Hausa novels 2023

  • Home
  • Ciwon Idanuna
    • Internet
    • Market
    • Stock
  • Agola
    • Dvd
    • Games
    • Software
      • Office
  • Mijin Biza
    • Child Category 1
      • Sub Child Category 1
      • Sub Child Category 2
      • Sub Child Category 3
    • Child Category 2
    • Child Category 3
    • Child Category 4
  • Kwarata
  • Health
    • Childcare
    • Doctors
  • Inda Ranka

Sunday, December 31, 2017

ANTIN YARA Page 21-30

 December 31, 2017     ANTIN YARA 1-END     No comments   

ANTIN YARA Page 21-30

.

Mum da miher sun fito a tare kan maryam a sunkuye, tayi saurin  durqusawa qasa ta gaishe da mum din manosh cikin fara'a da sakewa sosae mum ta amsa mata gaisuwa tare da tambayanta ya mutanen gidan, sun dae gaisa sosae amma kan maryam a sunkuye yake. Mum tace ki saki jikinki fa , nan kaman gida ne haka dae sukaci gaba da hira mum ta kama hanya ta tafi ta barsu ita da miher. Miher ta kawo mata kayan maqolashe kala kala, maryam bata iya cin komai ba in banda ruwa da tasha. Suka dan yi hira kadan daedae lokacin dad din manosh ya shigo yana kiran miher da sauri tace naam dad, sannan ta fita taje wurin dad dinta, yace ke da wa kuka shigo?? Tace nida wanda bro manosh zae aura ne. Tazo gaida mom ne nan dae tace dad bari tazo ta gaishe ka, tayi sauri ta koma taje ta kira mrym da sauri ta fito kanta a sunkuye ta durqusa har qasa ta gaishe da dad shima ba laifi cikin fara'a ya amsa. Koda suka gaisa ya wuce dakinshi ita kuwa maryam tana kallonsa a nitse ta sake tabbatarwa wannan shine mutumin da nan da bazata taba mantawa dashi ba a rayuwarta.

Jiki sanyaye ta koma falo suka zauna dae, ita kanta miher ta lura da sauyi daga gareta amma bata ce mata komai ba. Maryam ta dan zauna na kusan 30 mins tace to gaskiya zata tafi saboda batason dare yayi miher tace bazaki tafi ynxu ba dole se bro manosh ya dawo dan shine zai maida ke gida maryam tace aa ni bamuyi haka dashi ba dan allah ki tashi ni zan koma gida. Miher taga dae da gaske takeyi dan haka ta kira bro manosh a waya ta sanar dashi bada jimawa ba yazo daedae lokacinda suka fito tayi sallama wa mum zata tafi, mum ta hada mata goma ta arziki ta rako ta har kofar falo sannan ta juya ,  shi ko dad daman ya riga da ya fice. Ko da ta iso wurin mota tana tsaye shi ko manosh ya danno shi da marwan kallonta yakeyi tun daga sama har qasa saboda kayan ya bala'in mata kyau murmushi kawae takeyi tare da gaishe da marwan bayan sun gaisa ne manosh ya matso kusa da ita yace wato bazaki gaishe ni ba kenan?? Shuru tayi batace mishi komai ba tace nidae ka kaini gida yace ae ba ni na kawo ki ba wanda ta kawo ki saeta maida ke,maryam ta maida kallonta gun marwan tace marwan kaji abinda yace ko,marwan yace rabu dashi muje in maidake,duka manosh ya kaiwa marwan tare da cewa ina ruwanka acikin hidimata,marwan yace da ruwana mana aunt muje in kaiki gida kinji tare da dannan keyn mota ya bud'e mata gaba ta shiga ta zauna sannan manosh ya karb'e keyn a hannun marwan yace zaka zauna a baya kenan,marwan yace eh ba matsala,maryam tayi mirmushi yayinda miher tasa mata goma na arzikin da mum ta had'ota dashi sukai sallama manosh yaja mota suka tafi.

Tunda suka fara tfy manosh da marwan ne suketa hira itakam tayi shuru tana ta tunani a ranta. Manosh ya lura cewa akwai sauyi tattare da ita,yace kira sunanta a hankali apple,juyowa tayi suka had'a ido sannan ta mayar da kanta gefe,shuru yari bai sake cewa komaiba har suka iso girei,marwan yace jirani abokina bari naje gun rash a tsatstsaye yanzu zan dawo.

Bayan marwan ya tafine su kuwa suna zaune a cikin mota manosh yace apple meyake damunki? Murmushi tayi tace bakomai,yace no apple karmu fara haka dake pls ki gayamin dan nasan akwai wani abu,tace gaskya naji dad'in yadda aka karb'eni a gidanku mum naka tana sona sosai nagode sosai tana murmushi tare da kallon kyawawan idanunsa,shima idanun nata yake kallon yayi da yakejin shaid'an yana zugashi da cewa kayi kissing nata manosh,maryam taga kallon da yake mata ya fara wuce gona da iri dan haka tayi saurin kawar da kanta tare da cewa zan shiga gida. Manosh ya dawo hayyacinsa yace bakomai apple kin cancanci a k'aunaceki domin kina da halayya na gari masu kyau daban sha'awa,dad'i taji tace ai kaima haka,dan azamanin yanzu da kyar asamu namijin da baya iya tab'a koda hannun budurwansa shiyasa kullum nake k'ara sonka manosh nasan cewa kana min so na gaskyane kuma mai tsafta. Jikinshi yayi sanyi dajin kalaman maryam,yayi hamdala a cikin zuciyarsa yace Allah nagode maka danafi k'arfin shaid'an a wannan lokacin Allah ka k'ara kareni akan sha'awar da nakeyiwa maryam ameen. Ta katseshi da cewa ya naga kayi shuru,yace bakomai kawai bana so ki tafine harse marwan ya dawo,murmushi tayi tace toshikenan kamin hira,yace kedai zaki min,tace ni nawa sun k'are ai,yace to mata biyu nake sofa in aura dake da kuma wata kin amince? Murmushi tayi tace eh na amince mana ai halal ne kana iya yin hud'uma,dariya sosai manosh yakeyi,wanda yake burge maryam dan manosh ya had'u wlh sedai sam bai fiye yin dariyaba wanda ta lura hakanma dan itace yakeyi se kuma dasu marwan ko miher. Manosh ya tsargu da irin kallonsa da maryam takeyi yayi sauri tsayawa da dariyan nashi yace "apple why are looking at me like that?" Kunya sosai taji dan batama san ya akai taketa kallonshi hakaba,kuma aduk lokacin take kallonshi sha'awarta tane kawai yake kamashi. Maryam tace ina son ganinka aduk lokacin da kake dariya dan kanamin kyau sosai manosh,jiyayi kamar ya rungumeta dan yadda yake ji,amma seya daure yayi d'an murmushi tare da d'aukan wayarsa ya kira marwan yace ganinan zuwa mutafi sannan ya katse wayar maryam tana kallonshi,shi kuwa bai sake kallontaba hannayenshi suna kan siterin mota yace apple am goying,mamaki taji amma setace tonagode Allah ya kiyaye hanya yare da bud'e kofar mota ta fita se nanne shima ya fito tare da d'aukan abubuwan da mum ta bata yake mata har zauren gidansu ya ajiye.

Tace nagode tana murmushi,kallonta yayi batare dayayi murmushi yace *minfu miyatti* sannan ya wuce motarshi ya shiga yaja yana mata bye,ita kuwa murmushi kawai take mishi daga k'arshe ta d'aga masa hannu sannan ta wuce gida.

Maman maryam tayi farin ciki sosai dajin yadda aka k'arb'i maryam hannu bibbiyu,ga kuma zannuwa da less masu tsada ga sarka da turare da mum din manosh ta bata.

Maryam ta koma d'aki tana kwance se kuma ta tashi ta bid'e kit nata ta d'auko memori tasa a wayarta ta sake tabbatar da cewa lallai wannan shine mahaifin manosh,hawayene suka fara zuba a idanunta se taji wayanta na k'ara,koda ta duba *peach &cream* ne seta d'auka tare da share hawayenta tace hello,manosh yace apple mun tafi,tace to Allah kare nagode,yace ameen *i luv u* murmushi tayi tare da cewa *she luvs u 2* dad'i yaji yace thankyou apple,tace always *peach* wayyo Allah manosh kamar zaiyi hauka yana mirmushi ya katse wayar yatana lumshe ido,marwan yace bari in karb'eka dan naga kamar ka gaji,dariya sukayi dukkansu sannan manosh ya fizgi motar kamar zasu fire sama,marwan yace a'a mudaije a hankali kaga dukkanmu tuzuraire hhhhhh

Maryam kuwa wasu zazzafan hawayene suke zub'o mata tinda ta ajiye wayar. Tace inason sosai manosh,yanzu ya zanyi kenan? Wayarta ta d'auka ta kira uncle ibrahim bayan sun gaisa tace dam inaso miyi magane in baka cikin mutane,yace ok bari na kiraki.

Bayan ya katsene ya sake kiranta yace yes aunty ina jinki,tace ka tuna da wannan vedion dana tura maka a wayarka,yace ai devio d'aya kika tab'a turamin na wanda ya buge mahaifina ko? Hawaye ya sake zubowa a fiskarta tace eh shi,yace eh har yanzu yana wayana ai,tace bakowa bane wannan mutumin illa mahaifin manosh yah ibrahim. What! Mahaifin manosh kikace,tace eh shine na tabbatar da hakanne yau danaje gaida mahaifiyarshi yah ibrahim bazan iya b'oye makaba dannima mahaifinka mahaifinane sannan mun dad'e muna nemanshi se gashi kuma ashe shine mahaifin manosh,kukane yaci karfin maryam take ta katse wayar. Hankalin ibrahim ya tashi sosai ya rasa meyake mishi dad'i musamman dayaji maryam tana kuka,don ya dad'e dasa son maryam a ranshi tun mahaifinshi yana raye ya sanar dashi,amma se mahaifinshi yace karka damu ibrahim ka gama karatunka tukunnan maryam 'yace aguna nima zafin samun kwarin gwuiwa idan ka gama karatu ka samu aiki se inyiwa mahaifinta magana tunda amininane. Hakan yasa ibrahim ya hakura yabar abin a ranshi amma kash *muna namu Allah yana nashi* hankalin ibrahim atashe ya wuce gidansu maryam.....

.

Uncle ibrahim yana isa yayi sallama,maryam ta fito tare da amsa sallamar,tunda ganin fiskarta ya tabbatar tayi kuka. Kallonta yakeyi mai cike da kauna,yace ina mama,miryarta k'asa ba tare data kalleshiba tace tana d'aki. Ibrahim yace aunty meyasaki kuka,shuru tati ta kasa cewa komai,ya sake cewa aunty pls banaso in sake ganin hawaye a fiskarki wlh na yafewa mahaifin camtain amma saboda kece kawai wlh dabadan keba danayi k'aransa,aunty kin wuce duk yadda kike tunani aguna sannan babanki ya rik'emu kamar uba tun bayan rasuwan mahifinmu dan haka ki wantar da hankalinki kinji wlh komai ya wuce zan samu baba anjuma muyi maganan.

"Maryam ta d'ago da kanta tana kallonshi tace nagode sosai yah ibrahim,basan dame zan biyakaba a duniyannan Allah yabar zumunci. Murmushi yayi mata tare da cewa ameen aunty pls kicire komai a ranki karki nunawa captain wani canji sannan karki sanar dashi kinji,to tace dashi yace to ai seki murmushi dan fishi bai kamacekiba,dariya takeyi wanda yake kara mishi kaunarta a ranshi nan sauyin kallon da yake mata ya canja,wanda ita ita da kanta ta lura da hakan,take jikinta yayi sanyi,shi kuwa juyawa yayi ya tafi batare daya sake cewa komaiba.

Tunani sosai maryam ta shiga akan yanayin yah ibrahim tace kodai sona yakeyi to? Kai a'a da sona yakeyi aida ya dad'e da fad'a kawai dan kila dan kokarinane yasa yake sona haka amma kuma meyasa yakemin wannan kallon da manosh yake min sannan ya tafi babu sallama?

Wayanta ta d'auka ta kirashi bugu d'aua ya kayse ya kirata ta d'auka da sanyin murya tace yah ibrahim katafi babu ko sallama? Yace am sorry aunty bazan iya tsayawa inaci gaba da kallonki bane,tace todai ai semuyi sallama koh kamar dai yadda muka saba. Murmushi yayi yace tokiyi hakuri aunty nayi laifi,murmushin ta mayar mashi tace ba komai ya wuce dama shiyasa na sake kiranka. Yace tona gode aunty ina so in miki wata tambaya pls ki gayamin karkiji kunyana,tace to inaji, "you love camtain right?" Shuru tayi dan bata tab'a tunanin jin wannan tambayan daga garesaba,yace aunty kinyi shuru,tace yah ibrahim yana da wani haline mara kyau kodai kasan wani abu mara kyaune game dashi? Yace "aunty" namiki tambaya kimin tambaya,cikin sanyin murya tace yah ibrahim bazan iya b'oye maka komai a duniyannan ba "yes ina sonshi" amma wlh idan yana da wani aibu kagayamun ko kuma baba,tunda dama ai nace kayi bin ike akanshi. Ibrahim yace hakane aunty wlh bayi da wani aibu ko hali mara kyau kawai dai na tambayekine,tace tomeyasa kamin tambayan? Yace yanzu nayi laifi kenan,yace bakayiba nima ina so ka gayamin me dadilin tambayan? Yace idan muka sake had'uwa zan gayamiki yayinda nake kallon fiskarki kinji,tace toshikenan nagode,yace ok bye sannan ya katse.

Maryam dai da tunanin maganansu ta kwana a rai kuma daahi ta tashi.

Rashida ce taje gun maryam,lokacin tana zaune a gaban *computer* tana sanye da blue jeans da kuma jan top mai dogon hannu ta nad'e kanta da *light brown* gyale k'arami,rashida tace kai amma kinyi kyau a kayannan bari in miki *picture* ai kuwa maryam tayi dariya fararen hakwaranta suka bayyana rash ta dauka tare da cewa gaskya ki turawa captain wannan pic din dan yayi kyau sosai wlh. Murmushi maryam tayi tare da kab'ar wayan rash tana ganin pic din, nan suka koma kan k'aramin gadonta tana shirya books nata rashida se d'aukata takeyi,maryam tace ke ya isama mana.

Dariya rash tayi sannan suka fara hira nanne maryam take gaya mata cewa mahaifin manosh ne ya buge mahaifinta kumata gayawa yah ibrahim,hankalin rashida ya tashi sosai ta mik'e tsaye tace mahaifin manosh fa kikace,maryam tace eh wlh wlh shine kinsan jiya naje gaida mum nashi acan naganshi. Rashida tace wlh bazai yuba,ya rabani da mahaifina shikenan aahe manosh bai sami mahaifi nagari wlh tunda har zai iya yin kissa sannan kuma ya gudu mugu mara imani wlh Allah ya isa mana. Maryam tace dan kiyi hakuri rash kidena fad'a haka,rash tace ai wlh ba mutumin kirki bane tunda haka yake Allah yasa camtain karya d'auko halinsa dan wlh indai halinsu d'aya to ina tausaya miki maryam. Maryam tanata bata hakuri amma ina rash se kuka takeyi harta fara cewa to yanzu kinsan hakan tome kuke ciki da captaim maryam? Maryam tace kamar ya rash? Rash tace har yanzu kina son captain, maryam tace rash wani irin magane haka kuma pls kiyi hakuri ki nitsu pls,rash tace in nutsu,hakan ya nuna har yanzu kina tare da captain kenan maryam mahaifina fa mahaifinkine,kuma har zaki iya ci gaba da soyayya da d'ansa,lallai nagode danke mahaifin na raye shiyasa keto marwan d'inma daga yau bani bashi tunda shi abokin manosh ne koma ince amininsa dan haka kema daga yau *bani bake maryam* tana kaiwa nan ta ta fice tanata kuka sosai.

Mamakine sosai ya kama maryam dajin kalaman rash,dan tunda suka taso ko musu bai tab'a shiga tsakaninsuba kowa ya sansu kuma yasan shak'uwarsu sannan maryam tana son rash sosai fiye da sauran k'awayenta dan haka se abin ya dameta sosai, dama mamanta ta tafi angiwa dan haka ta rufe gida tabi bayan rash.

Kuka sosai rash takeyi itama mamanta bata gida dan yare suka fita da maman rash d'in sunje barkan haihuwa. Maryam tace haba rash yau har zaki iya furta cewa *bake bani* akan manosh,rash nasan ina son manosh amma wlh soyayyar da nake miki yafi wanda nakeyiwa manosh,domin shi zan iya rabuwa dashi amma ke na d'aukeki tamkar k'anwatace da muke ciki d'aya meyasa zakice haka dan Allah? idan rash jajur dan kuka tace wlh karyane maryam dakam nasan kina sona amma banda yanzu dan haka ki fita kibar mana gidanmu ki fita bana bukatan in sake ganinki dake da kowa nakima ki fita anan da k'arfi ta hank'e maryam har waje se jinta tayi ta mannu da mutum ta bayanta. Da sauri ta goge hawayen idonta tare da juyowa se sukayi ido hud'u da yah ibrahim take hawaye yaci gaba da gangarowa a fiskanta ta juya tana kallon rashida da tsoro ya gama kamata dan ganin yah ibrahim datayi.

Wucewa maryam zatayi da kukanta se yah ibrahim yayi saurin rik'o hannunta yace auntyn kiyi hakuri meya had'aku? Karon farko kenan danamiji ya rike hannu maryam bata iya cewa komaiba se kokarin fisgan hannunta takeyi agun yah ibrahim tace dan Allah ka sakeni yah ibrahim zan tafi gida,yace no aunty dan Allah ki tsaya yana rike da hannunta ya juya rai a b'ace yana kallon k'anwarshi rash yace ke meya faru,jiki na rawa ta gaya mishi,ya e shine yau da hannunki harkin iya hankad'e maryam rash? Ina ruwanki azan,yana rik'e da hannun maryam harya isa gun rash *belt* d'in jikinshi ya zaro rash ta fara kuka tare da cewa dan Allah yah ibrahim kayi hakuri wlh bazan sakeba.

Rash ta tsorata sosai dan tasan halinshi sarai, kukda dai bai tab'a dukantaba tunda take. Maryam tayi saurin shiga tsakaninsu tana hawaye tace dan Allah ya ibrahim karka dake pls,tsawa ibrahim ya dakawa maryam wanda dukkansu seda suka tsorata yace aunty ki matsa! Rash ta rike maryam sosai tana bashi hakuri. Maryam tace kayi hakuri yah ibrahim amma sedai ka dakemu dukkanmu tana kuka sosai.

Jikinshi yayi sanyi dan yadda yaga maryam take kuka haka ya sake *belt* din a k'asa rash kuwa da gudu ta fita ta wuce d'akin mamanta ta kulle da key. Maryam ma tazo zata wuce amma seya tareta,kuka takeyi tace yah ibrahim zan tafi gida,yace *aunty am sorry pls akan abinda rash tamiki*,maryam batace komaiba tace pls kaban hanya in wuce,yace sekin share hawayenki,bai jira me zataceba yasa hannunsa yana share mata,tayi saurin kawar da kanta gefe tare da buge hannunsa daga kan fiskanta,amma ina seya sake mayarwa tare da rik'e hannunta yace pls aunty ki dena kuka wlh har cikin raina nake jin kukanki sabo da yadda nake *k'aunarki tunda dad'ewa*. Da sauri maryam ta d'ago da kanta suna kallon junansu sosai har cikin ido,hakan ya sake rikitar da ibrahim sosai aise ya tsinci kanshi da fara matso da fiskarshi dedai nata da niyan kissing nata. Idanunta ta zaro tare da bigeshi gefe tayi saurin barin d'akin da gudu ta wuce gida,shi kuwa wani ajiyar zuciya ya sauke huuuuuh! tare da nadaman abinda yake son aikatawa...

.

Maryam tana komawa gida ta wuce d'akinta dama mamanta bata dawoba,ta kwanta tana kuka sakamakon tunawa da kalmomin rash agare. Dan bata tab'a zaton cewa wani abu zai shiga tsakaninsuba.

Wayartace ta fara ringing kodata duba se taga manosh ne,haka tak'i d'aunkan call d'n nashi har sau 3.

Bayan azahar ya sake kiranta seta d'auka hello,yace apple ina kiga shiga haka,tace sorry bacci nakeyi dan kaina da yake ciwo,ya kake yasu mama,yace eyyah sorry apple ya jikin naki,tace da sauki sosai,yace zanzo da yamma kinji,tace to nagode sekazo.

Dab la'asar manosh yazo abdallah yana kiran sallah,alwala yayi yayi sallah sannan suka zauna hira da abdallah inda yake tambayarshi ina marwan,makosh yace yana gun aiki,nan dai sukai ta hiransu manosh se dariya yakeyi seda aka watse sannan maryam ta fito babu ko fara'a a fiskanta.

Ta k'arasa da sallama,suka amsa sannan abdallah yace auntyn yara yanaganki haka babu ko murmushi, tace bakomai abdallah banajin dad'ine,yace sannu Allah ya baki lfy,tace ameen sannan ya kalli manosh yace toni zan tafi seka sake zuwa,manosh yace to bari na baka sako,yace to,sannan manosh ya bud'e motarshi ya fito da leda da gani kayayyaki ne a ciki yan kanti ya mik'awa abdallah. Abdallah ya karb'a yace wazan kaiwa?manosh yace nakane na baka kyauta,godiya sosai abdallah yayi yace auntyn yara ki tayani godiya,mirmushi tayi tace mungode Allah ya saka da alkhairi suka amsa da ameen sannan abdallah ya tafi.

Maryam tace ko zamu shiga cikin gidane,yace yau kuma,tace eh ko kuma muje zaure in shinfid'a maka taburma wlh bana jin dad'ine,manosh yace amma kinje hospital ne,tace banjeba dan ko su mama basu saniba,yace tomeyasa,tace babu komai,kallonta yakeyi tun daga sama har k'asa sannan ya d'auki wayarsa ya kira muh'd ya gaya masa cewa inda hali yazo girei ya duba apple nashi sannan ya katse wayar tare da cewa to muje zauren karki fad'i min anan,murmushi tayi sannan ta wuce gaba shi kuwa ya fito da sayayyan fruits daya mata da sauran abubuwan kwad'ayi yabi bayanta lokacin taje d'auko taburma da karamin carpet ta shinfid'a mishi carpet din ita kuwa ta zauna a taburman.

Sam tak'i kallon manosh dukda dai tana son ganinsa dan yau red top ne a jikinsa da black jeans se kamshi yakeyi. Shi kuwa kallonta yakeyi sosai,can dai tace meyasa ka kira muh'd ai naaha magani,shuru yayi kamar baijitaba yana ci gaba da kallonta,da taga yayi shuru seta d'ago da kai tana kallonshi suna kallon juna,murmushi tayi tace nika dena min irin wannan kallon bana so,yace tobase ki hananiba,mik'ewa tayi taje ta yanko mishi kankanan daya kawo mata dasu apple ga greves dadai sauransu tayi jerensu a tirai kamar fiskan manosh sannan taje ta ajiye mishi ta yadda zai gane fiskanshi tayi drawing. Mamaki sosai yayi yanata kallon drawing d'in danya burgeshi sosai harya bashi sha'awan ci,amma kuma bayaso ya b'ata drawing d'in,kawai setaga ya d'ako wayanshi yanata d'aukan pic din friut d'in.

Bayan ya gamane yace fiskan waye kenan wannan,tace na wanda zaisha,dariya yayi wanda ya k'ara mata sonshi azuciyarta,yace haka fiskana yake kenan? Tace eh amma dai fiskanka yafi wannan kyawun gani. Dad'i sosai yaji amma baice mata komaiba,wayansane ya fara ringing ya d'auka ok bari na fito. Kallonta yayi yace bari muh'd ya shigo kuma ki tabbata kin gayamishi abinda yake damunki kinji ko, mamaki sosai tayi har mh'd yazo kenan,tace to sanna ya fita suka shigo tare.

Muh'd yayi sallama ta amsa sannan suka zauna tace ina wuni,yace lfy lau aunty ya jiki ashe bakiji dad'i ba,tace eh amma da sauki,manosh yace ba wani sauki wlh dairewa kawai takeyi danko a gida basu saniba. Muh'd yace haba aunty pls kidena wasa da rashin lfyanki karki sawa kanki ciwo kinji,mirmushi tayi tace kainane fa dama kuma nasha paracetamol,manosh yace towayace kisha? Murmushi tayi tare da kallonshi cikin zolaya sannan ta taahi ta wuce gida. Manosh yanata binta da kallo,muh'd yace haba prince irin wannan kallo haka,manosh yace wlh bata da lfy daga ganinta daurewa kawai takeyi pls ka gwadata sosai. Muh'd yace "calm down dude" zata samu lfy insha Allah. Faro mai sanyi ta kawo musu sannan ta zauna,muh'd yace mungode amma wannan fiskan yamin kyau kamar fiskana. Dariya sukayi dukkansu,manosh yace a'a kaje can samira ta maka naka wannan fiskan nawane kuma bazaka ciba,dariya mh'd yayi tare da d'aukan inibi d'aya yasa a bakinsa yace shikenan zanen ya b'aci. Manosh yace gaskya baka kyautaba,memakon ka jira in fara sha kafin kasha,mikewa maryam tayi ta sake d'auko inibi tazo ta mayar inda mh'd ya cire sannan tace shikenan magana ya k'are.

Dariya sukayi sannan manosh ya far sha cikin nutsuwa take satar kallonshi,dan bai tab'a cin wani abu suna tareba se yau.

Muh'd yace nagode aunty gaskya abin ya burgeni nima zance samira ta dinga min. Manosh yace copy copy,murmushi sukayi sanna muh'd yace aunty meke damunki ne? Tace wlh ciwon kaine kawai,k'irjinta yana mata ciwo amma sam tana jin kunyan cewa harda k'irjinta. Muh'd yayita tambayoyinta tana bashi amsa sannan yace ok ina zuwa bari inje inzo,manosh yace akwai wani damuwane,yace no bakomai sena dawo sannan ya tafi.

"Manosh yace kin tabbata abinda kike ji kenan?"

"Tace eh kanta na kallon wani gefen"

"Manosh yace apple bana so ki b'oyemin komai imma kina jin kunyan muh'd toki gayamin tunda baya nan"

Maryam taga bazata iya b'oyewaba dan yadda take jin k'irjinta,setace da k'irjina yana min ciwo sosai.

"Kallonta yakeyi cikin damuwa,dan yana lura da yanayinta yasan tana jin ciwo tadai k'i fad'ane kawai.

"Sunanta ya kira a hankali yace apple?

   Kanta ta d'ago ta kalleshi har idonta yayi jah tace na'am tare da sunkuyar da kanta,yace se kuma inane yake miki ciwon? Tace shikenan....bata gama k'arasawaba taji cikinta ya kame kamar an soka mata wani abu,innalillahi wa'inna ilaihirraji'un taketa nanatawa a zuciyarta.

Manosh yace ya kikayi shuru,tace bakomai ina zuwa,bata jira mezaiceba ta mik'e ta wuce gida yana binta da kallo. Koda ta k'arasa gun mamanta ta wuce a d'aki ta cire doguwar himar nata ta fad'a kan gado tana cewa mama cikina ya kameni sosai yana min ciwo. Hankalin maman ya taahi sosai tayi kanta tana mata sannu tare da tofa mata addu'oi,tace bak'on ya tafine? Cikin jin ciwo take magana tare da kame cikinta tace basu tafiba suna zaure.

Mama ta rasa yadda zatayi seta d'auki wayanta ta kira baban maryam ta gaya mishi komai,shima hankalinsa a tashe ya kira number yah ibrahim yace lallai yaje gida.

.

Bada b'ata lokaciba yah ibrahim yazo a zaure sukaci karo da manosh. Su gaisa sannan yace ina maryam d'in? Manosh dabaisan komaiba yace ta shiga ciki,yah ibrahim yace kasan bata da lfy,yace eh na sani harma abokina ya dubata yanzu. Kan yah ibrahim ya d'aure seyace bari in shiga ciki dai dan yanzu babanta ya kirani yake cemin bata da lfy sosai cikinta na ciwo,a razane manosh ya mik'e yace ciki kuma,tacewa yanzu kenan ko,ibrahim yace eh sannan ya wuce ciki akabar manosh cikin damuwa sosai.

Maryam se juyi takeyi tana addu'oi,har ya ibrahim yayi sallama,mama ta fito tace bari na fito da ita sannan ta koma tasawa maryam himar,shi kuwa yah ibrahim da sauri ya kira rash a waya yace tazo yanzunnan kuma cikin shiri.

Bada b'ata lokaciba sega muhammad yazo sakamakon wayan da manosh yayi mishi. A tare sukazo da rash ta gaishesu sannan ta wuce ciki,maryam ta fara hangowa babu yadda take mama tana rik'e da ita ita maeyam bata iya ko mik'ewa tana sunkuye kuma rik'e da cikinta.

Da sauri rash ta k'arasa ta riketa sosai tana mata sannu. Hankali mama a tashe tace gaskya zan biku muje asibitin nan dan hankalina zaifi kwanciya,waya tama baban maryam,sannan ibrahim yaje ya sanar dasu manosh komai,se manosh yaba ibrahim keyn motanshi yace ya d'auki su mama a ciki shi kuma zasu tafi da muh'd. Haka kuwa akayi su manosh suka tafi shida muh'd sannan ibrahim ya bud'e musu motar, da sauri abdallah yazo dan yadda yaga mama da rashida suna rik'e da auntyn yara,baice komaiba ya karasa yace lfy mama,tace wlh maryam ce ba lfy zamuje asibiti. Subhanallah nima zan biku, ibrahim yace shiga baga to,abdallah ya shige gaba su mama kuwa suna baya suka kama hanyan jimeta.

.

Asibitin da muh'd yake aiki sukaje, aka wuce da ita kai tsaye. Ae a lokacinne manosh da muh'd suka gaida mama sannan muh'd ya wuce duba maryam.

"Yana shiga rashida ta fito ta wuce gunsu mama,shi kuwa manosh kunya sosai ya kamashi gaahi k'ananan kayane a jikinshi,nan ya kira su majid cikin k'ank'anin lokaci suka zo dukkansu ukun.

Marwan majid da muhsin sukaje suka gaida mama sannan suka gaisa da ibrahim. Rashida tana gefe ita da abdallah sannan marwan ya k'araso suka gaisa ranta a b'ace,amma seya d'auka kodan rashin lfyan maryam ne.

Muh'd ya fito su manosh suka k'arasa da sauri donjin meke damunta harda yah ibrahim d'in da abdallah. Mama da rash kuwa suna tsaye a gefe guda.

Muh'd yace *ulcer* kawai babu wani abu, kuma dole zata zauna a asibiti dan se'an k'ara mata ruwa har leda biyar. Sannan yayi mata allura yanzu dan har tayi bacci ma, ibrahim yace to mun gode kayi duk wani abunda ya dace pls yanzu medame ake buk'ata? Muh'd yace haba aiba komai wlh already nasa mata ruwan karka damu babu wani abu da ake buk'ata kudai tayamu da addu'a kawai. Godiya sosai ibrahim yayi sannan yace bari naje na sanar da mama dan hankalinta a tashe yake,muh'd yace muje inyi mata bayani.

Bayani sosai muh'd yayiwa mama tare da cewa ta kwantar da hankalinta maryam zata samu lfy insha Allah. Godiya mama tayitayi sannan ya tafi gunsu manosh.

Manosh yace zan iya ganinta,majid yace jeka ka kanga inba hakaba ai bazamu gane hankalinkaba ad'an lokaci kad'an kashi harka fita hayyacinka kamar ba sojaba, dariya sukayi baima kulasuba ya wuce d'akin tana kwance babu himar a jikinta se atamfa d'inkin doguwar riga daga sama ya bada shape amma k'asan a bud'e yake. Karon farko kenan da manosh yaga maryam babu himar ajikinta,mara ce sosai gata 'yar karama bata da jiki sam,amma k'irjinta a cike suke. Bai k'arasaba ya janyo k'ofar ya koma gunsu majid yace muje ko,dan muma mamanta damar shiga, haka sukayi musu sallama suka wuce yacewa ibrahim ya rik'e key din motarsa dan zirga zirga,amma sam ibrahim yak'i seda ya bashi key din,shi kuwa manosh ya karb'a suka tafi.

Auna tfya mama da rash suka wuce d'akin da maryam take harda ibrahim da abdallah.

Tausayin maryam ya kama rsah sosai tayi dana sanin gaya mata kallomin jiyan dukda dai tasan bashine silan rashin lfyanba amma tana k'aunar maryam a ranta sosai.

Manosh kuwa ya gayawa mum nashi da kuma miher,sannan yacewa dad nashi yana so ya bashi kyautar mota guda d'aya dan zaibawa su maryam ne dan abinda ya faru yau,da baijeba kenan se sunyita neman motan hawa. Dad d'in manosh business man ne sosai kuma yanda gidan saida motocin,sannan yana k'aunar manosh sosai,dan haka yace manosh yaje ya d'auki duk motar da yake buk'ata. Godiya sosai manosh yayi dama suna hira da abdallah sosai kuma abdallah ya gaya mishi motar da maryam take so saosai a ranta shine *307 red* dan haka ya wuce yaje ya d'auko mata red d'in kuwa guda d'ayan kenan ya rage aka rubuta sunan maryam akan takardun da komai sannan yazo dashi gida ya nunawa mum da miher sukaita murna tare da addu'oi yace bari ya watsa ruwa sesu tafi shida miher...

.

miher tayi shiga na alfarma,daidai nan lubna ta kirata a waya tana tambayanta ya maganan zuwa tambayane nasu bro manosh,nan miher take gaya mata cewa ai maryam bata da lfy tana hospital d'in su bro muh'd yanzu hakama ina jiran prince ya fitone mu tafi.

Lubna tace eyyah Allah ya bata lfy,a ranta kuwa tace Allah yasama ta mutu.

Koda wasa lubna bata gayawa miher cewa tasan maryam ba,kuma bata yiwa miher tambayoyi akan maryam d'in sam,dan gudun zargi.

Manosh ya fito cikin shigar indians da blue sari na maza yayi kyau sosai,ya mik'awa mihaer key d'in *benz* nashi yace taje zai bita a baya. Mirna sosai tayi yau bro manosh yabarta tayi driving da kanta. Tana gaba yana binta a baya da *307*din apple nashi.

*Atiku abubakar mall* suka nufa inda manosh ya kashe kud'i sosai harta flaks seda suka saya mata da cups su plate dukdai wani abu da zasu buk'ata a hospital haka mihar tayi ta d'auka, se kallonsu akeyi don yadda sukayi kyau shi kuwa captain ko dariya bayayi se amsa waya da yakeyi. Mihar tana biye dashi bayan sun biya kud'ine suka tafi tana gaba yana binta a baya har,suka isa hospital d'in.

Lokacin yah ibrahim da abdallah sun koma girei domin suyiwa maman rashida bayani kuma tayi abinci dasu. Manosh yacewa miher ta shiga idan maman maryam bata d'akin tozai shigo,ai kuwa seta shiga da sallama da kuma kayayyaki sosai a hannunta har rashida ta tayata da wasu,sannan ta sake komawa ta kwaso sauran nanma seda rash ta tayata sannan suka gaisa maryam tana bacci har yanzu,mihar tace yamai jiki,rash tace da sauki wlh,tace Allah ya sauwaka mama fa? Tace mama sun fita da baba amma inaga sun kusa dawowa.

Da sauri mihar ta fita taje ta sanar da bro manosh,kafin su shigo maryam ta farka tana cewa mama zansha ruwa,dama yah ibrahim yad'an sayo abin tab'awa kad'an dan haka rash ta mik'a mata ruwan tasha sosai sannan ta koma ta kwanta rash tana mata sannu da jiki,tace yawwa.

.

Manosh da mihar suka shigo da sallama,kunya sosai maryam taji tace rash mik'amin himar d'ina,da sauri tad'an rataye matashi a k'irjinta sannan suka k'araso.

Rash suka gaisa da manosh yace ya mai jikin,tace da sauki yace to Allah ya bata lfy tace ameen sannan rash tace mihar mud'an basu guri ko,tare suka tashi suka fita sannan yazo ya zauna akan kujeran da yake kusa da gadonta yana kallonta. Kunya sosai taji ta dai daure ta tashi ta zauna tare da gyara rufe jikinta tace ina wuni,kallonta kakeyi tare dajin k'aunarta yana ratsashi yace lfy apple ya jiki,tace da sauk'i.

Yace wato dama kina jin jiki shine kika cemin kaine yake miki ciwo ko,mirmushi tayi tace amma ai da sauki yanzu. Yace drip d'in harya k'are ne? Tace eh yace se bayan isha za'a samin wani,yace ok Allah ya baki lfy apple,tace ameen tare dajin kunyanshi sosai danba himar a jikinta dukda dai ta rufe jikinta amma yana iya hango kananan kitson dake kanta gata da bak'in gashi.

Ya maida kallonsa kan wayanshi yace ina wayanki,nan ta mik'a mishi ya karb'a ba tare daya kalletaba ya shiga galary, pic d'in da rashida tayi mata da kayan daya saya matane ya gani pic d'in sun mishi kyau sosai atake ya turasu zuwa wayanshi sannan yasa mata credit na 3k seya mik'a mata yace kimin kyau a hotonnan ya nuna mata wayanshi.

Murmushi tayi tace nagode meyasa ka tura baka sanar daniba,yace tokiyi hakuri bazan sakeba. Batace komaiba se kuma tace nagodefa da d'awainiya Allah ya saka da alkhairi,shuru yayi kamar baiji metaceba yana ta dannan wayanshi.

   Ita kuwa se kallonshi takeyi dan yadda yayi kyau sosai. Batate daya kalletaba yace apple nifa bana so ayita kallona,kinya sosai taji dan tasan bai kalletaba,tace nifa ban kallekaba,yace kin kalleni mana aina ganki,tace ta ina kenan yace ta idona mana, dariya tayi tana ci gaba da kallonshi se wayanshi yayi k'ara ya d'auka yadai miher,tace bro mum da dad nata sun dawo dayake sunsan kana ciki se basu shigoba,yace ok tnx sannan ya katse wayar tate da mik'ewa tsaye yana kallonta. Itama shi take kallo tace ina zakaje,yace zan tafi in barki ki huta mana,kawai jin bakinta tayi tace mishi pls karka tafi yanzu,yace meyasa bakya so in tafi,tace haka kawai,ka zauna kamin hira.

Ba musu ya koma ya zauna yaci gaba da danna wayanshi yana magana batare daya kalleta yace su mama sun dawone kuma suna waje shiyasa nake so in tafi dama ina son inga baba. Tace to ai bakomai suma bazasu shigoba inhar sunsan kana ciki,yace eh hakanne yasa zan tafi ai. Yanayin manosh yana burgeta sosai da wasu irin abubuwansa,sam seyaso kallonta kafin ya kalletan,sannan kamar bakoda yaushe yake son magana ba. Shuru tayi tanata kallonshi sosai tana yaba kyansa a ranta,seyace tunanin me kikeyi apple,shuru tayi,yace pls ki dinga cin abinci sosai sannan ki dena cin yaji dan abdallah yacemin kina cin yaji sosai. Mamaki tayi sosai,tace yaushe kukayi hira dashi haka,yace ina ruwanki,tayi murmushi tace to zan dena insha Allah tunda yana nemar yimin illa. Manosh ya mik'e yace apple am goying amma zanyi missing naki wlh yau bazamuyi hiraba kenan tunda mama tananan bazan iya kiran wayankiba amma zan dawo safe kinji, tace to nagode sosai. Yace Allah ya baki lfy tace ameen sannan ya nufi kofar fita,harzai bud'e kofa tace eeem....tsayawa yayi cak tare da juyowa yace yes akwai wani abu ne,mirmushi ta mishi tace bakomai seda safe,shima murmushin ya mata tare da cewa idan akwai ki gayamin,tace akwai abinda nake so amma zanyi maka texsn,yace ok ina jira sannan ya fita.

.

Manosh ya gaida mama cikin girmamawa sannan ya gaida da baba tare da cewa dama yana son magana dashi,daidai nan yah ibrahim yazo da abinci sosai a kwando suka gaisa sannan ya wuce.

Miher da rash suka shiga da mama sega yah ibrahim,miher ta gaishesa sannan ya ajiye abincin tare da cewa aunty ya jikin dai,tace da sauki sosai,yace to Allah ya baki lfy tace ameen sannan ya fita gunsu baba inda suke magana da manosh. Godiya sosai baba ya dingayi tare da cewa ibrahim kagafa mota ya kawowa maryam wannan kyauta yayi girma dewa wlh dukda dai kace mahaifinkane yayi mana mun gode sosai,nanma ibrahim yayi godiya sosai,sannan yaje ya kira mama itama baba ya gaya mata godiya,sosai sukayi wanda baizai misaltuba,manosh yaji dad'i sosai a ranshi sannan ibrahim ya rakashi hargun motarshi sukayi sallama,sannan ya kira miher a waya,nan ta musu sallama tace zasu da mum nata da safe,rash ce ta rakata har wajen mota sannan suka tafi.

Koda baba ya gayawa maryam kyautar da manosh yayi mata da taimakon babanshi mamaki sosai tayi,babanta ya nuna mata takardun motan dukda sunanta a jiki,dan kunya bata iya cewa komaiba anata tayata murna sannan baba yace zasu tafi shida ibrahim seya tuk'a motar maryam d'in shi kuwa baba yahau nashi suka tafi ibrahim yanata mamaki.

Manosh yayiwa maryam texs kamar haka

_am still waiting my apple_

_akan abunda kike so_

Koda maryam ta karanta setaji a yanzu kam bazata iya cewa komai se tace

_Allah ya saka da alkhairi_

_wannan kyauta yayi girma dewa my peach banajin zan iya sake tambayar wani abu_

Bayan manosh ya karantane seya ce

_pls apple kigayamin indai kina so inyi farin ciki dan ina k'aunarki sosai apple nd i can do anything just for you sweetheart_

dad'i sosai maryam taji sannan ta sake tura mishi

_ba wani abu bane illa flower_ _i love you nd i love flowers so verry much peach_

.

Koda ya gama karantawa murmushi yayi yace indai wannan ne sekin gaji dashi dan lambunsa guda zanyi a gidanmu my apple,da haka yayi bacci.

Washe gari da safe ya shirya seda ya tambayi maryam tace su baba sunzo sun koma,ita da mama da rash ne,yace ok ganinan zuwa tace to sekazo.

Koda manosh yazo cikin kakin sojojinshi yake se kallonshi yakeyi,office muh'd ya wuce yace yadai abokina ya wifey nane da jiki,muh'd uace tofa tu ba'a baka ba,kar dai harka shirya kenan se tafya,manosh yace wlh kuwa driver yana waje daga nan airport zamu wuce,muh'd yace ok jeka ka fito se in rakaka,manosh ya wuce d'akin da sallama dama mama ta fita tunda maryam tace manosh yazo taje can d'aya d'akin gun wasu matan da y'arsu ba lfy suma.

Manosh ya shigo kenan rash ta mik'e tare da gaisheshi sannan ta fita,ita kuwa maryam flowers d'in kawai take bi da kallo da kuma yadda yayi kyau a kakin sojojin. Akan kujeran ya zauna suka gaisa seya ajiye mata flowern a gefenta,da sauri ta d'auka tana murmushi tare da shinshinawa taji wani k'amshi mai dad'i wanda yasa ta limshe idanunta tace _thankyou so much captain_,murmishi yayi yana kallonta yadda take ta murna da ganin flowers d'in,itama shi take kallo yare da d'auko *ring*mai kyau na maza ta mik'a mishi batare datace komaiba. Hannun yasa ya karb'a tare da cewa thankyou apple naji dad'i sosai,yasa a yatsan hannunshi tare da pecking d'in yatsan nashi yana mata murmushi tare da cewa ya jikin,tace naji sauk'i sosai wlh,manosh yace alhamdulillah zuwa gobe za'a sallameku insha Allah nizanyi tfy kuma zankai 1week kafin in dawo su dad zasuje gun baba dan asa mana rana kinji?

Sam maryam bataso tfyan manosh ba haka kurun tad'an canja fiska,shi kanshi ya lura da hakan seya sauya muryanshi yace "apple r u aokey?" Tace yes am fine ina zakaje? Yace zanje kaduna ne,karki damu kinji zan dawo insha Allah addu'arki nake buk'ata apple,kallonshi takeyi tare da tausayin kanta tace Allah ya kare min kai,yace ameen suna kallon junansu ciki so sannan tayi saurin kawar da kanta gefe tana kallon flower daya kawo mata,manosh bazai iya jurewaba dan haka ya mik'e tare da cewa nizan tafi apple ga wannan,ya ajiye mata kud'i a gefen gadonta sannan ya nufi kofar fita. Har yakai gun k'ofan kanta na kallon flowern,seya juyo yana kallonta sam taqi kallonsa har ya gama kallonta sannan yaja k'ofa ya fita harzai kulle kenan seta d'aga kanta suka had'a ido cikin tausayin junansu yace _i love you so much apple_

_tace i love you too manosh_

Harda d'an kwalla a idonta sannan yaja kofar da sauri ya rufe,ita kuwa hawayene suka zubo mata kona menen oho....

.

Hankalin maman maryam ya kasa kwanciya,seta kira baban maryam a waya tana tambayanshi ko maryam ta iso? Baba yace a'a bata isoba,hankalinta ya sake tashi tace malam yaci ace ta iso ai,shi kanshi hankalinsa ba'a kwance yakeba,amma seyayita kwantar mata da hankali da daddad'an kalamai yana cewa kinsan fa maryam da taimako da kuma tausayi,zaiyu wani abinne ya tsaida ita a hanya amma bari nabi sawunta.

Mahaifin maryam ya rufe shop nashi yabi hanya ai ko seyaga almajirai sunata d'iban abinci a k'asa kuma ya tabbatar da cewa wannan kulan abincinshine. Wayansa ya d'auka ya kira matarshi ya tambayeta cewa me kika dafa minne yau,tace shinkafa da miyace mai had'e da wake,katse wayan yayi ya kama fad'in *innalillahi wa'inna ilaihirraji'un* tare da duduba guraren kozai hango maryam amma sam se *rivom* nata daya hango wanda shida kanshi ya sayo matashi.

Hankalinshi ya tashi sosai,ya kira number'n maryam yanata ringing amma ba'a d'aukaba har kusan sau biyar. Haka ya wuce gida a rud'e inda ya had'u da yah ibrahim da abokanshi suka gaisheshi ya amsa amma suna ganinshi sunan akwai abinda ke faruwa,ibrahim yace baba lfy kuwa,yace lfy lau ka biyoni gida.

Haka suka juya abokanshi suna tsaye daga waje su kuwa suka wuce gida. Mama tana jin sallama ta fito tare da cewa malam lfy,nan ibrahim ya gaisheta sannan baba ya gaya musu duk abinda ya gani a hanya sannan yayita kiran number'n maryam shuru. Addu'a suketayi dukkansu tare da tunanin to ina maryam take?

Ibrahim ya kira rashida da sameera a waya suka ce mishi sam maryam bata zoba,ya sake kiran zahida da amina suma sukace bata zoba,nan ya wuce gidan hajiya iya nanma batanan,koda hajiya iya taji lbrn hankalinta a tashe harda kukanta dan yadda take son maryam a ranta.

Nan tayi lullub'i ta wuce gidansu maryam inda mahaifiyarta taketa addu'a tare da kwalla a idonta. Duk wanda yaji yasan ba lfy bane domin maryam bata tab'a yin hakaba,ga kuma rivom da mahaifinta ya gani agun yasan lallai akwai matsala sosai.

Bayan anyi sallan azahar ne mahaifin maryam yayi bayani a masallahi akan a tayasu da addu'a. Duk wanda yaji seyayi addu'a dan base na gaya muku daliliba.

     Cikin k'ank'anin lokaci magana ya baza ko ina a garin girei. Ibrahim ya kira manosh a waya amma yanata ringing bai d'agaba,hakan yasa ya kira number'n marwan bugu d'aya ya d'auka bayan sun gaisane yake ce mishi manosh fa,domin yayita kiranshi amma bai d'aukaba,marwan yace wlh ni ina office ne maybe baya kusane. Ibrahim yace ok dama wlh maryam ce aketa nema tun d'azu taje kaiwa mahaifinta abinci har yanzu shuru babu ita babu lbr,ahanya akaga kulan abincin a zubar a k'asa sannan an tsinci rivom d'inta har haryanzu babu wani lbr.

  *innalillahi wa'inna ilaihirraji'un* marwan yaketa nanatawa tare da mik'ewa yayi gun manajer'nsu bayan sunyi magana marwan ya d'auki motarsa se gida.

Miher ya gani a tsakar gida zata fita,nan dai suka gaisa yace ina prince,tace yana bacci bayajin dad'i kanshi yana ciwo. Marwan yace ok sannan ya wuce d'akin miher tanata binshi da kallo dayya taganshi tasan ba lfy,haka kawai taji ta fasa tfyan dan tana so taji menene da sauri tabi bayan marwan ta lab'e daga bakin kofa inda taji marwan yana cewa "dude" "dude" ahankali manosh ya bud'e ido yana mamakin ganin marwan a wannan lokacin. Marwan yace sorry na tashe ya jikin,yace alhamdulillah lfy? Marwan yace ka kashe wayar kane,manosh yace no a silent nasa dan ind'anyi bacci wlh ya akayi,marwan yace "dude" akwai matsala baga'a apple ba tun 11:40am yanzu gashi har 3:20pm,kuma duk inda ake tunanin tana zuwa anje bata nan sannan........da sauri manosh ya mik'e tare da d'aukan wayanshi yaga miss call din baban maryam dana ibrahim dadai wasu daban,number'n apple ya kira yanata ringing amma sam bata d'agawa. Kamar zaiyi kuka ya sake kiran wayan yanata cewa "pls apple pick d call okey" where are you apple,wurgi yayi da wayan seda screen d'inshi ya pashe ya shige toilet da wuri,shi kuwa marwan ya d'auko wayan amma ina ba'a ganin komai taci screen.

Manosh ya fito ya shirya suka fita ko mum nashi bai sallamaba,daya ga miher yace miher maryam ta kiraki?miher da jikinta yayi,sanyi tace a'a,yace kiyita kiran numbern ta sannan ki gayawa mum cewa ba'aga maryamba nina fita.

Hawaye miher ta fara dan yadda taga bro nata ya hargitse a lokaci d'aya.

Basu wuce ko inaba se girei,inda suka isa har parlon mahaifinta yana zaune da mutanen unguwa,sukayi sallama tare da gaisuwa sannan manosh ya farayiwa baba tambayoyi kamar ba surukinsaba,shi kanshi baba yasan manosh a rikice yake,manosh yana gama jin komai ya musu sallama suka wuce gurin yayita dube dube amma baiga komaima. Abokinsa *faruq* ya kira wanda yake aiki a *mtn office* yace faruq matar da zaura an d'auketa wayanta a kunne yake inaso kabin min line nata pls insan a ina take da sauri dan Allah. Da sauri faruq ya fara neman line na maryam amma baiga komaiba da tana inda babu netwrk,nan ya sake duba kira na k'arshe daya shiga wayarta ba'a d'aukaba yaga lokacin tana *gurore* sannan yanzu baya iya ganin inda suke. Faruq ya kira manosh yace captain d'azu kaine ka kirata last kuma ya shiga lokacin tana gurore. "Whats! Gurore fa kace faruq? Faruq yace tabbas captain karka damu zanci gaba dabin line d'in inga suna inda ba netwrk ne.

.

Katse wayan manosh yayi yace ina tausaya musu wlh tunban kamasu kowaye yayi miki wannan aikin "he will pay for it wlh" dan bazan barshiba. Marwan yace muje gida mu shirya manosh,manosh yace no karka damu ka koma kawai yanzu motarmu zaizo zamu bi bayansu,marwan yace ok "dude but pls becarefull,daidai nan motan sojojin ya iso wani ya fito daga gaba manosh ya shiga sannan shi ya shiga baya suka tafi,sega majid yazo suka wuce girei gun iyayen maryam,koda marwan ya gaya musu inda maryam take mamaki sosai sukayi,mahaifiyarta kuwa kuka sosai takeyi,makota sunata bata hakuri.

Abdallah yana zaune a masallaci tare da samari da sauran yara anata karatun qur'an amma abdallah hawayene kawai yakebin fiskanshi.

K'awayentama duk sunzo sunata kuka

Manosh ya kira muhsin yace pls zan tura maka pic na apple kai gidan TV da radio dake adamawa dukka duk wanda yaba da wani bayani akwai babban kyauta ageshi,mihsin yace ok "dude" pls ka kwantar da hankalinka insha Allah za'a sameta cikin k'oshin lfy,manosh yace Allah ya amshi addu'anmu tnx "dude" sannan ya katse wayan.

Maryam ta fara bud'e idanunta tare dayin addu'a harta gama bud'esu dukka tana k'arewa d'akin da take kallo. Katiface kawai a d'akin da wani zanin gado se tsami yakeyi ga akwati da tarin taba wiwi dasu totolin sune kawai a wannan d'akin. Nan danan taji gabanta ya fad'i tanata addu'a tare da mik'ewa ta murd'a kofan amma setaji a kulle yake,nan ta tuna da wayanta datasashi cikin pants nata tun lokacin da suka bige mata abincin babanta. Da sauri tasa hannunta akan pants d'in cikin ikon Allah taji har yanzu wayan yana jikinta,hamdala tayiwa Allah sannan ta ciroshi da wuri dama a silent yake,kodata duba missed calls babu adadi a cikin,da sauri ta kashe wayan gabad'aya dan ganin 7:00pm ne ko sallan azahar batayiba. Kofan data gani ta bud'e taga toilet ne amma babu kyan gani sam a cike yake da k'azanta,hancinta ta d'aure da d'ankwalinta ta shiga da yake akwai ruwa ga kuma morning fresh da izal nan da nan ta wanke shi tas sannan tayi alwala wayanta yana cikin pants nata ta shinfid'a d'ankwalinta tayita biyan sallolinta.

Tana cikin yin sallanne se taji ana bud'e kofan tare da shigowa. Daga jin muryanshi kasan d'an giyane,yana cewa daga zuwanki har kin fara mana kashi ko kashi kin bud'emu da wari kota ina,koda yake shinkafa da wake kuka dafa a gidanku yau shiyasa,ga abinci nan idan kin gama sallan sekici,bayan ya ajiyene ya d'auki kwalin sigari sannan ya tafi.

Bayan maryam ta idar da sallolintane tare,dayin addu'in neman tsari sannan ta dubi abincin daga gani a resturant aka sayo,amma sam bata ciba seta tashi tasa sakatan d'adkin ta ciki sannan tashiga toilet ta kunna wayanta tare da kiran number'n mahaifinta bai d'aukaba dan yana tlband'aki,dan haka ta sake kiran mahaifiyarta bugu d'aya ta d'auka tare da cewa maryam,maryam tana magana a hankali tace na'am mama sannan,ta fara kuka tana cewa mama ya kuke ku kwantar da hankalinku ina halin lfy amma bansan a ina nakeba...bata k'arasaba taga call d'in manosh,tace mama zan sake kiranki bari inyi magana da manosh,to maryam Allah ya kareki zan sake kiranki bayan kunyi wayan kiyi k'ok'ari kozaki gane inda kike dan azo a taimaka miki su waye suka d'aukeki? Maryam tace wlh mama har yanzu bansan komaiba ina kullene a wani d'aki banga kowaba har yanzu. *innalillahi wa'inna ilaihir raji'un*suketa nanatawa ita da mamanta suna hawaye amma ita maryam daurewa takeyi kar ajita tana waya azo a karb'e.

Banyan maryam sun gama hira da mamane se call d'in manosh ya shigo. Da sauri ta d'auka tare da cewa hello peach,wani sanyi yaji har cikin ranshi yace apple ina fata basu miki komaiba,cikin muryan kuka tace eh bakomai amma ina jin tsoro sosai dan ga dukkan alamu mutanen bana garibane domin kayan shaye shaye ne cike a d'akin kota ina peach,hankalin manosh ya sake tashi sosai yace ki b'oye wayan apple zan kiraki anjuma i love you aunt ki kula da kanki pls zanyi k'ok'arin gano inda kike kinji? Ok Allah ya taimaka peach bansan inda nakeba bare in gaya maka,pls aunt ki dena kuka "i will soon come to you" nasan inda kike already,ina nake pls ka gayamin,calm down apple kina *numan* ne nima yanzu haka muna numan d'in zanzo inda kike yanzu ki b'oye wayanki zan kiraki anjuma okey? Ok thankyou,i luv apple,i luv u too byeee...

Read More

Share this

WhatsApp

ANTIN YARA Page 11-20

 December 31, 2017     ANTIN YARA 1-END     No comments   

  1. ANTIN YARA Page 11-20

.

Auntyn yarane take koya musu karatu a cikin gidansu dan har black bord babanta ya mata dan koyar da yara,gidan nasu d'an daidaine ba wani gidan masu hali bane,amma dai koda yaushe gidan tass yake. Tsakar gidan flour ne na silinti se'a shinfid'a katuwar taburma ana karatu.

Marwan ne a hanya zuwa girei duba abokinsa da bayaida lfy,ya kira manosh a waya amma yayita ringing bai d'aukaba. Bayan yaje sund'an tab'a hirane se yayi mishi sallama ya kama hanyan koma,kiran salla yaji muryan k'aramin yaro nan danan imani ya k'ara ratsa marwan yace kai bari dai na k'arasa kawai nayi la'asar tunda an kira. Har gun masallacin ya isa ya paka motarshi ta gefe seya hango wani yara,ya k'ara gun masallacin yayimasa sallama yaron ya amsa tare da cewa salla zakayi,marwan yace eh wanene ya kira sallah yanzu,yaron yace nine,marwan yace masha Allah amma kana da murya mai dad'i menene sunanka,yace sunana ABDALLAH,marwan yace suna mai dad'i gaskya inaso mu kulla abota dakai,abdallah yace to shikenan ya sunanka,yace marwan,abdallah yace kaima sunanka da dad'i ga buta kayi alwala a nan girei kake,yace a'a ina jimetane,abdallah yace ayyah nikam anan girei nake kagama gidanmu can ba nisa,marwan yace to ashe zan dinga zuwa kana koyamin k'ira'a,dariya abdallah yayi yace sedai kaje gun Auntyn yara ta koya maka itace malamata,yace waye kuma Auntyn yara,abdallah yace itace malamata kokuma ince malamar yaran unguwannan harma dana nesa.

Marwan yace bari dai muyi sallah ko semuyi hira,yace to sega yara sun fito daga gidansu maryam mata sun wuce gida maza kuma sun nufi masallaci. Kowannen sallama yayiwa 'yan masallacin sanan suka hauyin alwala,marwan yana ta ganinsu abun ya burgeshi sosai.

   "Bayan an idar ne marwan yace da abdal muje can muyi hira se in tafi. Bayan sun k'arasane yace ina jinka kagani na mijine kuma babba kanaga auntyn yaran zata koya min karatun, yace a'a kam kayi girma sedai in zaka dinga zuwa masallacinnan daga magrib zuwa isha kullum ana karatu da kuma litattafai masu yawa. Dad'in hirannasu sosai marwan yakeji yace to yaran can da suka fito daga gidancan fa kodai koyarwa ake acan,yace eh auntyn yara ce mai koyarwa bayan azahar zuwa la'asar,biyanta akeyi,abdallah yace a'a fisabilillah dai ai auntyn yara kowa natane kuma kowa ya santa babba da yaro babu wanda zai iya gaya maka halinta don ta cika goma cip cip. Dariya sosai marwan yayi yace matar aurece,abdallah yace a'a budurwace kuma kuma kasan me,marwan yace a'a,abdallah yace auntyn yara macece mai tarin ilimin addini dana boko gata da son mutane sam bata da kyamar d'an adam aduk yadda ta ganshi,kuma tana son taimakon dan adam,gata kyakkyawa sosai amma kuma 'yar karamace.

     Dariya sosai marwan yayi yace kai abdallah duk ita kad'ai kodai ka kara da nakane,yace wlh da gaske ko inkirata ku gaisa ne,marwan yace a'a kace mata me?abdallah yace ince mata tazo abokina yana so su gaisa,marwan yace zata fito,yace eh zata fito bari inje.

.

Maryam tana sanye da aldoguwar riga jah ta nad'a gyalen akanta tana k'okarin fitowa,se abdallah yayi sallama ta amsa tare da cewa abdalla rashida fa ta shirya kuwa,abdallah yace wlh ban saniba zaku fitane,tace eh zamuje jimeta duba zahida ba lfy,yace to muje dama gunki nazo zaku gaisa da abokina. Mamaki ya kama maryam tace aboki kuma,yace eh,tace to muje se suka fito a tare.

Marwan ya zubawa budurwan kallo har suka k'araso tayi mishi sallama ya amsa sannan suka gaisa,tace to abdallah mun gaisa nizan wuce,abdllah yace to ai shima jimeta zaije abokina ka sauketa dan Allah. Marwan yace tobakomai abokina auntyn yara muje,batayi mamakin jin sunata a bakin marwanba,se tace a'a wlh da wata k'awata zamu tafi yanzuma gidansu zanbi kafin mu wuce,abdallah yace abokina yayatace bari naje na kirata yana juyawa sema ga rashidan tahowa,yace kama ganta,murmushi maryam tayi tace daga yin aboki se kuma a d'aura mishi nauyi,abdallah yace to ai hanyanku d'aya,marwan yace sosai kuwa kuma ai zan samu lada ko,abdallah yace kwarai lokacin rashida ta iso suka gaisa sannan abdallah yayi mishi sallama har ya juy se kuma yace abokina bani numbern wayanka,marwan yana fad'a mishi shi kuwa yana sawa a wayansa sannan yace nagode sena kiraka,marwan yace tonagode sena sake zuwa.

Rashida ta kaftawa maryam ido akan ta zauna a gaba,badan tasoba hakata zauna ita kuma rashida tana baya suka tafi. Koda suka fara tfy babu wanda yayi magana acikinsu,se marwan yace auntyn yara ina zakuje a cikin jimeta,tace gurin NTA ,yace ok gaskya abdallah yarone mai hankali yaron ya shiga raina sosai wlh,maryam tace mungode,yace yace inzo zaki dinga koyamin karatu,tayi murmushi tace toba damuwa seka zo,marwan ya d'auki wayanshi yace hello Majid yane,majid yace ka dawone,yace na kusa isowa dai,yace ok idan ka shigo kamin waya,marwan yace ok sannan ya katse wayan.

.

Babu wanda ya k'ara cewa komai har suka iso har gidan,sannan suka fito tare da cewa mun gode fa,yace bakomai wlh kozan dawo in maidakune,maryam tace a'a za'a mai damu mungode sosai,yace to shikenan nima na gode.

Har seda suka shige gidan sannan yabar gurin yanata yaba kyau da nutsuwan maryam da kuma halaiyarta da abdallah ya gaya mishi.

Hira sosai sukayi da zahida sunata nishad'i gwanin sha'awa,zahida tace samira tacemin sunje mubi ko,maryam tace eh wlh se gobe zasu dawo, zahida tace ku tashi muje YAKUBU SHOPPING LPAZA zan sayi always da kuma kayan ado sun k'are,rashida tace ashe dai kin warke to muje kar muyi dare.

"Shopping sukayi dukkansu d'an daidai sedai maryam tayiwa yaranta tsaraba. Harsunzo fita se maryam taga key wata ya fad'i daga cikin bag nata batare data saniba, da sauri ta d'auka ta bita hargun motar k'irar HENESI tace 'yar'uwa kin yarda key d'inki,yarinyar ta juya suka had'a ido ta karb'a tare da cewa ayya nagode sosai kuma kinga keyn motatace wlh bansan ya fad'iba nagode sosai,maryam tace karkimin godiya 'yar'uwa inaso kema ki taimaki mutane uku a rayuwarki sannan suma kice su taimaki wasu ukun,murmushi tayi tace to shikenan ya sunanki,tace sunana maryam,tace eyyah ni kuma sunana LUBNA,tace ok sannu lubna se anjuma,lubna tace dan Allah bani number ki mana,nan taba maryam wayanta tasa mata number sannan tayi flashin,maryam tace zanyi saving lubna ko,lubna tace eh nagode sannan ta wuce gunsu zahida suka tafi.

.

maryam basu koma gidansu zahida dan gudun kar dare yayi musu daga nan sukayi sallama har suna k'ok'arin tare mota sega drivern manosh yayi parking tare da fitowa suka gaisa se yace oga ne yace inzo in maidaku gida. Murmushi maryam tayi tace to mungode,har zata bud'e gaba seyace no madam ku zauna a baya bakomai,batasoba amma haka suka zauna ya kaisu har gida sannan suka mishi godiya.

Marwan ne ya kira abdallah a waya suna hira yake tambayarshi cewa auntyn yara tana da saurayine? Abdallah yace eh akwai dai masu sonta dewa amma babu wanda take tsayawa dashi gaskya,meyasa to,yace wlh ban saniba nidai ban tab'a ganin tana hira da waniba a matsayin saurayi kana sontane? Marwan yace aboki kashe wayan zan kiraka kaji,abdallah yace to tare da kashewa.

"Marwan ya d'auki call d'in manosh yace captain busy busy nakiraka d'azu dan naje girei dama in tambayeka akan apple ne kuma inje mu gaisa se kuma baka d'aukaba. Manosh yace wlh ka bari kawai aikin namu ne se'a hankali harka dawo kenan,eh tun d'azuma,manosh yace ai kuwa gidansu ba b'oyayye bane a girei sunanta maryam amma amfi saninta da auntyn yara. K'irjin marwan ya buga yace auntyn yara,manosh yace eh wlh tanada son yarane shiyasa ake kiranta da hakan. Marwan yace ok sedai inka dawo semuje kawai,yace to shikenan sannan sukaci gaba da hiransu.

Bayan sun gamane ya sake kiran abdallah yace abdallah kabar wannan maganan auntyn yaran kaji,abdallah yace meyasa,marwan ya bashi lbr tas akan maryam da manosh abokinsa ko kuma ince amininsa. Abdallah baiji dad'iba dan ayau kawai amma se yaji yana son marwan kuma yanaso su kasance tare da auntyn yara. Marwan yace ya kayi shuru,yace bakomai wlh naso had'aka da aintyn yara abokina kana da kirki sosai,marwan yayi murmushi yace karka damu abokina shiyafi dacewa da auntyn yara danshi bai tab'a furtawa mace kalmar soba se akanta,ni kuwa nayi sosayya abaya har an gama komai da komai na auranmu ana saura 2weeks tayi zazzab'i na kwana d'aya shikenan ta tafi ta barni,tun lokacin ban kara furtawa wata mace kalmar soba shekara guda kenan. Lbrn yabawa abdallah tausayi yace Allah ya jikanta da rahama,yace ameen. Abdallah yace amma abokina dan Allah in tambayeka mana,marwan yace ina jinka,abdallah yace kana son auntyn yara? Marwan yace eh shiyasama na kiraka dan inji ko an mata miji,to ashe itace aminina yake bamu lbrnta kaga gara danyi shuru dan haka maganar ya zama sirri a tsakaninmu kuma kagayawa auntyn yara koda mun sake had'uwa wataran karta nuna mun tab'a had'uwa kaji? Abdallah yace Allah sarki abokina insha Allah zan gaya mata kasan me,yace a'a,yace da har ina tunani idan airenku ya tashi da auntyn yara zakayi mana walima namu na MAZA wanda zanyi karatu sosai dan yadda nake son auntyn yara kuma k'awar yayat ce. Dariya sosai marwan yayi yace to ai yanzuma bai b'aciba za'ayi insha Allah ka zauna cikin shiri kawai zan gayawa abokina ayi mana waliman mazan kaji,dad'i abdallah yaji yace wlh kana da kirki nagode,marwan yace nima na gode seda safe.

.

Maryam tana kwance a d'akinta abdallah ya kirata ya gaya mata komai. Mamaki tayi sosai tace eyyah dama shine abokinsu d'ayan kenan da suka gayamin bai samu zuwaba, abdallah yace eh shine,tace bakomai abdallah nagode kaji ka gaisheshi,yace zaiji sannan tace yau dai barita kira manosh.

"Ringing d'aya ya d'auka tare da cewa slm aunt,yadda yake kiranta yana mata dad'i sosai ta amsa wslm ina wuni,yace lfy sannan ya katse ya sake kiranta. Ta d'auka tana murmushi tace ya aiki,yace alhamdulillah yasu mama,tace lfyansu lau min godefa kasa an dawo damu gida,yace bana son godiyanki aunt,meyasa bakicemin zaki fitaba,tace bakomai,yace to daga yau idan zakije wani wuri kidinga gayamin pls,tace to shikenan,yace me kokeyi aunt,bakomai,yace zakiyi bacci kenan,tace eh,yace bazaki min hiraba,mirmushi tayi tace name kenan,yace ina kikaje yau,tace munje duba k'awatace zahida bata da lfy,yace eyyah sorry Allah ya bata lfy ta ina take a jimeta,nan dai ta mishi kwatance yace ok nasan gurin ai akwai wani abokin dad nawa acan,tace eyyah,yace daganan kuma se kukayi ina,tace YAKUBU SHOPPING PLAZA,yace me kika saya kuma dawa kuka had'u mutane nawa suka tsaidake? Dariya tayi yana mirmushi yace "yes tell me" tace babu wanda ya tsaidamu sannan mun had'u da wata sunanta lubna, uace lubna? Tace eh nan dai ta bashi lbrn,yace ok akwai wata lubna dana sanine k'anwan marwan abokina da bai samu zuwaba ita k'awar miher sista nace shiyasa na sake tambayanki,tace eyyah tama bani number"nta. Yace hakan yana da kyau ai Allah yasa ita ce,tace ameen.

Sunanta ya sake kira aunt,tace na'am,yace kin iya amsawa da NA'AM d'innan kamar ke kika k'irk'iri kalmar,dariya tayi sannan yace me burinki na gaba aunt,shuru tayi batace komaiba,yace tambayarki nakeyi fa,tace karatu,yace ehen seme,shuru tayi seyace aure,tace uhm,dariya yayi yace mezai hana kiyi auren sekiyi karatun a d'akin mijinki,kasa cewa komai tayi dan kinya,yace aunt bakice komaiba,tace tome zance,yace kice eh zanyi aure se incigaba da karatuna,dariya tayi sosai shima ya tayata,tace hmm,yace "whats is hmm?' Tace bakomai, yace aunt ki bari muyi aure sekiyi karatu kinji inaga hakan zaifi koh,batace komaiba,yace kokinaga bazan yadda kiyi karatubane,sisterna miher tana karatu 100 level kima majid ne zai aureta amma dole tayi karatu dokan dana kafawa majid kenan kuma ya amince,so kinga bakida matsala dani indai akan karatune aunt. Dad'i sosai taji tace to zanyi tunani akai,yace ok my apple kiyi tinani tare da shawara "i will be waiting okay?"tace ok nizan kwanta,yace to aunt ma'assalam,tace bissalam tare da katse wayar tana mai farin ciki tare da k'ara jin sonshi na ratsata.

Washe gari maryam ta shirya taje gun wata makwabciyansu mai suna Hajiya iya. Tsuhuwace mai kirki dason mutane kowa yasanta a unguwan,kuma kowa yasan yadda take k'aunar maryam sosai ta d'auketa kamar jikanta. Gata kala kala takeyiwa maryam dayake tana da d'a a yola mai kidin ne sosai dan haka maryam take morewa agunta.

.

Lubna ce kwance a gida tana chartn setaga numbern maryam akan list nata. Nan take ta kirata suka gaisa sosai sannan maryam ta mata godiya.

Samira ta dawo daga mubi dan haka sukazo gun maryam ita da rashida sunata hira se wayan maryam ya fara ringing,tana dubawa taga zahida ce,tasa a handfree suka gaisa,se take gaya mata cewa majid marwan muhsin da kuma muh'd sunzo su gaisheta,maryam batayi mamakiba dan dama manosh ya tambayeta unguwansu. Maryam tace eyyah sun kyauta Allah ya biyasu su,tace ameen gaskya k'awata sun had'u,dariya su samira sukasa tare da cewa kai zahida kodai...zahida tace wlh kuwa muhsin ya kyasa yanzuma muka gama waya dashi,dariya suka sakeyi se maryam tace shikenan abu yayi kyau to Allah ya tabbatar da alkhairi,zahida tace ameen nagode sosai.

  Koda maryam ta ajiye wayan dariya sukayi tare da shewa sukace lallaifa abu yayi kawaye da abokai hahahah. Maryam tace ya isa mana duk randa mukayi waya da manosh seyace in gaisheku,sukace to amaryan captain muna amsawa,kallonsu takeyi tana murmushi tare da cewa amarya tun bamuje ko inaba,rashida tace ai zakuje,dariya sukayi sannan ta d'auki kiran manosh tasa a hands free slm,yace wslm aunt kin tashi lfy,lfy lau ya aiki,yace kai kibari akwai akwai gajiya ban samu na kiraki da safeba wlh ban zauna bane hope kina lfy,tace lfy lau,yace yasu mama,tace duk k'alau suke,yace bakije gun baba a shop bane,tace eh se zuwa anjuma,yace ok,tace yanzu zahida take gaya min cewa su majid sunje sun dubata mungode fa,yace bakomai wlh muhsin wai yana ciki,dariya tayi tace to Allah ya tabbatar musu da alkhairi,yace ameen,ina samira da rashida da amina,tace muta tate dasu amma banda amina,yace to banisu mu gaisa,tace to sannan ta mikawa samira sukasha hida yanata mata raha,tace ab'asan soja da dariyaba amma kai gashi kanada far'a,yace kika sani kodan ina son k'awarkine,tace no bahaka bane,yace toya akayi kika sani,tace kowa ya shaidi soja baya wasa kuma ba dariya,manosh yayi murmushi yace to ai ni k'aramin sojane,manya ne suke hakan kuma sud'inma ba dukka bane. Sameera tace ina fata dai zaka rik'e mana friend namu da kyau,yace base kin fad'a samira "because i luv her over" dariya tayi tace to Allah ya barku tare musha biki,yace ameen nagode sosai,tace yawwa ga rashida. Rasha tace captain zance nece kodai prince manosh dan sunan naka na larabawane,dariya yayi sosai yace duk wanda kika kira,tace captain d'in dai ina wuni,yace lfy ya kuke ya apple d'ina,tace lfyanta k'alau ya aiki,yace alhamdulillah,tace to Allah ya sanya alkhairi adai rik'e mana ita amana dan kaine mutum na farko data amshi soyayyarshi,yace insha Allah rash bazaku samu wata matsala daga gareniba dan nima itace mace ta farko data fara shiga jinina,rash tace jini gabad'aya, yace "yes ina ji da ita sosai pls ku kula min da ita sosai" rash tace to gaskya munji dad'i Allah ya barku tare,yace ameen nagode da addu'arku,tace bakomai gata nan.

Maryam tana murmushi tace hello,yace eeeeh aunt ya akayine,tace babu,yace friend naki suna da kirki sosai wlh kun burgeni gaskya saura zahida da amina ki turo min number'nsu dukkansu kinji,tace ok mungode,yace banace miki bana son godiya ba,tace ai ya zama dole,yace nidai banaso,tace to shikenan byee yace byee.

Yaune manosh ya dawo daga abuja,nan kuma dad nashi ya dawo daga tfy. Manosh yaje har palo ya gaida dad d'insa sannan ya gaya masa ra'ayinshi akan maryam,dad yace a ina take,yace a girei ne,k'irjin dad nashi ya buga amma seya ce to badamuwa zanyiwa iyayen abokanka magana semuje,manosh yace yace to dad nagode,dad yace Allah ya sanya alkhairi yace ameen sannan ya wuce d'aki ya shirya da sauri cikin kananan kaya yasha turare sannan ya d'auki kits d'in tsaraban maryam yayiwa mum sallama yace zanje girei ne,tace to Allah ya kare,yace amin ya fita. Miher ta bishi har waje tace bro gun yarinyar ne,yace ke sunanta maryam ba yarinyaba, tace to ka gaisheta,yace yawwa k'anwata barima in baki numbernta ki dinga kiranta kuna gaisawa kinji, mihar tana son bro manosh sosai dan yana sonta kuma yana kulawa da ita sosai sam bayaso yaga an b'ata mata rai,dan haka itama taga ya dace taso abinda yake kauna dukda dai ita tasoshi da k'awarta lubna amma hakan baiyuba.

.

Shida muhsin da marwan da muh'd suka tafi danshi muhsin yana gun zahida,hakama majid yana gun miher. Wayanta ya kira yace aunt gani a waje,tace yaushe ka dawo daga abujan,yace d'azu,mamaki sosai tayi dan bai sanar da itaba,tace to ina zuwa.

Munbern rashida da samira ta kira tace pls kuzo yanzu,ba jimawa sukazo ta d'aya kofar bayan,duk himarne a jikinsu suka fita.

  Salam,suka amsa wslm,bayan sun gaisa ne manosh yace dama bakisan marwan ba toshine wannan,tace eyyah sannu,yace yawwa maryam ya kike ya hakuri damu,tace bakomai,yace to idan yayi badaidaiba ki sanar dani zan hukuntashi,dariya sukayi sosai,muh'd yace zamu hukuntashi dai,maryam ta gabatar da rashida da kuma samira, sannan suka fara hira,manosh yace aunt yane,tace bakomai,yace muje daga can kinji su marwan zasu damemu,muh'd yace gara dai kam,tana dariya suka d'an matsa gefe.

Hannunsa a aljihu yace baba yana gidane,tace eh,yace yasan munzo,tace eh nagayawa mama kuma nasan ta gaya mishi,yace ok kinsan bana so kiyi laifi,murmushi tayi tace ya k'anwarka,yace miher lfyanta k'alau tamace in gaisheki,sannan na bata numbernki,tace eyyah ina amsawa,yace tun bata gankiba amma tana sonki sosai. Maryam tayi dariya tace nagode ina majid da muhsin,yace suna hira gun zahida majid kuma na barshi a gida gun miher,tace tofa,yayi dariya yace kinga marwan da muh'd ma sun biyonine dan su fahimci juna dasu samera kinga in Allah yayi se ayi bikinmu rana d'ara d'aya,dama akwai wani abokina YUSUF AHMAD shima sojane ya tab'ayin aure matarsa ta rasu agun haihuwa ita da bbyn dukka se bai sakeyin aureba,shine na had'ashi da amina. Maryam tace eyyah Allah ya jikansu,yace ameen kinga shikenan za'ayi bikin abokai da kuma k'awaye ko? Murmishi tayi tace to Allah ya tabbatar,yace ameen meyasa bakya son yin magane, tace bakomai,yace kinaso nima inyi shuru ne,tace a'a se wayansa ya fara ringing,bak'uwar numbern ce ya d'auka tare da cewa hello,muryar mace ce tace yah manosh lubna ce, yace ok lubna ya kike ya gida,tace lfy lau ka dawo lfy,yace lfy lau wlh yasu mama,tace lfyansu lau dama na kirane in maka sannu da dawowa,yace to nagode sosai numbern ki kenen,tace eh shine,yace ok thankyou,tace ok seda safe sannan ya katse wayar tare da saving d'in numbern a wayanshi maryam tanata satankallonshi da yake hasken wayan yana haska fiskanshi.

Gaskya manosh ya had'u take fad'a a ranta,seya katseta da cewa kina satan kallona ko,kunya taji sosai dan batasan ya gantaba,tayi mirmushi tace a'a,yace eh mana aina ganki,meyasa zakiyi sata bayan ni nakine,dariya tayi wanda ya baiyana fararen hakwaranta,yace nima bari na haskaki to,wayanshi ya haska fiskarta tayi saurin juya kanta,seyace to shikenan na dena,sannan ta juyo yace inga wayarki,ba musu ta mik'a mishi,yanata danne danne ashe numbernshi yake dailing dan yaga wani suna tasa mishi, ita kuwa tanata kallonshi tana k'ara jin sonshi a ranta. Yace "PEACH & CREAM" gaskya sunan yamin dad'i sosai apple thankyou,murmushi tayi tare dajin kunya tace wato dama sunan dana samishi ya duba, wayan ya mik'a mata ta karb'a tare dajin kunya se wayanta ya fara ringing,dubawa tayi taga UNCLE IBRAHIM,d'auka tayi tace slm uncle ibrahim ina wuni,yace lfy lau aunty ya gida ya fama da yara,tace lfy lau ya aiki,yace alhamdulillah muna kai,tace Allah ya taimaka yace ameen yasu mama da baba,tace lfyansu lau wlh, yace dama na kira mu gaisane,tace nagode sosai tana mirmushi shi kuwa manosh se kallonta yakeyi.

"Bayan ta gamane manosh yace kar inyi laifi amma waye wannan? Tace brothern rashida ne brothernmu dukkanmu, tun muna primary yake mana lesson a gida har secondary, da shine yake koyar damu a gida tare da sauran yara,bayan tfyan shi NYSC ne yace indinga koyar da sauran yaran,kuma duk yan unguwan uncle ibrahim muke kiranshi.

.

Manosh yace ok,amma akwai wani abu kuma bayan wannan? Tace a'a meyasa ka tambaya,yace to ai naga ya kirakine kuma da dare,murmushi tayi a zuciyarta kuwa tace wato dai kishi kake, tace ai duk muna waya dashi hardasu sameera bawai ni kad'ai bane,kuma ya zama kamar d'an gida dan hargun mama yana shiga su gaisa sannan ya tafi. Manosh yayi magana a zuciyarshi yace gaskya akwai atsala,afili kuma yace ok tobakomai apple zamu wuce kar'in rik'eki dewa, tace to mungode Allah ya kiyaye hanya ka gaida miher,yace zataji insha Allah sannan suka k'arasa gunsu marwan.

Manosh yace to muje guys,muh'd yace amma baka kyautaba danka gama hiranka sekace muje,yace to ai ahikenan nima ba gamawa nayiba kawai dai hakura nayi dan haka kuma ku hakura,marwan yace to rashida nagide sannan yace aunty maryam mun gode sosai semun sake zuwa dan yanzu kam ni kad'ai zan dinga zuwa prince yana takura mana,dariya sukayi lokacin manoah ya fito da k'aramar kits a mota yace to shikenan nima hakan yafimin kowa yayi zuwanshi,manosh ya mik'awa maryam kits d'in batare dayace komaiba tasa hannu ta karb'a tare dayin godiya sannan ya mikawa samira wani leda yace ga tsarabanku,godiya sukayi sosai sannan sukayi sallama suka tafi.

.

Ahanyane manosh yake ce musu akwai matsala gaskya dole su dad suzo da wuri ayi tambaya dan ban yarda da uncle ibrahim d'innan da apple ta gayaminba. Dariya su muh'd sukasa tare da cewa soja da tsoro,yace a'a kunsan fa bana zama sosai,shi kuwa yanzu idan ya dawo daga NYSC ai suna tare kenan 24 gaskya da sake. Marwan yace tobase ke hakuraba tunda ya zama sirikina zan nema maka wata ai,duka manosh yakaiwa marwan yace d'an iska wlh zanyi maganinku bazaku sake biyoniba,hakadai suketa hira da hara har suka isa gida lokacin muhsin ya dawo dagun zahida nan dai sukaita tsokanan manosh wai gaskya seka dage tunda ku biyu masoyanta. Nima dai sad-nas nad'an tayasu kad'an

.

Washe gari miher ta kira maryam a waya suka gaisa sosai take ce mata iher ce k'anwar captain manosh,murmushi maryam tayi sannan suka sake gaisawa,miher tace dan Allah ki rik'e min bro na da kyau dan ina sonshi sosai banaso ya shiga cikin damuwa ta dalilinki pls auntyna,maryam tace insha Allah hakan bazai faru ki kwantar da hankalinki,dad'i sosai miher taji sukaita hira sannan sukayi sallama.

Mahaifin manosh kuwa tunda yaji cewa a girei d'ansa yake neman aure se hankalinsa ya tashi,amma dai dukda haka ya gayawa aminansa sunce,zasuje nemawa manosh aure dan yana son ayi biki da wuri,amma se iyayen,sukace abari tunda AZUMI yazo se bayan sallah se suje tunda su marwanma sun sami nasu matan,dan haka aka yanke shawara za'aje bayan sallah.

Soyayyan abokai da k'awaye dai yana tafiya yadda ya kamata abin gwanin ban sha'awa. Sannan abinda zaifi burgeka a soyayyarsu shine soyayya mai tsafta sukeyi,bakamar irin soyayyar da akeyi a zamanin yanzuba,seka budurwa da saurayi suna kissing d'in junansu wasuma har huging kai wasuma har tab'a jikinsu suke bari namiji su aganinsu hakan shine wayewa ko kuma iya soyayya amma fa ku sani bakomai bane se sab'on Allah da kuma ragewa kanki mutunci a idon saurayin.

Wlh mafi yawancin maza suna son tab'a jikin mace,wasu sunayi yin hakan dan nasu manufarne wasu kuma sunayin hakanne dan su gwada macen,idan kika yarda yaci gaba da tab'aki to wlh wani daga ranan bazaki sake ganin ya dawoba dan zai d'auka duk samarinki haka suke miki tunda yasan halin mazan. Amma idan kika taka mishi birki dole ne zaiyi respecting naki sosai kuma bazai tab'a rabuwa dakeba sedai in dama ba aurenki yake sonyiba.

  "Amma zamanin da muke ciki yanzu sedai addu'a" se kaga budurwa ta nemi yaro k'arami kona makotanta ta goyashi sunce hospital wai tanaso tayi planing dan ta bada tazara,su kuwa doctor ko nurse ba tare dasunyi bincikeba sesu sama duk kalan planing d'in da take buk'ata shikenan budurwa ta maida yaro taje ta samu saurayinta wanda dama shine ya bata wannan shawaran waidan ya kai sadakinta gidansu yana ga ai yanzu kam shikenan kin zamat tashi,shiyasa taje tayi planing domin su shek'e ayarsu kafin suyi aure ya santa tun a waje,kuma bazai tab'a aurenkiba tunda ya samu abunda yake so,koda kuwa ya aureki tofa bazai dinga ganinki da mitunciba kuma wulak'anci kala kala zai dinga miki bayan zunibin da kika kwasa wa kanki. Hmmm 'yan uwana mu kula mu dinga yiwa kanmu fad'a mu kare addininmu da kuma martabarmu ALLAH YASA MU DACE MUFI K'ARFIN ZUCIYANMU AMEEN.

.

Addininmu ya koyar damu addu'oi iri iri,zamanin yanzu seda addu'a. Ina masu yara,ko k'anne ko jikoki dadai sauransu mu tsaya tsayin daka dan nemowa yaranmu ilimin addini kafin mujega na zamani,kuyi k'ok'ari kusa yaranku a ISLAMIYYA. Mu kasance masu yiwa yaranmu addu'oi da fad'in alkhairi akansu idan sun b'ata mana rai bawai muyi musu bakiba. Wannan addu'a tana kore komai,tana kare komai a fad'in duniyannan dan haka mudinga yiwa yaranmu safe da yamma. Fiyayyen halitta ANNABI MUHAMMAD (S A W) yace koda sabon gida mutum yayi tofa wannan addu'a ita kad'ai zakayi batare dakayi sauk'an QUR'AN ba ko kuma yanka, addu'a ce mai kyau sosai.

AUZU BI KALIMATILLAHI TAMMAT,MINSHARRI MA FALAK3脳 sannan shine yace adinga yiwa yara sau 2 a rana ma'ana safe da yamma so uku2. Allah ya gafarta mana kurakurenmu ameen.

Lokacin musabak'a yayi. Kuma auntyn yara itace aka d'auka a girei local gov, inda aka shiryashine a mubi local gov. Duk wani malamin sunna ya halarci wannan musabak'an amma banda manosh sakamakon yanayin aikinsu,amma  friends nashi duksun halarci gurin inda maryam muh'd Attah kokuma ince aunty'n yara zata karanta SURATUL BAK'ARA.

K'ira'a kakeji yana tashi masu imani se zubar da kwalla sukeyi,dole abin ya birgeka mai sauraro da kuma mai kallo. Koda akazo kan maryam ana kiran sunanta jama'a suka d'au kabbara ALLAHU AKBAR kaje ji yana tashi a wannan gurin, himar d'inta milk colour har k'asa mai hannu sannan tafiya takeyi cikin nutsuwa harta k'arasa ta k'arb'i abin karatu ta fara da korar shaid'an sannan ta fara karatu馃槗馃槳鈽�. Ba iyayen maryam kad'aiba,harda wandama basu santaba seda suka zubda kwalla da murya da Allah ya bata mai dad'i sauraro,su majid masuji dad'i muryantaba se a yau da take karatu,kowa da abinda yake fad'a a ranshi akan maryam. Miher kuka takeyi sosai dajin karatun maryam tana mai jin haushin kanta data fifita karatun boko sama dana addininta.

Har aka tsaida maryam sannan ta tsaya suma kansu malaman badan sunsoba sedan lokaci yayi nata kamma harya wuce. Kabbara kawai akeyi da k'arfin gaske su muhsinma da muryansu sosai suke kabbara yayinda manosh yake jiyowa daga wayansa da miher ta kirashi yanata sauraro,wani k'aunartane na susamman yake shigansa wanda shi kansa bazai iya baiyyanawa. ALLAHU AKBAR, dan Allah FANS kuma kuce ALLAHU AKBAR!nasan ku kanku maryam ta burgeku,k'ilama baza'a rasa masu zubda kwallaba danjin haushin kansu na rashin neman ilimin addini,tofa ku sani lokaci mai k'ure mukuba ba'a tsufa da neman ilimi Allah ya bamu ilimi bar albarka damu da 'ya'yanmu ameen.

.

Bayan an kammalane ake kiran wanda sukazo na d'aya, a suratul bak'ara maryam itace tazo na d'aya. Koda aka kirata kuka takeyi harta isa inda *sheik malam balalau* ya bata kyautarta masu sayawa tanata hawayae ta k'arb'a harda key'n mota, jama'a suna ta kabbara.

Hakadai aka gama taron  miher ta k'ara gurinta ta rungumeta tana tayata murna tare da murmushi sosai a fiskarta. Itama maryam d'in rungumeta tayi sannan k'awayenta su su 4 d'in suka rungumeta kowa yana tayata murna su muhsin suka k'araso gunta suna tayata murna dad'i taji sosai ga abokan arziki dukdai se zuwa akeyi ana tayata murna. Bayan tad'an nutsu ne se miher ta mik'o mata waya tace bro na zaiyi magana dakai, karb'a tayi tare da komawa gefe tace slm.

"Wslm my appale congratulatoins" tace "thankyou"ya aiki,yace ki bari kawai kawai wannan aikin namu baiyiba gadkya dayasa nayi missing taro kamar wannan,am verry sorry my apple,tave bakomai wlh wa'yanda ka turoma yayi wlh naji dad'i sosai Allah yabar k'auna,yace ameen apple gaskya bansan mezan ceba wlh dan lokacin da nakejin karatunki ni kaina bansan yanayin da nakeji ba,murmushi tayi tace dama kaji,yace yes miher ta kirani naji tun daga farko har k'arshe. Tace eyyah nagode zamuyi waya anjuma kaji,yace ok wait,tace to menene,yace *I LUV U* murmushi tayi tace *minfu mi yid'ima* sannan ta kashe wayar yanata dariya tare dajin dad'i a ransansa da samu mace kamar maryam.

Duk kyautan ta rabar da wasu,mota *honda civic ce* ash ta samu dan haka ta mallakawa mahaifinta shi kyauta.

Ranan auntyn yara tana tafiya zataje kaiwa mahaifinta abinci seta ga wani mutum jikinsa duk jini yana buk'atan taimako,da sauri ta k'arasa tace subhanalillah lfy bawan Allah,yace wlh wanine ya bugeni da mota ko tsayawa baiyiba,kwalla ne kawai maryam ta fara dan yadda yaji rauni tace amma mutane sam babu imani a wannan zamanin, nan ta tsaida wani mai mashin tace dan Allah ka taimaka mishi,ba musu ya taimaka zai kaishi asibi,tace Allah ya kare Allah ya baka lfy,yace ameen 'yan mata nagode gaskya kina da hali mai kyau,murmushi tayi tace bakomai d'an'uwa amma a maimakon godiyan da zakamin,inaso idan kasamu dama kataimaki mutane uku a rayuwarka,suma kuma kace su taimakawa wasu ukun,yace insha Allah,sannan mai mashi yace yaja suka tafi.

Maryam tana tafya tana tuanin mahaifin su rashida k'awarta,shima wanine ya bugeshi da mota amma sam yak'i tsayawa wanda hakan shine sanadiyan rasuwanshi dayake uazo da k'aran kwana.

Hajiya iya tana zaune a palonta tanata zubda hawaye ita kad'ai,tana cewa yah Allah ka yafemin da irin wannan zalinci da son zuciya irin nawa,Allah ka bani mafita akan wannan abi dana aikata tun kafin inbar duniya.

Lokaci yata ta tafiya yau azimi saira sati, bayin Allah sunata raba abinci wa talakawa, manosh da abokansa suka had'a kayan abinci sosai buhu sugar shinkafa gero gyad'a da dai sairansu suka raba a jimeta da gidan marayu sannan suka aika da sauran wa gidajen surikansu.

Su kuwa 'yan matan sayayya na musamman suka musu na kayan azumi.

Azumi saura 3days uncle ibrahim ya dawo, murna agun yara ba'a magana, shima yayi kewarsu sosai nan dai akaita ihun da tsalen dawowansa. Ibrahim mutum ne mai kirki ga hankali da nutsuwa bafulatanine baida hanke sosai amma kyakkyawane. Suna kama sak da albdallah,rashine kawai tayi kama da mamansu amma sukama babansu marigayi suka d'auko.

Lokacin maryam tana gidansu rashida ita da samira,dan haka suka fito sukaje gunshi suna mishi sannanu da dawowa. Kallonsu yakeyi cike da kewarsu ya e sannunku na sameku lfy,sukace lfy lau sannan suka k'arb'i kayansa suka wuce mishi dashi gida.

Bayan isha ibrahim yazo gidan su maryam kamar yadda ya saba. A tsakar gida maryam ta shinfid'a masa taburma,bayan sun gaisa da mamane yana zaune suka gaisa da maryam suna ta hira dai daga nan mama ta wuce d'aki.

Ibrahim yace ya bayan rabuwa,tace alhamdulillah gaskya munyi kewarka sosai ,yace to ai nima haka kuma alhamdulillah yanzu kam na kammala se muka aiki ayita tayamu da addu'a. Maryam tace to Allah ya baka mai albarka yace ameen result naku shuru ko,tace eh wlh har yanzu,yace naji ana cewa soon zai fita,tace to Allah yasa muga alkhairi,yace ameen ya fama da yara,tace bakomai aina saba yanzu suma kullum sesun tambayi yaushe zaka dawo,yace eyyah ai sunce tunda na dawo yanzu to auntyn yara seta huta ka karb'eta,murmushi maryam tayi tace hakadai suke fad'a tun kafin ka dawo. Yace hakan za'ayi ai dan kina k'ok'ari abubuwan suna miki yawa aunty,tace wlh bakomai har yanzu ni aunty ce,yace eh mana har gobema,dariya tayi shima haka sunata hira har isha suna jiyo miryan abdallah mai dad'i yana kiran sallah,se yace bari na tafi seda safe ki gayawa mama na tafi,yace to a huta gajiya,yace tonagode sannan ya tafi.

Lubna kuwa abun duniya ya dameta taji ance bayan sallah za'aje tambayan aurensu manosh,gashi tasan maryam ce yarinyar da manosh yake so. Hankalinta a tashe tuni ta dena kiran maryam bayan zagi kala kala da takeyiwa maryam, harta hakura ta dena dan sam maryam bata kulata.

Wasu 'yan iskan maza y'an iska ta nemo y'an shaye shaye tace tanaso su sace maryam sannan su watsa mata *acid* a fiskanta ta biyasu kud'i sosai tare da basu address d'in maryam da kuma nuna musu hotonta,amma tace su bari se bayan azumi ma'a dai bayan sallah da kamar sati d'ati d'aya sesu d'auketa.

Yau aka d'aiki azimi maryam tana gun hajiya iya suna hira, hajiya tace maryam kiyita sani a addu'a kinji,maryam tace insha Allah hajiya.

Azumi yanata tfy,maryam sunayin abincin masallaci ita da mahaifiyarta sannan wasu sukan shiga dan su tayasu aiki dab magrib se'a fita dashi kofar masallaci ayita rabawa bayin Allah irin qanda gwamnati take rarraba a unguwannin nan.

.

Azumi yanata tafiya,abdallah se samun kayan sallah yakeyi agun jama'a. Dan shine mai kiran sallah a masallaci gashi da shiga rai. Ranan manosh manosh da marwan sunje girei se marwan yace aboki abdallah zoka gaisa da abokina wanda zai auri auntyn yara.

Abdallah yazo suka gaisa cikin fara'a yace dama kaine kake neman auntynah,manosh yace eh nine,abdallah yace to Allah ka rik'eta da amana karka cutar da ita dan Allah dan ance soja suna dukan matansu. Dariya sosai su manosh sukayi sannanya rik'o hannun abdallah yace har abada abdallah,karka sa ranni zan wulak'anta maryam domin ina k'aunarta fiye da yadda nake k'aunar kaika kuma wlh bacika baki nake makaba kaji? Abdallah yace alhamdulillah naji dad'i sosai Allah ya tabbatar muku da alkhairi,sukace ameen,sannan yace auntyn yara ta aikeni bari aje aje na dawo,sukace to seka dawo sannan ya tafi.

Abdallah yaje gunda uncle ibrahim yake da friends nashi yamusu slm tare da gaisuwa sannan yace yah ibrahim gurinka nazo an aikoni,ibrahim yace to ina jinka,se kuma abdallan yayi shuru,ganin shurunne ibrahim ya mik'e yace to muje gefe ka kaya mun.

Bayan sun koma gefene abdallah yace yah ibrahim auntyn yara ce ta aikoni gunka,dad'i sosai ibrahim yaji da akace auntyn yara yana sonji menene aikan. Abdallah yace tace wai tayita kiran number'nka amma yak'i tafiya,wai inzo ince maka tayi bak'i kuma tana so gu gaisa dasu. Ibrahim yace bak'i wani iri maza ko mata?abdallah yace maza wanda yake nemanta da kuma aunty rashida. K'irjin ibrahim ya buga sosai yace abdallah dama zance danaji da gaskene kenan akan auntyn yara? Abdallah yace eh yaya hakane tare da sunkuyar da kansa k'asa yana tusayin yayan nashi don shi kad'ai yasan irin k'aunar auntyn yara da yakeyi amma dayake bai gama karatunshiba shiyasama baiyiwa mahaifinta magana akaiba yafiso seya gama komai na karatunshi. Ibrahim yace kaje ina zuwa,sannan abdallah ya tafi jikinshi a sanyaye.

Ibrahim ya kunna wayanshi ya kira number'n maryam ringing d'aya ta d'aunka tare da salma,wani irin dad'i yaji har cikin ranshi dajin daddad'ar muryanta. Yace aunty wai kina nemana,murmushi tayi tace eh na kira wayanka ban samuba,yace wlh na kashene saka makon damuna da akayi,tace eyyah,yace ganinan ina zuwa ki basu hakuri kinji,tace laa bakomai wlh sunanan a waje dama gurinka kawai sukazo. Yace tonagode da mutuntani da kikayi aunty se anjuma,tace bakomai aikafi haka a guna uncle ibrahima nima nagode.

Koda ya ajiye wayan shi kad'ai yasan meyakeji a cikin ranshi game da maryam.

Ya k'arasa gumsu da sallama suka gaisa sosai kuma cikin fara'a dama shi ibrahim na kowane kamar dai maryam d'in. Hira sukayi sosai kamar sun dad'e da sanin juna,yayi musu tambayoyi suka bashi amsan gaskya domin wani abunba manosh b'oyewa yakeyi,sam bayaso asan mahaifinshi mai arzikine. Haka sukaitayidai har suka gama sannan suka sallama ibrahim ya wuce gida,se manosh ya kira maryam a waya yace aunt pls ki fito in ganki zamu wuce,tace har gun gaisa kenan zaku tafi,yace eh wlh ibrahim yana da kirki sosai wlh gaskya naji dad'in had'uwa dashi,dad'i taji da aka yabi ibrahim tace nagode nidai bazan fitoba aiba gurina kazoba,ya marairaice murya yace pls aunt kinga marwan yanata min dariya ai gara shi tunda rashi bata nan hankalinsa a kwance "pls come aou aunt"kodon fita kunya a idon marwan don wlh yau idan muka koma shimenan ya samu abun tsokana harsu majid sesunji. Dariya tayi tare da katse wayar d'inkin atamface a jikinta na fitet gaun seta sa himar iya gwinwanta ta fito.

Tunda ya hangota yake murmushi tare da k'are mata kallo harta iso gunsu tana murmushi,marwan yace ai wlh banso ki fito har addu'a nakeyi a raina amma se gashi kin fito meyasa aunt,mirmushi tayi tace saboda banaso ku mishi dariya,manosh yace "thankyou aunt"tare da kaiwa marwan bugu a bayansa yayi saurin shigewa mota gurin tuk'i ya rufe kofar maryam tanata dariya. Manosh ya dawo da kallonshi kan maryam yace wato har kin fara min yanga ko,tace aiba yana bane dama gun uncle ibrahim kukazo ba gunmuba,yace eh amma dai ai kinsan zanso in gaki ko,tace to ai gashi ka ganni kuma ni zan wuce gida,yace nidai ban sallamekiba tukunna,tace to sallameni,murmushi yayi wanda ya k'ara mishi kyau tana kallonshi shi kuwa wani gurin yake kallo daban. Tace wlh ka dingayin mirmushi yana k'ara maka kyau,dad'i yaji sosai yace wauace ki kalleni,mirmushi tayi tace ni ban kallekaba kawai dai na fad'a makane,yace kin kalleni mana kuma ai ke kika sani na fara murmushi sosai wlh,tace ahakan,yace "yes" ki tambayi miher zata gaya miki ni gaskya bancikayin fara'aba, yace hmmm to gaskya nidai ka dinga yi kaji,yace ai inayi kuma danke.

Tace to shikenan zan wuce,yace meyasa kikemin hakane aunt kodon kinga ina sonki sosaine shiyasa kike min haka,tace a'a wlh aiba guna kazoba kuma ai min gaisa,yace to shikenan mun tafi,tace kayi fushi kenan,yace a'a banyiba kawai dai zamu tafine,kallonshi takeyi amma sam yak'i kallonta kuma yana tsaye yana fiskantarta,tace toshikenan Allah ya kiyaye hanya,yace ameen sannan ta juya ta shiga gida,mota ya bud'e yashiga marwan yaja suka tafi.

Manosh ya saba idan suka bar girei seya kira maryam a hanya,amma yau sam sebai kirataba abun yad'an dameta tace to kodai fushi yayine? Har bayan 2hrs bai kiraba,kuma a wannan lokacin tasan suna gida,marwan ne ya kirata yace aunt mun iso gida lfy,tace alhamdulillah tona gode sosai,yace bakomai wlh mune da godiya sannan sukayi sallama.

Har bayan isha manosh bai kira maryam se taji taba kyauta mishiba dan tasan fushi yayi dukda dai basu tab'a samun matsalaba se yau. Har 9:00pm seta d'auki wayanta ta kirashi yanata ringing harya d'auke,zata sake kira kenan setaga call d'inshi,ta d'auka cikin sanyin murya tace hello

Shuru yayi baice komaiba

Ta sake cewa hello

Nanma shuru yak'i yayi magana, tace hello manosh,

Karon farko data kira sunanshi kenan,seyaji dad'i har cikin ranshi amma baice komaiba,ta sake cewa "manosh pls talk 2me" yace me kike so nace miki aunt? Tace wai fushi kakeyi danine, shuru yayi uanajin daddad'ar muryanta,ta sake cewa "manosh am talking to you" yace inace ni kike kora agaban marwan ko? Wani iri taji a ranta dan yadda yayi maganan batasan lokacin datace "am so sorry manosh i din't main to hurt you pls?" Nanma shuru yayi,ta sake cewa manosh wai bazaka min magana bane kuma kanajina? Yace "yes" take jikinta yayi sanyi tace manosh am sorry pls,nanma shuru yayi seta katse wayan. Hankalinta ya tashi sosai tayi dana sanin yimasa hakan.

Har 10pm manosh bai sake kirantaba,seta tsinci kanta cikin damuwa sosai sam ta kasa sakewa,dan tana son manosh sosai acikin ranta. K'arar shigowar texs tayi a wayanta da sauri ta d'auka ta bud'e taga

_Am sorry too apple_

   _I love you so much_

   _Nd i will call you leta_

   _Am talking with my dad now okey,manosh loves you so verry much apple_.

Maryam tana gama karanta texs d'in taji dad'i sosai a ranta tayi murmushi tana mai k'ara jin sonshi na ratsa jikinta,tace i love you too peach tare da rufe idanunta tana murmushi.....

.

Seda manosh suka gama magana da dad nashi,sannan ya koma d'aki ya kira maryam har gurin 11:00pm. Maryam har tayi bacci,ta jiyo wayanta na k'ara da d'auka tare da sawa a kunnenta amma idonta a rufe yake tace hello,cikin muryan bacci, yace "apple am sorry for waking you up"tace "don worry manosh am fine"muryanta ya kashe mishi jiki gabad'aya atake yaji inama tana kusa dashine.

Sakeyin k'asa da muryanshi yayi yace "are you sure" tace "yeah am fine"ai manosh aiseya fara juyi akan gadonshi yace "no apple you have to sleep"zan kiraki da asuba kinji,tace "okey good night" yace sweet dreams apple,murmushi kawai ta mishi tare da katse wayar. Manosh ya sauke ajiyar zuciya yace "ooh my apple"Allah ya nunamin ranar da zan mallakeki a matsayin matata,da wannan tunanin bacci ya kwasheshi.

Wannan karon manosh baiyi tfy ba,har akayi nisa da azumi sannan suka kaiwa 'yan matansu kayan sallah a d'inke kuma masu tsada,da kuma redimate ga fashions ga takalma da jaka da turare komai dai suka had'o musu kowa da irin nashi,sannan sukayiwa iyayensu,harta abdallah seda manosh da marwan suka mishi kayan sallah.

Almajirai sam basa so azumi ya k'are,gashi indai a girene to kusan rabinsu sunsan maryam. Daidai da sabulun wanki ko omo haka zatayita raba musu 1/1 tace suyi wanki dashi,dan haka suna sonta sosai.

Azumi ya k'are yau gobe sallah se murna akeyi su maryam ansha kitso gata da gashi amma sam ita tafi so tayi kitso akan tabar kanta haka,su rashida kuwa wanke kai kawai sukayi amma zahida kitso tayi da ameena babale,su samirane yan wanke kai,gashi suna lalle gayu dai sosai sukayi.

Manosh bai samu zuwa rananba dan haka maryam tayi *cake* mai dad'i kuma had'ad'd'e dama duk sallah tanayi. Mhaifinta kuwa drinks ya sayo kala kala dan yasan 'yar tashi da jama'a bugu da k'ari suna son maryam sona hak'ik'a zai iya kashe duk dukiyarsa dan farin cikin maryam,shiyasa ma idan ka shiga d'akin maryam wlh bazaka tab'a zatan cewa a cikin gidansu d'akinta yakeba dan yadda mahaifinta ya gyara mata shi,gurin zuba littattafaima na musammanne,ga computer komai dai se wanda ya gani.

Yau take sallah kowa se murna su maryam suka shirya shirya tafiya *idi* anko suka sha ita da rashida da samira da himar nasu neavy blue toyobo dogaye har k'asa masu hannu sunyi ado sosai se k'amshi sukeyi. Mama tazo tace to maryam kinyi bak'o a waje,tace bako kima mama,tace eh,da sauri ta mik'e ta fita kawai setaga drivern manosh ne da *406* ash wai yazo ya kaisu masallaci. Mamaki ya kama maryam tace wlh kaje kawai masallacin fa babu nisa da k'afa zamu tafi,yace a'a madam idan na koma fad'a zaimin kiyi hakuri. Shuru tayi tace to ina zuwa,nan ta koma ta sanar da mamanta,mamanta tace to maryam kuje kawai tunda haryazo, haka suka fito abdallah ne a gaban motan su kuwa ukun suna baya sunata salati zikiri har suka isa, sannan yayi pakin a gefe shima yaje akayi sallah.

*Allahu Akbar Allah ka k'ara dauwamar damu a musulunci ameen*

Bayan an idarne sukaita hotuna a wayansu,ai se suka hango uncle ibrahim da friends nashi nan suka wuce aka gaisa sannan sukayi pictures da uncle ibrahim da kuma friends nashi yana tsaye kusa da maryam hotunan sunyi kyau sosai,shima driver se d'aukansu yakeyi a tap batare da sun saniba,amma sam bai d'auki su ibrahim ba.

Bayan sun gama ne sukayi sallama sannan suka zo gun drivern ya maidasu gida. *cake din* maryam ta zuba mishi a kula tare da soyayyen naman kaza da kuma ruwan faro mai sanyi ta bashi,karb'a yayi tare da godiya ya tafi.

Bayan tfyanshine ta kira manosh tace mun godefa,yace bamun b'ataba meyasa kika kirani,tace godiya na kira in maka sannan kuma....yace sannan kuma me, tace inaso ka kawo min *miher* anjuma mu yini,yace coman kike bani kenan,tace *no captain* alfarma nake nema,yace nak'i bazan kawotaba,tace haba mana pls ka kawota,yace nak'i d'in,tace to shikenan ni zanzo gurinta anjuma,murmushi yayi yace zan turo azo a d'aukeki sannan ya katse wayar ya sake kiranta.

Ta d'auka tace bana bukata dama zamuje gun zahidane se mu wuce gurin ameena. Yace wa kika tambaya babu inda zakije,tace saboda da me,yace ra'ayinane hakan,shuru tayi tace to shikenan ka kawomin miher dan tace seka yadda kafin take fita wani girin pls ka barta,yace sekin ce *am sorry peach* dariya tayi tace menayi to,yace nidai na gaya miki,tace ok am sorry peach,murmushi yayi yace tosekin fad'a da muryana,tace ni mace kai miji ai muryanmu dabanbanci bazan iya ba,yace to bazata zoba,tace pls mana captain,yace wlh sekinyi muryana, nan dai ta gyara muryanta wai a dole zatayi irin nashi,ai tun bata k'arasaba take dariya shima haka take ta katse wayar tanata dariya shima hakanne muhsin yace ku kamashi muje gun malam mahmud yayi mishi ruk'iyya inaga yad'an samu matsala ne,daroya sosai manosh yakeyi harya shiga gida,mum da miher se binshi da kallo sukeyi,miher tace the prince lfya kuwa,yace wlh maryam ce take haukatani uama manta mum nashi tana palon,ai take ya seta kanshi yace mum dama kina nan ne,yad'an sosa k'eya,tace nidai inaso akawomin maryam d'innan inga mai sunana kuma sirikata,miher tace dama yau nake so inje in bro ya yadda zuwa jibi kuma se inje mu taho tare.

Manosh yace a'a ki bari dai jibin se driver ya kaiki ku taho tare,miher bata so hakanba amma tasan manosh magana d'aya yakeyi dan haka ta sanar da maryam cewa baza samu zuwaba se jibi,maryam bataji dad'iba dan batayi zaton manosh zaik'iba.

.

Da yamma su manosh sukaje gaisuwa gun surukansu tun daga gun mahaifin ameena suka fara har na zahida sannan suka wuce gire mota 3 masu zafi.

  Kyakkyawan k'arb'a aka musu dama  ansan da zuwansu. Koda sukaje gidansu rashida da samira sannan suka wuce batare dasunyi hira da 'yan matanba.

Bayan sun komane ya kira maryam se fushi takeyi waidan ya hana miher zuwa. Babu irin rarrashin dabai mataba amma tak'i tanata fushi. Yace am sorry apple zan kawota jibi da kaina kinji,tace banso indai kai zaka kawota bazaniko inaba,yace to shikenan bazan zoba zan kiraki anjuma pls zan d'auki wani kiran kinji,tabace komaiba ta katse wayan shi kuwa ya d'auki wayan oganshi.

.

Kamar yadda manosh yace yau miher ta shirya driver ya kaita gun maryam,mirna sosai maryam tayi bayan sun gaisa da mamane se suka wuce d'akinta,ita kanta miher d'akin ya burgeta dukda dai ita 'yar masu akwai ne. Hira sukayi kad'an maryam ta cikawa miher ciki da abin mak'ulashe sannan tace bari in yiwa mama sallama semu tafi dan in dawo da wuri koh,tare suka mik'e sukai mata sallama tace a gaishesu sannan suka tafi.

After dress ce red a jikin maryam tayi kyau sosai taga sun tsaya a wani katafaren gida. Koda aka bud'e gate se taga ashe cikin yafi wajen had'uwa,bayan sun k'arasane taketa ganin flawers kala kala masu kyau sosai. Miher tana rik'e da hannunta se gaisheta gards din sukeyi har suka k'arasa palo, me zata gani...hoton miher da manosh ne da kuma iyayensu,jikinta yayi sanyi tanata fad'in *innalillahi wa'inna ilaihirraji'un* tabbas maryam bazata tab'a mance fiskan wannan mutumin da take tunanin shine mahaifin manosh ba,acikin ranta kuwa tace wlh bazan tab'a b'oyewaba koda hakan zaisa in rabu da manosh peach d'inaba. Miher tace yanaga kina ta kallon hotonmu da iyayenmu nadai fi bro manosh kyau,murmushin kawai tayi tace nidai bance komaiba,miher ta kaita d'aya palon sannan ta zauna tace ina zuwa bari na kira mum sannan ta wuce wani kofa,ita kuwa tana zaune kanta a sunkuye tana tunani.

Read More

Share this

WhatsApp
Newer Posts Older Posts Home

Popular Posts

  • RAINA KAMA BOOK 2 Page 11 to 20
    Tunda aka bud'e mana muka fito hadimansa sukayo caa akan mu, kowanne k'ok'arin nuna farincikin sa yake ga Galadima.     Casuke A...
  • RAINA KAMA BOOK 2 Page 31 to 40
    Na dad'e ina barci kafin Na tashi, nayi mamakin ganina ni kad'ai, bansan time d'in da Galadima ya ficeba, sakkowa nayi daga gado...
  • RAINA KAMA Book 1 Page 1 to 10
    RAINA KAMA......!!♦_*                _{Kaga gayya}_          *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!._* 👉🏻1⃣      *Matsanan ...
  • RAINA KAMA BOOK 2 Page 21 to 30
    Yanda ya rik'e hannun yasani fad'in “please yalla6ai akwai zafi fa”.         Sassauta rik'on yayi, ya sauke ajiyar zuciya, murya...
  • BARIKI AUREN SOJA Page 51 to 60
    Motocine guda shida aka ajiye musu sababbi dal suna sheki ta tsakiyar tasha Adon balloon kana gani Kasan motar AMARYA ce ta fito tareda su ...
  • KASUWANCI NA Page 61 to 70
    Ameer kasa jurewa yayi gaba daya jikinsa ya fara rawa,tunawa Meenat tayi ba Muharraminta bane sai ta dan matsa kamar zata fada kasa ta wayan...
  • KASUWANCI NA Page 31 to 40
       A kunyace na Zauna a daya daga cikin kujerun palon nima sannan nace Ina yini kazo lfy,cike da fara'a ya amsa lafiya Alhmdllh Madam, d...
  • UMMU AYMANA Part 6
      *UMMU AYMANA PART 6* Suna isa Asibitin likitoci suka rufu akanta,wanda da taimakon Allah bata jimaba ta farfaɗo se kuka takeyi,prince kasa...
  • MIWASMITI Page 31 to 40
    Kuka ta Kuma saki gamida kamo hannushi ta matse a tsakiyar qirjinta Dan jin wani irin suka da yake mata Ga jiri da takeji gaba daya bata gan...
  • MACIJINE SHI Page 31 to 40
    _________________Kai tsaye part ɗin nanny Adeeb ya nufa da fattu,suna zuwa kuwa nanny ta gyara ko ina sai ƙamshi ke tashi,dakin fattu suka...

Categories

  • 'YA'YA DA KUDI 1-END (8)
  • 'YA'YA MATA 1-END (9)
  • 'YAR BOKO 1-END (6)
  • 'YAR FULANI 1-END (14)
  • 'YAR GIDAN TSOHUWA 1-END (6)
  • 'YAR JAMI'A (9)
  • 'YAR MAFIYA 1-END (6)
  • 'YAR TALAKAWA 1-END (7)
  • AGOLA 1-END (17)
  • AKIDATA BOOK 2 Page 45 -End (11)
  • ANAL 1-END (12)
  • ANTIN YARA 1-END (6)
  • AUREN JARI 1-END (9)
  • BAKAR MACE 1-END (3)
  • BARIKI AUREN SOJA 1-End (8)
  • BINTU 1-END (7)
  • CIN AMANA KO FANSA 1-END (10)
  • CIWON IDANUNA 1-END (7)
  • CIWON IDANUNA AUDIO (2)
  • DAGA TAIMAKO 1-END (5)
  • DAKON SO 1-END (4)
  • DAMA TA BIYU 1-END (13)
  • DR BOBBY 1-END (11)
  • DUBU CIKAR MAI CARBI 1-END (7)
  • FULANI 1-END (11)
  • GURBIN IDO 1-END (1)
  • HADIN ALLAH 1-END (8)
  • HIBBAH 1-END (4)
  • INA ZAN GANSHI 1-END (7)
  • INAYA 1-END (9)
  • JIDDARTIL KHAIR 1-End (1)
  • JIHADI 1-END (10)
  • JUWAIRIYYA 1-END (7)
  • JUYAYI PAGE 1-END (6)
  • KASUWANCI NA Page 1-End (1)
  • MACIJINE SHI 1-END (1)
  • MAH NOOR 1-END (5)
  • MAIMOON 1-END (10)
  • MAKARANTAR KWANA 1-END (5)
  • MAKAUNIYAR KADDARA 1-END (10)
  • MATAR ALI 1-END (10)
  • MIWASMITI 1-END (8)
  • MOTAR KWADAYI 1-END (4)
  • NAMIJI BAYA KADAN 1-END (16)
  • NI AYS NAKE SO 1-END (16)
  • RAINA KAMA 1-END (1)
  • RAYUWATA 1-END (6)
  • SHIMFIDAR MIJINA 1-END (3)
  • SONE AJALINA 1-END (5)
  • SURBAJO 1-END (14)
  • TUDUN DAFAWA 1-END (4)
  • TUZURU 1-END (6)
  • UMAR KO FARUUQ 1-END (5)
  • UMMU AYMANA 1-END (8)
  • UMURNIN IYAYE 1-END (7)
  • WAMINAL HOOB 1-END (9)
  • YAN MATAN ZAMANI 1-END (6)
  • ZAYN MALIK 1-END (10)
  • ZUCIYA KOWA DA IRIN TASA 1 (10)
  • ZUMA SAI DA WUTA PAGE 1-END (7)

Social Plugin

  • facebook
  • twitter
  • instagram
  • youtube

Hausa novels 2023

Search This Blog

Powered by Blogger.

Blog Archive

  • July 2023 (7)
  • June 2023 (65)
  • April 2023 (33)
  • March 2023 (132)
  • January 2020 (10)
  • December 2017 (62)
  • November 2017 (33)
  • October 2017 (38)
  • September 2017 (39)
  • August 2017 (75)

Report Abuse

  • Home

Total Pageviews

Copyright © 2023 To Hausa novels 2023 | Powered By WwW.aysnovel.com.ng
Design By Aysha Adam | Theme By WwW.aysnovel.com.ng | Distributed By Aysha Adam