Bata kara jinjina Lamarin ba sai da taji da zasu tafi Ya Jafar na Fadin su Anty Shamsiya zasu zo su wuni Zasu zo kawo su yima Ya D'anmalam barka da Dawowa bazata iya Tuna Rabonsu da gidan ba Mallam baya barinsu suna Barin matansu suna zuwa sai da wani Dalili mai karfi ammh sai gashi yanzu zasu zo Anty Shamsiyan Tsohon ciki gareta Haihuwa ko yau ko Gobe,Anty Fadilan ne keda karamin Ciki Sannan gidansu Daya Tare sukayi Gininsu.
Amina na zaune a wajen anata Hira tayi kamar bata awajen Tsaki take ja acikin Ranta Har ga Allah tana so taga wannan Ya D'anmalam din nan Duk da Tasanshi ammh ayanzu bazata iya Nuna sa ba ko ta Tuna da Kamaninsa ba.
Sanin da tayimai Tana yarinya ne Lokacin Jidalinta ne agabanta da kuma ta fara girma in yazo har ya koma basa Haduwa sai dai tana jin Labarin zuwan nasa,Wannan karon Taji tana son ta gansa wanda har Aba a Fuskarsa yana Nuna Farincikinsa.
Ba gidansu kadai ba Har chan gidan Baba Mallam,Dazu da Rana hanne tazo ta jata sujeta tayasu aikin Sinasir da Waina,Saboda Ya Danmallam yana so Amina tayi kwanciyarta taki zuwa Hanne Tagaji tatafiyarta ko ajikinta Tasan zuwa gobe zasu koma Daidai.
Washegari da Safe Amina ke da Sharan Tsakar gida Hamida kuma Wanke wanke tana fa Sane tana Idar da Sallar asuba ta koma barci ba wanda ya Damu sanin ita ba Karatun asuba take yi ba,Su Ya Zeenatu suna Idar da karatunsu suka fara shirin makaranta Ya Zulaiha ke kitchen tana Hada abun kari,Yau basu da Jarabawa suna gida.
Hamida tana gama karantunta ta fita Waje ta fara Hada kayan wanke wanke zuwa wajen Famfo Mamanmu ta Fito Daga Dakin Aba da Hijabi da Carbi a Hannunta Da Sauri Hamida ta gaisheta ta amsa tana Fadin"Bake keda Shara ba Daman..?
Hamida tace"Amina ce ke da Wanke wanke..Jiya tace nayi wanke wanken Ita zatayi Sharan..!
Mamanmu kai kawai ta kada ta wuce Kitchen wajen Zulaiha.
Ya Zeenatu ta fito Cikin Shirin makaranta tsakar gidan ta kallah tana Fadin"Wake da shara ne..?hala Amina ce..?
Hamida na Duke tace"Eh itace..!
Karamin Tsaki taja tana Fadin"Indai Amina ce..Ba"ajin kowa Ranar aikinsa sai ita..!
Tafada Lokaci daya tana komawa Cikin Dakin Amina tayi Daidai tana barci taji An Daga mata Duka abaya Da Sauri ta Zabura tana Fadin"Kan Uba..Wani dan...!
Ta kasa karisawa ganin ya Zeenatu tsaye tana kallonta Lokaci Daya da Hararanta Baki ta Tura kafin ta wani Juya ido cikin kunkuni tace"To wai don Allah me nayi..?
Ya Zeenatu tace"Bansani ba..Nasha Zaki karisa Ashariyan da kika fara ne..!
Amina tawani Tona baki tana kunkuni Tana Fadin"To haka kurum..Ni..!
Zeenatu ta Make bakin Amina da yasa tayi Shuru cikin Bacin rai tace"Kinsan Allah? Da Safan nan zan Dirji bakin ki bana son Rashin kunya..!
Amina Bakinta ta Dafe tana Dubawa taga Danshi Cikin Zare ido tace"Jar uba..Kan bala balagagge..!
Ya Zeenatu tace"Ko kan uban Balan ne...Malama ki tashi kije kiyi mana Sharan Tsarkan gida waje duk datti kin zo kin kwanta kina barci kuma kinsan aikin ki ne..!
Amina kamar tayi kuka bakinta na mata Zugi tace"To ni nace bazan yi bane..!
Ya Zeenatu da har ta juya ta dawo tana Fadin"Me kika ce..?
Amina tace"Toh..nace..!
Ya Zeenatu ta juya tana Kyafci Lokaci Daya tana Fadin"Da kin maimaita da kin sani..!
Wajen gadonta taje ta Zauna tana kokarin saka Safa,Amina na zaune sai Hararanta Take tana kunkuni Lokaci Daya tana Fadin"Haka kurum..Allah ya isa na..ban yi miki komai ba..Allah ya sakamin Wuta balbal Yasin..!
Ya zeenatu na jinta bata yi mgana ba Sanun Halin Amina ko za"a Mutu bakinta bazai mutu ba.
Amina kin fitowa tayi sai da Ya zeenatu ta kara mata mgana ta Zare mata ido tana Fadin"To wai bana ce toh ba..ba cewa fa nayi bazam yi ba..!
Tana jin haka taje ta Fadama Aba yana Zaune ne yana Duba Tarkadun Lissafin kwan kajin da aka Fita dashi Daga gidan gona ya Dago kai yana kallon Zeenatu kafin yace"Kiramin Aminar..!
Tana daga kwancen Zeenatu ta Dago Labule tana Fadin"Ki tashi kije Aba na kiranki..in kin rainamu shi ai bazaki Rainasa ba..!
Amina ta rike baki afili ta Furta"Munafuki dai bai ji Dadi ba..!
Kara Dago Labule ya Zeenatu tayi tana Kallon Amina da Sauri ta mike tana Neman Hijabinta Lokaci Daya tana yar waka"Kan munafiki dai baya gashi..ko yayi sai ya sauke..!
Ya zeenatu tace"Dani kike Amina..?
Sai data saka Hijabinta Na Hadda kana tace"Nifa badake nake ba..Wakata kawai nake ba"aji na ambaci Suna ba Atoh..!
Tafada tana wucewa tana ta kunkuni Ya Zeenatu ta bita da Harara Domin in ta tsaya Biyema Amina sai ta makara.
Fuu kamar kububuwa ta fito sai Dakin Aba da sallama kamar Mutuniyar arziki ya amsa mata kafin ya bata izinin Shigowa.
Kanta na kasa ta shiga chan gefe ta Zauna Sannan ta dago kanta tana Fadin"Ina kwana Aba..!
Bai kalleta yana Rubutu Bisa Takarda yace"Lafiya..Ya akayi akace an saki aiki kikace bazaki yi ba..?
Amina ta yamutsa Fuska kafin tace"Nifa karya takemin Aba..nace zan yi fa..!
Sai Lokacin ya dago yana kallonta Cikin wani yanayi itama kallonsa take yi Cikin Daure Fuska yace"Zeenatun ke miki karya..?Sa"arki ce..?
Amina ta Tura baki kafin tace"Aba har fa Baki ta fasamin..Wannan ai Zalunci ne..!
Aba ya karkace kai yana Kallonta,Yana kara nazarinta Har yau bata Chanza ba Ganin zata ma batamai Lokaci yasa yace"Tashi kije kiyi aikin da aka saki. daga yau in na nakarajin ana Fada Dake kan aikin da kika san naki ne..sai naci Mutumcinki Sannan Gargadi na Karshe kada na kara jin kin kara kiran wani Dan"uwanki Azzalumi kina jina ko..!
Amina tayi kasake tana kallon Aba aranta tana ayyana yadda ba"a taba goyon bayanta Kullum itace bata da gaskiya ganin tayi shuru yasa yadan daga Murya yana Fadin"Kin ji ko baki ji ba. ?
Amina ta Tura baki kafin tace"Naji Aba..Ammh..!
Hannu ya Daga mata bai kalleta ba yace"Tashi ki bani waje....!
Dole ta mike sanin Halin Aba Tunda yace haka bai Bukatar kara jin mganarta kamar Amina ta Buga ita kadai haka ta fito kamar kububuwa Taje ta Dauki Tsitsiya ko Hijabin Jikinta bata Cire ba ta Fara waka da Karfi tana Fadin"Munafuki dai baya gashi..Ko yayi sai ya Sauke.!
Ba wanda bai jita ba Har Yaya Dake Daki Tana Shirya Jawaad kai kawai ta Kada aranta tana ma Amina Fatan Shiriya.
Ya Zeenatun ma tana jinta tayi mata Banza Mamanmu ce ta fito tana Fadin"Amina ki bar wakar nan..Ko kin manta Aba din ku na gida..?kina so yaji ya fito ya saba miki ne..,?
Amina ta Dago tana Fadin"Mamanmu bana son munafunci ne..Cewa nayi bazan yi sharan ba..?an wani je an Hadani da Aba yamin Fada..!
Mamanmu tace"Yi hakuri yi shararki..Kada ki kara tanka kowa zan ma Zeenatun mgana..!
Saboda Mamanmu yasa ta kama Bakunta ta Cigaba da Sharan,Har tazo wajen da Hamida ke tsunggune tana wanke wanke tayi ta yarfo mata Shara da Datti Hamida ranta ya baci ta Dago Tana kallonta Lokaci daya tana Fadin"Bana son Rashin mutumci Amina baki ganni bane..?ai sai kice na tashi ki share ko..!
Amina ta balla mata Harara kafin tace"Dayake baki da ido ne..Kada Allah yasa ki tashi ta kanki zan bi na wuce..!
Tasan zata aikata kuma abokin Jidali take nema yasa Ta tashi Tsam ta bata waje ta Share ammh duk da haka sai da bata mata wasu kwanukan sai da ta kara Dauraye Amina tana gama Sharan ta koma Daki tayi kwanciyarta tana ta kunkunin mgana Har su ya Zeena suka karya ita da Jawaad suka fita Idi na Jiransu da su Abida..
Hamida data ga Amina bata tashi ta yi Breakfast ba,i ta tayi mata mgana sai ta mata Banza ganin haka yasa ta karisa kusa da ita tana Fadin"Amina ki tashi ki karya..Mutuninki aka Soya Dankali da kwai..!
Amina ta Tsaki tana Fadin"Baza aci ba din..Ina ma Ruwanki dani Cikin ki ko Cikina..?
Hamida ta rike baki tana Fadin"Allah ya baki Hakuri..!
Amina tace"Ameen in da gaske kike..!
Ita dai Hamida ta fice zuwa Dakin Yaya ta bar ma Amina Dakin Mamanmu kuma tana Dakin Aba ta kaimai abun karyawa ya Zulaihat kuma ta shiga wanka adakin Mamanmu.
Amina tun tana kunkuni har barci ya Dauketa bata sani ba Bata Farka ba sai da taji Ihun Hanne asaman kanta Lokaci Daya tana Kiran sunanta"Amina..Amina tsshi..!
Amina ta Bude ido ta ga Hanne Saman kanta bakinta Har kunne Cikin Dariya ta rike Hannunta tana Fadin"Ki tashi Ya Danmallan sun dawo..Yanzu su ya Jafar da ya shamsu suka je Airport zasu Dauko su..!
Amina wani Kololon Takaichi ya zo mata wuya batasan Sadda ta Fizge hannunta ba tana fadin"Shine zaki zo ki tasheni ina barcina..?tsakanina Dake Hanne wlh sai Allah yamana Hisabi..!
Ta karishe Fada tana Sakin Tsaki kafin ta juya tana fadin"Ni ina ruwana da wani Dawowarsa..!
Hanne Jikinta yayi sanyi ta kalli Hamida Dake Tsaye da Sauri Hamidan tace"Kiyi Hakuri Hanne..!
Hanne ta mike batace komai tayi yake kawai kafin tace"Na tafi Hamida..Sai kin shigo..?ai zak zo musu sannu dazuwa ko..?
Hamida tace"Sosai ma zan shigo insha Allahu..!
Daga haka ta fice Amina na jinta tana Fadama su Mamanmu a waje tana jin Sanda Yaya ke fadin"maraba..Maraba..!
Tsaki ta kara ja aranta tace"Kamar wani Gold..?ita zata so taga wannan Mutumin nan..da harda Yaya da bata wani Shiga Sabgan mutane tana ji dashi..!
Bayan tafiyan Hanne Hamida ta kalli Amina Dake ta Zakuda Kafada Daga kwancen tana Fadin"Amina ammh kinsan baki kyauta ba ko..?Hanne fa kika ma haka..!
Amina na Daga kwancen ta Dago kanta kafin tace"To uwata..Hadiza ina jinki..?gayamin abunda nayi wanda ban kyauta ba..!
Tafada Lokaci Daya tana Mikewa Zaune kamar abun arziki.
Hamidatace"Koma me zaki ce..Gaskiya ne sai na Fadamiki baki da wacce tafini Amina..bai kamata kima Hanne haka ba kada ki mamta Hanne yadda take awajenki..Ko ni da muke gida Daya ban kai Hanne Daukan Jidalinki ba Amina Tana ta Murna tazo fadamiki Dan"uwanta ya Dawo kalli yadda kika gwasaleta alhalin batayi Fushi da abunda kika mata Jiya ba yau kuma ta dawo..Wlh ban taba ganin Hanne ta Damu da Halinki ba sau yau..kwallah sai da taru acikin Idonta..!
Amina tayi kasake tana jin Hamida ko ajikinta Ganin haka yasa Hamida ta Cigaba da Fadin"Kuma kada ki manta Ya D'anmallan d'an Hajiya da Baba Mallam ne ko domin yadda suke Kaunarki bazaki musu kara ba..?
Amina ta yamutsa Fuska kafin ta mike tana Fadin"Ke kikasan wannan..Sannan wai da gaske kike Hanne Fushi tayi..!
Hamida ta kalleta Cikin jin Haushi kafin tace"Watarana Amina.Zaki Tuna Damu har kinemu mu bamu kusa Dake ballatana mu gayamiki gaskiyan..!
Amina tayi tsaki ta wuce tana Fadin"Ai da nasan Fushi tayi..Da nasani na Dago na kalli Fuskar ta..Tabdijam waya ga kunu In hanne tayi Fushi..!
Ta Karishe Fada tana Dariya Hamida ta Bita da kallon Yaushe Amina zata Damu da wadanda suka Damu da ita ne..?
Abunda bata sani ba Bawai bata Damu bane A"a ita tana da Saurin Shanye abu,Tana ganin ai ba wani abu bane..Zasu shirya da Hanne tasu bata Baci Shiyasa bata Cika Damuwa ba don sun yi irin wannan ba Ta tabbata ko Kowa ya kyaleta Hamida da Hanne suna gefenta Har acikin Ranta ta basu matsayin dasu basu sani ba.
Kitchen taje ta karya abunta Sannan ta Fito ta isa Dakin Mamanmu bata Ciki tana Dakin Aba Amina ta rike Baki ganin Har 10 ta wuce ammh Aba bai Fita Lalle Ya Dan Malan na zuciyar kowa ta tabbata Saboda Dawowarsa ne Aba bai fita ba
Dakin Yaya ta Leka ta iske ya Zulahait na karatun textbook din Biology Lekawa tayi domin ita bata fiya shiga Dakin batace"Ya Zulahat yaya fa..?
Kanta na Duke bata Dago ba tace"Gata na goyata abaya na..!
Amina ta karkace baki tana Hararanta kafin ta yi kasa da Murya tana Fadin"Ta kusa aure..Ta kusa aure an kusa a bar mana gida..!
Tajita tana mgana yasa ta Dago suna Hada ido ta washe baki kafin tace"Ina kwana Yaya. !
Da karfi Saboda Yaya taji kuma tajin tana gyara kayanta ne Ta girgiza kai kawai chan kuma sai ta dan Murmusa Amina tayi wucewarta aranta tace nasan taji ita yayan nan kowa tana mai Dariya bandani Saboda ta Tsaneni..!
Afili ta Furta"Da ace Aba bai auro Mamanmu ba Al"quran wajen Hajiya zan koma ina zan iya..!
Zulaihat kam sai da ta Toshe kunnenta Amina Mtsalace wlh yarinyar nan kamar mai Almatsutsai
Dakinsu ta koma ta iske Hamida ta Shiga wanka gadonta ta Haye harda jan Zani tana wani Lumshe ido Hutu Dadi ita bataki ma akyaleta kada ta koma makarantar ba ina Laifi takai har Jss3 tafi wasu ma kuma ai ta samu na yaki da jahilci.
*******
Ya Shamsu ne ya fara shigowa Shashen Hajiya babba da wata Jaka ta matafiya irin ta yan Saudiya haka,Hajiya na cikin Dakinta Hanne da Ya Aisha afalon suna ganinsa suka Mike gabadayansu Cikin Murna Ya Aisha tace"Shamsu har sun iso..?
Yana ijiye Jakar nan Tsakiyar Falon yace"Eh suna Haraban gida..Ina Hajiya..,?
Hanne tace"Tana Dakinta..!
Juyawa yayi yana Fadin"Ya D'anmalam yace ku gyara Dakin ku akwai bakuwar da zaku sauke..!
Daga haka ya fice Hanne bata Tsaya ba ta Ruga Dakin Hajiya tana Kiran sunanta sun kusa cin karo Cikin Fada tace"Miye haka ke kullum baki abu Cikin Hankali..?
Tana Dariya ta makaleta tana Fadin"Hajiya su yaya sun iso..!
Kwace jikinta tayi tana Fadin"Shi ne me..?kika rikeni kamar zaki gadani..!
Ta fada tana kariso cikin Falon kafin ma tace wani abu Shamsu ya Sake shigowa da irin Jakar Dazu Ko kafin Hajiya ta samu bakin mgana taga ya Bada Hanya yana Fadin"Bismillah..!
Gabadaya Kofar suka Zubama Ido Hajiya tasan ba D'anmallam bane Domin shashen Malam yake fara isa in ya Dawo kasar kafin ya shigo wajenta sannan in Sakina ne kuma Shashen Uwarta take sauka sai Daga baya take zuwa ta gaisheta.
Bata gama wannan mamakin ba wata Farar balarabiya Jajir da ita kamar ka Taba jini ya fito ta bayyana agaban Shamsu Cikin Shigar Doguwar Abaya baka tayi Rolling din gyale asaman kanta irin yadda matan Larabawa sukeyi,kyakyawace sosai ko gasan kyau zata iya shiga kuma taci sannan Doguwa ce mai Jiki kadam Hannunta Dauke da wata karamar Jaka ta mata Hannanyenta sunsha Jan kunshi kwanin Sha"awa da Burgewa Tunda ta shigo Ta saki Fararan Hakoranta da suka kara Fito da kyanta Tana kallonsu Hajiya.
Suma ita suke kallo Cikin mamaki harta Hanne data saki baki da Hanci tana kallon Tsabar kyau yau datake jin Labari yau gashi ta ganin ma Idonta.
Ya shamsu ne ya Katsesu da Fara gaida Hajiya ta amsa tana Dan Boye mamakinta.
Da Sauri yace"Hajiya bakuwa ce..Ya D'anmallam yace na kawota Shashenki kafin ya shigo..,!
Hajiya bata nuna wani Damuwa ba ta Washe baki tana Fadin"Toto..Nifa nace bakin labarawa da Safen nan..Maraba maraba Sannu da zuwa..!
Tafada Cikin Sakewa Duk da batasan me Hajiyar ke fadaba Tunda batajin Hausa sai larabci ance Tabarman Fuska tafi tabarman zama yadda take ta mata Dariya yasa ta gane tana mata Lale ne.
Shamsu ta kalla daya ijiye jakar hannunsa inda ya Sauke Dayan Dazu tace"Shukran..!
Mirmishi yayi mata shima aransa yana Fadin ina Yaya Danmallan ya Samo Balarabiya mai kyau haka sai da bai tanka ba ya Fice Daga Falon.
Hajiya ta kalli SAROOD tana Fadin"Maraba lale..Kariso mana..!
Hanne ta saka Dariya tana Fadin"Hajiya wayace miki tana jin Hausa..?
Hajiya tace"Oh to..To ku da kuke yara yanzu kwakwalwar ku take ku mata mgana da labarci kuce tazo ta zauna ai batayi ta tsayuwa ba..!
Aisha ce taje ta kamo hannunta tana mata Sannu da zuwa Cikin Harshen Larabci batayi mamaki ba Sanin Daman Umar ya fada mata zataji dadin zama a Nigeria Domin agidansu akwai masu jin yarenta
Har kan Daya Daga Cikin kujerin Falon ta zaunar da ita sai dai bata Zauna ba ta Zame ta Zauna akasa Cafet kanta na kasa Umar ya fadamata Shashen Mahaifiyarsa za"a kaita Shiyasa kanta na kasa ta shiga gaida Hajiya da Harshenta Hajiya na jin Larabci tun abaya don ma Shekaru da kuma Rashin yinsa Lokaci zuwa Lokaci.
Cikin jin Dadi ta amsa mata da Tambayan Hanyan ta amsa da Alhamdulillah kanta na kasa Muryanta Dadi Cikin Harshenta.
Hajiya ta kalli su Aisha tana Fadin"Aisha ce mata ta tsshi a kasa..Ta zauna kan kujera..ke kuma Hanne kwashe kayan nan kikai Dakin ku..Ki kuma Shiga Kitchen ki Hado mata Ruwa da Lemo..!
Daga haka ta wuce zuwa Dakinta Aranta tana Tunanin to wacece wannan yarinyar da D'anmallam ya Taho da ita kuma kai Tsaye a bata Masauki a shashenta da wannan Tunanin ta karisa Dakinta bazatayi gaggawa ba koma me ke ciki tasan Malam ya sani Tunda tasan yaronta bazai Taba zuwa da wata garin nan batare da Izinin Malam din ba..!
Kowacce tayi abunda Hajiyar ta sakata Hanne ta kwashi kayan zuwa Ciki Aisha kuma tace mata ta Hau kujera sai taki Mirmishi Kawai tayi.
Kafin Lokaci an cika gabanta da Ruwa da kunun ayan da sukayi Jiya da Daddare.
Bata taba ko Daya ba tana gefe kanta na kasa tana wasa da adon Kwalliyar Dake Cikin Jakarta Hanne da Ya Aisha suna gefe suna kallonta kowacce aranta tana ayyana kyau kamar ita tayi kanta wannan Balarabiyar da Tambayan Ina Ya Danmlam ya samota..?
Hajiya tana Shiga Bedroom dinta Wayarta Dake kan gado na neman Dauki tana Dubawa taga D'anmalam ne,Da Sauri ta Dauka Tana Fadin"Danmallam kun iso Lafiya..!?
Dagachan Falon Baba Malam Baba Sa"idu na zaune akasa kusa da Baba Malam Dake kan kujera Cikin Farin Raawani suna mgana shi kuma yana Daga chan gefe kamar zai bar Falon kansa na kasa yana Shafa Sumar kansa da bata da yawa.
Cikin Tattausan Muryan da ban taba jiba wacce ta Chakule da Labarci Yasa bata fita saosai kamar yana Koyonta yace"Mun sauka lafiya Hajiya..!ya muka Sameku..?
Hajiya tace"Duka muna Lafiya..!
Sai kuma Shuru ya biyo baya Hajiya Bata Damu ba Sanin Halinsa ko Waya ya Kirata sai ya bata Lokaci kafin ya ce wani abu bayan sun gaisa.
Kamar ana Fizgan mganar Daga bakinsa yace"Hajiya kinga Bakuwa ko..?
Hajiya tace"Eh fa..Yanzu na Dawo Ciki Shamsu yace kai kace ya Kawota Shashena..!
Karkaace kai yayi kamar mace kafin yace"Eh Hajiya..Aisha na kusa ko Hannatu..!?
Hajiya tayi mirmishi tace"Suna Falo Tare da Bakuwar D'anmallam ko na fita na kirasu ne..?
Sai da yayi shuru jin bai yi mgana ba yasa tasan yana jin nauyin yace ta kai musu wayar ne yasa ta Nufi kofa tana Fadin"Kada ka damu..bari na fita na kai musu wayar..!
Da kamar yace ta barshi bari ya Kira Sarood din ammh Hajiya Har takai Falon ji kawai yayi tana Fadin"Lafiyanku kuka zauna kuka tasa Bakuwa agaba kuna kallo..?bana son Shanshanci..Ke Aisha karbi Waya yayanku na son mgana Dake..!
Tafada tana mika musu wayar ganin yadda suka wani tasa Bakuwa gaba suna kallon Dariya sukayi harda Hanne yana ji sanda tace"Wlh Hajiya tana da kyau baki gani ba..?
Hajiya ta tsaki kafin tace"Bangani ba..!
Daidao Sanda Aisha tamai Sallama Cikin Girmamawa ta gaisheshi ya amsa Lokaci Daya yana Fadin"Ke da Hannatu meyasa bakuje makaranta ba..?
Da Sauri tace"Yaya ai muna Jarabawa ne.kuma yau bamu dashi ni da Sadiya da Ikram duk muna gida Hanne kuma sun gama Jssce suna gida suma sai an koma Firstime..!
Kansa ya kara shafawa ya manta fa ko Dazu Shamsu ya fadamai haka da sukaje Dutse suka Daukosu Daga Filin Jirgi,Dayake ta Kano suka Sauka Daganan suka Hawo Jirgin Daya kawosu Dutse.
Cikin Muryansa mai Cike da Zati yace"Kunga bakuwa ko..?
Tace"Eh yaya..Mai kyau da ita wlh ya sunanta..!?
Dan Bakinsa ne ya Motsa kafin yace"Sarood..sunanta batajin Hausa ki rika mata Labarci yanzu dai me kuka bata..?
Kai Tsaye tace"Ruwa da abun sha..Muka fara bata yaya..,!
Kamar bazai yi mgana ba sai chan yace"Aisha ki kaita Dakin ku kice mata tayi wanka..Ta huta tukunnah kina jina..?
Da Sauri tace"To yaya..!
Kai Tsaye yace"Mika mata wayar na Fadamata..!
Ba musu ta mikamata tana Kallomta Tace"Yaya..!
Karba kwwai tayi ba Domin ta gane ba tana kara a kunne taji muryansa Nan da nan ta washe baki basu san me ya Fadamata ba suka ga ta mike Lokaci daya tana mika Aisha wayar Ita kuma tayi gaba sai gata tana Binta abaya Har Dakinsu Hanne ta Bisu da kallo kawai
Har Toilet din sai da Aisha ta nuna mata sannan ta Fice ta barta bayan ta ja mata Kofar Dakin Hajiya ta shiga ta Isketa tana Duba wani Turaran wuta da aka aiko mata Daga garinsu Maiduguri duk da yanzu Saboda Rashin Zaman lafiya Danginta duk sun Dawo Cikin maiduguri wandanda suka Rage Mahaifinsu ya Dade da Rasuwa.
Mikama ta wayar Tayi Hajiya ta karba batayi mgana ba ita bata wannan Shisshigi sai Aishan ne tace"Hajiya Dakin mu yace na Kaita tayi wanka ta Huta..!
Kai kawai hajiya ta gyadamata bata ce komai ba ba irin su daya da Aisha ba Abida ba mai Shigen Surutu ba da hannatu,yasa bata Dameta ba ta fice ta barta sai Faman Raba Turarenta take zata Bama abokan zamanta Sauran ta aika ma su mamanmu Dashi haka Hajiya take Ko sun san da abu ko basu sani ba Sai ta Dibar musu wannan Kirkin nata kowa yana Girmamata Saboda shi.
Sanda ya gama wayar ajiyar Zuciya ya Sauke lokaci Daya yana Sauke wayar Daga kunnensa,kusurwan Falon Mallam yake kallo inda Cabet din Jerin Littafansa suke,Tunani yake yi yazai yi ya Sanar da Hajiya ya kara aure..?ga Halin da Sakina take Ciki Tunda ya Fadamata an Daura musu aure da Sarood take kuka taki cin abinci ta Daina mai mgana Har yau da suka so gida Allah ya gani bai taba son Sarood ba ammh Tana da kimar da bai isa ya Wulakantata ba.
Daga Bayansa yaji Baba Sa"idu na Fadin"UMAR Baba mallam na mgana..?yace ko baka gama wayar bane..?
Jin Haka yasa Lokaci Daya ya Dago kansa Tare da Juyowa Ya fara Tako Doguwar Kafarsa Zarara saman Tattausan Cafet din Dake Falon Malam din
Tsarki ya Tabbata ga Shugaban Hallitun Duniya..Domin Tsabar kyau da Zati da kwarjini wajen bawan Allah nan,Shi ba Fari bane kuma ba Baki ba Fatarsa wani irin Fatace mai kalan Haske kamar na yan Moroci Tattausa Saboda jin Dadi da Hutu tana Sheki Dogon Namiji ne wanda ake Kira Ingarma yana da Fadin Kirji Daga Kafadunsa zuwa cikinsa ya Bude,FUSKARSA doguwa ce Sambal masu Dauke da matsaikatan Idanuwansa da Gashin gira dana Ido..Hancinsa Dogo ne ammh ba Sosai ba wanda ya karamai kyau da Zatinsa Sannan Bakinsa Zagaye da Saje baki wanda ke karamai kwarjini Daga kasa kuma gemunsa wanda yabar gemu kadan wanda bau wuce kamu Daya ba.
Wanda ya Dace da Zagayyen Bakinsa mai dan Fadi kadan da Tudu,yana Sanye Cikin Pakistan Riga da Wando na yan Saudiya Rigar Tawuce gwiwansa Sannan wandon bai rufe kwarin Kafansa ba Kansa Sanye Cikin Hula irin ta Larabawa karamar nan wacce iyakarta rabin kansa mai Kulin Gashin Sakan Hulan Daga sama Wanda ya ba Sumar kansa Daga kasa zuwa sama sama Bayayyana Duk da ya Asketa ammh gatanan tayi kwance gwanin Burgewa sannan Goshinsa ga Bakin Tabon sallah nan wanda ke karamai kwarjini da Haiba.
UMAR YUNUS ABDURRAHAMAN BAZANGA kenan Namiji kwara Daya Tal da Bayan Sa"idu Mallam ke matukar kauna acikin Ransa a Cikin Jerin ya"ya ashirin din da Allah ya basa mai tarin baiwa da Allah kadai Daya Hallicesa ya sani mai kimanin Shekaru Talatin da Takwas zuwa da Tara aduniya.
Har ya kariso ya zauna Kusa da Baba Sa"idu Baba Malam da Baba Sa"idu basu daina kallonsa ba.
Suna kara yaba kyan zatinsa ko su kansu kwarjini yake musu Tabbas Qur"ani ba karya bane kana ganin Mahaddacinta kake ganewa Saboda Natsuwar dabam take.
Kansa na kasa Cikin Muryansa mai Zaki yace"Afuwan Baba..na kira Hajiya ne..!
Baba Malam ya gyada kai kafin yace"Kace Shashenta ka Sauki bakuwar taka ko..!?
Kansa na kasa ya gyada kai Baba malam ya cigaba da Fadin"Hajiya ko bata san mutum ba ita din mai karamci ne..Zata karramata matuka..!
Baba Sa"idu yace"Sosai shiyasa nace a kaita chan kaawai..!
Baba Malam yace"Da kaji an ambaci Hajiya Jikin ka na rawa ka yabeta..Ina mamakin yadda ZAINABU ta kwacemin SA"IDU NA..!
ya karishe Fada Cikin Zolaya.
Baba Sa"idu na Dariya Danmalam kuma Mirmishi kawai yayi.
Kafin Baba Sa"idu yace"Haba dai..Ai Tsakanin Uwa da d'a akace sai Allah baba..Kuma haka Tsakanin Uba da Dansa sai Allah har Abada Sa"idu na Baba Malam ne ba shi ba duk wadanda ke karkashin sa naka ne Baba..!
Baba Mallam Zuciyarsa kamar Farar takarda ya gyada kai kafin yace"Allah ya albarci Rayuwarka Kai da iyalanka Sa"idu..!
Suka amsa shi da Umar atare,Kafin Baba Malam yace"Ni na hana Sa"idu ya Fadama Hajiya komai..na bari sai ka zo..Ko sauran abokam zaman nata ban Sanar da kowa ba..Ina Fatan ka Fadama ita Dayar iyalin naka ko..?
Kansa na kasa yace"Eh na sanar da ita tun muna chan..!
Mallam yace"Dakyau haka ake so..Allah ya zaunar daku lafiya..Sai ka zama jajirtattacen adalin zama da macen Fiye da Daya sai Adali Umar..Bana jinka nasan bazaka taba aikata wani abu mara kyau ba..Sannan itama Diyar Kattab din indai Halin Mahaifinta ta Biyo Har Abada bazakayi nadama ba..!
Baba Sa"idu yace"Allah ya sa...!
Kansa na kasa shidai bai ce komai ba basu Damu ba Sanin Halinsa Shuru Shuru bai da Hayaniya.
Baba Malam ne ya kalli Baba Sa"idu yana Fadin"Sa"idu ka tafi wajen aika..Nima anjuma kadan zani Gidan Sarki Tun jiya Sakon sa ya isoni yana son ganina..Umar kuma ya shiga Cikin Gida ya gaida iyayensa zuwa anjuma sai mu zauna gabadaya domin a gabatar da Bakuwar data shigo Cikinmu Gabadaya..!
Baba Sa'idu ya jinjina kai yana ma Malam Allah ya kiyaye Hanya.
Tare sukayi mai Sallama suka Fice shida Baba Sa"idu sun Dade aharaban gidan suna jingine jikin Motar Baba Sa"idun suna mgana kafada na gugan kafada Malam na daga cikin Falonsa yana Hangesu ta Wandow Falon Lokaci Daya ya saki kayattacen Mirmishi.
In ka gansu kamar wasu yaya da kaninsa uwa daya uba Daya ya Tabbata abunda bazai iya Fadamai bane yake Sanar da Sa"idu Akwai Shakuwa da Fahimta a Tsakaninsu Yana Daukansa kamar kaninsa Shima yana Daukansa kamar yaya kuma Uba agaresa
Sun dan jima suna mgana kan yana Fadamai bai Tsara Karin aure yanzu ba, sai dai kana naka Allah na nashi ne Baba Sa"idu na ta bashi Wasu Shawarwarin kafin suyi sallama ya Shiga Mota ya wuce Gidan gona yayinda Shi kuma ya Fara takawa yabar Filin Haraban gidan zuwa Shashen Hajiya ammh Kuma Ransa da da Kallonsa na Shashen Anty Amarya yana Tunanin ko Sakina ta Daina kukan..?ya manta Rabonsa Daya ga taci wani abu sai ruwa kawai..!
*Janafty*
*TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*
*Sadaukarwa ga Halima Yusuf gwarzo (Besty) Alherin Allah ya kai miki a dukkan inda kike*
*🅿️09*
Cikin Tafiyarsa ta natsuwa ya karisa Shashen Hajiya babba kamar yadda yake a ka"idarsa sai ya fara isa shashen Mallam sun gaisa sannan sai ya shiga cikin gidan Daya bayan Daya ya Bisu ya gaishesu.
Hajiya na cikin Dakinta har alokacin Daya shigo Aisha ce da Hanne har Lokacin afalon yana Shigowa Cikin Sallamarsa da Muryansa mai Zaki da Sanyi a koyaushe,Lokaci daya da kamshin Turaransa na Arab yayi musu Sallama..!
Gabadayansu suka mike Cikin Fara"a da Murnan ganinsa domin sun Dade basu gansa ba Tun Karshen wanchan Shekara sanda yazo Lokacin Duba Hajiya ce Datayi ta Fama da Kafa suna makaramta basu gansa ba kuma Kwana Biyu yayi ya koma.
Hannayensa duka Sanye Cikin Aljihun wandonsa ya Kariso Tsakiyar Falon gabadayansu har suna Hada baki wajen gaisheshi da yanayin Natsuwarsa ya kallesu yana amsa gaisuwarsu yana kara ganin girmansu acikin Idanuwansa.
Kai Tsaye yace"Hannatu Aisha meyasa baku je makaranta ba..?
Da Sauri Aisha tace"La yaya bana Fada maka ba..!
Sai Alokacin ya tuna da Sauri yace"ohm.Sorry na manta..Allah ya bada sa"a..!
Suka amsa da Ameen gabadayansu sai kuma yayi shuru yana kara nazarin Falon kamar me neman wani abu basu Damu ba Sanin Halinsa Sannan babu wani Shakuwa sosai a Tsakaninsu Tunda shi Babba ne sannan Lokacin da suka taso baya kasar yana Madina so zamansa Dasu bashi da yawa ammh duk da Haka yana da Kwarjini da baiwar da kowa ke girmamasa,ba Duka yake yi ba ba kuma Fada ba,Shi ina ma ya zauna ballatana yayi Hukuncin ..?in yazo kuma bai wani Dadewa yake komawa sai dai AllAh ya riga ya bashi wannan girman kuma ya Dauka kamar yadda In mallam yayi mgana bamai Musamai haka shima mgana Daya zai yi Cikin kwanciyar Hankali da Salama kowa zai shiga Taitayinsa bawai bashi da Sakewa bane, bai da yawan wasa da Dariya sannan bai da mgana ballatana Hayaniya yana da Matukar Sanyi Sosai a lamuransa.
Kamar ma ya manta daasu acikin Falon Saboda yadda yayi Shuru bai kara mgana ba sai chan ya kalli Aisha kafin yace"Ina bakuwar ku.?
Da Sauri tace"Na kaita Dakinmu na nuna mata Tiolet tana ciki na barta Tun dazu..!
Kai ya gyada kadan kafin yace"Ina Hajiya..?
Wannan karon Hanne ce ta nuna mai Dakinta tana Fadin"Tana ciki Yaya..!
Bai tsaya kara mgana ba ya Kama Hanyar zuwa Dakin Hajiya Cikin Natsuwarsa kannensa suka Bisa da kallon Sha"awa Duk cikin gidan nan ba kamarsa Sai dai abiyo bayansa.
Sai da suka Tabbatar da ya shiga Dakin Hajiya sannan Hanne ta Juyo Tana Fadin"Ya Aisha kinga yadda Ya D'anmalam ya kara kyau kuwa..?Wlh nima ina son naje Madinar nan Watarana..!
Aisha tana jinta batace mata komai ba illah ta Cigaba da Duba Littafin Dake Hannunta Hanne bata Damu ba Sanin Halin Aishan itama din mai Sanyi ce.
Hajiya na Tsaka da kasafin Turaranta Taji Sallamarsa Cikin Sanyi da Haiba Lokaci daya da Kamshin Turaransa mai Sanyaya Zuciya batasan Lokacin data saki Mirmishi ba Cikin Farinciki ta amsa sallamar tasa tana jaye kayan gabanta Lokaci Daya tana mai maraba.
"Maraba..Maraba..Maraba da Danmallam maraba da bakin madina Bakin Larabawa..!
Sai alokacin hakoransa kadan suka Fito yana Mirmishi gaban Hajiya ya Duka kansa na kasa yace"D'anmallam dai Hajiya..?Har yaushe ne zaki Fara Kirana da Umar ne..?Alhalin Baba Sa"idu Sa"idun sa kike kiransa Hajiya..!
Hajiya na Dariyan Farincikin ganin Yaronta ta kauda mganar da cewa"Masha Allah..Danmallan me kuke ci a Madinar ne.?gabadaya ka Sauya ka koma kamar Balaraben chan..!
Kai kawai ya gyada yana Shafa Gemunsa kafin yace"Hajiya bakomai..Sai nasaran addu"an ku gareni..!
Hajiya tace"Hakane..Allah ya kara Tsareka Allah ya Dafa maka Allah ya albarkaci Rayuwarka..!
Ya amsa da Ameen kafin ya Dago yana Fadin"Hajiya baki ce Allah ya bani Zuru"a ta gari ba..!
Hararansa tayi kafin tace"Ko ban Fada ba..Ina maka wannan addu"ar D'anmallam..!
Daman yasan haka zatace yadda Hajiya ke kunyarsa ko Ita Bafullatanane sai haka Tambayan kowa da kowa yayi tace duk suna Lafiya,Shuru ya biyo baya shi bai ce mata ba itama yasan bazatace ba Hajiya nada wannan Halin bata matsa ma Mutum akan abunda tasan Dole zata saani Shiyasa bata ce masa komai kan Sarood ba shima bai ce mata ba.
Kansa na kasa yana Duke ita kuma tana Cigaba da Zuba Turaranta Ganin Yaki zama kuma yaki tashi yasa ta kallesa tana Fadin'Ka zauna mana..Kada Tsugunnen ya gajiyar Dakai..!
Kai ya girgiza kafin yace"Hajiya Ina da gajiya ajikina..So nake na shiga na gaisa da su Hajiya uwa..Kafin naje nayi wanka na Huta..!
Kai ta gyada kafin tace"Hakan ma ya kamata..Mallam ya fitan ne..?
Kansa na kasa yace"Bai riga ya fitan ba ammhh yace yanzu zai fitan..Muna ma nan Haraba ni da Baba Sa"idu yanzu ya wuce gidan gona..!
Hajiya tace"Sa'idun Zainabu da Malam..ya shigo mun gaisa tun zuwansa..!
Bai yi mgana ba ita kuma ta kallesa tana Fadin"Dame zaka Karya..?nasa dai yaran sun yi maka Sinasir da waina..Bansan kuma me zamu ba wannan bakuwar ba kasan ku achan ba irin Cimar mu bane naku..!
Sai alokacin ya Dago kafin yace"Da kuli Hajiya..?
Kai ta gyadamai tana yar Dariya shima Mirmishin yayi yana Fadin"Yaushe Rabona da waina da kuli Hajiya..?Naji dadi sosai su dafamin ruwan Tea da na"a na"a,su hadomin da waina din ita kuma Sarood su hada mata Tea su soya mata Kwai is ok..!
Hajiya bata wani Damu ba tace"Shikenan.Ammh a Shashen mallam zaka Huta..?ko yanzu zaku isa gidan naku..?
Da Sauri yace"Sai Dare hajiya..Dakin su Shamsu zan yi wanka na Huta zuwa an juma..!
Hajiya tace"Na manta ne da na saka su Akilu sun gyara maka Dakinsu Nazem ka Zauna aciki..!
Kai ya kada kafin yace"Bakomai Hajiya nan din ma ya isa..!
Hajiya tace"Ai shikenan..!
Yana kallonta Kafin yace"Hajiya Turare kika fara saidawa..?
Hajiya tace"A"a Goggonku Yakura ta aikomin dashi shine nake rabawa zan aikama sauran iyayanka Sauran kuma na matan Sa"idu ne..!
Danmallam ya Murmusa kafin yace"Su yaya suna Lafiya..!
Hajiya tace"Duka suna Lafiya..!
Daganan sukayi shuru hirar ta kare ya Dade kafin ya tashi ya mata sallama ya Fice,Bayan ya fito su Hanne sun zata zai nemi Sarood sai dai bai ce musu komai ba ya Fice bayan Fitarsa Hajiya ta leko tace Hanne ta Dafa Ruwan Tea ta soya kwai ita kuma Aisha taje wajen Shamsu ta karbi key din Dakin Su Nazem ta dan gyarama Danmallam ya samu wajen da zai karya ya Huta.
Dukkansu da toh suka amsa Aisha tatashi ta saka Hijabi ta Fice,Hanne kuma ta shiga Kitchen.
Daga Dakin Hajiya Shashen Hajiya Uwa ya isa Tana ganinsa Cikin Fara'arta ta fara mai maraba itama Dukawa yayi yana gaisheta ta amsa tana Fadin"Umaru basai ka jira mu zo sannu da zuwa ba..!
Kansa na kasa bai ce komai ba tayi Dariya ya tambayeta yaran tace kowa Lafiya sai ga Umaima ta fito ta gaisheshi ya amsa yana kallon Hajiya uwa kafin yace"jikinta ya daina tashi ko..?
Hajiya Uwa tace"To ya dai yi Sauki Umaru..!
Kai ya jinjina kafin yace"Allah ya kara afuwa..Nazo mata da wasu manganuna in na Huta zan kawo mata ta fara amfani dashi mu gani..!
Hajiya Uwa ta fara mai godiya yana amsawa Har ya fice tana Rakasa da addu"an haka take ita tana da Kirki kamar Hajiya take.
Daganan sai bangaran Haj.Nasara itama ta karbesa sosai suka gaisa da Tambayan bayan Rabuwa Ikram ya gani tazo ta gaisheshi ya amsa yana kallonta ganin ta girma har zai tambayeta meyasa bataje makaranta ba sai ya tuna da mganar Aisha sai ya Fasa Yana Shirin Fita ne Take tambayansa ko da ba Sakinar suka zo bane..?
Cikin Haibarsa yace"Tare muke da ita..Tana bangaran Anty Amarya..!
Baki ta tabe batace komai ba yayi mata Sallama ya fice yana fita tace Ikram ta shiga Kitchen ta Dafamai Tea da soya kwai,Saboda Umar Domin in yazo garin ba wacce bata kokarin kyautatamai kamar yadda zata kyautatama Malam.
Kai Tsaye Daganan sai Shashen Anty Amarya ita kam koda ya Shiga bata Falon Sa"adatu kadai ya gani Tana Kwance saman kujera ko Sallamarsa ma bataji ba sai dai ta gansa saman kanta Cikin Muryansa yana Fadin"Ke baki jin sallama ne..?
Kamar ta kifa haka ta sauko daga kan Kujeran tana Raba ido Cikin Kifta ido Tace"Sannu da zuwa ya D'anmallam..!
Bai amsa mata illah Falon Dayake bi da kallo kafin yace"Ina Anty..?
Da Sauri ta mike tana Fadin"Tana Dakinta ita da Ya Sakina..!
Baima ce ta Kirata ba yaga ta wuce sai bai kirata ba Hannayensa Cikin Aljihun wandonsa ya kurama waje Daya ido kamar mai nazari.
Sa"adatu sai da tayi knooking Domin Tun isowar Sakinar tana kuka suka Kule Cikin Daki ita da Anty basu Fito ba,Kuma sun kulle kofar Daga ciki Anty Amarya da Ranta ke bace domin ta gaji da Lallashi da Tambayan Sakina meke Damunta taki gayamata gabadaya Tunda suka iso take kuka taki mgana ballatana tasan meke Faruwa..
Dagachan tace"Waye..?
Da Sauri Sa"adatu tace"Nice Anty..!
Tashi tayi taje ta Bude Kofar da Sauri Sa"adatu tace"Anty Ya D'anmallam yazo yana Falo..!
Da sauri tace"Yazo .?
Ta daga kanta Sakina ta juya tana kallo wacce ta Dunkule kan gado tana kuka kafin ta Dawo da kallonta kan Sa"adatu tana fadin"Kice mai gani nan zuwa..!
Daganan Sa'adatu ta juya ita koma ta maida kofar ta Rufe ta Dawo bakin makeken gadon Dake Bedroom din inda Sakina ke Dunkule ta Dade tana kallonta kaf ta gama Hasashenta bata hango abunda zai sa Tunda suka iso Sakina ke wannan kukan ba ta kuma yi Tambayar Duniyar nan Sakina taki Mgana.
Kai ta kada Kafin tace"Ai shikenan Tunda bazaki mgana ba..ga Umar din chan yazo..Bari naje na tambayesa kila shi ya fadamin abunda ke faruwa..!
Har ta bar Dakin bata Dago Daga kukan datake yi ba ballatana tasaka ran zata kalleta
Ta iskeshi Tsaye bai ko zauna ba Sadiya ta fito sun gaisa Sa"adatu ta shiga Dakinsu ta Fadamata zuwanshi.
Yana ganin Fitowarta ya Rage tsawonsa ya Durkusa kan kafafunsa yana gaisheta ta amsa Lokaci Daya Tana zama kan Daya daga cikin kujerun Dake Falon.
Daga gaisuwan ne bai kara cewa komai ba kansa na kasa yana kallon adon Zanen jikin Tattausan Cafet din Dake Falon.
Anty ta kalli su Sadiya kafin tace"Ku tashi ku shiga ciki..!
Ba musu suka mike zuwa Dakinsu sai da taga Shigewarsu kana ta maida Hankalinta kansa kafin Tace"Umar meke Faruwa ne..?ko kun samu Sabani da Sakina ne .?Tunda kuka iso take kuka gatachan kwance kuma nayi Tambayan Duniyan nan tayi banza dani har yanzu taki cemin komai..Shine nace bari kai na Tambayeka meke faruwa ne .?
Kansa na kasa bai Dago ba abu Dayane ya kara bashi mamaki me Sakina ta Dauki kanta ne..?tana Tunanin kukanta da Rigimanta zai sa afasa komai..?ai ta makaro Domin bakin Alkalami ya riga ya Bushe..Sannan bata isa yasa ya Sauya abunda Allah ya Tsaramai ba Duk da karin aure bai Cikin Tsarinsa.
Yasan yana da Sanyin Hali baya son Damuwa da Hayaniya ammh tasanshi Yana da zuciya mai karfi wanda in yagaji da baka baki bazai biyema iskancinka ba zai Fita batunka ne kamar ita yadda tayi mai tun suna Madina yake bata baki ganin yadda Hankalinta ya tashi bayan ya gayamata bayan an Daura auran Abunda yasa ya Biyemata yana ganin ya bata mata Tunda shima abun Daga sama yazo mai ammh akallah ba Dadi Kaji Mijinka yayi aure Lokaci Daya sai dai ya gaji da Lallashinta zai kyaleta In ta gama kukan don kanta ta Hakura shi bai kuma san da wani Kalma zai kara lallashinta ba.
Anty Amarya ta gaji da jiran amsar sa bai ce mata komai ba gabanta nata Faduwa kada matsalan yazama babbace Fiye da Tsammaninta.
Yasa ta gyara zama tana Fadin"Kayi Shuru..!?Ina fatan Allah yasa abun bai kai ku ga Saki ba..?
Sai alokacin ya Dago yana kallonta bata ga wani abu a Fuskarsa ba Illah Haibarsa da Zatinsa Cikin kakkausan Muryansa mai Cike da Sanyi yace"Babu ma mgana makamancin wannan Anty..!
Ajiyar rai ta sauke na samun natsuwa kafin tace"To me ke faruwa..?
Nan ma Shuru yayi mata ta kara kallonsa tana nazarinta har ta Fidda rai da zai yi mgana sai chan taji yace"Tunda bata gayamiki ba..Bakomai kenan..!
Kai Tsaye ya fada batare da Tunanin wani abu ba ya mike yamata Sallama ya Fice Daga Dakin tana Binsa da kallon mamaki.
Aranta tana ayyana wani abun Meke Faruwa..?meyasa Sakina taki mgana..?tana ji ajikinta koma miye babban al"amari ne sannan ta godema Allah daya kasance ba Zencen Saki bane Komai miye ai zai zo da Sauki.
Tashi tayi ta koma Dakin ga mamakinta sai ta iske Sakina ta shiga wanka sai taji Dadi,Yasa ta fita da Sauri zuwa Dakin su Sadiya tace su tafi Kitchen su sama ma Sakina abunda Zata karya dashi Dakin ta koma ta iske Sakina ta fito Fuskarta Duk ta kumbura idanuwanta duk sun shige Saboda kuka.
Anty Amarya ta kalleta tana Fadin"Ko kefa Sakina..?
Dagowa tayi ta kalleta Fara ce kyakyawa Daidai Misali sannan ita din mai matsakaicin Tsawo ce Tana da Jiki kadan da Jikin mata.
Kai Tsaye tace"Ya gayamiki wani abu..?
Anty tace"Kema kinsan bazai yi mgana ba..Umar yafi Ubansa Miskilanci da kyaluwa..!
Dan Mirmishin Fatan baki tayi Lokaci Daya tana Cije bakinta Towel ne Babba ajikinta taja Kujeran gaban madubi ta zauna ta Fara Shafa mai,Acikin Ranta tana jin kanta yayi mata Girma kamar zai Rabe Biyu Saboda Tsananin Kunar da zuciyarta ke mata.
Tana gama Shafaa mai ta Sauya kaya Cikin Wata Riga da wando Saukakku,Lokacin Sadiya ta shigo mata da Faranti shake da kayan karyawa Tea kadai ta sha bata iya cin komai ba,Bakinta ba Dadi Saboda yanayin Datake ciki.
Tagama kenan sai ga Anty Amarya ta shigo Dakin tana kallon Farantin Dake gabanta take fadin"Ya haka..?naga baki ci komai ba..?
Sakina na Sake komawa kan gadon tace"bakina ba Dadi Anty..!
Anty ta waro ido kafin ta karisa gefen gadon ta zauna tana Dafata Lokaci Daya tana Fadin"Ke na tabaki da Alheri Sakina..Allah yasa abunda muka Dade muna jira ne..?
Cikin Mamaki take kallonta kafin tace"Me kenan..?
Kai Tsaye tace"Ciki mana Sakina..Naji kince bakin ki baya Dadi..shine nake Tunanin kodai kodai..!
Da Sauri ta katseta ta fadin"Ba ciki bane Anty..Wannan al'amarin yafi gaban na..Rufo kofa kizo kiji..!
Da Sauri tatashi ta Rufo kofar ta Dawo ta Zauna kusa da ita kamar wata kawarta.
Sakina ta Fara matsan kwallah kafin tace"Anty Umar fa aure ya kara..!
Anty tayi wani Sansarai rai kafin tace"Aure wani irin aure kuma..?
Sakina ta ballo Hawaye saman kumatunta kafin tace"Aure da kika Sani Anty..Abun bakin cikin ma bai Fadamin ba sai da aka Daura auran. !
Anty Amarya ta Dafe Kirjinta kafin tace"Daman da gaske kike yi Sakina..!Wani irin aure kuma ana Zaune kalau..!
Sakina tace"Uhm yadda kikaji haka naji Anty..Ni ba komai yafi Tadamin Hankali ba..Irin matar daya aura..Anty Balarabiya ina ni ina kishi da Balarabiya..?
Ta karishe fada tana Kuka Wiwi Anty Amarya ta Dora Hannu akanta tana Fadin"Na shiga tara ni Marliya..?wannan wani irin kaddara ne..?
Sakina ta kwanto da kanta Saman Cinyar Anty Amarya kafin tace"Kaddara mai muni ma Anty..Kinga kyan yarinyar..?wlh ko gasar kyau ta Shiga sai taci..Tafini komai da komai ta bangaran kyau da Zati da nasaba da asali Wlh Anty wannan suka fara zama da Umar ni Bora zan zama..!
Ta karishe Cikin gunjin kuka Anty Amarya gabadaya jikinta rawa yake yi Cikin Tashin Hankali tace"Wai garin Yaya haka ta faru...?Diyar wacece ya auran..?
Sakina tace"Diyar abokin Baba Mallam ne..!
Anty Amarya tace"Kattab..?
Da Sauri ta Daga kai kafin ta cigaba da Fadin"Ita..Diyar su din nan kwara Daya Sarood..yadda Umar din yace min shi Abu kattab din ne ya bashi Auran kuma bazai iya kin karba ba..Ni ban sani ba saida aka Daura auran a Satin da zamu taho..!
Anty Amarya gabadaya Hankalinta baya Jikinta Har Sakina ta cigaba da Fadin"Tashin Hankalina Daya Anty..In tazo ta Haihu fa..?wlh Bora zan zama a idon Umar da Danginsa na zama bani da wani amfani..!
Da Sauri Anty Amarya tace"Ina.karya ne..Ba wanda ya isa wlh..!
Ta fada Lokaci Daya tana Ture kan Sakina Daga Jikinta ta mike tana Mazari Cikin bacin rai tace"ba wanda ya isa ya maidake baya Sakina..Kamar yadda ban zama baya ba..Wani Cikin ya"yana bazai taba zama baya ba..!
Take Fada tana Huci Sakina ta Mike Zaune tana Sharan kwallah kafin tace"Nama zama..Domin da ita muka zo kasar nan..!
Da Sauri ta zaro ido tana Fadin"Eyee...!
Sakina ta Daga kai tana Fadin"Eh tana ma Cikin gidan nan..Inaga Shashen Hajiyarsa yace shamsu yakaita..!
Anty Amarya ta rike Haba Kafin tace"Kenan iyayen nasa sun san da Labarin auran shine mu bamu ji ba..?
Sakina tace"Ni bansani ba..Ammh dai Malam ya sani Da Baban su Jafar tunda naji suna mgana tun muma chan..!
Anty Amarya ta Lailayo Ashar ta Dankara kafin tace"Sa"idu...Sa"idu..Ko bai kira Malam ba..Ina mai Tabbatar miki Sa"idu zai fara kira..Sa"idu ne ja gaba kan komai..Ko Malam da Hajiya basa tsallaken Shawaran Sa"idu abunda yace shi akeyi acikin Gidanan Sakina..!
Sakina ta Sharce majina tana Fadin"Anty ya zamu yi..?wlh karki so ki ganta Kinga kyanta..?
Anty Amarya Haushi ya kamata ta Ballama Sakina Harara tana Fadin"Kyan me..?kyanta na banza..Takai ki wayau ne..?Kyan ne kawai ammh batakai Budewar ido ba ..ina taje ina ta taka..?Irin wadanan kyan ne kawai da zaman waje Daya na Tabbata bata samu wata Sakewa ba..!
Sakina tayi shuru tana kallonta kafin tace'"Eh kam..kamar sakara haka take..Sai dai namiji ba ruwansa da wannan..!
Anty Amarya tayi Mirmishi kafin tace"Kada ki damu kanki..Ki Share Hawayenki kada ki kara kuka..Waannan auran wani matakin Nasarmu ce Sakina..!
Sakina tace"Taya ya..?
Anty Amarya ta kama Hanyar fita tana Fadin"kidai ki saka ido kawai..Mu zuba mu gani..!
Shege ka fasa..!
Daga haka ta Bude Kofar ta Fice tana Tafe tana Mirmishi ita kadai kamar an ce mata an biya mata aikin Hajji.
Falo ta koma ta Zauna ta Dora Kafa Daya kan Daya tana Kadawa kamar wata yar yarinya yar shekara Goma sha.
Sakina kuma tana Fita ta koma ta kwanta Damuwarta ya ragu,Saboda tasan duk abunda Anty tace kada ta Damu to tasan cewa kada ta Damun komai zai zama Daidai,Daman ga Rashin barci ga Damuwa yasa batasan Lokacin da barci ya kwasheta ba Cike da Mafarkin yadda makomarta zai kasance Tsakaninta da Umar da Sarood.
******
Amina sai gabda Azahar tatashi Daga barci tana mika Hamida bata Dakin yasa bata damu ba tatashi ta shiga waanka Lokaci daya ta Dauro alwala sai da tazo tayi Salla kana ta Sauya kaya ta saka Riga da Sikat na wani leshi da Mamanmu ta Dinka musu ita da Hamida.
Sannan ta fita Tsakar gida ba kowa ko'ina tsit,Kitchen ta Zarce ta iske ya Zulahait ta gama abinci Kuskus da Miya da nama Amina tayi Dariya kafin tace"Mijin ya Zulaiha zai ja kaya Wlh...!
Haka take fada tana Dariya kafin ta Diba iya sonta ta cika nama ta koma gefe taci tayi kat ta koshi,sannan ta fito taje bakin Famfo ta wanke hannu Dakin Mamanmu ta leka ta isketa tana Sallah Tana jin Hayaniyar Hamida a dakin Yaya taki Shiga Daki ta koma ta Sake kwanciya taci ta koshi Takaichinta Daya bata zuwa da Littafin hausa agida iya makaranta take karatunta ko boko ko Islamiya.
Ammh bata zuwa dashi gida ba Domin tana jin Tsoro ba ko wani abu ba, Aron daman iya makaranta ne ana tashi zainab take karba Saboda na mamanta ne take aro mata itama ba"a Sani ba agida.
Yasa barci ya kara Daukanta bata Sani ba sai Bayan azahar ta tashi Shima Mamanmu ce tatasheta tana Fadan ta Daina barcin yammah ba kyau.
Lokacin datasahi ta ga mamanmu Sanye da Hijabi tana Mitsike ido ta Sauko Daga kan gadonta tana Fadin"Mamanmu ina zaki na ganki da Hijabi..?
Mamanmu tace"Gidan Mallam zamu shiga ni da yaya..Danmallam sun iso tun Safe..!
Zamu je maraba da barka da zuwa..!
Amina ta tabe baki kafin tace"Mamanmu sai ku bisa..?bashi zai zo ba..?
Mamanmu na Dariya tace"Basai kin Fada ba zai zo..ammh yana da kyau mu bara zuwa din..!
Ta fada tana Ficewa Lokaci Daya tana Fadin"Ki tashi kiyi sallah tunda ke bazaki shiga ba..Tun dazu hamida tatafi..!
Mamanmu bata tsaya ba ta fice Amina tana so ta tambayeta chan gidan nasa Hamida tatafi ko gidan Baba Malam..?
Bata samu mai bata amsa ba yasa ta Tabe baki ta fito Bakin famfo tayi alwala tazo tayi sallar Ta gaji da kwaciya bayanta har ya gaji yasa ta zauna tana Tunane tunane Zulaihat na Dakin Yaya tun Safe batama zauna adakin ba Tana jin tashin mganar Ya Zeena na tashi,Yau Alhamis ba islamiya Shiyasa suke gida.
Bata fita ba Sanin Yau jidalinta na Saman kanta in taje Bakinta bazai yi Shuru ba kuma baza"a samu Zaman lafiya ba.
Yasa ta Cigaba da zama inda tayi Sallar har ya Zeenatu ta Shigo ganin yadda Amina ke zaune da Hijabi yasa abun ya bata mamaki yasa ta kalleta kafin tace"Amina yau kuma Lazimin yammah aka fara..?
Amina ta kalleta shekesheke kafin tace"Uhmm..!
Daga haka bata kara mgana ba Ya Zeena tayi Dariya tana fadin"Gwara dai kiyi shuru..yau gidan ya Sarara..!
Amina batace komai ba Tunani take taje gidansu Hanne ko A"a tana Shawara da zuciyarta ne Har ya zeena ta Dauki abunda zata Dauka ta Fice ta bar Amina nan zaune tana cigaba da Shawara tasan Hanne Sarai in taje sai ta basar da ita Kafin su shirya.
Tana nan zaune har su Mammanmu suka Dawo bata tashi ba har Lokacin kuma Hamida bata Dawo ba Amina ta Mike tana Fadin"Alqur"an sai naje naga ni..Hamida iyayan gulma ba"a Dawo ba..!
Ko Hijabin jikinta bata Cire ba,Ta fice batare da tace ma kowa gata zuwa ba.
Mazan duk basa nan suna msallaci wajen karatun yammah Da Baba Mallam ke yi,yasa kai Tsaye ta Nufi Shashen Hajiya Babba.
Daga Kofar ta fara kiran sunan Hanne kafin ta shigo tana Fadin"Hanne ni zaki Wulakanta ina ta Kiranki kinyi banza dani..!
Tafada Lokaci Daya tana Shigowa Falon batare data Tsaya Lura da kowa ba,Idanuwanta suka fada kan Hanne da Hamida dake gefe sun hada kai suna mgana Amina ta rike baki Tana Fadin"Hamida an ci amanata..Shine ko ki tasheni sanda zaki taho..!
Tafada Lokaci Daya tana karisawa gabansu Hannu tasa tana jan hannun Hanne Lokaci Daya tana Fadin"Hanne taso kiji..!
Hanne taki tashi lokaci Daya tana Fadin"Ba inda zani..Lokacin da naje ina miki mgana kin manta me kikacemi ..?
Amina tace"Hamida ce zata Hadamu Hanne..?Haba hannenta Hannen Aminene..!
Tafada tana Dariya har tana Jan kumatun Hanne da Duk Dauriyanta sai da tayi Dariya.
Hamida tace"Amina kinzama abun kallo kin shigo baki gaida kowa ba..!
Sai alokacin ta juya tana bin wadanda ke falon Idonta ya Sauka kan Sa"adatu lokaci Daya ta balla mata Harara,Sai kuma wacce ke kusa da ita Tana Sanye da Babban lullube asamaa kanta Sakina ce Anty Amarya ta saka Sa"adatu ta rakota tazo ta gaida Hajiya bayan sun gaisa Hajiya ta shige ta barsu da yara.
Sakina taki tafiya ne tana so taga ta inda Sarood zata fito Saboda ta tabbatar tana Shashen Hajiya,Shi kanshi Umar din bata kara jin motsinsa ba ance yana Masallaci Wajen karatun mallam
Sai ga Amina ta shigo Tunda ta shigo Kowa ya koma kallonta Saboda yadda ta Fado falon kamar Daga sama.
Amina ta Dawo da kallonta kan Hamida kafin tace"Su waye..?
Ta fada tana yamutsa baki Da Sauri Hanne tace"Matar ya D'anmallan ce Anty Sakina..ki gaisheta..!
Amina taja Tsaki da karfi kafin tayi mgana Hamida tace"Amina don Allah...!
Yasa bakinta ya mutu,Ranta bace ta Juya tana Fadin"Ina yini..!
Sakina sai da ta kare ma Amina kallo sama da kasa kafin ta tabe baki tace"Lafiya..!
Lokaci daya tana kallon Sa"adatu kafin ma tayi mgana tace"Amina ce..Ta gidan Baba Sa"idu..!
Sakina ta Tabe baki ta kauda kai ita bata gabanta abunda ke gabanta ya Isheta tana so ta Sako mganar Sarood wajen Aisha sai dai bata so ta Fahimceta sannan Aishar ma Azkar ne a Hannunta tana karantawa bata bi ta kan abubuwan dake Faruwa acikin Falon ba.
Amina ranta yakai kololuwa abaci da karfi tace"Jaruba..Kayyasa..!
Hanne bata bari ta karisa ba ta Tashi Tsaye ta Toshe mata baki lokaci Daya ta jata suka zauna kan kujera tana Mata rada a kunni.
"ke ya D'anmallan yazo da bakuwa wata balarabiya mai kyau baki ganta ba..?
Amina jin gulma yasa ta saki baki tana Fadin"Kice Wlh..?wacece tana ina..!?
Hanne tace"Tana Dakinmu..Bamu san ko wacece ba..Hajiya ma bata ce mana komai ba..!
Amina ta mike tana jan hannu tana Fadin""muje naganta..!
Hanne ta mike tana Fadin"Ke banza batajin Hausa sai labarci..!
Amina tace"Muma mun iya..Kaifa antum ne sai mu sakar mata..!
Sai da Hanne da Hamida sukayi Dariya dukkansu suka Dumguma zuwa Dakin Sa"adatu da Sakina suka Bisu da kallo banza.
*Janafty*
*TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*
*🅿️10*
Koda suka shiga Dakin sun iske Sarood na zaune gefen gado tana Danna wata karamar farar wayar Dake hannunta ta sauya kaya zuwa Saukakkan riga ta larabawa Sannan mayafin kanta ya zame kadan wanda ya bama Gashinta Daman bayyana har gadon bayanta.
Amina Sakin baki tayi tana ganin Tsabar kyau da zati ita kuma Sarood tana ganinsu ta washe bakinta Hakoranta Farare suka bayanna Ta gane Hanne Hamida da Amina ne bata gane ba ammh ai tasan Kannen Umar ne,Hannu ta mika musu alaman su matso kusa da ita Lokaci Daya tana Sauko da Tattausasun Fararan Kafafunta a saman Cafet din Dakin kafarta kamar ta jaririn da aka Haifa yau bai taba taka kasa ba.
Kamar masu neman gafara haka suka buga Layi agabanta bayan ta saka Hannunta Zara zara da yaji Jan kinshin Larabawa ta matsar da Farantin da Hanne ta kawo mata Fankwasau kuma tacida yawa Saboda mai gishiri akayi.
Daya bayan Daya ta fara tambayansu Sunayensu cikin Harshen labarci wanda sai ma sun Dage suke iya gane abunda take fadi,Amina ce karshen Fadamata Sunanta Lokaci Daya tana mika mata Hannunta alamun musabaha.
Sarood bata da bakunta gata da Sakewa nan da nan ta karbe hannun Amina Cikin Fara"arta,Amina taji hannu kamar auduga batasan sanda tace"Jar uba..Kun ji hannunta kamar Auduga .?ina ga tunda aka Haifeta bata taba wani aiki ba..?kayya sannan Hanne kunga gashinta mai kyau ce Wlh ta Burgeni..!
Har acikin Ranta ta kejin Sarood din ta kwanta mata Har tana Ji dama ace itace matar Ya D'anmalam din da wannan Banzar Sakinar.
Jin abunda Amina tace ne yasa suka rika bata Hannu Daya bayan Daya alamun musabaha su ba gane ma mganar suke ba in tayi musu mgana sai dai su daga kai Amina ce take ji kuma bazata taba nuna tasan ma tana ji ba Amina bayan Baba Mallam ba wanda yasan Wacece Amina A zahirinta.
Tasata sukayi kamar sun samu Tibi suna kallon Duka motsinta Sai dai ta kallesu ta Murmusa Amina ta Raba gefen kunnen Hanne tana Fadin"Hala Budurwansa ne..?
Hanne tace"Kai..Bana Tunani ko kila Diyar abokin Baba mallam ne Dake chan Madina .!
Hamida tace"Zata iya yiyuwa haka din ne..Kila tana so tazo taga kasarmu shiyasa ta biyosu..!
Da haka suka bar mganar Musun ammh acikin ran Amina Tana Tunanin haka kurum sai yazo da ita..?da wata akasa.
Basu da Niyyar Fita sai Hirarsu sukeyi sai dai ta kallesu tunda baji take yi ba, basai ga ya Abida tashigo ba, Amina na ganinta ta kyabe baki a hankali Tace"Ga uwar iyayi ta shigo..Uwar sa ido..!
Ai bata gama mgana ba ta Rike kugunta Tana Fadin"Ji yaran nan..Uban me kuke yi..?kun wani zo kun zauna kun sakata gaba sai kace kuna jin abunda take cewa..?
Hanne ce tace"Mu fa ba Damunta muke yi ba..Muna Hirarmu ne muna kallonta..!
Abida ta saki Tsaki kafin tace"To ku tashi ku fita ku barta ta Sake..Kauyawa kawai..!
Dole suka tashi Amina ta Zumbura baki tana kunkuni fadi take"Mu ba kauyawa bane..Kema ai ita kika zo kallon..!
Tana ganinta sanda take mganganun Yasa tace"Ke Amina da wa kike..?
Amina tace"Ni nayi mgana ne..?
Hanne don Allah me nace..?
Tafada tana gwalo idonta dukkansu suka Hada baki wajen Fadin"Bafa tace komai ba ya Abida..!
Kwafa tayi kafin tatasasu suka bar Dakin ita kuma Sarood sai kallonsu take tana Mirmishi..
Koda suka fito falo ba su Sakina sun koma Shashen Anty Amarya Amina tayi Tsalle ta Dire kan kujera ya Aisha Dake gefe ta kalleta da Sauri tace"yi hakuri ya Aisha..!
Tana kunshe bakinta ganin yadda take Hararanta Fitowar Hajiya yasa Amina ta Mike Zaune tana Fadin"Hajiya ina yini..!
Hajiya tace"Mamah..yaushe kika zo..?
Amina tace"Ban dade da zuwa ba..!.
Hajiya tace"naga zuwan Hamida tun dazu nace kina ina tace kina gida..Sanda su yaya suka zo ma na Tambayeki..!
Amina kanta na kasa tace"Gani nazo Hajiya Lokacin kina Daki ne..!
Hajiya tace"Barka da zuwa Mamah..!
Kafin ta juya tana Kallon Abida Lokaci Daya tana Fadin"Sakina ta koma wajen Amarya ne..?
Ta daga mata kai tana fadin"Sun tafi tace wai in kin fito ace ta wuce kanta ke ciwo zataje ta kwanta..!
Hajiya bata Damu ba ta juya tana Fadi "Hanne ku zo ku karbi Sako ku kaima su Hajiya uwa..!
Daga haka ta shige Ciki Hanne Tajeta karbo Sakon Turaran wutan Har ta juya ta Dawo tana Fadin"Hajiya ina nasu mamanmu..?
Hajiya tace"Yanzu na basu da suka shigo yi ma D'anmallam barka da zuwa. !
Jin haka yasa ta fita zuwa falon tace ma su Amina su taso suje Amina Kirkiri tace ba inda zataje Dole Hanne da Hamida suka fita Shashen Hajiya uwa suka fara zuwa suka kaimata Tana ta godiya sai wajen Haj.Nasara itama tana godiya tana cewa ace ma Hajiya sai ta shigo Shashen Anty Amarya kuwa tana ciki ita da Sakina Ya Sadiya suka bama Sakon sukayi Fitowarsu suka koma Shashen Hajiya suna Hiransu Abida ta shiga Kitchen tana soya kaza Ya Aisha kuma ta koma Dakin Hajiya tana gyara mata sai su kadai afalon suna ta Hayaniya.
Amina ce ta kalli Hanne kafin tace"Wai ni banga ya D'anmalam din ba..?ko yana gidansa ne chan kofar arewa..?
Hanne tace"A"a yana nan gidan..Tun Safe Dakin su ya Nazem aka gyaramai ya yi wanka ya huta..yanzu haka yana masallaci tare da mallam sai Dare zasu wuce gidansu in ji Hajiya..!
Amina ta gyada kai kafin tace"Shi nazo gani gashi ban ganshi ba..!
Hanne tace"Zai shigo ki tsaya don Allah..!
Hamida tace"Nima ina so na gansa..Na dade ban gansa ba wlh Amina mu kara jira mu gani..!
Amina batace komai ba sai chan ta rage murya tana Fadin"Ku jinin al"adarku sau nawa kuka gani..?
Hanne ta kalli Hamida itama ta kalleta kafin tace"Ni tun na Farkon nan ban kara gani ba..!
Hamida tace"Ni ya kara zuwar min Sau Daya wanchan watan..!
Amina tayi tagumi tace"Hanne bamu da lafiya ne..?nima fa daga sau dayan nan fa ban kara gani ba..!
Na tambayi mamanmu tace kada mu damu zai zo haka yake yi..!
Hanne tace"Eh mana kin manta ya Sayyadi yayi mana a islamiya yace in yazo na farko kafin ya kara zuwa ana Daukan Lokaci..!
Amina ta kalli Kirjin Hanne ta kalli nata ta kalli na Hamida kafin ta Bushe Da Dariya Hanne ta Daga mata Duka tana Fadin"Kefa baki jin mgana..!
Amina na nuna kirjin Hamida tana Fadin"Hamida zan siya miki Breziya in muka gani a hanyar makaranta..!
Tafada tana Dariya Hamida ta ji kunya ta juya Baya Saboda ita Nonuwanta sunfara girma har ana gani A hijabi Saboda yanayin Jikinta..sabanin Amina da kirgan Dangi makale a kirji har gwara Hanne ma sun Fara bayyana.
Hanne tace"to ai sa"adatu ma tana Saka abunta..!
Amina tace"ita wannan ai ko uwarta ta siya mata mara kunya ce..!
Na taba gani a Littafin Haussa fa ance maza na son Nono shine in nayi sallah nake Rokon Allah ya bani kada yazo banidashi nayi aure mijina ya karomin Kishiya..!
Gabadayansu baki suka rike suna kallonta kafin su fara kallon kofar Dakin Hajiya ganin ba kowa yasa suka Fixgeta sai Chan lungun Falon atare suka Hada baki wajen fadin"Amina daman baki daina karatun Littafan Hausanan ba ko..?
In akaji labari fa..?
Amina na Dariya tace"Dilla kun cika Tsoro..!
Hanne tace"Na Dauka da ya Sayyadi ya kamaki a makaranta ya Dakeki kin daina..!
Amina ta yi wata Dariya kafin tace"Aminene ikon Allah..Ni duka ai baya sani na fasa abunda nayi niyya..In ma zaku daina wannan Tsoron ku daina ku zo kuma ku fara Wlh Dadi kunga Love..?nace ni ko su ya Zulahait da zasu aure basa wannan Love din da mazajensu koda yake ko waya fa basu da ita ta ina zasu ma kirasu" ta karishe fada tana yar Dariya Hanne tace"Allah ya shiryeki Amina..'
Tace Ameen Hamida kuma ta kasa mgana Domin ta gama Sarewa da Lamarin Amina girma kawai yake karawa.
Suna nan har shidda na yammah Amina ta gaji ta mike tana cema Hamida"Kinga tafiyata in ke baki tashi ba..!
Hamida ta mike tana Fadin"Mu bari bayan mangariba mu tafi kinga yanzu kila su ya jafar suna waje zai mana Fada..!
Amina tace"Allah yasa yankamuzai yi ba Fada ba sai na tafi..!
Hanne tasan bazata tsaya ba yasa taje ta Dauko hijabinta Dakin Hajiya suka je suka mata sallama tana bakin gadonta waya na Hannunta tace"Mamah ku bari Abida ta gama Pepe Chicken din nan mana ta Dibar muku..!
Amina na jin haka tace"Hajiya ko Tafashasshe ne abamu hakanan..!
Dariya suka mata Har da Hajiya kafin tace"Kuje Abida ta baku..!
Amina tace"Ya Abida taf..Hajiya sai dai in kizo da kanki dama yar aljannah ce ya Aisha ..!
Ya Aisha na Gaban wardrope din Hajiya tana gyara mata tana jinta batace komai ba Amina fa yanzu zata yabeka anjuma ta zageka tas.
Hanne tace"Allah yasa ya Abida ta jiki..!
Amina ta Zunguri kafadarta tana Fadin"Ke in ta ma taji fa..?sai nayi abunda na saba nace bada ita nake yi ba..!
Hajiya na jinsu tayi Dariya Amina manya Kafin tace"Kuje dai ku ce mata ni nace..!
Dole suka wuce Kitchen din suna Shiga tana ganinsu ta Fara masifa"me aka zo min Ehe..?ba kwa son aiki sai Ci ko..?ku fita ku bani waje bana son Iskanci..!
Amina ta kalli Hanne itama ta kalleta Hararansu tayi kafin tace"Bana son munafunci lafiya..?
Hanne tace"Hajiya ce tace ki bama su Amina nama wanda baki soya ba zasu tafi ne..!
Abida tace"Bazan bayar ba..Kada Allah yasa su tsaya din..Ke Hamida ki bari na gama in Amina zata tafi ki barta tatafi din..
Sai na gama Duka sannan Wlh zan baku. !
Kyam suka tsaya suna kallonta ta juya baya ta cigaba da aikinta ganin sunki Tafiya yasa ta Juyo tana Fadin"Kuka tsayamin aka..?zaku wuce ko kuwa..?
Amina ta fara juyawa Hanne zatayi mgana ta rike hannunta kofar Kichen din suka Labe Amina na fadin"Wlh sai na Sata tunda taki bani da lalama..!
Basu ma yi mamaki ba Domin Amina bata Fadar abunda bazata iya shi ba.
Hijabinta ta Tattare sai da ta bari hankalin ya Abida na wajen juya Naman dake cikin kasko ta fara Sanda ta shiga kitchen din sai ji tayi kawai an Dumbuzu Naman Daya Rage bata soya ba har Garin Sauri tana Zubar da wani a kasa Abida ta Juyo taga sanda Amina ta Ruga Su Hanne suka mara mata baya suna Dariya fitowa tayi da Gudu da Abun suya a hannunta yana Digan mai tana Fadin"Kai kai..Ni yaranan zaku raina ko..?wlh na kama yarinya sai na Lahira yafi ta jin Dadi barin ma Amina zaki gane dani kike..!.abun ya bata mata rai kamar ita yaran nan suka ma haka su ko juyowa ma basuyi ba Hanyar Fita Amina ta kama Tana Fadin"Ku ka tsaya wlh ta Sauke Haushina Akan ku..!
Ta kawo bakin kofar kenan tana juya baya bata ma kallon gabanta Daidai Lokacin aka Bude kofar Shashen na Hajiya Lokaci Daya da shigowa Amina bata sani ba da karfinta ta juyo Hannunta Damke da naman data Diba sai Gaf taji tayi karo da Mutum ammh kamar Da Icce taci karo Saboda ko gizau na Tsayen bai yi ba sai ma itace ta koma da baya Kamar zata Kifa da Azama da wani Zafin Nama ya ciro Hannunsa guda Daya daga Cikin Aljihun bakin wandon Dake Jikinsa ya Rike hannunta Cikin Tsausatsayi wanda Naman ke Ciki gabadaya maikon da ruwan Tafashen ya gama Mamaye hannunsa..
Ammh duk da haka bai saketa ba sai da ya Dagota da hannu Dayan nan ta Tsaya da Kafafunta Idanuwanta na Runtse domin ta gama Sadakarwa ta Fadi Numfashi take saukewa shima da azama ya saki hannunta yana Bin Hannunsa da kallo ransa nan take ya baci kyamyami garesa Har tsikar Jikinsa na tashi.
Cikin Tatattausan Muryansa ammah Cikin Fada yake fadin"Ke wata irin mara Hankali ce..?kina tafiya ba natsuwa kamar wata namiji..?
Muryan daga sama ta jita sannan kafin ta gama Daidaita Natsuwarta ta Bude Dara daran idanuwanta Daga baya taji Hanne na Fadin"Sannu da zuwa Ya D'anmalam..!
D'ANMALAM..!
DAM gabanta ya fadi kenan da Ya D'anmallam ta ci karo bata sani ba..
Da sauri ta Bude idonta ta Sauke akansa alokacin bama ita yake kallo ba Hannunsa na Sama kamar wanda kashi ya taba yana kallon Hanne yace"Hannatu meke damun ku..?wani irin wasan banza ne wannan..?
Yafada har Giransa na sama yana Hadewa waje Daya ya Abida Daga Kofar Kicthen ranta fes tasan sai ya D'anmallam ya chasa mata su sosai.
Amina batasan ta saki baki tana kallonsa ba Domin kamar mayen karfe na janta haka taji ta kasa Daina kallonsa Duk da bai juyo ma gareta ba Kyau da zati kawai da wani Haiba take gani da Hange da kuma wani Dattako da wajen Baba Mallan kadai tasan dashi.
Hamida jin Hanne tace ya D'anmallan yasa ta gaisheshi ya amsa bai Damu Daya kalleta ba Yasan dai Cikin yaran gidan ne saboda ai ba Duka suka taso agabansa ba.
Hannunsa ya kallah kafin ya Yamutsa Fuska yace"Miye wanna..?wacece ta shafamin wannan kazantar a Hannuna..?
Yafada yana kara kyamatar hannunsa nasa Amina Girman idonta ta Bude tana kara kallonsa Daga sama har ksa Yana Sanye da Jallabiya mai Ruwan Madara,Da bakin wando sai kansa Sanye da Hula irin ta yan Saudiya karama iyakarta rabin kan nasa Fuskarsa tayi wani Haske mai Annuri sosai da Zati Lokaci Daya.
Abida na jin abunda yace ta kariso Tana Fadin"Ya D'anmallan gwara da Allah ya kawoka..Nama suka zo suka Satarmin Hajiya ta sakani suya..!
Cikin mamaki yace"Nama..?
Da sauri tace"Eh ga shugabarsu na..Amina wlh yaya har tana Zubarda Naman a kitchen bata da natsuwa kamar yadda ka Fada kazamar ce..!
Tafada tana nuna Amina wacce ke Tsaye tana kallonsa ga Hannunta Dunkule da Naman data Sato din
Shi ko da suka ci karo ya Rikota bai Tsayama kallonta ba Duk azatonsa Sa"adatu ne ko cikin yaran gidan sai yana kallonta yaci gabansa yayi wani Dif saboda yadda Fuskarta ta Tsaya aransa yana so ya Tuna mai irinta Saboda Tsabar kwarjinsa akaron Farko Amina taji ta kasa Jurre kallon Cikin Idanuwansa Sai da ta sadda kanta gabanta na Fadi haka kurum taji Wani tsaro karon Farko da kunyar da Amina bata taba jin irinta ba.
Ganin yadda ya Dawo da kallonsa kan Abida ne Cikin Alamun Tambaya.
"Amina...?
Da sauri tace"Amina..Diyar Baba Sa"idu ne..Yar wajen yaya ce fa..!
Ga Hamida ma itama duka na gidan Baba Sa"idu ne..!
Sai alokacin ya kara kallonta yasan wannan Fuskar matar dayake ganin kimarta bayan Hajiya babba ne wato yaya.
Shi bai ma san tana da Wata karamar yarinya ba ya Dauka Jawaad ne Autanta Saboda in yazo yana ganinsa Tare da Baba Sa"idu shi bayansu Jadwa sai su Jaleela yaran nan duk ba Saninsu yayi ba.
Hayaniya ce bai so sannan hannunsa kyamkyami ya ishesa yasa yace"Nama kuke sata agidan Baba Mallan..?
Yafada Cikin Sanyinsa a karon Farko Hamida da Hanne basu Dauki Jidalin Amina ba suka Hada baki Wajen fadin"Bamu bane..Wlh Amina ce ta Shiga ta Dauko..!
Suka fada suna Nunata Amina taji kamar kasa ta Bude ta shige saboda kunya tana jin idanuwansa akanta Ga hannunta Dauke da Nama Ruwan maiko na Diga da Sauri ya kauda kai ya wuce da Hanzarinsa cikin Natsuwa
"Ita mace da natsuwa aka santa..Hakane ke bambamta ta da Namiji..Sannan kazanta ko a addini bashi da kyau Hadisi ne guda Ko Sallah bata cika sai da Tsabta..!
Bai ko kara kallonsu ba ya shiga Kitchen din ya tara hannunsa a sink ya wanke har da saka Omo yana jin karnin Naman a Hannunsa karamin Tsaki yaja kafin yace"Kazamar yarinya kawai..!
Suna nan Tsaye kamar an Dasasu ya Fito Abida ssa Dariya take musu suna ganin ya fito Hanne taja hannu Hamida suka fice da Sauri ammh Amina ta kasa gaba ta kasa baya.
Kunya da wani abu data kasa sanin Dalili taji wani abu sunan yau an kunyatata Duk da gaban Hanne da Hamida ne an kirata mai Satar nama kuma kazama kuma mara natsuwa har ana Dangantata da Namiji wadandan kalmomin sun taimaka wajen sata ta cigaba da Tsayuwa a wajen Saboda ji tayi kafafuwanta sun kasa Daukanta.
Tana tsaye a wajen taji yana Tambayan Abida Hajiya tace tana ciki Tana kuma jin Sanda ya fara taku zuwa Dakin Hajiya yana Shigewa Abida ta saka Dariya tana Fadin"Bera mai satan Nama..!.
Sai ga Idanuwam Amina sun ciko da kwallah suna Shirin zubowa.
Su hamida sun fara gaba suna juyowa suka ga ba Amina Hanne tace"Amina bata taho ba..?
Da sauri suka juya suka koma suna Shigowa falon daidai Yana fitowa Daga Dakin Hajiya shi da Aisha yana mata mgana ganin haka yasa suka kasa ma Amina mgana shi kan yama manta dasu sam Aisha Dakin da Sarood take ta shiga ba jimawa sai gata ta dawo tare da ita tana ganinsa ta Nufesa kamar zata Rumgumesa sai ya rike hannuwanta Hanne nata Zungurin Amina duk son gulmarta wannan karom bata Dago ba Domin har alokacin bata gama Dawowa daidai ba.
Mgana suke da harshen Larabci Cikin kwarewar da in ba ka iya Sosai ba bazaka gane komai ba, ba Dadewa ya Dauko waya daga gaban Aljihun jallabiyansa ya bata Sannan ya Saki hannunta Tana Sakin mai kayattacen Mirmishi yana Shirin juyowa Hanne ta Fizgo hannun Amina suka jata suka fita da sauri har suna Bugo kofar Falon da sai ya da maida Hankalinsa wajen.
Ganin bai ga kowa ba yasa ya barsa shima Ficewar yayi suna ganinsa labewa sukayi a wajen Bayan Shashen Hajiya,sai da ya wuce suka Fito Hanne ta kalli yadda Amina tayi zata Rantse da Allah bata taba ganinta Cikin wannan Halin ba
Da Sauri tace"Amina lafiya..?ko wai Fadar sunanki da mukayi..?
Da Sauri Hamida tace"Wlh shi ba irin ya jafar bane..Kinga idonsa kana mai karya sai ya ganeka..!
Amina bata ma Tsaya bi ta kansu ba Naman Dake hannunta ta saki ya Zube a kasa,kawai ta kada kai ta wuce Suka Bita da kallon mamaki suna kwala mata Kira bata amasasu ba.
Suka fita har suna Hadawa da gudu ganin ana ta Haraman Alwala Domin lokacin Sallah ya kusa.
Amina bata tsaya musu ba Har suka iso gidan Ya Zeena na bakin Famfo tana wanki mamanmu na Shimfida Darduma kofar Dakinta Amina ta shigo ba sallama Ya Zeenatu ta dago tana Fadin"In kika gyara Halinki ai ke baki cika Amina ba..ki rika shigowa gida kamar Kafira..!
Mara natsuwa kawai..!
Amina ta jita ta kuma ji sanda Mamanmu kr fadin"Zeenatu bana son haka..?ban ce ki daina shiga Harkan Amina ba..,!?
Ita dai sai da ta danganta da kan gadonta taci kukan data ke rikewa ya zo mata Kamar wacce aka Daketa ta Fara kuka tana jin Hanne da Hamida akanta suna tambayanta tayi kamar bata jisu ba.
Kuma taji sanda ya Zulaiha ta shigo ita da ya Zeena ganin Amina na kuka yasa suka tambayesu sanin halinta ba kasafai take da Saurin kuka ba.
Hamida ta fara maida yar da akayi tazo wajen bayanin abunda Danmalan yace Amina ta Dago afusace tana Fadin"Eh yace min Kazama mara natsuwa ko..?haka kika so kice munafuka..!
Tafada tana Sakarmata Jajayen idanuwanta da sai da ya basu Tsoro.
Sai a ka rasa mai mata mgana har ta Fice Fuu Daga Dakin Zeenatu ta kwashe Dadariya tana Fadin"Ba Duka ba Zagi ashe mgana na Ladabtar da Amina bansani ba..?
Hamida dai da Hanne sun kasa mgana ajikinsu yayi sanyi.
Yasa suka fita suka fara shirin yin alwala Jam'i suka bi Amina na Dakin Mamanmu ta Dunkule kan kujera ko Sallar batayi ba tana jinsu a Tsakar gida suna Fadin yau Yaya Danmalan ya bada Sallar Itama ai taji Sanyayyar Muryansa yana Karatu Karatun da Har ita tayi karya tace bai natsar da zuciyarta ba tana jin Yaya na Fadin"Allah Sarki mun yi kewar karatun D'anmallam..!
Daman in yana nan shike bada Salla har ya koma..!
Amina aranta tana ayyana yadda yau yaci Zarafinta sai taji gabadaya Duhu ya mamaye saninta dashi an sha ce mata mara natsuwa da kazanta ammh yau sai abunda ya Zafeta fiye da koyaushe.
Tana jin sanda Hanne ta ke ma su Mamanmu sallama tatafi gida sai Alokacin Amina tatashi tayi sallar Tana Tura baki.
Ganin yan jidalin na kusa yasa bama wanda ya sake bi ta kanta.
Sai dai tun Safe Hanne ta Dawo Lokacin Amina ta dan Huce Tana zaune bisa gadonta ita da Hamida alokacin Ya Zulaihat bata Dakin ya Zeena na makaranta.
Hanne tace"kunsan wani abu..?
Hamida ce ta girgiza kai Amina kuwa Yamutsa Fuska tayi kawai duk da Hannen na kusa da ita ne.
Hanne tace"Ashe balarabiyar nan mai kyau dinan da ya D'anmallan yazo da ita matarsa ce..!?
Amina ta Zaro ido kafin ta mike tana Fadin"ki bari don Allah Hanne..?
Hamida tace"Nima naji Mamanmu da yaya suna mgana da safe..Wai Aba ya Fada musu jiya da Daddare..!
Hanne tace"Kwarai muma jiya Mallam ya taramu har da ita ya fada mana aka gabatar da ita acikin mu Ashe Diyar dai abokin Baba mallam ne na Madina ya aura ma Ya D'anmallan diyar tasa achan Madinan.!
Amina tace"Ya su Sa"adatu sukayi..?Ina Anty Sakinar..!
Hanne tace"Abun mamaki basu nuna komai ba Anty Amarya tafi kowa ma karban Abun tatashi ta Rumgume Anty Sarood din agaban kowa tana mata maraba..!
Amina tace"Jar uba..Wlh na karya ne..Wannan matar din..?
Hanne tace"Bakisan wani abu bama..Ta kwace ta Daga Shashenmu tace ma Hajiya ita ke Saukan Anty Sakina to yanzu bata Sauya ba ita zata Sauki Anty Sarood jiya ai shashenta ta kwana..Sai da Safen nan suka wuce gidansu kuma Anty Amaryan ta rakasu Mallan yace taje..!
Amina sam Labarin bai kwanta mata Baki ta Tabe kafin tace"Uhmm!
Daganan bata kara mgana ba aranta bata yarda don Allah tayi ba Matar da ko su Mamanmu suna Fadin Rashin Kirkinta sun ce ko Aba bata cika mgana Dashi ba tana jin Haushinsa Sabida Hajiya da Baba Malam.
Tundaga Ranar Amina bata kara yarda ta koma gidansu Hanne ba Duk kuwa da Tasan ya Danmallan yana gidansa ammh ai kusan nan anguwan yake zama Saboda bada sallah haka kurum taji batason su kara Haduwa Ya riga ya gama da ita tunda ya ce mata kazama kuma mara natsuwa bawai ta tsaneshi bane sai dai Acikin Ranta bai burgeta ba,duk da baya Duka ammh kuma yana mganar da zai saka ka kwana kana kuka aran Amina tasa masu sanyin Halin nan ba masu Kirki bane to Danmalam yana Daga cikinsu.
******
Shiryen shiryen Biki ya cigaba da Gudana ta kowani bangare kamar yadda Al"adar gidan mallam take ana Saura kwana Goma sha Hudu Biki Aka je akayi jerin Dakunan Amarya Tunda kayan suna isowa kowacce inda zata Zauna aka Sauke nata,Ikram aka fara ma nata Jerin nan Kusa da gidan Sarki Inda Dan Sarki Mahaifin Sultan din ya gina mai wani Dankarern gida su Mamansu suke je jeren su da su Hajiya,Sai Ya Zulaihat da ita agarim jigawa aka mata nata jeren agidan mijin nata Daya gina duk da kano zasu koma da zama inda yake aiki itama su yaya suka je dasu Hajiya uwa.
Sai Ya Sadiya itama Garin Dutse aka mata Jerin duk da itama bayan Bikin America zata bi mijin nata.
Ya Aisha sune yan kaduna Anty Amarya ce kan gaba ita da Hajiya Nasara da Mamanmu suke je suka mata Jerenta suka Dawo..
Daganan shiri ya cigaba da kamkama ta kowani bangare..
Tun ana Saura Sati Daya Biki baki suka Fara zuwa goggo Husai ita da Jadwa suka ssauka Daga Jordan gidan Dan"uwanta ta sauka Baba Sa"idu.
Asatin Shiri Daya akeyi na Walimar su ya Zulahait da za"a hada da Saukasu a Haraban makarantar Islamiyarmu za"ayi Taron,Gida ko"ina ya cika ba matsaka Tsinke duk da Baba Mallam baya son taro ammh ai bai isa ya Hana Dangi zuwa ba,Mutanen gusai ma sun iso,sannan ga su Ya Nazifa tazo jidda ma tazo ya Akila ma haka ya Fatima tazo gidan Baba Sa"idu ma ya cika su Jaleela yan lagos sun sauka jamila ce bata zo ba uwar mijinta ba Lafiya sai Jawahir itama ta iso.
Ana jibi Daurin aure Hidaya matar ya Nazir ta iso Daga Lagos ashashen Hajiya uwa take Sauka Daman in tazo,Ya Nazir sai jibi zai iso tace.
Amaran kuma Kaf dinsu suna Gidan su Ya Jafar chan Hajiya ta roki Baba Mallam ya bari suka tafi Danginta yan Maiduguru sun zo suna chan suna gyaran Amaran sannan Bakin bazanga ma mata sun zo mazan sai Ranar Daurin aure.
Kowa yazo yaga Balarabiya sai yace Daga ina sai ace Amaryan D'anmallan ne Abunda ke bama kowa mamaki yadda Sakina tajata ajiki Ko'ina suna Tare kamar kawaye,Sarood bata da Zabin kanta sai abunda Sakina tace kamar itace jagoranta.
Da su ake ta Hidima gidansu suke kwana ammh kullum suna nan anguwan Danmallam shi kanshi yayi mamakin yadda Sakima ta Saki Lokaci Daya sai da yafi kowa Murna da hakan ganin yadda ta karbi Sarod Hannu Bibbiyu Hajiya bata ce komai ba Domim ita a kan Hurumim D'anmallam Mallam yafi ta karfi ta wannan bangaran.
Amina Bakinciki take in za"ayi taro Saboda yadda kowa ke mai dasu jakai yayi ta sakasu aiki.
Kusan ita da Hamida da Hanne gidansu suke kwana Saboda su ya Zeenatu suma chan suka tare da Amaran yau aka kawo musu Sabbin kayansu da Hijabai Dukansu iri Daya na Amaran ne kadai ya bambamta sai na iyayensu mata.
Yau kwata kwata basu zauna ba sai saasu aiki akeyi,aikin ma na Wahalan Cirema yara pampers ko Ronensu su kuma suna ta aikin yi Cake da Donut da meatpie,suna ta sakawa cikin Takeway wanda za"a raba gobe wajen Walima ga Drinks nan da Ruwa cikin Falon Aba na Hidima da Rabo banda wanda ke chan Gidan Baba Mallam rabawa akayi nan ana Snaks gidan Baba Mallan suna gyaran kayan Miya na abincin da zasu yi su ya Jaleela kuma ana fama da suyan kaji da Nama.
Sakina dai bamai ganinta tana Shashen Anty Amarya ita da Sarood ko aiki batayi ba kuma wanda ya Damu duk da itama chan gidansu akwai Biki Tunda yayanta da suke Uba Daya Sadiyan zata aura.
*Janafty*
*TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*
*Sadaukarwa ga Halima yusuf gwarzo (Besty) Alherin Allah ya kai miki har inda kike*
_Ya Allah ina rokon ka da ka Saukar da Farinciki,salama da kwanciyar hankali Da Aminci, zaman lafiya Da kaunar juna,sadaukarwa da yarda da,kima da mutumtawa, martabawa agidan auranki *AISHA ALTO* (Sisina) Allah yasa,kin shiga a sa"a Allah yasa gidan zamanki ne na har Abadan Da"iman Ameen_
*🅿️11*
Amina ta gaji da sakasu Reno ya"yan da ake yi ko kuma dawainiyar Cire pampers duk wanda Yarta ko D'anta yayi kuka su ake kwalama Kira su zo suyi Dawaniya Hamida da Hanne basu nuna gajiyawarsu ba sai Amina Domin ta tsani in ana sha"ani a Rika nuna su yara ne basu isa komai.
Dalilin haka yasa taja su hanne suka koma Chan koridon gidan wajen Dakunan da su ya Jafar sukayi zama Tun suna matasa sai ya zamana nan Aba ke sauke yan"uwansa maza in sun zo Daga gusai ko wasu baki dai Dakunan duka akwai Cafet da katifu aciki Wannan karon ma nan yan gusai suka sauka matan mazan sai Ranar Daurin aure zasu taho.
Cikin guda Daya su Amina ke kwana Tunda Dakinsu su ya Jaleela sun zo sun koresu chan gidan baba Mallam ma ko"ina ya cika Tunda kowani Shashe cike da yake da baki Daga Duka bangaran matan kowacce Danginta sunzo Shashen Hajiya ba matsaka Tsinke cike Taf da Danginta na Maiduguri.
Nan Amina ta jasu suna Fira Yawancin Firan Labarin Littafan Hausa ne da Amina ta smu yar"uwan yi suna ta Hiran Zafira D'iya take wajen Aba tunda Babbar diyar goggonsa ce Sa"aninsu Amina ce koma nace kawarsu ce suna Dasawa da ita Saboda indai Mamata mamanta zata zo da ita take zuwa itama ta fara karance karancen Littafansa Hausa shine suka Hade da Amina suna ta Labarinsu Hanne da Hamida Tagumi kawai sukayi suna kallonsu suna mamakinsu.
Amina ce ta kalli Zafira tana Fadin"Kin karanta garin kallon Ruwa...?Labarin Faruq da khaleesat..?
Hannu Zafira ta bata suka Tafa Lokaci Daya tana Fadin"Kai kai..Na karanta wannan Littafin yayi Amina..Salon soyayyar Faruq dabam ce..!
Tare suka saka Dariya Hamida ta tabe baki tana Fadin"Ke Zafira a ina kike samun Littafan nan kina karantawa..?ammh Mamata bata sani ba ko..?
Zafira tace"Anty Aina take dasu..In ta ijiye sai na sata na karanta kuma ina aron wasu a makarantar mu..!
Amina ce tace"Hamida munafuncinki ya baci..To bata Sani ba ko zaki je ki Fadamata ne..?
Hamida tace"Ina Ruwana..?ammh aikwai ranar da Dubu zata cika..Nama fi Tsausayamiki yadda su ya Jafar zasu Bandashenki Domin sai kin Daku Abunda ko Lokacin su ya Jadwa basu yi wannan karance karancen ba Sai ke..!
Amina ta daka wani Tsaki kafin ta Tabe baki tace"In sun kamani kada su bar ni da Rai kin ji Hamida..? Ni fa bana son munafunci malama in kina son Fada musu ai ba sai kin zo kina wani Yadamin mgana ba ke bazan Fasa Karatun ba yanzu na Fara in ma baki je kin Fada ba sunanki ba Hamida .!
Tafada tana kumfar baki ganin Abun na neman zama fada Hamida na Fadin"Da ina son na Fada da Tuni an wuce wajen kema kin sani..! Kawai gaskiya nake Fada miki..!
Amina tace"Munafunci ba..Kin Saba..Hamida ki kyeleni ko?ance ba"a son gaskiyan ko Dole ne..?
Ni bana son sa"ido kowa yaji da kansa mana .!
Hamida zatayi mgana Hanne ta Tareta da Fadin"Kyaleta Hamida..!
Hamida itama ta fara harzuka cikin Daga Murya ta fara fadin"Saboda me .?Saboda ita tafi kowa sai ta rika yadda taga dama ana kyaleta..?ai ba wani abu nace ba Fadan taso kanta nayi mata ina amfanin karatun Littafan da takeyi..!alhalin bata maida hankali a duka karatunta da zai amfaneta watarana..Ammh da anyi mgana sai ace a kyaleta to bazan yi Shuru ba nima yau ina daidai da Jidalinta Wlh..!
Ta karishe Fada tana Hararan Aminar Dake kallonta kamar taga Kashi.
Kafin ta yi Dariyan gefen baki tace"ban fi kowa ba Hamida..Ammh ni Dake ba Daya bane .ke sunanki Hamida ni kuma Amina nake..Ance ba"ason gaskiyan ko ana Dole ne..?ke wai ina ma Ruwanki da Rayuwata ne. ? anki a Tsaya ayi karatun sai me..?har kina Fadin zaki iya da Jidalina na Rantse da Allah baki da wannan Juriyan da zaki iya dani in kuma zaki iya Bismillah..!
Ta Fada Lokaci Daya tana Chakumo Wuyan Hijabin Hamida suka Mike Atare Hamida ta Zuciya zata rikota Hanne da Zafira suka Tareta suna Fadin"Amina saketa..!
Amina na Hararanta tace"Ku gayamaya ta daina Shiga harkata..ana Dole ne nace ta kyaleni ko..?
Hanne tace"taji..Saketa..dafa mutane acikin gida in akaji fa kina ta Daga Murya.
Amina ta Saki Hamida tana Fadin"Aji mana..Sai mene..?
Daga bayansu sukaji ance"Meza"aji din..?
Gabadayansu suka juya suna kallon mai mgana Anty Shamsiya ce matar ya Jafar Tsaye daga Bakin koridon Daga alamu bayi zata shiga Domin ga Buta nan a Hannunta da Katon cikinta agaba tayi wata katuwa ba kyan gani.
Amina Tayi kamar bata ganta ba ta Juyar Dakai Hanne ce tayi saurin cewa"Bafa komai Anty Shamsiya..!
Tana kara nazarinsu tace"Fadan da kuka saba kuke yi ko..?
Da sauri Zafira tace"Wlh ba Fada bane..!
Kai Tsaye tace"To tunda ba Fada bane ku zo ga aiki..Daman tun dazu Jaleela ke nemanku zaku Daukar mata Walid ya hanata aiki Zahra ma sai Cigiyarki take ashe ku gaku anan wajen..!
Amina Sai hararanta take ta kasan ido ita ko Fadi take"oya ku zo ku wuce..Zahra ai ga su Hannatun nan fa...?ana ta nemansu..!
Ta juyatana fada daga Cikin Gida su Hamida sun tafi Amina na wajen taki Tafiya Shamsiya ta kalleta tana Fadin"Ke da kike Tsaye fa?
Amina ta Tura baki cikin kunkuni tace"Kiji da kanki dai da wani katon bakin ki..!
Tana kallonta yasa tace"Badai zagina kike yi ba ko Amina..?
Da Sauri Amina tace"ni..?cewa fa nayi gani nan zuwa..!
Kwafa tayi kafin ta juya tana Fadin"Kada ma kizo..Jaleela gafa Aminar nan taki zuwa kinsan ta batasan aiki..!
Amina ta Mele baki tana Fadin"Ai ni ba Jaka bace..!
Su hamida sun shiga cikin gida yasa ta bisu jin Ya Jaleela sai kwala mata kira take yi tana shiga taga an saka su Hanne Wanke wanke mai uban yawa Daga nan ta Tsaya afili ta Furta"Jaruba..Kamar wasu jakai..!
Bata gama Rufe baki ba aka Rankwasheta asaman kanta Dafe kan tayi tana kallon Ya Jaleela Dake Tsaye kanta Da yaronta Walid a hannunta.
Mika mata shi tayi tana Fadin"Ke da ba Jakar ba..Karbesa ki cire mai pampers ki wanke mai ina ga ya batashi ne kije Dakin mamanmu wajen kayana ki Bude karamin akwati zaki ga kaya da pampers ki Sakamai ki goyasa sai rigima yake min..!
Amina bakinta kamar zai Fado Saboda Takaichi hakanan ta mika hannu ta karbesa yadda take yi ne yasa Jaleelan kallonta tana Fadin"Kada ki kadamin da yaro..Nasan Zafinsa ko bazaki yi bane..?
Amina Dakyar tace"ni fa ban ce bazan yi ba..!
Jaleela tace"Au naga kina neman min kuka ne..?daman baki iya komai ba Mamanmu ta gama bataki..!
Ya Jawahir Dake kusa dasu tana Bare leda tace"Kamar kin sani Allah yasa ta iya ma saka pampers din..?Dama Hamida kika saka ko hannatu.Amina kiyuwarta da son jikinta bai barta ta iya komai ba..!
Jaleela ta kara Dungurinta tana Fadin"Sai kazanta..da Rashin kunya zaki wuce kiyi abunda na sakaki ko sai na mareki..!?
Acikin kunkuninta tace"Ni ba kazama bace.Haka kurum ko da haihuwa ni nayi ta wahala da yara..!
Suna ganin tana mgana Jaleela tace"Me kike cewa ne..!?
Wucewa tayi tana Fadin"Ni ban yi mgana ba..!
Hanne da Hamida suna Duke suna Dariya kwafa tayi ta wuce wajen Bayin waje ta dukar da yaron da bai wuce shekara Daya da rabi ba ta Zare mai ido ganin zai fara kuka tace"Kai kama bakinka..bar ganin idon uwarka Wlh kana min kuka sai na Dirkeka..!
Tafada tana Zaremai ido kamar yasani sai yayi Shuru kwafa tayi tana Fadin"Shegen yaro mai kama da Ubansa..!
Tana Ciremai pampers din tana Ta Mai masifa ubansa ya sha Zagi harda uwar ma,Amina Fadi take""Kun iya haihuwa..ammh bakusan yadda zaku reni ya"yanku ba Amina ai ba Jaka bace..!
Inda Allah ya taimaka Fitsari kadai yayi aciki a Bola ta watsashi Tana Fadin"Allah yaso ka..Da kayi kashi Wlh bazan wanke maka ba..Sai da na Sake nadeka dashi..!
Ko Tsarki batamai ba Ta Daukeshi Fuu Sai Dakin mamanmu Dayake suna ta aiki ba wanda ya Lura da ita Tana shiga ta Dungurar dashi a kasan Cafet ba kowa afalon Yasa ta Zare mai ido tana Fadin"Kai zauna anan..In ka sake ka tashi sai nayi wuji wuji Dakai..!
Gwanin Tsausayi haka ya koma ya Zauna yana so yayi kuka Lekowa tayi taga hankalin kowa baya kanta ta bar Walid chan ta sababo wajensu Hamida Daidai kunnenta tace"Ku taso mu gudu..!
Hamida ta kalleta dasu Hanne da Sauri tace"Wannan uban wanke wanke yaushe zaku gama..?ai biki suka zo su yi aikinsu ne nidai kunga tafiyata in kuna son kuyi ta aiki ku zauna..!
Tafada tana wucewa ba wanda ya Lura dasu domin yammah ta Farayi suna ta aikinsu.
Zafira ce ta fara tashi tana Sake Hijabinta Data Daure Lokaci Daya tana Fadin"Amina jirani muje..!
Daman ita ke wankewa Hanne da Hamida na Daurayewa ganin sun wuce yasa Hanne ta kalli Hamida tana Fadin'"Mu bisu Hamida in muka Tsaya Laifin duka zai shafemu..!
Ba musu suka Tsame hannunsu Daman da Hijabansu ajikinsu,Su Amina sun riga sun fita daga Tsakar gidan su Hanne Jawahir ta Hanga da Sauri ta fara kiransu"Kai ina zaku kuma..?kun gama aikin ne..?
Ai ina kafa mai naci ban baki ba su Amina Dake jiransu ganin suda gudu yasa suma suka Ruga Jaawahir ta saka Salati tana Fadin"Yaran nan basu da mutumci sunbar aikin sun gudu..!
Zahra ce ta jita tace"Amina ce zata ce su gudu..ammh Hamida da Hanne basu da kiyuya.!
Jawahir tace"Amina na Dakin Mamanmu tare da Walid..!
Bata rufe baki ba Mamanmu ta Fito da Walid a hannunta tana Fadin"Jaleela garin yaya ki bar walid a daki shi kadai sai faman yanka ihu yake..?
Zahra suka kalli juna da Jawahir kafin Tace"Daman na Fadamiki..!
Jaleela nachan suna aiki Saka Abu a Takeaway aka mika mata Walid ta karba Tana Fadin"Sai naci uban Amina Wlh..!
Zahra tace"Inda kika ganta ba..ai sai ma kin ganta sannan kici uban nata..!
Gabadaya Dariya aka saka ana Fadin Halin Amina sai Allah ya Shirya.
Su basu tsaya ba sai da suka fita Daga gidan sannan suka Tsaya suna Haki Hanne tace"Ya Jawahir ta kamamu tana ta kiranmu muka gudu..!
Amina tayi Dariya tace"da kun tsaya..!
Tafada daidai Lokacin da sukaji Hayaniya suna juyawa suka ga ashe Karatun Baba Mallan ne aka tashi Maza sun fara fitowa daga masallaci.
Hamida ta zaro ido tana Fadin"Mu shige gidan Baba malman gasu ya Jafar nan sun fito masallaci kunsan in ya gammu a waje sai yayi mana mgana..!
Amina tace"mu tafi gidan su ya jafar inda su ya zulaiha suke muga abunda suke achan..!
Dukkamsu sukayi Shiru suna kallon Amina kafin tace"Dilla mu bi ta nan baya bamai ganinmu..!.
Jin haka yasa suka yarda nan da nan suka Zagaya suka bi ta baya suka fara Tafiya akuyan Daure ta samu Sake sun san gidan Dayake ba wani Nisa Sosai a kasa sukaje sai gasu abakin get din gidan Amina ta fara buga get din gam gam..gam gam.kamar zata Fasa kofar
Daga chan sukaji Muryan Abida tana Fadin"Waye haka..?ana zuwa kada ya balla get din..!
Ido suka gwalo sun san Halinta kafin suyi mgana ta Bude get din Tana kallonsu tasha kunshi ja hannu da Kafa Hararansu ta farayi Daya bayan Daya kafin tace"Daman Araina sai da naji kune..To kuma uban me kuka zo yi..?ko nan da sa"anninku ne..?
Amina tayi Saurin cewa"Mufa mun zo muga amare ne..!
Abida ta ballaa mata Harara kafin tace"ku musu mene..?kaji min yara da iyayi to bAzaku shiga ba ku juya ku koma..nasan ba wanda yasan kun fito Daga gida..!
Hanne tace"Muna ganinsu zamu tafi ko Amina..?
Da Sauri Amina tace"Eh Wlh..muma kinga basai amana irin kunshinki ba..ko Hamida..!
Gabadayan su suka amsa Domin su ba wanda yabi ta kansu ma mganar kunshi gwara Hanne da Hamida suna ma kansu Amina kuwa sai dai in Mamanmu ce ta kamata ta kunsa mata.
Abida ta Daure Fuska Kafin tace"To wlh bazaki shiga ba irin lalle na ko..?ni sa"arku ce..?kuna yara da ku sai son shiga cikin manya dillah ku wuce ku bama mutane waje..!
Amina ta tura baki kafin tace"To mu leka..!?
Abida tace"To leka..!.
Da Sauri Amina ta Zura kai ta wajen Hannun Abida Data Bake get din zata Leka taji ta Daketa abaya Dayasa ta Dawo da kanta da Sauri Abida tace"Matsa ku bani waje..Marasa kunya kawai ba sa"anku anan..!
Tana gama Fadin haka ta fara kokarin maida get din Amina ta kalleta tana sosa inda ta Daketa da karfi tace"Dadin abun ai ke ba Amaryan bace Ehe..!
Tana gama Fadin haka ta Zura da gudu su Hanne suka mara mata baya Abida ta saki baki tana kallonsu afili ta Furta"Yaran nan sun bala"in Raina ni..!
Kan bala"i zamu hadu ne duk sai kun ci ubanku..!
Tafada kafin ta maida get din ta Rufe suna Shashen ya jafar ne suna ta Hayaniya amaran Dayake Duka yan"uwan Hajiya daga Maiguduru ne sukayi musu Lalle da Kitso da kuma gyaran jiki nan suke kwana Anty Shamsiya yau chan gida zasu kwana ita da Fadila.
Daganan da suka fito sai da suka kusa gida suka Daina gudu suka Duka suna Hutawa Amina ta Dago tana Haki tace"Ya Abidar nan muguwar yar bakin ciki ce..!
Ta hanamu shiga mu gani ance ana ta mu su gyaran Amare..!
Hanne tace"Eh su yakura ne fa suma tun ranar da sukazo hajiya ta turosu nan..!
Amina tace"Ai dai zamu gansu gobe duk Tsiyanta nifa daman tunda naji muryanta nasan sai ta bamu mtsala..!
Zafira tace"bata da kirki ne..?
Amina ce"Ko kadan..Bata da mutumci ya Abida kina ganinta haka..!
Gabadayansu dariya suka saka Amina ta Cigaba da Fadin"Ke kinga gidansu Hanne..?Kaf ba mai mutumci yasin..!
Hamida tace"Kai Amina ga ya D'anmalam ai bai taba Dukanmu ba..!
Amina tayi jim kafin tace"Shi kuma wannan dama dukan yake yi da Mganarsa..!
Hanne da Hamida suka Kalli juna suna Danne Dariya Amina ta gansu ta Hararesu tana Fadin"Munafukai..!
Zafira tace"Me ya faru ki bani labari..?
Da Sauri Amina tace"Wlh kuka Fada mata sai nayi muku Rashin Mutumci..!
Dariya suka kara saka mata ta kwalo musu ido Zafira na magiyan su Fada mata Amina ta Faki idonsu tace"Wayyo bayanku maciji..!
Ai bata gama Rufe baki ba suka Zura aguje tabi bayansu tana Dariya.
Allah ya taimakesu sanda suka Dawo an shiga Sallar mangariba sai suka Lallaba suka Shige gidan Baba Malam.
Shashen Hajiya ba waje duk ya cika duk da wasu suna Kitchen din gidan suna ta soyan kaji su da su Baba Lami yan aikin gidan.
Karsahenta dai Shashen Hajiya uwa suka Shige sukayi salla adakinta ita bata ma nan tana Shashen Hajiya taje suna mgana..
Sallar kadai sukayi suka Fito su leka chan su leka chan har shashen Anty Amarya sai da Amina tace suje saboda tana son ta kara ganin gulma
Akwai suna shiga suka iske Sakina da Sarood zaune kugu Daya Jidda na Kan Cafet tana ta Hada Turaran wuta da Sabulun Salo cikin wasu kananun Robobi ita da wasu Daga cikin Dangin Anty Amarya..basu ga Sa"adatu ba bata nan tatafi kunshi an samu Sake.
Hanne ne kadai da Hamida suka gaida su Sakina banda Amina Data yi keme keme Anty Amaryan bata Falon.
Anty Sarood ta ganesu tana ta yi musu Mirmishi.
Sakina taga Amina na wani kallonsu Daya Daya yasa tace"Ke..Baki da kunya ko..?
Baki iya gaisuwa bane..?
Amina ta yamutsa Fuska kafin tace"Na gaisheku..!
Sakina tace"Karya kike..Hanne kadai da Hamida suka gaishemu da wannan yarinyar..!
Ta fada tana nuna Zafira.
Amina ta Tura baki batayi mgana ba Jidda ta dago tana kallonta Kafin tace"Wai Amina daman baki daina wannan Rashin ta idon ba ko..?ko ni ai baki gaisheni ba..?
Amina ta yi wani jim kafin tace"Ina yininku..!
Daga haka ta juya tana Jan hannun ZAafira Dake kusa da ita.
Sakina ta rike baki kafin tace"'Yarinyar nan bata da kunya..!
Amina na kunkuni tace"Eh din ai na gaisheki tunda kuma ba Duka miki zan yi ba..!
Da karfi tayi suna ji ta fice Jidda ta girgiza kai tana Fadin"Kamar ba yar gidan Baba Sa"iduba kaf ya"yan gidanan ta fita zakka..Allah ya shirya..!
Sakina batayi mgana ba baki kawai ta Tabe ta juya tana ma Sarood mgana Wacce ta maida hankalinta Sakina na jin Labaraci tun anan balle kuma Da suka koma chan Zama da Larabawan yasa yaran ya zauna mata sosai.
Kitchen suka shiga suna neman abinci sun samu Jallop din shibkafa da aka Dafa da Rana.
Amina idonta na kan manya manyan Baho cike da Naman kaza da Naman rago duk am soya Amina da nama Tuni Ranta ya biya.
Akitchen din sukaci abinci suna cikin ci Amina tayi ma Hanne Rada"Yasin sai na saci naman chan..!
Hanne tace"In aka kamamu fa..!
Amina tace"Dillah bamai ganinmu..!
Har suka gama cin abinci Amina na Tunanim mafita Su baba Lami na Kitchen da sauran mutane suna ta aiki kowa Hankalinsu baya kansu Anty Nasara ce ta shigo ta gansu yasa tace"Me kukeyi a kitchen..?
Kuje waje mana ku sha iska..!
Dole suka fice Hanne nama Amina Dariya ita kuma tayi Fuska
Shashen Hajiya suka koma suka samu chan gefe suka zauna bama wanda ya Lura dasu Amina aranta tana Takaichun yadda in ana sha"ani bamai bi ta kansu aranta tace ai suma sun girma sun wuce yara yanzu.
Suna nan har akayi sallar Isha"i suka tashi sukayi salla.
Sai alokacim Hajiya ta gansu tace"kuna nan ashe..?na zata kuna gidan Sa"idu ne..!
Hanne tace"Tun dazu muna nan..!
Tana Sauri ne ana mata mgana yasa ta wucesu Amina tace"Kowa baya bi ta kanmu..!
Hamida tace"Wlh fa kallemu kamar wasu almajirai..!
Amina tayi dariya kafin tace"Almajiran ne mana duk inda mukaje ana koranmu..!
Hanne ce ta ma Amina Rada a kunne tana Fadin"Kin fasa satan naman ne..?
Amina tace"A"a
Ku tashi muje..!
Haka suka sake ficewa Kitchen din Amina ta leka taga ba kowa sai su Baba lami su kuma suna ta Hidiman yanka Albasa suna Hira Amina ta yafito hanne tana Fadin"Ku tafi daga chan..Ni zan shiga na Debo mana zan taho..!
Hanne ta mika mata wata bakar Leda Data Dauko daga Dakin Hajiya tace"Zubo mana anan..!
Zafira ce tazo zatayi mgana Amina ta mata alaman tayi shuru Hanne ta mata rada tana fadin"Ke nama Amina zata sato mana..!
Zafira tace"Yauwa daman wlh tun dazu miyauna ya tsinke..!
Amina ta Sadada ta shiga kitchen din ta Duka ta Bude ledan ne ta rika Zuba Nama Har sai da ta Kusa Cika Hanne da Zafira suna daga bakin kitchen din suka hango Anty Amarya zuwa da Sauri Hanne tace"Amina Ga Anty Amarya nan ki taso..!
Jin haka yasa ta taso da gudu su kuma sun riga sun ruga har tana bangaje Anty Amarya,Da tayi baya tana Fadin"Ke ke..Waye anan..!
Ina Amina bata tsaya ba sai Aharaban gidan inda su Hanne ke jiransu Anty Amarya bata ga Fuskar Amina ba.
Ta shiga kitchen tana yi ma su Lami Fadan suna barin yara na Shigowa.
Haraban gidan akwai haske tunda an kunna Gen yasa Amina ta jasu suka shige wani dan lungu Dake Wajen kofar Shiga Shashen mallan da dan Duhu kadan suka ZAuna Amina ta Fito da Naman Hamida ta zaro ido tace"Amina kin Debo da yawa in aka gane fa..?
Amina ta tura wani nama bakinta Tunda naman sa ta Debo na kajin suna kusa da Baba lami yau gidan Gonar Baba malam yasha Diban kaji da Shanaye.
Sai da ta cika bakinta sannan tace"Dillah kefa kin cika tsoro..Abu da yawa wazai gane..?
Zafira ta mika hannu zata Diba Amina ta make hannunta tana Fadin"Kada ki samin hannu ko na Hanaki wlh..!
Jin haka yasa ta Dakata Amina ta Dauki Tsoka Hudu hudu ta basu Ta bama Hanne Biyar ta Dauki Sauran tana Fadin"Mai sata ke da wannan..!
Hamida tace"Kai Amina naki yafi yawa..
Amina ta balla mata Harara tana Fadin"To Sarkin korafi..Dayake ke kika je kika Debo naman..!
To wannan ma in baki so bani kayana..!
Tafada tana mika mata hannu Hanne tayi Saurin cewa"Hamida karbi abunki..Mun ji Amina tunda ke kika Debo Dauki wannan..!.
Amina ta murguda baki kafin tace"ko baku yarda bama..In mutum yaji Haushi yaje ya Debo nasa. !
Hamida tasan da ita take yi ammh bata tankata ba suna cin namansu Zafira ke fadin"Wai shanaye nawa aka yanka da kaji..!
Duk gidajen nan fa akwai Nama ko"ina ka shiga. !.
Amina tace"Waya sani Zafira..?kila sun kai dubu kajin Shanayen kuma kila goma..!
Tafada tana Tura naman bakinta Hamida tace"Haba inaga ma sun fi..Kinsan in ana Biki haka ake ta Yankosu ana shigowa dasu..!
Zafira tace'Cab...ai gidan Gonar ta kare..!
Amina tace"Ke..kina da Hankali kuwa..?Kinsan adadin Dabbobin Dake gidan gonar nan ta baba malam..?
Ke babban waje ne fa na taba gani a Wayar Ya jafar da yazo yana nuna ma su Mamanmu na rantse da wanda Raina ke hannunsa gari guda ne..!
Hanne ta karbe da cewa"To yaushe zamu je mu gani..?bamu taba zuwa ba..?
Amina tace"Kuma fa hakane..?to ammh Aba chan yake zama fa..?ya zamu yi mu je chan Hadeja Road ne fa..?
Hamida tace"Nidai ba ruwana..!
Amina tace"Sai me..?ke dai kin cika Tsoro..Hanne bari nayi shawara na Rantse koda bala'i sai mun je mun gani ko da zamu dawo a yankamu ne..!
Hanne tace"A"a fa ni wasa nakeyi..!
Amina tace"Ke fa sai an je..Inaga ma gobe saboda bama wanda ya Damu damu..!
Hanne zatayi mgana kenan sukaji mgana a kofar Falon Baba maallam gabadayansu suka Leka suna ganin Ya Uzairu ne ya fito Daga Falon mallam din Bayansa ya Shamsu ne sun saka Takalmansu sun nufi barayin da Dakumansu suke
Amina ta juyo tana Fadin"Jaruba..Daman ya Uzairu ya Dawo ne..?
Hanne tace"Eh mana tare suka zo da Ya Zulfa..!
Amina tace"Harda Ya Nazem..?
Wannan karon Hamida ce tace"A"a shi naji Ya Zahra na fadin sai gobe yace zai taho yana da Karatu gobe..!
Amina tace"Mugayen gidan.com zasu Taru Lokaci Daya bala"i..!
Hanne tana Danne Dariyanta take Fadin"Har na tuna ya Nazeem sanda ya miki Dukan Tsiya Lokacin muna aji hudu kin Tuna. ?
Amina tace"Kan bala"i ina zan mata..Ranar ai mariya na Tsungula ya kamani Shine ya fitar dani gaban aji kusan awa daya nasha ya manta dani ne na Daga Murya nace Tattasan da ka shanya ya isa Bushewa sai kazo ka kwashe..!
Gabadayansu suka saka Dariya Hamida tace"Kin ga kwashewa kuwa..Amina kin Daku fa hannu. Ya Nazeem..!
Amina ta Ciji yatsa Kafin tace"Kuma Wlh har yanzu ban yafe ba Wuta bal bal har kabarinsa..!
"kai su waye anan..?
Mganarta ta Katse ne sanda aka Dallaresu da Filita Lokaci Daya da mgana suka Tsorata gabadayansu sukayi Tsumu Tsumi.
Ya Uzairu ne zai fita shago ya Siyo katu yaji mgana daga bayan shine ya Haskasu da wayarsa.
Karisawa yayi gabansu yana kallonsu Daya bayan Daya ya ganesu mamaki ya kamashi me suke anan..?
Cikin Tsawa yace"Su waye anan..?
Hanne ce baki na rawa tace"Mune ya Uzairu..!
Amina kuma namanta take kullewa a leda yace"Ke miye wannan..?
Daidai Lokacin da su ya jafar suka fito daga Falon Baba Malam daman tun Fitowarsu masallacin Sallar isha"i suka Dumgumo suka shigo.
Bayansa Ya Nasir ne sai ya Da'nmalam Daya fito Daga karshe.
Jin mganar ya uzairu yasa Ya jafar Daya sanya Takalminsa yake fadin"Kai Uzairu lafiya..?kai da su waye..?
Juyowa yayi yana fadin"Wlh yaya zan wuce naje siyan kati naji mgana ta nan ina Haskawa naga yaranan bansan Uban da sukeyi anan lungun ba Cikin Duhu..!
Dukkansu matsowa sukayi shi da Ya Nasir banda Ya Danmallan Dake gefe yana Danna Wayarsa.
Gabadayansu suka Haskesu da Fitulan wayarsu Ya Nasir yace"Lalle nema yaranan to ku fito don kaniyanku..!
Ba musu suka mike suka firfito Amina ce ta karshe tana Boye abunda ke hannunta ya Uzairu ya jawota yana Fadin"Bani abunda kike Boyewa..?
Baki ta Tura kafin tace"Bafa kom..!
Bata karisa ba ya make bakinta yana Fadin"Bani kafin nayi kasa kasa Dake mara kunya..!
Hannunta Dafe da baki da mikamai ya karba Daidai sanda Ya Jafar ke fadin"Me kuke yi anan da Daddaran nan..?
Gabadayansu sun kasa mgana Ya Nassir ya fara Duba bayansa yana Fadin"Inaga sai sun ji ajikinsu..Kai shamsu Dubamin Sanda don Allah..!
Ya karishe Fada da karfin daya Janyo Hankalin D'anmallan kansu ya Zura wayarsa gaban Aljihun farin yadin dake jikinsa Riga da wando.
Shamsu Daman tun farko ya fito jin haka yasa ya shiga Dakinsu ya Fito da wata Bulala mai kyau katuwa da ita ta duka yaran mutane A islamiya
Ai Hanne da Hamida na ganin ya mikoma ya Nasir har ya Fara Nade Hannun riga suka Duka harda Zafira Data fara fadin"Wlh ba komai..!
Sai kuka ya Uzairu ya Bude ledan sai ga Nama da Sauri yace"Ya jafar nama ne aledan nan..?
Gabadayansu suka ce Nama..?
Cikin mamaki Har da ya D'anmallan Daya kariso wajen basu sani ba.
Da Sauri zafira tace"Eh nama ne..Dama Dama..Amina ce ta sato a Kitchen shime muka zo nan ta san mana muna ci ammh Wlh bamu yi komai ba..Amina ce ko Hamida..?
Hamida da Hanne sun kasa mgana Amina na Tsaye ko gizau.
Ya Jafar yace"ai ta saba indai Satan Nama ce..Amina ta saba..!
Ya D'anmallan sai Lokacin ya Fahimci mganar ya kuma kare ma su Amina Dake wajen kallon idonsa ya Fada kanta yadda take wani Juya ido.
Aransa yace"Again..?satan nama..?
Meke damun yarinyar nan..?
Ya Nasir ya kalli Amina yana Fadin"Anan gidan ne kike mana Satan nama..?kin ce abaki an hanaki ne..?
Ya karishe fada cikin Tsawar dayasa Baba Mallam da Aba Dake cikin Falon zaune suna mgana sai da sukaji.
Amina kuwa baki ta Murguda kafin tace"Ni ba barauniya bace..Ba sata nayi ba..!
Ya Nasir yaga sanda ta mai haka yasa ya Daga Bulalar ya Shimfida mata yana Fadin"Karya zan miki..?kuma ni kike juyama baki zaki gane yarinya kwana Biyu jikinki na kaikayi..!
Ya Jafar yace"Dake ta shegiya bakinta baya mutuwa..!
Amina ko ko gizau ya kara Lafta mata wannan karan da karfi tace"Ai ba Sata nayi ba..ni ba barauniya bace..!
Dukanta yake tana mgana su Hanne sun koma gefe har sun fara Hawaye..
Ya Danmallam mamakin Taurin ran yarinyar yake ganin da Har yanzu ko Dukawa batayi ba kuma bakinta bai Daina mgana ba
Su ya shamsu na gefe suna Dariya.
Ya Danmallam yaga dukan yayi yawa yasa yace"Kai Nazir bar dukanta hakanan mana..!
Ya Jafar yace"Ka bari ya Daketa baka ga bata da kunya ba ai tare sukayi Laifin da yan"uwanta meya su ba"a Dake su ba..!
Sai ya kasa mgana Idanuwanta yake kallo ko kwallah basu Tara ba kuma bata tare dukan ba,Idonta kyam ba ko alamin nadama ballatana ta bada Hakuri.
Yana auna Shekarunta ne har ya isa ta Zama kangararriya irin haka..?
Yana cikin wannan Tunanin yaji mganar Baba Malam a sama yana Fadin"Kai kai Nasiru..Kaga naka nan..?ka samu jaka ne dake dukanta kamar ka samu namiji Dan"uwanka..?
Sai Lokacin suka Lura dasu shi da Aba suna Tsaye ran Malam ya baci da azama ya kariso wajen Har Alkyabban Dake jikinsa na neman Rinjayansa.
Gaban Nasir ya tsaya ya Fizge Bulalar yana Fadin"Sau nawa zan gaya muku ba kyau Horo da duka..?Wlh banta Hora ku da duka ba sai Nasiha mai yasa kuma bazaku yi haka ba..?
Ya nasir kansa na kasa yace"Baba ra..!
Hannu ya Dagamai Lokaci daya yana Fadin"Bana son jin komai..Bana son Sarkaci kai Umar agabanka suka Tasa yarinya karama da duka baka Tsawatar musu ba..!
Danmallam ma ya kasa mgana Dakyar yace"Kayi hakuri Baba..!
Aba Dake gefe yace"Baba da barsu sun mata Hukunci Amina ce..Amina ai bata jin mganar kowa..!
Aran Danmallam yace"Kenan ta gagara..!
Baba Mallam ya Dagamai hannu yana Fadin"Kaima ka fita idona Sa"idu..!
Jin haka yasa suka fara basa Hakuri ko kallonsu bai yi ba ya Juya ga Amina Data ga Baba mallan ta fashe da kuka Tana Fadin"Ce min fa yayi barauniya Baba..Ni kuma bana sata Daga na Diba naama shikenan..!
Baba malam ya rikota yana Fadin"Bai kyauta ba..Mamata ai ba ta sata..Kuma naman da kika Diba ai na Gidanku ne ba wanda ya isa ya hanaki daina kuka Share hawayenki kinji..!
Yana Fada yana goge mata Hawaye Ya Danmalam mamaki ya cikasa ya Tabbata ko cikin kannensa bai taba ganin Baba mallan yayi ma wata haka ba..Kenan ita wannan Dabam take.?
Su ya jafar ko basu yi mamaki ba sunsaba ganin haka.
Har su hannen haka ya taso su ya Damka musu Amina yana Fadin ku shiga Cikin gida..!
Amina tace"Gidanmu muke kwana nan ya cika..!
Baba mallam ya kalli su shamsu kafin yace"Ku rakasu sai kun tabbatar da sun shiga gida kana ku dawo..!
Hakanan basu so ba suka tasa su Amina suka rakasu gida ya shamsu kam harda Tsaraban rankwashi.
Baba malam bai Tsaya Sauraran ban Hakurin su ya jafar ba ya koma Falobsa Ransa bace.
Aba ya Sauke Numfashi yana Fadin"Ku tafi gidajenku..Yau baba malam ransa ya baci..An taba Amina..!
Ba wanda yayi musu suka juya wajen Motocinsu ya Danmallam dai na tsaye aransa yana ayyana wasu abubuwa kafin ya Tabe baki kawai.
Don Allah mu ding yi ma junanmu Uzuri kusan hakan nan ba zan ki Typing ba sai da wani Dalili Biki naje bani agida sai jiya da yammah na Dawo bana cikin Natsuwar da zan iya Rubuta wani abu shiyasa aka samu Tsaiko..!
*Janafty*
*TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*
0 comments:
Post a Comment