ππ»2⃣1⃣
.......Har safiyar yau jikina sai k'amshin turaren Galadima yakeyi, feena dake kwance kusa dani tace, “Mrs Galadima! k'amshin nan nakufa yayi over”.
Harara Na dalla mata, tareda kai mata bugu ta kauce tana dariya, Bilkeesu ma dariyar takeyi, ta jawo wayarta tana fad'in “jama'a kunma tunamin, bara na duba comments d'in jama'a akan pictures d'in jiya”.
Zumbur natashi zaune ina kallon Bilkeesu, “Bilkeesu kinada kai kuwa? yanzu nan hotunanmu kika mik'ama duniya?”.
Da sauri Ameera tace, “to miye aciki, ai gamma mak'iya masu yad'a hotunan wancan 6atacin har 6utiyarsu Na rawa sugani yanzu kin zama halalinsa, ai wlhy jiya kusan kwana nayi karanta comments d'in jama'a akan pictures d'in, idanma mu bamu turaba wlhy abokansa sun yad'a a kowacce kafar yanar gizo, kuma yarinya harma a news wlhy an nuna, idanma baki saniba live aka nuna komai awasu gidajen tv”.
Hannu na d'ora aka kawai nafashe da kuka saboda bak'inciki, nace “dan ALLAH harda abinda yaymin?”.
“sosaima kuwa”. ‘cewar Ameera’.
Kukana yakuma k'arfi sukuma suka saka dariya harda rik'e ciki sukeyi, nikam wlhy kukan gaske nakeyi basu saniba.
Munubiya ce ta fahimci hakan, saita rungumeni tana k'ok'arin rik'e dariyarta data kasa rik'uwa.
Ahaka aunty salamah tashigo tasamemu, “kai lafiyarku kuna dariya kuma ita tana kuka?.”
Labari suka bata, ita kanta dariyar tayi, “yo miye abin kuka anan, koba komai ai ya nunama duniya yana k'aunarki, 'yan bak'in ciki kuma yasaka musu ciwon zuciya”.
Kallonta nayi ina shar6ar hawaye, “yanzu nan aunty salamah kema haka zakice? mutum yamin wannan iskancin a bazama duniya sannan kuringa d'aukarsa abin kirki? yanzu dan ALLAH idan su Abba suka ganifa? tunda ance harma gidajen TV aka nuna”.
“kajimin yarinya, yo ina kuma ruwan su Abba, mijinki nefa yanzun, to ai su inna ma duk sun gani agida, haka suma su abban”.
Zumbur nayo tsalle tsakar d'akin hannuna bisa kai nace “galadima ka kasheni wlhy, ka cuceni ALLAH ya isana”.
Dariyarsu k'aruwa tayi, suka shiga yi harda hawaye. yanda kukasan Na bibbigesu haka nakeji.
Aikam yinin ranar ban yarda Na had'a ido da kowaba agidanmu, har lokacin da innarmu suka kiramu sukai mana fad'a itada mama Rabi'a da inna lami.
Munci kuka tamkar zamu k'arar da hawayenmu.
Zuwa la'asar fa anfara shirin kaimu gidajenmu, saifa lokacin hankalina dana Munubiya yakuma tashi sosai, domin abinda ake gudun yazo (rabuwaπ, sabo turken wawa).
Muna d'aki nida munubiya kowa zazza6i ya rufeta, yayinda iyayenmu keta k'imtse-kimtse, ita kanta innarmu jikinta yayi sanyi lakwas, saboda ganin abinfa da gaske ake, tafiyar zamuyi mu barta.
Suma sauran amaren kowacce Na d'akin uwarta, wasunsu kam ko'a jikinsu, hankalinu kwance Dan d'okin auren sukeyi su.
Anayin sallar magriba inna lami tazo tasakamu mukayi wanka, ana shiryamu muna kuka, bayan mun saka atanfa iri d'aya da aka bamu da gyale aunty Salamah tafara zazzage mana turarurruka ajiki.
Duk wasu tarkace an had'a manashi kowa a handbag d'insa, sannan aka tarkatamu dukkan mu amaren zuwa falon Abbanmu, dukkan iyayenmu mata suma suka shigo, harda innaro da gwaggo Safiyya.
Nasiha aka shiga mana mai ratsa jiki, mukam sai shar6ar kuka mukeyi mu dukanmu, hakama iyayenmu mata bakowa ya iya yimana nasihar ba. tun ana mana fad'an naji ana rad'e rad'in isowar wasu daga cikin angunan, wani kukan bak'in cikine Yakuma tahomin saboda tuna ni nawa Auren nanda shekara 1 ya k'are.
Rungume innarmu mukayi yayinda akace mufito masu d'aukar amare duk sun iso.
Innarmu Itama kukan takeyi, da gyar aka ciremu daga jikinta, an fara fita dasu fiddausi saboda motocin d'aukarsu duk sungama isowa, nice dai basu isoba.
Suna kuka da komai aka fita dasu, yayinda dangin iyayensu mata kowa tabi tawagar mortar tasu amaryar, danginsu abbanmu kuwa rarrabuwa sukayi, domin su sami zuwa kowanne 6angare suma.
Motocinsu Na fita daga anguwar na gayyar abokan Galadima suka shigo, mitocine a Jere kuma masu yawa, abokan yaa marwan ma dama su suke jira, dan ance dole sai Munubiya tamin rakkiya sannan tunda nice k'arama.
Bushe-bushen algaita yafara tashi anguwar tamu, dukda darene hakan bai hanasu busa kayarsu ba, hakan ya tabbatarma da 'yan anguwa tawagar gidan sarauta sun iso kenan.
Mata hud'u sun shigo gidanmu tareda kuyangi, Alk'yabba mai azabar k'yau da suka kawo aka sakamin, sannan aunty salamah takuma fesheni da tirare dagani har Munubiya.
Da k'yar aka 6an6aremu daga jikin innarmu, tana kuka munayi, haka aka fita damu k'ofar gida wajen motoci.
Motar datafi kowace tsari da k'yau aka sakamu nida munubiya, sannan inna lami da gwaggo Safiyya suka zauna a gefenmu.
Kuka muke rik'e da hannun juna, har aka Isa damu cikin masarauta.
Mom itace zaune a matsayin Momma uwar Ango kenan, Dan haka aka kaini sashenda take tareda dangin Momma.
Tarba ta mutunci aka mana, irin wadda kowad'anne iyaye suka kai 'yarsu gidan wani aka mata wannan tarbar hankalinsu zai kwanta sosai.
Su inna lami basu wani dad'eba suka fara mik'ewa, saboda suna son mik'a Munubiya itama.
K'ak'a rak'a k'aka, yanzufa akeyinta, danni da Munubiya mun rik'e hannun juna gamma munk'i saki, anyi lallashin da ban magana amma munk'i, da k'yar aka rabamu muna kuka tamkar ranmu zai Fifa. mun burge jama'a da basu tausayi sosai, sai hotuna ake zuba mana kuwa a wayoyi, (yo gidanne kwanyar da lantarki ko inaπ₯Ίπ‘).
Mom tasakani a jikinta tana lallashina da bani hak'uri, bayan fitarsu aka kaini wani d'aki, har lokacin ina shashshekar kuka, su Ayusher duk suna tare dani, basubi Munubiya ba, dan sunsan ita yau yaa Marwan zai shiga daga cikiπππ.
Har lokacin mom Na tare dani, zazza6ine mai zafi yarufeni kuwa, amma dukda haka saiga wata mata wai tazo shiryani, Ashe za'ayi Mother's event ne acikin gidan dakuma wanu Abu dasuke kira wai tarbar amarya a masarautar.
Babu yanda zanyi, haka Na zauna tamin kwalliya Na shirya cikin less lemon green, aka sakamin alk'yabba mai k'yau itama, yanzuma har hular aka sakamin, Dan haka fuskata arufe take, saina sami damar yin kukana hankali a kwance.
Mom da kanta tazo ta kama hannuna muka fita, yayinda kuyangi ke binmu abaya.
Filine aka k'awata da haske, anmasa decoration da kayan sarauta Na kwalliyar gida, anutse kowa yake zaune, babu wata hayaniya sosai, (abinka da lamarin manya toπ₯³).
Yaukam Galadima cikin ainahin basarakensa yafito, domin komai Na jikinsa Na sarautane, yasha alk'yabba kalar tawa, sai dai tasa ta maza ce, hard'e yake a zaune bisa wata kujera 2sita, wlhy wanda baima saniba saiya d'auka sarkinne gaba bad'aya, yaci mur fuskarnan d'inke, yasha rawani abin zak'k'yau kamar nabama (gwaurayen group d'ina shiπ₯΄⛹π»♀).
Gefensa mom ta zaunar dani, tunda aka shigi wajen dani suka d'auki tafi, fuskata a rufe take, ba kallon kowa nakeba, saima hawaye dake cigaba da zirara har yanzun.
Mom tad'an ja hancin Galadima ya murmusa, sannan takamo hannuna tasaka cikin nashi tabar wajen.
K'amshin turarena da nasa ya had'e yabada wani kalar k'amshin Na musamman.
Dukda kukana a hankali nakeyi mara sauti hakan bai hanashi jin ajiyar zuciyar danake saukewa ba, yad'an matsa hannuna dake cikin nasa amma baiyi magana ba, nima sai bance komaiba nacigaba da kukana.
An fara gudanar da addu'oin fatan alkairi da zaman lafiya agaremu, sannan akamin barka da zuwa cikin wannan masarauta mai d'unbin tarihi, Mom takar6a tayi jawabi irina uwar kwarai mai tarin mutunci da kamala. aka shiga tafa mata, saboda taburge kowa.
Hakama aunty Mimi tayi jawabi mai birgewa, sannan mama Fulani tafito cikin tsantsar izzarta da k'asaita tayi welcoming d'ina a wannan family, hakama matan Sarki, saikuma k'annen galadima mata da yayunsa, yayun momma da k'annenta, komai yana tafiyane cikin nutsuwa, nidai ba ganin kowa nakeba, amma ina sarrarensu, har lokacin kuma hannuna yana cikin Na Galadima, yakan d'an murzashi time to time.
Duk Na k'agara a tashi wlhy, dan jikina yayi masifar zafi saboda zazza6i, shikansa Galadima yanajin zafin a hannuna, ganin kamarma ina rawar sanyi saiya kwantoni jikinsa.
Ban musaba, saboda babu abinda nake buk'ata a lokacin kamar kwanciya, ga barci ga ciwo da gajiya.
Bayan angama jawabai da k'yaututtuka da kowa kan bani wad'anda aketa zuwa ana jibgewa a gabanmu aka fara gudanar da liyafar cin abinci kamar yanda komai yake a tsari, sai abinda kakeso za'a kawo maka.
Muma ankawo fruits salad da gasashen kaza da snacks sai drinks da wani abinci dabansan miyeba an ajiye agabanmu.
Da hannu Galadima yayi kiran aunty Mimi, ta k'araso inda muke.
“my k'ani lafiya dai? Ko abincin bai matabane?”.
“no aunty bama abinci baneba, batada lafiya fa, ta6a jikinta kiji”.
Hannu aunty Mimi tasaka a wuyana, tausayi nabata saboda zafin da jikina ya d'auka, “to yaza'ayi yanzu? ko tad'an k'ara hak'uri kad'an tunda naga ankusa tashi, kasan halin mama Fulani, kuna tashi yanzu zata d'aukeshi wani Abu daban, dama wannan d'an kwantar da itan dakayi ajikinka inaji tana maganar bakada kunya wai”.
Guntun tsaki yaja yace “canta matse mata, indan tagadama tacika masarautarnan da surutu, nanda minti 30 inba'a gamaba zamu tashi kawai”.
“karka damu zama'a gama insha ALLAH”.
duk maganar dasukeyi ina jinsu, sai naji tausayin kaina ya kamani, domin nafahimci nanma akwai mai irin halin innaro kenan. Wasu hawaye suka silalomin a kumatu, sauk'i nama auren 1year ne Na kama gabana.
Daga ni har shi babu Wanda yaci wani Abu har aka tashi a taron, lokacin 12pm, yanzuma mom ce takama hannuna muka koma 6angaren da aka fara kaini, muna shiga kwanciya nayi, bayan mom tasakani cire alk'yabbar jikina, duk kunya ta rufeni, ganin haka yasata ajiyemin kayan barci masu kauri ta fita, a hanzarce na shirya na saka hijjab sannan na kwanta, saida ta kintaci time sannan suka shigo itada aunty Mimi da Galadima sai wani ba'indiye, Ashe abokinsa ne dayazo biki, kuma doctor ne.
Galadima ya zauna a bakin gadon kusada kaina, dayake na juya musu bayane, bargon Dana rufa har fuskata yad'an janye, Idan Akash yay tambaya saishi ya d'an rankwafo Dan yaji amsar da zan bada, saiya maimaita masa abinda na fad'a.
Bayan gama tambayoyin Akash yace damuwa ce da gajiya kawai, ya rubuta maganin daza'a sayo min, (duk cikin harshen ingilishi suke maganar).
Kar6a Galadima yayi ya d'auki waya yakira Harun, sunan maganin ya Sanar masa sannan ya yanke wayar, mintuna 10 saiga Samha takawo maganin.
Ya kalli mom yace, “amma bataci abinciba ai”.
Kallon Samha mom yayi, tace “taje ta had'o min tea.
Samha na kawowa duk sai suka fice suka barni dagani sai shi, shima Akash fita yayi.
Bargon jikina ya yaye gaba d'aya, muryarsa a dake yace “tashi kisha”.
Shiru na masa, hakkane yasakashi kausasa muryarsa, “wai bak'ya jinane?”.
Yun k'urawa nayi na tashi da k'yar, kad'an na saci kallonsa, harya cice kayansa na d'azu, yana sanye da dogon bak'in wando da T-shirt mai gajeren hannu, gefen wandon anmasa zane layi 2 da farin zare. fuskarshi babu walwala kamar kulum.
Mug d'in tea n ya mik'omin bayan na gyara zamana na jingina da gado, ALLAH ma ya soni sanye nake da hijjab.
Kar6a nayi dan nima nasan harda yunwa ke cina, inaga rabona dawani abincin kirki tun ana jibi d'aurin aurenmu, (ranar kamu).
Nasha rabin cup d'in na mik'a masa, bai kar6aba yashiga hararata, cikeda k'asaitarsa yace “cup d'in kawai nake buk'atar gani, kina 6atamin lokaci zanje na kwantane”.
Tamkar na makeshi haka naji, na harareshi nima a k'asan ido, muryata na rawa nace “wlhy na k'oshi, zanyi amaine”.
Bai tanka minba kuma bai k'ar6i mug d'inba, hakan ya nunamin dole dai saina shaye kenan, haka na rumtse idanu na shanye na mik'a masa mug d'in.
Kar6a yayi ya ajiye saman table glass d'in dake gabansa, sannan yad'auki magungunan ya 6alla min, bana tsoron Magani sai allura, dan haka babu musu na kar6a nasha tareda ruwan daya bani a cup.
Ina gamawa na zame na kwanta, mik'ewa yayi yaja bargon ya lullu6a min sannan ya fice batareda ya tanka minba.
Babu dad'ewa barci ya kwasheni, bamma San su Ayusher sun shigo sun kwantaba suma. da yake gadon babbane duk sai ya d'aukemu.
Washe gari natashi dad'an sauk'i, sai dai kewar munubiya data innarmu, harma data gayyar tsiyar 'yan gidanmu, sauk'i nama d'aya ina ganin su Feena.
Break fast mai rai da lafiya aka kawo mana, su Ameera sai zuba santi sukeyi, nidai uffan bance da suba, nad'an tsakura kad'an na turo, maganin jiya na d'auka nasha na safe, dan har lokacin kaina na ciwo kad'an-kad'an, babu dad'ewa barci yay awon gaba dani.
Ban farkaba sai 12, shima tadani akayi, wai za'ayi ko hawan mi, nidai wannan bidi'a ta isheni hakanan wlhy.
Shiri akamin yanzuma cikin farin less, sanan aka samin alk'yabba, yanzun ma fuskar tawa a rufe take.
Gaskiya gidan sarauta akwai girma, dan shimafa dole akirasa da suna wani gari guda kam.
A mota aka sakamu zuwa inda za'a gudanar da hawan, dukda kuwa acikin gidanne fa, nida Samha ne kawai a mortar, tana ta zubamin surutu har muka isa.
Wata daban santa bace ta fitar dani daga motar, tana rik'e da hannuna har gurin da aka tanada domin zamana, yanzun fuskata a bud'e take, ba'a sakamin hular alk'yabba d'inba, dan muna zama awajen matar data fidoni ta ciremin, sai dai kunya tasani kasa kallon kowa, duk tsiwata inada tsananin kunya da rashin son zama wajen da mutane suka cika yawa.
Aunty Mimi ce a gefena na haggu.
Ban iya kallonba saida ta min magana tana kamo hannuna, dole babu yanda na iya na kallesu, su Galadima ne a saman dokuna shida samari kusan biyar duk da irin shigarsa ta sarauta, dokunan suna a tsaitsaye, da alama umarni suke jiran abasu, dan kamar gasace zasuyi.
Caraf muka had'a ido dashi, murmushin gefen baki ya sakarmin, cikeda mamaki na janye idona daga kallonsa.
Ana busa wani k'aho kowa yabama dokinsa k'aimi suka rera da gudu, nanfa hankalin kowa yakoma kansu ana zufa tafi, babu wata hayaniya dan bawani yawane damuba, kusan ma wajen duk 'yan matane sai abokan Galadima dasuke son ganin al'adar dabasu saniba. Saikuma yayunsa mata irinsu aunty Mimi, amma babu manya kamar su mom awajen.
Ni ban saniba Ashe wannan tafiya saisun zagaye masarautar su dawo, Wanda yafara zuwa shine na d'aya.
Muna nan kusan mintuna 30 saigasu aguje suna tada k'ura, ko ganin fuskarsu ma ba'ayi sosai bare kagane wanene a gaba.
Jinai kawai ansaki tafi kowa na ambatar Galadima! Galadima!!, wai Ashe shine yafara isowa. ya diro akan dokin yana murmushi da goge hannunasa da handkerchief d'insa daya zaro aljihu, sannan yagoge fuskarsa.
Ruwa wani dogari ya mik'a masa, ya d'auka daga saman tired'in da aka d'oro yabud'e Goran, batareda ya saka kofiba ya hau shan kayansa, tas ya shanye ya jefar da robar, suma sauran duk ruwan suke sha.
Daga nan hotuna akayi, sannan yazo har inda muke ya kama hannuna, wai Ashe nima yanzu dole saina hau dokin, ahakane zamuje sashe-sashe, dan kowa yanacan yafito waje yana jiran zuwanmu.
Banta6a hawa dokiba sai yau, dan haka jikina yakama rawa. Muryarsa can k'asan mak'oshi yace “k bak'auya ki nutsu”.
Maganarsa saida tabani haushi amma ya zanyi, da taimakonsa na hau dokin bayan dogarai sun baza rigunansu yanda baza'a ga hawa naba.
Saida na hau da k'yau sannan shima yaje ya hau nasa, kuyangine a gabanmu suna zuba flowers, a bayanmu kuma dogarai, gefe da gefenmu ma dogaraine, wasu suna busa algaita wasu suna kid'an taushi, sai gayyar abokansa biye damu abaya dasu Ayusher da 'yammatan masarautar.
Ahaka muka dinga zuwa sashe -sashe inda duk sun firfito, duk muna akan dokin bamu saukaba, sai dai mukan risina alamar gaisuwa. fuskata kuma tana abud'e yanzun kowa Na ganina, saida muka zagaye ko ina a masarautar sannan aka maidani wajensu mom. Lokacin la'asar tayi.
Dukna damu saboda kiran munubiya danaketa yi wayar akashe, tsakin danakeyine ya saka Ayusher tambayata, na fad'a mata.
Dariya tayi, “yo banda abunki ina zakiji munubiya kuwa, yaa marwan nacan nashan amarci kema kin sani ai, kema zuwa gobe wazai kiraki ya samu, Galadima nacan yana kwa.....”.
Filo na d'auka Na jefa mata a fusaka, suka sanyamin dariya kuwa.
★★★★
Nasha kuka yayin tafiyarsu Ayusher, inaji ina gani suka tafi suka barni nikad'ai cikin wad'anda ban saniba.
Tun magriba aka shiryani tsaf cikin wata tattausar atanfa, sannan aka d'oramin alk'yabba, wlhy nagaji da saka alk'yabba r nan, saboda nauyi sukemin, har mamaki nakeyi yanda su basu damuba.
Zan iya cemuku nidai yau wanka akamin da turare dan kowane lungu da sak'o na jikina saida yasha ruwan turare, ruwan danayi wanka dashi kansa na musamman ne, nayi k'yau harna gaji.
An fiddoni aka sakani cikin mota, sannan aka nufi sashen Galadima dani. Dukda nasan auren Contract nayi, hakan bai hana zuciyata luguden dakaba, tunda bamuyi wata yarjejeniya dashiba ta zaman da zamuyi, addu'a natayi a zuciyata ina tunano innarmu da munubiyata da kewarta ta gallabeni, jinake tamkar mun shekara 5 bamuga junaba, bamu ta6a yini ba'a tareba, saigashi yau munyi kwana da yinima, ko'a waya bamuji muryar junaba.
Duk da fuskata a rufe take hakan bai hanani shaida 6angaren Galadima ya had'uba, dan k'amshinsa ma da banne.
Muryar wata na tsinkayo a cikinsu tana fad'in wai falon Galadima za'a kaini, gabana yakuma fad'uwa.
Nidai naji mun iso inda turaren Galadima yafi ko ina yawa, inaga nanne falon nasa, gawani lallausan Abu danake takawa a k'afata, sun zaunar dani akan wani laushin dayafi Wanda nake takawar, sannan sukayi addu'a suka fice.
Tunda suka fita ban iya d'ago kainaba, dukda falon tsitt yake alamar babu kowa cikinsa, sai k'arar AC kawai da ni'im taccen k'amshin dake tashi, a falon, sai TV dake magana can k'asa an rage k'arar sosai, hawayen danaketa rik'ewa tun d'azun suka shiga ziraro min a kumatu. a hankali nakejin takun takalmi na tunkaro falon.........✍πΌ
Muhad'u tomorrow idan munkai da rai da lafiya, yau kaina namin ciyo kuyi manage da wannan pleaseπ€¦π»♀.
Ko Galadima zai angwance oho marππ₯³.
⛹π»♀⛹π»♀
*_ALLAH ka gafartama iyayenmuππ»π_*
*_Typingπ²_*
*_HASKE WRITERS ASSO...π‘_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ceπ€π»_*
ππ»2⃣2⃣
..........Takun takalminsa yana bada sautine dai-dai da kowacce dak'ik'a na bugawar zuciyata, gaba d'aya saina nemi jarumtata na rasa, musamman da firarsu a Ayusher tashiga dawomin a zuciya.
Zuciyata tashiga tsitstsinkewa, saikace ba Munaya mai tsiwarnan ba da rashin barin kota kwana, kululu cikina yabada sauti lokacin da aka murd'a handle d'in k'ofar. kamshinsa ne ya buso min har cikin hancina.
Shikam cak yatsaya yana kallona da mamaki, yasan wannan aikin aunty Mimi ne ko mom, yakuma tamke face saboda tsaro ba tsorobaπ.
Oho ni bamma san yanayiba, nima tawa ta isheni a zuciya, dan wani tsoronsa ALLAH ya dasamin lokaci d'aya. kusan mintuna 2 yana a tsaye tamkar bak'on falon, yayinda k'amshin turarena ke dukan hancinsa, yau da ace auren soyayya yayi da wadda yakeso, babu abinda zai hanasa sauke nauyin daya damesa tsawon shekaru. a hankali yacigaba da takowa har cikin falon, ya zauna a kujera mai zaman mutum biyu cikeda izza, k'afarsa d'aya a kan d'aya yana wani kallona a k'asan idanu, shiru kakeji tamkar bama a cikin falon.......
Muryata a sanyaye nace “ina yini”.
tamkar bazai amsaba, saikuma yace “lafiya”.
Daga nan kowa yay shiru.
Knocking d'in k'ofar da akayine yasakashi sauke 6oyayyar ajiyar zuciya, cikin muryarsa mai kama da anmasa dole ya tambayi wanene?.
Cikeda girmamawa sarkin k'ofar yace, “nime ranka ya dad'e, dama an kawo sak'one”.
Kansa ya jingina da kujera, sannan yace “su shigo”.
Kuyangi kusan biyarne suka shiga falon da sallama, duk muka amsa akan la66a, suka dire kayan hannunsu sannan suka zube suna kwasar gaisuwa agaremu, hannu kawai ya d'aga musu, nidai koma motsi banyiba, dan nima kunyama nakeji idan naga sun durk'usa suna gaidani, danfa wasuma sun girmeni sosai wlhy, wasuma sun haifeni, kai sarauta dabance gaskiya, al'amuransu sunada wahalar gaske, nidai harma yanzu ban fahim ci komaiba wlhy.
Bayan fitarsu da kusan mintuna 4 naji alamar mik'ewarsa, yanzu ma baice dani uffan ba yashige wani d'aki danake k'yautata zaton bedroom d'in sane a wajen.
Guntun tsaki naja, a raina nace ALLAH ka rabamu da girman kai dai wlhy.
Ban damu da cire hular alk'yabba d'inba, dan sanyin Ac yasa ban takura ba, sai zamana dana gyara sosai yanda zanji dad'i da k'yau a saman lallausar kujerar, duk da har yanzun a tsoracen nake kuwa. dan wannan d'an jinkan yafi k'arfina, zai iya amfani da k'arfinsa ya cutamin batareda yayi la'akari da matsayin auren namuba.
Shikam yana shiga d'akin nasa yafara k'ok'arin cire bottom d'in rigarsa, idon sane ya sauka akan gadonsa dake lailaye da zanin gado blue, dan komai nasa na nan white and blue ne, sa6anin na India dasuke White and Golden, kuma matsawa yayi sosai saboda ganin farin k'yalle dake saman bedsheets d'in.
Tsaki yaja yana fad'in “waisu wad'annan mi suke nufi da shinfid'amin wannan farin abun a saman gado? samazo su d'auki kayansu yanda suka ajiye, motsww”. Yakuma jan tsaki sannan ya shige bathroom.
Acanma yana wankan yana jera tagwayen tsoki, bai wani dad'eba yafito sanye da bathrobe milk, hannunsa rik'eda k'aramin towel yana goge fuskarsa zuwa kansa.
Bai shafa maiba, wando yasaka da t-shirt duk milk color marasa nauyi, da alama yayi shirin barci kenan, ya d'auki turarensa na barci mai sanyin k'amshin ya faffeshe jikinsa, sannan ya saka silifas bak'ak'e a k'afarsa yakuma fitowa..
Kallona yayi da mamaki ganin ko fuskarta na kasa bud'ewa, ya ta6e baki da cije lips nashi saman ya zauna bisa tattausan carpet d'in tsakkiyar falon inda kuyangin suka ajiye kayan d'azun.
Tankwashe kafafunsa yayi yashiga bud'e kwanikan domin duba abinda ke ciki. “halan kekam bak'ya jin zafi?”.
Yayi maganar yana zuba fruits salad a k'aramin bowl na tangaran mai k'yau.
Shiru nayi tamkar ban jishiba, shima saiya shareni yaja bowl d'in gabansa yafara sha a hankali tamkar bayaso.
Duk abinda yakeyi ina kallonsa ta k'asan ido, saboda kaina Dana jingina da kujera.
Kusan mintuna 5 yana shan fruits salad d'in tamkar wani k'aramin yaro, dan ko Rabin Wanda yazuba baiyiba, araina nace abincinma sai an masa sarauta kenan.
Idanunsa ya d'ago yana kallona, “k wai bakijin ana Miki maganane? bazaki bud'e face nakiba?”.
Saida naja kusan seconds 20 sannan na janye hular alk'yabba d'in.
Janye idonsa yayi yacigaba da shan kayansa, nikuwa saima na zame na kwanta a kujera, dama 3setter ce, idanuna na maida na lumshe saboda ciwon da kaina yakeyi kad'an-kad'an, ga kewar innarmu da munubiya dasu Aryaan na damuna, ga wannan auren na fargaba na addabar zuciyata.
Dukda yaga kwanciyar danayi bai tankaba, ya kammala shan fruits salad d'in yamik'e, saman kujera yakoma ya zauna, ya d'auki wayarsa yana latsawa, saikuma ya ajiye ya d'auki remote ya canja tasha zuwa labarai.
Haka muka zauna tamkar kurame, shi yana kallon labarai yayinda nikuma barci 6arawo ya saceni batareda na shirya ba, to gajiya na nuk'urk'usata.
Shi duk bai farga barci nakeba harya kammala kallon labaransa ya kashe tvn, kallona yayi da nufin min magana saiyaga kamarma nayi barci a haka.
Yay d'an jim yana tunanin tayaya zai tasheni, danshi soyake ya shige yayi shafa'i da wutiri ya kwanta, a ganinsa kuma bai kamata ya barni a wajenba.
Matsowa yayi kusada kujerar, ya d'an bubbuga hannun kujerar, dama barcin nawa baiyi nisaba, na bud'e idanuna dasukayi d'an jaa a hankali, saboda barcin dana fara.
“tashi muje ki kwanta”.
Gabana ya fad'i, amma saina yunk'ura da k'yar natashi zaune.
Ganin ya nufi k'ofar futa sainaji d'an sanyi, tashi nayi nabi bayansa muka fita, bakowa falon alamun duk suntafi makwanci. Wani falon muka shiga daban kuma, gaskiya shima ya had'u, komai na cikinsa lemon green ne da milk, sai tashin k'amshin turaren wuta da air fresheners masu dad'i yake. bai tsaya ananba yay gaba, nidai ina binsa abaya kawai, munshiga k'aton bedroom tamkar nasa, saidaifa aganina nasan yafi had'uwa duk da ban ganiba, nanma komai lemon green ne acikinsa, sai labuloli milk kamar falon, shima yanata tashin k'amshin.
Juyowa yayi ya kalleni “nan shine d'akinki”. ‘yayi maganar tamkar an masa tilas’.
Uffan bance masaba, sai d'aga masa kai nayi alamar naji, shima bai sake cewa komaiba ya fice abinsa.
d'akin na shiga bi da kallo, yamin k'yau sosai, na cire alk'yabba jikina ina sauke numfashi, sanan na cire sark'a da 'yankunne da bangles d'in duk na zube saman madubi. Suma kayan na hau cirewa dan bazan iya barci da suba, sai kuma na shiga tunanin inda zan samu kayan barci? tunda lefena suna gidanmu ba'a kawoba, akwatin da'a kawoni dashi kuma jiya ban Ganshi a d'akinba, zuciyatace tabani shawarar duba wardrobe d'in dake d'akin, banyi musuba naje na bud'e, a mamakina saina ganta da kaya, sai dai duk k'ananune, kayan barcinma babu na mutunci, tamkar zan fasa kuka haka naji, da k'yar nasamu wasu Riga da wando masu sauk'in fidda tsiraici, duk da suma d'in dai sai a slow.
Gadon na hau amma saina kasa barci, kewar 'Yar uwata yadawomin sabuwa, na tashi zaune na fashe da kuka.
Ina zaune ina kukana sai kawai naga mutum yashigo min da sallama ciki-ciki.
Da Sauri na jawo gyalen dana ajiye gefe na yafama jikina, plate d'in hannunsa ya ajiye a table d'in dake jikin gadon, dan harya kwanta yatuna banci komaiba, gani yayi bai dace ya barni da yunwa ba, danni bak'uwace yanzu a gidan, dole sai an bani zanci.
Tamkar bazai tankaba saikuma ya kalleni, “mike faruwa kike kuka?”.
Wasu kwallanne masu zafi suka sake kwararomin, na sharesu da gefen gyalena nace, “wlhy ni tsoro nakeji, ban ta6a kwana ni kad'aiba, dan ALLAH ka kiramin Samha ta tayani”.
Shiru yay ya tsaya kawai yana kallona, azuciyarsa yace kajifa wannan yarinyar dawani batu, kawai saina tafi kiran Samha ta tayata kwana?. guntun tsoki yaja, Wanda yasakani d'agowa na kallesa. Ya cije lips d'insa sannan ya juyo yakuma kallona “mikike nufi da bazaki iya kwana ke kad'aiba? kin san dai babu wanda yasan manufar aurenmu, daga ni sai ke sai muftahu, dolene ki koya ma kanki iya kwana ke kad'ai d'in, sannan inason kisanfa dolene ki dinga canja behavior naki agaban mutane, domin su agaresu aurene mukayi kamar kowa, sannan ta wannan hanyarne kawai zamu iya samun wani avoidance a kan case d'inan, nasan kinada wayo dan haka saiki bud'e idanunki dan kema zaki iya zama security d'in kanki da kanki, game da zaman gidannan kam za'a samu mai koyar dake komai, dan komai a tsare yake, sauran bayani zamuyishi daga baya, kisa a ranki zaman da zamuyi dake zamane na taimakon juna irinna abota, bayan aiki ya kammala zan baki sakinki kamar yanda nayi alk'awari”.
Duk da hawayen dake neman zubo mini haka na had'iyesu, cikin aro jarumta nace, “insha ALLAH komai zai tafi yanda yakamata, kuma zaka sameni mai tsare gaskiya da amana, ALLAH yabamu nasara, ina fata da lokaci yacika komai ya bayyana zaka cika alk'awarin sakina?”.
Batare da ya kalleniba yace, “zaki sameni mai cike alk'awari insha ALLAH koda ace bamu cika shekararba komai ya bayyana zan sakeki, idan kuma ashekara 1 bamu samu yanda Muke soba zamuyi 2 ne kamar yanda nafad'a miki tun farko, amma inama addu'ar kafin shekara komai yazama done OK?, ga abinci nan kici, kiyi addu'a ki kwanta, zakiyi barci insha ALLAH”.
Batareda ya jira cewata ba yay ficewarsa, kusan mintuna biyu idona na kallon k'ofar, saikace zanga dawowarsane, mamaki yabani sosai, dama yana magana mai yawa irin haka? Kuma cikin kwantar da murya. na sauke ajiyar zuciya tareda bud'e plate d'in daya ajiye, gasashen namane mai rai da lafiya, yawu nane ya tsinke, gashi dama inajin yunwa, na mik'e na bud'e fright d'in dana gani ad'akin, ruwane kawai aciki aka zuba, guda d'aya na d'auka na dawo saman gadon na zauna, inacin naman ina hawaye, gaba d'aya kewar 'yan uwana ta gallabeni, musamman Munubiya, waya na d'auka na kuma gwada kiranta, amma still akashe, wasu hawaye masu zafi suka kuma kwararowa a kumatuna, naman na ture gefe naciga da kukana, saida nayi mai isata sannan natashi nashiga toilet d'in d'akin na wanko fuskata da bakina na d'auro alwala, a fright d'in na saka naman da sauran ruwan na kwanta kamar yanda yabani shawara, addu'ar barci nayi sannan narufe ido. tunani yace salamu alaikum, haka naita juye-juye a gadon, barci 6arawo bai saceni ba sai around 3. daga nan ban sake sanin inda nakeba saida naji ana bubbuga gefen filon danake kwance.
Da k'yar na bud'e idanuna dasuka kumbura saboda kuka da rashin isashen barci. Galadima ne tsaye a kaina, sanye cikin jallabiya ruwan hanta, tamasa k'yau dukda kallon fisha na masa.
Agogon d'akin ya kalla sannan ya juya zai fita yana fad'in “kitashi kiyi salla”.
Da k'yar na iya sauka, dan jikina duk ciwo yakemin, ga barci danake masifar ji. daurewa nayi nafara wanka da ruwa mai d'an zafi sannan nayo alwala nafito, salla na gabatar ta asuba nayi addu'oina sannan namik'e na koma gadon, dan danan barci ya kuma kwasheni.
★★★★★★★
A gidanmu bayan kwashemu dukkan amare washe gari 'yan biki suka fara kama gabansu, sai makusanta ne kawai aka bari.
Lokacin da su Ayusher suka koma sun iske innaro na zuba tijara a tsakar gida, wai an munafunceta ba ace ta fitoba lokacin da akazo d'aukata, dama tasan innarmu bak'in ciki take mata karta dangwali arzik'i, to kuwa ita k'adangaren bakin tuluce, babu yanda aka iya da ita, duk wani makirci da innarmu zata shirya mana akan karmu taimaka mata dolene tanan matsayin uwar ubanmu.
'Yan gidanmu fa abin nema yasamu, saifa aka hau dariyar gatsa-gatsa suda sauran bak'in su.
Innarmu kam murmushi kawai tayi, zuwa yanzun ita ta wuce k'aramar yarinya, dama sarai tasan bawai nadamar gaskiya innaro tayiba, kawai dai wani abu dake a ranta kawai. Ko lek'owa batayi tsakar gidanba, barema tanuna tasan da ita takeyi.
Shigowar su Ayusher da kaya nik'i-nik'i na biki da mom tabasu yasa innaro waryar leda d'aya tana fad'in munafukai, Ashe kune aka tura domin Ku tattaro komai, to ALLAH ya fiku, kafin mai biri yaga mai gona mai gona yaga biri”.
Ayusher zatayi magana mama Rabi'a ta hanata, haka suka shige da sauran kayan suna k'unk'uni.
Innaro na bud'ewa taga duk drinks ne aciki saita biyo bayansu, ledar ta dangwarar a k'ofar falon tana kunfar baki, “bazansha kayan ruwan ba kayan fitsari, yanzu-yanzu a canjamin kokuma na kwashe komai babu yanda za ayi dani dangin tsiya dangin rashin asali, kai ALLAH yarabamu da bak'ar zuciya mai cike da nunkufurci dai wlhy”.
Babu wanda ya tanka mata, Mama Rabi'a ta bud'e komai ta d'iba mata, tanuna ledar datafi kowacce girma da mama Rabi'a bata bud'eba, “to uwar iya, ita waccan ledar miye aciki?”.
Da sauri Bilkeesu ta d'auke tana murgud'a baki, “wlhy babu mai baki wannan, domin a lissafe suke, kuma mu aka bamawa bawaniba, zannuwane”.
“to 'Yar karoro, kekuma asuwa gand'oki muje biki? Aiba uban wani ya Haifa min Auwalun ba daya haifi munaya, saiki bari sai ALLAH yabaki farin jinin auren koda kansilan anguwarkune sannan kimana iyayi, kujimin bak'ar banza kawai”.
Baki Bilkeesu ta ta6e, suka ja ledar itada feena suka shige tsohon d'akinmu, yayinda su Ayusher da Ameera suka take musu baya.
Daga mama Rabi'a har innarmu babu wanda ya dakatar dasu.
Aiko sai innaro ta saka kuka wai su Ayusher sun zageta agaban innarmu batace komaiba.
Duk abinda ke faruwa 'yan gidanmu na tsaye cirko-cirko suna dariya.
Yaa Hameed daya shigo gidanne yazo har inda innaro ke tsaye a k'ofar fallon innarmu yana tambayarta lafiya?.
Cikin kuka da shar6e majina ta kora masa bayani, Kansa kawai ya girgiza, danshi lamarin innaro baya burgesa. Da lallashinsa tahak'ura tafita yarakata har gidanta da ledar da mama Rabi'a ta zuba mata kayan bikin.
Acanma zage-zage taitayi tana aibanta innarmu, kunya dukta ishi gwaggo Safiyya ga sauran 'yan biki suna saurarenta, gwaggo Safiyya fitowa tayi ta baro gidan, gidanmu tashigo tazo tana bama innarmu hak'uri.
Murmushi innarmu tayi, tace, “wlhy babu komai gwaggonsu, ai inna nima mahaifiya tace, mizaisa dantamin Abu yazama ya 6atamin rai, ai ta Isa danine shiyyasa”.
Innarmu ta bama gwaggo Safiyya tausayi, tana k'ara jinjina hak'urin innarmu a ranta, tabbas da acikin sauran matan gidanne da innaro ta magantu, dan ba raga mata zasuyiba, danma suna Shankar mazajen gidan su Abbanmu.
★★★★**•°•°•°•**★★★★
Su Munubiya amaryar yaa marwan, πbaiwar ALLAH taban tausayi, dan kallo d'aya namata nasan yaa Marwan ya ajiye muskilamci ya kashe arnaπ.
Duk takuma zama wata silent, tana kwance a falonta dayayi k'yau da tsari, hannunta dafe da kanta, idonta arufe tamkar nai barci, tunanin innarsu da kewar 'Yar uwarta ya gallabeta, gashi tun shekaran jiya yaa Marwan ya kar6e phone nata ya kashe, tayi rok'on duniya yabata takira Munaya da innarsu amma k'ememe ya hana, yadai kira mata innar sun gaisa jiya da daddare, amma munaya yace ba yanzun ba. hawayene suka ziraro ta gefen idonta.
Tun d'azun yashigo yake kanta tsaye bata saniba, tsigunnawa yayi saitin fuskarta yafara share mata hawayen, da sauri ta bud'e idonta, ganinsa yasata tashi zaune tana k'ak'aro murmushi damasa sannu da zuwa.
Bai amsaba, sai zama dayayi kusada ita yajawota jikinsa ya rungume, “haba my baby yanzu kukannan bazai k'areba? ko har yanzu wajen yana ciwonne nasake had'a miki ruwan zafin ki shiga?”.
Kanta ta girgiza masa tana kuma matso hawaye, murya na rawa tace “ina kewar Munaya”.
Tausayi ta bashi, tareda mamakin tsantsar k'aunar da sukema juna itada 'Yar uwar tagwaicinta, shikuma wlhy bayason kiran Munayar ne saboda karsu shiga hak'in Galadima, amma yanzu kam bashida mafita, yakai dubansa ga agogon falon, 11:49am, maybe zuwa yanzu sun tashi, wayarsa ya d'auka ya lalubo number Munaya yafara kira. cikin sa'a kuwa sai gata tashiga.
Mik'ama Munubiya yayi, cike da d'oki ta kar6a tana murmushi tana hawaye, shi saima abin yaso bashi dariya.
Ina cikin barci naji ringin d'in wayata, da k'yar na lalubota batareda na dubaba nayi picking kawai, a kunne na kara cikin muryar barci nayi sallama.
Daga can Munubiya ta amsa mani.
Ai zumbur namik'e zaune danjin muryar gudan jinina, “Sweetheart kece? Wlhy I Miss u so much ”. ‘nafad'a ina share hawayen dasuka ziraromin’.
Itama Munubiya hawayen takeyi, muryarta na zuga tace “miss u 2 sweetheart, I love you I love you for ever”. sai kawai ta rushe da kuka tareda fad'awa jikin yaa Marwan dake kallonta tana rera kukanta.
Hannu yasaka yana bubbuga bayanta yana murmushi, yayinda nima naketa maimaita mata kalmar I love you ina kuka.
Wayar yaa marwan ya kar6a, muryarsa kawai naji yana fad'in “to kukan ya Isa haka kema, kar Galadima yagani ya d'auka munyi miki wani abune, sai anjima idan kin nutsu masake kiranki”.
d'if ya yanke, batareda yajira amsa taba.
Sai kawai nakuma ruahewa da kuka na fad'a saman filoluwan da suke zube a saman gadon.
Galadima dake tsaye bakin k'ofar yazo dubani saboda dangin mom da zasuzo mana sallama, saiya koma da baya bai bari na gansaba, zuciyarsa tana masa tunanin dawa nake waya? har nake jera masa kalaman I love u?.
Ya d'an ta6e bakinsa, tareda kauda tunanin a zuciyarsa, to shi inama ruwansa, kwana nawane zai bani takardata na kama gabana.
Falonsa yakoma ya zauna yana jan tsakin Aiken mama Fulani na d'azun data tuna.
Yakuma jan tsakin yana gyara zamansa, dolene ya takama tsohuwarnan birki da wuri, inba hakaba tana neman Shiga masa hanci.
Abinda yafaru d'azunne da safe kusan around 7:30, yadawo daga masallaci bayan yaje ya tadani yadawo d'akinsa, zaune yake a doguwar kujera a falonsa yana azkar kamar yanda yasaba a kowacce Safiya ta duniya. sarkin k'ofane yamasa knocking.
“waye?” yayi tambayar batareda ya bud'e idanunsa dasuke a rufe ba.
Sarkin k'ofar ya amsa da “nine ranka ya dad'e, dama Amintacciyar kuyangar Fulani Ce ke Neman iso”.
Saida yaja guntun tsuka sannan yace tashigo.
Babu dad'ewa saigata kuwa, saida tayi sallama a k'ofar yabata izinin Shiga sannan ta shigo, risinawa tayi (dan ya hanata durk'usa masa saboda ta manyanta sosai) tana fad'in “barka da Safiya ranka ya dad'e”.
Idonsa yabud'e a kanta yace “kin tashi lafiya”.
“lafiya lau ranka ya dad'e, dama Fulani ce tace azo a d'auki yankin jiya”.
Bai fahimceta ba, dan haka yace “miyene hakan?”.
“ka gafarceni ranka ya dad'e, yankin farin k'yallen mutuntaka da aka shinfid'a a gadonka jiya”.
Bakinsa ya ta6e, ya maida kansa ya jingina tareda maida idonsa yanda suke, kusan minti 1 harma ta fidda ran zai amsa, saitaji yace “kije kawai, zan kawo mata da kaina”.
Idanu tad'an zaro waje saboda mamakin zancensa, amma babu yanda ta iya, kowa a masarautar yasan murd'ad'd'en hali irinna Galadima, saidai akwaishi da kirki da yawan k'yauta. ta risinar da kai, “na barka lafiya ranka ya dad'e, afito lafiya”.
Uffan baice mataba harta fice tarufo k'ofar.
Azkar d'insa yacigaba dayi batareda ya maida hankaliba.
Mom ce takirasa a waya, bayan ya gaidata cikin mutunci ta sanar masa gasunan zuwa sashensa suyi sallama, dan jirgin 1pm zasubi ya maidasu tasu masarauta.
Wannan dalilinne yasakashi zuwa Sanar min, amma saiya Tatar ina Waya da fad'in I love you ina kuka kuma, shine yajuya batareda yayi maganaba.
Kamar na sani natashi na gyara gadon fes, nad'anyi shara dukda babu wani datti, toilet nashige nayo wanka.
Ina tsaka da shiri najiwo sallamar da wata murya ketayi tun d'azun, a gurguje na shirya naje na bud'e k'ofar.
Yarane matasa a durk'ushe can gefe a falona, sai wad'anda suka d'an girme musu su biyu.
Ina fitowa suka zube suna gaidani, abinda baka saba ganiba to, duk sai kunya ta kamani, nace “please Ku tashi minene ya faru?”.
“d'aya acikinsu tace “ gimbiya ranki ya dad'e, ki gafarcemu mune masu miki hidima. ni sunana Alawiyya nice mai gyara miki makwancinki kawai da shiryaki, sukuma wad'annan zasu cigaba da sauran hidimominki, irinsu gyaran falo, girki, wanki, baki labari, da sauransu”.
Babbar jaka uba, shirinma sai anmin kamar wata 'Yar baby, nidai naga idi gaskiya, wannan wace iriyar rayuwacw haka?.
“ranki ya dad'a zamu iya fara aikinmu?”. Alawuyya takuma maimaitawa a aladabce.
Kafin nabata amsa muka jiyo gyaran murya a abayanmu. dandanan naga sun juya suna kwasar gaisuwa, jikinsu har 6ari yakeyi.
Hannu kawai ya d'aga musu, kafin yabud'e baki da k'yar yace, “miya faru ne?”.
Alawuyya takuma rissinar dakai tace, “ranka ya dad'e mune masuma gimbiya hidima”.
Shiru tamkar bazai amsaba, yad'an yamutsa fusaka yana gyara tsayuwa “wanene ya turoku?”.
“ranka ya dad'e mama fulani ne”.
Baice komaiba ya ra6a ta gefena zai wuce ciki, harya kusa shiga sannan yace, “zaku iya tafiya zan nemeku”.
Atare suke fad'in godiya muke ranka yadad'e, ALLAH ya kiyayeka, yatsare bayanka da gabanka.
To tunima yariga yashige, nikam tausayi suke bani wannan abun dasukeyi, nace “please kutashi kuje kawai”.
“to ranki ya dad'e, godiya mukeyi........
Nidai juyawa nayi nashiga d'akin nima, dan banason wannan kirarin wlhy.................✍πΌ
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*ππ»π
*_Typingπ²_*
*_HASKE WRITERS ASSO...π‘_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ceπ€π»_*
_____________________________
_Wannan page d'in na sadaukar dashi agareki Hafsat writer d'in *HAFEEZ* na gode sosai, ALLAH yabar zuminci, Bilyn Abdull na yinki irin sosai d'inan dearπ₯°π₯°π€π»❤._
______________________________
ππ»2⃣3⃣
..............A saman sofa na iskeshi zaune, ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya yana waya. Idanu ya d'ago yad'an kalleni ya janye.
kunyace takamani saboda babu ko gyale ajikina, gashi kayan sket da rigane, kamar munafuka haka nawuce inda akwatina yake da aka kawo da safe, nima farkawa nayi kawai na gansa a d'akin.
Gyale na d'auka na yafa, sannan naje bakin gadon na zauna ina sauraren wayar dayakeyi, abinda na fara lura da halayensa shine, shi mutumne marason hayaniya, komai nasa zaka sameshi a nutse yakeyi, yanzu haka a d'aki d'aya muke zaune, amma ba komai nakeji ba a maganar dayakeyi, ga jan aji tamkar wani mace, jinin mulki dake yawo a jikinsa ne ke k'ara masa k'asaita da izza.......
Gyaran muryar da yayce yasakani d'agowa na kalleshi, idonsa a kaina, Dan haka muka had'a idanu, kowa janye nasa yayi cikeda basarwa.
Saina samu kaina da cemasa “ina kwana”.
Saida yaja wasu seconds sannan yace, “kin tashi lafiya?”.
“Alhmdllh” kawai nace masa nayi shiru.
Shiru mukayi babu Wanda yasake magana, yanata aikin latsa wayarsa, nikam ina satar kallonsa da mamakin wannan halayya tashi, shi koma takura bayayi? ina dad'i dan ALLAH kai kenan kullum baki 6amπ€.
Kusan mintuna 5 muna a haka, bakajin komai a d'akin sai k'arar AC, ni dukma sanyin ya isheni. batareda ya d'agoba yace “mikike buk'ata akawo miki break fast?”.
ALLAH shi k'yauta, nafad'a a raina kafin nace, “ko miyema”.
Idanunsa ya d'ago yana kallona, baice komaiba ya janye ya mada ga wayar. sai kuma yasaka a kunne, “mom ki basu su kawo abincin ta tashi”.
Bansan mitace masaba daga can, naga dai yayi murmushin gefen baki tareda yanke wayar.
Ya kalleni yana gyara zamansa, tareda kuma shan mur alamun maganar da zaiyi important ce, “ki kimtsa su mom zasu iya shigowa a kowanne time, dan zuwa anjima zasu tafi, duk yanda dai zaki nuna musu wani Abu yashiga tsakanina dake kiyi, dan banason su tafi dawani zargi a ransu OK?”.
Duk da na fahimci inda zancensa ya dosa, hakan bai hanani yimasa kallo mamakiba, nace, “kamar ya ban ganeba fa ni”.
Shima kallon mamakin yamin, kamar zaiyi magana saiya fasa kuma, yad'an furzo huci a bakinsa kafin ya cije lips nashi da d'an k'arfi. tsaye yamike yana zuba wayoyinsa cikin aljihun ash d'in wandonsa, sannan yafara tafiya, sai da yakusan fita sannan yace, “ki nuna musu tamkar wata mu'amullar aure tashiga tsakaninmu, wannan shine kawai mafita, idan kin gama kizo kiyi breakfast”. ficewarsa ya ida yi.
Yayinda nikuma na sauke ajiyar zuciya, danni maganganun nasa duk sunzomin a cirkud'e, to mom d'in nasa ba'a gidan takeba kome? Sannan kuma ai mu yakamata muje mu gaisheta bawai ita tazoba aganina, mi hakan ke nufi?. banida mai bani amsata, dan haka namik'e a gadon ina sauke numfashi, inason kiran Munubiya amma ina tsoron yaa marwan. wayar innarmu nakira, amma a kashe, idona yacika da k'walla, murya na rawa nace “wayyo innarmu I miss u wlhy”.
jinake tamkar nayi tsintsuwa naganni a gida, dama ashe akwai randa zatazo na kwana Na tashi ba'a gidanmu tareda munubiya taba? gaskiya masu cewa aure da dad'i basuda kai wlhy, dan ALLAH ina wani dad'i anan?.
Da Sauri Na goge hawayena saboda jin maganar Samha a kaina, jikinta a sanyaye ta zauna kusada ni, nima saina yunk'ura natashi zaune ina murmushi da share sauran hawayen fuskata.
“Samha yaushe kika shigo”.
Kanta ta langa6e gefe cikin damuwa tace, “Aunty yanzu na shigo, miya sakaki kuka? ko Uncle Sam.... ne?”.
Murmushi namata, danni dariya wannan shagwa6ar tata ke bani, ko kad'an bata d'aukar kanta ta girma, “A'a Samha, ba shi baneba, ina kika shigene haka?”.
“ina nan, tun d'azun naso zuwa Amma mummy ta hanani, yanzu ma tare muke dasu mom, suna falo kisaka Al'k'yabba muje”.
Kallon jikina nayi, nace “bara dai na saka hijjab, ALLAH Alk'yabba d'inan nauyi takemin”.
Dariya Samha tayi, “lallai aunty ai Indai kina gidannan dole saikin sakata, sai dai indan kun taho india, yanzu mafa dole ki saka”.
Badan nasoba na d'akko Samha ta tayani sakawa, sannan muka fita bayan nafesa turarrurruka na masu dad'in k'amshi.
A zatona suna falona, ashe suna nashi, Samha na rik'e da hannuna tamkar wata 'yar jagora har sashensa, Wanda sai yanzune nake d'an kallon wasu abubuwan, dukda face d'ina arufe take da hular alk'yabba. Sallama mukayi a k'ofar falon akabamu izinin shiga, gabana na dukan tara-tara muka shiga, duk zatona irin sunada yawa d'innanne, saina gansu su 5 kawai, kuma duk manyane, mom kawai na gane acikinsu, sauran ban sansuba, saikuma shi boss d'in yana zaune a kujerar mai zaman mutum d'aya kamar ma yana wayane. ban zauna akujera ba sai a k'asa, mom tayi saurin fad'in “a'a d'iyata tashi ki zauna saman kujera mana”. kaina na girgiza muryata a raunane nace “a'a nanma ya isa” sannan a ladabce na gaishesu. cikeda fara'a da sha'awa suka amsa, shi kansa uban gayyar saida ya kalleni, yaji dad'in girmamawar dana bama k'annen mahaifiyarsa.
Samha ta gwargwad'ama mom magana a kunne, wai ta iskeni ina kuka. murmushi kawai mom tayi, tasan kukan bai wuce na shiga kwaryar manyaba, ga d'an nasu dagani jarumine (aikam mom ragone tunda ba abinda kike tunanin baneππ€§).
Kallon Galadima tayi dake harar Samha, “gulmammiya mikike fad'a? tashi kibar falon nan”.
Tashi tayi tana tunzura baki, “wlhy Uncle Sam ni Vance wani abuba, Mom dan ALLAH wani Abu nace?”.
Murmushi mom tayi, tace “a'a bakice komaiba”.
Batareda ya kalleta ba yace, “naji, tunda kin rakosu wuce ki tafi”.
Fita tayi tana daddaga k'afafu, yaja guntun tsuka, yayinda su mom suke mata dariya da tsokana irinta kakanni, nidai kaina na k'asa nima ina murmushin rigimar 'ya da Uba, duk dama har yanzu bansan yasukeba, naji dai tana Uncle kawai.
Bayan fitar Samha d'aya acikin matan ta kalleni, d'iyarmu cire hular kisha iska kinji, mu nan duk iyayenki ne, daina jin kunyarmu.
Babu yanda na iya, dole na zame hular Alk'yabba d'in, amma kaina na duk'e sosai yanda bazasuga fuskataba, nasiha mai ratsa jiki da 6argo suka Shiga mana daga ni har harshi, duk jikinmu sai yayi sanyi k'alau, nikam kukama nakeyi, Dan dama kad'an nake jira a ta6ani na fashe. sun dad'e sosai sannan suka ajiye min k'yaututtuka suka tafi harda shi domin musu rakkiya.
Bayan fitarsu saina shiga rera sabon kuka, saida nayi mai isata sannan natashi da nufin tafiya nawa d'akin, kallon falon nashiga yi, masha ALLAH, komai yayi a falonnan, kujerun Navy blue ne, sai labuloli da Carpet sun kasance Silver da kwalliyar k'ananun flowers blue, babu wani tarkace sosai, wani hotonsa ne yay masifar d'aukar hankalina, gaskiya hoton ya d'auku, yana sanye cikin kayan sarauta akan dokin dashima yasha kwalliya, murmushin dake d'auke a face nashi shine Yakuma k'awata tsarin hoto, ga hoton irin k'aton nanne kamar kamasa magana ya amsa maka.
Na juya na kalli d'ayan dake bangon kudu, shikam sanye yake cikin farin wando k'al da farar riga itama, ya tsuke k'ugunsa da bak'in belt, takalmansa da hularsa duk bak'ake, yana awani k'aton filine daya k'awatu da korayen ciyayi, hannunsa rik'e da wani k'arfe ga k'aramar boll a gabansa, nan ma fuskarsa washe da murmushi, har hakwaransa sun fito waje, a raina nace dama d'an wasan Golfππ» ne? kokuwa yasaka kayanne kawai?.π€
Da sauri na juyo jin motsi a bayana, sai kunya ta kamani ganinsa tsaye hard'e da hannayensa a k'irji yana kallona, gudun karya zaci kallon hoton nake sainayi saurin cewa “dama kana buga Golf? ”.
Murmushin gefen baki yayi, yatako a hankali ya zauna a kujerar dake kallon hoton, shima idonsa na kan hoton, ya d'ora k'afarsa d'aya kan d'aya....
Jin yayi shiru yasani juyowa na kalleshi, a tunanina kobai ji baneba, ido muka had'a, kowa ya janye cikeda basarwa, saiya lumshe nasa tareda jingina da kujerar, tamkar anmasa dole yace “kinason wasanne?”.
Nace, “kusan haka, duk da bansan kan wasanba har yanzun”.
Murmushi naga yayi kawai amma baice komaiba.
Nima saiban sake cewa komanba na juya zan fita. idanu ya bud'e yabini da kallo harna fice.
Yana mamakin yanda bata da tsoro, zai iya cewa itace yarinya ta farko budurwa dakan iya masa magana kanta tsaye bada wani shakkuba atare da ita.
Tabbas a wannan fagen ya yaba mata, domin takafa tarihin da manyan 'yan mata masuji da mulki da Kansu suka kasayi, akwai 'ya'yan sarakuna da yawa dakesonsa amma sukan kasa fad'a masa, sunsha shan alwashi akansa amma da zarar sun had'u dashi sai alwashin nasu ya gudu, hakama 'ya'yan manyan attajirai, kuma baisan abinda yasa sukejin shakkar tasaba, shidai kawai abinda yasani baya sakar musu fuska, to ita wannan tatsitsiyar yarinyar koda fuskar tasa takai hadarin gabas murtukewa bata Shankar masa magana, ya cige lips nashi yana ta6e bakinsa wanda shiyasan dalilin yin hakan.
★★★★★★
Mama Fulani tagama cika tayi fam da rainin wayon Galadima, ba'a ta6a angon dayay abinda Galadima yayiba a masarautar, duk randa ango zai shiga d'akin amarya za'a kai farin k'yallen dasuke kira (yankin mutuntaka) a shinfid'a agado, washe gari za'a aika a d'ako domin kowa yaga mutuncin da yarinyar takawo, sannan dolene kuma kakawota da safe ta gaida matan Sarki da Sarki kafin yafita fada, saikuma sauran jama'ar gida wad'anda suka kasance iyaye.
Amma saboda rashin mutuncin fand'ararren yaron can anje d'aukar k'yallen yace zai kawo da Kansu saboda shine shugaban marasa kunya na duniya, ta aika bayi masu hidima damata CID ya korosu wai zai nemesu, gashi ana neman k'arfe uku na yamma amma har yanzu baizo gaisuwa ba shida matarsa, sai bayintane ke sanar mata sunga yarako dangin uwarsa lokacin dazasu tafi, amma ita tunda yazi bikinnan bama ta sakashi a idonta ba sai ranar da akayi Mother's and tarbar amarya event ta gansa awajen. yaron nanfa yana shigar mata hanci da yawa fa, bari taga iya gudun ruwansa da k'arshen wutsiyar iskancinsa, ai ko ubansa bai Isa mata abinda gagararren yaronnan ke mata ba a gidannan.
★★★
Shi baima San tanayiba, Dan tun bayan fitar Munaya daga sashensa yatashi zuwa masallaci sallar azhur, ana idarwa ko yarda su had'u da Sarki baiyiba ya shiga gida, shigewarsa yay bedroom, yayi kwanciyarsa domin yasamu yad'an huta, jikinsa duk ciwo yake masa, saboda ainan-ainan na al'adar biki, dukda yasan ko Rabin hidimar da harun yayi shi baiyiba, saima ka rantse Harun shine angon wlhy.
Bai wani dad'e da kwanciyar ba barci ya kwasheshi hankalinsa kwance.
★★★★
A gidanmu ma dai bak'i kowa yakama gabansa, an barsu daga su sai su, da daddare Abba yace ashirya da safe kowacce abita da akwatunanta, shi baiga dalilin ajiya ba.
Duk sun amsa da to, amma kowacce burinta ace da ita aka kai nawa, Dan sunason suyo kallon kwaf, basu gamsu da labarin da 'yan kai amarya suka fad'aba akan gidana Dana munubiya, su a tunaninsu ma an aurenine domin a maisheni baiwa, yaushe nakai matsayin da har d'an Sarki guda mai sarautar Galadima zai gani yace yanaso, bayan lungu da sak'on hotunan mun gama zagaye duniya ni da shi.
K'ilama da gaske yagama lalatani d'in.
Haka dai sukaita gutsiri tsomarsu da kushe irinta masu hassada, duk da wasu abubuwan suna dawo kunnen innarmu batako damuba, ita dai babu abinda zatace ma ALLAH sai godiya, tunda 'ya'yanta kowanne yasamu matsugunni, yanzu saita maida hankalinta ga ibadar ALLAH da tarbiyar yaranta biyu maza dasuka rage, sune basu gajiba indai tozarcine.
★★★★★
Zuwa la'asar mama Fulani tafara k'ananun magana akan rashin nuna shaidar Munaya takawo budurcinta, dakuma rashin fitowarsu gaida mutane.
ALLAH Sarki Aunty Mimi sai abin ya dameta ganin yanda aketa k'ananun magana a masarautar, hakkane yasata nufar sashen Galadima, babu zancen jiran a mata iso, sarkin k'ofa yabata hanyar tashiga.
Tun'a falon farko daya raba sashina da nasa tace bayinta su jirata.
Babu kowa a falonsa, Dan haka ta zauna tad'au waya ta kirasa, dan batasan halin dayake acikiba, baikuma kamata tashiga kai tsayeba, balle yanzu yanada mata.
Fitowarsa kenan daga wanka saboda tashin dayayi a makare baisamu sallar la'asar ba, sai anan d'aki yayita sannan yashiga wanka. Wayar ya kalla yayinda yake goge ruwan fuskarsa, ganin aunty Mimi yasashi picking call d'in, saiya saka a Hans free yana cigaba da hidimarsa.
“my aunty kin 6uya fa”.
“na 6uya ko ka 6uya my k'ani, gani zaune ai a falonka”.
“kai haba dai? to bani kamar 5minutes na shirya nafito”.
“ok babu damuwa”.
Bai wani dad'eba yafito sanye cikin farin boyal mai shara-shara, yayi k'au sosai, sai zabga k'amshin turarensa yakeyi na koyaushe. daga shi har Aunty Mimi suka sakarma juna murmushi, ya zauna kujerar dake kallonta yana fad'in “sweet aunty na ni kad'ai”.
“anya kuwa yanzu bamu raba da Munaya ba my k'ani?”.
Murmushi yayi wadda har hak'waransa na bayyana, ya d'ora k'afafunsa d'aya kan d'aya yana gyara zama, “in haka kikeso my Aunty saiku raba ai”.
dariya tayi tace, “nama bar mata. wai kasan mike faruwa a gidannan kuwa?”.
“A'a saikin fad'a”.
“tun kafin tafiyar su mom aka fara k'ananun magana a masarautar nan, wai anzo kar6ar yankin mutuntaka ka hana”.
“mtsoww!” yaja tsaki yana jingina da kujerar da lumshe idanunsa, “Aunty Mimi dan ALLAH karki biyema wannan jahilcin kema” yabud'e idonsa akanta, ransa a d'an 6ace yacigaba da fad'in “kawai da Wanda yakai sanin sirrinka da Wanda ma baikaiba wai duk sai sun sani?, a wace ayar alkur'ani ko hadisi akace dan ka tare da matarka a daren farko sai duniya ta sani?. ita mai aiko a d'auki k'yallen ince agaban kowa na gidannan lokacin da abunnan yafaru take fad'in bakinta bazai iya maimaita k'azantar danayiba?, to kuma tunda tariga da tasan nayi k'azantar abaya miye na aiko da wani k'yallen banza da wofi? wlhy fa suka kaini k'arshe zan shuka rashin mutunci kinji na rantse”.
Shiru Aunty Mimi tayi tana kallonsa, tasan ransa yakai k'ololuwar 6aci, dan Galadima yanada hak'uri sosai, gudun kar matsala ta biyo saboda ciwonsa saita kwantar da murya, “haba my k'ani kwantar da hankalinka mana, ai abun bana 6acin rai baneba kaji, haba my habibi”.
“Aunty Mimi nagaji ne wlhy, rashin mutuncin masarautar nan yafara isata, nifa komai zan iya kawoshi karshe a wannan karon”.
Tasowa tayi ta zauna kujerar gefensa, ta kama hannunsa “please cool down mana my man, kaci gaba da hak'uri tamkar yanda kakeyi abaya, ALLAH yana tare da masu hak'uri, Momma bazataji dad'in wani Abu yabiyo bayaba, hakama Abie duk da yana a kwance zuciyarsa zatayi kunci, kansu ai sukema wa, yanzu ina k'yallen? ”.
Iska ya furzar daga bakinsa, sannan ya nuna mata bedroom d'insa da hannu.
Tashi tayi tashiga, a saman sofa taga k'yallen dan haka ta d'akko ta fito. zama takuma yi a kusa da shi, “my K'ani ina zamu samu syringe?”.
Idonsa yabud'e ya kalleta, “syringe kuma? mizakiyi dashi?”.
“Sameer duk abinda zamuyi mu kare mutuncin mahaifanmu da lafiyarka muyishi mu zauna lafiya. yanzu dai kasa wani ya kawo mana”.
Baice komaiba yajawo wayarsa yakira Muftahu, buk'atarsa ya fad'a masa sannan ya yanke wayar batareda yajira cewar Muftahun ba.
Wata hirar Aunty Mimi ta d'akko masa, tun yana basar da ita, har ya fara tanka ta, daga nan suka cigaba da hira.
Knocking d'in k'ofar akayi, Galadima yace, “waye”.
Sarkin k'ofa yace, “ranka ya dad'e yalla6ai Muftahu ne yazo yace amasa iso”.
“kace ya shigo”.
Da sallama Muftahu ya shigo, ya rissina ya gaida Aunty Mimi sannan yabama Galadima hannu suka gaisa cikin musabaha.
Ledar hannunsa ya mik'ama Galadima, “no kabama aunty mimi”.
Aunty Mimi ta kar6a ta fiddo da Syringe ta 6are daga ledar, had'awa tayi tare da Allurar sannan ta janyo charger ta d'aure tsintsiyar hannunta, Galadima da Muftahu dai kallonta sukeyi, allurar zata tsira Galadima ya rik'e “mizakiyi hakane Aunty Mimi?”.
“Sameer! wannan itace kawai mafita, kabari kawai na d'iba a saka musu, da safe saika basu”.
lips d'insa ya cije da k'arfi, yashiga kwance charger data d'aure hannunta, “ki barsa zan saka musu nawa, yanzu ma koda an saka zai bushene, dan yayi wuri ai”.
“karfa kazo ka shukani”.
“karki damu zanyi, kema kin sani ai, tunda na amsa to zanyin”.
Mik'ewa tayi tana fad'in “shikenan to, bara na duba k'anwata itama”.
Kansa kawai ya jinjina mata, yayinda muftahu yamata sallama ta fice.
“wai mike faruwa? ranka ya dad'e”.
Tsaki Galadima yaja, yay shiru kusan minti 2, har Muftahu ya yanke tsammani da samun amsa. labarin komai yabashi.
Shima Muftahu tsuka yaja, “wai dan ALLAH yaushe za'a daina jahillar al'adarnan a masarautar nan? abinda ba addini ya wajabtaba sun kama sun rik'e, kuma duk matsalar tsohuwar nan ce wlhy, masarautu nawa ne suka daina wannan abun, amma mu takafa ta tsare, ALLAH lokacin da akayi na Uncle Hayatudden, kunya abinnan yabani saboda shi kawai nata6a gani, sashe-sashefa haka akaita nuniyar abinnan a masarautar nan wlhy”.
Wani mugun tsuka Galadima yaja saboda haushi da abin yakuma bashi, fitarma da yay niya saiyaji yafasa.
★★★
Ni bansan mike faruwa ba ma, ina d'aki kwance duk kewa da kad'aici sun gallabeni, ga wayata babu caji saboda na manto cajan a gida.
Nayi zurfi a tunani naji ana sallama. firgigit nayi sannan na amsa, hijjab d'ina najawo na saka, ina k'ok'arin tashi tashigo. da Sauri na mik'e ina mata sannu da zuwa, dan nariga da na shaidata itace aunty Mimi. rissinawa nayi na gaidata, ta amsa cikeda fara'a sannan ta zauna. mik'ewa nayi na nufi freight domin bata ruwan amma saita dakatar dani ta hanyar kamo hannuna.
“no k'anwata barshi kinji, yi zaman ki, ya zaman kad'aici da bak'unta?”.
Kaina a k'asa nayi murmushi kawai, sannan nace “Alhmdllh aunty”.
“masha ALLAHU k'anwata, babu dai wata matsala ko?”.
Kai na na d'aga mata alamar babu, daga nan mukayi shiru saboda rashin sabo.
Zuwa can nace, “ina Samha?, tun d'azu tace zata dawo amma har yanzu?”.
Murmushi tayi, tace, “sun fitane itada Sauban tun d'azun, amma nasan suna hanyar dawowa kam”.
“Ayya ALLAH ya dawo dasu lafiya”.
Ta amsa da amin tana mik'ewa. har falona namata rakiya, inajin dad'in yanda take nuna tana sona.
*******
A can kuwa bayan Muftahu yafito daga wajen Galadima sai yayi murmushi, tabbas yasamu hanyar dazata zame masa tsanin *CIKAR BURINSA*, da wannan kawai zai iya cin galaba akan Galadima.
Da wannan tunanin ya hau mota yabar masarautar gaba d'aya.
Mikake k'ullawa ne Muftahu?π±
★★★★★★
Bayan sallar isha'i ina zaune ina karatun Alkur'ani Galadima ya shigo, ban daina ba saida na kai aya sannan, na d'ago domin gaidashi sainaga idonsa a kai na.
Janyewa nayi nace “barka da dare”.
Bai amsaba cewa kawai yayi “tashi ki shirya zamuje gaisuwa cikin gida”.
Nima sai ban amsa shiba namik'e kawai na maida Alkur'anin inda na gansa. tashi yayi yafita danya bani damar shiryawa. banja wani lokacin mai tsayiba nafito cikin Alk'yabba, tsaye na iskeshi a falona, batareda yace uffanba yafara k'ok'arin fita, nima sai nabi bayansa batareda na tanka d'inba.................✍πΌ
π₯³mun tafi sashen mama Fulani, maison jin yanda zata kaya saiya biyoni.
⛹π»♀⛹π»♀⛹π»♀
Barka da juma'aπππ»
*_YA ALLAHA KA GAFARTAMA IYAYENMU_*πππ»
*_Typingπ²_*
*_HASKE WRITERS ASSO...π‘_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ceπ€π»_*
ππ»2⃣4⃣
............ Tunda muka fito masu hidimar sashensa suketa zubewa suna gaishemu, hannu kawai yake d'aga musu, nikam ma ba amsawa nakeba.
Wata mota aka bud'e mana muka shiga, mamaki ya kamani, shin ba'a cikin gidan bane?. banida mai bani amsa dan haka nayi gum.
Duk da darene muna ganin bayi dake yawo tsilli-tsilli, ga ko'ina kwanyar da haske, a k'ofar wani sashi ya tsaya da motar.
Kallona ya juyo yayi, cikin muryar nan tasa ta k'asaita yace, “basai na fad'a mikiba, kinsan yanda ya kamata ace kowa ya ganmu, nan sashen kakarmu ne mai suna mama Fulani ”.
Kai na na gyad'a masa, sannan muka fito saboda anbud'e mana dama tuni.
Tunda muka fito ake kwasar gaisuwa, nikam sai binsu da kallon tausayi nakeyi, su shikenan a bautama wasu zasu k'are, basu da wani 'yancin Kansu......
Tunanina ya kakare, lokacin danaji tattausan hannunsa cikin nawa, kowannen mu saida yaji shock, nad'an rumtse idanuna, yayinda shikuma ya cije lips.
Saida aka mana iso sannan muka shiga. kata faren falone na alfarma, iyakar k'yau da tsaruwa yayi, saikace ba falon tsohuwa ba, ga k'amshin turare na musamman na tashi,.
Bafulatanar tsohuwace mai jikin fulanin asali, dankuwa akwai k'yawu iya k'yawu, tabbas wannan a zamanin k'uruciya anyi asalin k'yak'yk'awa, sai dai gajarta tamata tsiya kamπ€£π€.
A kishin gid'e take, yayinda hadimai ke zagaye da ita, kowanne da aikin dayakeyi. Shigowar mu tasakasu kowa tasaki tanemi hanyar fita kamar yanda tabasu umarni. Bai saki hannuna ba har muka k'arisa gabanta, yayinda ita kuma idonta ke akan hannayenmu dake sark'e dana juna ko k'yaftawa batayi.
Saida ya taimaka min na zauna bisa tattausan carpet d'in dake falon, gaf da mama Fulani kad'an, sannan shima ya zauna kusa dani.
“Ranki ya dad'e barka da hutawa”. Nima sai bayi saurin gaisheta.
Cikeda izza da tak'ama ta d'ago idanu tana kallonmu, a raina nace (ga wadda tafi Galadima izza ashe, ko dai itace sarkinπ±?)..
Kamarma bazata amsaba, saikuma naga ta gyara zamanta, idonta a kaina tana k'aremin kallo, “sai yanzu ka gadamar zuwa gaida mutanen saboda giyar amarci na kwasarka?”.
Wani k'asaitaccen murmushi Galadima yasaki, Wanda ban ta6a Sanin ya iya shiba, “kusan haka ranki ya dad'e, kinsan masu iya magana kance amarya kota buzuzuπ ce d'okinta akeyi, bare ni kuma mai wannan dirarriyar macen doguwa k'yak'yk'yawa abun buk'atar kowanne namiji”.
Idanu na zaro domin mamakin maganarsa, kakarsa yake fad'ama hakan?. maganarta Ce yaja hankalina itama........
Saida ta yamutsa fuska tana guntun murmushi, duk da maganar Galadima ta daki zuciyarta kwarai da gaske, ta kalleni da k'yau, “to ke dirarriyar mace abinda mijin naki yafad'a gaskiyane kuwa? dan mu bamu gani a k'asa ba”.
Gabana yashiga fad'uwa, dan bansan mizan Ce mataba, 6oyayyiyar ajiyar zuciya na sauke saboda jin Galadima na bata amsa, dukda kuma amsar tashi itama tazomin a rud'ani.
“to ranki ya dad'e miye amfanin gani a k'asan?, tunda nida ALLAH ya halattama ganin naga kayana”.
Yanzu kam a kufule tace, “a titi ko?”.
Ya murmusa yana kallona, “tunda Nina gani ai babu damuwa ranki ya dad'e, koda a titinne kuwa, bawai dole bane saike kin gani a gida ba”.
Rasama mizata cemasa tayi, sai can tace inbanga na matarka ba ai naga na Uwarka da yayar uwarka ko?”.
“well hakanefa ranki ya dad'e, amma nasan kafin kiga nasu, kema anga naki, so banga laifin hakanba ai”.
Kutt, tsantsar 6acin rai na hanga a fuskar mama Fulani kuwa, nidai kam sun d'aure kai na da wannan zantuka nasu masu kama da gugar zana, wannan dai baza'a kirashi wasan jika da kaka ba, dan baimayi kama da wasanba, nataso gidanmu na yawa da tun ina k'aramata nagama sanin miye habaici miye gugar zana ko shagu6e. tabbas naji a raina akwai lauje cikin nad'i gameda wannan masarautar, dan tundaga zuwana zuwa yanzu naci karo da abubuwan mamaki bila adadin, ashe ba'a rabu da bukarba an haifi habu kenan, nabaro guguwar gidanmu na fad'a tarnak'in gidan sarauta mai wahalar zama, ni dai ALLAH ka taimakeni komai yafita filima kafin shekara d'ayarnan na kama gabana, bazan iya da kitimurmurar wannan gidan sarautar ba gaskiya.
Mun mata sallama muka fito tana jifan Galadima da kalmar “fand'arrare mara mutunci, wlhy zanyi maganin kane, amma zan kira uwar taka naji idan itace ta baka wannan sak'on kabani”.
Baice uffanba sai murmushi daya saki yakamani na tashi, munje bakin k'ofar zamu fita yajuyo yana kallonta, salute nata yayi sannan yace, “da safe za'a kawo miki jinin budurcin matata OK?”.
Gaba nane yafad'i, da mamakin yanda yay furucin babu ko kunya bare shakka. nidai kam narasa yanda zan fassara wannan lamari, har muka shiga motar ina juya zantuttukansu a raina.
Mun isa sashen dayafi kowanne sashe girma a gidan, sannan ya had'u iya had'uwa shima, Hadimai sunfi yawa anan fiye da ko ina, anan d'inma dai gaisuwar ce aketa mana.
Mun isa wani k'ofar mai azabar k'yau, matar dake zaune a k'aramin falon farko ta rissinar da kanta tana fad'in “lale marhabin da Galadima, Gimbiya barkanki da zuwa fadar masarautar gagara badau”.
Murmushi nayi na jinjina mata kai, amma gogan naku fuska a d'inke yace “Amana iso ga mai martaba idan bai kwantaba jakadiya”.
“angama ranka ya dad'e, 6auna mai tafiyar k'asaita, bajimin zaki sa d'auka sa yak'i, magajin masarautar gagara badau........
Hannu ya d'aga mata alamar ya isheshi haka..
Ruf tarufe bakinta sannan tashige wata k'ofar, kusan mintuna 5 saigata yafito tana fad'in mu shigo.
Jama'a karkuce nayi k'auyanci, tabbas ni Munaya yau naga daular duniya, dolene sarakuna suringa tunanin kamarma bazasu mutuba, yo irin wannan daular inbakayi yak'i da shaid'anba ai bautar ALLAH ma saika bari, dole suke halaka juna akan sarauta kam lallai.
Wanda nakeda tabbacin shine sarki yana kishingid'e a kilisarsa, idonsa bisa TV yana kallon labarai, sai wata hamshak'iyar mace dake cikin ado na kece raini da alfarma zaune a gefensa, koba a fad'a makaba kasan matar sarkice.
Yanzu ma har gabansu muka isa hannun na cikin nasa, dukda mutsu-mutsun kwata danakeyi yak'i saki, saima k'ara damk'ewa da yayi, nesa dasu k'ad'an muka zauna, cikeda girmama Galadima yace “barka da dare Abba?”.
Murmushi sarki yayi, yace, “Galadima sai yanzu ake ganinka?”.
Murmushi yayi yana shafa gefen wuya alamar jin kunya, ya kalli matar yace “barka da hutawa ranki ya dad'e”.
Fuskarta d'auke da fara'a ta amsa masa..
Nima na rissina na gaidasu cikin tsantsar ladabi.
Sun kar6amin fiye da yanda nayi zato, matar tamik'amin hannu alamar na matso gareta, banyi musuba na matsa, hannuna takama tana murmushi, “yaya bak'unta gimbiyarmu?”.
Muryata a kunyace na amsa da “Alhmdllh ranki ya dad'e”.
Murmushi sarki dake kallonmu yayi, ya maida kallonsa ga Galadima da shima idonsa na kanmu. “yarona babu dai wata matsala ko? ”.
“Alhmdllh Abba babu komai”.
“to Alhmdllh ai haka muke fata mu dama, ALLAH yayi muku albarka, yabamu zaman lafiya na har abada da zuri'a d'ayyiba, wadda musulunci da Muslims zasu alfahari da ita............” Nan yashiga mana nasiha mai ratsa jiki da 6argo, har lokacin hannuna na rik'e ga matar sarki, wadda k'amshin turarenta kemin dad'i sosai a hanci.
Mun dad'e anan, dan sai kusan 9pm muka fito, tare da gagarumar k'yauta ta mukullin mota da sarki ya bani, matar kuma tace zata aikomin da tata insha ALLAH.
daga ni har Galadima munyi godiya sannan muka fito, sai juya keys d'in nake ahannu inajin wani makahon dad'i, wai nice da mota har biyu, yanzu Abbana da Dady sun samu kenan, saura baba k'arami, dan nikam babu abinda zanyi dasu, iyayena zan baiwa.
Daga nan munje 6angaren sauran Matan sarki, sai kuma na k'annen babansu Galadima d'in, mune har sashen da aunty Mimi ta sauka,, k'yaututtuka dai nasamesu sosai, harda masu sark'ok'i da sauransu, mun dad'e annan fiyema da ko ina, dan har 12 muna can, sunata hira tsakaninsu, danni dai ban iya cewa komai, sai sun sakoni ne nakanyi murmushi, musamman Sauban sarkin tsokana da Samha sarkin surutu, galadima kam ba komai yake tankasuba, shida aunty Mimi ke maganarsu jefi-jefi, khaleel ma sanda mukaje yayi barci. saida aunty Mimi tace mutashi muje sannan muka dawo namu 6angaren.
Sai da yarakani har d'akina sannan ya juya yafita batareda yace uffanba.
Binsa kawai nayi da kallo ina sauke ajiyar zuciya. Ni ban ta6a ganin murd'ad'd'en mutum irin wannan mutuminan ba, wlhy miskili yafishi dad'in zama, danshi na lura ba muskili baneba, tsabar jin kai ne kwai ke d'awainiya dashi.
★★★
Shikam har yayi shirin barci yagama yay shafa'i da wutiri maganar Mama Fulani na caccakar masa rai, ya murmusa kawai saboda takaici, ya zauna saman kujera d'akin, Syringe d'in d'azu ya d'akko da k'yallen yana jujjuyawa a hannu, wani sashe na zuciyarsa na cewa kawai yayi dabaran Aunty Mimi, wata kuma nacewa kar yayi tunda ba addini baneba, koma Dan ya k'ular da zuciyar mama Fulani, to amma kuma ita yarinyar za ana kallonta wani iri ai kuma a masarautar, harma sudunga tunanin ta zubar da mutuncinta a wajene kamar yanda mama Fulani tace, gara yayi kawai dabarar Dan fatansa harsu rabu baya son wani abu na family d'insa ya shafeta. Wannan shawarar da zuciyarsa ta yanke masa yasashi jawo charger ya d'aure hannunsa, jijiya ta bayyana, ya rintse idonsa yayinda ya tsira allurar, cikin cije lips yaja jinin kad'an sannan ya zare ya danne da auduga yanajan tsaki, charger d'in ya kwance yay wurgi da ita saikace itace tamasa laifinπ€£π€.
d'aukar gyallen yayi ya yamutsashi da hannu duk yayi Squeezing sosai sannan ya matse jinin ajikinsa yad'an yayyarfa bayan yazuba shi awaje d'aya da yawa. sai wani yamutse fuska yakeyi tamkar yaga kashi, kokuma jinin ba daga jikinsa yafito ba. ya ajiyeshi gefe sannan yamik'e yafito, a duzben d'in falo ya saka syringe d'in da kad'ar yakoma ciki, saida ya wanke hannunsa sannan ya haye gadonsa ya kwanta yana wani 6ata rai.
Nima can bayan na kammala hidimata kwanciyar nayi cikeda kewar 'Yar uwata, yauma nadad'e banyi barciba, sai daga baya ya saceni.
Washe gari bansan miya faruba naji busar algaita na tashi a k'ofar sashenmu, yayinda aketa cillara gud'e-gud'e dake tashi, ina niyar fitowa domin ganin abinda ke faruwa Galadima yashigo da d'an hanzarinsa, hannunsa d'auke da k'aramin tire da kofin shayi akai. “hau gado ki kwanta” yay maganar yana ajiye kofin a table d'in gaban gadon.
“miya farune?”. na tambaya cikin binsa da kallo.
“ok zauna tambayata har su shigo ciki, oya malama ki hau”.
Nidai duk mamaki ya isheni, kamar wadda aka make haka na hau gadon na zauna, kallon face d'ina yayi yaga babu wata alamar dawani zaiga nashiga wani hali, dolene ya canja yanayina kenan idan har yanason ya tsira daga kwakwaf d'in wannan shirmen kafin su shigo.
Kawai sainaga ya hayo gadon shima, kuma kaina yayo gadan-gadan, na bud'e baki da nufin tambayarsa dalili, kawai naji bakinsa cikin nawa. tsorone ya kamani da fargaba, sai kawai nahau dukan bayansa da k'ok'arin turesa, haka dama yakeso, yazam nayi yunk'urin kwatar kaina har nad'an jigata yanda kowa zai d'auka wahalar daren jiyanne. kuma rikicewa nayi saboda wasa daya fara da wasu 6angare na jikina,, so kawai nake na kwaci kaina awajensa, tun ina iya yunk'urin turesa harna kasa, dama nima nasan ganganne na iya da wannan basamuden mutuminπ€£π€ (munaya tafad'a ba nibaπ⛹π»♀).
Sai da yaga nayi lakwas ina hawayene kawai na daina tureshi sannan ya d'agani yana sauke numfashi, nikam saina kuma fashewa da sabon kuka, (kai jama'a Galadima akwai barikiπ±π€) yanajin takun isowar su Fulani da kirarin kuyanginta sai yayi saurin jan bargo ya rufamin zuwa cikina, yawani kwantar da murya yana fad'in “please my jannat kiyi hak'uri hakanan, kukan ya isa kinji, tun daren jiya kike Abu d'aya, haka ai kowacce mace tayi sannan tazama uwa, ALLAH dai yayi miki albarka, kifad'amin wace kauta kikeso saboda tukuycin budurcinki daki kawomin har gidana”.
Idanu nad'an zaro saboda tsorata, mi wannan gayen yake nufi? wai ko dai Galadima yana shaye-shayene ban saniba, abunda yazo yamin daban sannan yakuma d'akkomin wani zancen daban.........
Gyaran muryar da akayice yasamu waigawa ni da shi, kakarsa ce ta jiya a atsaye dawasu mutane biyu, gabana ya fad'i da matsananciyar kunyar su, Dan inada tabbacin sunji ko sunga abinda yamin, ko dai saboda su yake wannan abun? da sauri naja bargon na rufe fuskata saboda kunya.
Yayinda shikuma ya kalli mama Fulani yana wani susar gefen wuya kamar gaske, “o ranki ya dad'e kune? bar kanku da zuwa Ku shigo mana, saima Ku tayani lallashi ai”.
Matannan buyu gud'a suka callara a tare, yayinda mama Fulani ta kafama Galadima idanu, alamun tuhuma. kansa ya d'ago shima suka kalli juna ya sakar mata wani lallausan murmushi, kafin ya janye idonsa ya maida a kaina danake k'udundune cikin bargo.
d'aya cikin matan ta rissinar da kanta, cikin girmamawa tace, “Ranka ya dad'e ko zaka bamu waje mu k'imtsa ta?”.
Kallonta yayi, fuskarsa d'auke da murmushin Dana sakama suna na rainin hankali, cike da k'asaitarsa yace, “na hutasheku jakadiya, danni tun a daren jiya na gyara matata”.
Mama Fulani dake kallonsa a zuciyarta tace amma dai yaronnan d'an rainin wayone wlhy, gaba d'aya ya shirya komansa dai-dai ta yanda babu wanda koda ta k'aryata zai yarda da ita, Dan tabbas tasan duk k'arya yakeyi gameda wannan k'yallen, gashi lungu da sak'o na gidan angama nuna k'yallen, saboda ma ya raina mata wayo ba 6angarenta aka kaiba, sashen matan sarki ya aika da k'yallen, zancennan ma da akeyi ita bataga k'yallen ba har yanzun, Dan ba'a kai mataba, kowa ya d'auka daga sashenta ya fito, tunda ita ake fara kaimawa tagani sannan Matan sarki.
Had'a ido sukayi da Galadima, bakin ya ta6e mata, tareda d'age gira sannan yasaki murmushin Dake k'ular da mama Fulani aduk lokacin da yayisa.
Ta had'iye wani yawun bak'in ciki tareda kauda kanta gefe, su jakadiya kam tuni sun yi nisa wajen kar6o k'yaututtukan da kuyangin kowane sashe ke kawowa daga Matan gidan da iyaye, duk abama Munaya.
Dole mama Fulani ta k'arasa gaban gadon tasakama munaya turare da Sanya mata albarka tamkar yanda al'adar gidan ta tanadar, sannan takama hannunta ta saka mata bangles na goal masu k'yau da d'aukar idanu. Ta shafa kan munaya tana murmushin yak'e. sannan tadawo gaban Galadima shima takama hannunsa ta d'aura masa agogon Azurfa mai k'yau.
Salute nata yayi yana fad'in thanks my sweet Granny ”.
Uffan batace masaba tajuya tafice daga d'akin. yayinda su jakadiya suka take mata baya.
Suna fita ya sauke ajiyar zuciya tareda dafe kansa yana jan tsaki, nima kaina na bud'e amma nakasa tashi saboda kunyarsa data dabaibayeni.
Kusan mintuna 5 muna a haka, ni inata hawaye da jamasa ALLAH ya isa a zuciya, ga la66ana sai zugi sukemin saboda Sumbata d'inma na mugunta yamin. shikam yana dafe da kansa har yanzun yana sauraren kukan danake rairawa.
Zamansa ya gyara ya juyo yana kallona, fuskarsa a matuk'ar d'aure yace “tashi ki zauna muyi magana”.
Yanda yay maganar yasani tashi zaune batare da na musaba.
Yad'an kalleni ya janye idonsa sannan ya mik'amin Handkerchief d'insa daketa tashin k'amshi alamar na goge hawayena. Kamar bazan kar6aba dai saikuma na kar6a na goge fuskata.
Nanma shiru mukai nawasu mintuna da basufi 2 ba, nakula magana yakeson min amma yanata mulmulata a zuciya saboda jin kai, kuma d'agowa yayi ya kalleni saikuma yay gyaran murya kad'an, “em kiyi hak'uri, bamuda wata mafita sai wannan, munada wata kidahumar al'adane a masarautarnan, dolene randa katare da matarka sai kowa yasani ta hanyar ganin jini ajikin k'yallen da aka shinfid'a muku a gado. mukuma namu auren yasha banban dana saura, banida niyyar zalintarki na maidaki bazawara sannan na sakeki, inason idan mun rabu duk mijin daya aureki yasameki cikin mutuncinki, shiyyasa bazan aikata abinda suke buk'atar ba. ajiya anta surutu saboda bamu bada wannan shaidar ba, shiyyasa a Daren jiya nayi wata dabarar daban, fitowata kenan daga wanka najiyo busar algaita da gud'a alamun k'yallen yagama zaga masarautar, shiyyasa nayi azamar d'akko coffee d'in da aka had'amin zansha nanufo nan dashi, Dan Muftahu yakirani ya sanarmin zafa azo har sashena domin sanyamiki albarka da k'yaututtuka dakika samu saboda kin kawo mutuncinki, yanayin dana ganki nasan zasu gane shirina, shine dalilin yimiki wannan abun dan fidda zuciyarsu daga zargi, karki d'auka nayi mikine da niyya koki kalleni cikin mutane masu sa6a alk'awari”.
yana gama fad'a yamik'e zai yafice, nidai kaina ak'asa jinake tamkar namasa masifa amma kwarjininsa ya hanani, saida yaje bakin k'ofar zai fita sannan ya kuma furta “kiyi hak'uri, Sameer baya zalunci”. ya ida ficewarsa kawai.
Duk da na yarda da abinda ya fad'a, hakan bai hanani rushewa da sabon kuka ba, nace mugu kawai ALLAH ya isana wlhy, na shafa la66ana da da haryanzu zugi sukemin suda k'irjina wlhy, dan tsabar mugunta shine yama tsaya iya bakin amma harda wani wajen, ALLAH ya isana nidai.
π€£π€£kujifa, mutum da sadakinsa Munaya ke kiransa da mugu da jamasa ALLAH ya isaπ, yau munga auren Contract readersπ⛹π»♀⛹π»♀.
Tunda abunnan yafaru bamu sake had'uwa da shiba a ranar da yinin washe gari , kullum dai Samha kan kawomin abinci tareda kuyangin Aunty Mimi.
★★★★
Bayan sallar isha'i damuwa da rashin jin innarmu da Munubiya ya gallabi zuciyata, jinai bazan iya daurewa ba, dan haka na yanke shawarar zuwa na rok'esa ya aramin charger kona samu nayi charge wayata, duk da ma banida isashen credit aciki. na d'au turare nad'an fesa kad'an sannan nazura dogon hijjabi nafita zuciyata na d'ar-d'ar.
Na dad'e k'ofar falon tsaye ina tunanin yanda zan shiga, daurewa nayi nai Knocking, wata murya naji ta amsa sa6anin tasa, akace “waye?”.
Saida gabana yad'an fad'i, cikin rumtse idanu nace “nice”.
Galadima dake kwance cikin kujera idonsa a lumshe yana sauraren Muftahu yabud'e idonsa da sauri.
Shikam muftahu cewa yayi “bismillah ranki ya dad'e, ki shigo”.
Na tura k'ofar ahankali na shigo da wata sabuwar sallamar, Muftahu ne kawai ya amsa cikin washe baki, (yayinda k'asan zuciyarsa ke wata iriyar murna ganin shirinsa zai tafi dai-dai kenan). Galadima kam idanu kawai ya zubamin cikeda mamakin miya kawoni?.
Gaisawa mukayi da Muftahu cikin mutunci. saiya mik'e yana fad'in “ranka ya dad'e nikam na wuce, zuwa Safiya zamu k'arasa maganar kawai”.
Kansa kawai ya d'agama Muftahu n.
Muftahu ya kalleni yace “gimbiya mu kwana lafiya”.
Na murmusa sannan na amsa da “to ALLAH ya tashemu lafiya”.
Koda Muftahu yafita sainayi tsaye nakasa magana ganin ya zubamin idanu, ganin banida niyyar magana saiya nunamin kujera alamar na zauna. shima yana tashi zaune sosai.
Ban musaba na zauna.
“miya faru?”. ‘yafad'a yana zuba Hollandia fresh milk a glass cup d'in gabansa”.
d'agowa nayi nad'an kallesa, dai-dai yasaka kofin a bakinsa zai sha, janye idanuna nayi ina kuma had'e fuska. aransa yace kai wannan yarinya akwai jan ajin tsiya.
Saida naja wasu seconds sannan nace charger zaka aramin please, nabaro tawa a gida, gashi inason waya da munubiya da innarmu.
Crossing kafarsa yayi yana cigaba da shan free milk nashi tamkar bai jini ba, harna fidda tsammanin zai tanka min, sainaji yace, “ina wayar?”. yay maganar da mik'omin hannu alamar na bashi
Mik'ewa nayi na kai masa wayar ina tunanin mizaiyi da ita?.
Koda ya kar6a saiya mik'omin cup d'in hannunsa bayan yak'ara fresh milk d'in a ciki.
Na girgiza masa kai alamar na k'oshi.
wani kallo ya watsamin daya sani kar6ar dole. nadawo mazaunina na zauna, inata rik'on cup d'in amma nakasa sha, haka kawai naji hankalina bai kwanta da fresh milk d'in ba, bawai zargin yazuba wani Abu nakeba, haka kawai dai banjin sha.
Shikuma ya basar dani yanata juya wayar kawai a hannusa, basan miyake kalloba ajikinta.
Kallona yayi yace, “kin rik'e Number su?”.
“eh” nafad'a batareda na kallesa ba.
Wayarsa ya d'auka guda d'aya ya had'omin da tawan ya mik'omin, “kije kuyi wayar kawai, da safe sai a nemo miki charger d'in”.
Na tashi naje na kar6o tareda cewa “nagode” najuya nafice da cup d'in fresh milk d'in a hannu na.
Bina yayi da kallo harna fice, ya sauke ajiyar zuciyata kafin ya cije lips nashi domin jin mararsa tad'an rik'e masa kad'an.
Koda naje d'akina saina kasa ajiye fresh milk d'in, haka kawai naji kuma sha'awar nasha, nako d'aga cup d'in na shanye tas sannan na zauna ina juya wayar tasa datamin k'yau, saina tuno wayarsa daya barmin ranar idi, na ta6e bakina kawai nafara saka number innarmu..............✍πΌ
Hummm mi zai biyo baya bayan shan fresh milk kuma?. da zuwan muftahu?.π€₯
Wannan amsar sai ranar Mondayπ€«. naso yimuku wannan weekend d'in amma munada biki gsky.πππ»
*_hhhh naji k'orafinku sister's, ammafa ko pages biyu nakeyi ba isarku zaiyibaπ, wlhy bama nida time d'in yin typing 2pages a rana, saboda inada aure, akwai nauye-nauye a kaina nima, masu kuma so nagama kafin azumi suma ina basu hak'uri, bazai yuwu nagama kafin azuminba, dan azumin kad'an ya rage, kuma banason datse labarin nan kamar yanda nayi a SIYASA KO KABILANCI, zanbi a hankali na gama, wlhy nafiku son nagama nima Na huta, Dan dana fara buk zai fara cizona a zuciya nima, so kawai nake naga nagamaπ, karku manta ko tarihin masarautar su Galadima sameer har yanzu bamu saniba, Dan haka zamuyi, iya inda muka tsaya saimu cigaba bayan salla idan ALLAH ya kaimu da rai da lafiya, Dan kamar yaune ai.πππ»._*
Ngd sosai da soyayyar dakuke nunama buk d'innan, ina sonku nima har cikin raina, ina fata zaku fahimceniπππ».
❤❤❤❤❤❤❤
⛹π»♀
*_ALLAH ka gafartama iyayenmuπππ»_*
*_Typingπ²_*
*_HASKE WRITERS ASSO...π‘_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ceπ€π»_*
ππ»2⃣5⃣
..........Bugu biyu ta d'auka, jinayi tamkar anmin bishara da aljanna dan dad'i, lokacin danaji muryar innarmu tayi sallama cikin sanyinta sai kawai na Sanya mata kuka.
Ita kuma daga can batasan wayeba, a sanyaye tace “baiwar ALLAH ko bawan ALLAH lafiya kuwa?”.
Murmushi nayi, gakuma hawaye na kwaranya, nace “innarmu nice fa”.
Cikeda d'okantuwa tace, “Munaya kece? ya kuke?”.
Murmushi nayi mai sauti, nace “innarmu ina yini? inasu Aryaan? Wlhy ina missing d'inku innarmu, ALLAH kamar na dawo gida”. na k'are maganar da sakin kuka.
Kallon juna sukayi da Abbanmu, da yake girkin tane tana d'akinsa, sukama juna murmushi, Abba yace, “haba dai munaya ta jaruma ce da kuka haka? Ina aka ta6a kai mutum gidan miji yayi sha'awar dawowa gida inbada yawoba?”.
“wayyo Abbanmu I miss u so much kaima wlhy”.
Dariya suka sanyamin shida innarmu, Abba yace, “yo ga sakaran yarinya, miyeto na kukan hakan? Yaya mijin naki da jama'ar gidan?”.
“komai lafiya lau Abba, sai kewarku, musamman ma Munubiya, ALLAH ina kewarta Abba, dan ALLAH kace ya kaini na ganta”.
Yanzu kam dai su Abba sosai sukemin dariya, saikuma suka shiga tsokanata, tun ina kukan harna ware nima ina dariya, munyi hira sosai, kafin Abba yace “saida safe hakanan, karda ki k'are masa kud'in, ki gaidashi”.
Cikeda farinciki namusu sallama, da cewa zankirama gobe.
Na yanke wayar ina murmushi, Munubiya na kira itama, cikin sa'a tashiga kuwa. tana kwance jikin yaa Marwan yana d'an rage zafisaπ€«, wayar tafara ring, shine yamik'o mata, ta amsa tana kallon number, irin Special number d'in Nance, wadda zaka ganta a tsare. (π€«bara na Baku, amma banda matan aure 07000000000π)⛹π»♀⛹π»♀.
Saida ta kalli yaa marwan ya d'aga mata kai alamar tayi picking sannan ta d'aga.
Muryar Munaya dataji yasata mik'ewa zaune zumbur cikeda d'oki.
Kowa yay kewar d'an uwansa, dan haka ko gaisuwa bamu tsaya yiba muka shiga fad'ama juna yanda mukai missing. muka 6alle hira kamar zamu ga juna tacikin wayar..
Mun d'au tsawon lokaci munayi kafin yaa Marwan yasamu dole yin sallama, wayar ya kar6a ya jawo matarsa ya rungume, zatayi magana ya d'ora yatsansa a bakinta alamar tayi shiru tareda yanke wayar ko sallamar arzik'i bamuyiba.
Inajin sukur-sukur d'insu ta wayar, dan haka na tuntsure da dariya ina fad'in oni su yaa marwan Ashe dai ashe?....ππ€.
Number Fauziyya na gwada itama akashe, nace lallai amarci yayi dad'i kenan?, itama Ayusher na kira number busy, 'Yar tara, nasan tanacan itada khamees ana soyewa.
Feena ma wayarta Switch up, nad'anyi tsok'i na ajiye wayar Na tashi domin yin shirin barci, dan yau ina cikin farin ciki, tunda naji muryar families d'ina.
Tun bayan fitar Munaya kam Galadima yafara jin canji a jikinsa, a hankali yakejin wani feelings na bijiro masa, kamar wasa abufa yafara tsamari, tun yana basarwa har mamaki yafara kamashi, shin wai mike faruwa ne dashi haka? bazaice baya sha'awa ba, yanayi sosai, dan wani time d'inma saiyasha tablets, ko allurar kwantar da sha'awan, amma baita6a jin irin na yauba, k'arfin sha'awarsa yasashi katange kansa daga dukkan abinda zai iya zurmasa ga halaka har yazama hanyar tsanin aikata zina. duk da jiya yad'ansha wahala saboda abinda yafaru tsakaninsa da yarinyar can duk da shi yayine badan yaji wani abuba, amma Abu yaso zamar masa Matsala a yinin gaba d'aya, sai dai tunda yaje yay allura sai nutsuwa tazo masa.
Dauriyarsa ce take Neman zuwa k'arshe, sai kawai jikinsa yafara rawa, da bin bango yashiga bedroom d'insa, drowan gefen gadomsa yabud'e yad'iba drugs kusan uku ya watsa a baki, ruwa ya d'auka frigate ya korasu suka wuce.
Humm abanza wai man kare, maimakon yaji sauk'i saima abin ya k'aru. yadawo falo saman doguwar kujera Yakuma kwanciya bayan ya kashe AC n gaba d'aya, Dan k'ara dulmiyar dashi yakeyi.
Nima d'in agareni kusan hakane, kad'an-kad'an nafara jin tsigar jikina Na tashi.
Kamar wasa ina wanka sai Abu yafara shan kaina, abinda bansan ma'anarsa ba yafara bin jinin jikina da 6argo, na lumshe idona ina hango abunda yafaru tsakani na d'azun da Galadima, duk dani wahala ma nasha, wani feelings na tashin hankali yafara bijiromin, idanuna harsun sauya kamanni, da k'yar nayi wanka nafito, ko towel d'in ban cireba na saka hijjab Na d'au wayarsa Na fita, koda nayi sallama a k'ofar falonsa banji ya amsa ba, nayi har sau uku shiru kakeji, shikam yana kwance yana jina, amma bakinsa yakasa koda motsawa barema ya amsa min, saima muryata dake sakashin jin wani zirrr, duk sanda nayi sallamar sautin muryata na motsawa da tsigar jikinsa ne, gaba d'aya gashin jikinsa ya tashi.
Jin shirun yayi yawa natura k'ofar kawai Na Shiga abuna, azatona ko barci ya d'aukesa kokuma bai jiniba.
Ganinsa kwance saman doguwar kujera yasa gabana d'an fad'i, gawani iri dana kuma ji jikina yayi, dagashi sai boxer da vest, hannunsa d'aya dafe da mararsa, d'ayan kuma dafe da kansa, kauda kaina nayi daga kallonsa saboda tsorata da ganinsa a ainahinsa, gaskiya ba k'aramin namiji bane guy d'innan, duk kunya ta isheni, ban ta6a ganin namiji ba a haka, yo samarin gidanmu basa zama haka. duk tunanina barci yakeyi, na ajiye wayar saman cikinsa a hankali, kamar yanda naga d'ayar a ajiye, caraf ya rik'e hannuna da hannunsa daya dafe kansa, tsoro yakamani lokacin daya bud'e idonsa yana kallona, jazur idon yake abin tsoro. Muryarsa a matuk'ar sanyin daban ta6a Sanin yana da shiba yace “mi zakiyi?”. idanu na nad'an waro waje cikin tsarguwa nace, “mi zanyi kuma? wayarkace fa na ajiye maka”. ajiyar zuciya yad'an sauke, ya zuba min idanu batareda yasakimin hannunba. Gaba d'aya jikina yakuma rikicemin, jima nake tamkar Na fad'a kansa saboda abinda nakeji, ganin karna aikata abinda zanzo ina nadama saina zare hannuna dad'an k'arfi, jikinshi babu kuzarin kirki, danhaka yasaki hannun kawai, nikuma na juya nafice daga d'akin da saurina.
Lips d'insa ya cije da matuk'ar k'arfi kamar zai huda, Yakuma dafe mararsa datayi tamkar zata fashe masa, kai bazai iya daurewaba, domin zai iya mutuwa wlhy, ganin yarinyarnan kuma Yakuma birkita tunaninsa. idonsa yarigada yarufe, ya manta matsayin Auren Nasu, duk da gargad'in da wani sashen zuciyarsa yake masa akan alk'awarin daya d'auka, burinsa kawai ya sauke wannan nauyin kozai samu nutsuwa, da k'yar yamik'e ya fice zuwa d'akina.
Nikam INA zuwa na zube saman gado bayan Na zare hijjab d'in, dagani sai towel, marata data d'aure tamkar zata fashe na rik'e da hannu biyu Ina hawaye, wai wannan wace iriyar masiface ne?, nashiga uku ni Munaya, mike shirin faruwa dani ne?..
“innalillahi” kawai nake iya karantawa saboda tashin hankali, jikina harwani rawa yakeyi, ko kad'an bansan Galadima ya shigo d'akinba, dan nafad'a wata duniya ta daban, babu zato kawai naji mutum yafad'o jikina yana sauke numfashi wani na k'orar wani, wata wawiyar runguma yamin tareda matseni ajikinsa gam, kai kace cikinsa zai maidani.
Humm maimakon na turesa sai nima nakuma k'ank'amesa, banyi k'asa a guywaba wajen maida masa murtani abinda yakemin..
Daga ni harshi kowa yafita hankalinsa, dan idonmu yarufe bamusan mi Muke aikatawa bama.
Hankalina bai nemi dawowa ba saida naji Galadima na neman kasheni, duk da inajin lokacin dayake jero addu'a amma ban dawo dai-daiba, nayi nisan da banajin kira kam, saida mai gayya mai aiki ke shirin faruwane na farga.
Ina yayi Nisan da bazaiji kiranaba balle kuka da magiyata akan karya cutar dani, yatuna alk'awarin daya d'auka please, baimasan inayiba, duka, cizo, yakushi, babu kalar da ban masa ba, amma bawan ALLAH nan saida yamin biji-biji, dukkan fushinsa na shekarun baya saida ya fanshe a wannan daren.
Nayi kuka harma ba'a jin sautin fitarsa, a jama'ar gidanmu kuwa ai mutum d'ai-d'aine ban kiraba, duk tsanar innaro danayi ranar saida nakirata ta taimakeni (π€£Munaya anga idiπ).
★★★*★*★*★★★
A can kuwa muftahu Na fita sukaci karo da Harun, kallon-kallo akama juna, cikeda tsantsar mamaki Harun yace, “wai Muftahu mikake shiryawa ne?”.
Kallon rainin hankali muftahun yamasa, yagyara tsayuwarsa yana wani murmushin da bakowa zai iya fassara Shiba, “ban fahimci tambayar takaba, amma mikake nufi?”.
Harun ya d'an hararesa, “Muftahu karka rainamin wayo, tabbas nasan ni da kai duk abokan Galadima ne, bayan zumunta dake a tsakaninmu, amma shige masan dakake fiye da kowa a wannan tsakanin yana bani mamaki”.
Muftahu ya ta6e baki yana wani basarwa, kafin ya kalli Harun a wani yanayi, “Harun kana sakamin idone kenan a al'amurana? humm bazance ka bariba to, kacigaba, ni da kai d'an halak ka fasa, idan kaga dama ka kunna wutar jefani bayan kaga abinda zanyin, wannan ba damuwata baceba, inar Na cimma burina right?”.
yana gama fad'ar haka yabar wajen kawai. Yayinda Harun yabishi da kallo kawai tamkar wani soko, a zuciyarsa yana tunanin mi Muftahu ke shiryawa ne akan Galadima? tun kwanaki yakeson fargar da Galadima illar kusanta Muftahu a jikinsa, amma abin kamar wani tsafi, da Zarar sun ke6ance da Galadima to saikaga Muftahu a wajen, saikace mai gani har hanji, kenan yakamata yasake shiri akan Muftahu?.
Da wannan tunanin shima yashige mota yabar gidan, saikuma Galadima ya fad'o ransa, waya ya d'auka ya kirashi, amma saiyaji Number busy, hakanne yad'an sakashi nutsuwa, a tunaninsa ko Galadima yana wayane dasu Momma. (A time d'in Munaya Na waya da phone d'in Galadima).
★★★*“*“★”*”*★★★
Yanda ta tashi a firgice haka shima ya tashi, jikinsa ya jawota ya rungume saboda waige-waige da takeyi tana kwala kiran sunan MUNAYA!.
jinta a jikinsa saita d'an sami nutsuwa, cikin kuka tace, “yaa marwan mike faruwa da 'yar uwata ne?, nayi mafarkinta cikin mawuyacin hali tana kuka da kiran sunana Nazo Na ceceta”.
“sorry baby, ki kwantar da hankalinki mafarki ai ba gaskiya baneba, maybe shaid'anune kawai suka taswuranta hakan a gareki, amma ba d'anzun kuka gama wayaba? kofa awa 5 ma ba'ayiba da gama wayar taku?”.
“hakane yaa marwan, amma acikin awa 3 wani Abu bazai iya faruwa ba? ka kiramin ita please naji?”.
“no kiyi hak'uri, dare yayi gaskiya, babu yanda za'ayi mu kirata a wannan time d'in, k'arfe 1 fa ta wuce, 2 ma saura, karkuma ki manta tanada miji itama yanzu. Muyi addu'a ALLAH yasa alkairine, da safe saiki kirata ko?”.
Cikin share kwalla ta d'aga masa kanta, a hankali ya kwantar da ita a jikinsa bayan shima ya kwanta, yad'an furzo huci kafin yakai hannu yana shafa kanta tareda sumbatar goshinta yacigaba da bubbuga bayanta a hankali, kowa yana yin adu'a, ahaka barci ya kwashesu, duk da sun dad'e basu koma ba, musamman ma Munubiya da mafarkin yak'i barin ranta, Dan takasa yadda Munaya Na cikin k'oshin lafiya gaskiya, ka wai dai dan batada yanda zatayine ta hak'ura.
*****★★★*★★★****
Hawaye kawai nake iya zirarwa, amma kwakwkwaran numfashi bana iyawa saboda jigata, zan iya danganta abinda Galadima yayimin da fyad'e, dan baya cikin hayyacinsa ko kad'an, kamar yanda nima nawa ya gushe daga farko nabashi gudunmawa. (Nasan duk mai hankali ya k'iyasta a yanda Galadima ya zomin zai tabbatar dolene na jigata d'inπ).
Tunda yasamu nutsuwa yana gefena a kwance kawai, a hankali memory d'in brain nasa ke tariyo masa abinda ya aikata tamkar a mafarki, ya bud'e idonsa da hanzari akaina, domin kuma gaskata abinda yafarun, shin da gaskene ya aikata? “innalilahi” yashiga maimaitawa dan ganina kwance a gefensa ina hawaye, daganin yanda nake a kwancen ina fidda numfashi d'ai-d'ai kasan nagama jigata, yabi d'akin da kallo cikin tsantsar takaici, yaushema shikam yazo d'akinnan? “Hasbinallahu wa ni'imal wakil. mike faruwa danine ni Sameer? wace k'addarace kuma ta kutsoma rayuwata? yanzu nan ni Muhammad Sameer ne da wannan d'anyan aikin? miya samu tunanina haka?.......”
Tunaninsa ya tsaya cak lokacin daya jiyo dasashshiyar muryata ina kiran innarmu da Munubiya, muryata a raunane, runtse idanunsa yayi tareda mik'ewa zaune da k'yar, dan jikinsa gaba d'aya yayi week, ga wani masifaffen ciwo da kansa keyi. da k'yar ya iya kuma bud'e idanunsa a kaina, babu shiri yakuma runtsewa saboda tsorata da ganin yanda yamin, hawaye kawai yaji suna neman zubowa a face nashi saboda shi mutum ne mai tausayi, bayason yaga ancutar dawani bare kuma shi da Kansa ya aikata, jarumtar had'iyesu yayi tareda kuma bud'ewa, yazubama fuskata ido batareda ya iya cemin uffanba, yama rasa ta inane zai fara shikam, mizai fad'amin kuma a yanzu Na yarda dashi? mizai cemin shikuwa?.
Innarmu dana sake ambata murya a sark'e yasakashi saurin kallona, baisan yarik'o hannuna ba ya rumtse anasa, la66ansa sai motsawa suke amma yagaza yin magana, shi yanzu ma baisan wane irin taimako zai baniba, bai ta6a irin hirarnan dawani abokiba balle yace yasan ya zaiyi, bai ta6a aikata zinaba, zai iya rantsuwa da Ubangijin daya haliccesa bai ta6a ta6a jikin wadda ba muharramarsa ba, sai ita Munayar daya d'auketa randa yasa a sato masa ita. Kuma ko muharramar tasa bazai wuce yarik'e hannun taba shima ba kowaba wlhy, inhar kacire Samha Momma Aunty Mimi ko Mom, sukad'aine mata Muharramsa da zaice yanada shak'uwa ta musamman dasu, amma shi ko yaran masarautar nan bama kowacce zai iya ambatarta da sunanta dai-daiba.....
Rashin ya cika da tashin hankali, kukan danakeyine yasakashi waigen phone nashi, baiga komaiba, tunawa yayi ba d'akinsa baneba nan, ya saki hannuna ya sakko agadon bayan ya suturta jikinsa, jikinsa gaba d'aya ya mutu, ahaka da sand'a yakai falonsa, wayarsa dake a saman kujera ya d'auka, to inama zai dosa shikam? wazai kira akan wannan abin kunyar daya aikata? tunanin bincike a network ne ya fad'o masa a rai, maybe yasamu bakin zaren, Google yashiga yay d'an rubutu yahau Searching, amamakinsa kam saigashi sun bashi, saiya kuma wata tambayar, nanma yasamu amsa dai-dai, “Alhmdllh” yafad'a yana mik'ewa rik'e da wayar.
Inda yabarni ya iskeni, Toilet yawuce kai tsaye, yayinda nabishi da kallon tsana, nikad'ai nasan minakeji akansa, ayanda nakeji ko wuk'a aka bani zan iya fidda masa hanji waje, tabbas yanzu nakuma yarda banida wayo, yanda tun farko Na yarda da maganar wai auren yarjejeniya mukayi da Wanda yafi k'arfin ajina da matsayina, inma banda wauta irin tawa tayaya mutum kamar Galadima zai nemi kulla aure dani?, Na manta namiji zai iya komai domin cikar burinsa, k'ilama *AUREN 'DAN'DANE* yayi dani, ai sainaji wani kuka ya tokaremin mak'oshi, har ina neman shid'ewa.
Kamar yanda yaga sunsa ya had'a ruwa mai zafi-zafi, sannan yafito, ficewa yakumayi, babu dad'ewa sosai yadawo yakuma shigewa toilet d'in, ni dai idonama Na rufe gaba d'aya, dan bana k'aunar ganinsa.
Jinai kawai an kama hannuna ana k'ok'arin tadani zaune, wata azaba naji har cikin kwalwar kaina, saina fashe dawani marayan kuka Wanda yasakashi saurin sakina nakoma Na kwanta.
Runtse idonsa yayi saboda jin addu'ar danake jero masa ta neman sakayya ga ALLAH tsakanina dashi, wani bai ta6a masa makaman ciyar addu'ar nanba, amma gashi matarsa ta sunnah tana masa, duk da yasan hak'in sane ya k'ar6a agareta hakan bai hanashi jin bak'in cikiba, dan aganinsa inada hujjar masa addu'ar da tafi wannan muni, tunda Bahaka mukayi dashiba.
Cikin tsantsar damuwa ya d'aukeni zuwa bayin, yayinda nikuma nake kuka ina fad'in ya saukeni, duk da a hankali nake maganar yana jina.
Ba k'aramin daga mukayi dashiba wajen taimakona, harda cizonsa nayi a damtsen hannunasa, aiko yacizu wlhy, dan hakwarana saida suka huda lallausar fatarsa, (to dama ba wahala tasaniba fatar) amma a mamakina sainaga ko gezau baiyiba, kuma Na tabbata yaji zafin cizonnan, saidai bansan dalilinsa Na daurewaba, da k'yar ya samu nayi wankan tsarki kuwa, dan saida yakusa makeni ma dan haushi sannan nayi, harya dawo dani d'akin ban daina jera masa ALLAH ya isaba a fili da kiransa mugu azzalumi.
Duk da kalamaina suna sukar zuciyarsa haka yadake yanuna tamkarma baya jina.
Bashida maganin dasuka rubuta akan matsalata, sai dai yanada Wanda zai iya taimaka min kafin zuwa Safiya ya nemo wancan.
Haka yakawo min maganin da tea wai nasha, harara kawai Na zuba masa Na maida kaina Na kwanta batareda nako motsaba balle yayi zaton zan tashi.
Shima baice komaiba yakamani ya tayar, hannunsa da k'irjinsa nashiga bugu, ina kuma kaimasa cizo, amma k'arfin ba d'ayaba, bai barniba saida ya tadani, sannan ya wani ci uban Magani fusakarsa amatuk'ar murtuke, yace “kinsan ALLAH koki kar6a kokuma....humm”.
Yanda yay maganar kuma sai tsoro ya kamani, Na watsa masa harara kafin nabud'e bakin, da kansa yabani shayin, sannan yabani magani. mugun Ashe harda Na barci, cikin mintuna k'alilan barci yay awon gaba dani.
Sai lokacin ya samu damar sauke ajiyar zuciyarsa tareda dafe kansa dake tsananin sara masa. Duk yanda yaso yayi tunanin ya akayi hakan tafaru yakasa, saboda matsanancin ciwon da kansa kemasa, dole yamik'e zuwa d'akinsa, shima ruwan mai zafi yay wanka dashi sannan ya tsarkake jikinsa ya fito, Magani yasha ya haye gado ya kwanta shima, yasan bazan farkaba a nan kusa.
Maganin barcin da shima yashane yasaka barci suresa shima.
★★★★★(())★★★★★
Tun daga shigar Muftahu wajen Galadima har zuwa sanda ya zuba Abu cikin milk d'in Galadima lokacin daya Shiga bedroom d'insa d'aukar Abu suna kallo, har ya girgiza ya ajiye kwalin da sauri inda ya d'auka, fitowar Galadima zamansa da files d'in daya bama Muftahu Na masu buk'atar taimako a asibiti da aka kawo masa zai biya, har shigowar Munaya falon Galadima da fitar Muftahu, zamanta da kar6ar wayarsa zuwa fitarta itama, yanda Galadima yafara fita hayyacinsa har dawowar Munaya sashen takawo masa wayarsa, fitarta dakuma bin bayanta dayayi, hankalinsu ne yad'an tashi ganin yadad'e bai dawoba, gakuma a yanayin daya fita.
Hakanne yasaka aka turo wasu mata biyu da kayan fruits wai sukawoma Galadima domin suyi CID d'in yana ina?.
Sai dai sarkin k'ofa kuma yace saiya musu iso, kamar yasani saiya rufe k'ofar ta ciki sannan yanufi sashen Galadima d'in, yayi sallama tafi sau 15 amma babu amsa, ya tabbata da yana kusa daya amsa, komawa yayi yace musu ai yamayi barci, su koma dashi kawai, babu magiyar dabasu masaba yak'i bud'e musu, dan yarigada yasan komai Na kitumurmurar gidan, sannan yasan Galadima bayacin abincin kowa a masarautar, ko ankawo su yake bamawa, idan kaga yaci abincin dawani yadafa a masarautar to tabbas aunty Mimi tana k'asar, sunzo tare kotazo ta iskeshi. dan haka yahanasu shiga, harma yad'an tsargu da tunanin kawai wani Abu a k'asa ganin sun jajurce dason shigar.
Ransu a 6ace sukabar wajen, inda aka aikisu suka koma, sun Isar da abinda yafaru.
Hakan kuma yakuma tada hankalin masu Aiken nasu, domin an ruguza musu plan d'insu kenan...........✍πΌ
π€hummmm.ρ¬»Ή⛹π»♀⛹π»♀⛹π»♀
_ko Yaya za'a kwashe tsakanin Galadima da Munaya da safe kumaπ€£π€, Munaya team amin afuwaπ₯³ππ»ku kora da wananπΎπΊπ»π₯π·π₯πΈπΉππ._
ππ»
*_Masu karatu nasan kowa yamatsu yasan tarihin masarautar su Galadima, insha ALLAH zakuji, inason muzo ga6ar daya kamata kuji d'inne insha ALLAH, saura k'irisπππ»._*
Barkanmu da dawowaπ✋π».
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*π
*_Typingπ²_*
*_HASKE WRITERS ASSO...π‘_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ceπ€π»_*
ππ»2⃣6⃣
..........Da kuka na farka, duk da naji dad'in jikinna kuwa, dan banajin azabar kamar jiya, tashi nayi zuwa toilet danna d'auro alwala, na tuna labarin da wata k'awarmu ta ta6a bamu akan yanda taita ciwon jiki, saida mijinta yata mata ruwan zafi a ranar, ruwan mai d'an zafi na had'a na shiga ciki, nasha zafi kuma naji dad'i, amma inajina kamar ba a dai-daiba maganar gaskiya, haka dai nasamu nayi sallar asubahi, ina tsaka da sallar yashigo da nufin tadani, ganin na tashi ma saiya juya yafice abinsa zuwa masallaci shima.
Koda na idar kwanciya nayi saman abin sallar nacigaba da kuka na, ina kuma tunano abinda yafaru a jiya tamkar a films ko novels ko mafarki, babu abinda zuciyata keyi sai tsinemar, a yau d'inan dolene saiya bani Sakina natafi gidanmu, nafasa auren Contract d'in ma, da dai na zauna da mugunnan gwamma nakoma gidanmu nacigaba da rayuwa dasu innaro yafimin....
Tun d'azun yana tsaye a kaina, tausayina yakamashi, dan yasan shine silar kukan mawa, bayason zalunci ko kad'an, amma saigashi shine da aikatawa kuma, zama yayi a bakin gadon, cikin muryar nan tasa mai kama da anmasa tilas yace “tashi zaune muyi magana”.
“baza na masa, a zuciyata nace bazan tashiba mugu kawai, bakada abinda zaka fad'amin na yarda, azzalumi, dama abinda ka shiryawa rayuwata kenan? Dan kaganni d'iyar talakawa banida k'arfin gogayya da kai, tabbas nayi kuskuren yadda da Wanda shikansa ma bai gama yadda da kansaba, ALLAH ya Isa wlhy tunda ka ketamin mutunci har abada bazan yafe makaba, kullum cikin sallata saina sakoka da neman sakkaya ga mahaliccina akan zalincin dakami.........
A fili kuma nace, “kagama zalintata kazo kanamin mazurai da mulki, ank'i tashin”. a hankali nake maganar banyi tunanin yana jinaba, sai tsawa kawai naji ya dakamin
“k!!!!!”.
Yafad'a cikin daka tsawa, Ashe tunda nafara maganar ya rumtse idanu saboda yanda Kalmar zaluncin suke sukarsa a zicciya, ban ta6a ganinsa a wannan yanayinba, a cikin fad'a yace, “Niba azzalumi baneba, zina nayi dakene!? dazaki dunga aibantani damun duk furucin dayazo bakinki? to bara na tuna miki idan kin manta, SADAKI na biya na auroki! tun jiya kike fad'an magana amma na shareki, ni sa'an kine? wlhy idan bakiyi wasaba zan koya miki hankali! danaso muyi magana ki saurareni mana kiji mizance?.........”
Zumbur namik'e zaune, duk da azabar da k'asana kemin, na kallesa ido cikin ido ina zubda kwalla nace, “bakada abin fad'a shiyyasa bazan saurarekaba, bar ganina 'Yar talaka bana d'aukar raini wlhy, mina maka ne? miye had'ina da kai kaketa bibiyar rayuwata da bala'i, tunda na had'u da kai ban kuma samun nishad'iba, wlhy bazan yafe makab.......
Jikake bamm! ya make bakina da bayan hannunsa, cikin zazzaromin ido yace bazaki nutsuba Ashe?”.
Naji zafi sosai, dan haka nafashe dawani marayan kuka mai ban tausayi, ga wani bala'in tsoronsa daya kuma shigata, maganar ma a tsorace dama nayita, Dan tsabar bala'i na hango cikin idonsa Dana kallesa.
Kansa ya dafe da hannu, jiyake tamkar ya tariyo jiya a rayuwarsa ya goge dukkanin abinda yafaru
Ganin bazan sauraresan ba da gaske saiya tashi ya fice yabarmin d'akin.
Nakuma 6arkewa da kuka.
Koda yafita a falona ya zauna, ya dafe kansa daya koma masa ciwo k'asa-k'asa yau, tunaninsa yafara komawa baya daga jiya zuwa yau, shin miya sakashi wannan matsananciyar sha'awar ne wai? dan bai ta6a jin makamancin feelings irin na jiya ba, da sauri yamik'e yanufi sashensa, a falo ya tsaya, ya d'auki kwalin hollandia fresh milk d'in jiya yana dubawa, shi dai yasan shine last abu daya sha a jiya, to kenan koma miye daga cikinsa yake?. to amma ai ba yaune yafara shan fresh milk ba a gidannan balle yace kuma shine. kwalin ya ajiye yakuma dafe kansa, gaba d'aya tunaninsa ya kulle, dama shi indai yana cikin 6acinrai to komai nasa birkicewa yakeyi, dolene saiya kwantar da hankalinsa zai iya kamo bakin zaren. a kujerar Yakoma ya kwanta, ko azkar yakasayi yau, babu dad'ewa barci yakuma kwasheshi anan.
Itama Munaya daga kuka barci yay awon gaba da ita a wajen.
Har Samha suka kawo abinci duk barci suka Tatar sunayi, tasan halin Uncle Sam shiyasa bata tadasu ba, kad'an daga aikinsa ya mammaketa a safiyarnan.
Su duka sai wajajen 12 suka farka, kowanne yatashi da damuwarsa.
Tunda nayi takun farko nakuma tabbatar da akwai matsala, dan ruwan zafin da yaymin jiya kad'ai ya isa na daina jin zafinnan irin haka, balle kuma nima nayima kaina da safennan, amma maimakon k'asana yabar zafin saima zugi yake k'arawa, gashi idan nashiga ruwan, zafi nakeji sosai.
Yanda nake takawar ina hawayene yabashi mamaki, dan aganinsa yakamata nasamu sukuni saboda yanda yamin jiya. bansan yashigoba, maganarsa kawai naji..
“Wai mike faruwane? Ko dai kinji ciwone?”.
Wata uwar harara dataso bashi dariya na zuba masa, amma saiya danne baiyiba, takowa yayi har inda nake yakama hannuna na fisge, ya d'aure fuska shima yana hararata, “k! Wlhy kinutsu kafin na canja miki kamanni”.
“yo kammani na yaushe kuma zaka canja min? bayan Wanda ka canja min yanzu? dama haka kake? a fuska kamar babu ruwanka amma sai zalunci taf zuciyarka”.
Idonsa ya runtse dan bayason Kalmar zaluncin nan danake jifansa dashi, jinai kawai an fusgoni an zaunar a bakin gadon, nakuwa fashe da kuka ina fad'in “wayyo zafi, munubiya Azalumin nan zai kashe miki ni”.
Ko kallona baiyiba yafice, ina nan ina kuka saigashi yadawo da wayarsa a hannu, ya zauna saman sofa batareda ya kalleninba, bashida mafita saita kiran Akash, dan yanason sanin minene matsalar datake sakani wannan kukan da complain d'in zafin, yasan koya tambayeni ba fad'a masa zanyiba..
Da turanci suka gaisa, amma da zaiyi tambayar saiya canja harshe zuwa yaren daban saniba.
Akash yace saidai idan ciwo taji, dan bai kamata ace tana Complain zafi irin haka ba, zataji ciwo kam amma bawai yanda yake nuna masa yanzun ba.
Galadima ya gyara zamansa sosai yace “to ai na sanar maka fyad'e akama yarinyar fa”.
Akash yace “zata iya kai shekara nawa yarinyar?”.
'Dago ido yayi ya kalleni kafin ya janye yana fad'in “Maybe 19years ko 20 kawai”.
“ai bama yarinya baceba can sosai, inaga taji ciwone gaskiya, yakamata doctor ya dubata gudun samun matsala, amma kabada gudunmawa a hukunta Wanda yay abunnan my man, please ka kwatarma yarinyar hak'k'inta wajen azzalumin nan”.
lips d'insa kawai ya cije maganar Akash na sukar zuciyarsa, da Akash yasan shine yay aika-aikar dabai ce hakaba. sallama sukayi ya yanke wayar, saikuma yafara tunanin doctor d'in dazai nemo ya dubani, dan bashida damar fita dani a gidan yanzun.
Can doctor Hafsat ta fad'o masa a rai, ita kad'ai zai iya aminta tasan matsalarsa, dan ya yarda da ita sosai, yasan zata masa k'yak'yk'yawar fahimta.
Kiranta yayi bayan sun gaisa cikin mutunci ya fad'a mata matsalar ta yanda zai iya, dukda ya 6oye mata wacece keda matsalar ta fahimcesa, d'an murmushi kawai tayi tana girgiza kai da tausayin yarinyarnan data shiga hannun Galadima, duk abinda zata buk'ata tagama had'ashi sannan ta fito, matsalar gidansu data Sani yasakata yin shiri tamkar ba doctor ba.
Shiru d'akin yayi, sai kukana dayake fita a hankali, shikam ya zubamin idanu yana kallona k'asan ido, zaune yake k'afa d'aya akan d'aya, ya jingina da kujera, saika rantse idonsa a rufe yake, amma yana kallonane ahaka.
Bayan doctor Hafsat tazo k'ofar fada saita kirashi, dan baza'a barta kai tsaye tashigaba.
Ina kallonsa ya fice bayan ya yanke wayar daban San dawa yakeyinta ba.
Kusan mintun 20 saigasu sunshigo dawata mace, ba yarinya baceba can gaskiya, zasu iya zama sa'anni da Galadima d'in, dan haka na tashi zaune na gaidata cikin girmamawa.
Ita kuma ta amsa cikeda fara'a.
Kallon Galadima tayi dayake tsaye yana kallonmu, “ranka ya dad'a kozaka bamu wajene”.
Murmushi yad'anyi yana fad'in babu damuwa.
Yana fita matar ta zauna kusa dani a bakin gadon, fuskarta d'auke da murmushi tace, “sunana doctor Hafsat Abu, friend d'in Galadima ce tun a primary school”.
Murmushi nayi mata na yak'e kawai.
Takuma gyara zamanta tana kallona, please dear karkiji nauyina, ki fad'amin matsalarki kai tsaye, dan ba'a wasa da wannan matsalar, takan zama babban Abu anan gaba ga d'iya mace”.
Kai na jinjina mata ina hawaye, sannan nace “inajin zafin wajen sosai”.
“ok kozaki iya kwanciya nagani”.
Ido na waro waje a tsorace, sai kuma nayi k'asa da kaina saboda kunya.
Tayi murmushi tana kama hannuna, “karkiji kunya akan lafiyarki dear, please ki daure kinji”.
Kai kawai na gyad'a mata sannan na kwanta, babu yanda zanyi dole na yarda ta duba, kanta kawai ta girgiza da mamakin Galadima, saikace Wanda ya kusanceni da k'arfin tuwo?, ai wannan kam da wani doctor d'inne saiya yima Galadima fad'ama wlhy, dan ko kad'an bai bini a hankaliba, amma ciwon daya jimin bazai zama mai cutarwa ba insha ALLAH.
da kanta yanzu ta had'amin ruwan zafi tazuba wasu magani, sannan ta taimakamin har zuwa bayin ta nunamin yanda zanyi. ban cutar da kainaba na nutsu nayi komai yanda tace, dukda inajin zafi kuwa, bayan nafito saina sameta zaune ta gyara gadon tsaf, gakuma abinci a ajiye, da alama Galadima ne ya kawo, tsareni tayi da lallashi naci abincin ma yanzun, sannan tabani magunguna nasha, ta kalleni da murmushi, “ALLAH yak'ara lafiya gimbiyarmu, indai zaki cigaba da kulawa kamar yanda na nuna miki insha ALLAH nan da 2days zaki dawo normal, ga drugs d'inan saikina sha, shima wannan cream d'in kina matsi dashi awajen a koda yaushe”.
Kaina na jinjina mata sannan nace “ nagode Aunty”.
Sallama tamin tafice.
A falo ta iske Galadima, bayan tamasa bayanin yanda yakamata a kula dani saita kallesa cikin tsokana, “ranka ya dad'e kafayi 6arna gaskiya, Shifa wajenan ba a nuna masa k'arfi, please a kiyaye”.
Murmushi kawai yayi baice mata komaiba.
rakiya yamata tareda mata alkairi sannan yadawo.
A kwancen data barni ya iskeni, zama yayi gefen gadon yad'an kalleni ya janye idonsa “yaya kikeji yanzun?”.
Baki na turo masa, amma ban tankaba. shima bai damu da amsawar tawaba, ya basar kawai ya d'akko wata maganar.
“nasan babu abinda zan fad'a ki yarda dani tabbas, sai dai zankuma maimaita miki SAMEER BAYA ZALUNCI, koda wasa ban ta6a kawo zan aikata hakan agarekiba har kibar k'ark'ashin kulawata, bansan miya shiga kainaba a jiya”.
Kallonsa nayi ina hawaye da takaicin maganarsa, nace “bakasan miya Shiga kankaba ka d'auki fresh milk kabani? bayan kasan mika zuba”.
Shima kansa ya d'ago yana kallona, cikeda k'asaitarsa yace “ban fahinceki ba, mikike nufi? dan ina son na kusance ki sainayi amfani da wani abu? da hakan naso daret zanzo gareki tunda nasan nabiya sadaki ai, tunda ba tsoranki zanjiba ko?”.
“dama ai bazaka fahimceni ba tunda Kasan ka aikata ai, kuma ai alk'awarin zama tamkar abokai kamin ba irin wannan ba”, na had'e hannuna alamar rokoππ» ina kuka nace “dan girman ALLAH ina rok'onka kabani Sakina a yau natafi gidanmu, wlhy nafasa auren Contract d'in, koma waye yayi abun ni na yafe masama, kawai ka sallameni”.
Yama rasa mizai cemin shi, ajiyar zuciya yad'an sauke, kafin ya cije lips nashi, “shikenan, zan miki yanda kikeso, amma kibari ki warke, bai kamata ki koma gida ahakaba”. ‘yana gama fad'ar haka yatashi yafice batareda yaji amsa taba.
Duk da naso yabani sakina a yau, amma zanyi hak'uri na warke d'in kwana nawane.
******
Yinin yau haka mukayishi duk zukatanmu babu dad'i, Galadima kam ai ciwon mara saiya nemi dawo masa sabo, jiyayi kawai yana sake buk'atar kasancewa dani, haka yayta dannewa har zuwa dare, dan bazai kuma yarda yin gangancin nanba. ganin yana neman mutuwa yay shiri a gaggauce yafito domin zuwa hospital.
Tunda yafito suke zubewa gaisheshi, hannuna kawai yake iya d'aga musu, dan kallo d'aya zaka masa ka tabbatar yanada damuwa, da sauri sarkin mota yazo yabud'e masa ya shiga, suma dogaran dakan bisa idan zai fita sai duk suka taso.
Tundaga fitarsu gidan Muftahu na kallonsu, yad'an murmusa kawai abinsa. (πwlhy Reader's suka kamaka zaka gane bakada wayoπ‘)
Shi kad'ai yasan azabar dayakeji a jikinsa, yana kwance cikin kujerar ne sai faman cije lips yakeyi.
Tunkan sarkin mota ya tambayama ya sanar masa asibitin da zasuje.
Sarkin mota ya amsa cike da girmamawa da tausayin shugabansa, dama shi tunda yaga yafito ya fahimci akwai matsala.
Tun amota yakira wata number yana tambayarsa ko yana asibiti?. Dr Jalal ya amsa da eh yana nan.
Yanke wayar yayi kawai baisake cewa komaiba. Dr jalal yabi wayar da kallo yana mamakin Galadima da halinsa, kiransa yakuma yi shi dan bai fahimci inda maganar tasa ta dosaba. sai dai harta yanke bai d'aukaba, yana k'ok'arin sake kira yaji ana Knocking d'in k'ofar.
Amsawa yay da yes tareda izinin shigowa.
Wani dogari ya bud'ema Galadima k'ofar yashiga, da hanzari Dr Jalal yamik'e yana murmushi da masa welcome.
Hannu kawai ya iya d'aga masa ya zauna kujerar gaban decks d'in.
Shima Dr jalal saiya zauna, “ranka ya dad'e lafiya dai ko?”.
Saida yaja wasu Seconds sannan yafara ma Dr jalal bayanin damuwarsa, ya sanar masa mararsa namasa ciwo tun jiya, kuma ada bata masa kamar hakan.
Shiru Dr jalal yay yana nazarin maganar tasa, saida yakai aya sannan yace “ranka yadad'e kokasha pills ne?”.
Kallonsa Galadima yayi, “pills kuma? wane irin tambaya kakemin haka?”.
“afuwa ranka ya dad'e, matsalar taka tayi kama da wanda yasha tablet ne, mikaci na k'arshe jiya?”.
cikeda nazarin maganar Jalal yace “fresh milk ne last abinda nasha jiya da daddare”.
“to amma bayan shi kafara jin matsalar?”.
“kusan haka gaskiya”.
Dr jalal dai shiru yayi, dan ya tabbatar wannan aikin desire tablets ne, amma koya fad'a dawuya Galadima ya yarda, sai kawai yashare ya had'a masa drugs da injection yamasa, yace yad'an kwanta na kamar 20 minutes a office d'in. bai musa masaba ya shiga inda jalal kan huta idan yaso, saiya kwanta kawai, dan shima bazai iya tafiyarba, d'akin ma da taimakon jalal d'in yashigo.
Ni bansan hidimar da akeyiba, dan rabona dashi tun bayan munyi maganar saki, abinci ma tun Wanda doctor tabanine a cikina, sai kusan 8 Samha takawo min kayan fruits dawani Abu mai dad'i daban san minenebaπ.
Ta zauna mund'anyi hira kafin tafice. a bakin ta nakejin wai jibi Friday zasu koma India.
Na danci abinda takawo nasha magani nayi kwanciyata cikeda kewar 'Yar uwata dana kanyi akowanne dare.
Galadima kam bai dawo ba sai kusan 1pm, yana shigowa sashensa yawuce yay shirin barci ya kwanta, Alhmdllh zuwa yanzu yaji k'arfin jikinsa, sai dai zuciyarsa nata cud'a masa tunanin ina yasamo pills? dan shima yafara yarda da maganar jalal, musamman idan ya tuno furucin Munaya na d'azun da safe.
To kenan wani ya zuba masa bai saniba? to amma wazai zarga shikam? duk wad'anda suka shigo wajensa a jiya amintattun sane, Sauban, Samha, Harun, Muftahu, duk sun shigo wajensa a jiya, amma Muftahu shine last shigowa, shiru yay yana nazari, can kuma saiya cije lips d'insa ya lumshe idanu yana shafa gurin Dana cijesa.
A haka barci ya kwasheshi.
★★★★
Munubiya tashiga damuwa sosai akan rashin jina a waya, takira number ta yafi sau goma amma switch up, gashi yaa Marwan ya hanata kiran number dana kirasu a ranar, yace wai number Galadima ce bai kamata su damesa ba.
Haka taci kukanta a yinin ranar, saikace mara lafiya haka ta yini, zuwan su Ayusher ne ma yad'an sanyaya ranta har suka janye mata hankali da yawan tunani, a ranar gidan suka yini cir, sunsha hira da labarina, kowacce tana missing d'ina.
Sunce suna son zuwa amma an hanasu, wai gidan danake ba gidan da ake zuwa any how bane ba, babu yanda suka iya haka suka hak'ura.
*********
A gidanmu ma yau sukayi niyyar kawo min akwatinana da abinda ba'a rasaba, amma ankira wayata akashe, wannan yasa Abba yace abarni akaima su fauziyya nasu. ni daga baya idan an sameni akai min nawa d'in.
Duk inda akaje da innaro ake zuwa, kowacce ta taima gidanta kallon kwaf kenan, sotake taga gidan wacce tafi acikin sauran 'yan uwana.
ALLAH ya taimaki munubiya lokacin dasukaje gidanta yaa Marwan yana gidan, hakama su Ayusher.
Fita yayi yasiyo musu abubuwa yakawo, sannan suka zuba musu girkin da sukayi, babu ko kunya suka mik'e kafafu suka ci abinsu, to dama gidan Fauziyya ne kawai suka samu sukaci abinci, su Safara'u kam casukai basu fara girkiba, dan ita haleematu ma ruwa wannan bata basuba, banda innarmu akaje, dayake kowacce idan za'aje gidan 'yarta banda ita ake zuwa.
Zasu taho kuma yaa Marwan yabasu kud'in mota, dukda kuwa a mortar Dady yaa Anas ya kaisu.
Tunda suka dawo gida aka shiga labarin yanda aka iske gidan kowa, nanfa wad'anda gidan 'ya'yansu ba'a samu wani abun kuzo aganiba sai suka fusata, kunsan dai halin jama'ar gidan namuπ€£, wannan Abu saida yakawo rikici, fad'a sosai sukasha abinsu, itadai innarmu k'ala bata ceba, saima ta maida hankalinta ga girkin dare datakeyi, ga innaro sai habaici takeyi, saida gwaggo Safiyya tazo da k'yar ta lalla6ata tafita.
Matan anguwa makwafta kam sun masa kunne suna saurare da kwasar dariya, dan lamarin gidanmu yazama kamar na 'yan wasan kwaikwayo.
Duk tsiyar dasukeyi dady yana gidan yana jinsu, amma ko lek'owa bai yiba, danshi bashida hayaniya ko kad'an, balle daya fahimci abin yashafi 'yan bani na iya d'in gidan ne, dariya kawai yayi yace ALLAH ya k'yauta. kad'anma kenan ai, bakuga komaiba tunda yanzu kuka fara aurarwar, kuma har yanzu da sauran 6ur6ushin amarci ga yaran harsu Aunty khaleesa kam dake cikin watanni na hud'u da auren.
★★★★★
Alhmdllh yanzu kam naji dad'in jikina, dan ko ciwonma banaji, sai shirye-shiyen kayana nakeyi dan yau nakeson tuna masa batun sakina, tun shekaran jiya rabona da ganinsa, harma na d'auka baya gidan sai d'azun da safe Samha take cemin ai tare suka fita itada Uncle Sam da Sauban birnin gayu da asibiti zagayen marasa lafiya, sune har Asibitin mahaukata, tace duk atsorace take ALLAH yasa kartayi mafarki.
Ni dariya ma tabani yanda take bani labarin kamar a firgice take.
Komai nagama had'ashi tsaf, Galadima kawai nake jira, amma abin haushin har kusan 4pm babu labarinsa, gani nayi zan zauna jiran gawon shanu, dan haka na mik'e zuwa sashensa.
Nayi sallama yafi 7 amma babu amsa, sai kawai natura na shiga, a zatona rainin wayonsane da mulkin ya motsa, babu kowa a falon sai wani k'amshi dake tashi na musamman, ko ina kuma need a gyare,, a yanda naga yanayin falon kamar babu kowa a sashen gaskiya, dan komai akashe yake har AC, dawuya kuma yana nan kaga AC n sa a kashe, duk da haka saina d'an zauna ina k'arema ko ina kallo, kai kace yau nafara shigowa, hotunansa da bana gajiya da kallo naketa kallo yanzun ma, idona nacikin zageye-zagaye saina hango wani k'aramin frame na photo, bana ganin mutanen jiki sosai dan haka namik'e tsaye, ga hoton na isa, yana a kusurwar d'akinne ta gabas, saman wani d'an katako da aka k'awata wajen, bayan foton akwai flower babba mai k'yau, sai aka jigina hoton jikin flower d'in.
K'yak'yk'yawan mutum ne ajiki Wanda kallo d'aya zaka masa ka hango tsantsar kamaninsa da Galadima, saikuma mace a gefensa itama masha ALLAH, Galadima kuma yana satar kamanninsa da ita, musamman idonsa ha6arsa dawasu abubuwa, saikuma wadda nake k'yautatama zaton aunty Mimi Ce kusada matar, shima namijin ina tunanin Galadima ne, yana cinyar mutumin, bazai wuce 5 to 6 years ba a picture d'in, Anty Mimi kuma bata wuce 10 ba, sai tsohon ciki ajikin matar, dukda ban saniba sainayi tunanin iyayensane, duk cikin kayan sarauta suke.
Samha ta fad'amin iyayensa suna india, Abbansa bashida lafiya, ban wani tambayeta komaiba, iyanan naji kawai.
Hoton na maida na ijiye ina murmushi, sun birgeni gaskiya sosai, flower d'in nabi da kallo, itama tamin k'au, gawani k'amshi mai dad'i datakeyi, kuma nalura da dare kamar tana wuta haka. Hannuna na kai na ta6a ganye d'aya ajiki, sainaji Ashe ta roba Ce ma, mamaki ya kamani, banyi zaton ta roba bace wlhy, dan tayi k'yau.
Har zan bar wajen, kamar ance na d'aga kaina saman p.o.p d'in ta jikin kusurwar sainaga tamkar CCTV camera, amma bakowa zai iya fahimtar hakanba, domin ansata cikin tsantsar kulawa, gabanane yafad'i, nayi azamar kauda idona tamkar ba ita nake kalloba, saina d'an gyara zaman flower d'in kawai nabar wajen zuciyata na tsitstsinkewa, toshi miye nawani saka CCTV camera a falonsa?, komawa nayi na zauna, zuciyata nawasu tunane-tunane daban.
Sai lokacin tunanin koma bayanan yazomin, abinda Nagano ya hanani lek'a bedroom d'insa, dan nasan zai iya ganin komai ta CCTV camera d'insa.
Sai kawai natashi na fice nakoma nawa d'akin.............✍πΌ
Hum masu karatu kuna zaton Galadima bai fahimci Muftahu namasa zagon k'asaba kuwaπ€?. kuduba yanda ya shashantar da binciken ya akayi yasha desire tabs a fresh milkπ€.
To koma dai miye kumuje zuwa, ai masu iya magana kance *Karshen alewa k'asa*πππ».
Humm ya kuke ganin sakin da Munaya ta nema? Shin zata samu? kokuwa zai bita bazai bayarbaπ€?.
Kumuje zuwa dai a page nagaba my guysπ₯³⛹π»♀⛹π»♀⛹π»♀
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*πππ»
*_Typingπ²_*
*_HASKE WRITERS ASSO...π‘_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ceπ€π»_*
ππ»2⃣7⃣
...........A gajiye yadawo gidan, daga masarautar su papi yake, dan shine yamasa kiran gaggawa a daren jiya, yau tunda safe ya tafi, dan jirgin 7am yasamu, shine sai yanzu yake dawowa.
Saman kujera ya zube yana furzo iska, sarkin mota daya biyoshi dawasu kaya ya ajiye, yana niyyar fita yajiyo maganar Galadima d'in. tsayawa yayi yajuyo yana kallonsa.
idonsa a rufe yace, “kunnamin AC ”.
“to ranka ya dad'e”. sarkin mota yafad'a yana risinar da kai alamun girmamawa.
Ya dad'e zaune a wajen idonsa a rufe, jin ana kiran salla a masallacin masarautar yasashi mik'ewa da k'yar yanufi bedroom d'insa. makunnar fitilar ya laluba, haske ya gauraye d'akin, komai normal kamar yanda yabarsa. anutse yafara zame sky blue d'in shaddar jikinsa. wanka yashiga, bai 6ata lokaci sosai ba yafito, jikinsa ya goge tsaf yajawo jallabiya fara tas mai dogon hannu yasaka, tamasa k'yau sosai, yad'an fesa turare yafita da hanzari jin za'a tada sallar magrib.
Nagaji da jiransa har zuwa magrib, bansan hawaye sun fara bin kumatuna ba, ahaka nayi sallar magrib, nayi alk'awarin ko yanzu yazo yabani sakina a gidanmu zan kwana, bayan na idar yau ko doguwar addu'a banyiba nadawo kan sofa na zauna tareda rabga tagumi na zubama akwatina idanu.
A wannan yanayin yashigo ya sameni, cikeda mamaki yake bin akwatin gabana da kallo, shi yama manta dawani maganar saki da mukayi.
Ban San ya shigoba saida yad'an bubbuga hanun sofa d'in, firgigit nayi ina kallonsa, bansan murmushi ya su6uce minba da ambatar Alhmdllh.
Idonsa ya janye a kaina ya zauna bakin gadon “lafiya na ganki da trolley?”. Yay maganar cikin kuma d'aure face.
Nikam ban damu da yanayin nasaba na rashin walwala, dan narigada na fara sabawa ma da hakan, nad'an murmusa ina ta6e baki, nace “kayan tafiya gida na had'a”.
Yi yay tamkar bai jiniba ma, ya zaro wayarsa dake ring yana kallo, a mamakina sai naga yayi murmushin gefen baki tareda saka wayar a kunne. “Amincin ALLAH ya tabbata a gareki my Momma”.
“tare dakai Muh'd d'ina, yakuke? Ina d'iyata?”.
Murmushin yakuma yi tareda satar kallona, yace, “gata a gefena Momma, Yaya jikin Abie?”.
“jiki Alhmdllh wlhy, yaushe zaku tahone? kun barmu mu kad'ai nida jakadiya”.
“kai Momma duk kuyangin gidanann kice kuna cikin kad'aici?”.
“to Muh'd ai d'a dabanne a zuciyar iyaye, musamman ma mu damuka k'agara muga sabuwar d'iyarmu”.
Bakinsa yad'an ta6e yana murmushi, “karki damu Momma zaku ganta wataran, amma su aunty Mimi ai inaga gobe zasu taho jirgin darema suka samu”.
“haka tacemin, amma kufa to? dan banjiKu a lissafin masu tahowaba?”.
“nima insha ALLAH zan biyo bayansu bada dad'ewa ba Momma, dan nayi missing d'inku, bazan iya gama hutuna ananba gaskiya”.
“ita kuma d'iyar tawafa?”.
“nan zan barta mana Momma, duk k'arshen wata zanzo na ganta kamar yanda na saba”.
“lallaikam, to yanzu dai saika nemi tickets kafin Safiya, gobe idan ALLAH ya kaimu kutaho dasu Haneefa domin takawa yaga d'iyarsa, idan kun k'are hutun tare anan zuwa k'arshen watan saika maidatan”.
Tunda tafara maganar gabansa yafad'i, yawani marairaice murya tamkar yana a gabanta, “please Momma wannan shawaran kumafa? dan ALLAH karkice haka ba yanzu ba sai nan gabafa zatazo?”.
“to nidai nagama magana Muh'd, za6i kuma yarage naka ai, bani ita mu gaisa time d'in gogema takawa jiki yayi zan shige”.
Ransa a 6ace yamik'omin wayar, banyi magana ba na kar6a dan naji yana Momma ai nasan mahaifiyarsa ce. gakuma yanda yaketa kwantar da murya irinna ladabi da shagwa6a.
Cikin nutsuwa da tsantsar girmamawa na gaisheta, daga can ta amsa min cikeda kulawa, bayanin daya firgitani naji tanamin, na waro idanu waje cikin tashin hankali, amma sai na kasa musa mata, na shiga amsawa da to cikin rawar murya.
Duk da AC d'akin zufa nakeyi, nida ke shirin fecewa gidanmu yau da takardar saki amma shine ake rok'ona nayi shiri gobe zamuje India, na taresu ni Munaya, ban kuma fahimtar dukkan sauran zantukan nataba, sai maganar k'arshe naji datace nabashi wayar.
Murya na rawa namata godiya da Addu'ar samun lafiya ga abban su Galadima, taji dad'i sosai kuwa, dan har sautin murmushinta ina jiyowa, hannuna har rawa yakeyi namik'a masa wayar, yana kwance idonsa a lumshe, damuwace a fuskasa karara, muryata na rawa nace, “gashi tace abaka”.
Batare da yabud'e idonba ya kar6a, a kunne yasaka wayar, cikin kwantar da murya yace “haba sweet Momma na a sassautamin mana”.
Murmushi kawai tayi daga can, tace “ai iya sassaucin dazan maka kenan Muh'd, gobe idan ALLAH ya kaimu ka kaita gidansu tama iyayenta sallama da 'yar uwar tagwaicinta”.
“amma Momma..... ”
“kasan banason maida magana baya ko? kayi yanda nace kawai”.
Shiru yay bai iya cewa komaiba harta yanke wayar gaba d'aya.
Ransa a6ace ya tashi zaune, wayar Harun ya kira, yana d'agawa ko gaisuwar bai amsaba yace, “Harun inason tickets guda biyu na India”.
“lafiya dai ko Galadima?”.
“Normal” kawai yace ya yanke wayar.
Harun ya girgiza kai, dan yaji alamar ransa a 6ace yake.
Mintuna basu wuce 5 ba yakirashi yace an samu naka, sai dai ita kuma batada passport ai, dolene da safe sai Anje anyo, amma na darene jirgin.
“yayi” kawai yace nanma yay shiru.
Harun nason masa wata tambayar amma babu dama, sai kawai ya yanke wayar.
Nidai ina dafe da kai abin duniya dukya isheni, shikenan an ruguza min plan d'ina.
Tashi yay yafice batareda ya kuma ko kallona ba, ban damuba, dan nima tawa ta isheni, yana fita hawayen bak'in ciki suka zubomin a fuska, ban samu damar sharewa ba na zame na kwanta a sofar.
Yana fita sashen mai martaba yaje, bayan jakadiya tamasa iso yashiga, gaidashi yayi cikin saisaita yanayinsa kafin yamasa bayanin zai koma India gobe, saboda kiran gaggawa daya samu daga doctors d'in Abie.
Fatan alkairi mai martaba yamasa, kafin ya tambayesa maganar nikuma fa.
Kansa a k'asa yace, “ranka ya dad'e da ita zamu tafi, idan komai ya dai-daita saina maidota”.
“to shine nan, hakan yayi ai” nasiha sosai mai martaba yayi masa, tareda jan doguwar addu'a wa jikin Abie, ya dad'e a can sannan yafito.
★★★★
d'ayar wayarsa daya manta a kan gadona tashiga ring, ban d'auka ba harta tsinke, aka kuma kira ta yanke, saga nan ba'a sake kiranba, tunanin kiran Munubiya ne ya zomin, Dan haka na tashi zaune ina share hawayen fuskata na d'auki wayar nasaka number, Dan na haddace ta akai, harta tsinke bata d'agaba, saida na sake kira sannan tad'aga.
Acikin rashin sanin wanene tayi sallama a d'arare, amsawa nayi ina jan ajiyar zuciya, cikeda d'oki tace, “Sweetheart kece? ykk?”.
“lafiya lau munu...., ke kad'aice a gidan dan ALLAH”.
“eh nikad'aice yaa marwan bai dawo masallaciba. miya farune?”.
“magana zamuyi Munu.... amma kiyi hak'uri da 6oye miki da nayi tun farkon matsalar, banason ki tashi hankalinkine shiyyasa” tun daga farkon maganar aurenmu da Galadima a randa suka saceni har zuwa yau ban 6oye mata komaiba, inayi ina kuka, itama daga can kukan takeyi harda shashsheka.
Cikin Jan aziyar zuciya tace, “Naso nafahimci wani Abu tunkan aurenmu, amma ganin bakicemin komaiba na share, banga laifinki ba na aminta da auren yarjejeniyar kamar yanda ya buk'ata, domin kowaye a irin matsayinki abinda zaiyi kenan inhar yana tausayin iyayensa. Abu d'ayane gaskiya sai naga kamar bazai aikataba”.
“mikenan?”.
“Saka miki desire tabs dakikace, kiduba yanda kikace yadamu sosai, Munaya kofa saka mikin yayi babu laifi, tunda hakinsane, sadaki yabiya ya aureki, inma banda wautarki koda auren Contract d'inne kukayi ai ba'a fatar sakin ko. atunaninki innarmu wane tashin hankali zata shiga idan ance aurenki ya mutu cikin kwanaki 5 kawai da arenmu, ni yanzun shawarar dazan baki ki kwantar da hankalinki kuje India d'in, ki duba mahaifinsa, saikiga tarbar da parent nasa zasu miki, daga nan samu san mafita, idan sakin zaki nema kinga saiku rabu, idan kuma zaki iya zama da shine shikenan, saimuyita addu'ar ALLAH ya dasa masa sonki a zuciya”.
“Humm, Munubiya kenan, kinga kuwa tashin hankalin danake ganowa a masarautarsun nan, wlhy akwai babban lauje cikin nad'ifa, bazan iya wannan rayuwarba gaskiya, dan tanada wahalar gaske, shi kansa ba ta6a sona zaiyiba, dan tun farko dawata manufa ya aureni ai”.
Murmushi Munubiya tayi mai sauti, tace “amma ke kina sonshi?”.
“ALLAH ya kiyaye, ni wlhy bana sonsa, kuma ban tunanin zansoshi ko anan gaba”.
Dariya Munubiya tayi, harda kwantawa a gado, cikin dariyar take fad'in “to badai asan maci tuwoba sai miya ta k'are, kika sanima kona samu baby's d'ina a jiyan”.
Kwafa nayi kawai, nace can dai a bakinki, kedai mukema fatan ALLAH yasa mun samu, ki shirya min kayan dad'i gobefa zanzo kinji Sweetheart ”.
“karki damu habibati, a gaidamun Galadima ango”. tayi maganar cikeda tsokana.
Aiko sai Munaya ta saka mata kuka.
Dariya ta tuk'e Munubiya tayanke wayar tana mamakin yanda Munaya tayi sanyi, dawuya Munaya kaga ta zauna yima Abu kuka, koyafi k'arfinta tanada jimirin wahala, lallai Galadima baije da wasaba ashe.ππ
Koda tayi sallar isha'i saida ta saka 'Yar uwarta a addu'a, fatanta wannan auren ko igiya d'aya karta samu rauni barema akai ga saki. ta d'au alk'awarin cigaba da sakata a addu'a a kowacce sallarta.
Nima ina ajiye wayar tashi nayi nayo alwala nayi sallar isha'i d'in.
Kallon hotuna na zauna yi awayarsa, duk kusan ma bawasu pictures bane na azo agani, daga hoton wayoyin salula sai na kamar kayan waya Daba a had'aba da computers, mamaki ya kamani, saikace mai k'era waya?, nidai gajiya ma nayi na ajiye wayar, har barci ya kwasheni ban kuma jin labarin Galadima ba.
Shikam tunda yabaro wajen mai martaba suka fita shida sarkin mota, birnin gayu plaza yaje, yayi wasu 'yan abubuwa sannan ya gana da ma'aikatan wajen. Sai kusan around 11 ya dawo gidan, ko sashena bai kallaba ya shige d'akinsa, abinda duk zai buk'ata yad'an harhad'a, yakira Wanda zai kira awaya akan wasu harkokinsa sannan yay shirin barci ya kwanta..
Washe gari da asuba ko tadani bai zoba kamar jiya, ALLAH yasama nariga da na saba da tashi sallar tun a gidan mu, dan haka akan lokacin na tashi nayi kayana. barci nakuma komawa, ban tashiba sai 9am.
Wanka nafarayi, ina tsaka da shafa mai yashigo da sallama ciki-ciki, na zawo hijjab da sauri na saka.
Bakinsa ya ta6e yana kauda kai gefe. “ki shirya zamu fita”. ya juya ya fita.
Da kallo na bishi ina girgiza kai, oh ni, saikace anmasa dole sai yayi maganar?.
Dukda bansan inda zamuba saina d'okantu da fitar, kobabu komai nasha iska ai, danni gidannan jinsa nake tamkar wata duniya daban ba duniyarmu ta mutaneba, yo komaifa gidan akwaishi, makaranta ne asibiti k'aramine, wajen wasan yarane, babufa yanda zaka fita waje inba doleba, musammamn ma mu matan aure, garama mazan da masu fita karatu kuma.
Shiri nayi cikin zani da Riga na atanfa, sunmin kau sosai, danni fa saima naga kamar fatata tawani d'an murje hakannanπ..
A falona na iskesa zaune, muka had'a ido kowa ya janye nasa cikeda basarwa, saida yagama k'asaitarsa da mulki sannan yatashi, sanye yake cikin milk d'in shadda datasha ainahin aikin masu sarauta, takalmansa ma hakanne, sai fidda k'amshin turarensa mai narkar da mutane yakeyi, sajennann ya kwanta luf bisa face nashi, hular na hannunsa bai sakaba.
Gaba yayi nabisa abaya ina takuna d'ai-d'ai, takalmana masu sauk'in tsini sai bada sautin kwas-kwas sukeyi.
Mun tarar da motocin dazamu fita dasu a shirye guda 3, an wankesu sai d'aukar idanu sukeyi, gaisuwar da hadiman gidan suke mana muketa kar6awa, nikam banason abunnan wlhy, amma shi ko'a jikinsa.
Bud'e mana motar akayi muka shiga, nida shi muna baya, sai sarkin mota agaba, yayinda mota biyun kuma dogarai suka shiga.
Babu Wanda yay magana tunda muka fita, nidai kawai kallon hanya nakeyi da mamakin ina muka dosa?, mun Isa immigration office Ashe passport za'amin, abinka da manya, cikin 1hour aka kammala min komai. Bamu bar office d'inba saida harun yazo ya kar6i passport d'in domin nema min visa, daga nan muka fito.
wani dad'ine ya rufeni danaga mun doshi hanyar gidan mu, shi kansa ya hango farin cikin dake shinfid'e a face d'ina, ya janye idonsa daga kallona ya maida kan kallon mutanen anguwar daketa hada-hadarsu hankali kwance.
A dai-dai k'ofar gidanmu motocin suka paka, da hanzari na nemi 6alle murfin zan fita.
Caraf ya damk'e hannuna, juyowa nayi ina kallonsa tamkar zanyi kuka, idonsa a lumshe yake tamkar ma baisan miyayiba.
“dan ALLAH ka sakar min hannu naje”. ‘nayi maganar tamkar zanyi kuka’.
Banza yamin, saida yamula dan kamsa sannan yabud'e idonsa a kaina yana hararata, “ki nutsufa, ko an fad'a miki haka akeyi?”.
Baki na tunzuro gaba.
Ya janye idonsa daga kallona yana kuma matse hannuna cikin nasa.
Ni ban saniba Ashe wai dole sai an nema masa ison shiga gidan namu, sarkin mota dai tuni yafita dama.
'Yan anguwarmu sunyi cirko-cirko suna kallon motocin, jira kawai suke suga Wanda zai fito aciki, dukda sunga masu jajayen riguna a tsaitsaye, alamar daga masarauta ne.
Muna a haka saiga yaa hameed yafito daga cikin gidanmu dad'an hanzarinsa, inaga yazo gaidasune, dan kullum Safiya duk sai sunzo shidasu yaa Shafi'u.
Jikin motar damuke ya k'araso, sarkin k'ofa yay knocking d'in glass d'in 6angaren Galadima. duk da yasan yana kallonsu shi.
Sauke glass d'in yayi a hankali, sannan yama sarkin k'ofa nuni daya bud'esa, har yanzu hannuna yana cikin nasa kuma. Ya d'auki hularsa ya saka.
Cikeda fara'a Yaa Hameed yake masa barka da zuwa, sai lokacin ya saki hannuna, sannan yazura k'afarsa d'aya yafito, nima dogari d'aya yazagayo da sauri yabud'emin, na fito, handbag d'in hannuna dogarin ya kar6a yana zubomin kirari.
Kallofa Yakoma sama ga 'yan anguwarmu, kowa sai kallona yake yana fad'in ashe munaya Ce, kai masha ALLAH, kugafa auren sati d'aya harta canja kamanni, lallai sarauta dad'i.
Inda yaa Hameed da Galadima suke na zagayo, suna rik'e da hannun juna sunyi musabaha, fuskar yaa Hameed a washe, yayinda ta Galadima ke d'ukeda wani munafukin murmushi.
Cikin murna nace “yaa Hameed I miss u”.
“miss u too Darling sister. bismilla ranka ya dad'e kumuje ciki to”.
Atare muka shiga ciki, ina gaba suna bina a baya shida yaa Hameed.
Matan gidanmu kowacce na mak'ale jikin window d'inta tanason ganin Galadima, yayinda Aryaan da Aiyaan suka shek'o da gudu kaina, ganin haka suma sauran yaran sai suka shek'o, duk na tarbesu cikeda farinciki da kewa.
Ni nama manta dawani Galadima muke tare, Ashe shi yanata kallonmu cikeda sha'awa.
yaa Hameed yamasa jagora zuwa falon Dady.
Nikam ai d'akin Innarmu sha, tareda gayyar 'yan tarbata.
A zaune na iske innarmu tana ninke kayan su Aryaan, da alama wankewa tayi, sai tausayinta ya kamani, yanzufa kowanne aiki dole itace zatakeyi, babu mai tayata, jikinta na fad'a ina hawaye.
Itakam tace “kajimin ja'irar yarinya, to miye abin kukan kuma? wai nikam yaushe kika lalace da sauri kuka haka Munaya?”.
“innarmu kewarku cefa wlhy”. nashiga gaidata, cikeda farincikin yanda na koma a kwana 6 kacal take amsamin, sai jero hamdala take a zuciyarta.
Zainab k'anwar Fauziyya tashigo d'auke da tire an d'oro zo6o da ruwa akai.
“inyee, kaga su zee anzama 'yan matafa, kace bad'i sai aure kenan?”.
Fuskarta ta rufe tana fad'in kai Aunty kibari please, innarmu kice ta daina”.
Innarmu dariya take mana itakam, saiga Rahma itama tashigo, saiga Ameenatu da Khadija ma, lallai bad'ima Ashe zamu aurar da yawa, a kwana ki 6 d'innan sainaga yaran duk sunmin girma a ido. Nasha mamakin su na zuwa gaisheni, dan bansa akaba nikam, araina nace ko jama'ar gidanmu dun fara canja haline dai?.
Muna haka saiga innaro tamkar an jehota, kowa ido ya zuba mata, dan shigowa tayi tana masifar wai bamu fara shiga gidan taba nida Galadima.
Na kalleta a d'age ina ta6e baki, “yo banda abinki innaro ai sai nafara ganin Uwata, dan banida kamarta kaf duniya”.
Ha6a tarik'e tana kallona “eh lallai kam, yo ai Dama ke halin uwarki gareki, ba mutuncine dakeba, ballan tana yanzun kuma ido yak'ara fetsarewa ansan komai na aure”.
Zan maida mata murtani innarmu ta harareni, shiru nayi na k'yaleta badan nasoba.
Shima Galadima yana falon Dady yasamu tarbar mutunci daga maman Fauziyya, dan matan gidanmu babu wadda ta aika masa dako ruwa, yaji dad'in tarbar daya samu kuwa, musamman yanda su Abba suka nuna masa tamkar d'ansu, baiyi dubi da sarautar dake kansaba ya duk'a har k'asa yakwashi gaisuwa wajen iyayena uku.
Hakan yamusu dad'i, domin ya mutuntasu, kuma sun kuma tabbatarwa shid'in mai tarbiyyane.
Anan yamusu bayanin munzo musu sallama ne zamu tafi India.
Fatan alkairi su abbanmu sukai mana da k'yak'k'yawar addu'a, daga nan sukad'an ta6a hira dashi, dukda yana nonnok'ewa saboda kunya irin ta jinin hausa Fulani.
Nikam can innarmu ta iza k'eyata nashiga kowanne d'aki na gaidasu, sai kallon k'urulla suke bina dashi, anason ganin wata makusa a jikina, amma sai basuganiba kuwa, komai sai sambarka. Aikam bak'in ciki tamkar ya karsu, kowa hassada nacin zuciyarsu (kai jama'a ALLAH yarabamu da cutar hassada komai k'ank'artattaπ’ππ»)
Na dad'e d'akin maman Fauziyya sosai, dan acanma naci abinda tad'an girka mana mara nauyi, yaa Hameed yazo ya d'auki na Galadima da kansa.
Sashenmu na dawo inatama innarmu shagwa6a, duk nabi na nanik'e mata, dukda tureni datakeyi. Nashiga tsohon d'akinmu harda kukana, komai nanan yanda yake, harma dawasu 'yan tarkacenmu daba a gama badawa ba, haka kawai bamu mutuba d'akinmu Yakoma kango, anan na d'akko cajata da wayar Galadima daya barmin a filin idi, sai wad'ansu 'yan abubuwa danake buk'ata.
Na fito ina tambayar innarmu waye ya d'auki wani hotonmu dake saman mirror nida Munaya?, tacemin maybe Ameeran inna lami Ce ko Bilkisu, dan taji suna rigima akan d'aukar Horton.
Shigowar Galadima da yaa Hameed tasaka innarmu yin shiru, nikam ban daina daddaga k'afa k'asaba ina k'unk'unin miyasa tabari suka d'auka?.
Galadima dake k'ok'arin zama yad'ago ido yad'an kalleni sannan ya janye.
Yaa Hameed ne yace kekuma lafiya?.
Fad'a masa nayi tamkar zanyi kuka, yace “to kuka zakiyi?”.
“ALLAH yaa Hameed inason hotonfa”.
“ai saiki hak'ura yanzun tunda sun d'auka ko?”.
Innarmu da Galadima dai gaisuwa sukeyi, babu Wanda ya tanka mani. shi saima mamakin ta6arar danakeyi yake a zuciyarsa.
Nikam bansan yana yiba.
Sosai yaji innarmu ta burgesa, yakula ko kad'an ba halinta nabiyoba, dan ita tanada sanyi, dagani batada hayaniya, amma nikam ai sai addu'a.
Yad'an jima anan dukda ba hira sukeba, kowa kunya na cinsa, a raina nace dama yanda kunya guy d'inan ashe?.
Alkairi mai yawa ya ajiyema innarmu, dawata leda da yaa Hameed yabiyosa da ita, sannan yafita innarmu na saka masa albarka yana amsawa cikeda jin dad'i, jinta yake tamkar Momma d'insa.
Daga nan saida yashiga kowanne d'aki, sannan yaa Hameed ya rakashi gidan innaro.
Abba ne yashigo yana fad'in a tattaro lefena muwuce da kayanmu.
Na marairaice fuska nace Abba abarsu anan, kagaba tafiya zamuyi can d'in babu kowa.
“a'a Munaya bazai yuwuba, idan mun ajiyesu anan mizamuyi dasu?, kitafi da kayanki, duk randa dai kuka dawo suna d'akinki ai.
Badan nasoba na amince, amma naje wajen kayan ina fitar da wasu, ni saima yau naga lefen, gaskiya su Galadima sun zuba kud'i a wajennan.
Duk matan gidanmu atanfofi na fidda musu, maman fauziyya kam guda biyu, sannan yaran gidanmu 'yan matan yanzu kowa nafidda masa wani abun, su Aryaan ma dukda mazane kowa na fidda masa abinda zai iya amfani dashi.
Sai su Ayusher da inna lami da Ameera, Bilkeesu ma da nata, hakama mama rabia, na ware akwati guda na lodama Munubiya kaya sosai aciki, aunty salamah ma da nata, sai gwaggo Safiyya da yaranta mata, itama innaro jarabatu na fidda mata, su Abbanmu ne dai narasa mizan basu aciki.
Innarmu na kira tagani, ta kalleni tana fad'in “munaya bazasuga an kwashe kayanba?”.
“a'a wlhy innarmu bazasu ganiba, kowafa da sashensa a gidan, kuma babu mai shiga harkar wani, idan na barsu mizanyi dasu? Kayan sunmin yawa ai”.
“to shikenan, ALLAH ya saka da alkairi”.
Na amsa da ameen ina fad'in “ganaku nan keda su Aiyaan innarmu”.
“a'a ni bazan d'auki komaiba, bakiga yama kawomin abuba, ga kud'i dama bansan ko nawa bane”.
Kuka na Sanya mata akan saita kar6a, babu yanda ta iya ta amsa, amma saida tarage. Sai dai tana fita na maida mata harda k'arima.
Zainab Ce ta kaima kowa nasa, kowacce rai babu dad'i ta amsa, sotayi ace daga 'ya'yantane wannan abun arzik'in yafito bawai innarmu ba, (basusan shi Ubangiji babu ruwansaba, yakan azurta Wanda yaso Yakuma k'ask'antar da Wanda yaso a lokacin dayaso).
Babu wadda tazo godiya sai maman fauziyya, nace “oho dai, aikin banza wai talaka ya girmi sarkiπ€·π»♀”.
Banyi maganar su d'auki motarba, dan sonake nasami cikon d'ayar nabasu su duka ukun.
Nima naje na gaida innaro, dasu Abbanmu, naje gidan innaro lokacin su Galadima harsun fito,, na iske Ashe gwaggo Safiyya tama koma jiya, sai d'iyarta Habiba datake zawarci aka bari anan.
Munsha hira da ita, tanata yaba k'yan da nayi.
Innaro kam dukda jana datake ajiki sai basar da ita nakeyi, amma hakan bai hanata yaba Galadima ba, catake wai na more miji, nafi kowa morewa a gidanmu.
Nidai banda ta6e mata baki da bak'ar magana babu abinda nakeyi, bata damuba saboda neman gindin zama take ajikina.
Bamu baro gidanmu ba sai gab daza'a shiga sallar juma'a, an taho da motata da lefena, duk kayan daza'a bana mutane kuma na barsu a can, harna Munubiya.
Su Abba sunsha alkairi awajen Galadima Ashe, hakama matan gidanmu d'akin kowacce daya shiga saida ya ajiye alkairi, sunata kukan zuci da fad'in inama-inama 'ya'yansu ne a wannan daularπ€£π₯΄.
Zamu shiga motane ina sharar kwalla baba k'arami yace namusu godiya wajen Galadima, kaina kawai na iya d'aga masa.
Innarmu bayan tafiyarmu har 'yan kwalla tayi, matan gidanmu kam duk haushinta sukeji, idan kacire maman fauziyya.
Daga nan gidan Munubiya muka nufa, amma anan bai shigaba, yace naje zuwa anjima zai dawo mutafi, dan yanzu zaije sallar juma'a.
Kai na kawai na d'aga masa, nafita bayan dogari d'aya yabud'emin k'ofa, basu bar gate d'inba saida sukaga na shige ciki, ya maida kansa jikin kujera ya kwantar tareda lumshe ido, abinda yafaru a gidanmu kawai yake tariyowa, yakula family nawama sai a hankali dai. Sunada shigen irin halallayyar family d'insa.
Nikam da gudu nashiga ina kwala kiran sunan Munubiya, itama yafito aguje muka rungume juna, sai muka fashe da kuka kawai, ALLAH ma ya somu yaa Marwan yarigada yafita masallaci.................✍πΌ
*_Masoya bansan yanda zan nuna muku tsantsar farin cikinaba, amma tabbas inajin dad'in Comments naku, kuyi hak'uri da rashin amsawata d'ai-d'ai, kunmin yawane wlhy, ga massages na PC, idan kuma nagama typing d'inan kaina d'aukar zafi yake, ko son ta6a waya banayi wlhy, naga wasu suna d'auka kamar wulak'ancine rashin amsawar, wlhy ba haka bane, kumin afuwa da uzuri please & please, duk da nasan bazan iya k'yautatama kowa acikinku yanda yakamata ba, dole wani yaga gazawata koyayane tawani fanninπ._*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmuπππ»_*
*_Typingπ²_*
*_HASKE WRITERS ASSO...π‘_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ceπ€π»_*
ππ»2⃣8⃣
...........Bansan yanda zan musalta muku farin cikin damuka tsinci kanmuba nida 'yar uwata Munubiya, abin kawai ba'a magana.
Duk da bata yarda zan zo d'inba amma bata fasa tanadar min duk abinda tasan inasoba, tarasa inda zata sakani dan dad'i, gaskiya gidan munu yayi k'yau sosai, gashi an cika ko ina da kaya, kasancewar harda nawa aka had'a mata, muna yin salla muka 6arke da hirar yaushe gamo, a haka yaa marwan yazo ya samemu, yaukam abin mamaki naga fara'a a fuskarsa, nace lallai aure yayi citta kenan, yanda yake bama Munubiya kulawa sai abin ya birgeni, kamar Na lashesu kuwa Dan dad'i. Haka muka yini muna tad'i har lokacin sallar la'asar yafita salla.
A lokacinne aunty Salamah tazo gidan, Ashe Munubiya ce takirata ta fad'a mata zamu tafi India yau da daddare, mun tarbeta da murna sosai, yayinda ita kuma taketa yaba wai munyi k'yau. mukaita rufe fuska alamar kunya.
Shawarwari taita bamu akan rayuwar aure da yanda zamu tattali mazanmu, babu ko kunya take 6aro mana komai, sai mune muketa sunkuy da kai, itakam ko a jikinta, ta rarraba mana wasu buks da ke d'auke da abubuwa masu amfani dazasu bada gudunmawa a zaman takewar aure, nidai bawai na d'auki nawa da muhimmanci baneba.
Wajen 5 tatafi, tafiyarta babu dad'ewa saiga Galadima da yaa marwan sun shigo, Ashe wai ya dad'e a k'ofar gida zaune, ya kira yaa marwan yace baya gida amma gashinan zuwa.
Shine yajirashi amota harya iso suka shigo tare. Sun gaisa da Munubiya a mutunce, ta shirya musu abinci, da yace yagode sauri yakeyi, amma munu ta marairaice wai yaza'ayi mijin 'Yar uwarta yak'i cin abincin gidanta, in baimasa baneba ta sake masa.
Murmushi yayi ya zauna yaci kad'an, yayinda mukuma muka shiga d'aki dan mu basu waje suci abincin, d'an kuskus d'inmu mukayi muma, takuma kwantar min da hankali akan auren nawa da wasu 'yan shawarwari, da nunamin fushinta akan abinda nace nama Galadima d'in, ta nunamin wannan ba tarbiyyar da iyayenmu suka bamu baneba, gaskiya karna sake irin haka, kuma nabashi hak'uri akan hakan, nace “to amma tayaya zan basa hakurin?”.
'Yar takarda ta d'auka tayi rubutun tabani wai nabashi.
Na kar6ane kawai badan ina tunanin zan bayar d'inba, duk da nasiharta ta shigine gaskiya, kuma nima tun a ranar nayi nadamar ce masa azzalumin gaskiya, Duk da nasan a cikin fushine Nima Na fad'a, Dan nashiga rud'ani sosai akan abinda yayimin daban zataba.
tabani kayan da aunty salamah takawo a Leda, batareda na dubaba na amsa.
Itama k'yauta mai tsoka yamata sannan muka fito, nida ita kowa yana sharar kwalla, bamason rabuwa da juna, amma yazamuyi? aure ya rabamu.
Daga nan gz yaa marwan muka nufa gaida mama rabi'a, namayi mamakin yanda yasanta, nankam tare muka shiga, su Ayusher suka rukunkumeni cikin tsantsar farinciki da kewa.
Bamu dad'e sosaiba itama ya ajiye mata alkairi muka fito, su Feena ma yabasu kud'i wai su sai kayan kwalliya, hakama Ahmad, yaa Fadeel dai mun tarar baya nan, yakoma inda yake bautar k'asa.
Nanma saida nayi kuka dazamu taho.
Saida muka shiga mota ina sharar hawaye sannan ya kalleni cikeda k'asaita yana ta6e baki, “ke wai bak'ya tsoron hawayenki su k'are ne?”.
Bance masa komaiba nacigaba da kukana, shima saiya shareni.
★★★***★★★
Koda muka isa Masarauta bamu wuce sashenmu kai tsaye ba, wasu 6angarorin gidan mukaje mukai musu sallama, harda sashen mama Fulani, yauma dai babu magana mai dad'i tsakaninta da Galadima, nifa lamarin nasu na d'aure kaina gaskiya.
Mai martaba kam munsha addu'a a wajensa, sannan muka fito.
Mun shiga sashenmu ana kiran sallar magriba, zan shige yace “kiyi azamar shirya kayanki trolley d'aya, karki wani kwashi kaya dayawa”.
Da to kawai na amsa nayi shigewata ciki.
*_7:30pm_* Muka bar masarautar, nida shi da Samha motarmu d'aya, muna baya tana gaba.
d'ayar motar kuma Sauban da aunty Mimi da khaleel ne aciki.
Mun sami rakkiyar Harun da Muftahu sai wasu k'alilan daga masarautar.
Tom nidai ba k'auyace a airport, dan banta6a shiga jirgiba, amma kunsan mutuniyar taku da Jan aji,π€¨ saina Fiske abina nima inajan citta tamkar wadda ta saba.
Duk abinda yadace ayi anyi mana, musamman ma ni danake sabuwar fita k'asar, harun yad'an sha cukuniya a kaina tunda rana.
9pm dai-dai jirginmu ya shilla a gajimareπππ«.
Lokacin da akace asaka belt ban sakaba, sai shine ya jawo yasakamin batareda yace uffanba, yana jikin window nikuma ina gefensa, sai bayan mu khaleel da Samha, can baya kuma aunty Mimi da Sauban.
Ina lafe jikin kujera, yayinda shima yake kwance ya jingina bayansa, wani English novel ne a hannunsa yana karantawa, dama tun amota yake rik'e da kayansa.
Da akazo tambayarmu mi muke buk'ata Coffee kawai yace yacigaba da karatunsa, nima ta tambayeni saina girgiza mata kai alamar bana buk'atar komai.
Janye book d'in yayi yana kallona, saikuma ya janye ya maida kanta, harta bar wajen ya kirata, yace takawo min abinda su Samha sukace sunaso.
Bance komaiba nidai, shima saiya cigaba da karatunsa.
(*************)
Alhmdllh mun sauka kasar India, k'asar da nake gani a films, abin mamaki sainaga dogarawa ne sukazo tarbarmu, saikuma Akash dawani danaji Galadima yakira da beejay.
Bamu 6ata lokaciba mukabar airport d'in, a nawa tunanin sainaga rayuwar tasu kamar dai tamuce gaskiya, saidai banbancin sutura zuwa wasu mu'amullat haka, mutane sunata hidimarsu da kai kawo hankali kwance.
Masha ALLAH na fad'a yayinda muka isa gidan danake k'yautata zaton nasu Galadima ne. gidan kam yamin k'yau gaskiya, su beejay basu shigaba suna saukemu suka juya, mune muka Shiga hannuna aunty Mimi tarik'e, yayinda su Samha suke agaba.
Galadima kam mun barsa a harabar gidan yana waya.
Ai kaina bai gama kwancewa ba saida muka shiga falon gidan, hummm manyan k'asarmu sunajin dad'insu gaskiya, yo kanada irin wannan gidan a k'asar daba takaba to k'asarka kumafa?.
A falo muka zube bayi suka Shiga hidima damu, muna zaune a wajen Galadima yashigo, shima zaman yayi ya aza k'afa d'aya bisa d'aya, Sauban yazuba ruwa a cup yabashi, kar6a yay yana fad'in “thanks”.
Ya kalli baiwar datake shirya abinci daga can gefenmu, “k zonan”.
Da sairi ta ajiye spoons d'in hannunta tanufo inda muke, agabansa ta zube tace “gani ranka ya dad'e”.
“kisamu wata ta tayaki Ku gyara d'akin can nakusada Samha yanzun nan”.
“angama ranka ya dad'e”. tayi maganar cikeda tdantsar ladabi.
Aunty Mimi Na najinsa batace uffanba. Shigowar momma tasaka khaleel tashi da gudu yaje ya tarbota, itama Samha zuwata ta kwakwameta, tunkan ma afad'amin nagane mahaifiyarsu Galadima ce, koda yanda fuskar kowannensu ta washe da farincikin ganin juna.
Hankalinta Na kaina tana murmushi da fad'in “oyoyo d'iyata”.
Zamowa nayi daga kujerar na durk'usa har k'asa ina gaisheta, ta k'araso inda nake ta kama hannuna ta tadani nakoma saman kujerar, “zauna kinji, sannunku da zuwa, kinsha hanya ko?”.
Murmushi nayi ina duk'ar da kaina.
Galadima yace “wai Momma dan ALLAH duk baki ganmu baneba?”.
Kallonsa tayi cikin Hararar wasa, tace, “yo naganku bata taku nakeba”.
Su aunty Mimi dariya suka Sanya, yayinda Galadima yad'an 6ata rai yana fad'in “da tsohuwar Zuma dai ake Magani Momma”.
“a fad'arka ba, amma sabuwa ma aitafi aiki da dad'i”.
Nidai murmushi nakeyi, Dan wasan nasu ya burgeni, inason ganin family haka cikin farinciki, gaskiya sai sunfi jin dad'in zaman nan fiyema da masarautar sun can.
Gaishe-gaishe aka shigayi, kowa yana k'ok'arin bama Momma labarin yanda biki ya kasance, sai dad'i takeji da sanya albarka, nidai nida Galadima babu mai cewa komai.
Mik'ewa Galadima yayi, “bara nad'an watsa ruwa Momma”.
“to afito lafiya Muh'd”. ta kalleni nima, “d'iyata tashi kibi mijinki kiyi wanka kuzo ga abinci”.
Harya fara tafiya saiya tsaya, juyiwa yayi yana mata magana a yaren daban saniba.
Ta galla masa harara da masa dak'uwa, itama bansan mitace masaba. naga dai ya tura baki yaci gaba da tafiyarsa. ita kuma tace natashi naje.
(Wai ashe cayay mata ai yasa a gyaramin d'akin da zan zauna, shine tamasa dak'uwa tana cewa d'akin safa?, shi idan ance Araba mana d'aki saiya amince?, to tare zamu zauna, shine yakuma cewa ammafa d'akinsa ai ba kowa ke shigaba, tace tasani aii, muje nima sirrinsace ai, shinefa ya tura baki gaba).
Kamar an maken k'afafu haka nabisa abaya muna taka steps d'in benen, har muka isa k'aramin falo mai k'yau, komai farine a wajen, TV ce kawai takasance bak'a.
Falon yad'anyi k'ura alamun ba'a gyaraba (babu mai aikin dake hawa samansa, gashi kuma sunyi tafiya suduka, Momma kuma batada time d'in gyara masa d'aki).
Guntun tsaki yaja yana yamutsa fuska, d'an zaman danayi dashi na fuskanci bayason k'azanta komin k'ank'antar datti yata yamutse fuka kenan, bamu tsaya ananba muka shiga bedroom d'in bayan yabud'e, mayataccen k'amshinsa yana manne da d'akin, sai dai nan d'inma yayi k'ura, waya yazaro yayi kira, ashe Samha yakira, yace “k zoki gyaramin d'aki”.
Bai jira cewarta ba ya yanke wayar.
Bance masa uffanba nima nataka nawucesa, bina yayi da kallo dan yaga ina zanje?.
Zanin gadon na yaye duka, nacire rigar filaluwan tareda rumfar da akama gadon, shidai kallona kawai yakeyi, yana tsaye jingine da bango (baiyi tunanin zance zan gyaraba).
Knocking d'in da akayine yabada izinin shigowa, Samha ce d'auke da kayan tsintsiya, ta zubesu a k'asa tana fad'in “aunty kibarsa zan gyara”.
Kaina na girgiza nace “barshi Samha, nunamin kawai yanda zanyi, kije kema ki huta”.
Nunamin komai tayi, har inda bedsheets suke, tafice a d'arare da zaton Galadima zai hanata yace takoma ta gyara.
Amma saitaji baice komaiba, yama kauda kansa gefe kamar baisan munayiba.
Bathroom nashiga, nazage sosai na tsaftaceshi, Dana k'urarce kawai, duk abinda zaisa toilet k'amshi da tsafta nasakashi, saida naganshi need sannan nafito, ban iskeshi a d'akinba, Dan haka hankali kwance Nagyara bedroom d'inma nagama, nasaka kamshi sosai. falon nafito danufi gyarawa, sainaga Samha harta gama itama tana saka air fresheners masu dad'in k'amshi, da turaren wuta irin namu na gargajiya.
Sannu da aiki namata, itama tamin, Galadima yafito daga wata k'ofa yawucemu batareda ya tankaba, bedroom d'in yakoma.
Kallon Samha nayi nace, “saura wannan d'akin daya fito cikin ko?”.
“ai Aunty wannan d'akin dakansa yake gyarawa, babu mai shigarsa duk gidannan inba Momma da Mummy na da shiba”.
Cikin mamaki nace “miya sa to?”.
“d'akin sirrinsa ne aunty”.
Ban fahimci maganarba, bankuma tambayeta ba, ta tattara kayan damukayi amfani dasu tafice tana fad'in “aunty bara naje nayi wanka, dama wankan zanyi yakirani”.
Kaina kawai na iya d'aga mata, saman kujerar na zauna shiru ina nazarin maganarta, miye kuma ma'anar d'akin sirri? nashiga k'ololuwar nazari banyi zaton time yawuce hakaba, k'afata yad'an shura, nad'ago idona ad'an firgice na kallesa, haryayi wankan yana sanye cikin jajayen kaya na Adidas, sun masa k'yau sosai.
Juyawa yay zai sauka k'asa yana fad'in “kitashi kije kiyi wanka”.
Bai jira cewata ba ya sauka.
Nima saina tashi nayi yanda yace, d'akinsa sosai ya had'u gaskiya, harma bansan Yaya zan fasalta mukuba, nasan farin Abu namai tsaftane, lallai yanada tsafta, daga bedroom parlour zuwa bathroom nashi komai farine, bedroom d'inne kawai keda d'an sirkin Golden kad'an-kad'an shima.
Nidai ina wanka da d'unbin tunani, haka kawai naji kwad'ayin son Shiga d'akin sirrin nasa.
Koda na fito saina saka zani da riga na atanfa, ban shafa komaiba na d'auki turarensa na saka saboda neman maganaπ. ina tsaka da saka turaren Samha tashigo kirana.
Ajiyewa nayi na d'auki gyale nabi bayanta.
Falon k'asa muka sakko, inda aka shirya abincin saman wata lallausar darduma, duk suna a zaune har Momma, kusada Galadima daketa cin abincinsa ko kallon mutane bayayi Aunty Mimi ta nunamin wai na zauna.
Kamar nafasa kuka haka naji, Sauban dake gefen haggunsa yace, “auntynmu har yanzu amarcin bai k'are bane? kin shige d'aki kinyi bulum”.
Murmushi kawai nayi na k'asa ce masa komai, dan yabani kunya gaskiya, nakula kuma yanada yawan tsokana, aunty Mimi kam dariya tayi, yayinda Samha tarufe baki tanayin tata.
Momma tamasa dak'uwa, “o kai Sauban ALLAH ya shiryeka, kowama bazaka d'agama k'afaba?”.
Dariya ya kumayi yana satar kallon Galadima dayay tamkar baya wajen, yace “to ai gaskiya nafad'a Momma. dan ALLAH aunty ba haka bane?”.
“gaskiyarka fa Sauban”. Aunty Mimi ta fad'a tana dariya.
Momma tace “barsu kinji my daughter, ci abincinki”.
Kai na jinjina mata cikeda kunya.
Galadima dai har yanzu baice k'alaba, baima d'ago ya kallemu ba.
Haka muka ci abincin nidai duk a takure nake, kamar yanda yafara cin abinci haka yarigamu kammalawa, tashi yay yabar wajen, yakoma can saman wasu kujeru guda biyu ya zauna, laptop d'in dake saman table d'in wajen ya d'auka ya kunna, da alama shiya ajiye kayansa.
Bayan mun gama duk muka mik'e, kowa ya hau shirin zuwa asibiti duba Abie, time d'in barcin sane shiyyasa ma Momma tasamu tataho, jakadiya kawai aka bari a wajen, itama a waje, da yake in time d'in barcinsa yayi kowa fitowa yake daga d'akin a barsa shi kad'ai.
Galadima saboda aikin da yakeyi yace muyi gaba shima zai taho.
Momma tace “to matarka ta zauna ta jiraka, mudai mun tafi”.
Kamar zaiyi magana saikuma yayi shiru, cigaba yayi da aikinsa harsuka fice, jinai kamar nace nidai zan bisu kawai. Amma na makaro, dan harma sun fice abinsu.
Ganinai tsayuwa ta isheni, shikuma d'an latsin baice na zauna ba, sai kawai naje na zauna d'ayar kujerar dake kallon tasa, nima na d'ora k'afa d'aya kan d'aya tamkar yanda yayi. nayi gefe da kaina cikin basarwa.
Daina danna System d'in yayi, ya d'ago idanu yana kallona, yayinda yake Murza hannunsa na haggu daya d'ora guywar a hannun kujera hannun yana sama, yinai tamkarma bansan yana kallona ba kwata-kwata.
cije lips d'insa yayi kad'an, ya janye idonsa ya maida ga system d'in, aransa yana mamakin izzar yarinyarnan, tabbas data fito gidan sarauta da anga mulkin tsiya.
Falon shiru babu kowa, tunda kuyangin suka gama hidimarsu duk suka koma 6angarensu dake can baya.
Kusan mintuna 40 yagama abinda yakeyi, laptop d'in ya kashe sannan ya mik'e, batare da ya kalleni ba yace “muje”.
Saida na d'an ja wasu seconds sannan na mik'e, saidama ya juyo ya kalleni, dan har yakai k'ofar fita.
Gyalena na maida saman kai nabiyo bayansa, a k'ofa na iskeshi tsaye, na fito shikuma ya daddana wasu madannai agefen k'ofar, Ashe wai security yasaka.
Ranar farko danaga yayi tuk'i da kansa, dogarin dasuke gate suka bud'e mana muka fice.
Tunda muka tafi ba Wanda yayma wani magana, shi yanata deriving d'insa nikam ina kalle-kalle abuna, mun Isa katafaren asibiti mai k'yawun gaske, inma badan sunanba da saika d'auka wani wajen shak'atawa ne, asibitin ya had'u gaskiya, har ciki muka shiga bayan security sun mana 'yan tambayoyi dakuma gaisawa da sukayi, naga alamar sun sanshi sosai, amma duk da haka saida akai searching d'inmu.
Abin ya birgeni gaskiya, inda aka tanada domin parking ya tsaya, ya kashe motar sannan muka fito kusan a atare, bai tafiba saida na zagayo, muka jera zuwa ciki, yanata gaisuwa da jama'a, ina mamakin yanda ya iya yarurrukansu, nikam dai saidai da turanci nake gaishesu, kuma ba kowaba.
Mun fara zuwa office d'in wani doctor, suka d'an tattauna akan cigaban da aka samu na jikin Abie, mun gaisa dashi yaymana murnar aure, murmushi kawai nayi, sai Galadima ne ya amsa masa.
Daga nan muka shiga d'akin da Abie yake jiyya, iyalansa su aunty Mimi duk suna zagaye dashi, nidai a raina danaga d'akin nace oni kamar ba Asibitiba?.
Tunda muka shigo fuskar dattijon dake kwance a gadon ta fad'ad'a da murmushi, kallo d'aya namasa naga kamanninsa dana hoton d'akin Galadima na Nigeria.
Gabansa muka k'arasa, Galadima ya durk'usa yarik'o hannunsa, nima saina durk'usa ina gaidashi da Hausa.
Momma ce tazo ta kamani na tashi, cikin wani yanayi tace, “d'iyata ai Abban naku baya iya magana kinji”.
Da sauri na kallesa, ya sakarmin murmushi, sai kawai na mayar masa hawaye nabin kumatuna domin tausayi, duk kallona sukeyi sukam, harda Galadima.
Kuma zamewa nayi na durk'usa a gaban gadon, cikin rawar murya nafara jera masa addu'ar samun sauk'i wajen ubangiji. duk suna amsamin da amin.
Murmushi yakasa barin face d'in dattijon, Wanda k'aunata take shigarsa har zuciyarsa, Momma takuma d'agoni a karo na biyu ta rungume tana lallashina.
Galadima ya had'iye hawayen dake Neman zubo masa shima, yafara gaida Abie dake murmushi, da ido ya nuna masani wai ya lallasheni mana.
Sai Galadima yayi murmushin jin kunya yana susar k'eya.
Murmushi Abie yayi sosai, har hakwaransa na bayyana.
Ban ta6a jin tausayin Galadima ba sai yau, dama haka suke cikin tashin hankali? Lallai dan ba'aga dariya a fuskarsa ba ba laifi baneba, nama yabama k'ok'arinsa yanda yake zirga-zirga tsakanin Nigeria da nan d'in.
Ahaka akaita firar dani bana fahimta, danshi Abie da idanu yake maganar.
Bamu baro asibitinba sai dare sosai, a can mukayi salloli dacin abinci.
Mun taho muka baro Momma a can, jakadiya ma ta biyomu, dama Momma kad'ai ke kwana a wajensa, shima ba kullumba, dan wasu ranakun basa bari a kwana dashi, a sati sau uku take kwana a wajensa.
**********
Tunda muka baro asibitin tsohonnan ketamin yawo a zuciya da ruhi, sai cud'awa nake da kwancewa, inason jin labarin masarautar su Galadima gaskiya.
Yanzun ma iza k'eyarmu aunty Mimi tayi muka wuce d'akinsa, muna zuwa bathroom yashiga, kusan mintina 25 saigashi yafito, da Alama wanka yayi, harya sauyo kayan barci aciki, dama da abinsa yashiga.
Nima tashi nayi nashiga da nawa masu kauri a hannu. Wankan nayi da shirin barci, sannan nasako hijjab na fito.
Saman gado na iskeshi yawani barbaje a tsakiya, alamar baya buk'atar wani ya hau.
Na ta6e bakina, a raina nace koma bakayi hakaba ai bazan ta6a had'a makwanci da kaiba, aikin banza kawai, naja tsaki a zuciyata.
Saman sofar d'akin na hau na kwanta, inata tunanin Abie da ma tsalarsa.
Kasa daurewa nayi, na kallesa nace, “ wai miye matsalar Abie (kamar yanda naji suna fad'a)”.
Shiru yamin, harma na zata yayi barci, sai can yacemin “ciwone dai kawai”. daga haka yaja bakinsa yay shiru.
Nima shirin nayi, dan bakuma nida abin fad'a, musamman yanda yabani amsar.
Nidai zan iya cewa barcina na daren ranar rabi da rabine, kewar 'yan uwana da bak'unta, gakuma matsalar babansu Galadima data k'asa Barin zuciyata.
Da asuba narigashi tashima, na fito toilet bayan gama d'aura alwala na iskeshi zaune bakin gado dafe da kai, k'ala bance masaba nad'au abin salla na shinfid'a, tashi yayi ya shiga bayin yana Jan tsaki a zuciyarsa, Shifa wlhy dukya takura, yasaba zamansa shikad'ai a d'akinsa, yanzu duk anzo an cika masaπ.
Haryaje k'ofar toilet d'in yadawo baya, doguwar riga ya d'auka ya shige, saida yay wanka da brush sannan yayo alwala yafito sanye cikin jallabiya blue.
Turare yad'an fesa sannan ya d'au key d'in mota yafita, Ashe inda yake zuwa sallan can gaban gidanne, kuma daga sallar asuba yake wucewa asibiti ya kar6i Momma tataho gida itakuma, duk ranar weekend haka yakeyi, yanzu kuwa yana cikin hutune.
Da yake ina sallah yafita, banyi zaton yafita kenanba, bayan na idar saina d'an kwanta, maganar d'akin sirrinsa ce taita cin zuciyata, namik'e nafita, saida na lek'a falon k'asa naga babu kowa sannan nadawo, cikin tantama na murd'a k'ofar d'akin, sai naga ta bud'e, banyi zaton hakaba gaskiya, musamman danaji an kira d'akin dana sirri. (bakisan ya manta bane bai rufeba Munayaπ dan harda security a d'akin).
'Dakin k'aramine bashida wani girma, gaba d'aya bangon d'akin zagaye yake da hotuna, sai Computers guda hud'u da kuje d'aya gabanta akwai deck's babba, wanda duk Computers d'in akansa suke, sai pens da yawa cikin wani d'an Abu, gefe kuma k'aramar loka Ce ta glass cikeda takardu, gakuma tarin wasu takardun kashi-kashi da akayi kamar files a seman decks d'in, matsawa nayi jikin bangon nafara kallon picture's d'in, hotunan mutanene daban-daban, harda wasu manya dana Sani a TV, mafi yawa yayi rubutu a k'asan kowanne photo, bana fahimtar rubutun gaskiya, danhaka nacigaba da kallon picture's d'in kawai, harda na mama Fulani,π
π±
Kutu melesi hotona fa jama'a a d'akin sirri, naga idi, nakaranta rubuntun k'asan yafi sau goma ban fahimci komaiba, saiwasu lissafi-lissafi kamar mai rubutun Mathematicsπ«.
Na Muftahu nagani a k'arshe, abinfa ya d'aure minkai, mu kuma ni da amininsa Muftahu miya kawomu d'akin sirriππ»?.
Agogon d'akin na kalla naga 7am tayi, da sauri nafita gudun karya zo ya sameni.
Na rufe k'ofar a hankali nakoma bedroom d'insa, ajiyar zuciyata na sauke ganin bai dawoba.
Zama nayi na zabga tagumi ina tunanin ma'anar wad'ancan pictures d'in dana gani, danma a tsorace nake, ban nutsu tsaf naganibaπ€¦π»♀.
Ban sauka k'asaba saida 9am tayi agogon k'asar, na iske su Samha suna breakfast, harda Momma, na durk'usa har k'asa na gaidasu itada aunty Mimi, cikeda fara'a suka amsa.
Momma tace “ai nayi zaton barci kike, shiyyasa na hana a tadoki”.
Cikeda kunya nace “a'a na tashi tun d'azun”.
Aunty Mimi ta zaunar dani kusada ita, Sauban ya had'omin komai na breakfast d'in.
Yanzun ma a kunyace naci abincin, kunyata na burge Momma sosai.
Bayan mun kammalane Momma ta kama hannuna muka shiga d'akin ta, a bakin gado ta zaunar dani itama ta zauna, anutse ta kira sunana.
Hakan yasani maida hankalina a kanta nima dan nakula magana mai muhimmanci zamuyi da ita............✍πΌ
*_tofa, mi Momma zata fad'ama Munaya kuma?._*π€
*_Ya ALLAH ka gafartama Iyayenmuπππ»_*
*_Typingπ²_*
*_HASKE WRITERS ASSO...π‘_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ceπ€π»_*
ππ»2⃣9⃣
...........“Munaya taimakona nakeson kiyi akan mijinki”.
'Dagowa nayi na kalleta cikin tsantsar mamaki, saina sinne kaina alamar jin kunyar ta, nace “Umarni zaki bami Momma, domin ke mahaifiyatace”.
Murmushin jin dad'i tayi kamfin takamo hannuna cikin nata, “Alhmdllh Munaya, nagode da wannan karamci naki, yanzu nakuma aminta Muh'd yasamu irin macen danake musu addu'a shida d'an uwansa, ALLAH yayi miki albarka. nasan dukkanin yanda aurenku ya gudana”.
Gabana yafad'i, a raina nace badai Na yarjejeniyar ba?.......maganarta ta katsemin tunanin.
“Mahaifina Sarki Abdul'fatah shine yasakashi aurenki saboda abinda yafaru daku, Wanda nasan k'addarar Muh'd ce kawai tashigo dake cikin lamarin. Kafin nafara neman alfarmar zan fara baki tarihin masarautar su Muh'd, da dalilin zamanmu wannan k'asar daba tamuba tsawon shekara 24 kenan”.
Kaina na jin jina mata, nace “to Momma”.
Zamanta ta gyara sosai yanda zataji dad'in fad'ar abinda ke a bakinta.
*_MASARAUTAR GAGARA BADAU A WASU SHEKARU DASUKA SHU'DEπ€_*
Masarautar gagara badau masarautace mai d'unbin tarihi, da mulkinta ya gudana hannun sarakuna masu yawa, a hasashen masana masarautar sarakuna a k'ala 51 ne suka mulketa harda Sarki na yanzu, wato *Sarki jalaludden Abubakar*.
Sunan masarautar awani shud'ad'd'en lokaci ba *gagara badau* ake kirantaba.
Tasamo sunan gagara badaune dalilin wani Sarki daya mulki masarautar a zamani mai shud'ewa.
Abaya mulkin masarautar basai ka mutuba yake barin hannunka, a'a, da zarar anyi yak'i kayi sakakin da aka ci masarautar tom dolenefa kayi murabus a nad'a wani kuma. kuma bawai cikin 'ya'yankaba, saidai asamo wani hazik'i a masarautar a nad'ashi sarautar.
Tom alokacin Sarki Hameesu Alasan sai aka kawowa masarautar wani gagarumin hari dayaso girgizata. Sarki Hameesu yanada wani d'a da ake kira da suna *Barde* amma asalin sunansa shine Salisu. lokacin da aka kawo musu harinnan ba'a cikin shiri sukeba, amma haka Salisu barde yay saurin had'a mayak'a suka tunkari wannan runduna, bak'aramin gumurzu akashaba, sojojin masarautar Sarki Hameesu duk sun salwanta, amma hakan bai tsorata Salisu ba, yacigaba da bata kashi shida wasu 'yan tsirarun mayak'a, ALLAH mai iko saigasu sunci wannan runduna data kawo musu hari.
Wannan nasara da Salisu yasamuce tasaka babansa Sarki hameesu sauka a kujerarsa aka nad'a salisu. tundaga ranar takoma *_MASARAUTAR GAGARA BADAU_* abin nufi annan salisu barde yazama gagara badau.
Bayan Sarki Salisu gagara badau sarakuna kusan goma sunyi mulki kafin Sarki *_ABUBAKAR_* kakansu Muh'd kenan, mahaifin su takawa.
Shima ya gaji sarautarne a hannun mahaifinsa Yusufa.
Rana d'aya aka nad'a Abubakar Sarki shida amininsa d'an sarkin kan karofi yarima Abdul'fatah, mahaifin Abubakar Yusufu abokine ga Sarki idres na ll, dan haka rana d'aya suka yanke shawarar yin murabus suka nad'a 'ya'yansu.
Sannan aka d'aura musu aure kuma a ranar da matan da su Sarki Yusufu & Idres suka za6a musu.
Gimbiya Marawuyya (mama Fulani) d'iyace ga waziri Sama'ila k'anin Sarki idris, a masarautar Idrees kenan, Sarki idres bashida d'iya mace, dan haka ya d'auki mama Fulani d'iyar k'aninsa yabama Abubakar d'an Sarki Yusufu a masarautar gagara badau, shikuma Sarki Yusufu ya d'auki Khadeeja (inno) yabama Abdul'fatah d'an Sarki idres.
To Ashe ita gimbiya Marayuyya (mama fulani) tana masifar son yarima Abdul'fatah ne, kuma yasani, amma ya nuna mata shi dama gimbiya Khadija (inno) k'anwar abokinsa Abubakar yakeso.
Tun daga lokacin gimbiya Marayuyya (mama Fulani) ta tsani Khadija (inno), ko wani Abu yahad'a masarautunsu bata mata magana, sai zagi da habaici.
Sukuma iyaye basusan gimbiya Marayuyya nason yarima Abdul'fatah ba, sukayi wannan had'in aure. (Iyayen mama Fulani ma sunso ta Auri yarima Abdul'fatah d'in domin sarauta ta dawo tasu)
Gidan sarauta idan an shata layi babu mai k'etarashi, dan haka gimbiya Marayuyya da iyayen ta dolen suka hak'ura da auren yarima Abubakar (tunda acanma suna saka ran gadar sarautar) haka aka kawota gagara badau. ita kuma Khadija (inno) aka kaita masarautar su Mama fulani.
Kusan atare duk suka haihu, saidai Khadija (inno) namiji ta Haifa, yayinda Marayuyya (mama Fulani) ta Haifa mace.
Duk da ba masarauta d'aya sukeba hakan yasaka mama Fulani bak'in ciki, dan aganinta inno taje zata gaje musu masarauta, ita kuma bata samu damar gaje tasuba. A haihuwa ta biyu kuma sai inno ta Haifa mace, mama Fulani kuma ta Haifa namiji. Alokacin kuma duk mazajen nasu suka k'ara aure, daga Sarki Abubakar har Sarki Abdul'fatah. kamar atsare haka sukaita kuma aure har suka cika mata hurhud'u.
A masarautar gagara badau Mama Fulani na zuba mulkinta a masarautar, yanda kasan itace sarkin, dayake shi Sarki Abubakar yanada hak'uri da sauk'in kai.
Humm matan Sarki Abubakar duk basu haihuba, sai mama Fulani keta zubo 'ya'ya. Saikuma amaryar Sarki ta uku ta Haifa d'anta namiji, kusan tare da mama Fulani a haihuwa ta hud'u, duk da mama Fulani itace da manyan 'ya'ya mace 1 maza 2 hakan bai hanata shiga tashin hankaliba, saita shiga tsangwamar gimbiya bagobura da aibanta d'anta *Saifudden*, wani lokacin har shegantashi tayi, saida Sarki Abdul'fatah yazo har masarautar ya taka mata birki sannan.
Mama Fulani tasaka sauran matan Sarki Abubakar sun juyama gimbiya bagobura baya gaba d'aya, batada sakewa ko kad'an acikin gidan. Sarki Abubakar yasan komai dake faruwa a gidansa, amma saiyayi tamkar bai ganiba, bakuma Dan mama Fulani tafi k'arfinsa baneba, yadai zuba mata idanu kawai yaga iya gudun ruwanta.
Ahaka yaran suka taso, gimbiya bagobura ma bata sake haihuwa ba, sai mama Fulani ce takuma biyu, mace 1 da autanta namiji Hayatudden.
Saifudden da jalaludden sun tashine tamkar tagwaye, dukda Saifudden ya girmi jalaludden d'in dakusan 1½ kuwa. danma mama Fulani na hana jalaludden sakewa da Saifudden ne. Kokuma Kamaludden da Shamsudeen suyita dukan Saifudden idan sun gansa tareda jalaludden d'in.
Ahaka Saifudden yatashi cikinsu a tsangwame har suka girma suka zama manya.
Saikuma wani Abu tashin hankali ya samu, a time d'in da mama Fulani ke ganin sarauta zata dawo wajen 'ya'yanta sai ubangiji ya nuna mata ikonsa.
Dan kuwa Shamsudeen da kamaludden sai sukayi had'arin jirgi zasuje umara duk suka rasu.
A time d'in a marine kawai ba a saka mama Fulani ba, amma hauka tuburan tafara a masarautar gagara badau. Saida aka had'a da addu'a sannan talafa, saita kullaci gimbiya bagobura, wai ita tama 'ya'yanta asiri suka mutu domin d'anta Saifudden yagaji sarauta.
Gimbiya bagobura zata tada hankalinta Sarki Abubakar yace tama kwantar da hankalinta.
Bayan mutuwar su Kamaludden babu dad'ewa aka had'a auren gimbiya Zakiyya d'iyar Sarki Abdul'fatah da Saifudden aure, shikuma lokacin Jalaludden da Rafi'atu d'iyar wani Sarki.
Aikam sai mama Fulani ta hau bala'i wai munafunci aka shirya. Babu Wanda yabi takanta akasha biki.
Gimbiya Zakiyya da gimbiya Rafi'atu kusan atare suka haihu a time d'in, gimbiya Zakkiya ta Haifa d'iyarta mace, saidai tana haihuwarta ko ganinta batayiba takoma ga ALLAHπ.
Wannan shine silar aurena dana Saifudden.
Dan bayan rasuwar yayata gimbiya Zakiyya da kwana 7 aka d'aura min aure da yarima Saifudden, domin nacigaba da rainon abinda tabari.
Banason Yarima Saifudden, domin ina masa kallon *Mijin yayata* amma banida yanda zanyi, dole na aminta da auren domin yima iyayena biyyaya.
Nasha wahalar zama dashi, saboda shi hankalinsa yana kan yayata ne marigayiya, silar soyayyar danake nunama Habeefa (aunty Mimi) d'iyar da gimbiya Zakiyya tabarine ya siyamin soyayyar yarima Saifudden, a hankali har shak'uwa tafara shiga tsakanina dashi. Soyayar dayakema 'Yar uwata saita dawo kaina.
Sai daifa inashan wahalar mama Fulani, duk da kuwa itad'in (Gwaggona ce) tana amsa sunan k'anwar mahaifina, amma k'iyayyar datakema mahaifiyarmu gimbiya Khadija (inno) saita shafemu, duk da abaya tana ik'irarin son mahaifinmu Sarki Abdul'fatah kuwa. Kamar yanda yayata gimbiya Zakiyya tasha wahalarta a gidan nima hakane, saima tawa taso fin ta 'Yar uwata, bansan dalilintaba, wai Ashe dan ina tsananin kama da inno neπ.
“Ina fata dai kina fahimtata Munaya” ‘Momma tayi maganar tana kallona dana rabga tagumi inajin cakwakiyar masarauta.
Kaina na jinjina mata cikin damuwa.
Saitayi murmushi tacigaba da fad'in.
Mama Fulani taso d'iayarta ta farko gimbiya Mansura ta auri yayanmu yarima Abubakar, Wanda babanmu Sarki Abdul'fatah yayma amininsa takwara.
To saikuma hakan bata faruba, dan ita tata dabarar itada iyayenta, idan Yayana Yarima Abubakar ya auri gimbiya Mansura sarauta takoma hannunsu kenan, tunda yarima Abubakar shine magajin masarautar mu, kinga ai d'ansa ne zai gajesa kenan, idan tahad'a auren kuwa yazama jikanatane da masarautar nan gaba.
To saikuma tsarin nata bai yuwuba, saima nida yayata mukazo masarautar gagara badau tushen mahaifiyarmu mukayi kane-kane, gashi kowa yana Saran Saifudden shine zai gaji masarautar gagara badau alokacin, tunda manyan 'ya'yan Sarki Abubakar sun rasu, Saifudden kuma shine babba namiji a lokacin.
Shiyyasa takuma d'aukar karantsana ta d'aura mana muda gimbiya bagobura.
Bayan haihuwar Haneefa babu dad'ewa gimbiya bagobura ta rasu, rasuwar data gigita yarima Saifudden kenan da Sarki Abubakar har ma da jama'ar masarautar gagara badau, amma banda mama Fulani da sauran matan Sarki, dansu hakanma dad'i yamusu.
Sanadin rasuwar gimbiya bagobura Sarki Abubakar ya kwanta ciwo, sai yayi murabus yace a d'aura d'ansa Saifudden a madadinsa.
Wannan Abu yama kowa dad'i a masarautar, amma banda mama Fulani dakejin tamkar tamutu dan bak'in ciki.
Saidai batada yanda ta iya, tanaji tana gani yarima Saifudden yazama Sarkin masarautar gagara badau.
Alokacinne kuma akace dole ya k'ara aure, dan Sarki baya zama da mace d'aya, gashi kuma ni ban haihuba har lokacin.
A rana d'aya aka d'aurama Sarki Saifudden aure da mata biyu. Nanfa mama Fulani tashiga jansu ajiki wai dan a kuntatamin, tana kuma koya musu yanda zasu kuntatama shi Kansa Saifudden d'in.
Sarki Saifudden nada shekara 9 a karagar mulki ALLAH yayma Sarki Abubakar rasuwa, mutuwarnan ta girgiza mahaifinmu Sarki Abdul'fatah sosai, dan saida aka had'a masa a addu'a.
Tun daga wannan lokacin masarautar gagara badau takoma hannun mama Fulani, dan sai yanda tace tanaso Sarki Saifudden zaiyi, dayake shi mutumne mai sanyin hali, baya ta6a sa6a mata.
Duk da haka wannan bai ishetaba, hattada yanda za'a gudanar da mulki saita tsara.
Har lokacin amaren Sarki Saifudden babu wacce ta haihu.
Cikin ikon ALLAH sai gani da ciki, babu kitumurmurar daba aima cikinnan nawaba d'anya zube amma ALLAH ya k'addara mijinki *Muhammad Sameer* saiyazo duniya.
Lokacin Dana haihu shekarar haneef 10 cif a duniya.
Muhammad shine jika namiji na farko da aka fara haihuwa a masarautar gagara badau, dan kuwa matar Jalaludden ma mata taketa haihuwa.
Daga nan nima ban sakeba saida Muhammad yacika shekara hud'u, yanda Saifudden yasha tsangwamar mama Fulani haka Muhammad ma yashata tun yana yaro.
Shima Sameer hak'urin mahaifinsa Saifudden ya gado sosai, dan ko abu aka masa saidai yayi kukansa ya goge hawaye, koni bazai sanarmawa ba, saidai in wata baiwa tagani ko Haneefa (aunty Mimi) su sanarnin.
Da *Ciwon zuciya* na haifi Sameer, dan haka kullum cikin kaffa-kaffa muke dashi saboda gudun samun matsala ga lafiyarsa, da yawa jama'ar gidan sukan masa abune wai dan zuciyarsa ta bugaπ ya mutu. sun manta rayuwa da mutuwa duk Na ALLAH ne.
Da sauri na kallo momma.
Ta d'aga min kai tana murmushin takaici, “hakane d'iyata, kullum burinsu kenan akan Muhammad tun yana yaro..
Ranar wata litinin da asuba Sarki Saifudden yafita sallar asubahi sai kawo manashi akayi cikin gida, wai yafad'i ana tsaka da sallah.
A lokacin kafafunsa ne kawai basa aiki, amma sauran jikinsa yana motsawa.
Nice naita wahalar jinyarsa, ga cikina yafara tsufa, sai jakadiya ke taimakona, amma sauran matan Sarki ko'a jikinsu.
A hankali ciwo yacigaba da girmama a jikin takawa, tun ana kafa har yadawo duka jiki, idonsane kurum ke aiki a lokacin.
A asibitin garinan muke jiyyarsa a time d'in, a asirce batareda jama'ar gari sun saniba.
Acikin wannan tashin hankalin na haihu Namiji, shine Abubakar (Sauban).
Nidai lokacin kawai ina rainon Sauban ne, amma rabi duk Haneefa ce (aunty Mimi) yayinda kulawar Sameer takoma hannun k'anwata Zaituna (mom), autarmu kenan, dan dole aka dawo da ita wajena tana taimakamin.
Na haifi Sauban babu dad'ewa aka maida sarautar Saifudden akan Jalaludden d'an gidan mama Fulani, saikuma lokacin jama'ar gari suka San Sarki Saifudden bashida lafiya ma.
Ko kad'an ban damuba, danni ta lafiyar mijina nakeyi ma.
A lokacin anta kananun magana akan zargin mama Fulani dawasu kuma manyan attajirai, dan akwai wani zaman sirri da sarki Saifudden yayi dawasu attajiran k'asar ana jibi abin zai sameshi, kuma anga yafito ransa a 6ace daga tattaunawar, alamar sun buk'aci wani Abu ya hanasu kenan. suma angansu ran nasu A 6acen. Nikam bamma maida hankali akan wannanba, mahaifina Sarki Abdul'fatah shine kawai tsaye akan ciwon Saifudden, saini kuma da jakadiya.
Masarautar kuwa ai duniya sabuwa. Matan Sarki Saifudden ma duk sun kama gabansu, sunce bazasu iyaba.
Shekararmu d'aya a asibiti babu wani canji, saima jikinsa dake neman fara ru6ewa saboda komai sai an masa. Baya iya d'aga koda d'an yatsane. (Tun farko likitocinmu na nan sun Sanar damu an masa allurar gubane, kuma guba mai had'ari, dan babu makarinta, itakuma tana sakar da jijiyoyin jikine su daina aiki gaba d'aya, wannan yasaka jikin Sarki Saifudden ya sandareπ.
Wani amintaccen likitanmune yabada shawarar mu maidashi India dansu sunada kwararrun likitoci, kuma zaifi samun kulawa da tsaro a can.
Wannan shine silar dawowarmu wannan k'asa, da cuku-cukun mahaifina Sarki Abdul'fatah, dan komai namu mukam ya k'are, duk abinda Sarki Saifudden kedashi yagama k'arewa a neman Magani.
Tunda muka dawo India kuwa Sarki Saifudden yafara samun kulawa ta musamman, saidaifa maganar ta kud'ine. Wasu sarakuna da yawa sun bamu gudunmawa, wasuma suna akan bamu.
Sanin Zara bata barin dami, gashi kullum cikin buk'atar kud'i muke sai mahaifina yakafa wasu sana'oi da sauran kud'enmu, tanan muke samun kud'in shiga. Karatun Muh'd da Haneefa kuma Mahaifiana ke d'aukar nauyi..
Tundaga primary har jami'a anan Sameer yayi karatunsa.
Kiyayyar Saifudden kuma ga mama Fulani saita dawo jlkan Muh'd gaba d'aya, kokad'an bata k'aunar ganinsa, kullum tsakaninta dashi sai aibantawa da jifansa da kalamai masu had'ari ga yaro.
Tunda Muh'd yafara sanin Kansa, yaga halin da mahaifinsa yake saiya fara canjawa daga mai hakuri zuwa mai zafi.
Ga ciwonsa kuma, duk yabi yayta kuntata zuciyarsa akan ciwon mahaifinsa da burin d'aukar fansa.
Muh'd mai fara'a da barkwanci yakoma mutum marason magana da azabar rashin d'aukar raini, duk da hakurinsa nanan bai dainaba, dan zakata masa Abu ya shareka kamar bai ganiba, sai randa yazo k'arshene zaka gane kurenka a wajensa.
Mahaifina Sarki Abdul'fatah shine yamatsa tun Muh'd na secondary school dole idan akayi Hutu yazo najeria, dan acewarsa tahakane kawai zai fahimci sarautar gidansu.
Muh'd ya karanci Engineering ne, dama tun yana yaro kingansa kullum cikin son had'a Abu yake, shine tsinka wayar fitila tsinka ta redio ya had'a wani abun, tunma ina masa fad'a harna bari kawai. Ashe abincinsa awajen yake. Yanzu haka sunada Company na had'a wayoyiπ± da Computersπ»π₯, da sauran kayayyaki dai. Sannan yana wasu business domin dai muke samun kud'ad'en kulawa da mahaifisa da sauran matsalolinmu, dan babu mai kulawa damu a masarautar gagara badau sai Sarki Jalaludden.
Wani zuwa da Muh'd yayi Nigeria shine aka bashi sarautar *Galadima*, galadima Sarautace mai k'arfin gaske, dan sai d'a mafi soyuwa ga Sarki ko k'ani ake bamawa. Kuma akance batada banbanci da sarautar waziri, dan duk abinda waziri zaiyi Galadima ma zai iyayinsa. Akwai ma wasu abubuwan da daga Sarki sai Galadima kan yisu a fada.
Da da farko nace ya mayar musu amma sai mahaifina yace a'a, ai hakan da sukayi dai-daine.
Sharrin kuwa dakika sun masa, har tsautsayi ya jefaki a ciki, sunyine dan hankalinsa ya tashi, har takai zuciyarsa ta buga ya mutu sun huta.
Dan ayanzu ne suke ganin sunfa *kashe macijine basu sare kansaba* Galadima yazamar musu *RAINA KAMA.....*, basuyi tunanin zaikai tsawon rai hakaba, saboda Ciwo mai had'ari dake a tare dashi.
Shikuma Muh'd yafi karkata hankalinsa ga jama'ar wajene sukama mahaifisa haka, koda akwai jama'ar masarautar gagara badau to kalilanne, kuma mama Fulani kawai yake zargi.
Nikuma ba ita kad'ai nake zargiba, amma yakasa fahimtata gaba d'aya har kawo yanzun kuwa. Dagashi har Haneefa sunfi zargin jama'ar waje, don mutananen masarautar suna 6oye musu ainahin fuskarsu ta zalunci, mama Fulani ce kawai tata take a bayyane.
Wannan yasaka tun sharrin da akai muku nasaka amin bincike a kanki, Alhmdllh ban samu wata matsalaba a tarihinki,, daga nan na dukufa addu'a da neman za6in ALLAH.
bamma kai ga furtama kowa matsalata ba sai mahaifina Sarki Abdul'fatah (papi) yace Muh'd saiya aureki.
Nasan ba sonsa kikeba, amma ina rok'on ubangiji da yasa wataran kuso junanku, kinada tarbiyya da wayon da zaki iya canjamin Muh'd, dan banason hallayarsa ta yanzu, nafi son nake ganin walwala atare dashi a ko yaushe, ki taimakeni ki shiga rayuwarsa sosai, dan ke macece, sai kin fishi zama cikin jama'ar masarautarsu, zakuma ki fishi fahimtar halayyarsu, sannan kidinga bashi shawara akan abinda yadace dashi. Inaji a jikina zaki iya canjamin Muh'd, saboda kinada hankali. gudun kar wani yasakama zuciyarki tunani daban yasaka nace yakawoki da wuri, domin kisan yanda zaki rayu a masarautar, kafin kutafi insha ALLAH komai Na zamantakewar masarauta za'a koyar dake kinji”.
Kaina Na gyad'a mata, sannan a sanyaye nace “Momma namiki alk'awarin zai taimakesa akan matsalarnan, kuma zan bama rayuwarsa gudun mawa insha ALLAH, Sai dai Abu d'aya ne ban ganeba”.
“miye baki ganeba d'iyata?”.
“Abokinsa Muftahu, shima a masarautar yake?”.
Murmushi Momma tayi, tace “daga Muftahu har Harun duk 'yan masarautar ne, Muftahu kakanni suka had'a dasu Muhammad, da kakan Muftahu da Sarki Abubakar kakansu Muh'd uwarsu d'aya ubansu d'aya, shikuma Harun d'an waziri ne na yanzu, kuma shima wazirin haifaffen gidanne, saidai inason sanin ko wani Abu kika gani tareda wani acikinsu?”.
Kaina Na girgiza alamar A'a.
Momma ta sauke ajiyar zuciya, “Munaya saikin dage kinji, domin Na had'aki da aiki mai wahalar gaske, mai kuma sark'akiya, musanman akan halayyar Muh'd, dan bai yarda da kowaba dakike ganinsa nan, koyaya Abu ya had'aku sai yayi zargin turoka akayi garesa, kuma zaka Shiga jerin wad'an da yake tuhuma. amma kekad'aice mafi kusanci da Muh'd yanzu, zakifi kowa sanin matsalarsa da wuri, saikuma kin fimu fuskantar tunaninsa, danni kinga jinyar mahaifinsa tasa banwani zauna dasu irin sosai d'innanba, yanzu haka kafin nasan matsalarsa 'Yar uwata Zaitun (mom) tasani ko Haneefa (aunty Mimi), garama Sauban.
Nace “shikenan Momma ki tayamu da addu'a kawai”.
“insha ALLAH muna kan yimuku kullum, ALLAH yayimuku albarka, ya albarkaci aurenku da dukkan rayuwarku da abinda zaku haifa”.
Ban iya amsawa ba, kaina Na k'asa nikam, ko azuciya ma ban amsaba, dan nayi alk'awarin zai taimakesa kamar yanda ta buk'ata. Amma ina gamawa zan nemi sakina, koda nanda shekaru 2 ne kuwa, amma gaskiya Na tausayama Galadima, dan nakula yana cikin tsakkiyar mak'iyane masu fuska biyu. abinda kuma nalura da Momma bata ganeba shine Galadima bawai bai yarda 'yan gidansu nada saka hannu akan ciwon babansa bane, baya dai nunawane kawai, sai dai bansan dalilinsaba.
CCTV camera d'in dana gani a d'akinsace tadawomin a rai, maybe ya sakatane domin sanin masu shiga da fita koda bayanan.
Haka Na kusan yini cikin damuwa da tausayinsa, dan duk saiya bani tausayi wlhy. shiyyasa zaka gansa kullum shiru-shiru, gaskiya 6angaren hak'uri Na yarda yanada hak'uri kam.
***********
Yau saida yamma mukaje muka duba Abie, mun iske Galadima baya asibitin, dama tun da rana yazo gida yay wanka yakuma fita.
Har dare muna a asibitin, saida Galadima yazo muka taho tare, ina gaba ni da shi da khaleel dake barci a cinyata, yayinda sauban da aunty Mimi da Samha ke baya.
Maganar da samha ta fad'amin d'azun a asibiti ta dawomin a rai, Ashe mahaifinsu ya rasu suma shekara 2 kenan, itace d'iyar Aunty Mimi ta farko, sai Hakim da suka rasu tareda babansu, saikuma khaleel auta. Suma a Nigeria da suke zaune, bayan rasuwar mahaifin nasune suka dawo nan india, duk da dangin mahaifinsu sunso kar6arsu papi yahana, babansu tsohon Governor ne shima, mutuwar tasa kuma akwai lauje cikin nad'i shima, dan ya tsananta akan binciken ciwon surukinsa Abie sosai, shiyyasama ake zargin an kasheshine saboda wani Abu daya gani.
Har muka Isa gida bansan hirar dasukeba a baya, dan shima Galadima baya cewa uffan.
Shine ya kar6i khaleel a hannuna, ya sa6ashi a kafad'a muka shiga ciki, har d'akinsa ya kaisa. ni lokacinma harna haye saman..........✍πΌ
Barkanku da juma'a.
Zanyi last page gobe idan ALLAH ya kaimu da rai da lafiya⛹π»♀⛹π»♀.
Network yanata min iskanci tun jiya shiyyasa kuka jini shiru☹
*_YA ALLAH ka gafartama iyayenmu_*πππ»
*_Typingπ²_*
*_HASKE WRITERS ASSO...π‘_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ceπ€π»_*
ππ»3⃣0⃣
..................Da sallama ciki-ciki ya shigo, nayi saurin maida zip d'in rigata sama nafasa cirewa, a sace ya kalleni yawuce bakin gadon ya zaune tareda dafe kansa.
Kallonsa nayi Na kauda idona nima, kusan mintuna 3 kowa da abinda yake tattaunawa da zuciyarsa. d'agowa yayi yakuma kallona, kamar an masa dole yake maganar cikeda k'asaita, “k! Wai bazakima Momma magana ba kikoma d'akinki?”.
Kamar bazanyi maganaba saikuma nayi batare da Na kallesaba, “inaga kaine yakamata kamata maganar ai, dan nima zanfi son haka, duk nabi Na takura zama da Namiji d'aki d'aya”.
Banza yamin bai sake tankawa ba, saima yamik'e yana jan k'aramin tsaki, nikam Na ta6e baki a zuciyata ina fad'in ka iya fad'ar R kafin kamin mazurai.
Baima san ina yiba, yaje wajen wardrobe d'insa ya d'auki kayan barci yanufi bathroom.
Murmushi kawai nayi, danni rayuwar mutuminnan mamaki take bani, ina dad'i kabi ka k'untata kanka irin haka? baka hira da kowa, baka dariya, shifa ko kallo inba labaraiba ban ta6a ganin yanayiba, hakama wak'a banta6a jin yana jiba, koranar dana duba wayarsa karatun Qur'an kawai nagani da Tafseer. nakai dubana gawata 'Yar kanta dakecan gefe a bedroom d'in nasa, mafi yawanci littatafan addini ne awajen, sai English Novels. (To yayi karatun addinine? tunda naji Momma tace anan India ya girmaπ€). Wata zuciya tacemin su India basuda musulmai ne?. “hakane kumafa” nafad'a a fili ina mik'ewa.
Ganinaima bara nacire kayana kafin yafito, daya fito saina shiga nima.
Har ga ALLAH banyi tunanin fitowarsa ba yanzun, dan haka hankalina kwance na zuge zip d'in rigar, na cireta gaba d'aya, shima sket d'in nayi k'asa dashi yafad'i k'asa.
Juyowarnan da zanyi da nufin d'aukar towel dana ajiye saman akwatina sai kawai naga mutum tsaye a k'ofar bathroom, hannunsa rik'eda k'aramin towel yayi tsaye yana kallona.
Bansan Na kwalla k'araba wlhy, Na rarumi towel d'in nayi saurin kare jikina, ALLAH ma yaso k'ofar a rufe take, dan dawuya su Aunty Mimi sujini.
K'arata tadawo dashi daga sumar tsayen dayayi, yawani kauda kansa cikeda basarwa yana ta6e baki, saikuma yaja guntun tsaki yaje bakin gadon ya zauna yana cigaba da goge fuskarsa, dan har yayi shirin barcinsa a ciki.
Jinayi tamkar na makesa, d'an rainin hankali yagama kalleni zai wani miskile fuska asfa baiga abin kalloba. hijjabin sallata na janyo Na saka, sannan nawuce bayi ina hararsa.
Ina shiga yamik'e yana wani munafukin murmushi, abin salla ya shinfid'a ya kabbara shafa'i da wutiri.
Nadad'e abayin nak'i fitowa, saida nabar jin motsinsa duka sannan Na fito, dayake nayi shirina a bayin nima, nazata ya kwanta, amma saina iskeshi zaune a kujerar dake gefen kantar littatafan nan ya bud'e laptop yana danne-danne, gefensa kofine yanata turiri, da alama coffee ne aciki.
Yad'an juyamin baya kad'an, dan haka cikin sand'a Na rufe k'ofar, nakuma tako a hankali har zuwa wajen sofa Na kwanta, duk zatona baya ganina, Ashe yana kallon duk abinda nakeyi ta gefen idonsa.
A ransa yace munafunci. cigaba yay da aikinsa hankaki kwance, bai bar wajenba har kusan 1:30pm, maimakon ya kwanta sainaga yashiga bayi ya d'auro alwala.
Nima har time d'in barci yakasa d'aukata, maganar Momma tanata min yawo a zuciyata, tunanin ta inda zan taimaki Galadima kawai nakeyi.
Ina kallonsa ya kabbara salla. saida yay kusan raka'a 6 yanayi yana sallamewa, daganan ya d'auki alku'ani yafara karatu k'asa-k'asa.
Masha ALLAH nafad'a a raina, danjin yanda muryarsa ke fita cikin karatun littafi mai tsarki, gashi yana fidda kowane harafi cikin tsantseni da kwarewa. Tun ina saurarensa har wani barci mai dad'i ya saceni, bansan lokacin daya kammala ba yazo ya kwanta.
Muduka makara mukayi sallar asuba yau, dan haka shima yau a gida yayi.
Bayan ya idar waya ya d'auka naga yayi kira.
Bayan an d'aga daga can sukayi gaisuwa, jin ya tambayi ya Nigeria Na gane da 'yan can yake wayar. yacigaba da fad'in.
“Nuren naga ka turomin hotonsa, shin a inane yake haka?”.
Bansan mi akace masaba daga can, naga dai yayi kwafa, sai yace “ya maganar Minister? dan nagansa wajen d'urin aurena, ban kuma yi zaton zai zoba”.
Canma aka kuma yin wata maganar.
Zamansa yagyara, yakuma jingina da bangon, dayake yana kan abin salla har yanzun. “kayi k'ok'ari Nuren, yanzu abinda nakeso dakai shine, akwai yarinyarsa d'inan datake karatu a nan jami'ar Abuja, inason a sacemin ita k'arshen watannan, yanzu ka saka ana bibiyarmin komai nata, Shikuma Alhaji Balala driver n sa zaku d'aukemin, dan bincikena ya ganomin shekarunsa 30 dawani Abu yana masa aiki, kuma randa su Alhaji balala sukayi zama da Abie shine ya kaisa masarautar mu, inada tabbacin zai San wani Abu koda kad'anne, kuyi aikinku da kulawa Nuren, banason asami matsala kamar wancan time d'in, gobe kashiga birnin gayu plaza kuyi zama Na musamman da Saleem akan maganar CCTV camera data daina aiki randa abinnan ya faru, ni naso Na zauna dashi, amma kaga Momma tamatsa akan dawowata”.
bayan nacan yagama magana.
Yace “ok babu damuwa, zan turo maka number yarinyar, saiku bibiyeta tanan. sai anjima, ka gaidamin Mom d'ina”.
Koda ya ajiye wayar saiya koma gado ya kwanta abinsa, nikam ina zaune sai cud'awa da kwancewa nakeyi, ban fahimci wayar tasaba gaba d'aya, shin wanene kuma NUREN!? shikuma miye alak'arsa da Galadima kuma?.
Tabbas aikina bazai yuwuba saina San wanene NUREN, wane kuma aiki yakema Galadima a sirrence, su waye wad'annan mutanen biyu daya ambata Minister da Alhaji balala? suna cikin wancan case d'in Na Abie ne? kokuwa tasu dabance?.
Kwanciya ta na juya yanda zanji dad'in tunanin da k'yau, saikuma naga ai ba sanin waye Nuren bane matsalata yanzu, kamata yayi nafara sanin shi kansa Galadima d'in da rayuwarsa, na tuna maganar Momma da tece “shi mutumne dabashi da yadda”. Mutum mara yarda kuwa yanada wuyar sha'ani, kad'an na juyo na kallesa, idonsa a rufe yake, amma ban yarda barci yakeba, na janye idona nima na maida lumshe, barcine mai nauyi ya kwasheni, harya fita bamma saniba inata barci, babu kuma Wanda yazo ya tadani.
Sai around 11:30 na tashi, wani masifar ciwo kaina yakemin, haka dai na tak'ark'ara nayi wanka, nagyara d'akin sannan na sako k'asa, gidan shiru tamkar babu kowa, sai television daketa aiki, zama nayi bisa kujera dafe da kaina.
“ranki ya dad'e lafiya dai?”.
Bud'e idona nayi a hankali, sai naga jakadiya ce, namata murmushi tareda yunk'urin tashi zaune, “wlhy kaina ke ciwo jakadiya, halanma ke kad'aice ma a gidan?”.
“subahanalla, sannu ranki ya dad'e, bara na samo miki abinci saikisha magani, eh ni kad'aice ranki ya dad'e su Sauban sun tafi makaranta. Gimbiya Mimi kuma tana asibiti itama, taga kina barcine shiyyasa tahana a tadaki”.
Nace “ALLAH sarki”.
Wucewa tayi zuwa kitchen, babu dad'ewa saigata tadawo da tire, a gabana ta ajiye tana fad'in “gashi ranki ya dad'e, kici saikisha magani kafin Magajin gari yadawo saikuje asibiti”.
Kallonta nayi da mamaki, “jakadiya waye magajin gari kuma?”.
Tayi 'Yar dariya, “ranki ya dad'e ina nufin mai gidanki, ai magajin gari nake cemasa”.
Murmushi nayi ina girgiza kai kawai, na had'a tea nasha, sannan nasha maganin, anan falon na kuma kwantawa, barci yakuma kwasheni.
Jakadiya na zaune tana gadina.
Da sallama ya shigo, jakadiya ta amsa tareda mik'ewa da sauri ta kar6i kayan hannunsa tana masa sannu da zuwa, yad'an saki fuska yana amsawa. d'aya acikin kujerun ya zauna, sai lokacin idonsa ya sauka kaina.....
maganar da jakadiya take masa ce yasakashi janye ido daga kaina ya maida kanta.
“ranka ya dad'e akai kayan samane?”.
“no jakadiya kibari zan hau dasu, ai sunmiki nauyi, ita wannan mike damunta tayi barci anan?”. ‘yay maganar yana maido idonsa kaina’.
“kanta ke ciwo ranka ya dad'e, amma tasha magani ma, shine barcin ya kwashe a wajen”.
Ido yad'an tsuramin, kafin ya cije lips d'insa kad'an.
Jakadiya tajuya zuwa kitchen, babu dad'ewa tadawo da ruwa ta ajiye masa.
Sannu yamata sannan yad'auka yana sha, itakuma tabar wajen.
Kofin da yasha ruwan ya ajiye, ya maida kansa jikin kujerar ya jingina kansa, tareda maida k'afarsa d'aya kan d'aya, lumshe idonsa yayi, ta k'asan ido yake kallona, tsawon lokaci yana a haka, yayinda nikuma nake barci bansan yana yibama.
Kamar an tasheni saina bud'e idona a hankali, dashi na fara tozali, dan haka namik'e zaune da sauri, tareda warware d'an kwalina na yafa, dan gown d'in material ce a jikina, gashi irin mai santsinan, kuma rigar takamani sosai, a raina nace dukma yagama kalleni, wama yasan tun yaushe yake anan?.
Duk abinda nakeyi yana kallona, sometimes yarinyar nan takan bashi dariya, a d'an zaman dayayi da ita yalura tanada kunya, saidai batason raini, bakuma tada tsoro ko kad'an, ganin ina Neman mik'ewa saiya bud'e idonsa.
Harna fara tafiya saina juyo, danjin kamar ana kallona. idonsa a kaina, amma saiya wani basar tareda janyewa.
Kaina kawai na girgiza, harzan cigaba da tafiya saina tuna nemanfa kusanci nake dashi domin cika alk'awarin Momma da zanyi, baya na dawo nakoma na zauna, muryata a sanyaye nace, “sannu da dawowa”.
Sosai na bashi mamaki, dan haka ya kalleni da k'yau, kamar zaiyi magana saikuma ya fasa, kusan minti 1 dawasu Second's sannan yace “mike damunki kika kwanta anan?”.
“kainane ke ciwo amma yama daina”. maganar dayayice tabani mamaki.
Mik'ewa yayi yana fad'in “ba gulma tasaki k'inyin barci jiyaba, dole ai kitashi da ciwon kai”.
Galala nabishi da kallo, kai wannan guy d'in yafara bani tsoro, dama yasan banyi barciba jiya kenan? Anya guy d'innan baya gani har hanji� nabishi da kallo yayinda yake taka step d'in benen cikeda izza, hanunsa d'aukeda ledojin daya kwashe a falon, saida ya 6acema ganina sannan na sauke ajiyar zuciya.
★*★*★*★*★*★*★
*_Nigeria_*
Tun bayan zuwanmu sallama da tafiyarmu 'yan gidanmu sai suka dainama innarmu magana, musamman yanda sukaga anata fita da abubuwan dana bari a baiwa mutane, innarmu ko'a kwalar rigarta itakam, bata damu da rashin mata maganar dasukeba, harkokin gabanta kawai takeyi hankali kwance.
Innaro kam kud'in da Galadima yabata suka sakata d'agama innarmu k'afa, ko gaidata tayi cikin salama take amsa mata, a jiya harda siyoma su Aryaan sllifas, wai taganine a hanya sun mata k'yau ta siya musu, murmushi kawai innarmu tayi damata godiya ta kar6a.
Wannan k'yauta tasaka mamansu yaa Hameed kasa hak'uri taita sakin habaici, daga nan sauran matan gidanmu suka d'auka suma, innarmu saita saka karatun alkur'ani ma a waya tashige d'aki tarufe kanta.
Har sukaci suka tsire dan kansu sukayi shiru.
Kusan k'arfe hud'u na gamma saiga Zarah wujiga-wujiga tashigo gidan, ga ciki yafito masha ALLAH, Innarmu dake tsakar gida tana wankin kwanuka tayi saurin cewa “zarah lafiya?”.
Jikin innamu tafad'a ta fashe da kuka, “innarsu 2 ki taimakeni zai kasheni, wlhy bani na d'auka masa kud'iba, narantse da ALLAH........”
Tuni 'yan gidanmu duk sun fito, danjin kururuwar Zarah, mamansu yaa hameed tazo ta janyeta daga jikin innarmu, “k mahaukaciyar inace dabazaki nutsu kisan wazaki fad'ama matsalarki bane?”..
Oho ita Zarah ba wannan bane matsalarta a yanzun, takuma fad'awa jikin mamansun tana kuka da rantsuwar ba ita ta d'auki kud'iba.
Ganin tana neman yage musu zani a kasuwa sai mamansu tajata suka shige d'aki.
Wata dariyar gatsatsa maman Safara'u tayi, tareda ta6e baki tana kallon Gwaggon Haleematu dake k'usa da ita “to anfara da bismillah kenan? Wata 6 an koro yarinya da duka?......
Caraf Momy Hadiza ta k'ar6e “yo mai kashi a gindi ai baya toshe hanci yace makwafcinsa na wari, kidai iya bakinki tunda kema kinkai gidan wani”.
“can a bakinki, nakai kuwa, kuma tawa zama daram babu yaji balle nik'a gari, tunda ba auren hange-hange da tauye hak'in wasu namata ba, ai bama saikin zak'eba, munsan mai kaza a aljihu dama baya jimirin Asss!, indai nice kinga tafiyata, kiyi da wani ba niba”.
Tamkar Momy Hadiza zata daki maman Safara'u haka ta hayayyak'o mata, wannan hayaniya ce tafara jawo kunnen makwafta gidanmu, saiga innaro tamkar an jehota, ta shiga tambayar ba'asin hayaniyar, dansu Abbanmu duk suna wajen aiki.
Duk shiru sukai mata, sai innarmu Ce da maman Fauziyya suke fad'a mata abinda yafaru.
d'akin mamansu yaa hameed tashige domin jiyo ba'asin dawowar Zarah n.
Itadai innarmu jikinta duk yayi sanyi, wannan zamanin ko aurar da yaranka mata kayi tsugunne bata k'are makaba, dan sai ALLAH yabasu mazaje na garin dazasu iya hak'urin zama da juna, aurene tunkan ayisa zakaga angama kwashe masa albarka wajen buruka da bidi'oin biki, ga iyaye yanzu gaba d'aya hankalinsu Yakoma ga d'irkama 'ya'yansu kayan mata kawai ba koya musu dabarun zaman aurenba, sun manta kayan mata basu kad'ai bane ma'aurata ke buk'ata a zaman aure, sudai sukan kawo wata nutsuwane da kuma dank'o cikin rayuwar auren, gaba d'aya yanzu zakiga gidajen auren Malam bahaushe sun canja, wuyarta dai akai yarinya miji ya kauda mata budurcine, wata biyu yayi yawa kwarnafinsa ya kwanta saiya fara Neman makusarta, gakuma yaran basuda wata dabara dazatasa su taka tsantsan ga zamantakewar, har yakai an sami sassaucin cin zarafi daga mazajen nasu, to an nuna musu kayan mata sune kawai jigon aure da hangar mallakar mijin kansa, to ALLAH ka zaunar mana dasu lafiya dai agidajensu.
Nace amin innarmuπππ»
★★★★
Kusan minti 10 da shigarsa saina tashi nabi bayansa, waya nakeson ya aramin nayi kiran su innarmu Susan mun sauka lafiya.
Saida nai sallama yabani izinin shiga sannan, saman sofa na iskeshi zaune yana latsa waya, da alama waya yagama ko zaiyi.
Zama nayi a kujerar da yake karatu takusa da kanta, na kwantar da murya cikin sigar ladab nace “yalla6ai ka aramin waya dan ALLAH nayi kiran innarmu da Munubiya”.
Biris yay dani, sai zuwa can yad'ago ido ya kalleni, ya motsa baki zaiyi magana amma jin kai ya hanashi, saiyay shiru kuma yacigaba da latsa wayar, saida yamula dan kansa sannan yajawo ledar daya shigo da ita, wata k'aramar pink d'in souvenirs bag yamik'o min batareda yace uffanba.
Tasowa nayi zuwa gabansa zan kar6a, hanun bag d'in k'aramine, dan haka hanunmu ya had'u waje d'aya, ni da shi kowa saida yaji shock, yay saurin janye hannunsa, yayinda bag d'in tayi k'asa zata fad'i yay saurin kuma k'ok'arin tarewa kamar yanda nima nakawo hannun hagguna da sauri. Sai kawai na damk'e hannunsa kanmu ya gwaru waje d'aya.
Kowanne dafe kansa yayi da sauri, yayinda hanun damarsa dana hagguna suke tallafe da juna mun tare bag d'in karta fad'i.
Na kallesa tamkar zanyi kuka, dan wlhy naji zafi, kansa kamar kwakwa☹.
Hararata yayi yana fad'in “k wane irin kaine dake haka?”.
Haushi saiya kamani, shi baiga nasaba sai nawa, na matso kwallar dasuka cikamin idona, cikin turo baki nace “kana niyyar fasan kai, shine zaka maida abun kaina?”.
Hanunsa daya dafe kai yasaka ya d'an bugi bakina, “k kinma rainani wlhy”.
K'asa na durk'ushe kawai nasaki masa kuka. ya waro ido da mamaki yana kallona, wannan d'an abin dayamin shine na kuka? yarinyar nan akwai rainin hankali fa”.
Ganin abin nawa azimunne saiya mik'e tsaye, tareda d'iremin wayarsa bisa cinyata ya shige bathroom.
Yana shiga nama bayansa gwalo, dama duk cikin takune, sonake kawai nagano lagwansa. goshina nad'an shafa dan gaskiya naji zafi, saima naji wajen kamar yafara kumbura.
Ban tashi a wajen ba nashiga loda numbar innarmu, amma tak'i shiga, saina saka ta Munubiya, itama tak'i tafiya, nad'an ja tsuka, ina kuma shafa goshin, kamar wasa wajen sai rad'ad'i yakemin, ina cikin mulmulawa da matse baki yafito, kallona yad'anyi kamar zai basar saikuma ya kasa, ya k'arasa jikin wardrobe d'insa yana bud'ewa, “har yanzu goshin zafi yake?”.
Kamar zanyi kuka nace, “eh wlhy ”.
Daina abinda yakeyi yayi yajuyo yana kallona, saikuma ya maida drowan yarufe yanufe inda nake zaune. A gabana ya d'urk'usa, k'amshin sabulun wankan ya daki hancina, hannunsa na haggu ya d'aura bisa kaina, ya d'aura na damar akan goshina, sanyin damshin ruwan da taushin hannunsa suka ratsa goshina, a hankali yafara mulmula goshin, nafara matse baki ina rik'e hannunsa, dan wlhy akwai zafi, “please kabarsa dan ALLAH, wlhy akwai zafi fa”, bai saurareniba, duk rik'e masa hannun danake saida ya mulmulamin sosai sannan yamik'e yana hararata da ta6e baki, “halan kekam kina jaririya ba'a miki wankan jegoba?”.
Baki na tunzuro masa, nace “ka kira innarmu ka tambayeta mana, ni ina zan sani”.
Batareda ya shiryaba ya murmusa yana barin wajen. Kayansa ya d'auka yakoma bayi danya sanya.
Nikuma saina mik'e nakoma kan sofa d'in ina bud'e bag d'in d'azun. kwalin wayane mai k'yau, wani dad'i ya kamani, amma saboda jan aji saina maida na ajiye gefena, nacigaba da danna kiran su innarmu.
A haka yafito ya sameni, yana sanye cikin Brown d'in wando da Navy blue t-shirts mai gajeren hannu, ya tsuke k'ugunsa, bai kalleniba yawuce wajen wani kwando mai k'yau da aka zuba sandunan wasan Golf a cikiπ, guda biyu ya ciro, sannan ya tako inda nake yana fad'in “bani wayata idan kin gama”.
Fuska na marairaice nace “ALLAH kagani bamma yiba, tak'i shigama”.
Wayar ya kar6a ya duma number, bakinsa ya d'an ta6e “k bak'auyar inace dazaki kira number a haka? ko nan k'asarkice?”.
Tunawa nai da saina saka + ashe, nace “oh namanta saina saka + wlhy”.
Aljihu ya saka wayar, “saiki bari sai wani time d'in kuma, yanzu sauri nake ana jirana”.
Da sauri nace “zan bika please, wlhy gidan shiru babu dad'i”.
Yana fesa turare yace, “ba yauba, baga jakadiya nan a gidanba, yanzu kuma Khumar zai d'akko khaleel a school ai”.
Shiru nayi bance komaiba, saiya juyo ya kalleni, ganin na kwa6e fuska cikin damuwa saikuma yaji wani iri, juyawa yayi yagara kwalar rigarsa, kafin yaje drowan gefen gadonsa ya d'akko wasu album na pictures har hud'u, saman cinyata ya ajiye batareda yace uffanba, yakwashi sandunansa yakama hanyar fita, batareda ya juyoba yace “wad'annan kayan nakine ki duba”.
Kafin nabasa amsa harya fice abinsa.
Kaina na girgiza ina ta6e baki, a fili nace, “Alaramma mara R ALLAH ya gyarakama Momma kai dai”. (Kifad'a a gabansa mana yarinya. π€£π€).
_______________,,___________,,,______
Da sauri mamansu yaa Hameed ta kwa6e bakin Zarah alamar tayi shiru, saboda shigowar innaro, innaro bata kulaba, dan haka ta zauna a kujerar falon idonta akan Zarah, ganin yanda duk jikinta shatin duka, “kekauwa zara'u miya sameki haka? Ga ciki?”.
Harara mamansu yaa hameed taketa zubama Zarah, amma ina bata kulaba, ta share kwallar fuskarta tana fad'in “innaro wai kud'i ya ajiye a gidan jiya, shinefa yaduba yau bai ganiba, ina kitchen yashigo yana tambayata wai kona canja musu wajene? shine nace bammasan yashigo da kud'i gidan ba bare harna canja musu waje, ko rufe baki bai bari nayiba ya fallamin mari, nikuma naji zafi namasa ALLAH ya Isa, shinefa kawai yacire belt d'in jikinsa yahau buguna, wlhy da k'yar nagudo na fito, nasan idan nashiga gidan Siyama zai iya bina har can, tunda gidan d'an uwansane, dak'yar nasamu napep a anguwar nataho gida”.
Innaro tarik'e ha6a tana fad'in “oh ni marwanatu jikar Falalu, yanzu shi Sa'eedunne yamiki haka da hankalinsa? toke kin tabbata baki d'aukar masa kud'iba?”.
“wlhy innaro ban d'auka ba, kinji na rantse miki, shi dama halinsane haka?, indai ransa ya6aci ko kika masa kuskure sai dai kawai kiji mari, wlhy zuwana gidannan tun bankai satiba yake marina idan namasa Abu, yaune harda duka, gashi ko kad'an bashida hak'uri, Abu kad'an yagani saiyayi tsogumi, idan kuma kin masa na kirki bazai yaba mikiba, dawuya kimabasa Abu sau 10 bai kushe 8 a cikiba, 2 kuma bawai zai nuna yaji dad'i banebaπ’”.
“kai amma wannan yaro anyi wulak'antaccen yaro, yoshi dama dukan mata yake akasa nabashi jikata? Bari su Auwalun suzo, koti zansa su kaishi, sai an kwatar miki hak'inki,”.
“nidai babu wani court k innaro, kawai akirasa amasa bayani a sasantamu nakoma d'akina, inason mijina wlhy”.
“enyeee! A lallai zara'u kinkai kuwa, nikike fad'ama kina son mijinki? to dan ubanki auwalu saiku tashi ki koma yanzu, idan yagadama anjima akiramu jana'izar gawarki”. fuuu tafito tana sababi, kayaya tunta da maimaita maganar da Zarah tafad'a mata yasaka 'yan gidanmu fahimta komai, wasu dad'i har tsakar kansu, (yo dama gidanmu kowa bawani son d'an uwansa yakeba, salon munafurcine kawai da bariki na tsoffin mata).
'Daki Momy Hadiza tashige takira Siyama danjin k'arin bayani, anan Siyaman ke sanar mata wai dama ba wannan ne karon farko da Sa'eed d'in yay Complain Zarah na d'auka masa kud'i ba”.
Momy Hadiza ta rabga salati tana fad'in “k 'yarnan da gaske?”.
“wlhy kuwa Momy, yanzu haka ma gashi anan gidanmu suna maganar da Sulaiman”.
“to ALLAH ya k'yauta, ni dama auren ya mutu ki zauna daga ke saike, danni bama na k'aunar wannan had'in gambizar family d'in, komai yaro yamaka ido nakai”.
“yo nifa Momy wlhy yanzu haka bama magana da Zarah, daga ranar mun had'u da ita a gidan sunan Hanan k'anwarsu, toni shine ya kaini da kansa, itakuma Ashe bashi yakawitaba, shine ta tambayeni miyasa ban biya mata mun taho tareba? Nace mata ai shine yakawoni, itama nazata Sa'eed d'inne zai kawota, shinefa taketa faman fushi da gaba dani”.
“eye, kice tafara miki hassada kawai saboda taga mijinki tafi kulawa dake? to wlhy bance ki d'aga mata k'afaba, karma kituna da ubanki da ubanta ciki d'aya suka fito”.
“insha ALLAHU Momy bazan raga mataba”.
“yauwa 'yar albarka. Yanzu yamaganar kud'in damukayi ranar? kinsan fa bikin nata tahowa?”.
“zan aiko miki Momy, wai Momy da gaske Munaya bata Nigeria? ”.
Tsaki Momy Hadiza taja, cikin bak'in ciki tace “haka dai iyayenta sukace, mudai bamuda tabbas tunda ba'a gabanmu jirgin yatashiba, anzo dai mana sallamar munafunci itada wannan miskilallen mijin nata”.
“aikam Momy indai da sunzo d'in to da gaskefa sun tafin, dan Sulaiman yacemin yaga Galadima a airport shekaranjiya da sister d'inan watawa, shikuma yaje raka babansune zaiyi tafiya”.
“suyita tafiyar mana, kema dan sakaraice ai, yo mi mijin nata yafi naki? Amma kod'an Honeymoon d'in nan da ake zuwa ke kin kasa sakashi ya kaiki”.
“lallai momyn nan, shikenan tunda laifina kike gani, nidai zan kiraki anjima, yanzu jirana suke nakai musu abinci”. ‘bata jira cewarta ba ta yanke wayar’.
Takaici yakuma kama Momy Hadiza, saitaja tsaki, amma saboda munafurci saita nufi d'akin mamansu yaa Hameed jiyo abinda ya maido Zarah gida. (Fuska biyuππΏ).
*******************
Hotunan na ajiye nafara bud'e wayar, woow irinfa wayarsa ce komai da komai, saidai tawa pink ce, gakuma extra condom na wayar har kala uku, kai gsky wayar tayi babu k'arya, layin dana gani a ciki na d'auka na saka sannan na jona charge saboda d'oki, sauran ledojin nahau bud'ewa, duk kayan sawane k'ananu marasa nauyi, kuma bamasu fidda tairaiciba, zan iya sakasu gaban kowa, a raina nace Ashe Galadima yanada kirki haka?, saida nagama had'a kayan waje d'aya sannan na haye gadonsa da yaune karon farko zan haushi, nawani 6ararraje ina kallon hotunan, wasu hotunan abin dariya wlhy, dan wasu yana yarone k'arami, wani a makaranta, wani awajen wasan yara, wani a masarautarsu, wani tareda mom, wani da aunty mimi da sauban, duk inda suke da Abie saida nayi kuka, dan abie duk yana kwancene, k'alilanne yakeda lafiya sannan. wasu kam ya zube wayoyi yanata had'e-had'en abubuwa na wasan yaraπ.
Kallon hotunan ne suka d'aukemin hankali har wani lokaci dasu Sauban suka dawo, bamma san sun dawoba saida Samha tahawo saman.
Zama tayi tanamin bayanin wasu mutanen jikin hotunan muna dariya, bamu sakkoba saida Sauban ya hawo yakiramu.
******
Sai bayan isha'i suka dawo shida aunty mimi.
Ina d'aki zaune har sannan ina kallon pictures d'in ya shigo, d'ago kaina nayi na kalleshi tareda amsa masa sallamar. Namasa sannu da zuwa.
Ciki-ciki ya amsa yana zubewa bakin gadon, d'an kwanciya yayi kusan minti 10 kafin yamik'e yashiga bathroom, kusan 1hour sannan yafito maybe su yalla6ai an sauke nauyine (π½π€).
Yau saida na jirasa harya idar da shafa'i da wutirinsa, dan magana nakeson muyi, ganin ya idar ya zauna latsa wayane nace “dan ALLAH yalla6ai in tambayeka?”.
Batareda ya d'agoba yace “uhmm”.
Zamana na gyara cikin nutsuwa nace, “shin tunda Abie yafara jiyya anta6a masa maganin gargajiya ko amaida hankali ga addu'oi haka?”.
Yanzun kam d'ago ido yayi ya kalleni, dama tunda nafara maganar ya dakata daga latsa wayar.
“lips d'insa yad'an cije, kamar zaiyi magana saikuma yay shiru.
Nace “kayi hak'uri idan nashiga hurumin daba nawaba”.
Nanma shiru yamin, saida yaja wasu mintuna kafin ya ajiye wayar yagyara zamansa, cikin alamun bak'in ciki yace, “duk an gwada masa, saidai gaskiya bakamar yanda aka maida hankali gana asibitinba, saboda anriga da an sanar mana Allurar gubace aka masa, amma muna k'ok'arin sakashi a sallalolinmu na farilla dana nafila. Kullum addu'oinmu akansa yake”.
Ajiyar zuciya na sauke, nace “ALLAH yabashi lafiya, yakawo mana iyaka, yakuma bashi ikon cinye jarabawar nan”.
“amin yafad'a a la66ansa”.
Dagani harshi babu Wanda yasake magana har muka kwanta, saidai yauma banyi isashen barciba, inata cud'awa da kwancewa, har gabannin asubahi kafin barcin ya saceni..................✍πΌ
_To Alhmddlh my sweet fans, zamu dakata anan kenan, saikuma ALLAH yakaimu bayan salla darai da lafiya, zanbar wannan a matsayin *RAINA KAMA..... PART ONE* yanda zamu tafi a tsare kawai, basai mundawo ba kuma mushiga tunanin inama aka tsaya? Ina kuma za'a tashi, a *RAINA KAMA PART TWO* zamuga yanda Munaya zata taimaki Galadima kamar yanda Momma ta buk'ata, shin zai bata had'in kaima Kuwa? domin kunji Momma dai tace bashida yarda? ya matsayin auren Zarah? Muftahu yaya zata kasance idan Galadima ya cafkoshi? shin Munaya tanada wani fikra ne game da ciwon Abie?. wannan amsoshin duk suna cikin *RAINA KAMA PART TWO* da zaizo bayan sallah insha ALLAHU my guys, one Luvπππππππ₯°ππ»_
_tabbas banida bakin godiya a gareku, saboda addu'oi da mahaifina ke samu agareku, Comments naku suna matuk'ar sakani a farinciki sosai, ngd ALLAH yabar zuminci, duk inda masoyin wannan buk yake yasaka aransa yana can k'ark'ashin zuciyar Bilyn Abdull.π₯°π₯°π₯°π₯°πππππππππππππ»π€π»._
_ga azumi zamu shiga, 'yan uwana dan ALLAH mu maida hankalinmu ga ibada, sadaka da k'autatama marasa k'arfi, marayu,, k'autata mu'amullarmu da jama'a dayin amfani da abinda malamai zasu fad'akar damu, karya zam kullum muna wahalar zuwa tafseer amma bamu d'aukar komai, da bayan salla yawuce munkuma koma kan munanan ayukanmu, karmu manta irin wannan watan saikuma mai rabon gani, sau 1 tak yake zuwa mana akowacce shekara, wani yawuce agaresa kenan har Abadan, zata iya yuwuwa nice maπ, zata iya yuwa kece 'Yar uwaππ»π, zata iya yuwa kaine d'an uwaππ»π. dan ALLAH mu gyara please & please, muyi amfani da damarmu kafin ta kufce mana, (kullu nafsin za'ikatul maut, kowane rai saiya d'and'ani mutuwa, ubangiji bai turo maka date d'in da rundunar mala'iku zasuzo d'aukar rayin nakaba,π mutuwa bata kwankwasa k'ofa, batada wata alamar yanda zatazo ta riskeka, kana tafiya ne, ko kana barci, ko kana salla, ko zaune, ko kana hira, ko kana aikata wani sa6o, ko kana wani abin alkairiπ, ya ALLAH ka d'auki ruhinmu muna masu imani agareka da tsoranka, ALLAH ka gafarta mana, kamana maganin abinda muka Sani da wandama bamu saniba._
_ina rok'on dukkan Wanda na 6atamawa a yayin wannan rubutun ko kafin shima dan ALLAH Ya gafarceni, nidai na yafema kowa._π’ππ»
*_duk masoyina na gaskiya Dan ALLAH inason yasakani a ddu'arsa ta cikin azuminnan koda sau d'ayane, idan munada Rabon haihuwa adunaya nida mijina ALLAH ka azurtamu da samu masu albarka cikin sauk'i da rahamar ubangijin talikai, idan ba alkairi bace agaremu ALLAH kasamana hak'uri da juriyar azuciyataπππ», ALLAH kayaye mana dukkan damuwarmu baki d'aya._*πππ»
Dan ALLAH ko sau 1 yane kar'a manta daniππ»π
Amin afuwa zan rage groups saboda yawan groups d'in suna cimin data wlhy, idan nayi sub na wata d'aya ko sati bata yimin take k'arewaππ».
Ngd sosai, ALLAH yabar zuminci, ALLAH yasa munada rabon sake had'uwa a bayan salla, ALLAH ka kar6i ibadunmu baki d'aya. yabamu juriya da hak'urin ibadar dake tunkaromu nanda kwana 1ππ».
Happy Ramadan Advanceππ₯°π₯°π₯°π₯°πππππ»
0 comments:
Post a Comment