Washe gari tun da farar safiya Fadime ta dauko littafin da biro, duk abun da ya faru sai da ta rubuce shi tsaf sannan hankalinta ya kwanta. Bayan ta gama ta fito waje tana lekon dakin Amo, sosai take jin kamar ta labarwa wani a sanadinta komai ya faru kuma tana tsoron kar Bappa ko Inna su ji, kusa da Inna ta zo ta tsaya tana gaishe ta kamar ba ita ba.
鈥淚nna naje na debo ruwa?鈥�
鈥淓h amman kamin ki fita ki yi addu'a dan Allah鈥�
Inna ta amsa mata da halshen fulantanci, da sauri Fadime ta nufi inda tulun yake ta dauka tana fadin.
鈥淎i na yi addu'a kuma idan zan fita sai na sake yin wata鈥�
鈥淲ai ina tulun jiya?鈥�
Fadime ta zare ido sosai.
鈥淎i da naji tana cewa ita Mayya ce sai na jefar da tulun na gudu, sai ya fashe鈥�
Ta tsuke fuska kamar wata tsohuwa, Inna ta dauke kai bata sake ce mata komai ba, Fadime na ganin haka ta nufi hanyar waje da saurinta ba abun da take son gani kamar Wasim, so take ta labarsa masa abun da ya faru so kuma ta nuna masa jindadinta. Kamin ta karasa gurin har da gudunta zuciyarta sai wani zillo take kamar zata fito, ko gurin ruwa bata je ba ta doshi inda ta san zata ga Wasim, ta kuwa ta ki sa'a domin ta same shi a jikin dutsen tsaye yana jiranta. Nesa da shi ta aje tulun ta karasa inda yake da sauri.
鈥淚na kwana鈥�
Be amsa ta ba sai yawo yake da idonsa a fuskarta, fuskarsa dauke da murmushi zuciyarsa kuma cike da shaukin ganinta.
鈥淛iya ashe wannan magen Inna Amo ce kishiyar Inna, tana ta rawa tana ta ihu鈥�
鈥淒a gaske?鈥�
鈥淲allahi kuwa na rantse da Allah鈥�
Amsa mata da yai yasa ta jidadin bashi labari har da nuna masa yadda yake tana rike ciki. Tun yana murmushi har ya fara dariya, yadda take nuna masa Amo ta yi sai tai wani irin burgeshi har yake jin kamar ya hade ta ta zauna a cikin cikinsa.
鈥淚 like you...鈥�
Ya furta cike da shauki. Sai ta tsaya cak yana murmushin mamaki.
鈥淢e kace? Ashe ka iya turanci?鈥�
Ya dauke kansa yana dan murmushinsa mai kyau.
鈥淢e kika ji na ce?鈥�
鈥淵ou say you like me!鈥�
鈥淏a kiji da kyau ba, yanzu dai shikenan kin huta ai babu mai sake miki komai鈥�
鈥淎mman wannan kawun nata yace na saurari sakamako na wai鈥�
Matsawa yai kusa da ita ya ture hular kanta ta fada baya ya shafa gashin kanta.
鈥淏abu wanda zai sake taba ki ina nan Fadime ki yarda da wannan! Ba ki cuwa ga kowa duk wanda ya zabi cin ki to ya ci mutuwa鈥�
Ya yi murmushin jindadi tare da mika masa hannunta.
鈥淭o taba min hannuna鈥�
Ya kalli tafin hannun.
鈥淚dan na taba kika ji sanyi fa鈥�
鈥淪hikenan na huta鈥�
Ta fada tana zare manyan idanuwanta da suka karawa fuskarta da far'arta kyau. Yayi murmushi.
鈥淚dan kuma baki ji ba fa?鈥�
Ta yi shiru tana dariya kamar yar 4 years.
鈥淣i kuma ba zan yarda ba鈥�
Ya fada yana daga mata gira idonsa cikin nata kamar zai cinye ta.
IYA POV.
Mamakin karfin Halin yarta Zainab ya hana ta sukuni, sam batai zaton yadda ta sakar mata ciwon kai da baya zata iya tafiyar nan ba.
鈥淚dan kin san wata baki san wata ba鈥�
Ta mike tsaye ta daga carpet dinta ta walware kurwarta ta jefata sama sai abu ya tashi kamar tantaba yai saman dakin kamin ya bat ya bata. Sannan ta nufi gurin da take aje kayanta na tsafi ta dauko tukunyarta ta kai bakinta jiki tai magana ta kara tukunyar a kunnenta, sannan maida ta aje ta nufi karkashin gadonta ta dauko wata kwarya ta fiddo wata karamar wuka, ta maida kwaryar ta dawo gurin carpet dinta ta janye dorowar dake sama ta daga carpet din ta dauko kurwar Auwal ta nufi bandaki da ita, sai davta rufe bandakin sannan ta warware zaren jikin sai ga wata yar tsoka mai kamar lakka, kafarta ta daga ta saka tsokar a kasa, a take tsokar ta zama zakara, irin marar lafiyar rakazan nan da basu da kuzari sosai kafafuwansa ta danne ta saita wukar saitin wuyansa ta yanka sai jini.
鈥淪ai ki dawo da hujja!....鈥�
Ta furta cikin bacin rai tana jin wani irin bakinciki na tafiyar da Hajiya Karama tai.
HAJIYA KARAMA (ZAINAB) POV
Cikin rashin kuzari ta gama shirinta, sakon da Auwal ya turo mata cewar baya jindadi ya tayar mata da hankali sosai, har take jin kamar ta koma Yola. Tana zaune a dakin kiran Shattima ya shigo wayarta. Kamar mai jira sai tai saurin picking.
鈥淗ello鈥�
Yana jin muryarta ya san bata cikin walwala.
鈥淗ey Hajiya Karama Lafiya dai?鈥�
鈥淲allahi Auwal ne ya turo sako wai ba ya jin dadi sosai, kuma ina ta kira be daga ba, so ina ta tunanin ko na koma ne鈥�
鈥淣o pls har kin riga kin je, ki dauri kawai zuwan na zama na banza, ai ba zaki dade ba right?鈥�
鈥淓h da naje na dauko hotunan maybe gobe ma na dawo鈥�
鈥淭o zai fi da ace ki dawo baki yi komai ba, ko kin dawo ai ba warkar da shi zaki yi ba, police din da zasu raka ki suna waje suna jiranki sun kira ni yanzu鈥�
鈥淥kay thank Youu鈥�
Ta sauke wayar zuciyarta na raya mata wani abu marar dadi da bata san minene ba, a rayuwarta bata taba samun namijin ta dake so a dabi'a da mu'amala ba kamar Auwal komai nasa ya mata, natsuwarsa kudinsa kyaunsa da komai ma, ya kwanta mata a rai sosai b kamar sauran mzan da idan ta ji tana sonsu yau ba gobe ta ji bata so ba. Haka nan ta mike tsaye ba dan ta so ba sai dan maganar da Shattima yai mata ta dauki jakar kayan aikinta ta fice daga dakin, sai da ta shiga tai ma Hajiyar gidan sallama sannan ta fito harabar gidan inda ta hango police din su biyu tsaye jikin wata 406 suna jiranta. Karasawa tai suka gaisa sannan dayan ya karbi jakarta ya saka a back seat ita ma ta shiga ya rufe motar ya koma gaba, ya tashi motar aka bude musu gate. Kamin su kama hanya ta fito da wayarta aikawa da Auwal sako.
鈥淚na ta kira baka picking how are you feeling now? Get well soon pls i love you...鈥�
Tana aika sakon idonta ya cika da hawaye for no reason, sai ta maida dubanta gurin titi yana sauke numfashi a hankali.
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number聽 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
03/12/2021, 09:24 - 馃馃馃馃: 27
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence to 08036126660*
FADIME POV.
Sai da ta cika tulun ya dorata sannan ta kalleshi tana murmushi.
鈥淣a gode鈥�
Murmushi yai mata as respond yana ta kallonta har ta fara tafiya, tana yi tana gaigensa sai murmushi yake mata har ta daina hangosa, wani kalar dadi take ji tun da ya fada mata babu wanda ya isa ya taba ta yana raye ya bata lasisin yin ma kowa yadda take so kenan. Hango mota fake a kofar gidansu na kara da police biyu yasa ta tsaya cak sai kuma ta dan koma baya ta boya, a tunanin ko Amo ce ta dauko mata police din, domin ta manta da zancen da tai da Xainab, har sai da ta hangota.
鈥淥h ashe ita ce鈥�
Ta fada tana washe hakora, abun ka da mutumen kauye yayi arba da n birni, sosai ta cira kafa ta karasa kusa da motar yana kallon Zainab baki har kunne.
鈥淜e ce...!鈥�
Zainab ta mata wani kallo from head to toe, sai wani kallon zanar take kamar mai kyankyami.
鈥淓h鈥�
Ta amsa kamar wacce bata son magana.
鈥淚na zuwa鈥�
Fadime ta fada sannan ta shiga cikin gidan da sauri, tsakanin sauke tulun kanta da labartawa Inna abun da ya kawo Zainab ba zaka iya fadar wanda ya riga wani ba. Mamaki ne ya cika Inna ta san Fadime ba dai wauta ba kam, in ba shi ba daga haduwa da mace a birni ki fada mata inda zata same ki bayan baki san ta ba baki san inda ta fito ba.
鈥淜in san idan Bappan ki yaji sai ya miki doka ko? Irin wannan shisshigin ya rabaki da shi Fulani amman baki jin magana鈥�
鈥淎i ba zai ji ba, ba zaki fada ba, kuma fa ita daukar hoto kawai zata yi鈥�
Fadime ta fada tan dafa Inna kamin Inna tace komai Zainab tai sallama ta shigo cikin gidan. Inna da Fadime suka hada baki gurin amsa mata, cikin karamci da girmamawa irin n Fulani Inna ta shiga bukkatarta ta dauko mata sabuwar tabarmarta ta shimfida ma, Zainab ba adan ta so ba ta zauna domin har ga Allah kyankyaminsu take.
鈥淪annu baiwar Allah鈥�
Cewar Inna tana aje mata kwanon kokon data dama.
鈥淵auwa ya gida ya aiki?鈥�
鈥淔atar kun iso lafiya鈥�
鈥淎lhamdulillah, am sunana Zainab ni photographer ce ma'a mai daukar hoto, ina daukar hoton duk wani abu da na san zai kawo min cigaba a sana'a ta, da kuma abun da zai kawo min daukaka, wannan shi ne katin shaida ta鈥�
Ta mikawa Inna id card dinta, cikin hanzari Fulani ta kai hannu ta karba ta soma karantawa.
鈥淜amin mu shigo nan sai da na fara biyawa gurin mai garin garin nan na yi magana da shi sannan na karaso nan, mun hadu da wannan yarinyar a Katsina few days back ta fada min gidansu da yadda zan same ta zata min jagora na yi aikina, ba a nan har a garin Garuk...鈥�
鈥淕aruk?鈥�
Inna ta fada tana dafa kirjinta. Cikin hanzari Fadime ta kashewa Zainab ido daya tana mata alama da tai shiru.
鈥淎a b ni zan kai ta can ba fa, ni wa na sani a can, ita tace zata je tare da police ko?鈥�
鈥淓h akwai wadanda za su min jagora zuwa can, a nan zan dauki hotuna ne kawai鈥�
Fadime ta mike tsaye da sauri ta nufi gurin garken shanunsu.
鈥淭o zo ki fara鈥�
Zainab ta mike tsaye ta nufi kofar fita, sai da ta fice sannan Inna ta kira Fadime tana mata gargadi.
鈥淜e wa kika sani a garin Garuk? Kin san yadda ake fadin garin nan ko? Fadime ki kama kanki ban son janye-janye鈥�
鈥淏a ni zan kaita ba, ni ma fa tsoron garin nake, ai ban je ba鈥�
鈥淣a dai fada miki鈥�
鈥淭au鈥�
Ta amsa da baki, zuciyarta kuma cike da son zuwa daman tana neman dalilin zuwa garin. Shigowar Zainab yasa Inna ta mike tsaye ta koma bukkarta, Fadime kuma ta tsaya jikin shannun har sai da Zainab ta gama gyara camera ta soma daukar hoto da ma gidan gaba daya. Suna fitowa waje abun ka da mutane kauye sai aka musu taro ana ta kallonsu, tun daga kan gidaje har gonaki sai da Zainab ta dauka, ba laifi garin ya burgeta ita kanta ba zata iya shaidar when last taga inda ake gidajen zana kamar a nan ba. Sai da ta gama sannan ta janyo Fadime gefe tana tambayarta.
鈥淵anzu ya za'ayi muje garin?鈥�
鈥淏ari naje ma fara dubawa idan yana nan鈥�
鈥淥kay karki dade鈥�
Da sauri Fadime ta sace kafa a cikin taron mutane ta zagaya zuwa inda zata ga Wasim, sai da taje ta duba ta dan jira na lokaci bata ganshi ba, ta dawo ta sanar mata, ko kadan Zainab bata jidadin hakan ba domin ta kwallafawa ranta zuwa garin, domin hotunan can da za su dauka zai fi daukar hankali fiye da na garinsu Fadime, ita kanta a yadda aka bata labarin mutane tana tsoron zuwa garin, ba dan tana neman suna da kuma daukaka ba babu abun da zai sakata tai wannan kasadar.
A garin da wuni har yamma after every one hour sai Fadime taje ta duba ko zata ga Wasim amman shiru, duk yadda Inna ta so Zainab ta ci abincinta bata ci ba, ita wai kyankyami take, sai police din aka bawa ita kuma aka siyo mata biscuits da lemun roba ta sha. Sai da yamma lis Fadime ta koma dajin tun kan ta karasa ta ji busarsa saita dawo da gudunta ta sanarwa Zainab.
鈥淵a zo, na ji busarsa鈥�
鈥淒a gaske?鈥�
Zainab ta tambaya gabanta na dan faduwa domin har ga Allah tsoro take ji kawai karfin hali ne irin na 蓷an maye.
鈥淎mman yanzu zan fadawa Inna cewar zan rakaki rijiya mai gaba dubu ki dauki hoto, sai ki sa police din nan su kori yaran nan kar su bi mu鈥�
鈥淥kay鈥�
Ta amsa mata tana gyada kai, domin da kamar rada suke maganar dan kar Inna ta ji. Sai Fadime ta kalli Inna dake wanke-wanke tace.
鈥淚nna wai zan rakata rijiya mai gaba dubu ta dauki hoto鈥�
Inna ta yi ma Fadime wani wawan kallo ta shiga mata fada da yaren fulatanci.
鈥淔ulani wai baki da hankali, taya zaki je rijiya mai gaba dubu da yamma haka? So kike ki kwaso wani abun kuma鈥�
A maimakon Fulani ta maida mata da yaren sai tai da hausa saboda Zainab ta ji.
鈥淎i ba zuwa zan yi kusa da rijiyar ba, nuna mata kawai zan yi n dawo鈥�
鈥淒an Allah ki taimaka min, shine kawai abun da ya rage min, sai n a koma in ya so gobe sai na dawo naje can garin Garuk din鈥�
Zainab ta fada da siffar magiya. Sai Fadime ta zaro ido kamar gaske.
鈥淎haa har da can zaki je? Ni tsoro nake ji鈥�
鈥淏a da ke zanje ba, ba man zan biyo ta nan ba, yanzu dai muje ki rakani na dauki hoton鈥�
Fadime ta kalli Inna da ta tsayar da wanke wanke da take tana kallonta.
鈥淚nna na raka ta? Ba zan matsa kusa da rijiyar ba na miki alkawari鈥�
Ba kasafai Fadime take requesting abu a gurin Inna ta kasa mata ba, ba dan komai ba sai dan tana son ta sosai da kuma ganin ita kadai ta rage mata a duniya.
鈥淜arki dade鈥�
鈥淭au鈥�
Fadime ta amsa tana washe baki, Zainab ta mike tsaye da sauri suka fita. Ko da suka fito ma babu mutane a waje sai police din dake zaune karkashin wata bushiyar dogon yaro, kai tsaye Zainab ta nufi inda suke ta sanar musu inda zata je tare da Fadime sannan ta bi bayan Fadime dake tafiya. Hanyar da zata ta sadasu da rijiyar Fadime ta bi sai da su kai nisa sannan ta karya kwana ta dauki hanyar da zata sadata ta bakin dutsen. Suna tafe tana tunanin abun da Wasim ya fada mata dazun, daman abun ya tsaya mata a rai.
鈥淲ai idan mutum yace maka i like you yana nufin so kenan?鈥�
Ta tambayi Zainab tana kallonta, a maimakon Zainab ta amsa mata sai tai mata banza, ba dan bata ji ta ba sai dan tana ganin Fadime ba ajinta ba ce da zata tsaya tana magana da ita, ba dan ma tana neman abu a gurinta ba da ko kallo bata isheta ba. Banza da Zainab tai mata sai yasa ta ji ba dadi sai dai bata nuna ba bata kuma sake ce mata komai ba har suka nisa cikin dajin. Busar sarewar Wasim ne abun da ya fara sauka a kunnuwan Zainab, daman Fadime ta saba da jin busar b tun yau ba, ita kam a gurinta ba bakon abu ne ba, wani irin natsuwa da shauki ne suka ziyarci Zainab, busar sarewar irin busar nan ce mai shiga zuciya da jini ta kwantar da hankali mai saurarenta, irin busar dake dacewa da ko wane kalar yanayi, a take ta ji ta kagara tai arba da mai busar, a rayuwarta bata taba arba sa wani abu mai burgewa da daukar hankali kamar haka ba, indai haka al'adar mutanen garin take tabbas zata burge kowa.
鈥淲ow.... 鈥�
Ta furta jin yadda suke kara dorar inda busar ke fitowa, ita kuma tana jindadin busar na karuwa a kunnenta, babu tsoron komai take ta ratsawa cikin gonar masarar tana ta son arba da mai busar. Fadime na gaba Zainab na binta a baya har suka haura saman dutsen, zaune yake ya basu baya ya saka sarewarsa a gaba sai busa yake, Fadime ta taka har kusa da shi sai ya mike tsaye ya juyo yana murmushi.
Wani irin faduwa gaban Zainab yai kwarjininsa da haibarsa suka tsaya mata cak a zuciya, ta saba ganin maza babu riga a jikinsu, gaisa da namiji taba jikinsa ko zama kusa da shi duk ba bakon abu bane a gurinta, amman a yau tana jin ta wata iri ta dabam ganin Wasim da irin kirar da ba ko wane namiji ke samu ba, komai na fatarsa Jikinsa a jere yake, fatar jikinsa jata ba kamar ita b da take fara fol, ga jiknsa all his muscle ya fito gwanin sha'awa, wani abun daya kara masa kyau walkin dake daure a kugunsa ko ba komai ya dabbaka al'adarsa, ga kuma kyau fuska a dogon hanci da fararen idanuwa da suka kara masa kwarji da haiba.
鈥淲ow....鈥�
Wannan karon a ranta a furta tana ta kallonsa irin kallon nan na burgewa. Shi kam kallo daya yai mata ya dauke kansa ya maida hankalinsa gurin Fadime.
鈥淭un dazun nake ta zuwa ban ganka ba, wannan matar tana daukar hoto ne kuma tana zon zuwa garin ku na fada mata zaka kai ta鈥�
A take murmushin dake fuskarsa ya gushe, ya saka hannunsa biyu ya dafa kafadar Fadime.
鈥� A garin mu ba a yarda da duk wani abu na cigaban zamani ba, kamar waya camara da sauransu, kuma ba kasafai ake karbar baki ba sai da wani dalili, idan nace zan kai ku zaki jefa ni a matsala鈥�
Fadime ta turo baki ta bata fuska.
鈥淣i dai n riga na ce mata zaka kaita fa...鈥�
Bakinsa ya cikawa iska ya busar ya maida dubansa gurin Zainab, matsowa tai kusa da shi ta mika masa hannunta ba tare da tunanin komai ba.
鈥淗i sunana Zainab...鈥�
Kallon hannunta yai kamin ya kalli fuskarta, sannan ya mika mata nashi hannun yana kallon cikin idonta, wanda hakan be yi ma Fadime dadi ba sai ta ji wani iri zuciyarta ta sosu.
鈥淜e jinin Iya ce...鈥�
Wani irin dauke numfashi Zainab tai tana kallon Wasim idonta kamar za su fito, tambayarta yake ko kuma fada mata yake? Tsoro ne ya kamata.
鈥淜a santa ne...?鈥�
Ta tambaya murya na rawa, be bata amsa ba yanje hannunsa yana kallon Fadime data kara bata fuska saboda ya gaisa da Zainab, shi kuma a zatonsa saboda yace ba zai kai su ba ne.
鈥淪hikenan...鈥�
Sai kuma yai shuru yana nazari. Zainab kam mamaki ya kusa kasheta, wata kila ya sani ne saboda shi matsafi ne ai zai iya karantar komai a tare da ita, sai a lokacin ta kara gasgata abun da ake fada a game da mutanen garin.
鈥淶an kai ku amman ba yau ba, ko kuma na tafi da ita kawai ke ki zauna鈥�
Ya fada yana kallon Fadime sai ta makkale kafada kamar wata yarinya.
鈥淎a ni ma ina son na ga garin ai鈥�
Zainab ta dora da.
鈥淣i ma yau kawai na ke da dama, gobe zan koma garin mu鈥�
鈥淚na ne garinku?鈥�
Fadime ta tambaya sai Wasim ya amsa mata.
鈥淵ola鈥�
鈥淓h Yola...鈥�
Zainab ta maimaita cikin tsananin mamaki.
鈥淜a san garin ne?鈥�
Nan ma be ce mata komai ba ya rika fuskar Fadime dake ta mamaki ace tun daga kasar Yola ta zo nan dan kawai daukar hoto.
鈥淜omai aka baki karki ci, ki min alkawari ko minene aka baki ba zaki ci ba?鈥�
鈥淣a yi鈥�
Ta fada tana daga hannu.
鈥淜o da nama ne鈥�
Ta bude baki tana yar dariya.
鈥淜ai har da Nama?鈥�
鈥淓h鈥�
Ya amsa mata da fuskar dake nuna ba da wasa yake ba. Sai tai yar siririyar dariya ta kawar da kai.
鈥淭au鈥�
鈥淣i fa...?鈥�
Zainab ta tambaya ganin ita be ce mata komai ba.
鈥淜i ci鈥�
Ya amsa mata ba tare da ya kalleta ba, yana cigaba da kallon Fadime ya ce
鈥淶an je na samo muku tufafin da za ku canja鈥�
鈥淗ar sai mun canja tufafi? Ni gaskiya tsoro nake ji ko dai mu bar shi, Inna ma bata san zan je ba鈥�
Fadime ta fada da iyakar gaskiyarta domin tsoron ya fara ratsata tunawa da gargadin da Inna tai mata. Zainab ta fisgota da karfi.
鈥淲allahi baki iya ba, sai da muka samu dama zaki ce a fasa...鈥�
Bata karasa ba, Wasim ya daka mata tsawa yana nunata da yatsa.
鈥淜arki sake...鈥�
Shan jinin jikinta tai ta make a gurin kamar babu mutum domin b karamin razana tai ba.
FALMATA POV.
Babu wanda ya san abun da ya samu goshinta har sai da garin Allah ya waye, ganin Baba n tsaye yasa Tumba ta nuna damuwarta kamar gaske.
鈥淜e miya samu goshinki?鈥�
Ta tambaya cikin daga murya da nuna tashin hankali kamar da gaske ta damu.
鈥淎 gidan da nake aiki ne na bugu da kofar ban lura ba鈥�
Falmata ta amsa tana tana goshin nata daya kumbura yana mata ciwo.
鈥淎yyah sannu鈥�
鈥淵auwa鈥�
Ta amsa tana kallon Tumba domin ta san ba dan Allah take mata sannun ba. Sai da risina har kasa ta gaishe da mahaifinta sannan ta kalli Tumba tace.
鈥淶an wuce aikin鈥�
鈥淭o Allah ya tsare鈥�
A natse ta nufi kofar fita tana tafiya da sauri sauri, domin jin take kamar da ta isa ne Sirleem zai kaita gurin gyaran kunne, babu abun da take so a yanzu kamar jinta ya dawo daidai. Kusan tun da ta fara aikin bata taba jin tana son zuwa ba kamar yau, duk wani nisa da gajiya da take ji idan zata ji sai ta neme shi ta rasa a yau, ko da ta isa masarautar 7:39am. Kai tsaye ta nufi bangaren Ammy kamar yadda ta saba, tana kokarin shiga gate din ta ji an tabota, sai ta juyo da sauri, hadinar data taba ta ta nuna mata Jurry, daga inda Jurry take tsaye ta daga mata hannu alamar ta wuce, sai ta sanda kanta kasa ta shige gate din b tare da tunanin komai ba. Sai da ta isa kofar falon Ammy ya danna door bell din sannan zuciyarta ta raya mata cewar wata kila bangaren da matar take shi ne bangaren Sirleem.
A yau ma Jekafiya ce ta bude mata kofar, Falmata ta risina har kasa ta gaisheta sannan ta fada mata bukatarta.
鈥淒an Allah ina nemn izini misalin 3pm zan je asibiti鈥�
鈥淭o za a sanarwar Ammy鈥�
Jekadiya ta amsa mata da karfin sanin cewar bata ji sosai sai an yi da karfin. A natse Falmata ta mike tsaye ta nufi dakin yaran ta fara aikinta. Bayan ta gama aka kawo mata abun karyawa sai ta dauki tray ta fita waje can gurin Garden ta zauna ta ci abincin mai rai da lafiya, sannan ta dawo da kayan gurin data saba aje su ta dawo dakin yaran gurin rainonsu. Cikin kwana biyun nan sun fara sabawa da ita musamman Labib yadda yake far'a da zillo idan ya ganta sai ka rabtse da Allah daman can a hannunta ya bude ido, ita da su da gan game da an dace ne domin ita na tana son yara balle kuma wa'dannn da suka kwanata mata a rai, take wuni tare da su basa barin hannunta har sai sun yi bachi. Misalin biyu da yan mintuna wata hadima ta shigo dakin ta sanar mata cewar an mata izini fitar, a lokacin tana goye da Luma dake ta aikin kuka alamar bachi take son yi.
鈥淒an Allah kin san agogo ki duba min ko karfe nawa?鈥�
鈥淓h biyu da minti arba'in da takwas鈥�
Hadimar ta fada tana kallon agogon bangon dake dakin yaran.
鈥淣a gode鈥�
Falmata ta amsa ta, sannan ta dauko Labib da abun wasansa ta nufo falon Ammy da shi, Jekadiya na zaune falon tare da Iya, Iya na ganin Falmata ta yi wani abu da kai ta dauke fuska kamar ta ga kashi, gaban Jekadiya Falmata ta sauke Luma da Labib sannan tai mata sallama ta tashi, sai ta juya sannan iya ta iya dago kai ta kalli bayan Falmata domin a yanzu tsoron hada ido take da ita.
鈥淣i kam Jekadiya da ni ce, da n bawa Ammy shawara, Babban Mutum ya nemi matar aure ya huta da irin yaran nan yan kama guri zauna, ba a san halinsu ba鈥�
Jekadiya ta yi murmushi.
鈥淎i ko matar aka kawo kin san ba su ke raino ba, dole mai raino za a dauka, kuma an kusa inshallah ni ma dazun Ammy take min albishir鈥�
Iya ta gyara zama cike da son jin labari.
鈥淎n samo masa wata kenan...?鈥�
鈥淓h inshallah鈥�
鈥淎llah yasa ma yar gida ace a huta, idan kuma ya kasa samun waje ba ga Hajiya Karama ba鈥�
Jekadiya ta mata kallon mamaki jin furuncinta.
鈥淗mm ita ma wannan yar gida ce, tun da Mai girma Waziri ba bari ba ne鈥�
鈥淓h haka ne, kam kai Mashallah Yar wajen Waziri ce kai mashallah鈥�
Iya ta fada ba dan ranta ya mata dadi ba, zuciyata sai kokarin gano mata take wace yar Waziri a ciki.
**
Wajen gate din Falmata ta fito ta tsaya, tana ta raba ido, ta kusan minti ashirin a tsaye sannan ta hango Sirleem ya fito daga bangarensu cikin wata motar wacce ba ta jiya ba ash colar, tun daga nesa da gane shi ne domin ta dade da haddace fuskarsa sai da ya kawo kusa da ita sannan ya rufe gilashin motarsa ya mika hannunsa ya bude mata front seat sai ta zagaya ta shiga ya tashi motar suka nufi gate.
鈥淚na wuni鈥�
Be amsa mata ba sai ya sakar mata murmushi yana cin apple.
鈥淏ismillah鈥�
Ya mika mata da dayan hannunsa dayan hannun kuma yana tuka mota da shi.
鈥淎a鈥�
鈥淒a dai kin ci ni da matsala鈥�
Bata ce matsa komai ba, domin bata ji abun da ya fada ba, bisimillar da yai mata ma ta gane ne saboda ya miko mata.
鈥淶an kai ki na aje ne, saboda akwai aikin da zan yi idan kin gama sai Momy ta dawo da ke鈥�
Ya rada mata.
鈥淭au鈥�
鈥淔ada min me kika yi har Babanki ya mareki haka?鈥�
Ta yi shiru tana mursa yatsun hannunta.
鈥淎 lokacin da aka kore ni aikin a nan gidan ne, sai Umma ta ce ma Babana wai ta gan ni da wani mutum muna aikawa assha鈥�
Ya kalleta yanayin yadda take maganar kadai ya isa ya sakar maka cewar tana daf da fashewa da kuka.
鈥淎bun nan akwai ciwo sosai kazafi, bayan shi kuma aka hada miki da duka I'm sorry鈥�
Bata ce masa komai ba, sai kokarin tare hawayenta take. Wannan karo daga muryarsa yai ta yadda zata ji.
鈥淪hiyasa kika yi kokarin guduwa ko? Now i realize irin wuyar da kike sha a gidanku, amman kin san me?鈥�
Ta girgiza kai.
鈥淚dan kika yi hakuri wata rana zaki ga ribar hakuri, amman idan kika gudu zaki afka wata rayuwar ne da ba lallai ne ki dace hannun kwarai ba, kuma idan zaki yi aure ko kika haihu abun zai biki ya bi zuri'arki ne, ki bata future dinki ki koma dana sani鈥�
Nan ma shiru tai bata ce komai ba, ido ya kura mata kamar ba tuki yake ba.
鈥淵a ma sunanki?鈥�
鈥淔almata...鈥�
鈥淜ina da Kyau...鈥�
Wani irin dadi ne ya lullubeta, an sha fada mata tana da kyau daga maza har mata yan'uwanta amman bata tab yarda da tana da kyau ba saia yau da Sirleem ya yabe ta, bata taba jindadi dan an fadi cewar tana da kyau a sai yau da Sirleem ya fada.
鈥淜ina da Kyau鈥�
Ya sake maimaitawa yana kallon pretty face nata.
鈥淒a kin bi duniya zaki yi arzik ki samu duk abunda kike so, amman zaki rayu cikin kunci da nadama, just like Mansura, banbancinki da ita ke wahala ce tasa kika gudu ita kuma auren dole za ayi mata shiyasa ta gudu鈥�
Ta dan dago kadan ta kalleshi cike da jin nauyinsa.
鈥淏ata son shi ne?鈥�
Ya tabe baki yana kallonta sai kuma ya kalli titi ya kwanto kamar saurayi da budurwa suna fira.
鈥淯hmm kusan haka, kin san su yarbawa idan akaiwa mace aure mostly su suke ciyardar mazansu, ita kuma tace ba zata iya wannan ba, hasalima bata son auren yarenta, daga haka ta gudu daga Ondo zuwa Lagos, sai ta fada hannun wani mawaki dan iska, shi ya koya mata iskancin har ya zame mata business, idan za ayi rawa ko wani abu da ita ake zuwa, ni kuma naje studio wani aiki sai na hadu da ita, ta fada min tana son waka kuma she's my big fan, hakan yasa na hada ta da wani manager na dake Kaduna, after ta zo Kaduna ta yi waka sai wakar ta karbu saboda ta fadi dalilin guduwarta, ba ni kadai ba mutane da yawa sun tausaya mata, at that time da muke magana da ita sai ta nuna min da ace zata samu ta gina kanta da zata daina karuwancin domin abun yana damunta, i like that girl saboda tana da addini but a lokacin can Zina ta zame mata ado, so i decided to help her sai na kama mata gida a Kaduna, na zuba mata komai a ciki saboda ita ta daina karuwancin, and i got lucky ta daina din, amman sai duniya ta dauki cewar na kama mata gidane saboda na maida ita karuwata, i face alot of challenges saboda haka har daga gurin Hajiya, to me taba mace rumgumarta gaisawa da ita ba komai ba ne a gurina, amman ban taba zina ba, har gaban Ubangijina zan fadi wannan, so kazafin da akai min ya min zafi amman hakan be saka na rabu da ita ba, ina ziyararta time to time, kamin na ankaro boom...! ta fada so na, a lokacin da ta tallata min kanta ba zan iya ce mata a'a, i accept it na saka ta istibira'i and guess what?鈥�
Ya karasa yana kallon Falmata da murmushi a fuskarsa, sai kuma ya bawa kansa amsa.
鈥淪ai Hajiya tace ba zan auri ta, saboda yare ce kuma karuwace sai dai na auri Nana, bana son ta amman haka na daure ina ta koyawa kaina sonta, saboda Nana bata daga cikin irin matan da nake so, ina son mace mai hankali da natsuwa da sanin ya kamata ba irin Nana ba, kuma ni bana son farar mace a yadda nake fari sai na samu baka zai fi bada kala ai, ina son mace mai addini da natsuwa kuma black beauty just like you鈥�
Ya fada daidai lokacin daya fakin harabar asibitin yana murmushi. Duk wani abu da Sirleem ya fada Falmata ta ji shi sai inda ya saka turanci ne kawai bata gane ba. Kallonsa tai kadan sai ta ji ya ji ya cika mata ido sosai har sai da gabanta ya fadi, sunkuyawa tai har ya fita motar ya zagayo ya bude mata side dinta.
鈥淜e baki ba ni labarinki ba鈥�
Ya fada saitin kunnunta bayan ta fito motar.
鈥淏a ni da labari鈥�
鈥淣o kina da your Family Papa Mama da kowa ma karatunki shekarunki and so on...鈥�
鈥淣i...鈥�
鈥淓h... 鈥�
Sai kuma ta shiru bata sake ce masa komai ba har suka soma nitsawa cikin asibitin, a lot of people sai kallonsa suke wasu na gaisawa da shi ciki har da masu daukar hoto da shi.
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number聽 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
03/12/2021, 09:25 - 馃馃馃馃: 28
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence to 08036126660*
FALMATA POV.
Shine a gaba tana biye har suka shiga office din Momy, tsaye suka same ta basu baya tana sanye da rigar likitoci tana duba wasu takardu dake gabanta.
鈥淢omy how are you鈥�
鈥淔ine kun shigo?鈥�
鈥淓h amman nan zan barta akwai aikin da nake, idan an gama sai na aiko driver ya dauke ta鈥�
鈥淥kay you can go鈥�
Ta fada ba tare da ta juyo ba, shi kuma be damu ba ya nunawa Falmata kujera.
鈥淛e can ki zauna鈥�
鈥淭au鈥�
Sai da ta zauna sannan ya juya fice yana yi ma Momy sallama. After ya fice Momy ta juyo fuskarta shakaf da hawaye ta kalli Falmata tana kokarin danne kukanta, sai kuma ta zagaya ta zauna a kujerarta tana hawaye. Falmata dai sai kallonta take ganin babbar mace kamar Momy tana kuka. Kuka sosai Momy tai sannan ta saka tissue dake gaban teburinta ta goge fuskarta.
鈥淵a goshinki...?鈥�
Ta tambaya da muryar kuka sai kuma ta sake fashewa da kuka. Ganin hakan yasa Falmata ta ce.
鈥淜o na kira Sirleem?鈥�
鈥淎a, ba matsalar shi ba ce matsala ta ce ni kadai鈥�
鈥淏aki da lafiya ne?鈥�
鈥淚na lafiya, kawai ina jin ciwo ne idan ana min gorin haihuwa, akwai ciwo a rashin haihuwa, idan na ga yara kamar ke ko kasa da ke ina jin kamar na sace, yan'uwan mijina da abokiyar zamana suna min abubuwa saboda ni ban haihu ba, kun zo a lokacin da wani abun ya bata min rai ne鈥�
鈥淚nshallahu zaki haihu, aure haihuwa, mutuwa duka lokaci ne鈥�
Momy ta share hawayenta tana jin yadda kalaman Falmata suka saukar mata da natsuwa.
鈥淗aka ne, haka mijina yake fada shi ma be cire rai da cewar zan haihu ba, ni ma ban cire rai ba ko dan rikon da nake ma Ameer ina fatar Allah ya dube ni ya ba ni haihuwa鈥�
Ta karasa idonta na cika da hawaye. Sannan ta dauko takarda ta rike biro tana tambayar yadda Falmata take ji da kuma lokacin da abun ya fara, after ta yi nata bincike ta kira likitan kunne ya dubata ya rubuta mata magani, da kanta ta karbi takarda maganin taje ta siyo mata a pharmacy dake asibitin sannan ta dawo office din waya a kunnenta.
鈥淭o ka biyo ka sauke min bakuwa a Masarautar su Sirleem鈥�
Tana fadar hakan ta sauke wayar ta mikawa Falmata maganin, kamin ta shiga mata bayanin yadda za ta yi amfani da shi. After like thirty minutes Ameer ya shigo Office din, hannunsa rike da makullin mota.
鈥淭ashi kuje shi zai sauke ki gida鈥�
鈥淭au na gode Allah ya saka da alheri鈥�
鈥淎meen, drive carefully鈥�
鈥淥kay Mom鈥�
Ya amsata sannan ya juya suka fita tare da Falmata, a tare suka jera har gurin da ya aje motarsa, sai ya shiga sannan yai unlock din motar ta bude ta shiga.
鈥淚na wuni鈥�
Ta gaishe shi ba dan ta san zai amsa mata yadda zata ji, bata a damu da sai ya amsa mata din ba, ta maida hankalinta gurin titi tana kallon motocin dake shigowa cikin asibitin a yayinda su suke kokarin fita. Lokaci zuwa lokaci yake kallonta haka nan yake jin takwanta masa a rai natsuwarta ya masa. Sau daya ta juyo ta kalleshi sai ya sskar mata murmushi ba ta sake kallonsa ba har suka isa bakin gate din Masarautar, sai da ta masa godiya sannan ta bude motar ta fita, be bar gurin ba sai da ta shige cikin Masarautar sannan yaja motarsa ya gaba. Cikin masarautar ta shigo rike da ledar maganinta dake cikin hijab, kai tsaye ta nufi bangaren Ammy, tana isa ta danna door bell din wata hadimar ta bude mata, babu kowa a katon falon sai ac da katuwar plasma, dakinsu yaran ta nufa, a hankali ta tura kofar ta shiga, sai ta samu Luma ta yi tana ta bachi, Labib kuma baya dakin, fita tai daga dakin ta sauka saka gaba daya ta nufi Garden daman da yamma haka a gurin take zama ko da yaran, balle yanzu da babu ko daya a hannunta.
SHATTIMA POV.
Ya farka da tunanin maganar da sukai jiya da Baba Waziri, babu abun da yafi tsaya masa a rai kamar maganar aure da kuma transfer, ba wai baya son zama kusa da iyayensa ba ne, irin halin da Mai Martaba yake ciki yana daga masa hankali gashi kuma idan yana gari dole ne sai an saka shi cikin harkokin sarautar. Sakon DSP Nura ne ya shigo wayarsa cewar police din daya bukata suna waje suna jiran Zainab, call list dinsa ya shiga ya kira Zainab ya sanar mata, sannan ya mike tsaye ya fito harabar gidansa, a zahiri motocin dake jera a harabar gidan yake kallo, abadini kuma zuciyarsa na can ta lula wani gurin da tunani. Juyawa yai koma ciki yana shiga ya tube tufafin jikinsa ya shiga bathroom yai wanka ya fito ya shirya cikin kananan kaya sai kamshin turare yake kamar wani sabon ango. Keys dinsa ya dauka da wallet dinsa ya nufi motarsa Baba Adamu na ganin haka ya taso da sauri.
鈥淩an ya dade masarauta zamu je?鈥�
鈥淣o zauna abun ka ni kadai zanje鈥�
Ya furta yana bude motar ya shiga, kamin yai warming din motar har mai gadi ya bude masa gate. Kai tsaye ya dauki hanyar da zata sada shi da masarautar daman can a ka'ida ba a masarauta yake kwana ba sai idan ta dauro, duk wani abun daya shafi masarautar yana nisanta kansa da shi domin ko kadan sarautar bata burgeshi. Tun daga babban gate din har cikin gida ake ta mika masa gaisuwa amman be amsa ko ka daya ba, daman can kasaita bata barinsa amsa gaisuwa balle kuma yanzu da tunani ya saka shi gaba. Yadda ya fito cikin motar yana takawa sai ka rantse da Allah ba zai mutu a saka a cikin kasa ba, kallo daya zaka masa kasan cewa jinin sarauta ne, domin sarautar ta nuna a tafiyarsa da maganarsa da isarsa da fuskarsa da kamalarsa ga wani irin kasaita a tafiyarsa kamar shi ne sarkin ma. Kai tsaye ya nufi bangaren Mai Martaba sai ya kararda shi yana bachi, hakan yasa ya dawo bangaren Ammy, sai da ya fara duban yaransa dake hannun Jekadiya sannan ya nufi dakin Ammy ba tare da ya tambayi mai rainonsu ba. Ammy bata dakin Sai Nana dake aikin mata abincike a wardrobe ganin Shattima yasa jikinta ya fara rawa.
鈥淵a Shattima sannu da zuwa鈥�
鈥淵auwa Sis Morning baki je school ba鈥�
鈥淓h sai gobe?鈥�
鈥淲hy鈥�
鈥淏ana jin dadi ne, kuma na fadawa Driver yaje makarantar ya fada鈥�
鈥淢e ke damunki?鈥�
鈥淔ever amman an sha magani鈥�
Tana amsa masa ta nufi kofa da sauri, shi kuma ya bita da kallo cike da kulawa. Tana fita Ammy ta shigo rike da plate din wainar kwai a hannunta.
鈥淢orning Ammy鈥�
鈥淗ow are you?鈥�
Ya dan tabe baki alamar ba Kalau ba.
鈥淭unani ko rashin lafiya?鈥�
Ammy ta tambaya yana mika masa farantin.
鈥淭unani dai鈥�
Sai tai murmushi.
鈥淲aziri ba zai yi abun da zai cutar da kai ba, ni kaina na dade ina son ka dawo garin nan da aiki ka ki, yanzu kuma baka isa ka sabawa Umarninsa ba鈥�
Ya sauke ajiyar zuciya a hankali yana kallon Ammy.
鈥淢aganar Auren ma bana fatar ka saba masa, tun da har ya zabi rufe ido ya aura maka yarsa be kamata kace aa ba鈥�
鈥淚 accept it鈥�
Daga haka be sake cewa komai ba. Be koma bangaren Mai Martaba ba sai da suka fito daga sallah la'asar. Ko da ya shiga falonsa sai ya same shi a ciki zaune, ko'ina na falon duhu ne kamar dare, bayan kuma yamma ne akwai haske a ko'ina. Ganinsa a falo ma abun ma farinciki gurinsa domin a da kullum yana kan gado kwance, amman yau gashi akan kujera zaune. Kamin ya karasa kusa da shi yai masa sallama, Mai Martaba ya dago kansa a hankali ya kalli Shattima, wanda siffarsa da ke shimkide a siffar Shattima kallo daya zaka masa ka san jini daya ne. Gaban Mai Martaba Shattima ya zauna yana murmushi.
鈥淏arka da Yamma Mai Martaba ya kufan jiki?鈥�
鈥淎lhamdulillah鈥�
Mai Martaba ya amsa yana ta kallon Shattima.
鈥淣 ga jiki ya fara kyau Alhamdulillah鈥�
Shattima ya fada cikin jindadi, sai Mai Martaba yai murmushi ya ce.
鈥淎n samu shigowa?鈥�
鈥淓h Baba Waziri ne ya kira ni jiya, akan maganar fitar da kai waje da kuma aurena da neman transfer鈥�
A hankali Mai Martaba ya sauke ajiyar zuciya.
鈥淗akan yana da kyau, ni kaina aurenka yana cikin rai na, neman transfer ma yana kyau, domin kai ne babba a yanzu, sai dai magana fita da ni waje a bar wannan maganar鈥�
Shattima ya dago ya kalleshi.
鈥淪aboda me? Ba san inda za a dace ba Mai Martaba duk fata muke yi鈥�
鈥淗akan yasa nake son maka wata wasiya, na san matsalar auren nan yana damunka, ina son nai maka wasiya cewar kai ta aure ko da kuwa yau zaka aura gobe ta mutu, to jibi ma ka sake auren wata, a koda yaushe ina maka kallon babba a cikin iyalina, ina jin dadi da alfaharin da Allah ya bani kai a matsayin da, Omar ina maka wasiya da ka ji tsoron Allah, kuma ka rike yan'uwanka tsakani da Allah babu banbanci ko nunawa wani ya fi wani...鈥�
A take jikin Shattima yai sanyi, sai ya ji kamar Mai Martaba na masa wasiyar bankwana ne. Shiru mai Mai Martaba yai na dan lokaci sannan ya cigaba.
鈥淩ayuwa a gida da Family irin wannan akwai wahala, amman idan ka jure Allah zai taimakeka, bana son ko bayan raina a samu rabuwar kai a tsakaninku, bana son tsabani ko kiyayya ta shiga tsakaninku, ka yi kowa biyayya ka bawa kowa hakkinsa...鈥�
Mai Martaba bai karasa ba Shattima ya katse shi jin kamar kunnuwansa da zuciyarsa ba za su iya daukar abubuwan da Mai Martaba yake fada masa ba.
鈥淚nshallahu zaka samu sauki Mai Martaba鈥�
Mai Martaba ya gyada kai.
鈥淪auki yana tafe da yarda Allah, amman sauki na har abada, sauki wanda daga shi babu wani ciwon Inshallahu, ni kadai na san me nake ji akan ciwon nan Omar, bayan ciwon jiki a nake kwana da shi kullum na tashi da shi, ga ciwon tsoron rabar mutane da tunani, na yarda wannan jarabawa ce, babban Sarki kamar ni ace bana iya shiga cikin mutane, bana iya sauraren al'ummata, ina jin tsoron abun da zan fadawa Ubangijina, ina jin kamar sauka ta cancance ni wata zuciyar kuma na raya min idan nai hakuri nan ba da jimawa ba zan tafi na bar Sarautar, ba barin sarautar ce tashin hankalina ba, yadda zan tafi n bar ku, rashin hadin kanku da irin matsalolin da kuke samu tun a yanzu da nake raye, babu uban da zai so ya tafi ya bar iyalansa a watse kansu a rarrabe, kai ne babba Omar dan Allah ka kula da yan'uwanka, na san na dora maka abu mai nauyi, amman Allah zai taya ka, ka bi Hajiya Bilki kamar Ammy, kuma kai ta hakuri da yan'uwanka, musamman Mama Aisha (Nana) ita ce karama a cikinku ita ce kadai ta tashi bata san gata da dadin uba, bata san ta rabe ni ba saboda lalurata, ka kyautata mata ka zame mata uba, kuma kai hakuri da halayenta akwai kurciya a tare da ita, sannan ka saka ido akan tarbiyar Karima, ka bi kanen mahaifinka kamar ni.... Kuma kai ta hakuri da rayuwa鈥�
Shattima ya rufe idonsa da suka gama cika da hawaye.
鈥淚nshallah zaka same ni mai cika umarninka Mai Martaba鈥�
鈥淎llah ya maka albarka鈥�
鈥淎min鈥�
Ya amsa yana jin kamar ya fashe da kuka.
鈥淎njima idan Ammy ta shigo, zan sa ta duba maka takardun wasu filaye da gidajen da baka san da su ba, akwai kuma takardar da nai rubutu na wadanda nake bi bashi da kuma wadanda kasuwanci ya hada mu, zan hannata maka su ka aje inshallah鈥�
Uffan Shattima be ce zai iya kara cewa ba ya mike tsaye.
鈥淎 tashi lafiya Mai Martaba鈥�
Ya fice daga falon da sauri kamar zai tashi sama, be taba daukar haka wasiya take da nauyi ba sai a yau. Gaba daya jin yake duniyar na juya masa, ta ina zai fara ina zai sauke why mai martaba yai masa wannan wasiyar a yanzu.? Why him? Har ya iso bangaren Ammy kirjinsa be daina nauyi ba, ga zuciyarsa sai bugawa take kamar zata fito, nauyin ba kirjinsa kadai yake ba har a kansa ji yake kamar Mai Martaba ya dauki wani katon dutse ya dora masa a kai. Sai ya samu kansa a falon Ammy sannan ya soma tambayar kansa abun da ya kawo shi a falon, but he need to see his mother maybe ko zai samu saukin abun da yake ji. Hakan yasa ya nufi dakin yana kokarin tura kofar dakin ya shiga ya ji muryar Nana.
鈥淣i sai na tafi鈥�
鈥淣ana kina ganin rashin kunyar da kika min zai barki ki rayu in peace, kina min tsawa your own biological mother鈥�
Tsaye yai jikin kofar yana kallon Ammy dake zaune kasa ta jingina da gadonta tana kallon Nana kamar Nana ce uwar ita ce yar.
鈥淲hat is happening?鈥�
Nana kamar mai jira ta juyo gurinsa da sauri ta soma masa bayani kamar zata yi kuka.
鈥淵a wai bikin yar Farin gida da ake wai Ammy ba zan je ba, kuma Amal kawata ce ita ce ta gayyace ni ita kanwar Amarya ce class din mu daya鈥�
鈥淵aushe ake bikin?鈥�
鈥淵au ake budar kan Amarya, kuma ba cikin manyan zan tsaya ba, ni gurin su Amal zan tsaya鈥�
鈥淪hikenan je ki fara shiri tun yanzu, zaki je anjima鈥�
Da sauri ta rumgume shi tana murna.
鈥淭hank Youu Ya I love you鈥�
Ta sake shi sannan ta fice daga dakin cikin murna ranta fes tun da Shattima yace zata je. Sai da ta fice sannan ya nufi inda Ammy take ya zauna gefenta sai shi akan gadonta ya zauna tsabanin ita data ke kasa zaune.
鈥淎mmy why kika hana ta zuwa?鈥�
鈥淏ata son makaranta, duk abun da aka ce tai ba zata yi ba, sai kuma a rika bin ra'ayinta ana mata yadda take so?鈥�
Shiru yai yana kallon yadda idon Ammy ya cika da hawaye, sai ya ji tausayinta ya rufe masa zuciya.
鈥淎mman idan kina irin kalaman nan marar dadi a gareta wani abu zai iya samunta, kuma still mu ne zamu shiga matsala, she's still young鈥�
鈥淟ike a baby?鈥�
Ta tambaya hawaye na sauko mata.
鈥淚na jin kamar ace Nana tana da wata uwar ba ni ba, da yanzu na maida ta hannun mahaifiyarta na gaji da wanne zan ji鈥�
Ta fashe da kuka. Hakan yasa Shattima yaji damuwarsa ta karu, ya mike tsaye jiki ba kwari ya fice daga dakin domin ko kadan baya son jin kukan mahaifiyarsa. Dakin yaransa ya nufa or maybe zai samu peace of mind a can, Luma kadai ya samu a dakin tana ta bachi, kusa da ita ya zauna ya shafa fuskarta a hankali yadda ba zata tashi ba, sannan ya mike tsaye yana sauke ajiyar zuciya ya nufi gurin windows dakin wanda ke saiti da Garden din bangaren Ammy, tsaye yai jikin window yana kallon itacen dake garden din wani iska mai dadi yana bugunsa, hannayensa ya dora jikin window wanda hakan ya bashi damar hango Falmata dake zaune a garden din tana ta kallon wani gurin na dabam kamar mai tunani. A inda take tsaye na kasa baya iya hango na sama sai dai na sama ya hango na kasa.
Hango Sirleem da tai tafe yasa ta mike tsaye tana jiran ya karaso kusa da ita, tun daga nesa yake sakar mata murmushi har ya karaso.
鈥淣aje daukarki Momy tace tasa Ameer ya kawo ki, na shiga bangarenku n karbi takardar maganin wata hadima tace min kina Garden鈥�
鈥淓h ta bani maganin ma鈥�
鈥淥h Momy akwai karamci sai da ta siya maganin ma鈥�
Ya fada yana murmushi domin kadan daga halin Momy ne taimako da karamci ga tausayi da son mutane.
Ya kai hannu ya karbi maganin yana dubawa.
鈥淭a fada miki yadda za ki yi amfani da shi?鈥�
鈥淓h ina son sai na je gida sai na fara idan zan kwanta鈥�
鈥淎mman dai yau ba zaki kai dare kamar jiya ba ko?鈥�
鈥淪ai yaran sun yi bachi tukuna鈥�
Ya mika mata ledar maganin yana fadin.
鈥淭o ya kamata ki samu Mai Napep din da zai rika kai ki ya dawo dake, zan biya shi鈥�
Kallonsa kawai take baki sake tana mamakin yadda yake da karamcin da son taimako har haka. Kamin tace komai yace.
鈥淏a ki ba ni labarinki ba fa鈥�
Ta yi kasa da kanta, ba dan bata ji domin duk maganar da yake mata yan mata ne cikin daga muryar ta yadda zata ji, ba ita kadai ba har wanda ke kusa da su ma zai iya ji.
鈥淗ey....鈥�
Ya fada yana leken fuskarta. Sai ta dago ta kalleshi, ta sake maida kanta kasa.
HAJIYA BILKI POV.
Hajiya Bilki ta sauke ajiyar zuciya jin abun da Aminiyarta kuma matar Waziri wato Hajiya Talatu take fada.
鈥淲allahi kuwa鈥�
鈥淜i ce kina cikin tashin hankali, to wai Waziri lafiya yake kuwa?鈥�
鈥淣i ina na sani, sai wani fadar yake duk na sake yi ma dan da'uwansa kazafi a bakin aurena, ina zaman zamana zai dauko min wata masifar, wannan duk na Ammy na na sani, shi kuma baya iya musa mata tun da ta shanye shi, daga ni har Maijidda jiya ba mu runtsa ba, kuka kawai take鈥�
鈥淎i dole tai kuka za akai ta ga halaka, yarinya tana zamanta za a aura mata mutuwa, Wallahi ki tashi tsaye karki yarda sam a kai ki a baro鈥�
鈥淎i ba zan yarda ba, sai dai ayi wacce za ayi, amman ba zan Waziri ya aurawa Shattima yata ba, ko ana zaune kalar ai ba zan yarda ba balle kuma mutum ya zama maye, idan dama ta ki hagu zan koma, idan ta gwada be yarda ba be janye maganar ba, garin su mutanen nan zanje ayi masa asiri ya janye鈥�
鈥淎i haka ya dace gaskiya, sai muje tare, kaji min tashin hankali鈥�
鈥淲ai sai fdar yake indai ba Shattima ya fasa ba Wallahi ba za a fasa auren ba, so yake yana aura masa ita ta mutu, waya sani ma ko Ammy ce take cinye masa mata, ko kuma can garin tsafe tsafensu suka kwaso wani mugun abu鈥�
Hajiya ta dade tana magana da Hajiya Talatu kamin ta katse wayar shi M saboda shigowar Nana.
NANA POV.
Tana Fita daga dakin Ammy ta nufi bangaren Hajiya. Tana tura kofar dakin ta shiga sai Hajiya tai wa Hajiya Talatu sallama ta kalli Nana tana murmushi.
鈥淒aughter鈥�
鈥淣a'am Hajiya dan Allah wayarki zaki ara min na kira driver na鈥�
鈥淭o gashi鈥�
Ta mika mata wayar, Nana ta kai hannu ta karba ta fice daga dakin tana nemo line AA call list din Hajiya domin bata yi saving number ba. Bugu daya ya dauka.
鈥淗ello鈥�
鈥淪ardauna鈥�
鈥淣a'am鈥�
鈥淜a shirya anjima da 8 ka zo ka kai ni gurin budar kan Amarya鈥�
鈥淥kay鈥�
鈥淜arka wuce 8pm鈥�
鈥淥kay鈥�
**
Ya amsa mata tare da sauke wayar tare da saka ta aljihu sannan, ya marasa cikin gidan yana nade wandonsa.
鈥淎nti wanki da yamman nan鈥�
鈥淭o kayan sun yi datti, kai kuma ba zama kake ba鈥�
Hannayensa ya jefa cikin ruwan ya soma taya ta wankin, daman can idan tana wanki ya kan taya ta ko kuma yai mata, kayan su Khaleel da Aymana duk shi yake wanke wa, har girma yana mata idan yan kwarai na saman kai, ko kuma ya mata rabin girkin ita kuma ta karasa. Sai da ya fara dauraye tufafin yana shanyawa sannan ya dauko mata wani labarin.
鈥淎nti ina tunanin komawa makaranta fa鈥�
鈥淢akarantar lafiya? Ni ba ni da kudin biya maka makaranta yanzu, kai kuma ba aikin wahala kake so ba balle ka taimaki kanka鈥�
鈥淎i wani aikin zan samu mai soka soon, zan gyara gidan nan na masa fenti na saka masa tayis na siyo miki gas, ke har makka sai na kai ki na siya miki mota, su Khaleet na saka su makarantar kudi, komai zai zama normal...鈥�
Kallonsa tai.
鈥淎A baka rabu da yarinyar nan ba ko? So kake ka jefa kanka a matsala ko?鈥�
鈥淣i fa na rabu da ita bana tare da Ita sam sam sam鈥�
鈥淵a dai kamata ace idan nai maka magana ka ji, idan na ce ka bari ka bari, ba ka da wanda ta fini a yanzu, baka da gata sai ni, kasan bamu da kowa sai Allah, idan ka shiga wani hali aka kama ban san ya zan yi ba, aje min wankina鈥�
Ya kalleta a sanyeye.
鈥淏a maganar yarinyar nan ba ne Anti鈥�
鈥淣i dai ka aje min wankina鈥�
Ya cire hannunsa ganin da gaske take domin babu alamar wasa a maganar ta balle kuma a fuskarta. Wannan abun yake tsoro ya dade yana son labarta mata ko kuma sammata wani abu amman yana tsoron abun da zata fada, domin shi kansa ya san ba shi da gatan daya wuce Antinsa a yanzu, ita ce uwarsa ita ce ubansa ita ce komai nasa.
鈥淜a rika taka tsantsa da rayuwa AA, neman kudi ba hauka ba ne bana son ka jefa kanka a matsala, na rasa uwa n hakura, na rasa uba na hakura, na rasa miji na hakura, yanzu kam bana jin idan na rasa ka zan iya rayuwa, kai kadai ka rage min, ni ma ni kadai na rage maka, ya kamata ace idan na maka magana ka ji, ka san irin wahalar da muka sha kamin mu kawo yanzu, kasan irin fadi tashin da nai kamin na samu na gina kaina, muna zaune cikin rufin asiri kana kokarin jefa mu a hadari?鈥�
鈥淚dan akan yarinyar nan Allah ya min arziki, ba fa akanta ba ne鈥�
Uffan Anti bata sake ce masa ba, ta san akanta ne tun da har yai ma kansa addu'ar arziki. Ganin yadda ranta ya bace yasa ya tashi ya nufi gindin murhu ya fara saka itace zai hura mata wuta.
鈥淜arka kunna wutar nan鈥�
鈥淕irki zan dora miki鈥�
鈥淏a mu da abun dafawa kwado zan yi鈥�
Ya kai hannunsa ya taba aljihun wandonsa, yana da kudi amman ba damar ya bata tace ina ya samo ko kuma tace ba zata karba ba. Mikewa yai tsaye ya dawo bakin kofar dakinsa ya zauna yana kallonta, har ga Allah be jidadin yadda ya ga ranta ya bace ba, domin Anti Rabi ita ce a matsayin uwa a gareshi duk wani abu da uwa take yi ma da, Anti Rabi ce tai masa lokuta da dama zata hanawa yaranta abu ta bashi, babu abun da zai nema ta ki yi masa sai idan bata da hali
鈥淒a kin aje wanki gobe na karasa miki鈥�
Ta masa banza, sosai ranta ya bace ta san yadda AA yake da shegen son kudi, ba zai yi sata ba amman yadda ya lakewa yarinyar nan tana tsoro kar ya janyo musu abun da yafi karfinsu. Mikewa yai tsaye ya shige cikin dakinsa ya bude akwatinsa yana duba kayan da suka fi fitar da shi.
鈥淵arinyar nan ma da safe bata bar ni naje gidansu ba balle na kara samo wani abu鈥�
Ya fada cikin jin haushi yana tuna kiran da tai masa dazu da safe ta sanar masa cewar ba zata je makaranta ba.
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number聽 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
03/12/2021, 18:50 - 馃馃馃馃: 30.
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence via 08036126660*
FADIME POV.
kamin su karaso ya Wasim ya kalli Fadime ya ce.
鈥淜arki yi magana kuma komai aka baki karki ci鈥�
Ta daga masa kai wasu hawaye masu zafi na sauko mata. Ganin hakan yasa ya kai hannunsa ya rika wuyan hannunta. Mutane na karaso kusa da shi suka risina masa alamar girmamawa.
"Erregeak zure ahoarekin ikusi behar du"
_Sarki na bukatar ganin tare da bakinka_
Be ce komai yaja hannun Fadime ya fita daga cikin runfar, Zainab na ganin haka ta bi bayansu da sauri, mutanen da suka zo kiransa suka rufa masa baya. Ta inda mutane suka fito ya nufa rike da hannun Fadime wanda ta kasa daina hawayen da take. Ta bayan wani guri wanda yafi kama da kasuwa suka bullo, duk inda Wasim ya dora kafarsa sai an risina masa an dauke ido daga barin kallonsa alamar girmamawa da biyaya. Sun yi tafiya mai dan nisa a kafa kamin su isa bakin wata babbar kofa ta itace an mata gate har da masu gadinta. Wasim na isowa gurim kofar aka bude masa suna risinawa har sai da ya wuce sannan suka tashi. Hakan yasa Fadime ta ji wani girma ya kamata, ko ba komai ta ci alfarmar Wasim ita ma an risina mata, a nan ta kara yarda babu wanda ya isa ya taba ba, kimar Wasim da sonsa suka kara ninkuwa a ranta. Shiga cikin gurin yasa daga Zainab har Fadime suka manta da abun da ya kawo su gurin, wata sabuwar duniya ce, kuma babbar daula mai zaman kanta, babu komai a dayan bangare sai katuwar gona mai cike da manyan itace wanda har baka iya hango cikinta saboda hudu, ta gafe daya kuma kana jin kwarar ruwa alamar akwai korama a gurin. An bi ko'ina na harabar an haska shi da wutar ice wanda hakan ya bawa Zainab da Fadime damar ganin irin kwaliyar da aka yi ma gurin da koren ganye mai yanayi da ganyen ayaba. Sai da suka isa gaban wata kofa sannan Wasim ya cire talkaminsa na fata, ya nasa kafarsa a gurin, Zainab da Fadime kan daman ba su shigo garin da talkami ba. Wata katuwar fada ce da aka shimfida mata gashin farar damisa, tun daga bakin kofar har zuwa inda Sarkin yake zaune kan wata kasaitacciyar kujera da zaka iya rantsewa ba itace ne aka saffara ba. Daga hannun kujerar har jikinta an masa kwaliya da farar azurfa. Ginin fadar kuma an masa kwaliya da fatar zaki inda Sarkin zai dora kafarsa da hannunsa ma kan Zaki ne a gurin. Tsirarun mutane ne a cikin fadar ciki har da Liya dake tsaye gefen Sarkin dake hakimce saman kujera fuska babu annuri.
Nan da nan jikin Fadime ya fara rawa, kafafauwanta suka fara lankwashewa kamar wata musaka. Nesa da Sarkin Wasim ya tsaya ya saki hannun Fadime ya risina da kafarsa daya ya dukarda kansa ya kwashi gaisuwa.
鈥淏arka da wannan lokacin Shugaba鈥�
Ya fada da yarensu, a maimakon Sarkin ya amsa masa sai wata tsohuwa ce mai bakin zane ta amsa masa tana takowa zuwa inda yake tare da jero masa tambayoyi.
鈥淪u waye wannan Shugabana?鈥�
Wasim ya mike tsaye da kyau yana kallon tsohuwar kamar ba zai amsa mata ba.
鈥淵an garin nan ne, be zama lallai ki san kowa a garin nan ba鈥�
Ya amsa mata da yarensu, kamin Liya ta nuna Fadime data magana da yaren da su kadai suke ji.
鈥淣a san wacan yarinyar, yana zuwa gurinta, a wani gari da yake yamma da garin nan...鈥�
Fadime ta kara fito da idonta waje, duk da kasancewar bata san me Liya take fada ba amman nuna ta take, gashi ta ga Wasim ma a nan shi ya risina a maimakon a risina masa, take mararta ta kara cika da fitsari, hannunta ta kai ta bugu Wasim yana kallonta ta soma masa magana a cikin ranta.
鈥淔itsari nake ji fitsari鈥�
Ta fada a ranta tana mutsika masa ido tana masa alamar yadda zai gane. Shi dai kam be fahimci komai ba hakan yasa ya maida hankalinsa gurin Liya.
鈥淚na magana tana magana saboda an daure mata ta yi yadda take so a masarauta, mi zai saka na fadi abun da ba shi ba a gaban Shugaba? Ya zama lallai sai kun san kowa a garin nan ba, amman lallai ne kowa ya san ku鈥�
Ya fada da yarensu yana watsawa Liya wani mugun kallo. Hannu Sarki ya daga sai tsohuwar taja baya ta nufi wani guri daya fi kama da bukka a cikin fadar, bata dade ba ta fito rike da ture wanda ke dauke da soyayyen nama, ta mikawa Zainab.
鈥淐i鈥�
Ta fada da yarensu, Zainab ta kai hannu ta dauki yanka daya da sauri ba dan ta san abunda ta fada ba, jiki na rawa ta kai bakinta ta tauna ta hade, daga lokacin ne gaban Liya ya fadi ganin ba tai komai ba. Tsohuwar ta matsa da naman kusa da Fadime.
鈥淐i鈥�
Tana fadin haka Fadime ta kalli Wasim da sauri, sai ya amsawa tsohuwar da yarensu.
鈥淏ata cin nama鈥�
鈥淣a yau ne kawai, kuma umarnin Shugaba ne, ci鈥�
Ta karasa tana kallon Fadime, da sauri Fadime ta kai hannu ta dauki yanka daya tana kuka ta kai bakinta, bata ko tsaya tauna shi ba ta hadiye. A take ta ji wani abu ya taso mata tun daga cikin cikinta ya nufo makoshinta, wani irin kaikayin bala'i ne ta ji a makoshinta, daga Wasim har tsohuwar da Sarkin da Liya kallonta suke.
鈥淲acan ta mu ce wacan bare ce鈥�
Tsohuwar ta fada tana nuna Fadime, tana yin baya-baya, wani irin ihu Fadime ta saka ta rike makoshin tana kuka.
鈥淲ayyo kaikayi wayyo Allah kaikayi鈥�
Da sauri Wasim ya maida ita bayansa, yana kallon Mahaifinsa, Zainab kam mutuwar tsaye tai a gurin ganin ita ta ci be mata komai ba, amman ga Fadime rike da makoshi wasu yawu masu yauki na mata zuba kamar kubewa sai kuka take tana wani irin tari, tana yagar wuyanta da yatsun hannunta. Murmushin jindadi ne ya fadada kansa a fuskar Liya tana kallon yadda Fadime ke tari tana susar wuya cike da shauki.
鈥淓rrugabea da, nire errua da ez dakiela ezer, tira egin nion鈥�
鈥淏ata da laifi, laifina ne bata san komai ba, ni na janyo ta鈥�
Ya fada yana ta kokarin tare Fadime daga kallon da Sarkin ke mata. Hakan da yai kadai ya isa ya karantar da Sarkin cewar son ta yake.
鈥淲ASIM...!鈥�
sarkin ya fada yana gyada kai a hankali tare da kara hade rai kamar bakin hadari, Fadime kam faduwa tai a gurin hankalinta na kokarin bacewa saboda kai kayin bala'i da take ji a makoshinta, Wasim ya duka da sauri ya rike ta. Zainab na tsaye a gurin tana shafa wuyanta ba dan tana jin komai ba sai dan tambayoyin da take da su.
NANA POV.
Wani irin murmushi take tana kallon kanta a madubi, ita kanta ta san ta yi kyau matuka red gown din dake jikinta ta haskata, daman can Nana ba mace ce mai son doguwar kwaliya ba, hoda ce kawai a fuskarta sai jan baki data shafa. Mikewa tai tsaye ta dauki purse dinta ta saka takalminta sannan ta nufi kofa tana takawa kamar wata Amarya. Ko da ta fito babu kowa a falon Ammy hakan kuma ba karamin dadi yai mata ba, sai ta nisa ta hanyar da Ammy take hana ta fita, da sauri sauri ta rika tafiyar gudun kar ta hadu da Ammy ta hana ta zuwa budan kan. Tana isa cikin fadar Ammy ta bude kofar ta baya ta fita. Daidai kofar AA ya faka motar, daman tun 7:40pm ya iso ya aika wata Hadima ta fada mata ya iso sai ta umarce hadimar ta fada masa ya dawo ta kofar fadar Ammy. AA na ganin Nana ya fito daga motar yai tsaye yana kallonta, gaba daya ta sake ta masa mugun kyau kamar ba ita ba, abun ka da marar jiki sai sigar ta kama jikinta kamar wata yar tsana. Ita kanta kallonsa take domin yayi kyau fiye da kullum ba zaka ganshi ka ce direba ba ne dan masu kasa haka ya fito. Murmushi ta sakar masa ganin yadda yake kallonta, sai shi ma ya mayar mata da murmushin ya bude mata gidan baya, saukowa tai a hankali ta shiga motar sai ya rufe ya bude mazaunin direba ya shiga ya zauna, sai ya samu kansa da rashin natsuwa har sai da ya juyo ya kalleta, be taba ganinta da kwaliya ba sai a yau, ashe haka take da kyau? Ya raya a zuciyarsa.
鈥淜in yi kyau鈥�
Ya furta a fili yana jin wani irin girmanta na kama shi, duk sai yaji ta zame masa kamar ba ita ba ya ji nauyinta na sauko masa.
鈥淣a gode kai ma ai ka yi kyau鈥�
鈥淭hank Youu, ina zamu je?鈥�
鈥淴&L Hotel鈥�
Ya juya yana shakar kamshin turarenta daya cika motar ya bata da na shi karamin turaren. Madubin motar ya saita ya juya ta inda zai rika ganin fuskarta sannan ya kunna wutar motar ya kunna ac. A hankali yake ta tuka motar yana satar kallon Nana ta madubin motar, a duk lokacin da suka hada ido sai ta saka masa murmushi. Daga ita har har shi babu wanda yai wata magana har suka isa.
X&L Hotel babbar Hotel ce a garin Yola, wanda manyan mutane suke zuwa yin taro ko biki ko sauka idan ta kama, ko kuma shakawatawa.
A harabar Hotel din ya faka motarsa sannan ya fito ya bude mata ta fito.
鈥淶aka shiga ciki?鈥�
鈥淎na bari a gashi?鈥�
鈥淵es zan ce kai bodyguard dina ne鈥�
鈥淥kay鈥�
Ya rufe motar yana jindadi, daman can ya dade yana son ya shiga gurin domin ya dade yana jin labarin Hotel din sai dai be taba zuwa. A maimako tai gaba ya bi bayanta sai ta tsaya ta jera tare da shi, yadda ya ci ado ita ma ta ci sai abun ya bada kala kamar saurayi da budurwa, a tare suka doshi wata karamar hanya da aka kawata kamin su karasa wani saurayi ya kira sunan Nana, da sunan da Zainab take kiranta da shi.
鈥淏aby鈥�
Nana ta juyo tana arba da saurayin ta washe hakora ta doshi inda yake, AA kuma ya tsaya a gurin yana kallonsu, side hug tai masa suka gaisa.
鈥淗ow are you?鈥�
鈥淚'm fine, kai ma ka zo biki鈥�
鈥淵eah friend din mu ne zai yi aure, amman mu ba ciki zamu shiga ba, waya kawo ki Sirleem?鈥�
Juyawa tai ta kalli AA a ganin be cancanta ta kira direbanta ba a yadda ya ci gayun nan.
鈥淣o wani ne鈥�
鈥淥kay sai mun hadu ciki鈥�
Ya fada yana sannan ya nufi hanyar shiga gurin. Ita kuma ta juyo ta dawo gurin AA.
鈥淢u tafi鈥�
鈥淏a zamu je din ba鈥�
Ya fada yana watsa mata harara.
鈥淢e akai?鈥�
鈥淵a zaki rumgume wani kato da ba muharramin ki ba鈥�
鈥淭o ai cousin dina ne鈥�
鈥淏a cousin ba kwarkwata, bari na sake ganin kin rika hannun wani sai na fasa miki kai鈥�
Ya karasa da kwafa ita kuma ta turo baki.
鈥淭o Wallahi zan ma koreka daga aikin鈥�
Ya kwaikwayi muryarta yana yatsina fuska.
鈥淭o Wallahi zan ma koreka daga aikin鈥�
鈥淜uma karka bi ni ciki, ba zan shiga ba鈥�
鈥淲allahi sai na biki, sai na shiga, kuma muna shiga ciki kika ga wani kika masa magana sai na bata miki rai鈥�
Ya fada with serious face, yana kara hade mata rai kamar irin shi ne boss ita take aiki karkashinsa. Tana yin gana ya bi bayanta sai ta juyo tana turo baki.
鈥淜a daina bina鈥�
鈥淪ai na biki kuma ki kaiwa wani namiji magana sai na bata miki rai鈥�
Wani irin abu taji kamar ta saka kuka, sai kuma ta juya ta cigaba da tafiya yana binta bayanta har suka isa gurin. Bata nuna gate pass din ba sai kawai ta fada masa sunanta.
鈥淣ana Aisha Abdallah Jari鈥�
Da sauri ya bude mata kofar ta wuce AA ya bi bayanta yana fadin shi bodyguard dinta ne. Kato dakin taro ne da aka kawata da ado na zamani ga haske ko'ina kamar rana, mutane ta ko'ina kana ganin bikin kasan na manyan mutane ne. Kusa da kofar AA ya tsaya Nana kuma ta fara raba ido tana kallon mutane, ta nan ta hango Hajiya Babba cikin matan manya sai far'a take ana ta fira, can kuma ta hango kawarta Amal, da sauri ta nufi inda suke Amal din na ganinta ta rumgume ta tana murna kamin ta ja mata kujera ta zauna, duk abun da suke idon AA na kanta ita a tana yi tana satar kallonsa, tana son ta bar kujerar ta koma wata inda take hango wasu friends nata, da zarar ta mike tsaye sai AA ya bata mata fuska na babba da yaro sai ta koma ta zauna tana watsa masa harara tana turo baki. Sai da ya tabbatar ta natsu sannan ya fita daga gurin ya koma cikin motar ya zauna.
Kari aka fara yi ma Amarya wanda hakan yasa su Amal din tashi ita da kawayenta, suka nufi gurin Amaryar aka bar Nana ita kadai, wata kawar Amal din ce mai suna Rukayya ta dawo gurin ta aje handbag dinta ta cire sarkarta ta zinari ta saka a jakar.
鈥淪is dan Allah zan bar jakata a nan ki kula min, sarkar tana damuna ne鈥�
鈥淥kay鈥�
Nana ta amsa duk da bata san ba sai a lokacin. Yarinyar na barin gurin zuciyar Nana ta fara raya mata ta dauki sarkar, hannunta ya soma wani irin kai kayi, wani abu ta soma ji ba dadi, har ta kai hannunta a jakar sai kuma gai saurin cirewa tana kallon jama'ar gurin da ba su kula da ita ba. Dagawa tai daga zaunen da take ta saka hannunta a kasa ta dannenshi amman bata ji ya daina mata kaikayi ba, ba kaikai irin wanda aka saba ji ba kai kai yi a daukar abu wanda take jin a duk lokacin da so satar wa Ammy ko Mai Martaba kudi. Ciro hannun tai tana yarfarwa sannan ta kai cikin jakar ta dauko sarkar mai tsada ta saka a purse dinta ta mike tsaye da sauri ta fice daga gurin.
Sai da ta fito daga gurin sai kuma tai tsaye idonta ya cika da hawaye, bata taba abun da ba na Ammy ba sai da yau bata taba sata in public place like this ba sai a yau. Ji take kamar ta koma ta maida kuma tana jin tsoro. Takawa ta fara yi ta nufi gurin motarsu, tana isa ta bude motar ta shiga gidan bayan. AA dake zaune ya juyo ya kalleta.
鈥淎n gama bikin ne?鈥�
鈥淎a鈥�
Ta amsa da muryar kuka, jin hakan yasa ya juyo da kyau ya kunna wutar motar yana kallonta, sai hawaye ya gani a fuskarta.
鈥淵a akai?鈥�
鈥淲ani abu nai鈥�
鈥淲ani abu na mi?鈥�
Ta yi shiru sai kuma ta ce.
鈥淪ata nai na saci sakar wata kawar kawata鈥�
Ba shiri AA ya zaro ido.
鈥淪ata kuma?鈥�
鈥淓h ai be kamata nai sata ba ko?鈥�
鈥淭hen why kika yi?鈥�
鈥淚 don't know i just feel like ina son nai, amman be kamata nai ba, kuma na san akwai camera a gurin zata nuna ni, kuma yarinyar ni ta bawa ajiyar jakarta鈥�
鈥淣ana me zai saka ki yi sata? Why, be kamata ace kina sata ba Nana baki bata sunan gidanku da mahaifinki, mi kika rasa ma da zaki yi sata? Why?鈥�
鈥淏an sani ba, haka nan kawai nake yi鈥�
Ta amsa shi tana kuka, wani tunanin ne ya zo masa kar dai ace kudin da take kashewa sato su take?
鈥淚na sarkar?鈥�
Ta bude purse din ta dauko ta mika masa.
鈥淕ashi鈥�
Ya mika hannu ya karba.
鈥淎kwai gate pass ne鈥�
鈥淓h鈥�
Ta ciro ta mika masa, sai ya karba.
鈥淜i koma ciki ki dauki wayarki sai ki samu gurin da babu mutane sosai ki kara wayar a kunne kamar kina waya, idan tai magana ki ce kin bar jakar ne kin je ki yi waya, zan shigo yanzu鈥�
鈥淎mman bani da waya Baba Waziri ya karbe鈥�
Ya kika mata wayarsa.
鈥淩ike wannan鈥�
Ta Karba sannan ta bude motar ta fita ta nufi gurin tana share hawayenta gabanta sai faduwa yake. Da kallo ya bita har ta shige sannan ya sauke ajiyar zuciya yana jin wani iri a ransa.
鈥淪o. That's mean kudin da take bani satarsu take yi? What's wrong with her?鈥�
Ya furta yana ganin rashin dacewar hakan, sannan ya bude motar ya fita ta doshi guri.
FALMATA POV.
Tara da yan mintuna yaran su kai bachi amman tana zaune a dakin domin cika umarnin Shattima da jekadiya ta fada mata sai 10 zata tafi gida, ko kadan bata jidadin hakan ba, sai dai bata isa tai musa ba balle ta tsaba, ta sani suna mata haka ne saboda kawai bata da galihu, saboda tana aiki karkashinsu. Wannan abun kadai ya isa yasa ta kara kaunar Sirleem a ranta, ko ba komai ya tausaya mata, ya nuna mata kulawa kuma ya taimaketa. Sai da goma tai sannan Jekadiya ta shigo dakin.
鈥淶a ki iya tafiya yanzu, direba na waje yana jiranki, daga gobe har kullum zai rika zuwa daukoki misalin 7am鈥�
鈥淭au na gode鈥�
Ta fada tana risinawa sannan ta mike tsaye ta fice daga dakin. A natse ta shigo falon Ammy, al'adar ta ce indai akwai mutane a falon ba zata fice ba sai ta taje ta gaishesu. Hakan yasa ta karasa gaban Ammy ta kwashi gaisuwa sannan ta risina gaban Yarima ta mika masa gaisuwa. Kara ma Ammy ta amsa shi kam ban da kallonta komai be yi ba, babu alamar amsar a tare da shi. Mikewa tai tsaye ta nufi kofar fita, fitarta da kamar minti daya ya mike tsaye ya nufi backyard din falon Ammy, tsaye a gurin yana kallon yadda ta nufi motar, da kuma Sirleem daya fito daga bangarensu ya doso inda take.
鈥淚na wuni, Malam dan Allah kai ne aka ce zaka kai ni gida?鈥�
Falmata ta tambaya tana leken Baba Adamu dake gaban motar.
鈥淓h ni ne鈥�
Ya amsa mata, sai ta matsar da kunnenta kusa da shi.
鈥淒an Allah sake fada bana ji sosai鈥�
鈥淓h ni ne鈥�
Ya fada da karfi.
鈥淭au na gode鈥�
Ta mike tsaye tana jin alamar mutum a bayanta, da sauri ta juyo sai tai arba da Sirleem.
鈥淕ida zaki je?鈥�
Ya rada mata a kunne yana murmushi.
鈥淓h wannan zai kai ni gida鈥�
鈥淚na maganinki yake?鈥�
鈥淕ashi鈥�
Ta fada tana kokarin fiddo da hannunta cikin hijabin, bata karasa ba ya kai hannunsa cikin hijabin ya karbi maganin ya dora saman motar yana amsa gaisuwa da Baba Adamu ke masa, sai da ya fitar da maganin na digawa sannan ya rika fuskarta ya ja hijabinta baya ya fito da kunnuwanta ya kwantar da kanta ya diga mata maganin a kunne daya, ya saka mata kada sannan ya sake digawa a dayan kunne ya saka mata kada kana na rufe maganin.
鈥淜arki yi wasa ki rika amfani da shi kullum, ta fada min magani ne mai tsada ta siya miki鈥�
鈥淚nshallah, na gode Allah ya saka da alheri鈥�
鈥淣ever mind鈥�
Ya fada yana fadada fuskarsa da murmushi sannan ya bude mata bayan motar, ta shiga ya rufe ya daga mata hannu, ita kuma ta juyo tana kallonsa ta bayan motar har suka fita daga harabar sannan ta juyo ta zauna daidai tana jin wani irin abu a zuciyarta mai wuyar fassara, abun da bata taba ji ba sai a yau, abun da ba zata iya fadar ga kalarsa ba balle yanayinsa, idanuwanta ne suka cika da kwalla sai ta rumgume hannayenta ta lumshe ido.
**
Sai da suka wuce sannan Shattima ya bar backyard din ya dawo cikin falon ya zauna kusa da Ammy.
鈥淣i kam sai nake ganin kamar Sirleem ba son Nana yake ba鈥�
Ammy ta kalleshi.
鈥淜amar ya?鈥�
Ya daga kafadunsa, alamar haka nan dai.
鈥淚dan baya son ta ai ba zai nuna ba, tun da ba dole aka masa ba, ya dai rage kula ta ne kamar baya, saboda kun saka masa ido鈥�
Be sake cewa komai ya ciro wayarsa dake aljihu, ganin Number Baba Waziri yasa ya mike tsaye ya fice daga falon. Kasa ya dauko gaba daya sannan聽 ya kara wayar a kunnesa da sallama. Bayan sun gaisa Baba Waziri ya ce.
鈥淏an jika ba, tun da muka yi magana, idan Maijidda bata maka ka fada min wanda kake so, ba abu ne da zai dauki lokaci ba balle nai ta jiranka鈥�
Shattima yayi shiru kamar ba Waziri ne a wayar ba, can kuma ya sauke ajiyar zuciya silently ya ce.
鈥淚na sonta Baba, amman dan Allah a tambaye ta idan ita ma tana so na, kar a mata dole鈥�
鈥淢ashallah, Allah ya hada kanku ya fada zaman lafiya sai ka fara shirye-shirye tun yanzu鈥�
鈥淣a gode Baba鈥�
Ya furta sannan ya sauke wayar tare da sauke wani dogon numfashi. Data kunna ya shiga wani side ya siye ticket din jirgin da zai tashi zuwa Katsina a gobe.
**
Shattima na fita falon, Iya ta shigo lullube da zane, tana shigowa ta fadi gaban Ammy tana zuba mata kirari bakin nan cike da goro, sai da ta kalli ko'ina a falon ta ga Jekadiya ce kadai a falon sai Ammy sannan ta kara matsawa kusa da Ammy tana wasar hakora.
鈥淩anki ya dade, ina da magana鈥�
Da gangan Ammy ta ki kallonta ba dan wulakanci ba sai dan nuna isa, daman can Allah ba hada jinin Ammy da Iya聽 saboda Iya ta fiye shiga hanci da kuddudumi ga salo irin na tsofin mayu, Ammy kuma bata son haka.
鈥淭au ina jinki鈥�
Ta kalli Jekadiya tana dariya, kamin ta sake kallon Ammy.
鈥淒aman wata yar shawara ce na zo da ita鈥�
Sai kuma tai shiru kamar mai tsoron fada. Ganin hakan yasa jekadiya ta ce.
鈥淚ya ki bude baki ki yi magana, Ammy na saurarenki鈥�
Iya ta juyo gurin Jekadiya tana yar dariya kamar ta kunya.
鈥淒aman na ce wai akan Babban Mutum ne, na ce mi zai sa sai an tafi nesa鈥�
Ammy ta kalleta domin ta fahimci inda zancenta ya dosa tun kamin ta karasa, Jekadiya kuma gabanta ya fadi duk da ta san ba wai ta fada ne ta siffar gulma sai dai ta san Ammy ba zata jidadi ba ta fada mata abu kuma aji shi gurin wani.
鈥淲annan lauye lauyen da kike ba zai fitar da ke ba, da kin fito kin fadi maganarki a fili da Ammy ta fahimta鈥�
Iya ta shafa zanenta tana murmushi.
鈥淒aman cewa nai me zai hana a hada Babban Mutum da yar'uwarsa? Ai ba sai an je can nesa ba an dauko bare tun da ga abu a ciki gidan鈥�
Jekadiya makis tai a gurin kamar an kama munafuki, ta rasa abun cewa. Ammy ta juyo da kyau tana kallon Iya.
鈥淓h lallai haka, jindadi yayi muku yawa ke da yarki, har hauka take raya muku wannan, shine dalilin shigewa Shattima da Zainab take? To ai kalar zaren ba kalar yadin ba ne, kuma lalacewar takalmin sarki yafi karfin sakawa kafar bafade, Maijidda ce bare? Yar waziri ce nesa? Gata da sakin fuskar da ake muku a gidan nan ya muku yawa shiyasa har raini ya shiga ciki, har kike iya duban idona ki fada min wannan maganar, Iya wai ko kin manta waye ke?鈥�
鈥淎a ina ya zan manta... A gafarce ni Hajiya salo na ne... Amin afuwa鈥�
Iya ta fada da dariyar kunya, zuciyarta tab da tsanar Ammy sai kallon kurwarta take.
鈥淭o daga yau sai yau, ba ke ba ko Zainab kar na sake ganin kafarta a falon nan, idan kina bukatar wani abu ko yin wani abu ki nemi iso karki sake shigo min falo, idan kika yi wasa ba a masarautar ba a yola gaba daya ma sai na canja miki zama鈥�
鈥淭o Ammy ba za a kara ba ayi min afuwa a gafarta min鈥�
Ta farasa tana fashewa da kuka, ta mike tsaye rumgume da kunyarta ta fice daga falon, tana kuka kamar gaske.
Ammy ta kalli Jekadiya da duba na mamaki.
鈥淜in ba ni mamaki, ban yi zaton haka ba, amincewa da ke kuma farinciki abun da Waziri yai yasa na labarta miki taya zaki dauki sirri ki baza a kunne Iya?鈥�
Jekadiya ta rasa inda zata saka kanta, a take ta hau rantsuwa, tana labartawa Ammy yadda akai ta Iya ta ji.
鈥淲allahi ranki ya dade ban yi hakan da nufin labarta mata komai ba, a gafarce ni, ni kaina murna ne yasa na fadi haka, ban yi zaton zata kawo wannan tunanin ba, Wallahi ba halina ba ne鈥�
Ammy bata sake ce mata komai ba ta mike tsaye a fuce ta shige dakinta cikin mamakin yadda Iya ta iya karfin halin wannan tunanin, har ma ta iya furtawa.
***
Iya na shiga dakinta ta maida kofar dakin ta rufe.
鈥淚dan ba yi da lala ba ayi da tsiya, tsaya mu gani ida ita ma Maijidda ta mutu sai wacce kuma? Wata rana da kanki za ki zo kina rokon na taya ki nemawa Shattima auren Zainab, ita kadai ce matarsa kuma da ita kadai zata haifa masa yaya, daga lokacin ne komai zai dawo na mu, ke kanki Ammy sai kin zama abar tausayi...鈥�
Ta fada cikin wani irin zafin rai na jin zafin abun da Ammy tai mata.
鈥淭ana jin kanta matar nan kamar ita ce sarkin, ke kuma bari na gani zaki taya ni yake ko kuma ta gawa za ki yi鈥�
Ta karasa tana janyo wasu sabbin tufafin a cikin wardrobe dinta, atamfa mai kyau da tsada ya janyo ta dora saman gado domin bata son gobe ta tsaya jiran komai.
Haka ta kwana cikin bacin rai da sakesake kalakala a ranta, kamin garin Allah ya waye duk ta matsu, karfe tara ta shirya cikin atamfar data ciro jiya, ta dauki turare ta fesa sannan ta dauki jakar kudinta da makullin dakin ta fito, ta rufe dakin ta nufi kofar fita sai gaisawa take da hadimai kamar ta Allah, kowa sai bata girma yake har ta isa gate din. Sai da ta fita daga unguwar gaba daya sannan ta samu Napep ta shiga tana fadin.
鈥淢alam Unguwar Waziri鈥�
Ta shiga ta zauna har tana kwafa.
_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number聽 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
03/12/2021, 18:51 - 馃馃馃馃: 31
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence via 08036126660*
AA POV.
Yana isa gurin ya nuna musu gate pass din sai suka bude masa kofar ya shiga, a inda ya san Nana ta zauna dazun ya kalla sai ya hango babu Nana a gurin ba kuma kowa a har jakar da take fada babu, a take zuciyarsa ta raya masa yarinyar ta dauki jakarta ko kuma wata ta sata, kai tsaye ya nufi gurin yana ta rabon ido ko zai hango Nana. Gaban teburin ya tsaya yana ta sake sake a ransa, be san yarinyar ba haka kuma be san inda zai sameta ba, wata zuciyar na raya masa ya aje sarkar a kasa yai tafiyarsa, sai dai kuma be zama lallai ta gani ba wani zai iya gani ya dauka, hakan kuma ba zai wanke Nana daga zargi ba, ba kuma zai hana idan an bincike CCTV ta gurin ta nunata ba. Be raba dayan biyu ba, wata budurwar da ba zata wuce sa'ar Nana ba ta doso teburin tare da Amal, hankalinta a tashen.
鈥淭o wai ina kika aje jakar?鈥�
Amal din ta tambaya tana duba gurin, sai yarinyar ta amsa mata kamar ta fasa kuka.
鈥淲annan kawarki na bawa na ce ta rike min, ina gama karin kudin na dawo na ga jaka a bude ba sarka kuma ita yarinyar bata nan鈥�
Jin hakan yasa AA ya dan matsa kusa da su.
鈥淢alama ke kika jefar da sarka a nan?鈥�
Daga Amal har yarinyar dagowa sukai suka kalleshi, kamin su kalli Sarkar da yake nuna musu, yarinyar ta kai hannu da sauri ta karba.
鈥淲allahi ba jefarwa nai ba, sai dai idan sata kai baka samu damar fita da shi ba ka maido鈥�
鈥淣o a kasa na ganta, na dauka sai na rasa wa zan bawa鈥�
AA ya fada da sauri yana kokarin kare kansa, Amal ta masa wani kallon rashin yarda.
鈥淭o me ya kawo nan bangaren mata ma? Kuma har ka ga sarka a kasa?鈥�
鈥淏elieve me ban dauka sarkar nan ba鈥�
Bata ko saurareshi ba ta nufi wajen securities din da suke kofar shigowa, AA ya ganin ta nuna inda yake yaji yawun bakinsa sun kafe, gabansa yai mugun faduwa, domin ba a taba zarginsa da sata ba, domin be tana daukar abun wani ba duk kuwa da kasancewar yana da son abun duniya. Tare da Amal din securitin suka zo suna zuwa ba su tsaya komai ba sauka yi ma AA wani irin mugun riko. Hango hakan da Nana tai yasa ta dawo gurin da saurin, daman can gefe a tsaye ta kara waya a kunne kamar yadda AA ya fada mata ta yi, tsaye tai a gurin rike da wayar tana kallon AA.
鈥淏an dauka ba, a kasa na ganta Malam karka cikin mutunci a nan鈥�
AA na rufe baki Yarinyar ta soma karyata shi.
鈥淲allahi karya yake sarkata a jakata na sakata鈥�
Take police din ya tsinka masa mari ya fisgi rigarsa suka turashi gaba, abun ka da abu a bainar jama'a sai mutane suka sako musu na mujiya, kallo ya dawo kansu. Mutuwar tsaye Nana tai ta rasa abun da zata yi idonta ya cika da kwalla ganin an tisa keyar AA gaba da sunan satar da ita ta aikata, gashi tun a gurin sun fara dukanshi, ta kasa cewa komai Amal kuwa sai kokarin labarta mata abun da ya faru take.
鈥淜in je can gurin waya kin bar jakar Rukayya ashe washe wannan mutumen ya hango sai zuwa yai ya daci sarkarta, mun kama shi sai fadin yake wai tsintarta yai a kasa鈥�
Nana ta kasa cewa sai kallon AA take har aka fice da shi daga dakin taron, kamar a sama Hajiya Babba ta dafa Nana domin sai a lokacin ta lura da ita, sai dai ita Nana ta lura da Hajiya tun farkon shigowarta.
鈥淒aughter lafiya dai?鈥�
Rukayya ce labarta mata abun da ya faru, domin har lokacin Nana gani take kamar a mafarki ne komai ya faru.
鈥淭o sai ku yi hankali kuna sake jiki a ko'ina kuma kun san akwai inda ba mutanen arziki musamman irin wannan gurin鈥�
Cewar Hajiya Babba kamin ta kama hannun Nana kamar gaske.
鈥淶o mu zauna a can鈥�
Binta Nana tai kamar bawa da ubangidansa ta nufi inda Hajiya take ta zauna kusa da ita, kamar wacce bata cikin hayyacinta haka ta rika gaisawa da manyan matan da suke tambayarta ina Ammy, wasu abokan Ammy ne wasu kuma na Hajiya Babba, hannunta na rike da wayar AA sai shafa waya take a hankali. Bata taba sanin wani abu mai suna tashin hankali ba sai a yau, bata taba jin nadama a aikata wani abu ba kamar wannan, he is innocent right? Ita tai causing komai, kuma ya karbe ta ba tona mata asiri ba ya dauki laifin a kansa bayan ya san ba shi ya aikata ba. Bata san lokacin data mike tsaye ba, zata fara tafiya sai Hajiya ta rikota daman haka take nuna mata son munafurci har take ganin kamar ta fi son ta da Ammy.
鈥淒aughter tafiya zaki yi?鈥�
Nana ta kalli Hajiya idonta tab da hawaye, ta yi shiru sai kuma ta tuna Hajiya mai share mata hawayenta ne a koda yaushe.
鈥淗ajiya ina son magana da ke鈥�
Hajiya ta mike tsaye tana kai bakinta saitin kunne ta Nana a zatonta maganar ta baki da baki ce kawai, sai Nana taja hannunta suka fita daga gurin, sai da suka isa gurin da AA ya faka motarsu sannan ta sake hannun Hajiya ta sunkuyar da kai kasa.
鈥淟afiya dai daughter fada min matsalarki鈥�
Nana ta kalleta tana fashewa da kuka.
鈥淗ajiya wanda aka ce ya saci sarkar nan ba shi ya sace ta ba鈥�
鈥淏an gane ba鈥�
Cewar Hajiya tana kallon Nana da mamaki, zuciyarta na cika fal da farinciki jin furuncin Nana ta san wata kila zata fadi cewar ita ta saci sarkar wanda shi zai fi komai yi mata dadi a yanzu, saboda Ammy za a zaga ita kuma yabe ta na ganin tana son hada auren Nana da danta.
鈥淣i na sata.... Amman ban san miyasa n sata ba...ban san mi zan yi da sarkar ba...鈥�
Hajiya ta kamo hannunta.
鈥淭o ya akai yace shi ne?鈥�
鈥淵a fanshe ni ne, amman ba shi ya dauka ba, ni na dauka Hajiya ki taimaka masa kar a masa komai dan Allah, Wallahi Sardauna ba barawo ba ne na yarda da shi鈥�
Hajiya ta ji wani abu ya sauko mata tun daga saman kanta har cikin kafafuwanta.
鈥淜e wa kika ce?鈥�
鈥淪ardauna鈥�
Nana ta maimaita tana kuka sosai, domin wata kalar nadama ce ke rabarta.
鈥淜e sake fadi na ji鈥�
Hajiya ta sake tambaya baki saki.
鈥淪ardauna, Hajiya Wallahi ba barawo ba ne, dan Allah ki taimaka masa kar su masa komai saboda da ni鈥�
A take kallo ya koma sama, sai murnar Hajiya ta koma ciki, wani kalar fever ta ji yana sauko mata.
鈥淪aurayinki ne?鈥�
鈥淎a shine sabon direbana鈥�
Nana ta fada har muryarta a shakewa, jikinta sai bari yake irin na wanda kuka yake cinta sosai. A take Hajiya ta saka salati.
鈥淟a'ilaha illala muhammadu rasulullah sallalahu alaihi wassalam, ki ce ni na siya da kudina鈥�
Nana bata kula zancen ba balle har ta gane inda ta dosa, wani irin dogon numfashi Hajiya ta ja ta sauke tana kara nanata sunan.
鈥淪ardauna...鈥�
Jin hakan yasa Nana ta rike hannayenta.
鈥淗ajiya dan Allah ki taimaka kar a masa komai鈥�
Hajiya ta jata jikinta ta rumgume tana rarrashinta kamar gaske.
鈥淒aina kuka yanzu zan kira Babanki Jarma na fada masa ya binka inda aka kai shi鈥�
Tana fadin hakan ta saki Nana ta nufi gurin motarta, Nana ta bi bayanta da sauri. Direban Hajiya na hangota ya fito cikin motar ya bude mata gidan baya, kamar daman abun da take jira kenan tana isa ta shiga gidan baya ita da Nana shi kuma ya tashi motar. Nana ta kwanto jikin Hajiya hawaye a sauko mata, can kuma ta dago hannunta tana ta kallon tafin hannun ita kanta bata dauka bayan Ammy da Mai Martaba da take yi ma sata ba zata iya yin wata a public place like this, kuma sarka. Ta jimke hannun wasu hawayen a sauko mata. Ganin hakan yasa Hajiya ta ciro wayarta a jaka ta nemo number Jarma, sai da wayar ta dade tana ringing sannan ya daga.
鈥淗ello Jarma鈥�
鈥淗ajiya barka da dare鈥�
鈥淒an Allah yar wata muka samu, wani yaro ne yai sata a gurin bikin da muka zo na yar Faro Ambassador, shine police suka tafi da shi, to ina son ka saka a binciko mana wane police station aka kai shi鈥�
鈥淭o yayi, amman kin yaron ne?鈥�
Hajiya kamar tana jira ta amsa da karfi.
鈥淓h sunanshi Sardauna, shine sabon direban Nana鈥�
Daga dayan bangaren Jarma ya amsa da kuzarinsa.
鈥淪ardauna fa kika ce Hajiya?鈥�
鈥淓h a taimakawa daughter na kar ta shiga damuwa, gani tare da ita, zan kira ka anjima鈥�
Bata jira abun da zai ce ba ta kashe wayar tare da kai hannunta ta taba Nana.
鈥淜i daina kuka ai komai zai zo da sauki tun da na fadawa Jarma鈥�
Nana ta rumgume Hajiya tana jin wani irin son ta a ranta, domin ta tabbatar da Ammy ce ba zata mata haka ba. Apartment din Hajiya direban ya faka motar, sai Hajiya ta fito rike da hannun Nana ta nufi cikin gidan da ita, har cikin dakinta ta kai ta kwantar.
鈥淜wanta a nan ki huta鈥�
Ba musu Nana ta kwanta a gurin, Hajiya kuma ta karasa ciki ta aje jakarta ta fice daga dakin rike da wayarta. Tashi Nana tai zaune ta kunna Power button din wayar sai ta samu wayar a pattern da katon hoton AA a din daya cika screen din wayar, wani irin tausayinsa ne ya kara sauka a ranta, ji tai kamar bata da natsuwa idan bata san halin da AA yake ciki ba, hakan yasa ta mike tsaye ta bi bayan Hajiya.
Hajiya ta na fitowa daga dakin, ta shiga second room dinta ta rufe ta kira number Jarma, wannan karon bugu daya ya dauka.
鈥淛arma鈥�
鈥淗ajiya鈥�
鈥淛arma a nemo inda yaron nan yake, maganar bokan ta tabbata sunanshi Sardauna鈥�
鈥淗ajiya ai ni abun ya bani mamaki, ace har kin san shi鈥�
鈥淣i ma sai yanzu nake saninsa, amman ni na siye macijin da hannuna, domin ni na dauke shi aiki ba tare da sani ba, kuma ba tare da na yi bincike ba, ina cikin tashin hankali Jarma ka nemo yaron nan鈥�
鈥淒ole zan saka a nemo shi ai, ba ke dai ce a matsala ba har da ni鈥�
Jarma ya amsa daga dayan bangare.
鈥淜uma idan an samo shi, ka fada min da wuri, a juyar da case dinsa daga sata zuwa kisan kai, a tura shi gidan kaso, ko nawa ake ashewa zan kashe, ka shigo da safe zamu yi, domin dole ne mu koma gurin mutanen nan kar abubuwan su kara mana yawa, ina murna Nana ta fara dan hali sai kuma abu ya juye min haka鈥�
鈥淕askiya kam ya kamata mu koma garin nan daga can ma sai su sanar da mu wacece Fadime ita ma kar ta ribance mu鈥�
鈥淗aka ya kamata, muna ta sanyin jiki abubuwa suna faruwa da mu, ya kamata mu yi maganin komai tun a yanzu鈥�
鈥淲ai daman Nana ta fara dan hali Hajiya鈥�
鈥淗mm Jarma kenan, ai har abunda ya fi sata sai Nana ta yi, ba ni da buri sai na ganin kukan Ammy kuma sai ta yi shi indai ina raye, yanzu dai ka nemo yaron kuma ka san wanda aka hannatawa case din, gobe ka zo ka karbi kudi ayi komai tun da wuri, abun ai ya zo mana da sauki tun da har haka ta faru鈥�
鈥淪hikenan Hajiya zan shigo gobe inshallah鈥�
鈥淵ayi kyau sai anjima鈥�
Ta fada tana sauke wayar, tare da sauke wata doguwar ajiyar zuciya.
鈥淒ole ne na shirya jibi nai tafiyar nan, idan ba haka ba ban san me zai sake faruwa ba, ya kamata na tari Fadimen ita kuma tun kamin ta tare ni鈥�
Line Hajiya Talatu ta nemo ta aika mata kira, ringing daya ta dauka kamar daman can jiran kiran take.
鈥淗ello Talatu鈥�
鈥淗ajiya ina cikin tashin hankali, Waziri ya dage sai ya hada auren nan鈥�
Ta amsa da muryar kuka wanda hakan ke nuna ta ci kukan har ta gode Allah.
鈥淣ima ina cikin nawa tashin hankali, amman dai ki shigo gobe sai mu yi magana, be kamata mu kyale yarinya akaita ga halaka ba鈥�
鈥淪hiyasa nake son tun wuri mu tafi garin nan tun da aikinsu kamar yankan wuka ne, su wargaza komai tun abu be yi nisa ba鈥�
鈥淗mm ke dai ki shigo gobe kawai鈥�
鈥淭au Allah ya kai鈥�
Hajiya ta sauke wayar tana jijjina lamarin bokayen nan sai yanzu ta kara tabbatar ba da wasa suke aiki ba, kuma dama ta dade tana son irinsu masu aiki kamar yankan wuka. A yanzu ne take jin ya zame mata dole ta je garin ko dan maganin matsalolinta.
**
Shirun da Nana ta ji ne ya tabbatar mata da Hajiya ta gama wayar da take, sai ta daga daga jikin kofar wasu sabbin hawaye masu zafi na sauko mata. Why Hajiya zata juyar da case din to kisan kai bayan tace zata taimake ta? Mi Sardauna yai mata? Anya ya cancanci haka? Da sauri ta ta bar kofar ta dauki hanyar da zata sadata da part dinsu hawaye na sauko mata kamar ba gobe, daman ta bi bayan Hajiya ne da zimmar ta sake rokonta sai ta tararda kofar dakin a rufe tana kokarin turawa ta ji sautin muryarta na tashi kadan-kadan hakan yasa ta kai kunnenta domin ta ji abun da Hajiya take fada, domin azatonta zata ji ko Jarma ya gano inda suke ne ko kuma wani abu sai gashi ta ji mummunan abu da bata taba mafarkin ji ba, kuma ba tai zato daga Hajiya ba.
鈥淢iyasa ma nai satar to? Why?鈥�
Ta tambaya cikin kuka tana jin haushin kanta. Ganin bata da mai taimakonta a yanzu wanda zai fito da Sardauna, bata isa ta tunkari Ammy da wannan maganar ba, daman daga Hajiya sai Zainab ne suke mata gata a gidan, sai kuma Shattima, sai dai ba zata iya fada masa ba, gudun kar Ammy taji ko Baba Waziri. Silently ta isa bangarensu ta shige dakinta ba tare da kowa ya sani ba. Maida kofar dakin tai ta rufe ta jingina da kofar ta fashe da sabon kuka tana kallon hoton AA dake gaban wayarsa. Haka ta shafe awa uku zaune a gurin tana aikin kuka abun da bata taba ba, idanuwanta da fuskarta suka kumbura, tun tana jin kuzarin kuka har ta nemi kuzarin ta rasa. Can ta mike tsaye ta cire tufafin jikinta ta dauki tufafin bachi ta saka ta shiga bandaki ta wanke fuskarta, sannan ta fito ta hau saman gadon ta kwanta ba dan tana jin zata iya bachin ba sai dan jin jikinta da take da rashin kwari. Misalin 10 da yan mintuna kiran Anti Rabi ya shigo wayar AA dake hannun Nana.
Second Mother shine rubuce a wayar dauke ta emoji din heart. Kasa daukar kiran tai sai kawai tai rejecting call din ta kashe wayar gaba daya.
鈥淚nnalillahi鈥�
Ta furta, she can't remember when last ta furta wannan kalmar ma. Bata taba jin ta a tashin hankali irin yau ba, abun da ta ji Hajiya Babba na fada ya fi daga mata hankali fiye da halin data jefa AA. Sauka tai saman gadon ta bude kofar dakinta ta fito falo, babu kowa a falon an kashe kayan kallo wanda hakan ke nuna Ammy tana bangaren Mai Martaba ko kuma tana shirin tafiya ne. Dakinta Nana ta dosa tana taba kofar ta ji ta a bude sai ta tura ta shiga, duk wani tsoron kar Ammy ta ji da take da gudun fadanta ko dukan Baba Waziri sai ta ne meshi ta rasa, bata da buri a yanzu da ya wuce AA ya zama free. Daga bakin kofar ta tsaya tana kallon Ammy dake tsaye jikin wardrobe dinta tana daukar wasu kaya, ta jikin madubin wardrobe Ammy ta hango Nana sai ta juyo tana wani kallo fuska ba yabo ba fallasa.
鈥淵a akai?鈥�
Nana ta kalleta hawaye na sauko mata, sai kuma ta nufi inda take ta karasa har kusa da ita.
鈥淎mmy... 鈥�
Sai kuma tai shiru hawayen na sauko mata.
鈥淎mmy na san ni da ke don't get along, amman dan Allah ki taimaka min鈥�
鈥淢inene?鈥�
鈥淎 gurin bikin da naje dazun na su Amal na saci sarkar gold ta kawar Amal, nasan be dace nai sata ba right? Na sani amman ban san miyasa nai ba, direbana sai ya karbi sarkar yaje ya maida shine suka ce shine ya dauka kuma Wallahi ba shi ba ne ni ce, shine suka kira masa police aka tafi da shi, dan Allah ki taimaka Ammy a fito da shi pls鈥�
Ammy ta saki kayan hannunta sun zube kasa, tana yi ma Nana wani irin kallo kamar na tsoro kamar na mamaki, a take idonta ya cika da kwalla. Tassss ta dauke Nana da wani irin mahaukacin mari, cikin wani irin zafin nama da bata taba sanin tana da shi sai yau.
鈥淪a... Sa... Sa... Sata Nana?鈥�
Ta furta daker hawaye na sauko mata, Nana kam tun da Ammy ta tsinka mata mari tai bata da sauri tana ma Ammy wani kallo tsoro domin ji take kamar babu fuska a jikinta.
鈥淣a san be dace nai ba Ammy na sani....鈥�
Ta furta a rikice tana girgiza ma Ammy kai. Sai kuma ta juya da gudu da fice daga dakin, Ammy ta bita da kallo baki sake, wani abu ta ji yana mata yawo a zuciya yana neman numfashinta, da sauri ta rike murfin wardrobe din ta jingina ta zauna a kasa tana numfashi daker.
鈥淚nnalillahi wa'inna ilaihirraji'un鈥�
Ta furta daker tana ta kokuwa da numfashinta.
FADIME POV.
Hannu biyu Wasim ya saka ya dauki Fadime ya ya nufi kofar fita, zaratan mazajen da suke fadar tsaye suka nufishi sai Sarkin ya daga musu alamar su kyaleshi. Zainab na ganin hakan ta bi bayansu yadda yake tafiya da gudu sai ka dauka biyo shi akai Fadime kam sai tari take hankalinta ya dade da barin jikinta. Duk inda ya nasa kafarsa Zainab sai ta nasa tata, har suka isa wani karamin gida mai dauke da dakuna uku, dakin farko ya shiga wanda shi ya fi ko wane daki girma. Yana shiga ya kwantar da Fadime gaban makahon bokan ya soma magana da shi da yarensu.
鈥淜aka ka taimaka mata ta daina tarin nan kar ta samu matsala鈥�
Bokan ya mika hannunsa ya taba fuskar Fadime.
鈥淲asim miyasa ka aikata haka?鈥�
Wasim be tsaya bashi amsa ba ya nufi inda bokan yake aje magani ya bude ya dauko wani garin magani ya cika hannunsa da shi ya zo ya zuba a bakin Fadime sannan ya dagata ya jinginar da ita jikinsa. Tana yin tarin garin maganin ya bi ta cikin makoshinta sai kaikayin yai kasa, haka ya rika sauka kasa kasa har ya daina mata gaba daya. Wani irin sanyayyiyar ajiyar zuciya ta sauke ta lumshe ido sai bachin wahala. Duk abun da ake Zainab na tsaye kusa da Fadime, yadda yake ta kula da Fadime sai abun ya burgeta duk kuwa da kasancewar rabin hankalinta yana gurin nama da ta ci be mata komai ba. Daukar Fadime yai ya kwantar da ita kan wata shimfida dake dakin, ana dakin bokan kuma kakansa kadai yake da tabbacin zai aje Fadime mahaifinsa ko wani be taba ta, domin be isa ya fitar da ita daga garin ba tare da izinin sarkin ba, gudun kar a cutar da ita daga baya. Hannun Zainab ya riko ya fito da ita daga cikin dakin ya zagaya da ita wani guri mai hudu.
鈥淶an kai ki gida yanzu鈥�
鈥淥kay鈥�
Ta amsa da sauri daman abun da take nema kenan.
鈥淎mman camera tana can mun baro鈥�
鈥淜i tsaya a nan karki je ko'ina鈥�
Ya fada yana yin baya baya, kamin ya fice daga gidan, ko minti uku be yi ba ta hango shi ya dawo rike da jakar tata. Yana isowa ya mika mata jakar.
鈥淩ike ta da kyau ki rufe idonki karki yarda ki bude鈥�
鈥淭au鈥�
Ta rufe idon da sauri, sai ya rika saitin kunkurunta ya kai bakinsa saitin goshinta, yayi hakan ne ssboda kar ta bude idon, domin matukar bakinsa na kan goshinta ba zata iya bude idon ba. Wani irin tsam taji a hikinta, duk yadda ta so ta bude idonta Jin kamar tana kan wani abu sai ta kasa, har sai da ta ji kafafuwanta a kasa, sannan ta bude idon a hankali ta sauke su a fuskar Wasim da hasken fari wata ke haska fuskarsa. Nesa kadan da gidansu Fadime ya sauke ta, ya kai hannunsa jikin walkinsa ya tsinki wani ziri daya ya kama hannunta ya daura mata.
鈥淪haidar kin zo garin mu鈥�
Ta kalli zaren sannan ta kalleshi.
鈥淵arinyar fa?鈥�
鈥淶an kula da ita, ba zai yiyu ta dawo yanzu ba, ki yi tafiyar ki kawai karki bari iyayenta su ganki鈥�
Ta daga masa kai tana binsa da kallo har sai da ta daina hangoshi sannan ta aje jakar ta dauko wayarta ta kunna, number police din ta kira, bata wani dade tana ringing ba ya dauka.
鈥淗ello Hajiya鈥�
鈥淜arka bari mutanen dake tare da kai su san na kiraka, kai musu sallama ka Fada musu tun da ban dawo ba ku za ku wuce, sai ka same ni a gurin karfen sabis鈥�
Ta fada tana daga kanta ta kalli karfen, sannan ta kashe wayar ta fara tafiya da kafa zuwa inda karfen yake, bata karasa ba sakon kar ta kwana wato sms ya shigo wayarta da line Auwal, jiki na rawa ta bude, sai tai arba da mummunan abu.
鈥淎llah yayi ma Auwal Sa'ad rasuwa, idan akwai bashi a tsakaninku ki fada, ko ka fada a sauke nauyi鈥�
Sai da ta karanta sakon sau ba adadi sannan ta yarda hausa take karantawa, bata san lokacin data saki jakar hannunta ba.
鈥淵a Allah........鈥�
Ta furta da karfi tana jin wani irin kuka na taso mata.
鈥淎llah kasa ba gaske ba ne鈥�
Ya shiga neman line Auwal din sai ta ji shi a rufe, ta sake bugawa ta ji shi a rufe, hannu ta dora saman kai hawaye a sauko mata.
鈥淗ow...鈥�
Sai kuma ta shiga neman line matarsa kai tsaye. Bata dade tana ringing ba matar ta dauka.
鈥淎ssalamu Alaikum鈥�
Ba karamin jihadi Zainab tai ba na danne kukanta ta amsawa kawarta.
鈥淲a'alaikissalam, ya gida?鈥�
鈥淟afiya Kalau Zainab, sai kewa da bakinciki鈥�
鈥淒a gaske ne?鈥�
鈥淎i ba a karyar mutuwa, Auwal ya tafi ya bar ni, na shiga liyin zaurawa yayansa kuma sun zama marayu鈥�
Ta karasa cikin kuka. A sanyaye Zainab ta sauke wayar hawaye na bin fuskarka.
鈥淚nnalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un鈥�
Ta kashe wayar ta durkushe a gurin fuskar Auwal nata yi mata gizo, kamar daga sama ta ji wani irin kuka ya sauko mata.
***
Cikin hikima police din suka yi ma Bappa Sallama suka kamo hanya, ya bar su sun tafi ne kawai Saboda ganin su police ne, ba dan haka ba, da ba za su tafi ba yarsa ba ta dawo ba, duk kuwa da kasancewar sun fada masa cewar ita Zainab din tana can wai dare yayi ba za su iya jira ba, idan ta dawo ta kwana a nan da safe za su zo su dauke ta. Suna tafiya Bappa ya koma cikin gida ya rufe Inna da fada ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, Inna kam sai kuka take ga fadan Bappa gashi kuma tashin hankalin rashin ssnin halin da yar gudaliyar yarta take ciki ba, abun sai ya zame mata biyu ta rasa inda zata saka kanta.
_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number聽 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
03/12/2021, 18:51 - 馃馃馃馃: 30.
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence via 08036126660*
FADIME POV.
kamin su karaso ya Wasim ya kalli Fadime ya ce.
鈥淜arki yi magana kuma komai aka baki karki ci鈥�
Ta daga masa kai wasu hawaye masu zafi na sauko mata. Ganin hakan yasa ya kai hannunsa ya rika wuyan hannunta. Mutane na karaso kusa da shi suka risina masa alamar girmamawa.
"Erregeak zure ahoarekin ikusi behar du"
_Sarki na bukatar ganin tare da bakinka_
Be ce komai yaja hannun Fadime ya fita daga cikin runfar, Zainab na ganin haka ta bi bayansu da sauri, mutanen da suka zo kiransa suka rufa masa baya. Ta inda mutane suka fito ya nufa rike da hannun Fadime wanda ta kasa daina hawayen da take. Ta bayan wani guri wanda yafi kama da kasuwa suka bullo, duk inda Wasim ya dora kafarsa sai an risina masa an dauke ido daga barin kallonsa alamar girmamawa da biyaya. Sun yi tafiya mai dan nisa a kafa kamin su isa bakin wata babbar kofa ta itace an mata gate har da masu gadinta. Wasim na isowa gurim kofar aka bude masa suna risinawa har sai da ya wuce sannan suka tashi. Hakan yasa Fadime ta ji wani girma ya kamata, ko ba komai ta ci alfarmar Wasim ita ma an risina mata, a nan ta kara yarda babu wanda ya isa ya taba ba, kimar Wasim da sonsa suka kara ninkuwa a ranta. Shiga cikin gurin yasa daga Zainab har Fadime suka manta da abun da ya kawo su gurin, wata sabuwar duniya ce, kuma babbar daula mai zaman kanta, babu komai a dayan bangare sai katuwar gona mai cike da manyan itace wanda har baka iya hango cikinta saboda hudu, ta gafe daya kuma kana jin kwarar ruwa alamar akwai korama a gurin. An bi ko'ina na harabar an haska shi da wutar ice wanda hakan ya bawa Zainab da Fadime damar ganin irin kwaliyar da aka yi ma gurin da koren ganye mai yanayi da ganyen ayaba. Sai da suka isa gaban wata kofa sannan Wasim ya cire talkaminsa na fata, ya nasa kafarsa a gurin, Zainab da Fadime kan daman ba su shigo garin da talkami ba. Wata katuwar fada ce da aka shimfida mata gashin farar damisa, tun daga bakin kofar har zuwa inda Sarkin yake zaune kan wata kasaitacciyar kujera da zaka iya rantsewa ba itace ne aka saffara ba. Daga hannun kujerar har jikinta an masa kwaliya da farar azurfa. Ginin fadar kuma an masa kwaliya da fatar zaki inda Sarkin zai dora kafarsa da hannunsa ma kan Zaki ne a gurin. Tsirarun mutane ne a cikin fadar ciki har da Liya dake tsaye gefen Sarkin dake hakimce saman kujera fuska babu annuri.
Nan da nan jikin Fadime ya fara rawa, kafafauwanta suka fara lankwashewa kamar wata musaka. Nesa da Sarkin Wasim ya tsaya ya saki hannun Fadime ya risina da kafarsa daya ya dukarda kansa ya kwashi gaisuwa.
鈥淏arka da wannan lokacin Shugaba鈥�
Ya fada da yarensu, a maimakon Sarkin ya amsa masa sai wata tsohuwa ce mai bakin zane ta amsa masa tana takowa zuwa inda yake tare da jero masa tambayoyi.
鈥淪u waye wannan Shugabana?鈥�
Wasim ya mike tsaye da kyau yana kallon tsohuwar kamar ba zai amsa mata ba.
鈥淵an garin nan ne, be zama lallai ki san kowa a garin nan ba鈥�
Ya amsa mata da yarensu, kamin Liya ta nuna Fadime data magana da yaren da su kadai suke ji.
鈥淣a san wacan yarinyar, yana zuwa gurinta, a wani gari da yake yamma da garin nan...鈥�
Fadime ta kara fito da idonta waje, duk da kasancewar bata san me Liya take fada ba amman nuna ta take, gashi ta ga Wasim ma a nan shi ya risina a maimakon a risina masa, take mararta ta kara cika da fitsari, hannunta ta kai ta bugu Wasim yana kallonta ta soma masa magana a cikin ranta.
鈥淔itsari nake ji fitsari鈥�
Ta fada a ranta tana mutsika masa ido tana masa alamar yadda zai gane. Shi dai kam be fahimci komai ba hakan yasa ya maida hankalinsa gurin Liya.
鈥淚na magana tana magana saboda an daure mata ta yi yadda take so a masarauta, mi zai saka na fadi abun da ba shi ba a gaban Shugaba? Ya zama lallai sai kun san kowa a garin nan ba, amman lallai ne kowa ya san ku鈥�
Ya fada da yarensu yana watsawa Liya wani mugun kallo. Hannu Sarki ya daga sai tsohuwar taja baya ta nufi wani guri daya fi kama da bukka a cikin fadar, bata dade ba ta fito rike da ture wanda ke dauke da soyayyen nama, ta mikawa Zainab.
鈥淐i鈥�
Ta fada da yarensu, Zainab ta kai hannu ta dauki yanka daya da sauri ba dan ta san abunda ta fada ba, jiki na rawa ta kai bakinta ta tauna ta hade, daga lokacin ne gaban Liya ya fadi ganin ba tai komai ba. Tsohuwar ta matsa da naman kusa da Fadime.
鈥淐i鈥�
Tana fadin haka Fadime ta kalli Wasim da sauri, sai ya amsawa tsohuwar da yarensu.
鈥淏ata cin nama鈥�
鈥淣a yau ne kawai, kuma umarnin Shugaba ne, ci鈥�
Ta karasa tana kallon Fadime, da sauri Fadime ta kai hannu ta dauki yanka daya tana kuka ta kai bakinta, bata ko tsaya tauna shi ba ta hadiye. A take ta ji wani abu ya taso mata tun daga cikin cikinta ya nufo makoshinta, wani irin kaikayin bala'i ne ta ji a makoshinta, daga Wasim har tsohuwar da Sarkin da Liya kallonta suke.
鈥淲acan ta mu ce wacan bare ce鈥�
Tsohuwar ta fada tana nuna Fadime, tana yin baya-baya, wani irin ihu Fadime ta saka ta rike makoshin tana kuka.
鈥淲ayyo kaikayi wayyo Allah kaikayi鈥�
Da sauri Wasim ya maida ita bayansa, yana kallon Mahaifinsa, Zainab kam mutuwar tsaye tai a gurin ganin ita ta ci be mata komai ba, amman ga Fadime rike da makoshi wasu yawu masu yauki na mata zuba kamar kubewa sai kuka take tana wani irin tari, tana yagar wuyanta da yatsun hannunta. Murmushin jindadi ne ya fadada kansa a fuskar Liya tana kallon yadda Fadime ke tari tana susar wuya cike da shauki.
鈥淓rrugabea da, nire errua da ez dakiela ezer, tira egin nion鈥�
鈥淏ata da laifi, laifina ne bata san komai ba, ni na janyo ta鈥�
Ya fada yana ta kokarin tare Fadime daga kallon da Sarkin ke mata. Hakan da yai kadai ya isa ya karantar da Sarkin cewar son ta yake.
鈥淲ASIM...!鈥�
sarkin ya fada yana gyada kai a hankali tare da kara hade rai kamar bakin hadari, Fadime kam faduwa tai a gurin hankalinta na kokarin bacewa saboda kai kayin bala'i da take ji a makoshinta, Wasim ya duka da sauri ya rike ta. Zainab na tsaye a gurin tana shafa wuyanta ba dan tana jin komai ba sai dan tambayoyin da take da su.
NANA POV.
Wani irin murmushi take tana kallon kanta a madubi, ita kanta ta san ta yi kyau matuka red gown din dake jikinta ta haskata, daman can Nana ba mace ce mai son doguwar kwaliya ba, hoda ce kawai a fuskarta sai jan baki data shafa. Mikewa tai tsaye ta dauki purse dinta ta saka takalminta sannan ta nufi kofa tana takawa kamar wata Amarya. Ko da ta fito babu kowa a falon Ammy hakan kuma ba karamin dadi yai mata ba, sai ta nisa ta hanyar da Ammy take hana ta fita, da sauri sauri ta rika tafiyar gudun kar ta hadu da Ammy ta hana ta zuwa budan kan. Tana isa cikin fadar Ammy ta bude kofar ta baya ta fita. Daidai kofar AA ya faka motar, daman tun 7:40pm ya iso ya aika wata Hadima ta fada mata ya iso sai ta umarce hadimar ta fada masa ya dawo ta kofar fadar Ammy. AA na ganin Nana ya fito daga motar yai tsaye yana kallonta, gaba daya ta sake ta masa mugun kyau kamar ba ita ba, abun ka da marar jiki sai sigar ta kama jikinta kamar wata yar tsana. Ita kanta kallonsa take domin yayi kyau fiye da kullum ba zaka ganshi ka ce direba ba ne dan masu kasa haka ya fito. Murmushi ta sakar masa ganin yadda yake kallonta, sai shi ma ya mayar mata da murmushin ya bude mata gidan baya, saukowa tai a hankali ta shiga motar sai ya rufe ya bude mazaunin direba ya shiga ya zauna, sai ya samu kansa da rashin natsuwa har sai da ya juyo ya kalleta, be taba ganinta da kwaliya ba sai a yau, ashe haka take da kyau? Ya raya a zuciyarsa.
鈥淜in yi kyau鈥�
Ya furta a fili yana jin wani irin girmanta na kama shi, duk sai yaji ta zame masa kamar ba ita ba ya ji nauyinta na sauko masa.
鈥淣a gode kai ma ai ka yi kyau鈥�
鈥淭hank Youu, ina zamu je?鈥�
鈥淴&L Hotel鈥�
Ya juya yana shakar kamshin turarenta daya cika motar ya bata da na shi karamin turaren. Madubin motar ya saita ya juya ta inda zai rika ganin fuskarta sannan ya kunna wutar motar ya kunna ac. A hankali yake ta tuka motar yana satar kallon Nana ta madubin motar, a duk lokacin da suka hada ido sai ta saka masa murmushi. Daga ita har har shi babu wanda yai wata magana har suka isa.
X&L Hotel babbar Hotel ce a garin Yola, wanda manyan mutane suke zuwa yin taro ko biki ko sauka idan ta kama, ko kuma shakawatawa.
A harabar Hotel din ya faka motarsa sannan ya fito ya bude mata ta fito.
鈥淶aka shiga ciki?鈥�
鈥淎na bari a gashi?鈥�
鈥淵es zan ce kai bodyguard dina ne鈥�
鈥淥kay鈥�
Ya rufe motar yana jindadi, daman can ya dade yana son ya shiga gurin domin ya dade yana jin labarin Hotel din sai dai be taba zuwa. A maimako tai gaba ya bi bayanta sai ta tsaya ta jera tare da shi, yadda ya ci ado ita ma ta ci sai abun ya bada kala kamar saurayi da budurwa, a tare suka doshi wata karamar hanya da aka kawata kamin su karasa wani saurayi ya kira sunan Nana, da sunan da Zainab take kiranta da shi.
鈥淏aby鈥�
Nana ta juyo tana arba da saurayin ta washe hakora ta doshi inda yake, AA kuma ya tsaya a gurin yana kallonsu, side hug tai masa suka gaisa.
鈥淗ow are you?鈥�
鈥淚'm fine, kai ma ka zo biki鈥�
鈥淵eah friend din mu ne zai yi aure, amman mu ba ciki zamu shiga ba, waya kawo ki Sirleem?鈥�
Juyawa tai ta kalli AA a ganin be cancanta ta kira direbanta ba a yadda ya ci gayun nan.
鈥淣o wani ne鈥�
鈥淥kay sai mun hadu ciki鈥�
Ya fada yana sannan ya nufi hanyar shiga gurin. Ita kuma ta juyo ta dawo gurin AA.
鈥淢u tafi鈥�
鈥淏a zamu je din ba鈥�
Ya fada yana watsa mata harara.
鈥淢e akai?鈥�
鈥淵a zaki rumgume wani kato da ba muharramin ki ba鈥�
鈥淭o ai cousin dina ne鈥�
鈥淏a cousin ba kwarkwata, bari na sake ganin kin rika hannun wani sai na fasa miki kai鈥�
Ya karasa da kwafa ita kuma ta turo baki.
鈥淭o Wallahi zan ma koreka daga aikin鈥�
Ya kwaikwayi muryarta yana yatsina fuska.
鈥淭o Wallahi zan ma koreka daga aikin鈥�
鈥淜uma karka bi ni ciki, ba zan shiga ba鈥�
鈥淲allahi sai na biki, sai na shiga, kuma muna shiga ciki kika ga wani kika masa magana sai na bata miki rai鈥�
Ya fada with serious face, yana kara hade mata rai kamar irin shi ne boss ita take aiki karkashinsa. Tana yin gana ya bi bayanta sai ta juyo tana turo baki.
鈥淜a daina bina鈥�
鈥淪ai na biki kuma ki kaiwa wani namiji magana sai na bata miki rai鈥�
Wani irin abu taji kamar ta saka kuka, sai kuma ta juya ta cigaba da tafiya yana binta bayanta har suka isa gurin. Bata nuna gate pass din ba sai kawai ta fada masa sunanta.
鈥淣ana Aisha Abdallah Jari鈥�
Da sauri ya bude mata kofar ta wuce AA ya bi bayanta yana fadin shi bodyguard dinta ne. Kato dakin taro ne da aka kawata da ado na zamani ga haske ko'ina kamar rana, mutane ta ko'ina kana ganin bikin kasan na manyan mutane ne. Kusa da kofar AA ya tsaya Nana kuma ta fara raba ido tana kallon mutane, ta nan ta hango Hajiya Babba cikin matan manya sai far'a take ana ta fira, can kuma ta hango kawarta Amal, da sauri ta nufi inda suke Amal din na ganinta ta rumgume ta tana murna kamin ta ja mata kujera ta zauna, duk abun da suke idon AA na kanta ita a tana yi tana satar kallonsa, tana son ta bar kujerar ta koma wata inda take hango wasu friends nata, da zarar ta mike tsaye sai AA ya bata mata fuska na babba da yaro sai ta koma ta zauna tana watsa masa harara tana turo baki. Sai da ya tabbatar ta natsu sannan ya fita daga gurin ya koma cikin motar ya zauna.
Kari aka fara yi ma Amarya wanda hakan yasa su Amal din tashi ita da kawayenta, suka nufi gurin Amaryar aka bar Nana ita kadai, wata kawar Amal din ce mai suna Rukayya ta dawo gurin ta aje handbag dinta ta cire sarkarta ta zinari ta saka a jakar.
鈥淪is dan Allah zan bar jakata a nan ki kula min, sarkar tana damuna ne鈥�
鈥淥kay鈥�
Nana ta amsa duk da bata san ba sai a lokacin. Yarinyar na barin gurin zuciyar Nana ta fara raya mata ta dauki sarkar, hannunta ya soma wani irin kai kayi, wani abu ta soma ji ba dadi, har ta kai hannunta a jakar sai kuma gai saurin cirewa tana kallon jama'ar gurin da ba su kula da ita ba. Dagawa tai daga zaunen da take ta saka hannunta a kasa ta dannenshi amman bata ji ya daina mata kaikayi ba, ba kaikai irin wanda aka saba ji ba kai kai yi a daukar abu wanda take jin a duk lokacin da so satar wa Ammy ko Mai Martaba kudi. Ciro hannun tai tana yarfarwa sannan ta kai cikin jakar ta dauko sarkar mai tsada ta saka a purse dinta ta mike tsaye da sauri ta fice daga gurin.
Sai da ta fito daga gurin sai kuma tai tsaye idonta ya cika da hawaye, bata taba abun da ba na Ammy ba sai da yau bata taba sata in public place like this ba sai a yau. Ji take kamar ta koma ta maida kuma tana jin tsoro. Takawa ta fara yi ta nufi gurin motarsu, tana isa ta bude motar ta shiga gidan bayan. AA dake zaune ya juyo ya kalleta.
鈥淎n gama bikin ne?鈥�
鈥淎a鈥�
Ta amsa da muryar kuka, jin hakan yasa ya juyo da kyau ya kunna wutar motar yana kallonta, sai hawaye ya gani a fuskarta.
鈥淵a akai?鈥�
鈥淲ani abu nai鈥�
鈥淲ani abu na mi?鈥�
Ta yi shiru sai kuma ta ce.
鈥淪ata nai na saci sakar wata kawar kawata鈥�
Ba shiri AA ya zaro ido.
鈥淪ata kuma?鈥�
鈥淓h ai be kamata nai sata ba ko?鈥�
鈥淭hen why kika yi?鈥�
鈥淚 don't know i just feel like ina son nai, amman be kamata nai ba, kuma na san akwai camera a gurin zata nuna ni, kuma yarinyar ni ta bawa ajiyar jakarta鈥�
鈥淣ana me zai saka ki yi sata? Why, be kamata ace kina sata ba Nana baki bata sunan gidanku da mahaifinki, mi kika rasa ma da zaki yi sata? Why?鈥�
鈥淏an sani ba, haka nan kawai nake yi鈥�
Ta amsa shi tana kuka, wani tunanin ne ya zo masa kar dai ace kudin da take kashewa sato su take?
鈥淚na sarkar?鈥�
Ta bude purse din ta dauko ta mika masa.
鈥淕ashi鈥�
Ya mika hannu ya karba.
鈥淎kwai gate pass ne鈥�
鈥淓h鈥�
Ta ciro ta mika masa, sai ya karba.
鈥淜i koma ciki ki dauki wayarki sai ki samu gurin da babu mutane sosai ki kara wayar a kunne kamar kina waya, idan tai magana ki ce kin bar jakar ne kin je ki yi waya, zan shigo yanzu鈥�
鈥淎mman bani da waya Baba Waziri ya karbe鈥�
Ya kika mata wayarsa.
鈥淩ike wannan鈥�
Ta Karba sannan ta bude motar ta fita ta nufi gurin tana share hawayenta gabanta sai faduwa yake. Da kallo ya bita har ta shige sannan ya sauke ajiyar zuciya yana jin wani iri a ransa.
鈥淪o. That's mean kudin da take bani satarsu take yi? What's wrong with her?鈥�
Ya furta yana ganin rashin dacewar hakan, sannan ya bude motar ya fita ta doshi guri.
0 comments:
Post a Comment