鈥淒auki daya鈥�
Cikin ladabi Falmata ta saka hannu ta dauki lemun daya kamar yadda ta bata umarni ta nufi dakinsu, tana shiga tai shirin bachi babu komai a fuskarta sai murmushi yau kam ranta fes ta ga sabon video M2, har ta kwanta sai kuma ta tashi tana rare wakarsa a hankali tana rawa tana kallon inuwarta wacce kyandir ya haska, sai ka rantse da Allah ba Falmata bace yarinyar da ko a hanya ka hadu da ita ba zaka taba saka ran tana magana ba. Sai da taji motsin shigowar Naja sannan ta yi addu'ar bachi ta kwanta.
Washe gari ma kamar ko yaushe, sai da ta gama komai sannan ta shiga tai wanka ta saka wasu tufafin ta fito ta sha kokon da Tumba ta dama, kamin ta sake mika mata wani rubutun ta karba ta sha da Bismillah. Sannan ta fito ta kama hanyar zuwa gurin aikinta tana tafiya a natse, kana kallonta ka ga natsantsiyar yarinya mai kamala da tarbiya.
Ba ta yi mamakin sake karo da Iya a Harabar gidan ba, domin kusan kullum sai ta ganta a gidan duk da bata san aikinta ko alakarta da masarautar ba, amman ta tabbatar da ita din wata babba ce a ciki. Ta gaishe ta kamar yadda ta saba sai dai Iya bata amsa mata ba yau kam ko kallon inda Falmata take Iya bata son yi. Sai dai gaishe da kowa sannan ta wuce cikin gidan, a tsanake ta hau stairs din ke sada mutum da falon Ammy sannan ta danna door bell. after like 5 minutes Shattima ya bude mata kofar, wani irin jan numfashin Falmata tai ta yi mutuwar tsaye a gurin tana kallon Shattima idonta a waje kamar irin ka ga wanda ka dade ba ka hadu da shi ba ko kuma kake mafarkin gani, ba ido kadai ba har bakinta a bude yake a wannan lokacin. Shattima kan sakin kofar yai ya dawo falo ya zauna yana taba wayarsa daman indai shi zai ce mata ta shigo ko ya tambaye abunda take so sai dai ta shekara a gurin, budewar ma ta yi sa'a yana tsaye jikin kofar ne. Na so kafarta tai ta shigo cikin falon tana cigaba da kallonsa kamin idonta ya sauka a gurin Hajiya Karama wacce ke kallonta, wani irin kallonsu take kamar bata taba ganin mutane ba, ita a rayuwarta bata tana ganin fararen mutane da farinsu ke haskawa sosai kamar Shattima ba, gaba daya kallon Balarabe take masa sam bata yarda bafullanin mutum ne take kallo ba, ta kallin fatar jikinta da take baka ta sake kallon Shattima, ba farin ba ko gashin kansa da ke a gyare abun kallo ne, ga wani dogon hanci kamar biro kai ko cikin larabawan wannan na musamman ne. Shi ne abunda zuciyarta take raya mata.
鈥淢e kike so?鈥�
Hajiya Karama ta tambaya, a lokacin ne Falmata ta kara rikicewa, ta sara abunda zata ce, gaishe su zata fara yi ko fada musu aikin da ya kawo ta, tun da take zuwa gidan bata saba karo da daya daga cikinsu ba sai yau, sai dai jiya ta hango Zainab a stairs sai dai bata dauka a kusa kyauta yayi haka ba sai yau.
鈥淢e kike so?鈥�
Zainab ta daka mata tsawa, a take jikim Falmata ya hau rawa sai ta fashe da kuka domin ba karamin tsorata tai ba.
鈥淓asy mana鈥�
Shattima ya fada yana kallon Hajiya Karama.
鈥淭o ana mata magana sai tai ma mutane shiru, kuma sai kallonmu take kamar mayya i hate nonsense鈥�
Ta karasa tana mikewa tsaye ta fice daga falon tana wani yatsinar fuska kamar ta ga abun kazanta.
鈥淏aaba ware鈥�
Shattima ya kira taohuwar yana kallon inda take tsaye rike da turaren wuta, sai a lokacin Falmata ta lura da ita da wasu masu aikin da ke can gaban Plasma suna gogewa. Da gudu Baaba ta karaso gabansa.
鈥淎llah ya kara maka lafiya鈥�
鈥淎 tambaye ta me take so鈥�
Ya fada kamar baya son magana. Baaba ta kalli Falmata da har lokacin kuka take tana shasshekar kuka ta ce.
鈥淜e yar talakawa fadi ki yi kwashi gaisuwa kuma ki bude baki ki fadi abunda kike so鈥�
Falmata na jin haka ta fadi kwance a gurin rib kamar an jefar da ita cikin muryar kuka ta ce.
鈥淚na kwana鈥�
Da ace shi kadai ne adakin da Allah kadai yasan kalar dariyar da zai yi, domin ba karamar dariya ta ba shi ba, sai dai ko da wasa be nuna hakan ba sabanin hakan ma sai ya kara hade rai.
鈥淲acece ita?鈥�
鈥淎llah ya baka yawan rai ita ce mai gyara dakin yan uku鈥�
Baaba ta fada tana daga masa hannun kamar mai gaisuwa, ya kalli Falmata daga inda take kwance ya kare mata kallo sannan yai mata alama da ta mike tsaye da hannunsa, da sauri ta tashi ta share hawayen idonta tana jiran wani umarnin. Da ido yai mata alama da ta wuce dakin tai aikinta, da sauri ta wuce, cikin rashin natsuwa tai aikin ta fito kamar wacce ta saci wani abu haka ta rika leken falon da babu kowa sannan ta fice.
AA POV.
Be yarda ya fadawa Anti Rabi cewar bayan kudin da Nana ta bata ba ta sake ba shi wasu, sai dai ya sha fada kuma ya sha gargadi akan cewar kar ya sake kula ta.
鈥淜ai ko kallon inda take kar ka sake yi鈥�
鈥淭o ai ba za a koma ba鈥�
Ya fada ne kawai amman wani bangare na zuciyarsa na kara raya masa yadda zai sake samun wasu kudin haduwarsu ta gaba, tun da ta karbi lambarsa yake jiran kiranta.
鈥淲allahi Allah ne ya ji tausayi na ya kawo min yarinyar nan, Allah kadai ya san me babanta ke yi鈥�
Ya fada a ranshi yana aikin saka talkaminsa, sai da yai ma Anti sallama sannan ya fice daga gidan, kamin ya isa gurin aikin nasa har addu'a yake Allah yasa yau ma ta zo, ya kuwa taki sa'a domin ya tarrarda ita zaune a gurin tana ta boye fuskarta kamar yadda ta saba, wannan karon be tsaya komai ba ya nufi inda take, Nana na ganinshi ta fara dariya.
鈥淭un dazun na zo鈥�
鈥淢uje waje mu yi magana鈥�
Ya fada yana kallon daidaikun mutanen da ke wajen, domin safiya ce ba kamar da rana ba ko dare da ake taruwa sosai a restaurant din. Mikewa tai tsaye ta riga shi fita sannan ya fito ya same ta tsaye a inda ta tsaya jiya.
鈥淜in samo min aikin driver?鈥�
Ta bata fuska kamar za ta yi kuka.
鈥淎 a ta hana鈥�
鈥淒aman karya kike yi鈥�
鈥淒a gaske ne mana鈥�
Shiru ne ya biyo baya na tsawon lokaci, sannan ya sake kallonta ya ce.
鈥淵au ma kina son na kai ki wani guri ki boya?鈥�
Da sauri ta daga kai.
鈥淓h Eh鈥�
鈥淭o kawo kudi na karbo babur din, amman yau ya ce sai an bashi 4k鈥�
Bata tsaya komai ba ta bude jakar ta dauko kudin ta mika masa.
鈥淣a je can waje na jira ka kamar jiya?鈥�
鈥淓h鈥�
Ta nufi hanyar fita shi kuma ya koma ciki gurin abokinsa Bashi, ba laifi yau ya manna masa 500 sannan ya karbi key babur din ya fito ya kunna ya hau ya fito da shi waje, yana isowa bata tsaya komai ba ta hau ya boye fuskarta, sai da ya su kai nisa sannan ya fara tunanin inda zai kai ta, ya san zai ba zai sake kaita gidan Anti Rabi ba, bayan dazun da safen nan ma sai da tai masa gargadi, to ina zan kaita? Ko ya kaita gidan Gwaggonshi? Ko gidan Kawu Bala? Kuma idan na kaita suka gano abunda cewar boyeta na yi za su min fada? Sai tambayar kansa yake yana neman mafita, be an karo ba yaji kamar an bugu babur din da suke kai yana kokarin saita babur din suka fadi kasa daga shi har ita, babur din ya haye shi ita kuma ta mulmula ta fada kwalbati.
Kamar ita ta fi kowa ihu a duniya haka ta kwala ihu ta fashe kuka na gaske tana duba hannunta da yaji rauni da kafarta, daman can ko allura aka ce za a mata sai anyi da gaske take tsayawa balle kuma wannan da ta gurje a hannu da kafa da gefen fuska.
鈥淲ayyo Allah Wallahi sai na fadawa kowa, sai an kashe ka yau Wallahi kai ne ka ji min rauni kai ne ka fadar da ni da babur, sai na fadawa kowa yau sai an kashe ka鈥�
Cikin wani irin kuka da tsoro take fadar hakan tana kallon jikinta, AA na jin haka ya manta da nasa ciwon ya taso ya nufo ta ya daga ta, mutane sai sannu suke musu, ganin yana jan kafar wani yace
鈥淶aka iya jan babur din kuwa鈥�
鈥淓h zan iya ku taimaka ku dora min ita dan Allah鈥�
Sai da ya hau sannan suka dora masa Nana dake ta ihu tana fadin sai ta fada a gidansu. A hankali ya fara tafiya gabansa na mugun bugawa kamar zai fito, sai da ya samu wani mai chemist sannan ya faka babur dinsa a gurin ya sauko ya rikota ta sauko ya shiga da ita cikin chemist din, zaunar da ita yai sannan ya ce.
鈥淏ari na gyara fakin din babur di na鈥�
Bata ko kula shi ba tana ta kuka da duba kafarta domin har a cinya ta ji ciwo. AA na isa ya haye babur din ya auna a guje be be nufi ko'ina ba sai unguwarsu, kamin ya isa har wani zazzabi ya rufe shi babu muryar da yake ji sai ta Nana tana fadin sai ta fadawa yan gidansu yau ko sai an kashe shi, laifi goma da ashiri, ga boyon da yake mata ga na fadar da ita akan babur dinsa dan ya san yarinyar yar masu abu ce wata kila ma ita kadai iyayenta suka haifa ya san kuma ba za su kyale ba.
Kamar wani mahaukaci haka ya shigo gida hannunsa na ta jini sai dingishi yake. Anti na ganinshi gabanta ya fadi.
鈥淟afiya AA鈥�
Kasa ce mata komai yai ya zauna bakin kofar dakinta ya dafe kanshi.
鈥淟afiya hadari kai?鈥�
鈥淓h yarinyar ce ta roki na kawo ta nan shine na sake aro babur, muna tahowa sai wani mai Napep ya kade ni muka fadi ta ji ciwo ni ma na ji鈥�
Anti Rabi ta daki kirji.
鈥淢e? La'ilaha illallahu Muhammadu Rasulullah Sallalahu Alaihi Wassalam鈥�
AA ya kalleta a tsora ce ya soma magana gumi na karyo masa.
鈥淜uma Wallahi na ji tana cewa sai ta fadawa duk yan gidansu, wai yau sai an kashe ni tun da na fadar da ita akan babur鈥�
A take cikin Anti Rabi ya murda, ta dora hannu aka ta fashe da kuka.
鈥淜a gani ko? Sai da na gargade ka amman baka ji ba, Allah kadai ya san waye ubanta mun shiga uku, ina yarinyar take?鈥�
鈥淣a barta a can wani chemist na gudo鈥�
鈥淜ai Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, mun shiga shida鈥�
Ta fada tana nufar butar da ke tsakar gida ta dauka ta nufi bandaki. Mikewa tsaye AA yai ya fice daga gidan, chemist din unguwarsu ya nufa yana isa be ko tsaya gaisawa da abokin nasa ba ya ce.
鈥淒an Allah Ilya kai min treatment din ciwon nan kuma ka min allurar malaria, ina jin zazzabin malaria na ta so min鈥�
_________________
Waye zai zo ya cece AA 馃ぃ馃槀
Me iya take kullawa? 馃
Anya dai Hajiya Karama mace ta tana neman miji da kanta kamar yadda kike?馃槬
Wai me Falmata ta tarewa Tumba ne?馃槶馃ぇ
03/12/2021, 08:07 - 馃馃馃馃: *馃悇馃悇 FULANI 馃悇馃悇*
By Khadeeja Candy
*6*
HAJIYA BABBA POV.
鈥淛arma har yanzu ban ga komai ba鈥�
Ta fada tana karewa Jarma dake zaune a gabanta sanye da babbar riga, kansa kuma da rawani.
鈥淜ina gaggawa ne kawai Hajiya, ba gashi mun fara ganin haske ba? Komai a sannu ake binsa鈥�
Ya dauke kai tana kallon wani bangare na dakin.
鈥淏a Mai Martaba nake magana ba, Shattima shine matsalata a yanzu鈥�
鈥淒a Shattiman za mu fara kamin Mai Martaba ya biyo shi, idan mu ka yi gaggawa to kamar muna fallasa sirrinmu ne, ya kamata mu bi komai a sannu鈥�
鈥淎 sannu na ke bin komai Jarma, domin burina dole ne ya tabbata, Talba kadai na ke son ya yi mulkin garin nan, so na ke na ga Ammy na zubar da hawayen bakinciki, shekarun da ta saka na yi a damuwa so na ke ta ninka a cikin bakinciki, na san a yanzu tana farinciki da ciwon Mai Martaba saboda tana ganin Shattima ne zai gaje shi ko? Hmmmm鈥�
Ta karasa tana murmushin gefen baki. Jarma ma murmushin yake yana kallonta zuciyarsa na saka masa burinsa.
鈥榋a mu kawar da Shattima da Mai Martaba, amman dan ki ba zai yi milkim garin nan ba, indai ina raye鈥�
A zahiri kuma sai ya gyara babbar rigarsa ya ce.
鈥淒a sannu komai zai wuce Hajiya, kuma kar Salim ya fasa neman Nana鈥�
Sai a lokacin Hajiya ta dawo da kallonta a gurinsa.
鈥淎i dole ya neme ta, tun da har Mai Martaba ya sallama masa babu wanda ya isa ya shiga tsakaninsu, dole ne Ammy da zuri'ar ta su dawo karkashin kulawata, duk abun da tai min a shekarun baya sai na maimaita mata shi鈥�
Ta karasa zancen fuskarta na sauyawa alamar bata son tuna bayan.
鈥淜omai zai wuce Hajiya komai zai zama tarihi da yardar Allah鈥�
Ya daga masa kai tana sauke wani dogon numfashi.
鈥淗aka ne, tashi ka je kar a fara yi mana zargi鈥�
鈥淶argi kuma na nawa? Sai dai kar a koma鈥�
Ya fada yana mikewa tsaye da murmushi a fuskarsa, sannan ya dan risina mata.
鈥淣a bar ki lafiya鈥�
Da kallo ta bishi har ya fice sannan ta mike tsaye ta nufi gaban drawer ta dauki wayarta ta aikawa Hajiya Talatu kira bugu daya ta daga tana jerowa Hajiya Balki wani irin kirari da ke kasa kan Hajiya fashewa.
鈥淎n gaishe da Talatu Uwargidan Waziri鈥�
Talatu ta risina kamar Hajiyar ce a gabanta.
鈥淎llah ya kara miki lafiya da imani, Surukar Ammy kuma Uwar Sarkin gobe, a ganki a bar ki kuma a bi ki a dole鈥�
Hajiya Bilki ta yi wani irin kasaitaccen murmushi.
鈥淵anzu Jarma ya fita daga nan鈥�
鈥淭sohon makiri, Allah yasa dai ba ki masa zan ce na ba, domin tsab zai labartawa Waziri komai ya kashe mim aure a asirance鈥�
鈥淭aya za ayi na bar shi ya san shirin mu Talatu? Bayan na san shi akwai kwadayin masarautar nan a ransa? Ubansa daya fa da Mai Martaba kuma babu yadda be yi ba Mai Taba ya bashi Babbar masauta ya ki, yanzu kuma kike tunanin baya sha'awar wannan?鈥�
Hajiya ta dan yi jimm tana murmushi mai sauti
鈥淢u dai gama da bangaren sauran ne sannan mu dawo kansa, na kira ki na ji yadda ake ciki鈥�
鈥淶an shigo da kaina ranki ya dade, domin maganar ba ta waya ba ce鈥�
鈥淚na jiranki鈥�
鈥淭o ranki ya dade鈥�
Daga haka ta aje wayar ta juya ta fice daga dakin, kofar dakin bata kara idam an bude ko an rufe gashi akwai yar tazara sosai tsakanin dakunan da inda aka jera kujerun falon, hakan ne yasa Sirleem be ji motsin mahaifiyar tasa take tsaye a bayansa tana kallon Mansura wace ke a fuskar Laptop dinsa yana video chat da ita ba. Har sai da ya ga Mansurar ta kasa karasa maganar da take tana kallon gafensa, sannan ya juya sai yai arba da mahaifiyarsa. Da sauri na rufe laptop din.
鈥淗ajiya Barka da fitowa鈥�
鈥淏an maka iyaka da yarinyar nan ba?鈥�
Ya sinne kai kasa, ya kasa cewa komai gabansa sai bugawa yake da karfi. Wata irin tsawa ta daka masa rai bace
鈥淲aye miye hadin Bayarabiya da bafullatani ne Sirleem? Me ta baka ka sha da baka iya rabuwa da ita? Ni uwarka ban isa na ce ka fita hanyar Mansura ka fita ba? Me yake damunka ne?鈥�
Dagowa yai ya kalleta cike da ladabi ya ce.
鈥淗ajiya ba fa cewa nai zan auri Mansura ba, Mansura kawata ce kawai, i think Nana kike so na aura ai鈥�
鈥淵es wannan kuma dole ne, auren Nana ya zame maka wajibi matukar ina raye, yaushe rabon da ka je ka dauki Nana ku fita ko na kira a waya? Amman ka zauna kana video call da wata yar iskar yarinya marar tarbiya, kuma a cikin falona鈥�
Cikin wata kalar murya dake nuna bacin ranta ta karashe maganar tana nuna shi da yatsanta da ke rawa kamar zata doke shi.
鈥淚'm sorry鈥�
Shine abunda ya fada ya mike tsaye ya dauki system dinsa ya fice daga falon. Zaunawa tai saman kujerar tana kokarin daidaita fushinta.
AMMY POV.
Bayan Waziri ya gama zayyana mata komai, sai ta amsa masa da.
鈥淥kay babu wata matsalar zan saka Shattima ko Jarma ya wakilce shi tun da kai ba zaka samu zuwa ba鈥�
鈥淛arman ma yafi dacewa tun da shine Dattijo kuma kin ga abu ne na manyan mutane鈥�
鈥淭o sai a yi ma Jarma magana da wuri ya shirya komai kamin lokacin鈥�
鈥淶an sanar da shi鈥�
Waziri ya fada yana karantar yanayin matar dan'uwan nasa. Har ya mike tsaye da zimmar yai mata sallama ya fice sai kuma ya koma ya zauna ya kalleta.
鈥淗ajiya ko dai akwai wata matsalar ne?鈥�
Ammy ta sauke ajiyar zuciya, daga inda take zaune ta saka hannunta na dama ta rike kanta, a take idonta ya cika da hawaye abun ka da mai neman kuka an fada masa mutuwa.
鈥淚na cikin damuwa Waziri, na rasa da wanne zan ji, matsalar Nana ko ta Mai Martaba ko kuma ta maganganun da suke tasowa a masautar nan?鈥�
鈥淢atsalar Mai Martaba tana damun kowa, addu'a yake bukata da kuma kulawa, gulma kuma ta daina damunki daman duk daukaka ta gaji haka, za ka samu akwai hassada da kiyayya da kananan maganganu, sai dai Nana nake son na ji abunda ya same ta?鈥�
鈥淎bubuwan da take min bana jindadinsu, tun jiya take damuna da zancen sai an canja mata driver yau da safe har tsawa ta daka min akan haka, taya yarinyar da ke neman albarka za ta yi ma mahaifiyarta haka? Yanzu kuma na duba drawer dubu dari uku da saba'in na aje a ciki yanzu na duba na ga babu kudin sai dubu talatin da biyu suka rage, abubuwan da Nana take suna tsorata, kuma suna damuna, ba a nan kadai ba Nana ko dakin Mai Martaba ta shiga indai idonta ya ga kudi sai ta saka yadda tai ta dauke su, ina tsoron kar wannan abun ya zame mata hali, ga shi bata da natsuwa duk wani abu na masu hankali Nana ba ta yinsa....鈥�
Ta karasa hawaye na sauko mata, ba dan komai ta tsaya ta fada ma Waziri damuwarta akan Nana ba sai dan sanin shi ne kadai mutumen da zai tsawatarwa Nana ta ji kuma shine mutumen da idan ta fada masa damuwarta ko damuwar Masarautar nan yake fadi tashin ganin ya same mata mafita.
Waziri ya kankance ido irin na su na manya yana mamaki.
鈥淢e take yi da kudin da take dauka?鈥�
鈥淲allahi ban sani ba, amman kai kanka kasan babu abunda Nana ta nema ta rasa鈥�
鈥淶an daukar mata mataki kuwa, amman duk da haka ki rika gamawa da addu'a ta tsari da kuma ta shiriya鈥�
Sosai Ammy ta jidadin maganar Waziri domin tana ji a ranta kamar ba zata iya da Nana ita kadai ba. Har ta bude baki ta yi magana sai ta Yusra ta shigo dakin da gudu har tana haki.
鈥淎mmy Nana ta fadi ta ji ciwo gata can an kawo ta....鈥�
Tun kan ta karasa Ammy ta mike tsaye hankalinta a tashe ita da Waziri suka fita daga dakin. A kwance suka samu Nana saman gadonta an saka mata bandeji a kanta da kafarta da hannu, Shattima na tsaye tare da Hajiya Karama, Driver ba kuma yana daga bayansu jikinsa sai rawa yake. Da sauri Ammy ta zauna saman gadon ta taba jikinta.
鈥淢e ya same ki Nana?鈥�
Ta kalli Shattima da Hajiya Karama, sannan ta kalli Ammy, ko da wasa bata kalli Waziri ba domin yadda take tsoronsa ko mutuwarta albarka.
鈥淢ai Babur ya kade ni, na fito daga school ina jiran Driver ya zo ya dauke ni be zo ba har babur ya kade ni, sai wani ya kai ni asibiti aka saka min wannan shi ne ya kawo ni nan ma da motarsa鈥�
Nana na fadar hakan driver ya risina kasa yana rokon Ammy.
鈥淗ajiya dan Allah dan Annabi amin afuwa, uzuri ne ya rike ni shiyasa ban samu isa da wuri ba鈥�
Ammy bata ce komai ba sai duba jikin yarta take cike da damuwa.
鈥淵ou fired, saboda ita aka dauke ka aiki, then why all this? Har mai babur ya kade ta ta ji ciwo wani dabam ya kawo ta gida鈥�
Zainab ta fadawa driver, a take ya fara magiya yana kallon Ammy.
鈥淎n kore ka aka ce fita ka bar dakin nan鈥�
Ganin Ammy za ta yi magana yasa Shattima ya nanata masa abunda Zainab ta fada domin abunda yake da niyar yi kenan, cikin rashin dadin rai driver ya fice daga dakin fuskarsa kamar zai fashe da kuka.
鈥淢e kike son ki ci? I will cook for you鈥�
Ammy ta tambaye ta cike da kulawa, sai Nana ta kawardar fuska ita aka dole har yanzu fushi take da Ammy.
鈥淏ana son komai鈥�
Ammy ta hade abu da karfi sannan ta mike tsaye ta nufi kofar fita sai kuma ta juyo ta kalleta fuskarta da mamaki.
鈥淎mman ya akao kika fito ba lokacin tashi daga school ba? Ya akai suka bar ki kika fito? Yanzu fa karfe 11:40am how?鈥�
Shattima ya kalleta.
鈥淎mmy za mu yi wannan maganar daga baya yanzu dai ta samu lafiya鈥�
Ammy bata sake cewa komai ba ta juya ta fice. Sai a lokacin ne Waziri yai magana.
鈥淎n kori direban ko? To kin samu abunda kike so idan ma ke kika tsara haka saboda a kore shi burinki ya cika, amman bari na fada miki daga yau school bus ce zata rika kai ki makaranta tana dauko ki, ba ki wayar ki鈥�
Ya mika mata hannunsa sai tai saurin kallon Shattima tana son saka kuka, kai ya gyada mata alamar ta ba shi din, sannan ta kai hannu ta bude school bag dinta ta dauko wayar ta mika masa tana hawaye. Shattima ya zauna kusa da ita kenan Waziri ya ce.
鈥淒aga yau kar wanda ya sake daukar kudi ya bata ko ya siya mata waya, daga kai har Zainab shi ma Sirleem zan masa magana鈥�
Da mamaki Zainab ta kalleshi sai dai babu damar tambayarsa dalilin hakan dan ta fi kowa sanin waye Waziri.
鈥淶ainab je ki kira Baaba ta zo ta bincike dakin nan duk inda kudi suke ta fito min da su, kuma ta kwashe kayan kallon nan da system din nan bana son ganinsu a nan鈥�
Ta amsa masa ta to, sai da ta kalli Shattima sannan ta fice zuciyarta cike da tambayoyi. Waziri ya kalli Nana.
鈥淒a kin ji sauki ke za ki fara gyara dakinki da kanki, ba za a sake miki ba, ko tufafin da ke saka miki a wardrobe daga yau ke zaki saka idan sun yi datti ki wanke da kanki鈥�
Ta kankame Shattima tana fashewa da kuka.
鈥淲ayyo Yaya mutuwa zan yi鈥�
鈥淜in dade baki mutu ba鈥�
Waziri ya daka mata tsawa yana matsowa kamar zai doke ta, da sauri Shattima ya mike tsaye ya tare ta.
鈥淎yi hakuri Baba zan mata magana鈥�
Shi kan shi Shattima sai da Waziri ya watsa masa harara sannan ya fice daga dakin, wanda hakan yayi daidai da shigowar Baaba, a take ta hau aikinta sai da ta bincike dakin tsab ta fiddo kudi ba kanana ba har da dollars din da Nana take daukowa dakin Mai Martaba ta fito falo ta kawowa Waziri sannan ta kira Sarkin Dogarai ya cire tv da decoder da system din dake dakin. Nana na ji na gani aka kwashe kayan aka bar mata daki wayan daga gadonta sai wardrobe da dan karamin dinning dinta na karatu domin har hotunan artists da saka sai da Waziri ya saka aka cire su a lokacin da ya sake dawowa dakin dan ganin idan an yi yadda ya ce.
鈥淵aya Wallahi Baba Waziri da Ammy basa so na鈥�
鈥淪hiiiiiiiiii kar na sake jin wannan kwanta ki yi bachi idan kin tashi zan kira Doc Deen ya duba ki Okay鈥�
Ya daga masa kai sannan ya mike tsaye ya fice daga dakin. Tai saman gadon ta fara kuka na gasken gaske tana jin kewar mhaifinta domin ta tabbatar da yana raye babu wanda ya isa ya mata haka har shi Baba Wazirin da kansa. Can kuma ta fara murmushi mai sauti tunawa da yadda AA ya rude a lokacin da suka fadi din, sai a lokacin ta soma dariyar abunda ya faru tsakaninsu tun haduwar farko har zuwa yau.
FALMATA POV.
Cikin rashin jindadin ta isa gida tana jin ina ma ace tana da wata dama da zata hana kanta aiki a gidan da ta huta, domin abunda Zainab tai mata a yau be mata dadi ba ga Iya data saka ta gaba ga wahalar tafiya kasa kullum kuma ta dawo.
Sai dai babu yadda ta iya idan tace zata bar aikin ta san sakamakonta a gurin Umma wacce tai ruwa da tsaki ta sama mata aikin saboda ta rika bata albashin. Kamin ta isa gidan sai da ta biya ta gidansu kawarta Khadija ta su kai yar fira har ma ta kunan wakar Sirleem M2 a wayar Khadija ta kalli video wakar sannan ta wuce gida. Tana isa bata ko tsaya hutawa ba, ta dauki bokitin diban ruwa ta nufi bohol daman diban ruwa ne abu na farko da take idan ta dawo daga aikin, sannan tai surfe.
Haka ta cika komai na gidan sannan ta zuba surfe ta surfe iya wanda zata iya ta wanke ta bawa dabbobi kasarin, ita kuma ta debi ruwa tai wanka ta shirya cikin uniform dinta na islamiya wanda ya gama kodewa har ya fara yagewa a wani gurin ma. Ta dauki jakarta ta makaranta ta nufo dakin Iya.
鈥淯mma makaranta zan je鈥�
Iya ta hankada fillonta ta dauko naira talatin ta jefo mata.
鈥淜wadon da mu kai be ishemu ba, ga talatin nan ki siye awara ko dankali鈥�
鈥淭o na gode鈥�
Ta saka hannu biyu ta dauka sannan ta juyo ta fito daga dakinta idonta cike da kwalla. Idan zalinci da danne mata hakki ko kuma sakata aikin wahala ba yau Tumba ta saba ba, amman ta kasa sabawa a kullum idan akai mata sai ta yi kuka, cikin damuwa taje makarantar sai dai a yadda suke cikin ajin da dalibai ana wasa da dariya yasa ta waye kamar ba ita ba.
Kwalama ta siya da kudin a lokacin da suka tashi daga makarantar, bata ci abincin kirki ba sai da dare da aka sauke tuwo. A yau ma sai da wani ya sallamo mata wani dabam ba na jiya ba, shi ma ya mata siyaya kuma ya bata kudi after ya kunna mata wakar Sirleem M2 ta kalla a wayarsa. Yau kam kamin ta kwanta iya ta bata rubutun ta sha, hakan yasa da safe ba ta bata ba. Sai a kullum Falmata bata fashin bismillah idan zata sha addu'ar safe da yamma kuma ta zame mata jikin duk da karancin shekarunta.
Cikin tsoro da tunanin abunda akai mata a jiya ta shiga masarautar ga kuma tunanin haduwa da Iya. Sai dai har ta isa bakin kofar falon Ammy bata hadu da ita ba sai dai hakan be saka ta fidda ran haduwa da ita a dakin yaran ba ko a falon. Sai da ta karanta addu'ar neman tsari sannan ta danna door bell din, ba dadewa Nana ta bude mata kofar sai ta tsaya kallonta.
鈥淢e aka yi?鈥�
Har kasa Falmata ta sirina ta gaishe ta sannan ta ce.
鈥淶an gyara dakin yan uku ne鈥�
鈥淭o shigo鈥�
Nana ta matsa daga jikin kofar tana dingishi ta koma a set din kujerun farko da suke falon ta zauna ta cigaba da cin plantain chips. Da sauri Falmata ta shiga dakin ga mamakin yau kam sai ta samu Luma a kan gadon jarirai ta mike tsaye tana ta ihu sai zabura take kamar ana tsikararta. Da sauri Falmata ta karasa inda take tana kallonta.
鈥淟aaaaaaaaaaa鈥�
Ta fada tana kallonta cike da burgewa sai dai ganin yadda take zabura kamar mai tsoro yasa ta karanta ayatul kursiyu ta tofa mata a kai sannan tai bismilla ta kai hannu ta dauke ta tana mata wasa. Tana juyowa ta yi arba da Shattima tsaye bakin kofar yana kallonta fuska a hade. A rude ta aje yarinyar ta juyo ta kalleshi da sauri tana girgiza masa kai alamar ita ba ta yi komai ba.
鈥淲allahi Wallahi.... Wallahi ganin nai tana kuka tana zabura shiyasa nai mata addu'a kuma na dauke ta, Dan Allah kai hakuri na shiga uku鈥�
Ta fashe da kuka ta duka har kasa tana rokonsa kamar ance mata dukanta zai yi. Be ce mata komai ba ya karaso cikin dakin ya dauki yarsa wacce ke faman kuka tun da Falmata ta maida ita cikin gadon, be ce mata komai ba ya fice. Ita kuma bata fasa kuka tana nadamar abunda tai ba har ta yi aikin ta gama ta fito, ba karamin dadi ta ji ganin babu kowa a falon ta fice da sauri har lokacin hawaye take.
Sai da ta fito daga habarar Ammy sannan ta ji kamar ana binta a baya, da sauri ta juya suna yin arba da Iya gabanta ya buga da karfi.
鈥淪hattima ya ce a fada miki karki sake dawowa daga yau鈥�
Kasa cewa komai Falmata tai Iya kuma ta juya ta koma ciki tana rumgume da hannayenta a baya. Babu wacce ta fado mata a rai sai Tumba, ta san idan ta fada mata abunda tai aka kore ta zata kara mata da nata ne.
Sai dai ya zame mata dole ta fadi gaskiya dole ne ta fada mata gaskiya. A kullum idan zata je gida tana ganin tafiyar tana mata nisa amman ban da yau da take cikin tashin hankali sai ta ga kamar an ragewa hanyar tsawo.
03/12/2021, 08:09 - 馃馃馃馃: *馃悇馃悇 FULANI 馃悇馃悇*
By Khadeeja Candy
*7*
Dogon wando ne da da yellow t-shirt a jikinta, kanta ba dankwali gashin kanta na dunkule guri daya da ribbon, se kai tana ganinsa ka san ya kwana biyu ba a taba shi ba. Tana tafe tana dingishi har ta shigo cikin falon, Rima na kallonta ta dauke kai ta cigaba da damna wayarta, hakan yasa Nana ta ja mata tsaki kamar ba yayarta ba. Ta kalli Juwairiya wacce ke tambayarta abunda ya same ta.
鈥淎nty Jurry ima Hajiya?鈥�
鈥淭ana dakinta, Nana me ya same ki?鈥�
鈥淗adari na yi鈥�
鈥淕arin ya?鈥�
Nana ba ta ce mata komai ba ta nufi hanyar dakin Hajiya, bata ko yi knocked ba ta tura kofar dakin ta shiga tana kiran Hajiya wacce take ganin har ta fi mata Ammy. Hajiya da ke makale da waya a kunne tana ganinta ta sauke wayar da sauri tana fadin.
鈥淪ubhanallahi Daughter me ya same ki?鈥�
鈥淗adari na yi鈥�
Nana ta fada kamar zata fashe da kuka, da sauri Hajiya ta mika mata hannu alamar ta karaso fuskarta na nuna tsantsan damuwa. Nana ta karasa kusa da ita ta zauna bakin gadon sai Hajiya ta kwantar da ita jikinta.
鈥淕arin ya hakan ya faru daughter?鈥�
Irin karyar da tai ma su Ammy ita tai ma Hajiya.
鈥淎mman an kore shi ko?鈥�
鈥淵es Ya Shattima ya kore shi鈥�
鈥淒a ba a sallame shi ba, da sai na saka an hukunta shi sannan na masa korar wulakanci鈥�
Hajiya ta fada cikin bacin rai, wanda hakan ba karamin dadin yai ma Nana ba. Babu abunda ta rage bata fada mata ba akan abunda Baba Waziri yai mata jiya har da hawayenta. Hajiya ta shafa kanta tana murmushi
鈥淗aba daughter kar hakan ya dame ki, ba dai ina raye ba babu wanda ya isa ya taba ki, nan da kwana biyu zan maida miki duk wani abu da Waziri ya cire a dakinki, ni kaina ya min magana wai ni da Sirleem mu daina ba ki kudi ko siya miki wani abu, amman kin san ba zan yi haka ba ko? Domin ni ina kaunarki sosai鈥�
Nana ta rumgume ta.
鈥淣a gode Hajiya, za ki rika ba ni kudi?鈥�
鈥淪osai ma, duk lokacin da kike bukatar kudi ki zo ki min magana, amman fada min me kika masa?鈥�
鈥淣i ban masa komai ba, ban san miyasa yai min haka ba daman can shi baya so na ai鈥�
鈥淢u ai muna sonki, bari na kira Sirleem ya zo ya kai ki wata asibitin a duba ki鈥�
鈥淎 a Ya Shattima ya Kora Doc Deen ya duba ni jiya鈥�
Ta mike tsaye jin maganar asibiti, domin zuwa asibiti da allura sune manyan makiyanta a duniya. Hajiya ta mike tsaye ta nufi wardrobe dinta ta bude ta dauko kudin da za su kai 20k ta juyo ta dawo kusa da Nana ta mika mata kudin.
鈥淜arbi wannan ki siye wani abu鈥�
Da sauri Nana ta saka hannu ta karba tana murmushi.
鈥淣a gode鈥�
Murmushi Hajiya tai mata a respond ita kuma ta saka kudin cikin aljihun wandonta ta juya tana dingishin ta fita daga dakin, Hajiya ta bita da kallo tana murmushi. Hakan da Hajiya tai mata ba karamin dadi yai mata ba, daman can ta san babu mai sonta sai Hajiya domin ta fi kowa sakar mata kudi ita da Hajiya Karama. Sai da ta fito daga bangaren Hajiya gaba daya sannan ta fiddo kudin ta karga 20k ne cif ta maida a inda ta saka dazun sannan ta nufi hanyar da zata sadata da bangarensu.
鈥淚magine Muhseen ya tafi be min sallama ba鈥�
Cewar Zainab tana mamakin tafiyarsa ba tare da saninta ba.
鈥淵ana busy daman Mama Fulani kawai ya kawo, any problem?鈥�
Shattima ya fada ba tare da ya kalleta ba.
鈥淣o kawai na ji tafiyar ta sa a ba za ta ne, ita ma Mama Fulani ban ganta ba ai ko tare suka tafi?鈥�
鈥淭ana cikin garin gurin yan'uwa鈥�
Ya bata amsar still be kalleta ba sai aikin taba System dinsa yake, ita kuma tana shafa wani mai a fuskarta jikinta sanye da sleeping dress wando da riga. Suna haka Nana ta shigo falon ta nufo inda suke tun kamin ta zauna Zainab ta ce.
鈥淎mmy na nemanki鈥�
鈥淢e nai?鈥�
Zainab tai murmushi
鈥淪ai kin yi wani abu Ammy zata nemeki? Haba Baby ta shiga dakinki bata ganki ba na fada mata kin tafi bangaren Hajiya, tace idan kin dawo na turo ki鈥�
Ta juya ba dan ranta ya so ba ta nufi dakin Ammy, a kasan carpet ta samu Ammy zaune rike sanye da hijab hannunta rike da carbi. Ta karasa ta sauna bakin gadon tana turo baki tana kin kallon mahaifiyarta. Ammy ba ta bi ta kanta ba ta kalleta a natse ta ce
鈥淵a jikin na ki?鈥�
鈥淒a sauki鈥�
鈥淣a shiga dakinki ban same ki ba, Zainab tace kin je bangaren Hajiya Balki me kika je yi?鈥�
鈥淣aje na fada mata duk abunda Baba Waziri yai min鈥�
鈥淒a kika fada mata sai ta miki maganin me?鈥�
Turo baki tai ta mike tsaye ta nufi hanyar fita sai da Ammy ta daka mata tsawa.
鈥淣ana....! Ina magana zaki tashi ki fita?鈥�
Ta juyo tana turo baki amman bata dawo ta zauna ba.
鈥淒aman ai na san ba so na kike ba, gidan nan daga Ya Shattima sai Hajiya Karama sai Hajiya Babba kadai ke so na, sai Mai Martaba....鈥�
Mikewa tsaye Ammy tai ta karasa inda Nana take ta fisgeta iya karfinta ta jefar kasa sai da kanta ya bugi gadon dakin. A take Nana ta bude baki ta fara ihu daman kukanta na kusa, da gudu Zainab da Shattima suka shigo dakin, Zainab ta nufe ta da sauri ta rika ta.
鈥淏an mata komai ba ta jefar da ni kasa鈥�
Ta fada cikin kuka tun kan Zainab ta tambayeta.
鈥淥kay tashi muje room dinki鈥�
Da taimakon Zainab ta mike tsaye suka fice daga dakin. Shattima ya zauna kusa da mahaifiyarsa yana karantar yanayinta.
鈥淎mmy ki rika dagawa Nana kafa she is still young, ba isa tai irin wayon da kike so tai ba鈥�
Ammy ta kalleshi.
鈥淲ata yarinya kamar ta tana da hankali da tunani, wata yarinya kamarta ta san ciwon kanta, Nana ban isa na ce kar ki yi ba ta bi umarnina, ban isa na hana ta ba ta hanu, bata san komai ba sai a bata kudi ayi mata kaza, abunta ya fara yawa ace Nana idan ta ga kudi sai ta saka hannu ta sata?鈥�
鈥淣onono Nana ba zata taba haka ba In-Sha-Allah, Ammy ki daina mata wannan fatan, tana dauka ne saboda tana ganin a gidansu ne, kuma wannan halin da ta yi wayo zata daina鈥�
Ammy bata ce komai ba ta sauke ajiyar zuciya. Jin muryar Hajiya Babba yasa Shattima mikewa tsaye ya fito falo. Cikin girmamawa ya gaisheta ta amsa mishi da far'arta kamar ko yaushe tana kare masa kallo.
鈥淗ajiya Zainab tana ciki?鈥�
鈥淓h tana ciki鈥�
Binsa tai da kallo sai da ya isa gurin system dinsa sannan ta dauke kai ta tura kofar dakin Ammy ta shiga. Daga bakin kofar dakin ta tsaya tana kallon Ammy.
鈥淗ajiya Zainab kin kyauta kenan?鈥�
Ammy ta mata kallon rashin fahimta.
鈥淢e ya faru? Karaso mana kika tsaya daga bakin kofa鈥�
鈥淎 a bar ni a nan da ina da muhimmaci a gareki ai da kanki zaki aika min abunda ya samu Nana, ko ba komai Nana yata ce kuma surukata ina hakkin sani鈥�
Surukata yafi komai yi ma Ammy za fi domin har ga Allah bata son hadin nan na Sirleem da Nana, sai dai babu yadda ta iya tun da sai da aka tambayi Nana da kanta tace tana son shi sannan akai musu baiko. Murmushi karfin hali Ammy tai tana kokarin maida abun ba komai ba.
鈥淗aba dai, dan 蓷an wannan sai ace sai an tashi hankalinki, garin shiritarta ne taje ta ji ciwo kuma ba wani rauni ne sosai ba, kin dai san halin Nana da raki shi ne kawai鈥�
鈥淯hmm ko da ace ba ni na haifi mijin da Nana zata aura ba, na ga dai nima uwa ce a cikin gidan nan, ko ciwon kai Nana take ya kamata a fada min, abunda kike yi sam ba yi ba ne, yau idan Mai Martaba ya fadi ya mutu haka zamu tai zama cikin rashin hadin kai? Idan yau kika fadi kika mutu ni zan rika Nana ya kamata dai a gyara...鈥�
Tana fadar hakan ta juya ta fice daga dakin rai a bace sai dai bacin ran na iya fuska ne be kai zuci ba. Ammy kuma ta ja dogon numfashi ta sauke ta lumshe ido. Ba tun yau indai ta hadu da abokiyar zamanta sai ta fada mata wata maganar marar dadi, me ya kawo maganar mutuwar Mai Martaba ko nata a nan? Kan abunda be kai ya kawo ba?
Sai da ta fice daga bangarensu sannan Shattima ya mike tsaye ya rufe system dinsa ya dauke ta ya nufi dakin Nana. Zaune ya same su ita da Zainab suna ta kyalkyalar dariya bakin kofar ya tsaya yana kallonta yana murmushi.
鈥淵a Shattima zo nan鈥�
Ya karasa ya zauna dayan side dinta da ta nuna masa da hannunta.
鈥淢e kuke kallo?鈥�
鈥淐omedy鈥�
Ta amsa masa tana karbar wayar daga hannun Zainab ta mika masa. Kadan ya kalla ya mike tsaye.
鈥淎 sha kallo lafiya鈥�
Ya juya ya fice, ita ma Zainab din ta mike tsaye.
鈥淏ari naje mai wanka kamin na shirya kin gama鈥�
鈥淥kay鈥�
Ta cigaba da kallon hankalinta kwance bayan Zainab ta fice. Shattima na fita daga dakin Nana ya nufi dakin da ya aje yaransa ya dauko su ya dawo da su dakinsu wanda Falmata tai masa tas sai kamshi yake.
FALMATA POV.
Kamar wacce zata sanarda mutuwar wani haka ta shiga cikin gidan cikin tashin hankali da fargaba ga tsoron da ya cika mata zuciya har ya bayyana a fuskarta. Tun daga sallamarta zaka fahimci akwai damuwa da tashin hankali a tare da ita balle kuma idan kai arba da fuskarka.
Kamar mai koyon tafiya haka ta karasa kusa da Tumba da ke aikin tsintar shinkafa ta risina kan ta ce komai hawaye ya fara isar da sakon abunda zata sanar.
鈥淯mma dan Allah ki yi hakuri鈥�
Umma ta aje tray shinkafar tana mata kallon uku saura kwata.
鈥淏an gane na yi hakuri ba, me kika min macuciya?鈥�
Ta fara yarfar da hannu.
鈥淪un kore ni daga aikin鈥�
A take Umma ta saka, sam bata kawo kora daga aiki Falmata zata fada ba, a daukarta wani laifin tai mata na dabam.
鈥淎mman wannan Ya kin iya bakinciki, dan kudin da zan samu kike wa Hassada? Ni zaki yi ma cuta?鈥�
Da sauri Falmata ta girgiza kai tana wani irin kuka mai ban tausayi.
鈥淎 a Wallahi ba dan shi ba ne鈥�
鈥淭o me kika yi ma wai suka koreki? Taya za su kore ki haka nan kawai ba tare da kin musu komai ba?鈥�
Bata boye komai daga abunda ta aikata ba wanda take kyautata zaton hakan ne yasa aka koreta, wato tofawa Luma Addu'a har mahaifinta ya gani.
鈥淭o uban waye ya kai ki yi musu addu'a ke ashibi yar neman yabo ko? Makira shegiya yar iskanka, ni za ki yi wa bakinciki? Bari Babanki ya dawo sai na miki wanda ya fi wannan鈥�
Tana fadar hakan ta mike tsaye ta kai hannunta a kirjin Falmata ta fara murzar kirjinta iya karfinta. Wani irin kuka Falmata ta saka tana rike hannun Umma.
鈥淯mma ciwo mutuwa dan Allah ki yi hakuri鈥�
Bata saurareta ba har sai da ta murja iya yadda take cin zata cutarta da ita, tun da ta san idan aka murza kirjin burduwa mai tasowa ciwo take ji sosai. A rana Falmata ta wuni da kirjin nata kamar dutse yana ta mata ciwo bayan nauyin da yai mata. Bayan sallah isha'i tana zaune saman tabarma ita da Naja sai dariya take mata, ita kuma ta takure guri daya tana ta tunanin abunda Umma zata saka Baba yai mata sai ta ji sallamarsa, wani irin tashin hankali ta ji kamar ance mata ga mutuwarta nan. A yau Naja ce ta amsa sallamarsa taje ta karbo ledar hannunsa tana masa sannu da zuwa sai far'a take.
鈥淏aba sannu da zuwa鈥�
Falmata ta fada muryarta na rawa tana masa wani irin kallon tsoro dan ji take kamar ma Umma ta mata sherin ne. Sai akai sa'a yana kawowa daidai inda take tsaye Tumba ta fito daga dakinta tana fadin.
鈥淭o Malam sai ka san abun yi, Fulani dai so take ta lalace, kama ta nai a kofar gida ita da wani da ban san ko waye ba yana taba mata kirji鈥�
A bala'in firgice Falmata ta mike tsaye tana kallon tana kallon Umma, a take Umma ta zaro mata ido.
鈥淜o karya na ke?鈥�
Falmata ta girgiza kai da sauri.
鈥淎 a ba karya kike ba Umma amman Wallahi ba zan kara ba dan Allah kui hakuri....鈥�
Tun kan ta karasa Baba ya wanke mata fuska da mari biyu masu kyau, yasa kafarsa ya shure kafafuwanta ta fadi kasa tana jin kamar babu naman fuska a fuskarta, ga kunnenta yayi wani dummmm jin tai yai dogon zango, kamar an aiko shi haka ya hau dukanta yana fadin shi zata kawa abun kunya, gaba daya ta kasa kuka komai ya zo mata kamar a mafarki ga shi bata jin komai daga cikin abunda Baba yake fada kamar mai dukan Namiji haka Baba ya rika shurin Falmata yana dukanta har da saka kafarsa ya danne mata ruwan ciki sai da tai amai sannan Umma ta rugo da gudu ta rike shi tana kuka.
鈥淗aba Malam daga fada maka abun dan ka mata fada sai ka hau yi mata wannan dukan, idan ka kashe ta fa, yarinya marainiya zaka mata wannan dukan鈥�
Kuka take riri tana fadin haka iya karfinta wanda hakan yasa makonta su shigowa suna tambayar ba'asi, babu abunda ta rage sai ma kari da tai cewar wani ta gani yana taba kirjin Falmata. A lokacin ne Falmata ta ji wani irin kuka ya zo mata da karfi ta shiga ambaton Allah tana kiran mahaifiyarta da bata raye.
鈥淚nnalillahi wa'inna ilaihirraji'un, Mama Mama Mama Mama Mama, na shiga uku mutuwa zan yi, Bana jin komai Mama Baba Baba鈥�
Ta unkura zata tashi ta ji ba zata iya ba, hakan yasa ta koma ta kwanta a kasan ta rike kunnuwanta tana wani irin kuka mai shiga zuciya. Tumba ta nufi inda take ta rika tana kuka kamar ba ita ta kitsa komai ba, kokarin dagata take amman Falmata ta kasa tashi sai kuka take. Mutane wasu na bata hakuri sai dai mafi yawa sun girgiza da jin dalilin dukan da mahaifinta yai mata, domin Falmata yarinya ce mai natsuwa da kamun kai wacce ake ganin kamar wata yarinyar matashi irinta a unguwar, wasu cewa suke sai dai idan saurayin ne yake son lalata amman Falmata ba halinta ba ne, wasu kuma sun yarda wanda hakan bacin suna a gareta da kuma tarbiyarta, a yadda kowa yakr ganin Tumba tana rikon Falmata tana mata gatan da bata yi wa Naja ma da take yarta sai suka yarda da abunda ta fada a ganinsu ba zata mata sheri ba.
Har aka ci aka shude Falmata na kwance a gurin tana kuka, bata jin abunda mutanen suke fada har sai idan sun yi da karfi, fuskarta ya kumbura sosai kafarta sai ciwo yake kamar an cire mata shi, sai da dare ya raba sannan ta rarafa daker ta shige dakinsu bata ko karasa kan shimfidarta ba ta kwanta a gurin a kasa tana kuka a hankali, babu komai a ranta sai kewar mahaifiyar ta kalaman da tai mata na bankwana.
鈥淶an tafi na barki ciki taradadi Fulani, Allah ya zama gatanki, na san za ki sha wahala kuma za ki ga banbanci da kiyayya, amman ki rike Allah shi sai miki gata, kuma kar ki yi wasa da addu'a鈥�
Mama..... Ta kiran sunan mahaifiyarta a hankali tana jin kamar ace tana kusa da ita, sai kuma ta fashe da matsanaicin kuka.
__________
Falmata baiwar Allah Iya ta ja miki wahala yau 馃槶
Nana yar...... 馃
03/12/2021, 08:09 - 馃馃馃馃: *馃悇馃悇 FULANI 馃悇馃悇*
By Khadeeja Candy
*8*
Da wani irin zazzabi Falmata ta farka, fuskarta ta kumbura gaba daya jikinta sai ciwo yake idonta ma ya kumbura sosai sakamakon kukan da ta kwana tana yi.
Babu abunda ta fasa daga cikin aikin gidan da ta saba, ta sani sarai idan ta saka kuiya ko tace ba zata iya ba wani karin wahalar ne. Tana aikin tana kukan zuci har ta yi ta gama, ta dawo dakinsu ta zauna ta gefe daya dan bata iya zama daidai.
Tumba ce ta shigo dakin tana kare mata kallo.
鈥淏a za ki tashi ki je gurin aikin ba?鈥�
Kallon Tumba tai kamar zata fasa kuka, bata jin abunda ta ce sai dai tana ganin bakinta na motsi.
鈥淏an ji komai ba Umma鈥�
Ta fada muryarta na rawa kamar yadda jikinta ma yake rawa dan ganin take kamar dukanta Tumba za tai ko ta sake mata wani mugun sherin. Wani kallo Tumba tai mata.
鈥淣i za ki fara yi wani sabon siyasa?鈥�
Ganin Tumba ta nuna kanta da yatsa yasa ta nemi duk inda wani kuzari yake ta tattaro shi ta saka a jikinta ta mike tsaye ta karasa kusa da Tumba dan jin abunda take fada.
鈥淲allahi ban ji me kika ce ba Umma bana ji sosai鈥�
Ta fada kamar zata fasa kuka, Tumba ta san Falmata ba zata mata karya ba, ba zata mata haka da gangan ba, yanayinta kadai ya isa ya sanar da gaskiyarta.
Tumba ta dan tabe baki, sai a lokacin ne take girmama marin domin ba marin wasa Baba yai ma Falmata ta ba, gashi fuskarta har ya kumbura.
鈥淐ewar nai ki tashi ki tafi aikin鈥�
Tumba ta fada cikin daga murya ta maimaita mata ta yadda za ta ji. A take Falmata ta fara murza yatsun hannunta so take ta sake tuna mata cewar sun koreta amman sanin waye Tumba yasa dole tai shiru ta sauke kanta kasa.
鈥淏a za ki je, ki ba su hakuri ba?鈥�
Wannan karon ta ji domin Tumba da karfi tai maganar.
鈥淭o鈥�
Amsa tana motsa jikinta daker domin ba karamin tsami yai mata ba. Tumba ta juya ta fice daga dakin. Falmata ta nufi gurin da Hijabinta yake ta dauka ta saka ta fito. Da gangan Tumba ta kira ta karbi dumamenta ganin Baba na tsaye yana shirin tafiya.
Falmata ta nufi inda Tumba take da zimmar karba ba dan ta ji abunda tace ba sai dan ganin tana miko mata kwanonta. Ba dan tana jin yunwa ba domin komai ya fitar mata a rai, kan ta karasa Baba ya daka mata tsawa.
鈥淜ar ki karbi abincin nan, ba za ki sake cin abincin gidana ba, tun da kika zabi iskanci....鈥�
Cak Falmata ta tsaya ta kasa karasawa gurin da Tumba take zaune taka miko mata dumamen, ta ji abunda Baba yace saboda yanayin muryarsa irin mazajen nan da idan suna magana daga murya suke, balle kuma ita da baya iya yi mata magana a hankali.
鈥淗aba Malam ba a horo da yunwa, na san Falmata ta yi laifi amman ka dubi girman Allah ka yi hakuri, ba a biye ta yaro鈥�
鈥淣i dai na fada miki ban yafe a bata abincin gidana ba, ba zan ciyar da karuwa ba鈥�
Ya fada kai tsaye sannan ya nufi kofar fita ko inda Falmata take be kalla ba. Baki sake Falmata ta bishi da kallo hawaye na sauko mata zuciyarta na mugun kuna, kamin ta kalli Tumba wacce ke kukan karya.
鈥淲allahi da na san haka abun zai zama da ban fada maka ba, wannan abu be min dadi ba ni Ramatu鈥�
Bata iya ji yo komai amman tana gani ganin yadda bakinta ke motsi ta san da kuma kukan murnafurcin da take, ta san ta shirya komai ne. Daker Falmata ta hade abun da ya tsaya mata a wuya sannan ta nufi kofar fita tana jin kamar ta mutu a yau ta huta, taya zata rayu a idan ubanta kuma ace ba zata ci abincin gidan ba? Miyasa Tumba zata mata haka? Me tai mata? Saboda ta fadi gaskiya? Mi ya kaita fada mata gaskiyar? Miyasa ma yasa ta aikata tun farko? Tana tafiya tana tambayar kanta tambayar da bata da amsa hawaye sai aikinsu suke a fuskarta.
Gidansu kawarta Khadija ta nufa, sa same a tsakar gidan tana wanki kasancewar yau assabar babu school, Khadija na ganin Falmata hankalinta yai mugun tashin.
鈥淚nnalillahi ke lafiya me ya same ki?鈥�
Bata ji abunda Khadija tace ba amman tabbas ta ga bakinta na motsi. Hakan yasa Falmata ta fashe da kuka, ta sani an nakasata kenan.
鈥淜hadija Umma ta min shari ta ce Baba ta ga namiji yana taba ni, Baba ya min mari biyu kuma ya doke ni, ya ce kar a sake bani abincinsa, Khadija bana iya ji yanzu sai an yi magana da karfi na shiga uku鈥�
Wani irin rirrike Khadijar take tana fadin kukan kan ya samu hanyarsa, a take Khadija ita ma ta fashe da kuka ita da kawarta aka rasa nai rarrashi wani. Mahaifiyar Khadija ta saki tsintsiyar hannunta tana hawaye.
鈥淲ai me kika tarewa matar nan ne? Wani irin zallumci ne wannan?鈥�
鈥淎llah ya isar miki Falmata Allah ya saka miki鈥�
Khadija ta fada cikin kuka, kamin ta kama kawar tata su nufi baranda su zauna. A gidan Falmata tai wuni Maman Khadija da Khadija suka kitsa mata idan ta koma ta ce wa Falmata taje gurin aikin ta ba su hakuri sun maida ta.
鈥淜ullun idan ta tura ki aiki ki dawo nan ki zauna sai lokacin komawarki gida yayi sannan ki koma, abinci kuma ki zo nan ki rika ci kullum鈥�
Maman Khadija ta fada mata a kunne cike da tausayawa, domin idan bata mata rada ba ba zata ji abunda tace ba. Falmata ta gyada kai.
鈥淣a gode鈥�
鈥淏abu komai ai yiwa kaine, wannan rashin imani na Tumba yayi yawa, ko dan tana ganin bata haifa ba ne take haka? Wannan wace irin zuciyata ce?鈥�
鈥淎llah zai saka mata In-Sha-Allah鈥�
Khadija ta fada tana sharewa Falmata hawayenta. Sai da Falmata ta auna lokacin komawarta sannan ta fita daga gidansu Khadija ta kama hanyar gida tana ta jin tsoro domin gani take kamar asirinta zai tonu Umma ta gano bata je aikin ba.
AA POV.
Tun shekaranjiya da yai hadari da Nana be sake fita aiki ba, ba dan kuma baya iya fitar ba, sai yai amfanin da accident din da yai yace musu ba shi da lafiya zai dauki sati yana jinya, tsoro ya cika masa ciki yana ganin kamar idan yaje zai iya haduwa da Nana ta kira wani tace gashi nan a kama shi wata kila ma Babanta Soja ne ko Alkali a masa daurin goro. Anti Rabi kam ba a magana domin ko kofar gidan aka taba sai ta ji kamar zuwa za ayi a tafi da ita da AA.
鈥淏abu irin gargadin da ban maka ba, amman baka ji ba, gashi nan ka je ka kwaso mana abu kai baka cikin natsuwa ni bana ciki鈥�
Kallon Anty Rabi yai yana murmushi, duk irin tsoro da fargabar da yake idan ya tuna Nana da yadda take wasu dabi'un sai ya samu kansa da annashuwa, ba laifi tana da wauta and he likes that ko dan kudin da take sake masa.
鈥淏abu fa wani abu Anti, da za su kamamu ai da ba za su kai yanzu ba a nemo inda nake ba, ina tunanin bata fada ba ne saboda ita ma bata da gaskiya ai鈥�
鈥淗mm ka sani ko ana can ana nemanka?鈥�
鈥淚dan nemana ake ai ta san gidan nan, kuma ta san inda na ke aiki鈥�
Ya fada har lokacin murmushi yake.
鈥淢aybe yar farin ce tana da wauta sosai鈥�
Ya fada a fili sannan ya mike tsaye, da gaske he miss her, Allah ka dai ya san irin karyar da tai, da kuma irin sakin da za tayi, no wait ta ma isa gida? What if inda ya barta wani abun ya same ta? Ko ta bi wani kamar yadda ta bishi, ai ba kowa ne na gari ba right? Idan ta nunawa wani kudi zai ma iya kidnapped dinta. A take hankalinsa yai mugun tashi wayarsa dake aljihunsa ya ciro ya chiga contacts sai a lokacin ya tuna ai shi ya bata number sa kuma bata kira shi ba.
Gaba daya sai ya ji ba shi da natsuwa tunaninsa be kawo masa haka ba sai yanzu, and if wani abu ya same ta shi ne sanadi, domin shi ya barta a gurin kuma ya san abunda yai be kyauta ba. Gaba daya sai ya ji hankalinsa yai mugun tashi, be bari Anti Rabi ta fahimci komai ba ya shiga dakinsa ya cire vest din jikinsa ya dauki wata bakar t shirt ya saka ya fito.
鈥淎nti bari na leka nan waje鈥�
鈥淭o Allah dai ya tsare idan ka ji baka natsu ba ka dawo gida dan Allah鈥�
鈥淥kay In-Sha-Allah鈥�
Sai da yai addu'ar fita daga gida sannan ya fita gidan. Kai tsaye gurin aikinsa ya nufa duk da ya san ba lallai ne ya ganta ba, sai dai sanin cewa tana yawan zuwa gurin wata kila ma an zo nemansa.
SHATTIMA POV.
Ya saba every end of the week yana ziyartar dakin motsa jiki, but wannan karon sati biyu be je ba saboda be samu zama ba. Hakan yasa yake jin jikin kamar ba nasa ba, tafiya yake a hankali kamar wanda baya son taka kasa da daidaiya yake bin ko'ina da kallo har ya shigo bangaren mahaifiyarsa.
A falo ya tararda yaransa, Iya na zaune kusa da su tana musu wasa sai dai gaba dayansu wani laye suke kamar basu jin bachi.
鈥淏abban Mutum an shigo?鈥�
Iya ta fada baki har kunne.
鈥淓h Iya ya gidan?鈥�
Ya amsa mata yana leka yaransa.
鈥淕ashi nan fa sun sha ado, yanzu na gama gyara dakinsu鈥�
Da mamaki ya kalleta.
鈥淢ai gyaran bata zo ba ne?鈥�
Iya ta tabe baki tana mikewa tsaye.
鈥淲annan yarinyar, bata zo ba, wata kila sai gobe ko jibi鈥�
Shattima be ce komai ba, but maybe dan ta kamata tana yi ma yaransa addu'a ne yasa ta ji tsoro ta ki dawowa.
鈥淜arka damu ba dole sai an kawo wata ba, ni kaina zan iya kula da su da dakinsu鈥�
Dan murmushi yai.
鈥淗aba Iya ai ba girmanki ba ne, idan bata dawo ba dai za mu samu wata鈥�
Iya ta yi murmushi tana kallonsa.
鈥淗aka ne Allah ya taimaka, bari na maida su dakinsu鈥�
鈥淎mman a samo wacce zata tsaya da su bana son a na barinsu su kadai鈥�
鈥淎n gama Babban Mutum鈥�
Ta amsa masa har da dan risinawa, shi kuma ya wuce dakin mahaifiyarsa. Kwance ya same ta waya a hannunta tana latsawa, sai da ya zauna sannan ya mika mata gaisuwa. Sai ta dago ta kalleshi.
鈥淟afiya Kalau Shattima鈥�
鈥淎mmy ina tunanin gobe zan koma鈥�
Bata ce masa komai a har na tsawon minti uku. Hakan yasa ya sake cewa.
鈥淎mman ba zan yi dadewar wacan lokacin ba zan dawo鈥�
鈥淵a dai kamata ka nemi transfer gaskiya, ka fi kowa sanin halin da mahaifinka yake ciki鈥�
Kwankwaso kofar dakin da akai ne ya hana shi cewa komai, be kuma dago ta kalli kofar ba, sanin wanda ya shigo dakin ba bayan Ammy ta ba shi umarni, kamshin turaren kadai ya isa ya sanar nasa cewer Sirleem ne domin ya san kalar turarensa kamar yadda Sirleem din ma ya san na Shattima. A kasa ya zauna yana mikawa Ammy gaisuwa sai ta amsa masa da murmushi tana kokarin tashi daga kwancen da take.
鈥淵a gida ya aiki?鈥�
鈥淎lhamdulillah, dazu Hajiya ke Fada min Nana ta samu accident鈥�
鈥淓h amman da sauki sosai鈥�
鈥淎llah ya tsare gaba鈥�
鈥淎min鈥�
After some minutes ya mike tsaye yana mata sallama.
鈥淪hattima ba ku gaisa ba鈥�
Daga shi har Shattiman ba su dadin maganar Hajiya ba. Domin kowa jin kansa yake ba ma kamar Shattima, ko da wasa Shattima be dago ya kalli Hajiya ba gudun kar ta masa umarni da ido cewar ya gaisa da Sirleem domin shi ya cancanci Sirleem ya gaushe shi ko dan neman auren kanwarsa da yake. Sirleem ya kasara inda Shattima yake zaune ya mika masa hannu sanin cewar idan za a shekara dari a haka Shattima ba zai ce masa uffan ba.
鈥淪hattiman ai ban kura da kai ba sai yanzu鈥�
Sirleem ya fada yana mika masa hannu. Hannun kawai Shattima ya mika masa suka gaisa ba tare da ya kalli Sirleem ba balle har wata kalma ta fito daga bakin Shattima. Sai da Sirleem ya nufi kofa sannan Shattima ya daga kai ya kalleshi, sai kuma ya dauke kai ya kalli mahaifiyarsa wace ke kallonsa tun lokacin da Sirleem ya mika masa hannun.
Sam Sirleem be jidadin abunda Shattima yai masa ba, ya sani ba tun yau Shattima ya saba nuna masa cewar shi ne dan masu gida shi kuma agola, ba shi kadai ba har Zainab wacce kusan matsayinsu daya da shi haka take nuna masa isa tana takama.
Kamin ya karasa fita falon Nana ta kira shi.
鈥淵a Sirleem鈥�
Juyowa yai ya kalleta be ce komai ba, sai da ta kalli kofar corridor dakin Ammy sannan ta karaso inda yake.
鈥淵a jikin na ki?鈥�
鈥淣a ji sauki, Ya Sirleem ban karya ba鈥�
鈥淲hy?鈥�
Ya tambaya cike da mamaki ganin har 5pm ta kusa ace bata karya ba. Sai da ta sake kallon corridor sannan ta ce.
鈥淒an Allah zaka kai ni restaurant na ci abinci? Amman karka tambayi Ammy?鈥�
Ya kalli inda take kallo sai kuma ya kalleta kamar ya musa mata sai kuma wata zuciyar ta hana shi.
鈥淎lright muje鈥�
鈥淜aje can bangarenku ka jira ni, bari na dauko mayafina鈥�
Har ta juya sai ya kira ta ta juyo.
鈥淣ana... An hana ki fita da ni ne ko me?鈥�
鈥淶an fada maka a mota kaje can ka jira ni鈥�
Bata tsaya jiran abunda zai ce ba ta koma dakin ta dauko kudin da Hajiya ta bata 20k ta saka a cikin skirt dinta sannan ta saka wani karamin veil ta fito da gudu kamar ba ita ce ke ciwon kafa ba. Kamar wacce tai wani kaifi take tsoron a ji haka ta sauka stairs din ta nufi bangarensu Hajiya gabanta sai faduwa yake kar tai arba da Shattima ko Zainab ko wani wanda zai fadawa Ammy ta fita tare da Sirleem.
Can bangaren Hajiya ta nufa sai dai bata shiga ciki ba ta nufi gurin da motocin gidan suke, tun kan ta karasa ya bude mata front seat tana shiga ta rufe motar da sauri.
鈥淴&Y restaurant za mu je, kuma ba fita za ka yi ba, ni zanje nai mana takeaway Please鈥�
Jinginar da kansa yai jikin motar yana kallonta. Can kuma ya tashi motar suka fara tafiya.
鈥淲aya hana ki fita da ni hala?鈥�
鈥淏abu鈥�
Da bashi amsa tana taba kudin da ta boye jikinta dan ta tabbatar idan suna nan.
03/12/2021, 08:22 - 馃馃馃馃: *馃悇馃悇 FULANI 馃悇馃悇*
By Khadeeja Candy
*10*
FALMATA POV.
Haka ta kwana da ragowar yunwa a cikinta, washe gari tun da asubar fari Tumba ta fito ta fara kunna wuta a lokacin Falmata na waje tana alwala sallah asuba, baya ta gama ta shiga daki ta dauki hijabinta zata saka tai sallah sai ta ji an rikota sakamakon kiran da ta yi ta mata bata ji ba.
鈥淜arki sallah bari ki yi wanka鈥�
Ta rada mata a kunne, ba ta isa tace mata bari na gama sallah ba, dan haka ta aje Hijabin ta fito bakin kofar dakin ta zauna tana ta kallon wutar da Tumba ke ta aikin fetawa tana tura ledodi, nan da nan ruwan sukai zafi sai ta dauko wani garin magani ta zuba a cikin ruwa ta juya shi sannan ta sauke ta tsirka mata da ruwan sanyi.
鈥淶o dauki ga shi nan ki yi wanka maganin tsari ne鈥�
Tana maganar tana mata alama da abunda take nufi irin yadda ake ma kurame. Falmata ta tashi daga inda take zaune ta dauki ruwan maganin ta shiga bandaki ta cire kayan jikinta ta watsa ruwan ta fito. Da hannu tai mata a alama da ta zo, sai Falmata ta aje bokitin hannunta ta karasa inda take tsaye, duba ta tai dan ta tabbatar idan ta yi wanka, ga kuma shaida ta gani maganin ko'ina a jikinta.
鈥淭o je ki yi sallah ma鈥�
Nan ma alamar kurame tai mata, sai Falmata ta juya ta shige cikin dakin ta dauki wasu tufafin ta saka ta saka hijabinta ta fara sallah.
Bayan ta gama tai addu'ointa kamar yadda ta saba sannan ta fito ta gyara ko'ina na gidan tai wanke wanke, ba ta ko tsaya tambayar abincinta ba ta fice da zimmar zuwa gurin aikin karya.
Tana tafe tana nemawa kanta mafita, ta sake komawa gidansu Khadija ko kuma dai ta koma gurin aikin ta sake ba su hakuri? Domin idan wata yayi Tumba zata tambayi kudinta na albashi to me za ta ce mata? To idan ma ta koma za su karbe ta ne? Sai ta rasa wanda za tai, daga karshe dai ta yanke shawarar zuwa gidansu Khadija domin har ga Allah ita yanzu tsoron zuwa gidan can take, abun da bata sani ba Naja na biye da ita a baya tana lekenta kamar yadda Tumba ta saka ta. Sai dai ita bata lura ba har ta shige cikin gidansu Khadija. Yau kan bata samu Khadija a gidan ba dan ta tafi islamiyar safe kasancewar yau Sunday, Maman Khadija bata tsaya komai ba ta zubo mata abinci, Falmata ta zauna ta ci sai da ta koshi sannan ta nemi guri ta kwanta tai ta bachinta. Sai kusan azahar sannan Khadija ta tashe ta, firgigit ta mike tsaye dan lokacin komawarta gida yayi har ma ya dan gota.
Duk yadda Maman Khadija da ita Khadijar kanta suka so Falmata ta tsaya ta ci abinci sai ta ki gaba daya hankalinta ya tashi kar ta koma late Tumba ta doketa.
鈥淜o na zuba miki a leda?鈥�
鈥淚dan ta gani zata iya min fada鈥�
Duk da rada Khadija take mata maganar. Bata jira abunda Khadija zata sake cewa ba ta fice daga gidan hankalinta a tashe, da sallama ta shiga gidan Naja ta amsa mata tana tabe baki.
鈥淎she idan an tura ki aiki gidansu Khadija kike zuwa kina zaunawa ko? Ai na biki dazun na gani鈥�
Naja ta fada cikin daga murya ta yadda Falmata zata iya jinta. Wani irin bugawa gabanta yai da karfi, da zaro ido tana kallon kofar dakin Tumba sai ta nufo gurin Naja ta riketa.
鈥淒an Allah Naja karki fada, dan Allah ki rufa min asiri鈥�
Tana rufe baki Tumba na fitowa daga dakinta ta tsaya bakin kofa rike da kunkuru tana hararar Falmata, da sauri Falmata ta mike tsaye ta fashe da kuka, a take tsoro ya kamata ta rika ganin kamar Tumba dukanta za tai sai ta fara ja da baya baya tana ganin Tumba ta motsa ta fice daga gidan da sauri. Komawa tai gidansu Khadija ta zauna, a can ta wuni har dare ba ta fada musu abun da yasa ta gudo ba, sai dai suna ganin yadda hankalinta ya tashi sun ssn ba lafiya ba. Sai bayan sallah isha'i Naja ta zo kiranta, cikin rashin kuzari ta tashi suka fita daga gidan tare tun kan su karasa gida ta fara kuka.
Suna shiga cikin gidan fara rabawa jikin gina tana kallon mahaifinta dake watso mata harara.
鈥淕ata nan ashe idan an turata aiki gidansu Khadija take shiga, yau aikin komai ba tai ba can ta wuni, ni dai dan Allah ka yi mata tsakani da yarinyar ba ma yarinyar kirki bace Wallahi鈥�
Tumba ta fada tana narke murya kamar gaske.
鈥淲ato Falmata duk abun da za a fada miki ba kya ji ko? Kullum sai kin tsiro wani bakin hali ko?鈥�
Bata ji abunda Tumba ta fada ba amman ta ji abunda mahaifinta yace shi da yake da tsawa yake mata magana.
鈥淶o nan....鈥�
鈥淏aba dan Allah ka yi hakuri sun kore ni kuma ina tsoron komawa gidan da? Allah kai hakuri gobe zan je鈥�
Ta fada cikin kuka.
鈥淶o na ce....鈥�
Ta fara tafiya tana kuka tana kallon Tumba tana jin kamar ta taso ta zo ta cece ta, irin yadda mahaifiyarta take mata idan za a doke ta, gabansa taje ta tsaya ta rika hannunta ya murde iya kar karfinsa sai da ta fasa wani irin ihun ta fadi kasa.
鈥淲ayyo Baba Wayyo Baba dan Allah kayi hakuri, ka yafe min Baba karka kashe ni dan Allah鈥�
Sakin hannun nata yai ya rika hijabinta yaja ta daga inda take kwance har gurin da tumakinsu suke daure, ya kwance igiya daya ya daure mata kafa tamau, zai juya ta riko kafarsa.
鈥淒an Allah Baba ka yi hakuri, karka ba ni na kwana a cikin tumaki dan Allah Baba鈥�
Kasa juyowa yai kuma ya kasa tafiya har cikin ransa yake jin kukan yarsa idonsa suka cika da hawaye, amman sai ya ji ba zai iya mata komai ba bayan haka, fisge kafarsa yai ya fice daga gurin ya barta tana ta kuka. Tun tana kukan tana kiran sunansa tana bashi hakuri har koma kiran Tumba tana bata hakuri daga kashe sai ta hakura ta kwanta a gurin tana ta hawaye, ba hawayen kwana a gurin kadai ba har da hannunta da take jin kamar ya karye saboda mugun rikon da Baba yai ma hannun nata, ga kafarta da ya daure da karfen rodi ya tsuke mata kafar sosai.
Ba tai wani bachi kirki ba saboda kuka da ciwon hannu da kafa da kuma warin fitsarin dabbobin dake gurin, sai da rana ta fara fitowa sannan Tumba ta zo ta kwance ta.
鈥淣a gode鈥�
Falmata ta fada tana kallon Tumba da idanuwanta da suka kankance tsabar kuka da wahala, ba ta yi zaton za ta kwance ta wuri haka ba ya dauka ko sai ta kwana biyu ko fiye ma.
鈥淭ashi kije ki shirya ki tafi gurin aikin鈥�
鈥淭o鈥�
Ta fada jikinta na ta rawa wani irin sanyi take ji yana ratsata kamar zazzabi na son rufe ta. Duk yadda ta so tai wanka kamin ta fara yin sallah sai ta kasa saboda hannunta bata iya komai da shi ga kafarta ma dingishi take, haka nan dai ta wanke jikinta sannan tai alwala ta shiga dakinsu ta saka wasu tufafin tai sallah ta fito tana jin jiri na dibarta ta durkusa a wahale ta gaishe da mahaifinta.
鈥淏aba ina kwana?鈥�
Be amsa ba daman yana tsaye ne yana sauraren abunda Tumba take fada masa akan Khadija cikin tsawa ya ce.
鈥淏abu ke babu Khadija daga yau, balle har ki je gidansu, na miki tsakani da ita鈥�
鈥淭o Baba鈥�
Ta amsa masa tana jin kamar ba zata iya numfashi ba, ga idonta sai ciwo yake, mikewa tai tsaye bayan ta gaishe da Tumba ta nufi kofar fita kamar wata musaka ta fice daga gidan. Da kallo Baba ya fita har ta fice sannan ya sauke ajiyar zuciya a hankali ta yadda Tumba ba zata ji ya juya ya koma cikin dakinta.
Kai tsaye Masarautar Falmata ta nufa a ranta tana ta addu'ar Allah yasa su karbe ba, domin idan ba su karbe ta ba bata san yadda zata yi ba, kamar yadda ta saba sai ta gaishe da kowa take shiga ciki, sai dai bata tsaya jiran su amsa tun da ko sun amsa idan ba su kwarai ba ba ji za tai ba. Sai da ta kawo gate din da zai sadata da bangren Ammy cikin rashin sa'a ta hango Iya tsaye ita da wasu matan gidan tana magana, a take jikinta yai sanyi, ta san ko kowa zai ji rokonta ya karbi uzurinta ban da Iya, duk da baya san wacece ita ba amman ta lura da bata son ta tun farkon zuwanta gidan, bayan Iya akwai Zainab da Shattima su ma tana tsironsu ba ma kamar Shattima da shi ya kamata da kansa tana taba masa ya.
聽 Ji tai ba zata iya karasawa ciki ba ba kuma zata iya komawa gida ba, sai kawai ta koma gurin kofar babban gate na uku ta zauna tana ta kukanta marar sauti.
*****聽 聽 聽 *****聽 聽 聽聽 *****聽 聽 聽 *****
鈥淚nnalillahi wa'inna ilaihirraji'un鈥�
Shi ne abun da kowa yake fada, Ammy ta karbe ta daga hannun Baaba tana jirgizawa, amman babu alamar rai a tare da ita
鈥淗ajiya a kira likita鈥�
鈥淜o kuma a je asibiti kai tsaye ba鈥�
Ammy ta hada hankalinta a tashe, Iya ce ta karaso gurin tana tambayar abun da ya faru.
鈥淲allahi Luna ce, ta buga kwallowa, tana ta ihu ko da muka daukota jikin yayi zafi kamar wuta, daga nan bata sake motsi ba鈥�
鈥淚nnalillahi鈥�
Iya ta fada tana karbarta daga hannun Ammy.
鈥淎yi sauri a tafi asibiti ai ba tsayawa za ayi ba鈥�
Ammy da kanta ta shiga ta dauko mayafinta ita da Baaba da Iya suka nufi asbitin. A lokacin ne labarin ya karade Masarautar kowa ya san abun da ake ciki ban da Nana da hankalinta be kai can ba, domin tana bangaren Hajiya kuma Hajiya ba ta yi magana a gabanta ba ita kadai ce a falon tana ta kallon Tv duk da hankalinta baya wajen.
Ta kusan minti talatin a falon sannan ta taso ta dawo bangarensu, ta tararda manyan masu hidimar gidan zaune a falon cikin har da wasu kanen mahaifinta mata da suke zaune cikin masarautar, amman Nana bata tsaya ta kula kowa ba balle ma ta tambayi abun da yake faruwa. Kai tsaye ta wuce dakinta ta shige da rufo kofar ta hau saman gado ta kwanta, jikinta na bata ba lafiya ba amman ba zata iya tambaya ba.
Sai da ta ji hayaniyar na so ma yawa har da masu kuka sannan ta fito ta tsaya jikin kofar dakinta tana kallon Hajiya Karama dake kuka sosai ita da sauran matan, Shattima na zaune kan cushion kansa a kasa Iya kuma na zaune kasa tana kusar kuka kamar ba gobe. Sai a lokacin gabanta ya so ma faduwa, kar dai Mai Martaba ya rasu? Da sauri ta karasa fitowa ta nufo gurin da Shattima yake zaune ta zauna tana tambayarsa.
鈥淵a miya faru why kowa yake kuka?鈥�
鈥淲e lost Luna鈥�
Ya amsa mata ba tare da ya kalleta ba. A take ita ma ta fashe da kuka ta riko shi.
鈥淵a How?鈥�
Dagowa yai ya kalleta da idonsa da suka rine su kai ja, kana ganin kasan ransa a bace yake.
鈥淟okacinta ne yai鈥�
鈥淚ta take?鈥�
鈥淭ana ciki za a mata sutura鈥�
Ya fada bayan ya nuna mata kofar da bakinsa, kallon kofar tai sai ta kwantar da kanta jikin yayanta ta fashe da kuka sosai. Kusan a falon Shattima ne kawai be yi kuka ba, sauran daga masu kuka suna ihu sai masu hawaye domin ko ba ka yi niyar kuka ba ganin yadda Iya da Nana da Zainab suke kuka dole ya baka tausayi ga kuma Shattima da ya kasa kallon kowa ya kasa tashi daga gurin.
Sai da ana daf da za a fara mata sallah sannan Hajiya Balki ta shigo falon da Hijabinta da carbi a hannun tana kuka. Sai da aka fara shigowa gaisuwa sannan yaranta suka shigo suka zaune a falon Ammy ana amsar gaisuwa da su.
Da dare Waziri ya tara kowa na gadan ya fada musu kar wanda ya sanarwa Mai Martaba da maganar mutuwar Luna. Kuma wannan zaman gaisuwar shi ne na karshe duk wanda ya zo sai dai yai musu ya tafi. A cikin daren Mama Fulani ta dawo daga kauyen da tafi sakamakon wayar da aka buga mata aka labarta mata abunda ya faru.
Misalin ten Shattima ya shigo falon tare da wasu friends dinsa su kai ma Ammy gaisuwa sannan ya wuce da su bangaren Hajiya Balki su kai mata gaisuwa ita ma.
聽 Bayan sun fita Mama Fulani take cewa.
鈥淣i wannan abun har mamaki yake bani Wallahi, abu kamar ba banza ba鈥�
Ammy ta kalleta.
鈥淲ani lokacin ana munana zato, saboda an san akwai makiya kuma babu abunda basa iyawa, haka Waziri yake yawan fada wai yana ganin kamar da sa hannun wani a lamarin gidan nan鈥�
鈥淵a Waziri yana da gaskiya, ni kaina sai da mu kai maganar da shi, kuma maganarsa abun dubawa ce, tsakani da Allah da can ba haka ake ba, ki duba ki ga yadda suka mai da Mai Martaba ace kana sarki babban sarki amman an maida ke a daki zaune komai sai dai a labarta maka iyalinka ma ba kowa ke shiga ya ganka ba?鈥�
鈥淭o wa za ka yi zargi Fulani? Wasu dabam ko kuma a cikin masarautar ko a tsakaninmu, kanensa ko yan'uwa ko kuma matansa? Yanzu abunda ake ta yayatawa a gidan nan wai har da sa hannu a cikin ciwonsa saboda ina son da na ya gaji mulki鈥�
Mama Fulani ta rike baki.
鈥淚ko sai Allah ke kuma鈥�
鈥淲allahi hake ake fada ance na mallake masarauta ni na ke da ikon kowa sai yadda na yi, in ban da rashin tunani taya macen da zata auri mutumen tun tsufansa har kawo yanzu da yara suka girma sai kuma na ce wai ina son ya mutu a dora dana? Wallahi ni ban taba yi ma Shattima kwadayin sarautar nan ba, Shattima da be cika son damuwa ba ina ma zai iya da sarauta? Yau ko babu ran Mai Martaba akwai kanensa masu so na nesa da na kusa, kuma sarautar yanzu ai ta sama waka sani waya sanka me ka tara me kake da shi, ni ban taba masa fatan hawan wannan sarautar ba ko can da balle kuma yanzu鈥�
鈥淲allahi Hajiya karki ce dan muna uwa daya uba daya nake wani zargi, Wallahi har ga Allah ba dan muna uba daya da jarma ba wallahi sai nake ganin kamar har da sa hannunsa a lamarin nan, saboda kwadayenyen mutum ne, kuma ya so a bashi sarautar nan tun tuni鈥�
Ammy ta sauke ajiyar zuciya.
鈥淲ani lokacin sai ka yi zaton da ba haka yake ba, mu dai mun bar wa Allah komai yai mana magani鈥�
鈥淎mman gaskiya a tashi tsaye nema masa na hausa鈥�
鈥淎i an gwada, idan aka masa na hausar sai ki ga kullum abun na kara gaba har tsoro yake ba mu, kuma kin ga idan an karbo ta nan ita ma Hajiya Balki ta gurinta tana karbowa sai ka rasa wanene na kwarai wanene mugun, shiyasa aka ce adaina ba shi gaba daya a cigaba da masa addua kawai鈥�
鈥淎llah ya kyauta鈥�
鈥淎min鈥�
Ammy ta amsa, sannan ta kai hannunta ya janyo cooler abincin da ke gefen gadonta sai ga Nana ta shigo sanye da kayan bachi, ta zauna kusa da Ammy kanta a kasa.
鈥淵a akai?鈥�
鈥淏a komai Ammy nan zan kwana鈥�
鈥淭o sai ki kwanta tare da Gwaggonki, ni kin san dakin Mai Martaba zan kwana鈥�
鈥淣i dai da ke nake son na kwana please鈥�
鈥淣o ba zai yiyu ba Nana tsoro kike ji?鈥�
Ta gyada kai.
鈥淭o kije dakin Zainab ki kwana ya miki鈥�
Ta gyada kai sai kuma ya kwantar da kanta jikin Ammy. Ammy ta shafa kanta zuwa kafadarta.
鈥淜in ci abinci?鈥�
鈥淎a bana so鈥�
鈥淕obe dai za ki koma school鈥�
Ta dago kanta da sauri ta kalli Ammy.
鈥淎n samu sabon driver ne?鈥�
鈥淣o School bus za ta zo ta dauke ki鈥�
Ta bata fuska har ga Allah ita dai bata son zuwa makaranta.
鈥淎mmy no please鈥�
鈥淏a ni na saka ba Waziri ne, kamin ya bar nan ma sai da ya fada min zaki koma gidansa da zama idan an gama gaisuwa鈥�
Da sauri Nana ta bar jikin Ammy ta koma jikin kanwar mahaifinta wato Mama Fulani.
鈥淢ama Fulani dan Allah ki saka baki bana son zama gidan Baba Waziri Wallahi鈥�
鈥淵a Waziri ai daman ba shi da dadin zama da yara ba ke kadai ba duk yara ba son zama gurinsa, zan masa magana ya bar ki zauna nan sai ki cigaba da karatunki鈥�
鈥淓h dan Allah鈥�
Nana ta fada cikin kuka tana daga mata kai. A dakin ta kwanta duk firar da Mama Fulani da Ammy suke tana ji ta labe sosai kamar mai bachi alhalin idonta a bude yake.
Misalin sha biyu Ammy tai ma Mama Fulani sallama ta sannan ta leka Nana.
鈥淣ana...鈥�
鈥淣a'am鈥�
鈥淏a ki bachi ba? Tashi ki je dakin Zainab ki kwanta, ko nan kike so?鈥�
鈥淎 a zan je can鈥�
鈥淕oodnight鈥�
Ammy ta fada tana shafa bayanta, har cikin ranta take kaunar yarta, sai dai dabi'un da Nana take yasa basa jituwa da Ammy har Nana take ganin kamar Hajiya ta fi Ammy son ta. Sai da Ammy ta fice sannan Mama Fulani ta fashi ta shiga bandaki, da sauri Nana ta mike tsaye ta bude wardrobe Ammy ta inda ta san tana aje kudi ta fara mata bincike, tana yi tana kallon kofar bathroom bata samu komai ba yasa tai saurin rufewa ta fice daga dakin da sauri. Zainab na zaune gaban system dinta tana duba wani aiki Nana ta kwankwaso kofar dakin.
鈥淲aye?鈥�
鈥淗ajiya Karama ni ce鈥�
Jin muryar Nana yasa ta tashi taje ta bude mata kofar.
鈥淏aby鈥�
Ta kirata da sunan da take kiranta da shi.
鈥淣a'am nan zan kwana鈥�
鈥淭os shigo鈥�
Ya matsa nata daga jikin kofar, sai da Nana ta shig sannan Zainab ta rufe dakin ta dawo ta zauna a inda take tana hamma. Nana ta cire talkamin kafarta ta kwanata saman gadon tana ta kallon zoben zinarin da Zainab da aje kan bed side drawer.
聽 聽 聽 聽 聽 Washe gari aka tashi gidan kowa shiru shiru ba ma kamar Ammy da Zainab, Ammy ta tsorota da mutuwar Luna ne sai take ganin kamar so min tabi ne zata iya rasa mijinta, gashi kwana biyun nan sai mafarke take da bata gane kansu. Zainab kuma ta damu da mutuwar kuma ta damu da halin da Shattima zai shiga duk da ta san ba zai nuna ba amman abun yana nan cikin zuciyarsa.
Kowa yana falon suna karyawa ban da Ammy dake kitchen tana hadawa Mai Martaba nasa abun karyarwa dabam. Kadan kadan Nana take cin abincin tana sanye da uniform dinta sai satar kallon Shattima take da ya ke ta kurba tea shi a hankali. Sirleem ne ya shigo falon be yi sallama ba sai da ya iso dinning room din, Shattima ne kadai ya amsa masa Zainab kam tai kamar bata gan shi ba.
鈥淚'm sorry for your lost Allah ya yasa masu ceto ne my condolences please鈥�
Ya mikawa Shattima hannu, Shattima ma ya miko masa nasa suka gaisa.
鈥淭hanks鈥�
Shattima ya fada yana kallon Ammy wacce ta fito daga kitchen din tana murmushi.
鈥淪irleem鈥�
鈥淣a'am Ammy barka da tashi ya hakuri?鈥�
鈥淎l-hamdulillah鈥�
鈥淎llah masu rahama鈥�
鈥淎min Thank U鈥�
Yana kokarin juyawa Nana ta mike tsaye da sauri ta ce.
鈥淵a Sirleem dan Allah zaka sauke ni makaranta?鈥�
鈥淣o School bus zata zo ta dauke ki鈥�
Ammy ta amsa mata, Nana ta bata fuska kamar zata fasa kuka. Sirleem be ce komai ba ya juya ya fice daga bangaren gaba daya, daman saboda yai ma Shattima gaisuwa ya shigo, saboda jiya be masa gaisuwar saboda baya son fitowa cikin mutane.
Daga bangaren Ammy ya koma bangarensu, sai ya tararsa falon ba kowa tsabanin dazun da ya bar kanensa suna karyawa. Kai tsaye yai nufi bangaren corridor da zai sadashi da dakin Hajiya. A hankali yake takawa har ya isa kofar dakin, yana kokarin kai hannunsa ya tura sai ya ji shi a rufe.
鈥淗mmm ai na jidadi Wallahi an rage mugun iri, sauran su bi baya mu huta, da sannu mugun abun su zai koma musu ai, kin ga idon shi wai? Da wannan makirar sai kuka take kamar yarta鈥�
Shiru yai yana sauraren muryar mahaifiyarsa. Can kuma ya ji ta ce.
鈥淭o shikenan bari na duba yanzu鈥�
Fasa kwankwasa kofar yai ya juyo zuciyarsa cike da tambayoyi kala kala. Da wa Hajiya take? A waya take magana ko da wani? Be shiga dakinsa ba ya sauka downstairs. Ya nufi gurin motarsa tun kan ya karasa ya danna key hannunsa, yana isa ya bude motar ya shiga, be san inda zai je ba at this early morning, but haka nan dai ya tashi jikin nasa ba dadi yau, haka yasa kowa ya karya shi yana gefen falon zaune.
03/12/2021, 08:22 - 馃馃馃馃: *馃悇馃悇 FULANI 馃悇馃悇*
By Khadeeja Candy
*11*
A hankali ya fara driving din da dayan hannunsa dayan kuma yana shafa fuskarta da ke annuri kamar wani sabon ango. Tun ka ya karasa babban gate din ya hango wata duke ta rufe kanta wanda hakan ke muna alamar kuka take. Very slowly ya karasa kusa da gate din, ya mika hannunsa ya dauko facing cap dinsa ya saka ya dauki bakin gilashinsa dake cikin motar ya saka, sannan ya sauke gilashin motar yana kallonta, kuka take a hankali wanda in baka saurara sosai ba zaka iya ji ba.
鈥淜e...鈥�
Ya kirata da muryarsa mai dadi sauraro, sai dai yanayin da yai mata kiran ba zata iya ji ba, saboda ita din ba ta da lafiyar kunne a yanzu.
鈥淗ey....鈥�
Still bata dago ba dan bata san ma yanayi ba. Be sake na uku ba ya data gilashin motarsa ya cigaba da driving dinsa sanyin ac motar na ratsa ko'ina na jikinsa. Kamin ya karasa babban gate din wayarsa tai ring, cikin very low volume, hannunsa ya sa ya ciro wayar daga aljihunsa yana dubawa yai arba da Mansura. Murmushi yai kamin yai picking call din da Bluetooth din dake kunnesa.
鈥淗ey Baby鈥�
鈥淏aby kana ina?鈥�
鈥淕ani zan fito daga gida鈥�
鈥淚na zaka je?鈥�
鈥淚 don't know kawai na ji bana son zaman gidan ne鈥�
鈥淏aby i miss you鈥�
鈥淢iss you too, on wednesday zan dawo Kaduna鈥�
鈥淚 can't wait ina jin kamar na biyoka yanzu, i miss everything about you, your smell, your hug, your smile and everything, ina jin kamar idan ka auri wata ba ni ba zan iya mutuwa鈥�
Ya karshe maganar da muryar da ke nuna tana daf da fashewa da kuka, sai tausayinta ya kara shiga zuciyarsa.
鈥淓ven if na auri Nana still zan aure ki, Hajiya ta yarda na auri Nana first then na auri duk wacce nake son aure daga baya, and i promise you....鈥�
Sai kuma ya kasa karasawa what if yai mata alkawari kuma ya tsaba? What if Hajiya ta hana shi aurenta gaba daya?
鈥淚 know lokaci zai zo da zaka kasa daga kirana ma, but no matter what ina son kasan cewa ina kaunarka Sirleem, Hajiya tana son ka auri Nana ne saboda Nana ta fi ni kyau, ta fini kurciya ta fini asali ta fini komai, na san idan ka aureta za ka manta da ni ne鈥�
鈥淐-omon kin san kyau ba ya rudata, da dan kyau ne da Allah kadai ya san matan da zan so, ke kanki da ba mu kawo yanzu ba, kyau be cikin tsarina hasalima na tsani mace mai kyau sosai that's why nake son black girl very dark, but ever since i found you bana bukatar komai鈥�
Ta yi shiru kamar ba zata ce komai ba.
鈥淣a rabu da kowa saboda kai Sirleem pls karka juya min baya鈥�
鈥淏a zai taba faruwa ba kin san ina son ki ai鈥�
鈥淚 love you too鈥�
He kiss her on the phone, sannan su kai sallama ya aje wayar a saman cinyarsa, ya cigaba da driving dinsa hankali kwance ba dan ya san inda zai je ba, shi din ba kamar sauran mutane ba ne da zai iya fita any how ko zuwa ko'ina at any time, wani gurin yana zuwa za a fara masa ihu ana cewa za ayi hoto da shi ko a fara masa video ko tambayoyi, shi kuma abun da ya tsana kenan a rayuwarsa, that's why be cika son zama ko'ina ba sai a family house dinsu indai yana cikin garin Yola.
Wayarsa ce ta sake ring for the second time but this time around Hajiya ce, hannunsa na dama ya kai ya danna Bluetooth din kunnensa.
鈥淗ello Good morning鈥�
鈥淜ana ina?鈥�
鈥淣a fita鈥�
鈥淎i na san ka fita ba na aika kiranka ba babu kai a dakin kana ina?鈥�
鈥淲ani abu kike so ne Hajiya?鈥�
鈥淏an isa na tambayi inda kake ba?鈥�
鈥淚na son na karya ne a waje鈥�
鈥淜a dawo yanzu gida zaka karya鈥�
鈥淎mman Hajiya har na iso fa鈥�
鈥淯marni na baka鈥�
Tana fadar hakan ta kashe wayar, runtse idonsa yai for one second ya bude, ya juya motarsa ya dauki hanyar gida. Inda ya bar yarinyar dazun a nan ya sake tararda ita, sai dai wannan karon ba kuka take ba, zane zane take da yatsanta a interlock din dake gidan.
聽 Ya dan sauke gilashin motarsa kadan ya leko kansa.
鈥淜e me kike nan wai?鈥�
Bata ji me yace ba balle ta dago ta kalleshi, kana bata ji karar mota ba balle hankalinta ya bata an tsaya kusa da ita ne. Yanzu kam he realized bata ji domin ya daga muryarsa fiye da dazun da yai mata magana. Horn din motarsa ya danna sai ta dago da sauri ta kalli motar. Marar mota ce fes mai bakin gilashi, an sauke gilashin motar a amman kadan mutumen ciki na sanye da facing cap da katon bakin gilashin ido wanda ya boye fuskarsa. Directions dinta yake kallo tana gani ta san ko dai magana yake mata ko kuma kallonta yake. Mikewa tai tsaye ta kabe jikinta tana kallonsa hawayen da ya bushe ya bata mata fuskarta. Hannunsa ya leko kadan yai mata alama da ta zo sai ta kanne kafada alamar ba zata zo ba, jikinta be bata cewar mutumen da ya kore ta ba ne, domin wacan ya fi wannan fari, idan ma shi din ya za'ayi ya kira ta? And wannan din da ke kiranta waye? Wat if marinta zai yi? Ita dai jikinta be bata mutumen arziki ba ne domin ya ki sauke gilashin motar gaba daya balle a iya tantance ko waye ne, gashi ya saka gilas da facing cap.
Sirleem be sake kokarin ce mata komai ba ya ja motarsa zuwa gate din bangarensu, haka ta bi motar da kallo har ya shige sannan ta mike tsaye ta fara tafiya tana dingishi har ta isa gate din farko, sai da ta fara lekawa ta gani idan Iya na nan, ganin babu kowa yasa ta jidadi kuma ta ji kuzarin cira kafarta ta karasa har harabar gidan. Bata kai karamin gate ba school bus ta shigo harabar tsayawa tai kallon daliban da ke ciki ba karamin burge ta su kai ba, a rayuwarta tana sha'awar ace mace tana karatu, abun yana burgeta ace wannan yar makaranta ce, tsabanin ita da bata iya karanta komai a cikin boko. Nana ce ta fito ta kofar gaba tana ta turo baki ta shiga motar sannan driver motar yaja motar suka fita daga gurin. Bin motar tai da kallo tana tuna lokacin da Yayanta Fadil ke zuwa makaranta a lokacin tana karama sosai, yana yawan fada mata abun da ake makarantar, yana yawan ce mata ita ma idan ta kara wayo Baba zai saka ta kamar yadda ya saka shi, amman yanzu komai ya gushe, ta rasa mahaifiyarta Babanta kuma ya tsaneta, yayanta kuma ya tafi ya barsu, kanenta uku kuma suna kauye ita kadai take rayuwa cikin wahala.
鈥淜o ina Yaya Fadil yake yanzu?鈥�
Ta tambayi kanta idonta na cika da hawaye, a hankali ta fara taka stairs聽 din tana jin yadda kafarta take diban tsantsin gurin kamar ta fadi. Cikin wani irin tsoro ta danna door bell din dake gefem kofar lake, sai ta koma gefe ta labe jikin fulawoyin kasko dake gurin tana leken ta ga wanda zai bude kofar. Daya daga cikin tsofin dake aikin a gidan ce ta leko tana tambayar waye, Falmata bata ji abunda tace ba sai dai ganin tana waige waige yasa ta fito daga inda take boye tana kallon matar.
鈥淜e kika kwankwasa kofar?鈥�
Falmata ta daga kai alamar Eh ba dan tana jin abun da tace ba sai dan nuna da tai. Matar ta koma ta sanar sannan ta sake dawowa tai ma Falmata alama da ta shigo da hannu kamar ta san idan ta fada ba zata ji ba. Babu kalar addu'ar da Falmata bata karanta ba kamin ta saka kafarta cikin falon, tana shiga sai ta tsaya daga jikin kofar ta rakube ta kasa kallon kowa balle ta tantance waye da waye a ke cikin falo.
鈥淢e ya hana ki zuwa kwana biyu?鈥�
Bata daga kai balle ta gane tambayar da Ammy take mata, gashi ba ji take ba sosai ba a yanzu.
鈥淜e yar talakawa ba magana ake miki ba...鈥�
Wannan kam ta ji sarai, domin tsawa ce Baaba ta katsa mata, a take jikinta ya hau rawa hawaye suka ce sallamu alaikum.
鈥淏a kuka za ki yi ba bude baki ki yi magana....鈥�
A nan ma ta ji domin ba da wasa Baaba take daka mata tsawar ba. A lokacin da ta dago kanta sai ta rasa kan waye zata sauke su, Shattima ko Zainab ko Ammy ko Wasu bakin fuska da bata sani ba?
鈥淚dan ba za tai magana ba ta fice ta ba mu guri mana鈥�
Zainab ta fada cike da kufula, da sauri Falmata ta girgiza kai kamar ta san abunda Zainab ta fada.
鈥淒an Allah ku yi hakuri, bana iya jin komai idan ba a fada da karfi ba, ko kuma kusa da kunnena鈥�
Gaba daya kallonta suke, ba maganarta kadai ba, hawayen da ke fita daga idonta ma da yadda numfashunta ke shudewa ya isa ya sanar da irin tsoron da take ji.
鈥淏aaba matsa kusa da ita ki tambayeta abun da take so鈥�
Shattima ya fada a hankali yana kallonta.
鈥淭o Ranka ya dade鈥�
Baaba ta matsa kusa da Falmata wacce tak take jiran a sake ce mata ta juya ta zura a guje, daf da kunneta Baaba ta rada mata.
鈥淢e kike so?鈥�
A lokacin ne Falmata ta duka kasa ta hade hannayenta tana kallon Shattima hantar cikinta na mugun kadawa.
鈥淗akuri na ke son na bashi, Dan Allah yai hakuri ya maida ni aikin, na san na yi kuskuren taba masa ya amman ba da wata manufa nai ba, dan Allah ka yi hakuri ka kyale ni na cigaba da aikina, idan baka hakura ba ban san yadda zan yi ba鈥�
Shattima kallonta kawai yake ba dan ya fahimcin inda ta dosa ba, domin be san ya koreta ba, sai dai idan ita ta kori kanta saboda ta kasa natsuwa da abun da tai. Ta share hawayen idonta tana hade yawu daker.
鈥淪anadin korar da ka min yasa Babana ya mare ni kunnuwana suka rufe, har Ban iya ji sosai, idan baka maida ni ba zai iya kashe ni鈥�
Wani irin jan numfashi take tana maidawa, daker ta maganar ga kukan tsoron kar su ki karbarta ga kuma na kallonsu da take a gabanta. Ammy ta kalli Shattima.
鈥淭a maka wani abun ne?鈥�
Ya girgiza kai ya dan tabe baki alamar no.
鈥淲aya kore ki?鈥�
Ammy ta tambaya sai matar ta rada mata a kunne.
鈥淲annan matar wacce take nan gidan ita ta fada min cewar ka koreni, kar na sake dawowa鈥�
鈥淲ace mata?鈥�
Ammy ta sake tambaya tana son tantance gaskiyarta. Sai Baaba ta rada nata a kunne.
鈥淲annan wacce take saka zane da mayafi kala daya, wata Dattijiwa ban san sunanta ba鈥�
鈥淚dan kika ganta za ki gane ta?鈥�
Falmata ta gyada kai bayan Baaba ta rada mata. Duk abunda ake Zainab bata ce komai ba Shattima ma be sake cewa komai ba kallonta kawai yake, ba wai tausayi ta bashi ba, kawai kallon mamakin wanda ya koreta da sunanshi yake, shi dai ya san be koreta ba, waya ce ya koreta? Bayan be yi magana da kowa akan haka ba.
聽
鈥淢e kika aikata ne?鈥�
Ammy ce ta sake tambayar, Baaba tai isar da sakonta a kunnen Falmata, sai Falmata tai kasa da kanta ta kasa cewa komai sai hawaye take tana yarfar da hannunta. Dawowar da za tai sai tai arba da Iya wacce shigowarta kenan a falon ko karasowa inda suke ba tai ba.
鈥淕ata nan ita ce鈥�
Falmata ta fada da sauri tana nuna ta, gabanta sai ya ninka na dazun bugawa, tsoronta ma ya ninka na dazun kamar wace ta ga wani horo, gashi Iya ta sako mata jajanyen idonta tana kallon komai na jiki da jininta.
聽 聽 A lokacin ne kallo ya koma gurin Iya wace ta karaso kusa da su ta yi wani tsayi hannayenta a baya.
鈥淵a akai?鈥�
鈥淵arinyar nan ta ce kin ce Shattima ya koreta daga aiki鈥�
Iya ta juya sake kallon Falmata bayan Ammy ta fada mata haka, sai ta nuna kanta.
鈥淣i na fada miki haka?鈥�
A zaton Iya Falmata ba za ta iya cewa komai ba, musamman irin yadda ta ga ta tsaya kallonta kamin Baaba ta rada mata.
鈥淓h ke kika ce Wallahi ba karya na ke miki ba鈥�
鈥淥kay Iya ita za tai karya kenan? How are you da kika iya munafurci?鈥�
Zainab ta nufo ta tana fadin haka, Falmata dai sai kallonta take irin na kurma, sai dai tana gani ta san fada take mata. Iya ta yi saurin riketa.
鈥淎 a karki dake ta wata kila dai wata tai mata haka amman ba ni ba鈥�
鈥淭a rasa wanda za ta lakawa sai ke? Ke kadai ce a gidan nan ne?鈥�
Wannan karon Falmata ta ji abun da Zainab ta fada saboda ta fada ne cikin tsawa tana hararta. Sai Falmata ta girgiza mata kai.
鈥淚dan bata ce ba ba zan mata karya ba, Wallahi Allah yana shaidata ta fada min haka鈥�
Shattima ya mike tsaye yana fadin.
鈥淜o ma dai minene ya wuce je ki yi aikinki鈥�
Shattima ya fada bayan ya mike tsaye, yan'uwan Ammy da suke falon dai ba su ce komai ba na su ido ne kawai. Zainab ta juyo ta kalleshi.
鈥淜amar ya ya wuce? How yarinya za tai wa Iya kazafi ba ayi komai ba and you are telling us ya wuce like how? Har umarnin taje ta cigaba da aikinta kake ba ta鈥�
Wani wawan kallo mai kamar harara Shattima ya watsa mata, kamin Iya ta wanke mata fuska da mari, da sauri Zainab ta dafe kunci tana kallon Iya. Falmata kuma da bata gama fahimtar abun da ke faruwa a tsakaninsu ba tai kara shan jinin jikinta tana jin kamar ita aka mara.
鈥淗ar abada karki sake, taya Babban Mutum zai ba da umarni ke ki ce ba haka ba? Har kin isa? Waye ke da za ki fada masa abun da zai yi?鈥�
Zainab ba ta ce komai ba ta bayan hawayen da suka wanke mata fuska wanda ta manta rabon da hawaye ko wani abu damuwa ya rabeta, sai da ta kalli Shattima da ke tsaye yana kallonsu sannan ta kalli Ammy, har lokacin tana rike da kuncinta da ke ta mata zafi, da sauri ta fice daga falon tana jin wani irin fusata marar misaltuwa. Sai da ta fice sannan Ammy ta ce.
鈥淚ya da ba ki mareta ba ai鈥�
鈥淪am ba zan lamunci kowa yai ma dan cikinki maganar banza ba, balle har ya musa masa, ban yarda wani yai masa ba ina ga yata? Na sani Zainab kadai ta rage min a duniyar amman Wallahi da zata cigaba da musa miki ko Babban Mutum sai na yafe ta gaba daya a duniyar nan鈥�
Kowa na cikin falon jinjina kai yake yana ganin ta girmama Ammy da Shattima, ban da Ammy da take ganin kamar da biyu tai haka, ko dai tana jin kunyar abun da Falmata ta fada ne tana son kare kanta ne, ko kuma da wata manufar tai. Shattima be ce komai ba ya fice daga falon.
Kallo Falmata kawai Iya tai ta dauke kai ta fice ita ma daga falon. Da kai Ammy ta nunawa Falmata dakin yan uku, sai ta tashi jiki ba kwari ta nufi dakin, yau biyu ne sabanin waca zuwan nata na karshe da ta tararda da daya, sai dai yau ko da wasa ba ta kalli inda yaran suke ba, har tai abunda zata yi ta gama bata kula yaranba, tana daf da gamawa Shattima ya shigo dakin ransa a bace cikin tsawa ya ce.
鈥淵a za ki yi shara da yara a cikin daki? Baki da hankali ne?鈥�
Da sauri ta juyo ta kalleshi ta girgiza masa kai.
鈥淚dan na taba su zan iya yin laifi, dan Allah kai hakuri鈥�
Ta duka har kasa ta hade hannayenta tana bashi hakuri, wani dogon tsaki yaja ya karasa cikin dakin ya kai hannunsa ya dauki dayan ya dora a wuyansa dayan kuma a dauke ta da hannunsa. Kamin ya fice Falmata ta karasa aikinta duk ta tsawwala. Tana gamawa ta fice da sauri kamar wacce aka kora.
WASIN POV.
Yana daga saman icen guava zaune yana kallon yadda mawakan cikin gidan sarautar suke busa suna rawa daga su sai walki a jikinsu, ga wuta kara a tsakiya sai tashi take a tsakiyarsu, mahaifinsa kuma yana zaune a saman wata kujerar ice wacce aka mata kwaliya da fatar damisa, sai kallon masu wasan yake yana murmushi cike da jindadin, kusan rabin garin duk suna tsaye a gurin suna kallon yadda ake wasar, mazajen da suke tsaye kuma jikinsu sai rawa yake suna jin kamar su fada ayi da su.
A cikin masu wasan har da Liya wacce ke sanye da rigar fatu, ta sako gashin kanta har baya, sai tai masa kwalliya da gashin tantaba yai mata kyau kamar wani ribbbon, hannunta sanye da wuri kamar yadda duka kafafuwanta suke sanye da su, duk wani motsi nata sai sun motsa, wuyanta sanye da kokon kan mujiya wanda ya bushe aka yi mata tsarka da shi. Wasa take sosai kamar wata yar buri, yadda take wankwasa hannunta da jikinta sai ka dauka wata macijiya ce. Mikewa tsaye Wasin yai ya fara busa sarewarsa sai gurin ya dauki wani kalar sauti mai dadi ga iska na kadawa yana daukar busar tana karade ko'ina na gurin. Wani irin kuzari ne ya kara shigar Liya sai ta ji kamar dominta kadai yake busar, a lokacin ne ta fara kada kafafuwanta da kunkurunta wurin da ke jikinta yana ta kara, sauran yan rawan kuma sai suka rika buga kafarsu a kasa su ma wurin da ke daure a kafarsu ya rika kara.
Duk abunda ake ran Sarkin cike yake da farinciki da annushuwa, domin wasan ba karamin kayatarwa tai ba, kuma wasa ce wacce ya samu asali tun kaka da kakanin. Bayan ya gama rawar aka shigo da gassashen naman kuraye, yanka daya ake yankawa kowa ya dauka ya ci, haka ake a duk lokacin da akai wami wasa, ta nan suke iya gane wanda ba jininsu ba kuma ba dan garin ba, idan kai ba dan garin ba ne ka ci naman kurar a take makoshinka zai fara kaikaiyi, domin naman tsafafen nama ne.
Sai da aka gama komai sannan Wasin ya saka daga kan bishiyar, ya isa gaban mahaifinsa ya kwashi gaisuwa, sannan ya fara tafiya barin garin, daman shi be saba kwana a cikin garinsu ba. Yana tafiya yaji ana binsa a baya, tsayawa yai cak ya duba tafin hannunsa, sai sunan liya ya fito rubuce a cikin manyan baki. Juyawa yai ya kalleta sai ta sakar masa murmushi ta biye hannayenta a baya tana wasa da su.
鈥淵a akai?鈥�
Ta girgiza masa kai alamar babu komai, sai kawai ya juya ya cigaba da tafiyarsa, sai ya sake jinta a bayansa, sake juyowa yai ya kalleta nan ma kan ta girgiza masa, sai ya nuna mata bayanta, tana juya bata ga komai ba ko da ta juya har ya bace. Dariya yai ta kwala masa kira da iyakar muryarta.
鈥淲asin.......鈥�
Manyan duwatsun da suke gaban garin ta fara kallon duk da kasancewar dare ne, sai dai akwai hasken farin wata da zai iya bata damar ganin duwatsun ban da abun da yake kansu domin sun mata nisa sosai.
A saman icen da ya saba kwana ya hau ya kwanta yana ta kallon manyan taurarin da suka haska samaniya su kai mata ado, ga iska mai sanyi sai kadawa yake.
0 comments:
Post a Comment