Tana zaune ya turo kofar dakin ya shigo hannunsa rike da takeaway da robar ruwa, mikewa tai tsaye da sauri tana kallonsa, kallo daya yai mata ya dauke kai ya aje mata abincin ya fice. Bata bukatar ya fada ci zata yi a yadda take jin yunwa ko da guba aka saka a abincin zata iya cinsa. Naman kazar ta fara cinyewa rabon da ta ci nama har tun na sallah, shimkafar ma sai ta ji kamar ta fi ko wace wane abinci dadi saboda bata cin abinci mai dadi a gida.
Ruwa kan kadan ta sha saboda ta riga ta cika cikinta da ruwan fonfon da ta sha na bandaki. A maimakon ta hau saman gadon ta kwanta sai ta kwanta a kasa, tana ta kallon pop bachin yace mata ba dai shi ba, yadda ta ga rana haka ta ga dare, babu komai a cikin ranta tunanin kudin Tumba data taba idan ya maida ita gida yace guduwa tai ta san Baba zai iya saka wuka ya yanka ta ne, wasa wasa ta ji ana kiran sallah asuba, kamar yadda tai a jiya haka ta shiga bandakin tai alwala ta fito ta sake shimfida dankwalinta tai sallah. Tana cikin addu'a Sirleem ya turo kofar dakin ya shigo. Tea mai kauri ya aje mata da bread sai sake mikewa tsaye kamar dazun tana kallonsa.
鈥淒an Allah karka maida ni gida鈥�
Uffan be ce mata ba, daman kuma be da niyar ce mata komai yana aje mata tea ya juya ya nufi kofa.
鈥淲allahi idan ka maiyar da ni Baba ya ji cewar na gudu sai ya yanka ni, kuma Umma sai ta kusa kashe ni saboda na taba mata kudi鈥�
Daf da zai fice ta fadi haka, sai ya tsaya cak ya juyo ya kalleta, tausayinta ya kama shi how old she is da zata zabi guduwa da bar gidansu? Ko bata fada masa ba ya san ana azabtar da ita tun da har ta zabi barin garinsu da gidansu ta zo inda bata san kowa ba, amman rayuwarta yake ji kar ta aikata irin abun da Mansura ta aikata ya zame mata tabo, a kurciyarta zata iya lalata rayuwarta, amman idan tai hakuri da wahala zata ci riba kuma zata wuce kamar ba ayi ba.
Juyawa yai ya fice daga dakin, ita kuma ta zauna ta fara kuka tana tunanin irin mugun dukan da Baba zai mata, bata tunanin zai barta ta rayu ma idan ko har ta rayu to sai dai ta zama musaka.
Misalin 6:30 ya sake turo kofar dakin, ya tsaya daga jikin kofar yana kallonta, ya same ta a yadda ya fita ya barta, tana kuka kuma bata taba tea ba.
鈥淔ito muje鈥�
Mikewa tai tsaye ta nufi kofar hawaye na sauko mata kamar dan irin wannan ranar kawai ta tanade su. Bata ce me zata ce masa ba, tun da har ya kasa sauraranta ta san ba zai fahimce ta ba, a yanzu ba ta da wanda zata karantawa damuwata balle ya nade mata kuncinta. Ta yarda a gidansu bata da gata, a nan din ma bata da gata. Da kanshi ya bude mata gidan gaba ta shiga ta zauna ya rufe sannan ya zagaya ya shiga mazauninsa ya ja motar.
Tun da ya fara tafiya wata kalmar bata shiga tsakaninsu ba, daji take kallo tana share hawayenta lokaci zuwa lokaci, ta sadakar kuma ta yardar da kaddarar da ta rabo da gida, ta yarda wata kaddararce take bibiyarta a yanzu na fadawa wata damuwa. Tun yana tukin tana kallon titi har bachi ya sallama mata ita kuma ta amsa masa cikin sauki, daman tun jiya basu hadu ba. Sai da ya tabbatar da bachin nata ya yi nisa sannan ya faka motarsa gefe ya fita ya zaya gefenta ya bude mata a hankali kwantar mata da kujerar ya rufe, kamin ya dawo motar ya ciro wayarsa ya kira Mansura bugu daya ta dauka.
鈥淪irleem ina yarinyar nan ta kwana?鈥�
鈥淭un jiya na saka ta a motar Yola鈥�
鈥淚na ta kiranka baka dauka ba tun jiya, kuma ka san zan samu鈥�
鈥淪hiyasa na kira ki yanzu鈥�
Ya fada yana kallon Falmata ta cikin farin gilashin motarsa, bachinta take hankali kwance kamar wacce bata da damuwa. Ta saka hannu ta share hawayen idonta.
鈥淜ana ina kai鈥�
Ya daga kansa yana kallon katon dajin.
鈥淪omewhere.... Anjima zan kira ki鈥�
Be jira cewarta ba ya yanke wayar ya maida aljihu ya zagaya ya shiga motar ta cigaba da tukinsa. After every deep breath sai ya kalli Falmata wacce ke ta ranko bachi har ya shiga garin Yola.
Kai tsaye ya nufi GRA, a gaban wani katon gate ya faka motarsa sannan ya fita ya doshi gate din yai knocking, babu bata lokaci mai gadin ya leko.
鈥淩anka ya dade kai da kanka kake buga gate鈥�
Sirleem ya dan yi murmushi.
鈥淎llah yasa Momy dai tana ciki鈥�
鈥淵anzu yanzu ko ta dawo鈥�
Mai gadin ya fada yana matsa masa daga kofa. Sai da ya danna key mota yai ta shiga lock sannan ya shiga cikin gidan. Kato gida mai yanayi da na turawa domin babu hayani sai kukan tsuntsaye dake saman itatuwan da suka zagaye harabar gidan su kai masa ado, ga wasu manyanna alfamar. Entrance din ya hau ya isa gaban kofar yai knocking.
Wata kyakyawar mata ce ta bude masa kofar fuskarta dauke da murmushi matar zata yi 40 to 42 years tana sanye da farar atamfa, sai farar t labcoat dake saman atamfar.
鈥淐elebrities ganinku sai da ticket, sai kuma idan kun so kawo ziyara鈥�
Dan murmushi Sirleem yai ya naso kafarsa cikin falon mai cike da sanyi ac.
鈥淏a ma ziyara na kawo ba ni alfarma na zo nema鈥�
鈥淭o yau kuma a gurina鈥�
鈥淣a san ke kadai zaki min ai鈥�
Ya fada yana kokarin zaunawa.
鈥淵anzu yanzu na dawo daga aiki, lemme go and change鈥�
Sai da ta aje masa lemu da ruwa sannan ta nufi upstairs ta shiga dakin farko. After like thirty minutes ta fito sanye da Hijab din dake nuna alamar sallah ta gama, sai da ta sauko kasa ta zauna sannan Sirleem ya kalleta yace.
鈥淲ata yarinya ce na hadu da ita a Kaduna, ban ji labarinta ba amman a yadda na fahimta tana shan wahala ne a gurin rikon nata ko gurin Babanta, saboda tace min mamanta ta rasu, kuma ta gudo ne daga gidansu zuwa Kaduna, bayan kuma bata san kowa a can ba, so idan na kyale ta a can rayuwarta zata iya lalacewa shiyasa na zabi dawo da ita gida saboda yar nan Yola ce鈥�
Iya nan ya tsaya yana sauke numfashi a hankali, tun kamin ya gama labarta mata abubuwan ta soma jin tausayinta.
鈥淎llah mai iko ina yarinyar take?鈥�
鈥淢una tare a mota, ina son kije gidansu ne tare da ita, ki ce ke kika kadeta kuma hankalinta ya gushe sai yanzu ta farko ta fadi gidansu kika kawo ta, saboda ta nuna min idan ta koma gida Babanta ya ji cewar ta gudu zai yankata, kuma ta taba kudin ko waye i don't know zan tambaye ta kudin sai na bata鈥�
鈥淎llah mai iko, wasu suna neman haihuwa wasu kuma suna wulakantawa鈥�
Momy ta fada cikin rashin dadi rai, Sirleem yayi murmushi yana kallonta cike da tausayinta, kamin ya mike tsaye.
鈥淏ari na shigo da ita鈥�
鈥淥kay鈥�
Fita yai daga falon, ko da ya isa gurin motar ya tararda ta farka tana ta kalle kalle, unlock din motar yai sannan ya bude side dinta.
鈥淔ito鈥�
Ta fito kamar daman can umarnin take jira, be yarda ya shiga cikin gidan ba sai da ya saka ta a gaba, ita dai tafiya kawai take ba dan tasan a ina take ba a Kaduna ko kuma a Yola? Ina zai kaita? Shine abun da take ta tambayar kanta, rage tafiya tai har sai da ya sha gabanta sannan ta bi bayansa suka shiga cikin falon.
Wani irin kallo Momy take mata na tausayi, karamar yarinyar kamar wannan ace zata gudu ta bar gida? Ta jefa rayuwarta a hadari?
鈥淪annu zauna nan鈥�
A maimakon Falmata ta zauna a kujerar da Momy ta nuna mata sai ta zauna kasa ta sinne kai gabanta na faduwa, bata ji me tace mata ba amman ta san alama take mata da ta zauna.
鈥淵a sunanki?鈥�
Momy ta tambaya, Falmata kan bata ma san tana yi ba dan kanta a kasa yake kuma ba ji take ba.
鈥淏ata ji sosai sai kin daga muryar鈥�
Sirleem ya amsa mata, sai tausayinta ya kara kama Momy, ta dan daga muryarta ta sake tambayarta.
鈥淔almata鈥�
Ta amsa ta ba tare da ta kalleta ba.
鈥淪annu Mamana鈥�
Momy ta fada cike da tausayawa sannan ta mike tsaye ta nufi kitchen, cornflakes ta hada mata da madara sannan ta dauko wani plate da zuba mata fruits ta dawo falon ta aje a gabanta.
鈥淵anzu na dawo aiki ban dora komai鈥�
A nan ma Falmata bata jira tace mata dauki ki sha ba, dan yunwar da take ji ta musammance, sai ta dauki cup din ta cire cibin ta aje ta kafa kai ta sanye shi dika, wani irin dadi ta ji har cikin kanta domin bata taba shan cornflakes ba. Tausayinta ne ya cika Momy har ta rasa me zata ce sai kallonta take kamin ta kalli Sirleem.
鈥淜a kaita ciki ta yi wanka ta huta鈥�
鈥淣o Momy Hajiya na jirana, na fi son a kaita gidansu sai tai can鈥�
Ya kalli Falmata.
鈥淣awa ne kudin da kika taba?鈥�
鈥淒ubu biyar ne鈥�
Ta amsa masa muryarta na rawa, sai yasa hannunsa aljihu ya ciro wallet dinsa ya kirga 5k ya mika mata, sannan ya sake kirga 10k ya mika mata.
鈥淲annan idan kin je ki samu wata sana'a ki rika yi鈥�
Ta yi saurin girgiza kai.
鈥淎a idan aka gan ni da kudi da yawa za a iya dukana鈥�
Sirleem be ce komai ba ya maida kudin wallet dinsa ya mike tsaye.
鈥淜a kaita gurin motana zan kira oga na fada mishi鈥�
鈥淥kay鈥�
Tare suka fito da Falmata ya nuna mata motar Momy.
鈥淜i jirata a can, idan ta zo ki fada mata unguwarku, kuma duk abun da tace ki ce eh haka ne鈥�
Sai da yai maganar ne Falmata ta gane cewar sun iso Yola kenan, kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki haka ta nufi gurin motar da Sirleem ya nuna mata ta tsaya tana karewa gidan kallo.
AA POV.
Ganin bakuwar number yasa gabansa faduwa, duk kuwa da Nana ta fada masa cewar bata fada a gida ba, amman ya kasa natsuwa. Haka yai ta kallon wayar har tai ringing ta gama sannan mike tsaye ta fito daga dakin Hindu ya nufi waje, a nan kiran ya sake shigowa sai da yai Bismillah uku sannan ya dauki kiran, jin muryar Nana yasa hankalinsa kwanta ba.
鈥淪aurdauna鈥�
鈥淣a'am鈥�
鈥淵auwa kai ne, ya kake?鈥�
鈥淚na lafiya鈥�
鈥淜ana ina?鈥�
鈥淚na ina? Ina Yola鈥�
Ya amsata yana juyawa ya gani ko wani na binsa, ko kallonsa.
鈥淜a zo gidanmu na fadawa Hajiya tace na kira driver, ka bashi key din motar鈥�
Wani irin dadi ne ya lullube shi, ya matsa kusa da wata transforma ya fada ta yana jin kamar ya rumgumeta.
鈥淒a gaske Nana?鈥�
鈥淲allahi da gaske, ka zo yanzu ka ji鈥�
鈥淭o ina ne unguwarku?鈥�
鈥淜asan Turaki area鈥�
鈥淓h鈥�
鈥淭o ka zo nan daga shigo kace ina ne gidan Mai Martaba idan kan zo kace gurin Nana ka zo, sai ka kira line nan鈥�
Wata kalar kabbara yai ya lumshe ido ya bude ya rumgume transforma da hannu daya
鈥淎llahu Akbar yanzu Nana ke yar sarauta ce?鈥�
Dariya Nana tai ta tashe wayar ba tare da tace masa komai ba. Wayar ya kurawa ido yana tuna farkon haduwarsu, sai yaji abun kamar a mafarki, duba yai yaga babu mai kallonsa sai ya fadi yai sujada sannan ya mike tsaye yana gyara rigarsa.
鈥淪hikenan Kakata ta yanke saka, na yi arziki malam鈥�
Da sauri ya koma cikin gidan ya canja tufafin jikinsa ya fito ba tare da ya fadawa kowa ba, ya fito ya tari mai achaba ya hau.
Ba a sauke shi ko ina ba sai Turaki area (Fake area) Unguwar masu arziki da naira unguwar da babu irinta kaf a fadin garin Yola, manyan gidanjen yake bi da kallo kamar be saba bi yana wucewa ta unguwar ba, wani karin dadi yake ji a ransa, yana sauka ya mikawa dan a chaban 500 yace ya yafe nasa canjin, cikin tsoro tsoro ya karasa gate din ya gaisa da masu gadin ya fadu musu gurin Nana ya zo, ba su yarda da shi ba sai da ya kira wayar ta daga tai musu magana sannan aka barshi ya shigo.
Gaba daya rikecewa yai ya rasa ina zai bi ganin masarauta mai kama da wata unguwa, saboda fadi da girma gashi an raba ko'ina part part, kai tsaye ya nufi apartment din Hajiya yana tafe yana jin wani dadi na daukarsa sai raba ido yake yana kallon amsu aikin dake kai da kawo da sauran mutane dake ta sha'aninsu. Bakin gate din ya tsaya ganin mota na fitowa a zatonsa Nana ce sai ya gata wata marar jiki ta tsaya daidai shi da motar.
鈥淵a kai?鈥�
鈥淣a zo gurin Nana ne鈥�
鈥淢e zata maka?鈥�
鈥淣ine sabon driver da za a dauka鈥�
Jurry ta kare masa kallo from head to toe sannan ta watsa masa wani banzan tsaki.
鈥淢alam fita ka bamu guri ba za a dauke ka ba鈥�
鈥淎mman Nana tace na zo鈥�
鈥淣ana ita take da ikon kanta i say out...鈥�
Ya juya da sauri ya fice aransa yana fadin.
鈥榃allahi ba zai yiyu na ga samu na ga rashi ba, dole ne sai an dauke ni鈥�
***
Nana ta kwanta saman gadonta tana dariya, ba karamin dadi ta ji ba na samun number sa da tai, daman kuma ta san ba zata mata wahala ba indai a line Hajiya ne. Duka numbers din da ta duba a call list tashi ce kawai ba suna.
Wani irin dadi take ji zai zama driver ta domin har ga Allah yana burgeta kuma gashi yana jin maganarta komai tace masa. After some minutes kiransa ya shigo wayar Hajiya dake hannunta ta daga tai magana da mutanen dake gate din sannan ta kashe ta mike tsaye ta fice daga dakin.
SHATTIMA POV.
Relaxing yai akan kujera yana busar da iskar bakinsa, manyan idanuwansa na wani lumshi alamar bachi yake ji da kuma gajiyar tiyatar da ya gama a yanzu. Wayarsa dake gaban teburin ce tai ringing Sunan Hajiya Karama ne rubuce a gaban screen din, sai da ya dan matsa da kujerarsa baya sannan ya amsa.
鈥淗ello Sis鈥�
鈥淪hattima ya aiki?鈥�
鈥淎l-hamdulillah how is kids?鈥�
鈥淪una nan kalau, on Saturday zan zo Katsina fa gurin aikin da na ce maka鈥�
鈥淥kay this Saturday?鈥�
鈥淵eah na san dai ba zaka je asibiti ba ranar right鈥�
Ya dan tabe baki kadan kuma yai shiru na wani lokacin kamin ya amsa mata.
鈥淶an je da Yamma鈥�
鈥淥kay ni da safe zan shigo鈥�
鈥淎llah ya kai mu鈥�
Ya fada bayan yayi shiru kamar ba zai ce komai ba. Aje wayar yai be kashe ba, daman can haka yake ko shi ya kira ka sai dai kai ka kashe, shi nashi aje waya ne kawai. Ya mike tsaye yana murmushi yana kallon screen din wayar dake dauke da hoton yayanshi.
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence via 08036126660*
03/12/2021, 09:21 - 馃馃馃馃: *Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence via 08036126660*
Hannun rigarsa ya fara budewa sannan ya bude ya fara bude maballan rigarsa yana ta kallon kansa a jikin madubin dake gabansa. Dan murmushi yai kamar wanda ya tuna abu sannan ya juyo ya cire rigar gaba daya ya dora saman gadon ya dauko vest ya saka ya sauko kasa.
Kai tsaye kitchen ya wuce ya dauki cup ya aje sannan ya bude fridge ya dauko lemun tsami ya matsa a cup din ya bude durowar kitchen din ya dauko wata farar roba ya bude ta debi kanwa kadan ya zuba a cup din ya saka karamin spoon ya garwaye sai da lemun ya hade da kanwa sannan ya daga cup din ya shanye yana bata fuska tsamin na kai masa har cikin kai. Ra'ees ne ya shigo kitchen din sai zuba kamshin turare yake.
鈥淪hattima ni zan wuce鈥�
Ra'ees ya fada daga tsayin da yaje bakin kofar kitchen din. Juyowa Shattima yai ya kalleshi, irin kallon nan na ina zaka je? Indai Shattima ne zai bude baki ya tambaye shi ba sai dai kar ya sani, ba dan komai ba sai dan magana taba masa wahala, yana da nauyin baki furta wata kalar tafi komai yi masa nauyi a baki da jiki, abu ne mai wahala ka ganshi a cikin mutane ko da kuwa Ammy ce ko Zainab yana fira, sai dai yai shiru yai ta saurarensu idan sun gama ya tashi wani lokacin kuma sai yi murmushi idan an fadi abun dariya idan kuma tambayarce zai iya ce maka eh ko aa ko ya girgiza kai. Magana ta fi komai yi masa wahala a rayuwa, gashi kuma likita haka nan dai yake ta fama kamar dole.
鈥淶an je kauyen kaita, akwai wani aiki da nake son yi a can鈥�
Ra'ees ya amsa masa ba tare da ya jira ya tambaye shi ba, daman kuma ya san halin abokin nasa indai sai ya tanbaye shi ne sai a mutu a tsaye.
Shattima na son ya tambayeshi me zai je yi a can kuma yaji ba ya bukatar wahalar da kansa, sai kawai ya tabe baki ya daga masa hannu.
鈥淪afe trip鈥�
鈥淭hanks鈥�
Ya juya ya fice daga kitchen din, kamin ya isa gurin motarsa Yayarsa ta masa kira ya kai uku domin mijinta ya shirya shi kawai ake jira. Da motarsa ya isa gidanta sai ya aje motarshi ya shiga motar mijin suka kama hanyar Kaita daga Katsina.
Suna tafe suna firar kasa da rashin tsoron da ake fama da ahi da yunwa, har suka isa, a cikin garin kaita suka yi sallah sannan suka yi tambaya aka fada musu hanyar da za su bi ta kaisu garin Bandalo. Alhaji Tukur ne yake jan motar Ra'ees yana front seat, yana karewa garin kallon, garin Bandalo gari ne mai cike da burgewa, tun farkon shigowa garin zaka fara arba da manyan gonaki, domin garin ya kasu kashi biyu ne, fulani makiyaya sai kuma hausawa da kusan sune rabin garin, daman fulanin irin masu yada zango nan ne a gari, yamma da garin ne bangaren fulani kana daukar hanyar da tai can zaka fara arba da bukoki da shanu da masu kiwon shanun gwanin burgewa.
鈥淩abun da na ga bukka da idona ni har na manta鈥�
Ra'ees ya fada yana kara bawa idonsa abinci, sai da su kai nisa sosai sannan Alhaji Tukur ya tsaya kusa da wasu fulani suka zaune gaban wani massalaci na kasa yana tambayarsu Malam Jauro.
鈥淒an Allah muja cijiyar wani Malam Jauro Sama'ila鈥�
鈥淜un zo gida, daga ina kuke?鈥�
鈥淒aga birni mun zo, gurin Matarsa ne Amo鈥�
Wani bafullatanin mai tsaga a fuska ya mike tsaye.
鈥淢uje na karasa da ku daman gidan Modibbo zan je鈥�
A kafa yake tafiya su kuma tana binsa a kasa har suka isa kofar gidansu Fadime, gidansa ne mai girma da aka zagaye da zana an share gaban idan tas ga kasar gurin ta kwanta kamar yashi. Malam Bala da kansa ya sallama cikin gidan sai Hajjo ta amsa masa ta fito ta gaishe shi tana karewa mutanen kallo da yaren Fulatanci yake tambayarta ina Malam Jauro, sai ta fada masa baya nan ya tafi gona.
鈥淭o ga baki nan ki fadawa Amo, ni bari naje na kira shi鈥�
Ya fada mata da yaren fulatanci, sannan ya kallesu yace.
鈥淶anje na kira shi yanzu nan, yana gobarsa鈥�
鈥淭o sannu da kokari mun gode sosai鈥�
Duk suka fada Ra'ees har yana dan risinawa domin ya yaba sosai da yadda mutumen yake ta musu karamci.
Yana tafiya Amo ta fito baki har kunne tana dariya ta nufo su da hijabinta mai multi colors tabarma rike hannunta Hajjo kuma na rike da kwanon ruwa dake cike da kindirmo. Icen dake kusa da kofar gidansu ta nufa ta shinfida kusu tabarmar a can, sannan ta karbi kwanon dake hannun Hajjo ta a gurin.
鈥淗annunku da zuwa Hannu da zuwa, kun sha hanya鈥�
Ta hangame musu bakin nan nata mai cike da goro tana musu Sannu ga wata uwar dariya da take musu ta murna da ganinsu domin bata dauka za su zo din da gaske ba. Ra'ees ne ya fara zaunawa yana amsa gaisuwarta kamin mijin yayarsa ya zauna shi ma.
Da sauri Amo ta koma ciki gida da murnarta, ta nufi dakin Inna wacce ke zaune dakin tare da Fadime tun safe, saboda kukan da Fadime take ta yi, tun tana dan jin tsoron abun da ya faru jiya har ta fara dauriya tana lallashin yarta, duk kukan da Fadime take na hawaye ne kawai bata yarda ta bude bakinta, gudun kar ta sake tsorota wani domin ita ma tsoron muryar take, gashi Bappa da Inna sun hata ta fita balle taje ko zata ganshi ta roki ya gyara mata nuryarta ta koma daidai.
Hankali Inna da Fadime be kara tashi ba, sai da Amo ta leko bukkar tace ga masu neman auren Fadime nan sun taho, Fadime kamar an mata allurar kuka haka ta ji, Inna kam sai tausayin Fadime ya kamata dan ta san yadda take daukin zuwa wannan ranar.
鈥淭o su gaisa da Malam tukuna mana鈥�
鈥淓h na aika Hajjo ta kirashi yanzu鈥�
Amo ta juya ta fita tana jin wani irin dadi marar misaltuwa, tasan a komai yanzu ita za a saka a gaba. Cikin hawayen Fadime ta mike tsaye tana nuna ma Inna tufafin jikinta da alama so take ta canja ta, tana son tai magana tana jin tsoro muryar.
鈥淭o wai Fulani hakan zaki tafi musu kanar kurma? Komai sai dai ki da hannu?鈥�
Fadime. Ta dan turo baki ta fice daga bukkar ta nufi bukkarta ta dauko atamfar dake can masa ghana must go, ta tube rufafin jikinta ta debi ruwa ta shiga bandaki. Sai da ta kori kadangaran da ke gurin dan kar su sako mata ido suna kallon tsiraici sannan ta cire zanenta, sama sama tai wanka ta fito tana ta ayyana yadda mutumen yake a idonta, bata ma tsawa shafa mai ba ta saka atamfar ta daura dankwali ta dauko mayafi ta dora a saman kai, ta dauki karamin madubin ta kalli kanta. Dan murmushi tai kamar ba ita ce take kukan tun safe ba har rana. Can zuciyarta ta bata cewar ta shafa hota ai yan birni ne, da sauri ta kwance kullin hodar ta kasa dake cikin farar leda ta dagali kadan ta shafa ta shafa janbaki, abun ka da farar mace sai tai kyau sosai pink janbakin ya haskata ita kanta sai da tai murmushi. Ta dauko talkaminta na sallah ta saka ta fito tsakar gidan ta zauna, Inna na kallonta ta saki murmushi ganin yadda yarta ta fito Ma-sha-Allah, daman can Fadime akwai iya kwaliya ba kamar ta sauran yan matan kauyen ba.
鈥淭o kwalli fa鈥�
Inna ta fada tana kallonsa. Sai Fadime tai murmushi kamar ta bude baki tace ai su yan birni basa saka kwalli kuma ba dama tun da muryarta ta zama abun tsoro, duk da bata da tabbacin muryar tana nan har yanzu ko kuma ta dawo normal a yadda take, abun haushi ma muryar shanun bata fita kadan kamar an saka loudspeaker haka take shiga kunne mutane.
Gaba daya Fadime kasa natsuwa tai taje jikin zanar tana lekensu sai dai bata ga fuskar ko daya daga cikinsu ba kasancewar sun bata baya ne suna magana da Bappa da wani abokinsa. Wani irin tsalle ta buga tana jin kamar ranar za a kaita dakin mijin. Amo de na zaune bakin tata bukkar tana murmushi a ranta tana ayyana ko kwana nawa Fadime za tai kamin ta mutu, ta dayan bangaren kuma tana ta mamakin yadda jiya ma wani abun ya same ta na sauyawar muryar kamar yadda Inna ta fada mata, dan ita dai bata nan komai ya faru.
Yanzu kam ta fara gasgata cewar Fadime ta hadu da aljanu domin su kadai zasu iya cire nata wutar sai kuma maye irinta ko mai tsafi, wata kila shiyasa ita ta kanta ta nemo mata miji, ko da yake mijin ma daga gani maye ne kamar ita ko zai iya cin kurwa Fadime ko kuma zata gagareshi ne kamar yadda ita ma ta gagareta?
鈥楤ari na gani yanzu za a sake cirewa鈥�
Ta fada a ranta sannan ta mike tsaye ta shiga cikin bukkarta, ta mika hannu a karkashin gadon ta na kara ta dauko wata yar karamar tukunyar kasa wacce ke rufe da jan kyalle ta bude kyalle ta kai bakinta ta fara kiran sunan wani aljani tana masa kirari kamin ta fadi bukatarta sannan ta kai kunnenta tana saurare. Can ta sake kai bakinta.
鈥淏akin bunsuru zan yanka maka鈥�
Sannan ta aje tukunyar wacce aljaninta na maita yake ciki ta maida ta karkashin gado, ta sake janyo wata tsohuwar roba mai murfi ta bude ta dauki wata yar karamar soyayyar kurwa ta kai baki, har wani lumshe ido take tana shude yatsan hannunta.
鈥淪aratu kam akwai dadi鈥�
Ta fada tana kokarin maida robar a inda take, sai davta gyara komai tsaf sannan ta mike tsaye ta fito, a tsakar gida ta samu Bappa tsaye yana nunawa Inna kudin da suka ba shi.
鈥淭o gashi nan since ase goro鈥�
A take ta ji ranta ya bace akan me zai fara nunawa Inna bayan itace uwargida, sannan ita ta kawo ma Fadime mijin nan, sai dai bata yarda ta nuna musu komai ba ta washe baki tana murna kamar gaske.
鈥淭o Fulani tashi kije ku gaisa鈥�
Bappa ya fada. Abun ka da mai nema sai tai zumunt ta mike tsaye, jikinta sai rawa yake zuciyarta na bugawa da karfi, tana son ta tambayi Inna idan taje me zata fara cewa kuma tana gudun tai magana aji muryarta bata sani ba ko har yanzu muryar tana nan.
鈥淜arki musu magana Fulani, duk abun da suka ce miki sai dai ki daga musu kai ko ki yi dariya, idan suka tambaye ki ki nuna musu wuyanki wuyanki ke ciwo鈥�
Inna ta fada, sai Fadime ta gyada kai ta sinne kai kasa tana dan jin kunyar Bappa, har tafiya sai da Fadime ta sauya ta fara irin na yan zamani a hankali take takawa har ta isa inda suke, tana kokarin zaunawa a saman shimfidar ta tuna cewar bata saka turare ba, gashi dai yan birni suna son kamshi tun da su ma taji sai kamshin suke, sau daya ta kalli Ra'ees ta dauke kai dan ta fi sa ran shi ne mijin nata ganin ya fi kurciya. Da hannu ta gaishe su irin yadda kurame suke yi sai suka kalli juna shi da Alhaji Tukur, domin ba a fada musu cewar ita din kurma ce ba, ga kyau iya kyau amman ba magana. Duk abun da suka tambaye sai dai tai musu na kurame, Ra'ees sai wani irin kallonta yake shi kam gaba daya ta tafi ta imaninsa duk da kasancewar ta kuma. Rashin maganar ba karamin cutar Fadime yai ba domin ta so tai musu turanci su ji cewar ta iya ingilishi kamar yar birni, tsoro tsoro take wai kar su dauka ita kurma ce su fasa aurenta, sai a lokacin ne ta tuna cewar Inna tace ta fada musu wuyanta ke ciwo. Sai ta kai hannunta ta dafa wuyan tana nuna musu.
鈥淲uya? Ciwo yake?鈥�
Alhaji Tukur ya tambaya a nan kam Allah ya bata ikon magana.
鈥淓h tun jiya鈥�
Ba shiri ta zaro ido ta rufe bakinta da sauri, Alhaji Tukur ya kwanta a gurin ya danne kansa sosai yana fadin.
鈥淪alamun kaulin min rabbirrahim鈥�
Ra'ees kam tsakanin mikewa tsaye da fallawa da gudu ba zaka iya fadar wanda ya riga wani ba, a maimakon yai daji sai ya gaishe gidan makotansu, matan gidan na daka suka saki tabare kowace ta shiga dakinta da gudu suna ihun kwarto. Aka bar Ra'ees tsakar gida sai rawar sanyi yake ga wani uban fitsari daya cika masa mara, tun da yake a rayuwarsa be taba ji murya irin da Fadime ba, zanar gidan ya fara bi da kallo zuciyarsa na raya masa garin aljanu suka zo. Cikin tashin hankali Bappa ya kawo kofar gidan makocin nasa yana fadin
鈥淪ubhanallahi鈥�
鈥淜ado fito gidan matan aure ne鈥�
Matan auren da Bappa yace sai Ra'ees yaji kamar Bappa yace masa gidan matan aljanune saboda sune a ransa, a maimakon ya fita sai ya shige bukkar dake kusa da shi gumi har karyo masa yake, aiko ba shiri matar ta saka ihu ta fito daga dakin da sauri.
鈥淲ayyo Jama'a ga kwarto鈥�
Sai da Bappa ya shigo yaja hannun Ra'ees suka fita daga gidan, idon Ra'ees na kasa yana ta kallon kafafuwansu so yake ya ga kofatai, dan shi gaba daya ya gasgasta aljanun ne, domin har yanzu yana jin muryar Fadime cikin kunnensa.
鈥淒an Allah dan Annabi karku mana komai鈥�
Ra'ees ya fada yana ta kallon kafafuwansu, kana ganinsa kasan baya cikin hayyacinsa natsuwa ta bar jikinsa, Alhaji Tukur tuni ya shige cikin mota ya rufe ta budewa Ra'ees dayan side din yana masa alama da ya zo da rugo su gudu.
鈥淚nna duk ke kika kore min miji kin ce na taba wuyana na fada masa ciwo yake gashi nan ya gudu鈥�
Fadime ta shiga gida tana kuka tana fadin haka cikin muryarta mai bantsoro, Inna da Amo suka shige bukka daya da gudu jikinsu na rawa, a tsakar gidan Fadime ta fadi ta bude muryarta mai ban tsoro tana kuka, da sauri Bappa da mutanensan dake gurinn Ra'ees suka sake shi suka nufo gida da gudu, a nan Ra'ess ya samu sa'ar aunawa da gudu ya shige motar da Alhaji Tukur ya tayar, Alhaji Tukur ya fisgi motar kamar sun sato mutum.
Suna barin kofar gidan muryar Fadime ta koma daidai, kukan da take rirewa ya dawo normal muryarta ta ainahi, aiko da sauri ta tashin ta kabe jikinta ta nufi waje, ganin babu su babu labarinsu yasa ta zube a kasa ta fashe da sabon kuka gaban abokanin Bappa da yan gari da suka fito kallon ikon Allah.
FALMATA POV.
Kamar ance daga kanki ki kalli sama, sai ta hango wani tsaya a backyard din yana kallonta, baki ne wulik kamar ita sai dai ita din ta fishi kyau, waya rike a hannunsa sai dai ba wayar yake kallo ba ita yake kallo, sauke kai tai kasa tana wasa da yan yatsunta ta dayan bangare kuma tana ta tunanin irin hukuncin da zata fuskanta idan suka isa gida, wata kila Baba ya sake korarta ko kuma ya doketa ko ma ya tsine mata kamar yadda Tumba take fata. Bata raba dayan biyu ba Momy ta fito sanye da wani farin lace da mayafi red da jakarta ma red, tun kan ta karaso ta danna key motar ta cireta daga lock.
鈥淏ude ki shiga鈥�
Momy ta fada tana mata alamar da zata gane. Ba musu Falmata ta bude motar ta shiga gidan gaba Momy ta zauna a mazaunin direba tai warming din motar, mai gadin na gani haka ya bude mata mata gate.
鈥淚na ne unguwarku?鈥�
Momy ta tambaya da muryar da Falmata zata iya jinta. Falmata ta fada mata cikin sanyayyiyar murya, kallonta kawai Momy tai taja motarta suka kama hanya. a bakin hanya Momy ta faka motarta domin unguwar irin unguwar nan ce da Mota bata shiga sai babur ko kuma mutum ya taka a kafa. Falmata na gaba Momy na binta a baya har suka isa gidan, ba karamin Hijadi tai ba na saka kafarta cikin gidan duk kuwa da irin yadda zuciyarta ke bugawa kamar zata fasa kirjinta ta fito. Da sallama ta shiga Momy ma ta dora da nata sallamar tana karewa gidan kallo.
Tumba ce ta amsa musu tana kallon Falmata da mamaki da kuma dake bayanta rike da jakarta, tun kan Momy tace komai Tumba ta shiga dakinta da sauri ya dauko tabarma ta shimfida mata.
鈥淪annu da zuwa sannu da zuwa鈥�
Tumba ta fada tana kallon Momy, kana ganinta kasan ba karamar mace ba ce,ba a shekaru ba a aji da zubi da kuma tufafin dake jikinta sun isa su sanarwa Tumba cewa wannan matar Hajiya ce, can ta kalli Falmata sai ta fashe da kuka.
鈥淔ulani ina kika shiga? Tun da shekaranjiya babu ke babu labarinki hankalinmu duk a tashe ko ruwa na kasa sha, Malam ma jiya cikin dare tashi yai ya zauna saboda baya iya bachi, yanzu kam ban gama da fadawa Allah bukatata ba na bayyana mana ke cikin aminci, ashe kina tafe鈥�
Kamar da gaske ta damu da Falmata haka hawaye ke bin fuskarta, Momy na kallonta cike da tausayawa duk da bata da da tasan yadda batan mutum yake tayardar hankali balle kuma danka. Falmata dai ta kasa cewa komai duk kuwa da kasancewar taji abunda Tumba take fada, dan ba da karamar murya take maganar ba.
Sanin cewar Falmata bata ji sosai kamar yadda Sirleem ya fada mata yasa, Momy ta daga murya gurin yi ma Tumba bayani.
鈥淭ana tafe ne a hanya, ina ta horn bata ji ba, har kadeta, sai ta suma da taimakon mutane muka kaita asibiti, bata farka ba sai yau, shine na tambaye ta ina iyayenta tace nan ne gidansu, shine na zo na rakota, daman na san sai hankalinku ya tashi鈥�
鈥淎llah sarki, ai dole hankalinmu ya tashi kam tun da maraya babu shi a kusa da kai dole hankali ya tashi鈥�
Tumba ta fada tana kallon Falmata da taji wani sanyi a ranta, sanadiyar karyar da Momy tai, ta san ta wanke ta gurin Tumba har ma da Baba kuma ga kudin Tumba Sirleem ya bata. Abun da Tumba ta fada yasa Momy ta kare mata kallo, tun nan ta fahimci wacece Tumba, idan tai hada labarin da Sirleem ya bada da kuma yanayin Falmata sai ta fahimci cewa Tumba tana yi ne kawai saboda ta ganta, domin ita na tasan yadda matan uba suke.
Momy ta saka hannunta a jaka ta dauko 5k ta mikawa Falmata.
鈥淕a wani Allah ya baki lafiya, kin ga mun manto maganin gida鈥�
Falmata ta saka hannu biyu ta karba, saboda a gaban Tumba ne bata isa tace a a ba.
鈥淗aba dai har da wahala haka? Ai da kin barshi mun gode sosai Wallahi鈥�
鈥淏a komai ai yiwa kai ne, ni zan tafi sai anjimanku鈥�
Momy ta fada tana mikewa tsaye, har bakin inda ta aje motarta Tumba ta rakota tana mata godiya sannan ta juyo ta dawo gida. Tana shigowa Falmata ta mike tsaye ta mika mata kudin duka.
鈥淎i kara ma data kade ki gashi mun samu 10k鈥�
Tumba ta fada tana kirga kudin.
鈥淒ubu biyar kudin adashenki ne, a lokacin da naje ban same ta ba sai na wuce da kudin gurin aiki kamin nakai ne abun ya faru鈥�
鈥淏a komai ai dai kari yafi kara, ni da na dauka ko guduwa kika yi da kudina Wallahi, ashe kadeki akai鈥�
Falmata dai ba ta ce komai ba, ta mike tsaye zata shiga dakinsu zuciyarta fal da farincikin abun da Sirleem yai mata.
鈥榊ana da saukin kai be da girman kai ba da wata matsala a rayuwarsa, yana son mutane kuma yana taimako鈥�
Ta fada a ranta sannan ta bude jakar kayanta ta dauko hular daya taba bata tana tabawa fuskarta da murmushi.
鈥淜a taimake ni ka tsiratar da ni yau鈥�
Wannan karon a fili tai maganar ta rumgume hularsa tana jin wata sabuwar kaunarna na shiga ranta, ko a da can da bata san halinsa ba tana son sa balle kuma yanzu da daya taimaketa.
鈥淭o sai ki fito ki tafi wajen aikin tun jiya ba kije ba kar su ce ba zasu baki albashi ba ko su koreki鈥�
Cewar tumba daga wajen da take zaune ranta cike da farinciki. Da sauri Falmata ta mayarda hular ta fito ta saka takalminta.
鈥淶an wuce mata da kudin adashen ne ko kuwa?鈥�
鈥淎a ni zan kai mata da kaina, Wallahi da ban ganki kin dawo ba kuma na aika tace ba ki kawo mata kudin ba, har wani zazzabi na ji ya ta so min, sai yanzu kaina ya zauna ciwo鈥�
Ajiyar zuciya Falmata ta sauke ta kalleta sau daya ta dauke kai ta nufi hnayar fita. Ina aka ganki yaushe kika dawo shine abunda kowa yake tambaya domin Tumba ta yada cewar wai dan Baba ya daketa shine ta ji haushi ta gudu, sai a lokacin ne wasu suke fahimtar Falmata bata ji sosai domin sai sun yi da karfi take jin abunda suke fada, shakku ya fara shiga zukatan mutane game da irin rikon da Tumba take mata, duk kuwa da kasancewar Falmata bata taba fadawa kowa matsalarta ba bayan kawarta Khadija, sai dai labarin da Tumba ta yada da kuma ganin Falmata ta dawo har ta fadi cewar kadeta akai ya ba mutane mamaki.
Babu wani abun kirki a cikinta kasancewar bata karya batun suka taso a gidan Momy kuma cornflakes kawai ta sha har yanzu bata jin jikinta da karfi, sai dai karfin zuciya da Sirleem ya sama mata a yanzu, ita kanta ta san dawowarta yafi tafiyarta a yanzu duk kuwa da irin wahalar da take sha.
A yau kam kallo daya zaka mata ka fahimci tana cikin farinciki da annushuwa, abun da ya dade be rabe ya ba. Ta shiga cikin gidan tana tsara yadda zata shimfida musu karyar da Sirleem ya koya mata. Kamar kullum yau ma gidan na cike da mutane kowa sai shanin gabansa yake, ita ma ta nitsa kai tana tafiya har ta isa gate din Ammy. Tana shiga ta ci karo da Iya tsaye ita da Zainab da alama wata maganar suke, wani irin faduwa gaban Falmata yai sakamakon ido hudu da suka yi da Iya har sai da kanta ya sara, addu'o'i ta fara karantawa tana kallon Iya wacce tai saurin dauke kai ta juya gurin flowers kamar ta rude ta fara taba su, Zainab ma ta lura da hakan sai ita a tunaninta Iya tana tsoron Falmata ne.
鈥淏arka da yamma鈥�
Falmata ta fada tana risinawa Zainab. Wani uban tsaki taja ta dauke kai ta nufi gurin mahaifiyarta.
鈥淲ai tsoronta kike ji ne Iya?鈥�
Iya bata yarda ta juyo ba sai da Falmata ta shige falon farko.
鈥淏a tsoronta nake ji ba, makircinta nake tsoro, domin zata iya zuwa tace na harareta, kuma tun da har ba ni da gata a gidan nan Ammy zata iya yarda wata kila ma ta koreni ta daga masarautar nan鈥�
Zainab ta juya tana kallon falon da Falmata shiga kamin ta juyo ta kalli mahaifiyarta.
鈥淗aba dai Iya, a yadda kike a cikin gidan nan har wata ta isa ta zo a kwana biyu tace zata saka ki tsoronta?鈥�
Iya ta dafa ta.
鈥淭o ai ta fini gata ne Zainab鈥�
鈥淜amar ya?鈥�
鈥淜ina tunanin ina da gadon sarautar gidan nan ne?鈥�
Zainab ta girgiza kai alamar a'a.
鈥淜ina tunani ni ko ke akwai wanda za a bawa gadon Mai Martaba idan ya mutu?鈥�
Nan ma kan ta girgiza.
鈥淣a isa na samu Ammy da wata magana da dauka? Tsawon shekarun da nai ina bauta musu?鈥�
Zainab ta dan yi shiru.
鈥淓h ai wani lokacin ma Ammy tana neman shawararki a wasu abubuwan鈥�
Iya ta yi murmushi tana girgiza kai.
鈥淜arki yaudari kanki, tana daukar shawarata ne idan ta yi daidai da abun da take so, ban isa nace ga yadda za'ayi ba ayi sai dai yadda aka yi ni na bi, shiyasa kullum nake nuna miki hanya kin kasa gani, ina son na samu matsayin da zan iya cewa eh babu mai musa min, idan kuma na ce aa babu mai daga ido ya kalle ni balle yace dan me? Shekarun da nai ina bauta a gidan nan kar su tashi a banza鈥�
Har Zainab ta bude baki tai magana sai wayarta tai kara, kiran Auwal ya shigo mota, murmushi ne ya kayata fuskarta ta amsa kiran da sauri daman abun da take jira kenan.
鈥淗ello Baby鈥�
鈥淣a'am yakike?鈥�
鈥淕ani a waje鈥�
鈥淥kay ina zuwa鈥�
Ta sauke wayar sannan ta kalli Iya cikin jindadi.
鈥淕ashi nan ya zo, Iya ki je dakinki zai shigo ku gaisa鈥�
鈥楰in kuwa ja masa mutuwa鈥�
Iya ta fada a ranta a fili kuma sai ta sakar mata murmushi ta gyada mata kai, sannan ta nuna ta da yatsa da fuskar dake nuna ba da wasa nake ba tace
鈥淭au na ji, amman zancen tafiyar nan a bar shi karki waiwayi garin nan鈥�
Zainab wacce har ta juya ta juyo ta kalli Iya da mamaki a fuskarta.
鈥淏an gane kar na waiwayi garin ba, daman na taba zuwa ne?鈥�
Iya ta daga mata hannu.
鈥淛e ki tarbi bakonki zamu yi magana鈥�
Zainab ta juya ta nufi hanyar fita tana sanye da doguwar rigar atamfa sai dan karamin mayafin dake kanta.
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence via 08036126660*
03/12/2021, 09:21 - 馃馃馃馃: *Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence via 08036126660*
UNCLE AA POV.
sai da ya fita daga Masarautar gaba daya yai nisa da ita ya tabbatar da babu mai jin abun da zai fada sannan ya sake kiran line, ringing daya Nana ta dauka sai ya marairaci murya kamar zai yi kuka, a zahirin ma zai ya kukan domin ya lura msarautar ba karama bace idan kuwa har ta tabbata ba zai yi driving din ba ai ba karamar hasara yai ba, sarki guda? Sarkin ma na Yola, ga yarsa da bata san zafin kudi ba.
鈥淣ana na san kina son ki taimake ni ne saboda ni maraya ne, ba ni da uba ba uwa daga ni sai Yayata muka rage, kin ga wannan aikin da zaki sama min ba karamin taimako zaki yi ba, Allah kadai ne zai iya biyanki, kuma ni yanzu kin zama uwar dakina kuma uwata mai share min kukana, ban yi zaton za a hana ni aiki a gidan ku鈥�
Nana dake zaune a falon baki tana jiran shigowarshi ta tashi daga kwancen da take.
鈥淢iya faru鈥�
鈥淚na shigowa na hadu da wata yarinya mai kama da bebin roba tace min wai ba za a dauke ni aikin ba, ba ki ji yadda na ji ba Nana, amman nasan ina da Allah, ina dake kuma zaki min gata ni kuma zan zama mai biyaya a gareki ba zan taba sabawa umarninki ba鈥�
鈥淜ana iya yanzu?鈥�
鈥淣a ma fita daga gidan na yi nisa kar ace na yi wani abun鈥�
鈥淜a dawo yanzu gani nan fitowa鈥�
Nana ta kashe wayar a fusace, wani irin dadi ne ya lullube shi.
鈥淎llah na gode maka da ka hada ni da yarinyar nan Allah, Allah kasa ta rika jin tausayi na tana bani kudi, Allah sani bani da komai sai burge da wankan karya Allah ka min arziki ta hanyar yarinyar nan Allah鈥�
Ya fada yana kallon sama, ya ci wanka kam iya wanka idan ka ganshi kamar dan wani shege, bayan ko har wuni yake da yunwa wani lokacin, juyawa yai ya nufi hanyar komawa cikin masarautar.
A fusace Nana ta isa Part din Hajiya, dan yana fadar mai kama da babin roba ta gane cewar Jurry ce dan tafi kowa rashin kiba a gida sai fari kamar zabiya, Hajiya na zaune tana tauna maganar Jarma wacce ta hanata sukuni ciki har da zancen tafiyar da babu dawowa wa zai yi tafiyar? Waye Sardauna waye Fadime balle kuma Falmata? Shigowar Nana yasa tai saurin daukar remote ta canja channel kamar da gaske kallon take.
鈥淗ajiya kin ga Yaya Jurry ko? Wai ta kori driver na wai ba zai yi aikin ba鈥�
Nana ta fada kamar ta fasa kuka, sai Hajiya ta mika hannu ta rikota.
鈥淛urry tace za a daukar miki sabon driver ko ni?鈥�
鈥淜e鈥�
鈥淭hen why maganarta zata taba ki? Je ki kira driver鈥�
鈥淵a shigo yana harabar gida鈥�
鈥淭o kije ki bashi key din, nawa ake biyan wacan?鈥�
鈥�35k鈥�
鈥淲annan zamu ba shi 40k, zan kira Waziri na fada masa a saka shi a list鈥�
Da sauri Nana ta rumgume Hajiya tana murna.
鈥淭hank You Hajiyata I love you鈥�
Sai da ta aje mata wayarta sannan ta fice daga dakin. Ta gate din Hajiya ta fito sai ta same shi kusa da gate din tsaye, tana kallonshi taji ya matukar burgeta saboda yayi wanka mai kyau, daman can kuma ko kallonsa tai nishadi take ji.
鈥淜a zo?鈥�
鈥淓h鈥�
鈥淣a yi ma Hajiya magana tace za a baka 50k per month鈥�
鈥淒a gaske?鈥�
Ba shiri AA ya zauna a dan simitin da aka zagaye fulawa da shi a gurin.
鈥淭o zan maka karya ne ko na taba maka karya鈥�
Nana ta fada da dan fada fada, sai da yai kamar ya rama sai kuma ya tuna a inda yake sai ya dariya.
鈥淎a Hajiyata na gode sosai, yanzu na tabbatar da ke yar gata ce, amman sarkin ne Babanki ko kuma rikonki ake a gidan?鈥�
鈥淚na ruwanka?鈥�
Nana ta fada tana turo baki dan ita dai bata son yawan tambaya da bincike.
鈥淏a ruwana fa鈥�
Ya amsa mata da sauri yana sosa kai.
鈥淭o bari na je na karbo maka makullin motar, amman nan ba gidan mu bane ka biyo muje gidan mu鈥�
鈥淭o nan gidan su waye?鈥�
鈥淲ai ina ruwanka?鈥�
鈥楧aga gani idansu wannan bebin robar ne shiyasa ta hana a dauke ni aiki dazun, kai no kila ma wanki take musu daman wadanda ba yayan kowa ba sun fi komai falako idan sun yi abu, ni ma nan da kwana biyu zan sayi mota ana fara budawa a gari鈥�
Ya fada a ransa a fili kuma murmushi kawai yake yana kallon Nana wacce ta wuce apartment dinsu yana binta a bayata. A bakin gate ya tsaya ita kuma ta shiga ciki.
FALMATA POV.
sai da ta kusan minti ashirin a tsaye sannan aka bude mata kofar, sallama ce abun da ta fara yi sannan ta shiga cikin falo cikin tsoro tsoro kamar wacce tai laifi.
鈥淛ekadiya tabo min yarinyar nan鈥�
Wacce Ammy ta kira da Jekadiya ta kyafato Falmata da sauri tana nuna mata Ammy.
鈥淜u zo tare zan yi magana da ita鈥�
Jekadiyar ce ta yi saurin karasowa kusa da Ammy kasancewar tafi kusa, sannan Falmata ma ta karaso tana mikawa Ammy gaisuwa irin ta sarki da talaka duk kuwa da bata da tabbacin zata amsa. Haka Ammy ta shansu a gurin sai da suka kusa bushewa sannan tace.
鈥淭ambaye ta miya hana ta zuwa aiki jiya鈥�
Jekadiyar ta rada mata a kunne, sai Falmata ta kitsa musu irin karyar da Momy tai ma Tumba. Sai da Ammy ta kare mata kallo sannan ta dauke kai tana kallon Nana wacce ta shigo falon a yanzu.
鈥淎mmy key din motar za a bani ga driver can ya zo鈥�
Wani banzan kallo Ammy tai mata.
鈥淏a a bincike ko waye shi ba za a bashi aiki a gida nan? Ba al'adar gidan nan ba ce鈥�
鈥淗ajiya ta bincike shi ta san gidansu, ni ma kuma na sanshi鈥�
鈥淔ine.... Amman duk yai garkuwa dakw ba zan bada ko naira ba, sai dai ya kashe ki鈥�
Nana ta yi shiru bata ce komai ba, sai turo baki take gaba, sai da taga Ammy ta dauke kai sannan ta wuce dakin Ammy ta dauko key din ta fice. Ammy ta bita da kallon takaici sannan ta kalli Falmata tace.
鈥淜in iya addu'a鈥�
Jekadiyar ta rada mata.
鈥淓h na iya sosai鈥�
Ammy na kallonta cike da burgewa tace.
鈥淲aya koya miki? Mamana kamun ta rasu, kuma ina da Hisnul muslim na iya addu'oin sake da yamma鈥�
Dan murmushi kadan Ammy tai tana jin gamsuwa da natsuwar Falmata a ranta, tana jin kamar ace Nanarta ce a haka.
鈥淭o zaki rika musu addu'ar safe, da kuma yamma, za su rika wuni a hannunki har sai sun yi bachin dare sannan ki tafi gida, da safe kuma zaki zo tun 7am, idan kuma iyayenki za su yarda su barki ki rika kwana a nan shikenan鈥�
Sai da Jekadiyar ta rada mata sannan Falmata ta amsa.
鈥淭o Hajiya鈥�
鈥淛ekadiya a karbo yaran a gurin Iya, a fada mata an samu mai reno鈥�
Jekadiya ta tashi dan cika umarnin Ammy, Falmata na zauna a gurin har Jekadiya taje ta karbo Labib da Luma ta kawo su falon Ammy.
鈥淏ismillahi Rahamanin Rahim鈥�
Falmata ta fada a lokacin da Jedakiya ta mika mata Labib. Hakan kuma ba karamin burge Ammy yai ba, sai ta ji hankalinta ya kara kwantawa da ita. Wani irin murmushi da annashuwa ne suka mamaye fuskar Falmata, daman can tana son yara sai take jin kamar ance mata dauki ga yayanki nan ki yi raino. Da hannu Ammy ta nuna mata hanyar dakinsu sannan ta kalli Jekadiya tace.
鈥淜i karasa mata bayani鈥�
鈥淭o ranki ya dade Allah kara miki lafiya鈥�
Jekadiya ta bi bayan Falmata rike da Luma. Sai da suka shiga cikin dakin sannan Jekadiya tace.
鈥淒uk inda kike so za ki iya shiga a cikin gidan nan dan raino, ana fita da su waje amman ba sosai ba, idan kuma zaki gyara dakin sai kin kai su dayan dakinsu tukuna, a yanzu dai duk sun iya zama suna koyon tsayi ne, sai ki kula da su sosai, ana ba su madara da kunun waken soya da nake hada musu, Ni ko Iya ne muke musu wanka da safe mu shirya su haka ma yamma, aikinki canja musu pampers鈥�
Falmata ta gyada kai tana kallon jekadiyar wacce ta ke mata bayani cikin hikima da natsuwa, bata taba ganin ta ba sai hau haka zalika Jekadiyar ma bata taba ganin Falmata ba sai yau domin a lokacin da aka kawo ta gidan Jekadiya ta tafi mahaifarta ganin family.
HAJIYA BABBA POV.
After like 10 minutes da fitar Nana a falon Sirleem ya shigo, har ya zauna saman kujera be yarda ya daga kai ya kalli Hajiya ba, saboda ya san fushi take da shi.
鈥淜a kyauta, ka bar nan ka je Kaduna gurin Karuwa ko? Yarinyar da Mahaifiyarka bata son mu'alamar ka da ita鈥�
Sai a lokacin ya dago ya kalleta amman ya kasa furta komai.
鈥淲ai Sirleem yaushe zaka yi hankali ne? Mansurar nan fa ina jin ma ta tsufe ka ko ku zo wari miye riba a auren irin wannan kuma yarinyar da ba kabilarka ba? Me Mansura take da shi da Nana ta rasa?鈥�
Wayarsa dake silent yake kallo kiran Mansura ne yake shigowa kamar tasan maganarta ake. Ba tare da ya dago ba tace.
鈥淶an auri Nana ne kawai Hajiya saboda kina son aurena da ita, amman ba dan Nana tana cikin irin matan da nake so ba鈥�
鈥淜o kaso ta ko karka sota duk uwarsu daya, kai bari ka ji na fada maka, ko da Nana zatai cikin shege ta haihu sai ka aureta, kai da za a ce Nana tana ta Hiv dole ne ka aureta, dan dole ne burina ya cika, dole ka yi min abun da nake so鈥�
Kallon Hajiya kawai yake, zuciyarsa na raya masa da kamar akwai manufa a auren da Momy take son hada tsakaninsa da Nana, baya son yai wani mummunan tunani akan mahaifiyarsa kuma baya son zatonsa ya zama gaskiya, why ma Hajiya zatai haka? Mikewa yai tsaye.
鈥淶anje na kwanta鈥�
Bata ce masa komai ba, ta dauke kai.
鈥榃aya sani ma ko kaine zaka lalata abun da aka fada鈥�
Ta ayyana a ranta, can kuma ta sauke ajiyar zuciya.
鈥淜uma wani lokacin fa bokayen nan suna karya, waya sani ko karya suke dan su ci kudi? Kai ni ban ma yarda ba gaskiya鈥�
Ta fada a fili bayan ta tabbatar da cewar Sirleem ya fice daga falon.
FADIME POV.
鈥淜oni abu dai be yi kyau ba鈥�
Bappa ya fada cikin rashin jindadin abun da ya faru, muryarta ta dawo daidai bayan sun riga sun tafi, a yanzu kam kowa ya yarda Fadime tana da aljanu, domin su kadai ne zasu iya saka mutum haka. Daker da sudin goshi aka saka Fadime cikin gida, wani irin bakin haushin Wasim take ji tana jin kamar ta dauki wuka taje ta kasheshi, ba a taba zuwa ance ana sonta ba sai yanzu, kuma daga birni amman yasa muryarta ta zama abun tsoro sun gudu.
鈥淚nna Hajjo ki ce musu muryata ta dawo su dawo dan Allah鈥�
Amo dai bata ce komai ba sai hadiyar yawu take, domin ita ma a yanzu tana dan tsoron Fadime. Haka Fadime ta wuni a gidan tana kuka kamar an mata mutuwa data tuna sai ta ji kamar ma ba zata iya shan ruwa ba, ga wani uban haushin Wasim da take ji, har alwashin ta ci cewar indai ta samu sa'ar fita taje dajin nan sai ta samu dutse ko kuma ta je da wuka ta caka masa.
Daker ta yi bachin dare kamin safiya ta waye duk ta matsu, so take kawai ta samu sa'ar fita taje dajin tai masa kacakaca domin dai yanzu ta gane shi din makiyinta ne, sai yanzu ta gano dalilin mafarkinsa da take ashe dan ya cutar da ita ne, yanzu ga miji ya zo amman yayi sanadin guduwarsa.
Kokon da Inna ta dama mata kadan ta sha tace mata zata je gidansu Ma'u.
鈥淏a fitarki ba ki dawo da hitina, ni tsoron hitarki nake鈥�
鈥淚nna daga gidansu ba zanje ko'ina ba, kawai labari zan bata鈥�
鈥淭o Allah ya tsare amman ki kiyaye Malam yace kar na barki ki fita fa鈥�
鈥淵anzu zan dawo鈥�
Ta fice daga gidan cikin sauri kamar zata tashi sama, a maimakon ta nufi gidansu Ma'un kamar yadda ta fada sai ta dauki hanyar dajin, tana tafe tana matsifa har ta isa, da yake yau da masifa ta zo sai ta haye saman dutsen ma ta zauna tana jiransa, zuciyarta ta cika har ta kusa fashewa, ga kuka da take jin kamar zai subuce mata, data tuna abunda ya faru sai ta ji kamar ta fashe kuka.
鈥淏a zan yi kuka a nan ba amman Wallahi yau ba zan kyale ba鈥�
Maganar take kuka na subuce mata, kuma har ga Allah tsoro take ji, dan mutumen da zai iya dabon maciji kuma ya mayarda muryarta abun tsoro tasan ba karamin shu'umi bane. Kasa ta hango shi tsaye yana dago mata hannu, duk irin kaurin guiwarta da masifar da ta zo ta so sai fa ji kamar basa tare da ita saboda tsoron ganinsa da tai. Mikewa tai tsaye ta sauko saman dutsin ta tsaya a kasa. Kallonta yake cike da burgewa yana murmushi.
鈥淢e nai?鈥�
Kallonsa tai kamar ta daka masa tsawa tai masa masifa kuma tana jin tsoro waya sani ko ya maida ta bera yanzu kuma.
鈥淢utanen sun zo?鈥�
鈥淢iyasa ka karesu?鈥�
鈥淣i na koresu?鈥�
Ta fashe da kuka.
鈥淪un gudu sun ji muryarta abun tsoro, yanzu ba za su sake zuwa ba, kuma gashi nan babu mai zuwa hadda birni suke ma kuma suna da mota, kuma ni ina son shi ya min, yanzu shikenan ba za su sake zuwa ba鈥�
Kuka take da gasken gaske tana hawaye shar har idonta sun fara ja. Shi kam kallonta kawai yake yana murmushi kukan da take ma burgeshi take, a rayuwarsa be tana haduwa da macen da komai nata yake burge shi ba kamar Fadime.
鈥淶auna鈥�
Ta ki zama sai kuka take, kafadunta ya dafa ya zaunar da ita sannan shi ma ya zauna yana kallonta kamar zai cinyeta.
鈥淎i wasu za su zo ko?鈥�
鈥淏abu wanda zai zo ni ba'a so na, Kuma fa yan boko ne鈥�
Ta kara fashewa da kuka, sai yai dariya.
鈥淣i ma nasan boko?鈥�
Kyaleshi tai sai da ta gama kukanta sannan ta kalleshi tace.
鈥淭o what is a now?鈥�
At first murmushi ya fara kamin ya tintsire da dariya, daya bayyana fararen hakoransa, ya shafa kansa sannan ya kai hannunsa ya cafko wutar bayanta.
鈥淎n sake saka miki wutar nan fa鈥�
Wani uban zabura Fadime tai ganin hannunsa na ci da wutar.
鈥淜ai ne kake saka min ita鈥�
鈥淣i ai ba zan cutar da ke ba, kuma idan aka sake saka miki wutar nan to zata kona mai ita ne鈥�
Ya fada da fuska dake nuna babu alamar wasa a maganarsa. Ita dai kallon tsoro kawai take masa kamin ta fara tafiya a hankali tana yi tana waigensa har ta samu ta daina hangosa sannan ta lafta da gudu kamar an korota.
SHATTIMA POV.
8pm yana zaune dakin karatunsa yana operating system dinsa Ra'ess ya shigo gidan. Mikewa yai tsaye ya kashe wutar dakin ya fito ya hanyo kofar, silently ya shiga kitchen ta hada ma kansa coffee yana fitowa Ra'ess na kawowa kofar kitchen din.
鈥淚nnalillahi wa'inna ilaihirraji'un鈥�
Ra'ess ya fada da karfi yana kallon Shattima dan be san da akwai mutun a cikin kitchen din ba, tun abun da ya faru a kauyensu Fadime ya kasa dawowa daidai ga shi ya kasa daina jin muryar a kunnensa.
鈥淎re you okay?鈥�
Shattima ya fada yana kallonsa, sai ya shafa fuskarsa yana jin kamar gumi na sauko masa.
鈥淚'm not, Wallahi i'm not....... kai......!鈥�
Ya fada sannan ya karasa cikin kitchen din ya bude fridge ya dauko ruwa mai sanyi ya sha sannan ya firo falon ya zauna, Shattima dai a tsaye jikin kofar yana kallonshi. Can ya dago ya kalli Shattima.
鈥淣eman aure na je wani kauye, amman na rasa ganewa, amman garin ai akwaishi, sai dai idan su wadanda muka je gurinsu ne aljanu, malam kaji wata murya?鈥�
Ra'ees be karasa ba Shattima ya tintsire da dariya kamar ba shi ba, daman can ya san Ra'ees da tsoro, amman a yanayinsa na yau ya tabbatar da abun da ya gani babba ne ba karami ba, but the funniest part is neman aure fa suka je kamar yadda ya fada, be fada masa komai ba a matsayinsa na babban abokinshi gashi yanzu sun dawo da wahala.
鈥淚t's not funny Man ba abun dariya ba ne鈥�
Shattima ya gintse dariyar da murmushi.
鈥淭hen kuka kake son nai? Imagine ka je neman aure ba tare da sanin best friend dinka ba?鈥�
Sai da Shattima yai maganar sannan Ra'ess ya tuna cewar Ammy tace kar ya bari ya san komai sai magana ta yi karfi.
鈥淜ai ba fa aure zan kara ba, wani na raka鈥�
Ya fada yana kokarin kawarda tunanin Shattima daya kasa daina murmushi ganin yadda gumi yake ta karyoma abokin nasa.
ZAINAB POV.
Sai da suka gaisa sannan ta shigo da shi falon baki a inda ta saba shigowa da shi idan za su fira, sannan ta tashi ta shigo cikin gida ta saka mai aikin gidan ta jera masa abinci da lemu.
Be ci komai ba, dan babu abun da yake bako a cikin abun da aka shirya masa, ruwa kawai ya sha ya cigana da danna wayarsa.
Ba a dauki dogon lokaci ba ta dawo fuskarta dauke da murmushi zuciyarta kuma cike da kaunarsa ta zauna a kujerar dake kusa da tashi.
鈥淶ata fito yanzu ku gaisa, idan ka gaisa da ita sai na kira Ammy ku gaisa鈥�
Ya gyada mata kai yana kara kallon kyakkyawar fuskarta wacce ke dauke kamar masa hankali a ko yaushe, ba ma shi kadai ba most mazan da suke sonta kyauta ne yake daukar hankalinsu.
鈥淎llah yasa dai kar sai magana ta yi karfi matarka tace na ci amanarta鈥�
Gyara zama yana cigaba da kallonta fuskarsa dauke da murmushi.
鈥淎i ba haram mu kai ba, kuma ko da baki nemi ni ba, ni zan kawo kaina da kaina gurinki, idan na fada miki cewar na dade da kaunarki cikin raina ba za ki yarda ba鈥�
Ta yi murmushi.
鈥淶an yarda ma ganin yadda kai saurin amincewa da ni鈥�
Lokaci daya suka daga kai suna kallon Iya wacce ta shigo falon cikin shiga ta alfarma kamar ba ita ba. Ba laifi ta sake masa fuska kamar da gaske tana na'am da shi din, har kasa ya kai ya gasheta Zainab kuma tana ta kallon Iya cikim jindadi, a iya tunaninta irin wannan ranar Iya take jira na ganin surukunta. Halshe Iya ta fitar kadan ta laso kurwarsa dake yawo a bayan kansa tasa hannu ta jimke ba tare da ita Zainab din ta kura ba balle kuma shi da ya ki yarda su hada ido.
Cikin mutunci da girmamawa suka gaisa sannan ta mike tsaye tana Allah shi masa albarka ta fice. Sai ya ciro bandir din yan dubu ya mikawa Zainab.
鈥淏aby gashi ki bata ta siye goro鈥�
Zainab ta karba tana murmushi ta bi bayan Iya ciki farincikin yau uwarta da mijin da zata aura sun gaisa da juna.
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence via 08036126660*
03/12/2021, 09:22 - 馃馃馃馃: *Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence via 08036126660 or 08061371579*
ZAINAB POV.
Sai da ta kira masa Ammy suka gaisa sannan ta raka shi har gurin mota, sannan su kai sallama. Part din Ammy ta nufo rike da kudin da ya bata yace ta bawa Ammy 100k, dayan hannunta kuma rike da wayarta sai juyawa take har ta isa cikim falon. Kusa da Ammy ta zauna amman a kasa yayinda Ammy take zaune a saman cushion ta aje mata 100k din.
鈥淎mmy gashi yace a baki ki siye goro鈥�
Ko kallon inda kudi suke Ammy ba tai ba, tana ta aikin jar carbin da take ta ce
鈥淚na fatar kin kira masa Hajiya ya gaishe ta鈥�
Zainab ta dan yamutsa fuska.
鈥淢iye hadina da Hajiya Ammy鈥�
鈥淗adin da kike da shi da ni鈥�
Ammy ta amsa mata tana kallon cikin tsakiyar idonta. Sinne kai kasa Zainab tai sannan ta mike tsaye.
鈥淎mmy tafiya gobe ce In-Sha-Allah鈥�
鈥淜i kirashi ya zo ya gaishe ta idan kin dawo鈥�
鈥淭o鈥�
Ammy ta dauke kai ta maida gurin plasma, ko kadan Zainab bata jidadin abun da Ammy tai ba na cewar ita da Hajiya daya suke a gurinta bayan kuma har a bada ita ta san ba za su tana zama daya ba. Tana fitowa bangaren Ammy ta nufi dakin mahaifiyarta, sai ta same ta zaune bakin gado ta dora kafa daya saman daya tana kallon kofar kamar tana jiran shigowarta.
鈥淵a tafi, yace idan ya fadawa iyayensa zai sanar da ni sai a sanar da dangi na鈥�
Iya ta kalleta a yayinda take kokarin zama kusa da ita.
鈥淣a ga har yanzu ba ki gane hanya ba, to bari na kai miki gidan, ke a yanzu duk soyayyar da kike yi ma Shattima ta me ce?鈥�
Zainab ta yi mata wani kallon rashin fahimta da mamakin furucinta.
鈥淏an gane ba?鈥�
鈥淏aki taba sha'awar ya zama mijikin ba? Me Shattima ya rasa wanda wannan yaron yake da shi?鈥�
鈥淪hattima yana da komai Iya, tabbas ya kai a so shi amman mi kallon dan'uwa nake masa鈥�
鈥淏abu alakar jini a tsakaninki da shi balle ta tsoka, ni da ke da duk wanda ya san waye mu a gidan nan kallon bayi yake mana, har yanzu baki fara tunanin samun yanci ba? Baki fara tunanin yadda zaki zama matar sarki kamar Ammy ba? Baki fara tunanin wata rana Shattima zai zama sarki ba?鈥�
Iya ta karasa tana bude mata ido tana ji kamar ta hau ta duka. Zainab ta girgiza kai.
鈥淎a ban taba yi ma Shattima kallon miji ba, ban taba jin sonsa a raina ba, ina masa kallon dan'uwa ne, saboda ya dauke ni kamar kanwarsa, yana kula da matsalolina yana nuna damuwarsa akaina, mahaifiyarsa kuma ta dauke ni ya, kanwarsa ta zama kanwata wannan kawai ya isheni, idan tunaninki na hada aurena da Shattima ma ne to ki daina, ki kina ganin akwai wanda zaki cilasta min sonsa ki aje, Auwal kawai nake so a yanzu kuma shi zan aura鈥�
Tana kaiwa nan ta mike tsaye a fusace ta fice daga dakin, ta rasa gane dalilin Ammy na son cilasta mata son Shattima, tabbas Shattima yana da kyau yana da siffar da mace sata ganshi ta hade yawu amman ita bata taba masa kallon miji ba.
Bayan fitar Zainab Iya ta kada kai ta bude tsokar dake hannunta, ta mike tsaye ta isa gaban madubinta ta bude durowar madubin ta dauko bakin zare ta nade tsokar wacce ke ta motsi kadan kadan alamar akwai rai a tare da ita.
鈥淜in jawa yayansa zama marayu, matarsa tai takaba ke kuma sai mu gani idan zaki auri gawa鈥�
Ta karasa tana zare ido cikin bacin rai. Zainab na isa dakinta ta bude karamin fridge dinta ta sha ruwa sannan ta kwanta saman gadon tana ta mamakin yadda tunanin iya ya bata wannan, saboda su ta zama abunda ta zama a yau saboda su aka santa a instagram har ta samu aikin photography duk wannan be isa ba? Akan me zata hararo hada aurenta ta Shattima bayan ta san shi ma kansa Shattima be taba mata kallon so ba, kuma sai a yanzu da ta samu wanda take so?
Cikin daren ta shirya duk wani abu da zata shirya na tafiyarta, sanin jirginsu zai tashi 9am yasa tun cikin dare taje tai ma Ammy sallama, sannan ta shiga gurin mahaifiyarta.
鈥淚na tunanin tun 8:30 zan isa airport, maybe ko da zan wuce ba ki tashi bachi ba鈥�
Iya ta kalleta tana jin haushinta har yanzu.
鈥淣i ban taba zuwa garin ba, amman sai fada miki kar na waiwayi garin kuma baki tashi fada min ba sai a yanzu da gobe zan wuce? Sometimes Iya bana iya gane鈥�
Uffan Iya bata sake ce mata ba, hakan yasa Zainab ta mike tsaye ta nufi kofa, sai Iya ta zira halshe ta laso kurwar yarta, ta jimke ta a hannu, sai da Zainab ta fita sannan ta mike tsaye ta nufi gaban madubinta ta dauko zare ta nade kurwar ta bude wardrobe dinta ta dauko wata tukunyar kasa ta bude bakin kyallen dake kai ta fadi bukatarta sannan ta maida ta aje ta rufe wardrobe dinta ta mike sokar tsaye wacce tai ma wani tsoro daya da zare ta masa gefen tsoron sai ta sake saka yatsanta ta matsa gefe, ta nufo gefen gadonta ta daga karamin carpet dake gurin ta saka tsokar ta maida carpet din ta rufe tana ta zare ido kamar za su fito.
鈥淪ai ki yi tafiyar na gani鈥�
*** *** ***
Zainab na kokarin kai hannu ta bude kofar dakinta ta ji kanta ya tsara da karfi ya amsa har gurin bayanta.
鈥淥uchhhhh鈥�
Ta fada tana dafa kan da dayan hannunta sannan ta karasa cikin dakin ta bude durowar ta ta dauko magani ta balla ta sha, sannan ta kwanta tana jin kamar ciwon na karuwa, cikin karfin hali ta kunna data ta shiga instagram sannan ta leka whatsapp tana kokarin ashe datar ta sauka kiran Auwal ya shigo wayarta, dan murmushim karfin hali tai sannan tai picking call din.
鈥淎s usual i just call to say good night baby鈥�
鈥淭hank You i love you鈥�
鈥淚 love you more, ki kula min da kanki鈥�
鈥淪ure鈥�
Ta aje wayar tun kan ya kashe saboda bata son yin magana ciwon kan da gefen hakarkashinta ya soma matsa mata da ciwo, ko tufafin jikinta bata iya canjawa ba ta kwanta hakan nan saman gadon. Bata farka ba sai da sanyi asuba ya soma shigowa dakin, kasancewar bata kwanta a natse ba ko window dakinta bata rufe ba.
Bandakinta ta shiga tai wanka tai alwala sannan ta fito daure da tawul tana jin kan har yanzu be daina mata ciwo, ko mai bata shafa ba ta saka abayarta ta saka Hijab tai sallah sannan ta saka alarm a wayarta ta sake kwantawa. 8:30 ta farka ta kashe alarm din ta dauki karamar jakarta ta rataya babbar kuma ta janyo ta ta fito dakin rikw da wayarta da kuma ticket dinta. Sai da ta saka key a kofar sannan ta nufi hanyar da zata sadata da bangaren Ammy duk da tasan ba lallai ne ta same ta a bangarenta ba at this early morning matukar ita ke da girki yau.
Kamar yadda tai tsamma haka ta samu falon cike da hadimai masu gyara gurin kullum safe, kai tsaye ta nufi dinning ta hada ma kanta tea ta riko cup din ta fito dan ba zata iya jira ya huce ba, arba da tai da Jekadiya yasa ta saki murmushi.
鈥淛ekadiya yaushe kika dawo?鈥�
鈥淒a yamman jiya, fatar Hajiya karama tana cikin koshi lafiya鈥�
鈥淚na kalau yanzu ma tafiya zan yi鈥�
鈥淎mmy tace hadimai su raka ki airport鈥�
Jekadiya ta fada tana kallon Zainab sai ta nuna kanta.
鈥淣i...?鈥�
Sai jekadiya ta gyada mata kai.
鈥淜awarai kuwa鈥�
Dan murmushin jindadi Zainab tai a iya saninta, jinin gidan ne kawai ake yi ma rakiya da hadimai idan zasu tafi wani gurin, amman yau Ammy ta karramata.
鈥淪una waje suna jiranki, Baaba zo ki rika mata jakarta鈥�
Jekadiya na rufe baki Baaba ta zo a guje ta karbi jakarta dake hannun Zainab ta wuce.
鈥淣a gode Jekadiya鈥�
鈥淎ikin Ammy ne鈥�
鈥淎 mika godiya ta a gareta, Allah ya kara mata lafiya鈥�
Ta fada da murmushi a fuskarta, sannan ta bi bayan Baaba ko da ta fito hadimai har hudu na tsaye jikin motar da zata shiga da diriban da zai kaita suna jiranta, duk da ciwon da take ji be hanata jindadi da kuma nuna farinciki akan abun da Ammy tai mata ba.
FADIME POV.
Ba karamin mamaki ne ya cika Amo ba ganin yau ma ba wutar ya kai ta fita? Waya sake cire mata ita? Tana wanke kwaryar da take zuba manshanu idonta na kan Fadime dake taya Inna zoya gida. Ganin karan zai kare yasa Inna ya yaba gyalenta ta nufi dajin dan yi yayeyaye. Fadime na ganin ta tashi tai saurin baro gaban wutar ta nufi Amo tana fadin.
鈥淚nna Hajjo idan zaki je birni zaki fada musu cewar muryana ya dawo daidai? Su dawo鈥�
鈥淎a tare dai za mu je su gani da idonsu saboda su yarda鈥�
Fadime ta yi murmushi cike da jindadi.
鈥淓h shikenan ma sai su gan ni da idonsu鈥�
Sai da Fadime ta juya sai kuma ta juyo sakamakon kiran da Amo tai mata.
鈥淚dan kin je daji kina haduwa da wani ne?鈥�
Fadime ta yi shiru tana nazari, ta fada mata gaskiyarta ko ta boye?
鈥淎a ni bana haduwa da kowa, cewa akai ana ganina da wani ne?鈥�
鈥淎a kawai dai yadda kike dawowa ne wani lokacin yake bani mamaki鈥�
鈥淏ana ganin kowa, sai daji sai duwatsu, sai bishiyoyi鈥�
鈥淎llah ya kyauta鈥�
Ta fada a ranta tana ayyana cewar duk ranar da Fadime zata je daji sai ta zama mage ta bi bayanta dan ganewa idonta.
鈥淎mman Inna Hajjo idan zaki je da ni sai kin yi wayo dan Bappa zai iya cewa ba za aje din ba鈥�
鈥淭o Allah yasa su bari, ko na Innarki ta bari ba lalle ne Malam ya bari ba, amman zan masa magana na ji鈥�
Fadime ta juya ta koma gurin zamanta cikin jindadi, tana cigaba da juya gidar dake kan wuta. Sai da Inna tai kara mai yawa sannan ta shigo cikin gidan ta sauke ta cigaba da soyar gidar. Yunin ranar Fadime da tunanin zuwa birni ta wuni a ranta, ta dayan bangare kuma tana ayyana cewar ba zata sake zuwa gurin Wasim ba balle har ya samu nasarar yi mata wani sherin domin har yanzu haushinsa take ji.
A daren ranar saboda farincikin za aje birni yasa Fadime bata ko jira Inna tace mata ta dauki gidar ta tafi da ita dandali ba ta zuba da kanta ta kirga.
鈥淭a dari takwas ce Inna鈥�
鈥淭o idan kin siyar duka ki dauki hansi ki kawo min dari bakwai da hansin鈥�
鈥淭o Allah ya bamu sa'a鈥�
Tare da Hajjo suka fita, ita ta dauki gyada Hajjo kuma ta dauki dawon (Fura) da Amo take sarowa gurin Larai, har suka isa dandalin babu wanda da wani uffan daman can Hajjo da Fadime ba wani shiri suke ba, yadda basa son kula junansu abun har mamaki yake bawa mutane ganin suna gida daya ko da kasancewar mahaifin Hajjo daban. A inda ta saba zama ta zauna tana ta rabon ido a dandalin sai kallon yadda samari suke watsawa yan matansu kudi take, abun da yafi burgeta kenan fiye da komai, a take zuciyarta ta tafi wani bangare tana tunanin yadda kowa zai ji idan aka fadi cewar dan birni zata aura, idanuwanta sai gizon fuskar Ra'ees suke mata.
Ba kasafai take siyar da gidar idan ta zo da ita ba, domin mafi akasarin masu siyen abubuwa dandali maza ne ita kuma bata da samarin da za su siya balle su mata juye, sai dai a aiko yaro ya zo ya siye, an siye sosai samari da yan mata da kuma yaran da ake aikowa. Wani ma da ya zo sai yace ta kirga masa ta nawa ce gaba daya.
鈥淭a dari hudu da 20 ta rage鈥�
鈥淭o ki yi sadaka sai na baki kudin鈥�
Ta daga kai tana kallon mai maganar jin kamar ta san muryar, saurayi ma mai kira da siffar samartaka yana sanye da dogon wando sai rigar fulani, ya saka hullar sanyi a kansa irin ta fulani sannan yai rawani ya rufe rabin fuskar yadda ba za a iya ganewa ba. Hannyensa take kallo a lokacin daya kika mata yan dari biyar guda hudu fari ne sol duk da kasancewar wutar karar tana maida mutanen dake gurim jajaye da irin haskenta, sai dai baya haka hasken farin mutum fita balle kuma wannan da yake da haske sosai ga mazantaka dake nunawa a jikinsa, ta karbi kudin ta kirga 2k
鈥淣a dauka duka?鈥�
Ya gyada mata kaina yana ta kallonta kamar wanda be tana ganin irinta ba. Ba shiri Fadime ta jenye tray gabanta ta fara masa godiya, tana jin wani irin dadi marar misaltuwa ita ma yau an mata irin yadda ake ma sauran yan mata, be ce mata komai ba ya duka ya dauki kulli gya蓷a ta juyar sandar dake hannunsa ta korar shanu ya raba gefenta ya bi hanyar shiga gari, da kallon mamaki da jindadi Fadime ta bishi baki har kunne.
鈥淜iyaye鈥�
Ta fada tana daga masa hannu duk da be waigota ba. Yarinyar dake kusa da ita taja tsaki.
鈥淢tscheeeessss bakauya kawai sai kace kanta farau鈥�
鈥淒alla can matsa yarinya kin ji zafi kin yi hassada kin ga na fara samari, kuma ke ce yar kauye jahil da ko turanci bata iya ba, bakinki ma warin zunubi yake, ehhhh yarinya kin ji kunya beeeee ige zalla tumba yake yake鈥�
Fadime ta fada tana mata gwalo tana mata tsowa. A take yarinyar ta mike tsaye ta kwance ganwonta ta daure kugunta.
鈥淜e Fadime wallahi ki shiga hankalinki dan ni na fi karfinki鈥�
Fadime ta dubi zubin Bintalo ta san ko a kalle bata isa ta kalli Bintalo da harara ba balle tace zata bugeta, sai ta duka ta dauki tray tana fadin.
鈥淚dan kin isa ki tsaya na je na kai wannan tray a gida ki ga yadda ake hauka, Wallahi fadan kaza zan miki鈥�
鈥淭soro kike ji yarinya shiyasa kike son ki gudu, kin san ba zan taba raga miki a balle ki sha da dadi鈥�
鈥淜e dalla can gafara jahila da bata iya turanci ba, nonsense stupid girl, if you dare touch my body i will regret it鈥�
Dan turanci da Fadime tai yasa hankalin samarin dake wajen ya dawo kanta har ma da matan, suna ta kallonta cike da burgewa, Bintalo kuma tai cikinta ta ci kwalarta zata fara dukanta sai Fadime ta saki tray ta fara bamkarewa tana aljanun karya.
鈥淢u zaki taba mu aljanu?鈥�
Ba shiri Bintalo ta saketa ta auna da gudu yan matan dake kusa ma ko wacce ta ari kafar kare, Fadime dadi ya kume ta ta fadi a gurin tana ta kuka kamar gaske, duk abun da take ana bata hakuri da masu tofa mata addu'a kudinta na mallake a hannunta, sai dariya take cikin Hijabin daya rufe mata fuska. Da taimakon samarin gurin aka rikata aka kaita gidansu. Inna na ganinta kamar a sume hankalinta ya tashi Amo ma bakin kofa ta fito ta tsaya tana kallon ikon Allah. Fadime kamar ficewar mutanen da suka kawota take jira ta fara wani sabon kuka wanda yai daidai da shigowar Bappa, sai ta fara karkace kai.
鈥淒ole ne a barta taje birni gobe, dole ne sai an nemo wannan saurayin, dole ne ace ya dawo ayi auren kun gane....?鈥�
鈥淓h to to鈥�
Inna ta amsa da sauri jikinta na rawa, jin Bapppa be ce komai ba yasa ta fara tunanin ko dai ya gano ta.
鈥淢un san cewa ka fadawa Baban abule cewar ya kara aure ko ba haka ba Bapppa?鈥�
Bapppa ya gyada kai dan ya san daga shi sai abokin nasa su kai wannan maganar, kuma abokinsa ba sa'an Fadime ba ne balle yace shi ya fada mata, yanzu kan ya fara yarda aljanun ne sai dai ba zai yarda su cutar masa da ya ba.
鈥淜warai kuwa an yi haka, wai me kuke nema a jikinta ne?鈥�
Fadime ta yi shiru tana tunanin abun da zata fada, can ta tuno da som bada magani da take da kuma maganar wutar da Wasim ya fada mata ko ma karya ne yai mata shi yake saka mata wutar yau zata mata rana.
鈥淢agani zamu fada, saboda akwai mayu a ko'ina masu bin mutane da wuta, kuma akwai mugayen bil'adama鈥�
Fadime na rufe baki, Amo tai fuu ta shige bukkarta tana jin mararta na cika da fitsari, ga wani uban rawa da jikinta yake kamar mazari. Bappa ya girgiza kai.
鈥淎 a ni 拼ata ba zata yi bokanci ba, haramun ne sam ba zan bari ba, ko dai ku fita daga jikinta ko nasa bulala yanzu na zaneku kuma na muku karatu na kone ku鈥�
Fadime na jin zancen bulala ta kwanta a gurin.
鈥淢un tafi sai anjimanku bye bye bye鈥�
Ko minti biyu bata yi ba ta mike tsaye wai aljanun sun tafi. Inna dai sai kallon tsoro take mata. A daren Amo kasa fita rawa tai duk kuwa da irin yadda jikinta take tsuma na son fita rawar da take, gashi gobe Bapppa zai juyo da girkinta ba damar fita tun da kwana biyu biyu suke. Haka nan dai ta daure ta fito tsakar gidan, sai ta zagaya can bandakin dan wuta har ta fara fita jikinta, tana shiga ta fara 蓷aye fatar jikinta ta cireta tsaf sannan ta aje a gefen wani dutse da ba za a gani ba ta fara karanta wasu abubuwa tana rawa da halshe tana birke ido, sai ta fara kankancewa tana yin kasa ta dora hannayenta a kasa irin yadda dabbobi suke yi, a take jikinta ya fara gashi hallitarta ta canja daga mutum zuwa bakar mage, tsale daya tai ta tsallake zanar da aka zagaye bandakin da ita sai gata a filin dake harabar wajen zanar, a nan ma cigaba da karanta abun da take karantawa gashin ya fara barin jikinta ta dawo a mutum sai ta mike tsaye ta fara rawa wuta na fita a jikinta idonta ta sauya kala kamar ba nata ba, halshenta sai rawa yake kamar zai zazzago kasa, sai dai kafafuwanta suna nan a na mage tana ta rawa da su tana barin sawu, can kuma ta sake zama magen ta tuma ta dafa kan bukkar Fadime tana wani iri kuka na tayardar hankali, Fadime na fara ihu ta sauka ta nufi makotansu. Sai dai bata yardar ta bar sawu a na makonta ba saboda ta san, idan maye yai rawa da dare, da safe idan aka duba inda yai rawar zaka tararda sawun irin dabbar daya zama yai rawa, idan doki ne ko zaki ko mage ko kare ko akuya ko kura ko saniya duk za a gani matukar sun yi rawar a kasa.
(Allah ka mana tsari da mayu da duk wani abu mai cutarwa, suna cikin al'umma ba iya gane su sai Addu'a)
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence via 08036126660 or 08061371579*
03/12/2021, 09:22 - 馃馃馃馃: *Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence to 08036126660*
Tun a jiya da Ammy ta fada mata cewar zata rika zuwa aiki 7am sai ta aje daukan ruwa, tana tashi da safe ta share ko'ina ta yi wanke wanke sannan ta shiga tai wanka, ta shirya ta saka Hijabinta ta fito garin ma be gana wayewa ba, ta fito ta saka talkaminta ta isa kofar Tumba wacce ke dunkule tana bachi.
鈥淯mma Umma鈥�
Sai da ta jera mata kira ya kai goma sannan ta amsa.
鈥淵a akai?鈥�
Tumba ta amsa da karfi.
鈥淶an tafi aiki鈥�
鈥淭o ki tafi mana ina bachi zaki wani tashe haba mana鈥�
Falmata ta juya ta kama hanya, sai da tai addu'ar fita daga gida sanna ta fita tana tafe tana kallon unguwar ta so da mutane ba su gama fitowa ba. Idan Tsohuwa mai koko ta biya, ta shiga gidan da sallama, tsohuwa dake zaune tana kunna wuta ta amsa mata.
鈥淔almata ce鈥�
Sam bata ji abun da tsohuwar tace ba sai kawai ta dora mata da gaisuwa da kuma bukatar abun da ya kawo ta.
鈥淎n tashi lafiya, Tsohuwa dan Allah kina da goro ki sammanin?鈥�
Tsohuwa ta gyada kai tana murmushi.
鈥淓h ina da goro kuwa yau goro za a ci鈥�
A nan kam ta ji abunda tsohuwa tace domin tsohuwa ta fada da karfi tana unkurin tashi.
鈥淓h dan kunne zan like鈥�
Daki tsohuwa ta shiga ta dauko goro daya ta raba rabi ta mikawa Falmata.
鈥淕ashi yar albarka鈥�
Falmata ta saka hannu biyu ta karba.
鈥淣a gode Allah ya saka da alheri鈥�
Ta juya cike da jindadi ta fice daga gidan, a yau ba ta titi ta bi ba saboda tana son diban furen tunfafiya da yake a tsakankanin gidanjen da ba a gama ba na unguwar. Ta cikin unguwa take tafiya har isa gaban wani katon gida da aka fara gine ba a karasa ba, gefen gidan ciyawa ce sai tunfafiyar da ta fito da yawa wata babba wata karama, sai dai ba ko wacce ce ke da fure ba, haka ta rika bi tana dubasu har ta samu wacce ke da fure ta tsinka ta jimke tare da goron sannan ta kama hanya.
Sai kusan 7:40am ta isa, kamar kowa kowa hada hadarsa kawai yake ita kuma tana tafe tana rabon ido ko zatai yi arba da Iya, so take ta kara tabbatarwa idan har da gaske mayya ce, jiya dai kam bata ganta ba har ta bar gidan. Cikin sa'a kuwa Falmata ta hangota tana magana da suwa hadimai da alama nuna musu take inda za su gyara. Da sauri Falmata ta balla goron ta saka furen tufafiyar a baki tana taunawa, sai mulgunar baki take kamar wata tsohuwa, tana isowa gurin Gate din ta mikawa Iya gaisuwa sai kallonta take.
鈥淏arka da safiya鈥�
Suna hada ido Iya tai saurin kawardar kanta tana yamutsa fuska kamar wacce tai arba da kashi, ta daga mata hannu alamar ta wuce ta wuce kawai.
鈥淎lmu dauko min karen can鈥�
Ta nuna karen iccen mangoro daya fado tana ta kokarin juyawa dan kar ta sake ganin Falmata, da sauri Falmata ta nufi karen ta dauko ta miko mata da yatsu biyu dan kara tantancewa, domin a iya saninta ba a nuna maye da yatsu biyu yatsan manuni da mai binsa ba a mika musu abu da shi ko a nune su da maye da mai sirihi donin manuni yana karya lagon mutun, Mama ta taba fada mata haka tun bata girma sosai ba. Falmata na mika mata karen Iya taja baya ta bude baki tana kallon yatsun Falmata.
鈥淵a haka haka? Miye haka kuma? Miyasa zaki yi haka? Amman dai baki kyauta ba, ke wai wace irin yarinya ce鈥�
Maganar kawai take kamar wacce ta rude sai kallon karen da Falmata mika mata take ta kasa hada ido da Falmata dake ta aikin taunar goron tana kallon cikin idon Iya da mugun mamaki. Jefar da karen tai ta nufi cikin gidan tana waige Iya, a yanzu kam ta tabbatar Iya mayyace dan ga zahiri ta gani, abubuwan nan biyu da tai bayan na shekaranjiya da ta fara mata addu'a ta kawar da kai.
鈥楰e nan ita din mayyace, amman su ba su sani ba鈥�
Ta fada a ranta, tana cigaba da tafiyar tsoro na kara shigarta domin bata taba arba da maye ido da ido kamar yanzu ba. Har da isa bakin kofar tai knocking aka bude mata bata daina tunani ba. Har kasa ta kai ta gashe da Jekadiya sannan ta mike tsaye ta nufi dakin yan uku, samunsu tai a kwance suna bachi, kamar yadda aka fada mata ba a shara idan suna cikin daki dan haka ta dauki Labib a hankali ta fito da shi daga dakin ta nufi dayan dakin da aka nuna mata jiya, tana shiga ta samu babban gado da kayan wasan yara kala kala a dakin kamar wani karamin kamfani, ga fentin dakin pink, washe baki tai tana kallon yadda aka tsara dakin kamar ba a mutuwa, wai kuma nan dakin yara ne, ko da yake ko a tsarin gidan ta duba ai ta san sun isa.
Sai da ta gama bawa idonta abinci sannan ta aje Labib akan gadon dake shimfide da zanen gado dan ubansu mai taushi da laushi ga shi sai sheki yake kamar an zuba masa kyalkyali. Juyawa tai ta fita ta dauko Luma ita ta dawo da ita dakin ta kwantar kamshin dakin sai dukan hancinta yake.
Komawa tai dayan dakin ta gyara shi tsab sannan ta dawo inda suke ta tararda da sun farka har sun fara kuka, da sauri ta dauki Labib ta rarrashinsa sannan ta fita dashi daga dakin ta koma dayan dakin ta dorashi akan gadonshi ta bude wardrobe ta dauko madararsa ta dama masa da ruwan zafin dake cikin flask aka dora a dorowar, ta zuba a cikin fidarsu ta fara bashi. Sai da ta tabbatar ya koshi sannan ta dauko Luma ita ta shayar da ita, bandakinsu ta shiga ta hada musu ruwan zafi sannan ta fito ta fara cire musu tufafinsu ta saka su a cikin ruwan dumin data hada ta wanke musu kashi, ta nade su cikin wani farin tawul. Cikin kuzari Labib ta hau wasa Luma kuma tana da kuka sama sama. Kanta Falmata ta dafa ta karanta masu addu'ar tsari wacce Annabi S. A. W yake karantawa jikokinsa, sannan ta dora mata da ayatul kursiyu, sai da ta gama da Luma sannan tai wa Labib, ganin taki daina kuka yasa ta goyata da tawul tana jijjigata, tana yi ma Labib wasa daga tsayen da take.
Wata hidimar ce ta shigo dauke da babba tray ta aje wa Falmata a gabanta.
鈥淎nce ki aje yaran ki fita waje ki karya鈥�
Falmata ta sauke Luma dake bayanta ta mikawa matar sannan ta duka ta dauki tray ta fita waje, kamin ta isa har wani hadiyar yawu take, biredi ne yaka biyar sai kwai ga dankali da plantain da tea mai kauri ga kuma ferfesun kayan ciki a gefe har wani tiriri suke, Falmata fitowa tai daga bangaren gaba daya dan kar ma ta zauna a inda za a ga lomarta ta zagoyo ta gaban ita cen lemu dake kusa da babban garden ta zauna, kayan cikin ta fara kaiwa aiki tana yi tana ashe hannu kamar sabuwar mayya.
AA POV.
Daga bakin kofar dakinsa Anti Rabi ta aje masa dumamem tuwon shimkafa da miyar taushe da tai jiya, sai ya wani yatsine fuska.
鈥淜ai ni ba zan ci dumame ba daga yanzu na daina cin dumamae鈥�
Anti Rabi ta kalleshi da mamaki.
鈥淭o yau kuma?鈥�
鈥淓h daga yau gurin aiki zan rika karyawa, na san abincin kala kala zaka yi asuwaki kaji ka kuskure baki da lemu, Malam harka irin da mutunci鈥�
鈥淓h nan kuma ta rashin mutuncin ce ba, ka ma samu sa'a mun tashi da dumemen da koko zaka gani, gurin aikin da basa iya baka komai sai ka siye鈥�
Anti Rabi ta fada tana harar shi.
鈥淎mman dai tsakani da Allah kina ganin zubina kin san ni ba jini talaka ba ne, kawao dai Allah ya kawo ni cikinku ne, ni yanzu na fara jin kamshi arziki kusa kusa, kin san ance arziki kashi ko? To na fara takawa鈥�
鈥淲ato dai baka rabo da yarinyar nan ba AA? Sai ka jawa kanka wata matsalar?鈥�
鈥淎a fa ni ko sunanta ma na manta, ina nan dai ina addu'a kin san mai neman a gurin Allah baya fidda rai鈥�
鈥淎llah dai ya kyauta kuma tsare dan ni wannan neman kudi naka har tsoro yake ba ni鈥�
Yar dariya yai ya shafa kansa.
鈥淲ato ba zaki gane ba ne Anti saboda kina cikin geto area, da ace kina zaune a birni ko? Ga babbar mota ga kato gida ba irin wannan ba, ga kajin safe sa da rana namam rago da dare soyayyar hanta, Wallahi wannan baki baki nan jikinki ma duk bacewa zai yi, ai kudi sun yi a rayuwa, Ni wallahi har jin nake kamar masu kudin garin nan duk yan'uwana ne yanzu鈥�
Ganin yadda take kallonsa da kamar tsoro da kamar mamaki yasa shi daukar talkaminsa yasa yana fadin.
鈥淭o wai waye baya son kudin nan ne dan Allah? Kudi fa Anti bama neman haram amman halal kam sai inda karfi ya kare鈥�
Ya nufi kofa yana laleben aljihunsa dan tabbatarwa idan makullin motar da aka bashi yana nan ciki.
鈥淣a tafi ni鈥�
Sai ya waigo ya kalleta jin bata masa addu'a sai yai ma kansa.
鈥淎llah ya tsare ya kai ni lafiya ya dawo da ni lafiya, Anti ayi ta addu'a kudi fa suna tafe mun fara taka matakin nasara鈥�
Ita dai bata ce komai ba har ya fice, tsoro take kar ya saka kansa a wata mummunar hanyar, wannan son kudin nasa yayi yawa. Mai achaba ya tara ya hau ya fada masa inda zai kai shi, kamin su isa gidan ya sauka ya biyashi sannan ya doshi gurin masu gadin gate din ya gaisa da su, tana kallon cctv camera dake leke a gurin, a nan ma sai da suka tare shi suna tambayar inda zai je.
鈥淣i ne sabon direban Hajiya Nana kun gane ko?鈥�
Ya fada yana jin wata isa sai kace wani sarki ko wani mai babban mukami. Ba su yarda ba har sai da aka ce ya kirata yai magana da ita, sai ya kira number Hajiya bata dade tana ringing ba aka daga.
鈥淗ello Hajiya Nana鈥�
鈥淲ake magana?鈥�
Jin babbar murya yasa shi duba wayar ya gani idan number ce ya kira, sai ya sake maida wayar a kunne sa.
鈥淎A ne sabon direban Nana, da wannan wayar muke magana da ita shiyasa na kira na fada mata gani na zo zan kaita makaranta masu gadin sun tare ni sun hanani shiga鈥�
鈥淏a su wayar鈥�
Hajiya ta fada daga dayan bangaren, sai AA ya mika musu suka karba su kai magana da ita sannan suka bar shi ya wuce, kai tsaye ya nufi gurin da motar take, tun kan ya karasa ya matsa key din, sannan ya bude ya shiga yai warming dinta yai reverse ya fito daga daga parking space din ya zo bakin kofar fadar Ammy ya faka. A iya tunaninsa kamin Nana ta fito za a fara bashi abun karyawa ne, hakan yasa ya fito ya tare wani bawa dake aikin mopping din gurin yace.
鈥淒an Allah Malam dan shiga ka ce musu sabon direban Hajiya Nana ya iso yana waje鈥�
鈥淏a ni da hurumin shiga ciki Malam, sai dai kai ma wadancan hadiman magana鈥�
Kai tsaye AA ya nufi matan ya fadawa daya ya dawo cikin motar ya zauna. Ba a dade ba sai ga ya hango Nana ta fito sanye da uniform yai saurin fitowa daga motar ya bude mata kofar, ita kuma sai kallonsa take tana murmushi wani irin dadi take ji zai fara tukata, sai da ta shiga ya maida motar ya rufe, ya shiga mazaunin direba ya ja motar suka fita.
鈥淗ajiya ina zamu je?鈥�
鈥淲ani guri mu huta sai lokacin dawowa daga makarantar yayi sannan mu dawo鈥�
Kallonta yai ta madubin gaba sai ya ga ta kara kyau kamar ba ita ba.
鈥淚na kenan? Hajiya鈥�
Ta kara kwantawa tana kallon titi.
鈥淲ani guri dai鈥�
鈥淭o amman biya zaki yi ko?鈥�
Ta kalli madubin ta watsa masa harara.
鈥淓h lallai mai wannan yaron, ban ce na saka an dauke ka aikin鈥�
鈥淎ikin da aka daukani daban, kin kaiki makaranta daban, har inda zan boye ki sai kin biya shine deal din鈥�
鈥淎iko zaka ja na koreka daga aiki鈥�
鈥淎i ba kika dauke ni ba, ita wannan Hajiyar ai ta sani shiyasa ta amince ni ina jin ma kamar yar'uwarmu ce, kuma duk kika fada sai na fadi cewar ba ki zuwa makaranta guduwa kike鈥�
鈥淣i kuma na ce ke kai kake kai ni wani guri ka boye, shiyasa ka ce na dauke ka aiki鈥�
鈥淣a ce karya kike鈥�
鈥淎i ba a karyata dan Sarauta kana cewa karya nake za a maka bulala ko a saka ka aikin wahala ko a rufe a gidan yari鈥�
Ya dan yi shiru yana tunani sai kuma ya marairaice murya
鈥淣ana yanzu haka zamu yi dake, ni da na dauke ki kamar Mamana ina tunanin komai ke zaki min ko tufafi zaki iya siyamin amman sai fara saka min da wannan, yanzu fa ma yunwa nake ji鈥�
鈥淜arka sake ce min Nana Hajiya鈥�
鈥淚ndai kina son na rika ce miki Hajiya sai dai ki biya鈥�
Da sauri Nana ta kalleshi ta cikin madubi.
鈥淓h lallai kai baka ma da wayo, ai wanda ya dauke ka aiki ka zama yaronsa鈥�
鈥淓h amman ai idan mutum yana aiki a gidan masu kudi gata ake masa, balle ke Nana da kike yar gata ina jin kamar ke dai aka haifa ko?鈥�
鈥淏an sani ba, kai ka cika gulma da tambaya鈥�
Murmushi yai be sake ce mata komai ba.
鈥淣i bani da kudi yanzu kuma karka kai ni school ma fada maka鈥�
Ta fada ganin ya dauki hanyar makaranta har suna kusan isa.
鈥淢iyasa baki son makaranta Hajiyata?鈥�
鈥淗aka nan dai bana so?鈥�
鈥淲ani abu ake miki a makarantar ne?鈥�
鈥淏a abunda ake min bana son zuwa dai sai na rika jin kamar zan yi kuka bana son school ni鈥�
Juyowa yai ya kalleta ta wani hade rai ta turo baki kamar zatai kuka.
FADIME POV
Tun cikin dare ta labartawa Inna wanda ya zo yai mata juyen gida.
鈥淚nna na fara farinjini ko?鈥�
Inna dai bata ce mata komai ba sai kallonta take da fitilar kwan dake haskata.
鈥淜ina jin wani ciwo?鈥�
鈥淎a鈥�
鈥淭o ki yi addu'a kije ki kwanta鈥�
鈥淭o Inna ki min addu'a ni wuya take bani har na manta da wasu addu'oin ma鈥�
鈥淭o yayi kyau鈥�
Ta mike tsaye ta dauki kyandir daya ta kunna ta nufi bukkarsu, tana shiga ta dauko littafinta ta fara rubuta abubuwan da suka faru sannan ta aje ta kwanta ba tare da tayi addu'ar ba. Can cikin dare ta fara jin ana wasa da bukkar ta fara ihunta kamar yadda ta saba tana kiran Bapppa sai da ya taso ya shigar da ita bukkarsu sannan aka samu zaman lafiya.
Washe gari sai ta farka cikin jindadi abubuwa biyu, Amo zata je da ita birni a yau kuma jiya an mata juye ta fara farin jini kenan, ko karyawa ba tai ba taje gidansu kawarta Ma'u ta labarta mata abunda ya faru jiya da dare sai wani shauki take yana jindadi. Sai da hantsi ya fito sosai ta dawo gida ta sha kokon da Inna da dama, ta dauki tulu zata je deban ruwa.
鈥淔ulani ki kula kin san kullum kika je sai wani abu ya faru ko?鈥�
鈥淎a zan yi addu'a babu abun da zai faru鈥�
鈥淭o Allah ya tsare鈥�
鈥淎min鈥�
Ta kallame tulun ta bi hanyar, kana ganinta kasan tana cikin nishadi domin farincikinta ya kasa boyuwa sai far'a take. A maimakon ta isa gurin ruwa kai tsaye inda wasu yan mata biyu suke deba sai ta nufi gurin duwatsun kamar ta san Wasim na tsaye a gurin yana jiranta, tana hangoshi ta karaso kusa da shi da sauri tana murmushi.
鈥淜ai dai jiya... An tashi lafiya dai鈥�
Har ta fara bashi labari sai kuma ta tuna cewar bata gaisheshi ba, wani zancen bata kaunarsa na abun da yai mata duk ya kau saboda farincikin an mata juye.
鈥淟afiya kalau鈥�
Ya amsa yana kallon cikin idonta kamar zai cinyeta.
鈥淛iya wani yai min juye鈥�
Yayi murmushi har lokacin kallonta yake wani irin mayen kallo da yake saka shi nishadi da annashuwa, tana matukar burgeshi gashi yadda take abubuwanta tana saka shi nishadi.
鈥淜in jindadi?鈥�
鈥淓h sosai mana, sosai ma ai na fara farin jini a haka kenan ko?鈥�
Ya gyada mata kai yana murmushi.
鈥淜ila son ki yake鈥�
Ta yi dariya.
鈥淎mman ai ina da miji dan birni鈥�
鈥淚dan shi ma dan birni ne fa鈥�
鈥淎a dan kauye ne鈥�
鈥淭o idan wacan ba mijinki ba ne fa?鈥�
鈥淎i zan taba hannunsa na ji ko da sanyi, taba ni na ji鈥�
Ta karasa tana mika masa tafin hannunta dake bude, kallon hannun yai ya sake kallonta.
鈥淚dan na taba ba kiji sanyi ba fa?鈥�
鈥淪hikenan鈥�
鈥淎a ba shikenan ba, ba zan hakura ba鈥�
鈥淜amar ya?鈥�
Ta tambaya da dariya dan bata gane nufinsa ba. Sai ya lakaci hancinta yana murmushinsa mai kyau.
鈥淜amar haka鈥�
Ta taba hancin tana dariya, dariyarta ce tasa ya kara fadada murmushinsa yana kallonta cike da burgewa.
鈥淛e ki debi ruwanki, zan je garin mu sai anjima鈥�
鈥淭o Bye Bye good bye鈥�
Ta daga masa hannu sannan ta juya da tulun ta nufi gurin ruwan ta fara deba. Ba laifi ta dibi ruwan da dan yawa ba ta kai gida, tana shiga Amo na shigowa gidan rike da kwayar da ta aro makota.
鈥淔ulani ina kika fito?鈥�
鈥淩uwa na debo鈥�
鈥淭o tahi ki sirya yanzu zamu tafi鈥�
Ta fada cikin rashin jindadin rashin sani zata tafi deban ruwa da sai tabi bayanta ta ga abunda take a dajin, amman ai akwai gaba bayan deban ruwa tana zuwa kiwo ai, ya ma fi dadi shi da take zuwa da yamma.
Ko da goma tai Fadime ta shirya cikin atamfarta ta karamar sallah ta saka yello Hijab ta fito da sauri domin Amo na waje tana jiranta. Inna dake aikin kirbin dawo (fura) a tsakar gidan ta kalli Amo cikin rashin jindadi tace
鈥淎mman Malam be ce aje da ita ba Amo鈥�
鈥淗aba dai Inna Fadime yanzu tafiyar zuwa birni sai an fada masa? Ai cikin hikima zaki ce masa rakiyata tai ba sai an fada masa abun da zai kai mu ba鈥�
鈥淭o Allah ya dai ya tsare, Fulani ki yi addu'a鈥�
Amo ta kalli Inna da sauri ta rufe ta da fada.
鈥淜amar ya tai addu'a sai kace wanda zai je gurin mugun abu, idan baki yarda da zuwanta ba tai zamanta a gida, daga ina nema mata abokin rayuwa sai abu ya zama matsala鈥�
鈥淎mo addu'a ai tana da kyau ga musulmi ba dan fatan wani abu ya faru ba鈥�
鈥淜e wuce muje鈥�
Fadime ta fice da sauri Amo ta bi bayanta, Inna ta bisu da kallo tana addu'ar Allah ya tsare mata yarta, bata son zuwan a ganinta be dece ma ace an tafi da ita ba wai dan wanda ke sonta ya ganta abun be ma bada kala ba kuma ba al'adarsu ba ce.
Tafiyar awa daya da mintuna arba'in a mota suka iso ciki gari, Amo bata fita daga motar ba sai da ta laso kurwar macen dake kusa da ita ta nade a zane sannan suka fito ita da Fadime suka kama hanyar gari. Sai da ta fara biyawa ta guraren da take sayarda danyen manshanunta sannan suka shiga cikin tsakiyar garin, Fadime har ta fara gajiya dan bata saba da tafiya mai nisa ba, ko a kauyensu idan Inna ta aike ta nesa bata zuwa dan bata saba dogon yawa ba, gashi rana sai dukansu take yar hodar da ta shafa ma duk ta goge.
鈥淣i dai na fara gajiya鈥�
鈥淎i mun kusa isa, bari na shiga gida nan鈥�
Fadime ba dan ranta ya so ba ta bi bayanta suka nufi wani madaidaicin gida Amo ta kwankwasa, yaron gidan ya fara bude gidan ya leko.
鈥淲aye?鈥�
鈥淔adawa Innanka tana siyen manshanu鈥�
Yana juyawa Amo ta laso kurwar yaron, a maimakon ta saka ta a zanenta ta kulle ko a jakar kudinta ko ta jimketa a hannu sai ta duka ta saka ta a karkashin kafarta gashi talkamin ya dauki zafi, aiko yaro kan ya karasa ya fadi tsakar gidan ya fara birgima yana rike kai. Mahaifiyarsa ta fito da sauri tana tambayar ba'asi, kamin ya leko waje ta ga Amo tsaye tana lasar baki.
鈥淗ajiya kina siyen mansanu?鈥�
Aljanun da suke kan matar sun fi karfin na Amo, a take jikinta ya bata cewar Amo manya ce, kamin tai wani unkuri aljannun suka fara takawa kanta suna kokarin riko Amo.
鈥淪ake masa kurwarsa鈥�
Kamin Amo ta kuce daga rikon matar Fadime har ta cire talkaminta tana shirin gudu, Amo ta juyo da sauri da zimmar gudu mata ta biyota kanta babu ko dankwali tana fadin.
鈥淪ake masa kurwarsa鈥�
Mazan dake unguwar suka taso da sauri suka nufo inda Amo take wasu na fadin matar musa police ce miya faru, ita kuma bata fasa fadin abunda take fada ba, sai kuma ta fadi ta birkice tana ihu aljanun suka taso da gasken gaske, a take wani makocinsu ya daga waya ya kira mijinta ya fada masa abunda ke faruwa.
鈥淒aga na kwankwasa kofar gidan yaro ya leko nace ya fada mata tana siyen mansanu sai kawai ta leko wai na sake masa kurwarsa鈥�
Amo na gama magana wani saurayi ya dauke ta da mari.
鈥淚rin ku ne masu shigowa cikin gari kuma maita ko?鈥�
Ba kadan taji zafin marin ba, amman karfi hali irin na maita ba zai barta ta nuna ba, kuma ba tai niyar sakin kurwarba. Fadime dake tsaye gefe ta shafa fuskarta tana jin kamar ita aka mara, ga mutane maza da mata sai fadi suke matar Musa Police ce, gudun kar ace tare suke yasa Fadime ta fadi a gurin ta fara karyar aljanu tana birkice ido.
鈥淭a kamani ta kamani Wayyo kurwata鈥�
Wasu maza suka nufita ta sauri suka dauko ta suka aje karkashin wani ice sannan aka dauko yaron daya ki dawowa hayyacinsa suka aje kusa da Fadime, suka dauko itace dayan ya bugawa Amo a kafa.
鈥淭sallaka su sai kin tsallaka su, ko mu kashe ki Wallahi鈥�
Amo mamakin abun da Fadime tai mata ya fi na abun da mutanen suka mata, a dolen dole suka cilastata ta cire tufafin jikinta ta koma daga ita sai vest da under skirt, ta ware kafafuwanta ta tsalaka yaron ba tare da ta taba shi ba, domin idan taba shi kurwar ba zata dawo ba, amman idan bata taba shi ba kurwar duk inda take a jikinta zata fado kasa ta shige jikin mai ita.
Tsallaka uku tai ma yaro sai ya mike tsaye kamar a firgice yana neman mahaifiyarsa, sannan aka cilastata ta tsallaka Fadime, ita ma uku tai mata sannan Fadime ta mike tsaye ta fara neman talkaminta da ta saki.
鈥淚na talkami gida zanje?鈥�
鈥淶aki iya tafiya?鈥�
鈥淓h鈥�
鈥淚na ta hadu dake? 鈥�
鈥淜an hanya tace na zo na nemo mata canji鈥�
A nan mutane suka saka salati ana ta nanata maganar, daman masu manyan wayoyi tuni suka fara dauka, mazan nan duka hau dukan Amo kamar an aikosu amman ko alamar hawaye babu a idonta balle tai kuka idonta ne dai suka kara rinewa da ja, sai kallon mutumen da ya mareta da farko take tana jin zafin marin har yanzu.
Fadime na daukar talkaminta ta mike hanya, ba dan tasan inda zata ba ita dai burinta ya cika tun da ba agano tare suke ba, har da hadawa da gudu sai wagen bayanta take har ta kawo titi tana kokari karya kwana wata farar mota mai bakin gilashi ta dan bugeta kadan, abun ka da mai neman kuka an fada masa mutuwa sai kawai ta fadi a gurin tana ihun kafarta.
SHATTIMA POV.
Yana kallon wayar tana ringing kamar ba zai daga ba, har sai da ta kusa yankewa sannan ya danna picking ya saka a speaker.
鈥淗ello Shattima ina airport鈥�
Jimmm yai kamar be ji abun da Zainab take fada ba sannan ya mike tsaye rike da kofin lemun tsakin.
鈥淕ani nan zuwa鈥�
Ya nufi kitchen ya aje kofin, sannan ya dawo dakin ya dauki wayar ya kira Ra'ees, bugu daya ya dauka domin ya san Shattima be son jira.
鈥淭akardun suna hannunka ne?鈥�
鈥淵eah gani tare da su鈥�
鈥淶an biyo yanzu na karba鈥�
Ya saka wayar aljihu ba tare da ya kashe ba, sannan ya dauki keys dinsa ya fice. Yana saukowa kasa ya shiga farar motarsa dake fake a gurin ya danna horn kamin ya isa gate har mai gadin ya bude masa gate. Kai tsaye ya nufi unguwarsu Hajiya Asiya yayar Ra'ess dan karbar takardun a hannun kanenta kuma amininsa. Kadan kadan yake tukin amman hakan bd hana shi bugun wata matashiyar yariyar ba, wacce ke sanye da atamfa da yellon Hijab, gilashin motarsa ya sauke yana jin ihunta tana fadin kafarta, kamin yai wani unkuri har ta mike tsaye ta nufo inda yake cikin masifa
鈥淜ai baka ga ka kade mutum ba?鈥�
Ido ya sakar mata yana ta kallonta da mamaki, ya kasa cewa komai yarinyar da za a kade imlndai har da gaske ta ji ciwo ai ba zata iya tasowa tace masa ya kadeta ba.
鈥淲ayyo kafata鈥�
Ta fada da kuka shi kam kallonta kawai yake kamar dan kallonta kawai akai shi.
鈥淜o kurma ne kai baka magana鈥�
鈥淚na yi鈥�
Ya amsa ta yana lumshe ido ya bude, sai da ya amsata sai ta ji kamar ba shi ba, because be cika magana any how ba duk kuwa da kasancewar kadeta yai. Samun kansa yai da bude motar ya fito ya duka yana kallon kafarta.
鈥淐iwo sosai鈥�
Ta fada kamar zata yi kuka, kansa ya daga ya kalleta.
鈥淢uje na kai ki asibiti?鈥�
鈥淜o ba kai ni asibiti ba ka siya min kaza da yoghurt kawai sai ka bani kudin mota ko ka kai ni garin mu dan Allah鈥�
Ta fada tana hade hannayenta alamar rokonsa take, sai ya mike tsaye yana gyada mata kai, ya kai hannunsa ya bude mata gidan baya sai ta shiga da sauri.
鈥淣a gode鈥�
Ya rufe sannan ya shiga yaja motar zuwa gate din su Hajiya Asiya, sannan ya ciro wayarsa ya tura masa Ra'ees sako cewar yana waje.
鈥淢u nan da muka zo ban san kowa ba, gurin wani muka zo鈥�
Fadime ta fada masa ba tare da ya tambaye ta, kallonta yai ta madubin gaba be ce komai ba, kuma daman ba zai ce din ba tun da surutu be sha masa kai ba. Fadime na hakimce cikin motar ta hango Ra'ees ya fito a gate din dake gabansu. Ba shiri ta gwalo ido waje.
鈥淟aaaaa Wallahi shine shi ne wanda muka zo nema鈥�
Ta fada cikin wani irin jindadi tana dan kare fuskarta. Nan ma dai Shattima kallonta kawai yai. Ra'ees na isowa ya bude motar ya shiga ya zauna ya ja ganbun ya rufe yana mikawa Shattima takardu yana masa bayani, sai Fadime tai dan tari kadan shi kuma ya juya ya suna hada ido ta sakar masa murmushi, a take yaji mararsa ta cika da fitsari.
鈥淚nnalillahi wa'inna ilaihirraji'un dan Allah ki yi hakuri na jawa kaina bala'i鈥�
Gaba daya kallon aljana yake mata, ganinta a motar Shattima, bayan yasan Shattima be taba saninta ba, a iya tunaninsa shi kadai yake ganinta ma. Hakuri da ya bawa Fadime sai ta ga kamar yana nufin tai hakuri ba zai aureta ba, sai kawai ta fashe da kuka, nan shi ma ya saka kuka.
鈥淲ayyo Allah dan Allah ki yi hakuri ki yi shiru鈥�
Wani irin rawa jikinsa yake yana jin cewar ya saka aljana kuka. Ita ma kukan take shi kuka ita kuka. Shattima kasa hade dariyarsa yai har sai da ya dora kansa kan sitarin motar tsakar dariyar da ta cika masa ciki.
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence to 08036126660*
03/12/2021, 09:22 - 馃馃馃馃: *Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence to 08036126660*
Shattima kasa hade dariyarsa yai har sai da ya bude motar ya fita ya jingina da motar ya rike cikinsa. Fitar Shattima ce tasa Ra'ees ya hankalto da ya bude motar ya fita shi ma, kamar kyaftawar ido haka ya fice daga motar ya rufe, sai kuma yai tsaye ya kasa tafiya, gaba daya gani yake kamar mafarki yake, taya yarinyar dake kauye zata shiga a motar Shattima? Bayan kuma Shattima be santa ba?
Dariyar da Shattima yake ne yasa shi dawowa hayyacinsa har ya kalli Shattima da shi kansa zai iya rantsuwa be taba ganin dariyarsa kamar haka ba. Shi kan sam be ga abun dariya ba dan ya san me ya ji a lokacin da yake je kauye kuma ya san abun da ya gani a yanzu, a tunaninsa Shattima yana masa dariya ne saboda ya fashe da kuka ba tare da dalili ba, dan a iya tunaninsa shi kadai yai arba da Fadime a gidan baya.
鈥淢an this is not funny, ni na san me na gani Wallahi, kuma na san me na ji鈥�
Ya fada muryarsa na rawa, can dai ya ji kamar be gansu ba ya fara karanto ayatul kursiyu ya shafa ma kansa zuciyarsa sai bugawa take da karfi kamar zata fasa kirjinsa ta fito.
鈥楤a dan dai aljanu suna da cuta ba, ai ba wani abun nai mata ba, neman aure kawai naje kuma bama nawa ba, rabon ayi, shine kuma zata rika bina ina ganinta why? Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un鈥�
Cikin ransa yake ta wannan sake saken yana jin kamar ya zuba da gudu ya shige gida ya bar Shattima a gurin.
鈥淩a'ees ban tab daukar tsoron ka ya kai haka ba鈥�
Shattima ya fada har lokacin dariya yake, ban ya wacce yai har ta soma saka masa tari.
鈥淏a zaka gane ba ne Wallahi.... Ka ga me na gani wai?鈥�
Ya fada yana zare ido kamar zasu fito tsabar tsoro.
鈥淏a yarinya ba ce?鈥�
鈥淜a ganta kai ma?鈥�
Ra'ees ya tambaya yana wani zuro kai, dan ya tabbatar idan da gaske Shattima ne ko kuma aljanun ne suka sake masa siffar Shattima, daman can Ra'ees matsoraci ne sai dai yanzu abun ya fi kamashi, domin be taba jin mutum da muryar saniya ba sai da yaje garinsu Fadime. Shattima sai da yai da gaske sannan ya iya gintse dariyarsa.
鈥淓asy Ra'ess wannan yarinyar nemanka ta zo鈥�
Ra'ees ya ji kamar ba shi ne ba, wani sanyi ya taso tun daga kan dan yatsan kafarsa har cikin kansa, ya share fuskarsa yana ta faman haki kamar wanda yai gudu ya gaji.
鈥淣i abun da nake son na gane, kai ma ka ganta ne ko ni kadai na ganta? Me zai kawota a motarka? Shattima wai kai ne dai?鈥�
Shattima ya daga kansa sama yana kallon hadarin dake haduwa a garin yana murmushi wani iska mai dadi na shiga ta hancinsa.
鈥淵anzu nan na hadu da ita, kadeta nai my mistake鈥�
Ya fada bayan ya sauke kansa. Be da bukatar yai masa dogon bayani domin ya fahimci Ra'ees be shirya saurarensa a yanzu ba, kallo daya zaka masa ka karanci irin tsoro da tashin hankalin dake tare da shi. Sai kawai ya koma cikin motarsa ya rufe gambu, Ra'ees dan dukowa yai ya leka cikin motar a lokacin kan Fadime na cikin Hijabin tama kuka kamar wacce akai wa mutuwa. Da sauri ya dauke kai ya matsa jikin motar ya rufe masa motar. Reverse Shattima yai sannan ya hau titin unguwar har lokacin murmushi ne a fuskarsa zuciyarsa cike da nishadi. Sai da ya kama hanyar airport sannan ya kalli Fadime ta madubu har lokacin kuka take da gaske gasken domin ko kadam bata jidadin rasa Ra'ees da tai a rayuwarta ba.
鈥淢e kike yi ma kuka?鈥�
Ta dago jajayen idanuwanta ta kalleshi hawaye na mata zuba kamar ruwa.
鈥淏a kaji me yace ba, nai hakuri ya fasa fa kenan鈥�
Samun kansa yai da wani murmushin yana kallonta ta madubun gaba sai dai ita din bata sani ba idonta be ma kai kan madubi ba kuka kawai take, ta dayan bangaren tana blaming Wasim domin shi yaja mata komai tun farko. Kirciya da rauta kawai Shattima yake gani a fuskarta domin yana da irinta, kuma kana kallonta kasan yarinya ce tsawon kafafuwa ya soma janta.
鈥淶an bi ta airport na dauki kanwata sai na kai ki tasha, amman ki daina kukan鈥�
Ya fada yana jin kukan da take rerawa yana damunsa.
鈥淭o鈥�
Ta amsa daker tana hade kukan, Fadime bata taba ganin airport ba sai a lokacin, a nan da nan ta manta da kuka tana ta kallon mutane da kuma manya motoci da suke kai kawo a harabar. Sai da ya faka motarsa sannan ya ciro wayarsa ya aikawa Zainab da sako cewar yana waje yana jiranta.
鈥淚dan za a je wani kasa ake suwa Airport a shiga jirgi ko?鈥�
Ta tambaya tana jin sanyin ac na ratsata, shi dai be ce mata komai ba, sai kallonta yake ta gaban madubin, a nan ta tuna da Inna tace tai addu'a kuma ba tai ba ta fito, sai ta duke kanta kasa ta karanta abun da ta iya sannan shafa a hankali dan kar ya gani, zuciyarta na raya mata ko dai siyar da ita zai yi ya samu nama a arha a banza, duk abunda take Shattima na kallonta.
Cikin kankanen lokaci Zainab ta iso gurin motarsa daman tun a lokacin da ta kirashi tana airport din zaune, duk da irin ciwon kan da take ji bata isa ta sake kiransa ba tasan ransa zai iya baci yace ta matsa, ba isa kuma ta tari texi ta tafi ba dan ta san zai zo idan ya zo be same ta ba ransa zai bace. Ta buga bayan motar sai ya bude mata boot boot bayan ta saka jakarta ta rufw ta zagayaon ta bude front ta shiga ta zauna.
鈥淲elcome to KT鈥�
Shattima ya fada bayan ta kalleta kadan ya dauke kai.
鈥淭hank you Wallahi kaina ke ta ciwo da gefen bayana鈥�
鈥淢aybe zaman jirgi ne鈥�
鈥淭un kan na taso nake jin ciwo鈥�
Shattima be ce mata komai ba sai tukin motar yake. Fadime dai ya gidan bayan tana ta tunani ai ance idan masu fillar kai suka kama mutum baya iya magana right okay then bari tai magana ta ga idan zata iya.
鈥淏arka da yamma鈥�
Ya gaishe da Zainab sai Zainab ta juyo da sauri ta kalleta Fadime ta sakar mata murmushi yake, Zainab ta dan yamutsa fuska tana mata kallon wata yar kauye can kuma ta kali Shattima.
鈥淲ho is she?鈥�
Kafadunsa ya daga alamar be sani ba yana murmushi.
鈥淪he's so comedian鈥�
鈥淚'm not a comedian鈥�
Fadime ta amsa masa kai tsaye, daga shi har Zainab kallonta su kai, never thought tana jin turanci balle ma har ta iya maidawa.
鈥淐an you speak English?鈥�
Zainab ta tambaya, sai ta daga mata kai.
鈥淵es da kin je kauyenmu kika ce Fadime yar gidan Bapppa kowa ya san ni ce daya kawai, saboda ni na iya turanci idan aka kawo wasika a garin gurina ake zuwa na karanta, idan wani bako ya zo ni ake kira na masa turanci idan baya jin hausa, duk garin Bandalo babu yarinya mai jin turanci irina, Bappa ya sani makaranta tun ina karama kuma yana biya kullum idan zai je Kaita da ni yake zuwa idan mun tashi sai na jira shi ya gama cin kasuwa sannan mu dawo, har aka fara barayi sai aka rufe makarantarta gaba daya, yanzu mun daina zuwa amman ban manta komai ba na iya ina jin komai鈥�
Tun da Fadime ta fara bayani bata tsaya ba sai da ta kai aya, irin yadda ta ga duk sun kalleta yasa ta jidadi ba abun da take so a duniya kamar aji ta iya turanci ita ma. Zainab ta saka hannu biyu ta dafe kunnenta.
鈥淵ou are so talkative.. Haba.... 鈥�
鈥淟et her be she entertained me鈥�
Shattima ya fada yana murmushi, yana ganin ganin lokacin da Fadime ta murgudawa Zainab baki ta hararenta kasa kasa, tana daga ido suka hada ido ta madubin sai zaro ido alamar ta ji kumya tai saurin rufe fuskarta da tafin hannayenta. A nan ma Shattima murmushi yai he don't know why take burge shi? It's because ta saka Ra'ees ko kuma because she's silly girl? Har yanzu ya kasa daina murmushin abun da Ra'ees yai, and she's pretty kana ganinta ka ga fulani shi kuma yana son haduwa da yarensa, daman can ya san yaran fulani akwai wauta. Ba tare da ya kalli Zainab ba ya ce
鈥淕idan Hajiya a Mutu zan kai ki鈥�
鈥淣o bana son zama gidan Hajiya a Mutu ka sani鈥�
鈥淏a zai yiyu na kai ki gidana ba鈥�
Ta kalleshi.
鈥淲hy?鈥�
鈥淜in san ba zai yiyu na zauna dake a can ba daga ni sai ke鈥�
鈥淎mman saboda na sauka a inda kake ne yasa na fada maka na zo, if ina son zama a gidan Hajiya Matu zan sauka a can ne kai tsaye鈥�
Uffan be ce mata ba ya cigaba da tukinsa. Fadime kan mamaki ya ishe sai tunani Zainab take a ranta
鈥楧aga gani yar iska ce shiyasa tace tana son ta kwana a gidansa, Allah sarki shi na kwarai ne shiyasa babu ruwansa鈥�
Tana kallon ya faka motarsa gefen titi kusa da wani mai siyar da kaji ta hade yawu. Mutumen ya zo da sauri.
鈥淕uda biyu daban daban鈥�
Mutumen ya juya ya koma da sauri ya cire biyu da suke kan wuta ta sarasu ta saka a leda dabam dabam ya nufo Shattima. Kamin ya karaso Shattima ya sauke gilashin baya ta inda Fadime take ya masa nuna da ya bata. Cikin girmamawa mutum ya mika mata Shattima ya mika masa 5k sannan ya matsa gaba daya yai horn mai shagon ya zo da gudu.
鈥淜ana da yoghurt?鈥�
鈥淓h akwai ta Alhaji鈥�
鈥淜awo daya babba鈥�
Mutumen ya juya da sauri be dade ba ya dawo da yoghurt din a leda nan ma Shattima gilashin baya ya bude aka mikawa Fadime.
鈥淣a gode Allah ya biyaka鈥�
Ya fada tana karba da hannu biyu, sannan ya rufe gilashin ya juyo ya kalleta.
鈥淚na ne garinku?鈥�
鈥淏andalo鈥�
Ya dan yi shiru alamar tunani kamin yace.
鈥淚na ne Bandalo?鈥�
鈥淵ana cikin Kaita鈥�
Zainab ta juyo ta kalleta sai kuma ta kalli Shattima.
鈥淕arin da zanje ne fa, yana cikin Kaita ai, a kusa da garin akwai wani Kauye ma da nake son zuwa Garuk鈥�
Fadime ta zaro ido
鈥淣a san garin ai ina da... 鈥�
Har zata ce saurayinta sai kuma ta tuna.
鈥淒an'uwa a can dan'uwana ne, mutanen garin ma basa saka tufafi鈥�
鈥淵es yes yes and garin ku akwai bukkoki ko?鈥�
鈥淓h kowa yana da bukka ma a cikin muke kwana, har da shanu ma ni ma ina zuwa kiwo ai, daga can garin muka zo neman wani tare da kishiyar Inna ta, amman wai sai wasu mutane suka ce wai mayyace wai ta kama yaro, suka fara mata duka鈥�
鈥淭o yanzu ina take?鈥�
Zainab ta tambaya
鈥淭ana can na barta hannunsu ni gudu mai kar ace nima mayya ce, na yi karya na ce ban santa ba naji ana cewa mijin matar police ni kuma na gudu nace ni ma ban santa ba, kar a laka min Maita鈥�
A nan ma Shattima murmushi yai, Zainab tai fuskar mamaki.
鈥淢inene maita kuma?鈥�
Fadime tai shiru, ita ma dai taji ana cewa maita ko mayu bata san minene shi din ba if ma zata fada bata san yadda zata bayyana ba.
鈥淗ow old are you?鈥�
Nan ma bata cewa Zainab komai ba, sai hadiyar yawu take tiririn kaza na sauka a cinyarta.
鈥淶aki kai ni garin na ku har ma da can garim Garuk din?鈥�
鈥淓h Babana shine sarkin fulani yankin yamma na Bandalo鈥�
Murmushin jindadi Zainab tai dan ya kwana mata gidan sauki, ga yar gari ta samu wacce zata mata jagora.
鈥淪unana Zainab, I'm photographer daman zuwan da nai a nan zan dauki hotona ne kin san masu daukar hoto suna daukar abubuwa kala kala saboda samun Cigaban sana'arsu, an fada min mutanen garin Garuk ba su yarda da cigaba ko wane iri, ku kuma kuma da bukkoki wanda ba kasafai ake samun ba, wannan dalilin yasa na zo tun daga Yola dan na dauki hotuna鈥�
Fadime ta gyada kai alamar gamsuwa.
鈥淎she ke ma kina da surutu鈥�
Ba karamin haushin maganar Fadime Zainab taji ba, amman ba zata iya nuna mata ba tun da tana son ta taimaketa. Shattima kan murmushi kawai yake yana kallon Fadime cike da burgewa, sannan ya juya ya ja motar suka hau titi.
鈥淭o yanzu ya zamu yi?鈥�
鈥淜i bini muje garinmu sai na kira shi ya kai ki har garinsu daman ban taba zuwa ba鈥�
鈥淣o ki kwana a nan gobe sai muje garin na ku鈥�
鈥淎a na san hankalin Inna zai tashi idam bata gan ni ba, ni gida zanje, kuma Bappa na ai zai iya dukana ma鈥�
鈥淥kay zaki bani addirenshi idan na shirya sai na same ki a gari?鈥�
鈥淓h鈥�
Zainab ta dauko wayarta ta rubuta address din da Fadime ta fada mata sannan ta aje wayar ta bude jakarta ta dauko 2k ta mika mata.
鈥淕ashi na gode鈥�
Fadime ta bude ido.
鈥淒a gaske?鈥�
鈥淵es take it鈥�
鈥淭hank you鈥�
Ta fada tana karba cike da far'a. Har tasha Shattima ya kaita ya ciro 5k ya mika mata.
鈥淶a ki iya gane garinku ai ko?鈥�
鈥淓h kai ina ganewa fa鈥�
Ta bude motar ta fita cike da murna ga kazarta har biyu a leda da yoghurt ga kuma 7k hannu. Ta nusa kai cikin tashar ta nemi motar Bandalo, cikim sa'a ta samu har ta kusa ciki sai dai a motar akwai yan kaita akwai yan kuma wadanda za a kai Bandalon kai tsaye. Sai da motarsu ta tashi sannan ta fara tunani ko Amo ta wuce ko kuma tana can? Kila ma ta riga ta isa gida gashi har kwayar manshanun nata an fasa.
0 comments:
Post a Comment