Nace wayar waye wannan Balaraba..?
Ya karishe fada cikin Tsawa Lokaci daya yana sakar mata jajayen idanuwansa da suka sauya Launi Saboda bacin rai.
Awannan gabar kowa bai da bakin mgana Yaya bazata kare Amina ba Daman Hamida da Zeenatu bazasu iya cewa komai ba Mamanmu ce Daman ke da wannan ikon itama ta rasa mafita Domin Amina ta bata komai wannan kiran wayar da kalaman Aminu ya gama tabbatar da cewa Amina ta aikata abunda ya Fada din.
Amina kuwa jikin Mamanmu ta shige jikinta ba inda bai rawa shikenan ta gama wayo wannan Ranar daman take tsoro gashi tazo ta sameta bata shirya ba.
Aba baya duka sai dai Fada baya Hukunci da kansa sai dai su ya Jafar ammh duk ranar da ka shiga hannunsa sunanka Sorry bai iya Duka ba in ya fara bai iya bari ba,Shiyasa wani Lokacin baya son bacin ransa kuma baya son yayi duka.
Tasani komai ya gama baci bata kuma da kalmar da zata kare kanta ballatana Har Mamanmu ta samu kwarin gwiwar kareta kamar yadda ta saba.
Aba ganin mamanmu tayi shuru ta kasa mgana sai kuka take taya Amina yasa yayi mirmishin Saman baki Mirmishin Dayafi kuka ciwo yace"Balaraba mgana nakemiki..?
Nace wayar da Amina ke amfani da ita wayar waye..?
Mamanmu ta Dago cikin wani yanayi kafin tace"Wayata ce..,ammh wlh..!
Bai bari ta karisa ba ya Daga mata Hannu Cikin wani yanayi muryansa ta Cunkushe waje Daya yace"Basai kin ce komai ba Balaraba..Na Fahimci komai..Duk Abunda Amina ta aikata ko take aikatawa da saninki da kuma Daurin gindinki Balaraba..!
Mamanmu ta Kallesa cikin wani yanayi haka ma Yaya bata samun Zarafin mgana ba ya cigaba da Fadin"Eh da saninki mana..in baki sani ba Meyasa kike barinta da wayar..?ai na Fada muku ku daina bari suna Daukan wayoyinku saboda gudun irin wannan ko ban fada ba..?ammh baki ji ba..Komai Amina zatayi mai kyau ko mara kyau Daidai ne awajenki Balaraba baki Taba nuna mata Tayi ba Daidai ba wannan ne so..?wannan ba So bane Balaraba..Kuma kin Cuceni kin Latatamin Tarbiyan da nayi shekaru ina ginata kan ya"yana bazan yafe miki ba..!
Yake fada cikin wani yanayi muryansa kamar ya yi kuka,Yaya mamaki yasa tama kasa mgana ballatana Mamanmu data kafe Aba da ido zuciyarta na suya mamakin kalamansa ya kamata.
Amina kuwa rudewa tayi da kalaman Aba da sauri ta mike daga jikin Mamanmu ta rarrafa gaban Aba cikin kuka take fadin"Aba Wlh Mamanmu bata sani ba..Bata sani ba..!
Kafa yasa ya Shureta in ya kalleta ransa har wani kara baci yake,Dukewa tayi awajen tana kuka cikin Fusata yace"Karya kike ta sani..Tasan komai akanki..Balaraba tasan komai akanki Amina..Hadizam haihuwanki kadai tayi ammh Matsayin Uwa balarabace gareki baki yarda da kowa ba sai ita..Abun bakinciki ace kamarni acikin gidana na samu mai Bijirema Umarni na..SAnnan Tsorona Daya tun yaushe kika fara haka Amina..?
Na Dade ina addu"an kada watarana ki Zama Zakkan da mutane ke Fada sai gashi Tun ba"a je ko"ina ba Abunda nake tsoro ya faru....!
Yake fada cikin bacin rai kafim Lokaci Daya ya Dago Amina wuyanta ya Shake Cikin Zare mata ido yana Fadin"Ban yarda Dake ba Amina..Dom Ubanki ki Fadamin saunawa kika yarda yayi Lalata Dake..?
Ki Fadamin yaushe kika san maza haka ban sani ba Amina Duk kafa kafan da muke ni da Baba Mallam a kanku..bamu tsira ba..?
Ki fadamin nace kafin raina ya baci na Shakeki kimutu kowa ya huta..!
Zuwa Lokacin Amina ta fara kokuwa da Numfashinta Yaya bazata ce komai ba Tana baya hankalinta atsshe Hamida da Zeenatu kuka Mamanmu kuma kalaman Aba sun gama kashe mata jiki ganin Amina ta kusa Mutuwa ne kada ayi kisam kai yasa Mamammu ta mike da Sauri ta isa garesa tana kokarin bambare hannunsa a wuyan Amina Lokaci Daya tana Fadin"Haba Abansu zakayi kisa ne..?
Kalli fa zaka kasheta Amina bata Numfashi..?
Take fada Cikim kuka Hannu yasa ya Tureta da karfi da sai da ta Fadi kugunta ya Bugu wani kara ta saki da yasa Yaya dasu Hamida sukayi kanta da yatsa ya nunata yana Fadin"Kada ki kara sakamin baki in ina ma ya"yana Hukunci balaraba..Domin ke ba Matata bace Yanzu
NA SAKEKI Saki Daya..Tunda na Fahimci kin bada gudummuwa a Lalatamin tarbiyar Amina..!
Ya fada Cikin bayyana bacin ransa Ba su Hamida Dake rike da Mamanmu ba Hatta Amina Dake kokuwa da Numfashinta sai da kalaman Aba suka Girgizata ta zaro ido tana kallon Aba Cikin Firgita da rawan baki Hamida hannu ta Dora akai Zeenatu kuwa hannun Yaya ta kamkame tana kuka wacce ta saki Mamanmu kamar bata da laka ta koma ta zauna Dabas kanta na juyamata ji take kamar amafarki komai ke faruwa
Cikin Muryan da basu taba sanin Yaya tana dashi ba ta Kira Aba Cikin Tsawa"SA'AIDU..Me ka aikata haka..?
In har baka gode mata kan Amina ba bazaka zageta ba..Kayi kuskure kayi kuskure Sa"idu kayi saurin gyarashi kafin Lokaci ya kure maka!
Kallonta yake yi bai yi Nadama yace"Kema Kada ki kara sakamin baki..In kuma ba Haka sai ranki ya baci..!
Yaya sai hawaye Amina ta zama bala'i tayi sanadin mutuwar auran matar da ta zama bango gareta Kallon Amina kawai take ta Durkushe tana wani kuka kukam Nadama da bakin ciki acikin Ranta Tana Tunanin Dama ace
.Dama ace bata Hadu da Aminu ba Dama ace bata yarda dashi ba..Da duk haka bata faru ba me ta aikata..?
Ta kashe auran Matar da ko Uwar data Haifeta bata kaita sonta ba Matar data kasance wata aba mai Daraja a wajenta ita kam Amina wannan Ranar bakar Ranace a wajenta soyayya bata mata adalci ba ta Datse mata komai alokacin da bata tsammaci Lalacewar abubuwa kamar yadda suke Faruwa ba.
Kuka take kamar ranta zai fita ta Rararrafa ta kama Kafan Aba cikin kuka take fadin"Don Allah kayi hakuri..naji ni ka Hukuntani kayi ta Dukana har sai na Daina Numfashi ammh kada ka saki Mamanmu Na Rantse da wanda Raina ke hannunsa Mamanmu bata sam komai ba Wlh bata sani ba!
Take fada tana kuka wannan karon ba Aba bane ya Tureta Yaya ce Lokaci Daya ta shiga Dima ma ta Dundu kota ko"ina Bataji bata gani tana kuka Tana Fadin"Kin yi asara Amina..Kin yi asara Tunda rashin jinki yasa,kikayi Sanadiyar Mutuwar auram matar da bata taba barinki ke kadai ba akowani Hali Tana Tare Dake..Kin Fita Zakka Amin Da gaske ne ke Zakka ce..Tunda kika Rama Alheri da Sharri..Ki ka kuma yi Sanadiyar Mutuwar auran da ya yi Shekaru na rasa da wani suna Zan kiraki ji nake in na barki da Raina bam Huce ba..!
Kowa ya kasa hanata Yaya bada wasa take dukam Amina ba Fadi take"Abun kunya zaki jawo musu Amina..?
Su kike ki kasheta ki huta..?
domin ita kadai ke Daukema Jidalinki Amina kin fara bin maza?
Aure kike so baki fada anyi miki ba.?
Gwara na fara kasheki na Huta kafin ki zo ki Kashe sauran Rayuwanka da suke kare miki..!
Dukanta take yi kamar bata cikin Hayyacinta Amina na kuka bakimta na Zubar da jini take fadin"Wlh yaya bana bin maza
Wlh ni ba yar iska bace..!
Bakinta bai mutu ba..Daman bazai taba Mutuwa ba yau da Mamanmu zata Ceceta bata ceceta ba tana gefe har alokacin Shock din Daya kamata bai saketa ba sannan ko tana son tashi ta kasa kugunta ya Bugu da Gadon Hamida ta kasa tashi Kuka take daga Zaune ba kukan kalaman Sa"idu kukan yadda Amina ke kuka Yaya na Dukanta Cikin karyewan Murya tace"Yaya ki daina dukan ta don Allah..Ki bari raina na kuna..!
Yaya ta Dago idonta jajir tana Fadin"Yau dai..Yau dai Kadai ki bari na Shiga Lamarin yarinyar nan..Ki barni na yau kadai!
Mamanmu sai ta kasa mgana Ya Zeenatu ne taga Abun ya rikice Aba na Tsaye bai yi mgana ba Shima baya son ya kara saka mata hannu ne sai ya Illlatata,Rugawa tayi ta Fice Daga Dakin ba Mayafi ba Takalmi ta nufi waje ita ta Bude gida sai gidam Baba Malam an Rufe get haka ta Dinga Bugawa da karfi megadi yana Lekowa ya ganta ya Bude Mata da Sauri yana Tambayanta ko Lafiya ina bata Tsaya Sauraransa ba da Farko Cikin Gida ta so ta wuce sai taga Falon Baba Mallam abude ssi ta kwashi gudu zuwa chan.
Yana Tsaye gaban makeken Dirowan Dake falonsa mai shake da Littafai da Farin Gilashinsa da Jallabiya yana Duba wani littafi ne sanda Zeenatu ta Fado kamar an korota tana Haki Sama Sama Hakinta yaji da Numfashinta yasa ya Juyo da sauri ganinta Cikin wannnan yanayin yasa Hankalinsa ya tashi da sauri ya baro inda yake Tsaye ya kariso gabanta Cikin Dattakonsa yace"Zeenatu meke farruwa ne..?
Ganin yadda ta Duke ne tana kuka Jikinta ba inda baya rawa yasa yace da Sauri"Kada kicemin wani abu ne Mummuna ya samu Sa"idu bayan yanzu bada Dadewa ba yabar nan wajen..!?
Zeenatu na kuka Dakyar ta iya cewa"Aba..Ya saki mamanmu..Sannan ga yaya chan na Dukan Amina..Baba mallam kazo kafin su yi kisan kai..!
Hankalinsa nan da nan ya tashi Cikin wani yanayi ya shiga maimaita"Innalillahi wani"inna ilaihirraju"un..!
Muje gidan muje..!
Yake fada yana karisa wajen Daya Ijiye wayarsa ya Daukota yabi bayan Zeenatu data Fice da Sauri Lambar Hajiya Babba ya Kira bai rude ba sosai Saboda yana ta Kiran sunan Allah..
Itama ta tsorata data ga Kiran nasa Domin bata Dade da komawa Shashen nata ba ba ita keda dashi ba Hajiya Nasara ce,Cikin Wani yanayi ta Daga Wayar tana Fadin"Mallam lafiya dai ko..?
Cikin Dattakonsa yace"Ki sako mayafinki ki Sameni gidan Sa"idu..!
Zumbur ta mike daga kwancen Datake tana Fadin"Innalillahi me ya Faru ne Mallam?
Cikin Natsuwarsa yace"Bansani ba..Sai mun je zamu ji..Ki yi Sauri..!
Daga haka ya Datse kiran cikin Sarsarfa ya Fice Daga falon bayan ya saka wayar tasa aljihu Tuni Zeenatu ta fice Daga gidan megadi ganin Mallam ya fito da kansa yasan ba Lafiya bai Tsaya tambayansa ba ya shiga mai Fatan Dawowa lafiya
Gudu gudu sauri sauri Baba Mallam ya isa gidan su Amina kamar zai fadi Saboda Damuwa zeenatu na shiga Dakin ya shiga Saboda ya Jiyo kuka da mgana Har Lokacin Yaya Dukan Amina take yi Cikin Tashin hankali ya karisa gabanta baasusan da shigowarsa ba mganarsa kadai sukaji Daga sama
"Kada ki Sake Dukanta HADIZA...!
Ya fada Cikin Kaushinsa kamar koda yaushe,Cak yaya ta Tsaya sai Lokacin Aba ya gansa Mamanmu na gefe tana kuka tana ganin Baba Mallam tace"Yauwa gwara da Allah ya kawo ka..Mallam kalli Dukan da suka ma Amina..?
Kashemin ita zasu yi.?
Aminar Baba mallam ya kallah Goshi na zubar jini baki ma haka gabadaya bakin ya sumtuma sun sauya mata kammani Tama Daina kuka sai Hadiyar rai kawai Daidai shigowar Hajiya Babba cikin tashin Hankali ganin yanayinsu yasa tace"Wai meke faruwa ne..?
Sa"idu..?
Ba wanda ya iya mata mgana Sai Lokacin Mamanmu ta iya mikewa Dafe da kugunta Baba mallam ya kalleta Sau Daya ya kauda kai Hajiya Babba ya kallah yana Fadin"Hajiya kama Amina..bari na kira Idi yakai ku Asibiti mafi kusa a dubata tana Zubar da jini..!
Sai Lokacim Hajiya Babba ta Lura da Amina da sauri ta karisa ta Dagota tana Fadin"Innalillahi waye yayi mata wannan Dukan..?
Zaku kasheta ne..?
Amina kuwa ganin Hajiya yasa ta fashe da kuka tana Fadin"Hajiya ki fadama Aba da yaya..Wlh bana bin maza..Ki kuma fadamai ba Ruwan mamanmu don Allah ya janye Sakin da yayi mata..!
Hajiya ta ji ta shiga Tashin Hankali Cikin wani yanayi tace"Innalillahi Wani"inna Ilaihirraju"un..!
Baba mallam bai saurari kowa ba ya Fiddo wayarsa ya Kira Idi Direba daman gidansa ba nisa yace mai ya Fito akwai Fitar da gaggawa yana Gama wayar ya juyo yana Fadin"Hajiya kuje har da Balaraba itama adubata!
Hajiya ta kalli Mamanmu yadda ta kasa Tsayuwa tana Fadin"Mun shige su ni Zainabu..Wai me yake faruwa ne..?
Baba Mallam bai mata mgana ba Aba ya kallah wanda kansa ke kasa yace"Biyo ni Dakinka..Ku kuma kuje Daga waje..Yanzu Idin zai iso..!
Daga haka ya saka kai ya Fice Aba yabi bayansa Falon Aba suka isa Baba Mallam ya fara shiga Aba yabi bayansa su kuma Hajiya ta kama Amina tana kuka jini agoshi da baki Hamida ta kallah Dake gunjin kuka tace"Miko mata Hijabi Hamida..!
Da sauri ta rarumo nata ta mika ma Hajiya ta saka mata Yaya kuma Ficewa Tayi Daga Dakin cikin yanayin da ba wanda ya gane.
Hajiya ta kalli Mamanmu Tana Fadin"balaraba sako mayafinki muje..Allah yayi mana mganin wannan masifar data kunno mana kai da Daddaran nan!
Zeenatu taje ta dauko ma Mamanmu Hijabi ta saka ta riketa Saboda Dakyar take iya takawa suka fita Kofar gida Har idi ya iso har ya fito da Mota suka shiga Hajiya da Amina da Mamanmu da Zeenatu Hamida kuma Hajiya tace ta koma gida Wani karamin asibitin kudi Hajiya tace Idi ya kaisu Saboda kada su bata Lokaci.
Achan Falon Aba kuwa suna shiga ko Zama Baba Mallam bai yi ba ya Juyo yana kallon Aba cikin wani yanayin Bacin rai Aba kansa ya maida kasa Domin in yana gaban Baba mallam baya iya Daga kansa saboda Biyayyah..!
Shuru na wani Lokaci yaji Baba Mallam bai ce komai shiyasa ya Dago kansa a hankali kafin ya bude baki zai yi mgana Baba Mallam ya Daga mai hannu Cikin Dattakonsa yace"Bana son jin komai yanzu..Kafin na tambayeka me ya faru..Ka maida Balaraba Dakinta in har kana so na Saurareka..!
Aba ya Dago kansa cikin wani yanayi yace"Baba m...!
"Bana son jin komai kayi abunda nace in har na isa Dakai..!
Dole yasa Aba yace"Shikenan..Na maidata Dakinta na Janye Sakin Dake Tsakanina da Balaraba..!
Sai alokacin Baba Mallam ya sauke Nunfashi ya samu kujera ya zauna yanuna Aba gefensa shima ya zauna kafin yace"Ina jinki...Fadamin abunda ya faru tundaga farko..!
Nan Aba ya Sunkuyar dakai ya Sanar da Baba Mallan komai ya karishe da Fadin"Abu daya yafi min ciwo..Meyasa Balaraba ta Boyemun..!
Sannan da Taimakonta ta Lalatamin Tarbiyar Amina Mallam..Na tabbata da saninta..!
Kallonsa kawai yake ya Dade bai yi mgana ba sai chan nisa ya fara mgana cikin Kaushinsa kamar ko yaushe"Sa"idu kaifa mai ilmi ne..To ina Ilimin ka yake..?
Me Annabi yace..?
Kada muyi Fushi..Kuma mu daina Saurin yanke hukunci cikin Fushi..Meyasa da haka ta faru baka bari kayi bincike ba kafin ka yanke hukunci ba..Kana da Tabbacin ita Balarabar ta sani..?
Baka sani ba..Kun taru kai da Hadiza kuna neman kuyi kisan kai..?
Yanzu inda wani abu ya faru mara Dadi wa gari ya waya Sa"idu.?
Kan Aba na kasa yace"Kayi hakuri Baba Mallam!
Mirmishi yayi kafin yace"Akoda yaushe ina Fada maka Duka baya Tausasa yaro..Sai ma ya kara karangarar dashi Nasiha da Lallashi ne mafita Sa"idu ban ji dadi ba..Kana aibata yarka ina ji ajikina Bamu aikata barna Lokacin kuruciyarmu ba..Muma Daga cikin ya"yanmu ba Zamu samu bara Gurbi ba Sa"idu...!
Aba ya dago yana Fadin"Yaron da take waya dashi fa Mallam..?
Ansan meke Tsakaninsu..?
Baba Mallan yace"Koma menene alheri ne Sa"idu..Baka haikema ya"yan wasu ba kaima da yardan Allah bamai haikema ya"yanka da yardan Allah..Wannan ai ba wani abu bane Komai zai daidaita Zan yi mgana da Amina yaron da suke wayar zan nemesa naji abunda ke Tsakaminsu in Yana sonta da Gaske ni zan ce ya Fito in nayi bincike na gari ne zan bashi Auran Amina Kamar yadda na Saba..!
Aba ya saki baki yana kallon Baba Mallam bai samu zarafin mgana ba yaji yace"Kiramin Hadiza..Itama na nuna mata ta Daina yanke hukunci Cikin Fushi..Sannan ku daina aibata ya"yanku Dafi ne garesu..!
Ba Musu ya mike ya fice koda yaje ya isketa tana ta kuka,Ya kalleta Cikin wani yanayi kafin yace"Kizo Falo na Baba Mallam na mgana..!
Da haka ya fice share Hawayenta tayi ta saka Hijabi ta shiga Falon ta samu Baba Mallam yayi mata nasiha sosai da jikinta yayi sanyi Cikin wani Rauni Yaya tace"Mallam Amina ta fitta zakka..Tayi Sanadiyar da saki ya shiga Tsakanin Mahaifinta da matar da ta Zamemata komai a rayuwa..!
Mallam ba Amina ce agabana ba
Kuka nake Saboda Alherin Balaraba ya koma Sharrin awajem Sa"idu..!
Baba Mallam yace"Wannan ya wuce Hadiza...Sa"idu ya maidata Dakinta Yanzu nan..Mganar Amina kuma ba Ruwanka zan yi mgaba da ita..,!
Dukkansu basu kara mgama ba Domin Duk Abunda Baba Mallam yace daidai ne Yaya hankalinta ya kwanta Dataji cewa Aba ya maida Mamanmu sai alokacin taji Hamkalinta ya kwanta.
Hajiya ce ta Kira Baba mallam awaya sukayi mgana basu ji me tace ba cewa kawai yayi sai sun dawo..!
Suna mgana ya kallesu yana Fadin"komai lafiya..Amina goshinta ne ya fashe anyi Dinki sai Balaraba data Bugu kadan..suna hanyar Dawowa..!
Kai suka gyada gabadayansu Baba mallam ya cigaba da musu nasiha yana Nuna musu illah yanke hukunci Cikin fushi da aibata ya"ya da kalamai marasa Dadi sunan nan sai gasu Hajiya sun Dawo falon Aba suka shigo Gabadayansu Hamida ta Tsaya Daga wajen Daman tunda suka tafi ta ke kuka Tasani Amina tana da Jidali sai dai bata taba Tsammanin Jidalin Amina yakai har ya huce yadda take tsammani ba
Amina da plasta a goshinta bakinta kuma wankeshi akayi ya Kumbura mamanmu kuma mgani aka bata baba Mallam ya kalli Amina Dake Nanike da Mamamanmu kafin yace"Hajiya ki tafi da Amina ta zauna awajenki har ta samu sauki..Ke kuma Balaraba kiyi hakuri kin ji..
Sa"idu ya maidake Dakimki Don Alllah ina so har Abada bayan mu anan kada wani yaji wannam mganar..!
Mamanmu tace"Insha Allahu mallam..Bakomai..!
Baba Mallam yaji Dadi yana ta saka albarka kafin ya Mike shi da Hajiya wacce ta Riko Amina da hannunta ke cikin na Mamanmu kanta ta Dafa tana Fadin"Kada ki damu
Har Abada ina nan a matsayin Mamanki Diyata.!
Gobe zan shigo na Dubaki zan zo miki da kayanki..!
Kai ta daga mata Zuciyarta ta Sauka Tunda Aba ya janye sakin da yayi mata radadin Dake ranta ya Sauka haka suka fito har kofar gida suka rakasu dukkansu Hamida ta rike ma Amina hannu sai haawaye Amina ta Rike Hamida tana Fadin"kuyi hakuri Hamida ku yafemin..!
Hamida ta saka mgana har Hajiya taja Amina suka tafi wannan wani irin almari ne..?
Bata fatan kara ganin mai kama da wannan Ranar.
Achan gidan Baba Mallam kuwa Su Hanne duk sun yi barci Dakinta Hajiya takai Amina ta saka mata Ruwa mai zafi tace ta shiga tayi wanka ta gasa jikinta ita kuma ta Fice Shashen Mallam shi yake karanta mata abunda ya faru bataji Dadi ba ammh Tunda Mallam yace zai yi mgana da Amina shikenan komai zai Daidaita.
Bata jima ba ta Dawo shashenta,Saboda Hajiya nasara tazo wajen Mallam koda ta koma Amina tayi barci Dayake an mata allura a asibitin Tsausayinta Hajiya taji wata Kaddaran bamu ke Dorama kanmu ba Allah ne..!
Hajiya shimfida tayi akasa ta kwamta ta bar Amina akan gadon sai Washegari ne su Hanne su ka ganta Shima Hajiya ce tace su shiga su Duba Amina bata da lafiya kafin su tafi makaranta Allah yasa ma suna Revesition ne su Amina su kuma su ya Abida suna Mock ne.
Da suka Tambayi me ya sameta sai Hajiya tace Zamewa tayi a bandaki Hanne tafi shiga Damuwa da Halin da Amina ke ciki,Sannan kuma Amina ta Riketa tana Fadin"Keda Hamida nayi muku laifi ku yafemin Hanne..!
Bata iya gane komai ba,Sai da Suka je makaramta suka hadu da Hamida ta Fadamata komai Hanne ta shiga Tashun hankali Fadi take" kin ji ko.Hamida..?
Amina ta Debo jidalin Dayafi karfinta..!
Hamida tace"So nake ta kara jin Sauki..Sai mu turketa ta Fadamama yaushe ta fara aikata abu batare data sanar damu ba..!
Hanne tace"Tabbas..!
Da haka suka bar mganar sun fada a makaranta Amina bazata samu zuwa ba bata da lafiya bayan sun dawo ne suka shiga Har hamida gidan Baba mallam ta Duba Amina har da su Sa"adatu da yake an Fada Aminar bata da lafiya da ya Shamsu yaga bai ganta ba Hamida ta Fada acikin mota sanda Idi ya Daukesu
Taji sauki sai dai Kumburin bakin kadan shima ya Sauka goshin ma yayi Sauki Mamanmu ma ta warware ta shigo har Fatan wake da Hanta tayo ma Amina Hajiya na mata tsiyan cewa ko ta mata kara ta bar mata Amina sai ta Biyota Mamanmu na Dariya tace"To karan me Hajiya..?
Zan iya kara akomai banda Abunda ya shafi Amina..!
Nan suka yi ta raha da Hajiya Amina taji Dadin ganin mamanmu ta Rumgumeta tana fadin"Mamanmu ki yafemin..!
Mamanmu ta shafa kanta tana Fadin"Kada ki damu..har Abada matsayinki bai Sauya ba Diyata..Allah yayi miki albarka..!
Su hanne suna son mgana da Amina basu samu zama ba itama tana so ta yi mgana dasu tana so ta fada musu komai Saboda taji sauki aramta tana cikin wani hali Bata barci Aminu na cikin ranta tana so tasan Halin Dayake ciki gashu bata san ta wacce hanya zata sani ba Duk abubuwan da suka Faru basu saka ya fita ranta ba yana nan a makale ta damu dashi ta Damu tasan wani Hali yake ciki.
Tunda ga Ranar bata kara ganin Aba ba ballatana Yaya ammh har ya Zeenatu tazo sun gaisa su ya Zulaihat ma duk Mamanmu ta fada musu sun kira sun gaisheta kuma ba wanda yasan me yafaru sai dai ace abandaki ta Zame har su Anty Amarya sun shigo sun Dubata duk da tana ta Bin Diddigi Dalilin ganin Amina agidan.
Sai da Amina ta kwana Hudu awajen Hajiya sannan suka samu kebewa da Amina suka tambayeta ta fada musu komai Hanne da Hamida suka Saki baki suna kallonta Amina ta cigaba da Fadin"Wlh bansan yaushe ne ba..Ban kuma sam Lokacin da soyayyar Amin ta shiga raina ba..Ammh wlh ina son shi ko da wannan abun ya faru ban ji ya Ragu araina ba ina nan kawai ammh ina cikin tashin hankali da Damuwa na san yana chan cikin Tashin hankali..!
Hamida tace"Kina nufin wannan dai gayen da muka taba gani..?
Amina ta daga kai Hanne tace"Amina kuskuranki ne..Meyasa baki barsa yaje wajen mallam ba..?
Amina ta Dafe kanta tana Fadin"Bansani ba Hanne..Bansan haka zai iya faruwa ba..Gani nake kamar komai bazai yi daidai ba in yazo..Kuma wlh yanzu Ina son Aminu bazan iya Rabuwa dashi ba kuban shawara..!
Hamida da hanne suka kasa mgana Hamida ce tace"Bamu ta cewa Amina..Mgana tana wajen Aba da Baba Mallan sai dai in zaki bi Shawaranmy kada ki nuna abunda ke Ranki..Ki bari har muga komai ya Daidaita..!
Hanne tace"Nima abunda zan ce kenan..Gwara ki tsaya kiji abunda zasu ce..ammh koni kaina zan so ki Boye abunda ke ranki..Ina ji ajikina Ki rabu da wannan Mutumin Amina Shine Alherinki..!
Amina kallonsu kawai take yi batace komai ba Rabuwa da Aminu ba abu bane mai Sauki,Abu ne da bazai taba yuyuwa ba Domin don basu san me take ji bane..!
Shuru tayi musu kamar ta bar mganar sai dai ta kasa sukuni Baba mallam bai ce mata komai ba kuma yana zuwa Dubata,ammh bai ce mata komai ba,ga Damuwar halin da Amin yake ciki tasani kila ita tafishi kwanciyar hankali tasan yadda yake sonta Allah kadai yasan wani Hali yake ciki
Kwana Biyar da Faruwar abun ta kasa Daurewa ta samu Hamida da Hanne ta Rokesu su samo mata waya ta Kira Aminu ko hamkalinta ya kwanta Hamida ta kalli Amina tana Fadin"Amina kada ki kara jawo wani Jidalin don Allah..!
Hanne tace"In dai zata kirasa ta Fadamai ya rabu da ita zan Dauko miki wayar hajiya..Ammh da sharadin wannan shine na karshe..!
Da sauri Amina tace"Naji Hanne..Naji..!
So take kawai tayi mgana dashi Hamida kamar zatayi mgana sai kuma ta fasa,Hanne taje ta Dauko Wayar Hajiya Amina ta shige Tiolet din Dakinsu Hanne su kuma suna Waje suna Tsaro kada wani ya shigo su Lalace.
Jikin Amina na rawa ta saka Lambar Aminu ta Kira tana Di..Di..Di..kamar Zuciyarta zata Fito gabda zata Tsinke Taji an Daga Cikin Sanyinsa akoda yaushe yayi sallama Amina Kafafunta sun fara rawa kawai sai ta sakamai kuka yana jin haka zumbur ya mike Daga kan gadon Hotel din daya kama yana Fadin"MEENATA..aminatu..Alhamdulillah..Amina na shiga wani Hali..Tun washegarin abunda ya faru ina garinku Amina kullum ina anguwanku ina ganin yan"uwanki ina so nayi musu mgana na rasa yadda zan yi..Meena kina ina ne..?
Meena ina so na ganki ki taimakamin in banganki ba wlh zan lalalace Meenataaaa..!
*Janafty*
*TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*
*Sadaukarwa ga Halima yusuf gwarzo besty*
_Jinjina ta musamman gareka NAZIFI YARIMA..Nagode da karamcinka gareni na yaba matuka Allahu ya bar zumunci Ameen_
*🅿️20*
Jin ta kasa mgana sai kuka take yi yasa ya kara marairaicewa yana Fadin"Meenata kina ji kuwa...?
Ki yi hakuri ki daina kuka ki bari nazo Domin nasan ta yadda zamu Bullo ma al"amarin Kinji ko..?
Gabadaya yadda yake mgana ya gama kashe ma Amina jiki Tsausayinsa ya kara kamata tasan yadda yake sonta tasan Halinsa bazai taba kwanciyar Hankali ba sai ya ganta sai dai bata da wannan Damar ayanzu komai ya gama Lalacewa.
Tana jinsa cikin Damuwa ya kara Fadin"In zo Amina..?Don Allah kada kice A"a..Ina son ganinki..!
Hawayenta ta share cikin muryan kuka akaron Farko tace"Bazai yuyu ba..Kayi hakuri Amin komai ya kare..!
Ta karishe fada cikin kuka Tsabar yadda kalamanta suka gigita yasa ya koma ya zauna gefen gadon Daya tashi Cikin wani yanayi yace"Bangane ba Meeenata..?
Me kuma ya kare tsakanina Dake..!
Amina na Danne bakinta da kuka tace"Komai daka Sani ya kare..Soyayya ta dakai ta zama Tarihi kayi hakuri ba Laifina bane..!
Sai kuma ta kara Fashewa da kuka kukan da Aminu yake jinsa kamar acikin Ransa.
Cikin Fitan Hayyaci yace"A"a Amina kada kimin haka..Kada ki ce zaki Rabu dani alokacin da nafi kowa Bukatarki kinsan bani da kowa sai ke sai Nenne wlh in na rasaki Meenata zan Lalace ki bari nazo na ganki..Ki bari na bayyana kaina Amina Ina sonki Rashinki babban Gibi ne ga Rayuwata Amina ki taimakeni..!
Yana mgana hawaye na Bulbulo masa kamar famfo batasan sadda ta saki kukanta da karfi ba,Lokaci Daya ta abude Kofar Tiolet din ta Fito tana Gunjin kuka,bata kashe wayar ba ta mikama Hanne da Hamida da suka yo kanta ganin tana kuka kan gadon su Hanne ta Fada ta na Sakin kukanta Wlh itama tana son Aminu kuma Rabuwa dashi babban Ciwo ne agareta ammh ya zatayi..?
Aba zai kasheta in ya kara jin Labari makancin wannan,Zai iya mata baki Watarana shiyasa take tsoro sai dai tana Tsausayin Aminu tasan yadda yake sonta da gaske ne zai lalace akanta in ta rabu dashi.
Hamida ce ta isa gareta tana Fadin"Menene Amina..?Don AllAh ki Daina kuka hakanan..?
Hanne ce ta Lura wayar na tafiya yasa ta saka wayar a speaker daidai Sanda Aminu ke fadin"Meenata kina jina..?
Don Allah kimin rai ki taimakeni na ganki..Wlh kwanana Hudu agarin nan Saboda ke in ban ganki bazan taba Samun natsuwa ba..!
Ayadda yake mgana kowa yaji sa sai ya basa Tsausayi Amina kara Fashewa da kuka tayi zuciyarta na suya ashe ashe akwai irin wannan Ranar da Farinciki zai koma bakinciki bata Tsammanci Ranar nan kusa ba bata zata zata zo yanzu ba..!
Hamida da Hanne jikinsu ya gama yin Sanyi Hanne ce tayi gyaran Murya kafin tace"Ba ita bace..sunana Hannatu ni yar uwartace..!
Da Sauri Aminu yace"Hannen Amina..Hannen Hamida ai na ganeki..Amina tana bani Labarinku..Don Allah Hannatu ki taimakamin naga Amina don Darajan ma"aiki Salallahu alaihi wasallam..!
Suka karisa gabadayansu Cikin tsausayinsa Hanne tace"Akwai matsala ne..abubuwa Dadama sun Faru wadanda bazasu fadu ba..Ina Kara Jadaddamaka Haduwarka da Amina bazai yuyu ba kayi hakuri..!
Tana shirin yanke kiran ne yayi saurin Fadin"Koda na minti biyar ne..?
Koda na ganta nayi mata sallama ne Hanne..?Amina itace ni Hannatu..Wlh in bata zan Lalace Hannatu..Nenne zata rasani zata rasani..!
Dagajin yadda yake mgana kuka yake gabadaya sai hanne ta kasa mgana Cikin Tsausayi take kallon Hamida wacce ta Zabga Tagumi Ta rasa mafita sai Amina Dake kallonta idanuwanta Jajir tana kuka Dagachan taji magiyarsa Cikin Raunin Murya"Ki taimakeni Hannatu..Nayi miki alkwarin wannan shine na karshe..Don Allah ina son ganin Amina..Don Allah..!
Hanne ta saki ajiyar rai kafin tace"Shikenan..Kazo da Daddare bayan Sallar isha'i..'
Cikin Rauni yace"Meyasa ba yanzu ba Hannatu..!?
Hanne tace"Ba dama ne..Kabari dai Daddare shima sai mun san yadda zamu iya ku hadun..!
Suna jin Saukan Numfashinsa kafin yace"Nagode kwarai..Nagode Hannatu..Bazan taba mantawa da karamcinki ba..!
Da haka Hanne ta Datse kiran Hamida tayi saurin cewa"Hanne kikasan me kika aikata kuwa..?
Hanne tace"Ya zan yi Hamida..?Tsausayi ya bani..!
Hamida tace"To yanzu ta yaya zasu hadu batare da wani ya sani ba..?
Nidai ina Tsoro fa..Yadda abubuwan suka Lalace In muka kara wani laifin ba Amina ba har mu bazamu taba Fita ba Hanne..!
Hanne shuru tayi batayi mgama ba sai chan tace"Zamu samu mafita Hamida..Kada ki damu..!
Amina dai kukanta kawai take yi Cikinsu an rasa mai Lallashinta gabadaya Tsausayinta ya gama kamasu suna Tunanin har yaushe ne Amina ta bari ta fara soyayya har tayi wannan Zurfin basu sani ba..!
Sai da suka gaji da jin kukan nata suka Fara bata hakuri kana ta Hakura ta Daina kuka sai dai idanuwanta sun kumbura ido ya sauya Launi saboda kuka har zuwa yammah sun gagara samun mafita Hamida ta kalli Hanne tana Fadin"Ki basa hakuri kawai Hanne..banga mafita ba..Waje fa kinsan su Baba mallam suna nan ta ina zasu hadu batare da wani ya gansu ba..!
Hanne dai batayi mgana ba tana ta Tunanin mafita ba har akayi sallar Isha"i basu samu mafita ba Ya Abida ce ta shigo ta gansu zugun zugum Dariya tayi tana Fadin"Ku kuma Lafiyarku kukayi zugum kamar masu zamam makoki..?Ko Aminar ce taki Warwarewa har yanzu ku cigaba da Iskancin naku..?
Cikinsu ba wacce tayi mgana itama bata Damu ba baki tatabe tana Fadin"Bakin Amina ya Mutu..Na Hamida da Hanne daman bai kai nata Tsini ba suma sun mutu..Allah Sarki..!
Ta karishe Fada Tana Dariya wannan karon Mirmishi kadai Hamida tayi mata Ta fice daman wani Littafin koyon Turanci ta Dauka cikin Jakar makarantar ta fice.
Hamida Bini bini ta kalli Hanne tana Fadin"Kin samo mafitan ne..?
Sai hanne ta Girgizakai Cikin Damuwa Hamida kan ce"Jikina na Sanyi..Ina ji kamar wani abu zai faru Hanne..!
Itama Hanne haka take ji ammh Tsausayin Amina take ji da Aminu Shiyasa ta kasa cewa A"a tunda Farko Tunanin wani abu tayi taja hannun Hamida suka fita Leke suka fara yi Domin ganin wadanda ke waje Allah ya taimaka ba kowa masallaci ma an Rufe ba Motar ya Jafar bata Ya Nasir kenan sun tafi gida Saannan Allah ya taimake su Aba ya Dawo da wuri ga Motarsa nan sannan sunji mganarsa afalon Baba Mallam da Hajiya Babba..!
Hanne ta kalli Hamida tana Fadin"Na samu mafita..In..!
"Su waye anan..?
Gabansu ya fadi da sukaji Muryan ya Shamsu Cikin Daburcewa suka juyo Hamida ce tayi mgana"Bakomai ya shamsu cikin gida zamu shiga..!
Yana Tsaye Daga kofar Dakinsu yace"Cikin gidam ina..?
Da sauri Hanne tace"Zan rakata gida ne ya shamsu..!
Kamar zai yi mgana sai kuma suka ga juya ya koma Daki ya Dauko Buta Makewayin Dake bayansu ya wuce bai karama kallonsu ba ganin haka yasa suka Sauke Numfashi Hanne taja Hannun Hamida suka Fice daga gidan zuwa gidansu wayar Hajiya tun mangariba ta Dauketa tana Hannun Hannatu.
Gidan su hamida suka je suka zauna Har Aba ya dawo sannan Hanne tatashi tace zata tafi Hamida ta rakata mamanmu har tana Fadin"Hanne baki kwanciyar anan..!?
Da sauri Hamida tace"Mamanmu Amina zata bari ita kadai in ta kwana anan..!
Mamanmu tace"Kuma fa hakane..To maza ki rakata Hamida ki Dawo Dare yayi..!
Da haka suka samu suka Fice Aba na Shashensa Yaya ta kaimai abinci suka Fice akofar gida suka Tsaya Hanne ta Leka Wani lungin jikin gidansu Amina Dake da Duhu kadan Tunda Kofar gidansu dana Baba Mallam gauraye yake da Hasken Gen da aka kunna Hamida ta nuna ma wajen tana Fadin"ZAn kirasa yazo ta nan su hadu..Ni zan Tsaya anan ki shiga ki Fito da Amina yau Hajiya Shashen baba mallam zata kwana zamu Tsaya Daga chan muna gadinsu kada wani yazo..!
Hamida ta kalleta cikin Tsoro kafin tace"Kina ganin ba Matsala..?
Hanne ta Sauke Numfashu tace"Insha Allahu..Ki fadama Amina kada ta bata Lokaci..!
Kai hamida ta gyada ita ta Fara wucewa zuwa gidansu Hanne ita kuma ta koma kofar gidansu Amina ta Danna ma Aminu kira Daman ta adana Lambar da sunan Amina.
Tana shiga kamar yana jira ya Daga Kiran kafin tayi mgana yace"Ina Hangenku tun dazu hannatu..Amasallacin gidanku nayi sallar mangariba ma..!
Hanne ta zaro ido ta fara waige waige Daga chan gaba ta hango hasken Mota motan a kashe sai kuma aka Bude Mota aka fito Cikin son Tabbatarwa Hanne tace"Kai ne Daga nesa..Ka fito a mota..!?
Cikin wani sanyi yace"Eh nine..!
Da Sauri Hanne tace"To ka kariso da Sauri..Yanzu Hamida zata zo da Amina..!
Daga haka ta datse kiran ta shigo gidansu Amina jikinta na rawa kada wani ya fito ya ganta Aminu da Sassarfa ya kariso duk ya rame kamar wanda yayi jinya yana Sanye da Riga da wando bakake ya saka wata Rigar Sanyi mai Hula ya Rufe kansa yana zuwa Hanne ta Leko sai da Tabbatar ba kowa sannan ta fito tana Fadin"Don Allah minti goma..Akwai Hatsari Aba na cikin gida hakama Baba Mallam sauran yayyinmu ma suna cikin gida kada ka bata Lokaci har komai ya Lalace don Allah..!
Hulan kansa ya cire fuskarsa ta bayyana Cikin Muryansa kamar ta waya yace"Insha Allahu Nagode Hannatu..!
Zatayi mgana kenan sai ga su Hamida sun fito Amina na bayanta da Hijabi tana Tafe kamar wata mara Laka ajikinta Allah ya taimake su ya Abida na Kitchen Hajiya kuma na shashen Baba Mallam suka samu suka Lallabo suka fito Allah yasa ba wanda ya gansu..!
Tundaga nesa yake kallon Amina Hankalinsa ya tashi da suka kariso yaga saman kanta da Ciwo an cire Plastan tuni,Da hanzari ya karisa gabanta yana Fadin"Meenata me ya sameki ne..?
Yadda yake kallonta haka take kallonsa Hawaye sun tarun mata ganin yadda ya rame hamida da Hanne sai suka koma gefe suna kallon Ikon Allah ganin yadda Amina ta Fashe da kuka Aminu ya Rude ya rasa ya zai yi Cikin wani yanayi yake fadin"kiyi wa Allah Amina kibar kuka ki Fadamin me yake faruwane..!
Hanne ce taga Tsayuwar bata da Amfani kada wani yazo ya gansu yasa tace"Amina ku shiga nan.Kinsan dai Halin da ake ciki ko..?
Tafada tana nuna mata lungun bayan gidansu da kai Amina ta amsa mata Kafin ta wuce tayi gaba shi kuma yabi bayanta su kuma sai suka koma Cikin Haraban gidansu Amina suka Labe Jikin Get gabansu na Fadi Fat Fat suna Tunanin anya basu yi ganganci ba..?
Amina kuwa suna shiga dan lungu ta Fashe da kuka ta Duke Aminu yabita shima ya Durkusa Kamar yayi kuka yana Fadin"in kika cigaba da wannan kuka Amina zan iya shiga wani Hali..Kiyiwa Allah ki Fadamin abunda ya Faru..!
Yadda yake mganar ne yasa Tsausayinsa ya kamata yasa ta Dago Cikin kuka ta fara Fadamai abunda ya Faru Tundaga farko sai dai ta boyemai Sakin da Aba yayi ma mamanmu akanta Ba saboda komai ba akwai Kunya ta ce an saki Mamanmu Saboda ita ta karishe Da Fadin"Soyayyarmu zata zama Tarihi ne Amin..Rabuwar mu shine Alheri Wannan abun da ya faru kadan ne akan wanda zai kara faruwa..Ni kaina nasan ba Domin baba Mallam na sona ba da yanzu wani Labari akeyi..Wlh bawacce tataba aikata abunda na aikata Bata sani ba..Ba Laifina bane Soyayyace ta jani inda ta kaini Ina sonka ammh kayi hakuri mu Kareta anan akuma yau Aminu...Don Allah kayi hakuri..!
Kuka take kamar ranta zai fita Aminu yaji kamar ta Chakamai mashi da Sauri ya Mike yana Fadin"Bazai taba yuyu ba Amina..Ina bazan iya Rabuwa Dake ba..Laifinki ne da kin bari na gabatar da kaina da Duk haka bai Faru ba..!
Yau ba sai gobe ba zan bayyana kaina Amina insha Allahu ke Rabona ce..!
Jin kalamansa yasa ta Mike da Sauri Har tana neman faduwa tace"Kada kayi haka..Lokaci ya kure abunda zaka aikata bazai kawo mafita ba Amin..!
Yana Kokarin Hana Idanuwansa zubar kwallah ya ke kallonta ta Duhun wajem Cikin wani yanayi yace"Menene Mafitan AMINA..?
Kada kice mafitan itace na Hakura Dake..Wlh in haka ta faru Zan Lalace Amina akanki ki taimakeni kimin Rai don Allah..!
Yake fada sai Hawaye Gwiwansa ya saka a kasa yana Rokonta Kada ta barsa Amina ta Rude batasan sadda ta saka Hannu ta Dago Kafadun Aminu ba Cikin kuka take fadin"Don Allah ka tashi..Na shiga uku..!
Yana Dagowa bai yi wata wata ba kawai ya jawota ya Rumgume kam kam kamar wani zai kwaceta alokacin Inda tasan sanadin wannan Rumgumar Zanen kaddaranta zata fara na Tabbata da Amina bata amince ba in da Aminu yasan sanadin wannan Rumgumar Amina zata haramta garesa da har Abada bai yarda yazo ba..Sai dai ina bakin Alkalami ya Riga ya Bushe..!
Amina ta kasa yin wani motsi ballatana ta kwace jikinta Tayi luf akirjin Aminu yana Fadin"Bazan iya Rayuwa baki ba Amina..Kinsan ina sonki..kinsan ina sonki in kika barni ina zan saka kaina..?
Amina alokacin Tunanin bai bata ta kwace jikinta ba,tsausayin Aminu da soyayyarsa ya Rufe mata idon da bataji bata gani.
Alokacin wani al"amari ya Faru wanda ya Faruwarsa ya Fallasa abubuwa Dadama kuma ya Watso wasu sirruka a waje alokacin kuma Zanen kaddaram Amina da wanda Allah ya Turo mata cikin Rayuwarta ya fara..!
Suna cikin waannan yanayin suka ga an Dallaresu da Hasken Fitila Lokaci Daya Cikin Muryansa da ko barci Amina Take bazata taba bace Mata ba yace"Su waye anan..?
Dam..!
Gabanta ya amsa hakama na Aminu arude ta Dago kanta Daga Kirjin Aminu karaf Hasken Fitilan ya Hasketa Tar Cikin Faduwar gaba da wani yanayi ya Jafar ya Zaro ido Cikin Tsawa yace"AMINA..!!!
Yadda ya Kira sunan ne ya Girgiza Zuciyar Amina Hanjinta suka Cure waje Daya kuma har Alokacin Tana Rike da Aminu shima yana Rike d ita Rudewa yasa sun kasa Sakin juna..!
Hamida Daga cikin gida ta kalli Hanne tana Fadin"Hanne gabana na Fadi..Inaji ajikina mun rusa komai fa..!
Ita kanta Hannen Jikinta rawa yake gabanta na Fadi Cikin Tsoro tace"Nima Hamida..Na farajin wani iri na fara Nadama fa Hamida..!
Hamida ta Bude baki zatayi mgana kenan Muryan ya Jafar ta shiga kunnensu sanda yake fadin"Innalillahi Amina me zan gani..?
Iskancin naki har yakai kikawo wani kato a kofar gidanku kuna shanshanci Amina..!
Dam gabansu ya fadi atare suka kalli juna suka zaro ido kafin suyi Rige rigen Lekawa ta kofa sai da suka kusa Sakin Fitsari a wando ganin ya Jafar Tsaye bakin lungun da su Amina suke ya Hsskesu da Hasken Fitila Fuskar nan kamar an aikomai da Sakon mutuwa.!
Hamida ta Damke hannun Hanne suna karkawa Lokaci daya suka Hada Baki wajen fadin"Mun shiga uku..Mun kara saka Amina acikin Bala"i..!
Agaban idonsu ya jafar ya taka ya Shiga lungu sai gani kawai sukayi ya Tunkudo Amina saida Hijabin jikinta ya Hardeta ta Fadi yaraf Cikin Fitan Hayyaci ya saka kafa ya Shureta yana Fadin"Tashi Tashi munafuka yau Allah ya Toni asirinki..Daman wannan Idanuwanki bakomai a Cikinsu sai iskanci Kee Amina yarinyar dake Rumgume da wani kato Amina..?
Tashi muje gaban Aba na Sanar dashi Abunda nagani tashi nace don Ubanki kafin nayi miki illah yanzu nan..!
Yafada yana kokarin kara Shurinta da Sauri Aminu ya rikosa Cikin wani yanayi yana Fadin"Kadaina Dukanta..Don Allah ka Tsaya ka Bincika wlh ba abunda kagani bane gaskiya..Ina son Amina kuma auranta zan yi..!
Ya jafar ya Fincike hannunsa bai yi wata wata ba ya Daga hannu ya Sharara ma Aminu mari lokaci Daya ya Nunasa da yatsa yana Fadin"kai har kana da bakin mgana Lallatacce kamar ka..?Allah ya isa Tsakanimu dakai Tunda kayi Samadiyar batamana kanwarmu kuma kabar kofar gidan nan kafin na Fito da matasan gidanmu su Illata ka yanzu nan..!
Shi bai Damu da kansa ba Amina yake kallo tama kasa kuka Zuciyarta ya Soye ta riga ta sani ajikinta tanaji Ba wani Tsumi ba Dubara ayadda ya Jafar ya gansu Allah ne kadai zai iya Fitar da ita shiyasa ta kasa motsi ko mgana!
Yana so yayi mgana bakinsa yayi Nauyi yana ji yana gani Ya Jafar ya isa ga Amina ya taso ta Bai yi wata wata ba ya Daga hannu Dama da Hauni ya Dauketa da maruka da sai da ta Koma ta Kife kamar zata Fadi ya Fizgota yana Fadin"Muje agaban Aba da mamanmu mai kareki..Ki Fada musu Tun yaushe kika fara Wannan Lalacewar Amina..!
Ya karishe Fada yana ingizata gaba,Aminu ya taka ya Bisa ya Dagamai hannu yana Fadin"Karka Nuna min iskanku na yan Tasha..Nima In akabi ta wani Fanni na Fika tashanci wlh zan kara Dauke ka da mari Kaji ma na rantse in baka bace Daga gani na ba..!
Ayadda Ya Jafar yake zai aikata Abunda ya Fada din sai ya koma baya Cikin Raunin Murya yace"Amina komai zai yi Daidai..Zan tafi Yola...su Alhaji Baba zasu zo nema min Auranki..!
Amina tana jinsa tana so,tacemai kada yayi haka,ammh kuma a wannan gabar bazata iya mgana ba Domin mganar bata da wani amfani..!
Hamida da Hanne suna jin Bude gidan ya Jafar suka Rumtuma zuwa Cikin gida ba inda jikinsu baya rawa Saboda Abunda zai iya Faruwa yau..!
Haka Ya Jafar yake iza keyar Amina kamar wacce tayi sata Yana tafe yana Dukanta Fadi yake"Amina kece Rumgume da wani kato..?
Yaushe kika fara wannan lalacewar..?
Yana Fadi yana Dukanta Saboda Wani Bakinciki ke kara kamasa in ya Tuna da yadda yaga Amina Rumgume jikin wani kato..!
Hanne da Hamida Dakinsu Hamida suka Fada suna Haki ya Zeenatu na kwance ta Mike tana kallonsu,Cikin wani yanayi tace"Lafiyarku kuwa..?
Kasa mgana sukayi jin Muryan ya Jafar Tsakar gida yana Kiran sunan Aba gabadayansu suka kara Tsurewa Hamida da Hanne suka kamkame hannun juna,Saboda Tsoro ya Zeenatu ne ta Mike tana Fadin"Muryan Ya jafar nake ji..?
Meya faru kuma..?
Tafada tana mikewa Tsakar gida ta Fita Daidai Sanda Aba ya fito shi da Yaya Sai kuma Mamanmu data fito Daga Dakinta Dankwali a hannu Tana Fadin"Lafiya hayaniya me nake ji..!
Ya Jafar Amina ya Tura gaban Aba sai da ta Fadi cikin Fushi yake fadin"Aba Gatanan ta fada muku tun yaushe ta fara Lalacewa..Yanzu nazo zan karbi mganin da za"a shafa ma mai sunan Mallam akansa kawai naci karo da yarinyar nan Rumgume ajikin wani Dan iskan kato ajikin gidan nan Aba..!
Gabadaya jikin Aba sai ya fara rawa Yaya,kuma Kirjinta ne ya fara Lugude Yayinda Mamanmu ta saka Salati tana Fadin"Innalillahi...!
Haka kawai take fada Hanne da Hamida dake cikin Daki suka kalli juna suka Gwalo ido,ya Zeenatu kuma zuciyarta sai da ta amsa Amina bazatayi haka ba Halinta bane..!
Ba wanda ya Lura da Aba Jiri ya kwashesa sai da ya Saka kafa ya Ture Amina Dake gabansa takasa kuka sai na Zucci Domin kukanta bazai taba Cetonta ba..!
Kadan ya Rage bai Fadi ba Yaya tayi Saurin Rikosa ta fashe da kuka Bango ya Dafa yana Fadin"Jafar fitarmin da ita Daga gidana..Ka fita da ita ban Haifi Dan da zai zamenin zakka ba ta ficemin Daga gida..!
Yake Fada sai hawaye Sharr Mamanmu ta Fashe da kuka tana Fadin"Na shiga uku ni balaraba..In ka Koreta ina zataje Abbansu..?
Wlh Amina bazatayi haka ba Halinta bane..!
Ta karisa wajen Amina ta Dago tana Fadin"Amina ki tashi ki fadamusu karya ne..Abunda Jafar ke fada ba gaskiya bane..!
Da manyan Idanuwanta Take kallon Mamanmu Lokaci ya kure bazata iya kare kanta ba batasan sadda tace"Gaskiya ne Mamanmu..Gaskiya ne ya ganni..Rum..Rumgume..!
Bata karisa ba Mamanmu ta Dauketa da Mari Cikin kuka take fadin"Karya ne..Ba gaskiya bane..!
Take Fada tana kuka kamar Ranta zai Fita Zuwa Lokacin hatta Hanne da Hamida sun fara kuka Aba kuma Yaya na Rike dashk Dafe da Bango Yana Hawaye..!
Ya Jafar ya kalli Aba yana Fadin"Aba kadaina kuka..Wannan yarinya Dukan mutuwa zan mata yanxu nan..Wai har dan iskan yaron yana Fadin sonta yake yi zai aureta..!
Aba ya girgiza kai yana Fadim"Na Rantse da wanda Raina ke hannunsa bazan aura ma Amina wannan yaron ba..Jafar Amina bazata samu abunda Take so ba..bata isa ba..!
Yafada yana jin wani Takaichi da Bakinciki Ya Jafar Cikin mamaki yace"Dama kasan shine Aba..?
Aba ya jinjina kai yana Bama Jafar Labarin abunda ya faru bai gama ba Ya Jafar ya Finciki Amina ya Fara Dukanta yana fadin"Kafin ki kashemana Uba ke zaki fara Binsa Amina..!
Dukanta yake yi kamar Allah ya aikosa Ba wanda ya hanasa Yaya kuka take tana rike da Aba Dake fadin"Hadiza kamani muje ciki..Jiri nake gani..!
Ya Zeenatu ma kuka take tana Fadib"Mamanmu ki cece Amina ya jafar zai kasheta..!
Mamanmu Dukewa tayi tana Fadin"Jafar kadaina Dukanta don Allah..Jafar kabari..!
Take fadi ko jinta bayayi sai ma Karisawa da yayi ya karyo ganyen Bishiyar Dake Tsakar gidan ya Shiga Lafta ma Amina wacce bata kuka ko kadan sai na Zuucii awannan gabar ta gagara tana jin kada ma wani ya Ceceta abarta ta Mutu ta huta ta saka Mamanmu kuka da Yaya,Aba ma yana kuka Saboda ita ai bata da wani amfani acikin wannan Rayuwar..!
Hanne ce Jikinta na Rawa da wayar Hajiya Dake hannunta ta Kira Baba Mallam wanda mamaki ya kamasa ganin Hajiya zaune gefensa suna Hira Cikin mamaki yace"Yau kuma Zolaya kike ji ne Abu..?
Kallonsa tayi kafin tace"zolayar mene Mallam..?
Wayarsa ya nuna mata yana Fadin"Kirana akeyi da wayarki fa..!
Cikin mamaki tace"To lafiya..?Wayata tana Daki na barta fa!
Jin haka yasa bai ce komai ba ya Daga Kiran kukan Hanne ya fara ji tana Fadin'Baba Kazo gidan Baba Sa"idu..Ya Jafar zai kashe Amina da Duka kazo da sauri..!
Baba Mallam Zumbur ya Mike Cikin tashin hankali yake tadin"Hajiya Wani abu ya sake faruwa..Muje gidan Sa"idu..!
Hajiya ta fara salati Hankalinta tashe ta Rarumi hijabinta ta saka Baba Mallam na kan gaba suka Fice Daidai Anty Amarya ta fito zuwa shashen Mallan taga fitarsu Cikin gaggawa tasan ba Lafiya itama sai ta Rufa musu baya ganinsu sun shiga gidan Baba Sa"idu yasa aranta tasan ba Lafiya Domin Baba Mallam baya zuwa gidan Baba Sa"idu haka kurum wani abu bai faru ba.
Cikin azama tabi bayansu Domin tana son Taga abunda ke faruwa..!
Abunda Su Baba Mallam suka gani Sai da Hankalinsu ya tashi Ya Jafar yayi m Amina Dukan kawo wuka Baba Mallan ne ya karbe sandan Hannunsa yana Fadin"Jafaru ashe baka da Hankali ban sani ba..?
Ya jafar na haki yace"Baba Mallam so take ta kashemana iyaye da bakincikinta..Shanshancinta ya wuce Tunanimku yau fa ganinta nayi a nan kofar gidan Rumgume jikin wani kato Mallam..Amina fa nawa take..?
Har ta gama lalacewa haka bamu sani ba..Shine kafin ta kashe su gwara ita ta Fara Binsu..!
Karaf manganganun akunnin Anty Amarya Data shigo Salatinta kawai akaji Tana Fadin"Innalillahi wannan yarinyar Tabbas zakka ce..Iskancinta nata har yakai haka bawanda ya sani..?
Kallonta kawai sukayi kowa ya kasa mgana Hajiya,Amina ta Duka ta Rumgume jikinta Duk ya Fashe da Duka Fadi take"Jafar kayi dukan ganganci..Ba haka akeyi ba..!
Mamanmu na gefe tana ta kuka ita da Zeenatu harta Jawaad Dake barci hayaniya ya tadashi ganin Dukan da Ya Jafar kema Amina sai shima ya Fara kuka..!
Baba Mallam Hankalinsa ya tashi Ya kalli Jafar yana Fadin"Ina Sa"idun..?
Da kyar yace"yana Dakinsa..!
Baba Mallam ya wuce gaba yana Fadin"Hajiya ki taikama Mamana..Kai kuma muje Ciki..!
Da haka ya tasa Jafar suka shiga Falon Aba Hajiya kuma Da Mamanmu suna Hawaye suka Daga Amina da Idanuwanta basa Buduwa Sai faman wash Wash take da kananun kuka Kilama ya Tardagata inji Hajiya Zeenatu ta kama musu suka yi Dakin Mamanmu da ita sai Lokacin Hamida da Hanne suka fito ganin Halin da Amina ke ciki suka Hade kai suna ta kuka Anty Amarya Fadi take"Ruwan zafi za"a Dafa ayi mata gashi..Allah ya kyauta bai mata karaya ba kinsansu in suka Fara Duka kamar mahaukata..!
Hajiya taji kamar ta Make bakinta sai dai batayi mgama ba batama san ya akayi tasan wani abu na Faruwa ba domin Anty Amarya sai dai ta Fadama wani Halinta..!
Ashashen Aba kuwa Baba Mallam suna shiga suka gansa kwance kan kujera Takure yana rawan Sanyi Fadi yake"Hadiza sanyi nakeji ki sakamin bargo..!
Baba Mallam ya Duka agabansa yana Fadin"Ashh Sa"idu me zan gani haka..?
Yana jin muryan Baba Mallam ya Bude ya Rarrafa ya tashi Zaune yana Cijewa Baba Mallam ya rikesa Hannunsa ya kamkame yana Fadin"Baba don Allah ina so cikin Almajiranka masu karatu ka Tallata Amina in akwai mai so..Bana so wunin gobe ya kare ban aurar da Amina ba..Ina jin tsorom wani abu ina Fargaba kada watarana Bakincikinta yayi ajalina..!
Baba Mallam yace"Baza "ayi haka ba kana cikin Fushi Sa"idu.
Mu Tsaya mu bincika zuwa gobe zan yi mgana da Mamantawa kan yaron Dake zuwa wajenta in har ya Chanchanta zan bashi Mamana..!
Jikin Aba na rawa yace"A"a Baba..Na riga nayi Rantsuwa ko bayan Raina Amina bazata samu abunda take so ba..Bata isa ta fita Zakka ba..Kada ka Saurareta Nidai ko Waye ka aura mata ta bar gabana na Daina ganinta ko zan samu Saukin Abunda nakeji..!
Baba Mallam yayi shuru yana kallon Baba Sa"idu ganin haka yasa ya kara Rike hannunsa sai Hawaye sharr yana Fadin"Kada kace A"a Baba Mallam
Kayimin wannan alfarman a mtsayin ka na Uba gareni ka yafemin in har ahalima suna goga maka bacin suna ka yafemim..!
Ya karishe Fada Cikin kuka,Da Jikin kowa saida yayi sanyi Baba Mallam yace"Kul..Kar na Sake ji..Kai jinina ne Sa"idu har gaban Abada..Kada ka Damu Zan aurar da Mamana kamar yadda ka Bukata sai dai bazan mata auran kaskasaci ba kafin waye wan garib gobe Allah zai bayyanamana Mijinta mafi Alherinta aduk inda yake Sa"idu kayi hakuri kada ka aibatata kila ita irin Tata Kaddaran kenan..!
Aba bai Sake mgana ba Tari ya Sarkesa kamar zai sheka Ya Jafar da Yaya suna Rike dashi yaya kuka kawai take Yadda take ji aranta baya Misaltuwa ita ta Haifi Amina Radadin da kowacce uwa take ji in Wani Daga Cikin D'anta ya zama zakka..!
Ganin Halin da yake ciki yasa Baba Mallam yace su tafi asibiti haka kuwa akayi Ya Jafar ya Tuka Motar Mallam dashi da Yaya suka tafi asibiti da Aba su Hajiya kuma suna tare da Amina da tasha gashi Ta samu Targade a Hannunta na Hagu da gocewar kashi a Kafarta Mamanmu da Hajiya suka Shafe mata da man zafi tana Hawaye sunayi Mamanmu ma kasa zama tayi ta koma Cikin Bedroom dinta tana kuka Anty Amarya na nan bata tafi ba da anyi abu sai ta Tafa Hannu tana Fadin"Oh..Allah dai ya shiryamana..An haihu dai a Ragaya..!
Sai da Hajiya ta gaji ta tanka mata da Cewa"Ki kama bakinki Domin kema Uwace..Akwai Sa"adatu da Sabeeha agabanki bakisam ina Kaddara zata kaisu ba!
Jin haka yasa ta Fara Fadin Hajiya na mata Mugun fata Cikin gatsali tace"Allah ya Tsareni kowa yasan ya"yana basu fita zakka ba..Daman ai wanda yasiya Rariya yasan zata Zubda Ruwa..!
Ba wanda ya kara bi ta kanta kuma taki Tafiya kamar mayyah har sai chan Dare Baba Mallam ya Dawo Jinin Aba ne yayi sama An bashi gado ya Jafar na wajensa zai kwana sai alokacin suka koma gida bayan Baba Mallam ya kwantar ma da Yaya da suka Dawo tare ita da Mamanmu hankali da kalamai masu sanyaya rai sun Daina kuka Amina kuma ta samu barcin Wahala Baba Mallam yace zuwa da Safe mai gyaran Targade zai zo ya gyara mata.
Sanda suka koma gida Dagashi har Hajiya sun kasa Runtsawa Fadi kawai Take"Na kasa gane meke Faruwa Mallam..?
Nasan Jafaru bazai yi karya ba..Nasam jikina na bani Amina ba haka take ba..!
Baba Mallam yace"Wani al"amari ne da Allah kadai yasan me ya Lullube aciki..!
Nan ya shiga Fadamata yadda sukayi da Baba Sa"idu ta sauke Tagumi tana Fadin"Kai..wata sabuwa to menene Mafita..?
Baba Mallam yace"zan kwana Istikara Zuwa Safe Boyayyan al'amarin zai bayyana Hajiya kema ki tayani..!
Da kai ta amsa mai,Tabbas sun kwana Gayama Allah Hajiya ce ma wajen Uku na Dare ta kwanta Baba Mallam sai karfe 4 ya iya barci saman Darduma bai tashi ba sai da yaji wayarsa Dake cikin Aljihunsa na Ringing yayi Zumbur ya Mike yana Lalubota yaga DANMALLAM.. !
Ne ke kiransa ajiyar rai ya Sauke ya Daga wayar da Sallama Dagachan bangaran Umar ya amsa cikin Sanyinsa yana Fadin"Baba..Nasan yanzu asuba ne a Nageria shiyasa na Bugo Domin na samu ladan tashinka Duk da nasan kila ma kana masallaci..!
Baba Mallam ya Mike a kasalance yana Duba agogon bangon Bedroom dinsa 4:55pm na asuba..!
Cikin karfin gwiwa yace"Na makara yau Umaru..Naji Dadin kiranka Allah yayi maka albarka..!
Ya amsa da Amen Cikin Farinciki kafin suyi sallama suna gama wayar Baba Mallam yayi kasake na wani Lokaci kafin Lokaci Daya Mirmishi ya mamaye Fuskarsa Hajiya ya kallah Dake barci ya karisa ya Bubbuga Gefen gadon yana Fadin"Hajiya..Hajiya..!
Mika tayi Cikin Tattatusan lafazi yace"Ki tashi mun makara sallar asuba..!
Mikewa zaune tayi tana Mutsike ido Lokaci Daya tana Fadib"Mallam kasamu mafita kuwa..?
Wlh da yarinyar nan na kwana araina ita da Sa"idu..!
Cikin Mirmishin data kasa gane masa yace"Kada,ki damu..Cikin ikonsa ya kawo mana Mafita tashi kiyi sallah ki shiga gidan Sa"idu ni kuma Daga masallaci asibiti zan tafi na Dubasa..!
Kai ta gyadamasa tana kallonsa ya saka akyabbansa da Rawaninsa ya Fice acikin ranta tana Tunanin wata mafita Mallam ya samu wannan Fara'ar dake fuskarsa ta bayyana Koma wata Mafita ce ta zauna sosai acikin Ran mallam din.!
Ina godiya sosai masu sharhi yan wattapad ina gaisuwa..!
*Janafty*
*TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*
*🅿️21*
Suna idar da Sallar Asuba Baba Mallam bai Tsaya ba Ya Nasir ya Tukasa zuwa asibitin Tunda shima nan ya sallaci sallar asuba Ya jafar tun Daran jiya ya kirashi ya fadamai kafin su tafi sai da Baba Mallam ya Umarci Shamsu daya kira Mallan ya"u mai Dori yazo ya Duba Amina..!
Haka kuwa akayi gari na waye bakwai na safe Ya shamsu yazo da mai Dorin,Koda yaje Hajiya Babba tana gidan Amina jiki yayi Tsami sai faman kuka take ashe kadan tayi Domin wajen gyaran Targade da Goshewar data samu sai da ta raina kanta sai da su Hajiya da Mamanmu suka Riketa Hamida da Hanne suna ta kuka Ranar ko shirin zuwa Hadda ba wanda yayi acikin gidan sai dai chan su Sa"adatu ne Idi Direba zai kaisu..!
Yaya kuwa Hada hadar abun karin da zata kai asibiti take yi ko afuska bata bayyana wata damuwa game da Amina ba Ita ta Aba take yi,ammh sai dai karkashin Ranta Damuwa ne Dankare wanda Tsabar kawaicinta yasa bata bari a Fahimceta ba, sai dai fa Uwa uwa ce kuma bazata Haifi abu da Cikinta tace kuma bata kaunarsa ba sai dai kawaici da wasu abubuwan da kansa Uwa ta kauda kai kan abunda ta haifa sanin Halinta ma ba wanda yabi ta kanta Domin kowa yasan Yaya bata taba Shiga Sha"anin Amina sai abun yaci Tura yakai mata makuran da zata tanka..!
Ya bada mgani an shafa mata Cikin kwana Daya ammh Amina ta Fita Hayyacinta ta rame sai ido,Tasha wuya cikin kwanakin Wuyan da bazata taba mantawa da ita ba Hamida da Hanne sun fi kowa sanin Amina tafi kusa dasu shiyasa lamarinta yafi Damunsu gabadayansu suma Suku suku suke kamar basu da Lafiya sun tasa Amina da Tagumi tana kallonsu sai dai yau karon Farkon Bakin Amina ya Mutu bata mgana sai ido sai kuka acikin Ranta wani abu ne mai Girma Tana ji ajikinta komai yazo karshe ta rasa Aminu shima ya rasata sannan abu mafi girma tana jin kamar wata Kaddarace zata faru da ita yasa abubuwa suka kwabe mata Lokaci Daya sai dai koma menene Tayi alkawarin bazatace komai ba Tunda mai Faruwa ta Riga ta Faru babu Tsumi babu Dubara..!
Dakyar Hajiya ta Lallasheta tasha Tea da Panadol Saboda Zazzabin Jikinta sai ta samu barci sai alokacin suka samu Daman karyawa Mamanmu da Yaya suna shirin Tafiya asibiti duk da sunyi waya da Ya Jafar yace ya Dawo gida Ammh Baba Mallan nachan suka barsa tunda safe Ruwan zafi ma Nasir ya koma gida ya Taho dashi Da kayan Tea..!
Ya Abida ta shigo ta Duba Amina kafin su wuce Hadda ya zeena ma bataje ba su Sa"adatu ne suka tafi dasu ya Akilu sai Umaimatu,Misalin karfe Tara na Safe Hajiya Babba da Yaya da Mamanmu da Anty Shamsiya matar ya Jafar suka tafi asibitin da aka kwantar da Aba domin su Dubasa shi kowa kagani rai da zuciya ba Dadi.
Wani private Hoptal ne Daki na Musamman Aba ke ciki Vip.
Suna shiga Baba Mallam kadai suka Iske awajensa Aba din yana ta barci su Mamanmu suka gaisheshi Cikin girmamawa ya amsa yana Fadin"Mungodema Allah..Ya jikin uwar tawa?Nace shamsu yazo da Mallam ya"u sun zo kuwa..?
Wannan karon Hajiya ce tace"Eh har ya gyaramata ya bada mgani an shafa mata tasha mgani koda muka fito ta samu barci..
Ya shi Sa"idun..Ya farka kuwa..?
Baba Mallam yace"Eh ya farka da Safe jikinsa da sauki sosai bai dade da komawa barci ba koda Nasir ya bar nan muna ta Hira dashi..!
Gabadaya suka amsa da Alhamdulillah mai sunan Mallam ne Dake bayan Shamsiya ya fara kuka Mallam yace Hajiya ta karbo shi ,ta kwatoshi daga baya Ta mikama Hajiya ita kuma ta mikoma Mallam ya saka Hannu Biyu ya karbesa yayi wayau Yayi girma kansa ya dafa yana Tofamai addu"a sai da ya gama sannan yace"Ciwon kunnin nasa fa.?
Kan Anty Shamsiya na kasa tace''Yayi sauki..yadaina kukan tun jiya daddare..!
Baba Mallam ya gyada kai yana Fadin"In muka koma gida zan bama Jafar wani mgani ku rika Digamai Daga Saudiya nazo dashi..!
Kai ta gyada kafin tace"Jiyan ma Da daddaren wajen Mamanmu yacemin zai zo ya karbo masa wani mgani shine baidawo ba sai waya naji yana Fadamin yana Tare da Aba a asibiti..!
Baba Mallam yace"Wlh kuwa..Ammh ai da sauki yana ta cewa ma a sallameshi ya koma gida..!
Mamanmu tace"Daman ai baisan zaman asibiti..!
Hajiya tace"Sai hakuri ya bari ko zuwa gobe ne in ya kara jin Sauki..!
Suna cikin mganar ne Aba ya Farka Daga barcin daya kwasheshi suka fara Rige rigen mai sannu Mamanmu tana kokarin Taremai Filo Sai Yaya ta rigata sai ta sakarmata Ya jingina da Filo sannan ya tashi yana amsa gaisuwansu Lokaci Daya yana Binsu da kallo cikin Tsausayinsa Yaya tace"Ga Ferfesun kayan ciki nayo maka..In zubo maka zakaci..?
Mirmishi ya saki kafin yace"Zubomin Hadiza..Nagode Allah yayi miki albarka..!
Akunyace ta amsa ta Duka tana Zubamai Cikin Filet din da tazo dashi,Kadan yace ta zubamai ta mikamai ya karba Baba Mallan na Fadin"Ashe girkinta kake jira shiyasa bayan Ruwan Tea kaki cin komai..Duka abincin da matan yaran nan sukayi bai taba komai ba Hajiya..!
Dariya tayi tana Fadin"Sa'idu ne fa..Tun farkon auransu Girkin Hadiza yasa ya faramin yajin cin abinci kaga Tunda yayimin yaji nasan Hadiza ta Curi Tuta..har yayi aure adakina Sa"idu ke cin abinci Mallam har haushi yake ji na kwace masa yaro..
Gabadayansu Dariya sukayi Saboda yanayin yadda sukayi mganar Aba ma sai da ya Murmusa bai ce komai ba yana kallon Yaya basu sani bane aduniya ita kadai ce macen da yake Fatan Har aljannah ta zama matarsa Saboda kyawawan Hallayarta Tunda suka zama miji da mata shekaru aruaru bai taba ganin Ranar data Daga Muryansa sama da tashi ba..Yana kokarin Boyewa ne Sai Hadiza matsayinta Daga Allah ne ko ya Boye Kaunarta bazai taba Boyuwa ba Tana da wani irin girma acikim Idonsa da Rayuwarsa da ba wanda ya sani ita yake kallo yana jin zuciyarsa na Sauka Duk da cikin Halin Dayake ciki ita kuma kanta na kasa tana da kunya ballatana gaban Hajiya da Baba Mallam..!
Yaci kuma Ferfesun duka ya Cinye ya Dora da kayan marmari sai gashi garas dashi sai dai kallo Daya zakayimai kasan yana cikin Damuwa,Ya Jafar daman bai shigo ba sai gasu shi da Nasir sun shigo suka kara gaida Aba daganan su Mamanmu sukayi sallama dasu Jafar zai maidasu Gabda zasu fita Hajiya ta dawo wajen Baba Mallam daya mikama Jafar takwaransa yana jadaddamai yazo zai bashi wani mgani Jafar din ya Juya kenan Hajiya ta kalli Baba Mallam tana Fadin"Mallam naji bakace komai ba Har yanzu..?
Kallonta yayi yana Mirmishi kafin yace"Nazir ya Kirani da Safan nan yace yana ta kiran wayarki baki Dauka ba..Sai daga baya Abida ta Daga kiran tace baki nan kina gidam Sa"idun..!
Kauda mganar yayi ta sani tace"Ina na sani..Gida na bar wayar..Suna Lafiya ko..?
Yace"Lafiya lau..Shehin ne dai ba Lafiya yacemin kwanansu Biyu asibiti Ciwon ciki ammh sun dawo gida shine nake fadamai nima ina asibiti ga yayansu Sa"idu ba Lafiya..!
Hajiya tace"Assh..Allah ya Sauwake in na koma na natsu zam kirasa..!
Kai ya gyada mata bai ce komai ba,sai ta kalli Aba da hankalinsa baya kansu ya Lula Tunanin Halin da Amina ta Jefasa Cikin Damuwa Hajiya tace"Sa"aidu wannan Tunanin babu Riba cikinta..Ka kwantar da Hankalinka ba wata mtsala insha Allahu..!
Aba ya sauke Numfashi kafim yace"Hajiya in ban aurar da Amina yanzu ba..Watarana Jidalinta zai iya ajalina..Kinga Hadiza bata mgana ko..?
Na rantse tafini jin Dacin Amina tafini Sanin Ciwonta Domin itace uwa gareta ina Tsoron yadda take shanye abubuwa watarana Amina ta Dauko abunda zai yi sanadiyar zuciyarmu ta Buga Dukkanmu mu fadi mu mutu..!
Hajiya ta kama baki tana Fadin"Assh..Haba Sa"idu bama zai taba Faruwa ba..!
Tari ya farayi sai kuma jikinsa ya fara rawa Da Sauri Hajiya tace"Mallam yace komai zai daidaita ko ba Haka ba..?
Tafada tana kallon Mallam din wanda ke kallonsu bai ce komai ba Rawanin kansa ya gyara kafin yace"Insha Allahu..Zan Daura ma Amina aure in an idar da Sallar azahar da yardan Allah..!
Baba Sa"idu da Hajiya suka kallesa da mamaki Aba ya rausayar dakai yana Fadin"Ina fata da bada wannan Lalattacen yaron da suka gama Lalacewa bane ko..?
Baba Mallam ya yi mirmishin su na manya kafin yace"Bashi bane Sa"idu..!
Hajiya tace"To waye ne Mallam..?
Sai da ya kara Murmusawa kafin yace"Da wanda Allah ya kaddara..Shine dai wanda Allah daman ya Rubuta Mijinta ne dashi za"ayi..!
Hajiya daman tasan bazai fada ba Tunda bai iya fadamata ba kuma bai Fadama Sa"idu ba to Tattabata bazai Taba Fadama kowa ba..!
Aba ne yace"Kada ka Tursasama Mutumin Kirki sai ya aureta Mallam..Ka hadata da irinta sannan ka Sanar da kowaye halinta Baba..Kuma ina so aje a gwada Amina kada yazo wajen Lalacewarta ta Samo wata cuta..!
"SA"IDU..!
Baba Mallam ya katsesa Cikin Tsawa da Bacin rai kafin yace"Kul na Sakejin wannan mganar daga bakin ka..ina da yakinin Har Abada acikin zuru"ata baza"a samu bara Gurbi ba...Duk da Allah na Jarrabatan bayinsa ta kowani Fanni Ammh ta wannan gabar ban yarda ba..Amina bazata taba Rusa Tarbiyarmu ba Sa"idu ba abunda zan ce ma wanda zai aureta illah ya Rikemin ita Amana kuma in Cucuta koda abayan Idanmu ne Ban yafe MASA BA..!
cikin kaushinsa ya karishe mganar da ta ja Hankalin Aba da Hajiya suka kalli juna bai kuma basu zarafin mgana ba ya kalli Hajiya yana Fadin"Kinsan suna jiran ki ko?
Kai ta gyada kafin tace"Shikenan Allah ya kara afuwa..!
Har ta juya zata tafi Baba Mallam ya Kira sunanta ta juyo Cikin bacin ran da bai barsa ba yace"Ki fadama su Balaraba kada wata cikinsu ta kira yaran nan dake gidan auransu tace zata Daga musu hankali ko Husai ban yarda afadamata ba..!bana so a adaga musu Hankali..!
Hajiya tace"Insha Allahu ba wacce zata ji..!
Kai ya gyadaa mata ta juya ta cigaba da Tafiya har takai kofa zata fita ya Kira sunanta wannan karon a Taushashe ta juyo tana Fadin"Mallam..!
Kai Tsaye yace"Umaru ya kiraki kuwa..?
Cikin mamaki tace"A"a rabona dashi Tun shekaranjiya da safe..! lafiya kuwa.?
Mirmishi yayi kafin yace"Bakomai..Allah ya kaiku gida Lafiya sai na dawo.!
Hajiya ta jinjina kai kafin ta Fice ya bita da kallo Daman ai yasan bazai taba Kiranta ba Shi ya Haifi Umar ammh yana Daraja kyakyawan Dabi"ansa..!
Aba ne yace cikin Raunin Murya"Kayi hakuri Baba..!
Hannu ya dagamai kafin yace"Nace ne kada na sake jin irin mganar makamancin wannan abakin ka..Ba hakuri nace ka bani ba..!
Cikin Sauri Aba yace"Insha Allahu..
Sai alokacin Baba Mallam ya saki Fuska yana Fadin"Allah yayi maka albarka kaida zuru"arka Sa"idu.Har Abada ban taba Nadamar samunka Cikin zuru"ata ba..Ka warke da wuri ban shirya rasa Da"a na farko ba..!
Ya karishe Cikin barkwamci Da sai da Aba ya Murmusa Lokaci Daya Hawaye suka cika kwarmin idonsa yake Fadin"Nagode Baba..Nagode Ban taba jin kai ba Uba kake gareni ba..Ina Alfahari dakai..!
Baba Mallan yayi wani kayattacen Mirmishi kafin yace"Nima ina Matukar alfahari dakai Sa"idu..!
*******
Tana cikin Tiolet din Bedroom dinta taji Ringing din wayarta Allah yasa ta Gama wankan ta Dauro babban zaninta ta fito wayar tana kan Mirror dinta ne Jikinta yana digan ruwa takai Hannunta saman wayar wanda taga yana kiran nata ne yasa taji gabanta ya Fadi..!
"MALLAM..!
haka kurum mallam awannan Lokacin bazai kirata ba,Dazu Shamsu ke fadin yana asibiti wajen Sa"idu Har wayar ta kusa yankewa bata Daga ba sai Daga baya ta Daga kiran tana Fadin"Assalamu Alaikum Mallam..!
Dagachan Haraban asibitin Baba Mallam yace"Marliya kina ina ne..?
Cikin mamakinsa tace"Ina gida mana Mallam..!
Kai Tsaye yace"Marliya abunda ya faru jiya gidan Sa"idu kuskure ne da Rashin Fahimta ko..?
Cikin Mamakinsa da Tunanin inda ya Dosa tace"Hakane..!
Cikim Dattakonsa yace"To mu barsa ahaka..Kada na sake naji mganar nan ta fita..In har najita a waje Nasan kece..Bana son surutu da mgana Hajiya kinsani bata da wannan Halin Saboda haka ki kiyaye..!
Anty Amarya taji ta Muzanta Ranta ya baci wato Hajiya ba ruwanta itace mai Surutu ko lalle ne Mallan dinnan.!
Danne bacin ranta tayi tana Fadin"Ah..Wlh ban fadama kowa ba Mallam..yanzu dai nake shirin shiryawa na shiga gidan na Duba Amina ya jikin Sa"adun..?
Fata ya samu Sauki..!
Cikin son Dakile mganar yace"Yaji Sauki..Kada ki fita ko"ina nima ganinan zuwa. !
Bai jira cewarta ba ya Datse kiran yana wani nazari yasanta da kananun mgana sarai shiyasa ya taka mata Burgi in ba haka ba,kafin wani Lokaci ta gama Fesama ya"yanta su kuma su fara yawo dashi mgana har ta fita wacce bata da wani amfani..
Ita kuwa Anty Amarya Sororo tayi da waya a Hannunta mamaki bakin ciki da Kishi sun Turniketa wayar ta Dangwar nan saman gado tana Fadin"Aikin banza..Abunda kake son ka Rufe mallan bazai taba Rufuwa ba..Ko ba"a bakina ba Lalacewar Amina sai ya fita Duniya..!
Abunda bai sani ba ta Fadama ya"yanta Sa'adatu da Jidda da Sadiya Jidda ce kawai bata Dauki mganar ba Ammh Sa"adatu har tana Fadin daman idanuwan Amina na rashin gaskiya ne sannan abakinta Anty Amarya tasan Amina na karancen karancen Littafan hausa Sadiya dai da Uwar ta fadamata batace komai ba Domin bata cika Hayaniya ba.
Wayar Sakina tayi ta nema ta Tsegunta mata bata sameta ba Shiyasa da Tuni Labari ya isa Saudiya Arabia..!
Tana shiryawa tana Tsaki ita kadai ta rasa me Hajiya Babba tafi su da Mallam yake Fifitata akansu ta manta tun Tale tale Take tare da Mallam din kwafa tayi afili tace"Daga ita har Sa"idun duk sai nayi mganinsu Algumgumai duk su ke zuga Mallam..Da basu da Tuni nice Tauraruwa awajensa da gidan gabadaya..!
Abunda bata sani ba,ba irin Mallan ake ma haka ba ko ta manta Malami ne wanda bai zauna ba,kariyar Allah Tana Tare dashi kuma ilkonsa bazai bari acutar da bawansa ba..!
Baba Mallam na asibiti kafin ya baro ya Kira ya Jafar yace ya siyamai Dabono da Goro mai yawa zai yi amfani dashi bai damu ba sanin kila Mallam din zai yi wani abu dashi sai dai abu daya ya bashi mamaki Dayace su samu sallar azahar anan masallacin gida shima gashinan zuwa..!
Koda ya tafi Aba na barci Nurse tazo tamai allura kila tana saka barci ne shi kuma sai bai tashesa ba Idi Direba ya Kira yazo ya Daukesa zuwa gida Kai Tsaye Shashensa ya wuce domin ya Shirya Tunda azahar din ta kusa Shi kadai kawai yake jin karfin Gwiwa da alhafarin wani abu akaron Farko zai cika wani Burin Daya Dade acikin ransa bai Mutu ba kuma da Ransa..!
Wanka yayi ya shirya Cikin Shadda Fara harda babban Riga dataji aikin Hannu ya Dora rawaninsa sai ya Fito Tar dashi Farin gemunsa na kyalli yana tashin kamshinsa kamar koda yaushe adaidai Lokacin ya samu wayar Jafar yana Fadamai ya siyo abunda yace asiya din Baba Mallan yace yana cikin gida gashinan Fitowa..!
Bai Fadama kowa komai ba acikin gida yayi alwalansa ya fito Mutane basu wani mamaki ba in yana gari dashi ake yin sallah duk da akwai Limamin masallacin Mallam Muhammad Dayyab in Baba Mallam bai nna shi ke kula da masallacin har ya jafar da Ya Nasir suna bada Sallah da Mangariba haka ko isha"i Mallam din ke sakasu saboda gaba in watarana ya fadi ya Mutu ace akwai masu bin bayansa Koda Umar da Nazir basa kusa akwai Jafar da Nasir manyan dake bin bayansu..!
Kowa ya zata Baba Mallam din zai bada sallah sai dai ana shiga masallacin yace Mallam Muhammad yajasu Sallar,to sai mamakin bai yi yawa Tunda yana haka sau tari dadama.
Mallam Muhammad ya bada salla ana Idarwa Baba Mallam dake sahun gaba ya matsa gabansa sukayi kuskus kafin Mallam Muhammad din ya sanar da Daurin aure da za"a Daura shi yanzu Baba Mallam sai annuri yake yi Ya Jafar da Nasir Dake layi na Biyu ya yafito da Hannu Sai Shamsu Dake gefe duk suka taso suka kariso gabansa gaban Liman Mallan Muhammad..!
Suna karisowa yace su zazzauna suka zauna nan gefensa Cikin Dattakonsa yace"Jafaru dauko sakon nan..!
Ba Musu ya mike ya fita daman acikin Motarsa ya bar Huhun goron da Ledan Dabibon yaje ya Dauko ya kawo ya Mikama Mallam ya karba ya Mikama Mallam Muhammad yana Fadin"Araba shi Liman..araba ma Jama"a..!
Ba Musu Limam ya bama Ladani Umarnin ya rabama kowa Dabino da Goronsa kamar yadda aka saba Cikin Kankanin Lokaci yabi layi layi ya bama kowa,Mutane basu yi mamaki ba sanin Daman amasallacin bazanga koda yaushe cikin kawo Daurin aure akayi shiyasa ba wanda ya damu ammh su Ya Jafar sun Tsargu ballema da suka ga yadda Baba Mallam ke ta Annushuwa kuma yana gaba gaba kan komai ko auransu Zulaihat bashi ya bada ba su ya Danmallam ne suka Zama Waliyansu..!
Basu gama mamaki ba sai da Liman yace"Allah ya gafartama Mallam an gama Raba Goron da Dabinon har yayi saura ma..!
Baba Mallam ya Jinjina kai kafin ya karkace ya zaro Bandir din kudi Sabbi yan Dubu Dubu ya ijiye gaban Liman Cikin Dattakonsa yace"Walicci zakamin Mallam Muhammad..?
Cikin mamaki yace"Waliccin wane kuma Allah gafarta mallam..?
Baba Mallan sai da ya kara Fara"ar Fuskarsa kafin yace"Waliccin Umarun Faruku zakamin aure zan kara masa ayau din nan acikin wannan masallacin..!
Liman yace"To..To..Masha Allah ai babu Laifi Allah gafartama Mallam sai Waliyan ita yarinyan su matso afara siga..!
Baba Mallam ya Murmusa kafin yace"Nine Waliyan Amarya..Ga Sauran yan"uwanta nan..!
Ya nuna su ya jafar da suke zaune mamakin kalaman Baba Mallam ya cika su.
Cikin karin mamaki Liman yace"Au kace Abun duk na gida ne..To masha Allahu..Ba bu laifi sai mu fara gabatar da siga ya sunan Amaryan..?
Sai da Baba Mallam ya gyara zama kafin yace"Sunanta AMINA..AMINA SA"IDU..!
Jafar da Nasir suka kalli juna kafin su juya suna kallon Baba Mallam Shamsu kuwa Kunni ya saki yana jin abun kamar almara..!
Liman ya washe baki yana Fadin"To..To..Masha Allahu wannan abu yayi kyau..Allah yasa a kulla alheri..!
Zamu fara gabatar da siga..Ladan ya Ciremana Lasifika..!
Da Sauri Baba Mallan yace"A"a abarta Liman..!
Liman cikin mamaki yace"Dokarka ce Allah gafarta Mallam ba"a Daura kowani aure cikin Lasifika..!
Baba Mallam cikin Annuri yace"Na yau kadai na Sauke Dokar liman..So nake naji Sautin Tattabatuwar auran Uwata da Umaru so nake na ji Sosai acikin kunnuwana Liman..!
Liman bai yi gaddama yace abar Lasifika,cikin Abunda bai fi mintina goma sha Biyar ba aka gabatar da siga aka kuma Tabbatar da Daurin auran AMINATU SA"IDU GUSAI da angonta Mijinta UMAR YUNUS ABDURRAHAMAN BAZANGA akan Sadaki Naira Dubu Dari Cif..!
Adaidai Sanda Muryan Ladan ta Karade Lasifikan yana kara Jaddada Daurin auran Amina da Umar din Akan Sadakin da uban Amarya kuma Uban ango ya Biya Mallam Yunus Abdurrahaman bazanga..!
Awannan gabar Alkawarin Allah ne ya cika..!
Zanen kaddara ya tabbata..!
Auran ya Dauru.!
"fallasa wasu sirruka ne..!
Dalilin wannan auran za"a rasa rai..!
Fuskokin wasu amintattu zata bayyana..!
Zuciyoyin wadanda basu taba Tsammani ba zata girgiza..!
Abunda basu taba zato ba ya faru alokacin da basu shiryama hakan ba..!
Wasu sun makara..Saboda Alkalamin ya riga daya Bushe ko sunzo kafin Lokacin Allah bazai sauya wannan kaddaran ba SABODA RUBUTTACIYA CE..!
Daurin auran daya Faru a kunnuwan mutane Dadama da suka cika da Dimbin mamaki wadanda da basu yarda ba Sa"idu ba dan Mallam bane yau suka kara yarda da mganar wasu Mutanen yadda Baba Mallan ke Hannu da Mutane kawai zaka Fahimci yana cikin Farimcikin da bai Taba tsintar kansa aciki ba shi ya Hana Jafar ko Nasir cewa wani abu suma sai sukabi ayarin yan gaisawa da Mutane suna faman amsa Fatan Alherai daga kowani bangare..!
Baba Mallam Dakyar ya samu ya Fito daga masallaci su Jafar ya kallah yana Fadin"Ku scigaba gda amsan Fatan Alheri jama"a bari nayi wata waya..!
Daga haka yayi nesa da Masallacin ya Fiddo wayarsa ya Kira Danmallam..!
Tana gabda Katsewa ya Daga Kiran Cikin Mutuwar Jikin da Baba Mallam ya Saukarmai Tun Safe daya Kirasa yana Fadamai zai aura masa Kazamar yarinyar nan..!
Cikin Farimciki Baba Mallam yace"Umaru..!
Dagachan bangaram Muryansa a shake yace"Na"am Baba..!
Bai jira cewarsa ba ko yanayinsa ba yace"Yanzu nan aka Daura auranka Da Uwata..Ayanzu din nan AMINA ta zama Amanarka Umaru..daidai da Rana Daya in kaci Amanarta ko ka Dannen Hakkinta Allah na kallonka sanna amatsayina na Mahaifinka ban YAFE maka ba Umar daidai da Rana Daya in ka Zalunci AMINA.!
ya karishe Fada Cikin kaushin Murya
Gabadaya sai yaji kamar Duniyar na Juyawa dashi wannan shine gaba kura baya Damisa..!
Baba Mallam bai Damu da amsar ba ya Cigaba da Fadin"Ina Alfahari dakai..Yau ka cikamin Burina Umar..albarkata da addu"an Allah ya baka Zuru"ata tagari bazata yanke Daga bakina ba..Ina Rokon Allah yasa Amina ce Sillar Arzikinka da Daukanka..Ina ji ajikina Uwata ce Farincikinka watarana ko bana Raye alokacin nasan zaka Tuna dani Umar..!
Jin Mallam kawai yake ta ina wannan kwailar yarinya zata zama Farincikinsa watarana..?
An dai hadasa da aiki Yarinya kazama ga rashin Natsuwa da Taurin kai da rashin ji yana zaman zamansa Mallan ya Debo masa aiki Sai dai shi Yaro ne mai Biyayya har abada baya Fatan Ranar da zai Sabama Iyayansa..!
Shiyasa Cikin karfin hali yace"Nagode Baba..Allah ya kara girma..Insha Allahu zaka sameni mai biyayya..!
Baba Mallam cikin jin dadi yace"Nasani..nasan bazaka watsamin kasa a ido ba..Allah yayi maka albarka..!
Ya amsa da Ameen Daganan sukayi sallama bayan ya tambayi jikin Aba yace da Sauki sannan suka rabu da juna da cewar shi Danmallan din zai kira wayar Baba Sa"idun Baba mallam yace ya Kirasa Jafar ya Tahomai da wayarsa da Safe..!
Abunda kowa bai sani ba Tun Da Asuban nan da Danmallam ya Kira Baba Mallam yaji aransa wannan mafitan ne Allah ya nuna masa.
Bai yi shawara da kowa ba kafin ya tafi asibiti wajen Aba ya kirasa suka Tattauna Komai Daga farko har karshe sai da ya Fadamai duk abunda ya Faru kwanaki da na jiya Daddare da kalaman Baba Sa"idu da Rokonsa garesa ya kuma Roki Danmallam Daya auri Amina ba domin Umarni ba sai domin daman Yana da Burin Hada Dansa ko yarsa da Ahalin Sa"idu..!
Umar bai iya cewa A"a ba..Mallam ya wuce gaddama garesa Cikin wani yanayi ya amsa masa da cewa Ya amince wannan kalaman nasa su suka Tabbatar da Kaddaransa da Amina Kaddaran zama amtsayin miji da Mata..!
****
Cikin wadanda Daurin Auran Amina da Danmallam ya shiga kunnensu yaya na ciki ita da Hajiya da Mamanmu kai kaf wadanda ke gidan sun ji hadda Amina uwar gayyar Domin tatashi alokacin Hamida ta taimaka mata tayi wanka tayi alwala tana Rama Salolinta ta idar kenan tana Zaune Saman Darduma alokacin ma Tunanin Aminu take da Tunanin Halin Dayake ciki.
Kamar mafarki Taji muryan Ladanin nan yana bayyana sunanta da na Ya Danmallam amtsayin mijinta da aka Daurama taaure yanzu nan.
Ta Rude kanta kamar ya Kulle domin bata gane komai ba Sama sama take jin Muryan Mamanmu Daga Tsakar gida inda suka zauna tun bayan Dawowarsu daga asibitu tana Fadin"Kunji Abunda naji kuwa..?
Kamar Naji ana Fadin an Daura ma Amina aure da Danmallam..ku Saurara,kuji..!
Suma sun ji din sai dai sun kara kasa,kunni Saboda su gasgata,Hajiya kuwa tun jinta na Farko ta tabbatar da Duk abunda taji gaskiya ne..Mallan ne fa tasani Daman shurunsa Zai iya zama koma menene..!
To duk abunda akeyi a masallacin kamar agidansu akeyi saboda lasifukun masallacin akwai kara sosai,Radau suka sake jin wannan al"amarin Daya basu matukar mamaki Yaya Dake Dakinta Tana zaune ne sai da ta mike yayinda ya Zeena ta kwalalo ido tana Fadin"Wlh Mamanmu da gaske ne..Amina ce..!
Hamida da Hanne suka kalli juna Cikin mamaki kafin Hanne ta Rumtuma Dakinsu Hamida tana Fadin"Amina..Amiaa..Kin ji an Daura miki aure da ya Danmallam yanzu a masallaci..?
Kallonta Amina takeyi da manyan Idanuwanta da suka Zama wani irin Cikin wani yanayi tace"Naji..Naji Hanne..ammh bangane komai ba wani Danmallam din..?
Ni Umar naji an ce fa..?
Tafada cikin wani yanayi Hamida ce da ta shigo cikin wani yanayi tace"Shine Umar din Amina..Yayansu Hanne..Mijin Anty Sakina da Anty Sarood wanda ke zaune a madina..!
Cak Numfashi Amina ya Tsaya ta Fara Kokuwa dashi bata samu zarafin mgana ba taji muryan Yaya tana Fadin"Hajiya kinsani..?meyasa kikabari Mallan yayi haka..?
Amina bata dace da kamilalle irin Umar ba..Bata dace dashi ba sam..bai kamata kuyi haka ba..!
Sai kuka,acikin ranta kuma wani Sasaauci taji Tana ganin kamar Addu"anta na Shekaru ne Allah ya amsa sai dai Tana jin Tsoro tana jin tsoron An Hada Kamili kamar Umar da Amina kada ta zama mai sonkai kada taso yarta Shiyasa tayi mgana..!
Hajiya kuwa tana zaune sai Mirmishi take saki Annushuwa ta bayyana acikin ranta kafin tace"Sun Dace Hadiza..Duk abunda kikaga Mallam ya yanke mai kyau ne..Naki addu"a ne Allah yasa Alheri muka kulla..Allah yasa su aminan juna ne..!
Da karfi Mamanmu ta amsa da Ameen tana sharan kwallah tace"Yaya Amina fa y'arki ce..Tayaya zaki rika Fadin mgana mara kyau akanta ya zataji in taji abunda kike fada!
Tana mgana tana sharan kwallah..!
Amina Daga cikin Dakinsu Hawaye suka kwanyomata tace"Naji..Naji Mamanmu naji..Gaskiya ta Fada ban dace ba..Ban dace ba..!
Batasan Lokacin da wani kuka ya kwace mata ba Lokaci Daya tana Fadin"Wlh bansani ba..Bansan wannan kaddaran ke Bibiyata ba da Ban fara son ka ba Aminu..Wlh bansani ba..!
Taausayinta ya kama Hanne da Hamida suka karisa gareta suka Rumgumeta suma sai kuka Riris kamar anyi mutuwa..!
Zuwa Lokacin Wannan Daurin auran mai Cike da Bazata da mamaki ya kama Yaduwa a gidajen nan guda Biyu Anty Amarya sai da tayi suman Wucin gadi bata kara gasgata mganar ba sai Da shamsu ya shigo ya kara Tabbatar musu agabansu akayi ita da Hajiya Nasara,Haj.uwa na shashenta bata fito ba Duk da tasan abunda ya Faru domin taji..!
Alokacin da Kowacce take kiran ya"yanta masu aure na nesa tana Fada musu Anty Amarya bata cikin natsuwa ballatana ta iya kiran wani ta Fadamai awannan gabar abubuwan sun bala'in shammatanta
Abunda kowa bai sani ba alokacin Baba Mallam na cikin Falomsa na Shashensa tare da baki Daga Yola..!
Yana gama wayar nan da Umar Motoci biyu suka gyara parking kofar Gidansu kuma wajensa suka zo ya karbesu hannu Biyu ya kuma Saukesu afalonsa zuwa Lokacin mutane sun fara watsewa..!
Jikinsa yayi sanyi da yaji kamar yayi gaggawa AMINU ne saurayin Amina da iyayansa sun zo neman auran Amina da kuma ban Hakurin abubuwan da suka faru..
Ashe ashe jiya da dadaddre Aminu Daga Gumel yola ya wuce Allah ne ya kaisa Lafiya yaje gaban Baba Alhaji ya Fadamai komai yana kuka da Rokon suje Gumel suba ma iyayan Amina Hakuri su bashi auranta sai dai abunda bai sani ba sun makara..!
Mallam yaga Dattakon Alhaji Baba yaji matukar kunya alokacin Dayake Fadamasu Amina ta haramta ga Aminu yanzu taron chan na waje na Daurin auranta ne..!
Yana ganin wanda aka kira da Aminu ya tashi ya fita yana Rangaji hawaye Sunaa zuba Daga idonsa.
Sai yaji jikinsa yayi sanyi yaa ji aransa kodai yayi gaggaawa ne..?
Aminu Dakyar ya kai kansa Bakin Motocinsu da suka zo dashi Wayarsa ya Dauko biyu biyu yake gani da haka ya Kira Nenne..!
Tana ganin kiransa gabanta ya Fadi Daman kiran nasa take jira tana Dauka tace"Aminu ya ake ciki..?
Cikin karyewar murya yace"Na rasata Nenne..Nasara MEENATA..
Na makara Nenne an Daura mata aure da wani bani ba..!
Yana gama fadin haka ya Datse kiran ya Sulale nan kasa Dirshen ya Hada kansa da gwiwa yana kuka kukan Rabuwa da masoyi Rabuwa ta Har Abada..!
Nenne Dake cikin gidansu na Yola gidan Alhaji Baba yayyinta da kannenta sun zagayeta suna tambayata Lafiya Cikin fitar Hawaye ta kalli Mahaifiyarsu tace"Hajjo ya rasata..Aminu ya rasa Amina....an daura mata aure da wani kafin su isa..!
Gabadaya suka hada baki wajen fadin"Innalillahi wani"inna ilaihirraju'un..!
Sun sani Aminu zai samu matsala Kaddaran ta riga fata duk wani ahalin gidannan yasan yadda Aminu yake kuka yana rokon Alhaji Baba yaje yane masa auran Amina..
Ya Aminu zai yi..?
Bakin Alkali ya riga ya bushe..!
Zanen kaddaransa bata Amina bace..Kila na watace chan Dabam
Inda ya sani..Dama..Dama ace bai Hadu da Amina ba..Dama ace komai daya faru mafarki ne..!
*Janafty*
*TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*
_Wannan shafin jinjina ce da godiya gareku masoyana a duk inda kuke masu Sharhi da masu fatan Alheri musamman yan Group dina na TA FITA ZAKKA COMMENTS SECTION da ku yan JANAF NOVELLA Tare da duka sauran gidajen marubuta da ake yin sharhin wannan Littafin nagani kuma na yaba naji dadi Allah ya bar zumunci gaisuwa ta musamman zuwa gare ku yan wattppdians kuma kuna kokari sosai nagode Allah ya bar zumunci.._
*🅿️22*
Zuwa dare duk wanda ya kamata yaji Labarin Auran Amina da Danmallam yaji,kowa mamaki kamasa yake yi in yaji Domin agabadaya da Dubawa ta mahanga ta Dan adam Amina bata Dace da Rayuwar Danmallam ba sai dai Ina Allah shi ke Tsara dukkan Lamuran sannan kuma ya zartar ya riga ya Dora alkalamin kuma ya Bushe akan Amina da Umarun dan bazanga..!
Aba yana asibiti ya jafar ya kirasa ya sanar dashi maimakon ya shiga bakinciki da takaici kamar yadda ransa ya darsu da Tunanin Baba Mallan yayi gaggawa domin Amina bata dace da Rayuwa irin ta kamili Natsattse Irin danmallam ba sai kuma sai yaji kamar zuciyarsa tayi son kai yaga kamar ita diyar tasa irin Mijin Daya dace da ita kenan baisan Lokacin Daya Daidaici gabas ba ya Fadi yayi sujudul Shukur ga Allah ya Dago yana Hawayen Farincikin da bai taba Zaton Daga jiya zuwa Dazu zai iya Fuskarta haka ba yadai ce zai aurar da Amina ammh acikin ransa yanajin kamar bai kyautu ba yana ji kamar wani al"amari zai faru ashe wannan al"amarin ne mai Daraja tuni kimar Baba Mallam ta kara Hauhawa acikin Zuciyarsa ya tabbata ko mahaifinsa Aminu gusai na Raye iyakar kaunar da zai bayyana masa kenan..!
Bangaran Amina kuma tun Lokacin Dataji labari data fara kukan nan bata Daina ba,Har Hajiya Babba da mamanmu sai da suka taru akanta suna ta bata baki bayan sun Fatattaki su Hamida Dake tayata kuka,Agabansu sai tayi kamar taji Duka Nasihansu ta daina Abu Daya ke mata yawo Aminu ta kasa gane wannan wata irin kaddarace da zata Raba ta da masoyinta ta kaita inda Har Abada baza"a taba sonta ba..Wannan wata irin kaddarace haka take ta Tambayan kanta..!
Hajiya Babba na tafiya Amina ta cigaba da gunjin kukanta har ta su Hamida sun daina sun koma suna Lallashinta,Ammh taki daina kuka Mamanmu kuma gajiya tayi ta rabu da ita ya Zeena ce ke kitchen tana samar da abunda zasu ci da wanda za"a kaima Aba Dake chan Asibiti suna Tunanin yasan abunda ke faruwa Tunda Baba Mallam baya Zartar da wani abu sai da saninsa shi da Hajiya Babba basu san wannan karon duka bai nemesu ba shi kadai dagashi sai Allah Daya barma Zabi bayaso yayi mgana da wani ko wata su ce ba haka ba shi yasa wannan karon ko Hajiya babba batasan me ya yanke ba Sai Daga baya..!
Tun Mganar da Yaya tayi ma Hajiya Babba ta koma Daki ko motsinta ba wanda ya sake ji,Sai Lokacin da iskancin kukan Amina ya isheta sannan ta fito ba wanda yaji Shigowarta illah Dundun data Dirkama Amina agadon bayanta wacce ke zaune kasa ta Hade kai da Gwiwa tana gunjin kuka alwala ta Dauro Dakyar shima sai da Hanne da Hamida sukayi ta magiya shine ita batayi sallar ba ta koma tana kuka..!
Dukkansu sai karan Dukan sukaji Amina ta bankare baya wannan Hannu shi kadai ne bata saba dashi ba Hannun Yaya ne..!
Cikin bacin rai ta kalli Amina tana Fadin"Ai bake bace da kuka ba Amina..Umaru ne da kuka domin shi aka Gurbanta ma Rayuwa..Mutum kamili kamarsa an Hadasa da wacce bata Dace dashi ba Amina kamar ki ace kin san Namiji..?Daman nasan wannan Firiritan nan naki watarana sai yakai ga haka har kina mana wani kukan banza to wlh ki kama bakin ki ko na sake Dana miki Dukan da sai kin Raina kanki Sakarya wawiya mara Tunani kawai..!
Ta karishe Fada Cikin Huci Amina na kuka tana Fadin"Wlh bana bin Maza..Ni ba yar iska bace..!
Yaya tace"Shi Jafarun zai miki karya ne..?yaron da yace ya ganki Rumgume dashi Ubanki ne shi..?wlh in bakin ki bai Mutu ba,zaki sha wahala ke baki ji kunya da Tsausayin kanki ba..?Mahaifnki nachan kwance asibiti taa Dalilinki Tir da Halinki Amina Tir wlh..!
Tafada Tana nuna ta da Hannu Cikin wani yanayi Hanne ce ta Dukar dakai Cikin wani yanayi tana Fadin"Don Allah yaya kiyi hakuri..Nasan Wacece Amina sai dai in kuskure akayi wlh bazata aikata abunda akace ba..!
Yaya bata samu bakin mgana ba Mamanmu Data Daga Labule tun dazu Tana jin yaya tace"Hanne ku kyalesu..Duk abunda zasu fada sun Dade basu fada ba..Abu Daya na sani Amina ba Haka take ba..Amina bazata Watsar da Tarbiyanta ba..Akwai abunda ba Daidai ba..!
Yaya tayi mirmishin Takaici kafin ta Juyo tana kallon Mamanmu Cikin Sanyin Muryanta tace"Yaushe ne Ranar da Amina zatayi kuskure ki nuna mata tayi ba Daidai ba..?
Yaushe ne Ranar da zaki bi bayam gaskiya ba bayan Amina ba..?
Mamanmu tace"Sai Ranar da na Tabbatar da gaskiyan kuke fada yaya..Ammh ayanzu har gaban Abada bazan bar Tsagin Amina ba..Amina Diyatace da nake mata soyayyar da ko ya'yan dana Haifa da cikina ban musu shi ba,Har abada bazan Daina Fadin kunyi kuskure Amina ba haka take ba..!
Yaya Batace komai ba kawai ta girgiza ta raba ta gefen mamanmu ta fice Mamanmu ta bita da kallo kafin ta maida kallonta kan su Hamida tana Fadin"Ku bata baki..Bari akawo abinci taci tasha mgani..!
Daga haka ta saki Labulen Dakin ta koma to a wannan gabar sai kukan Aminan ya tsaya cak kamar an Dauke ruwa Zuciyarta ta Bushe bata jira Lallashin kowa ba ta Gyara zama Daga zaune ta tada sallah domin jikinta har yanzu atsame yake bata iya Tsayuwa waje daya ta Gudanar da sallar ba..!
Wajen karfe Tara na Dare sai ga Ya Jafar da ya Nasir sun zo Amina na Daki taji Ya Jafar na fadin"Ina ita mara kunyar Aminar .?
Yaya Data Fito daga Daki tana gyara zaman Hijabin jikinta Da zasu tafi asibiti tace"Tana ciki..Tun dazu da taji Labarin abunda ya faru take kuka..!
Yaya Jafar sai da ya Lailaya ashar kafin yace"Yar iskace bata Daku bane..Ai wannan auran Baba mallam ya Daurasa ne ba domin ya dace ba wlh..!
Ya Nasir yace"Uhmm.Ni kuma ina ganin Daidai ne Jafar..Amina sai irin su ya Danmallan ne daidai dasu..!
Ya Jafar yace"Kamanta ne shi fa ba irin mu bane bai da Hayaniya bai kuma kaimu Zafi ba..!
Ya Nasir yace"Duk na yarda..Ammh kuma ya fimu Shekaru sannan cikin Ruwan sanyu yake Ladabtar da Mutum..Wlh ina ji ajikina Wannan al"amarin ba Tsarin Mallam bane Tsarin Daga Allah ne..Abu ne da Hasashe ko Tunanin mu bai taba kawo ba yanzu muka gama mgana da Ya Nazir shima haka yace..!
Ya Jafar yace"Nima ya Kirani yana Tambayana sai dai ina mamakin waya fadamai..?
Ya Nasir yace"Tab to har su Nazeem Dake Zaria sun ji Labari..Ya Danmallan din ne ban da masaniya ko ya sani..?
Mamanmu na zaune saman Tabarma cikin baranda tace"Nima yaran nan sai kirana suke Zulahait dai tace min Aisha ta Kirata ta fadamata itama tace Abida ta sanar da ita da wayar Hajiya..Suma mamaki suke suna son ji ko gaskiya ne nace musu gaskiya ne..!
Ya jafar yayi ajiyar rai kafin yace"Dawa dawa zamu koma asibitin..?
Mamanmu tace"Da yaya zaku je ni bazani ba zan zauna wajen Amina..!
Ya zeenatu tayi karaf tace"Ya Jafar don Allah zani..!
Tana rufe baki Hamida da Hanne suka Fito suna Fadin"Muma zamu don Allah..!
Sai da ya Hararesu kana yace"Bazaku ba..gobe da safanan za"a sallamesa..!
Mamanmu ce tace"Kaje dasu don Allah Jafar..Oh na manta ina mai ciwon kunni..?
Ya jafar yace"Yayi sauki sosai kin ma Tunamin ban karbi mganin da Baba Mallam yace nazo na karba ba..bari mu dawo..kuzo mu tafi Dare yayi kuma bana son rawan jiki yarinya ta natsu..!
Ba musu suka shiga Taitayinsu Ya Zeenatu ce ta Dauko kwandon data Zuba abinci yaya daman da hijabinta Jawad na gefenta sai su Hamida sallama suka ma mamanmu suka Fice,ya zeenatu da Hamida Motar Ya Nasir suka shiga ashe matarsa na gaba Anty Fadila da ita za"aje..!
Yaya kuma da Hanne suna Motar ya Jafar
Koda sukaje Aba yaji Sauki sosai sun samesa yana cin kayan marmari ga Ferfesun kayan ciki ne,da suka tambayesa wa ya kawo masa..?
Yace Hajiya Babba da Hajiya uwani yanzu suka fita Idi Direba ya kawosu ya riga ya koshi shiyasa suka ijiye abunda suka zo dashi Aba ya amsa gaisuwan Hamida da Hanne ya Kallesu Cikin kulawa yana Fadin"Ina Amina..?
Hamida tace"Tana gida Baba..!
Daman ta sani Amina na ransa ita din yarinya ce mai shiga rai kaunar da iyayanta Biyu suke mata Allah ne kadai yasanta sai dai baza su bayyanata ba Saboda kawaici da kuma Tunanin ba ita kadai suka Haifa ba
Daganan bai kara mgana ba Jawad yaja kan jikinsa yana Tambayansa ya makaranta yana bashi amsa basu Dade da zuwa ba sai ga Baba mallam ya shigo Cikin shigar Alkyabbansa da Rawaninsan nan suka Ramkwafa suna gaishesa ya amsa cikin Sakin Fuska yana kallon Su Nasir kafin yace"Ashe nan kuka zo..?
Kan Nasir na kasa yace"Eh Baba..Na kawo Fadila ne ganin bata zo ba..!
Yana zama saman kujeran Dake gefen gadon Aba da Ya jafar ya tashi ya bashi yace Lokaci daya"Yayi kyau..Kun kyauta Allah yayi muku albarka..!
Su hamida ya kallah ita da Hanne kafin yace"Naga zara ban ga wata ba..Ina mamana..?
Wannan karon Hanne tace"Tana gida Ita da Mamanmu Baba..!
Kai ya gyada kafin yace"In ta warware zamu daidaito ni da uwata insha Allahu..!
Ba wanda yayi mgana sai Su ya Jafar ne suka Murmusa kawai,Baba Sa"idu ya kallah yana Fadin"Kai ai ka warke tunda naga har kana iya Daukan Jawaad..!
Baba Sa"idu yace"Da sauki Baba..nacema ce su sallame ni yau sukace sai da safe in Likita yazo..!
Baba Mallam yace"Gwara ka kara samun karfin jikin ka kafin ka koma gida..!
Ganin suna gaisawa da Aba yasa su ya jafar sukayi shirin tafiya sai alokacin Baba Mallam ya kalli yaya yana Fadin"Hadiza bana son ganin wannan Damuwar afuskarki Daga gani kin ta kuka..Sa"idu ne babban banza shi ga inda ya kawomu ke kuma kina chan kina kuka har wata Cuta ta kamaki ta Miki illah ina amfaninta..?Ina ce Amina ce Matsalarku..?to ta fita Daga Hannunku ta koma karkashin ikon Umaru sai ku daina Damuwa..Ina ce ba Shikenan ba..?
Yafada yana kallon Aba da kunya yasa ya Sunkuyar da kansa Yaya kuwa kanta na kasa batayi mgana ba har sukayi musu sallama suka fice suka bar Baba Mallam anan da Jawad daya makale ma Aba yaki tafiya Baba Mallam yace a kyalesa in zai taho zasu taho tare. !
******
Tun bayan Fitarsu daga gidan ta Mike ta Leka Amina abinci ta Debomata Farar Shinkafa da Miya Kadan Amina taci don ma Mamanmu tana bata baki Tana Hadawa da Lallashinta Fadi take yi"Ki daina damun kanki ni nasan babu abunda kika aikata..Kuma mganar auran in baki so batare da kowa ya sani ba zan kira shi Danmallan din na Rokesa ya Sauwake miki..Ina Zaki iya da Sakina..?Matansa fa Biyu Kina yarinya Dake duka duka Shekarunki nawa Amina..?Sha Shidda fa Ko sha bakwai din Baki cika ba Har yanzu..Gaskiya akwai kwa ruwa acikin Hukuncin Mallam..!
Take fada cikin bayyana bacin ranta Amina kallonta kawai take batayi mgana ba to me zatace..?Tayi mgana ai bai da amfani komai ya riga ya kare ta rasa Aminu ta gama rasa komai Mganar Rabuwa da Ya Danmallam kuma bata isa ba har gaban Abada bazata watsama Baba Mallam kasa a ido ba kamar yadda bazata watsama Mamanmu ba uwa uba gasu Aba da yaya bata Fatan wani abu ya kara Giftawa,Ta riga ta sani Kaddara ta,kaita wani bingiren da Har yanzu ta kasa dora kanta a inda kaddaran ta jata ta kaita in tana tunawa ma sai wani Rauni da Faduwar gaba su Lulleta waje ne da har Abada zatayi Daraja ba ta sani..!
Har mamanmu ta gama bata tana ta Mita panadol ta bata tasha sai kuma ta shafa mata man zafi ajikinta Da Amina taji Dadinsa kwarai hawaye take yi da kukan zucci acikin ranta tana kara Ninka kaunar dake yi ma Mamanmu tana Fadin dama dama ana Sauya wani abu da Tuni ita Amina ta Dade da Sauya Yaya da Mamanmu amtsayin uwa..!
Amina bata sani ba Allah yana Boyemana wani abun ne kafin mu sani saboda kila alokacin in ya bayyana mana bamu da karfin gwiwan da zuciyan da zamu iya Dauka..!
Boyayyin Fuskokin wani Lokacin Alheri ne garemu kila sanda zasu bayyana Mun Tsaya da kafafunmu Raunin da zai bayyana garemu kadan ne..!
Sai da ta tabbatar da barci ya fara Daukan Amina kana ta bar dakin Dakinta ta koma bata Dangana ako"ina ba sai Cikin Bedroom dinta tana shigowa wayarta Dake kan gadonta ta sake Daukan kuwwa alamun kira ya shigo Da hanzari ta karisa ta Dauki Wayar sunan wacce ke kiran yasa bata Tsaya bata Lokaci ba ta Daga Daman ta sani zata kirata itama din Jiran kiran nata take yin bayan Tabbattuwaar abunda basu taba Tsammani ba..!
"Dayyaba Da saninki komai nawa ya Rushe..Dayyaba da saninki akamin wannan yankar bayan..Da Saninki kika bari yarinyar da ta Ratso cikin gabar aikina alokacin danake Hasashen ina gabda cin nasara..Na sani hakan zata faru shiyasa nake ta Kiranki tun dazu baki Daga Kirana ba..!
Tunda ta fara mgana wannan kamilar Fuska mai cike da Annuri da Tsausayi ta rine ta koma Bakar fuska mai Cike da mugunta da rashin Imani Cikin Wata Murya mai cike da Amon Takaici da Bakinciki tace"Da sanina Bazan bari haka ta faru ba Madina..!
Wlh ban sani ba..Kamar yadda kikaji abun Daga sama nima haka najisa..Shammatan mu Mallam yayi..Shammata mai girman da bamu Taba Tsammani ba Madina..!
Dagachan bangaran Agidan Baba Mallam ashashen Anty Amarya itama Cikin Tsakiyar Bedroom dinta tana Tsaye gaban makeken madubin Dakin nata tana kallon Fuskarta Data wani yarkace na Wunin yau kawai tun bayan Samun Labarin Daurin auran Amina da Umar..!
Cikin Muryanta mai Fadi da ba kowa ya santa da ita ba tace'"Lalle ko ya shammaceni Dayyaba..Sai da na Riga na gama Tsara komai..na gama Tunanin matsala tadaina shigomana cikin Aikinmu ashe suna chan suna Shirya ganina akasa..To basu isa ba..In a zaune suka kwana Ni Madina a tafe na kwana nayi alkawarin yadda bansamu Mallam ba ta bangaran Sakina Da Umar sai na Juya ragamar Mallam da duka abunda ya mallaka..Karya ne..Bayan sakina ba wacce ta isa Umar ya sota har ya Hada Jini da ita Sakina kadai keda Alhakin Haihuwa da Umar ita kadai ce Zata Haifama Mallam Yunus Bazanga Jika,Abaya nayi Sakacin da Har Ya"ya Biyu suka fara Fitowa daga Tsatson Nazir nayi sakaci Dayyaba..Sai dai kinsan aikin da mukayi ya"yan Nazir baza su taba Tasiri a wajen Mallam ba..Kacokan Burina na wajen Abunda Sakina zata Haifane..Sai da nace miki Mu kauda yarinyar nan Dayyaba kika ki bani goyon baya ta rasto cikin Aikin mu batare da Mun gayyaceta ba gashi nan yau Rana Daya ta Fadomin cikin Tsarina Tsarin da bazan taba bari ya Rushe ba Koda hakan na Nufin za"a rasa rai ne..Na kasa gane miki ko kin fara Sauya Ra"ayi ne na Sauya Duka Tsarina Dake..Kila kin hakura da Abunda Sa"idu yayi shekaru yana Kunsamiki ne shi da wannan Munafukar matar tasa..Ko kuma kin shagala kin Fara Kaunar wannan Hatsabibiyar yarinya Dake nemam batamin Shirina..!
Fuskar MAMANMU nake gani ta koma Jawur idanuwanta sun kala sun sauya Launi jijiyoyin kanta har sun Daga Saboda Bala"i cikin wata gigitaciyar Tsawa tace"Dakata Madina..!
Har Abada ni Dayyaba bazan manta Da Bakimcikin da Sa"idu shi da Hadiza suka Dade suna kunsamin ba..Wannan Kaunar wannan Tsausayin da Soyayyar da nake gani acikin Idanuwan Sa"idu kan Hadiza saura kadan su kaini kushewata Har Gaban Abada bazan yafe musu wannan ba..Sai sun Dandanan gudarsu bana yafiya.. ni din nafi Rama Sharri da Alheri..kamarni Sa"idu zai kallah gaban Ya"yana da Matarsa ya SAKENI madina kan wannan Shegiyar yar tasu..?Yarinyar da duk cikin ya"yan Hadiza nafi Tsananta saboda iyayanta sun fi sonta..Sa"idu ya Dade yana kunsamin Bakinciki ya fifita soyayyar Hadiza Fiye da tawa sannan yazo ya fifita ya"yan Hadiza Fiye da ya"yana Saboda Ban Haifi namiji ba ko..?akoda yaushe in na Bude ido na ga Jafar sai naji kamar na kashe kaina..Meyasa na barsa araye ban saka malamin mu ya Kashesa ba..Da yanzu ba haka ba Madina Da yanzu na Dade da kunsa ma Sa"idu da Hadiza bakin cikin da Har su koma ga Allah bazasu manta ba..Duk Saboda Cikar Burina na aro Fuskar da ba tawa ba Madina..Ina zaune cikin wadanda nafi Tsana ina Fifita ya"yam makiyiyata Fiye da ya"yana ina Faman kare ma wanchan yarinyar da bata da wani amfani a wajena...Madina Dukkanmu mafita muke nema saboda haka koma menene ki Fadeshi zan yarda zan amince zuciyata zafi take madina Amsa kuwar Sa"idu nake ji yana Fadamin ya Sake ni Saboda wannan Shegiyar yarinyar ina so suma su Dandana ina so suji yadda na daukii shekaru ina ji acikin raina..!
Anty Amarya tayi Mirmishin Dayafi kuka ciwo kafin tace"Sakacin ki ne Dayyaba..Tun Lokacin da aikin malam ya Tsallake Jafaru ya koma kan Amina nace a kaudashi kika yi yarda..Da yau baya Raye Da wane d'a Sa"iidu zai yi takama..?yau gashi dan Zaki ya Girma harda albarka Haihuwan wani karamin Zakin Dayyaba anya ke naki Tsarin ba Doguwar Tafiya bace..?
Da Sauri Mamanmu tace"Bana kallonshi a Faduwa Madina..Jafar da Abunda ya Haifa ba su da wani amfani kadan nake jira na karar da su..Yanzu ni Sa"idu zan fara mgani Tukunnah so nake naga bakimciki da Rauni acikin Idanuwansa Madina..!
Kai Tsaye Anty Amarya tace"Za"a rasa rai...YAYA ZATA MUTU...!
Mamanmu tace"TABBAS YA KAMATA TA MUTU..sai dai naso sai ta gama shakan bakincikin da na Dade ina Tanadama mata madina..!
Anty Amarya tace"Yanzu Lokacin Daya kamata ta Mutu ne Dayyaba..Mutuwar ta ne kadai zai sa kiga wannan Bakincikim acikin Idanuwan Sa"idu..Mutuwarta ne zai sai nima naga Sa"idu ya koma abun Tsausayi ya dade yana min katsalanda Shi da Hajiya Babba..Zamu fara ta kansa ne kafin mu dawo ta kanta da Saninsa aka Aurama Umar Amina..Da saninsa ta shigo Tsarina nima wannan Damar nake jira da Zan Dandana ma Sa'idu koda Rabin abunda nakeji ne game dashi..Komai na ke kokarin samu Shi da Hajiya babba sai sun tare ni Dayyaba..!
Cikin wata irin Dariya tace"TABBAS yakamata ta Mutu...!
Zata mutu..!
Anty Amarya tace"Zan kira mallamin mu Dayyaba zan sanar dashi ya yanke mata wa"adinta kafin wayewar gari bazan jira ba..bana son wannan karon asamu matsala..!
Mamanmu tace"Nima haka..Wayewar garin gobe Ranar mu ce..Na kosa na kosa naga wannan bakimciki akallon da zan ma Sa"idu..Babban kuskuransa shine ya Fifita komai na Hadiza akaina..Babban Raunina Ina SON SA'IDU..!
Anty Amarya tace"Shikenan kada ki damu ki Dauka an gama..Mganar kudi akwai wani abu a hannunki..?
Mamanmu tace"ki kamallah komai in mun hadu zamu warware komai..!
Anty Amarya tace"Shikenan..Mganar yarinyar nan baki ce wani Tsari zan kaita ba..?
Mamanmu ta saki Dariyan Nishadi kafin tace"Ban damu ba Madina..Ni Kaina na sani Dagani sai ya"yana..Ki kaita Duk Tsarin da kika ga Dama..Koda Tsarin na MUTUWA NE..!
Anty Amarya tace"Tsarin bana Mutuwa bane..Zata sha wahala ne kawai sai daga baya mu kaudata..Tsarin da na kai Balarabiyar nan Tsarin zan kaita Dayyaba..Hotuna zasu zama wajen Umar har Abada Sakina ce Zata Cigaba da amsa matsayin mata awajensa..Wannan alkawarin ne..!
Mamanmu ta jinjina kai tana Fadin"Hakan yayi daidai..Daga gobe komai ya Dawo hannuna..Daga Sa"idun har ya"yan nasa..basu san Wacece Dayyaba ba..Balaraba Ita suka sani..!
Dukkamsu Dariyan suka sheke da ita Dariyan cin nasara da samun Duniya lokaci daya suna yanke kiran atare..!
Abunda basu sani ba wani abun Allah ya Riga ya kaddaran Faruwansa bakin Alkalami ya Riga ya Bushe..!
Tabbas za"a rasa rai..Sai dai basu isa su Dauki ran wani ba..Daman chan ita ran Lokacinta yayi ne..!
Suna gama wayar ta Wurgar da wayar saman gado ta fara Zagaya Dakinta Cikin kaushin murya take fadin"Allah Sarki Yaya..Yau za"a amsa kiran Allah..!
Wayyo wayyo..!
Haka take ta fadi sai kuma ta kece da Dariya kamar mahaukaciya kafin ta koma ta Duke kuma sai ta saki kuka Lokaci Daya tana Fadin"Ba haka naso na zama ba..Sa"idu kai ne sila..Na soka Tun kafin ka fara son Hadiza..Me na rasa baka taba sona ba..?Kasha bansan auran biyayya kayi dani ba..?
Kasha bansan ka Tattara Zuciyarka ka bama Hdiaza ba..Wannan son shi ya ja maka kai da ita..Wannan Tsausayin shi zai kasheta Sa"idu..Ba Laifina bane..Laifin SOYAYYARKA CE..Bantaba son wani Namiji yadda na SOKA BA
Koda bazaka soni ba nayi alkawarin baka isa ka so wani ba..Komai na ya"yanta ya zarce nawa..Duk yadda naso hakan bata Faru ba sai da na zama koma baya agidanka..Kasha bansani bane.?bakayi karya ba nasan Amina ta fara soyayya da wani..bakayi karya ba..Nasani naki fadamaka Saboda Daman ina son damar da zata kara Ruguza rayuwar Hadiza..ban so abunda ya faru ya Tsaya nan ba na so ne Tayi Cikin shege na Tsawartsaku gabadaya..ba Laifina bane..Yaya ki yafemin Sa"idu ya ja miki MUTUWA..!
Take fada tana Hawaye Lokaci Daya Dadariya tana Tuna ranar data fara kama Amina tana waya da Aminu acikin bayinta bata nuna ta ganta ba..Hakan ya mata Dadi Domin bata kaunar cigaba Daga bangaran Hadiza ita da ya"yanta Tundaga Lokacin Da gangan take ijiye wayarta Har Aminan take samun Daman Dauka ta kuma fara Bibiyan Motsinta abunda kowa baisani ba Hatta Haduwar da take yi dashi duk tana sane..Taso ta shirya wani abu ne..Taso ta yi amfani da Amina ta Tsarwatsa Yaya da ahalinta sai dai Mallam ya shammesu matuka shammatam da basu taba Tsammani ba..!
Abunda bata sani ba..Ba Mallam bane Allah ne ya Rubuta abunda ya Faru Daki Daki..Su basu isa su Hana Al"amarin Allah ya Faru ba..Zanen kaddaran ya zama kuma bawa bai isa ya goge shi ba..!
Achan asibiti kuwa bayan fitan su ya Jafar Baba mallam bai kara cema Aba komai ba sai shine da kunya ta kamaasa yace"Nagode Baba..Allah ya kara Girma..Naji zabin da kayi ma Amina badomin kada nayi sonkai fa sai nace nafi kowa Murna da hakan..!
Baba Mallam ya yi mirmishi cikin wani yanayi yace"Sai da ga baya naga kamar nayi gaggawa Sa"idu.Abunda kuka zata ba haka bane..Jikina yayi sanyi naji kamar na so kaina nima dana aurama uwata Umaru a karancin Shekarunta na yarinta..Da ace na sani da na jira..Kadan da na aura mata wanda ke sonta Tsakani ga Allah ya kuma dace da ita..!
Yafada yana jin Tsausayin Aminu na kamasa yana Tuna yadda iyayansa suka nuna jimamin Lamarin bayan sun gayama mallan duk abunda Aminu ya fadamusu kan Amina ce ta Dakatar dashi na bayyana kansa sun yi sallama Cikin wani yanayi ya Rakosu har waje suka iske Aminu Cikin wani yanayi wanda Dole bawa ya Tsausaya masa..!
Baba Mallam yaji Dama ace ya Jirakadan..Da duk haka bata Faru ba..Sai da ga baya yaga kamar yayi gaggawa..Da ace Nazeem ya aura mata..sai daga baya yace dama Nasir ne..Umar yayi ma Amina girma Tazaran Dake Tsakaninsu kamar tazaran kasa da sama ne..!
Yaji da ace Aminu zai karbi Tayinsa Daya Aura masa Hanne ko Hamida Domin ya wanke kansa Daga wannan zargin sai dai ina Agaban idonsa suka sakashi a mota cikin wani yanayi suka Dauki Hanyar Yola..!
Shi kanshi Aba jikinsa yayi sanyi da bayanin Baba Mallam tun ma Daya bude baki yana fadamai abunda ya Faru bayan zuwansu Aminu..!
Dukkansu shuru sukayi sun kasa mgana sai chan Aba yace"Baba Komai fa Da kaga ya faru yau..tsarin Allah ne..Mu yi fatan wannan Auran ya zama Sillar warwarewan duka abubuwansu Allah ya amintar da zuciyoyinsu waje daya..!
Da Amen Baba Mallam ya amsa abunda basu sani ba sun yi addu"an akan gaba ammh Allah ya Riga ya amintar da Ruhin Amina da Umar waje Daya Alkaalamin kaddaransu ya Riga ya Bushe!
Sun dade suna kara Tattaunawa sai da Shamsu yazo shi da zai kwana da Aba ranar sannan Baba Mallam yayi mai Sallama ya koma gida Cikin Damuwa da Tunanin yayi gaggawa..!
Abunda ya Dade bai Faru ba yau ya Faru Baba Mallam bai isa shashensa ba kai Tsaye shashen Hajiya Babba ya Sauka kuma aidon matansa duk da Ba ita ke dashi ba Hajiya Nasara ne..!
Yana cikin Damuwar da ita kadai zata iya kwantar da mai hankali.
Haka yaje mata yana Fadin"Zainabu anya banyi gaggawa ba..?
Ina ji kamar na zalunci uwata..!
Hajiya bata Fahimci mganarsa ba sai da ya warware mata na zuwan iyayan Aminu ya karishe da Fadin"Meyasa na Zabi Umaru..?Meyasa ban zabi Nazeem ko Nasir ba..?Uwata tayi kankanta Umaru ba Tsaranta bane..ba zata iya zama cikin mata Biyu ba Hajiya..Nayi gaggawa..!
Yake fada lokaci Daya yana Cire rawanin kansa..!
Hajiya taji jikinta yayi sanyi itama Sai kawai ta Riko Kafadan Mallam tana maimaita Hasbunallahi cikin ikon Allah shima ya shiga amsa mata har ya samu natsuwa zaunar dashi tayi kan gado taje ta Debo masa ruwa mai Sanyi yasha yayi hamdala sannan ta kallesa tace"Bakayi gaggawa ba mallam...Daman chan Amina bata da miji sai Danmallam..Ba Tsarinka bane naa Allah ne..Ina ji ajikina wannan aueran Alheri ne zamu ji Dadinsa Watarana..shi kuma yaron Allah ya basa wacce ta fi Amina haka Allah yaso..!
Kalamanta sun kwantar mai da Hankali Cikin natsuwar daya samu yace"Ameen ya Allah zainabu Abu mai Tawagayen suna..Bani abinci in ci inji dadin saka miki albarka..!
Dariya kawai tayi tana Ficewa Daga Dakin ya Bita da kallo aransa yana Tunanin Har Abada bazai taba samun macen kwarai irin zainabu ba..!
Sai da ta dawo da farantin abinci ta Sauke agabansa sannan tace"Muna da bakuwa fa..?
Yana Saukowa saman Cafet din Daya malale Dakin yace"Bakuwa kuma..?
Tana kokarin zama gefensa tace"Eh Hajiya BATULA ce kanwar Uwani Tazo Dazu da yammah nan daga Tsafe..!
Bai ce komai ba illah kai daya gyada ita kuma sai ta fara kokarin zubamai Tuwon shinkafa miyar ogun din da akayi..!
*******
2:30pm na Dare..!
Acikin Tsakiyar Falon Hajiya Uwani Zaune suke ita da yar"uwanta kwara Daya da suka fito ciki Daya su ka kuma Taso acikin jerin ya"yan da Alhaji hamza mahaifinsu ya Haifa..!
Tayi aure mijinta ya rasu da Dadewa sai dai bata taba Haihuwa ba..Kuma tundaga Lokacin bata sake aure ba kasuwanci take yi..!
Haj.uwani Dakin da Umaimatu ke ciki ta kallah kafin ta sauke numfsshi Lokaci Daya tana Fadin"Anya Batula kina ganin ba Zunubaina ke shafan Umai ba..?
Duba kiga irin wahalar da mukeyi akanta har yanzu taki Lafiya Sa"o"inta duka Mallam ya aurar dasu ita ba Boko ba ba aure ba gani cikin kishiyoyi bana so aga gazawata..!
Wacce aka kira da Batula ta gyara zama suna kama da Hajiya uwani sosai..!
Cikin Yar dariya tace"Bai kamata ki karaya ba tun yanzu Uwani..Matsalan Umaima Daga Allah ne kin sani duk inda mukaje haka ake fadamana..Na Fada miki zata samu lafiya..Yanzu dai mu ijiye mganar Umaima agefe mu yi wacce Itace Dalilin zuwana..!
Haj.uwani ta gyara zama tana Fadin"Uhmm..Acikin Abunda muke so mu kauda Batula wani abun yazo ya kara shan gabanmu..Yakin ba yanzu zai kare ba Batula..Mallam yau da azahar ya Daurama Umar aure da Diyar Sa"idu Amina..!
Batula ta zari ido kafin tace"Aure kuma..?
Haj.Uwani tayi dariya takaichi kafin tace"Eh ba wanda ya sani sai da aka Daura mukaji..Kuma bai yimana bayani ba..Kina gani yazo ya shige shashen giwa bai nemi kowa ba..!
Batula ta karkace kai kafin tace"Shine yasa kika Tadoni tundaga Tsafe zuwa Gumel Uwani..?
Kai ta gyada mata karamin Tsaki taja kafin tace"Da kin fadamin tun awaya wlh da ban zo ba
Wannan ai karamin aiki ne..Me zai gagaremu Yarinyar wai me take takama dashi data baki tsoro..?
Haj.uwani tace"Ba komai yarinya ce karama Sa"ar Sadautun Amarya..Yanzu suke SS1 MA..!
Batula ta karaa sakin Tsaki kafin tace"Abu mai sauki..Ai tunda muka iya kai Sakina kasa kowa ma ta auri Umar sai mun kaita kasa..Hajiya babba ta samu Mallam da duka komai nasa to ta bar shi haka bata isa ta bangaran ya"ya kuma ta miki Zarra ba..Kada ki manta mu mukasa akayimana aiki kan manyan ya"yansa da sukaki zama kusa da Hajiyan da Mallam din mu ka Tura kurciyan Umar Madina yadda bazai ji sha"awan Dawowa gida ba kuma muka Tura Kurciyan Nazir Lagos yadda Har Abada zai iya zaman Gumel ba..Abu kadan ya ragemana Nazeem da Uzairu su gama karatu su Dawo gida Lokacin sai mu maida Sa"idu mara amfani alokacin Mallam bai da wata mafita sai ta ya"yanki sune Jagora Uwani!
Haj.Uwani Ta saki kayattacen Mirmishi tace"Kin manta baki Tunanin Jikokin ya"ya na ne kadai Mallam zai kallah yaji Dadi ba..Tunda Mama ta fadamana Mallam yana matukaar son ganin kwam Umar aduniya na Mike Tsaye,Duk Shigen Shigen Marliya sai da nasha gabanta Bata sani ba ko gobe Sakina ta samu Ciki sai ya Lalace Mama ta tabbatarmin Umar haka zai zo ya koma bazai taba ganin kwamsa aduniya ba..!
Batula tayi dariya kafin tace"Wai itama balarabiyar madina din kin gama mata aikin..?
Haj.Uwani tace"Tun yaushe..Tare suka sha mganin Mama cikin Ruwan Tea din da suka tako har Fadona na Hada musu sun koma ba Dadewa..Sakinar tayi bari har Umarun yaxo karban mata mgani da Marliya ta karbi mata na Hausa..Araina nace kyayi ki gama..Wannan gidan na Uwani ne da ya"yaanta..!
Atare suka saka Dariya kafin Batula tace"To wani mataki zamu Dora sabuwar zuwan namu..?
Haj uwani tace"Tsarin da na Dora na gabanta zan dorata..Duk da nasan ma Umar b abunda zai ci da wannan mara kunyar yarinyar sai dai kinsan Namiji baka rainasa..Awajena bata da wani amfani kamar yadda na Maida yaron nan NASIR mara amfani a wajen Mallam in ba ya gansa bama mantawa yake yi dashi..!
Wata Dariya suka saka har da Tafawa kafin Batula tace"Don Mallam din da Giwar suna Tsaye ne..Ai da tuni burin mu ya cika..!
Haj.uwani tace"Abu daya na kasa..Kai Maallam kasa shi da Hajiya..Mama tace har Abada bazan ci galaba akansu ba sai dai kan yaran
Basa wasa da ibada sannan azkar kamar ya zama jikinsu in ba ikon Allah ba Sihiri bazai taba kamasu ba..!
Batula tace"Shiyasa nace ki bar asaran kudinki..Mu koma inda Mama tace sai muga riba..!
Haj.Uwani ta saki kayayyatacen Mirmishi kafin ta koma ta kishingida kan kujera Lokaci daya tana Fadin"Aikuwa naga Riba Batula...!
Ashe ashe basu sani ba..Suna Tufka ne..Daga gefe wata Boyayiyar Fuskar tana Faman warwara..!
0 comments:
Post a Comment