Suna shiga Dakin Zafira ta yaye Hijabin Jikinta ta zauna Dabas kan Cafet din Dake Dakin ta Dago tana kallon Amina Dake Tsaye kyam takaicinta Daya yadda Ya Uzairu ya karbi Namanta bai bata ba Shi yafi kona mata zuciya ba Dukan Ya Nasir ba.
Zafira tace"Amina ke kam baki jin Duka ne..?
Amina ta wani kalleta a kaikace kafin tace"Me kika gani..?
Zafira tace"Gani nayi kina Tsaye sai Dukanki ake yi ko kiyi Tunanin Guduwa ma ballatana ki bada Hakuri..!
Hameda da gajiya yasa har ta kishingida tace"Tab Aminan ne zata bada Hakuri..!ai mutun Daya Amina na taba ganin ta bama Hakuri..!
Hanne na gefen ta ta karbe da Fadim"Yaya..Yaya ce kadai Amina ke bama Hakuri bayan ita ko Aba Tsayen nan take mai .Zuciyarta kamar ta Kafuran Farko..!
Zafira ta jinjina kai kafin tace"Tabdijam Haka kurum na zauna ayi ta Jifgana kamar wata Jaka..!
Amina ta Daga idonta Sama kafin tace"Duka ai baya kisa..Daya na kisa da Tuni ba Sauran Amina Zafira..Sannan mganar na bada Hakuri ma bai taso ba..Me nayi..?Amina bata bada Hakuri matukar tasan ita keda gaskiya..!
Zafira tace"Uhmm..Ko dai aljanu gareki. ?su suke saka ki wannan Taurin kan Amina..?
Amina ta mata kallon Tara sau ra kwata kafin tace"Sai dai in naki ne suka Dawo kaina yanzu .!
Da Sauri Zafira tace"Ni bani da Aljanu..!
Amina ta tari numfashinta tana Fadin"Nima haka..!
Daga haka ta samu chan Lungu Bayan ta Nanannde Hijabin jikinta tayi matashi Dakin ba Katifa Cafet ne kawai sai tarkacen kayansu da suka Kwaso zuwa nan baya ta juya musu aranta Allah ya isa kawai take antayama Ya Nasir da ya uzairu kafin ta Muskuta tana Fadin"Ai shima ba Zubar da naman zai yi ba ci zai yi..Wlh In na yafe Allah Tsinan..!
Suna jinta ba wanda ya tanka mata suna Hiransu sama sama Tsakaninsu Amina ko kala bata kara cewa ba tun tana jinsu sama sama,Har sanda Hanne tace"Naga fa ga Ya D'anmalam Dazu da su ya Nasir suka Turkemu..!
Hamida tace"Nima na gansa ammh bai yi mgana ba..!
Hanne tace"Baida Hayaniya ne..duk acikin Yan gidanmu yafi burgeni..!
Hamida tace"Gaskiya..!
Amina na jinsu batace komai ba Domin kwarjinsa ma ya isa yasa kakasa mai gaddama Dole ace baida Hayanjiya.
Har barci ya kwasheta ba ita ta farka ba sai da taji an Fara sallah Cikin Wata Zakin murya cikin Sanyi da Haiba Muryan Ya D'anmallam ne tunda ya Dawo Duka Khamsin Salawatun shi ke badawa ko da tatashi ta iske Hamida da Hanne na Sallah har da wasu ma yan gusai adakin suna Bin Jam'i.
Tashi tayi ta fice Suka kusa cin karo da Zafira ta Dauro alwala Daga cikin Gida.
Kallonta Amina tayi kafin tace"Meyasa baku tasheni ba..?
Zafira tace"Hamida ta gaji da tadake kin ki tashi..!
Wucewa tayi tana Fadin"Bansan munafunci barcin mutuwa nayi da har aka ta she ni naki tashi..!?
Zafira dai bata tankata ba ta shige Dakin ta tada Sallar Amina Raka"a daya ta Samu Allah yasa ma a Rak"ar farko Suratul Muhammad ya karanta ita kanta yana karatun acikin Zuciyarta wani natsuwa take samu wanda ta rasa Dalili ammh aranta take fadin Muryansa nada Dadi in yana karatu.
Suna Idar da Salla Mamanmu ta shigo Dakinsu suka Taru wajen gaisheta Hamida ta kallah tana Fadin"Hamida ku tsefe kanku na Roki Wasila zata yi muku Kitso da kunshi kafin Lokacin Walima..!
Hannatu kema ki tsefe Tunda nasan kema baki Kitson ba..!
Cikin Fara"a suka amsa mata Hanne ke fadin"Mamanmu irin kunshin Zafira za"amin..!
Tafada tana nuna mata Kunshi naSalatif ne mai gidan siga Mamanmu tace"Ba matsala sai tayi miki..Jiya Da Daddare ya kamata ayi muku..Nayi ta Cigiyarku baku dawo ba kuna gidan Baba Mallam..!
Amina taso na Tsefe miki kan na wanke da ke Wasila zata fara ta yar fa miki iri iri mai kyau..!
Ba musu Amina ta Mike tana Sosa kanta kafin tace"Mamanmu da kin barni..Ban yi niyyar kitson nan ba .!
Mamanmu tace"A"a Amina kan ya Dade ba..yafi wata biyu tun Wanda nayi miki din nan ne fa..?ki bari a Tsefe a sake wani..!
Amina ta make kafada kafin tace"Ammh bazan yi Kunshi ba..Bana son zama Mamanmu..!
Kallonta tayi ta Tube Dankwalin Dake kan Amina tana Fadin"Bakomai kiyi kitson kawai..!
Mamata Mahaifiyar Zafira Dake Dakin Tace"Balaraba gaskiyan Ya Sa"idu ne dayace kike kara bata Amina..Ammh wannan Katuwar Budurwan da yau ko gobe Gidan miji ne kike lallabata Ta gyara kanta..?bayan ke zaki mata Tsifan ki kuma wanke mata..?Anya Balaraba..!
Mamanmu tace"Amina fa yarinya ce..?nawa take..?in Lokacin ta fara gyara kanta yayi zata gyara Mamata..!
Mamata ta tabe baki kafin tace"Ai shikenan..adai taimaka ayi kunshi ta Rufe wannan Farar kafar kamar ta kato..!
Amina ta Tura baki hararan Mamata kawai take ta gefen ido Tana ganinta tace"Hararata kike ko..?na tashi na Gafjeki Wlh..,!
Amina ta kauda kai tana kunkuni Mamanmu taja hannunta suka Fice tana fadin"Don Allah ku kyalemin Diyata hakanan kada kambun baka ya kamamin ita..!
Da kallo suka bita har ta Fice Da Amina wacce ta Juyo tana musu gwalo..
Zafira tace"Wai Amina sai an mata Tsifa an wanke mata kai..?
Hamida tace"Ko kayanta bata wankewa sai Uniform Duka mamanmu ke mata ko ta sakani..In ba ita ta mata tsifa ta mata Kitso ba sai Kanta ya shekara bata Damu ba..!
Mamata tace"Kuma wamman ba so bane..Watarana ake ji ranar da zata gidan kanta sai ta gane bata da wayau..Irun su Amina kazaman mata za"ayi in an hadu da kishiya kuma ta ran mata ta zama Bora..!
Hanne tayi dariya kafin tace"Waya ga Amina tayi aure..!ina so naga mijinta yadda zasu zauna ballatana Har da Kishiya..!tabdijam..!
Hamida tace"Zasu ga Tijara ne da Jidali ganin idonsu..!
Mamata tace"Ubanta zata ci..Daman na Fadama Ya Sa"idu ya mata aure. tsab zata Saitu don Ubanta ai chan ba Balarabar da zata kare mata..!
Dariya suka saka Zafira na Fadin"Nima ina son ganin zaman auran Amina akwai Comdy..!
Dariya suka kara sawa har da Tafawa chan ma Tsakar gidan haka mutanen Gusai suka taso ma Mamanmu ganin ta Tasa Amina tana Tsefe mata kai.
Fadi suke"Balaraba kina sangarta Amina..?Tsifan ma sai anyi mata..?
Ita dai Fadi take"Eh mana..Nawa Aminar take?Sai fa wannan shekaran ne zasu shiga Sha shidda ita da Hamida..?
Yaya na jinsu ko tankasu batayi ba suna chan suna Hidiman yin waina da Za"a raba wajen Walima su ya Jawahir kuma suna Daki suna Tsara Memo da Turaran wutan tsinken da Zulaihat zata raba wajen Walima.
Ya Jaleela dai sai ta fito tayi mgana bayan ta kalli kan Aminar tace"Amina wlh ba karamar kazama za"ayi ba Watarana..kanta har Tsagan kitso ya bace..?in taje gidan auran naga Uban da zai rika zama yana mata Tsifan..!
Ya zulfa tace"Kila mijin zai rika zama yana Tsefe mata..!
Wata daga cikin kannen Aba Daga Gusai Talatu tace"Sai dai taci Ubanta..aai nan ba gida bane..!na jaki zata ci barin ma mazan wannan zamanin..!
Dariya suka saka Amina ta tura baki Tana Fadin"Kina jinsu ko mamanmu..?
Wai har fata suke nayi aure mijina ya Dake ne..!
Mamanmu tace"Kyalesu..Zulfa Jaleela zan saba muku..Ba ruwanku da Diyata..!
Basu kara mgana ba ganin Mamanmu ta Hade rai ba wanda ya kara tankawa har ta gama mata Tsifan wajen taje kan Amina sai Wash Wash take Ya Jadwa ta fito Daga Daki tana kallonta kafin tace"Kai Amina kin ji Haushi Wlh..!
Mamanmu tace"Jadwa..Zan saba miki Wlh..!
Jadwa ta juya tana Fadin"Nayi shuru mamanmu..!
Amina aranta fadi take"Bana ga jin haushi ba Ehe..!
Dakyar ta bari aka gama Taje kan mamanmu ta Debo ruwan zafi ta fara wanke mata kan wajen Famfo Amina Har da Hawayenta Wai Zafi take ji mamanmu na Faman Lallashinta Su Jaleela na kallonsu Tsausayama Aminan sukeyi ko domin gaba Watarana ba Mamanmu a kusa da ita.
Tana gama wanke mata yasha Iska ta Shafa mata mailn kitso ta kara Sharce mata taja hannunta suka koma Dakin da Wasila ke ma su Hamida kitson.
Har ta kusa gama ma Hanne daman kanta a Tsefe yake Mamanmu ta kalli Wasila tana Fadin"Da kin gama ma Hanne ki fara ma Amina Wasila..!
Wasila tace"Dole zan yi ma Amina kitsin nan..Kada ki kullaceni Balaraba..!
Mamanmu ta fice tana Fadin"Tunda bata som kunshi a kyaleta..!
To daman wacZai matsa mata Ana gamama Hanne aka fara ma Amina Wasila tace"Wani iri zan miki..!
Amina tace"shiku..Guda goma..!
Wasila tace"Daman bai wuce haka ba..In akayi miki mai yawa ina zaki iya Tsefesa bakar kazama..!
Amina ta Juya idanuwanta kafin tace"Nifa ba kazama bace..!
Wasila ta Dungure mata kai Tana Fadin"Rashin kunya Kadai kika iya ni gyara kafin na fasa yi miki kitson wlh..!
Amina bata kara mgana ba tana kallon su Hamida na kuskus Amina ta Daga baki Tana Fadin"In aan ci namata Allah ya isa Wuta bal bal..!
Suka kwashe mata Dariya Amina tayi kyafci Tana Fadin"Munafunci dai Dodo ne..!
Suka kara saka mata Dariya Sai suka kara kunnata ta rika Hararansu Wasila ta gaji da motsinta tace"Zaki Taaya ko kuwa na saki kan naki ne na kama na Hamida..!
Amina batace komai ba aranta Fadi take"Yadda kike baka a fuska har aranki ma haka mata sai Masifar Tsiya..!
Dakyar aka samu aka gama ma Amina Kitso kafin Lokacin Zafira da Hanne sunyi wanka har zafira taje raka Hanne gida ta Dauko kaya Hamida aka Fara mawa itama ita kuma Amina taje tayi wanka duk wanda yayi mata mgana sai ta Turamai baki tana kunkuni ta Zagesa shiyasa ma su Ya Jaleela suka yi kamar basu ganta ba Mamanmu ce sai yaba Kitson take tana Faman fadin sai tayi ma Wasila kyauta.
Amina koda ta fito wanka ta Iske Sabbin kaya Atamfa Hajiya Babba ta Dinka musu su uku ita da Hanne da Hamida da Dogayen Hijaban ankon Walima da su ya Zulaihat sukayi.
Amina ta Daka tsalle Saboda Murna Tana Fadin"Jar uba..Yau din nan ba wanda zai fimu na Rantse..!
Hanne tace"iri daya da nasu ya Abida Hajiya ta mana fa..?
Amina ta sha Dariya kafin tace"Su ya Abida yau kuma za"a sa anko da yara..!
Dariya suka dinga yi sai da suka jira an gama ma Hamida kitso kana suka karya da kunu da kosai da waina basu saka kayan ba Saboda su Hanne zasu yi kunshi Amina ta zauna ta jirasu aka Jera musu Salatif aka sanya musu Lalle Hamida tana ta lallaban Amina Tayi kunshi tace bazatayi ba da ta gaji ta Daga mata Murya tana Fadin"Don Allah ki kyaleni Hamida. haba kin cika kwazzaba..Nace miki bazan yi ba ko Dole ne..!
Wasila tace"Ke so ake a Rufa miki asiri ki Rufe farar kafar nan taki kamar ta maza..!
Amina ta Daga idonta sama Tana Fadin"Ni kafata bata maza bace..Kuma ai Farar kafar ta Allah ce ba wanda yace saka Lalle Dole ce..!
Wasila tace"Duk wanda ya auri Amina ya auri kazanta da rashin kunya..!
Amina tayi mata banza aranta tana Fadin"Tunda mijinki ya aureki nima zan auru..!
Lokaci daya tana kallon Wasila tana yar Dariya Domin Wasila baka ce Dulum sannan ga muni ba Laifi
Basu je ko"ina ba Saboda kunshin su Hamida sai Gabda La"asar suka Wanke kunshi suna ta Sauri Domin Tuni wajen Walima ya cika tun dazu su ya Abida suna chan suna ta Gyare gyare Tuni masu Kanofi sun isa da kujeru sun kafa komai mata ma sun Fara Tafiya da wasu kayan Rabo da kuma abinci.
Domin karfe Shida na yammah Za"a tashi Daga Walimar,Lokacin da suke Shiryawa ne Anty Hidiya ta shigo gidam Cikin gayunta Sanye da Wata Farin Leshi ta Nannade Jikinta da Lifaya ta saka Takalmi mai Tsini Da ya"yanta Yunus da Zainab suna Kiranta Zeeta.
Yaran basa jin Hausa sai Turanci Amina ta kyabe baki tace"munga Magofork karewar Turanci don Uban mutum..!
Tazo gaida Yaya ne Amina na mamakin kaf ya"yan Baba Mallam sun fi Ji da yaya kan Mamanmu komai suka samu sai kin ji Yaya Amina abun na bata Haushi Afili ta kan ce"Ai Mamanmu tafi ma yaya som mutane..!
Sun gama Shiryawa Cikin kayansu sun saka Hijabasu Takalman sallansu suka sanya,Duk yadda suka so su Zille Basu samu Dama ba sai da su Ya Jaleela suka tasa su suka Dora musu manyan Kololin waina almajirai kuma suka Dauki Buhunhunnan Take away sauran kayan kuma Ya Nazem da yazo dasu yayi ta Jigilan Daukansu zuwa Chan haraban makarantar Data Fara cika da Mutane kaf Daliban Isalamiya da Hadda Tare da malamai da kuma Duka bangarorin gidajen biyu sun Hallata.
Su Jadwa suka je suka zo da Amare da Amotar ya Nazeem,sun sha Fararan Hijabai Har kasa da Abaya bakake kamar Larabawa Hatta Kafarsu bakin Takalmi ne sun sha kunshi ja da baki Suna kyalin gyaran yan Maiduguri.
Daga chan gidan wajen Walima aka Zarto da su ko gida basu je ba.
Kowani Daki sun yi nasu ankon Banda anare da Baba Mallan yayi musu komai iri Daya su Ya Abida da nasu ankon tare dasu Amina data gansu dashi baki ta rike tana Fadin"Hajiya bata kyautamin ba..Sai fa da nace kada tayi ma yaran nan irin namu..!
Suna ta kunshe mata Dariya tana Hararansu.
Hajiya uwa ma da Danginta irin nasu Amina sukayi da Fararan Hijabai sai Dakin Haj.Nasara ma ita da ya"yanta da Tawagarta sai Dakin Anty Amarya itama da nata ita da ya"yanta da Danginta Less sukayi Sa"adatu sai uban iyayi take Amina ta tabe baki tana Hura hanci da karfi tace"Ba"adai Fimu ba Ehe..!
Sa"adatu tasan da ita take ta kalleta suka Harari juna kafin kowacce ta kauda kanta.
Duka gidajen ba wanda bai zo ba sai wadanda aka bari su Zauna agida Dokar Baba Mallam ne har Hajiya Babba ya bada Izinin taje Wajen Walimar Ya Nazir ya kawo su Duka iyayen nasu Anty Hidaya kuma da su Anty Shamsiya Amotar ya Nasir suka Taho.
Ya Jafar kuma ya Dauko su Mamanmu Sauran mutane kuma da kafa suka taho Tunda ba Nisa Anty Sakina da Anty Sarood kuma ya Uzairu Ya kawo su a Motar ya Danmalam,shi yana chan gida yana Hutawa baya son Hayaniya.
Wajen ya cika da Mutane,Walimar ta mata ne za"ayi wa"azin aure bayan an bama Amare kyautuka,Suma din sai sunyi karatu.
Shugaba ya fara Jawabi mallam Datti ya yi bayanin Yadda su ya Zulahait suka zama Zakwakurai a cikin makarantar ya fada cewa suna da Haddar Qur"ani da kuma Sauran Littafai a kansu makaranta suna alfahari dasu matuka.
Daganan aka fara gayyatosu Daya bayan Daya suma karatu suna kuka ana Kabbara bayan nan aka basu Kyatttuka,kowacce adarasin data fi kwarewa ya Zulahat taci kyautan Iya Tajhud da kuma Muryan karatu sannan ta ci kyauta kan Haddace Buhari da Muslim.
Su Ya Sadiya ma haka gabadaya gidanmu kowa mai kokari ne bamu da Malalaci ta bangaram karatu.
Daganan sai aka fara Rabon Waina da su Donut abunda aka sanya a Takeway.
Amina suna Daga chan baya ba wanda ya Nemesu su ya Abida ne da yan ajinsu ke ta raban har da su Mariya yan ajinsu Amina da Sa"adatu abun Rabon na abinci Gabadaya akayi ba bambamci Amina ta tabe baki Tana Fadin"Mu fa na lura a bikin nan kamar bamu da wani gata..Ji fa wai Rabon takeway din ma ba wanda ya Neme mu..!
Hanne ma taji zafi tace"Uhm..Wai har da su Mariya..!
Amina tace"ji sa"adatu dame tafimu..?Ai ba kowa bane yayi mana bakinciki sai ya Abida..!
Yanzu bamu da bakin mgana in an koma Hadda kowa yaga yadda aka yarsar damu kamar wasu bare..!
Zafira tace"Mu tashi muje muma ayi Damu mana..!
Amina tace"Sai kin dawo ban tashi Wulakanta ba..!
Wlh ya Abida sai ta tsinka ki a gaban Dubban Mutanen nan kawai mu Tsaya muga ikon Allah..!
Suna nan zaune suna kallon kowa Amina ta karkata kunnen Hanne tana Fadin"kalli Yan"uwan Anty Amarya..Sun fi kowa zagewa. wai suma chan gidansu ba"ana Bikin ba..?sun wani zosun cikamana gida..!
Hanne tace"Sai an sun tafi da Amarya zasu je chan suyi Bikin su..!
Amina tace"Gulma dai..Gani suke sun fi kowa ji yadda Sa"adatu take..!
Hanne tace"Kalli ma yadda take shigema Anty Sarood .Gabadaya sun kwaceta ni ko ganinta banayi..!
Amina ta Kurama Inda Anty Sakina da Anty Sarood ido da ke zaune Dukkansu Cikin Shigar Jallabiya baka Sakina ta saka farin hijabi bai kai kasa ba ammh Sarood bata saka ba Bakin Gyalen Jallabiyan ta nada akanta baka ganin komai sai Walwalin Fararan Hakoranta.
Sakina na mata mgana tana Dariya wasu Dangin Anty Amarya suna kusa dasu suna ta Hira kamar Sakina na Fassara mata abunda suke cewa ne..
Amina tace"Wlh ba don Allah suka jata ajiki ba..!
Hanne tace"Baba Mallam nata yabon Anty Amarya da Sakina..!
Amina ta tabe baki batace komai ba.
Suna nan zaune ana Rabo yan ajin su ya Abida nata Fama da jama"a kada su mike su Yamutsa wajen.
Mariya tazo gabansu da buhun Take away din tana Fadin"An baku..?
Amina ta ballata mata Harara kafin tace"Mu bama yunwarsa mun cisa agida har mun gaji..Wannan sai ke in an gama Rabon har sata sai ayi aje gida aci a kora da ruwan lemo an Dade ba"a Hadu ba gida babu makota sai D'ai d'ai..!
Mariya ta kallesu Tana mamaki Hamida tace"Bamu mariya ba"a bamu ba..!
Tayi yar Dariya ta Dauko musu leda uku .mai Ruwa da lemo ta miko kenan Amina ta kabar dashi ya zube akasa Mariya ta Dago tana kallonta Lokaci Daya tana Fadin"Miye haka Amina..?
Amina tace"Bansani ba..Mun ce bamu bukata ko..?
Ke kuma Hamida wlh ki fita Daga idona..Kina sawa wadanda basu kai ba suna raina mu..!
Mariya kwashe ki hada da wanda kika Sata..!
Mariya ta Duka tana kwashewa Cikin yar Dariya tace"Ko ba ku yi haka ba..Kowa ai yasan ku ba wata Tsiya bace Haushi dai kukeji an bani Rabo ku ba"a Kiraku ba..!
Amina ranta ya baci tana Kokarin mikewa Hanne ta rike ta tana Fadin"Kyaleta..ana jin kunyi fada kinsan ce za"a ce baki da gaskiya..!
Amina ta koma ta zauna tana Fadin"Bari mu koma Hadda wlh sai na Watsa ma Mariya mari in ban Daki bakinta ba Ranar asabar Allah ya Tsinan..!
Cikin su ba wanda ya kara mgana suna nan zaune ba wanda yabi ta kansu Zafira tace"Amina kin hanamu karba..gashi yana neman karewa bami samu ba..!
Amina tayi shuru kafin tace"Ku tashi muje..Koda bala"i sai mun Diba..!
Binta sukayi har zuwa aji Biyu inda aka Sauke duka kayan Rabon su ya Abida ne ke ciki suka Labe awaje suka Fito bata gansu ba suna ganin haka suka shiga ciki ya Umaima ce aciki sai wasu Daga cikin yan ajinsu sai ya Zeenatu suna mgana da wata.
Umaima ce ta gansu batayi musu mgana ba tana zaune tana Duba Wani abu a Littafin Azkar din dake hannunta.
Ganin haka yasa Amina ta kallesu a Hankali tace"Duka..D'auka..zura da gudu..!
Sun san yaran yasa suka Bita tana Dukawa suma suka Duka suka Dumbuza Ledojon suka Zura aguje Sai alokacin su ya Zeenatu suka juyo suna kiransu Zeenatu ta rike baki tana Fadin"Ya Umaima su Amina ne ko..?
Kai ta gyada batayi mgana bata son Hayaniya saboda ciwonta.
Badiya yar ajinsu ya Abida tace"Aminar gidanku ko"ina sai ta nuna Hali..!
Sai ga Abida ta shigo tana Fadin"in na rike su Amina sai nayi musu dukan Tsiya..!
Ya Zeenatu tace"Ki hadasu da ya Nazeem ne yaci ubansu..!
Kyafci tayi tana Fadin"Ku bar badawa hakanan..bari agama Walima sai mu fara Shirya na malaman mu ki hada musu da abun Rabon duka Zeenatu..!
Suka amsa mata kafin ta fice Chan ta hango su Amina akarshe suma cin abunsu hankali kwance suna Dariya kai kawai ta girgiza domin tasan in tayi mgama zasu Raba Hali ne gaban Mutane.
Mariya ce tazo gabansu tana Fadin"Kunci kun barsa ne naga har da Sata..?ana ci hannu baka Hannu kwarya..!
Amina ta balla mata Harara tana Fadin"Mariya in baki bar nan ba na Rantse na mike bazaki ji da Dadi ba..!
Mariya ta saka musi Dariya tana Fadin"Kudai ku ci kawai..!
Harda gwalo Amina tace"in ban dagi bakin yarinyar chan ba ba sunana Amina ba..!
Zafira na Tura Donut bakinta tace"Daga gani irin yan Shisshigin nan ne..!
Amina tace"Kamar kin sani..Tusa kai ba kwarjini..kamar mayya..!
Har Malaman da zatayi Wa"azin tazo suna chan baya suna Ciye ciye,Daya Daga Cikin matar wani abokin Baba Malam ne Sheik Ahmad Hadeja Ta iya Wa"azi sosai kawar Hajiya Babba ce ta na hallarta Dukkan wani Mahadara na mata sannan Har programme tana yi agidan Radio da Tv akan mata ta kuma yin Wa"azin aure irin wannan in gayyaceta Motace ta Lalace musu ahanya Anan garin Gumel din suke zaune.
Nan ta fara Lacra kan hakkokim mata akan Mijinta kafin ta gangaro kam Hakokin miji kan matarsa sannan ta bada Shawarwari sosai da kuma Mgugunar karin Ni"ima bangaran isalama domin Taimakom mata Hamida ta taba Amina tana Fadin"Ku Tsaya ku Saurara Wlh mgangunta akwai amfani aciki..!
Amina ta saki Tsaki kafin tace"Dilla mu kyalemu ta ina zai amfane mu..?ko kina cikin Amaran ne Hamida?
Hamida tace"A"a abun ba bakar mgana..Ko don gaba nake nufi..!
Zafira tace"Gaskiyan Hamida mu ma nan da Shekara Biyu muma amaran ne..!
Amina ta saki Tsaki kafin tace"Sai ku jira Lokacin..Me kuke ci na baka na zuba..?
Ba wanda ya tankata ita kanta Hanne ta maida Hankalinta kan malamar ganin haka yasa Amina ta maida Hanlinta itama Sai tabe baki take yi Domin ita bama wani fahimta take yi ba.
Shida saura Mintuna aka gama Wa"azin bayan an gama su ya Abida suka fara rabon su Jakunkuna da Karamin Frame na Ayatul kursiyi da su ya Aisha zata raba Daga bangaransu.
Sai ya Zeenatu da ita da kawayenta suna ta Rabonsu Turaran tsinke da Memo na ya Zulaihat su Sa"adatu kuma suna ta Rabon Turaran Wuta na Rushi,da su Sabulun Salo harda Fallen Atamfa,acikin Wata Katuwar Leda da mafitai na zamani.
Bangaran Haj.Nasara ma su na ta Raba Kananun Kofuna da Kuma Mug na shan Tea abun sai wanda ya gani.
Kowanne sai da su Amina suka Dauka ba"a sani ba Har da su Sa"adatu Amina tace"Da kudin Baba Mallam akayi sai mun dauka..!
Hamida na Dariya tace"Amina kina da Karfin Hali..!
Amina ta balla mata Harara,sukayi Dariya kafin ma atashi suka Gudu gida Saboda kada asasu wani aiki kamar kuwa sun sani ana ta Cigiyansu su taimaka a kimtsa wajen aka nemesu aka rasa sai su Ya Abida suka Bige da aiki chan aka barsu a makaranta bayan sun gama Sallaman malamansu maza Hajiya kuma ta Sallami Malama Hafsah da tazo tayi Wa"azin mata.
Duk a kasa suka koma gida su Ya Nazeem suna masallaci wajen Karatun Baba Malam.
Sai Bayan mangariba su ya Abida suka Dawo amaran kaf suna Shashen Hajiya Babba nan Zasu kwana Har sai gobe bayan Daurin auran za"a kai kowacce shashen Mahaifiyarta na karshe,Shine Falon Baba Mallam inda shi da Aba da kuma su ya Danmalam manya inda za'ayi musu Nasiha Tare da mazajen nasu sannan kowacce a Damkata Hannun mijinta.
Su Amina ko Abincin Dare basu ci ba suna ta cin kayan Fulawa Hamida tace"Kada ya danne mana zuciya mu kasa tashi..!
Amina tace"Dillah zuwa gobe da Safe ya Sabbabe..!
Sai da suka cinye kusan duka Sauran suka bama yara har suka koma suka kwanta suna Hira Daganan sai barci.
******
Anty Amarya na Falon Shashenta Cike da baki,Wayarta Dake hannunta ta Fara kuka tana Dubawa sai da gabanta ya Fadi agogon bangon Dake Dakinta ta Duba 12am na dare ta wuce Acikin Dakin akwai wadanda sukayi barci akwai wadanda basuyi ba.
Sulalewa tayi ta nufi Bedroom dinta nan ma cike da Mutane Dayan Dakin ta Nufa taga Sakina na ciki ita Sarood sai kawai ta Juya ta Fice Daga Shashen Har wata yayar Anty Amarya tana Fadin"Marliya ina zaki da wannan Tsohon Daran. ?Sha biyu fa ta gota..!
Ta fice tana Fadin"Yanzu zan dawo Ya Salamatu..!
Kitchen dinsu tana jin hayaniya su Lami suna aikin Miya zasu soya da Daran nan na abinci gobe nan zasu kwana ganin haka yasa tayi kamar zata je shashen Baba Mallan sai ta Shige lungun Dake tsakanin Shashen nasa da Bangaran Dakunan mazan gidan.
Jikinta na Rawa ta Daga kiran har ta katse sake kira akayi Cikin Makale murya tace"Miye haka DAYYABA..?
Kinsan fa gidan cike yake da Mutane..!
Shuru tayi na dan Lokaci da alamun Tana Sauraran mai mganar ne Daga Chan bangaran
Kafin na ga ta saki wata Kayattaciyar Dariya kafin tace"Daman nace sai an gama wannan Hatsaniyar zan kiraki muyi mgana..Balarabiyar banza..?tasha gabana har ta sakani Fargaba..Tuni nayi mganinta Daman na Fadamiki bayan Sakina ba macen da zata Kafu a gidan Umar bayan ita. wannan Burina ne in ban samu mallaka Malam ba..Zan samu Damar mallakan abunda yake Takama Dashi Dagashi har Hajiya Babban atafin hannuna suke Dayyaba..!
Shuru ya sake biyo baya kafin chan kuma ta kara Sakin Dariya tana Fadin"Kema saura kiris...Ki kara Hakuri kawai..SA"IDU ma matsalata ce Dayyaba..Shiyasa na Hada hannu Dake ni Burina bazai cika ba sai Sa"idu ya bar mallan..Kema naki Burin bazai cika ba MAtukar HADIZA na Numfashi acikin gidan Sa"idu zamu yi mgana..Hanya Dayace...Kawai da zai sa komai ya Dawo hannunmu.
Zamu yi mgana in Hankula suka kwanta..!
Kamar Motsi taji abayanta da Sauri ta katse wayar ta leka Shamsu ne ya Fito yayi alwala ya koma Dakinsu sai da ya Dade da shiga sannan ta fito inda Allah ya Taimaketa An kashe gen Duhu yayi sosai yasa ta Lallaba tana Waige waige ta shige shashenta Lokaci Daya tana Sauke Numfashi.
Sako ta Turama Lambar data kirata.
*Kada ki sake kirana..Sai ni na Kiraki da kaina..*
*Janafty*
*TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*
_Ina matukar godiya ga Tarin masoyan labarin Aminene ikon Allah..Nagode matuka Baiwar ba tawa bace ta Allah ce godiyar kuma zuwa garesa ne Allah ya bar zumunci nagode matuka da Alherinku gareni musamman Halima yusuf Besty Alherin Allah ya cigaba da Bibiyanki har gaban Abada_
*🅿️13*
Karfe Daya da Rabi na Ranar jumma"a 1:30pm aka Daura auran su ya Zulaihat a babban masallacin Gidan Baba Mallam bayan an idar da Sallar jumma"a masallacin Daman Kaf anguwan da Zagayenta shine babban masallaci,Shiyasa bayan karattukan Addini da akeyi da kuma Duka Sallolin khamsin Salawatu ana Sallar Jumma"a acikinsa.
Kamar yadda kowa ya sani ne al"adan gidan Baba Mallam Ranar jumma"a yake Daura auran ya"yansa To hakan ce ta kasance ayau din ma ana idar da Sallar jumma"a Daman kowa yasan da Daurin auran anguwan ta cika ta batse da manyan mutane kama Daga manya malamai Daliban Baba mallam,Angaye da duka Tawagan abokansu, abokansu ya Jafar da Sauran Mutanen anguwa da kuma Jama"a da basa Wuce sha"anin Babban malami irin Baba Mallam.
Bayan an gama Daura auran Gabadaya Tawagan angayen da abokansu da su ya jafar da su ya Danmalam dashi da abokinsa kwara Daya Tal Daya gayatta wanda ko bai gayyaceshi ba zai zo tunda sun zama Daya tare sukayi makaranta Tundaga matakin primary anan Gumel kafin aiki ya maida mahaifinsa Dutse,suka koma chan cikin ikon Allah kuma sai suka Sake hadewa a Dutse a Wata Bording school ta maza Inda suka Dora matakin Secondary Dinsu.
Aliyu Ahmad Gumel yanzu haka Lacture ne a School of Nursing Dutse acikin makarantar ma yake zaune da Matarsa mai suna Aliya da ya"yansu Hudu sai mahaifiyarsa dake tare da Iyalinsa mahaifinsa ya Dade da Rasuwa shine kadai amini kuma aboki ga D'anmalam wanda Tare ma suka zo da Iyalin nasa tana cikin gida wajensu Sakina,Kawaye ne ita da Sakina Tunda in dai suka zo garin suna zuwa Dutse wajensu sannan Aliyun yaje Madina shi da Aliya ashekarar da suka je Hajji sai suka Rankaya gabadaya suka isa makka suka Sauke Farali.
Gabadayansu cikin gari suka tafi wani kayattacen Waje inda sukayi Reception wanda Danmallam ya Dauki nauyin komai ya hana su Hajiya yin wani abincin Daurin auran Mallam ne kadai da Aba basu awajen,Suna chan gida sallaman baki mutanen bazanga da kuma yan gusai da ana gama Daurin auran suka juya
Ammh Tundaga kan su Zubairu har ma da Mutanen gari da abokan arzuka suna wajen Sun ci abinci sannan sai aka gaggaisa aka Dauki Hotuna Saboda Tarihi.
Gabadaya Iyalan Baba Mallam Fararan Shadda suka Sanya Sai illah D'anmallam da ya Nazir ne suka saka Shadda mai Ruwan kasa Babban Riga da Hula Aikin hannu kuma iri Daya wannan aikin Baba Sa"idu ne shi ya Dimka musu su Hudu Cikon su Baba Mallan ne wanda ya Dora Rawaninsa kan Hularsa mai sakar yan Maiduguri wato Zanna Bukar.
Angwayen kuma kowani Tawaga da nasu irin Tsarin Shigar Cikin Burgewa basu wani Dauki Lokaci ba Misalin Biyu da Rabi na Rana Motocinsu suka Fara Dawowa Kofar gidan Baba Mallam,Saboda Daukan Amran kamar yadda ka"idan take mata na cikin gida Ana ta Haraman Hada abubuwan Daya Dace kada a manta da wani abun
Amaren Shashen Hajiya Babba suka kwana kuma ba"a fito dasu ba sai da aka Daura aure dukkansu sun saka Shadda Fara mai aikin Gold sannan hijabinsu har kasa mai Ruwam Gold ne da Takalmansu,ayayinda su Hajiya kuma Shaddar su mai Ruwan kasa ce suma Dukkansu har da su Mamanmu Da yaya a ka"idan Biki su kayansu iri Dayane Baba Mallam ya hana Sauya kala sannan Tundaga kan su Amina har kan su Abida shaddarsu Kalan Sararin Samaniya ce Kuma Dinkin su Duka iri Dayane da kalan aikin zaren mai ruwan zuma suma Duka Hijabinsu mai ruwan zuma Tunda saka gyale sai da su gani wajen wasu Tundaga kan na gaba dasu har iyanzu ba wani wanda har ya gama zamansa yayi aure yasan yadda ake saka Mayafi wannan Tarbiyan Baba Mallam ce Hijabinki har kasa da Safa Nikab ne bai saka musu Dole ba wacce tayi Ra"ayi ta saka abunta
Hatta masu auran suma sun yi shaddarsu sai dai kowacce kalan ta ta Dinka.
Sai bayan an gama Daura auran Angwayen sun tafi cin abinci mallam da Aba sun gama sallaman baki wajen yadan Ragu da maza kana Hajiya Babba da Hajiya uwa suka taso Amaran zuwa gidan Baba Sa"idu domin suyi sallama kowace na Lullube Cikin Hijabi tana kuka yara irinsu Amina da basa jin mgana suna Bin bayansu rii,su ya Abida kuma suna Shashen Haj.Nasara nan suka Sauke kawayen Amaran in sun zo Duk su ba wani gayya suke yi ba yawanci Duk yan islamiyan su ne sai yan Hadda ko yan makarantar Bokonsu sai Daidai kowa ya sani su kansu sun isa gayya a sha"aninsu.
Dakin Mamanmu aka fara kai su bata wani Tsaya ba suma Dayake gidan yana Cike ne,addu"a kadai ta yi musu da Nasihan Hakuri kafin tace a kai su Dakin Yaya.
Hajiya Babba tace"zamu bar miki Zulaihat ku kebe a matsayinki na Uwa gareta..!
Mamanmu Dariya tayi kafin tace"A"a Hajiya..Ni Uwar Amina ce inda yau auranta akeyi bama sai kin ce mu kebe ba..Ammh Ai Zulaihat Diyar yaya ce ku mika mata ita Dakinta ta kara mata Fada ita da Sauran yan"uwanta..!
Ana ta Dariya Kowa wannan karamcin na Mamanmu yasa take da kima a idon kowa Musamman Mutanen Gusai Dangin Aba,ba musu aka Kwashesu sai Dakin Yaya tayi musu Nasiha matuka tare da Fatan Alheri Suna ta kuka banda Sadiya kanta dai na kasa.
Amina da Hanne da Zafira da Hamida suna Dakin Domin duk inda aka saka Kafa nan suke saukewa sai ana Tafiya su rika jama su ya Aisha Hijabi suna leken Fuskarsu ba wanda ma yake Lura dasu.
Zafira tayi ma Amina Rada tana Fadin"Wanchan fa naga bata kukan Rabuwa da gida ne..?
Amina ta kalli Sadiya kafin tace"Diyar Anty Amarya ce..Yayar Sa"adatu..Ai bazatayi kuka ba yar na gada ce..!
Zafira tace"Tab wai ina ma Sa"adatun ne yau duk ban ganta ba..?
Amina tace"Tana Shashensu mana .Ki bari zamu ganta ai duka za"a kaisu..!
Zafira tace"Yauwa sai na kara ganin Balarabiyar nan..!
Amina tayi Dariya tana Fadin"Basabam ba..bakauyiya..!
Ita dai Dariya tayi Hamida da Hanne suna gefe suna jin duk nasihan da ake mu su ya Zulaihat Banda Amina da Hankalinta ba bashi a wajen.
Basu wani jima ba Saboda Baba Mallan yace karfe uku kowacce zata mika Gidan Mijinta Gabadaya Har dasu Mamanmu da Yaya da su ya Jalela da Mutanen gusai aka Dumguma gidan Baba Mallam Dakin Hajiya Nasara suka yada Amaran itama Amtsayinta na uwa zatayi musu Fada da Nasiha,alokacin ne ya Zulfa ta hango su Amina Cikin mamaki ta tabo Jawahir tana Fadin"Jawa kalli yaran nan..?
Ta kallesu kafin tace"Baki gansu ba..?ai tun dazu suna kugu da manya ko su Abida basa wajen nan sai su nayi mgana Hajiya tace a rabu dasu..!
Zulfa tace"Amina ta na wani juya ido..Kamar wata babba..!
Jawahir tace"Ko an koresu sai Amina ta Rika Labe kamar baki santa ba..?
Zulfa tace"Allah ya shirya..!
Jawahir tace"Ameen. !
Su bama su san suna yi ba suna chan suna ta Gulmar wata Kanwar Haj.Nasara da take da kiba katuwa ce Amina na Danne Dariyanta kasa kasa tace"Chabdijam..Wayaga Him..Buhun Masara..!
Tana kallonsu suna Dariya kasa kasa Sai ta kallesu sai su kauda kai ganin hakane yasa suka koma Daga kofar Shigowa suna Dariya nan ma basu Dade ba suka fita zuwa bangaran Anty Amarya,chan suka iske Danginta Na Duste har da yayin angon Sadiya wadanda zasu tafi da Amarya sun zo su Sakina an ci wani Leshi mai Tsada an kashe Dauri Sarood ma ta saka Leshi iri Daya dana Sakina mai Ruwan Maroon da Kwalliyar blue gabadaya Cikin Dakin nan sai da ta Haskawa kowa yadda tayi wani kyau kamar ka ijiyeta kayi ta kallonta Masha Allah.
Zafira tace"Tsarki ya Tabbata ga Allah..Amina kinga kyau..!
Amina tace"Gaskiya kayan sun mata kyau..Ji Anty Sakina da ta saka Wlh kamar akuya..!
Tafada tana Dariya Hamida ta Zungureta tana Fadin"Kiyi a hankali Tana kallonmu kada ta gane..!
Amina na Danne Dariyanta tace"Kalleta..Sai kiba take karawa ga Gajarta kamar akifeta da kwarya..!
Hamida tace"Amina ki bari..ba kyau kushe Hallitar Allah fa..!
Amina ta balla mata Harara Tana Fadin"Anki a barin kabarinki Daya Dani ne..?nifa Hamida kin isheni Wlh badama ayi abu sai ki ce Amina kamar Ni kadai ce uwar Laifi..!
Hanne tace"Mu dai don Allah kada ku fara wannan Fadan..!
Amina tace"Gayamata ta Daina ambaton sunana..In ba Haka ba taga Tijara ganin idonta Wlh..!
Hamida ta tabe baki kafin tace"Daga Fadin gaskiya..?
Kuma da kike mganar Tijara.?har akwai Sauran Tijaranki da ban gani bane Amina..!
Amina ta Hura Hanci kafin tace"Tab..ai baki ga komai ba Hamida..!
Hanne ta raba Fadan da Fadin"Ku ga Sa"adatu chan..!
Jin haka suka koma inda ta Nuna musu Daga bakin Kitchen din Anty Amarya suna ta Fito da kwalaye suna Tarawa anan Tsakiyar Falon itama Less ne ajikinta,mai Ruwan kasa Iri Daya dana Jikin Sabeeha ta gansu yasa ta zo ta wuce ta gabansu Amina ta kalleta kamar taga kashi kafin ta Mele baki tace"
Aikin mur in ji tusa..!
Zafira tace"Ita bata saka irin kayan ku ba..!
Hanne tace"Ko Anty Amarya ai bata saka irin nasu Hajiya ba..Itafa komai nata Dabam take yi ita da ya"yanta Baki ga yawancin Danginsu da less ba kila su nasu ankon kenan..!
Zafira tace"Hala Baba Malam bazai yi Fada bane..?
Hanne tace"Ina ma zai Lura yana Fama da Jama"a..Kuma kinsan Hajiya ba ruwamta da wannan..Daman Anty Amaryan ne akwai kai kara da ance kace..!
Amina na jinsu kafin tace"Ko Uban me zasu saka Wlh basu fimu ba..!
Hamida tace"Infa..Bama zasu Fimu ba Wlh..!
Anty Amarya suke kallo da take ta Dafa Duka kawunan Amaran tana ta musu Nasiha da saka albarka.
Basu jima ba suka fito bayan sun bar Sadiya anan Shashen itama Ikram shashen Haj.Nasara aka maidata Su ya Abida basa nan wai sun tafi gidan ya Jafar Ya Uzairu ya tuka su zasu Dauko wasu kayan Amaran Dake chan gidan
Ya Aisha da ya Zulaihat Shashen Hajiya Babba aka maidasu,Sannan Hajiya ta fice zuwa Babban Store din gidan Inda su ya jafar da ya Nasir ke jiranta aka Bude aka Fara Fito da Buhun hunan Shinkafa taci da na Tuwo sai garan kayan abinci bangaran su Taliya da Sauransu sai manyan Bombi na su kayan fulawa da Akayi ma kowaccensu.
Harda da manshanu sai da aka saka ma kowacce Dukkansu garansu kowacce abu Biyu ne wani uku,Harda da su kuka Kubewa yaji,Fulawa da Sauransu kayan Kamshi Hajiya Babba ta saka su Baba Lami sun Dakasu kowacce an Dibar mata har da kayan Miya Tattasai Bushashe Tumatiri na angwangwani aka Siyan musu.
Sun Raba kayan gida Hudu kowacce aka kwashe mata Daya su ya Shamsu ke Fita dasu suna Lodawa a Motocin angwayen.
Hajiya Babba ta koma Shashenta ta Fito da wasu kayan Kitchen da zannuwan gado masu kyau na Saudiya,guda Biyu Daya na Aisha Daya na Zulaihat kayan Kitchen dim Biyu aka Raba duk da an siya musu wasu wannan karin ne saboda kayan aiki basa kadan,Bangaran Anty Amarya ma suna ta fito da kwalaye ita harda Nakiya suka kara ma Sadiya sai bangaran Haj.Nasara itama Danginta suna ta fitowa da wasu kayan Sai ga su ya Abida daman Tururuka suka Dauko na Ruwa da na Turaran Daki,Na Aisha da Zulaihat ne ta riga ta bama nasu sadiya ta bama iyayensu mata.
Kowacce Angwayen sun zo da Danginsu guda Biyu da zasu tafi da Amarya Ya Aisha Mata uku suka zo Daga barayin mijinta Daga kaduna ya Zulaihat kuma mace Daya,Sai ya Sadiya ita gasunan da yawa tunda Abun gidane Ya ikram kuma algaita Tuni ya Cika kunnin Mutane Tawagayan ya"yan Sarki manyan uku suka zo tafiya da ita.
Anriga an gama Loda Duka kayan Daga bangaran Duka Motocin guda Daya,Daya Kaduna Daya Jigawa Daya Dutse Daya kuma nan Gumel
Cikin gida ma duk an gama Shiryawa Ya Rage saura Falon Malam Dashi da Aba sai Sauran manya yayyi irin su ya Danmallam da su ya Jafar Daga Falon Baba Mallam shi zai fito da kansa ya Mika kowacce Motar da zata sadata da gidan Mijinta bayan ya mata Fatan Alheri.
Su Amina sun kasa sun Tsare a Kofar Shashen Anty Amarya suna Hiransu Sama sama,Jidda ce ta fito ta gansu Cikin mamaki tace"Ku kuma lafiyanku kuke tsaye anan..?
Hanne ce tace"Bakomai muna son ganim Tafiyar Amare ne..!
Jidda Tayi Dariya kafin tace"Ai Daga kan su Abida sai ku Duka Mallam ya Hadeku mu aurar daku rana Daya..Wannan fa ban gane ta ba..?
Ta fada tana nuna Zafira Wannan karon Hamida ce tace"Daga Gusai take Diyar kanwar Aba ce..!
Jidda tace"Goggo Husai..?
Hamida tace"A"a Mamata..!
Jidda ta gyada kai kafin tace"Allah Sarki naji ma ance goggon na kwance Zazzabi ya Rufeta ko..!
Hamida tace"Eh Tun jiya da yammah Shiyasa ma baki ganta tare da su Yaya ba..!
Jidda tace"Allah ya sauwake in an wuce da Amaran zan shiga na gaisheta..!
Daga haka ta koma ciki,Hanne ta Tabo Amina tana Fadin"Baki ce komai ba..!
Amina tace"Yan mganar basa kusa..ai duk cikin ya"yan Anty Amarya ina girmama ya Jidda ba ruwanta..Mara kirkin sai Sa"adatu itama ya Sadiya ba baya ba akwai gulma..!
Dariya suka saka Zafira tace"Wai ni ban gane wacece matar Ya Danmallam din ba..!
Hanne tace"Anty Sakina..?gatanan mai Less iri Daya dana Anty Sarood..Gajera..!
Zafira tace"Naga wata Doguwa Fara kusa da ita..!
Hanne tace"Ba ita ba wannan Anty Aliya ce matar abokin Ya D'anmallan ne ya Aliyu..!
Amina tace"Ke don Allah..?oh na tuna ko wanman abokin nasa mai zuwa gaida su Hajiya wani Dogo baki haka..!
Hanne tace"Shifa matarsa ce Dazu suka zo da safe ai kinsa kawar Anty Sakinan ne. !
Amina tace"Ke kam matar abokai..!
Dole su zama kawaye kuma Halinsu yazo Daya itama sai kiga tana maka kallon kashi kashi..!
Hamida zatayi mgana kenan sai ga Kanwar Haj.Nasara ta fito mai kiban nan tana Tafe jikinta na rawa waya ce a kunnenta ta fito tana mgana sai Goran Ruwa Dake hannunta.
Mai su Amina zasu ba Dariya ba gwara su Hamida suna Rufe bakinsu kada taji ammh Amina Da karfi take Hamida ta Daketa tana Fadin"Dillah Amina kiyi a hankali kada taji..!
Amina na Dariya tace"Jar uba kalli Wuyanta..Timama kenan..?Wlh ko Buhun Dawa albarka Markadi..!
Daidai sanda Matar ta Juyo tana kallonsu daman tun dazu da suka shigo taga suma mata Dariya yanzu ta fito tana waya tana jin Dariyansu.
Tana juyowa suka shanye Dariyansu ta Harari Amina kafin tace"ke wa kike cema buhun dawa..?
Amina ta zaro ido ta kasa mgana Tana Danne Dariyanta.
Hamida tayi Saurin cewa"Ba Dake muke ba..!
Da Sauri Amina tace"Ai buhun dawar ce.!naga kin ma fi buhun masara ..Dankari..!
Matar ta Zaro ido kafin tace"Ni..?
Amina na Dariya tace"Ku kalli Duwawunta asama Hanne..!
Matar ta nufosu gadangadan tana Fadin"Kaga min yan iskan yara marasa Tarbiya..!
Kafin kace me sun Zura a Sittin Amina ce kan gaba sai hanyar waje suka Nufa suna Dariya Ta riga ta saki jikinta Tana kuma Gudu tana waigen su Hanne Dake bayanta sai ji tayi Ta buge Mutum agabanta Da kuma karar Faduwar wani abu wanda ya bada Sauti Tus...chas..!
Baya tayi da Sauri bayanta ya Bugu da Goshin Hanne Dake bayanta Sauran Kadan su Fadi Hamida ta Rikesu tana Fadin"Zaku fadi fa..!
Sai alokacin Hamida ta ga wanda Amina taci karo dashi ta kuma Lura da yadda Haraban Gidan ya Cika da maza bayansu ya Jafar har da wasu bakin Fuska ma.
Salati ta saka ranta Jikinta ba inda bai Rawa hanne kuwa datagama Fahimta baya ta koma tana Kifta ido kamar wacce tayi karya
Amina kuwa Tsoro ne ya kamata sanda ta Dago ido ta ga Ya D'anmallan agabanta Fuskar nan tasa ba Annuri ko Kadan Cikin Shigarsa wacce ta kara Fitomai da kyansa da Zatinsa Lokaci Daya da kwarjinsa.
Shikadai ne bata iya Hada ido dashi bazata iya jure kallonsa ba Tunda suka Hada ido taji gabadaya bakinta ya Mutu gabbanta sun saki ta yi Saurin Sadda kanta kasa tana Bin waayarsa Tadata watse akasa kenan lokacin data ci karo dashi Tayi sanadiyar Faduwar wayar.
Kamar wacce aka kai kasa haka ta durkushe ta fara Tattara wayar tana Fadin"Bansani bane..Kayi hakuri..!
Su Hanne suka saki baki suna kallonta Hankulan mutanen Dake wajen ya Dawo kansu har su ya Shamsu sun matso da ya Nazeem kallonta yake tana Tatarra wayar tayi Daidai yace"Amina ce ko..?
Wlh Yaya kaci Ubanta yarinyar nan sam bata da Hankali..!
Bata kara mgana ba sai da ta Tattaro wayar ta Mike bata yarda ta Kallesa ba ta mika mai wayar kanta na kasa.
D'anmallam Cikin Takaici yake kallonta ya kasa karban Wayar wai meyasa yarinyar nan bata da natsuwa ne..?ji yadda ta kwaso gudu kamar wata ballagaza kamar wata Namiji..?
Ganin yaki karba yasa Abokinsa Aliyu Dake Gefensa ya saka Hannu ya karbi Watsatsiyar Wayar yana Fadin"Ba kyau gudu acikin gida..!
Yafada yana kallon Amina acikin Ransa yana Tunamin ko kanwar Danmallan ne to bai santa ba.
Sai da yayi mgana ne Amina ta Dago suka Hada ido da Aliyu sai alokacin tasan ba Ya Da'nmallam ya karbi Wayar tasa ba.
Gabadaya taji ta muzanta ne ganin da Maza awajen yasa ta Ja kafafunta zata wuce su hanne kuwa suna gefe sun Rakube kamar wasu marayu.
Ba zato kawai taji wani Dogon Hannu mai Laushi ya Riko Duka Kafadunta da karfi ya Dawo da ita gabansa Cikin Mutuwar jiki ta Dago manyan Idanuwanta ta Sauke a nasa da suka Fara Sauya Launi saboda bacin rai.
Ya Jafar suna chan nesa suna Hira da wasu abokansu su ya Nazeem ne ke kusa ya Nazir kuma yana chan gefe saman manyan Darduman da suka shimfida a Haraban gidan yana kallon meke Faruwa ammh bai maida Hankali ba Chart suke da Hidaya matarsa Tana Fadamai Hayaniya ya Isheta sai yake tambayanta tana ina..?tace tana Bedroom din Hajiya inda ta Sauka shi bai ma tsaya lura da abunda ke Faruwa ba.
Kamar mayen karfe haka suka Tsaya suna kallon Juna shi yana mata kallon Haushi da Takaichi ne ita kuma ta kasa Sauke idanuwanta ji take kowani gabobinta suna yin Sanyi kamar yana Hukuntasu duk Rashin kunyarta yau sai da aka ga Tsoro a cikin Idonta Lokaci Daya kuma Jikinta ya fara rawa.
Ya Shamsu ne ke fadin"Yaya ka bari ni na Chasa su basu jin mgana Daman Abida ta kawo min karan su jiya Wajen Walima suna ta Satan Takeway kamar baza"a abasu ba kuma Shugabar su Amina ce gatanan batajin mgana ta Raina kowa..!
Awannan karon a Saman Labbansa ya Furta"Sata again..?
Meke damun yarinyar nan ne..?tana so ta zama Wata gangarriya..!
Sai alokacin ta iya Sadda kanta tana jin kamar kafafunta bazasu iya Daukanta ba.
Cikin Muryansa mai Sanyi Da Zaki yace'"Meyasa kowani abu sai ace ke..?kece Satan nama..?abinci..?rashin kunya Kazanta sannan Main din shine Rashin Natsuwa..?ke kadai ce agidan..?
Ina ce su Hannatu age Mate dinki ne..?
Why..?
Ya fada yana Jijjiga Kafadanta kafin ya Saketa da karfi yana Fadin"Abunda ke Raba Mace da Namiji shine Natsuwa da kamewa..Duk macen da bata da Natsuwa sannan kazama ce ita..Sunanta ba Mace. sunanta ballagaza..!
Yafada yana jin Bacin Ransa na Sauka da Hannu ya nuna su Hanne yana Fadin"Daga ina kuke..?ina zaku cikin maza awaje..?
Hanne kamar tayi kuka tace"Ba..ba ko"ina..!
Hannu ya daga ya nuna su dashi yana Fadin"Duk yaran Dake cikin gidan nan ko yara kanana iyayensu basu bar su sun zo suna guje guje ba sai ku..?Ku yara ne..?wato duk iskancin ku da ake Fada akanku gaskiya ne ko..?
Hanne ta kwaso Rantsuwa tana Fadib"Wlh Yaya..!
Shutt up..!
Ya katseta da Karfi Cikin Bacin rai yace"In kun raina su Jafar ni sai na Ladabbar daku kafin na koma ku bar ganin bana Duka inna na Fara Dukan yarinya sai na Fasa mata jiki..Comom Ku wuce ko ku koma cikin gida Wlh ko da Wasa na ga Fuskar Daya Daga Cikin ku bama awaje ba anan Haraban sai na Karya mata kafa Daya..!
Ku wuce ku bama Mutane Waje..Wawayai kawai kun girma bakusan kun girma ba..!
Ai kafin ya Rufe baki su Hanne sun juya Sumai sumai sun wuce Amina ce kanta na kassa da idon kowa ke kanta ta kasa gaba ballatana baya Sau Biyu kenan ya Taba Tozartata na Farko Ba Mutane ya Abida ce kadai sai su Hanne yau kuma bayan su Ya Nazeem har da Bakib ido..
ya sake kiranta Barauniya,Sannan yasake ce mata kazama kuma yau harda ballagaza Gabadaya sai taji Ruwan Hawaye sun cika idonta aranta Fadi take"Ni ba barauniya bace..kuma ni ba ballagaza bace..!
Ammh ta kasa Furta haka afili Tama kasa wani motsi.
Aliyu ne ya Dafasa yana Fadin"Cool down Shehi..Bana som Fushin nan naka mara kyau..!
Ya Nazeem ne ganin Amina taki tafiya yace"Au ke bazaki wuce bane..?
Ya uzairu yace"Duka fa take so ya Nazeem ba"a shiga Jikinta bane..!
Mamakin Tsayuwarta yake Cikin Daga Harshensa yace"Bazaki wuce ba..?
Yafada kuma yana Daidaita Fushinsa Da Sauri Aliyu yace"Amina wuce ki koma Cikin gida kin ji ko..?
Ya fadi sunanta kamar yadda yaji an Fada Bata Dago ba kamar wacce muryansa ta bata gwarin gwiwa maimakon ta Juya sai ta fara Tafiya kawai da Sauri ya Shamsu yace"Ke ina zaki..?
Daman wanda zata Huce akansa take nema wanda yayi mata yafi karfin ta Ja dashi yasa jin muryan Shamsu ta waigo cikin Fada tace"To gida zani..!
Tafada Lokaci Daya tana Sakarmai Idanuwanta tana kuma Murgudamai baki harda Harara sai kuma Hawaye dukkansu sun gani Shamsu ya Zaburo yana Fadin"Ke ni kike juyama baki..?zan karyaki in na rike ki..!
Amina ta Tsaya kyam tana Fadin"gani..Kada kabarni da rai ya shamsu don Allah..!
Tafada tana kallonsa da Jajayen Idanuwanta..
D'anmallam yakalleta ta fa Daina bashi mamaki Aliyu yace"Kai shamsu kyaleta..baka ga yanayinta ba inajin ba ita kadai bace..!
Ya Nazeem yayi Dariya bai ce komai ba acikin Salo Salon iskancin Amina wannene basu gani ba
Ya shamsu yace"Wlh lafiyarta Kalau..Duk Salon rashin kunyarta ne Daman bata tsoron kowa ta bari nazo ta gani..!
Ya fada zai nufeta yaji D'anmallam ya Dakamai Tsawa yana Fadin"Shamsu kyaleta...
Ke bar nan wurin..!
Ba musu ta juya bayan ta kara juyama Shamsu baki tana kunkuni ta wuce tana Sharan kwallah D'anmallam ya Saki Siririn Tsaki yana Fadin"Kazama kaawai..!
Ya Uzairu yace"Yaya da ka bari Shamsu yaci Ubanta..Ko"ina ta Addabi mutane chan ma bata bari Baba Sa"idu ya Huta koda yaushe Fitinarta..!
Hannu ya Dagamai yana Fadin"Nace ku bar mganar ko..?
Dole suka koma suka zazzauna shi kuma sai Sakin Huci yake Kafadarsa Aliyu ya Dafa yana Fadin"Allah huci Zuciyar Shehi..Ungo wayarka kila sai ta Hau kan Teburim mai gyara..!
Karba yayi Lokaci Daya yana ganin yadda Sreen din wayar ya tashi aiki.
Karamin Tsaki yaja kafin yace"Yarinyar nan bata jin mgana..kamar ballagaza bata da natsuwa ji asaran da ta jamim
Wayar nan fa sai dai na Sauyata ta gama aiki..!
Aliyu yace"Is ok..Kayi Hakuri muna da kudin Siyan wata kannen namu ne sai Hakuri..naji Uzairu na Fadin Baba Sa"idu Hala Diyarsa ce..?
D'anmaallam ya gyada kai bayason mgana ba Domin Kada mallam yayi Fada da Tuni yana gida ya kwanta ya Huta.
Aliyu yace"haba na kamar su da Yaya..Hala Diyarta ne..?
Nan ma kai ya gyadamai Aliyu ya Kalli Umar yana shafa gemunsa yace"Irin su ne Sweet Sisty Shehi..Anya bazan kama Daya Cikin kannen nan namu ba..?tunda kai ka yi auranka da balarabiya..!
Danmallam ya kallesa a adage kafin yace"Wadanan yaran zaka kwasa..?
Aliyu yace"ofcourse sun fi Dadin harka ne..!
Danmallan yayi Tsaki kafin yace"Wlh baka da Hankali..kai yanzu Gemi gemai dakai AA kace wadanan yaran kake so ka aura..?Ya"yan Cikinka..?
Aliyu yace"Bangane ya"yan Cikina ba..?nifa ba Tsoho bane mallam Shekara Talatin da taran ma ban cika ba..Sai watan jibi..!
Wani Tsakin ya kara ja kafin yace"Me yayi Saura a arba"in AA..?Wlh da auran Fari mukayi dukkanmu da muna da kamarsu ko basu kai su ba suna Tsaransu..!
Aiyu na Dariya yace"Kai nifa ba Tsoho bane..Ko yanzu naso zan auri yar 12 ma ballatana yaran nan sun Haura 15..!
Dan mallam ya Dafe kansa kafin yace"Plz ka kyaleni da wannan Shirmen naka am not in d Mood..!
Aliyu na Dariya yace"Kai Shehi..Kaifa nasan sai ka cike kofa Danmallan fa kake..!sunnar nan sai ka ciketa..Ina baka Shawara in zaka kara ka karo irin yan yaran nan sun fi Dadin Sha"ani nidai kar ka manta ina kamun Daya Daga Cikinsu duk wanda ka bani am Greetfull..!
Danmallam ya fara ma Aliyu kallon ya Tabu ganin haka yasa ya Buga Kafadarsa yana Fadin"Am Serouis fa Shehi..!
Danmallam ya Kauda Fuska yana Fadin"Plx ka cireni cikin Shirmen naka..Kuma wlh in kace zaka auri irin yaran nan sunanka Sorry ka kai Jidali Gidanka da kanka am Telling u..!
Aliyu yace"Eh bakomai..Tanque for ur Advice..!
Ko kara kallonsa bai yi ba shi kuma Aliyu na Dariya yace"Tunda ka gaji dani..Bari na kira Aliya nace ta fito ita da yaran mu kama Hanya..!
Kamar bai son mgana yace"Ka bari yaran chan su tafi mana..!
Aliyu yace"Wasu yaran..?
Yamutsa Fuska yayi kafin yace"Amaran mana..!
Aliyu yayi Dariya yana Fadin"Shehi Umar..Mijin Sakina ango Saratu..!
Hararansa yayi kafin yace"Sarood na ce maka..!
Aliyu yace"oh..Sarood kasan bakin ya saba da Hausa ba irin ku da bakin ya Juye da Laranci ba..Angon Balarabiya..!
Yake fada yana Dariya Danmallam Mirmishi kawai yayi kafin yace"kana da matsala AA..!
Sa da aka fara Haraman fita da Amare su Hanne suka Tabbatar da Amiba bata gidan sun Duba ko"ina basu ganta ba.
Zafira tace"To ina taje..?
Hamida tace"Gida ta koma fa..!
Zafira tace"Muje to..!
Hanne ta harareta kafin tace"Jeki a karya miki kafa..
Zafira ta kama bakinta kafin tace"Au na manta ne kai ban kara zuwa Bikin Gidan nan Wlh..mu achan gusai in ana Biki ba inda bama zuwa bamai Takura mana..!
Hamida da Hanne suka ce Hamm atare sun kasa mgana.
Suna gani aka fita da Amaran suna kuka ammh ba Halin su bi Tawagan masu Rakiya.
Falon Baba Maallam aka shiga Dasu Hajiya Babba,Sai Hajiya uwa sai Yaya kadai suka shiga dasu.
Baba Maallam da Aba sai su ya Danmaallam da Su ya jafar ya Nazeem ya Nasir ya Nazir dukkansu dai mazan suna ciki hatta su ya shamsu Sauran matan kuma suna Waje suna Jiransu Ciki harda Sakina da su Sarood da Aliya sakina taso ta bi Sadiya zuwa Dutse Umar ya hanata yace ta bari Daga baya.
Nasiha ne maallam yayi musu,Kadan Ba da yawa ba Domin yace duk abunda zai Fada musu an sanar dasu sai Aba shima yayi nashi sai Ya Danmaallam sannan ya Nazir sai su ya Jafar hatta su shamsu sun musu sallama.
Daganan Baba Mallam ya ba kowacce Qur"ani Izu Sittin da azkar da Casbaha yace in suka rike kyautarsa sun gama Lafiya..
Daganan ya mike suka fito shi da Aba da Hannayensu suka saka kowacce a Motar da za"a kaita gidan Mijinta suna kuka suna Daga ma iyayensu Hannu.
Su ya jaleela da su ya Nazifa da su ya Fatima duk suna Kofar gida bakin Motocin suna sallama dasu sauran matan suna daga cikin gida.
Daya Bayan Daya Motocin Amaran suka tashi sai fatan Allah yakai Lafiya sannan mata suka koma cikin gida.
Alokacin ne Danmallam suka shiga cikin gida shida Aliyu suka gaisa dasu Hajiya sannan yace Aliya ta fito su tafi sai da taje ta ma Hajiya sallama ta bata kayan Cincin na biki tana ta Godiya.
Kafin La"asar suka wuce Bayan sun Rabu kan suma suna nan zuwa.
Sallar la"asar kadai yayi a anguwan ya Shiga Mota ya koma gidansa ya kwanta Saboda Hayaniya.
Zuwa Dare gabadaya Amaren Dake nesa sun isa Mazajensu sun kira Baba Maallam suka shaidamai sai Hamdala gidan kuma sai aka Fara Hada hadan kayan Tafiya zuwa gobe hatta su Ya Jaleela ma Baba Mallan yace kada wacce ta kai mai jibi agida ya Jadwa ne kadai zai Dagama Kafa sai visan su ya fito.
Ya Akila da ya Fatima gobe zasu bi mazajensu su koma su jidda ne jibi zasu koma ammh gobe Dutse zata sauka bayan tagama ganin Dakin kanwarta ta wuce kano..!
Su hanne sai Dare suka ga Amina adakin Mamanmu taci kukanta ta Share hawayenta duk yadda suka so su Zolayata yau Amina bakinta ya Mutu kazil batace ba haka suka kwana gari na wayewa sun sani suka Fara shirin tafiya Hadda harta su ya Abida kuwa.
Kafin su tafi sukayi sallama da Zafira aranar zasu tafi Allah Sarki Sabo kamar kada su rabu,ko kafin su Dawo makaranta da yammah yan gusai sun koma,gida ba kowa sai goggo Husai da Ya Jadwa da Ya Jaleela da gobe jirgi zatabi zuwa Lagos ya Jawahir ta bi yan Gusai sun koma.
Ya Zahra ma jirgin yammah tabi ita da Mijinta Daman yazo Daurin auran sai ya Zulfa da gobe zasu koma ita dasu Ya Uzairu su ya Nazir da Matarsa tun safe suka hau jirgi suka koma Lagos.
Chan gidan Baba mallam ma kowace Danginta sun tafi yan maiduguri kadai suka Rage sai gobe zasu wuce Ya Jidda ta Sakina da Sarood sun tafi Dutse tun Safe,Danmallam yaso ya hanasu Tafiya Hajiya tace ya barsu su tafi sai gobe zasu dawo.
Ta bangaran kowacce Danginta sun Tafi Sai daidai su Baba Lami nata Faman gyaran gidan.
Koda sukaje Hadda Amina bata manta ba sai da Taja Mariya da fada aka Fitar dasu Waje Mariya ta rika yima Amina Allah ya isa.
Ta kalleta tana Dariya kafin tace"Allah ya isa taki ce awajen Amina kin ga kaina tafi Dubu..
Take fada tana ma Mariya gwalo sai Da aka tashi Hadda aka Sallamesu da aka shiga islamiya ba haka ta Dinga Tsungulinta sai da aka kara Kadata waje.
*Janafty*
*TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*
*🅿️14*
Kimanin Sati Biyu kenan da Watsewar Bikin su ya Zulaihat baki na nesa da na kusa duk sun koma Gidajensu Goggo Husai ce mutanen Jordan da ya Jadwa basu Tafi da wuri ba saboda Mtsalan Visa sai cikin Satin nan suka samu tafiya.
Amaran suna gidajensu cikin Koshin Lafiya sai Fatan Allah ya Zaunar dasu Lafiya Bakin Madina ne kadai ya Rage basu koma ba suma suna ta Shirin Tafiya cikin karshen watan da muke ciki Zasu fara sabuwar shekarar Musulunci achan Madina din.
Yau ta kama Laraba ce Tun Safe Amina ke kwance kanta na ciwo Daga Dakinsu sai ta koma Dakin Mamanmu saboda Hamida ta isheta ta Mitar ta tashi ta gyara Kayanta data Zube kan gado wajen nemam Hula ta saka ma kanta ita kuma ta mata banza Tun bayan kallon Hamidan da tayi tana Fadin"Don Allah Hamida ki gyaramin kin ga fa ban da Lafiya..!
Hararanta Hamida tayi Kafin tace"Kin ma isa..?Wlh bazan gyara ba Daga neman Hula sai ki baro da Duka kayanki a kasa ai da gangan kikayi Tunda kinsan kina da mai gyara miki yau kam bazan yi ba ki tashi ki gyara da kanki ko kuma ki bar Kayan naki su Rube anan wajen..!
Amina kallon Hamida ta Rikayi acikin Ranta Tana Tunanin Hamidan ta Rage Mutumci yanzu ganin dagasken bazata gyara ba kuma tana ta Damunta yasa ta mike ta Bar mata Dakin Tana Fadin"Kici kanki ke Kadai..!
Allah yasa ya Zeenatu bata nan Tana makaranta Sai su agida tunda basu fara zuwa makaranta ba tukunnah.
Dakin Mamanmu ta shige ta Kwanta Chan saman gadonta Batama san tana ciki ba sai Daga baya ta shigo ta ganta Tashinta tayi tace ta tashi taci wani abu tasha Ko panadol sai da mamanmu tayi da gaske sannan Amina ta tashi tasha Tea ta Hada da Panadol ta koma ta kwanta Sai barci kuma barcin mai Nauyi ne ya Dauketa Ta Dadebatayi irinsa ba Tunda ba barcin Rana Amina keyi wani Lokaci ba.
Ba ita ta farka ba sai Wajen uku Saura na Rana taji kan nata ya Sauka sai kuma Kasala ya kamata ta kasa tashi ta koma ta kwanta Sama sama tana jin kamar tashin mganar mutane Daga Falon Mamanmu sai dai bazata iya tantance ko su waye ba Ita duk a zatonta su ya Zeenatu ne da Hamida yasa ta gyara Kwanciyarta sai Bayan La"asar taji mamanmu na Kiran sunanta Idanuwanta Cikin yanayin Barci da Nauyi ta Bude manyan Idanuwanta ta Sauke kan Mamanmu wacce ke Tsaye kanta tana Fadin"Amina ki tashi hakanan kiyi sallah kici abinci in kan bai Daina ba In Aba din ku ya shigo na Fadamai ko Asibiti sai akai ki..!
Amina na shirin komawa barcin Mamanmu tace"Tashi mana Amina...Kada ki koma barcin nan .!
Dole yasa ta mike tana Mika Lokaci Daya tana Fadin"Wash...!
Mamanmu na Shirin Fita Daga Dakin tace"Ki rika Salati mana Amina.!
Daga haka ta fice Daga Dakin Dakyar Amina ta zuro da Kafarta Ta Sauka Daga kan gadon tana gyara Zaman Doguwar rigar Dake jikinta na Wata jar Atamfa Sai ta Dauki Hulanta ta Rufe kanta sannan ta fito Daga Cikin Uwar Dakin kanta tsaye ta fito Falon Sai dai Fuskokin data gani ne yasa ta Dan Tsaya tana binsu da kallo kamar yadda suma suke kallonta.
SArood ne ta washe mata Fararan Hakoranta daya sa itama ta Sakar mata Dariya.
Sakina kuma Kanta na kasa tana Danna wayarta Sai da taji mamanmu na Fadin"Kin taso..?ki farayin Sallah sai kici abincin ina Fatan kan ya Sauka..?
Da kai ta mata mgama ganin yadda Sakina ta Dago tana mata kallon Sama da kasa,Mamanmu ta cigaba da Fadin"Matan D'ammallam ne suka zo mana Sallama jibi zasu koma tun Dazu suka zo Lokacin kina ciki kwance..!
Amina ko Tsayama bin mganar mamanmu batayi ba har takai Kofar Dakin Sanda Taji Sakina na Fadin"Yarinyar nan bata da kunya
Bata iya gaisuwa bane..?yar wajenki Hamida ta fita hankali da natsuwa..!
Sanda Amina takai Tsakar gidan Sai data juyo ta Harari Dakin na mamanmu kafin ta Murguda baki afili tace"Eh din baza"a gaishekin ba..Mutum sai gajarta kamar an kife kwarya..!
Tana jin Sanda mamanmu ke Dariya tana Fadin"Amina ta dai fi Hamida baki ne ita kuma Hamida ta fita Hakuri..!
Tabe baki Amina tayi kafin ta karisa Cikin Kitchen Babban Cooler da suke zuba abinci ta Bude Farar shinkafa Akayi miyar kifi bata wani Dameta ba,Kadan ta Diba ta saka Miyar nan Kitchen din ta zauna taci ta Bude babban Fridge din Dake Kitchen din ta Dauki Ruwa tasha Tana cikin shan ruwan sai ga yaya ta shigo Kitchen din,Kallonta tayi batayi mata mgana ba ta wuce tana Bude Dirowar saman Kitchen din Ko kallon inda Aminar take batayi ba sai da Aminar tace"Yaya duk yau ban ganki ba..!
Bata kalleta ba tace"ina zaki ganni tunda baki je inda nake ba..?
Meyasa baki je makaranta ba..?
Amina tace"Ban fa da Lafiya ne Tun Safe..!
Yaya ta Dauki kulin Ararrabinta Data ijiye ta fice Daga Kitchen din tana Fadin"Allah ya sauwake..Tunda kin ji Sauki ki kwashe kwanuka nan ki wanke yau hamida da Zeematu sukayi ta aiki acikin gidan nan..!
Baki Amina ta Tura afili ta Furta"Hamida bata da mutumci yanzu..Shine ko tamin ko..?
Kyafci tayi domin ta Tsani wanke wanke gwara tayi shara Daman Hamidan take tusama wanke wanken Sau tari ita kuma sai tayi shara to kwanakin nan taga Hamidan ta waye ne sai tace kowa yayi aikinsa.
Batasan komawa Dakin mamanmu Tanayin alwalanta ta shige Dakimsu kayanta kan gadonta Hamida ta Tula mata su baki ta karkace batayi mgana ba bayan ta idar da sallar kan gadon Hamida ta koma ta kwanta tana jin bayanta ya gaji Tunanin yadda zata fita tayi wanke wanken kadai take yi kara narkewa tayi In mamanmu tazo sai tace ciwon kam ya Dawo Dole Dai yaya ta kyaleta Domin mamanmu bazata barta ta fito bata da Lafiya tayi wani aiki ba.
Sai dai addu"arta bata ci ba Domin tana jin an Daga Labulen Dakin ta kara Lafewa har tana wani Nishi Sama Sama Yaya ta kalleta kamar tayi Dariya ammh sai ta kanne Cikin Kaushinta tace"Zaki taso zuwa aikin ki ko kuwa sai na shigo na iskoki kan gadon nan..?
Amina ta tura baki jin Muryan Yaya Kafim ta Mike Zaune tana Fadin"Kai Yaya ciwon kan fa bai daina ba..!
Labulem ta saki Tana Fadin"Ki gama aikin ki in bai Daina ba In Jafaru ya shigo sai ya kaiki Chemist ayi miki Allura..!
Ido Amina ta zaro Kafin ta Diro Daga kan gado afili ta Furta"Na yarda yaya bata Kaunata..!
Yadda ta Tsani Allura kuma sannan ma a rasa wanda zai kaita sai ya Jafar ai data Kade har gayenta an samu mugayen duk sum koma inda suka fito ya shamsu ne sai a islamiya suke Haduwa su ya Jafar kuma sai dai taji muryansu in sum shigo gaida su yaya bataama yarda su hadu tun bayan Watsewar sha"anin suna gida Tunda ba makaranta suke zuwa ba ko Hanne ta rage shiga wajenta itama Ganin haka yasa sai ta kwana Biyu bata shigo ba sai dai su hadu a islamiya da yammah.
Hakanan tana Tura baki tana kunkuni ta fito da kwamukan wanke wanke zuwa Bakin Famfo Dakin mamanmu ta leke bakowa ita ta shiga wanka su Sakina kuma suna Dakin Yaya Daga Tsakar gidan ma tana jiyo Tashin Hirar Sakina da yaya Sarai Sarai ta kwashi kwanukan da suka bata nan Falon mamanmu tana kunkuni ita Kadai.
"Sun wani zo sun bata mana kwanukan sun karamim aiki..Mtsewww..!
Nuku nuku ta dinga yi Saboda Mamanmu ta fito ta hanata sai dai Addu"arta bata amsu ba Mamanmu bata Leko ba sai ma yaya ce ta Leko raka su Sakina suka leka Dakin mamanmu suka mata sallama sai gasu sun fito Tare tana gyara Daurin Dankwalinta Lokaci Daya tana Fadin"Ke Sakina yar"uwar taki bata jin Hausar tamu sai labarcimu kuma bamu kware ba..!
Tafada tana Dariya Sakina ke Fadin"Mamanmu wanda aka Haifa achan yayi Rayuwarsa achan ina zai ji Hausa..?Sai dai hankali zata iya Tunda yanzu ta shigo Cikin mu..!
Yaya tace"Kwarai tunda ta auri Bahauahe ba..koda yake shima ai Danmallam din Harshensa ya Karye kamar Balaraban chan..!
Mamanmu tace"Ai ya Dade fa achan yaya..Ina jin yafi shekara goma ko..?
Sakina tace"Yana cikin shekarata ta ashirin ne fa naji yana Fadi..!
Mamanmu tace"Koda naji..!
Yaya tace"Zai yi fa Tun su Zahra na kanana fa alokacin..!
Ita dai Sarood sai dai tayi ta washe baki in ta tambayi Sakina me akace ne sai Sakina ta gayamata da Larabci Duk da itama ba wani kwarewa tayi ba Harda iyayi ita Adole tana jin Labarcin.
Amina na Tsugunne tana wanke wanke ta tabe baki aranta tace"Allah yasa ma tasanme take fadi..!
Mamanmu ce ta ganta cikin jin Dadi tace"A"ah jiki yayi kyau Amina..!
Dole ta Dago tana yake tace"Eh Mamanmu kam ya daina ciwo..!
Da sauri tace"Masha Allah..To kiyi Sauri ki gama kada mangariba ta Sauko baki gama ba!
Da toh ta amsa batare data kara mgana ba,har suka wuce har korido suka Raka su Sakina suna kara musu sallama da alkawarin agoben kafin su tafi zasu shigo gidan su kara yin sallama.
Tana jin har sanda su mamanmu suka Dawo tana mata Fadan tayi ta gama Ko mgana ma batayi ba da kai ta kara amsaa mata,nuku nuku ta Dinga yi sai tafi minti Biyar bata wanke Kwano Daya,Har Su hamida suka shigo sun Dawo Daga islamiya Ya Zeenatu ne ta kalleta tana Fadin"Har duhu ya shiga Amina kina zaune bakin Famfo alhalin kinsam har Aba yayi Fadan hakan.!?
Amina taso ta dago tace"Ina Ruwanki ne..?
Sai kuma ta fasa ta Tura baki ta Kauda kanta Ya Zeenatu ta wuce tana Fadim"Ke kika sani..!
Hamida ne ma tace"Kin warke kenan..!
Daman jiranta take sai ta mike ta Rike kugu tana Fadin"Ina Ruwanki..Im ma na warke in ma ban warke ba..Duk ba Damuwarki bane..Kada kuma ki Dameni Mutum ba Taimakaa maka zai yi ba sai ya isheka da mita akyaleni ko sai gobe ne in gama ina Ruwan wani..!
Hamida bata tanka ta ta wuce Daki abunta ta ijiye jakarta,Duk tana wajen suka fito sukayi alwala ba wanda ya tankata ta juye Jidalinta akansa itama sai Harare harare take yi karshenta dai kan Jawad ta Sauke Haushinta wai ya Watsaa mata Ruwa haka ta mike ta Rikeshi ta Falfalmai mari har sai da yayi kuka da kuka ya fita masallaci Lokacin Yaya tana Sallah Hamida ce awajen kuma batace komai Domin tasam ba karamin aikin Amina bane ta Dawo da duka jidalin kanta Shiyasa bakinta kanin kafarta ta koma Daki.
Amina har aka Idar da salla tana bakin Famfo bata gama wanke wankenta ba,Yau din ma Ya Danmalam ya bada Sallah Ita Rabonta da gansa tun Ranar Daurin aure da yayi mata wannan Tijaran ta gujema haduwa dashi Shine mutuum na Farko Daya taba Cin Zarafimta bata samu ko Baki ta Turamai ba yana da ta wata baiwar da komai Rashin kunyarka sai kaji Shakkarsa.
Afili ta Furta"a Muryansa kamar mai kirki nan kuwa cikinsa fal Tozarta Mutane..!
Bazata ce taji Sallamamsa ba Daga sama kamar acikin kanta taji Sansanyayyar Muryansa cikin Zatinsa yana Fadin"Waye anan..?
Ya ke fada domin Lokaci akwai Duhu kuma ba"a riga a kunna injin ba.
Kyam Amina ta kame Daga inda take Sai kuma jikinta ya fara rawa da taji Muryansa batasan Dalili ba Bata son Haduwa dashi bata son jin muryansa Domin Fadar mata da gaba Muryansa yake yi sannan Uwa uba ganinsa ba Alheri bane sai ya Tozartata.
Kokarin Fito da wayarsa yake ya Haskata sai Haske ya gauraye Tsakar gidam,Nepa sun kawo Wuta Daidai Lokacin da Idanuwan Amina suka shiga Cikin na Umar Dake Tsaye Gabda da ita yana kallonta kamar yadda itama take kallonsa.
Sanye yake da Jallabiya mai Ruwan kasa da Hula a saman kansa sai Bakin Wandon Dake jikinsa Tunda Jallabiyar bata kaai mai Kasa ba.
Fuskarsa ta kara kyau ya Kara Haske har wani Kiba taga ya karaa mata.
Cikin mamakin ganinta acikin wannan yanayin yake Fadin"Ke me kike yi anan da Mangriban nan..?
Yake Fada yana kara Nazarinta da Sauri ta Sadda kanta kasa ta kasa mgana,Jikinta ba inda baya rawa,Lebenta Kamar ya Nane haka taji ta Kasa mgana shi kuma Ransa ya fara baci yarinyar nan bata da kunya Rainin Da take yi ma su Jafar shi take so tayi mai yasa ya Dakaa mata Tsawa Cikin Bacin Rai yace"Bada ke nake mgana ba..?Kika bari na nazo wajen nan sai na Lahira yafi ki jin Dadi..!
Ki bari na taso ki gani..!
Tsawamsa shi ya fito da su Hamida Harda Mamanmu da Yaya sai suka ga Danmallamm
Mamanmu ce ta washe baki tana Fadin",A"a Umaru barka da zuwa!
Kallonta yayi kafin yace"Mamanmu me yarinyar nan take yi anan wajen nan har yanzu..?
Mamanmu tace"Amina ce wanke wanke take.!
Katseta yayi da fadin"Haba Mamanmu tana mace?
Da mangariban nan ita Kadai acikin Duhu bata tsoron lafiyarta.?
Mamanmu ta kalli Amina da Kanta ke Kasa tana ta fiki fiki da ido tace"Wlh Danmallam sai da nayi mta magana Tayi ta gama Kafin Dare yayi..Dayake ba Lafiya ne da ita ba..!
Amina taso daga wajen nan Hamida da Zeenatu ku taaimaka ku karisa don Allah ina ga Kan ne ya Dawo mata!
Zeenatu tace"Mamanmu Wlh lafiyarta kalau Aminar ce baki sani ba!
Hararanta tayi Kafim tace"Bazaki yi ba kenan?
Dole tayi shuru bata kara mgana ba Amina kuma kamar mumafuka kanta na Kasa ta taso tsomai Tsomai kamar Wata kazar da aka Cirota Daga Ruwan Zafi Danmallam ya bita da kallo Cikin kyama aransa yana Tunanin yarinyar nan ta wuce Tunaninsa
Yaya ce ta faraa mai maraba tana Fadin"Maraba da zuwan Dan mallam
Ga bakin Larabawa..Lale..!
Jin Muryan yaya yasa ya kariso Cikin Fara"a nan Tsakar gidan ta Shimfida mai Darduma ya zauma suka Fara gaisawa Zeematu da Hamida suka gaisheshi ya amsa kafin mamanmu tazo ta zauna su gaisa Daganan ta koma Daki ta bar su shi da Yaya suna ta Fira
Amina dai tunda ta samu ta shigo Daki bata kara fitowa ba Hamida da Zeenatu suka karisa aikin suka maida komai Kitchen suka share wajem abayin Dakin tayi alwala tayi sallah Ta Haye kan gadonta bata Damu da Kwashe kayanta akansu ta kwanta bata Damu ba
Ya zeenatu ne ta shigo tana ta Fada Fadi take"Wlh Amina ki rika Karisa aikinki..Domin nan gidam ba bawanki..Ni ba Hamida bace Darajan Mamanmu kikaci Wlh..!
Amina na jinta tana Danne Dariyanta Daga kwamcen Tana kallonta kai ta kada kafin tace"Ba Laifinki bane..Mamanmu ce take Daure miki gindin Iskanci Watarana ai ba Maman ko..?
Naga uban da zai zauna kina wannan iskancin bai ci ubanki ba..!
Ita dai bata tanka ba har ta gajii da Mitan ta fice bayan Fitar Danmallam Daman Sallama yazo yi ma su Yaya Gobe Jirginsu na dare me zai tashi zuwa Jidda a Filin Sauka da Hawa na Aminu kano.
Sai da ta ficen ne Amina ta fito da Dariyanta tana Fadin"Allah Sarki..Ya Zenatu kawar ya Abida...!
Hamida ta kalleta kafin tace"Ke kam ki tashi ki gyara kayanki Amina Harda fa Sabbi ciki..!
Amina ta kyabe baki kafin tace"In kin Damu ki gyaramin Hamida!
Hamida tace"Na rantse kuma bazan yi Kaffara ba..!
Tsaki Amina taja Kafin tace"To sai ki kyaleni malama!
Hamida tace"Yau anyi Fada da Mariya da Sa"adatu..Har da Dambe sai da mallam Auwal ya Zanesu..!
Da Sauri Amina ta Mike tana Fadim"Don Girman Allah..?
Hamida tace"Wlh suna Zage Zage..Kinsan Hanne da tsoro sai kuka take yi..!
Amina ta Daka Tsalle har da shewa kafin tace"Ahyayyeee...Yau naji Dadi karshen alewa kasa.
daman ai xaman munafunci baya karko..Tacizi yatsa Kafin ta cigaba da Fadin"Naso yau naje..Da sai na kara Yamutsa wajen munafukai..!
Hamida tace"Gwara dai da baki je ba..!
Amina ta balla mata kafin tace"Ga Shedan ko..?
Hamida kina shigarmin hanci fa ki kyaleni.!.
Hamida tace "Daga Fadin gaskiya..?ai ba karya nayi ba Da kina nan wajen Allah kadai yasan iya inda abun zai kai..!
Amina ta karkace baki kafin tace"Hanne wai me aka mata take kuka..?
Hamida tace"Me kuwa..?tsoro gareta Taga suna Ta kwasan Dambe..!
Amina tace"Aikin banza Hanne banza ce..Meye abun kuka..?
Allah ya Tsareni..!
Hamida dai bata kara mgana ba Domin Har ga Allah taji Dadin da Amina bata zo ba Domin Allah kadai yasan Iya inda Fadan nan xai kai Amina sai ta hau Fadan ta siyeshi ta kara Maggi da gishiri.
Waashegari Da Safe ta shiga wajen Hanne ta iske Su Sakina suna gidan suna ta shirin Tafiya Ya Jafar zai kai su kano Ya Nasir yana da aiki a asibiti.
Amina ta kalli Hanne tana Fadin"Wai ganin ana Fada da Sa"adatun ne kike kuka..?
Hanne tace"Ni bana son ganin ana Dambe ne..Ko ke kike Fada ai ina kuka..!
Amina tace"Wlh karya kike yi..Natan Dai kike kuka ke mai yar"uwa Ki kama Kanki Hanne Domin in kece Dariyama zata yi kina abu kamar wata sakarya..!
Hanne tace"Bakomai naji..!
Kinsan yau su ya Danmallam zasu koma..?
Amina ta tabe baki kafin tace"Jiya sun zo gidanmu naji Mamanmu na Fadin yau zasu koma
Dukkansu zasu koma..?
Hanne tace"eh mana..!
Amina tace"To in suka tafi sai yaushe..?
Hanne tace"Yace ma Hajiya sai wani abu ya taso..Im bai taso ba sai nan da wata Shidda zai zo..!
Amina tace"Allah ya tsare..!
Aranta kuma Fadi take"Allah ya raka taki gona..!
Lallabawa tayi ta gudu gida abunta batama san Tafiyarsu ba su yaya dai da mamanmu sun je sun karayin musu sallama sai yamma suka Dawo suna Fadin wai har ya Jafar ya Kira suna kano basu dai tashi ba sai Dare.
Sai washegari wajen chan Rana taji ana Fadin sun sauka a jidda Daganan zasu hau Mota zuwa Madina ko ajikinta Sai taji kamar wani Nauyi ya tafi Bata ko kaunar ganinsa ma ballatana jin muryansa.
*******
Bayan wata Daya..!
Amina na kwance da Safe tana barci Taji ihun Hamida asaman kanta tana Dukanta Lokaci Daya tana Fadin"Amina tashi..Tashi.!
Next week zamu fara zuwa makaranta an gama mana komai..!
Amina da sauri ta Bude idanuwanta cike da barci tace"ke a ina kika ji..?
Hamida tace"Yanzu naji Ya Jafar yana Fadama Mamanmu..!
Amina tace"Ina zamu koma..?
Hamida tace"Ina kuwa..?Unity...?
karamin tsaki taja kafin ta gyara kwanciyarta Tana Fadin"Yanzu dai chan zamu koma..?nifa na Tsani Unity din nam..Allah yasa banda munafukar nan Sa"adatu..!
Hamida tace"Kema kin sani..Gabadayanmu ne..!
Amina ta Yamutsa Fuska kafin tace"Ban so ba..!
Naso kowa ya kama gabansa..Ke ni fa Wlh nafi son zaman gidan nan akan komawa Shegiyar Unity din nan..!
Hamida tace"Ke yanzu zaman bai isheki ba..?Tab ni Wlh na gaji..!
Amina tace"Da an bari Second Term sai mu fara zuwa..!
Hamida bata bi ta kanta ba ta Fice tana Murna Amina ta Bita da kallon Na Tsausaya.
Da yammah ma sai ga Hanne tazo suna Murna ita da Hamida Amina tun Tana Daukan mganar wasa sai gashi ta Tabbata an kawo musu sabbin kayan makaranta na Senior da Jaka da takalma Da Safa da Sabbin Littafai ya Shamsu yakawo musu nasu Ranar Monday zasu fara zuwa.
Kowa na Murna banda Amina Tsakani ga Allah Hutun bai isheta ba ta so sai Second Time su koma makaranta ammh Ina ba wanda zai bar su su zauna agida ana kallonsu Takaicinta Daya Sa"adatu bata kaunar su na Hada Hanya don bata da yarda zatayi ne kawai.
Har ya Zeenatu sai da ta mata mgana Tana Fadin"Ke Amina Hanne da Hamida na Murnan Jjc yan SS1 KE banga kina yi ba..!
Amina tace"Murnan me..?Unity ce fa..?Daman wata kayan gabas ne ba nan ba..Ni gabadaya makarantar ta isheni..!
Ya zeenatu tace"Kina da aiki..Tun Zamamin su ya Nasir Unity ta kyankyshesu ballatana ke Zuwan yau yau..Yarinya Unity Dolen kowa ne indai D'an nan gidan ne ko dan Gidan Baba Mallam ne..!
Amina baki ta Tura bata kara mgana ba Ganin yadda ya Zeenatu ta zakal kale,Tana ta bayani Hamida na Tayata su adole suna kara yabon Unity a wajenta Tabe baki tayi aranta tace ko Ta Tsani makarantar nan ba Sauyi kowa ban yayi ya gama suma kuma nan din zasu gama..!
Kullum ba cigaba haba don Allah.
*Janafty*
*TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*
*🅿️15*
*Jumma"a*
9:00am
Labulen Dakinmu Mamanmu ta daga tana kallon Amina Dake zaune Saman gadonta ta tasa kayan da mamanmu ta gama wanke mata jiya ko fara ninkesu batayi ba.
Hamida na Gefenta itama wajen Dirowarta tana shirya Littafanta Cikin Sabuwar Jakar makarantarta Mamanmu ta kalli Amina Data Zabga Tagumi kamar wacce akace mata nata ya rasu Cikin Lallami tace"Amina baki Fara Ninke kayan nan naki ba ko..?yi hakuri ki adanasu ina aiki ne da na Gyara miki..Kwashesu ki saka cikin Dirowarki in anjuma in nepa sun kawo Wuta Zan saka Hamida ta goge miki sai ki adana Kayanki..!
Hamida na jin haka ta Dago tana kallon Mamanmu kafin tace"Ni kuma Mamanmu..?
Tafada Tana Bata Fuska Mamanmu tace"Eh ke..Ko bazaki yi bane..?
Tunda ita haka Allah yayi ta bata da Zafin nama ku kuma yan"uwanta ne kun fita karsashi ba sai ku taimaka mata ba..?
Hamida bata iya mgana ba ta maida kanta Gefe Amina kuma sai Danne Dariyanta take yi kafin tace"Dama ta barshi mamanmu..!
Bata bi ta kansu ba ta saki Labulan ta koma tana Fita Amina ta Fara Dariya Har tana ma Hamida gwalo kallonta Tayi kafin ta girgiza kai tana Fadin"Kiyi Dariya son ranki..Lokacin ki ne ammh ki sani akwai watan watarana..Da babu mamanmu ba Hamida wlh sai kin raina kanki..!
Kamar ba mace ba komai sai dai ki zauna komai Mamanmu tayi miki ko kuma ta sa muyi miki..!
Tafada Cikin jin haushi Amina ta kara saka Dariya kafin tace"ko ba mamanmu ba gaki ba..?
Hamida ta Harareta kafin tace"Ni kuma sai bazan yi aure ba sai na koma kula Dake..?Sannu Amina yar gata..!
Amina tace"To miye..?Sai ki auri kanin Mijina..!
Karamin Tsaki Hamida taja Amina ta kara saka Dariya tana Fadin"Hamdiya..Hamdiya..Hamdiya..!
Take Fada cikin Sigar waka Da sai da Hamida tayi Dariya tana Fadin"Ke kika sani..Allah yasa ki shiga gidan mai mata Biyu kece na uku..Ya"ya kadai sun isheki Amina..!
Amina tace"jar uba..ya auran ma kansa dai..Mai mata Biyun daya kwashi Amina ai mai Budurwan Zuciya ne..Sai yayi Nadama Tijara ne da Jidali ne zai gani harda na Siyarwa..!
Take Fada tana Dariya Hamida na Tayata Daganan suka shiga Hirarsu Amina na tusa kaya cikin Dirowanta batare data Tsaya Ninkewa ba Hamida tace"Kai Amina mugunta ma harda karan kanki kike yi mawa..?
Amina ta tsaki kafin tace"Ki kyaleni Hamida ni nagaji..!
Hamida ta mike tana Fadin"Zaki ma mike ne yarinya yau ke kike da gyara mana Daki..!
Amina tace"Kan bala balagagge..Ranar fa ni na gyara..?
Hamida tace"Ai ba sau Daya ake gyaran Daki asati ba malama..!
Amina ta Tura baki kafin tace"To nidai na gaji bazam iya ba..!
Hamida ta bita da kallo batayi mgana ba Amina ta cigaba da Fadin"Mutum kamar jaki aiki aiki..Ni wlh nagaji..!
Hamida baki ta rike ta kasa mgana wai Amina na Mganar aiki me takeyi..?
Aiki sai ya zama Dole Amina ke yi in ba zama ba zamanta take Mamanmu na Daure mata wajen iskanci sanin da tayi bafa zata gyara Dakin ba yasa tamike ta fara gyarawa Amina na Mata Dariya sama sama tana jinta tayi mata banza kamar bata jita ba.
Har ta gama gyara Dakin bata gyara wajem kayan Amina ba ganin haka yasa tace"Hamida Kashi nayi miki akan gado da baki gyara barayina ba..?
Hamida tace"Bansani ba.!
Amina ta tabe baki kafin tace"Allah ya baki Hakuri Anty Hamidaaa..!
Ta karishe Fada tana mata gwalo karaf suka Hada ido Hamida tace"Don Allah nake yin komai ni..!
Amina tace"Allahu akbar..Allah ya Biya malama Hamdiya..!
Danne Dariyanta take yi kada Hamidan ta gani ta fasa gyara mata Sauran kayan ma Hamida ta gyara mata ta Ninke mata da kyau ta saka Cikin Wardrope din Amina ta kuma gyara mata gadon ita Amina Tuni ta shiga Tiolet din Dake Dakin zatayi wanka.
Koda ta fito har Hamida ta gama gyaran Dakin ta share ta goge ta saka Turaran Wuta Amina ta Hura hanci tana Fadin"Kai Allah yayi ma Hamida albarka..!
Komai yana son gyara ko"ina yayi kyau tas dashi,Zama tayi ta shafa mai ta saka wata Doguwar rigar Material tana cikin Daura bakin Dankwalin abaya ne Mamanmu ta kara Daga Labulan Dakin ta leko tana Fadin"Hamida zo don Allah..!
Gishiri ya yankemin ina girki..!
Amina ta Dago tana Fadin"Bata anan fa Mamanmu tana waje..!
Mamanmu tace"Ai ban ganta bane..?
Ta juya tana kiran"Hamida
Hamida...hamida..!
Yaya Dake Kofar Kitchen tana Taya Mamanmu gyaran wake tace"Hamida fa ta shiga makewayi..!
Mamanmu tace"Gishirin nan fa ya kare Yaya..Bansani ba ina Dago Buhu sai bakomai aciki..!
Yaya tace"Yafa Dade ya kusa shekara Tun Gishirin nan da Jafar ya hado cikin Wani siyayyan kayan abinci ne fa..!
Mamanmu tace"Gaskiya ya jima..Gashi Babansu ya fita ba kowa agidan..!
Yaya tace"Sai dai ki kirasa a waya,ki Fadamai ko kuma ki bada asiyo in ya Dawo sai ki samar dashi..in za"ayi Siyayyan kayan abincin wannan Watan kada a manta da gishirin..!
Mamanmu tace"Nayi tunanin haka bari Hamida ta fito ta leka shagon baya ta siyomin ta dawo da wuri kafin cikin yayinsu su ganta nasha Surutu..!
Yayaa tayi Dariya kafin tace"Aifa kinsan su masu yayyi ne..!
Mamanmu tace"Nasani ne Yaya..Yaran da ba"ason ko nan da chan sufita..!
Hamida wai ina ta shige ne..?
Yaya tace"Ki aika Amina mana..Tunda Hamidan bata fito ba..!
Mamanmu tace"Yauwa..Amina..Amina..!
Ta tafi tana kwala ma Amina Kira sai gashi sun hadu a bakin kofar Dakinsu Tana Fadin"Gani Mamanmu..!
Mamanmu ta kwanto kudi a Haban Zaninta ta mika ma Amina Dari Biyar Sabuwa tana Fadin"Maza sa Hijabin ki kije Shagon nan na baya ki amso min gishiri na Dora sanwa kuma na Duba ashe Gihirin ya kare yi maza Amina don Allah..!
Amina ta karbi kudin ta koma Daki ta Dauko Hijabin Hamida Data gani Saman gadonta ta fito flat din Takalminta ta saka baki tazo tana Fadin"Gishirin nawa Mamanmu..?
Tana gaban Famfo tace"Ki siyomin babban Jakan nan..Ki hadomin da Amo Amina wannan naga bazai kai an juma ba kuma shima shikenan jiya Zeenatu tace ta Dauko acikin Kwalin..!
Da Toh Amina ta amsa zata fice Yaya na Zaune kan kujeran yar Tsugunno ta Dago kanta tana Fadin"Saura kuma ki Dade..!
Juyowa tayi tana kallonta kafin tace"Ina zani to..!
Ta fada tana Tura baki Hararanta Yaya tayi kafin tace"Daman baki bace..Inda aka ijiyeki ba nan kike Tsayawa ba..!
Mamanmu tace"Amina kyale Yaya..Yi maza ki dwo yar albarka.
Da haka ta fice tana kunkuni afili tace"Yaya bata taba Fadin Alheri akaina..Yoni ina zani..!
Sai kuma Tayi Dariya sanin Halinta sai ta iya juya alaqanta zuwa gidansu Hanne ta ma manta da aiken Mamanmu karamin aikin Amina kenan.
Sakamakon Safe ne anguwan tayi shuru ba kowa maza sun tafi wajen aiki yara kuma duk suna makaramta Shagon yana ta bayansu kadam ne ba zuwa shago suke yi ba komai na Bukatar gida a kasuwa ake siyo shi,sai dai in wani abu ya yanke kamar irin rana mai kama ta yau
Bazata kirga Sau nawa tataba zuwa shagon ba kamar bai fi sau Biyu ba,Shagon babban Shago ne babu abunda baya saidawa mai shagon ba Dan garin bane bakano neyazo ya samu waje sai Allah ya saka ma kasuwancin nashi Albarka.
Samda ta shiga shagon akwai Layin mutum uku agabanta sai ta koma gefe sai da aka sallamesu sannan ta matsa kusa da katan Shagon ta mikamai kudin Hannunta Lokaci Daya tana Fadin"Bani gishiri babbar jaka da omo..!
Karban kudin yayi yana kallonta Ganin bai taba ganinta ba yasa yace"Wani irin Omo..?
Amina ta yamutsa fuska kafin tace"Kowani iri..!
Dauko mata yayi duka yana nemam ya Hadasu a leda Daya da Sauri tace"Tsaya tsaya..Mallama a ina kataba ganin an Hada gishiri da Omo waje Daya..?
Yana yar Dariya yace"Au na manta ne..Yi hakuri don Allah..!
Hararansa Amina tayi batayi mgana ba ya Raba kowannen Ledansa Dabam yana Fadin"Nace ba..A ina kike ne..?
Naga bantaba ganinki ba..!
Amina ta Tsaya tana kallonsa kafin ta saka Hannu ta warce ledan hannunsa tana Fadin"Ina ruwanka..?malam bani Chanjina na tafi..Tunda ba Sana"ar kake yi ba tambayan inda mutanen da suka zo siyayya shagonka suke kake yi..!
Tsiwanta ke bashi Dariya yanzu ma Dariya yayi kafin ya Hado mata Chanjinta ya bata Kamar zata Dakesa haka ta Fizge chanji kadan ya Rage ta Hada da hannunsa baki ya rike yana Fadin"Kai..Allah ya baki hakuri..!
Ko jinsa batayi ba tayi wucewarta Hankalinta na kan chanjin hannunta Tana Kirgawa shi kuma ya Sawo kansa Shagon Kansa na kasa yana Danna Wayarsa Daga bayansa kuma wani ne kebinsa yana Fadin"Oga da ka bari na amso maka..!
"Bazan iya da shiriritarka ba Nura..Na ri..!
Mganarsa ta makale ne sanda suka ci karoda juna kusan Tsawonsu Daya In maya fita da kadan ne yasa suka Daki Goshin juna Dayasa kudin hannunta da Ledan duka suka zube a kasa shidai Allah ya taimakesa wayarsa bata Fadi baya riketa Dakyau.
Amina ta saki karamin Tsaki ta Duka tana kwashe chanjinta da omon Daya Fado a leda Daga saman kanta taji anaa Fadin"Baiwar Allah ki rika Tafiya kina kallon gabanki ok..?
Sai da ta gama kwashe komai kana ta Dago suka Hada ido Hudu dashi Kallonta yake yi da Fararan Idanuwansa kamar yadda ta sakarmai nataa manyan Idanuwan Cikin kallon kama Raina ni tace"Dakata mallam..Ni dakai waye baya kallon gabansa..?
Ni fita zan yi kai kuma zaka shigo acikin ni dakai wazai kalli gabansa..?
Ta karishe Fada tana Hararansa Harda Murguda baki kafin ta Raba ta gefensa zata wuce.
Cikin Wata sanyayyar Murya mai Cike da yanga taji tace"Ya zaki tafi..?,Alhalin baki bani hakurin Laifin da kikamin ba..?
Juyowa Amina tayi tana kara kallonsa kafin ta Nuna kanta tana Fadin"Ni..?
Kai ya gyada mata cikin yanga Lokaci Daya yana Jaye Hulan kansa Facing cap Kyakyawan Farar Fuskarsa ta bayyana.
Amina tace"ai ban yi maka wani Laifi ba ballatana na baka Hakuri..Kumani Amina ban cika bada Hakuri a laifin da ban aikata ba wani Lokacin ma ko nice bani da gaskiya bana Laushi da wuri..!
Ta saman Lebenshi yace"AMINA...!
Nice name..!
Kin fada min sunanki batare da na sha Wahala ba..!
Amina ta Tsaya sake da baki tana kallonsa Wabda ke gefensa ne yace"Oga..!
Bai bari ya karisa ba ya Laluba aljihunsa ya Dauko Walet dinsa ya Mikamai yana Fadin"Kayi abunda ya kamata Nura...!
Karba yayi yana kallon Ogan nasa Daya Fara susucewa ganin wannan Kwailar yarinya to kwaila mana wannan ta wuce sha Biyar tsawon kafa ne kawai Kafada ya Daga kafin ya Nufi Cikin shagon Dutse zasu koma yanzu nan Kati ya yanke ma Ogansa acikin waya suka Tsaya su siya to lokacin ankirasa a waya ya Dauka sai Ya kasa jira ya fito da kansa zuwa Cikin Shagon..!
Amina bata kara mgana ba ta fara tafiya da Hamzari ya sha gabanta yana gyara zaman Jaket din Dake Jikinsa Cikin Mamaki da Budewar ido Amina tace"Malam lafiya?Mtsamin Daga Hanya tunda bata gidan ku bace..!
Mirmishi yayi har sai da Fararam Hakoransa suka bayyana Cikin Muryansa yace"Wani ya taba Fada miki kina Burgesa..?
Yafada yana kallonta Cikin wani Salo Sai kuma taji mganar ta shigeta Cikin Sausasauta Murya tace"Ni AMINA ba wanda ya taba cewa ina Burgesa..Ni ai bana Burgewa kowa.!
Wayarsa ya saka Cikim Aljihun Jaket dinsa Lokaci Daya yana Fadin"To yau Ni AMINU BUBA nace kina Burgeni...!
Ido Amina ta zaro tana kallonsa mganar ta shigeta kanta ta kara nunawa kafim tace"Da gaske ina Burgeka..?
Kai ya gyada mata Sai ta washe bakinta kafin tace"Nagode..yau na fara ganinka ammh naji Dadin Haduwa Dakai domin kai ne Mutum na Farko Daya fara cewa Amina Aminene na Burgesa bazan manta da wannan ba..Thank you..!
Tafada tana Juya idanuwanta cikin bayanna Farimcikinta Shagala da kallonta yayi baisan ya Furta"She is Beautifull...!
Bai an kara ba yaga tana Shirin Tafiya da Sauri yace"Ya zaki tafi kuma ki barni..?
Da mamaki Amina tace"Bangane ba..?
Mirmishi yayi kafin yace"Ke yar nan garin ce..?
Da kai ta amsa mai cikin mamakinta da kuma kara ganin yarintarta yace"Ammh baki sanni ba..?
Amina tajuya ido kafin tace"To a ina zan san ka bawan Allah..?
Da sauri yace"Sunana Aminu..Aminu Buba..!
Nayi matukar mamaki da baki sanni ba Shekararki nawa ne..?
Amina tace"Shekarata goma sha Biyar da Wata Goma saura wata biyu na cika Sha shidda..!
Tafada tana Kirgamau da hannu Dariya ta kamasa har sai da Wushiryansa ta bayyana.
Tsayawa tayi tana kallonsa yadda yake Dariya abun sha"awa.
Cikin Matse Dariyansa yace"Amina..Amina kina Burgeni..!
Zan so na rika ganinki koda yaushe ko domin ki rika sakani Nishadi Aji nawa kike a makaranta..?
Kunya Amina taji yasa ta sunkuyar Dakai kafin tace"SS1 sai monday ammh zamu fara zuwa..!
Yana mata Dariya yace"Kice Jjc ne...!
Amina yan matan SS1..!
YAadda yake Dariyan ne ya fara Kular da ita yasa ta Hade ranta Nura Daya Fito Daga shagon tun dazu ya gaji da ganin wannan Drmar yayi gyaran Murya yana Fadin"Oga lokaci fa na Tafiya....!
Hannu ya Dagamai kafin ya fiddo da wayarsa yana mikama Amina Lokaci Daya yace"Sakamin Lambarki..Amina ai daman Amina kawar Aminu ce ko..?
Yafada yana Dariya itama Dariyan Tayi Domin Farat Daya taji ya burgeta kamar yadda yace itama ta Burgesa.
Noke Hannu tayi kafin tace"Ni ai bani da waya..!
Ido ya zaro kafin yace"Duk girmanki Amina saura fa wata Biyu ki kai shekara goma sha Shidda!
Ya karishe Fada Cikin Zolaya Da sauri Ta kauda kai tana Mirmishi Kara Tura mata wayar yayi yana Fadin"Ko lambar Antynmu Babu Amina..?
Amina tace"Tab..Bafa mai waya agidanmu Daga yaya sai mamanmu to ta yaya ma Jawaad ya jefata ruwa
Ta mamanmu ce kadai ta rage sai kuma ta Aba..!
Da sauri yace"To sakamin ta mamanmu ko ta Aba din..!
Ido ta zaro kafin tace"Tabdijam..Rufamin asiri ba ruwana kaga mallam bansan ka ba sai anjuma..!
Kafin yayi mgana ta wuce da Sauri harda gudu Kiran sunanta yake yana Amina..Amina ita ko Waige batayi ba sai dai ta kule ya Daina ganinta sannan ya Dafe kansa.
Nura ya kariso yana Fadin"Oga Oscar na Kira na fa kuma nasan kai yake nema..Sannan ka koma mota kafin mutane su farga Dakai..!
Lokaci Daya yana mikamai katin Daya siyo Airtel na 1k Mtn ma haka bai tsayama karba ba ya wuce Ya bude gaban wata Farar Bugatti ya shiga yana Fadin"Nura bana son mita..Kyale Oscar tukani muje kawai..!
Kai ya girgiza yana mamakin Yar yarinya karama Oga ya zauna yana bata Lokaci a kanta kafin ya Zagaya ya shiga Mazaunin Direba ya Tada Motar sukar bar Layin da gudu kamar zasu tashi Sama.
Koda Amina ta koma gida sai da Mamanmu tace"Amina ina kika Tsaya..?
Amina tace"Mamanmu chanji ne Babu..!
Da wannan karyan ta Kashe mganar Duk Surutunta ta kasa bama ko Hamida Labarin Haduwarta da Aminu buba kamar yadda yace sunansa Ranar duk in ta Tuna sai tayi Mirmishi ita kadai a kallah yau ita Amina ta samu wanda yace komai nata na Burgesa ashe itama Macece kamar kowa wannan yabon ya xauna aranta da Har Abada bazai fita ba.
Ko washegari a hadda bata yarda ta Fadama ko Hanne da bata boye mata komai ta kasa bata Labarin Haduwarta da Farin mutanin da ya kasa barin Ranta Ko yaya ta Tuna dashi sai ta murmursa acikin Ranta.
Da suka tashi Sallah ne Amina ta kalli Hanne suna wajen alwala Tace"Hanne ashe nima ina Burge mutane..?
Hanne na kuskure baki sai da ta Furzan da ruwan bakinta kafin su hada ido da Hamida suka kwashe mata da Dariya Duka Amina ta Dirkama Hanne a baya tana Fadin"Bana son iskanci ban tambayi Hamida ba sanin Halinta yar bakin ciki ce.!
Hanne na Dafe inda ta Daketa tana Fadin"Muguwa..Uban wa zaki Burge..?
Hamida ta Karbe da cewa"Sai dai ki Gunduri mutane Jidalinki Amina wlh bamai iya Daukansa sai mu da muka Saba..!
Hanne tace"Wlh wani waje duka zataci in taje tayi..!
Dariya suke ta mata ita kuma bata su take ba Hankalinta ya tafi Tana Jin Muryan Aminu sanda yake Fadamata Tana Burgesa ita din abar Burgewa..!
Daga Ranar bata kara musu mganar ba sai dai yana Ranta Lokaci bayan Lokaci yana Fado mata acikin Ranta.
Har tazo Ranar Monday suka fara zuwa makaranta Sun samu Dalibai irin su da suka Cigaba da Unity sannan akwai Sabbin Dauka kamar yadda aka saba Amina ta cigaba da abunda ta saba sai ma abunda yayi gaba ta addabi Dalibai da malamai Sai kuma akayi Rashin Sa"a aka hadasu aji Daya da Sa"adatu Hanne da Hamida Ajinsu Daya.
Amina kamar ta mutu saboda Bakimciki tace ma Hanne"Naso aji Daya aka hadamu hanne..Sai dai ban da Sa"a anhadani da Shegiyar Sa"adatun nan..!
Hanne tace"Ina Ruwanki da ita..?
Amina tace"Ta shiga Harkata Dakuwa zatayi..!
Sa"adatun bata shiga Harkan Amina Saboda Anty Amarya taja kunnenta Sosai kan Amina shiyasa ko Aminar Zata takaleta bata bi ta kanta.
An hadasu Aji Daya da Zainab Isa Kawar Amina sai suka Kulle atare Sit dinsu Daya Dalili kuma tana Aro mata Littafan Hausa na kishiyar mamanta take Sato musu ta kawo makaranta su karanta ita Zainab Amina take kawo mawa,ita sai agida ta ke shigewa Dakinsu ta Boye ta karanta sannan bayan su Hanne Zainab isa ta jure Gwagwarmayan Amina da Jidalinta.
Kwanci tashi ba wuya a wajen Allah su Amina sun mika cikin Zangon karatunsu na Farko a SS1 dinsu cikin salama da kwamciyar Hankali kamar Amina tayi sanyi Saboda ta Rage Tonon Fada sai dai jidalinta da Masifarta sai abunda yayi gaba Dakyar Hajiya ta rokar musu Baba Mallam ya bari Idi Direba yakai su gidan ya Ikram Dukkansu har da su ya Abida su Amina an sha Murna har Fada sai da taja su hanne suka shiga da karambaninta.
Abida tace"Kai amina bala"i wlh watarana sai takai kanta inda zata mutu..!
Ya Ikram tace ko ita sai da mijinta take shiga Gidan Sarki batama san Hanya ba sai ga Amina tana kutsa kanta Kusfa kusfa,Chan suka mata wuni sai yammah suka dawo suna Santin Haduwar gidan kamar aturai Amina tace"gaskiya gida biyu suka tabamin kyau..Daga gidan ya Danmallam sai gidan ya ikram..!
Hamida tace"Gaskiya gidansa shima ya Hadu tsarin daidai kamar aturai..!
Haka dai sukayi ta santin gidan Har Mamanmu na saka baki tana basu Labarin Tsaruwan gidan Sadiya Dake Dutse Amina tabe baki tayi batayi mgana ba sai da Hamida tace"Kai zan so naje ngani mamanmu..!
Yaya na gefe tace"Naji kamar ance cikin watan man zata bi mijin chan kasar Dayake aiki..!
Mamanmu tace"Nima haka naji Haj.Nasara na tadin ita da Haj.Uwa..!
Amina tace"Ni kam ban sha"awar zuwa..Nasan bazai kai yadda nake Hasaahe tsaruwa ba..Shiyasa naga yau Sa"adatu nata wani yamutsa Fuska araina nace an ga inda aka fi su..!
Hamida tace"Kai Amina baki son zaman lafiya..?
Balla mata Harara tayi kafin tace"Eh din ke kuma an tabo masoyiyarki..!
Ganin zasu fara fadan nasu ne mamanmu ta Tsawarta Ya Zeenatu na Gefen Yaya tace"ZAman lafiya ko na Minti Daya ne Amina bata kaunarsa..!
Amina na jinta ta Daga kanta sama aranta tana Fadin"Eh din..!
Nan dai mganar tatashi ta koma Tsakanin su Mamammu da su Hamida Amina bata kara saka baki ba Kada tata ta karayin zafi.
Ana cikin haka acikin Satin Matar ya Jafar ta Haihu Anty Shamsiya.
Su Amina Sai ana gobe suna suka samu zuwa barka shima din su Yaya da su Hajiya sukabi da zasu barka mamanmu ita ke zuwa tana Ma jariri wanka wanda yaci sunan Baba Mallam
Suna zaune Jaririn na Hannun Hanne Amina ta karkato tana Fadin"Wlh bakinsa Sak na uwar ne..!
Hanne ta Zunkuleta tana Fadin"Ba Ruwana Amina..kada taji.!
Amina na Danne Dariyanta ta Dago tana Fadin"Mamanmu kalli jaririn nan yana karami bakinsa babba..!
Hamida da Hanne da suka san mganar suka yi tsumu tsumi.
Hajiya Uwa ce tace"Banda abunki Amina ai jariri ne yana girma zai Sauya..!
Mamanmu tace"Mai sunan mallam fa Shamsiya ce Sak..Kila sai nan gaba zamu ga Jafaru..!
Akayi Dariya Shamsiyan na gefe batace komai Amina nata Dariya sai da suka fito zasu tafi Hamida ta jawota Tana fadin"Amina wlh ki bari ba kyau kushe hallitar Allah..!
Hanne tace"Kuma bata san me zata haifa ba!
Amina ta toshe kunnenta tayi gaba Tana Fadin"Nagode da wa"azi Malama Hamida da malama Hanne..!
Kyaleta sukayi ganin bazataji ba Washegari sun so su koma Mamanmu tahanasu tunda ya Jafar din yace ba suna ba Taro an dai yanka Raguna Mallam yaje yayi barka da kansa.
Ranar kwatsam sun je makaranta sai ga Zainab tazo da karamar waya Tecno mai memory,Tsohuwar ta Anty ta ce aka bata akwai Memory aciki ita Amina waya ba Damunta tayi ba Shiyasa bata Damu ba
Acikin yan ajinsu akwai masu waya Ranar an tashi Break Taji Zainab na ma wata Saratun ajinsu mganar ta Turamata Sabbin Wakoki
Tana Daga sit dinsu tana karatun Wani Littafin da Zainab ta aro mata mai suna Yar Jagora.
Duk da kunnenta baya wajen taji Sunan Radau acikin kanta.
Saratu ta kalli Zainab tana Fadin"Ni ban da wasu wakoki Zainab..Sai dai ina da Sabbin wakokin AMINU buba Da yayi kwanan in kina so sai na Tura miki..!
Kamar a mafarki taji ankira sunan ta Taba jin sunan ta kuma Haddace sunan acikin kanta.
Da Zumudi a Murnan Zainab tace"Yauwa don Allah sakamin..Ina son wakokinsa..!
Daga sama kawai suka ga Amina Sanda ta Dafa Saratu tana Fadin"Wani Aminu Buban..?
Da mamaki suke Binta da kallo kafin Zainab tace"Mawaki ne mai Tashe Amina..!
Ido ta zaro kafin tace"Da gaake..?kina da Hotonsa..?
Zainab cikin mamaki tace"Hotonsa kuma..?a"a ni bani dashi wakokinsa kawai nakeji shima a wayar ya Kamal nasansu..!
Saratu ce tace"Yayata nadashi in kina son ganinsa ki bari gobe zan turo miki..!
Da sauri Amina tace"Yauwa don Allah ki turomin akwai wani dana sani ne in so nagani ko shi ne..!
Da mganarta suka yarda da ita Washegari kuwa suna zuwa makaranta Saratu tace ma Amina ta Turo Hoton a wayarta Vivo Lokacin da Amina ta ga Hoton sai da Gabanta ya Fadi.
Yana Sanye cikin Riga da wando Ja da Fari Wandon Ja ne Rigar ciki Fara sai Jaker dinsa ja Takalmin kafarsa Booth ne fari haka ma Facing cap din Kansa Ja ne mai Kalan Fari yayi Tsayuwar matasan wannan zamanin Fararan Hakoransa mai Wushirya duka suna waje a kasan Hoton an sanya A.A BUBA..!
Sai alokacin Amina ta tuna yana ta Nanata mata bata sanshi ba..?Ashe cele ne shi to ita ina zata sanshi..?
Ba waka suke ji ba ballatana kallo.
Saratu ta karbi Wayarta tana kallon Amina Zainab isa ce tace"Shine..?
Sai ta samu kanta da girgirza kanta Saratu tace"Kila suna ne yazo Daya..Shi wannan Aminu Aliyu Buba sunansa mawaki ne mai tashe yadda naji ana Fada bai Dade ba sunansa yayi Fice..!
Amina na jinsu batace komai ba Zainab ce ta karba tana ganin Hoton kafin tace"Kyakyawa dashi kamar Bafullatani..!
Saratu tace"Ance Bafulatanin Yola ne..Karatu ya kawosa kano..ya fada Harkan waka..!
Amina ita Daga Lokacin batama jinsu Tana chan Tana Mirmishi Lalle Amina mai Sa"a ce yau ga Wanda Duniya ta sani ya Taba cewa tana Burgesa anya in ta Fadama Mutane zasu yarda da ita..?
Taso gaban irin su Sa"adatu ne ta tabbata sai Haushi ya kashesu ita Kadai kawai in ta Tuna A.A Buba ranta sai yayi Fari kanta ya kara Girma Ho..Sai ita Amina Aminene Manya kasa..!
*Janafty*
*TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*
*Sadaukarwa ga Halima yusuf gwarzo (Besty) Alherin Allah ya kai miki duk inda kike*
*🅿️16*
*Yola..*
BAYAN WANI LOKACI..!
Kwata kwata bai ji kiran sunansa da take yi ba sai da ta Daddage ta Dirkamai Duka a gadon bayansa kana ya dawo cikin Hayyacinsa Dago Shanyayyun Idanuwansa yayi ya zube akanta cikin kosawa yace"Haba Nenne..!
Haba..!
Ya ke fada yana sosa bayansa Hannu ta kai zata kara Dukansa ya mike Tsaye da Sauri yana Fadin"Haba mana Nenne..!
Wannan ai cin zali ne..!
Tana Hararansa tace"Awa na nawa a Tsaye akan ka ina ta mgana baka ji ba..?
Anya Aminu wani abu baya Damunka..?
Tun shekaranjiya da ka iso nake ganinka cikin Zurfin Tunani ko Mtsalan wajen aikin naku ne..?
Bayansa yake sosawa kafin yace"Shine Zaki Saki karfin da Allah yayi miki ki Dake ne..?
Haka ake yi Nenne..?
Kunnensa take neman taja ya matsa yana Dariya yace"Tsaya..Tsaya..Wlh hannunki kamar na maza saboda zafi..Nenne akwai karfi..!
Kinsan mu Jikinmj mai Laushi ne Nenne zata yi kisan kai..!
Yana yi yana Dariya itama Dariyan take Farar mace ce,kamar sa sai dai itama bata da wani Tsawo kamarsa Suna da Diban kama ta Hasken Fatarsa ba wata babba bace domin Iyakarta wajen Shekaru arba"in da wani abu.
Ganin ya shagala yana Dariya yasa ta Shamacesa ta Murdo Wuyansa yar kara ya saki yana Fadin"Wayyo Allah..Jama"a
Haba Nenne zaki karyamin wuya ne..?
Cikin Fada tace"Ka maidani kakar ka ko Aminu..?
Ga Breakfast dinka chan tun dazu har yayi sanyi kana zaune tunda ka zauna sai faman Tunani kake yi..!
Da sauri yace"To naji Sake ni in miki Bayani..!
Sakinsa tayi kafin ya juyo Kafadanta ya Dafa yana Fadin"To banda abunki Nenne duk duniya wa nake dashi bayan ke..?kece uwata kece Ubana, kuma kece kakata..Dole nayi wasa dake..!
Mirmishi ta saki kafin taja Hancinsa tana Fadin"Nima bani da kowa sai kai..Kasani ko..?
Yana yar dariya yace"Sai kuma Sabuwar suruka in na kawo miki..!
Baki ta washe gabadaya tana Fadin"Aminu da gaske kake..?
Innalillahi a ina take..?
Ganin yadda ta Rude ne yasa yace mata"Nenne..Haba..Nace in na samo miki Suruka bawai na riga na samu bane..!
Duka taso Dirkamai ya Zura da gudu zuwa Bangaransa yana Dariya itama Dariyan take Lokaci Daya tana Fadin"Zaka zo ka sameni karyan Tsiya kake..!
A tsakiyar kayattacen Dakinsa ya Tsaya Kafafuwansa ya Nitse kan Tattausan Cafet din Daya malale Falon,Hannunsa Duka ya saka saman kansa yana Birkita gashin kan nasa meke Faruwa dashi..?
Yarinya karama taki barin Tunaninsa Tun sanda ya baro Dutse ko da rana Daya bai iya mantawa da ita ba a dukkan abunda yake yi Tunaninta da yanayinta da mganarta suna Gilma masa ya Dauka da gaske mganarta da Tsiwarta ke Burgesa sai dai yanzu da Lokaci ya tafi abun bai sauya ba.
Duk Yanmata hadaddun Da suke Rubibi akansa bai ga wacce ta kasa barin Tunaninsa ba Irin Amina Yazo Yola gida ne domin ya Huta na kwana Biyu ammh tunda yazo bai da aiki sai Tunani ko yaso ya kaucema abun ya kasa bai kara Tabbatar da ba iya Burgesa yarinyar take yi ba Harda wani abu Dayake jansa wanda bai gama Sanin koma Miye ba,sai da yazo gida.
Abu Daya ya sani zai Nemota kusa dashi Domin ya samu Tabbacin Burgesa take yi ko kuma wani abu ne Daban wanda baisani ba.
Da wannan Tunanin ya karisa samam makeken Gadon Dake dakin ya Dauko Farar wayarsa Kirar Samsumg.
Nura yaronsa ya Doka ma kira da Sanyin Safiya sai da ma ya Kira ya Duba Lokaci 10:00am na Safe tun motsa jikin Daya fita ya Dawo ya shiga Dakin Nenne suka gaisa yazo Falo ya zauna ya shiga Tunani Tunanin yarinya karama wacce Bai taba Tsamannin zai taba Haduwa da ita ba.
Sai da yayi ma Nura Kira Biyu sannan ya Daga kiran cikin Alamun barci yace"Oga Lafiya kuwa..?
Karamin Tsaki yaja kafin yace"Bansani ba..Dillah mallam ka wartsake..Wani aiki zan saka ka..!
Da sauri Nura yace"Afuwan Oga ina Sauraranka..!
Sai da ya gyara Tsayuwa kafin yace"Yarinyar da muka Hadu da ita kwanaki..Nake son kafin nan da zuwa Dare in ji komai akanta in nace komai ina Nufin komai..!
Cikin Mamaki Nura Dagachan bangaran yace"Wata yarinya kenan Oga..!?
Cikin Bacin rai yace"Bansan yawan Tambaya kasani Nura..!
Shuru yayi mai domin bai gane wata yarinya ba Yanmatan ai suna da yawa ganin yayi shuru yasa yace"Ina yarinyar nan da muka hadu da ita a Dutse..Oh..Ba Dutse ba yama sunan garin da mukaje Shooting din wakar nan Last Month..!
Nura yace"Munje Hadejiya da Gumel sai Jigawa wanne Daga ciki..?
Aminu yace"Inaga Gumel ne in da muka Tsaya Shago siyan kati har naci karo da wata yarinya wata baka mai ido mai mgana tana da Tsiwa haka..!
Baki Nura ya Hamgame yana jin Ogansa mamaki duk ya cikasa Cikin mamaki yace"Wannan yarinyar Oga..?
Karama ce fa..!
Da sauri yace"Ina Ruwanka..Do as i say..in bazakayi ba zan kira T..!
Da Sauri yace"Zan yi..Zan yi..!
Bai jira cewarsa ba ya Datse kiran yana Fadin"Nura yana da matsala...!
Haka ya fada kafin yayi Cilli da wayar saman gado ya taka cikin Sassarfa ya Shiga Tiolet din Dake Cikin Bedroom din.
Aminu Aliyu Buba Haifaffan garin Yola ne Bafullatani ne ta bangaran uwa dana Uba,mahaifinsa da Mahaifiyarsa hatsarin mota sukayi suka rasu tun yana da shekara Goma aduniya kuma shi kadai suka Haifa karamar kanwarsa tun kafin ayayeta Ciwon kyanda ya zama ajalinta.
Sai Rikonsa ya koma Hannun kakarsa wacce ta Haifi Mahaifiyarsa,mahaifiyarsa tana da Tarin kannen da yayyi wadanda suke Uba Daya tunda alokacin matan babansu Hudu Aisha itace Wacce suka Fito Ciki Daya ita da mahaifiyarsa kuma Allah ya Doramata Kaunar Aminu tun sanda aka Haifesa yana karamin sa yana da kyau da kwarjini irin nasu na yara.
Sadaukarwan da Aisha tayi ma Aminu mai girmane wanda baki bazai iya Fadi ba saboda shi tayi aure aure har Hudu baata zauna ba Saboda duk inda Tayi aure sai tace da Aminu xata tafi wanda yake kamar kani gareta yana da Jikin girma yasa ya kamota ita kuma gata Daman bata da tsawo.
Yawancin Rayuwarsu a Yola sukayi an gaji da Mgana an kyale Aisha Domin tace matukar ba zata zauna da Aminu ba sai dai ta Hakura da aure da Kuruciyarta ta zauna agida tana kula da Aminu ta zamemai uwa da uba da yar"uwa shima komai ya samu itace Dalilinsa ta samu Sunan Nenne sunan Daya Bita kowa dashi yake Kiranta.
Kakkaninshi suka taimakamai yayi karati har matakin Secondary Nenne iyakarta Diploma bata cigaba ba Lokacin shiga Jami"a sai Aminu ya nuna kano yake son tafiya ba gaddama aka kai mai Cuku cuku ya tafi Tunda bayan ma haka Mahaifinsa Alhaji Buba ya mutu ya barmai Tarin kaddarori gidaje da Filaye.
Zuwansa kano ne mafarin fara wakarsa ammh bai taba Tsammanin ba Haduwarsa da wani abokinsa Oscar shima mawaki ne,Dakinsu Daya shima anan Buk din yake karatu Cikin ikon Allah kuma yana da Rabo acikin Harka cikin Lokaci sunansa ya fita bai samu matsala da kowa ba sai Nenne itace ta nuna tafi son ya maida Hankali a karatu ammh itama sai da yaja Ra"ayinta ta amince.
Kafin ya gama Jami"a Sunansa ya fita waka ta karbesa kuma ya samu Alherai da ita ba adadi yanzu haka yana cikin mawakan da Yan Film suke Damawa dashi Tun shekaru Biyu da suka gabata yana kasuwancin shigo da Motoci da karafuna Da kudin gadon Daya gada sannan yana da Shagon sai da gwala gwalai anan garin kano.
Yayi gida anan kano nashi na kanshi yaso ya Dauko Nenne su dawo Alhaji Babba yahana yace ba inda zai kaita Shiyasa ya gina mata gida kato shi da ita Ya Daukota suna zaune tare daga ita sai yan aiki da ya"yan yan"uwan tunda Duka auran duk da tayi bata zauna ba ballatana ta Haihu Aminu ne komai nata shima itace Duka Duniyarsa babu abunda bai ijiye mata na jin Dadin Rayuwa ba Domin komai ya Zama a wannan Duniyar itace Kan gaba.
Yafi zama a kano saboda Harkokinsa,Sai kuma garuruwan da suke zuwa in zasu shooting din waka Aminu baya shaye shaye kuma baya Harkan mata sai abunda ba"a rasa ba Matashi ne dan kimamin shekara 30 aduniya ne mai ji da kuruciya da kudi Yanmata sun na kawo masa hari ammh bai taba maida kai ba Nenne ma ta matsamai yayi aure ita da Alhaji Babba ammh suma baya maida kai sai yace Lokaci ne bai yi ba Yana so yayi aure saboda Farincikin Nenne sai dai bai sa nan kusa ba Domin bai Taba jin wata mace aransa ba yasan suna sonshi ne saboda suna da kuma Kudi ammh Haduwarsa da Amina komai ya Sauya yasani yarinya ce ammh kuma Rayuwarta Cikin Burgewa Bata da damuwar komai ashekarunta kudi ko suna basu da Muhimmanci awajenta
Har ya fito wanka Tunanin bai bar kansa ba yana son jin komai akanta Saboda yaga ta ina zai fara yana son ya kara ganinta nan kusa komawa Gumel ya kamasa Duk da wannan ne Lokaci na farko daya taba zuwa garin
Agurguje ya shirya cikin manyan kaya cikin gari zai shiga ya gaida Alhaji Babba kuma in ya je da kananun kaya Daga shi har Hajja sai sun tasomai Shiyasa yayi shigar Farar shadda riga da wando da Hula.
Daga Dakinsa kai Tsaye Dakin Nenne ya Nufa ya isketa tana gyara adon wata Sarkarta,bataji ma shigowarsa ba sai Hannunsa dataji ya saka ya karbi Sarkan yana Fadin"muga Abun da Nenneta take yi da bataji shigowata ba..!
Sai Lokacon ta Dago tana kallonsa Cikin Farimciki tace"Masha Allah..Ka ganka kuwa..?kamar bakai ba..Hala gidan Alhaji babba zaka je ko..?
Kai ya gyada mata yana Kokarin gyara mata sarkar lokaci Daya yana Fadin'Kina son sarkan nan Nenne..!
Hannu ta mikamai Tana Fadin"Sosai..Bani kayana kagani sakashi zan yi..!
Bai musa ba ya zagaya ta bayanta ya saka mata yana Fadin"Ko zaki shirya muje tare ne..?
Kai ta girgiza kafin tace"Ina da Bakuwa..Hajiya Iklima ta kirani tacemin zata zo kada mu fita tazo bata sameni ba..!
Dan baki ya tabe kafin yace"Ok..Bari na wuce ni..Sai an juma zan dawo domin zanshiga cikin gari mu gaisa da Friends dina mun kwana Biyu bamu Hadu ba..!
Kai ta gyadamai kafin tace"Shikenan kada kayi Dare..Sannan ina Fatan ka Karya..?
Da sauri ya gyada mata kai Saboda baya son ta takuramai kuma bayajin cin komai Dukawa yayi ya Sumbaci kuncinta kafin ya Fice da Sauri Ta Bisa da gudu tana Fadin"Aminu zan ci maka mutumci da Dabi"ar nan fa..!
Tana jinsa yana Dariya yana Fadin"Haba Nenne watarana fa Madina zamu koma Dole mu koyi gaisuwan Larabawa..!
Mirmishi take ita kadai Burinta ya gama cika Saura abu Daya Aminu ya samu matar aure ta gari taga ya"yansa shine Babban Muradinta.
Ranar Wuni yayi zirga Zirga achan gidan kakanin nashi ma Chaa akayi mai kan mganar auran kansa Kadai yake shafawa yana fadin Lokaci ne bai yi ba ko abokansa na nan Yola suna ta mai tsiya domin su kam daga masu yara sai masu kokarin Karin ta Biyu.
Bai shigo gidan ba sai bayan Isha"i shima sai da Nenne ta kirasa haka take Koda ya girma tana Tsaye kan Tarbiyasa ko yana kano Dare nayi zata Kira taji inda yake tana tsoron Gurbacewar Tarbiyan Matasan zamani akan Aminunta
Tare sukayi Dinner shi da ita da Wasu yan Biyu Hassana da Husaina ya"yan kawartace Hajiya Iklima ta bar mata su kwana Biyu tunda suna Hutun makaranta Daman suna zuwa Aminu ya saba da yaran suna da shiga rai su suka Daukemai Hankali ya manta da Batun kiran Nura sai da yaga Kiransa wajeb karfe Tara na Dare sannan ya Tuna.
Sabewa yayi ya koma Dakinsa baya so Nenne ta Fahimci komai yasanta yasan Zuciyarta yanzu sai ta Girmama abun Fiye da yadda yayi tsammani kiran ya katse sai kara kiran Nuran yayi yana Dagawa yace"Nura kada ka sanar dani sabanin abunda na saka ka..!
Ajiyar zuciya Nura ya sauke kafin yace"Tun bayan da muka gama waya Na shirya na tafi Gumel Oga..Ban sha wahala sosai ba Saboda gidansu yarinya ba Boyayyen gida bane..Gida ne da ko kai na Fadama sunan zaka san sunan..!
Cikin Mamaki Aminu yace"Wani suna kenan..?
Kai Tsaye Nura yace"yarinyar tana Daga cikin Ahalin babban Malamin nan Sheick Yunus Abdulrahaman bazanga..!
Aminu yace"Sheik Yunus Abdurrahaman Bazanga..?
Nura ya gyada kai kamar yana ganinsa kafin yace"Eh shi Oga...!
Aminu ya jinjina kai ai ba wanda baisan Mallam bazanga ba in baka sanshi a Fuska ido da ido ba kasanshi a Talabijin ko ajaridu ko kuma awajen wani Taro na Malaman sunna.
Cikin Kosawa yace"Ina jinka..yarsa ce ko Jikarsa..?
Nura yace"Shine bansani ba..Ban samu Cikakken bayanin Dangantar Mahaifinta da shi Mallam bazanga ba..Sai dai an bani Tabbacin kamar D'a yake garesa gidajensu suna jikin juna ne nan bayan inda muka hadu da yarinyar sannan Mahaifinta ne kan Duka kasuwancin Mallam din..Sannan iyalansu a Hade suke komai Tare suke Hatta Ragamar aurar dasu Mallam din ke gudanar da komai wasu suna Tunanin kanin sa ne wasu kuma suna Tunanin Shine Babbar D'ansa..!
Aminu yace"Naji wannan ita yarinyar fa..?me ka sani akanta..?
Nura yace"sunanta Amina Sa"idu Yarinya ce karama Tana aji Dayan babban Sakandiri yanzu a makaranta tana zuwa Hadda da Islamiya,Dokar gidan gaskiya yadda na samu Labari gidan Tarbiya ne basa fita Daga makaranta sai gida sannan basa Tadi da Samari ko auransu ana Tunanin auran Hadi ne sannan iyakarsu Sakandiri ake aurar dasu, su goma sha Daya ne agidansu itace Karama awajen Mahaifiyarta sannan matan babanta biyu..!
Aminu ya sauke Numfashi kafin yace"Yanzu ba yadda zan yi na kara ganinta..?
Nura yace"Ba mafita. domin ko makaramta Mota ke kai su ya dawo dasu..Mai bani Labarin ma yayi matukar mamakin Da nace masa mun ganta ya Tabbatrmin da Ahalin gida basa zuwa ko"ina..!
Aminu ya sauke Numfashi kafin yace"Ya zama Dole na Hadu da ita..Gobe zan shigo kano..ka shirya zamu koma Gumel..!
Daga haka ya Datse kiran ya bar Nura bakinsa Bude meke Damun AA.buba ne..?
Wannam yarinya zai kare mawa duk matsayinsa..?Tsaki yaja acikin ransa yana kunkunin yadda Aminun yasa shi zuwa gumel ayau din nan Allah yasa Bawani sha wahala ba Tunda ba Boyayyen gida bane, shagon da suka fara haduwa ya fara isa Daya tambayesa ya tabbatarmai shima bai santa ba wani ne a kusa Dayaji Mganar da sunanta da yanayinta yace ya santa kanwar abokin kaninsa ne Shamsu ya"yan gidan Bazanga ne a bakinsa ya samu Duka Labaran Daya zo ya Fesa ma Aminu dawowarsa kenan ko Hutawa bai yi ba..
Indai ko Oga son yarinyar yake ya kwafsa yar yarinya yar cikinsa bakomai Cikinta sai rashin kunya.
Aminu kuwa yana ji aransa ya zama Dole ya koma ya sake ganin Amina Saibyanzu ya kara tabbatar ma kansa bata sanshi ba gidan Malamai ba"a wani samun sakewa ballatana Har taji waka ko tasab sunanshi.
Yana ji ajikinsa kamar akwai wani abu mai girma Tsakaninsa da yarinyar bazai gane haka ba sai yaje ya kara ganinta ya kara tabbatar da abunda yake ji akanta.
********
*BAYAN SATI DAYA..!*
Gumel...!
"Wlh in na yarda Allah Tsinan..Kin manta jiya ma da muka dawo agidanku na sauka kenan yau gidannmu zaki sauka yarinya..!
Amina ta fada tana Faman Jan hijabin Hanne Hamida na gefe tana musu Dariya dukkansu kayan makaranta ne ajikinsu da Uban jakunkuna Hanne Fadi take"Sakeni Amina..Nace ne bazani ba..?
Amina tace"In sake ki ki shige gida..?naki wayon..?Hamida karbe jakarta..
Hamida ta warce Jakar makarantar Hanne Tana Dariya ya Zeenatu tazo shigewa gida da Katuwar jakarta Sabe a Hannu ta bisu da kallo kafin ta Tabe baki tana Fadin"Miye haka..?
Kudai bazaku bar yarinta ba..Kuna girma kullum kuna cin kasa..!
Baki Amina Ta tura batayi mgana ba Hamida ce tace"Ba ruwana Amina ce..!
Karamin Tsaki taja ta shige gida Abunta ya Abida ce Daga nesa ta hangosu kusan itace Karshen sauka Daga Motar,yau a waje idi ya saukesu motar ba Lafiya Dakyar ta kawo su gida gareji yace zai kaita shiyasa ya Saukesu anan waje su Sa"adatu tuni sun shige gida abunsu su Ya Akilu ne ke wajen jikin Motan.
Abida ta kalli Zubairu tana Fadin"Kalli yaran chan..?
Akilu yace"Bari na Tarkatasu su shige gida..!
Yafada yana Daukan Sanda ya fara Tafiya yana Fadin"Ya shamsu..Eh gasu nan suna wasan banza a waje..!
Kamar sun ga Shamsu da gaske suka Zura aguje su kuma suka kwashe musu Dadariya Abida ta shige get din gidansu ita da Zubairu Akilu yabi bayansu,su Amina suka Tsaya suna maida Numfashi Amina tace"Wlh Ya Akilun nan mugun dan saka ido ne..!
Hamida tace"So yake ya zama makwafin ya shamsu tunda shi ya gama..!
Akwai son yayi Displine..!
Amina tace"Barni dashi Watarana zamu yi mganinsa ne..!
Hanne tace"Badai kararara zaki sakamai ba irin na ya Shamsu..!?
Atare suka Saka Dariya Tuna abunda ya Faru wanchan satin Amina ta samo kaikayi a makarantar Islamiyansu taji su mariya na Fadin abun na saka kaikayi ta tsinko ta Dinga tusama Mutane Cikin Hijabi a ajinsu suna ta Soshe soshe,Shine ta sakama Shamsu Saboda ya Rankwashesu ita da Hanne basu gama Rubutu da wuri ba har aka tashi sun bata musu Lokaci shine suka Fakaicesa da Daddare Amina taja Hanne sukaje suka Watsamai akan Katifarsa da Safe suna Daki sukaji Hajiya na Fadin shamsu wani abu ya Sameshi jiya da Daddare kwana yayi susa da wanka sai da mallam ya dinga mai addu"a.
Sai da Amina ta kwanta Saboda Dariya Hamida ma bata sani ba Labari Hanne ta bata.
Amina na Dariya tace"Ai mallam Auwal ya saka an sare Ganyen mai kaikayin..!
Hamida tace"Ina Fatan kada ya Shamsu yaji Wlh sai na Lahira yafiki jin Dadin Amina..!
Hararanta Amina tayi kafin tace"To in ma yaji wlh ke kika fada!
Hamida tace"Ni kuma..?
Amina ta Bude baki zatayi mgana keman Idonta ya Fada kansa yana Tsaye Daga Kofar gidansu bai yadda sun kariso da Motarsu ba Tana baya Nura ke ciki yana kallon Ikon Allah
Sun fi awa Daya suna wajen nan agaban idonsu Motan makaranta tazo ta Sauke su Amina suka Firfito.
Ko alama bata manta dashi ba gani su Hamida sukayi hankalinta ya koma Chan gabansu yasa suka juya suna kallonsa yana Tsaye sanye Cikin Riga da wamdo bakake sai ya Dora Farar Jaket ya saka F.cap ya Rufe Fuskarsa sai dai ya Janyeta kadan.
Amina cikin mamaki tace"Laaa..Kai ne..!?
Mirmishi ya sakar mata kafin yace"Nine..Amina kina Burgeni..!
Fadin haka da yayi yasa ta washe baki ta fara takawa gabansa shima ya tako suka Tsaya daidai kofar gidansu Amina Hamida da Hanne suka saki baki suna kallonsu.
Amina Hannu ta Fara tafawa tana Fadin"Kai..Daman ina neman ka..?Ashe kai mawaki ne bansani ba..?
Ido ya zaro yana kallonta kafin yace"A ina kikaji..!?
Kai Tsaye Amina tace"A wayar wata yar ajinmu mana..naji suna mgana suka ambaci mai irin sunanka nace anunamin Hotonka kuma Wlh kai ne..Yauwa daman ina ta so na Fada ma su hanne don Allah ba kai kace ina Burgeka ba..?
Kallonta kawai yake yi yanjin wani Farinciki sai da ya ganta ya kara ganin yarintarta tana mgana ko Tsayawa ta kasa yi.
Kai ya gyada mata yana kallonta juyawa tayi ta riko hannun Hanne da Hamida ta kawo gabanshi tana Fadin"Yauwa don Allah sake fada musu..Kila su yarda..!
Tafada tana wani juya ido Dariya abun ya basa cikin gyara Tsayuwarsa yace"Amina Kina Burgenii..Wani ya Taba Fada miki u are so Beautifull..!
Amina taji wani Sanyi acikin ranta Cikin Alhafari ta kalli su Hanne da mamaki ya sa suka kasa mgana tace"Kun ji ko..?ai in na Fada muku sai kuce Karya nake..Nima fa ina Burge mutane
Kunga wannan babban mawaki ne yana tare dasu Umar.m sharif..!
Dasu Ani nihu kasan su ko kilama abokan ka ne..?
Take Fada tana kallonsa Cikin Dariyarta Kai ya gyada mata Cikin Dariyarta yace"Ai Ani nuhu abokina ne..yama ce yana gaisheki..!
Ido ta zaro kafin tace"Da gaske.?
Ya sanni ne..?
Yana Danne Dariyansa yace"Sosai ai yasan Amina..Amina ta Gumel abakin Aminu..!
Amina ta Dafe kirji Murna Duk ya Cikata Hanne taja gefen Hijabinta tana Fadin"AMINA kada wani ya fito fa ya ganmu fa.?
Hamida kuwa uwar tsoro sai waige take yi kafin tace"Amina kin sanshi ne..?
Hijabinta ta Fizge kafin tace"Dillah..ku na sanshi fa..Shagon chan muka hadu kwanaki da mamanmu ta aikeni..!
Har yace ina Burgesa ko..?
Tafada tana wani juya ido Kai ya gyada yana kallonsu Hamida kafin yace"Sosaima
gaskiya kuma Laifin ku ne da baku taba Fada mata ita din abar Burgewa bace!
Amina ta washe baki kafin tace"Kun ji ko..?yauwa gayamusu..Ni da suke cemin ina naga abun burgewa
Sai ma na gundiri mutane da Halina..!
Tafada tana bata Fuska da Sauri yace"Kada ki damu..Ni kina Burgeni..!
Hamida taga Amina ta Zake da yawa hannunta ta Fincika tana Fadin"Amina kada wani ya ganmu fa..?
Hanne tace"Bawan Allah don Allah ka tafi jidalin Amina ne kawai..In wani cikin yan gidanmu ya ganmu Dakai yau mun shiga uku..!
Amina ta kwace hanmunta tana Fadin"Dillah sai me..?iyaka duka ne kuma baya kisa..!
Hanne tace"Baba Mallam kinsan baya nan bamu da maceci sai Allah Amina..!
Wa kika taba ganin ya tsaya da wani..?ko su ya Abida kin taba gani..?
Amina ki shiga Hankalinki..!
Sai kuma tayi shuru ta tsaya tana kallon Hanne kafin tace"Kuma fa hakane..muje..bawan Allah sai an juma..Yauwa don Allah ka kara gaida min Ani nihu..!
Hamida tace"A ina kikasan Ali nuhu mu da ba kallo muke yi ba..?
Amina tace"Dillah Ani nihun ne baki sani ba..?dan wasam hausa fa ki bari gobe zan nuna miki hotonsa a bakin Unity ashagon nan ma kusa da shagon Bola gasu nan kala kala!
In Tana mgana Nishadi ke kamasa Shiyasa ya shagala yana kallonta baisan sun wuce ba suna gabda Shiga gidan ya Daga Muryansa ya Kirata.
Amina..!
Dukkamsu suka juyo suna kallonsa Cikin wani yanayi yana kallonta yace"Wlh da gaske nake yi kina Burgeni...
Sannan KUma..INA SON KI..!
DAM!!
dukkansu gabansu ya Fadi Amina ta zaro ido ya sake Daga mata kai kafin yace"Wlh da gaske nake ina sonki.!
Zan dawo ki jirani..!
Yafada yana kallomta Hanne da Hamida ta kallah kamar sun ga abun Tsoro suka Rumtuma suka shige gidan da gudu kai ya girgiza kafin ya Furta"Finally dai na gano abunda ke Damuna
Son yarinyar nan nake yi..!
Daga haka yajuya ya fara Tafiya wajen Mota Nura na ganin haka ya Tuko motar zuwa gabansa da azama ya Budamai gaban Motar ya shiga ya maida ya Rufe suka fara barin anguwan ammh Idanuwam Aminu na kallon Kofar gidansu Amina kamar tatafi da ransa Nura na binsa da kallonn Tsausayi.
Nura ya kada kai kafin yace"Ina muka Nufa Oga..?
Idanuwaansa na shigewa kamar mai barci yace"Mu koma Hotel..Nura son yarinyar nan nake yi..Bazan koma kano ba sai na samu Soyayyarta..!
Nura yace"Ta wata hanya..?
Dokar gidansu ce ba sa soyayya kuma na Fada maka..!
Bai damu ba kai Tsaye yace"Koma ta wata hanya ce
zan sakata ta soni
In ta soni komai mai sauki ne..!
Nura ya kasa mgana ya fara Tunanin Amina mayyace ta kama Ogansa.
Su kuma su Amina a haraban gidan sukaci Burki suka tsaya suna maida Numfashi.
Hamida tace"Amina mutumin nan bai da Hankali ammh ko..!?
Hanne tace"Ke ina ga wasa yake mata..!
Duk Amina na jinsu karo na Farko yau aka taba cewa ana sonta acikin Idanuwaan Aminu gaskiya ta gani ita kanta Zuciyarta ta kasa Fassara yanayinta yasa ta Biye ma su Hamida da Fadin"Bai da hankali..Inaga bai da hankali..!
Kai suka gyadata mata atare suka Furta"Gaskiya bai da hankali..!
Da haka suka watsar da mganar sukanufi Cikim gida Ammh banda Amina ta kasa goge Kalaman Aminu ko wani juyi tayi acikin Ranta sai taji muryansa.
Amina..Kina Burgeni..Kuma WLH INA SONKI.!
Batasan Dalili ba taji abun ya zauna acikin ranta sannan tana ji tana so ta kara ganinsa taga wannan Gaskiyan Data gani acikin idonsa..!
Mafarin komai...!
*Janafty*
*TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*
*🅿️17*
Da gaske yake yi Duk abunda ya fito Daga cikin zuciyarsa bai gasgasta haka ba sai da ya koma kano ya kasa zama kwana uku yayi ya saka Nura ya Tukosa zuwa Gumel,batare da Amina ta sani ba yake Bibiyanta ahotel yake zama In garin Allah ya waye zai zo kofar gidansu Amina Daga baya domin yaga tafiyarsu makaranta da Lokacin dawowarsu da Lokacin Tafiyarsu islamiya wasa wasa sai da yasan komai na Amina sannan yana Bibiyan dukkan Motsinta,Batare data sani ba Nura gajiya yayi ya koma Abunsa Tunda yaga alamun Ogan nasa ya kamun da gaske.
Baya sati bai shigo Gumel ba,Duk saboda Amina zai zo ya ganta yaji Sanyi aransa koda bata gansa ba koda bata sani ba ya gama yardan ma kansa Amina ta shiga ransa ta samu matsugunnun da bai zai iya cireta ba komai nata yana Burgeasa ne..
Amina bata son Aminu na binta ba Ba kuma wai don ta manta da mganarsa ba akowani Shafi na Tunaninta kalamansa bai bace mata ba sai dai Tundaga Ranar bata kara yarda sun kara mganar da Su hanne ba suma sun Dauki abun a wani abu dabam shiyasa suka watsar da mganar suka Cigaba da Harkokinsu.
Bata taba katarin ganinsa ba,Sai watarana sun dawo daga islamiya,Idi bai zo Daukansu ba Motar tana ta basu matsala ya shamsu ya Tarkasu su ya Abida ne ke baya su kuma suna gaba su uku kamar koda yaushe Sa"adatu na baya tare da sabeeha da Umaima ya shamsu da su ya Akilu suna bayansu sun taso su gaba Kafa kafa Hira suke a tsakaninsu Labarin littafi Amina ke bama su Hannu kasa kasa suna Dariya sun kawo kofar masallacin Baba mallam kamar an ce ta Daga kanta sama ta Hangosa abakin Masallacin yana Tsaye cikin irin Shigarsa kamar ko yaushe da Jaket baka Baki ta saki da Hanci tana kallonsa Cikin mamaki Farinciki yaji yau daya ganta ta gansa Hannu ya Dagamata Lokaci Daya da Mirmishi.
Su hanne sun juya suga me take kallo kamar ya sani ya Duka kamar yana Gyara igiyan Takalmi sai basu gansa ba Amina suka koma suna kallo kafin Hamida tace"Wa kike kallo Amina..!?
Sake kallon wajen tayi sai kuma taga bashi a wajen ta fara waige waige Ya Nasir ta gani yana Daukan Buta sai ta Fara Tunanin ko gizo yake mata yasa tayi saurin cema Hamida bakomai..!
Ta Dauka bashi take gani ba sai da washegari ta kara ganinsa Lokacin sun fito zasu islamiya,shima ya Ganta ya kuma mata Mirmishi gani na ukun da tayimai da Safe ne Ranar asabar zasu tafi Hadda ta fito tana jiran Hamida jikinta ya fara rawa Yana Daga Tsallaken su chan bakin wani gida Wannan karon bayan Mirmishi har sai da ya Daga mata hannu ta fara Tsorata tana Tunanin kodai ba Mutum bane Kila aljanine Datake ganinsa a ko"ina kuma ta kasa Fadama ko Hanne haka kurum bakinta yayi nauyin data gaza Furta komai.
Daga Lokacin kuma duk sanda ta fito gida sai tayi waige waige ko zata gansa sai dai bata kara ganinsa ba sai ta yadda da Tunaninta kila gamo tayi da aljani.
Harta da su Hamida sun fahimci kwana Biyu Amina ta rage karkasashinta da suka tambayeta sai tace bakomai basu damu ba sanin Halinta Lambo take halinta na tashi ne Lokaci bayan Lokaci kamar mai Bugawar jinnu.
Bata kara ganninsa ba sai bayan Shudewar kwana Hudu tsakani ta kara ganinsa a gabda gidansu Ranar Wata Laraba sun dawo daga makaranta,Gidansu Hanne ta Tsaya sai da tayi sallar mangariba Hanne ta Rakota Mazan gidan duk suna masallaci Baba Mallan na wa"azi
Har hanne ta rakota kofar gidansu suka Tsaya suna mgana yana Daga gefe basu ganshi ba har Hanne ta juya ta koma gida ita kuma ta juya zata shiga gida Taga mutum yasha gabanta.
Ta firgita taso ta yanka Ihu ne sai ya Hasko hasken wayarsa lokaci Daya yana fadin"Nine..Amina..!
Taji muryansa ai ta Haddaceta kamar Karatu Cikin tsoron da bata taba jiba ta fara waige akwai hasken a wajen Karo na farko taji mganar su Hamida in wani ya zo ya ganta fa..?
Abu ne da bai taba Faruwa ba..!
Tana ji yana Fadin"Amina kin bani Wahala..?wlh da gaske ina sonki..baki ga yadda na koma saboda ke ba...?
Yake fada yana kallonta da Dukkan Zuciyarsa Jikinta ne ya fara rawa domin taji motsi tunani take ko wani ne zai fito Daga gidansu ta manta ba kowa Aba bai dawo ba kuma Ya Jafar yana masallaci wani Firgici ne ya shigeta Dayasa ta Damki hannun Aminu suka sha kwanar Dake Tsakanin gidansu gabanta ne ke Dukan uku uku kamar ta rike kaya haka tayi saurin sakinsa kafin tace"Don Allah ka daina bina..Kaga bansan ka ba..Ka daina Bibiyata kada kajamin mtsala..!
Take Fada acikin idanuwanta yake ganin Tsoron wanda Daga gani tsoron ya shigeta Lokaci Daya.
Cikin Gyara tsayuwarsa yace"To in na Daina Binki ni ya zanyi..?
Wlh tallahi kin ji rantsuwan Musulmi ina sonki Amina sonki ya hanani zaman waje daya ki kalleni koda yaushe ina garin nan na kasa zaman Kano ballatana Yola koda yaushe korafin Nenne na ta daina gane kaina kuma Wlh duk kece Sila..!
Yadda yake mganar ne yasa ta ke kallonsa acikin idanuwansa ta Hango gaskiya aciki.
Sai dai ta tsorata wannan wani abu ne da bai dace yana Faruwa akanta ba Arude tace"Meyasa sai ni..?ni fa karamace akwai yayyina ga su ya Abida duk bakace su ba sai ni..?
Kai Tsaye yace Mata"Ni ban sansu ba ni ke na sani..kuma ke Allah ya Saka Kaddaran haduwarmu Amina..!
Amina ta zaro mai ido tana Fadin"To wlh ahir dinka da bina..Kada ka sakani Cikin mtsala in Aba ya Sani ko ya Jafar ko ya Nasir wlh kasheni zasu yi..!
Ka rabu dani Amina ba kamar matar da ka sani bane yarinya ce ni ban gama karatu ba..!
Da sauri yace"Nasani zan jiraki Amina da gaske nake ina sonki kuma na Rantse zan aureki..!
Amina ta Dafe kirjinta tana Fadin"In wani ya sani zaka jamin bala"i daman nayi suna..Amina tayi suna ka rabu dani don Allah ban san me kake fada ba..Don Allah ka tafi ka kyakeni..!
Yaji Rokonta bayaso ya ja mata matsala yasa ya ciro katinsa Daga aljihun wandonsa ya mika mata yana Fadin"Zan tafi badomin na tafin kenan ba..Zan tafi ne saboda kin Rokeni sai dai zan dawo zan rika Binki duk inda nasan zan ganki Amina banfara sonki da wasa ba Wlh..Wannan kati na ne da Lambobin wayata aciki duk sanda kikaji kina son mgana Dani ki samu waya ki kirani zan zo..!
Kin karba tayi ta noke hannunta Tana Fadin"Kasheni kake so ayi in aka ganni Dakai..?
Kai ya girgiza mata bai yi mgana ba illah Hannunta Daya kama ya saka mata katin kafin yace"Ba abunda zai faru..Ki sani Aminu Buba yana Tare Dake acikin kowani Bugawar Numfashinki Amina na barki Cikin Aminci..!
Daga haka ko waige ya Fice Daga Kwanar Jikin Amina ya fara rawa ta Murza katin hannunta.
A.A Buba tagani ajikin katin da address dinsa da jerin Lambobinsa kamar ta yardaahi sai kuma ta Fasa taji Ranta na janta data adana katin Kilan watan watarana yayi mata amfani yasa ta Dunkule katin a hannunta sai da ta leka ta Tabbatar daya tafi kana ta fito ta shige gida aharaban ta Tsaya tana maida Numfashi Cikin sikat dinta ta Boye katin bata so wani yagani bata Shiryama wannan Jidalin ba yafi karfinta wannan karon..!
Cikin kayanta ta Boye katin Boyo mai Tsawon da ba wanda zai gani kuma koda wasa bata taba Fadama su Hanne ba.
Bai yi karya ba Tun da karancin Shekarunta Ta Fahimci Aminu na cikin Duka bugawar Numfashinta ta Rage Walwala da yawan mgana Tun ballatana data Daina ganinsa data Kulle ido zata kwanta shi take gani da kuma Kunnuwanta na Sauraran Muryansa bata son so ba..Sai dai ta Fara Fahimtarsa a karance karancen Datakeyi sai dai tasan Shekarunta basu kai ta bama wannan a Tsarin a rayuwarta ba yanzu. Jadalin Gidansu soyayya ko manyansu basu yi ta ba ballatana ita saboda haka wannan Tunanin baya Cikin muhallinta.
Su hanne da Hamida sun gaji da korafin Chanzawar Amina ranar Tana jinsu da Hanne ta shigo tana Fadama Mamanmu har yaya tana Tsakar gida alokacin Hanne take korafin sauyawar Amina.
Zeenatu na wanki abakin Famfo tace"Nima na ganta kwana Biyu ba Tsiwa nace kila aljanun Salahancinta ne suka sauka..!
Hamida tace"Allah Nafi son Aminar mu ta baya..Wannan shurun shurun bana sonshi..!
Hanne tace"Ko ya Abida sai da tace Amina ta sauya..Sai Hajiya tace Hankali ne tayi girma yazo..!
Mamanmu najinsu tace"Kwarai da gaskiyan Hajiya..Hankali da Natsuwar da'ake mata gori ne Allah ya bata yanzu..!
Hamida tace"Mamanmu Amina kamar tayi gamo fa..?ko Aljanun Dare ne suka bata tsoro kinsanta da Fitan Dare ko tsoro bataji..!
Ya zeenatu ta saka Dariya tana Fadin"Waya sani ko ta hadu da Cika Lora..!
Gabadayansu suka saka Dariya Har Yaya Dake gyaran kubanta acikin Ranta tana Fatan Hankalin Amina ne yazo kada ace shurunta wata Tsiyar take shiryawa kamar yadda ta Saba.
Amina nadaga cikin Daki tana jinsu Mirmishi tayi ta Furta"Gamo nayi Hamida..Tabbas na gamu da jidalin Danike kira ni Amina..!
Satuttuka sun zo sun shude har an shiga wattani Amina bata kara Haduwa da Aminu ba,Sai abun yadan Fara Sakinta ta fara dawowa Daidai ta Fara Dawowa da walwalwarta har ya Zeenatu na fadin"Daman ai na Fada muku wanchan watan Salihan ne suka zo mata..!
Lokacin baki ta Murguda mata tana Fadin"ni bani da Aljanu..!
Sun saba gwara suyi mgana ta maida su ko Ya ya Amina ta sauya suna ganin Alamunta sannan in zasu fadi gaskiya basa jin Dadin ganinta asanyaye.
Har ta manta dashi ranar jumma"a Bayan La"asar Mamanmu ta aiketa ta kaima Hajiya kuka da aka aiko musu dashi mai kyau Daga gusai bata so zuwa Hamida ce ba Lafiya Cikinta na ciwo yasa Mamanmu ta matsa sai taje.
Tana Tura baki ta saka Hijabinta ta Fita Tana ji ya Zeenatu na Fadin"Mamanmu Amina fa bakinta take Tura miki alamun bazataje ba..!
Mamanmu tace"Zeenatu fita daga idona..Bana son sharri..!
Sai da ta Murmusa wani Lokacin bata san in akace ta zabi Tsakanin Mamanmu da yaya wacce zata zaba ba..
In tace zabi zatayi to sau goma mamaanmu zata zaba itace komai nata,Laifinta Dubu sai ta kare mata Ita da baba mallam Har Abada bazata manta dasu ba shi baya samun zama yanzu saboda suna ta zuwa gwaruruwa Da'awa ko ya zauna na dan kwamaki ne kuma suna makaranta sun Dade rabon da su samu Zama da Baba Mallam din Hakika tana kewarsa.
Leshin Bikin su ya Zulahait ne ajikinta da Farin hijabin mamanmu Dogo ita nata duk sun Yamutse ba guga.
Mamanmu ta wanke mata Hamida ba lafiya balle ta goge mata ya zeenatu kuwa ko mamanmu ta saka kafin ta Goge sai taci zagi da Mita da Dunguri in ma Zata gogen kenan
Lokacin data fito kanta na kasa ko alama bata gansa ba Kamar inuwa taji daga gefenta da kuma jikinta ya bata ana kallonta Tana Dagowa suka Hada ido.
Gabanta sai da ya fadi gabanta ta kallah Masallaci yana kulle ne Baba Mallam baya gari ba kowa sai yara Dake wasa da Famfo bakin masallacin bayanta ta kallah ba kowa yasa ta fara Sauri ta shige gidansu Hanne bata san ya Biyota ba Muryansa taji.
"In kika shiga baki Tsaya munyi mgana ba..Wlh zan biki cikin gidan..!
Amuryansa tasan zai aikata abunda ya Fada yasa ta Tsaya tsoro take ji wannan Jidalin yafi karfinta in wani ya ganta kashinta ya Bushe ko Baba Mallam bai isa ba sai su ya Jafar sun kusa Kasheta.
Ta daga kafa taga yana Binta sai ta Rude kawai sai ta Mike maimakon ta shiga gidansu Hanne shima yabi bayanta kafa kafa har sai da suka sha kwanar Layin kamar tana jira ta Dakata azafafe ta juyo tana Kallonsa Cikin Juya manya idanuwanta Tace"Kayi wa girman Allah ka daina Bina..Zaka jamin bala"i..!
Waka taba ganin yana Tsayawa da wani agidanmu..?
Kada ka jamin bala"in in ba so kake akasheni in wani ya ganmu tare ba..!
Yadda yake kallonta yasa ta gane baya Fahimtarta yasa ta Damke Ledar hannunta zata Ruga da Sauri ya riko Gefen Hijabinta Amina taji kamar ta Yanka ihu ballatana ma dataga wata Mota kamar ta ya Nasir da sauri ta Fizge Hijabinta tana Fadin"Innalillahi..Ka sakeni don Allah..!
Da sauri ya saketa Lokaci Daya yana Fadin"Zan kyaleki Amina..Ammh sai kin jiyo kin kalleni kin ga yadda Sonki ya maidani..?
Kamar bazata juyo ba yanayin muryansa yasa ta juyo tana kallonsa kallon ya shiga har cikin jikinta tana jin kamar Zazzabi zai kamata.
Ya rame sai dai ya kara Fari Wayarsa ya zaro yayi wani Danne danne ya kara kunni Lokaci Daya taji yana Fadin"Gata nan Nenne..Don Allah ki Roketa..ta ce tana sona..kada ki rasa Aminunki Nenne..!
Dagachan Bangaran Nenne tace"Bata wayar Aminu..Ni don ka kimin ne..da na Share kafata nazo har gabanta na Duka mata..!
A speaker ya saka wayar Cikin ido yake kallon Amina kafin yace"Nenne ta ce..Itace Duniyata..Takasa gane kaina na bata labarinki ammh nace kina Wahalar dani..!
Nenne tana jinki ki roketa don Allah ta Saurareni..!
Amina bata gama mamaki ba sai da taji muryan matar tana Fadin"Amina..Kina jina..Amina don Allah ki Saurari Aminu wlh yana sonki..Da gaske yake Aminu bai taba zuwa ya Duka yana min magiya kan mace ba sai akanki Amina ba don ni ba..Don Allah ki tsaya ki Saurareshi Yana sonki so na Tsakani ga Allah..!
Amina taji gwiwanta ya saki karamar kwalkwlwarta ta kasa Fassara mata komai
Sai da taji Nenne tace"Ko na Duka kan gwiyoyina ne Amina..?
Ina son ganin Aminu cikin Farimciki maraya ne bashi da kowa Amina don Allah ki tallafamai..!
Amina taji kwalla sun cika mata ido Tana ji Nenne na fadin"Kina jina Amina..Amina..!
Dakyar tace"Naji zan saurareshi
Saboda ke
Saboda ke..!
Da sauri Nenne tace"Nagode Amina..Allah yayi miki albarka Nagode..!
Take ta fada kamar zatayi kuka yanke Kiran yayi yama kallon Amina Cikin Galabaitar da yayi kwana Biyu da bai ganta ba yasha zata nemesa bata nemesa ba shi kuma ya kasa jurewa ya Fadama Nenne komai tayi tayi ya bari ta gayama Alhaji Babba sai atura manya Tunda gidan malamai ne yaki barinta yace sai ya samu Soyayyar Amina bai sani ba wannan kuskuran wannan Soyayar itace zata yi katanga Tsakaninsa da Amina har Abada Zanen kaddara ya riga ya zana bawa bai isa ya kauce masa ba.
Yaga tana Shirin juyawa ne batace mai komai ba yasa da Sauri yace"Kin ce mata zaki Saurareni fa Amina..!
Tsoro take ji wannan Tsoron ya shigeta Daga Fara Haduwa dashi.
Tasani wannan abun bai Dace ba ammh bazata iya Ture alfarman matar nan taji nauyinta.
Yasa ta waiga taga ba kowa sai yara Dake wucewa Daman anguwan bata da yawan Zirga zirgan jama"a
Wani Lungu tagani kamar hanya yasa ta Nufi chan tana Fadin"banda karfin Gwiwan Tsayuwa Dakai a hanya .Ina jin Tsoro ka Shigo nan..!
Bai musa mata ba ya bita Daga Farkon lungun suka Tsaya kanta na kasa tace"Meyasa sai ni.?
Agidanmu bawanda na Taba ganin yayi wata soyayya kowa da Lokacinta yayi Baba Mallam zai turo mata mijinta haka akeyi tun kafin a haifemu har kuma yau da muke bata sauya ba..Ka tafi kabarni ban dace Dakai ba ni ba wacce Kake nema bane..!
Bai barta ta Dire ba ya karbe da Fadin"Sai afara ta kanmu Amina..Ina sonki..Kuma soyayyarki bazata taba barina na kyaleki ba ki yarda dani..Ki soni na Rantse iki komai zai zama Daidai da kaina zan samu Malan namai bayani bazai hanani ke ba Amina..!
Kamar yana da wani abu a mganarsa yana mgana tana jin gaskiya a mganarsa ganin ta tsaya tana kallonsa yasa ya fara bata Labarinsa Tundaga Farko har karshe sai taji Tsausayinsa maraya ne cikin Sanyin jiki tace"Allah ya jikansu da Rahma..!
Ya amsa mata da Ameen yana Fadim"Kin ji kadan Daga Labarina Amina..?
Ke nasan komai akanki bana bukatar ji..Kice kina sona ko Hankalina zai kwanta..!
Ido ta zaro kafin tace"Komai fa kace..?
Kai ya gyada kafin yace"Eh..Harda Bakin Tsiwanki nasani..!
Sai ta rufe baki da Hijabinta tana kallonsa Yar dariya yayi lokacin Daya Hangi ledan hannunta yace"Wannan ledan fa..?
Ina zaki..?na tsaya yau ne kawai ba Domin nasan zan ganki ba yau jumma"a ba makaranta sai dai jikina ke bani zaki fito..!
Zuwa yanzu ta fara rage tsoronta Cikin Sanyinta tace"Sako ne Mamanmu ta aikeni na kaima Hajiya..!
Kai ya gyada kafin yace"Zan so na ga mamanmu nima..Yaushe zan je na gaisheta ko kuma yaushe zan gabatar da kaina wajen Mallam..?
Zai karbeni kuwa..?
Wlh ba waka bace kadai Sana"ata ina saida Motoci da kayan Gyaransu sannan ina da shagon gwalagwalai anan kano..Nayi alkwarin zan rike ki Amana..!
Amina ta katseshi da sauri ganin kamar baya cikin natsuwarsa yasa tace"Ba yanzu ba..Kada kaje ba yanzu ba..!
Kai Tsaye yace mata"Saboda mene..?
Bazata iya kallonsa ba yasa kanta na kasa tace"Yanzu ba Lokacin Daya Dace bane..!
Shuru yayi mata akwai tsoro atare da ita yasa ya dan Sausauta mata kansa ya Shafa yana Fadin"Lokacin yayi Amina..Ko ba yanzu zamu yi auran ba ina son na Rika ganinki duk sanda naso..!
Ido ta waro kafin tace"A"a bazai yuyu ba..!
Shima kai tsayen yace"Zai yuyu Amina..tunda kin hanani bayyana kaina ki samamin mafita..Zan susuce akanki baki ga alama ba..!
Amina tayi shuru ta kasa mgana ganin yadda ya marairaice yana kallonta ta kasa mai gaddama yasa tace"Sai dai mu rika haduwa anan lungu ko wanchan layin da muka Fara Haduwa..In wani ya ganni dakai agidanmu kasheni za"ayi..
Idanuwanta yake sha"awa in tana Taoro yasa yayi dariya kafin yace"To ta ina zaki san nazo..?
Amina tayi shuru tana Tunani kafin tace"Sai ka rika zuwa bayan kwana Biyu..!
Da gaske take yi ayadda ta Fada yarintarta ya gani yasa ya yi Dariya yana shafa sumar kansa yace"Amina ina aiki fa..?garin nan bansan kowa ba sai ke bazaki Tsausayamin Zirga zirga ba..In Nenne taji zatayi Fada dani nima zata kusa kasheni in taji ina yawo Tsakanin Titin Kano zuwa Gumel..!
Sai da ya fada Taga wautarta Ido ta Juya ta rasa me zatacemai bata so ta Fadi wani abu yaji ba Dadi Tsausayi yake bata ashe maraya ne.
Ganin tayi shuru yasa yace"Ina katin da na baki kwanaki..?
Kai tsaye tace"Yana gida cikin Dirowata..!
Kai ya gyada kafin yace"kina Daukan wayan Mamanmu ko..?
Kai ta gyada kafin tace"Tab...Ni kadai ke Dauka...Bata mgana in ko su Hamida ne sai ta Rankwashi mutum..!
Ta karishe Fada tana Dariya shima Dariyan yake yi kafin yace"Daga gani mamanmu din nan na sonki..Ko kice Auta..?
Amina tace"A"a ina da kani Jawaad..Mamanmu ta Dabam ce..Kamar yadda kace Girman Nenne a wajenka haka Mamanmu duk da ba ita ta Haifeni ba nafi sonta akan Yaya..!
Ido ya zaro yana kallonta kafin yace"Ba ita ce mamanki ba..?
Tana Dariya tace"Kaima kaji mamaki ko..?
Haka kowa ke fadi in aka shigo gidanmu Yaya kamar ba ita ta Haifemu dukkanmu mamanmu ce komai namu..!
Gyara Tsayuwa yayi yana Fadin"Bani kadan Daga Labarin Mamanmu Amina..Naji ina sonta kamar Nenne ta..!
Amina saboda Shaukin Labarin Mamanmu yasa Ta manta da Tsoronta da aiken da akayi mata ta shiga basa Labarin mamanmu da yaya da Aba da ya Jafar da su hamida ta karishe da Fadin"Ko sau goma akace in yi zabi Mamanmu zan zaba akan Yaya..Kwata kwata bata sona kullum bata Fadin Alherina..Mamanmu ko laifi nayi tasan shi bata Fadinshi sai ta Boye Laifina ko ya"yanta bata hada kansu Dani ni ta Dabam ce awajenta..
Kallonta yake sai yanzu yake ganin yarintatarta Uwa uwace kuma ai ta wuce wasa duk da alabarin ya Fahimci mamanmu macece ta kwarai ammh bai kai Amina ta Girmamata Fiye da Mahaifiyarta ba,sai dai ba yanzu zai nuna mata haka ba Lokaci bai yi ba sai nan gaba bai sani ba nan gaba na Tare da wani boyayyan Kaddara, kaddaran da bazata bashi Dama ya Nuna ma Amina Muhimmancin uwa ba.
Ganin Lokaci ya tafi yasa ya kalli Amina yana Fadin"Shida ta kusa..!
Lokaci Daya yana Kallon agogon Fatan Dake hannunsa Ido Amina ta Zaro kafin tace"Na dade..kada Mamanmu tajini shuru..!
Kai ya gyada kafin yace"Hakane ki tafi..Ki Ari wayar mamanmu kimin Flashing zan kira in naga Nombar zamu rika mgana Amina ai zaki min wannan alfarman ko..?
Gabanta na Faduwa tace"In aka ganni zan shiga uku wlh..!
Yana Dariyan mganarta yace"Zaki boye ai ba wamda zai gani ko..?
Saboda ni da Rokon Nenne..!
Ya fada yana marairaice mata jin haka yasa ta Daga kai da sauri yayi dan Ihu kafin yace"Nagode..Zan jiraki kinji..!
Da kai ta Dagamai kafin ta fara tafiya sai kuma ta juyo tana kallonsa hannu ya Dagamata kafin ta dagamai sai da tace"Yanzu Yolan zaka tafi..!?
Kai ya girgiza mata kafin yace"A"a kano zan koma Amina daman nan din A hotel nake kwana yau nazo saboda na ganki muna da Shooting gobe in Oscar bai ganni ba ai na Shiga uku Amina..Nura ma in ya fara kirana sai ya Kasheni da raina..!
Yadda ya fadi karshen mganar ne yasa ta yin Dariya tana wucewa da Sauri Lokaci Daya taji yana Fadin"Wlh Ina sonki Amina..Ni na sani ina sonki..!
Har takai gidansu Hanne Mirmishi bai bar Fuskarta ba kamar almara wani Farimciki take ji yana shiganta Tunasa take da Duka kalamansa sai taji kamar tana yawo a gajimare.
Sauri sauri tayi dataje gidansu Hanne Ko zama batayi ba Duk da Hanne tayi ta janta da Hira don ta zauna ta kosa ta ganta agida ta Nemi katin nan kada ace ya bace data Shiga uku.
Ko Rakiyar Hanne bata jira ba Data Shiga Daki ta Dauko Hijabi Tana jin Ya Abida na Fadin"Amina yau Ba"a son zama kuma..Sai faman sauri take..!
Hajiya ma sai da tayi mgana ita dai Amina gaba tayi koda Hanne ta fito ta wuce abunta Baki Hanne ta tabe kafin tace"Amina tsiyanta nada yawa..!
Amina bata ji kwanciyar Hankali ba sai da ta Binciko Katin nan Cikin Dirowarta bayan ta gama yin Dai'dai da kayanta.
Mamakinta ya ishi Hamida batayi dai mgana ba Ya Zeenatu ne tace"Wlh Amina ki kwashe mana kayan nan..Nasan Halinki sai kice kansu zaki kwana..!
Amina batabi ta kanta ba Sai da taga Katin nan sannan ajiyar rai ya kwace mata da sai da suka kalleta Dukkansu Hamida tace"Me kike nema ne wai..?
Amina tace"To kuma ina Ruwanki Uwar saka ido..!
Hamida ta tabe baki tana Fadin"Ki gyara kayanki kuma da kanki Wlh..!
Jin haka yasa Amina ta marairaice Tana Fadin"Kayya Hamida..Yi hakuri badake nake ba..Anty Hamida yar aljannah..Allah yasa ki auri Shugaban kasa muje Villah mu Bude Hanci wai waya ga Amina Aminene a Villa Jar Uba akwai Daga kai..!
Yadda ta karkacen ne yasa Dole har ya Zeenatu sai da Dara tana Fadin"Ke ai Tun get din farko Sojojin Villa zasu Wurgoki waje..!
Amina tace"Tab kaji ya Zeenan nan..Mune fa kalan masu kudi kalan yan gayu..!
Take Fada tana wani Fari Zeenatu na Dariya tace"Aifa kalan masu kudi a bushe kirji gandas Amina kamar kin shafi kasan kabari Ko Hanne fa ta Fara Nanna banda ke suna chan makale a kirji kamar na maza..!
Amina ta Chuno baki itama abun na Damunta kafin tace"Wlh nima abun ya isheni kaf yan ajinmu baki ga nasu ba Tumbul tumbul..Ni don Allah ko Hamida zata san min nata ne..?
Kalli nata kamar Lemu sun yi Bulbul dasu..!
Salati Zeenatu ta saka Hamida kuwa har da cin Tuntube wajen Fita ya Zeenatu tabi bayanta tana Fadin"Mamanmu ki fito..kiji Abunda Diyarki ke fadi..!
Da gangan ta koresu suna fita ta Dauko Katin tana kallo acikin Haban Sikat din ta Boye shi ta fara maida kayan tana kwalama Hamida kira.
"Hamida.Haba mana Hamidas..Zan yi miki zaman Daki na sati Daya zan tayaki gyaran gado..Yaya Hamida..Anty Hamidassassas..!
Take fada Hamida na jinta tayi mata banza Daga Tsakar gidan tace"Bafa zan tayaki ba ki gyara da kanki..!
Kamar Amina tayi kuka tace"Shikenan Baza"a ma ace Antyn ba Hamidan ba..Hamidu din..!
Ba Hamida ba Hatta Yaya Dake Dakinta tana jinsu sai da ta Dara Mamanmu na cikin Bedroom dinta ko ta jisu ma bata fito ba Jawaad ne ke wasa ya kyakyalce da Dariya yana Fadin"Ita kuma Aminuu ba..!
Zeenatu da Hamida suka saki Dariyan Amina na ciki na jinsu taji sunan Daya ambata yasa ta Daga Murya tana Fadin"Jawaad ina wasa dakai ko..?
Wlh in na kamaka sai na yi kasa kasa Dakai..!
Tagumi tayi tana maimaita sunan Aninu acikin ranta Tsikar jikinta sai da ya tashi wani yanayi ta shiga da batasan Dalili ba.
Sai ta gama gyara kayanta Tsab har Hamida data shigo sai da tace"Yau wata rana Amina anyi abun kai..!
Tana Hararanta tace"Yau jumma"a munafus aga ban gyara ba..!
Dariya take mata Lokacin data fita alwalar mangariba ta shiga Dakin Mamanmu tana Tiolet din Cikin Dakinta yasa ta Dauki wayarta ta Sake a Sikat sai dakoma Daki tayi sallar mangariba Lokacin Yaya da Mamanmu da su Hamidi sun fito baranda kamar yadda suka saba suna Hira ta Lallaba ta shige Dakin mamanmu har cikin Makewayi ta kuma Sakama Kofar key.
Kan abun bahaya ta zauna ta fito da waya da katin Duk yadda Tsoro ya Cikata kalaman Aminu na yana jiranta Cike da yakini yasa ta kwashe Daya Cikin Lambobin ta Doka mai Kira.
Sai da ta shiga har taji an Dauka sannan wata zuciya tace"Amina me kika aikata..?
Da sauri ta kashe sai dai ta makara Tunda yace ta kirasa yaji ajikinsa zata kira din yana ganin bakuwar Lamba yasan itace.
Karar wayar yayi daidai da Daukewar Nunfashi Amina kafin gabanta ya koma ya Fadi Dam..!
Ta rude yasa batasan ta Danna Dauka ba sai da taji muryansa yana Fadin"Hello Amina..
Nasan kece..Daman ina da yakinin zaki kirani..!
Fitar muryansa kamar wani Sinadiri ne ajikin Amina hakanan taji kamar komai yana kwance mata wannan Tsoron kuma yana Fita Daga cikin kanta.
Bata sani ba wannan wayar itace mafarin Kaddaranta Itace mafarin FITA ZAKKAN da tayi acikin Yan"uwanta da Danginta..!
Yanzu muka shiga labarin da sauran mgana agaba..!
*Janafty*
*TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*
*🅿️18*
In wata Kaddara zata sameka Sanadin wani abu to baka da tsumi ballatana Dubara sannan Tsoro bashi da muhalli a wannan bangaran to kamar hakane ya faru da Amina inda ta san Sanadin Aminu zanen kaddaranta zai bayyana da tasani zatayi zatace Daman Tun farko komai bai faru ba.
Amina bata taba tsintar kanta ahalin data tsinci kanta ba Yarinya ce mai son yabamata a nuna mata so da Muhimmanci zuciyarta karamace ba bu kowa acikinta shiyasa cikin Sauki Aminu ya samu Dama mai yawa akan Amina.
Tun fara wayarsu ta farko abun bai Tsaya ba sai ya cigaba duk sanda Amina ta samu dama zata Dauke wayar mamanmu ta shige Tiolet dinta ko na Tsakar gida,flashing take mai yana gani kome yake yi zai ijiyeshi ya Kirata su sha Hira cikin abunda bai gaza sati Biyu ba, suka yi wani irin Shakuwa ta ban mamaki ko shakka babu Aminu ya samu Matsugunni azuciyan Amina tana sonshi tana kuma Tsausayamai saboda Maraya ne.
Komai take aboye take yinshi bata taba yarda a Fahimci Halin data ke ciki Daman chan bata da tsoro sai da soyayyar Aminu yasa AMina ta koyi Munafunci da nuku nuku ko bata fito Fili ta Fada ba,kowa yasan tana cikin Walwala da Farimciki ba wanda yayi Tunanin wani abu daman ita Amina akullum cikin Jidali take da Tsiwa sai Chanzawar bai wani damu kowa ba Hatta dasu Hanne da suke tare da juna koda yaushe.
Kafin lokaci yaja Amina ta gama sanin komai na Aminu duk halin Dayake ciki in sukayi waya sai ya Fadamata Amina ta zama kamar wata bangonsa yana Tunanin ranar Daya rasata baisan ina Rayuwa zata kaisa ba komai nata yana Burgesa komai tayi a wajensa mai kyau ne.
Abokan aikinsa ba wanda baisan sunanta abaki ba Musamman ma Oscar,da Nura koda yaushe suna waya sai yace"Minata kinga Oscar ko..?
Yau bai barni na Huta ba. !
Minata kinga Nura ko..?
Yana sani yawan mgana...!
Komai nsshi itace"Minata kinji me Nenne tace..?
Wai bazata yarda na Daukeki zuwa kano ba Tare zaku zauna ayola kin yarda..?Ira iran irin wadanan zantukan Amina ta gama Haddacesu acikin kanta indai akan Aminu ne.
Taki bari su kara haduwa wannan Tsoron bai saketa tana aikata abunda ko su ya Jadwa zamansu ba wacce tayi Tsaurin idonta sai dai ina Zuciyarta bazata iya bata ma Aminu ba Daya matsa ta amincemai yazo ya ganta Ranar Jumma"a da basu da Ismilya Daman sun yi mgana jiya da Daddare zasu hadu in da suka Hadu Na Karshe Alayin Gaban gidansu bayan La"asar.
Haka kuwa akayi Tana idar da Sallar La"asar tace ma Mamanmu zata shiga wajen hanne ba wanda ya tankata sanin basu da Shamaki da gidan Baba Mallam
Mazan duk suna masallaci suna Karatu ta sabe ta tafi koda taje har ya iso yana Jiranta,Ranar sun sha Hira Amina ta kara sanin Aminu sosai ta kuma gama yarda ma kanta itama In bashi bazata iya auran kowa ba Ko alokacin yayi yayi ta bari ya Turo a tambayan mai Izini Amina ta nuna ba yanzu ba tana tsoro ko Ss2 Bata kai ba ta Tura Saurayi gida ai su ya Jafar sai su kusa kasheta da ranta Tana Tunanin da Sauran Lokaci bata sani ba Daga ita har Aminun wannan Tunanin nasu shine ya bada kofar shigowar wannan kaddaransu kaddaran da zata Haramta musu juna har Abada kila da bai bi mganarta ba da Kaddaran tajasu zuwa gurbi ko matsayin da suke Fata
Abu kamar wasa karamar mgana ta zama Baba Soyayya mai karfi ce Tsakamin Amina da Aminu agida ba wanda ya sani duk bayan sati uku yake zuwa ya ganta ta fita da Niyar zuwa gidansu Hanne sai su hadu alayin gaban gidansu wani Lokacin Nikab take sakawa saboda kaucema Idon Mutane wani irin so Aminu yake mata so mai zafin da komai zai iya yi kan Amina Yaso ta bashi dama ya Hidintamata ammh kuma taki yarda bata yi Tsaurin idon da zata karbi wani abu Daga wajensa ba Ranar da Dubunta ta Cika sai ta Mutu ta Dawo Saboda duka tasani akwai wannan Ranar watarana zata zo sai dai bata san yaushe ne ba ammh Tabbas akwai Ranar kin Dillanci.
Zuwa Lokacin ba wanda Aminu bai sani ba agidansu Amina da gidan Baba Mallam ba,su ya Jafar kuwa har ya Haddace Labarinsu da su Sa"adatu da basa ga maciji Hanne da Hamida kuwa Koda yaushe suna waya rabi Duk Labarinsu ne Ya riga ya sani Hamida da Hanne sune gaban goshin Amina sannan kaunar Dake tsakaninta da Mamanmu kaunace da Allah ne kadai yasan Girmanta.
Nenne kuwa koda yaushe suna mgana da Amina in yazo ko kuma in yaje Yola Nenne tana ganin abun kamar wasa sai kuma karamar mgana ta zama Ita dai jikinta bai bata ba tana ganin wannan hanyar da Aminu ya Biyo anya mai bullewa ce kuwa..?
Tana Tsorom watan Watarana komai yazo ya Rikice tasha cemai"Aminu Anya bazaka Daina Biyema yarinyar nan ba..!?
Kafita Hankali fa kai babba ne kana ganin wannan Soyayyar taku ta Boye ba wanda ya sani agidansu watarana in aka sani bazata Haifar maka da matsala ba..!
In ta fadi haka Dariya kadai yake mata yace"Haba Nenne..Bafa komai mai Wahalar Meena ce..In tana sona ko Duniya zata hade bamai rabani da ita so kada ki damu babu abunda zai faru..!
Kallonsa take yi bata cewa komai ba ganin idonsa ya Rufe ammh ajikinta Tana jin kamar zuwa gaba wannan zai zame ma Aminu kabule babba ma kuwa da bazai iya yin komai alokacin ba..!
Babu wanda ya taba Lura da Halin da Amina ke ciki sai dai an fara Lura da ta na yawan Shiga bandaki ta Dade bata fito ba,Ranar Bandakin waje ta shiga tafi minti Talatin bata fito ba Da Daddare ne duk suna Tsakar gida abaranda suna shan Iska Aba ya Dawo yana Shashensa Yaya tatafi wajensa Mamanmu ce da ya Zeenatu da Hamida sai jawad Dayayi barci kan katuwar Tabarman da suka baza anan Baranda abincin Dare suka gama ci su ka koma Hirar Anty sakina da Tayi barin yan Biyu,Achan madina din ance ta Zubar da jini sosai sai tafi sati a asibiti achan Anty Amarya taso taje Baba Mallam ya hana yace akwai mahaifityar Sarood da ita kanta Sarood din suna kula da Sakinar sai dai ance Danmallam din zai zo akwai mganin Hausan da zai tafin ma Sakinar dashi.
Duk Amina na cikin Bayin Tsakar gida tana jinsu suna waya da Aminu ya katse yace ta jirashi ya amsa wani kiran bata so ta fita kuma ya Sake kira ta shiga uku duk da wayar asilent take sakata kuma da sun gama waya take Goge Lambar tasa data Riga ta Haddaceta akanta.
Tana nan Tsaye tsabar sakama rai bata Damu da inda take wajen Najasa bane,Hankalinta kwance take shigowa suyi wayarsu domin nan din ne kadai mafita inda Hankalin wani bazai zo kanta da wuri ba.
Karaf taji Hamida na Fadin"Wai ina Amina ne..?
Mamanmu tace"Ba ta na cikin Dakin ku ba..!
Ya zeenatu na kishingide tace"Ina jin fa bata fito ba..Naga Daukan butatanta da shiganta Bayi indai ba yanzu ta fito ba to tana ciki..!
Hamida tace"Kai meke damun Amina ne..?
Kwanakin nan bata da aiki sai shiga bayi..Kuma sai ta Dauki Lokaci kafin take fitowa ko Basir ne ya kamata..!?
Mamanmu tayi shuru kafin tace"Nima na Lura mgana ce kadai ban yi ba..!
Ya Zeenatu tace"Ko basir din ne mamanmu..?
Kinsan fa tana saka yawan kashi..!
Mamanmu tace"Bari ta fito muji dai..Ammh yawan shiga bayin Amina bana Lafiya bane..!
Duk Amina na jinsu sai jikinta ya Saki Yanzu wani amsa zata basu..!
Bata gama Tunani ba Aminu ya sake kira sai ta manta da su mamanmu ta Dauka suka cigaba da Hirarsu.
Bata da Tsammani taji Muryan Hamida gabda kofar Bayin tana Fadin"Amina..Amina..!
Mamanmu shuru fa bata amsa ba..!
Jin haka yasa Mamanmu ta mike tana gyara Daurin zaninta Lokaci Daya tana Fadin"Zeenatu ba Lafiya..Gayama Aba dinku da yaya na shiga uku ni Balaraba..!
Take fada Cikin Rudewa Tunaninta Allah yasa ba masai Amina ta Fada ba basu sani ba
Zeenatun ta Rude itama ta kwashi Sauri zuwa Shashen Aba ta Fadamai jin haka yasa Amina tayi Saurin katse wayar jikinta ya fara rawa saboda Sauri yasa sai taa danne wayar ta kasheta Gabadaya ta Turata Cikin Wandonta Hamida na shirin Turo kofar Makewayin Amina tayi Zaraf ta fito har tana Bangaje Amina.
Sai Hamida ta saki baki tana kallon Amina datayi wani Fiki Fiki da ido.
Daidai Lokacin da Mamanmu ta Kariso tana Fadin"Jijjiga Kofar makewayin Hamida a bude take..Ami..!
Bata karisa ba ta ci karo da Amina Tsaye Cikin Sauke Numfashi tace"Alhamdulillahi..Wlh gabana ya Sare na zata kin fada masai ne..!
Da sauri Amina tace"Masai kuma mamanmu..!?
Tace"Yo eh mana..Wajen awanki Daya fa da shigarki bayi baki fito ba..ni har na saka Zeenatu ta Kira babanku da Yaya..!
Amina bata samu Zarafin mgana ba sukaji Muryan Aba yana Fadin"Balaraba meke faruwa ne..?
Sukaji Muryansa sai Amina ta Rude da Sauri ta matsa jikin Mamanmu tana Wurga ido.
Hannunta ta jawo zuwa Tsakar gida Hamida ta biyo bayansu Lokacin da Yaya ke fadin"Me ya samu Aminan..?
Zeenatu tace ta shiga makewayi tun dazu bata fito ba..!
Badai wanda ta shiga tun kafin Aba dinsu ya shigo bane ko..?
Hamida tace"Shine..Yaya mu mun zata ko ta suma ne ma abayin..!
Aba ya kalli Amina na Tsawon Lokaci yana Nazarinta yadda take Fiki Fiki da idonta ajikinsa yaji bai yarda da ita ba.
Cikin kaushinsa ya Kira sunanta "Amina..!
Sai da gabanta ya fadi da Sauri ta amsa"Na"am Aba..!
Kai Tsaye yace"Me kike yi a bandaki har na tsawon wani Lokaci..?
Kan Amina na kasa tana kokuwa da Fargabanta tace"Bakomai Aba..
Ya zeenatu tace"In baki da lafiya ne ki Fada a nema miki mgani..Wlh Aba kusan koda yaushe Amina cikin shiga Bayi take kuma sai fa an manta da ita take fitowa..!
Kallonta kawai yake yi yana kara nazarinta Hamida tace"Ni fa na Fara Tunanin ko Aljanu sun shafe ta ne..!
Har fa bayin Dakin Mamanmu tana shiga ni Ranar ma da ta shiga na shigo sai na rika jin mganarta kasa kasa har da Dariya fa..Aba..?
Kiris ya Rage Amina ta bata Dafe Kirji ba ta shiga uku Yaushe Hamida ta ji haka bata mata mgana ba..
Mamanmu ce tace"Mun shige su..Kuma shine baki Fadamin ba..?
Hamida tace"na manta ne mamanmu..Ammh Tabbas Amina bata da Lafiya..!
Kamar an Dasa Yaya da Aba haka suke bin Amina da kallo Mamanmu tana Salallami tana Fadin"Allah ya kaimu gobe zan shiga wajen Malam da kaina na Fada mishi Babansu kada fa ayi Shuru karamar mgana sai kaga ta zama Babba..!
Ya zeenatu tace"Mamanmu gama Turaran Hayakin nan da Baba mallam ya bada kika taba Turarama ya Zulaihat da suka taba Bigeta a makaranta..?
Yana cikin Dirowarki ki Turara mata yanzu agani in ma sune zasu bayyana..!
Mamanmu tace"Yanzu kuwa Zeenatu..!
Aba ne yayi gyaran Murya kafin yace"Ba fa wani Aljanun Dake Damunta..Ki tambayeta ko wani Cutar ne dabam..!
Jin haka yasa da Sauri Amina tace"Aba basir ne..Zafi nake ji in naje yin bayan gida sai yaki fita..!
Yadda ta fadi mganar yasa Dole ma ayarda Yaya ce tace"Ararrabi zaki sha yana mganin basir sosai..!
Aba ya juya yana fadin"Ku jika ku bata ta sha in bai yi ba zan ma Nasiru mgana sai ya kaita taga Likita nan General..!
Daga haka ya shige Falonsa,yaya kuma ta koma Daki ta Dauko Daddaken Ararrabinta da bata Rabo dashi ta Jikama Amina aruwa kadan ta bama Mamanmu hade da Sauran na Ledan tana Fadin"Tasha wannan yanzu..Gobe da safe ko atea ko koko sai ta kara sha insha Allah cikin zai saketa tayi bayan gidanta Lafiya lau..!
Mamanmu ta karba tana Godiya ita ta tasa Amina sai d ta Shanye duka tas tana yamutsan baki Saboda Bauri bata Damu ba Hankalinta ya kwanta Tunda ta isa barka asirinta bai Toni ba.
Tundaga Ranar Amina ta Rage shiga Makewayi tana waya Aminun, sai da aka kwana Biyu ta nemesa ta Fadamai Halin daake cikin Cikin Damuwa yace"Meena ki bar ni nazo naga Aba ko mallam..nagaji da wannan kumbikunbiyan..Da gaske nake yi ina sonki kuma auranki zan yi..!
Amina sai ta marairaice tana Fadin"Ba yanzu ba Amin..Aba ko mallam baazasu taba Sauraranka ba
Ko fa Ss2 ban shiga ba kuma aka"idan gidanmu sai kin kusa gama Candy ake Fara mganar auranki yanzu kana gani ko su ya Zeena bamu ji komai ba Har yanzu kuma basa su wuce shekarar nan mai zuwa ba ka Kara Hakuri akwai sauran Lokaci..sannan Zamu Rage waya na kwana Biyu..Gudun Faruwan wani abu wanda bazai mana Dadi ba..
Zan nemeka in na samu Dama..!
Bazai iya mata gaddama ba Saboda yana sonta kuma baya so ya sakata acikin matsala.
Atsukin Taji ance ya Danmallan yazo abakin Hanne sai dai kwana Biyu yayi ya koma Allah kuma yasa basu hadu ba,Don ko gidansu bai shigo ba,Tadai ji su Yaya nata jajanta Lamarin suna Fadin yace Sakina tasha Wahala sosai yaso ma ya taho da ita Mallam ne ya Hana shiyasa
Anyi haka da kwana Hudu Labari yazo kan ya Zulaihat itama ta zame a bandaki Ta fadi itama tayi barin Cikinta,Tana asibiti washegari kuma Yaya da Hajiya Babba da Hajiya Uwa Mallam yasa Idi yakaisu kano inda mijinta ke aiki nan suka koma sukaje suka Dubata ya Zulaihat taso ta dawo gida sai ta samu Lafiya Baba mallan yace maza Tunda uwar mijinta na nan da kanwarsa sun isa su kula da ita tana ji tana gani su Hajiya suka Dawo Gumel suka barta.
Sauran yan'uwa kuma sai a waya suka mata sannu da jiki har da su Amina da suka gama nacin abarsu suje Mallam yace ba wanda zai taka bama su ba,har su ya Abida Dake gaba dasu jin haka yasa kowacce ta maida maitanta.
Amina sun cigaba da mgana da Aminu sai dai tana shiga Bandakin waje koda yaushe,Domin haka Mamanmh ta Dinga Dura mata mganin Basir Asibiti kuwa sai da Aba ya Tambayeta ta warke ko kuwa sai sun je asibitin tace ta warke shiyasa sai ta sauya Taku.
Sai dare yayi in suna Tsarkar gida da an fara Hira sai ta fara hammar karya tace barci take ji ta shige Dakin Mamanmu chan kurya ta Kirasa da kuma taji motsi ta kashe wayar ta Boye ta Lafe kamar mai barci ba wanda ya Taba Fahimtar wani abu na Faruwa.
Idon Amina ya Bude tasan menene Dadin Soyayya,Domin karance karancen datakeyi sun kara taimaka mata sosai,Bayan su Hamida ba wanda yasan Amina na karatun Littafan Hausa su kuma Aminansu ne bazasu taba fada ba,Sai dai koda yaushe suna mata Fadan ta Daina Abunda take yi ita kuma sai tace ina Ruwansu..!
Kwanci tashi babu wuya a wajen Allah gashi har su Amina suna shirun Fara Jarabawar third Semester dinsu ns shiga SS2,alokacin kuma sun kwarari wajen wata bakwai tare da Aminu aboye batare da kowa ya sani ba.
Sai dai akwai ranar da asirinta ya kusa Tonuwa Aminu yazo tayi karyan Tana gidan su Hanne Fitanta kuma ba Dadewa sai ga Hanne tazo nemanta Hamida tace ai yanzu Aminar ta fita zuwa wajenta.
Hanne ta kalli Hamida cikin mamaki kafin tace"To bata je ba don ban ganta ba..!
Cikin mamaki Hamida tace"Wasa kike ko..?
Kusan fa duk jumma"a Aminar wajenki take kai har mangariba fa Hanne..!
Hanne ta zaro ido kafin tace"Ni..?
Yaushe rabon da naga Amina. ?ranar ne fa shima ana kiran sallar mangariba ta shigo sallah kadai tayi na Rakota gida..!
Hamida ta koma ta zauna tana waige waige kafin tace"To wlh Amina na fita kuma tace wajen ki take zuwa
Yanzu ma fa bata Dade da fita ba..!
Hanne tace"To abun mamaki ina Amina take zuwa..?
Hamida tace"Wlh bansani ba mu jira ta Dawo mu tambayeta..!
Wasa wasa Amina har bayan mangariba bata Dawo ba Hanne da Hamida sun fara shiga Damuwa har gida Hanne ta koma ta tambayi ya Abida ko Amina ta shigo tace bata ganta ba.
Ta sake dawowa ta Fadama Hamida,suka Rude suna wannan Tarardadin sai ga su ya Jafar sun shigo Sai suka kara Tsurewa kada su Farga ba Amina inda Allah ya Taimakesu har suka fita basu Lura ba Aminan ba,Suna Fita ba Dadewa sai ga Amina suna Daga cikin Daki sukaji ya Zeenatu na mata mgana tace Daga gidansu Hanne take
Ya zeenatu ta harareta kafin tace"Hannen ai kina fita ta shigo..?
Ko wata hannen dai ba wannan taki ba..?
Amina sai ta fara Kifta ido kafin tace"Dakin su ta barni na kwanta bansan yammh tayi ba sai yanzu..!
Ko kara kallonta batayi ba Jikinta asanyaye ta karisa Dakinsu kaifafun idanuwan Hanne da Hamida na kanta Hannunta take Boyewa Cikim Hijabinta kada su ga Zoben azurfan da Aminu ya bata yau batasan me zata ce musu ba.
Ganin yadda suka Zuba mata ido ne yasa tace"Wai lafiya..?
Wannan kallon kamar naci bashin ku..!
Tafada Cikin Hararansu Adole sai ta barsa da mganar dake ransu.
Hanne ce ta mike tana Fadin"Amina ina kika je..?
Amina tace"Ina kuwa..?
Ina zuwa akace kinzo gidanmu naga bazan iya dawowa ba na shiga Dakin ku na kwanta..!
Hanne ta kalli Hamida itama ta kalleta suka koma suna kallon Amina datake wani Kifta ido alamun ba gaskiya.
Hamida tace"Yanzu Hanne ta koma gida..Ya Abida tace baki zo ba..!
Amina ta saki karamin Tsaki Lokaci Daya tana Cire Hijabin jikinta take fadin"Bata ganni ba ko Hajiya batasan na shigo ba..!
Ruwanku ku yarda ko kar ku yarda..Ku Tsayama Zargina kukeyi na tafi yawon banza ko me..?
Hanne tace"Bata kawo nan ba..Muna gujemiki matsala ne..
Kinsan Fita zuwa waje ba Tarbiyanmu bane Amina kada ki Fara Halin da kike Dade baki yi ba..!
Amina ta Zabga ma Hanne Tana Fadin"Bangane ba..?
Kinga Hanne don Allah ki kyaleni bama son Hayaniya..!
Daga haka tayi saurin Fita Daga Dakin kafin su ganota Dakin Mamanmu ta Fada tana Kiranta.
"mamanmu Mamanmu..Na dawo..!
Tana fita Hanne ta kalli Hamida kafin tayi mgana Hamida ta Rigata da Fadon"Karya take yi wlh..Acikin idanuwamta naga Karya Hanne..!
Hanne tace"Nima nasan haka
To ina taje batasan Fadamana..!
Hamida tace"Wayasanin mata..?
Kila gidansu wannan Zainab isan taje aro Littafin Hausa kinsan Amina..!
Hanne tace"Ai ba Littafi a hannunta..!
Hamida tace"Zai iya yuyuwa bata samun bane..Ina zata Daya wuce nan..?
Hanne tace"Hakane..!
Daga haka suka bar mganar ammh kamar acikin sun kasa yarda da cewa Amina gidansu Zainab taje sun santa in ma chan taje zata gayamusu ammh abun mamaki yau Amina bata son Hada ido dasu suna Zargin akwai wani Sabon Al"amari game da Amina sai kuma basu san komenene ba..!
Tunda Amina taga sun Fahimceta sai tace Aminu ya Dakata da zuwa gidan su Hannen Data ke Fakewa dashi an ganota yasa sai ya kwana Biyu bai zo ba sai su yi mgana ta waya.
Watarana Ranar da ta zama mafarin bakaken Ranaku acikin Rayuwar Amina da bazata taba mantawa dasu ba.
Ranar da suka gama Jarabawarsu ta Karshe wajen kwana Uku basu yi mgana da Juna ba tasan yana chan Hankalinsa atashe jinta shuru ita kuma bata samu damar Daukar wayar ba akwanakin Mamanmu na Makale da wayarta bata samun Daman Dauka duk hanyar da zata bi tabi bata samu Dama ba.
Sai Ranar da Daddare Allah ya taimaketa Mamanmu ta ijiye wayar saman Mirror dinta Tana Dakin Aba tana gyaramai yau ita ke dashi.
Bata Kira ba sai da taji Dawowar Aba da kuma Kai da kawon Mamanmu ashashen nasa sai da taji tsit alamun Tagama Zirga zirgan sannan ta shige Kuryan Dakin Mamanmu ta Kirasa yana ganin kiran ya biyo baya Tana Dauka ya Sauke Numfashi yana Fadin"Da baki kirani ba yau Meenata..gobe sai dai ki ganni agidanku..!
Tasan zai aika shiyasa ta fara bashi Hakuri suna cikin mgana taji kamar Muryan Ya Zeenatu tana mgana da Sauri ta katse wayar,ta koma ta Lafe kamar mai barci sai dai abun da ya bata Haushi Falon Mamanmu Ya Zeenatun suka Dawo ita da Hamida suna Hira maimakon da da suke Falon Yaya ashe kanta ke ciwo ta kwanta Shiyasa suka barta ta Huta.
Sanin in bata Lallashi Aminu ba zai ballo mata ruwa yasa tatashi ta Fito Falo tana mika kamar mai barci.
Cikin Muryan barci tace"kun dameni ina barci Hamida..!
Ya Zeenatu tace"Sai ki sauya Daki malama..!
Bata ma Tsaya ba ta Tura baki tana Fadin"Na koma Dakinmu ni da Dakin uwata an koreni..!
Tana jin Hamida na mgana bata tankata ba ta koma Dakinsu sam Tunanin ta Rufe kofa bai kawo mata ba ta Haye kan gado ta kira Aminu daman yana Jira ya Kirata suka cigaba da mgana Korafi yake mata kan ya gaji zai zo yaga Aba ko mallan ita kuma tana kokarin numamai Lokacin bai yi ba.
Sam ta manta a inda take hankalinta ya Riga yayi gaba bata ji shigowar Kowa ba bataji motsin ba ko Tafiya kawai sai jin wata Gigitaciyar tsawar Muryan Aba ta karade Kunnuwanta Cikin kaushinsa yace"Amina..Amina Dawa kike mgana awaya..?
Ba Amina kadai Hanjin Cikinta suka yamutse ba har da Aminu Dake Sauranta ya Rude domin Baya son Amina ta shiga matsala..yana ji ya kara Daka mata Tsawar yana Kara Fadin"Nace da Uban wa kike waya da Tsakar Daran nan Amina..?
Tsawar da har Yaya sai da tadata ita Daga barci Mamanmu Zani a hannu Ita dasu Hamida suna Rigen rigen shigowa Dakin.
Bayan ya shigo gida ne ya manta bai kulle gida ba yasa ya kara Fita ya kan yi Dube Dubensa atsakar gida kafin ya kwanta in sun manta da wani abu ya Kaudashi yana jin Hiransu Hamida bai leka Falon Mamanmu ba sai dai har ya wuce ya rika jin tashin mgana kasa kasa yasa ya Dawo da baya sai ya Fahumci Daga Dakin yaran ne.
Kafafunsa suka jasa ya isa Bakin kofar Dakin Tar yaji muryan Amina tana mgana mamaki da al"ajabi yasa ya Daga Labulen Dakin ya Leka ya ganta kwance tabama kofa baya waya a kunnenta tana mgana duk da bayajin me tace cewa ammh yasan ko wata wayar ce bata Alheri bane.
Har ya tako ya shigo Dakin agabanta bata sani ba Bai gama jin jikinsa ya Saki ba sai da yaji Amina na Fadin'"Haba Amin dina..Kasan nima ina sonka..Kuma nayi maka alkawarin Rayuwa Dakai har Abada..!
Baisam Tunyaushe ta Fara ba sai da jikinsa ya fara mazarin da karkawan wani Bala"i ko yace wani Kangarewa ne ya samu Amina..!
Amina fa itace cikin Dare tana waya da wani Gardi tana Fadamai tana son shi yar Amina da batasan komai ba.!
Ganin yadda Amina ta yi sumar wucin gadi ne ga waya a kunnenta ta kasa Sauketa Saboda yadda Hanjinta ya Cure waje Daya.
Aba ransa ya baci baisan ya karisa gabda da ita ba sai da taji wani gishiri Gishiri wajen bakinta Mari ne Aba ya Kamtseta dashu sai da bakinta ya Fashe wayar ta fadi gefenta Daidai Sanda Aba ke fadin"Ba mgana nake miki ba..Nace da Uban wa kike mgana da Daddare acikin waya..!?
Amina sai ta Fara ganin hazo Cikin Daburcewa take fadin"Ba...ba..kowa Aba..ba kowa..!
Ransa ne ya kara baci Bacin rai ya Kwashe sauran Hakurinsa baisan sadda ya Hada kanta da jikin gadon data ke kwance ba ji kake kummm...!
Lokaci Daya ya hada da marin gefen Kumatunta yana Fadin"Zan miki karya ne..?
Nace zan miki karya ne..?
Yake fada Cikin bayanna bacin ransa Ihu Amina ta kwalla Saboda Ziyartan wani azaba Dataji asaman kanta da Aba ya,kumata Tuni wajen ya Fashe sai jini Daidai Lokacin da Aminu ya Katse kiran bazai iya jura ba bazai iya Juran jin Kukan Amina ba.
Innalillahi kawai yake maimaitawa ya kasa zama yana Zagaye kyakyawan Bedroom dinsa a kano.
Gabadaya su Hamida sun Rude sun kasa ma mgana Mamanmu ce da Sauri ta Dira gaban Amina Daidai Aba ya kara Daga hannu zai kara Sauke mata ta Tareshi tana Fadin"Babansu zaka kasheta ne..?
Nace zaka kasheta ne..?
Tafada Cikin Tsawa hannunsa na rawa ya Nunata yana Fadin"Kauce ki bani waje Balaraba..!
Yau Sai yarinyar nan ta Fadamin Tun yaushe ta fara wannan lalacewar bansani ba..?
Waya na kamata tanayi balaraba da wani kato tana Fadamai bazata iya Rqyuwa bashi ba wani shegen ne yake Lalatamin Tarbiya yarinya bansani ba..!
Yake Fada yana saka hannu ya Ture Mamanmu gefe da hanzari ya Riko Amina tana Ihu ya jawota ya makata da kasa,Daman Sa"idu bai iya Fushi ba bai iya Duka ba in ya fara kamar zai kashe haka yake yi.
Hamida da Zeematu suka Rike juna jikinsu na Rawa Hatta Yaya ta Rude Amina kuka take tana Dafe da kanta Aba ya saka kafa zai taka Amina yana Fadin"Zaki gayamin ko sai na kasheki na Huta..!
Yaya bata bari ba ta rikosa da Sauri Tana Fadin"A"a kabi a hankali kada kayi Hukunci cikin Fushi..!
Mamanmi kuwa Amina ta Tarairayo Jikinta ta fashe da kuka tana Taba jinin goshinta Lokaci Daya take fadin"Abbansu jini fa..Zaka kashemin Diyata ne..?
Bai Saurareta ba wayar ya Dauko Daga Saman gado yana Laluban wajen kira Lambar Aminu ce ta karshe kuma ita ya Kira yana so yaji wani Lalataccen ne ina Tarbiya yana Daga waje yana kokarin Rusa komai..!
Lokacin da Aminu yaga Kiran yana mgana da Nenne a Dayan wayarsa ne yana gayamata Halin da ake ciki ganin kiran yasa da Sauri yace"Nenne MEENA na kira..!
Tana so tace mai kada ya Dauka kila ba Aminan bane ammh bai jita ba ya Datse kiranta ya Dauki na Amina.
Aba a speaker ya saka wayar Daidai Sanda sukaji Muryan Aminu yana Fadin"MEENATA..meena Aba bai Dakeki ba ko..?
Hankalina ya tashi!
Su hamida suka kwalalo ido Amina ai sai taji miyan bakinta ya Tsaya Cak yau kafin safe kila sai dai Buzunta Aminene sai dai Tarihinta
Aba yaji kansa ya Sara Cikin kaushin Murya Da takaici yace"Ba Meenar bace..Uban Aminan ne Sa"idu..Waye kai..?Meyasa ka zabi ka Lalatamin Tarbiyan da nayi Shekaru ina ginata..!
Nace meyasa..?
Aba ya karishe cikin Tsawar data gigita su mamanmu Hatta Aminu dagachan bangaransa ya kasa mgana baisan sadda ya Datse kiran Ba shikenan komai ya kare.
Wannan Ranar daman yake gudu.
Yanzu ta ina zai fara?
Ko yace ba yaudaran Amina yake yi ba wazai yarda dashi?
Abun ya Zama wani iri..Al"amarin yayi kwabewar da bai da wata mafita.
Wannan shine mafarin komai Mafarin abubuwan dadama da zasu faru daga Rayuwar Amina da kuma Rayuwar wanda bai tsammmaci Aminar cikin Kaddaransa ba..!
*Janafty*
*TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*
0 comments:
Post a Comment