gana k'asa dasu damu kanmu, su zama masu girmamawa da mutunta na sama dasu a duk inda suka shiga, ya RABBI ka rinjayar da zukatansu ga bautarka domin rabauta a duniya da lahira, ka nisantar da zukatansu da gangangar jikinsu ga sa6onka komin k'ank'antarsa dagasu har 'yan uwansu gasunan guda biyu da k'annensu masu zuwa da dukkan y'ay'an Al'ummar musulmi. I love you so more and more my Darling children's, ina muku barka da isowa duniya gidan gwagwarmaya, ALLAH yabaku damar cinye jarabawar da ubangiji ya k'addaro a cikin tsawon rayuwar da zakuyi a dunia kafin Ku koma garesa”.*
Yaa marwan ya amsa da amin shima fuskarsa d'auke da murmushi.
Tashi Galadima yayi yaje gareshi suka rungume juna.
Galadima yace, “d'an uwana ina tayaka murna”. Yaa marwan ma yace, “ranka ya dad'e nima ina tayaka murna”.
Sakin juna sukayi suna dariya, saikuma suka kuma cafke hannun juna cikin musabaha da nuna tsantsar farincikin dake baibaye da zukatansu a yau d'innan.
Aunty Mimi kasa hak'uri tayi ta danno kai d'akin babu ko sallama.
To shigowarta cefa ta fallasa komai, kowa yasan d'unbin alkairin daya sauka a wannan families guda uku a yau. Dan danan labari yafara karad'e asibiti da gidajen su Galadima Dana su Munaya.
Masarautar gagara badau, masarautar su papi, su Momma duk labari ya Isar musu harda hotunan babies gaba d'aya, kafin kacemi labari yafara zagaye social media, *FANS NA RAINA KAMA FA* babu ala, dama duk sungama shirinsu, (danma ansamu sa6ani masu tafiya india🤣, Wanda basu kai ga tafiya ba ALLAH ya taimakesu saiku tattala kud'in jiyginku babu ruwana😹😂🤸🏻♀).
Bakin Galadima da Yaa marwan da dukkan ahalin wad'annan dangi kam yakasa rufuwa, hardamu ma masoyansu.
Yauma dai su doctor Farida da jama'ar asibiti sunsha k'yaututtuka, Dan Muftahu ya baza abin mamaki, ( lokacin da su sarkin mota zasu fitone yagansu kamar a rikice, shikuma zai fita daga masarautar shine ya tambayesu, sarkin mota ya fad'a masa, bai bisuba saiya wuce asibiti, shine yasaka aka canjama Munubiya d'aki, aka tanadi gadon Munaya kuma). dukda Galadima yayi mamakin ganinsa hakan bai sakashi tambayarsa ba ko katse masa hanzari, ko'a fuskama bai nuna mamakiba.
***************
Mama Fulani Na kishin gid'e bisa kilisarta kuyanginta Na bautar da suka saba, Wambai na gefenta yana nuna mata pictures na gidaje dayake son za6ar d'aya daza'a gina masa shima acikin masarautar, don mama Fulani tamatsa suyi aure, shi matawalle yamace bazai zauna da matarsa a k'asarba. Amma mama Fulani tace dolene saiya zauna.
Wata baiwace ta shigo jikinta sai 6ari yake, ta zube a gabansu tana huttai, Wambai ya daka mata tsawa.
Firgita tay tayi baya zata fad'i, Mama Fulani ta d'aga masa hannu alamun ya barta.
“haba Granny kina ganinfa yanda ta shigoma mutane a haukace, saikace wasu sa'ointane a wajen?”.
Uffan mama Fulani batace masaba, sai wani k'asaitaccen murmushi datayi tana kallon amintacciyar baiwarta, alamu tamata da ido na ta tambayi mi dattijuwar tazo dashi?.domin itace dama mai kawo ma mama Fulani duk wata gulma takowane 6angare a masarautar, Dan ita babu sashen dabata da 'yan lek'en asiri, kuma wannan dattijuwar baiwa itace shugabarsu, komai suka tattaro ita zasu fad'awa ita kuma takawo ga mama Fulani.
“mike faruwa tulluwa?”. Amintacciyar baiwar mama Fulani ta fad'a tana kallon dattijuwa tulluwa dahar yanzu jikinta baibar 6ariba.
“Ranki ya dad'e ki gafarceni da abinda nazo fad'a, banida za6in daya wuce hakan, domin da kiji a bakin wasu gara kifara ji abakina danki tabbatar nasan aikina”.
Mama Fulani ta hura hanci, yayinda izzarta ta k'aru, sosai ta tashi zaune idonta akan tulluwa.
Batareda tace uffanba tulluwa tacigaba da magana, Dan tasan ma'anar kallon ta cigaba da magana kenan.
“ranki ya dad'e yanzunnan labarin haihuwar matar Galadima ta iso wannan masarauta, ba haihuwar baceba abin girgiza abinda ta haifanne, idan kinbani izini sai na fad'a uwar gijiyata”.
Wani kakkauran yayu mama Fulani ta had'iye, Wambai daya cika yay fam da haushin wannan shegiyar baiwar ya Dalla mata harara, “dalla malama kifad'a kinwani zauna cancana magana kamar wata zuma”.
“ALLAH ya huci zuciyarka ranka ya dad'e, maganarce tanada nauyi. dama labari ya iso ta haifi yara uku ne maza biyu mace d'aya....”
Wambai yay masifar razana harda mik'ewa, mama Fulani kam ko motsi batayiba, sai wani k'ayataccen murmushi na k'asaitattun mata masu izza da mulki tayi, ta d'ago ido ta kalli Wambai cikin harara tace “kai kuma miye na mik'ewar?”.
Tunawa yay akwai kuyangi saiya saki murmushi basarwa, yace “mamaki mana Granny, 'ya'ya uku fa a 1 time, dolene na taya d'an uwana murna ai”. bai jira cewarta ba yafice da hanzari.
Lumshe idanu mama Fulani tayi bayan Wambai ya 6acema ganinta, ta kalli amintacciyar baiwarta fuska d'auke da murmushi nan tace araba k'yaututtuka, takuma sallami kowa.
K'yaututtukan da mama Fulani tasaka a rabama bayin gidan yasaka zancen haihuwar munaya yakuma karad'e lungu da sak'o na masarautar, masu murna nayi masu kuka nayi, dan kowa dai yasan magadan masarautar gagara badau sun iso, tunda kowa yasan Galadima ne magaji mai jiran gado, _(karku manta haryanzu sarkin yanzu sarautarsa ta ruk'on kwaryace, Dan mahaifin Galadima tsohon Sarki bawai mutuwa yayiba, sannan ba murabus yayi da kansa yace yabarma Sarki na yanzu sarautarba, so sarautar ruk'on k'warya yakeyi, kuma ko a yanzu tsohon Sarki yasamu lafiya dolene ya sauka yabashi kujerarsa, mai guri yazo kenan, mai tabarma dolensa ya nad'e🤷🏻♀)_.
**************
A 6angaren gidansu Munaya ma bata canja zaniba, Dan hassada k'ararace tafito a fuskokinsu da matuk'ar razanuwa, kenan arana d'aya Innarsu munaya ta wayi gari da jikoki 5 kenan? miyasa a komai sai Ai'sha ta fisu ne? bayan kuma sun fita gata sun fita dukiya, sukeda dangi da tarin 'ya'ya a gari, suke da ilimin zamani, k'asarsu ce ba karoro sukazoba?.
Innaro kam dai tadage sai zuba gud'a take da taka rawa, gud'artace ma ta ankarar da jama'ar anguwar mi ake ciki, dandanan aka cika mata gida ana tayata murna.
Babu kunya tasaka Shu'aibu ya kaita asibitin, bayan kwanakin munubiya biyu akan gwiwa kuma tasani amma bata ta6a nuna sha'awar zuwa dubata asibitin ba ma.😏
***************
Tunda kuyanginta suka fice tamik'e zaram itama, safa da marwa tafarayi na tsantsar tashin hankali a makeken falonta daya gama jin kayan alatu tamkar bana tsohuwa ba, zufa dukta jik'eta sharkaf, sai kuma maimaita fad'in “y'a'ya uku? Y'ay'a uku fa? wannan 'yar yarinyar ta haifa y'ay'a uku?, kai banma yardaba gaskiya, kodai k'aryane basuji d'ai-daibane?. jikinta na rawa ta jawo wayarta tayi Kiran Momma.
Momma dake cikin tsantsar farinciki saboda isowar labarin haihuwar jikokinta sabbi fil a Leda har uku, ta d'aga kiran mama Fulani.
A mutunce ta gaisheta kamar yanda ta saba koyaushe.
Mama Fulani bata amsaba, sai tambaya data jehoma Momma, “Zeenah ashe matar d'anki ta haihu? Amma aka kasa sanarmin sai dai naji a jita-jita?”.
Murmushi momma tayi, tace, “ranki ya dad'e a gafarceni, amma Nima yanzunnanma nakeji, dan suna isowa Nigeria tafara nak'uda tun a mota”.
Cikeda mamaki mama Fulani tace, “yo a ina ta haihun?”.
“anan Nigeria ne ai mama”.
“Ai nazata anan India ne shiyyasa na kira, to ALLAH ya raya, bara nasa a bincikan asibitin”. bata jira cewar Momma ba ta yanke wayar, murmushi kawai Momma tayi tana girgiza kai, ta k'agara Abie ya tashi a barci ta guntsa masa wannan daddad'an labari.
Saman kujera mama Fulani ta jefa wayarta tana cije la66anta da sakin wata k'aramar k'ara hawaye na zubo mata, ita kuma tata ta k'are, Matawalle ya dace da haihuwar wad'annan 'ya'yan ba Galadima ba, dolene tanemo mafita da gaggawa kafin lokaci ya k'ure mata.
🤣🤣🥴
★★★★★★★★★★
Kiran Momma daya shigo a wayar Muftahu ya saka shi mik'ama Galadima, dama shiya kirata ya Sanar mata haihuwar, ganin haka ta kirashi danya had'ata da Galadima, tunda taga suna tare.
Hakkanne yasaka Galadima fitowa harabar asibitin yana amsa mata, cikeda tsantsar farin ciki suka shiga taya juna murna, ya tambayi ina Abie, ta Sanar masa yana barcine.
Momma tace, “an sallamekune?”.
“a'a Momma, har yanzu suduka barcima suke, gashi magriba ma ta gabato anan, banama zaton sallamarnan yau, maybe sai zuwa safiya”.
Ajiyar zuciya momma ta sauke, tace, “to Muh'd yau fa barci bai gankaba, dolene idonka yazama abud'e tundaga kan doctors, Nurse's, da makusantanka, hankalin duk wani idon mak'iyinka yanzu akan wad'annan bayin ALLAH guda uku yake, sunsan shine kawai tarko mafi tsauri dazasu maka a yanzu, su zaituna suna hanya itada kuyangi 5 amintatu da zasu zauna daku, itama Zaitun (mom) bazata komaba sai anyi suna, anayin suna kuma Munaya zata koma gidansu tayi wanka irin na al'ada da kowa ya Sani, tunda kasan dokar masarautar taku kenan. Wannan kawai shine mafita”.
Ajiyar zuciya Galadima ya sauke, muryarsa cike da damuwa yace, “insha ALLAH Momma duk za'ayi hakan, amma zama gidan nasu bak'ya ganinsa kamar had'ari? tunda za'a iya tsutar dasu a can, dan babu wani tsaro”.
Murmushi Momma tayi har Galadima najin sautinsa, tace, “nasan abinda nakeyi ai Muh'd, bazance aturasu canba nasan zasu cutu, kaidai kawai kayi hakan, sauran bayani saika dawo zakaji komai, su zaitun nasan suna gab da isowa insha ALLAH. Papi ma yace yakira wayarka bata shigoba daga kai har Haneefa”.
“tab, yoni Momma ai banmazo da waya ko d'aya ba wlhy, duk nan na mantasu a mota, kima saka khumar ya kawo miki, saidai zuwa Safiya nasamu k'arama na r'ik'e”.
“to shikenan, dama haka nafad'a masa nima maybe kabar wayoyin anan, idan ta farka dai a kirani naji muryar d'iyata nima, konaji sanyi”.
Murmushi Galadima yayi yace “insha ALLAH Momma”.
Koda wayar ta yanke saiyayta juya maganganun momma a ransa yana musu fashin bak'i d'ai-d'ai. Haka ya koma zuwa cikin asibitin, dan anfara addabarsa da kallo, shi saiya rasama mi suke kallon? Shidai bayasha banban da sauran halitta bane, bakuma za'a kallesa ace ba bak'in fata bane, bakuma wasu kayan ado na musamman ya sakaba, hasalima k'yank'yamin kayan jikinsa yakeyi, dan sun kwana suna Neman yini a jikinsa, (tunda ba time d'inmu d'aya da India ba) yaja guntun tsaki yana k'arasawa ciki ya mik'ama Muftahu wayarsa.
***********
Sai bayan isha'i su mom suka iso, dan basu sami jirgi da wuri ba, a lokacin jama'ar gidansu Munaya suna asibitin, masu kukan zuci nayi masu murna da gaskiya nayi, hakama a wasu daga masarauta suna nan, wasu lek'en asiri kawai aka turosu, wasu ko na taya farincikine da tabbatarwa.
Yau dai yan gidansu Munaya suna kallon abin mamaki, da gaske dai inna Ai'sha tamusu fintinkau irinna jirgi, saidai hange daga nesa da harara cikin duhu.
Mom bakinta yak'i rufuwa, harda rungume Galadima, Nuren kuwa hardasu taka rawa🤣, Muftahu na masa lik'i.
Mutane abin ya birgesu, Galadima yay murmushi yana d'an dukan kafad'ar Nuren da Muftahu kawai.
Su Munubiya basu farkaba har sannan, doctors sunce babu wata Matsala, a barsu su huta sosai yanda zasu tashi da kwarinsu zuwa Safiya.
Dole dai Galadima yasa aka zuba police a asibitinan ranar, sauran kuma anbarma UBANGINJIN TALIKAI dake kallon motsin kowa.
Masu tafiya duk suka tafi, aka bar masu kwana kawai.
Galadima da ya dage anan zai kwana shima, da k'yar dai mom ta lalla6ashi ya tafi gida kodan yasamu yad'an huta, kallo d'aya zaka masa ka gane a matuk'ar gajiye yake, jijiyoyin Kansa sunyi rad'a-rad'a, ga yunwa waddama ya manta da ita da alama.
Wannan dare dai ya kwana rayashi da bautar ALLAH ne da godiya mai yawan gaske.
Innarsu Munaya ma dai kuka sosai tasha na dad'i, itama haka ta raya wannan dare, hakama Abba, shima yamik'a godiyarsa ga ALLAH dan lokacin dayake buri da tanadi ya cika, koba komai zai sauke nauyin dake rataye a wuyansa insha ALLAH.
Washe gari...............🤩✍🏻
*_media ko bala'i, kayi turanci a novel ace ka cika iyayi da son asan ka iya turanci🤦🏻♀, muda muke koyo muyi ace bamusan abinda mukeba🤦🏻♀, kai jama'a babu mai iyama 'yan social media sai ALLAH, ko uwarka ka yanka kagasa tasha mai kwallan tana d'iga, da wani yagama ci zaice bataji gishiri ba🙄, ALLAH ya shiryar damu muda bakunanmu dai.🙏🏼._*
_Ayshan sadiq sak'onki ya iso gareni, nakuma gode kwarai da gaske, saidai ina mai baki hak'uri da sauran fans d'ina, a gaskiya weekend d'inan ina muhimman abubuwane a cikinsa, bazan iya alk'awarin typing ba, sannan ni kaina idanuna 👁👁da Brain 🧠 d'ina suna buk'atar hutu, inada aure, akwai wasu hak'k'oki a kaina bana typing kawai ba, kunga yadace suma na basu lokacina, dan Ku gamsu nake zaman yin typing mai tsawo, insha ALLAH idan mukai hak'uri kamar yaune raina kama zaizo k'arshe abarma yayinsa Ku manta dashi saikuma wasu dazasu 6ullo daga sauran writers namu, dan haka muringa hak'uri da abinda ALLAH ya k'addara namu a lokacin da ya tsara, kar muyi gaggawa domin aikin shaid'ance, nima Ku duba nawa buk'atun amatsayina na mutum kuma mace mai rataye da igiyar auren. Ina godiya kwarai da gaske da k'aunar da kuke nunama wannan buk, bammasan yanda zan nuna muku farincikina ba kusan inajin dad'in Comments naku nima, amma ina sonku irin sosai d'inan a raina, kumuje zuwa guys, duk Nisan jifa k'asa zai fad'o👎🏻_
I love you mazga-mazga all.😘😘🥰🥰😍😍😍🤝🏻.
Ayshan sadiq, ina miki fatan alkairi a duk Inda kike😘😘😘😅🤝🏻.
*_ALLAH ka gafarma iyayenmu_*🙏🏼😭
[7/9, 11:05 AM] ❤y'ar K'asa❤: *_typing📲_*
💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._*
*_♦RAINA KAMA.....!!♦_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
~Book 2~ 👉🏻2⃣3⃣
...............Koda Muftahu ya sauke Galadima saiya sake shiri Yakoma asibitin, tunda ya shigo idon Nuren a kansa, sai mamaki ya kamasa, shin miya maido Muftahu asibitin? bayan kuma tare suka tafi da Galadima.
Bai masa maganaba dan karma yasan ya gansa, saiya saka ido a dukkan wani motsin Muftahu d'in, shidai Muftahu baisan yanayiba, dan baima je d'akinda su Munaya sukeba, sai zagaye-zagaye dayaketa famanyi har ALLAH ya wayi gari lafiya.
Wannan lamarifa ya zaune a zuciyar Nuren yanata kaikawo, anya kuwa ba suna zargine akan abinda ba haka yakeba?, dukda jami'an tsaro dake wajen Muftahu Nada damar aiwatar dadukkan abinda yay k'uduri tunda kowa namasa kallon makusancin Galadima, amma har ALLAH ya wayi gari baimayi wani yunk'uri na shiga d'akinba balle alamun rashin gaskiya, saima aikinsa dayay kama dana mai k'ok'arin bama wani abu kariya, “ya ALLAH ka warware wannan lamari cikin sauk'i kodan wannan bawa naka yasamu nutsuwa shima”. Nuren ya fad'a a fili yana d'aga hannayensa sama alamar rok'o.
Muftahu dake kallonsa yay murmushi yana amsawa da amin a la66ansa, daga nan yafice abinsa ya koma masarauta, saboda anata kiraye-kirayen sallar asubahi
****************
Misalin 7:30am Munaya ta farka, kamar a kunnen Munubiya itama saita farka, su mom dake d'akin suka shiga musu sannu, cikin tsantsar farin cikin farkawar tasu, dandanan aka kira doctor.
Alhmdllh babu wata matsala a tattare dasu, aka kikkimtsasu dagasu har yaran daketa barci irinna jinjirai, daga Munu... Har munaya dai kallon y'ay'a biyar sukeyi, amma tunaninsu ko cikin y'ay'an y'an uwansune.
Doctor Farida data lura da hakan tayi murmushi kawai. umarni tabama Nurses d'in abama kowa nata, kallon kallo akeyi tsakanin Munaya da Munubiya, amma kowa bakinsa yagaza furta komi, saisu kalli juna sukuma kalli jariran gabansu.
Doctor Farida dai dataga basuda niyyar d'aukar yaran tace “y'an biyu wannan itace k'yautar da ALLAH ya baku, Munubiya 2, Munaya 3.
Duk waro ido sukayi, Dan Na Munaya ne yabasu mamaki, tunda dukansu sunsan Na Munubiya dama.
Munubiya ta sakko daga gadonta batareda ta d'auki ko d'a d'aya anata ba, gadon Munaya ta nufo, ta durk'usa k'asa tana rungumo yaran, ga hawaye ga dariya tanayi, saikace sokuwa.
Munaya ma dai batabi takan nata d'inba, saita nufi Na Munubiya ta d'auka duk ta sakasu a jikinta, k'aunarsu Na ratsa dukkan 6argonta kamar yanda take k'aunar mahaifiyarsu.
Galadima da Yaa marwan dake tsaye a bakin k'ofa suka kalli juna suna murmushi, kowanne yana mamaki a ransa, anacewa y'an biyu akwai shak'uwa, sukam suna mamakin ta wad'annan Matan nasu, soyayyar dake tsakaninsu tanada ban mamaki da birgewa.
Galadima ya k'arasa ga Munaya da har yanzu take a tsaye idonta arufe y'an biyun Munubiya na jikinta, had'ata yay itada yaran ya rungume.
A firgice tabud'e ido, saitaji k'amshin turarensa, tayi baya kad'an yay saurin ruk'ota. Idonsa ya saka cikin nata yana wani murmushin dabata ta6a ganiba daga garesa. Ahankali ya furta haba “Maman y'an biyar a hankali mana”.
K'aramar harara ta sakar masa, ya saka k'aramar dariyar da tadawo da Yaa marwan daga duniyar daya tafi😳, danshifa mutunmin naku har yana Neman sakin layi🤭🥳.
Mom dake bayansu tayi gyaran murya, kowa saiyaja baya daga jikin matarsa🤣, suna wani susar k'eya.
Munubiya da Munaya sai suka koma kusa da juna, Munaya ta kama hannun Munubiya a cikin nata. ita mom dariyama suka bata, Dan haka tad'an dara tana fad'in “An sallamemu to yanzu ya za'ayi?”.
Munubiya da Munaya suka kalli juna, da alama dai basa buk'atar rabuwa, sudai su Galadima kallonsu suke kawai.
Ganinfa zasuyi daru sai mom tai murmushi, da ido taima Galadima da Yaa marwan magana akan su fita.
Babu musu suka fice, itakuma takama hannun Munaya da Munubiya ta zaunar a bakin gado. Magana take musu k'asa-k'asa wadda (banajin🙄).
Sai naga duk sunyi murmushi suna 6oye fuska. Itama murmushin tayi tana saka musu albarka. Dan murmushin nasu ya tabbatar mata dasun amince.
Daga nanfa shiri aka fara, kowacce aka had'a mata kayanta da y'ay'anta.
Gayyar gidansu Munubiya su mama Rabi'a suka kwashi nasu, nasu Galadima ma haka.
Manne da hannun juna suka fito, mutane sai kallonau sukeyi abin sha'awa da birgewa. Harda masu musu hotuna daga gefe..
Su doctor Farida ma saida suka matso akayi musu hoto danya zama acikin tarihin wannan asibiti.
Saida Munubiya ta saka munaya a mota sannan takona tashiga wajen mijinta itama, kowanne Na share hawaye, ba'a San ransu za'a rabasuba.
Saikace wad'anda za'a raba gaba d'aya🤣, kai ALLAH yabamu 'yan biyu😂⛹🏻♀⛹🏻♀.
★★★★★★★★★★★★
Tarba ta musamman su Munaya suka samu a masarauta, harma abin yaso basu mamaki, hakan dai baisa Mom tayi sake da yaran ba, duk wani motsi dai idonta Na Kansu, an musu rakkiya har sashensu dayasha gyara, yayinda Galadima keta kar6ar barka ga ahalin wannan masarauta, tun daga hadimai zuwa y'an uwansa na jini, maza da mata yaro da babba.
Za'ayi walimar cin abinda data sannu da zuwa ga y'an uku a masarautar k'arfe 8pm, wannan yasa ba'a jimaba aka barsu suka shige Dan Munaya tasamu ta huta.
Mamaki ya kama Munaya ganin an cika mata gado da tarkacen Teddy's, wannan abun haushi da yawa yake, kuzo Ku kama jera d'iyan aljanu agado kawai.
Sudai su mom suka jasu gefe aka kwantar da yaran, itama zama tayi abakin gadon tana dafe kai.
Aunty Mimi tace, “lafiya dai k'anwa?”.
“wlhy kaina ke ciwo aunty mimi”.
Sannu suka shiga yimata, mom tace, “bara laraba tazo ayi wanka kisamu kici abinci saiki sha magani”..
Munaya ta amsa da “to” tana d'an kwanciya a bakin gadon.
*********
Laraba amintacciyar baiwar inno tama Munaya cikakken wanka da babu algus acikinsa, itako sai raki takeyi da zille-zille. a haka dai aka gama wannan wanka, lokacin da suka fito sun iske yaranma Mom tamusu da kanta, ana tsaka da shafesu da mai itada Aunty Mimi.
Munaya dake d'aure da zani ta rufo babban towel a jikinta ta zauna a bakin gadon tana jingina da fuskar gadon, k'asa-k'asa take kallon yaran da mamakin anya kuwa itace wai ta haifesu? koda yake ba'a jayayya da ikon ALLAH ai, tanajin k'aunar yaranta a har cikin jininta, hakama Na y'ar uwarta, amma data tuna zasu rabu kwana kusa sai hawaye suka cika mata ido.
A dai-dai wannan time d'inne Galadima yay sallama, hannunsa d'auke da Leda fara.
Aunty mimi da mom dake sakama yaran kayan sanyi suka d'ago duk suka kallesa suna amsa masa sallamar.
Idonsa akan Munaya datai masa kallo d'aya ta d'auke ido, murmushi yayi kawai ya zauna a bakin gadon yanama su mom sannu.
Cikin tsokana mom tace, “aikin kud'i nikam nakeyi, musamman akan kishiya sa haushi, bar saurin godemin”, tai maganar tana dungure d'an hancin macen dake hannunta.
Murmushi kawai Galadima yayi, sai Aunty Mimi CE ke bama mom amsa da “habawa Mom, dukfa kishinki keda Momma kwayi Ku gama, itafa wannan sarauniyar saita za6a ta darje ehe”.
Mom tai dariya tana mik'ama Galadima ita, “yo da wannan nanannen hancinne zata za6a ta darje d'in? maji magani dai ai”.
Galadima ya lumshe ido yana manna yarinyar da k'irjinsa, k'aunarta Na rsatsashi, ya sumbaci goshinta sannan ya bud'e idonsa, kwantar da ita yayi akan cinyarsa ya bud'e ledar yana fiddo dabino mai k'yau da tsafta, a bakinsa ya saka ya tauna, kafin ya d'ora bakin nasa akan na yarinyar ya zuba mata, da farko yamutse fuska ta shigayi, taji bak'on abu a bakinta, saikuma a hankali tafara motsa d'an bakin, galadima dai yana kallonta da murmushi, dadai taji zak'i saita mamule abinta.
Mom tace, “oh su madan kamila kenan, anji zak'i”.
Dariya duk sukayi, ya d'auketa yamata kiran sallar hud'uba a kunnenta sanan ya ajiyeta a gefe yana fad'in “ALLAH ya rayaki akan sunnah da tafarkin gaskiya”.
Su mom suka amsa masa da amin.
Kallon Munaya daketa shafa manta kamarma batasan dasu a d'akinba yayi, yanda taketa wani basarwa shi mamaki tabashi, baiyi zaton hakanba gaskiya, cayake zata nuna tsantsar farincikinta akan yaran?. janye idanunsa yayi ya kar6i d'ayan yaron.
Shima haka ya tauna dabino ya bashi, sannan yamasa hud'uba da addu'a ya kwantar dashi. Kar6ar d'ayan ma yayi, Wanda bai cika kuzariba, yad'an masa kallon wasu mintuna yana tatta6a jikin yaron, sai kuma ya kalli mom da Aunty Mimi da suma kallonsa sukeyi.
Mom tace “Yaya dai Sameer?”..
K'aramar ajiyar zuciya yayi yana shafa sumar yaron, “mom yaronnan kamar baida kuzarin sauran 'yan uwansa”.
“nima na lura da gakan Sameer, amma maybe yanayinsa kenan, kasan kowa da yanayin da ALLAH yake yinsa ai”.
“hakane”. ya fad'a cikin sauke ajiyar zuciya, sannan ya d'auki dabino shima yamasa tamkar sauran y'an uwansa, yaron yadad'e bai shanye dabinon ba, daga Bayama saiya fara kuka mara sauti.
Rungumesa Galadima yayi yana hura masa k'aramar iska a kunne da d'an jijigashi, sai kuwa yayi shiru, shima hud'uba yamasa, ya kwantar dashi kusada y'an uwansa amma sai yaron yakuma Sanya kuka, gashi muryarsa bata fita da k'yau.
d'aukarsa ya kumayi yana murmushi da fad'in “oh little Sameer what happen?”.
Mom tace, “shagwa6a ce mana”.
Dariya Aunty Mimi tayi, yayinda Galadima da Munaya suka murmusa, Dan duk abinda ke faruwa tana allonsu ta gefen ido, amma ta basar kamar bata d'akin.
Fita Aunty Mimi da Mom sukayi suka barmusu d'akin.
tuni 6angaren ya rikice da k'amshin girki, dan cikin kuyangin da su mom sukazo dasune suke tsara girki wa maijego dasu kansu.
Tashi Galadima yayi d'auke da yaron a jikinsa ya nufi inda Munaya take zaune, tun d'azun tagama shafa man amma tak'i tashi ta saka kaya.
Zama yay kusada ita sosai jikinsa har yana gogar nata.
Da sauri ta yunk'ura zata mik'e, ya saka hannu d'aya ya ruk'ota yana maidata.
Kallonsa tayi fuska a cunkushe kamar zata fasa kuka, idanunsa ya saka acikin nata yanda bazata iya janyewa ba, aiko duk k'ok'arinta nason ta janye d'in ta kasa, sai cika sukayi da kwalla, dan yana ganin k'yallin ruwan hawayen.
Yad'an murmusa yana lumshe ido da bud'ewa a kanta. muryarsa cikeda k'asaita da sanyi yace, “kekuma salon taki murnar kenan?”.
Had'iye kukan dake Neman kufce mata Wanda itama batasan dalilinsa ba tayi, tayi murmushin takaici tana janye idanunta daga cikin nasa, muryarta a sark'e cikin sanyin rauni tace, “Ina tayaka murnar sosai yalla6ai”.
Lips nashi yad'an cije, ya lalla6a ya ajiye yaron da barci ya d'auka gefen y'an uwansa, Munaya duk tana kallonsa.
Kuma matsawa yay jikinta sosai ya jawota jikinsa, batayi yunk'urin hanashiba, kamar yanda bata hana hawayenta zubaba. Ya saka tattausan hannunsa yana share mata hawayen, “Friend dukda bansan miya sakaki kukaba ina mai baki hak'uri, wannan ranar bana buk'atar damuwar kowa sai farinciki, musamman ma daga gareki, ina rok'onki alfarmar fansar wannan damuwar taki da farinciki akan kowanne farashi, komai tsadarsa kuwa”. ya k'are maganar da sumbatar sumar kanta.
Murmushi tayi, ta d'ago daga jikinsa idonta akan yaran dake jere reras abin sha'awa. Shima d'in su yake kallo.
“bana cikin kowacce damuwa da kake tunani yalla6ai, kawai dai...” sai tayi shiru.
Kallonsa ya maido gareta, yace, “kawai dai mi yalla6iya?”. ‘ya k'are maganar cike da tsokana’.
Ta murmusa tana mik'ewa tsaye, wardrobe ta nufa ta fiddo sabbin kayanta cikin na lefe, bata kuma kallonsa ba ta wuce bathroom domin saka kayan.
Binta yay da kallo harta shige, yasaki miskilin murmushi yana kwantawa kusada yaran, a fili ya furta “yarinya nasan matsalarki”. yay maganar yana sumbatar kuncin na kusa da shi, sauran kuma ya shafa Kansu.
A haka Munaya ta fito ta iskeshi, ya ta6a wannan ya ta6a wancan, kallo d'aya tamasu ta d'auke kanta.
Sallamar da akayi a bakin k'ofar ya saka Munaya amsawa da bada izinin shigowa.
Laraba tashigo d'auke da tire babba.
Da sauri Munaya ta nufeta ta kar6a, Dan dattijuwace sosai, sannu ta mata tana fad'in “iya aida wanine ya kawo”.
'Yar dariya laraba tayi, tace, “dole na kula da amanar uwar gijiyata ai ranki ya dad'e”.
Munaya da Galadima suka kalli juna suna murmushi, Dan sunsan inno take nufi.
Laraba ta juya zata Fifa saboda ganin Galadima na nan.
Kiranta yay ta juyo, yace, “zokiyi aikinki kar Inno taga ta rame tace baki rik'e amanaba, nima yarana abincinsu suke buk'ata”.
Hararsa Munaya tayi, yay Biris kamar bai gantaba, saima d'an yatsansa daya saka cikin hannun yaron, shiko ya rik'e gam tamkar yasan minene.
Laraba tace Munaya ta zauna ga abinci taci..
Yamutsa fuska Munaya tayi, kamar zatayi kuka tace, “wlhy iya bakina banajin d'and'anon koda yawuna ma”.
“hakane ai saidai hak'uri ranki ya dad'e, dama wasu idan sun haihu sukanyi k'am baki, amma a hankali zai canja”.
Badan munaya tasoba ta zauna, laraba tabata kunu mai k'yau da aka dama don ita, sai k'amshin kayan yaji yakeyi, sai farfesu.
Kallon abincin kawai Munaya keyi, amma ko kad'an batajin sha'awar ci, ta tuna kwanakin baya da idan taga abinci jikinta har rawa yakeyi wajen son ci, hikimar ubangiji daban ce, ta d'ago ido suka kalli juna itada Galadima dake kallonta tun d'azu, a zuciyarsa yana tuna kwanaki uku rak dasuka shige, yanda ta maida abinci, murmushi yamata ta d'auke idonta ta maida ga abincin.
A haka Mom ta shigo ta iskesu, zama tayi tana fad'in “yanaga bakici komaiba?”.
Idon Munaya cike da kwalla tace, “ALLAH mom banajin d'and'ano”.
Zama mom tai kusada ita, tace laraba taje itama ta karya. Kunun ta d'auka ta tsiyaya a Kofi ta d'iba mata farfesun, “kar6a maza runtse ido ki shanye kunun nan d'iyata”.
Kunyar Mom ta sakata k'ar6a tana had'iye kwallarta, tafara sha badan tanajin dad'inba, sai dan tsatstsareta da ido da Galadima yayi shida Mom. ahaka dai tasamu tasha yafi rabi, dama yunwar takeji, dad'in bakinne kawai bataji, shima farfesun tad'anci, dandanan tafara zufa. tace,
“Mom dan ALLAH bara na kunna AC”.
“a ina?”. ‘galadima ya fad'a yana tashi zaune da sauri’.
Ita mom ma dariya ya bata, yawani had'e fuska yana harar Munaya, “malama babu wani AC da zaki sakama mutane anan, kina ganin yara duk da mura sukazo duniya saboda rashin jin maganarki.....”
Mom ta katseshi da fad'in “ai bama zai yuwuba, itada ke jego ko fankace a d'akinnan ai saidai kallo kuma, yanzu ruwan sha ma sai mai zafi”.
Galadima ya sakko daga gadon yana fad'in “hakan ai shine dai-dai wlhy, remote d'in AC d'in ya d'auka a lokan gefen gadon ya masa yanda bazata iya control d'insa bama gaba d'aya, sannan yafice abinsa yana murmushin mugunta.
Mom ta girgiza kai kawai, a ranta tana mamaki canjawar Sameer......
Maganarsa ce ta katse mata tunani, harya fita ya dawo baya, “mom ga maganinta nan tasha, kuma yaranan yunwa sukeji”. ‘yak'are maganar cikin marairaicewa’.
Dakuwa mom tamasa, “Sameer kaci kidanku, wai yaushe kama fetsare hakane ban saniba?”.
Fita yayi yana dariya, ta kirashi da sauri. Kuma dawowa yayi, tace, “kasandai Doctor tace a nemi madara, naga kuma bama kada niyyar hakan”.
Gaba d'aya fara'ar fuskarsa ta d'auke, yad'an shafi girarsa da d'anyatsa d'aya yana fad'in “Mom wai wace madara ga abincinsu?, ALLAH dai ai shiya haliccesu, kuma shine zai wadatasu da abincin nasu, amma kawai sai a kama wani danna musu wata madara? dan ALLAH mu ajiye zancen madarar nan ma gefe mom”.
Numfashi mom ta sauke, tasan murd'ad'd'en halin Galadima da dagewa akan ra'ayinsa, cikin kwantar da murya tace, “na yarda da maganarka, amma ita za'a tausaya mawa, shayar da yara uku bafa abune mai sauk'iba Sameer, wasuma d'ayane idan suna da fargabar shayarwa kaga duksun k'are sun lalace, koda dai sau d'ayane sai a ringa basu madarar a rana, tunda ALLAH dai baya hanaka yanda zakayi bane”.
Tashi Munaya tayi tana hawaye, taje ta hau gadon kawai tayi kwanciyarta, ta kula Galadima yacika son kansa, tanaga saita tuna masa da matsayin auren nasu da alfarmar yarda ta haifa masa y'ay'an dayake neman nuna mata mulki a kansu, aidai abin shayarwar a jikinta yake, sai kuma yanda taso tayi da kayanta, dolene ta takama wannan homar tasa birki.
Daga Mom har Galadima da kallo suka bita, yaja guntun tsaki yana juyawa zai fita.
Mom tace, “zaka siyo d'in?”.
A k'ufule yace, “zan duba”. Yay ficewarsa. shifa ya lura yarinyarnan ma batason yarannan, shin bak'in ciki take ALLAH yamasa k'yautar abinda kud'i baya sayane ko me? ALLAH zaiyi maganinta kuwa.
🤣🤣ho Galadima, uwa ta ta6a k'in d'antane🤦🏻♀.
★★★★★★★★★★★★
Mama Fulani dai yau tagaza gane kanta, duk yanda taso danne zuciyarta tayi murnar koda ganin idone ta kasa, shiyyasa ko zuwa wajen tarbarsu batayiba.
Takuma hana dukkanin bayinta da kuyangi shiga inda take.
Abinda bata saniba idon Galadima fes yake akan dukkan Wanda ya tayashi murna da samun k'yautar ALLAH, wad'anda bama su fitoba sun shiga black lists, kuma d'aya bayan d'aya saiya kartama kowa rashin m acikinsu.
★★★★★★★★★
Innaro kuwa dai saita hau tsiya dataji labarin su Munaya kowa mijinta ya d'auketa zuwa gidanta, tahau zazzaga masifa anmata ba daidaiba, babu Wanda ya kulata, dan masu zugatan suma hassada ta ishesu, basuda kuzarin taya 6era 6ari😂..
Haka tagama jarabarta takoma gida tana huci, Abba yasha dariya, danshi lamarin mahaifiyar tasu yanzu kallon rikicin tsufa kawai yake masa, inba rikicin tsufaba miye abin tada jijiyar wuya anan? Sunada damar hana yaran komawa gidajen mazajen sune?.
Shikam baba k'arami ma lokacin da take jarabar zuwa yay ya ra6a ta gefenta ya fice daga gidan.
Ai lamarin innaro sai ita🤣🤦🏻♀.
******************
A 6angaren Munubiya ma Alhmdllh, dukkan wata kulawa mama rabi'a tana tsaye akan 'yarta da jikokinta, sai zuba mata gata akeyi da k'yak'yk'yawar kulawa mai ban sha'awa.
Suruka ta gari dadi alkur'an💃🏻💃🏻😘😘.
★★★★★★★★★★★★
Mom dai da k'yar suka lalla6a Munaya itada Aunty Mimi ta amince ta shayar da yaran, suna sha tana kukan zafi kuma😹, sunsan zataji zafi tunda Na farkone, ga yaran a buk'ace suke dama, amma kukan datake yawuce Na zafi kad'ai, (basusan harda haushi Galadima bane😂🤭).
Mom data fahimci hakan saita fara lallashin da nuna mata muhimmanci hak'uri, su maza komai zasu iyayi akan y'ay'ansu, musamman ma shi da yake tsaka da d'okinsu yanzu, karma tabari irin wad'annam abubuwan su dameta, shima yafad'ane kawai amma zai sayo madaran”.
Itadai Munaya kai kawai take d'agawa amma batace uffanba, dan tagama Sanin Galadima da halinsa Na kafiyar tsiya da dagiya akan ra'ayinsa.
Bayan duk sunsha sun k'oshi Aunty Mimi tace ta kwanta ta huta kafin time d'in walimar yayi. ALLAH ya taimaketa maganin yasata barci kuwa, yaran Na gefenta suma suna nasu barcin, kowa cikinsa ya cika kenan😘.
Ajiyar zuciya Aunty Mimi ta sauke tana murmushi, tace, “Mom d'an nan naki bazai canja ba dai ashe? lamarin Sameer saishi wlhy, koda bayaso susha madarar saiya fad'a da harshe mai dad'i ba fad'aba”.
“Humm, kibari kawai, nifa harna fara murnar ya canja, Ashe yana nan yanda nasan kayana, yarinyar tanada hak'uri kuma wlhy, dan zama da mai halin Sameer saika daure, muma iyayen idan mun k'ureshi ba iya mana kawaici yakeba”.
Aunty Mimi tayi dariya, “papi ne mai tankwarashi kobai soba ai, idan yak'i bari abasu madaran dashi kawai za'a had'ashi, komin wadatar nono shayar da yara uku ba sauk'i ne dashiba, balle ita farin Shiga ma”..
Mom tace, “hakanma shine kawai mafita ai”.
***************************
*_8:15pm_*
Liyafar cin abinci tafara gudana a babban d'akin taro Na masarautar gagara badau, Munaya da y'an uku duk sunsha k'yau, hakama uban gayya Baban y'an uku Galadima, duk d'insu sunci kwalliyane cikin ainahin kayan sarauta, yaranma an nad'esu cikin k'ananun alk'yabbu. (Gado kenan🥰)
Kwai da kwarkwata Na gidan nan zaka sameshi a wajen, saidai marasa lafiya da wad'anda basa nan, mai martaba ma yana wajen, dan shine da Kansa ya shirya liyafar domin taya d'ansa murnar k'aruwa da kar6ar bak'uncin jarirai, yaran duk suna kusa dashi cikin d'an gadon da aka ajiyesu a ciki.
Kowa anan yake zuwa ya lek'asu, yamusu addu'a.
Yara sunsha addu'oi da k'yaututtuka ga iyaye da kakanni, abin zakkyau da birgewa.
Ita kanta Munaya tasha nata k'yautar.
( k'yauta da bajinta kan saka zama isashe a gidan sarauta, wannan babbar al'adace tamasu mulki a masarautun k'asar hausa, shiyyasa suke ado da ita akowanne motsinsu🤩👍🏻).
Tsakanin Munaya da Galadima babu uhum babu um-um, sai y'ar wullama juna harara (🤣nifa dariya suke ban), banga abin jin haushin junaba, duk da Na lura ita dama Munaya akwai haushi kaine ka jamin shan wahala😂, kaikuma Galadima k'asaita da jinkai ya sa kakasa fahimta balle kayi lallashi da kwantar dakai aji da y'an jariranka🤣.
To maji dai maga yanda za'a kwashe😹.
Sai 11 dai-dai taro ya tashi lafiya kowa ya kama gabansa.
Shirin kwanciya Munaya tayi, suma yaran aka musu, saiga Galadima ya shigo cikin tasa shirin kwanciyar shima, mom tace, “yauwa Sameer ya za'ayi kwanciyar kenan? A falo zaka kwanta saboda tsaro ko?”.
Murmushi Galadima yayi yana shafa kansa, yace, “kai Mom wai saboda tsaro”.
“ALLAH kuwa Sameer, lamarinne yanada ban tsoro ai, dukda nasan ga dogarainan suma suna aikinsu, gakuma mu kammu, amma dole saida namiji a kusa, da canai shima Nuren ya dawo nan Ku had'u”.
“mom kincika tsoro gaskiya, karki damu, ko ina Na sashennan akwai CCTV camera, kuma koyaya aka ta6a k'ofa ko windows akwai securitys a jiki zanji insha ALLAH”.
“To shikenan Alhmdllh, ALLAH yak'ara tsaremu da tsarewarsa”.
Galadima ya amsa da “amin” yana matsawa jikin gadon wajen yaran.
Munaya dake saurarensu a ranta tace to ALLAH ya k'yauta, a gidanka kana zama saida tsaro inaga kafita?, amma jibarsu a awajen walimarnan kaikace kowa zuciyarsa fes take babu wani k'udiri, lamarin sarauta sai ALLAH, kaita buri tamkar ALLAH yamaka alk'awarin dawwama a cikin duniyar ne, bazaka mutuba bazaka tsufa ba, ALLAH ka iya mana da iyawarka, da ace inada dama saina cirema yaranan burin sarauta a ransu, amma ya zanyi, tarigada ta zama jininsu sai dai addu'a kawai....... Saukar numfashin dataji a gefen wuyanta ya sakata saurin dawowa daga tunanin data tafi, ta waigo da sauri sai taga Galadima.
Fuska ta had'e shima yaci serious yana gyara zama.
Waige-waige ta fara saitaga babu kowa a d'akin, ashe Mom ta fita.
Baki ya ta6e ya nuna mata k'ofar bayi da d'an yatsa alamar mom tana ciki kenan.
Cikin zaro ido ta kalli yanda yazo yawani shige mata, saitaja baya, ai da kunya dai mom ta fito ta gansu a haka wlhy.
Yanda tayi d'in sai yaso bashi dariya, amma saiya had'iye, ya ciji lips nashi yana kallon yaransa, “tunanin mikikeyi ne? kinsan dai doctor tace jininki har yanzu bai gama sauka ba gaba d'aya, so ki kula, shi tunani baya kawo mafita sai matsala”. ya k'are maganar yana mik'ewa tsaye, itadai kallonsa kawai takeyi, bata ankaraba taji saukar tagwayen kisses a goshinta da kan bakinta.
Idanu ta ware waje baki bud'e, ko kallonta bai sakeyiba ya fice abinsa yana murmushi.
Mom data fito daga bayin ta girgiza kai kawai, don ganinda Galadima yamatane ya sakashi ficewa.
Kallon Munaya tayi tace, “to rufe bakin kema”.
Kunya ta kama Munaya taja bargo tarufe har fuskarta tana fad'in ka kasheni wlhy yalla6ai.
A falonsa ya iske Nuren haryayi shirin barci shima, yana zaune yana shan tea da laptop a gabansa yana aiki, Galadima ya zauna yana sauke numfashi.............✍🏻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏼_*l
*_typing📲_*
💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._*
*_♦RAINA KAMA.....!!♦_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
~Book 2~ 👉🏻2⃣4⃣
.............Kallonsa Nuren yayi da y'ar dariya, “angon jego ai dole kake sauke numfashi, irin wannan aiki dakayi haka? Y'ay'a uku fa a lokaci d'aya, a fuska dai kamar bazaka iya komaib.....”
Nuren bai samu k'arasawa ba saboda filon kujera d'aya daki bakinsa, wanda Galadima ya jefa masa.
Dafe baki Nuren yayi yana kallonsa cikin 6ata fuska.
Galadima ya cije lips yana fad'in “cigaba mana parrot ”.
Nuren ya cire hannun yana kwafa da jinjina kai, alamar zan kamaka ne.
Galadima ya ta6e baki yana hararsa, “yaro aini yanzu na daina halin yara, sai dai kayi da wani kuma”.
Dariya Nuren ya kwashe da shi, “o manya o manya, ai yakamata ma mai martaba yay murabus yabaka kujera kawai, kainefa Wanda kafara kafa tarihi a masarautar nan, Sarki Salisu barde shi yak'in filin daga yaje ya samo sunan gagara badau, kaikuwa yak'in kashe arna kaje kasamo sarakunan gagara badau”.
Girgiza kai kawai Galadima yayi yana fad'in “kai dai d'an iskane wlhy, yakamata papi sumaka aure kodan y'ay'an mutane su samu lafiya ma”.
“ni wlhy dama zakaje kace amin auren daka taimakeni”. Nuren ya fad'a cikin ta6e baki da d'aga kafad'a.
Murmushi Galadima yayi yana gyara zama, “ALLAH ya shiryeka to, mike tafiya akan al'amura?”.
Zama Nuren ya gyara yana komawa serious, “wlhy d'an uwa abubuwannan sun cika tsauri da yawa, a duka mutanen nan uku da yarinyarnan ta fad'a da gaske fa babu SD, amma ga pictures d'in wajen mutum 30 ka nunama Mumcyn Triple's ko zata ganeshi a cikinsu. dukansu yaransu tanderu ne, Sannan nifa inaga lokaci yayi da zaka binciki Muftahu face to face, dan lamarinsa yafara birkitan tunani gaskiya”.
“kafad'i gaskiya Nuren, nima kuma ina tunanin hakan shine mafita, dan ni kaina lamarin nasa yafara kaini ga dogon nazari”.
“To ALLAH yasa muji alkairi”.
“amin dai”. Galadima yafad'a yana mik'ewa, “nifa na shige zan kwanta, ka kwana lafiya”.
“ok ALLAH ya tashemu lafiya gwauro”.
Galadima yay dariya, batareda ya juyoba yace, “duk lalacewar goma dai tafi biyar albarka tuzuru”.
Nuren ya kwashe da dariya, yana fad'in, “oho dai, muma mun kusa zama gomar”.
★★★★★★★★★★★★
Zumid'i ya hana Momma komai, ta k'agara Abie yafarka yasha kanu, hakama su Samha su dawo school suji babban labari.
Ana cikin haka saiga Sauban tamkar an jehoshi, babu kunya ya rungume Momma yana fad'in “wayyo dad'i Momma y'ay'a uku fa wlhy, kuma dai-dai da ranar haihuwar Yaa Sam, dan yau birthday d'insa wlhy, ciwon aunty gimbiya ya mantar dashi”.
Itama rungumeshi tayi cikeda farin ciki, “hakane wlhy my love, yau ina cikin farinci mai tarin yawa, tarihi ya maimaita kansa da wani sabon salo mai banmamaki”.
“Wlhy nima haka Momma, kallafa pictures d'in babies d'inmu”.
Dukda tagani itama bata katse masa hanzariba ta kar6a wayarsa tana kuma kallo, harda na Munubiya.
Momma tace, “kai yau innarsu yazataji, jikoki 5 a lokaci d'aya, baiwar ALLAH, dama mahak'urci mawadacine, tayi kukan shekaru masu yawa ga lokacin dariya kuma yayi”.
“wlhy kuwa momma, nakira Yaa Sam batajeba”.
“Ai yama manta wayoyinsa a nan, kasan sun tafi hankalinsa ba kwance ba, nima da wayar Muftahu mukayi wayar”.
“wayyo Momma dan ALLAH kicema Yaa Sam mutafi gobe, wlhy kamar nayi tsuntsuwa na ganni a 9ja nakeji”.
Dariya Momma tayi, tarasa inda zata saka kanta dan dad'i.
Motsin da Abie ya farane yasakasu maida hankali garesa, idonsa ya bud'e ahankali a kansu. ganinsu tsaye kansa sunata murmushi saiya ma Momma alama da ido wai miya faru?.
Da sauri Sauban ya rungumesa yana fad'in “Albishirinka Abie d'inmu, matar Yaa Sam y'ay'a uku ta haifa”.
Ba k'aramin shock bane ya kama Abie, ya kalli momma alamar da gaske?.
Kanta ta jinjina masa tana murmushi.
Wasu hawayen dad'ine suka gangaro a kumatunsa, fuskarsa d'auke da k'ayataccen murmushi, A hankali yaketa jero Alhmdllh. Yace, “Mafarkina na shekaru da yawa yazama gaskiya Zeenah, tabbas ubangiji shine masanin gaibu, ya ALLAH na gode maka, godiya marar yankewa balle gajiyawa”.
A hankali yake maganar Amma su Momma naji saboda sun matsar da kunuwansu.
Dad'i duk yakuma lullu6esu, Abie yakuma fad'in “Zeenah wannan yarinya ta zama alkairi ga Ahalinmu, ALLAH ya albarkaci rayuwarta da abinda ta Haifa daku ma gaba d'aya”.
Sauban da Momma suka amsa da amin.
Yace a kira masa Galadima.
A time d'in sunta neman Number Mom amma bata wuceba saboda Network, hakama ta Nuren da Muftahu, daga k'arshe dai sun hak'ura ne sai wani lokacin a sake gwadawa.
Yau dai kam har doctor's d'in Abie sun shaida yana cikin farinciki, dan jikinsa ma ya nuna haka, k'arfin muryarsa ya k'aru, hakama bugun zuciyarsa dawasu yankunan halittun jiki dake bama d'an adam garkuwa, sun tabbatar a kowanne lokaci ALLAH zai iya gwada ikonsa ga wannan bawa, bayan tsawon shekaru daya d'auka a kwance sai an juyashi.
Wannan albishir ya k'ara yalwata farin cikin wannan ahali, saima dasu Samha suka iso, duk sun rikice da ihun murna, yau d'in ta dabance a ransu.
Isowarsu ce ta tunama Galadima da ranar haihuwarsa dai-dai da haihuwar yaransa, kuma dai-dai da haihuwar su Munaya ma😳😜.
Wannan abin al'ajab da yawa yake, ita kanta munaya sai lokacin ta tuna, wayar Ayusher ta kar6a ta kira Munubiya tana mata tuni da ranar haihuwarsu. dad'i ya kama Munubiya ma, dan itama ta shafa'a, sai murna kan murna ta k'aru🤸🏻♀.
**************************
Uban gayya dai Galadima da k'yar barci 6arawo yake sace sa a kowace rana, daya rimtse ido 'y'ay'an sa kawai yake hangowa, badan kar aga rashin hak'urinsa ba shikam da dasu zai ringa kwana.
O baban zumud'i😘😘😽.
A 6angaren yalla6iya ma hakane takan kasance, da taga laraba tayi barci dash Ayusher da Samha, (dayake itace take kwana dasu) saita tashi ta dinga d'aukarsu d'ai-d'ai tana runguma da musu addu'oi, jitake kamar ta had'iye kayanta ta huta kawai, takan dad'e tana Abu d'aya kafin barci yaci k'arfinta take kwantawa.
Tosu yalla6iya anaso ana kaiwa kasuwa😂😜.
*************************
Fad'a muku yanda abubuwa suka cigaba da kasance ga y'an barka ai 6ata lokacine ma, dangin Munaya ma sun taka rawar gani, Ayusher ma dai ta dawo nan zata zauna har ayi suna, hakama madam Innaro Galadima da kansa yaje ya kwasota🤣😜, aiko baki har kunne.
Gaskiya fans sannunku da k'ok'ari, irin wannan tururwa haka, lallai kunma Galadima halacci shida yalla6iya, ALLAH ya saka muku da alkairi dai my sweetness🥰🥰🥰😘😘😘😘❤🤝🏻.
Dole Galadima ya nemi waya da sim card ya lalubo su Abie da Momma d'insa da jakadiya dabasu samu zuwaba, suna shan hira a kullum shida su Abie ta video call, ga jarirai aita jera musu sunata shan kallo abin birgewa, Abie jiyake kamar yay tsuntsuwa ya gansa a 9ja, tsakanin nan yana cike da kewar k'asarsa ta haihuwa, yana fatan yakuma takata ko sau d'ayane kafin yabar duniya.
“Insha ALLAH zaka taka da yawa Abie😭”.
Mu tafi ran suna kawai😨⛹🏻♀⛹🏻♀.
Abubuwa da yawa sun faru a kwanakin bakwai d'innan, sai dai Alhmdllh bamasu tayar da hankali bane, dan jinjirai suna cikin k'oshin lafiya da kariyar ubangiji.
Samha dai konan dacan bata matsawa, duk wani motsinta nakan yaranan, tazama bodyguard d'insu itada Ayusher da hajiya innaro, dan itamafa ta kafa ta tsare🤣.
Mama Fulani dai ta danne zuciyarta tazo har sashen Galadima taga babies, harma suka samu k'yauta mai tsoka daga gareta.
Ana gobe suna masarautar gagara badaufa tayi dank'am da jama'a, dan bikin suna na ban mamaki Sarki ya shirya, abin ba'a cewa komai. Inno ma dai wannan karon ba'a barta a baya ba, tazo masarautar su sunan tatta6a kunnenta, kuma 6angaren mama Fulani ta sauka😳😜.
Koba komai zata kafa zata tsare, takuma raka ta jira🤸🏻♀😂 mana ga Mama Fulani.
Harun da baya k'asar yayi tafiya a fannin aikinsa yau ya diro a Daren suna cikin masarautar, dama tun yana can labari yagama Isar masa Galadima ya samu y'an uku, Muftahu da kansa ya kirashi ya Sanar masa haihuwar, Yakuma tura masa hoton babies😽🤥
*****************
Wajen 8pm Galadima suka dawo daga masallaci sallar isha'i, shikad'ai ya shige falonsa, dan yana son magana da Munaya, gaba d'aya yinin yau tun safe daya Shiga bai samu komawa wajensu ba saboda hidimomi sun masa yawa.
Ayusher ya kira, dan itama Munaya batazo da waya ba, lokacin da su Sauban zasu taho kuma basusan inda ta saka layinta Na Nigeria ba, sai sukaga babu amfanin d'akko wayarma.
d'agawa Ayusher tayi, Galadima yace ta bama Munaya.
Murya k'asa-k'asa tace bata da lafiya.
Tashi yay daga kwanciyar da yayi, yace, “ciwon cikin ne dai?”.
“eh shine wlhy Yaa Galadima ”.
Dukda kunyar shiga mutanen yake dole ya mik'e ya fita, sashen nasu kam Alhmdllh da yawan jama'a babu laifi, ga yawan bayi da suka k'aru saboda inno da tawagarta, dukda ba'anan ta sauka ba.
Tunda ya fito suketa gaisuwa da jama'a, wad'anda ma basu sanshiba yau sun gansa, musamman wasu a y'an uwan Munaya. cirko-cirko ya iskesu tsaye, Munaya Na kwance a gado ta cure waje d'aya da alama tanajin ciwon sosai, Aunty Mimi nata faman jijjiga yaron d'aya dake kuka.
Duk kallonsa sukayi, cikin damuwa yace, “ciwon cikinne?”.
Da eh suka amsa masa, ya taka zuwa gaban gadon ya zauna kusada ita, har zai ta6ata Mom tamasa nuni da a'a ya barta. dakatawa yayi shima ya zuba mata ido cikin tausayawa, gaba d'aya fita hayyacinta take idan cikinnan yana ciwo, kuma saida ta kwana biyu da haihuwa sanann yafara. ya tsira mata idanu ganin yanda take zufa, dukda garin akwai sanyin ruwan da akayi da yammaci.
Yakai tsawon mintuna 30 a zaune kafin ya lafa mata, ahankali tafara gyara kwanciyarta tana mik'ewa sosai, da Galadima suka fara had'a ido, yace, “sannu”.
Kanta ta d'aga masa cikin murmushin k'arfin hali, suma duk sukai mata sannu sauran.
Nanma ta amsa cikin d'aga kai. Maganin da laraba ta tace a Kofi ta mik'o mata, Na gargajiyane, kar6a tayi ta shanye tana yamushe fuska, ta mik'a mata kofin sannan ta zauna sosai.
Tausayinta ya kama Galadima, iyaye mata nashan wahala akan y'ay'a, ALLAH ne kawai zai biyasu.
Ganin ta dawo dai-dai duk sai suka fita suka basu waje, bayan Aunty Mimi ta d'ora masa babyn a cinyarsa.
Sannu ya kuma mata yana gyarama yaron kwanciya, murya a hankali tace, “ya daina ai, amma wlhy ciwon cikinnan yamafi haihuwar zafi”. ‘ta k'are maganar idonta cike da kwalla’.
Tausayi ta kuma bashi, ya matso kusada ita sosai yana ruk'o hannunta, yace, “insha ALLAH Akash zai zo miki da Magani zuwa gobe, zai daina gaba d'aya ”.
Kanta kawai ta d'aga masa amma batace komaiba.
Kukan da macen tayi yasakasu kallonta su duka, nuni yamata ta d'auketa.
Batayi musuba ta d'auketa ta saka a acinya, kamar jira suma sauran suka farka harna hannunsa, kai Munaya ta dafe tana fad'in “ni jikar fharuk ku shikenan da d'aya ya tashi kowa saiya tashi”.
Murmushi yayi, “to basu birgeki ba ma, sunyo gadonku ne keda Munubiya, Ku ba haka kukayiba?”..
“a'a mukam ba irin wannan mukayiba yalla6ai”.
“humm, ai inna ta sanarmin komai yarinya”.
Da mamaki Munaya ta waro masa ido, ya d'aga mata gira yana kashe ido d'aya.
'Dauke idonta tayi cikeda basarwa.
Shima saiya mik'e tsaye d'auke da yaron d'aya, ya kalli agogon dake a hannunsa sannan ya kalleta “inason ganinki”. daga haka ya sunkuya ya d'auki macen ya juya zai fita.
“wai ina?”. ta fad'a da saurin dan karya fice.
Juyowa yayi ya d'an kalleta, kamar bazaiyi magana ba sai kuma yace, “sashena”. bai jira cewarta ba yay ficewarsa.
Kanta ta dafe tana sauke ajiyar zuciya, shi bama ya ganin gida cike da mutane, fitinar yalla6ai yawane da ita wlhy. batayi yunk'urin binsa ba, saima zaman shayar da Wanda ya bari tayi, harsu Samha suka dawo ganin ya fita.
Shikam yanacan kwance a gado ya d'ora yaran saman cikinsa yana shafa bayansu, yayinda zuciyarsa ta tafi wata nahiyar tunani, ganin lokaci yaja bata zoba ya kalli a gogon hannunsa, shidai bazai kuma kiranta akan tazo ba, idan ta gadama kartazo.
Mom data lura babu sauran yaran ta tambaya, cikin kunya Munaya tace, “suna wajensa”.
Banbancin babba da yaro saurin fahimta, mom ta fahimci d'an nata yana buk'atar ke6ewa da matarsa, shiyyasa ya d'auki abinda dole tabishi inda yake ta kar6o..
Tace, “to aiko jeki ki kar6osu, dan shirin barci zan musu nima Na kwanta, gobe ba zama za'a samuba hidimomi zasuyi yawa”.
Kamar Munaya tai ihu haka taji, to a aiki Ayusher da Samha su kar6osu mana, ai ba dole sai itaba, amma babu yan da ta iya, dan bazata iya sa6a umarnin Mom ba dai.
Dogon hijjab ta d'auka ta zumbula, Mom kamar tayi dariya, a ranta tace, Munaya shi namiji ai ba'a hanashi yanda yaso, balle naku na yanzu da suke a fetsare ma.
Harzata fice mom tace, “shima zoki d'aukesa”.. Ta kalli mom d'in tana fad'in “mom aikuma zasuyi yawa wajen d'akkowa”.
“eh d'auka, basai ya tayaki ku d'akko ba”.
Babu yanda Munaya ta iya dole shima ta dawo ta d'aukeshi, sai wani k'yallo idanu yakeyi Lamar yasan mi akeyi.
Babu kowa a afalon, harma television an kashe, babu yanda ta iya dole ta nufi bedroom d'in, saida tayi sallama yabata izinin shiga sannan ta shiga.
Harta zauna idonsa a kanta itada babyn hannunta, saiyaga ta k'ara masa k'yau ma da girma.
Yace, “kin gama jan ajin? ai saki bari sai randa nazo tad'i ki jamin bawai yanzu ba”.
Munaya ta ciza lips d'inta kawai batare da ta tanka masaba,
Yaran ya kwantar gaba d'aya, sannan yatashi zaune yana fad'in “taso”.
“intaso kuma, ba magana kace zamuyi ba? please ka fad'a a haka”. ta fad'a kamar zatayi kuka, (Dan hirar innaro da laraba ta tuna da sukace jiya wata yarinya sati biyu da haihuwa ta yarda da mijin saiga ciki ya fito yaro Na wata uku, ciki wata biyu da sati biyu🤣, itama fa yanzu kaffa-kaffa zatakeyi da Galadima, inma baka badaba sai'a saka maka k'arfi🤭😂).
Tsaf Galadima ya fahimceta, dan haka yay wani miskilin murmushi yana fad'in “oh kina min bak'in cikin sake ajiye abin cikin kwan ne?”.
Sosai Munaya ta waro idanu, a firgice tace, “ban ganeba?”.
“Zaki gane lokacin da kika zo hannuna”.
Ta yunk'ura da sauri ta mik'e, ita tama manta da yaro ajikinta, ALLAH dai ya kiyaye tai saurin tarboshi, Galadima ma dirgowa yay daga gadon, saidai kawai ta gansa kusada ita.
Rungume yaron tayi tana sauke ajiyar zuciya, gashi mai kamar mara lafiyarne.
Shima Galadima had'ata yay itada yaron ya rungume, ganin haka saita mik'a masa shi ita ta janye jikinta. hannunta ya rik'o ya maidota, daga k'arshema janta yay zuwa gado, ya zaunar da ita shima ya zauna, fuskarsa babu walwala yace “Munaya badai haka kikemin ganganci da yaraba?”.
A tsorace ta girgiza masa kai idonta Na cika da kwalla, “wlhy yalla6ai a'a, yanzu ma Na shafa'ane”.
Taune lips d'insa yay tayi yana kallonta, haushima ya hanashi samo amsar bata, jima yake kamar ya maketa, anya zaibar yarinyarnan zuwa wani wankan banza can, taje tamasa wasarere da yara?.
Yanda ya koma duk saitaji babu dad'i, shi yaronma bafa kuka yakeba, yad'an dai firgita ne kawai yay kamar zai shid'e.
Saida ya gama cikarsa da batsewa sannan yay kwafa, ita shima abin yabata mamaki, shikenan yanzu y'ay'ansa kawai ya Sani, mutum bazai ta6a iya kuskure ba a Kansu saiya hauma mutane bala'i, shin ya fita sonsune itada tasha wahalar d'aukar ciki da haihuwa?.
Kwantar da yaron yay yanata wani had'e fuska, itama tasha kunu ta shareshi.
K'aton akwatin dake gefensu ya matso dashi, kayane Na jinjirai masu k'yau da birgewa, Wanda kallo d'aya zaka musu Kasan Na musamman ne, kala-kala ne amma kowanne set uku ne, abinda ya banbanta su wannan Na macene wannan Na mazanne. kowanne da takalma abindai masha ALLAH.
tsaf Munaya ta gama gani, ta kallesa tana fad'in “Sunyi k'yau”.
Yana basarwan nan tasa yace, “wanda zakuyi amfani dashi gobe ne, idan akwai abinda bai yiba saiki fad'a da safe a nemoshi, ga naki nan kema”. ‘yay maganar yana nuna mata d'ayan akwatin’.
Jawowa tayi ta bud'e, duk an d'inka kayan, kayane masu tsadar gaske Na mace y'ar gata, bama tasan ta rungumeshi ba Dan dad'i, sai jero masa godiya da addu'oin fatan alkairi takeyi.
Shima tuni ya manta da fushin ya rungume kayarsa yana murmushi. cikin kunnenta yace, “kinfi k'arfin komai a wajena friend dan kin gamawa Muhammad Sameer komai”.
Munaya ta murmusa tana d'an dukan k'irjinsa, tace, “kana shamin k'amshin ne nagama maka komai?”.
Hannunta ya rik'e yana murmushi, yamatso da fuskarsa gab da tata, murya k'asa-k'asa yace, “ke d'ince Zuma ce...... ”
Harar data dalla masa ta sakashi fasa k'arasawa ya wani basar yana kashe mata ido d'aya, “dad'ina dake akwai mazurai, gaki babu k'arfi ga tsoron tsiya”.
Munaya tayi dariya, “aka gaya maka banida k'arfi? kabari nakuma samun lafiya sai a gwada kwanji”.
Wata dariyar mugunta Galadima yayi yace really?”.
“yes” ta fad'a cikeda karsashinta.
Ya mik'a mata d'an yatsansa alamar su k'ula.
Babu musu tabada nata itama suka k'ula. Murmushi yaytayi saboda muguntar dayasan yana shiryawa, wadda ita Munaya bata fahimci komaiba a ciki saboda wauta.🤣
*_Washe gari_*
Ta kasance safiyar suna, inda aka rad'a sunan yara bayan sallar Asubahi, *_Abdurrahman, Abdurraheem, and Amaturrahman_* masha ALLAH Babies ALLAH ya raya Ku akan sunnah da tafarkin addinin Islam.
Yara sunsha Addu'oin fatan alkairi sosai, tun kuma a safiyar shagalin suna ya fara, dan kowa yana cikin walwala da farinciki, mai jego munaya ansha k'yau itada babies har an gaji, kamar ka sacesu ka gudu, hotuna dai suna shansu kala-kala a yau d'inan, Su Momma ma da basa kusa anata sambad'a musu, dan duk wani motsin da za'ayi Sauban da Samha basa gajiya da tura musu, sai sukaji tamkarma suna nan suma, saboda kallon komai suke tamkar live, farin ciki da walwala sun yalwatu a zuciyar Abie, bakinsa yakasa rufuwa dan tsabar nishad'i daya tsinci Kansa yau aciki.
Hummm babbar magana, kayan barka dai sun iso, fans yaufa nasha kallo, kaga Inda akeyi don ALLAH, ta bakin Munaya tace INA zasu da wad'annan kaya haka, lamarin tamkar fariyya, gashi kowanne sashe sai kawo nasu sukeyi, gidan sarauta manya, babu Wanda zaiso aga kasawarsa, ballema wannan kana k'inyi za'a CE bak'inciki kakeyi, shiyasa mama Fulani aka ware aka zuba kayan barka Na gani Na fad'a, daga gidansu Munaya ma su inna sun taka rawar gani dai-dai k'arfinsu, daga ita har Munubiya komai iri d'aya aka musu, kayan babies ne kawai Na munaya yafi Na munu saboda su su uku ne ita kuma Nata biyu.
Nanfa y'an gidan suka Shiga k'us-k'us d'in gulmar Ina inna ta samu kud'in yin wannan hidima haka? dansu basuyi zaton hakanba, musamman da abin yazo da yawa ma, itadai inna ma ko kallo basu isheta ba, hidimar gabanta da farincikin datake cikine a gabanta, bakinta yakasa rufuwa saboda farinciki da godiyar ALLAH mai sassauya al'amura a yanda yaso a kuma lokacin da yaso, idan ALLAH ya jarabceka karkayi bak'in ciki, hak'urinka zai iya zama sauyin alkairi a gareka, inama iyayensu Nada rai suga wannan k'yak'yk'yawar rana, ta share hawayenta tana murmushin farin ciki, sannan ta kira y'ar uwarta a waya suka cigaba da tattaunawa.
*****
K'arfe uku da rabi kuma za'a gudanar da gagarumar walima da aka kama babban hall Na musamman.
A wannan rana yara dai har fada aka kaisu sukayo gaisuwa da hotuna da mai martaba da gayyar y'an uwa da abokan arzik'i, su Harun dai sune gaba-gaba, uban gayya kuwa Muhammad Sameer Saifudden Galadima Baban y'an uku😂 ai ba'a cewa komai, koma ganinsa ba'ayi saboda tsabar shiga hidima, wannan suna ko bikidai iyaka kenan.
Nasan kuma fans duk kunyi shirin wannan walimar baje dad'i😋😋. Nifa buhu Na tanada walle😆, saura kuce Bily tacika zari da son banza kuma🙄, har y'an anguwarmu saina kar6oma gifts d'insu😜😂🤸🏻♀.
****************
Alhmdllh yaran Mununbiya ma an rad'a musu suna bayan sallar Asubahi, Namijin *_Aminudeen macen Ameenatu_* ALLAH ya raya wad'annan yara masu albarka😘😘🥰.
Yau daikam farin cikin da Abba da innarsu suke ciki 6ata lokacine ma, kai da dukkan masoyansu irinmu, masu bak'inciki kam Ku k'ara himma, hassada ga mai rabo takice😏🤷🏻♀.
Kowa nabashi dama ya k'iyastama zuciyarsa yanda bidirin suna yake guna, dan Alk'alamin Bily yau yayi k'ank'anta wajen wallafowa, sai mugama Na wannan satin bikin sunan bai k'areba😁.................✍🏻
Kuyi manage da wannan yau inada uzuri🤦🏻♀.
☺my Guy's a kafta kawai danjin yanda bikin suna zai gudana gobe idan ALLAH ya kaimu, kowa dai ya k'ure adaka dan karfa a kawo mana raini😕, kunsan dai halin mama Fulani, tana iya hanawa abarmu shiga😩🥺.
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭👏🏻
*_typing📲_*
💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._*
*_♦RAINA KAMA.....!!♦_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
~Book 2~ 👉🏻2⃣5⃣
................Aunty Salamah da kanta tazo yima Munaya kwalliyar zuwa wajen walima, saida tafara biyawa tama Munubiya sannan ta wuto nan, ta iske su duk a damuwar kukan da Abdurrahman ketayi, sai faman jijjigarsa akeyi amma yaro yak'i yin shiru, an basa nono yak'i kar6a, innro ta kar6esa ta hura masa kunne, ya kuma k'yak'yacewa da sabon kuka yana dunk'ulewa waje d'aya, tace “inaga kunnensa ke ciwo yaronnan”.
Munaya Na gefe zaune ta zuba tagumi kawai tana kallonsu, ita kad'ai tasan suyar da ranta ke mata, gashi Galadima baisan wainar da ake toyawa ba, yanacan tareda su Akash da suka iso yanzu.
Innaro ta dungureta, d'ago idanu tayi ta kalleta, ta mik'a mata Abdurrahman daketa sauke ajiyar zuciya, “d'iga masa ruwan nono kad'an acikin kunnen insha ALLAH idan aka dace zai daina”.
Kar6arsa tayi, ta d'ora kan cinyarta, dukma ta rikice ta rasa yanda zatayi, saboda sai mimmik'ewa yakeyi azaba na cinsa, ga Amaturrahman itada Abdurraheem suma sun d'akko nasu kukan, laraba ta rik'e matashi ta samu ta d'iga masa, ruwan nonon Na shiga yakuma mimmik'ewa yana kwalla ihun sabon kuka.
Saiga hawaye a na zuba a idon Munaya, tasaka hannu ta toshe kunen ta kozataji sassaucin jin kukan nasu dake d'aga hankalinta.
Tausayinta saiya kama laraba, tasan indai wannan ne yanzu ma aka fara, yaro d'aya ma ya kake k'arewa balle yara uku.
Cikin amincin ubangiji kuma duk sai sukayi shiru, innaro da laraba sunata faman jijjiga, itama Aunty salamah ta kar6i Na hannun munaya, tun suna ajiyar zuciya har barci ya kwashesu. Munaya ta shige bayi tana share ragowar hawayenta.
Baki innaro ta ta6e tana fad'in “lallai aiki yasamu mata, yo indai kukane yanzu ma kika fara”.
Daga Aunty salamah har laraba dai babu Wanda ya tanka.
Munaya kuwa data jiyota daga bayi tace “aniyarki ta biki, mai mugun fata kawai”.
Wanka tayo ta fito, Aunty salama kawai ta tarar a d'akin sai bayi biyu dake morping, suka durk'ushe k'asa suna gaida Munaya.
Hannu ta d'aga musu kawai dan batasonyin magana, har yanzu raunin tausayin Abdurrahman baibarta ba. ta kallesu duk suna kwance kan gado barci ya d'aukesu, yayinda Aunty Salamah ke zaune kan sofa tana warema yaran kayan da za'a saka musu.
Ta d'ago ido tana kallon Munaya, “haba auta kuka kikayi da gaske? Please kidaina musu kuka, ba'ason uwa Na zubarma d'a hawaye dukda wannan Na tausayine kinji”.
Munaya ta had'iye abinda yamata tsaye a mak'oshi tana gyad'ama Aunty salamah kai.
Saida Aunty salamah ta gama ware kayane sannan ta taso suka fara kwalliyar, anutse sukeyin komai, dan da sauran time, hakama Munubiya a nutse aka mata tata, anama Munaya tana kallon hotunan Munubiya, taji dad'in yanda y'ar uwarta tasha k'yau, dukda ma batakai ga saka kayaba.
★★★★★★★★★★★
Muftahu nata kai kawo a tsakar d'akinsa, tunanin tawace hanya zai fargar da Galadima kawai yakeyi, dan dolene saida hannunsa zaiyi wannan aikin, saboda had'arinsa, gudun kar reshe ya juye da mujiya, sannan aikin yana buk'atar takune da sirri.
Fitowa yay yanufi can cikin k'aton lambun masarautar indasu Galadima suke tareda mafi yawan y'ammata da samarin masarautar.
Wasu sunata hirarsu in group, wasuko hirar tasu ta masoya ce, Muftahu ya k'araso inda su Galadima suke, sun baza babbar darduma anata hira, Bama zaka ta6a Sanin suna lambun ba saboda sunacan ciki nesa da sauran yaran.
Galadima na zaune a gefe cikin kujera, ya d'ora k'afafunsa a wata kujerar, sanye yake da farar shadda d'inkin boda, fuskarnan babu walwala ko kad'an, gaba d'ayan hankalinsa yanaga system d'in daya d'ora bisa cinya yana latsawa.
Muftahu ya mimmik'a musu hannu sukayi musaba cikin fara'a. Amma tsakaninsa da Harun ba hakan baneba, kowa murmushi mai cikeda ma'anoni yay ma d'an uwansa, kafin su saki hannun juna. Muftahu ya matso kusada galadima shima ya bashi hannu sukayi musabaha, k'aramar takardar dake mak'ale a hannunsa ya sakarma galadima a hannu.
Kallonsa galadima yayi, sai yay masa murmushi yana signal da ido alamar ya duba.
Galadima bai ce komaiba ya cigaba da abinda yake ya basar da takardar. Muftahu kuma ya koma cikin su Harun aka d'ora hira, tamkar babu abinda ke damunsa.
Galadima baibi takan takardar da Muftahu ya basaba har tsawon wasu adadin mintuna, sannan ya bud'e ya duba.
_Ranka ya dad'e ina buk'atar muyi magana kafin a zauna wajen walima, magana mai muhimmanci please._
Iya abinda ke jikin takardar kenan.
Galadima ya d'an ja eyeglasses d'insa k'asan ido ya kalli Muftahu, cije lips nashi yayi yana janye idonsa.
Ya sauke k'afafunsa yana d'ora laptop d'in saman kujerar, ya d'auki ruwan gabansa yana sha da maida hankali garesu. jin hirar tasu ta y'ammata ce sai ya zuba musu ido kawai bai saka bakiba, dan shi dama ba'a wannan hirar dashi tun can da, suma duk sunsan haka, shiyyasa ko suna shirmensu basa sakoshi.
Ganin zasu saka masa cinwon kai saboda hayaniyarsu Na Neman yin yawa saiya mik'e d'auke da Laptop d'insa.
Duk kallonsa sukayi, Zayyan yace, “ina zuwa daddyn Triple's?”.
K'aramin tsaki yaja, da k'yar ya bud'e baki yace, “zaku samin ciwon kaine, zanje nad'an huta kafin time yayi”. ya k'are maganar da kallon agogon hannunsa.
Matawalle yay murmushi yana salute nashi, shima murmushin ya masa yana kaimasa rankwashi, ya kauce gefe yana murmushi, (dayake shima bai cika hayaniya ba).
Wuce warsa yay cikin takun nan nasa Na izza da k'asaita, da sauri wasu yaran masarautar dasuka had'a tasu dabar agefe biyu aciki suka taso suka k'ar6i laptop d'in hannunsa saboda girmamawa, ya mik'a musu yana murmushi, yana gaba suna binsa a baya, sai zuba masa surutu suke akan shagalin daza'a sha yau, shidai murmushi kawai yake musu babu magana, basu damuba, dan kowa yasan halin galadima a masarautar nan, haihuwar nan ma wasu da yawa zasu iya cewa sunga hak'oransa a waje. duk inda suka gitta ana kwasar gaisuwa, bayi kam zubewa suke domin girmamawa a garesa.
Har sashensa suka masa rakkiya, sarkin mota ya kar6a laptop d'in ya k'arasa masa da ita zuwa ciki..
Baibi ta ainahin k'ofar da zata kaishi babban falonsu ba, saiyabi wata k'aramar k'ofa da kai tsaye nasa sashen zai shige basai mata y'an suna sun gansa ba.
A falo ya iske Sauban kwance yana barci, da alama yagama yawonsa ne gajiya ta makesa, da kallo Galadima ya bisa, amma dan ya tabbatar da lafiyarsa saiya d'ora yatsunsa biyu a wuyan Sauban d'in, babu zafi, ya maida goshinsa saiyaji zafi sosai, Galadima ya girgiza kai, yasan dama ba lafiyace zata saka Sauban barci a irin wannan lokacin ba ana wannan hidimar.
Bai tasheshi ba ya shige cikin bedroom, zama yay a bakin gadon yana cire bottom d'in rigar guda uku, ya huro isaka daga bakinsa yana zamewa ya kwanta batareda ya cire rigarba, zuciyarsa tana ta jujjuya mi Muftahu yake nufi ne? wace magana zasu tattauna?. waya ya jawo da nufin kiransa, sai kuma ya fasa, jefar da wayar yayi yamik'e yana ida cire kayan gaba d'aya. ya shige wanka.
ya ja adadin wasu mintuna masu tsayi kafin ya fito sanye da bathrobe fara sol, sai k'aramin towel a hannunsa yana goge fuskarsa zuwa wuyansa.
Yana tsaye gaban mirror zai fara shafa mai ya jiyo ana knocking d'in k'ofar falonsa, Computer d'in daya ajiye wadda yake kallon kowane 6angare na sashen daga cctvs cameras d'in daya zagaye ko ina, tun zuwan dayayi Na k'arshe ya saka akayi masa wannan aikin, sannan ya d'auki mataki akan waccan cctv d'in da Munaya tamasa hannunka mai sanda da ita.
Sarkin k'ofa ya gani, sai kuma Muftahu daga can waje alamar yana jiran iso ne.
Guntun tsaki Galadima yayi, ya fito zuwa falo, Sauban dake barci ko motsi baiyiba balle yasan ana knocking d'in. yana daga tsaye yabama sarkin k'ofa izinin shigowa.
Cikin girmamawa yace, “ranka yadad'e yalla6ai Muftahu ne ke Neman iso”.
Da hannu Galadima ya masa nuni da ya shigo.
Sarkin k'ofa ya amsa da to sannan ya fice.
Komawa Galadima yay ciki yacigaba da shafa mansa, saida ya gama tsaf sannan ya zira jallabiya Brown ya fito.
A falo ya iske Muftahu zaune yana control d'in television da remote.
Galadima ya zauna a kujera mai zaman mutum d'aya, sai wani d'aure fuska yake.
Muftahu bai wani damuba, dan yariga ya saba da wannan ai.
Kallonsa Galadima yayi cikin lumshe ido yana fad'in “Mike faruwane?”.
Ajiye remote d'in Muftahu yayi, ya kalli Sauban dake barci.
d'an ta6e baki Galadima yayi, yace, “karka damu, kayi maganarka kai tsaye kawai”.
Cikin jinjina kai Muftahu yace, “Ok, babu abinda ke faruwa saidai shirin faruwar kam, Ranka ya dad'e bamuda isashen lokacin wata magana mai tsawo yanzu, saidai ga wannan takardar ka duba, so yanzu wannan ne akan ga6a, shine yakamata mu d'au mataki akansa, daga baya komi kenan namaka alk'awarin warware makashi, fatana dai ka fahimci wannan d'in saboda had'arinsa”.
Kar6ar takardar Galadima yayi, ya d'auki medical glasses d'insa daya ajiye a teble glass d'in dake gefen haggunsa ya saka, duba takardar yay a tsanake, cikin wani yanayi dake nuna tsantsar tashin hanki yace, “Muftahu wannan maganar gaskiya ce kokuwa? karkamin wasa da hankali a wannan karon dan bazan d'aga maka k'afa ba a wannan ga6ar alwashi nane”.
Murmushi Muftahu yayi, ya sauke ajiyar zuciya yana fad'in “Nabaka wannan damar, inhar kayi gamo da sa6anin hakan karka barni da numfashi ranka ya dad'e”.
Wani shegen Murmushi Galadima yayi, yamik'e d'auke da takardar ya koma bedroom batare da kuma kallon Muftahu ba.
Tausayin Galadima ya kama Muftahu, mik'ewa yay shima ya fice.
Jefar da takardar Galadima yayi akan gado yana taune lips nashi tamkar zai huhhudashi, wata irin suya zuciyarsa ke masa, lallai dolene ya jinjinama Munaya, dan ta taka rawa wajen shagaltar dashi wanene shi? minene burinsa?, ganin tunani bazai masaba yatashi jikinsa Na rawa yafara wasu had'e-had'en abubuwa, waya ya d'auka ya kira Ayusher, ta d'aga cikin hanzari tana mik'ama Munaya dake shayar da Amaturrahman data tashi daga barci tana kuka.
Kallonta tayi da mamaki tace, “wace Ayusher?.......”.
Galadima ya katseta da fad'in “ki kawomin kayanda su Abdurraheem zasu saka”. iyakar maganar da yay kenan ya yanke wayar yana cigaba da latse-latse, zuwa can kuma ya ajiye ya mik'e yana cire jallabiyar jikinsa.
Baki sake Munaya tabi wayar da kallo, mike damun galadima haka? Muryarshi irin wadda tasan asalin galadima ce, hakan na nufin akwai matsala kenan? to mine zaiyi da kayan da yara zasu saka?. batada mai bata wad'an nan amsoshin dan haka ta mike tana ajiye Amaturrahman d'in, aiko ta fashe da kuka an cireta bata k'oshiba, tsaki Munaya tayi tana fad'in “ai saikiyi tayi, ku matsala ubanku matsala mutum yarasa wazai kama.
Ayusher da Aunty Salamah suka kalli juna suna gumtse dariya.
Gyale taja ta lullu6a, dama tasaka doguwar rigar matirial kafin dai time ya k'arasa. ganin zata wuce yarinya na kuka Auntu Salamah tace, “dawo ki d'auketa mana, idan kinje can saiki bata nonon”.
Tamkar Munaya zata saka kuka haka ta dawo ta kwashi Amaturrahman ta fice tana k'unk'uni.
A falo ta iske Sauban Na barci, wucewa tayi cikin bedroom d'in kanta tsaye, amma saida tayi sallama ya bata izinin shiga.
Tun da ta shigo taga yanayin da yake sai gabanta ya dad'i, tamkar kazar da kwai ya fashema a ciki ta mik'a masa ledar data zubo kayan sannan ta zauna a kunyace saboda yanayin da yake babu kaya.
Ba tare da ya kalleta ba ya hau Fiddo kayan, ya zubesu saman gado yana d'aukar hotonsu a waya, yay latse-latse nawasu mintuna kafin yasaka wayar a kunne.
“Saleem ka dubamin kalar kayannan, koda basu kaisu tsadaba, yanzunan kataho ka kawominsu”.
Bataji mi Saleem yafad'a daga canba.
Muryarta a raunane tace, “yalla6ai mike faruwa wai?”.
Jajayen idanunsa ya d'ago ya kalleta, k'ala baice mataba ya mik'e ya d'akko wani k'aramin box ya dawo ya zauna, ita duk saima kunya takuma kamata, saboda dagashi sai boxer, amma taga ko a kwalar rigarsa bai damuba, hidimar gabansa kawai yakeyi.
Kwantar da Amaturrahman tayi kusa dashi ta tashi zuwa wardrobe d'insa, k'aramar t-shirt ta d'akko, tazo ta mik'a masa.
Ya d'ago ido yana zuba mata harara, dukda ta tsorata saita daure tace, “please mana yalla6ai”. tayi maganar muryarta a raunane.
Saida yayi k'aramin tsaki kafin ya amsa ya saka, wani abu da batasan minene ba taga yana mak'alawa jikin kayan yaran, saida yagama tsaf sannan ya maidasu a ledar, kallon Amaturrahman dake k'yalla y'an idanu zata fara k'aramin kuka yayi, ya shafa kumatunta batare da ya d'auketa ba.
Laptop d'in sa ya jawo ya saka eye glasses d'insa, ya kalli Munaya yamata alama da ido akan tazo.
Babu musu ta taso zuwa kusa dashi ta zauna.
Laptop d'in ya d'ora mata akan cinya yace, “wanene SD a cikin su?”.
Nutsuwa Munaya tayi tana kallon hotunan, cikin waro ido tace, “kai ga Fu'ad ai”.
Da mamaki Galadima yace, “Fu'ad!?”.
“eh wlhy yalla6ai, Wanda ya kaimu birnin gayu plaza ranar da abunnan ya faru”.
Kar6a laptop d'in Galadima yayi yakuma kallon hoton da k'yau yana taunar lips, kuma mik'a mata yayi batare da yace komaiba. itama batace dashiba tacigaba da bin hotunan da kallo sannu a hankali. Harta kai k'arshensu babu SD. ta kalleshi cikin damuwa, “yalla6ai babushi fa anan gaskiya”.
Kansa ya jinjina mata yana kar6ar laptop d'in, cigaba yay da danne danne, itadai Munaya tana kallonsa.
Kuma d'agowa yay ya kalli Munaya, “duba annan kuma fa”.
Kallon hotunan ta shigayi, canko saiga hoton SD, tace, “Alhmdllh gashi anan”.
Kallon hoton Galadima yayi, da mamaki yace, “kinsan wanene wannan kuwa?”.
“Ah! yalla6ai SD ne mana”.
“Munaya kin tabbata wannan ne kika gani a wajen Abba?”.
“Wlhy shine yalla6ai, bazan ta6a manta fuskarsa ba ai komai dad'ewa. balle acikin abinda bai rufa 2years ba, amma kasanshi ne?”.
Bai iya cemata komaiba, sai zuciyarsa dake wani irin bugawa da sauri-sauri kamar zata fad'o, mamaki ya hanashi motsin kirkirma, Alhaji Shehu Darma shine SD kenan, babban Amini kuma d'an uwa ga Mahaifin su Samha, innalillahi, ya abubuwa keneman koma masa rikid'ar hawainiya haka?, wannan fa Fu'ad d'in d'ane ga yayar Uwargidan Sarki mahaifiyarsu Matawalle, cikin cije lips ya buga hannunsa akan gadon yana fad'in “Kai!!!! miyasa hakane? miyasa duk Wanda Na yarda dashi shike fara bayyana a maicin dunduniyata?!! miyasa rayuwa tazomin da irin wannan rikicin ne?, oh God!!”. ‘ya k'are maganar cikin matsanancin k'araji, tareda runtse hannayensa waje d'aya.
Tsoro ya kama Munaya, ganin yanda duk ya rikice kamanninsa suka canja, idonsa yayi matuk'a jajur, jijiyoyinsa da gashin jikinsa duk sun mimmmik'e, ga Amaturrahman data tsorata lokacin daya buga gadon, d'aukarta tayi tahau jijjigawa.
Sauban ma a firgice ya tashi, ya hau waige-waige, ganin babu kowa a falon saiya nufo hanyar bedroom d'in Galadima, tabbas muryarsa yaji a yanayin da ba'aso. harzai murd'a k'ofar saiya fasa saboda jin kamar muryar Munaya tana magana.
Tunda tasamu Amaturrahman tayi shiru sai ta d'auki towel d'insa ta goyata, ta matsa kusadashi a tsorace, hannunta ta d'ora akan nasa daya dafe mirror, ko motsi baiyiba balle ya kalleta.
Murya a d'arare kuma a sanyaye tace, “please yalla6ai, fushi baisa a samu sauk'i saidai ya k'ara zafi, kaine kasha gayamin wani karatun baya buk'atar fassara ko dogon nazari, akan barsane kawai a yanda yazo, dukda bansan tushen matsalarba zan iya bada gudunmawa wajen kama bakin zarenta, kayi hak'uri ka kwantar da hankalinka, ita fahimta fuskace, ba fushinka ko tsantsar damuwa ne abin buk'atarba yanzu, d'ana tarkon dazai fara kamo maka hannun mak'iya shine jarumta, ka danne kuma ka daure, ni dama Dan banida ikon hana walimar nanne kawai, amma inaji a jikina akwai lauje cikin nad'i, saidai wad'anda suka nad'a d'inne bamuda ilimin saninsu sai ALLAH yaso Samar damu, amma ai duniya makarantace, idan su a can suka yini kaikuma saika nuna musu kwana kayi, lokuta da dama fushinka ke lalata maka aiki, dan inhar kana cikin fushi dukkan aikinka tafiyar hawainiya yake, wannan lagon naka suka samu suke wasa da hankalinka, koda ace wani ya salwanta cikin yarannan karka d'aga hankalinka, ALLAH n daya baka yafika sanin hikimar k'addara hakan, duk lokacinda kaga Matsaloli sun raunana, buk'atu kan kuma kan yalwata ne, kasa a ranka wannan wata damace tazo gareka, ai duk lokacin da aka rasa kwallo a cikin wasa, ba wasan ake dainawa ba, wata kwallon ake jehowa a cikin fili”.
Duk maganar da takeyi ko motsawa baiyiba, baikuma juyo ya kalleta ba, saidai alamu sun nuna yana saurarenta, ta janye hannunta ta juya zata fita tana hawaye.
Cak ta tsaya saboda rik'o hannunta da yayi, kusan minti 1 suna a haka, ta waigo ta kallesa, har yanzu yana a yanda yake, kallon hannunsa daya ruk'o nata tayi.
Bai kalletan ba kuma bai saki hannunba yace, “Lallai ina shaidama dukkan Wanda ya maida rayuwata data ahalina magijin kallonsa, zan tsiyayar masa da idanun, sannan zan kacaccala rayuwarsa Na binnesa da ransa”. ya mik'e tsaye sosai tareda juyowa ya jawo hannunta ta fad'o jikinsa, saurin dafe Amaturrahman dake bayanta tayi da d'ayan hannun. Ya saka idonsa dasuka firgitata cikin nata, fuskarsa dab da tata yace, “kedai kibama yaranki kariya kawai, dan sune fitilar zuciyar mijinki”.. sakin hannunta yay ya zagayeta yabar wajen.
Tamkar sokuwa haka ta bisa da kallo, yayinda zuciyarta keta kuma maimaita maganar tasa, _yaranta, kuma mijinta?_ mi yake nufi to?, amsar itace bata saniba.
Jitai kawai ya saka mata ledar kayansu Abdurraheem a cikin hannu, baice k'alaba yabar wajen zuwa gaban wardrobe d'insa yafara fiddo had'add'iyar Shadda gizna ash colour, sai maik'o take da d'aukar idonu.
Ganin ya shareta yana cigaba da hidimarsa itama saita juya ta fice.
Tunda Sauban yaji motsin kama handle d'in k'ofar yabar wajen da sauri.
Fitarta babu dad'ewa Saleem ya kawo kayanda Galadima ya umarcesa.
__________________________
Munaya Na komawa Aunty Salamah tahau shiryata, dukda taga a yanayin data dawo bata tambayeta daliliba, saida tagama gyara mata fuska tana gyara mata gashi Munaya tafara fad'a mata iya abinda taga ya dace kawai Aunty Salamahr ta iya Sani, sauran kuma sirrinta ne ita da mijinta.
Murmushi Aunty Salamah tayi, tace, “dukda banida tabbacin faruwar wani Abu dagani har Munubiya dama mun shirya hanyoyin d'aukar matakai saboda tsaro, kowa baisan dalilin Munubiya na dagewa akan ki dawo gida ki haihuba, amma ita tasan dalilinta, ba son zuciya ya sakata yin hakanba, Ubangiji Na kallon kowa kuma zaiyi maganin komai, tun a shekaran jiya Saleem yazo mungama tsara komai dama, kuma ya tabbatar min Muftahu yasan komai dan yaga alamar shima tsaye yake da k'afafunsa, inaga yau dai shine yabama Galadima satar amsa, kuma hakan da yayi shine dai-dai, saboda duk abinda zai faru a yau d'innan shi Galadima zai fara zargi”.
Munaya tace, “hakane Aunty Salamah, shiyyasa wlhy Muftahu yafara bani tausayi, ALLAH ya kawo ranarda zai wankesa ayi walk'iya aga kowa dai”.
Amin ya rabbi gimbiyar Galadima Sameer, ku kwantar da hankalinku, komai kam ya taho gangarar zuwa k'arshe, dan alamomi suna nuna haka”.
“nima inajin haka a jikina Aunty Salamah”.
Da wannan hirar aka gama gyaran kan tahau shiri cikin less d'inta Ash colour irin kamar kayan da Galadima zai saka kenan.
Hummm masha ALLAH, maganar k'yawun da Munaya tayima 6ata lokacine, amma tayi k'yau.
Yaranma tsaf aka gama shiryasu, abin kamar ka sacesu ka gudu, sunyi fes.
Kowa yagama hada-hadar shiri, ana fitowa daga sallar La'asar za'a fara kwasar mutane zuwa hall d'in da aka tanada.
*_4:00pm_*
Dukkan mai ruwa da tsaki akan wannan taro ya hallara a gaban motocin da za'a kwashi jama'a, ana fitowa daga salla kuwa aka fara tafiya.
Munaya dai tana d'aki bata fitoba, hakama Galadima saida ya dawo salla sannan yafara shiri ma shi.
Saida kusan kowa ya tafi sannan iyayen gayya suka fito.
Munaya ce tafara fitowa, kuyangi Uku Na d'auke da yaran a bayanta, yayinda wasu kuma ke take mata baya, a babban falon sashensu suka tsaya jiran fitowar Galadima.
Tunkan ya fito daddad'an k'amshinsa ya fara isowa, saikuma sautin takun takalminsa wanda tarihi yaso maimaita kansa ga munaya, dan takun nasa Na daidaituwa ne da bugun zuciyarta.
Yana gaba Sauban na binsa a baya, Tunda ya fito Kuyangin duk sukai k'asa da Kansu, yayinda ya k'araso sai suka zube k'asa suna kwasar gaisuwa, hannu kawai ya d'aga musu, idonsa akan Munaya wadda itama ta risinar da idonta tana masa kallon k'asan ido.
Ba k'arya yayi matuk'ar k'yau, komai nasa Ash colour ne, kuma kayan sarauta y'an asali, harda rawanin daya kuma fiddi ainahinsa Na jinin sarauta, rawanin ya sakaya sajensa hancinsa zuwa bakinsa kawai ake iya gani, idanunsa na cikin eyeglasses dabaka isa kaga kwayarsu ba, dan ya toshe su 6am.
Juyawa yay ya kalli Sauban dake gefensa, Sauban ya fiddo Alk'yabbar dake cikin bag d'in hannunsa ya mik'a masa, kar6a galadima yayi yana mik'ama Sauban had'ad'd'iyar sandar hannunsa da zaka iya d'auka ta gold ce, ya warware alkyabbar ya matsa gaban Munaya dake tsaye har yanzu, yayinda kuyanginta ke a dur kushe har yanzu suma.
Matsawa yay jikinta tamkar zai rungumeta, k'amshin turarensa ya cika hancinta ta lumshe idanu, ya sako alk'yabbar ta bayanta, Sauban na gefe yanata zuba murmushi da d'aukarsu hoto.
Tamkar sokuwa haka Munaya ta tsaya har Galadima ya gama saka mata alk'yabbar a jiki, ya juya Sauban yakuma bashi turaren dake cikin jakkar, feshi ya shiga yimata da turaren, zuciyarta sai kaikawo take yi na d'umbin mamaki da al'ajabin wannan salo,
Bayan ya gama ya maidawa Sauban turaren yanama Munaya nuni da suje da hannu.
Haka suka fito a jere Kuyangi na take musu baya, yayinda Sauban yake gefe yanata zuba musu hotuna a Camera.
Motar da Sarki ya bada ita aka bud'e musu suka shiga, Sauban ya kar6i yaran d'ai-d'ai ya mik'a musu, sannan ya shiga gaba kusada sarkin mota da Amaturrahman shima.
Motar ta d'auki shiru tamkar babu wani mahaluki mai numfashi, Galadima ya zubama Abdurahman dake hannunsa ido kawai yana kallo, yayinda ya sak'ala hannunsa d'aya cikin Na Munaya yana murzayatsuna a hankali.
Itama dai tayi shiru sassan jikinta Na kar6ar sak'on ninsa.
A haka suka Isa har cikin harabar hotel d'in, Wanda ya cika dank'am da motoci, duk Wanda yagani yasan yau taron Na manyane, kodan tsaro Na musamman da wajen ya samu tundaga farkon Layin da hotel d'in yake.
Sauban da Sarkin mota suka fito, ba'a bud'e su Munaya ba, kalonta Galadima yayi fuskarnan dai babu walwala har yanzu, batareda yayi maganar ba ya kamo kwalliyar zaren gaban alk'yabbarta ya matso da fuskarta kusa da tashi, ta bud'e baki zatai magana ya d'ora nashi.
Saida ya shanye jambakin lips d'inta tas sannan ya saketa yana zuba mata harara.
Idonta harsun tara kwalla, cikin lumshe idanu da k'asaitacciyar muryarnan tasa mai had'e da izza yace, “Sau d'aya nake gargad'i, karki bari nasake miki na uku akan fita da lipstick a baki”. ya k'are maganar da kad'a mata yatsansa.
Wani yawu Munaya ta had'iye kawai tana jinjina masa kai, wannan ikon ikoko yana bata mamaki, shiyyasa fa tace Aunty salamah ta saka mata janbakin kad'an, gashi yamata k'yau amma tsabar mugunta ya shanye, lips d'insa sai zafi yakeyi, ta harari Abdurraheem dake cinyarta, saikace shine yayi laifin🤭😂.
Bud'e musu akayi suka fita, Samha da Ayusher suka kar6i yaran.
Munaya taji matuk'ar dad'i da ganin ashe harda y'ar uwarta a walimar, itama sunsha k'yau cikin Brown d'in kaya itada yaa Marwan, tana cikin less irinna Munaya, kalarce kawai ta banbanta, shikuma Yaa Marwan harda babar riga, maganar k'yawun dasukaima 6ata lokacine, suma Yaa Fadeel da Feena suna d'auke da yaransu.
Sun shiga cikin hall d'in da tawagar rakkiyar Kuyangi da dogarai, masha ALLAH Munaya tafad'a dan ganin d'unbin jama'a da aka Tara a wannan k'aton hall, manyan mutane da iyalansu sun halarci wannan waje, hakama ahalinsu Munaya kwai da kwarkwata sunzo, harda y'an anguwarsu, duk yawan mutanen nan bai hana a saka mata kan tsaro masu tauriba a wajen.
Kowa saida su Galadima suka birgesa, abin akwai tsantsar birgewa da sha'a a cikinsa,
A cikin fans harda masu k'yasa Galadima🙆🏽.
barama namuku gulma, can Na hango muku tawan Miss xoxo fa idonta kamar zai fad'o, hakama zee bawa da Aysha dansabo da kdeey🤥, dukda harar da Maman Khady da takwara billy galadanci ke musu sunk'i rusunar da idanu, lamari ya girmama Slimzy harda k'ok'arin mik'ewa fa wai zata iya barin sadeeq d'inta, da sauri saffiya Huguma ta maidata mazaunin tana hararta, Ummi Ai'sha tace, “kai dan ALLAH Ku nutsu kar'ace 'yan Haske muncika ruwan ido”, Faxy Fation da party zarah da Feedohm sukace ai Galadima d'inne fa yaji gishiri da magi, Hafsat Rano ta toshe baki tana dariya, hajja kam yitai kamar bata wajen, sai loda nama take a baki, Ayusher da khaleesat dake kallonta sukace wai hajja bazaki rage filiba a cikinki?, Mamu gee tace, “kukuma ga sa ido” “kema k'ya fad'a dai” cewar zee yabour, Asmy b Aliyu datun d'an tai shiru itada Ummu Basheer suka yamutsa fuska suna fad'in “please kuja aji mana 'yan haske, kunafa ganin yanda aka karrama mu fiye da kowa, karku jafa a maidamu kujerar baya wlhy”. Ni bilyn Abdull da lamarinsu ya girmeni nace, “kubarsu kudai kawai, sosuke susa a hanamu ganin sarakuna, kokuma mama Fulani ta rainamu, kuna dai ganin innaro ma kanta yanda taja aji ta kwamushe a gefe tana mazurai.
Miss xoxo dake gefena tayi k'asa da murya tana dai-daita kanta, tace, “gaskiya kika fad'a tawan, nidai kinsan dama dai Galadima ya dad'e a k'ok'on raina, ko sau d'ayane kisan yanda kikayi aka mana hoto tare”. Nace, “karki damu tawan, Salfe ma zakuyi, amma fa ki kula, dan Munaya babu sauk'i”. “gulmar mi kukeyi?” cewar Ayusher tana jeho mana handkerchief d'in hannunta. zamanmu muka gyara nuna wani basarwa🥺, kunsan fa muma mun fara koya a wajen Galadima😜.
Lallai, fans sannunkufa, lallai kunma munubiya da Munaya kara, ko Galadima nasan kun gama birgesa aradu, irin wannan anko da kukasha, ko a UK albarka y'ay'an baba buhari😝.
____________________
Isowar Sarki Jalaluddeen da Sarki Abdul-fatah da tawagar wasu amintattun sarakunan abokan Abie ya saka kowa ya mik'e cikin girmamawa, saida suka zauna sannan kowa ya koma ya zauna, an fara bud'e taro da addu'oi ga jarirai da kuma kakansu sannan aka fara gudanar da abinda ya Tara jama'a cikin nutsuwa.
Kusan dai lamari Na manya, mudai Fans d'in raina kama sai zuba salfe muke, karkaje kabada labari ace k'arya ka zula bakajeba😆, shiyyasa muka kafa hujja koya kukace my sweet fans🤷🏻♀😂?.
Masu 6oyayyen shiri a zuciyaa fa sunata k'iyasata yanda abubuwan da suka shirya zasu gudana, saidai kuma idan sunsan wata basusan wataba, dan eyeglasses d'in idon Galadima Google ne😏, (wato camera ne) tundaga Inda yake yanayo zooming d'in wad'anda suka k'arshen hall d'in ma, duk Wanda zuciyarsa ta saka masa alamar tambaya akansa yana tantancesu ne d'aya bayan d'aya.
Nidai Galadima ka kula banda fans d'in raina kama😨🙆🏽.
Anyi nisa da taro harma Anfara zubama cikin maik'o da mask'i, ga mai zak'i da sanyi muna korawa, Galadima ya kalli agogon azurfa dake hannunsa sannan ya d'ago ya kalli Muftahu suka had'a ido, lips ya ciza, Muftahu daya fahimci yaren ya gyad'a masa kai, ya kuma kallon Saleem da Nuren da Aunty mimi Mom and Sauban Samha Ayusher, kowannensu Kansa ya gyad'a alamar fahimta.................✍🏻
Turk'ashi, tofa masu karatu, shin mike shirin faruwane haka? Wannan amsa tana page 26 da zaizo ranar Monday insha ALLAH. musha weekend lafiya sisters and brothers.🙋🏻🙋🏻🙋🏻
Barkanku da juma'at😁🤝🏻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭👏🏻
*_typing📲_*
💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._*
*_♦RAINA KAMA.....!!♦_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
___________________
_Writer's namu ina mik'o gaisuwa da babbar murya_.🙋🏻
*_(takwara) Bily s Fari, (mamana) Maryam IG, (mamana) Ummu hanan, Hauwa'u A Usman (jidda😘) Rufaida Umor, Qurratul ayn, Ai'sha Alto, Leemat, gwoggo😜 Asykhaleel, miss Xakss, Jameela Janaf, (takwara) Ummie Garkuwa, Khadeeja Candy, Billy Sarki, Sister Naja'atu, Reefat yahya, Sad-Naf, Maryam wasagu, Maman Shaheed, classic Feedo, Mzzdady._*
🙆🏽 _Yawane da kufa. Alkairin ALLAH ya kai gareku aduk inda kuke, bilyn Abdull na nayinku wujiga-wujiga🥰😘😘👍🏻_
___________________
~Book 2~ 👉🏻2⃣6⃣
...................MC yafara shelanta cewa wannan bikin sunafa an had'ashi da bikin birthdays ne, domin ranar haihuwar yaran tai dai-dai da ranar haihuwar iyayensu, dan haka suka had'e wannan biki a yau guri d'aya, dan a waccan ranar murnar haihuwar bata basu damar yanka cake ba😂.
Dariya aka sanya, saboda a yanayin barkwanci mc yayi maganar, Galadima kam ai kod'an murmushin ma baiyiba, garama Yaa marwan ya murmusa.
Galadima ya kalli munaya, cikin maganar nan tasa mai kamada an masa tilas yace, “Kina da sa'a”.
“Sa'a kuma?”. ‘Munaya ta fad'a cikin yanayin mamaki’.
Harya bud'e baki zaiyi magana sai kuma ya basar. ganin haka itama Munaya saita sharesa, dan takula yau y'an mulkin ne a kansa.
Saida ya gama shan k'amshinsa sannan yace, “wannan ne karon farko da Sameer yata6a bikin birthday”.
Baki munaya ta d'an ta6e, tana fad'in “Humm, kodai y'ay'anka suna da sa'a?, domin dai a dalilin haihuwarsu ne kayi”.
“ko kina jealous ne?”. ‘yay maganar cikeda basarwa’.
tura baki tai gaba.
Idonsa akan yaransa yace “idan kika bari na kama wannan bakin a wajennan humm.” ya cije lips d'insa.
Sanin k'aramin aikinsane ya akaita abinda ya fad'a d'in ya sata saurin gyara bakinta , tad'an saci kallonsa, ya wani Fiske tamkar ba shine yay maganar ba ma. ita dai tana mamakin kasaita da izza irinna bawan ALLAH n nan, jinin mulki yana da matuk'ar k'arfi a jikinsa. tunaninta ya katse lokacin da hankalinta ya koma kan abinda ke faruwa a hall d'in
Khaleel da Aiyaan, Aryaan ne suka turo cake mai k'yau da tsari, Wanda yasha kwalliyar White and Golden, an saka sunan Galadima da shekarunsa 31years a sama, a jikinsa kuma daga can k'asa ansa Muhammad Sameer (Dadyn Triples), an d'ora candlestick🕯guda uku, Sai hotonsa da yay k'yau sosai cikin shigar sarauta.
Galadima ya kalli Sauban da Samha, yasan dai wannan aikinsu ne, k'in kallonsa sukayi sukam ballema suyi gamo da tsarabar harara😅.
Ita Munaya ma sai yanzu taga Su Aiyaan, batayi zaton anzo da suba, tunda bataga yaran gidansu k'anana ba a waje, sai manya maza da matan Na ma'auri.
MC ya taso k'eyar su Khaleel har inda su Galadima suke zaune, kowanne aka d'ora masa yaro d'aya, suma mik'ewa sukayi bisa umarnin MC d'in, a tare suke takawa ita da shi, sai k'yastu ake zuba musu, masuyi a waya da masu cameras, sai gidajen TVs d'in da aka gayyata suna nuna live. Sun Isa gaban cake d'in hannunsa rik'e da sandarsa, kaikace sarkine da kansa (gaskiyar Munaya Galadima akwai k'asaita, Kodai sarkin da Kansa ya shafa masa lafiya🤭).
Bayan anmasa wak'ar happy birthday yayma munaya nuni waita hura candles d'in.
Cikin k'asa da murya tace, “yalla6ai bafa haka akeyiba, ka hura abinka da kanka”.
Hannunta ya kama ya matsa yanda zataji zafi, yace, “zakiyi?”.
Ai baima kai k'arshen maganarba ta risina ta hure wutar, hall d'in ya d'auki tafi. cake d'inma dan rigima wai saidai su yanka tare.
“haba yalla6ai, saikace Na wani aure?”.
Cikin ta6e Baku yace, “wama ya sani kona auren ne”.
Shiru tayi bata tanka ba, dan itadai fatanta a rabu lafiya, hannunta ta d'ora kan nasa dake rik'e da wuk'ar suka yanka taren. nanma dai tafin akayi. Ya lakata a d'an yatsa ya duk'o gasu Aiyaan ya daddan gwalama yaransa a hanci da kumatu, sannan ya juyo ga Munaya da haushi ya kamata, ai ita yakamata ma yafara sawa ba yaranba.
Itama akan hanci ya shafa mata yana fad'in “yalla6iya haushi kikajine?”.
Kafin tabashi amsa yakuma lakata ya shafama Aryaan Khaleel da Aiyaan suma.
Dole munaya ta had'iye maganarta. Amma ta kudiri saita rama.
Itama itada Munubiya k'aton cake nasu aka kawo kalar pink and White , Munu da Yaa marwan suka taso a tare.
Munaya da Munubiya suka rungume juna suna maijin dad'in tunawa da ranar haihuwar su, shekaru 20 cif da kwana 7. Sun yanka cake atare suka sakama juna abaki kad'an-kad'an, sannan kowacce cikin son tsokana ta lakatama y'ar uwarta a fuska suka rungume juna suna dariya da k'ananun hawaye, suncika shekaru 20 ranarda yaransu sukazo duniya suma.
Abin ya birge mutane, Munubiya ta matsa ga mijinta ta saka masa a baki kad'an, cikin murmushi yace, “happy birthday my heartbeat ”.
Tace, “Thanks you my luv” k'arasawa tayi ta sakama yaran munaya dasu Aryaan a kumatu, sannan ta sakama nata yaran.
Munaya danta rama abinda Galadima yamata, takai cake bakinsa kamar zata bashi, saida ya bud'e baki saita juya ta shafama yaran Munubiya a kumatu, sannan nata.
Yanda Galadima yay shock akan abinda Munaya tamasa sai mutane suka sanya dariya suna tafa mata, mai martaba da papi ma dai saida suka Murmusa.
Munaya ta dawo ta dangwalama Galadima akan hanci tana masa gwalo.
Shi kansa baisan k'asaitaccen murmushin ya kufce masaba, ya saka handkerchief ya goge yana dawowa mazauninsu ya zauna.
Daga nan aka fara gudanar da wasa, Comedian's sukazo sukad'an saka mutane dariya, saikuma mawak'a da suka bada nasu salon.
Tun da Galadima ya fara yawaita kallon agogon hannunsa su Muftahu duk suka sake shiri, dan lokaci yana gab kenan.
Galadima yay k'asa da murya batareda ya kalli Munaya ba, yace “ki shirya, shirinsu na farko d'aukewar wutar hotel d'in nan gaba d'aya, na gaba kuma shine banida tabbas. Yara dai ALLAH yana tare dasu, gakuma su Aryaan suma”..
Cikeda mamaki Munaya ta kallesa, sannan ta kalli yaran dake gabansu a wani d'an gado mai k'yau.
Jikinta har rawa yake tace, “yalla6ai mi su Aryaan zasu iya? Please k.....”.
Hannu ya d'aga mata alamar karfa ta ishesa yace, “wani ilimin aduhuwar daji kawai ake laluboshi, kinsan kuwa dolene a gamu da had'arurruka Aciki”.
batada za6i sainyin shiru, ta kalli su Khaleel daketa wasa da abinci a teble da suke zaune hankalinsu kwance. Hawayene ya cika mata idanu, yama za'ayi wad'an can sakarkarun yaran ace suna masu bama yaranta kariya? Yaushe suka gama sanin ciwon Kansu ma balle na waninsu? gaskiya wannan gangancine kawai, tasa handkerchief ta share hawayen da ke k'ok'arin zubo mata.
Duk abinda take Galadima yana kallonta. duk tausayinta saiya kamashi, ya tuna da wahalar datasha, amma bashida za6in daya wuce hakan, kuma itace tabashi k'arfin gwiwa ai, yasaka aransa ko salwanta yaransa sukayi zaiyi tawakkali insha ALLAH.
Duk Wanda yake cikin shirinsu Galadima ya gama shirinsa, haka suma mak'iya masu buri a shirye suke.
Gaba d'aya saura mintuna 25 atashi, saboda gabatowar sallar magrib, a kuma time d'inne Sarki Abdul-fatah da Sarki jalalludden dadai duk wani babba Wanda sukazo tare suka mik'e domin tafiya, ganin haka Galadima yama Yaa marwan sigina da ido akan ya fita da Ameen and Ameena suma, yabi tawagar su papi, dan baya buk'atar a cuta musu..
Jikin Yaa marwan a sanyaye ya d'auki yaran ya fita cikin dabara, yana kallon y'an uku, shidai dan kawai Galadima ya dagene, amma bai kamata a saka yarannan a matsayin tarko ba.
Munaya ma dai ta danne zuciyarta tayi shiru, tanason bama Galadima kwarin gwiwa.
Su papi na fita y'an rawar k'oroso suka fara wasa, mintuna goma da aka basu ya k'are, sai wani mawak'i ya fara nashi, nanfa y'an mata da samari aka samu nayi, dama ganin su mai martaba ne ya sakasu nok'ewa, ana tsaka da cashewa hall d'in yay d'iff, wuta ta d'auke agaba d'aya hotel d'in, mutane aka fara hayaniya kowa na k'ok'arin damk'e dukiyarsa a hannu da k'ok'arin kunna fitulun waya.
Gaba d'aya jikin Munaya yahau 6ari, ta fashe da kuka tana laluben gadon da yaran suke, ruk'ota Galadima yay yasaka a jikinsa, muryarsa na rawa yace, “please ki nutsu”.
“bazan iyaba yalla6ai, karsu......”.
Yay saurin rufe mata baki, da tattausan tafin hannunsa..... A dai-dai wannan lokacinne kuma wutar hotel d'in tadawo.
Hall d'in ya kuma kaurewa da hayaniya, zaram Munaya da Munubiya suka nufi gadon da yaran suke ciki, wayam babu komai.
Munaya tayi luuu zata fad'i, saurin ruk'ota Munubiya tayi, Galadima yataso daga inda yake shima zuwa garesu. hall d'in yagama rikicewa da tsantsar hayaniyar rashin ganin yaran, sai kallon kallo akeyi. Securitys d'in da aka baza sun rikice da wannan tashin hankali, dan sune mutane na farko da za'a fara tuhuma.
Rufe hotel d'in akayi aka hana kowa shiga balle fita,
Galadima ya shafama Munaya ruwa ta kawo numfashi, fashewa tayi da sabon kuka ta fad'a jikinsa, hannu biyu ya saka ya rungume ta shima yana had'iye kwallar bak'in cikin dake Neman zuboma idonsa.
Tausayinsu ya kama mutane da yawa, innaro harda kukanta, hakama inno, abinda yabani mamaki shine tsantsar damuwar da mama Fulani ta nuna, dan itacema tabama Galadima ruwa ya shafama Munaya ta farfad'o.
Da farko Munaya ta d'auka ko Galadima wasa yake mata yasan inda yaran suke, amma ganin damuwar da yake ciki saita kuma rikicewa, dandanan numfashinta yafara gagarar k'irjinta, ta mik'e a kid'ime, dan taji a jikinta kuka sukeyi, nononta sai tsitstsirawa suke, wani jirine yafara hajijiya da ita da zuciyarta ta k'iyasta mata zafa su iya kashe mata yara, luuuu tayi baya Galadima ya ruk'ota. sume musu ta kumayi.
Hankalin Galadima kuma tashi yayi, dole ya d'auki Munaya aka sakata a mota suka bar hotel d'in.
Sauran mutane kam kowacce mota zata fita sai an binciketa.
Yayinda Securitys d'in suka bazu ko ina na hotel d'in ana bincikawa.
Gida aka wuce da munaya, har suka isa tana jikin Galadima, yanata murza tafin hannunta kozata farfad'o, har d'ora bakinsa yayi akan nata ya jawo iskar numfashinta amma a banza, hakanne yakuma tada hankalinsa.
Kai tsaye d'akinsa ya wuce da ita, ya shimfid'eta a kan gadon ya cire mata alk'yabbar jikinta, Akash suka k'araso da hanzari shima, taimakon gaggawa yafara bata shida doctor jalal, cikin amincin ubangiji saigashi takawo numfashi, bama su bari tadawo dai-dai ba suka mata allurar barci.
Suna fita Galadima ya cire rawani da alk'yabbar jikinsa shima, ya sassauta bottom d'in wuyan rigarsa.
Safa da marwa ya shigayi a tsakar d'akin yana Mirza agogon hannunsa Wanda daka gani kasan ba normal agogo bane,.
Wayarsa datai k'ara yay saurin d'auka, d'agawa yayi yasaka a kunne, “Muftahu ya ake ciki?”.
Cikin hakki Muftahu yace, “komai yana tafiya yanda ya kamata ranka ya dad'e, har yanzu gamu muna bin bayansu, amma munkai inda yakamata ka fara Controlling namu, yanzu mun.......”
Da sauri Galadima ya katseshi ta hanyar fad'in “karka damu ina kallon Ku, saidai kilometer's d'in dake tsakaninku dasu fa yakai 1½, Saleem da Sauban sunfi kusa dasu, dan haka ku k'ara azama. daga lokacin da suka farga da abinda nasaka jikin Amaturrahman tabbas zasu cireshi, kuma zamu rasasune gaba d'aya”.
“Ok babu damuwa, ranka ya dad'e”.
Yanke wayar sukayi, Galadima ya bud'e wani k'aramin akwati ya fiddo kayan aiki wanda a ready dama yagama had'a komai, bajesu yayi akan gadon kusada Munaya, ya zauna yafara Control cikin matuk'ar kwarewa.
Saleem ya kira aunty Salamah wadda itama take tare dasu Ameer yaran da suka sace Muftahu, d'agawa tayi jikinta na rawa, “Saleem kuna inane?”.
“Aunty Salamah gamunan bayansu kad'an, amma mund'an basu k'afa saboda na kula sunfara fuskantar muna bin su, yanzu dai haka mun ajiye motarmu mun samu mashin”.
“Hakan yayi, insha ALLAH indai ta Anguwar da muke tsammanin zasu shigane kamar yanda kaji Harun d'in yay magana to tabbas mu dai mun iso, saidai suzo su iskemu, ka kira yalla6ai ka sanar masa yakamata ya fito yanzu”.
“no Aunty Salamah, bazai yuwu boss yabaro masarauta ba yanzu, saiya tabbatar mun Isa, saboda dukma inda suka shiga yana bibiyarsu, dan bazai saka yaransa a matsayin tarko ba babu tsaro k.......”
Tai saurin k'atseshi ta hanyar fad'in “yauwa ina zargin kamar gasunan a wata bak'ar mota sun wicemu fa”.
“Alhmdllh, su Ameer Susan yanda zasuyi su bisu bara na kira boss”.
“ok”. Kawai Aunty Salamah ta fad'a ta yanke wayar.
Kiran Galadima Saleem yayi, bugu biyu ya d'auka, “Saleem mike faru yanzu?”.
“Ranka ya dad'e gamu dai biye dasu, amma Aunty Salamah tacemin gasu tagansu”.
“wacece Salamah? ”.
Gaban Saleem ya fad'i, dan ya manta Galadima baisan Salamah ba, “Am sorry sir, idan komai ya dai-daita zan maka bayani”.
“Saleem!!!”. Galadima ya kirayeshi a tsawace.
Saida Saleem ya janye wayar akunnensa, muryarsa na rawa yace “ka yarda dani sir, wlhy itama ta kwarai ce”.
Ajiyar zuciya Galadima yayi, muryarshi cikin tsantsar damuwar yace, “wannan anguwar da kuke tanada hanyoyi da yawa, dan haka Ku fara amfani da live GPS navigation maps naku, yanzu zanyi settings komai yanda zaku ringa ganinsu duk layin da zasu shiga insha ALLAH, waye yake driving d'in a cikinku?”.
“nine sir”.
“ok bama Sauban wayar”.
Saleem ya mik'ama Sauban wayar, Galadima na fad'a masa yanda zaiyi, shikuma yana Controlling maps App d'in dake cikin System d'in cikin kwarewa, (dan shima Galadima bai barsa hakaba, dukda bashida ra'ayin karantar wannan fannin saida ya tsaya tsayin daka ya koyan saboda irin wannan ranar).
Saida Galadima ya tabbatar komai ya dai-daita, sannan ya kira su Nuren ma, suma suka dai-daita komai nasu, cikin sauk'i duk suka koma ganin inda yaran suke, saboda Galadima ya saka Abu jikin Amaturrahman, dukda bawai hotonsu ko video suke kalloba kai tsaye.
Duk da haka Galadima ke fad'a musu su shiga layin haggu, ko dama, kosu canja hanya dadai sauransu.
Duk Wanda yake a wannan masarauta yau hankalinsa a matuk'ar tashe yake, saifa kallon kallo da hasashen juna ake a zuciya, kowa yana zargin Wanda ya raina.
Hankalin Abie a matuk'ar tashe ya nemi ganin Galadima, koda sarkin k'ofa yazo yana knocking Galadima bai amsaba, kuma yana kallonsa ta CCTV.
d'an aike ya koma ya sanar Galadima ya kulle kansa a d'aki yak'i bud'e k'ofa.
Papi inno ya kira, yace maza taje sashen Galadima taga mike faruwa.
Ko kuyangi inno batajira sun mata rakkiyaba, hasalima babu Wanda yaga fitowarta a sashen mama Fulani, dan kowa a rikice yake da wannam bak'on lamari na satar yara.
Galadima daya ga sarkin k'ofa yabar wajen ya mik'e shima daga gaban kayayyakin da yake aikin, shaddar jikinsa ya cire yasaka bak'in wando da t-shirt, ya kawo bak'ar jacket mai k'yalli kamar rigar sanyi ya ajiye gefe, a bakin gadon ya zauna yana d'aura takalminsa yana cigaba damasu Sauban da Nuren bayanin hanya, a dai-dai lokacinne Inno ta iso sashen nasa, da hanzari Sarkin k'ofa ya bud'e mata k'ofar, bata jira wani isoba ko masa sallama ta turo k'ofar falonsa ta shigo, babu kowa a falon, komai ma a kashe yake. Bedroom d'insa ta nufa, nandai saida tayi knocking kam, saidai kafin yay yunk'urin tasowa ya bud'e mata ta turo k'ofar ta shigo, mik'ewa yay yana kallonta da d'aukar jacket d'insa zai saka.
Ajiyar zuciya inno ta sauke, saboda ganinsa normal.
“Ranki ya dad'e da kanki? lafiya dai ko?”.
“Inafa lafiya Muhammad? takawa ya aiko a kiraka ance ka kulle kanka, gashi baka sanar mana halinda yarinyar nan take cikiba”.
Galadima yace, ba kulle kaina nayiba, bansan kuma d'an aiken daga papi yakeba” ya juya yana kallon Munaya da cigaba da fad'in, “itama ta farfad'o, amma sun mata allurar barci”. ‘ya k'are maganar da daidaita zaman kwalar rigar jacket d'insa’.
Ajiyar zuciya inno ta kuma saukewa, tace, “to Alhmdllh. ina kuma zaka naga kana shiri?”.
Wani murmushin takaici yayi zuciyarsa dake gudun daya wuce kima da suya ya dafe, Inno dai ta zuba masa ido, takowa yay inda take ya kama hannunta ya rankwafo (dan yafita tsaho) ya d'ora bisa kansa, cikin murya mai nuna tsananin karsashi da alwashi yace, “kisamin albarka inno, zanje farautane”.
Da sauri ta janye hannunta daga kansa tana matsawa baya, “Muhammad mikake nufine? kana ganin tashin hankalin da muke ciki shine zaka k'irk'iro mana wani kuma? kana tunanin wad'annan mutanen zasu barkane? dama kai suke fako, shiyyasa sukayi tarko da bayin ALLAHn dabasu ji ba basu gani ba, su takawa cikin k'ok'arin d'aukar mataki suke, yanzu haka naga IG da kansa gashican ya iso bisa umarnin kiransu”.
Galadima dake tattara abinda zai amfani dashi yana zubawa a aljihu, yace, “inno Muhammad Sameer d'inku ba ragon namiji bane da zai zauna jiran Police d'in da suka gaza gano wad'anda suka durk'usar masa da mahaifi tsawon shekaru a yanzu kuma nayi tunanin zasu iya dawomin da gudan jinina har uku, ba sune sukamin tarko ba nine namusu tarko, idan tsoron na mutu kuke, Ku cire inno, ko babusu mutuwa tabbataccen abune rubutacce a kundina, kimin addu'a saina saina dawo”..
Biyosa inno tayi har babban falo tana Kiransa amma yak'i dakatawa, saima d'aga mata hannu da yakeyi, yana gab da zai fita ya juyo yana fad'in “karki d'aga murya da yawa ranki ya dad'e, dan kunnen magauta a bud'e yake”.
Yana fitowa Sarkin mota ya taso, dan suna zaune jigum-jigum a rumfar bunun dake sashen na Galadima, duk gaisuwar da suke masa babu ta wacce ya amsa, yau kam ko d'aga hannun basu samuba ma.
Basu damuba dan dolene kowa yamasa uziri.
Da kansa ya bud'e mota ya shiga mazaunin driver, Sarkin mota daya k'araso yace, “ranka ya dad'e ka gafarceni gani”.
Da hannu yamasa nuni da gefen mai zaman banza batareda yace uffan ba.
Sarkin mota bashida za6in daya wuce zagayowa ya shiga.
A 360 Galadima ya ja motar, kamarma ya manta yana cikin masarautane, saida suka fito gaba d'aya sannan ya bud'e baki da k'yar yace, “ka dinga kallon bayanmu, dan nasan dole za'a samu masu binmu”.
Da “to” sarkin mota ya amsa cike da girmamawa.
Sarkin mota yace, “tabbas ranka ya dad'e ana binmu”.
Cije lips Galadima yayi, ya canja hanya, cikin salon iya taku suka 6acema su Harun dake bin su tundaga masarauta.
Hankalin Harun ya tashi kwarai da gaske, dan bai shirya fito na fito da Galadima ba yanzu, saiya cimma burinsa, daga nan komai ta fanjama fanjam, iya zagaye-zagayensu baiga ko motar datai kama data Galadima ba.
Shima yana 6ace musu ya dawo kan titi sosai, Maps d'in GPS ne yazama jagoran Nuna masa hanya, da taimakon Sarkin mota kuma dayasan gari. Danshi Galadima ba tuk'i yakeba idan yazo 9ja, saidai idan ta kama tilas babu yanda zaiyi kamar irin haka.
Sunyi tafiya mai tsawo, yayinda yake Communication dasu Nuren dasu Saleem. A haka ya iso inda suke, duk fitowa sukayi daga motocin, shima Galadima ya fito, idonsa akan agogon hannunsa, yad'an kallesu sannan ya koma kan waya yana fad'in, “maps d'in ya nuna suna a wajennan, kunga kenan tsakanin gidajennan guda hud'une dake kallon juna?”.
“kwarai da gaske suna nan”. cewar Muftahu yana furzar da iska.
Galadima yace, “Sauban da Saleem zaku cigaba da Control namu”. ‘yay maganar yana ciro agogon hannunsa ya mik'a musu, “ga wannan kuci gaba da using dashi”.
Suka amsa da “to” suna kar6a. ya mak'ala abinda zai taimaka masa yaji magana, suma su Nuren duk yabasu suka saka.
Har zasu bar wajen ya dakatar dasu ta hanyar d'aga musu hannu, takawa yay gaban k'ofar gidan farko ya haska gaban gate d'in da fitilar wayarsa, babu abinda yake nema, ya matsa na biyu ma haka, komawa yay d'ayan 6angaren, yana haskawa saiga sawun tayar mota data shiga gidan, duk'awa yay ya d'iba k'asar wajen ya shinshina, ya d'ago ido ya kalli gidan yana jizar lips, saiya zubar da k'asar daya d'iba ya mik'e, da hannu yayma Nuren da Muftahu nuni nan ne.
Tahowa sukai garesa, Aunty Salamah datun d'azun suna daga cikin mota suna kallonsu suma suka fito ita da su Ameer.
A tare suka rissina suna gaida Galadima ya amsa yana bin su da kallon mamaki.
Da yake su Saleem sun sanar dasu Muftahu su Aunty Salamah d'in sai Nuren ya kuma yima Galadima bayani.
Aunty Salamah tace, “ka gafarcemu ranka ya dad'e, nasan zakayi mamkin mun shigo abinda ba'a gayyacemu ba, insha ALLAH zakaji dalilin shigowar tamu nan gaba. game da shiga gidan nan mungama komai, maza 5 ne da mata biyu, wad'anda shigarsu ta tabbatar min suna cikin hadiman masarauta su matan kenan”.
Kai kawai Galadima ya iya jinjina masa. daga nan yaymata nuni da zasu iya farawa.
Da taimakon su Ameer suka shiga gidan.
★★*★★★*★★★*★★
Fitar Galadima da kusan awanni hud'u, around 2am Munaya ta farka a firgice, Inno dake zaune akan Sofa, mom da Aunty Mimi kuma a gefen gadon suka kalleta, tashi Mom tayi da sauri ta nufeta tana rik'eta, itama Aunty Mimi ta taso.
Kuka munaya ta sanya tana fad'in “Mom sun mutu ko? Nasan dama kashesu zasuyi, Aunty Mimi dan ALLAH miye laifinsu su? kwanansu 7 fa kacal yau a duniya, mi suka sani game da abinda ake tuhumarsu? An durk'usar musu da kakansu, an hana mahaifinsu nutsuwar zuciya data rayuwa, shin wannan tabon bai Isa a barsu su taso da shiba a rayuwarsu? Har sai an had'a da salwantar dasu kenan?”. ta fashe da kuka maiban tausayi.
Tasowa inno tayi ta zauna a bakin gadon itama, kamo hannun Munaya tayi ta kwantar da ita a jikinta tana shafa kanta, yayinda itama kwallar kebin nata kumatun.
Aunty Mimi da mom ma duk hawayen sukeyi, kalaman Munaya sun ta6a zukatansu.
Lallashinta da magana mai dad'i suka shiga fad'a mata, sai sauke ajiyar zuciya takeyi, ga jikinta yayi ringim da zazza6i saboda nononta sun mata hak'e-hak'e, rabonsu da shansa tunda rana, tausayinsu ya kuma kamata, tasan yunwa da k'ishi ma kawai sun Isa su k'arar da numfashinsu, hawaye masu d'umi suka kuma gangaro mata a kumatu suna sauka jikin inno dake shafa kanta.
Shayi Aunty Mimi ta had'o mata, amma fir tace ta k'oshi, da k'yar inno ta samu ta lalla6ata tasha Quarter d'in kofin.
Mom tace, “wannan nono kid'an matsesu kozasu rage miki nauyi, dan shine yakawo wannan zazza6in”.
Bata musaba aka kawo k'aramin bowl ta matse aciki, Aunty Mimi ta zubar a bayi”..
Tanason tambayar ina Galadima tanajin kunya, sukuma babu Wanda ya sanar mata komai, kodan gudun k'ara tada hankalinta.
Magani suka bata tasha takoma ta kwanta, yayinda sukuma suka mik'e duk suka d'aura Alwala suna mik'ama Ubangiji kukansu, danshi masanin sirrin 6oyene, yana kallon komai, kuma shine zai kawo iyakar komai d'in.
★★★★★★★
Duk wannan abun dake faruwa su Momma babu Wanda ya sanar musu, saidai sukaji a jikinsu tamkar akwai matsala, sunta kiran numbers amma daga wadda zasu samu a kashe sai wadda network zai hanata shiga.
Sai suka d'aura ko shagalin sunan ne yakawo hakan.
*******************
Tunda Munubiya suka koma gidan kuka takeyi, ko kad'an tak'i sauraren yaran da keta tsula kuka suma, balle tabasu nono.
Ba itaba hatta su Ayusher dasu feena kukan sukeyi, hakama Samha harda shid'ewa, dan itama su tabi bata koma masarauta ba, Yaa marwan da mama Rabi'a ne kawai ke k'ok'arin danne nasu suna lallashinsu.
Yayinda dare yay nisa duk sai suka d'aura alwala suka zo suna mik'ama Ubangijin talikai kukansu da k'ok'on barar bama wad'annan k'anan alhaki kariya da fatan ku6ta.
A 6angaren gidan su Munaya kam duk hassadarsu yau dai sun tausayama gudan jininsu da yaranta, sundawo gidane kowa yana sharar kwalla da addu'ar ku6tar yaran.
Ita innarsu Munaya ma ai ba'a magana, ALLAH kad'aine yasan halin datake ciki, ta shige d'aki ta rufe kanta tana jera nafilfili, dan wannance kawai gudunmawar dazata iya bayarwa a garesu akan wannan lamari mai sark'ak'iya da yawa.
Abban su munaya ma yau harda hawayensa, dukda bashi da tabbas akan hasashensa yasan komai zasu iya, saboda SD yanada kusanci da wannan masarautar sosai, duk abinda ke hannunsa da bayanan daya ajiye ya shiga tattarasu waje d'aya...............✍🏻
😿Duk nisan jifa dai k'asa zai fad'o, kwana 99 na 6arawo, 1 kuma tak namai kaya.👎🏻
Fans insha ALLAH dai abuwa sun fara warwarar zare, sai mubi su Galadima muga yanda zasu dawo mana da triplets d'inmu gida😭, yau Munaya tabani tausayi daga ita har Galadima, dan shima dai dannewa kawai yake saboda jarumta, ALLAH ya rabamu da sharrin mak'iyi komai k'an k'antarsa, Harun da sauran munafukai MAZA BISA KANKU🏇🏻🏇🏻🏇🏻🏇🏻🏇🏻.
Barkanmu da dawowa my sweet fans🤕😡.
Yau bana cikin yanayin dariya😡