Shattima ya kalli Ammy bayan sauke wayar da yai a kunnesa.
鈥淔ateema ce wai an ganta a Abuja hannun Muhseen鈥�
Ammy ta kalleshi duba irin na mamaki duk da kasancewar bata cikin yanayin dadi, bata damu da hawayen da ke fuskarta ba ta ce.
鈥淲ane Muhseen din?鈥�
鈥淣a Mama Fulani鈥�
鈥淎 Abuja kenan?鈥�
鈥淓h ina tunanin abun da nai ma Hajiya Karama ne yasa ta janye kudirinta a kan Fateema, ita kuma mahaifiyarta ta kashe Maijidda鈥�
鈥淏a ka da tabbacin yarinyar ta bata ne saboda Zainab, sai na ke jin kamar babu sa hannunta a ciki, kuma be zama lallai dan Maijidda ta mutu ba ace Iya, domin Waziri ya fada min asibiti sun ce tafoit ce, amman na san mahaifiyarta da kowa kai zai zarga, idan har Iya ce ai ita sai ka aura suke mutuwa wannan kuma tun kamin ayi auren ta rasu鈥�
鈥淢ai son abun ka ya fika dabara Ammy, bana iya gane komai a yanzu, ba zan iya cire Iya daga zargi ba, kamar yadda zuciyata ta kasa aminta da Zainab鈥�
鈥淜a tafi gurin jana'izar kar ayi ba kai鈥�
A hankali ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya fice daga dakin, Ammy ta share hawayenta ta mike tsaye ta nufi dan karamin dakinta dake gefen wardrobe inda take canja tufafi, wani yadi marar nauyi ta saka ta saka Hijabinta sannan ta fito, sai kuma ta zauna bakin gadonta ta dafe kanta, babu wanda take tunani sai Hajiya Talatu, da Waziri duk da kasancewar ta san Baba Waziri mutum ne mai tawakkali sai dai be zama lallai Hajiya Talatu ma tai ba daman can ba son ta take ba balle kuma yanzu da zata ga kamar saboda za a hada auren yarta da Shattima ne ta mutu. Ammy ta kusan awa daya a dakin kamar mai kunyar fita, tana tunanin mikewa tsaye ta fita sai wayarta dake gafen gadon tai ringing, Hannu ta kai ta dauka ganin number Mama Fulani be bata mamaki a tunaninta ko zata sake wata maganar ko kuma ta fada mata cewar tana tafe.
鈥淎mmy...! Yarinyar ta fada miki abun da ta fada min?鈥�
鈥淜amar na me?鈥�
Mama Fulani ta labarta mata kadan, sai Ammy ta sauke ajiyar zuciya.
鈥淭a fada min鈥�
鈥淎mman kike zaune a nan? Har kina kallon Hajiya Balki? Kai ba ma Hajiya ba Balki zance, ta ashe miji da ta kashe miki miji ta tarwatsa rayuwarku?鈥�
鈥淏a komai ya kamata na yarda da shi ba, domin babu hujja kwarara a kan haka, idan nai tunani sai na ga ita ma ai tana da yaya fiye da yadda na ake da su da Mai Martaba, to mai zai saka ta aikata haka? Ko da ma ace akwai Hujja, idan nai unkurin yi mata wani abun za a zargi ko dan tana kishiyata ce ina son na kashe mata aure ne, kuma idan yarinyar kadai bata isa shaida ba鈥�
鈥淭o zauna nan kina jiran hujja, ai komai bincike yake so, kuma idan aka titseta dole wata rana a gano gaskiya, ke ma dai ina ganin sun dan taba ki kin zama wata Salahu zaune kawai kike a gida?鈥�
鈥淭o Fulani ya zan yi? Mijina ba lafiya, duk wata dawainiyarsa da kula da shi akaina yake, ga yayana ma ba su cikin natsuwa Nana ma daga baya baya nan ne na samu ta natsu, ga jama'ar gari da yan'uwa, ga Hajiya Balki ita kanta, abubuwa sun min yawa kwakwalta a cushe take鈥�
Ammy ta fashe da kuka tana jin kamar ta mutu ta huta.
鈥淭o ni tawa bata cushe ba, na kira wayar Waziri bana same shi ba, ki aika a fada masa na ce kar a kai Maijidda a kabari a kira Iya ta tsallakata鈥�
鈥淭afiya kam Maijidda ta tafi Fulani, sai dai fatan samun rahama鈥�
Haushi ne yasa Mama Fulani ta kashe wayar, Ammy ta mike tsaye ta saka wayar a jakarta sannan ta fito ta rufe dakinta. Ko da ta fito direbanta har ya faka mota yana jiranta, daman tun da ta saka Jekadiya ta fada masa yake jiran fitowarta, fitowa yai da sauri ya bude mata ta shiga, sai dogaran da suke dayar motar suka matso da motarsu gaba.
鈥淜a fada musu kai kadai zaka kai ni, gaisuwa ce bana bukatar rakiya鈥�
鈥淎n gama ranki ya dade鈥�
Ya fita motar da sauri ya isa gurinsu ya sanar musu sakon Ammy, sai suka ja motar zuwa inda aka saba ajeta, shi kuma ya dawo cikin motarsa ya shiga.
鈥淎llah ya ja zamaninki ya kara miki lafiya鈥�
Ammy dai bata ko kalli inda yake ba har suka isa gidan Waziri, a nan Ammy ta dauko mask dinta ta saka, daker suka samu gurin fakin a cikin gidan saboda motocin da suka cika gidan, haka Ammy ta fito ta ratsa cikin mutane tana sanye da hijabinta da kuma face mask ta wuce cikin gidan domin wajen gidan maza ne a ko'ina.
聽 Hankalinta be kara tashi ba sai da ta shiga bangaren Hajiya Talatu, baka jin komai sai dariyarta dariya bata wasa ba, irin dariyar da ake kyalkyaltawa wanda ake cewa bata da kyau ko a musulunci, mutanen da suke falonta kuma suna ta aikin kuka, kanen Maijidda da yayenta babu mai iya ba wa wani hakuri, Ammy bata san lokacin da hawaye suka fara saukowa mata ba, sai jikinta yai sanyi sosai.
HAJIYA BABBA POV.
Haka ta wuni ta kwana ba eh ba aa, bata cewa komai kuma duk abun da aka bata bata ci, sai dai tai ta kallon mutane, idan aka ce ci sai ta bude baki ta saka ta tauna amman ta kasa hadewa, haka take a ruwa ko tea ko ruwa duk abun da ta saka a baki ko yayanta suka saka mata sai ta kasa hadewa sai dai ya dawo mata. At first sun dauka ko damuwar abun da Sirleem ya aikata ne, sai dai ganin har an kwana an wuni bata canja ba gashi tsawon dare bata runtsa ba ya fara bawa Karima da Jurry tsoro. Sirleem kan tun da ya bar gidan be dawo ba sai washe gari misalin takwas a tunaninsa zuwa lokacin abun ya sauka a ranta ta dan huce. Ko da ya shigo dakin Kausar na zaune kusa da ita ta kama hannayenta ta rike sai kuka take.
鈥淗ajiya ina kwana鈥�
Ya fada da tunanin zata amsa masa ko da a cikin fushin ne, ko kuma ta kalli inda yake amman ba tai ko daya ba.
鈥淏a ta yi magana ba tun jiya, kuma komai aka saka mata dawowa take da shi, bata cewa komai kuma ba ta runtsa ba har garin Allah ya waye鈥�
Sirleem ya mike tsaye da sauri ya karasa kusa da ita ya kama kafafuwanta ya rike.
鈥淗ajiya dan Allah ki yafe min? Dan Allah ki yi magana, ki yafe min Hajiya鈥�
Tana bude bakin da zimmar magana sai bakin nata ya juye ya bar muhallinsa koma gefe daya, wato gefen kuncinta na hadu.
鈥淚nnalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un, Hajiya鈥�
Ta kalleshi yawu na zazzago mata kamar wata musaka. Take Sirleem ya fashe da kuka.
鈥淒an Allah ki yafe min Hajiya, ba zan sake tsaba umarninki ba, kuma zan saki Falmata yanzu, zan auri Nana, Wallahi ba zan sake saba umarninki ba鈥�
Ya juya ta sauri ya fice daga dakin, Kausar ma ficewa tai da gudu tana kuka. Sai ga Jurry da Rima sun shigo hankali tashe, su suka rikata ta mike tsaye da taimakonsu suka saka ta mota zuwa asibiti, suna isa abun ka da babbar asibiti kuma ga ta matar babban mutum sai su karbe ta da sauri suka shiga yi mata gwaje gwaje. Bata motsa ba sai da aka soka mata allura za a debi jininta.
鈥淲ashhhhhhhh鈥�
Ta fada yawu na biyowa ta bakinta da yaki rufuwa. Duk iya gwanje gwajen da sukai ba su gano ciwom komai ba, domin da farko likita ya dauka ko hawan jini ne domin shi ya fi yiwa mutum haka, sai dai ya auna ba awo daya ba be ga hawan jinin ba.
SIRLEEM POV.
Driving yake hawaye na sauko masa kamar ba gobe, ko a lokacin da ya rasa mahaifinsa be yi zubar hawaye masu zafi kamar yanzu ba, domin a yanzu yana ganin idan Hajiya ta mutu shi ne sila, domin be taba ganinta a hali makamancin wannan ba, be taba tunanin abun zai taba ta har haka ba.
鈥淗ajiya dan Allah ki yafe min鈥�
Ya fadi haka yana tukin ya fi a kirga, jikinsa sai rawa yake, kukan da yake ya saka zuciyarsa sai zafi take, kuka yake bana wasa ba, kuka irin na mace hawaye sun sama sa'ar lalata masa fuska, sai da ya iso gidan Momy sannan ya ciri tissue ya goge fuskarsa, rabonsa da gidan tun jiya da ya shiga ya ga Falmata sai dai be yi maganar komai da ita ba ya fito, be kuma koma gurin Hajiya Babba ba sai ya wuce gidansa ya kwana a can. A harabar gidan ya faka motarsa, ya bude gurin da yake aje paper, ya dauko diary ya dauko bironsa, sai ya dora kansa saman sitiyarin motar ya yana hawaye yana jin zuciyarsa kamar zata rabe gida biyu. Sai dai ba shi da zabin da ya wuce haka, sai dai har ga Allah baya son sakin Falmata. Dago kansa yai ya runtse ido ya cige bakinsa hawaye na cigaba da sauko masa, daker ya bude idon ya bude diary ya dora hannunsa dake rawa yai rubutu a jiki, sai ya fashe da kuka kamar ba namiji ba. Sai kuma yai sauri zarar tissue ya goge fuskarsa ya cire paper da yai rubutun a jiki ya bude motar ya fita. Brown jallabiya ce jikinsa kana ganinsa ka san yayi kuka ba kadan ba domin idonsa da farar fuskarsa ya nuna, sai da ya sauke ajiyar zuciya ya fi a kirga sannan ya nufi entrance din ya fara takawa har ya isa gaban kofar falon, wasu hawayen ne suka cika masa ido sai yai saurin sharewa ya danna door bell din. Babu bata lokaci Momy ta bude masa kofar daman tana zaune falo cikin shirinta na tafiya office domin duty safe take.
鈥淪irleem Lafiya?鈥�
Sai ya kasa kallonta kuma ya kasa ce mata komai har ta ba shi hanya ya shigo cikin falon.
鈥淚na Falmata?鈥�
Ya tambaya daker tana danne numfashinsa dake fisga.
鈥淭ana sama, wai me ke faruwa ne? Tun jiya bata ci komai ba ko tea da na kai mata da safen nan bata sha ba, ni ban gane komai ba kuma...鈥�
Kamar zata labarta masa zancen Ameer, sai kuma tai shiru ganin kamar be dace tai maganar ba a irin wannan lokacin da damuwa da samu muhalli a fuskar Sirleem. Be ce ma Momy komai ba ya nufi upstairs din zuwa kamar baya som tafiya, Momy dai ta bishi da kallo har ya haye sama ya shiga dakin Ameer inda Falmata take.
Yana shigowa Falmata ta mike tsaye da sauri tana kallonsa, shi ma kallonta yake sai hawaye suka samu hanya a idonsa, tana ganin haka jikinta yai sanyi sai ta hade hannayenta guri daya nata idanuwan suna ma hawayenta lalle marhabun. Takawa tai ya karasa kusa da ita yana kallonta sai kuma ya rasa abun da zai fada mata, ita ma kallonsa take tana hawaye daman ta dade da raya cewar Hajiya zata cilasta shi ya sake ta.
鈥淜a sake ki Sirleem matukar sakina zai saka Hajiya ta yafe maka, ka sake ni matukar sakina zai shirya tsakaninku da Hajiya...鈥�
Ta fada ararrabe saboda kukan da ke cinta. Kansa ya daga sama ya kalli pop tare da jan numfashi ya sauke, sannan ya sauke idonsa a kanta, cike da nauyin kafa ya cira ya taka zuwa inda take tsaye sai ya rumgume ta tsantsan a kirjinsa kamar zai sakata cikin jikinsa, hakan da yai sai ya bata damar fashe kurjin kukan da da ya girma yai kumbura a zuciyarta, ta dago hannayenta ta rike rigarsa saitin kirjinsa tana ta kuka kamar ranta zai fita, shi ma hawayen yake sai daya jika dankwalin kanta.
鈥淚 love you, Sirleem Love you so much鈥�
Ya furta cikin muryar mai karkarwar kuka, sannan ya hade yawun bakinsa ya sake ta ya kama hannunta ya danka mata takarda, karba tai tana wani irin dauke numfashi tana kallon fuskarsa tai baya baya sai ya juya da sauri domin ba ya son hada ido da ita, cikin hanzari ta kai hannunta ta kamo hannunsa.
鈥淪irleem karka bar ni dan Allah, idan ka tafi ban san ya zan kasance ba, kai ka kadai ne gata a yanzu kai ne rayuwata...鈥�
Ta fada tana jin wanin irin yanayi da bata taba jin kanta a ciki ba, idonta har wani hayaki suke.
鈥淣i kuma mahaifiyata ita ce rayuwata, ba zan iya jabar ki na bar mahaifiyata ba, ban taba ganin Hajiya a irin halin da na ganta a yau ba, ba zan jama silar bakincikinta ba...鈥�
Ya saka dayan hannunsa ya banbanre hannunta da ta rike hannunsa na dama da shi, ya fice daga dakin cikin sauri. Faduwa tai kasa tana wasu kalar hawaye masu zafi da kona fuska sai ta matse jikinta ta rumgume kanta tsantsa, ta sauke idonta akan hoton mahaifiyarta.
鈥淢a... Ma... Ma... Mama...鈥�
Ta furta daker muryarta na rawa, wani irin abu ta ji kamar zuciyarta zata kone mata kirji, faduwa tai durkushe ta kasa yarda Sirleem ya rabu da ita a lokacin da ta fi tsananin bukatarsa. Mikewa tai tsaye ta fita dakin da gudu, yadda ta sauko downstairs din ma sai da ya ba Momy tsoro kamar zata tashi sama haka ta nufi kofar falon ta bude, ta bi motar Sirleem dake kokarin fita gate tana wani irin kuka tana kiran sunansa.
鈥淪irleem.... Sirleem.... Sirlee....鈥�
Bata karasa sakamakon shakewar da muryarta tai sai ta fadi a harabar ta fashe da matsanaicin kuka. Momy ta fito da sauri ta yo kan Falmata ta kamata.
鈥淟afiya?鈥�
Kamar mai jira sai ta juyo da sauri ta kama hannayen Momy ta rike gangam.
鈥淢omy ya sake ni, Sirleem ya tafi ya bar ni dan Allah Momy ki ce ya dawo...鈥�
鈥淚nnalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un鈥�
Momy ta furta cikin rudani da rashin fahimta. Sirleem ma tukin yake yana hawaye yana jin jikinsa kamar ba shi ba numfashinsa har kokuwa yake da shi.
Ina mata wadan da suke son sayen kaya kamar su laces, atamfa, materials,shadda lace, normal shadda, atamfa lace, veil's, shoes and bags, da sauransu kuzo ga MAMAN AHMAD tazo dan tashare hawayenku kudai kunemeta ta wannan number聽聽 08032350261聽 banan kadai tatsayaba tanada kayan order kama dana kitchen,tufafi,kuma order ta Bata dadewa ,tana saida kayan gyara kamar su Al'ajabu,shu'umar humra wannan inbakida aure Bama saida maki,hadin kaza me yasin,akwai na mallaka wanda wannan ana rubuta shi atafin hannu ke zakiyi wannan,turaren wuta,kulacca,da sauransu
Mazauninsu nanan a samaru Gusau Zamfara state
Muna aika kaya kowace jaha da wajen kasar nan cikin aminci da yardar Allah kunememu kusha mamaki
https://wa.me/qr/MYY56BH3RMFDG1
03/12/2021, 18:59 - 馃馃馃馃: *Khadeeja Candy*
Tana yunkurin ta tashi sai ta ji cikin ya mata nauyi kamar an jefa mata katon dutse a ciki, da farko ta yi tsammanin ko dan ta cinye naman ne duka duk da ta san bata saba haka ba, ko mugun ci tai yana da wahala ta gagara tashi. Jinginawa tai da gadon tana dan hutawa na mintuna kamin ta sake yunkura ta ji ya fi na dazun nauyin gashi ba ciwo yake mata ba. Kallon cikin tai da mamaki yana da da girmansa kamar da, amman ya mata nauyin da bata isa ta mike tsaye ba. Hannunta ta kai ta bude rigarta tana duba cikin.
鈥淎a wai ya haka ne?鈥�
Ta tambayi kanta tambayar da bata da amsa, sai kuma ta rufe cikin ta sake mika dukan karfinta ta yunkura ta tashi nan ma ta kasa, ta sake yunkurawa a karo na hudu nan ma dai ta kasa tashin.
鈥淢a ke faru da ni?鈥�
Ta sake tambayar kanta, kamin ta sake yunkurawa sai ta ji nauyin ya sake karuwa fiye da dazun ma, shiru tai tana ta tunanin dalilin faruwar hakan a gareta bayan taba taba hakan ba, sam ba ta kawo cewar saboda ta ci kurwar Maijidda ba ne, har sai da ta ji kankarun dake cikinta na maita sun fara mata motsi, a firgice ta kai hannu ta dafa cikin tana zaro ido.
鈥淢iye haka kuma? Miyasa na ke jin haka yanzu yanzu?鈥�
Kadan kadan suke motsa mata sai kuma su tsaya, sau uku suna mata wasa a ciki sannan ta ji abun ya tsaya mata, a nan ta sake yunkurawa da dukan karfinta sai gata ta mike a tsaye nauyin da take ji duk ya daina ta koma normal kamar da, sai dai mamaki be bar ta domin bata taba yin haka ba kuma bata yi tunanin akwai wani abu da zai saka ta tai haka ba.
聽 Kwantawa tai saman gadon tana ta tunani kala kala, wata zuciyar na raya mata wata kila iyayen Maijidda sun bata magani mai karfi ne ta sha bayan ta kama kurwarta shiyasa ta ji haka, wata kila kuma wani izon ne akai mata, da wannan tunanin bachi yai gaba da ita, ta kwashi bachinta mai dadi har sai da ta hatse bata barka ba sai kusan la'asar, kamar wanda ta tuna wani abu haka ta sauko saman gadon da sauri.
聽 Bandaki ta shiga tai wanka da ruwan sanyi duk da kasancewar akwai sanyi sanyin hadari a garin, tana fitowa bata ko tsaya shafa komai bata saka wasu tufafin ta dauki tsohon gyalenta ta yafa ta saka talkami ta fito ta shiga dakin Zainab. Kwance ta same ta ruf da ciki tana ta aikin kuka.
鈥淲ai ke yaushe za ki daina kukan nan ne?鈥�
Zainab ta dago ta juyo tana kallonta da idanuwanta da sukai ja sosai saboda kuka.
鈥淏abu rana, domin babu ranar da bakincikin nan nawa zai gushe, dan haka babu ranar da wadannan hawayen za su tsaya鈥�
Iya ta tabe baki tana mamakin yadda Zainab take son wahalar da kanta.
鈥淭o idan kin gama kuka sai ki ta tafi gidan Waziri ayi gaisuwa da ke鈥�
Zainab ta tashi zaune da sauri tana kallon Iya cike da mamaki.
鈥淲aya rasu?鈥�
鈥淢aijidda yar wajen Hajiya Talatu鈥�
Baki sake Zainab take kallon.
鈥淢aijidda matar za a aurawa Shattima? Yar wajen Baba Waziri?鈥�
鈥淚ta fa, rai yai halinsa kin san kowa da lokacinsa鈥�
鈥淲aya fada miki ta rasu?鈥�
Iya ta dauke kai ta juya ta fita ba tare da tace komai ba. Zainab na ganin hakan tai saurin saukowa saman gadon ta biyo bayanta
鈥淗akan na nufin ke kika kasheta kenan?鈥�
Iya ta juyo ta kalleta.
鈥淒uk abun da zuciyarki ta raya miki ki dauka shi din ne, domin ba zan iya wanke kaina daga zarginki ba鈥�
鈥淏a zargi na ke ba, na san ai ke ce, amman ban yi tsammanin za ki sake aikata irin wannan abun ba, ko dan halin da na shiga, ammn hakan be dame ki ba, bayan duk zargi da kyamar da aka fara nuna mana? Kuma yanzu duk wannan be dame ki ba? Har zaki iya takawa ki je musu gaisuwa? Iya ke wace irin halittace?鈥�
Zainab ta karasa cikin kuka.
鈥淚dan ban tafi ba ai su ma sai su zarge ni kamar ke, kara na shiga ayi komai da ni, na watsar da komai nawa yanzu babu ruwana da wani Shattima balle danginsa har ta kai ga matar da zai aura, idan kim ga dama ke ma ki zo ki musu gaisuwa, domin babu ruwan Hajiya Talatu da abubuwan da suka faru bata mana komai ba鈥�
Zainab ta share hawayenta cikin wani irin bakinciki da takaici marar misaltuwa.
鈥淏a zan zo ba, kuma ba za ki dawo ki same ni ba鈥�
Tana kaiwa nan ta juya ta shige dakinta, Iya kam bata ce komai ba ta saka kafata ta fice daga gidan, a tunaninta Zainab ta yi hakan ne kawai saboda ta hana ta tafiya. Jikin window Zainab ta tsaya tana kallon Iya har ta fice daga gate din da mai gadin ya bude mata.
鈥淵a isa haka yanzu kan, komai ya kare鈥�
Ta juya cikin damuwa ta fice daga dakin ta shiga dakin Iya, wardrobe dinta ta bude ta soma bincikar kayanta har ta kai gurin atamfar da ta nade tukunyar tsafinta ciki, dauko dankwalin tai ta bude ta fiddo tukunyar tana kallo jikinta sai rawa yake, sai da ta hade yawu sannan ta dora tukunyar a saman gadon Iya tana ta jin tsoro. Can kuma ta tashi ta nufi wardrobe din tana ta kara dubawa ko zata ga wani abun, sai da ta zazzage komai na ciki ta duba bata ga komai ba, sai ta koma gurin da take yan komatsanta wato karkashin gadonta ta soma janyo abubuwan da suke nan, yawanci duk kayan cin abinci ne sai yan ledodi da talkalmi, mikewa tai tsaye ta dage katifar ta yadda zata ga komai, sannan ta dawo tana ta bude bude kwanonon, har ta bude kwanon da Iya ta zuba naman Maijidda a ciki, ganin maskin yasa ta dauka ta shinshina tana mamakin na inda ta samu nama domin ita har yau bata san ta kan maitar ba balle ta san Iya na cin kurwa ne, a tunaninta kashewa kawai take. Aje kwanon tai ta bude wani babu komai a ciki ta sake budewa shi ma wayam, hka ta rika budewa duk wani abu mai murfi ta kai ga kitsen da iya ta aje, shi ma shinshinawa tai ta aje tana mamakin inda ta samu nama ta soya ta cinye ba ta bata ba, bayan bata saba mata haka ba. Hannunta ta kai ta bude kwaryar dake rufe da faifai sai tai arba da aci balbal a ciki na gwangwani sai tsohuwar kaya da allurar, allurar ta fara dauka ta duba zuciyarta na raya mata cewar wata kila iya na tsafi da ita ne, sannan ta dauko kayar ita ma ta duba har ta yi baki sabar tsufan da tai.
鈥淢e take da wannan abubuwan kuma?鈥�
Ta tambayi kanta tana kallon kayar cike da kyankyami, daukarsu tai ta je ta shiga bandakin Iya ta jefasu a ciki, sannan ta fito ta dauki tukunyar dake saman gadon tana dubawa. Tukunyar kasa ce da aka rufe bakinta da jan kyalle, sai da tai kamar ta bude kyalle ta gani ko miye a ciki sai wata zuciyar ta hana ta, daga tukunyar tai sama ta buga ta da kasan tile din iya karfinta. Take rukunyar ta watse kasa sai ga wani dan karamin maciji a ciki mai kai biyu. Wani ihun tsalle Zainab da daka tare da saka ihu ta ta ranta a ana kare sai waje. Mai gadin na ganinta ya mike tsaye da sauri yana tambayar ba'asi.
鈥淗ajiya Lafiya?鈥�
鈥淢aciji dakin Iya鈥�
鈥淢aciji kuma ta ina ya bi鈥�
鈥淥ho je ka kashe shi dan Allah鈥�
鈥淜ai ai sai dai a kira mutane, ina ni ina kashe maciji wani ma aljani ne, ai shiyasa ake cewa kar mu yi saurin kasu su mu hada su da Allah su tafi鈥�
Ko kamin ya gama maganar Zainab ta bude gate din ta fita daga gidan gaba daya, shi ma binta yai gurin neman mutanen da za su kashe macijin, ba su wahalar samun zaratan maza ba domin unguwar akwai manyan samari duk da kasancewarta sabuwar unguwa, har cikin gidan suka shiga Zainab ta tsaya daga waje tana fada musu inda dakin Iya yake, daga bakin kofa suka tsaya suna dubawa ba su koma ba hakan yasa suka fara yamutsa dakin ko za su ga inda macijin ya boya, tun suna yi da dan tsoro tsor har su kao ma dakin daidai ba su ga komai ba, hakan yasa suka fara tunanin ko ya fito falo ne duk da kasancewar falon babu wani guri da zai iya buya, amman a haka suka rika duba ko'ina har kasan kujerun, har cikin kicin ba su ga komai ba. Daya daga cikinsu ya zo yana tambayar Zainab.
鈥淎mman ke kin ga macijin da idonki? Ko kuma tsoro dai kika ji?鈥�
鈥淣a ganshi Wallahi da idona鈥�
鈥淎bun mamaki ni ban ma ta inda zai iya shigowa ba, ko ban dakin ban ga wata hanya da zai iya biyowa ba鈥�
鈥淲ani lokacin a sabon gida ana samun irin haka gaskiya, domin iskokai suna haka, ko a gidansu Najeeb an yi musu haka kamin su samu zama lafiya鈥�
Dayan ya fada, maganar da yai sai ya saka Zainab ta tuna cewar tukunyar da ta fashe ta tsafi ce wata kila macijin aljani ba macijin gaske ba.
鈥淪ai dai idan iskan ne kamar yadda ka fada, amman dai ni na san na ga maciji gaskiya鈥�
鈥淭o sai dai ayi ta addu'a Allah ya tsare gaba鈥�
Amin din ma ta ji ba zata iya amsawa ba balle tace musuta gode, haka ta bi su da ido har suka fice sannan ta dawo kusa da dakin mai gadi ta zauna tana ta tunanin yadda zata koma cikin gidan.
********
Kusan kofar gate din gida biyu dake gefen na Baba Waziri dama da hagu fake suke manyan motoci na alfarma saboda rasuwar Maijidda, domin mutuwa mai ban tsaro duk wanda ya ji Maijidda ta rasu sai yayi mamaki domin ba a san ta yi ciwo ba sai idan na kusa da ita ya fada cewar ta kwana a asibiti da zazzabin taifot, hakan yasa har wandanda ba su san ta ba jin cewar budurwa ce suke zuwa gaisuwa, daman kuma Baba Waziri mutumen mutane ne, ta ko'ina zuwa ake masa gaisuwa ga familyn Hajiya Talatu da Hajiya Maryam su ma sai zuwa suke kamar an turosu, yan uwa abokai da suruku kai ma sai zuwa suke.
聽 Sai dai abun da kewa kowa tausayi shi ne Hajiya Talatu da ke ta shikar dariya ta fita hankali, sai kuma ta hada ta waka, duk wani abun da ta gani sai ta fade shi tace na jiya, hakan yasa aka sake maida ita a dakin aka rufe har sai da aka dawo daga kai Maijidda a gidanta na gaskiya, sannan Baba Waziri ya bada izinin a janyo mota a sakata a ciki a kaita asibiti.
Ana fitowa da ita duk abun da ta gani sai ta ce.
鈥淜ai wando na njiya? Ke riga ta jiya? Takalmi na jiya? Hijabi na jiya? Kai mota ta jiya, fulawa ta jiya... Fadime ta jiya, Falmata ma ta jiya, Sardauna ma na jiya, Jarma ma na jiya, Shattima ma na jiya, ga Ammy ta jiya, ga Nana ma ta jiya, kai Jurry ma ta jiya, Mai Martaba na jiya, Hajiya Babba ta jiya...鈥�
Komai ta gani sai ta fada ta ce na jiya, idan kuma bata fadi wani abun ba to zata kama sunanyen mutanen da suke ranta tana fada sai kuma ta bushe da dariya, sai dai babu wanda ya kawo komai a ransa kowa yana tunanin mutuwar Maijidda ne ya taba ta, haka aka sakata a mota aka nufi asibiti da ita yaranta sai kuke suke, ga mutuwar yar'uwa ga rashin lafiyar uwa.
Ana kiraye kirayen sallah la'asar mai napep ya sauke Iya gida na biyu kamin gidan Waziri, sai da ta fito sannan ta ba shi kudinshi tana jin jikinta na wani tsam tsam tsam kamar ba lafiya ba, habar zanenta ta kamo ta kai a idonta tana murzawa saboda ta samu idon yai ja ace ita ma ta yi kuka, domin abu ne mawuyaci ka ga maye na kuka, is hardly, suna da karfi halin bala'i da bushewar zuciya, sai da ta murza idon har ta ji ya dan soma mata ciwo sannan ta nufi gidan tana ta mitsika idon kamar munafuka.
聽 Haka ta ratsa cikin manyan motocin ta shiga cikin gidan, kai tsaye ta nufi bangaren Hajiya Talatu, tun a bakin gate din ta fara hango mutane a harabar wasu akan kujeru wasu akan tabarma wasu akan carpet, cikin karfin hali ta nufi gurin tana isa ta fara musu sallama tana kukan karya.
鈥淛ama'a to sannu mu da wannan rashi鈥�
Mutanen da ke kusa da ita suka masa mata duk da kasancewar ba kowa ya san ta ba a gurin, wadanda ta sani suka santa suna daga can ciki, sai da tai musu gaisuwa sannan ta mike tsaye tana kuka ta fara tsallaka mutane har ta isa bakin kofar falon ta shiga ciki tana fashewa da wani sabon kukan, can ta dago kai ta karewa mutanen da suke cikin falon kallo ka zata ga yaran Hajiya Talatu tai musu gaisuwa ko kuma wanda ta sani sai tai arba da abun da ba tai zato ba balle tsammani, tsaye tai cak lokaci daya ta daina kukan tana kallon ikon Allah. Maijidda take gani tsaye a kofar dakinta tana kallonta fuska babu annuri.
鈥淎hhh ahh ahh Jama'a ba Maijidda ce ta rasu ba?鈥�
Iya ta tambaya da karfi tana kallon Maijidda da ita kadai take ganinta. Duk mutanen da ke kallon kallonta suke har Ammy dake zaune a one seater rike da carbi da kuma abokiyar zaman Hajiya Talatu wato Hajiya Maryam dake kusa da kujerar Ammy.
鈥淛ama'a ba ku amsa ni ba, ba Maijidda ce ta rasu ba?鈥�
Ta sake tambaya da karfi.
鈥淚ta ce mana鈥�
鈥淭o ya nake ganinta gata nan a tsaye tana kallona鈥�
Iya ta fada tana nuna kofar dakin Maijidda, kusan duk wanda ke cikin falon sai da ya juya yana kallon kofar dakinta dake rufe babu wanda ke ganinta sai Iya, sai mutanen da ke kusa da ita suka fara matsawa suna mata kallon tsoro.
鈥淢aijidda...鈥�
Iya ta kira sunanta bata amsa ba, kuma bata motsa ba sai wani mugun kallo iya take ganin Maijidda na mata.
鈥淜e kika cinyenta kenan shiyasa kike ganinta, ku nemo maza su fitar mana da matar nan a tsareta can waje鈥�
Ammy ta fada daga inda take zaune, da saurin mutanen da ke gabanta suka tashi domin aiwatar da abun da ta fada, Iya kam bata ma san wainar da Ammy take toyawa ba domin hankalinta na gurin zanenta da ta ji ana ja, tana duba kasa sai ta ga Luna Luma da Labib.
鈥淟uma Luna Labib?鈥�
Ta fada tana dukan kirjinta, sai zaro ido take jikinta nata rawa, kamar jira ake ta dago nan ma sai ta soma ganin yayan Ammy da ta cinye da kuma Jakadiya da wata Jekadiya da duk matan da ta ci na Shattima sai da ta fadi sunansa domin ganinsu take ido da ido suna mata mugun kallo.
鈥淢iyasa na ke ta ganin mutanen da na cinye? Miyasa zan yi ta ganinsu bayam na riga na cinye kurwarsu? Ya haka wai haka? Lafiya dai? Me ke faruwa ne?鈥�
A gabar da tai maganar ne mazan da Ammy tace a kira suka shigo sai Ammy ta daga musu hannu alamar su dakata, matan dake jikin kofar kam tuni wasu sun yi waje wasu kuma sun masa can nesa da inda take.
鈥淢iyasa na ke ta ganin mutanen da na ci? Mai Martaba? To ai shi ban ci shi ba, na kurwarsa na nan aje ban cinye ba鈥�
Ta fada tana kallon Mai Martaba dake tsaye gabanta.
鈥淛ama'a ku min rai, ya haka wai?鈥�
Tana kiran jama'a sai kowa ya kara nisantarta, Ammy kuma ta mike tsaye da sauri tana nuna ta.
鈥淢ai Martaba fa kika ambata Iya? Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un ku kira min Wazari鈥�
Duk wani abun da Ammy take fada da hayaniyar mutane bata jin ko daya gaba daya idonta baya nuna mata komai sai nutanen da ta ambata su kawai take gani. Wani irin zafi ta soma ji a jikinta kamar ana yanka mata reza a fata, can kuma ta soma jin kankarar maitar dake cikin cikinta ta soma motsawa tana mata yawo. Da farko bata ganin kowa yankan kawai take ji ta ko'ina har sai da tai magana.
鈥淵ankana ake fa! A jikina ina jin yakan wuka鈥�
Kamar jira ake tai magana sai ta soma ganin mutane da ta cinye suna yankanta ta ko'ina kamar an aikosu. Mutanen da ke falon kam kowa ya hade waje daya yana kallon yadda take tisge tufafin jikinta tartsatsin wuta na fita a jikinta kamar ana 茩ira. 茦ofar Kitchen aka bude mutanen dake cikin falo suka samu fita ta gurin domin Iya na tsaye kusa da kofar falo ne.
SIRLEEM POV.
Cikin gidan ya koma a tunaninsa Hajiya Babba tana ciki kamar yadda ya fita ya barta sai ya samu bangaren Babu kowa sai Hadimai, wayarsa ya ciro ya kira Kausar sai ta dauka tana tana ta kuka ta sanar masa cewar suna asibiti, jikin na rawa ya koma motarsa ya dauki hanyar asibitin, kamin ya isa har ya matsu domin gani yake kamar yana sa za a sanar masa cewar ya rasa Hajiya Babba. A lokacin da ya isa ana cikin gwaje gwajen jininta ne yana gurin aka mata allura ta samu bachi, sai a lokacin ne suka samu labarin rasuwar Maijidda sai ba su da kuzarin zuwa dukansu domin hankalinsu yana gurin mahaifiyarsu. Karima ce ta kira sauran yan'uwa tana sanar musu abun da yake faruwa ita da Kausar, Sirleem dai yana zaune daga waje sai tunanin Falmata yake yana ta motsa hannunsa da ta rike shi da shi a hankali, sai a yanzu ya tabbatar yana sonta, sai dai idan har Hajiya ta zabi ya rabu da ita dole ne ya aikata ko dan samun farincikin mahaifiyarsa
Yana a gurin har la'asar a masallacin dake asibitin yai sallah zahar da la'asar abinci da aka kawo ma kasa ci yai gaba daya ba shi da natsuwa kuma hankalinsa ba zai kwanta ba har sai ya ga Hajiya ta dawo normal.聽
Jurry kam tun 2pm ta bar asibitin sakamakon wani azababben ciwon kai da ya saka ta gaba kamar kan zai cire har wani abu take ji a ciki kamar gero. A hankali Sirleem ya tura kofar dakin ya shiga sai ya samu Kausar a zaune ta kurawa mahaifiyarta ido, kana ganinta ka san ta yi kuka har ta gaji.
鈥淪is鈥�
Ta juyo ta kalleshi, sai ta ji tsanarsa cikin ranta saboda tana ganin shine silar ciwon Hajiya Babba. Dauke kai tai ba tare da ta amsa ba ta cigaba da kallon Hajiya Babba.
鈥淎n fadawa Ammy kuwa? 鈥�
鈥淎a ban kira ba ina ganin suna gurin gaisuwa, kuma ko na kirata ai dadi kawai zata ji鈥�
鈥淲ani irin dadi kuma Kausar?鈥�
鈥淭o son Hajiya take yi balle鈥�
鈥淜i daina wannan maganar, abun da ke tsakanin Hajiya da Ammy dabam babu ruwanki a ciki鈥�
Har zata sake magana sai dai ganin Hajiya ta motsa yasa duk suka maida hankali gurinta suna kallonta, ta dade tana motsin sannan ta bude ido tana kallonsu.
鈥淪annu Hajiya鈥�
Kausar ta fada, sai ta daga mata kai ta amsa daker
鈥淵auwa su waye ku?鈥�
Daga Sirleem har kasar kallon juna su kai da mamaki, ga bakinta yana nan kamar da be dawo daidai ba, sai dai wanna karon ta samu damar magana yunkurawa tai ta tashi tana karewa dakin kallo.
鈥淗ajiya ni fa Kausar鈥�
鈥淜ausar kuma? Wace Kausar din? Ko. Ke ce mu ka je tare da ke gurin bokan nan?鈥�
Ba shiri Kausar ta bude baki idonta na cika da kwalla.
鈥淗ajiya ta yi losing memory ta Ya ya鈥�
Kamin Sirleem da ke tsaye yace komai Hajiya ta girgiza kai.
鈥淎a ke ce dai ban san waye ke ba, Shi ai Sirleem ne dana ko?鈥�
Sirleem ya daga mata kai cike da nauyin bakin da ya kasa barinsa ya amsa. Sai ta kama rigarta tana wasa da ita kamar wata yar yarinyar tana turo bakinta dake gefe gaba.
鈥淚na Falmata? Daman ance yarinyar nan zata lalata mana komai, da Falmata da Fadime, da Sardauna, kuma sun lalata, babu abun da ban saka ayi ma Falmata ma amman bokan nan sai cewa yake wai na yi latti, daga nan muka tashi muka tafi Katsina ni da Hajiya Talatu da Jarma da Juwairiyya, saboda kawai abubuwa su daidaita amman komai be mana kyau ba, har sata an laka mata amman sai da ta lalata mana shiri鈥�
鈥淜ausar je ki kira likita鈥�
Sirleem ya fada zuciyarsa na bugawa da mugun karfi, da gudu Kausar ta tashi ta fice daga dakin tana kuka, Sirleem ya zauna kusa da Hajiya Babba yana kallonta cikin tsananin damuwa, sai ta kalleshi tana kokarin fashewa da kuka irin yadda shagwababbin yara suke yi.
鈥淜a ga sun fada mana akwai tafiyar da ba dawowa ashe Talba ne zai mutu鈥�
Sai kuma tai shiru kamin likita ya shigo ta sa ke cewa.
鈥淜uma na sake sa an yi ma yarinyar Fadime aiki fa, na kira aljani aka mata magani ta bata, da muka je can garin Garuk ma na fadawa wacan bokan ya nisanta ka da Falmata ya saka maka son Nana, kuma Nana ta lalace, a kashe min Shattima da Mai Martaba saboda na samu Talba ya hau sarauta amman duk na yi a banza...鈥�
Sirleem ya mike tsaye da sauri yana jin kunnuwansa kamar ba za su iya daukar abun da Hajiya take fada ba, da gaske ta aikata ko kuwa dai fitar hankaline ya saka ta haka? Runtse ido yai yana jin duniyar na juya masa, likitan na shigowa sai yai saurin daga kansa sama domin hana hawayen da suka cika idonsa zuba.
_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number聽 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
03/12/2021, 18:59 - 馃馃馃馃: Ina mata wadan da suke son sayen kaya kamar su laces, atamfa, materials,shadda lace, normal shadda, atamfa lace, veil's, shoes and bags, da sauransu kuzo ga MAMAN AHMAD tazo dan tashare hawayenku kudai kunemeta ta wannan number聽聽 08032350261聽 banan kadai tatsayaba tanada kayan order kama dana kitchen,tufafi,kuma order ta Bata dadewa ,tana saida kayan gyara kamar su Al'ajabu,shu'umar humra wannan inbakida aure Bama saida maki,hadin kaza me yasin,akwai na mallaka wanda wannan ana rubuta shi atafin hannu ke zakiyi wannan,turaren wuta,kulacca,da sauransu
Mazauninsu nanan a samaru Gusau Zamfara state
Muna aika kaya kowace jaha da wajen kasar nan cikin aminci da yardar Allah kunememu kusha mamaki
https://wa.me/qr/MYY56BH3RMFDG1
*Khadeeja Candy*
*BAN YARDA KOWA YA DORA MIN LITTAFI A YOUTUBE CHANNEL BA TARE DA IZININA BA, YIN HAKAN ZAI IYA JEFA CHANNEL DIN CIKIN MATSALA, DOMIN BA ZAN KYALE BA. DON HAKA AKIYAYE!*
Kuka take sosai daker Momy ta shigo da ita cikin falonta.
鈥淵aushe kuka yi aure?鈥�
Momy ta tambaya cike da mamaki, sai dai Falmata ba ta iya amsawa ba saboda kukan da take, Momy ta zauna kusa da ita ta dafa ta.
鈥淜i daina kuka kuka ba zai miki maganin komai ba, da kuka yana magani da ya miki magana tun a lokacin da kike matsala鈥�
Iyakar kokari Falmata ta yi na ganin ta daina kukan amman abun ya garara domin zuciyarta ta ki aminta cewar Sirleem ya bar ta kenan a lokacin da take tsananin bukatarsa.
鈥淚na takardar da ya baki? Ko da baki ya furta miki?鈥�
Falmata ta girgiza kai alamar aa ta nuna ma Momy upstairs, Momy dake tsaye ta nufi upstairs din ta shiga dakin Ameer tana dubawa sai tai arba da takardar a kasa, dukawa tai ta dauka ta bude tana karantawa.
鈥楤an abun da na aikata kuskure ba ne sai a yanzu da mahaifiyata ta shiga damuwa saboda ni, Na san kina tsananin bukatata, kuma na san rabuwar mu zai jefa ni a matsala fiye da ke, sai dai ba zan iya kin bin umarnin Hajiya ba, matukar ta bukaci na sake ki zan aikata hakan ko kuwa hakan na nufin karshen rayuwata ne, idan har ta zabi na sake ki, zan aikata haka zan aiko miki ta takardar sakin ba za sake dawowa gareki ba鈥�
鈥淭a ya akai Sirleem ya auri yarinyar nan? Yaushe? Miyasa ya boye min?鈥�
Momy ta tambaya sannan ta juyo ta fito daga dakin.
鈥淲annan ai ba saki ba ne鈥�
Momy ta fadi hakan a yayinda take saukowa daga stairs din, sai Falmata ta dago da sauri tana kallonta tare da mikewa tsaye.
鈥淭o minene?鈥�
Momy ta karasa kusa da ita ta karanta mata abun da ke rubuce a cikin takardar, sai Falmata ta shaye hawayenta tana jin sanyi a ranta. Momy kam kallonta kawai take irin kallon na na babba da yaro, ko ba a fada ba ta san Sirleem ya kai a so shi amman Falmata ta haukaci tana kuka ya bata mamaki domin a tunanin Momy Falmata bata san wani abu so ba.
鈥淶auna鈥�
Momy ta fada sai Falmata ta zauna ta sunkuyar da kai kasa. Momy ma ta zauna tana kallonta.
鈥淵aushe akai auren? Ya akai ya aurenki?鈥�
鈥淣i ma ban san shi ne mijina ba har sai daren da aka daura auren... 鈥�
Sai ta labartawa Momy abubuwan da ta sani har zuwa yau. Ba karamin mamaki Momy tai ba, so that's mean tun a lokacin da tai masa maganar Ameer kenan yana da wannan plan din ko kuwa daga baya ne? Shiyasa ya ki yarda da Ameer ya aureta? Momy ta sake kallon Falmata tana murmushi.
鈥淜o da ace Sirleem ya sake ki, na tabbata zai dawo gareki, kin san saboda me?鈥�
Falmata ta girgiza kai alamar aa.
鈥淪aboda yana sonki kuma so ba na wasa ba, duk namijin da zai yarda ya auri mace ba tare da sanin kowa na shi ba kuma auren fari ba dan komai ba sai dan ya taimake ta, to hakika wannan namijin ba karamin sonta yake ba, ko da makoci kike da shi ya damu da ke, za ki jidadi balle wanda ya zabi dauke ke kacokan daga wacan duniyar marar dadi a saka ki a wata rayuwar mai cike da daula da farinciki, kamin ke Sileem yana soyayyah da wata Mansura, amman be duba halin da zata shiga ba, shi ma be damu da duk irin abun da Hajiya da mu yan'uwan mahaifinsa za mu masa ba, ya runtse ido baya ganin kowa sai ke da damuwarki, duk da kasancewar ba ki yi boko ba, kuma ke ba yar wani mai arziki ba ce, Sirleem yana sonki sosai Falmata鈥�
Falmata ta dago ta kalli Momy sai Momy ta kama hannunta ta rike.
鈥淣a jidadin da ba ki auri Ameer ba, da yanzu dan'uwanki kika aura kenan? Kuma na jidadin da zuciya bata saka ni na aikata kuskure ba, da yanzu ban san da wane idon zan kalleki ba ke da dan'uwanki, Na miki alkawari Falmata Sirleem ba zai taba sakinki ba, ba zan bar shi ya sake jefaki a matsala ba, domin ba Hajiya kadai take da iko da shi ba, ni ma muna da iko da shi, kuma Allah be ce a bi uwaye a tsaba masa ba, ki kwantar da hankalinki kin ji?鈥�
Falmata ta daga kai wasu hawayen masu kama da na farinciki da alhini na sauko mata. Momy ta tashi ta shiga kicin ta sake hada mata wani tea tana da godiya ga Allah da be saka ta aikata dashen da kawarta Umaima ta zugata tai ba, kenan da ta yi mata dashe da kwan mijin mahaifiyarta kuma mahaifin yayanta. Falmata ta saka hannu biyu ta karbi kofin tea, tana sha a hankali kalaman da Momy tai mata suna ta mata yawo a kwakwalwa, upstairs Momy ta nufa after like 30 min ta sauko rike da jakarta da makullin motarta.
鈥淶an tafi gurin aiki鈥�
鈥淎llah ya tsare Momy ya dawo da ke Lafiya鈥�
鈥淎meen鈥�
Momy ta amsa tana kallonsa sannan ta nufi kofar fita ta fice. Sai da ta ji tashin motar Momy sannan ta aje kofin tea da ta gagara shanyewa ta kwanta kan 3 seater din tana sauke numfashi a hankali, idonta sai ciwo suke. Tana kwance a gurin har aka sallah azahar, sannan ta tashi ta shiga dakin Ameer tai sallah, ta hau gadon ta kwanta tana ta kallon hoton mahaifiyarta, sai kusan uku da yan kintuna Momy ta dawo, sanin ta bar Falmata a gida yasa ta biya tai musu takeaway, da key dinta ta bude kofar falon ta shigo, sai da ta da ta shiga dakinta ta aje jakarta da kayan hannunta sannan ta dauko leda daya ta nufo dakin Ameer inda Falmata take, ta tura kofar dakin a hankali domin a tunanin ko Falmata tana bachi ne sai ta ganta farke tana kwance saman gadon idonta na kan hoton mahaifiyarta hawaye sai sauko mata. Momy ta karasa kusa da ita ta aje mata ledar.
鈥淭ashi ki ci abinci na san ba ki ci komai ba ni ma kuma na dawo a gajiye shiyasa na yi mana takeaway be zama lallai na iya dafawa ba鈥�
Falmata ta yi saurin boye fuskarta tana amsawa Momy.
鈥淭o na gode鈥�
Momy ba ta ce mata komai ta nufi gurin da hoton yake ta juya shi, sannan ta fice dakin. Sai da ta fita sannan Falmata ta tashi ta share hawayenta ta sauko kasa ta bude abincin ta fara ci, turashi kawai take ba dan tana jin dadinsa ba, kamar yadda bata jin yunwa haka ma bata jin koshi, damuwar dake ranta ta saka ta ji bata bukatar komai, domin har a yanzu tana sauraren aiken Sirleem na takardar saki kamar yadda ya fada, a iya ganinta mawuyacin abu ne Hajiya ta barshi da aurenta.
Tana cikin dakin akai la'asar, ta shiga bandakin ta sake yin alwala ta fito ta gabatar da sallah, sannan ta daga hannayenta ta roki Allah ya zaba mata abun da ya fi zama alheri a rayuwarta, kuma ya saka komai ya zo mata da sauki kana ya sassauta mata abun da take ji a zuciyarta da kuma wanda take hangowa. Kamar wanda aka kulle haka ta sake zama cikin dakin har aka kira sallah magariba, sannan ta sake shiga bandakin tai alwala, kamin ta fito ta ji lokacin da aka turo kofar dakin aka shigo, sai dai a zatonta Momy ce ta shigo yin wani abu ko fada mata wani abu, hakan yasa tai hanzarin fitowa sai tai arba da Sirleem zaune gafen gadon yana kallon kofar bandakin, tsaye tai cak tana kallon fuskarsa da rama ta samu muhalli a gurin, zuciyarta na bugawa da mugun karfi. Sai ya mike tsaye ya miko mata hannunsa, kallon hannun tai sannan tai je gareshi da sauri ta saka masa nata hannun, sai ya rike gam ya jata zuwa jikinsa yai mata masauki da kirjinsa, kamkamshi tai hawaye na sauko mata, shi kuma ya daga kansa sama yana jin yadda hawaye suke bankwana da idonsa, ashe wani abun ya fi gaban kuka, duk wani abun da za ayi ma hawaye ko kuka mai sauki ne, domin a yanzu shi kasan be san inda hawayensa suke ba.
鈥楴a gode Allah da na aureki, na gode Allah da ban auri Nana ba, na gode Allah da ban sake ki ba, na gode Allah da gaskiya ta bayyana鈥�
Ya fada a ransa yana tunanin abubuwan da mahaifiyarsa ta fada, taya zai iya labartawa wani cewar mahaifiyarsa ta so kashe mijin da take aure saboda abun duniya? Ta ya zai bar wani ya san kanwarsa ta jini da ita aka hada baki a kashe mahaifinta? Lallai Allah yayi gaskiya domin ya fada a cikin yayanku da matanyenku akwai makiyanku! I can't believe da sa hannun Hajiya a lalacewar Nana, me Shattima ya tare mata har take son a kashe shi? Why all this? Ashe daman akwai manufa a aurensa da Nana? A yanzu auren Falmata ya bayyanar da komai, duk kuwa da kasancewar ba dan auren ne kawai ya saka ta shiga hali ba, ya tabbatar har da alhaki na cutar da innocent people.
IYA POV.
Duk wanda ke gurin tsoron taba ta yayi, saboda tartsatsin wutar da jikin ke fitarwa, ga shi ta saka hannu sai tisgar naman jikinta take saboda zafin yankan da take jin mutanen da ta cinye ma kurwa suna mata ta ko'ina, tun tana yi abun na hankali har ta fara ihu tana fadin ayi mata rai.
鈥淒an Allah kui min rai! Jama'a wai ba ku ganin abun da nake gani? Ba ku ganin yadda suke yankana?鈥�
Babu wanda yace mata uffan sai kallonta ake, ganin wasu sun fara fito da wayarsu suna daukarta yasa Baba Waziri ya rufe kofafin, ba dan komai ba sai dan mutuncin Mai Martaba.
鈥淲annan bala'in yayi min yawa, wadannan kaya ina za ninda su?鈥�
Ta fada tana faduwa kasa sai tisgar naman jikinta take tana ihu, sai ta fara mulmula tana jin nauyin dazun yana dawo mata.
鈥淜u fita waje ku sama manyan sanduna鈥�
Baba Waziri ya fadawa mazan da suke dakin sai uku daga cikinsu suka fita da sauri abun nema ya samu, ba su dade ba suka dawo, Baba Waziri ya ba su izini suka fara labtawa Iya iya karfinsu, wani irin uhu tai sai zabar ta zame mata hudu ga na mutanen da take gani ga yankan da suke mata ga kankarar maitar dake ta mata yawo a ciki tana sakar mata nauyi, ga kuma dukan da take ji ta ko'ina da bata san ta ina yake zo mata ba, dukanta suke duka bana wasa ba.
鈥淜ar a asheta Waziri kar a kasheta鈥�
Ammy ta fada tana hawaye.
鈥淏a kasheta za ayi ba, ubanta za a ci ta yadda idan akai mata magana za ta ji鈥�
Shine amsar da Baba Waziri ya bawa Ammy, su kam matasan suka saka Iya gaba da duka har sai da suka fitar mata da jini a jiki. Wani abun mamaki ana dukanta tartsatsin wuta na tashi a jikinta, sai da suka kusan kasheta har ta kai bata iya motsi sannan Baba Waziri yace su dakata. Ya motsa kusa da ita ya kira sunanta sai ta kasa amsawa.
鈥淢e zaki yi da kurwar Mai Martaba da kika kama?鈥�
Muryar kawai take ji amman iyakar ganinta bata ganin komai da kowa sai mutanen da ta ci ciki har da mahaifiyarta. Baba Waziri ya sake maimaitawa amman ta gagara amsawa, har sai da ya maimaita sauko kusan hudu.
鈥淪aboda... Na aurawa Shattima Zainab, sai na kashe sarkin sai Shattima ya gaji sarautar su haifa min jika鈥�
Ammy ta dora hannu saman kai tana kalmar shahada, kowa na gurin sai da ya cika da tsananin mamaki, Baba Waziri ya girgiza kai.
鈥淎zzaluma, ke da baki da gadonmu amman kin san ki yi kwadayin sarautar ku? Bayan duk hallacin da akai miki鈥�
Ta motsa daker tana fadin.
鈥淪una ta yankana鈥�
鈥淪u waye?鈥�
鈥淲adanda na cinyewa kurwa, ga su sun tsare ni suna ta yankana鈥�
Ta shiga zana sunayensu a wahalce.
鈥淎llah yasa su kashe ki, Azzaluma macuciya, macijiyar soshiya鈥�
Baba Waziri ya fada cikin bakinciki da bacin rai.
鈥淎 ina kika rufe kurwar Mai Martaba?鈥�
鈥淭ana gida鈥�
Ta fada kamar wanda ta kusa mutuwa muryar tai mata nisa.
鈥淭ashi muje ki kwance ta鈥�
鈥淏a kafa, kankarar maita ta min nauyi a ciki鈥�
Ta fada daker tana numfashi a wahale. Sai Baba Waziri yasa mutanen da suka mata duka su jata a kasa, bayan ya bada umarnin a shigo da mota har gurin kofar falon Hajiya Talatu.
Baba Waziri ya saka a ka dauko bargo kato aka rufa mata saboda feshin wutar da take, janta suka fara yi amman suka kasa janta sakamakon wani uban nauyi da tai kamar dutse, sai da suka hada karfinsu suka hadu su biyar sannan suka iya daukarta suka fito da ita waje shi ma daker, a cikin wata hilos aka saka ta Baba Waziri da wasu muhimman mutane suka shiga wata motar, Ammy ta shiga motar ta ita da driver ta sai da suna daf da fita sannan Baba Waziri ya kira Shattima ya labarta masa halin da ake ciki domin tun da akai jana'izarta akai gaisuwa 2pm tai sai ya bar gurin ya koma gidansa. Ko kamin su isa gidan Zainab da ke million quarters Shattima ya riga su har ya faka motarsa cikin gidan, sai dai be fito ba ya jira har suka karaso, Mai Gadin dai sai kallon ikon Allah yake ganin an zo da motoci ga Iya a bargo kamar wata mage.
鈥淪hegiya kafira sai nauyi kamar namam wuta鈥�
Daya daga cikin ssmarin ya fada a yayinda da suke ta kokarin ganin sun fito da ita daga bayan motar dake bude. Daker da sudin goshi suka dauko da ita daga motar suka nufi kofar falon dake bude da ita, domin tun da mazan nan suka fita Zainab bata taba kofar ba ta nufi makota ta zauna a can har sai Iya ta dawo.
鈥淲ani guri?鈥�
鈥淒akina鈥�
Ta fada daker domin idon nata ya rufe bata ganin komai sai duhu, sai da aka kira Mai gadin sannan ya nuna dakinta ba dan yana da tabbaci ba, ana shiga dakin su ka tararda da shi a yamutse, sai da suka ja baya sannan suka jan bargon suka budeta har lokacin bata daina tartsatsin wutar ba, kallo kawai take ba dan tana ganin komai ba.
鈥淜u daga gadon ku dauko min kwarya鈥�
鈥淕adon dake bude ko baki gani ne鈥�
Dayan ya fada.
鈥淭o ku ba ni kwarya鈥�
Da kafa dayan ya tura mata kwayar dake can gafe aje, sai ta taba ta fara lalabe har ta kama kurwar ta shiga kwancewa, ganin kawai suke hannunta na kwance amman ba su ganin zaren da kuma abun da take kwancewar gani suke hannunta na ta yawo, sai da ta gama ta daga hannun sama kadan saboda ciwon da suke mata ta jefa kurwa a nan kam sun ga zakara yayi sama sai ya bace. Ba dan suna maza ba da babu wanda zai tsaya a cikinsu, ita dai Ammy daman tana tsaye daga bakin kofa ne sai addu'a take, Shattima kuma yana tsaye kusa da Baba Waziri.
鈥淩anka ya dade a kar ta?鈥�
Dayan ya tambaya? Sai wani ya kama mishi.
鈥淟allai kam irin wannan bata da rana bata da amfani鈥�
Sai Baba Waziri ya daga musu hannu.
鈥淎a ba za mu kasheta ba, ta je can ta ji da alhakin mutanen da ta kashe鈥�
鈥淏ayan Mai Martaba sai kurwar waye a hannunki?鈥�
Shattima ya tambaya yana mata wani irin kallo na kyama da tsana, sai ta girgiza kai alamar babu kowa domin ta kai gabar da magana ma ba zata iya ba.
鈥淚na Zainab take?鈥�
Shattima ya tambaya sai mai gadin yai hanzarin amsawa.
鈥淭a tafi makota saboda macijin da ta gani, bari na kirata鈥�
Ya fita da sauri, cikin kankanen lokaci suka dawo tare da ita. Kasa cewa komai tai ganin halin da Iya take ciki ga kuma Shattima Baba Waziri da Ammy tsaye da kuma yan uwan Mai Martaba.
鈥淜e ma kina maitar ne?鈥�
Baba Waziri ya tambaya sai ta kalleshi ta kasa cewa komai hawaye suka sauko mata sharrrr kamar an bude fanfo. Shattima ya kalleta irin duban nan na kaskanci, sai Baba Waziri ya ce
鈥淣a baki daga yau zuwa gobe, ki dauki Iya ku bar garin Yola, idan ba haka ba duk abun da ya biyo baya ke kika ja, kuma idan muka sake ganin wani abu da ba mu yarda da shi ba, zamu nemo ku duk inda kuka shiga鈥�
Lokaci daya Zainab ta runtse ido tana jin kamar mutuwa ta dauke ta huta da duniyar gaba daya.
鈥淏oyewar da tai kuskure ne, sai dai be zama lallai ace tana maita ba, Baba ayi mata uzuri a kara mata sati so that ta siyar da komai na ta da yake garin nan ta bar garin鈥�
Shattima ya fada yana kallonta.
鈥淪hattima ina son ka sani, farin tuwon nan cikin bakar tukunyar nan ya fito鈥�
Baba Waziri fada sannn ya fice a fusace, haka ma saura suka fice aka bar Shattima a dakin da Ammy dake tsaye jikin kofa.
鈥淜in ban mamaki Zainab鈥�
Juyowa Zainab tai ta kalli Ammy.
鈥淜ina da damar ki zargeni da komai Ammy, ba ni da kalmomin da zan hada na furta na wanke kaina, na san komai ne a kurarren lokaci....鈥�
Ta yi saurin saka hannunta ta rufe bakinta saboda kukan da ya ci karfinta ta durkushe a kasa ta fashe da wani irin kuka.
Shattima dauke kai yai ya fice daga dakin Ammy ta rufa masa baya tana hawaye.
FADIME POV.
Sai da ta ci abinci ta koshi sannan ta tuna da sallah.
鈥淢alam ina zan shiga nai sallah鈥�
鈥淢uhseen鈥�
Ya fada mata.
鈥淢uhseen ina zan yi sallah dan Allah?鈥�
鈥淏iyo ni mu je鈥�
Ta mike tsaye ta fara binsa, sai kuma ta dawo ta hada plates din da ta ci abinci ta dauka ta bi bayansa da su. Wani dakin ya bude mota.
鈥淪higa akwai komai a ciki鈥�
Sai ta mika masa plate din.
鈥淭o ka aje wannan a muhallinsu ni ban san kicin din ba, kuma ita wannan Mama Fulani za ta iya fitowa ta min masifa ko? Ka ce tana da masifa ai鈥�
Ido kawai ya sakar mata yana mamakin yaushe yace mata Mama Fulani zata mata masifa saboda ta bar plate, bata bi ta kansa ba ta duka ta aje masa plates din ta shigewarta dakin.
鈥淣i da mijina Malam sai kallona yake yi鈥�
Ta fada da muryar da ita kadai zata iya ji, sannan ta tura kofar dakin ta rufe. Dukawa yai ya dauki plates din yana murmushi ya sauka kasa ya kai su kicin sannan ya sake hawowa sama ya shiga dakin Mama Fulani ko da ya shiga ya same tana ta masifa a waya, zaunawa yai a kam kujerar dake dakin yana taba wayarsa har ta gama sannan ya kalleta.
鈥淢ama kin dauki abun nan da gaske what if yarinyar nan karya take miki? Ko ma gaskiya ne idan baku da wata cikakkiyar hujja ba za su iya yin komai ba鈥�
鈥淎she ma ita Ammy ta san maganar, idan sun an shanye su mi masifa ta ba zata bar ni a shanye ni ba, Wallahi ba zan bar maganar nan ba ai har na siya tickets din tafiya gobe da yardar Allah, shi ma Waziri ina fada masa ya sa Iya ta tsallaka Maijidda wai abar wa Allah komai Maijidda ta riga ta rasu ka ji min shashanci鈥�
鈥淢ama dan Allah karki ce za ki shiga masarautar nan da masifa, mutuwa akai fa kuma shi kansa Sarkin ba lafiya ce ta ishe shi ba鈥�
鈥淜arka kawo min wannan maganar babu wanda zan saurarawa rashin lafiyarsa ba su ne suka saka shi gaba ba鈥�
鈥淏ari dan ki ya zo yai miki magana ko za ki ji鈥�
鈥淏a ruwanka Muhseen karka hada ni da Aliyu鈥�
Mama Fulani ta da da tana daga masa hannu, domin Aliyu ne kadai sai Abbah mutanen da suke saka ta ta yi abu ko kuma ta hanu idan sun hana ta, Aliyu saboda kaunarsa da take yana wahala ya hana ta abu ba bar shi ko ya roki abu ta ki yi masa, Abbah kuma saboda ya zama cikakken namiji ne da baya daukar raini.
Tashi yai yana dariya ya fito daga falon kamin ya karasa saukowa door bell din tai kara alamar akwai mutum abakin kofar falon, karasa yai ya bude kofar falon, sai yai arba da Aliyu Ataa na tsaye bayansa rike da babynta.
鈥淒an halak kaki ambato鈥�
鈥淜enan gulma kake鈥�
Aliyu ya fada fuska ba yabo ba fallasa kamar ba shi yai maganar ba. Muhseen yayi murmushi ya sakar musu kofar suka shigo. Kai tsaye Ataa ta nufi upstairs zuwa dakin Mama Fulani, Aliyu kuma ya zauna a falon shi da Muhseen, a kan gadon Mama Fulani Ataa ta sauke babynta ta gaishe da Mama Fulani sannan ta sanar mata tare take da Aliyu, Mama Fulani ta taso cike da far'a suka sauko tare da Ataa, sai da suka zauna sannan Aliyu ya gaishe da Mama Fulani, sannan ya kalli Muhseen ya ce.
鈥淚na Yasmin din?鈥�
鈥淵asmin ko Fateema ko talkative鈥�
Muhseen ya tambaya yana dariya, sai Aliyu ya masa wani kallo na rashin fahimta, kuma ba zai iya tambaya cewar be gane ba ko kuma miyasa ya ce haka ba, Muhseen ya mike tsaye yana murmushi.
鈥淣i zan tafi gida, gobe karfi nawa zaki tafi?鈥�
鈥淭ara鈥�
Mama Fulani ta amsa masa.
鈥淥kay鈥�
Ya nufi kofar fita, sai da ya fice sannan Mama Fulani ta ke dauko masa zancen abun da Fadime ta fada mata.
FADIME POV.
Sai da ta karewa dakin kallo sannan ta nufi kofar bandakin ta taba ta murda ta tura sai kofar ta bude, sai ga ta cikin karamin bandakin.
鈥淥h su kan yan birni sun ji dadi komai mai kyau ne, ji bandaki ne fa nan鈥�
Ta fada tana karewa bandakin kallo, sannan ta fara tabe tabe tana murda fanfon har ta kunno ruwa, sai da ta wanke hannunta sannan ta tara ta sha ba dan tana jin kishin ruwa ba sai dan burgeta da abun yai wai fanfoa bandaki.
鈥淎she haka irin na gidansu Shattima yake ko?鈥�
Ta tambaya kamar wani ne a gabanta, da zai amsa mata, ta wanke fuskarta ya fi a kirga tana kallon kanta a jikin madubi.
鈥淏arakalla Mashallahu鈥�
Ta furtawa kanta sai a lokacin ma ta lura da kalar atamfar da ke jikinta.
鈥淎llah na gode maka yanzu ina gani鈥�
Ta dade a bandakin tana tabe tabe sannan ta yi alwalar ta fito. Kalle kalle ta fara yi ko zata ga hijab da abun sallah, sai ta ji kamar an jefo dutse a window dakin, da farko dan tsoro ta ji sai dai ba sosai ba, kadan kadan ta taka ta isa gurin window ta daga lalulen ta leka bata ga komai ba. Sai manyan motoci da garden.
鈥淜ai ashe gidan sama na da dadi hmm, sai ka hango komai a kasa鈥�
Tana rufe bakin ana saka hannu a rufe mata bakin da karfi ta yadda ihunta ba zai fita ba, kamar wanda ya rufe mata bakin ya san za ta yi ihu sai ta fara kokuwar juyowa tana ihun da sautinsa ya ki fita, juyowa yai ya ita ta fuskance shi. Bude ido tai kamar za su fito wani irin farinciki ya lullubeta da kuma dan tsoro a lokaci daya, a hankali ya dauke hannunsa daga bakinta yana kallonta fuskarsa da murmushi idonsa kuma cike da kwalla.
鈥淵a akai ka zo nan? Waya fada maka ina nan? Yaushe ka shigo?鈥�
Be ce mata komai ba ya kai hannunsa yana shafa fuskarta, sai ta lumshe ido ta saka hannunta biyu ta rike hannunsa, tana jin wani irin farinciki kamar ta rumgume shi.
_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number聽 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
03/12/2021, 18:59 - 馃馃馃馃: *Khadeeja Candy*
Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
Ammy ta dawo gida cike da tunani kala kala, domin babu abun da Hajiya Babba bata labarta mata ba na abun da ta aika, a lokacin ne Ammy ta kara gasgata abun da Fadime ta fada, Shattima kadai ta labarwa abun da ya faru, sai Jekadiya ba ta sanarwa kowa ba saboda bata son ta sanarwa Baba Waziri a yanzu da yake cikin alhinin mutuwar yarsa. Sai dai ta kwana da tunanin abun a ranta tunanin sai ya zame mata kala biyu, ga na Iya ga na Hajiya Babba, sai ta ji tausayin Mai Martaba ya kara kamata da kuma yaranta da ake son ganin bayansu saboda abun duniya da za a mutu a bari. Haka ta kwana bangaren Mai Martaba da tunani kala kala a ranta,sai da ta gama azkar dinta sannan ta dawo bangarenta domin hada masa abun karyawa, ko da ta shigo sai ta samu Shattima zaune a dakinta yana latsa wayarsa, ganinta yasa ya dago yana mika mata gaisuwa. Sai ta amsa da murmushi tana kara jin son danta a ranta, lallai ta yarda idan ba kai cuta ba Allah ba zai bari a cutar da kai ba, idan an samu nasara to kadan ne wanda zata zo da jarabawa.
鈥淭un da sassafe haka ko nan ka kwana?鈥�
鈥淎a yanzu na iso鈥�
鈥淟afiya Kalau鈥�
Ya amsa yana murmushi, sai ta zauna tana kallonsa.
鈥淪hattima ka dage da addu'a, na san kana yi amman ka kara鈥�
鈥淚nshallah, mi ya faru?鈥�
鈥淜omai ai ya faru, lamarin na Iya kadai abun mamaki wanda na san ba dan addu'a ba da a yau ba mu kai haka ba, kuma bayan lamarin Hajiya Babba abun mamaki ne matuka鈥�
鈥淢e ya faru da ita?鈥�
Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta labarta masa abun da ya faru da kuma irin kalaman da Hajiya Babba take ta fada mata a lokacin da ta je ganinta.
鈥淗ajiya Babba ba ta ba ni mamaki ba kamar Jurry, mahaifinta? Kuma ni ma dan'uwanta ne, wace irin zuciya ne wannan?鈥�
Ta fada cikin tsananin mamaki marar misaltuwa. Ammy da idonta ya cika da kwalla ta ce.
鈥淪hiyasa ake son addu'a kana rokon Allah ya baka zuri'a ta gari mai tausayinka da kaunarka kuma wanda zata amfani al'ummar musulmi kuma Annabi yai alfahari da ita鈥�
鈥淎llah sarki Mai Martaba bayan duk dawainiyar da yai da ita tana jin ta kai matsayin da take ganin ya kamata a kawar da shi? Ai ko ba amana bata kama su yanzu ba, ba za su taba samun salama a cikin rayuwarsu ba, ko da ko abun da suke da buri ya kasance鈥�
Cewar Shattima yana jinjina lamarin da yake jinsa kamar ba gaske ba. At the same time ya ji wani irin kaunar Fadime ta kara shiga ransa, domin dukan abubuwan da ta fada sun tabba hakan na nufi ba karya tai ba, kuma ta taimaki rayuwarsu, a lokacin da yan'uwa na jini da kuma irin su Iya suke so ganin bayansu. Samun kansa yai da murmushi duk da irin hali yake ciki na mamaki da alajabin abun da Ammy ta fada masa.
鈥淪miling...?鈥�
Ammy ta tambaya tana kallonsa da dan mamaki, sai yai sauri kallonta domin be san yana murmushin a fili a tunaninsa iya cikin zuciyarsa ne yake.
鈥淎h Amman Mai Martaba ya san da wannan magana?鈥�
鈥淏ana son tada masa da hankali, ya zai ji ace matarka da Yarka suna kokarin ganin bayanka? Ga kuma Iya a gefe?鈥�
鈥淵eah amman dole ne zai sani, and the most important thing is komai ya bayyana a yanzu, and Inshallah zan sake sakawa a yi masa saukar kur'ane duk da an sha yi masa a baya, amman hakan ba zai haka mu kara ba, Ammy kuma ki kara tunatar da shi addu'a ya rike ta sosai鈥�
鈥淪hattima kenan, ni zan baka wannan shaidar da baya addu'a wata kila ta yanzu an manta da labarinsa, kuma duk da hakan zan saka a rubuta masa bismillah guda dubu ya sha, domin ita ma tsari ce sosai daga komai鈥�
鈥淎llah ya kara tsarewa, ni fa daman ina tunanin Sirleem ba son Nana yake ba kamar hadinta ne...鈥�
Shattima na kai Aya Nana na turo kofar dakin ta shigo.
鈥淎mmy ina kwana, Ya Shattima Good morning鈥�
鈥淢orning dear鈥�
Shattima ya amsa mata Ammy kuma ta sakar mata murmushi.
鈥淎mmy har yanzu shiru鈥�
Nana ta fada tana zaunawa kusa da ita, sai Ammy ta kai hannu tana shafa kanta murmushi kwance a fuskarta ko bata fada ba ta san abun da take nufi.
鈥淎lready na yi magana da wanda zai masa komai, so idan ya gama zai neme ni ni kuma zan masa magana, ai ni na ce zan yi ko?鈥�
鈥淭o maganar gidan fa?鈥�
鈥淗ankalinmu ne ba a kwance ba, kwana biyun nan kin sani, bana son na yi ma Mai Martaba magana shi kuma yai ma Waziri da maganar a yanzu, ki bari nan da sati daya idan komai ya daidaita sai mu ga abun da Allah zai yi鈥�
鈥淥kay Ammy wace makarantar kike ce a sama mishi?鈥�
鈥淏an sani ba tukunan, ya fada min dai engineering yake son yi, kuma na fadawa Prof a sama masa makaranta mai kyau mai tsada鈥�
Wata kalar dariyar jindadi Nana tai.
鈥淭hank Youuu Ammy...鈥�
鈥淜i karbi account dinsa a saka masa 1million ya siye tufafin tafiya鈥�
Shattima ya fada, sai Nana ta ware ido da karfi ta dawo kusa da shi ta rumgume shi tana murna.
鈥淭hank Youuu so much Yaya wow....鈥�
Sai kuma ta dawo gurin Ammy.
鈥淎mmy ara phone din pls鈥�
Bata ko tsaya jiran umarni ba ta dauki wayar ta fice da sauri tana murna. Bayan fitar Ammy ma ta kintse ta nufi kicin domin ita da kanta take shiryawa Mai Martaba abun da zai ci. Kamar fitarta Shattima ke jira ya aikawa Ra'ees da kira. Sai da tai ringing tana daf da tsinkewa sannan yai picking da muryar da ke nuna yanzu ya tashi daga bachi.
鈥淩a'ees鈥�
鈥淣a'am barka da asuba鈥�
鈥淕ida na ke son a nemo min within Katsina and Kaita gida mai kyau鈥�
鈥淜ai zaka zauna?鈥�
鈥淣o kyauta zan yi鈥�
Raees yayi hamma sannan ya karasa tashi zaune.
鈥淥kay amman wanda zaka bawa kyauta babba mutum ne ko karami鈥�
Shattima ya san dalilin tambayarsa da yake saboda ya san irin gidan da zai samo masa ne.
鈥淎 samo mai kyau dai karka damu da ko nawa yake, ina sonsa cikin kwana biyun nan pls鈥�
鈥淥kay鈥�
Ya amsa sannan ya kashe wayar, Shattima ya jingina da kujerar da yake zaune yana murmushi tunawa da lokacin da ya taba kade Fadime.
***
Karfe goma da yan mintuna direba da ya dauko Mama Fulani da Shattima da Aliyu da kuma Fadime ya faka harabar masarautar. A nan kallo ya koma sama gurin Fadime, girman masarautar da kyauta har tsoro ya bata ba dan ta san masarauta ba ce ita kan sai tai zaton unguwa ce mai zaman kanta ko wani babban kamfani. Yawan hadiman da suke ta harkokin gabansu ma kadai abun kallo ne, tafe take idonta na kalle kalle duk da kasancewar bata cikin farinciki da walwala saboda Wasim. Ita kadai aka bari baya tuni Aliyu da Muhseen sun wuce gaba sai Mama Fulani da ke binsu, sai da ta shiga bangaren Ammy ta gane bata ga komai a waje ba, domin tsaruwar falon da yadda aka kawata shi ya wuce misali, ko'ina kallo take tana bawa ido hakkinsu, sai a yanzu ta yarda wata sarautar ta fi wata lallai wani dan sarki ya fi gaban wani sarki, kamar wata kurma haka ta shiga cikin dakin Ammy sai kalle kalle take, idonta na sauka akan Ammy sai ta ji wani irin kwarjininta ya cika mata ido, gurin haske da gashin gira iri daya ne da na Shattima, sai dai Shattima ya fi ta kyau nesa ba kusa ba, zaunawa tai a kasa tana ta kallon tsadadden lace din dake jikin Ammy da ke gaisawa da Mama Fulani, jin an taba kofar dakin yasa ta juyo sai tai arba da Shattima da ya shigo sanye da farar shadda mai wani irin haske da daukar ido, bakar hular kansa ta saka fuskarsa har wani annuri take, ga dogon hancinsa ya kara fitowa kamar an ja shi, farar fatarsa ma sai shining take kamar wani balarabe, murmushin da ya yafawa fuskarsa sai ya kara fito da saka siffar zatinsa da kwarjinin da ya cika idon Fadime har ta mike tsaye tana kallonsa, gaba daya ya canja mata kamar ba shi ba, wata kila ba dan tana da tabbacin fuskarsa a wayar da tai da shi ba sai ta rantse da Allah ba shi ba ne.
鈥淶auna...鈥�
Ya fada yana nuna mata gurin zaman a dai dai lokacin da kamshin turarensa ya kai mata hari a hanci. Zaunawa tai ba tare da ta dauke idonta daga gareshi ba shi kuma ya wuce inda take yana yi ma Mama Fulani sannu da zuwa.
鈥淢ama barka da sauka鈥�
Sai da ya gama gaisawa da ita sannan ya kalli Fadime ya sakar mata murmushi.
鈥淭ashi ki zauna akan kujera mana鈥�
Bata motsa ba balle tai alamar tashin sai kallonsa take tana jin zuciyarta na bugawa da mugun karfi.
鈥淲acan akwai rigima tun jiya kuka take ban san abun da akai mata ba, na yi tambayarta har na gaji, yau kuma da ta tashi ba ta yi ma kowa magana ba鈥�
Mama Fulani ta fada, sai Ammy ta kalleta
鈥淜o bata da lafiya ne?鈥�
鈥淟afiyarta kalau鈥�
Shattima ya amsa yana kallon da tai masa mugun kyau kasancewar a cikin bakar abaya, irin kyau nan na fulanin asali masu haiba da daukar hankalin namiji.
鈥淚na Muhseen?鈥�
Ya tambaya ba tare da ya dauke idonsa daga barin kallon Fadime ba, kamar yadda ita ma ta kasa dauke nata idon, sai sakwanni suke turawa junansu.
鈥淪un fa riga ni shigowa, na dauka ma nan suka shigo ai, maybe sun wuce gurin Mai Martaba ne, na ji Aliyu na fadin ma zai koma yau鈥�
鈥淗mm dan wajen Fulani ba a son shiga mutane sai dole鈥�
Ammy ta fada, sai Shattima ya mike tsaye.
鈥淔ateema ya hanya? Za ki ba ni labarin jirgi dai ko?鈥�
Ta kasa cewa komai kamar ba ita ba sai kallonsa take, daman tun a jiya bakinta ya mutu saboda Wasim, yanzu kuma da ta zo nan ta ga wata sabuwar duniya sai ta raina kanta bakin ya kara mutuwa mututus. Murmushi ya sake sakar ya kanne mata ido daya for the first time, hakan ya saka ta hade yawu da karfi ta cigaba da kallonsa har ya fice daga dakin, sannan ta kai hannu ta dafa zuciyarta.
Ta inda Mama Fulani take shiga ba nan take fita ba, ta rufe Ammy da fada kan shirun da tai bayan sanin komai, bata kara sanin Annabi a faku ba sai da Ammy ta labarta mata abun da Hajiya Babba take, kamin a jera musu abun ci da na sha ta dauki wayarsa ta kira Baba Waziri ta sanar masa sun iso kuma tana son ganinsa kamin ta iso gidansa, bata kashe wayar ba sai da ta soma lasa masa zumar abun da ya faru, ko awa daya ba kara ba sai ga Baba Waziri a gidan cikin tashin hankali, a nan Mama Fulani ta zazzage masa komai na abun da ya faru kana Ammy ta dora da nata. Ba karamin baci ran Baba Waziri yai ba kuma be ga laifin kowa ba sai Ammy.
鈥淎mman kin ba ni mamaki Ammy, ni yar'uwa na daukeki ba matar dan'uwa ba, ta ya za a hada kai da matata a cutar da dan'uwana kuma kin sani ki kyale ba ki fada min ba? Ta ya matar dan'uwana za ta so kasheshi kuma ki zuba ido kina fadin baki da hujja, kin san abun da ake nufi da makiyi kuwa? Ashe baki dauki ran yayanki da kuma Mai Martaba a bakin komai ba kenan鈥�
鈥淎to ni ma abun da na gani kenan, kasan wannan har zaka boye yanzu hakaabun da take fada min wai bata labartawa Mai Martaba abun da Hajiya Babba take ba, ta dai fada masa an kaita asibiti bata da lafiya鈥�
Baba Waziri ya jinjina lamari.
鈥淣i na yi mamakin irin abun da Hajiya Talatu take yi, na san tana son Maijidda amman ba irin son da zai sakata shiga wannan halin ba saboda mutuwarta, shiyasa da aka kaita asibiti likitocin suka ce ba su ga komai ba kwakwalwarta lafiya kalau take, kuma sai sunayenku take ambata鈥�
鈥淣i ma na yi mamaki sai dai na yi zaton ko saboda mutuwar ne鈥�
Cewar Ammy tana sauke ajiyar zuciya.
鈥淒ole ne Mai Martaba ya san da wannan maganar, kuma har abada Juwairiyya ba zata taba yin albarka ba har abada鈥�
Baba Waziri ya fada cikin wani irin bakinciki da bacin rai marar misaltuwa.
鈥淜ar a tsine mata abun da ta aikata kadai ya isheta鈥�
Ammy ta fada sai Mama Fulani tai mata wani kallo.
鈥淎llah ya tsine mata albarka, yarinya tai yi kokarin kashe mahaifinta kuma ki ce kar a tsine mata, Allah ya kwashe mata albarka ita da uwarta鈥�
Ammy ta runtse ido tana girgiza kai ko kadan bata son abun da ya shafi tsinuwa domin ta san yadda take cin jiki da dukiyar mutum.
***
Sai dare Shattima ya sake saka Fadime a idonsa, fitar da yai dazun daga dakin Ammy gurin gaisuwa yaje be tashi ba azahar daga can kuma ya wuce asibiti zuwansa na farko tun bayan da akai masa transfer, guri shugaban asibiti ya fara zuwa suka gaisa da shi daman sun san juna yai masa maraba sannan yasa akai masa iso zuwa office dinsa, ko da isa ya samu office dinsa da komai a kintse, takardunsa da komai na sa da yake can Ra'ees ya turo masa su a nan kuma an jera masa sa komai, kwalayen da ke aje gefe ya rika budewa yana dauko abubuwan da ke ciki tare da dorasu a muhallin da yake so, a kwali na uku yai arba da littafin Fadime, murmushi yai ya zauna a saman kujerarsa yana karantawa tana da good handwriting domin duk abun da ta rubuta babu wanda be gane ba, gurin dariya sai yai murmushi, labarinta ne tun daga kan mafarkin da take har zuwa haduwarta da Wasim da abubuwan da suka faru har zuwa kadeta da Shattima yai da neman aurenta da Ra'ees yai komai sai da ta rubuta kadan ya rage littafi ya cika, samun kansa yai da dariya sosai a gurin da yake karanta karyar da yi ma su Bappa da kuma gurin da Wasim yake mata dabon maciji.
鈥淲ow...鈥�
Ya furta yana jinsa cikin nishadi marar misaltuwa, har ga Allah yana son Fadime ta dayan bangaren kuma yana jin dadin rabuwar da Wasim yai da ita. Ya wuni a asibiti har biyar na yamma sannan ya nufi gidansa, a nan ma sai ya rika tuna irin abubuwan da suka yi ta faruwa a lokacin da ya kawo ta gidan.
鈥淜o miyasa ta zama shiru yanzu鈥�
Ya tambayi kansa yana daura tawul.
鈥楳aybe saboda ta rabu da Wasim鈥�
Wani bangare na zuciyarsa ya ba shi amsa, sai ya kai hannunsa ya tura kofa bandakinsa ya shiga ya tsaya gaban madubi yana kallon kansa.
鈥淵es no one can take my place, ke dai kin jin kewa yarinya amman ba rabuwar kauna ba, ai ke ba ki san so ba, yanzu dai za ki sani鈥�
Ya fada with smiling yana kallon kyakkyawar kirar mazantakan da Allah yai masa. Ya shafa kansa yana murmushi tunawa da lokacin da take cewa ina ruwanta da ko shi waye, and the time da ta rike masa kafa akan ba zai tafi ya barta a gidan Zainab ba, da kuma lokacin da take fada masa Jekadiya ta zaunar da ita a kasa.
鈥淚 like her鈥�
Ya furta yana cire tawul din ya aje muhallinsa, sannan ya sakarwa kansa shawa ya lumshe ido yana maida numfashi a hankali. Bayan ya gama ya fito daure da tawul din ya shiga kicin cup ya dauko ya matsa lemun tsami a ciki ya saka kanwa ya zuba ruwa kadan a ciki ya sha.
Be bar gidan ba sai da akai magariba, a masallacin da ke unguwar yai sallah magariba sannan ya karasa masarautar yai isha'i a can, daman tun shigowarsa dakin Ammy ya lura Fadime bata ciki sai ya sulale ya nufi dakin Nana, duk da ba shi da tabbacin tana ciki, tura kofar dakin yai ya shiga, sai ya samu Fadime kwance a kasa gefen gadon Nana, tana ganinshi sai tai saurin tashi tana share hawaye. Karaso yai kusa da ita ta duka gabanta.
鈥淢iyasa kika kwanta kasa鈥�
鈥淕adon na Gimbiya ne ai, be kamata na hau ba鈥�
Ta fada tana murza ido, kallon gadon yai sai kuma ya kalleta.
鈥淣o ke ma ai sarauniya ce karki sake zama kasa鈥�
Ya zauna a gabanta yana kallon yadda bakinta ke motsawa.
鈥淜in ci abinci?鈥�
Ta daga masa kai alamar eh.
鈥淢e kika ci?鈥�
鈥淪himkafa da kaza鈥�
鈥淓yyy kaza dai?鈥�
Shiru tai bata ce komai ba.
鈥淣i dai zaka saka a kai ni gida gobe?鈥�
鈥淲hy gobe? Kin gaji da ni ne?鈥�
鈥淚na son na ga Bappana da Inna...鈥�
Ta fada idonta na cika da kwalla, sai yai murmushi.
鈥淒uk wannan saboda Wasim ne ko?鈥�
Kamar yace bude baki yi kuka, sai kawai ta fashe da kuka. Ido ya sakar mata hakan nan kawai ya ji cewar ba zai iya rarrashinta ba, tun tana kuka a hankali har ta fara yi da karfi.
鈥淏a zaka ce na yi hakuri ba, ba za ka ce na yi shiru ba?鈥�
Ya kalleta yana kallon yadda kuka yana mata kyau.
鈥淜in min kyau da kike kukan nan鈥�
Ta saka hannu ta dafe kirjinsa domin har ga Allah tana jin zafi a zuciyarta irin zafin da ba zata msaltashi a siffa ba balle har ta fadi yadda kirjinta yake mata. Mikewa yai tsaye ya isa guri tissue dake dakin Nana ya dauko box din gaba daya ya zo gabanta ya zauna ya cire tissue din ya kama kanta ya rike ya goge mata fuska ya gyara mata hancinta kamar wata yar yarinya.
鈥淭ashi ki hau gado ki kwanta鈥�
Ta make kafada alamar ba zata hau ba, sai ta kwanta a kasa. Mikewa yai tsaye ya dauko filo ya daga kanta dora mata kanta akan filon sannan ya janyo bedsheet din dake kan gadon ya lullube ta, haka nan kuma sai ya ji duk ya damu da rashin sakewarta kukan da tai sai ya dawo a ransa ya tsaya. Kwantowa yai kadan ya saita bakinsa saitin kunnenta ya soma karanta mata zuciyar kur'ane wato Yasin, cikin kira'a mai dadin saurararo da kwantar da hankali, lamo tai tana ta sauraren yadda zakin muryarsa ke ratsa kunnenta yana isarwa zuciuayrta da sassan jikinta, can kuma ta lumshe ido tana maida numfashi a hankali. Be kai karshen ayar ba bachi mai dadi yai gaba da ita.
ZAINAB POV.
Sai da ta ci kukan ta koshi sannan ta fito ta baro dakin zuwa dakinta, sai kuma ta rasa abun da za tai a dakin kamar wanda ta manta komai haka ta zama sai safa da marwa take a dakin tana tunanin abun da za ta yi. Sake fashewa tai da kuka, tana jin cewar mutuwa zata yi idan ta bar garin Yola, ta ya zata iya rayuwa garin da bata san kowa a can ba, kuma bata saba ba, gashi ba su yarda da komai na zamani ba balle cigaba? How? Ji tai ita kan ba zata iya bin Wasim ba hakan yasa ta juya da sauri ta fice daga dakin zuwa dakin Iya da zimmar yi masa magana sai ta tararda dakin babu kowa a ciki sai ko matsan kayan Iya. Juyowa tai ta fito ta koma dakinta ya shiga bathroom ta hada ma kanta ruwan wanka ta watsa a jikinta ta fito kamar wata marar lafiya, wardrobe dinta ta nufa ta dauko wani yadi marar nauyi ta saka bata shafa komai a jikinta ko turaren da take so a yau sai ta ji bata bukatarsa abubuwa da yawa sun taru sun mata tsaye a rai, idan ta fara tunaninsu sai ta ji kamar ta kashe kanta ta huta. Tana cikin dakin ta ji sallamar Mai gadinta, ba karamin faduwa gabanta yai ba, domin a yanzu tsoron komai take ciki har da sautin mutane. Haka nan dai ta unkura ta tashi ta fita cikin rashin kuzari, sai ta same shi tsaye jikin kofa yana matsar kwalla.
鈥淗ajiya yanzu aka kirani daga kauye wai Mahaifiyata ta rasu鈥�
Ya fada mata karyar da ya ke ta tsarawa tun dazun, bayan mahaifiyarsa ta dade da rasuwa, kawai ya zabi yai haka ne domin ya tsorota da jin cewar mayu ne kuma ya zai iya tafiya ya bar hakkinsa ba. Zainab ta yi murmushin bakinciki domin ta san karya yake yayi hakan ne kawai saboda ya tsiratar da rayuwarsa.
鈥淚na zuwa鈥�
Ta fada sannan ta juya ta koma ciki, albashinsa na watan gaba daya ta dauko ta ba mika masa.
鈥淜ana da gaskiya, dole ne zaka tsorata kuma ban ga laifinka ba na gode鈥�
Ta fada masa haka a yayinda yake karbar kudin, shi kam godiya kawai yai ya fice daga falon, sai ta juya ta koma ciki ta dauko babbar jakarta ta dauki wasu tufafin ta zuba a ciki da kuma wadansu abubuwan da zata iya bukata, sannan ta dauko wata karamar jakar ta zuba tarkacenta ta fito rike da makullin gidan a hannunta, sauran tufafinsa duk a ciki ta bar su sai da ita gurin motarta ta saka jakar sannan ta dawonta rufe ko'ina na gidan, sai kuma tai baya baya tana kallon gidan hawaye na sauko mata.
鈥淎llah duk yadda ka tsara a gareni haka zai kasance, Allah ka min mafita ka yaye min damuwata ka shiga cikin lamarina鈥�
Ta saka hannunta ta share hwayenta sannan ta juya ta nufi gate ta bude ma kanta ta dawonta shiga motarta ta fita da ita sannan ta sake dawowa ta rufe gate din ta saka masa key, har ta juya sai kuma ta juyo ta kai hannu ta taba gate din, sannan ta koma cikin motarta ta ja motar bata tsaya ko'ina ba sai gidansu kawarta Amina, duk da wani shiri suke irin sosai ba but ta san Amina mace ce mai amana kuma mai sanin ya kamata. Amina ta yi mamakin ganinta a irin wannan lokacin da ake ta kira kiren sallah magariba. Bayan sun gaisa Zainab ta kama hannunta ta danka mata keys din motarta da na gidanta, Amina ta kalli keys din da mamaki sannan ta kalleta.
鈥淣a meye?鈥�
鈥淣a motata ne da na gidana, na yarda ke shiyasa na baki ajiyar wannan, kuma dan Allah a rika kula min da gidana鈥�
鈥淢iya faru?鈥�
鈥淏a komai kawai zan bar garin nan ne, na wani lokaci ke kadai na yarda da ke a duk kawayena鈥�
Amina ta mike tsaye tana kallon yadda hawaye ke saukowa a idon Zainab.
鈥淒an Allah ki fada min idan wata matsala ce鈥�
鈥淶an kira ki a waya anjima, na baki mana, idan kuma kika ga na dauki lokaci ban dawo ba ki siyar da komai ki min sadaka鈥�
鈥淲annan wace irin magana ce Lafiya kike Zainab?鈥�
鈥淟afiya kalau na ke Amina鈥�
Ta fashe da kuka, tare da saurin mikewa tsaye domin bata son mijinta ya dawo ya tararda ita a gidan.
鈥淎mman zan fada wa Mai gidana, idan be aminta ba zan hannata fada miki a waya sai ki fadi wanda a hannatawa abun鈥�
鈥淏a matsala na gode鈥�
鈥淎llah yai miki mafita ya yaye miki ko miye a ranki鈥�
鈥淎min sai wata rana鈥�
Zainab ta fada cikin kuka sannan ta juya ta fice da sauri, daman ta cire akwatinta a wajen motar sai ta karasa ta ja shi zuwa gate Amina ta fito ta tsaya bakin kofar falonta tana kallon Zainab hawaye na sauko mata. A Hotel Zainab ta kwana tun a dare ta siye ticket din zuwa Katsina, washe gari ta shirya ta nufi airport cikin shiga ta doguwar rigar atamfa da mask sai dan karamin mayafi da kwatinta sai yar karamar jakar hannunta.
Karfe goma daidai jirginsu ya daga zuwa Katsina, sai a lokacin ne ta ji wani irin kewa da tausayin kanta ya kara kamata.
<<<<<<<<
Da 9pm zan turo wani Inshallah, jiya ban samu na yi ba saboda ba nepa.
_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number聽 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
03/12/2021, 18:59 - 馃馃馃馃: *Khadeeja Candy*
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
Lumshe ido yai ya bude har lokacin idonta a rufe suke tana murmushi.
鈥淔ateme..鈥�
Ya kira sunanta da muryar da bata taba jinsa da ita ba. Hakan yasa tai saurin bude idon sai tai arba da hawaye da ke sauka fuskarsa. Take hamkalinta yai mugun tashi.
鈥淢iyasa kake kuka? Me ya faru? Ko dan an taba min ido?鈥�
鈥淎a鈥�
鈥淭o me ya saka ka kuka?鈥�
Ya kai dubansa gurin rigar da ke jikinta sannan ya kai hannunsa ya kama hannunta ya dora saitin kirjinsa.
鈥淏an kwana na zo na yi miki鈥�
鈥淚na zaka je鈥�
鈥淏abu inda zan je?鈥�
鈥淭o miyasa kake min bankwana? Ko mutuwa zan yi?鈥�
Yayi murmushi wasu hawaye na sauko masa.
鈥淎a, bankwana na har abada鈥�
鈥淢utuwa zan yi? Ko jirgin zai yi hadari damu mu mutu?鈥�
Ya girgiza mata kainyana yawo da idonsa a fuskarta.
鈥淶an miki bankwana ne, irin na tafiya ba na mutuwa ba, zan tafi garinmu ja zauna tare da yan'uwana, ke kuma na bar ki da na kin yan'uwan?鈥�
Take ta ji wani iri sai a bata fuska kamar ta fasa kuka.
鈥淢e na yi?鈥�
鈥淏a ki yi komai ba, ba za ki taba min komai ba鈥�
Ya fada sannan ya kama tafin hannunta ya saka cikin na shi.
鈥淪aboda wannan...鈥�
Wani irin jan numfashi tai cike da tsoro, ba tsoro na ganin wani abun gudu ba, sai dan tsoro na sanyin da bata ji ba a hannunsa.
鈥淢iyasa ban ji sanyin ba?鈥�
Ta tambaya cikin tashi hankali. Sai ya bata amsa cikin kuka marar sauti.
鈥淪aboda bani ne mijin ba鈥�
Fashewa tai da kuka ta rumgume shi da sauri.
鈥淎a kai ne, kai ne Wallahi...鈥�
Hannunsa ya saka ya banbanreta daga jikinsa ya kama fuska hawaye na sauko masa.
鈥淒a gaske ba ni ba ne, ba ki taba hannun wani namijin kin ji sanyi ba?鈥�
Ta yi shiru tana kuka irin kukan dake shigewa cikin zuciya saboda bakinciki da zafinsa.
鈥淜a kara zuba min to鈥�
鈥淚dan zan zuba miki sau dari ki rike hannuna sau dubu ba za ki ji komai ba, saboda ba ni ba ne鈥�
鈥淎mman ni ai ni ce ni dai ina sonka haka nan鈥�
Ya sake rumgume kankan, sai ya lumshe ido hawaye na sauko masa.
鈥淜arka bar ni dan Allah, kai kadai na ke so, bana son kowa ni da kai na saba鈥�
鈥淶a ki saba da kowa ma, domin kina da shiga rai, kina burge wanda ya fahimci rayuwarki鈥�
Ta dago tana kallonsa.
鈥淢iyasa to zaka bar ni? Mi na yi?鈥�
Bude idonsa yai ya kalleta.
鈥淪aboda, addina da na ki ba daya ba ne, al'adata da ta ki ba daya ba ce, kuma ba ne mijin ba, domin ba ki ji sanyi a hannuna ba鈥�
鈥淎i ba dole sai na ji sanyin ba, Dan Allah Wasim ka daina min wasa鈥�
鈥淏a wasa ba ne, dole ta sa ni kaina ba dan na so ba ne, idan ban rabu da ke ba, Idonki ba zai bude ba, kuma da yanzu ba ki dawo hayyacinci ba, mahaifina ya dage akan dole na rabu da ke, idan ba haka ba ba zai bar ki ba鈥�
鈥淭o ka aureni a haka mana, Wasim dan Allah... Ina son idon ya rufe sai mu yi auren dan Allah鈥�
Ta durkushe a gabansa tana fashewa da kuka.
鈥淏a za ki ga ne ba ne, idan na yi haka b zaki jidadin rayuwar ba, ni ma kuma ba zan so haka agareki ba鈥�
鈥淣a gane baka so na yanzu? Saboda bana jin magana ko? Saboda ina ta yawan magana ko? Na bari daga yau ba zan sake ba, ko na ji maganar ta zo zan yi sauri na rufe bakina, dan Allah kai hakuri Wasim ina sonka, ni dai ina sonka鈥�
Juya mata baya yai ya dafe kansa yana ta hawaye, duk yadda za ta ji ya san b kai kwatar yadda yake ji ba, domin shi ya fara kamuwa da kaunarta, kuma ita zata iya samu wanda zai kula da ita ya biye rayuwarta ta manta da shi amman shi kamin ya samu haka abu ne mai wahala.
鈥淲asim... 鈥�
Ta kira sunansa cikin kuka, sai ya saka hannunsa ya share hawayensa ya juyo ya kalleta.
鈥淏a ki taba hannun wani kika ji sanyi ba?鈥�
鈥淏an son shi ban son ban son wacan, ni da kai na saba鈥�
Ta make kafada tana ta kuka tana fadin haka, sai murmushi da hawaye suka zo masa lokaci daya, sai ya duka daidai ita.
鈥淶an tafi, daman na zo ne na yi miki sallama, ba zan sake dawowa gareki ba, ba za ki sake ganina ba, amman bana son ki manta da ni, kamar yadda ni ma ba zan manta da ke ba鈥�
Ya kama hannayenta duka biyu ya sumbanta.
鈥淚na sonki sosai ina son ki san wannan, amman kaddara ta raba komai, ba mu isa mu canja kaddara ba, ina miki fatar alheri鈥�
Ya saka dayan hannunsa aljihu ya ciro abun hannu mai kamar na azurfa ya kama hannunta ya saka mata, sannan ya sake saka hannunsa ya dauko sarewa yar karama kamar ta wasan yara ya mika mata.
鈥淜i busa wannan a duk lokacin da kika tuna da ni鈥�
Ya sumbacin goshinta, sai ta lumshe ido ta matse sarewar a hannunta sosai, can kuma ta bude ido sai ta ga babu shi a gabanta take ta mike tsaye ta fara waige waige.
鈥淲as... Was.... Was....鈥�
Ba ta ko iya furta sunan saboda kukan da ya ci karfinta, sai waige waige take kamar sabuwar mahaukaciya tana kiran sunansa murya a dakishe, sai kuma ta tsaya can tana daukar numfashi kamar ba ita, domin zan ka rantse da Allah Fadime ba zata iya shiga irin wannan halin ba saboda wani ya barta. Jin tai a taba sai ta juyo da sauri, arba tai da Wasim dake sanye da tufafinsa na dazun wando tufafinsa sai dai fuskarsa ta yi kaca kaca da hawaye kamar an yi yakin kuka, idonsa ma sun rine sun masa mugun ja sosai kamar garwashi.
鈥淢utuwa zan yi dan Allah karka tafi, na ji wani abu a cikin zuciyata yayi min nauyi sosai kumaya danne numfashina.... Kuma... Yana sa ni ciwon kirj kamar zuciyar zata fito, dan Allah karka ta fi idan ka tafi abun zai dawo, zan iya mutuwa鈥�
Ta fada daker numfashi na sarke mata saboda kuka da kuma nauyin zuciyar da take ji abun da bata taba ba. Ta fadi hakan ne saboda bata taba sanin wani abu heartbreak na ainahin ba sai a yau, a strong feeling of sadness har cikin bayanta take jin ciwon.
Hannunsa ya saka ya rike fuskarta sai ya hade goshinsu guri daya ya lumshe ido yana maida numfashi a hankali, yana jin fiye da yadda take ji.
鈥淜a ce ya rufe idon ka ji? Na yarda ya rufe idon sai ya bar ni na aureka? Ina son ka Wasim dan Allah鈥�
鈥淚na sonki fiye da yadda kike so na Fateme amman babu yadda zan yi... Ba zan iya zuba ido ki cutu ba, ba zan iya rayuwa cikin farinciki ba bayan ke kinaa cikin wata damuwar鈥�
Ta kama hannunsa ta sake tabawa, ta sake a karo na uku, sai sake karawa sau ba dadin tana ta kuka.
鈥淲ayyo Allah na鈥�
Tana ta yakar kukanta tana sakawa a zuciya domin bata son ya fito, sam bata ma son ta yarda cewar Wasim zai tafi.
鈥淜o wani abun na yi maka?鈥�
Ya girgiza mata kai.
鈥淏a ki yi komai ba鈥�
鈥淜o saboda na ce Zainab Mayya ce?鈥�
鈥淶ainab ba mayya ba ce, Iya ce mayya, kuma ba saboda haka ba ne, na fada miki idan ban rabu da ke ba, idonki ba zai dawo ba, kuma asirin da Hajiya Babba ta yi miki da Hajiya Talatu ba zai barki ba, asiri suka miki aljani ya dauke ki daga can ya dawo da kenan kuma ya mantar da ke komai, kaka ya ki aminta ya yi magana da aljanin har sai idan na yarda ya rabu da ke, kuma dole na aminta saboda ba ni ne mijinki ba鈥�
鈥淲asim aa dan Allah... Ka bashi hakuri ka ce na ce dan Allah yayi hakuri鈥�
Yayi murmushin tare da hawaye a lokaci daya.
鈥淏abu wani abu da zamu iya yi, je ki yi ibadarki鈥�
Ya sake ta sai tsaye guri daya tana jin cewar idan ta matsa tafiya zai yi.
鈥淶an yi marmarin murmushinki, kiriniyarki da ma komai na ki, ina son ki sosai鈥�
鈥淪ake zuba min maganin鈥�
Ta tara mishi hannunta tana kuka sosai marar sauti, sai ya share hawayen idonsa yana kallon fuskarta.
鈥淏a ki yarda da ni ba ne Fateme?鈥�
Ta daga masa kai alamar eh bata yarda din ba, sai yai murmushi idonsa suka sake cika da kwalla.
鈥淭o rufe idonki na miki na ido鈥�
鈥淚dan na rufe sai ka tafi?鈥�
鈥淎a zan tsaya har sai kin yarda鈥�
Sai ta rufe ido daya ta bude daya, nan ma Murmushi yai yana jin kamar ya kurma ihu saboda zai bar Fadime, dabi'unta na daga cikin abubuwan da ke burgeshi.
鈥淒ole sai kin rufe duka....鈥�
Ya fada cikin kuka irin na masa, domin ya san tafiya zai yi ya barta, ba kamar yadda take zato ba. Sai ta rufe idon tana ta saurare ko zata ji wani abu ko ta gani amman shiru, hakan yasa ta bude idon sai ta ga babu kowa a dakin. Ta fi karfin minti talatin a tsaye tana hawaye sai sauraren abun da ke mata yawo a zuciya yake, can kuma ya kai hannu ta dauki sarewar tana dubawa hawaye har basa bari ta ga komai daidai. Dukawa tai ta aje sarewar ta nufi inda take ganin Hijab ta dauka bata ko tsaya neman prayer mat ba ta yi sallah a kan tile, tana sallah tana hawaye har ta sallame, a lokacin da ta daga hannunta tai addu'a sai ta rasa abun da zata roka, sai kawai ta fashe da wani irin kuka sosai.
***
Muhseen na daf da shiga mota wayarsa dake aljihu tai ringing ciro wayar yai yana duba sunan mai kiran Shattima ne rubuce akan wayar, picking yai.
鈥淗ello Shattima鈥�
鈥淢uhseen ya gida?鈥�
鈥淎lhamdulillah ya hakuri? Gobe zamu shigo Inshallah鈥�
鈥淎llah ya kai mu kana kusa da Fateema?鈥�
鈥淓h ka yi sa'a yanzu zan bar gidan Mama Fulani鈥�
鈥淎i kullum cikin sa'a na ke鈥�
鈥淓h kan tun da ka samu wannan talkative din鈥�
Muhseen ya fada da dariya sannan ya juya ya shiga cikin yana labartarwa Shattima yadda Aliyu ya fada masa sun tsinci Ataa. Kai tsaye ya nufi upstairs ya kwankwansa kofar dakin da Fadime take ciki sannan ya bude ya shiga, sai ya same ta zaune hawaye na sauko mata kamar wanda akai wa mutuwa. Mamaki ne ya rufe Muhseen sai ya sauke wayar daga kunnensa yana kallonta.
鈥淟afiya?鈥�
Hade kukan kawai take bata iya cewa komai, hakan yasa shi tunanin ko ta sake losing memory ta ne?
鈥淵asmin?鈥�
Nan ma bata amsa ba, domin jin take idan ta bude bakinta kuka ne zai fito.
鈥淟afiya?鈥�
Shattima ya tambaya daga cikin wayar, sai Muhseen ya maida wayar kunnensa.
鈥淜uka take?鈥�
鈥淜uka? Bata wayar鈥�
Muhseen ya karasa inda take zaune ya mika mata wayar.
鈥淪hattima zai yi magana da ke鈥�
Kin karba tai sai hawaye take tana fisgar numfashi da karfi.
鈥淏a ta karba ba鈥�
鈥淢e akai mata?鈥�
鈥淚 don't know鈥�
鈥淜ara mata a kunne鈥�
Muhseen yayi yadda Shattima ya fada ya kai wayar saitin kunnenta ya kara mata.
鈥淔ateema...鈥�
Shattima ya kira sunanta a hankali tare da fatar ta amsa mishi sai ya ji shiru.
鈥淔ateema talk to me, fada min matsalarki鈥�
鈥淎i duk kai ne ka taba hannuna har sanyin ya cire gashi nan ya taba ban ji sanyi ba鈥�
Bayan ta amayar masa da haka sai ta samu damar fashewa da irin kuka mai karfi wanda ya saka Mama Fulani da Aliyu da ke downstairs jin muryarta. Runtse ido Shattima yai kamar tana gabansa.
鈥淣a shiga uku....鈥�
Ya fada sannan ya yanke wayar ya sake kira sai Muhseen ya dauka wanda hakan yai daidai da shigowar Mama Fulani da kuma Aliyu har ma da Ataa saboda kukanta da suka ji.
鈥淜a hau online pls zan kira ta video call鈥�
鈥淥kay鈥�
Ya sauke wayar yana kallon Mama Fulani dake tambayar ba'asi.
鈥淲allahi ban sani ba, ni ma dai na same ta tana kuka ne鈥�
Mama Fulani ta shiga tanbayarta abun da akai mata amman Fadime ban da kuka babu abun da take, Aliyu dai na tsaye jikin kofa yana kallonta, Ataa ta matsa kusa da ita ta taba ta.
鈥淟afiya me ya faru? Ko wani ya mutu?鈥�
Nan ma bata iya samawa ba sai kuka take sosai. Muhseen ya yi murmushi domin shi a shirita ya dauki kukanta ganin ta ki cewa komai sai kuka take.
鈥淜una ganin wannan yarinyar kun san shagwababbiya ce, mai iya mata sai Allah sai Shattima, dan yanzu ta gama masa masifa a waya鈥�
鈥淭o shi Shattima da kansa?鈥�
Cewar Mama Fulani da dan mamaki, domin ta san waye Shattima.
鈥淜ar dai ayi na Ataa da Aliyu鈥�
Ataa ta yi dariya Aliyu kuma ya juya ya fice yana dan murmushi kadan. Mama Fulani ma ficewa tai tana murmushi ita da Ataa.Muhseem na kunna datansa kiran Shattima na shigowa ta Whatsapp video, picking yai sannan ya mikawa Fadime, sai ta ki karba.
鈥淏ata karba ba鈥�
鈥淎je mata鈥�
鈥淜ar ta fasa min IPhone fa鈥�
鈥淶a a siya maka wata, kai dai aje mata鈥�
Murmushi yai ya aje mata wayar a saman hijabin da take sanye da shi, sannan ya juya ya fita, kamar fitarsa ake jira sai sakon sms ya shigo wayarsa ta line Shattima.
_Kawo mata ruwa pls_
Ya wara ido kamar Shattima ne a gabansa.
鈥淭o duk dai鈥�
Ya fada sannan ya sauka kasa ya nufi kitchen, ruwa ya dauko mata tare da cup ya dawo dakin ya aje mata, har lokacin bata taba wayar ba, sai hawaye take ta yi. Shi dai be ce mata komai ba ya fice abunsa yana dariyarta.
鈥淔ateema鈥�
Shattima ya kirata, bata amsa ba kuma bata kallin wayarba, hakan yasa be samu damar ganin Fuskarta da kyau ba.
鈥淗aba Fatee na, ki amsa min mana, ba kin san nima ina cikin damuwa ba? Amman na damu da taki damuwar fiye da tawa鈥�
Nan ma shiru.
鈥淏a ki gode Allah da ya dawo miki da idonki ba? Ki ce Alhamdulillah wani na can yana neman idon be samu ba鈥�
Maganar yai sai ta ji kamar ya kara takalo mata Wasim sai ta rushe da kuka.
鈥淲asim fa ya tafi wai ba zai dawo ba, wayyo zuciyata鈥�
Ta fada daker tana kai hannu ta dafe zuciyar. At first he surprised ima ta ga Wasim din? Ina ya tafi?
鈥淚na kika ganshi?鈥�
鈥淵a zo yanzu yayi min bankwana ya ce ba zan sake ganinsa ba鈥�
鈥淏etter, kara ki rabu da mai kama da wannan aljanin ki huta ai鈥�
Ya fada a ransa a fili kuma sai ya ce.
鈥淪hi yace miki ba zai dawo ba?鈥�
鈥淓h... 鈥�
Ta labarta masa abun da ya faru daker sai wani sabon kukan ya taso mata. A yanzu kan sai ya ji kukanta ya fara damunsa, ba damuwa ta gundira ko gajiya da kukan ba, no damuwa na hawayen da take zubarwa kuma ta ba shi tausayi sosai domin ya san yadda abun yake, da ace mutun ya bar ka kara ya ace mutuwa yai hankali zai fi kwanciya kuma zuciya zata fi samun salama.
鈥淏a ni da sa'a, daman babu wanda ya tana cewa yana so na sai shi kuma shi ma ya tafi鈥�
Sosai ya ji ransa ya bace saboda damuwar da take ciki, ta dayan bangaren kuma sai ya ji Wasim din ya bashi tausayi domin rabuwa da abun da kake so abu ne mai wahala balle Fadime duk wanda ya shaku da ita ba zai so rabuwa da ita ba. Ba dan yana so ba yai ta sauraren kukanta har ta iya wanda take jin ya samar mata da sallama.
鈥淔ateema ki saurare ni kin ji鈥�
Ta kalli wayar da idanuwanta da suka rine suka yi ja sosai saboda kuka, farar fatar idonta har ta soma ja kumatunta ma kamar an mareta.
鈥淪hare hawayenki ki sha ruwa zan fada miki wata magana鈥�
Sai yai sa'a ta saka hijabin ta share hawayen ta goge hancinta sannan ta cire Hijabin gaba daya ta aje, ta hada uban gumi kamar ba dakin da ke da ac. Jingine wayar tai ta yadda zata iya kallonsa shi ma kuma zai iya ganinta, sannan ta bude ruwan ta zuba a kofi ta sha, ta aje tana wani irin mumfashi kamar ba ita ba, ita kanta bata san ranar da tai kuka irin wannan ba.
鈥淜in san cewa Babanki yana raye?鈥�
Ta daga mishi kai.
鈥淢amanki ma haka鈥�
Ta sake daga masa kai.
鈥淪u kadai sun isa ki tuna da su ki ji farinciki domin na tabbatar a yanzu suna can suna jiran dawowarki, bayan su duk wani abun farinciki da zaki samu a duniyar nan a bayansu yake, lokuta da dama muna gina rayuwarta tare da mutanen da be zama lallai mu rayu da su har karshen rayuwarmu ba, wasu su kam shigo rayuwarmu saboda su bar mana tarihi, su tafi ko kuma mu tafi mu bar su, sai dai abun da yake da muhimmanci idan mum tuna, shi ne yadda mu ka yi rayuwa da su, na san yadda kike ji saboda na taba jin fiye da abun da kike ji a yanzu, ke daya kawai kika rasa, kuma ba mutuwa yai ba, ni kuma fa? Na rasa mata da yawa ciki har da Maijidda da ta rasu a yau, na rasa yayana, na kai matsayin da bana kallon mace na ji ina sonta saboda halin da na ke ciki, ta dayan bangaren kuma ga mahaifiya ba shi da lafiya, kullum fargabata kar na rasa shi, a haka na koyawa kaiwa yin murmushi a inda ya zama dole, na ko yi hakuri kuma ya yarda cewar wannan kaddarata ce, wani be isa ya canja min ba...鈥�
Kalamansa ne suka soma tasiri a zuciyarta har ta saka hannunta ta soma share hawayenta.
鈥淲ani lokacin rayuwa tana zuwa ga mutum kamar ya zabi kasancewa a haka, wani lokacin kuma sai ta zowa bawa kamar shi ka fi tsana a duniyar nan, fada min bayan rabuwa da Wasim a yanzu kin taba shiga wata damuwa babba kamar haka?鈥�
Ta yi shiru tana tunani sai kuma ta girgiza masa kai alamar aa.
鈥淭o ki gode Allah jarrabawarki kadan ce, idan kin yi hakuri sai Allah ya baki wanda ya fi Wasim komai, kin ji?鈥�
Ta daga masa kai kamar gaske, sai yai murmushi har cikin ransa yake jindadin yadda hankalinta ya fara kwantawa.
鈥淪mile for me, na aje miki wani abu babba鈥�
A maimakon tai dariya kamar yadda ya bukata sai ta fashe masa da kuka mai karfi.
鈥淲ayyo Allah Wasim鈥�
Shattima ya dafe kansa yana jin haushin Wasim for no reason, sai dai har ga Allah baya son hawayen da Fadime ke zubar da hawaye saboda shi, jin ta yake a wani matsayi da bangare na zuciyarsa.
ZAINAB POV.
Kuka tai har na fitar hankali sai a yanzu ta gane ashe bakinciki da kukan da tai a baya duk wasa ne yanzu na gaske ya zo. Sai da tai kukan da take jin ta cancanci salama sannan ta saurarawa kanta ta mike tsaye tana kallon inda Iya take kwance galala tana ta fadin sunayen mutanen da ta ci, tsaye Zainab tai tana ta kallonta ta rasa abun da za ta yi, idan ma ta dauke ta bata san inda zata kaita ba, ta kasa yarda mutanen da su kai mata inuwa su ka bata masauki a zuciyarsu da muhallinsu a yau su suke mata wa'adin barin garin Yola gaba dayansa.
鈥淢iyasa zan zabtu da laifin da ba san lokacin da aka aikata shi ba? Why? Miyasa rayuwa zata min haka?鈥�
Ta tambayi kanta tana karewa dakin kallo kamar bakonta, duk abun da take Wasim na tsaye bakin kofar dakin yana kallonta, sake faduwa kasa tana shafa jikinta.
鈥淢iyasa abubuwan da ban aikata ba za su shafe ni?鈥�
鈥淪aboda ba ki zabi uwa ba, kuma ba ki za bi uba ba, haka ma ba ki zabi halin da kike ciki a yanzu ba, shin hakan be isa ya karantar ke cewar ba mu isa mu zabi yadda rayuwarmu zata kasance ba? Balle mutanen cikinta?鈥�
A firgice ta juyo ta kalleshi.
鈥淏anbanci rayuwata da taki kadan ne, dukan mu muna ciki wani hali鈥�
Yana maganar hawaye na sauko masa kamar ita.
鈥淏a zaka taba gane yadda na ke ji ba, na rasa komai na farinciki, rayuwar kunci ta bude min kofa, ina son na mutu a yanzu mutuwa kawai na ke so...鈥�
Ta karasa cikin kuka tana kallon hannayenta, sai ya karaso cikin dakin kusa da ita yana kallon Iya.
鈥淗ar yanzu kina da sauran farinciki, na tabbatar kina da wasu dangin da za su ba ki farinciki a rayuwarki, wata kila nan kusa ki manta da komai鈥�
Ya saka hannunsa ya tare hawayen idonsa.
鈥淶an tafi da ita, amman hakan ba zai hana ta mutuwa ba domin an mata aike ne, ke kuma a duk lokacin da kika shirya muna maraba da ke...鈥�
鈥淜enan mutuwa za ta yi? Shikenan na rasa kowa? Ba zan iya rayuwa ni kadai ba鈥�
Hannayensa ya saka ya dafa kafadunta.
鈥淏a zan barki ki yi rayuwa ke kadai ba, zan kasance tare da ke, kuma na miki alkawarin farinciki鈥�
Ya fada cike da kwarin guiwa saboda yana jin ta fishi shiga mawuyacin hali. Fashewa tai da kuka tana kallon Iya.
鈥淜omai ta lalace ina sonta, dan Allah karku kasheta, ita kadai ta rage min a yanzu, komai halin da ta shiga ina son ganinta bana son na rasa na rasa komai a yanzu鈥�
Masauki yai mata a faffadan kirjinsa, wanda hakan ya bata damar tausayawa kanta ta fashe da sabon kuka tana jin kamar ta hade zuciya ta mutu ta hutu. Shi kuma ya lumshe ido yana sauraren kukanta dake shiga har cikin ransa yana jin kukanta kamar Fadime da ya baro tana nata kukan!
***
A lokacin da Ammy ta dawo gida da tunani kala kala da kuma mamakin da bakinciki a lokaci daya na abun da ya faru da Iya, sai ta tararda Masarautar da wani sabon labari na rashin lafiyar Jurry da kuma Hajiya Babba. Tufafin jikinta kawai ta canja ta shiga bangaren Mai Martaba ta sanar masa halin da ake ciki, sannan ta fito ta nufi asibitin. Ko da ta isa ta samu Kausar da Karima a dakin Hajiya Babba kuma tana kwana sakamakon allurar bachin da akai mata, saboda yawan maganganun da take na abubuwan da ta aikata, Ammy bata san komai ba akan ciwon kuma wani be labarta mata abubuwan da Hajiya Babba take ta fadaa gadon asibitin ba, sai dai a ta yi mamakin ganin babu family ko daga daga bangaren Hajiya Babba haka ma daga bangaren Mai Martaba sai yayanta kawai, su ma suna ta soke kai kamar ba son kallonta.
鈥淛ekadiya tace Juwairiyya ma ba Lafiya, ita a ina aka kaita?鈥�
鈥淜anta ne yake ciwo, ban san inda aka kaita ba鈥�
Kausar ta amsa cike da damuwa, Ammy dai bata sake cewa komai ba sai kallon Hajiya Talatu take da baki ya juye gefe daya.
鈥淎nya babu hawan jini na ga shi ke saka haka?鈥�
Kamin su amsa mata Hajiya Babba ta fara motsawa ta juyo saitin Ammy dake zaune akan kujera, ta dade tana murza idon sannan ta bude ta sauke su akan Ammy dake ta mata sannu, Kausar da Karima kam hankalinsu ya mugun tashin, da sauri Karima ya nufi kofa tana fadin.
鈥淏ari na kira likita鈥�
Cikin hanzari ta fice zuwa kiran likitan, so take ya sake mata allurra tai bachi har sai Ammy ta fita.
_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number聽 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
03/12/2021, 18:59 - 馃馃馃馃: *Khadeeja Candy*
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
Kamar wacan tafiyar da sukai da Fadime, haka ta sauka garin Katsina kai tsaye ta nufi tashar ta samu motar da zata kaita garin bayan ta yi jinga da direban, shi kuma ya fada mata ya san garin amman zai kaita bakin kofar garin ne kawai ya dawo, tace masa ta aminta. Sai ta shiga motar ita kadai, suka dauka zuwa garin. Tana cikin motar shiru sai kallon hanya take, a duk lokacin da tai yunkurin kuka sai ta kasa, sai dai abun ya shiga zuciyarta ya zauna sosai ta yadda ko numfashi tai da karfi sai ta ji kirjinta yayi ciwo.
Kamar yadda ya fada nesa da kofar garin ya sauke ta daman tun a tasha ta biya shi kudinshi sai ta bude motar ta fita ta fara takawa da kafa tana tuna zuwansu na baya da Fadime, a lokacin da ta zo a boye kuma cikin rashin sani, tsabanin yanzu da ita kanta ta kawo kanta domin ta san zata gina rayuwarta a nan ne, garin da babu network babu tv babu mota balle wani abu na cigaban zamani. Tun kan ta karasa bakin kofar garin ta hango Wasim tsaye yana jiran isowarta hakan na nufin ya san da zuwanta kenan ko kuma an sanar masa. Sai da ta kai daf da shi sannan ta tsaya ita da shi suna facing din juna, ta kasa ce masa komai shi ma haka sai karantar damuwarta yake zuciyarsa na cika da tausayinta. Can kuma sai ya sakar mata murmushi ya kai hannu ya karbi akwatinta ta juya ya fara tafiya sai ta daga kai tana kallon kofar garin kamin ta juya ta kalli hanyar da ta biyo tana tunawa da Yola. Sai kuma ta juyo ta ni bayan Wasim har suka isa gurin da farin dokinsa yake ya taimaka mata ta hau ya dora akwatinta a sama, shi kuma ya rike linzamin dokin a hannu dayan hannunsa yana tafiya a kasa, kallon garin take da mutanen cikinsa kamar yadda su ma suke kallonta ganin tufafin jikinta dabam kuma ta hau dokin Wasim da kansa yana jan dokin. Tafiya su kai mai dan nisa sannan suka isa masarautar su Wasim, a nan ma shi ya taimaka mata ta sauko sannan yai gaba ta bi bayansa tana tafe tana kallon mutanen dake cikin masarautar da su ma kallonta suke suna saurin kawar da ido saboda Wasim. Banbanci wacan tafiyar da wannan wacan ta yi ta ne a cikin tsoro da zullum tsabanin wannan da bata jin komai ko da ace tana zuwa kasheta za su yi ta riga ta goge komai a zuciyarta. Wata matar ce mai kama da hadiman masarautar tai saurin zuwa ta karbi jakar da Wasim yake roko ta Zainab, shi kuma ya nufi cikin masarautar sai ta biyo bayansa suka shiga har ciki. Abun da ba ta yi zato ba ta samu daga sarki wato tarba da murmushi ya kuma ware mata hannayensa alamar ta karaso gareshi. Sai ta tsaya can bakin kofar fadar idonta ya cika da hawaye.
鈥淜araso gareni Yata...鈥�
Sarkin ya fada da murmushi a fuskarsa, daman can babu wanda ya kai yan garin Garuk son yan'uwansu balle kuma Sarkin da ya san cewar Zainab jininsu ce, hannu ta saka a share hawayenta sannan ta karasa inda yake ta rumgume shi kamar yadda ya bukata sai duk sauran yan fadar suka duka kasa suna kai mata gaisuwa, ko da ba mutanen kwarai ba ne at least ita dai tana da yan'uwa da za su iya karbarta a lokacin da duniya ta tsane ta.
鈥淣a gode鈥�
Ta fadawa Wasim tana kallonsa, sai ya sakar mata murmushi da bukarsa da tunanin rabuwa da Fadime yasa ta zurma ta haifar masa da rama sosai. Shugaba da kansa ya nuna mata inda zata zauna a kujerar dake kusa da ta shi, sannan ya gabatar musu da ita cikin farinciki duk da bata jin abun da yake fada sai dai tana kallon fuskarsa ta san farinciki yake. Bayan sarkin ya gama Wasim ya shiga yi masa magana da yarensu.
鈥淪ai dai ita tana kan addini ne na dabam tsabanin wanda mu kai ba, ina fatar ba za a hanata ibadar ta ba鈥�
鈥淚n har zata zabi dawowa gida cikin yan'uwa da dangin mahaifiyarta me zai hana ta watsar da komai ta rike na mu鈥�
Wasim ya kalleta.
鈥淜ina da ra'ayin barin addininki ne Zainab?鈥�
鈥淗ar a bada, ba zan taba barin musulunci ba, ko da kuwa hakan na nufin mutuwa ta ne鈥�
Ya juya ya kalli Sarki yana mayar masa da amsa da yarensu sannan ya dora da.
鈥淏e kamata a hana kowa yin abun da yake so ba, musamman mutane irina irinta wandanda su ka bar kasar nan su ka bar garin nan su ka shiga duniya su ga cigaban da duniya ta samu, an cigaba an wuce wannan babin鈥�
鈥淏a ma ra'ayin addininta鈥�
鈥淚dan har ba ku ra'ayin addininta hakan na nufi ba ku ra'ayinta, ni kuma zan iya daukarta mu bar garin nan, ba zai yiyu a kara mana wani bakinciki ba ni da ita鈥�
Ya fada da yarensu sannan ya kalli Zainab.
鈥淭a so muje鈥�
Zainab ta mike tsaye ta bi bayan Wasim. Sai ya shiga da ita can cikin masarautar a inda mata da yaya suke da kuma dakuna gwanin sha'awa, daki daya ya ware mata a matsayin nata sannan ya kawo mata uku wadanda zasu rika yi mata hidima. Wannan furucin da Wasim yai ya saka ba su hana Zainab yin sallah ko saka kalar tufafin da take so ba, hakan kuma da take sai ya burge mutanen garin musamman ganin tufafinta na zamani ne gashi idan ta saka za su rufe mata jiki har kasa, sai dai su matse ta kasancewar duk tufafinta haka suke mata. Idan ta fito waje tana sallah wani lokacin sai su yi taro suna kallonta, alwalar da take ma kallonta suke suna ganin ta yi wani abu na dabam da ba su saba gani ba, gashi bata jin yaren mutanen garin idan tana son magana da su sai ta sha wahala sosai, abinci ma bata iya cin komai sai yayan itutuwa saboda tana jin launin abinci gurin dadi da kala ba irin nata ba, ganin hakan yasa Wasim yake zuwa yana siyo mata abincin irin an yan birni, and haka zai zo ya zauna yana fira da ita duk da kasancewar shi kansa baya cikin sakewar zuciya sai dai a kokarinsa na ganin ya faranta mata rai sai ya samu kansa cikin faranta nasa ran, idan tana sallah kuma sai yai ta kallonta yana tunawa da Fadime. Yau ma kamar kullum yana zaune bakin kofar dakin yana kallon yadda take sallah a kusa da shi saboda zafin dakin yasa ta fito waje tana sallah. Bayan ta gama ta yi addu'a ya kalli kyakyawar fuskarta mai dauke da karamin baki da kuma fararen idanuwa ya ce.
鈥淲ai ku ba ku gajiya da yin wannan abun kullum?鈥�
Kallonsa tai.
鈥淜a taba ganin mutum ya gaji da ibadarsa? Wannan sallah da kake ganin duk musulmi kwarai ba ya yarda lokacinta ya fita be yi ta ba, hakan yasa ka ga ina kwatantan lokacin ta sai na yi, yin ta tana sakarwa mutun da natsuwa da kwanciyar hankali kuma yana kara kusantar da bawa ga ubangijinsa, sannan ibada ce da ake bawa mutun lada mai yawa a lokacin da yayi ta鈥�
Yayi murmushi ba dan ya gane wani bangare na bayaninta ba. Shiru ne ya biyo baya kamin ta kalleshi ta ce.
鈥淭un da na zo garin nan ina kokari na koyawa kaina zama da mutanen cikinta da yin rayuwata irin na mutanen garin nan amman na kasa, ina ta kokari na cire Iya a raina amman na kasa, har so nai na yi ma kaina alkawarin ba zan taba tambayar inda take ba, ashe ba zan iya ba saboda soyayyar uwa ta fi gaban wasa, komai zata bata maka rai wata rana sai ka ji kana bukatarta a kusa da kai鈥�
Wasim ya yi shiru yana kallonta sai hawaye take.
鈥淏e zama lallai ki yi rayuwa tare da mu ba, zan tsaya miki ki samu irin rayuwar da kike so a lokacin da kike so, ko da kuwa kasar nan za ki bari gaba daya鈥�
Kallonsa ta sake yi.
鈥淏ana son wani ya sake aikata wani kuskuren saboda da ni, ka fada min ina Iya take?鈥�
Mikewa yai tsaye yana kokarin kawar da maganarta ta biyu.
鈥淏a zan yarda na sake aikata wani kuskuren ba, dukan abun da zan aikata a yanzu Zabin Raina ne kuma ya zama dole ni ma a ba ni damar rayuwa kamar kowa鈥�
Yana kawai nan ya fara tafiya ba tare da ya bata amsar tambayart ta biyu ba, binsa tai da kallo zuciyarta na hararo mata abun da take jin kamar ba ta shirya masa a yanzu ba.
FADIME POV.
Duk Yadda Shattima ya so ta sake ranta ta koma rayuwa kamar da, a duk lokacin da tunarabuwarta da Wasim maganar da yai mata cewar ba zai sake dawowa ba, idan ta tuna kalmar sai ta ji kamar zata mutu, gaba daya ko abincin kirki bata iya ci, har sai da Shattima ya kebe da ita a wani karamin falon Ammy ya saka gaba da rarrashi da komai sannan ta ci kadan, ko nama domin kazar da ya saka aka soya mata na musamman bata wani ci ba, a daren ranar ma sai da yai mata karatu kamar jiya, sannan tai bachi shi kuma ya tsareta da idonsa yana ta kallonta sai jin yake kamar ya dauke ta ya bude cikinsa ya saka a ciki ya rufe. Washe gari ta farka da wuri saboda tun a daren da zata kwanta Shattima yayi mata albishir da maganar zuwa gida Katsina. Ba laifi ta dan sake saboda tana marmarin ganin iyayenta, a dinning ma da aka kira a karya ta dan ci abinci da yawa, tana ta daukin cin abinci a dinning kasancewar jiya a dakin Nana aka kai mata komai a yau kuma sai Ammy ta aika aka kirata ta fito aka karya tare da Nana da Mama Fulani, daman Aliyu da Muhseen tun ranar da su kai gaisuwa suka juya a mota suka koma Abuja.
鈥淔ulani a saka mata ido, Shattima ya ce bata cin abinci鈥�
Ammy ta fada tana murmushi domin ya jadadda mata cewar ta kula da abinci Fadime baya son ta tafi gida da yunwa shi kuma ba zai samu shigowa gidan ba sai da suna kusan tafiya. A duk lokacin da Ammy ta kira Mama Fulani sai Fadime ta amsa tana ganin kamar da ita ake domin ita ma ta saba a gidan Inna da Bappa suna kiranta da Fulani. Shattima be kira Bappa ya fada masa halin da ake ciki na Fadime ba, shi ma kuma be kira wayarsa ya tambaye shi ba har yau. Ammy da kanta ta shigar da Fadime bangaren Mai Martaba suka gaisa, sannan yai mata goma ta arziki bayan ya tabbatar mata cewar tare da Baba Waziri zata je kuma idan zun tafi Katsina za su sauka a masarautar Katsina ne a hada tawagar da za su mata rakiya har gida, saboda ta jaddadawa Ammy abun da take tsoron Bappa yai mata wato duka ko ma ya koreta gaba daya, ita kuma Ammy tana ganin ko da ba zai mata komai ba ta cancanci karramawa mai girma daga gurinsu.
Cikin wani irin farinciki marar misaltuwa ta fito bangaren Mai Martaba, ba ta sha wahala gurin gane hanyar dawowa ba ta hanyar kwaliyar da aka kawata corridor da zai sada mutum da bangaren Mai Martaba da akai, ta cikin gidan matansa bayan wacan komar mai gate nata na musamman da baki suke zuwa ta can, ga kuma fadarsa a can gefe daya.
Ko da ta shigo falon sai ta samu Shattima shi kadai zaune rike da cup din ruwan sanyi, sabar murna da farinciki ya saka ta manta da ko shi waye da kuma inda take ta soma aro kadan daga halinta na baya tana yafawa.
鈥淵aro ya...鈥�
Sai kuma tai saurin rufe baki tana kallonsa, sai ya bude mata ido ya watsa mata ruwan hannunsa.
鈥淵arinya yarinya... Mai Martaba yayi mata kyau鈥�
Kyalkyalewa tai da dariya kamar ba ita ba, shi kansa be san lokacin da murmushi ya bayyana a kumatunsa, murmushin da ya bayyana fararen hakoransa saboda farincikin da ya gani a fuskarta.
鈥淜o ba haka ba ne?鈥�
鈥淗aka ne鈥�
Ta fada tana dariya, sai ya mika hannunsa baya ya dauko sabuwar waya cikin kwali ya mika mata.
鈥淕a waya na siya miki, kin ga ba zan yi kewarki sosai ba, sai na rika kiranki da ita鈥�
Hannu biyu tana ta karba tana kara fito da ido waje tsabar mamaki.
鈥淣i ni Fadime? Waya? Wanda ake shafe shafe touching ko?鈥�
鈥淵eah Pretty鈥�
Sai ta zauna gabansa cikin wani irin farinciki marar misaltuwa ta fara kokawar bude kwalin wayar.
鈥淗andsome man, amman Wallahi ka biyani ni ma na shigo gari, amman boye ta zan yi ba zan bari Bappa ya gani ba鈥�
鈥淏a za ki daina halinki ba ko?鈥�
Sai tai masa gwalo kadan.
鈥淲asa na ke zan nuna masa, sai na ce amman kar ya karbe min ko? Zaka kira ni kuma?鈥�
鈥淢e zai hana ba dole na ji muryar Fatee na ba鈥�
Ta yi dariya sannan ta mika masa.
鈥淜unna min ka nuna min yadda zan yi tabe tabe鈥�
Yayi murmushi.
鈥淭abe tabe dai鈥�
鈥淭o shafe shafe鈥�
Ya sake yin murmushi.
鈥淭o touching touching鈥�
Ta fada da dariya, karba yai ya kunna wayar ya ciro line mtn ya saka mata a wayar sannan ya soma nuna mata inda zata taba, be ko gama ba ta ce.
鈥淣a ma gane komai har wanda baka nuna min ba, ba ni wayar鈥�
A garin karba wayar ta fashi ta tsaga daga kasa, wani irin turo baki gaba Fadime tai.
鈥淜a gani ko? Daman ba da zuciya daya ka ba ni ba鈥�
Wannan karon dariya yai, daman ana bada abu fiye da zuciya daya.
鈥淒a zuciya nawa na baki?鈥�
鈥淏iyu mana, dayar tana cewa a bawa ni dayar na hanawa鈥�
Camera ta shiga daman ta fi kwarewa can a lokacin da yake nuna mata, daukarsa ta rika yi hoto, shi dai be ce mata komai ba har tai mai isarta ta gama ta shiga daukar falon da hotunan Ammy da suke lake falo, duk abun da take idonsa na kanta wani irin abu yake ji kamar ya kamata ya rumgume.
鈥淜i je ki shirya karfe daya za ku tafi鈥�
鈥淏a da kai ba?鈥�
Ya daga mata kai alamar eh. Sai ta bata fuska
鈥淢iyasa?鈥�
Kafadunsa ya daga mata alamar shi ma be sani ba, domin ya so ya rakata sai dai yana jin kamar indan suka tafi tare ya baro ta zai fi shiga damuwa fiye da yai mata sallama a nan, duk da yana da tabbacin bayan tafiyarsa zata sake dawowa rayuwarsa. Dawowa tai kusa da shi ta zauna tana ta kallonsa, sai kuma ta ji kewarsa ta kama ta.
鈥淣i daman ba ni da sa'a sai na sabu da mutum sai ya tafi ya bar ni鈥�
鈥淎mman ai ke zaki tafi ki bar ni, ni da kuka ba ke ba鈥�
Ya fada da fuskar zolaya.
鈥淒an Allah ka rika kirana kullum ka ji鈥�
鈥淒olena ai Pretty鈥�
Bata yarda ba da shi za a je ba har sai da lokacin tafiyar yai, ta ga Shattima ya kirata daman ya bata agogon da ya taba bata lokacin da za su yi wacan lafiyar da su Bappa, a nan ta saka masa kuka tana jin kewarsa.
鈥淣o no ki daina damuwa zan kawo miki ziyara ai?鈥�
鈥淒a gaske?鈥�
鈥淚 promise鈥�
Da kasa ya kama saka hannunsa ya share mata hawayena.
鈥淒an Allah ka zo ka ji?鈥�
鈥淜in fara missing dina kenan鈥�
鈥淜uma kullun ka kira ni karka gaji鈥�
Ya daga mata kai tana jin kamar ya hana ta zuwa, da farko be yi niyar rakata airport ba sai dai ganin yadda take kuka yasa ya rakata airport din, da katuwar jakar kayan da ya saka ka siya mata masu tsada. Motarsa dabam ya shiga ita kuma ta shiga motar su Baba Waziri da mutanen biyu da suke tare da shi, suna isa airport ko minti talatin ba su ba jirginsu ya daga zuwa Katsina. Kusan duk wanda be saba shiga Jirgi ba zaka tarar yana jin tsoro a shigarsa ta farko da ta biyu har zuwa lokacin da zai saba, amman ban da Fadime ko wa can zuwan da su kai da Mama Fulani bata wani tsorata ba, kawai saboda tana cikin damuwa ne yasa bata maida hankali sosai a kai tafiyar ba, yanzu kan har dadi take ji a zaunar da ita kusa da window jirgin tana hangen waje, ta soma daukar hoto da wayarta har mutanen da ke cikin jirgin dauka take. Suna sauka Katsina zuciyarta ta fara kewar Shattima ta dayan bangaren kuma tana mata zillon na son ganin Bappa da Innarta. Ko da suka sauka airport din Motocin Mai Martaba na harabar da ake aje mota suna jiransu, a Front seat ta zauna mutumen da ke tare da Baba Waziri ya shiga gidan baya, cikin motar ma tana ta daukar reban da kanta. Masarautar Katsina suka sauka akai musu tarba ta ta musamman, sai da suka ci suka sha wannan aka hada su da wata tawagar da zata yi musu rakiya har garin Bandalo. Kamin a isa garin Fadime har ta ayyana yadda zata rika kallon kowa, domin tana jin kamar ta fi kowa dace saboda ta je Masarautar Garuk, da ta Yola haka ma Katsina. Tun daga shigowar manyan motocin guda hudu mutanen garin suka fara kallo suna mamaki wane babban mutum ne ya shigo garin, ita tai ta kwantance hanyar da za abi a isa gidansu a lokacin da ta suka shigo garin Bandalo. Kamar taron kasuwa haka kaiwa kofar gidan Bappa da fifi ana kallon manyan mutane da mamakin su waye a ciki, wasu dai sai fadin suke Fadime ta janyo musu da mata rigimar wasu kuma na fadi daga Katsina aka aiko a tafi da Bappa kowa dai da abunda yake fada, dogaran dake tare da Baba Waziri ne suka fita suka isa bakin kofar gidan Bappa suna masa sallama irin wanda dogarai suke yi a kofar gidan talaka. Inna ce ta fito jiki na rawa tana amsawa domin Bappa yana gurin sana'arsa a lokacin, daman abu ne mai wahala ka tararda shi a gida irin wannan lokacin. Fadime na ganin Inna ta yi saurin bude motar ta fito, Inna ma tsaye tai tana kallonta sai hankalinta ya bar gurin dogarawan da take musu bayanin cewar Bappa ba ya gida.
鈥淚nna鈥�
Fadime ta fada tana fashewa da kuka, sai Inna ta rufe baki jikinta na rawa kamar zata fadi a gurin, da gudu Fadime ta je ta rumgume ta, jamar'ar gari suka hau leke kowa na mamaki, kuka sosai Inna da Fadime suka yi, sannan ta rika hannu Fadime suka shiga gida, makota da yan uwa kusa ne suka fara shigowa suna mata barka, wani makocinsu ne ya hau babur dinsa ya isa har inda Bappa yake ya sanar masa dawowar Fadime da kuma motacin da aka shigo garin da su tare da ita, take Bappa ya rufe shagonsa ya hau Babur din mutanen suka kamo hanyar dawowa gida da tunani kala kala a ransa, shi dai tsoro ya fi kama shi sama a lokacin da yai arba da manyan motocin, fargabarsa daya kar ace wata jamgwal din ce Fadime ta sake janyo musu. Sai a lokacin ne Baba Waziri ya fito daga motar bayan an gabatar masa da Bappa a matsayin mahaifin Fadime, Bappa faduwa yai kasa yana kwasar gaisuwa jikinsa sai rawa yake, ko mutumen birni ya yaji a gaban sarki balle na kauye, da sauri fadawan da suke tare da Waziri suka zo suna gyara masa rigarsa suna masa kirari, gaisawa yai da Bappa sannan ya gabatar masa da kansa sannan ya isar masa da sakon Mai Martaba na kudi da kuma gaisuwa, daga bisani kuma ya gabatar masa da albishir din Shattima na gidanda ya siya masa a Kt, daya daga cikin mutanen da suke tare da Wazari ne suka kira Shattima yai magana da Bappa a waya sannan ya kara tabbatarsa masa da abun da Baba Waziri ya fada, kuma ya fada masa cewar idan ya kimtsa yai masa magana a waya zai turo Ra'ees ya dauke shi ya kai shi har inda gidan ya ke kuma ya hannanta masa komai, Bappa sai ya rasa bakin magana ko godiya sai kuka, yana ganin komai kamar a mafarki.
_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number聽 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
03/12/2021, 18:59 - 馃馃馃馃: *Khadeeja Candy*
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
Kusan duk wanda yake shakiki a masarautar kuma yake da alaka da Hajiya Babba ko Ammy da Mai Martaba ya jin abun da Hajiya Babba ta aikata, an fi jin nata sama da na Iya, domin ita take labarwa mutane abun da ta aikata da kanta, ga bakinta a juye gefe daya abun har ya fara tana kafarta da hannunta domin bata iya amfani da bangarenta na dama hagun ma sai ta dade tana tunani kamin ta iya mika hannu ta karbi abu ko ta rike, and when ever tana cin wani abu a bakinta ko da abinci ne sai ya zuba ta gafen bakinta ta zama kamar wata musaka, duk kalar juyin duniyar nan da akai mata bata gane Kausar ba, yar autarta ta manta da shafin rayuwar Kausar a cikin tata rayuwar, sai dai tai ta kallonta amman bata san wacece ita ba, gashi idan yanzu za ka fada mata abu anjima kadan ta manta sai an sake fada mata, amman bata mantawa da fadawa kowa labarin abun da ta aikata. Kusan asibiti uku Sirleem na canja mata yana ganin kamar za ta samu lafiya amman shiru. Hakan yasa danginta suka dauke ta aka maida cikin familynsu da niyar za a rika yi mata na hausa, hakan kuma be saka Sirleem ya saduda ba sai ya fara planing din fitar da ita waje. Hakan ya saka aka daga ranar da za a bikin mika masa ragamar kamfaninsa da kuma kananan kamfanonan da suke karkashinsa har zuwa karshen sabon watan saboda halin da yake ciki na tashin hankalin mahaifiyarsa da kuma kanwarsa Jurry, ciwon kai ya sakata gaba duk ta bi ta rame ko abu ta tauna a bakinta sai ta ji kan kamar zai rabe biyu, ruwa ne kawai zata sha ta samu salama amman bayansu duk abun da ta ci sai ta ji kamar zata mutu tsabar ciwon kai, duk asibitin da aka kaita cewa suke ba su ga komai ba, wasu kuma su ce tana shaye shaye ne ko ta taba yi shine abun ya dawo mata yana son taba mata kwakwalwa, alhalin bata taba shaye shaye ba, sai dai mutanen da suka ji abunda Hajiya Babba take fada ya san tare suka shirya sherin suna gane cewar hakkin mahaifinta ne da kuma abubuwan da suka kulla ne ya dawo kansu, daman can idan kai sheri abun ya dawo maka zai maka illa fiye da wanda akai wa sherin, musamman abun da ya shafi aljanu.
Two days after an maida Hajiya Babba gurin Familynta da suke nan Yola Karima da Kausar suka koma can domin kula da mahaifiyarsu yadda ya dace kasancewar bata da wanda ya fisu a yanzu domin mostly wadanda suke uwa daya uba daya duk sun rasu, sai dangin yaya da kane ko kuma yayansu, and when ever abu ya same mutun mai nauyi irin wannan ba kowa zai Iya jinyarka ba sai na ka, su kansu zama gidan ba zai musu dadi ba saboda abun da Hajiya Babba ta aikata duk da kasancewar babu mai tsangwamarsu sai dai su suna tsarguwa a cikin gidan sun saka sakewa, musamman Kausar da take ganin gidan ya mata empty saboda babu Hajiya Babba a ciki.
聽 Sati daya da maida Hajiya Babba Family house aka sallamo Jurry daga asibiti ba dan ta ji sauki ba domin babu abun da ya hausa, daman can babu jikin balle yanzu da ciwo yake ta mata dariya, sai ta koma kamar wata ce mai cutar kanjamau, daga asibitin kai tsaye aka wuce da ita family house na su, a ranar ne Sirleem ya shigo masarautar domin rabonsa da masarautar tun a lokacin da aka kai Hajiya Babba asibiti, bamgaren Ammy yai parking motarsa ya fito a matse ya nufi kofar da zata sada shi da cikin falonta, kamar wani bako haka ya shiga bangarenta, a da idan ya shiga kai tsaye yake wucewa dakinta saboda yana daukar kansa kamar dan gidan saboda Ammy bata tana nuna masa banbanci ba ko kadan, sai dai a yau sai ya samu kansa da kunyar shiga dakin nata, ba dan komai ba sai dan abun da mahaifiyarsu ta aikata, kusan Kausar da Karima da suke cikin hankalinsu ma duk suna cikin damuwa balle kuma da yake yayansu, a falo ya zauna har sai da Jekadiya tai masa sannan ya shiga dakin da sallama. Ammy dake zaune rike da cup ta amsa mata tare da aje cup din kasa.
鈥淪irleem ya ka zo mana da bakon abu haka? Daman can ka saba idan zaka shigo inda na ke sai an maka iso ne?鈥�
Ammy ta fada da muryar da ke karantarda mai saurarenta wato Sirleem cewar ranta a bace da abun da yai. Kasa dago kai ya kalleta kana kallonsa kasan yana cikin matsala da damuwa kala kala.
鈥淎gafarce ni Ammy鈥�
鈥淣a maka uzuri na yau kadai amman karka sake min haka, akwai abinci a dinning鈥�
Ammy ta fadi hakan ba da dan ta san yana jin yunwa ba ko akasin haka sai dan sanin cewa Hajiya bata masarautar a yanzu, bayan kuma ta san most zamansa a masarautar ne tare da mahaifiyarsa kusan cikin masarautar yake gudanar da rayuwarsa gaba daya.
鈥淣o na gode Ammy, daman magana na zo mu yi, kuma na roki wata alfarma a gurinki鈥�
Sirleem ya fada murya can kasan makoshi, har lokacin yana jin kunyar ya dago idonsa ya kalli Ammy. Ammy kuma sai ta gyara zamanta tana fuskantarsa domin alamunsa sun nuna mata maganar da yake son mata mai muhimmanci ce.
鈥淚na saurarenka鈥�
Ajiyar zuciya ya sauke a hankali sannan ya dan dago kadan yana matsar hannunsa na hagu a cikin na dama tare da hade yawun bakinsa.
鈥淎mmy... Na san kin ji komai kuma kij san komai a yanzu, kuma na san abun da Hajiya da Jurry su ka aikata ba abu ne mai kyau ba, kuma na san irin zafin da kike ji, amman hakan ba zai hana ni roka musu gafararki ba, dan Allah Ammy ki yafewa Hajiya abun da tai miki, kuma ina rokon ki ki roki Mai Martaba shi ma ya yafe mata, ita da juri, ba dan komai ba sai dan su samu sassauci a nan duniya kuma su tashi kiyama ba tare da hakkinku ba, Wallahi har ga Allah Hajiya ko wani be taba labarta mana wani abu ba ni da Kausar da Karima, na mu san komai ba kuma ina fatar laifin Hajiya ba zai yafe su ba...鈥澛�
Yana cikin maganar idon Ammy ya cika da hawaye.
鈥淢adallah da da kamar kai Sirleem, hakika Allah yayi yana fitar da mai kyau daga marar kyau, kuma yana fitar da rayeyye daga matacce, hakika Hajiya ta yi sa'ar samun da kamar kai, Allah ya maka albarka鈥�
Ta yi shiru tare da sauke ajiyar zuciya sannan ta cigaba.
鈥淜o kadan ban taba rikon Hajiya da wani abu a raina ba, duk da an san kishi gaskiya ne, amman a tunanina yadda muka girma a haka muna gina rayuwa da yaya komai ya wuce, sai dai ka san zuciyar dan'adam kowa da irin tasa kuma, hakika abun ya ba ni mamaki kuma ya tsorata ni, kuma zan yafewa Hajiya saboda saboda kai kadai Sirleem, ina son ka shaida Allah ma ya shaida na yafewa Hajiya abun da tai min na boye da na bayyane, ina kuma fatar saboda wannan abun da na yi Allah ma ya yafe min, kuma ina tabbatar maka cewar inshallahu Mai Martaba ma zai yafe musu, daman shi sarki ai baban kowa ne, koda baka da alaka da shi ka samu matsala a wani gurin ya sakan kira yayi sasanci balle kuma abun a gidansa? Na tabbatar zai yafe masu鈥�
Sirleem ya saka hannunsa ya taba idonsa dake cike da kwalla.
鈥淣a gode sosai Ammy Allah ya saka da alheri, kuma ina son ki roka min izininsa ina son na fitar da ita waje saboda nema mata lafiya鈥�
鈥淎a wannan kam hakkin Mai Martaba ne, nema mata lafiya cin ta da shan ta duk abubuwa da suka rataya a wuyansa saboda shi yake aurenta, hakki ne da Allah ya dora masa, kuma na san zai fitar da ita Inshallahu, duk abun da Mai Martaba zai yi a yanzu, yana cikin fushi ne da bacin rai dole mu masa uzuri, amman ina tabbatar maka idan ya sauko komai zai wuce鈥�
Sirleem ya kalleta da duba na girmamawa da ganin kima.
鈥淣a gode sosai Ammy, hakika da ko wace kishiyar uwa za ta zama kamar ke, da yayan kishiya da yawa ba su yi maraici ba鈥�
Ammy ya yi murmushi irin na su na manya.
鈥淪irleem kenan, kai ma ai da ce yayan kishiya za su zama kamar kai da ko wace kishiyar uwa ba tai bakinciki ba, baka taba ba nuna min banbanci tsakanina da Hajiya ba, Allah ya maka albarka鈥�
鈥淎min na gode, ni zan tafi a tashi lafiya鈥�
Ya fada sannan ya mike tsaye da zimmar lafiyar sai Ammy ta kira shi.
鈥淪irleem鈥�
鈥淣a'am鈥�
Ya amsa tare da juyowa ya, sai ta nuna masa gurin zama, komawa yai ya zauna.
鈥淜ar abun ya faru ya saka ka ji wani iri! Har yau har gobe har a bada mi mahaifiyarka ce, kuma Mai Martaba mahaifinka ne, bana son na ga wani canji ko rashin sakewa, kuma kar wannan abun ya saka wata matsala ko rashin jituwa ya shiga tsakaninka da Nana! Ka ji ko?鈥�
Ya dan dago kadan
鈥淎mmy, maganar gaskiya ni a yanzu ba ni da ra'ayin auren Nana, daman can ra'ayin na Hajiya ne ba nawa ba, kuma a halin da ake ciki a yanzu ina da aure...鈥�
Ammy ta masa wani kallo na ban mamaki tana gyara zamanta.
鈥淣a yi aure few days ago ba tare da kowa ya sani ba, kuma na yi hakan ne saboda na ceto rayuwar yarinyar da na aura duk da na san Hajiya ba ta son ta...鈥�
鈥淏an gane wannan maganar taka ba Sirleem ka yi aure kamar yaya? Kai kake ka haifi kanka balle kai aure ba tare da sanin mu ba? Hajiya ma bata sani ba kenan balle dangin mahaifinki wane irin aure ne wannan?鈥�
Sosai Ammy ta rufe shi da fada, domin hakan da yai ba karamin bata mata rai yai ba, tana masa fada ne a matsayinta na babba kuma mahaifiyarta wanda ko da ace Shattima ne ya aikata haka irin fadan da zata masa kenan.
鈥淎min aikin gafara Ammy, na san ban yi daidai ba, amman ba ni da yadda zan yi ne saboda....鈥�
Tsinta tsinta ya labartawa Ammy halin da Falmata take ciki da kuma yadda akai aure har ma da yadda Hajiya ta san komai.
鈥淏a dan aure yana da girma da kima kuma sunna ce mai karfi ba, da sai na saka ka saki yarinyar ba dan komai ba sai dan ka san cewa abun da ka aikata laifi ne babba, amman ba zan yi hakan ba saboda rayuwarka da tata, kuma abun da kai abu ne mai kyau sai dai ka yi kuskure babba gurin aikata hakan鈥�
Sirleem yayi shiru yana sauraren Ammy dake nuna masa bacin ranta.
鈥淏angaren mahaifinka ka bar mana wannan mu za mu sanar da su, saboda kar abun yai maka yawa, kai kuma ka je kai ta neman yafiyar Hajiya, saboda ba a son bacin rai mahaifiya, Allah ya baka ikon rike matarka da amana kuma ya hada kanku鈥�
鈥淎min Ammy na gode sosai, Allah ya faranta ranki鈥�
鈥淚dan ka gama boyun sai ka kawo mana ita mu gani, hakika yi dacen mata mai hakuri da tarbiya ga karatun addini na yaba da yarinyar sosai鈥�
鈥淚nshallahu Ammy鈥�
Ya fada sannan ya dan risina mata alamar girmamawa ya mike tsaye ya fice yana mata a tashi lafiya. Sai da ya fito zai shiga motar ya ji wani iri b dan komai ba sai dan tunawa da ada ne sai dai ya nufi bangaren mahaifiyarsa, amman a yau kam sai dai ya bar gidan zuwa na sa gidan..
Cikin damuwa ya isa gidansa, ya dade a motarsa kamin ya fito ya nufi kofar falon, da key din hannunsa yai amfani ya bude kofar falon ya saka kafarsa kamar wani marar lafiya kana ganinsa kasan yana cikin damuwa, kicin ya fara lekawa a zatonta Falmata na ciki, ganin bata nan yasa ya nufi upstairs kai tsaye, dakinta ya fara turawa ya shiga sai ya same ta tsaye tana duba rigar jikinta da alama wanka ta fito take shiryawa cikin rigar da skirt din yan kanti. Tana dagowa sai ta hangeshi ta cikin nadurbi yana takowa zuwa inda take, juyowa tai tana kallonsa.
鈥淪annu da zuwa鈥�
Be amsa mata ba ya sakar mata murmushi.
鈥淪hiryawa kika?鈥�
鈥淓h鈥�
鈥淛uya na saka miki zip鈥�
Ta juya kamar yadda ya bukata, amaimakon ya karasa saka mata zip din da ta fara sakawa sai ya zoke shi kasa ya saka hannyensa yana shafa bayanta kamin ya ganganra da su zuwa ya cika hannayen nasa da kirjinta ya lumshe ido ya kai bakinsa ya sumbanci wuyanta, sai ya ji kamar an yaye masa damuwarsa gaba daya a duniyar nan.
鈥淚 love you...鈥�
Ya furta mata murya can kasa kamar mai rada. Shiruuuuu tai tana sauraren yadda ta aiki da kirjinta idonta a cikin na shi suna kallon juna ta madubin da ke gabansu. Wani irin bugun kofa da karar bell suka ji lokaci daya, ba kara ta hankali ba, zare hannunsa yai daga jikinta yana motsar lips dinsa, sannan ya juya ya fita, sai ta maida zip dinta ta biyo bayansa ko da ta sauko har ya kai gurin kofar ya bude.
鈥淢ansura... Me kike yi a nan?鈥�
鈥淒ole ka ce me na ke yi a nan tun da ka yi aure macuci mayaudari鈥�
Ta fada cikin kuka sannan ta kutsa ta shigo cikin falon ta kalli Falmata dake tsaye gefen kujera.
鈥淎i daman na sani, wannan yarinyar ko? Wallahi ka ja mata matsifa kuma ka ja kanka, Wallahi yau har Hajiya sai ta ji maganar nan, kuma wallahi ba zan kyale ta ba鈥�
Falmata ta yi baya baya cikin tsoro idonta na cika da hawaye, Mansura kuma sai yin cikinta take kamar zata riko ta ta doketa.
鈥淪hiiiiiiiiiiiii鈥�
Sirleem ya fadawa Falmata ganin tana son yin kuka. Sannan ya kalli Mansura.
鈥淛i yadda kika tsoratata, miyasa ba ki yin komai cikin natsuwa ne Mansura鈥�
Mansura ta nuna kanta sannan ta nuna Falmata.
鈥淪aboda wannan shegiyar yarinyar zaka fada min haka?鈥�
鈥淜ar bakinki ya sake furta mata irin wannan kalmar, ba zan lamunta ba get out of my house鈥�
Sirleem ya fada a fusace sannan ya matsa kusa da Falmata ya ja matarsa ya rumgume.
鈥淣i ni ni ka yi kuskure Sirleem, sai na illataka na illata matarka mark my word鈥�
鈥淶a ki maimaita wannan maganar a kotu, kuma duk abun da ya samu matata ke ce鈥�
Tafi tai tana dariya.
鈥淓yyyy heyyyy On铆d脿r煤d脿p峄嵦€, ap岷固€y矛nd脿, atannij岷�, daman hausawa ba su iya komai ba sai cin amana, kuma Wallahi i swear to God sai ka san ka taba Yoruba, j岷� itiju, oleshiiiiii oooooooo鈥�
Ta fada cikin daga murya tana masa ihu, ya kyaleta ne saboda ba ya fada da mata a rayuwarsa balle kuma ita da ya san tana cikin jin haushi.
鈥淔ita ki bar min gida ko na saka a wulakanta ki yanzu nan鈥�
鈥淶an fita ba gida ba ne, zan fita ku kuma zai gagareku zama tun da kuka taba Yoruba kuma yarinyar sai da ya gama cin duwawuya tukuna ya auro ki..... Heeeeeee鈥�
Ta murguda ma Falmata mazaunanta cikin haushi sannan ta nufi kofar falon ta bude ta da karfi ta buga kofar sannan ta fice. Sakin Falmata yai ya karata har gate sannan ya gargadi mai gadin cewar kar ya sake bari ta shigo masa gida, ko da ya dawo cikin falon ya samu Falmata zaune tana kallon kofar cikin tsoro, domin ita dai bata taba shiga wani abu tashin hankali akan namiji ba sai yanzu.
鈥淭a tafi?鈥�
Yayi murmushi yana zaunawa kusa da ita.
鈥淏a dole ta tafi ba tun da ba gidanta ba ne, duk wannan iskanci da take tana yi saboda tana ganin kamar ba zan iya mata komai ba, amman zan yi magana da lauyana, za a mana tsakani da ita, domin ba zan yarda tai miki wani abun ba, ke kuma sai ki dage da addu'a鈥�
鈥淒aman bana wasa da addu'a, kuma bana jin wani abu nata zai same ta indai na tsafi ne, ni da Umma take ba ni magani da rubutu na sha, amman addu'ar da nake bata bar komai na ta yayi aiki a kaina ba, na yarda da Allah Sirleem babu abun da zai same ni鈥�
Murmushi yai yana kallon kyakyawar fuskarta.
鈥淐ome here鈥�
Ya jata jikinsa ya rumgume tsantsan kamar za a kwace masa ita.
0 comments:
Post a Comment