Kallon Mama tayi da kyau kafin tace "Mama wannan sabuwar shigar fa, da quruciya ba kiyi ba sai yanzu kawai saboda ki zubar mana da mutunci, waime kike so ki zamane Mama?"
"Ke, karki fad'a min maganar banza, ki fad'a min abinda kika kirani jiya kawai na tambaya, kece zaki fad'a min abinda ya dace."
Kallon qofar d'akin tayi sannan ta kalli Mama tace "Mama, me ki kawa Khairat?"
"Mtssss, dama akan haka kika kirani, to me tace miki na mata?"
"Ba ita tace min kin mata wani abu ba, amma dai naga kwanan nan tana wahala sosai bata da lafiya, nasan kuma ba zai wuce da hannunki ba."
Gyara zama Mama tayi tace "aina fad'a musu ba zan bari haka ba saina d'auki fansa, kuma yanzu ma ta fara gani, dan yanzu haka nima inada mutane kamar yanda take taqama tana dasu, kuma yanzu haka daga nan zan wuce wajen wata matace da akace tsohuwar karuwar ubanta ce, zanje mu cika aikinmu na gaba."
"Mama, Mama, wallahi babu ruwana idan ki kayi abinda za'a qara d'aureki, nidai in dan saboda ni kike haka to na yafe bana so, ki barni zan zauna da ita a haka, kawai ki cire hannu a al'amuran gidan nan dan Allah Mama."
Kallonta tayi tace "tun kafin ki mallaki hankalinki nake shiga na fita akan lamarin aurenki da Umar Faruk, daf da kaiwa ga gaci wallahi ba zan zubar da makamaina ba, dole na d'auki fansa tare da mallaka miki Umar Faruk a hannunki."
Kafin tayi magana ta d'auki jakarta ta bud'a ta fito da qullin magani ta bata tace "karb'i nan, a abinci zaki zuba mishi yaci, wannan kuma kije qofar d'akin waccen hatsabibiyar ki zuba mata, ba zata sake sha'awar qara koda minti d'aya ba a gidan nan."
Rumgume hannaye tayi tace "bana so Mama ki koma da kayanki, kuma meya rage a yanzun tunda gida ta kwana jiya."
Wata yar dariya tayi tace "da kyau, hakan ya tabbatar min aikin malamin nan yanayi fiye da waccen na baya."
"Mama sabon malami kika samu kuma?"
"Eh yarinya, ai ban fad'a miki ba sabon malami ne wannan, kuma kinga shekaranjiya ne kad'ai na fara zuwa wajenshi, amma gashi aiki yayi."
Da kyau ta kalli Mamanta tace "wallahi Mama yah Umar ya fara zargina akan haka, dan Allah ki daina duk abinda kike ki tuba ga Allah Mama, niko a haka ma zan zauna dashi tunda ina sonshi, ina jiye miki tsoron ranar da zaki sake jin kunya akan abinda kike aikatawa Mama."
Tab'e baki tayi tace "humm, shi yasa ma na taho miki da maganin matsalar nan, idan ki kayi anfani da wannan maganin na hannunki komai zai yaye."
Ta fad'a tana bata d'aya qullin maganin, ganin tana hararanta yasa ta karb'a tana turo baki, d'ora mata tayi da " ki tabbatar kinyi aiki dasu kamar yanda na fad'a miki, idan ba haka ba ki sani, wallahi wata rana saikin zubar da hawaye, dan ina tabbatar miki hankalinshi zai koma kan wacce bata da lafiya ne, in ba kiyi sa'a bama ya tare da zama acan gidan sai dai kawai yazo ya ganki ya koma, ni kinga tafiyata ina da abinyi."
Bata jira komai ba ta wuce gyalenta najan qasa sai yan mazaunanta dake motsawa, da takaici ta bita da kallo tana jin kamar ba tayi sa'ar uwa ba, qarqashin gado ta jefa maganin ta d'auki abincinta ta fara ci.
***************
Fitarta daga nan gidan wata qawarta ta wuce, koda taje kuma suka wuce kamar yanda ta mata alk'awari, wani matsakaicin gidane sai dai yana da kyaun gaske da kuma tsari, bayan sun gaisa hamshaqiyar matar tasa aka kawo musu ruwa, qawar ta Mama wacce ake kira da *'yar fara* ce wannan hamagiyar matar ta kalleta tace " xyar fara ina jinki."
Nuna tanti tayi tace "kamar yanda na fad'a miki a waya tun kafin muzo, wannan itace matar da take neman taimakonki."
Murmushi tayi da bakinta kad'ai ya motsa kafin tace "ta fad'a min komai a waya duk abinda ya shiga tsakaninki da 'yarsa, na yarda zan taimakeki ne a zahiri saboda kin samemu tsakiya da shirye shiryen zab'e, kuma akwai wani aiki da mai neman kujerar Mani Bukar ya biyani kud'ad'e danna kai Mani Bukar qasa kamar yanda ina d'aya daga cikin wanda suka sakashi yayi sama, dan haka karki damu zuwa gobe zan gama shirya komai, kuma zakisha mamakin abinda na shirya, tabbas Khairat zata ji ba dad'i itama."
Da farin ciki tanti tace "na gode sosai Hajia da wannan taimakon, kuma insha Allah Hajia za kiji babban biya."
D'an b'ata rai matar tayi ta kalli yar fara tace "yar fara ina fatan kin fad'a mata ba'a min wasa da maganar data shafi kud'i ko?"
"Ai karki damu Hajia, na fad'a mata komai a game dake, ba za'a tab'a samun matsala ba." cewar 'yar fara.
"To yayi kyau, zaku iya tafiya." tana fad'a ta tashita shiga wani d'aki ta barsu nan, tashi sukayi Mama na yaba matar tana ji inama ta zama ita, har saida 'yar fara tace "to ai matsalar kin tsufa ne, amma badan haka ba ai zaki iya hawa network kema."
Hararanta tayi tace "karki cimin mutunci mana, me kika d'aukeni?"
"Ba komai." cewar 'yar fara.
*Mamienmu amin afuwa*👏🙇♀
****************
Umar Faruk na zaune daf da Khairat yana bata magani zazzab'i tana sha, Mammie na gefen Khairat sai Mamie da Papa dake d'aya kujerar suna kallonsu, duk da dare yayi yana so yaje gida amma ganin jikin nata ba sauqi yasa ya kasa tafiya, tana shan maganin ta koma ta kwanta tana sake dunqulewa cikin bargon da Mamie ta d'auko mata, a hankali take lumshe ido alamar tana so tayi bacci, a haka har baccin yayi gaba da ita, tashi Umar Faruk yayi ya musu sallama zai fita, da k'arfi sukaga Khairat ta fad'o daga kan kujerar, a zabure ta farka itama tana kallon mutanen wajen, da sauri Umar Faruk ya qarasa wajenta ya kamata ta tashi ta koma ta zauna, fuska ba annuri yace "kalleni nan."
Kallonshi tayi ya sake had'e rai yace "wallahi ku daina wahalar da ita haka in kuna son zaman lafiya, kunga ina binku a hankaline saboda ina so mu rabu lafiya daku, tab'ata da kuke shine kuskuren da kukeyi."
Qwafa yayi ya mik'e zai nufi hanyar fita Papa yace "Umar Faruk, me yake damunta ne?"
Juyowa yayi yace "karku damu Papa, komai zaiyi daidai na baku tabbacin hakan."
Yana fad'a ya juya ya kalli Khairat, hararan sama da qasa ta masa taja dogon tsaki, fita ranshi a b'ace ba tare daya damu da abinda tayi ba, sam yau ma basuyi bacci ba ko kad'an, daga wannan ciwo sai waccen a haka suka kwana.
**************
Tunda Zuby taga shiru bai dawo ba sai ranta ya fara b'aci ta fara tunanin abinda Mama ta fad'a mata, ta kuma yarda tabbas wata rana zaice zai tare can tare da Khairat indai har ana haka tun yanzu, ganin Ruk'ayya ta kawo abincinshi ta aje kawai saita tashi ta d'auko maganin data jefa qasan gado ta duba wanda zata saka a abinci ta mayar da sauran, tsautsayi ya kawo Umar Faruk a lokacin da take zuba maganin a abinci, komawa yayi da baya ya saita kansa tare da had'e b'acin ranshi sannan yayi sallama ya shiga, ko kad'an bai nuna mata wani abu ba ya share kawai, wanka yayi sannan ya zauna cin abinci, bismillah yayi yana shu'umin murmushi ya kai lomar bakinshi, saida ya cinye wanda ta zuba mishi duka saboda yunwar da yake ji, dan duk lokacin da zai kai abu bakinshi saiya tuna Khairat, hakan yasa shima bai cika ci yana qoshi ba kwanan nan, da farin ciki Zuby ta kwana sab'anin Umar Faruk daya kwana yana kallon fuskarta, tsanarta na sake mamayeshi, daga qarshe kuma tunanin Khairat ya maye gurbin tunaninta dashi har gari ya waye.
Tana zaune harya gama shirinshi zai fita, juyowa yayi ya kalleta yace "ni zan wuce, babu komai?"
"Ba komai."
Hannu ya mik'a mata cike da qoqarin taushe qiyayyar da take mata yace "ina so zan gaisa da yarona."
Hannun ta mik' masa ta taso shi kuma ya bi cikinta da kallo wanda ya turo riga ya fito, shafar cikin yayi yace "nasan ka tashi lafiya, haka Papanka da mamanka, kuma nasan zaka kula min da kanka, ni zan tafi."
Sunkuyawa yayi ya sumbaci cikin sannan ya fice, saida ya gaishe da iyayensu sannan ya wuce gidansu Khairat, da shigarshi sallama kad'ai yayi ya samu duka mutan gidan tsaye akan Khairat dake ta birgima a qasa tana kuka tana cewar zuciyarta zata fashe zafi take mata, qarasowa yayi dan babu ma wanda ya amsa sallamar tashi, tsaye yayi shima yana kallonta idonta rufe sai hawaye dake fitowa, matsowa yayi da nufin zama kusa da ita kawai saita d'ago ta bulalo amai, duk da ta b'ata mishi jiki bai damu ba saida ya zauna ya fara taimaka mata da addu'a, a hankali a hankali ta fara samun nutsuwa da sauqi, bayan wani lokaci kuma sai bacci yayi gaba da ita, Mamie ce tace "Allah ka dubi yarinyar nan ka sassauta mata abinda yake damunta, Allah ka yafe mata kurakurenta badan mu ba." ta qarashe da fashewa da kuka.
Kallonta Umar Faruk yayi yace "dan Allah kuyi hak'uri ku daina kukan nan, insha Allah zata samu lafiya."
Cikin kuka Mamie tace "wallahi tausayi take bani, kwananta biyu yau a gidan nan amma har yanzu baccin da tayi baifi na awa biyu ba idan aka had'a, ace daga wannan ciwo sai waccen, da anji sauqin wannan kuma sai wani da danno kai, wallahi nidai ban tab'a ganin laulayi irin nata ba."
Gyara mata kwanciya yayi ya mik'e yace "ku kula da ita zanje na samo ganyen magarya, insha Allah zata samu lafiya da yardar Allah."
Yana fad'a ya fice daga gidan, zaune sukayi suna kallonta kafin ta farka kuma, ba dadewa kuwa ta farka tana dafe kai, Mamie ce ta kawo mata abinci taci amma sam tak'i ci, saida Papa ya lallab'ata ya rarrasheta kad'ai ta samu taci kad'an, tana gama ci ta tashi da gudu taje k'ofar shigowa falon ta fara amaye abinda taci, tana haka Umar Faruk ya shigo gidan, tsaye yayi yana kallonta da tausayawa saida ta gama ya rik'ota suka shigo, kallonta yake sosai duk da cikinta ya girmema na Zuby amma ko alamun fitowa baiyi ba, zaunar da ita yayi sannan ya bawa Mamie ledar hannunshi yace "ku jiqa wannan ku ajeshi a wuri mai kyau, zan nemeshi nan da kwana bakwai insha Allah."
"To shikenan." cewar Mamie tana karb'a.
****************
Misalin *09:30* na dare duk suna zaune a falon, Khairat na kwance akan cinyar Umar Faruk da yake so ya tashi ya tafi ta rik'eshi, hira suke sama sama wani jami'i ya shigo ba tare da sallama ba ya sarawa Papa alamar girmamawa yana fad'in,
"Yallab'ai, wata mata ce a qofar gida tace tana son ganinka, na tambayeta abinda ya kawota amma tace ita kai take son gani."
Shiru Papa ya d'anyi kafin yace "ok ba damuwa, kace ta shigo."
Juyawa jami'in yayi bayan ya amsa da "an gama yallab'ai."
Harsun fara tab'a hira sukaji ance "salam."
Kowa kallon qofar yayi dan ganin mai sallamar, zunbur Papa ya mik'e da tsananin mamaki yace " *Odette*, kece gidana, meya kawoki nan, kin manta rabuwarmu ne?"
Kowa dai da mamaki yake kallonsu harda Khairat da jikinta ya d'anyi dama, juyawa matar tayi ta kalli qofa tace " *Salim*, shigo mana."
Wani matashin saurayine da bazai wuce shekara sha shida ba zuwa sha bakwai fari sol dashi kamar matar, d'an gaye ne sosai irin matasa ne masu aji, turo yaron tayi gaba ya nufi Papa tace "kaje, yau dai na sauke wannan nauyi, kuma na huta da qorafinka kullum, kuma yanzu asirinmu zai rufu."
Daf da Papa yaron ya tsaya yana murmushi ba b'ata lokaci ya rumgume Papa yana fad'in "oh Babana, naji dad'in had'uwa da kai."
Papa daya kusa mtuwar tsaye da qyar ya raba jikinshi dana yaron yace "kai wace maganar banza ce wannan, waye uban naka?"
Hamshaqiyar matar ce tace "kunga na barku lafiya, saida safenku."
"Ke, wai miye haka, wanene wannan yaron?" cewar Papa.
Cike da yabqi da yanga tace "oh yi hak'uri fa, wannan ai shine *Salim* danka dana jima ina boye maka, amma kwanakin nan yana addabata waishi dole na had'ashi da mahaifinshi danya gaji da ganinka a tv kullum, nace yayi hak'uri amma sai yace zai fad'a a gidan jaridu da tv cewar shi d'in danka ne, shi yasa naga zaifi ayi komai asiri rufe ba tare da anyi tone tone ba, kasan zab'e ke tafe."
"Wannan ai maganar banza ce ma, kin sani na sani lafiya lau muka rabu dake, karki yarda kice zaki b'ullomin ta wannan hanyar, dan wallahi ba zakiji dad'i ba, kuma ki gaggauta fita min da wannan d'an iskan yaron kafin nasa a fitar min dashi."
Rai b'ace tace "a'a Mani, karka sake zagar min yaro wallahi, kuma idan kace baka yarda ba kai ka sani bana abu babu hujja, kamar yanda kasan bana qarya ko kuma cuta."
Jakarta ta bud'a ta ciro da takardu ta jefa mishi a qirji tace "wannan suna dauke da duk wasu bayanai tun daga lokacin dana d'auki cikin Salim har haihuwarshi, sannan akwai gwajin da asibiti sukayi na qwayoyin hallitunshi iri d'aya ne da naka, idan kuma baka yarda ba zaka iya sakawa a maka sabon gwaji."
Tana fad'a ta juya ta fita daga gidan, yaron kuma zaune yayi kusa da Mamie yana kallonta yace "bonsoir (ina wuni)."
Da sauri Mamie ta shige d'akinta tana hawaye, maida kallonshi yayi ga Khairat data tashi zaune tana kallon ikon Allah, da azama yaje wajenta ya zauna yana kallonta yace "wannan itace auntyna ko?"
Kafin ayi magana kuma ya kamo hannun Khairat yana maqalewa da nashi, badan rashin lafiya da matar nan ta gane kurenta cewar Khairat a zuciyarta, amma duk da haka cikin zafin rai ta d'aga hannu ta wanke yaron da mari ta nunashi tace "karka sake tab'ani dan kai ba d'an uwana bane."
Dafe kunci yayi yana murmushi yace "ke kuma haka kike tarban bak'inku, ba komai ke yayata ce zaki iya yimin komai."
Tashi tayi danta bar wajen amma saita zube saboda qafafunta da suka rik'e, Umar Faruk ne ya tashi ya d'auketa ya kaita d'akinta ya kwantar da ita, addu'a ya mata ya rufeta sannan ya fito ya bar d'akin dan tak'i kallonshi ma, yasan badan rashin lafiya ba da gidan nan ya hargitse yau.
Papa ya samu tsaye yana duba takardun nan har yanzu, indai har zaiyi anfani da abinda ya gani a takardun to tabbas Salim d'ansa ne, amma ba zai yarda ba dan haka Umar Faruk na musu sallama ya fita ya kira docteur d'inshi yace gobe zaizo, d'akin Mamie ya shiga ya samu tana kuka, zaune yayi ya fara magana da "Na'ima, dan Allah..."
D'aga mishi hannu tayi ta tashi tana share hawayenta tace "kar kaba kanka wahala wajen rarrashina, nima ba hushi nayi da kai ba, kawai dai banji dad'i bane saboda ban tab'a tunanin ka haihu a waje ba, amma inhar ina da hankali aibai kamata nayi hushi da haka ba saboda nasan komai a game da rayuwarka ta baya."
"Na gode da kika fahimceni Na'ima, amma wallahi nima ban tab'a sanin inada wannan yaron ba, kuma har yanzu ma ban yarda d'ana bane harsai Allah ya tashemu gobe munje asibiti an sake mishi wani gwajin."
*Wata sabuwa*
*Barka da Ranar Hausa ta duniya, Allah ya d'aukaka matan hausawa.*
29/08/2019 à 14:33 - Meerahgee❤: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*JIHADI*
_Umar faruk_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛
_Haka kawai sai kaga Allah ya had'a zuqatan bayinsa, ba gari d'aya ba bare unguwa, amma haka Allah ya had'amu har muke qaunar junanmu, Allah ubangiji ya baki lafiya my Meerahgee *(Maryam Gital)*, Allah yasa zakkar jikina kuma sanadin yake zunubanki, your Meerahgee again._💕💞
_Dan Allah ki daina wahalar da zuciyata ki fito ki naganki ko naji sanyi, Allah ya qara miki lafiya dawamammiya, *My BK* i love you_.
_Bismmilahir-rahman-rahim_
*Idan nayi magana dubannin rayuka zasu b'ace, dan haka nayi shiru.*😎
5⃣9⃣
Ba'a b'ata lokaci ba Papa ya d'auki Salim suka je aka sake mishi gwaji, ba yanda ya iya tunda gwajin ya bayyana d'anshi ne na cikinshi, daga nan kuma sai yaji yaron ya shiga ranshi, ashe shima Allah ya bashi namiji.
*Hummmmmmmm*
Koda suka zo gida Papa yasa aka gyara mishi d'aya daga cikin d'akuna, ana cikin haka ya had'a yaron tare da masu gadinshi suka je babban boutique aka siyo mishi kaya masu kyau da tsada, sabuwar rayuwa kenan wa Salim.
*Wacece Odette???*
Odette shahararriya kuma 'yar duniya ta gidan gaba, sun jima tare da Mani Bukar saboda gogewarta da kuma iya bariki da soyayya, tun kafin ya fara siyasa suke tare da ita, kuma tana d'aya daga cikin wanda suka bashi gudummuwa sosai harya hau kujerar da yake yanzun, a waccen lokacin zai iya cewa bayan mahaifiyar Khairat ita macen da yake so, amma a lokacin da shiriya tazo mishi saiya fad'a mata ya shiryu kuma itama ta tuba ga Allah, sam tace shi dai yaje amma ita tana nan har yanzu, saida mata babbar sallama sannan suka rabu cikin mutunci, amma shine yau tazo mishi da maganar yaro d'an shekara sha bakwai, wanda baisan dashi ba sai yanzu.
****************
Kamar yanda Umar Faruk ya kai Zuby école, haka ma yanzu duk da abinda ke gabanshi ajeshi yayi saboda lokacin tashinsu yayi, koda yaje ta taso daga inda take zaune harta shigo ta zauna yana kallon cikin dake maqale jikinta, saida ta rufe motar sannan ta kalleshi tace "sannu."
Bata jira amsarshi ba ta bud'a jakarta ta fiddo ledar awarar data siya ta bud'e, ba tare da kama hannun yaro ba ta fara gaigayar awarar ko kallonshi ba tayi, shi kuma kallonta yake da gani kasan yunwa take ji sosai, yanda take cin awarar sai yaji ta birgeshi yana ji kuma inama Khairat itama haka take cin komai, murmushi kawai yake mata har suka d'auki wata hanyar ta daban, sai lokacin ta kalleshi tace "yah ina zamu je kuma nan?"
Ba tare daya kalleta ba yace "zanje na siyar daku ne, ko baki san mace mai ciki tsadane da ita ba?"
"Hum, aiba zaka fara ba, dan nasan ko ka siyar dani ba zaka yarda ka siyar da magajinka ba."
Dariya yayi yace "gaskiyarki kam, amma taya zan siyar da uwar bayan itace mai haifawar? abune da ba zai yiwu ba ai a wajen Umar Faruk."
Kallonshi tayi ta cika baki da awara tace "kana sona ne har yanzu?"
Kallon qwayar idonta yayi amma ya kasa cewa komai, maida kallonshi yayi ga tuqinsa ita kuma tace "basai ka fad'a ba nasan baka sona."
Kallonta yayi yace "Zuby, kina so na b'ata lokacina wajen fad'a miki abinda kika sani, ko kuma kina sone dole saina ce miki ina qaunarki fiye da tunaninki, nasan kema kinsan da haka."
Ganin dai suna shiga wani wajen yasa tace "wai ina zamu ne?"
Kashe mata ido yayi hankali nutsu yace "ki yarda dani mana, ba zan cutar dake ba."
K'ofar wani matashin gida suka paka, shine ya fara fita kafin ta fito itama, goge maiqon dake hannunta tayi a hijabinta sannan tabi bayanshi suka shiga ciki, babu hayaniya gidan sosai hakan yasa sai wata dattijuwar mata ta musu iso ciki, suna shiga falon Zuby ta tsaya cak saboda ganin babanta Bala zaune da alama bashi da lafiya, saida Umar Faruk ya d'an ja hijabinta sannan suka samu wuri suka zauna, gaisawa sosai Umar Faruk yayi da mutanen Zuby na kallonshi dan yanda taji suna gaisawa alama ce ta yana zuwa gidan, kallon da Umar Faruk ya mata yasa ta kalli Bala tace "ina kwana?"
"Ina kwana yanzu?" cewar Umar Faruk.
"Ina wuni?" ta fad'a tana cika baki.
"Lafiya lau Zubeida, ya makarantar?"
"Lafiya lau."
D'aya daga cikin matance tace "wannan matarka ce?"
"Eh, amaryar ba." cewar Umar Faruk cike da kunya.
Bala ne ya d'ora da "kuma 'yata ba."
Da mamaki matan suka kalleshi yayin da Zuby ta kalleshi, babbarce tace " 'yarka kuma Alhaji, taya ta zama 'yarka kuma?"
"Eh, haka nace, 'yata ce kuma ta cikina, zaku iya bamu wuri." ya fad'a a kausashe.
Tashi sukayi suna kallon Zuby, Bala kuma kallon Umar Faruk yayi yace "ya jikin Hajia Khairat?"
Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace "jiki da dama."
"Allah ya qara sauqi, insha Allah zata samu sauqi, dan bata da haqqin kowa a kanta, hasali ma zuciyarta fara ce, taimakon mutane shine aikinta, kuma Allah yayi alk'awarin ba zai kunyartar da mai irin wannan hali ba."
Yatsa yasa ya share qwallar dake idonshi yana ci gaba da cewa "baiwar Allah, wallahi da inada maganin cutarta dana batashi, da ace kuma nasan inda zan samo mata maganin da zanje na samo mata koda kuwa zansha wahala ne, sai kash muna ji muna gani yarinyar kirki tana wahala babu yanda muka iya, alhalin ita bata jurar ganin talaka a cikin wani hali."
Cikin sanyin jiki Umar Faruk yace " sai dai muyi hak'uri kawai, Allahn daya d'ora mata shi zai yaye mata insha Allah."
Kallon Umar Faruk Bala yayi yace "shin kasan wacece Hajia Khairat a wajena, shin kasan taimakon da tayi mana a rayuwa? nasan zaka sani tunda matarka ce."
Katseshi Umar Faruk yayi da "a'a wallahi Baba, ko sau d'aya Khairat bata tab'a fad'a min wani abu daya danganceta ba."
Murmushi Bala yayi yace "kaji yar arzik'i, to Hajia Khairat da kake gani a yanzu haka nida iyalina muna rayuwa ne da taimakon da tayi mana, *wasu shekaru da suka gabata* na kasance mai munanan halaye, ta sanadiyar haka na rasa komai nawa saboda almubazzaranci, a lokacin da muka fara rasa abinda zamu ci nida iyalina sai hankalina ya sake tashi, a hankali sai rayuwa taci gaba da garani yanda ya kamata, nasan kuma hakan nada alaqa da cin amanar da nayiwa abokina wato Hamza, wata rana mun tashi gidan nan babu yara ma zasu saka a bakinsu bare manya, na fita da tunani samo musu duk abinda ya sawaqa , amma amma ina babu abinda na samo sai dawowa nayi, a ranar kuma akayi sa'a ana bikin wata yarinya anan, babbar sa'a da mukayi shine kasancewar Khairat a cikin qawayen amaryar, koda na dawo kasa shiga cikin gidan nayi saboda ba zan juri kallon yaran ba a wannan halin, hakan yasa na zauna a qofar gida na zabga tagumi, a lokacin Khairat ta fito daga gidan dake kallon nan gidan ta ganni a wannan hali, saboda kyakyawar zuciya yasa tazo inda nake ta tambayeni me yake faruwa, nan na fad'a mata halin da nake ciki, gani nayi ta zubar da hawaye da bansan kona miye ba,tambayarta nayi me yasa take kuka sai tace karna damu , komawa tayi gidan data fito ta jima kafin ta fito, abin mamaki da al'ajabi sai Hajia Khairat ta cire hauran makka dake haqoranta da k'arfi har suna mata jini ta bani tace naje na siyar, kuma ta bani hak'uri tace babu kud'i ne a jikinta kuma gashi wayarta ta d'auke bare ta kira, amma ta gargad'eni na gaggauta siyar da hauran guda biyu na siyawa yara abinci, duk da naso mata godiya bata bani damar hakan ba saboda tafiyarta da tayi, nan na tafi na siyar da hauran biyu kuma sunyi daraja sosai sannan na siyowa yara kayan abinci na kawo gida, kasan meya faru Umar Faruk?"
Kai kawai Umar Faruk ya girgiza yana kallonshi, d'orawa yayi da "wallahi yara na cikin cin abincin Hajia Khairat ta shigo gidan tare da wasu matasa da wasu kayan abincin, bata bar gidan ba saida ta tambayi duk yaran matsalolinsu na makaranta ta biya musu, wani babban alherin data sake yi mana da yasa na kusa mutuwa saboda farin ciki shine, kyautar *million d'aya* data bani tace naja jari, tofa tun daga wannan rana na d'auki girma da matsayi na bata kamar na mahaifiyata saboda mahaifiyata bata raye, kuma wallahi wallahi Umar Faruk, zan iya fansan ran Hajia Khairat da rayuwar d'an daya fito daga cikina, domin kuwa da gaba d'aya rayuwarmu tata ce, ina fatan Allah ubangiji ya dauke duk wani ciwo da radadi dake jikin Hajia Khairat ya dawo dashi kaina koda zai zama ajalina ne, wallahi a shirye nake dana bada rayuwata dominta."
Kallon Zuby yayi yace "shine yasa a lokacin data nemi taimakona ban kasa yi mata ba saboda ta wuce hakan a gurina, kuma banji dad'i ba sam dana samu labarin rashin kunyar da kike mata, kinga mijinki gashi nan?" ya fad'a yana nuna Umar Faruk.
Da qyar Zuby ta d'aga kai dan ita kanta jikinta yayi sanyi saboda girman al'amarin Khairat, ci gaba yayi da "to wallahi zan iya sashi ya sakeki inhar zaki din cin zarafin yarinyar nan, idan ma bai sakeki ta dad'i ba zan iya yin shari'a dashi danya sakeki, dan haka ki kiyaye in kina son zaman lafiya da albarka, kuma bawai na fad'a miki haka bane dan bana sonki ko kuma ina son aurenki ya mutu, a'a ina sone na nuna miki girmanta a gareni, ina fatan kin fahimta? Allah ya muku albarka ya baku zaman lafiya da hak'uri da juna."
Umar Faruk kad'ai ya amsa da "ameen Baba."
Haka suka dawo gida Zuby na sake jin kunyar Khairat da kanta, Umar Faruk kuma na sake jinjina al'amarin Khairat, dan inbai manta ba ta fad'a mishi ta manta sunan wanda tabawa hauran makkanta, ashe bata manta ba kawai dai bata son fad'a ne saboda kawai tayi dan Allah, a lokacin daya shiga wanka doushe ya lumshe ido ya furta a hankali cewa " *Allah ka azurtani da zuciya irinta bauwarkan nan, Allah ka cire min son abin duniya, Allah ka bani ikon yin komai dan kai, matata kuma Allah ka dubi kyakyawar zuciyarta ta son taimako ka cireta a halin da take ciki.*"
Nidai nace "Ameen."
_Haka ma team d'in Khairat da *"ameeeen."* suka amsa._
*Bayan sati d'aya*, ranar litinin su Zuby suku fara shiga jarabawa, Umar Faruk ya kaita dan zana jarabawa, sunyi sai dai Zuby saida tayi qwalla saboda sarewa da tayi, a lokacin da suka tashi Umar Faruk ya zo d'aukarta tare da Khairat daya d'aukota daga wajen awo, suna jirar fitowarta wata mota ta fito daga cikin makarantar, babban mutum ne amma yana ganin Khairat zaune a motar ya fito daga tashi yazo inda take, tana ganinshi ta sauke glass d'in motar suka gaisa, mutumin ne yace "Hajia Khairat na ganki anan, lafiya daiko?"
"Lafiya lau wallahi, munzo d'aukar qanwata ne."
"Allah sarki, anan take jarabawar itama?"
"Eh, anan take."
"Masha Allah, to Hajia meye sunanta?"
"Me yasa kake tambaya?" cewar Khairat.
"Hajia aimu qasa muke dake, bamu cika samun irin wannan damar ba, ba kuma zanyi wasa da ita wajen kyautata miki kema."
"Zubeida..." kallon Umar Faruk tayi tace "sunan babanta?"
"Hamza, amma ai kinsan ba shine originale d'in ba." cewar Umar Faruk.
Murmushi tayi ta kalli dattijon tace "Zubeida Hamza."
"Shikenan Hajia, ki d'auka qanwarki taci."
Cewar Khairat "amma dai a dinga duba cancanta , idan za'a dinga bawa mutane irinmu saboda wani abu, to wanda basu da alfarma fa?"
"Hajia aike ba kamar kowa bace, amma insha Allah za'a kiyaye."
Lokacin Zuby ta fito, gaishe da dattijon tayi sai taga yana washe mata baki ba kamar idan suna cikin makaranta ba, baya ta shiga tana fad'in "sannu."
Khairat ce ta fara amsawa da "sannu."
Saida ya aje Khairat gida sannan ya wuce da Zuby gida....
*Bayan gama jarabawa*, da daddare Umar Faruk ya dubowa Zuby sakamakonta, tun a hanya ya kira ya fad'a mata taci écris, zo kaga murna da farin ciki, cikin qanqanin lokaci fad'awa kowa, Umar Faruk dai kallonta yake yana ganin kawai ta samune a sanadiyar Khairat.
*A gurguje*
Umar Faruk dai ya zage damtse sosai wajen yiwa Khairat magani da addu'a, kuma cikin ikon ubangiji komai yayi sauqi yanzu, sai ciwon qafafu da yan abinda ba'a rasa ba, sai dai bai d'auki kowane mataki ba ga tanti ko Zuby, idan har lokacin arziqinka yayi to ba fashi , duk da hankalinshi ba'a kwance yake ba amma ubangiji na bud'a mishi tako wace hanya, yanzu haka da taimakon Allah har an fara aiki a compganinshi daya siya, ga kuma shaguna da yanzun suma suke shigo mishi da kud'i, yanzu haka baya qarqashin kowa zaman kanshi yake shima yana cin gumin kanshi, yanzu haka yana nan ya siyi wani babban fili daf da gidansu har an fara gini dansu koma gaba d'aya ahalinshi, kuma duka 'yan uwanshi maza suna tare dashi suma suna cin arzik'i, sai dai kawai ace alhamdulillah, a wajen Zuby kuma baqin cikine ya isheta saboda rashin nasara akan maganin data saka mishi, shi kuma dama ya dogara ga Allah ne yasan babu abinda zai faru dashi dama, kuma har yau bai nuna mata komai ba, idan ka ganta kace cikin yan uku ne da ita, shi yasa ma uwarta ke kiranta da uwar uku wani lokacin.
Duk da lokacin da Khairat ta d'auka a gida bata son komawa gidanta, kuma kullum Umar Faruk sintirin zuwa gidan yake, yanzu haka *cikinta na wata na biyar*, amma idan ka ganshi za kace cikin wata hud'u ne, sai dai yanzu da dama ciwo yayi sauqi, musamman amai da rashin son cin abinci, yanzu duka tana ci kuma tana sha, sai dai matsalar Salim a yawon sakata damuwa, dan yaron yazo da raini sosai da rashin kunya, Mamie kullum cikin baqin ciki take akan yaron, sai tsirfa iri iri kamar mai ciki, zuciya kuma bata da qashi sai Allah yasawa Papa son yaron saboda yana ganinshi namiji ne, da wannan taskun kullum basa farin ciki, ga kuma karb'ar kud'i da yaron ke yawan yi, amma duk abinda ya nema Papa yi mishi yake.
Wani bala'i daya taso musu shine yad'uwar maganar Salim a kafafen sada zumunta da gidajen tv da redio, wannan abu sosai ya tab'a mutuncin Papa har saida ya kai ya daina fita waje, ga kuma kira daya sameshi daga jam'iyarsu wai an cireshi daga partie d'insu, bai damu da wannan ba ko kad'an tunda dama tunaninshi barin siyasa, maganganu marasa dad'i kawai ake a social media da gidajen radio, sai dai masoyanshi na alaqanta hakan da yarfe na siyasa, hakan ya sake tadowa Khairat tsohon ciwonta na qirji da ciwon kai, hakan kuma ya d'aga hankalin iyayen nata da mijinta, hakan yasa Umar Faruk d'amarar binciko gaskiyar alamarin, dan yanzu suma iyayenshi ne ba ita kad'ai ba.
*Yau* ma kamar kullum zaune suke a falon ana hira sama sama, hankalinsu ne ya koma kan tv saboda wani shiri da ake tattaunawa akan manyan mutane har aka d'auko misali da Papa, mai gabatar da shirinne yakewa d'aya tambaya da "to yallab'ai me zaka iya cewa akan wannan magana, ace shuwagabanni daya kamata ace muna koyi dasu kuma sune suke aikata bad'ala a doron qasa?"
Mutumin da aka tambaya ne ya gyara zama zai bada amsa Mamie ta kashe tv, Papa kuma qasa yayi da kanshi cike da takaici da kunyar iyalinshi, shiru da falon ya d'auka yasa Papa cewa cikin muryar nadama yace " kuyi hak'uri ku yafeni, ni naja muku wannan abun kunyar, haqiqa na bar muku abinda har jikokinku zasu ji kunya, yanzu ne nake qara tir da rayuwata, ku yafe min dan Allah, nasan na cutar daku."
Babu wanda yayi magana sai Umar Faruk yace "kuyi hak'uri Papa, wannan itace jarabawarku, kuyi qoqari ku cinyeta, insha Allah Allah ba zai kunyatar daku ba kuma zaku samu sakamako koda ranar gobe ce."
Salim ne ya shigo yana wasa da makullin tsandareriyar motar da zab'inshi ce wato *Prado*, kai tsaye dinning ya nufa yana bud'a kwanukan abinci, tsaki yaja ya juyo yana kallon Mamie yace "wai me yasa ne ni ake nuna min wariyar launin fata a gidan nan ne? nasha fad'a bana cin macca amma dole sai an dafa, to yanzu me zanci kenan?"
"Uwarka, nace uwarka kaji, marar kunya d'an rainin hankali." cewar Khairat dake b'antarar d'anyan mangaro.
Yunqurawa tayi ta tashi tsaye da nufin
taje wajenshi, da k'arfi ta koma ta zauna kamar an jefata saboda ciwon da qafafunta keyi, rik'e hannunta Umar Faruk yayi yana kallon fuskarta yayi ganin yanda take hararan Salim yasa ya kamata suka tashi ya kaita d'akinta, duk da abinda Salim ke fad'a tana so ta tsaya Umar Faruk ya hanata, saida suka shiga ya kwantar da ita ya rufeta sannan ya kalli fuskarta yace "qaninki ne fa, ki kama girmanki mana karya rainaki."
"Wallahi ba d'an uwana bane waccen banzan yaron, rainin wayonshi yayi yawa, kullum da kalar iskancin da yake zuwa."
Wani mayan kallo ya mata ya kwantar da kanshi a qirjinta yana sauke numfashi, shafa kanshi tayi tace "ya dai baby?"
D'ago kai yayi yana kallonta a marairaice yace "Khairat nayi kewarki sosai wallahi, dan Allah ki daure mu koma gida Khairat kona d'an rage zafi, wallahi na kusa kaiwa matakin qarshe."
"Karka damu zan koma." ta fad'a a tak'aice.
"Yaushe?" ya tambaya.
Kallonshi tayi tace "nan da sati d'aya, lokacin na qara warwarewa."
Rumgumeta yayi yace "Allah ya yarda baby, zanyi farin ciki da wannan ranar fiye da farin cikin da nayi a lokacin da aka kawo minke gidana."
Ya jima suna hira saida yaga bacci ya fara dibarta sannan ya shafeta da addu'a ya rufe mata d'akin ya fita, Salim ya samu gaban Papa yana fad'in "Allah idan ba tayi hankali ba zanyi maganinta a gidan nan, yanzu kawai ka bani wani abu nan zanje na samu wani abu naci, tunda a gabanka ake nuna min bana da mahimmanci kuma ka kasa d'aukar mataki, dan anga uwata bata cikin gidan."
Kallonshi kawai Papa yayi yace "yanzu kace baka da kud'in cin abinci a wajenka?"
"Eh, bana da." ya fad'a yana hararan Mamie.
D'auke idonshi yayi daga kan Mamie cikin akasi suka had'a ido da Umar Faruk, wata arniyar harara daya gabza masa yasa yaji gabanshi ya fad'i, kallonsu Papa yayi yace "saida safenku."
Tunda Umar Faruk ya sanar a gida da Khairat zata dawo hankalin Zuby ya tashi, dan gani take yanzu zai rage nuna mata kulawa, duk yanda zaiyi dare a gidansu Khairat baya wuce k'arfe 10:00, kuma bata gansu ba bare taga me sukayi, dan haka hankalinta ke kwance, nan ta fad'awa Mama abinda ke faruwa, ita kuma fad'a ta mata tace da tayi aiki da maganin data bata da ba za taji sha'awar dawowa ba.
**************
Tunda sukayi maganar dawowarta sai kuma ciwo suka dawo, ya kuma fahimci gidan ne bata san zama yanzu, dan haka yayi shirin d'aukar mataki akan hakan.
Da sallama ya shigo gidan ya samesu falo tare da likitan Papa dake dubata, ko gaisawa basuyi ba ya zuba ido yana kallonsu shima, likitan ne ya d'ago ya kalli Papa yace "a gaskiya bansan dalilin da yasa cikin ke haka ba, amma dai abinda zan iya fad'a muku anan shine, da zaran ta fara naquda ku gaggauta kaita asibiti dan a mata tiyata."
A duburburce Umar Faruk yace "me, tiyata, akan me?"
Kallonshi likitan yayi yace "eh tiyata, saboda ba zata iya haihuwa da kanta ba."
"Akan me, kaine keda iko akan haka da zaka fad'i haka? babu wanda ya isa ya fasa min mata wallahi, zata haihu da kanta."
Likitan Papa ya kalla yace "kafi kowa sanin wacece 'yarka, dan haka nidai na fad'a muku abinda ya dace, idan baku ji ba zaku wahalar da itane da d'an cikinta a banza."
Ficewa yayi su kuma suka zauna Mammie ce ta kalli Umar Faruk tace "duba kaga abinda cikinta keyi fa."
Da sauri ya sunkuya gaban Khairat ya janye rigarta yana kallon cikinta, waro ido yayi cike da tsoro saboda ganin yanda dan cikinta ke motsi, bawai motsi bane kamar kowane, wannan kamar yana neman hanyar fitowa ne ta hanyar parka cikin nata ya fito, yawo kawai yake mata ko ina, ita kuma harta darrahe ta barwa Allah sai ruwa kawai dake fita a idonta, kallonta yayi yace "kiyi hak'uri Khairat, nasan zaki sha wahala, amma dole ayita ta qare."
Wasu hawayen ne suka sake bulbulo mata ta qara qamqame hannunshi, girgiza mata kai yayi alamar ta daina kuka, cikin muryar kuka cike da tausayin kanta tace " *Umar Faruk*."
Kallonta yayi sosai dan shine na farko tunda sukayi aure da yaji sunan Umar Faruk a bakinta, ci gaba tayi da cewa "ni kad'ai nasan me nake ji a jikina, na wahala iya wahala, nasan jarabawa ce daga Allah, wataqila had'e da hukuntani akan kurakuraina na baya, Umar Faruk bana jin zan rayu saboda azabar nake sha, amma ina so kamin alk'awarin zaka kula min da abinda zan haifa idan Allah yasa ya fito duniya, ina so ka bawa abinda zan haifa tarbiyar da ban samu ba, ka yafe min Faruk akan komai dana maka."
Hannayenta tasa ta janyo kanshi ta had'a goshinsu waje d'aya tana kallonshi tace "ina sonka Umar Faruk, ina qaunarka fiye da abinda yake cikin nan nawa."
Rintse ido Umar Faruk yayi hawaye suka zubo mishi ya d'an kawar da kanshi gefe kafin ya kalleta cikin kukan da bai tab'a irinshi ba yace "me yasa Khairat, me yasa zaki soni fiye da yanda kike son abinda yake cikinki? me yasa ba zaki kalleni a matsayin wanda yayi sanadiyar shigarki wannan halin, Khairat ban cancanci wannan soyayyar ba, ko kad'an ban cancanci wannan soyayyar ba Khairat."
Ya qarashe da sake fashewa da kuka, Mamie Mammie Papa duka babu wanda bai zubar musu da hawaye ba, saida suka ci kukansu babu mai rarrashi kafin Umar Faruk ya goge nashi hawayen ya tashi tsaye, kamata yayi suka nufi d'akinta ya kalli Mamie yace "dan Allah kuzo."
Bayanshi Mamie tabi saisu Mammie da yace ma "ku tayamu da addu'a."
Suna shiga d'akin ya zaunar da ita qasa ya sata tsakiyar qafafunshi, janyota yayi jikinshi sosai yasa bakinshi a kunnanta ya fara sambad'a mata karatu, tun yana karatun tana d'an motsi a hankali harta fara turmushe turmushe, Mamie ya kalla yace "ku kawo ruwan nan dana kawo tana sha."
D'aukowa Mamie tayi ta bashi ta koma gefe sai addu'a take duk wacce tazo bakinta, koda ya watsa mata ta kwamtsa qara tare da qoqarin fincikewa daga jikinshi, wani d'an banzan rik'o da yayi mata saida ya rufe idonshi saboda yasan zata wahala haka ma d'an cikinta, ko kad'an bai saurara mata ba haka ya dinga karatu da watsa mata ruwan nan, kuka take cikin gumjin murya ana fad'in yayi hak'uri zamu fita amma bai saurara ba, saima cewa da yayi "aina fad'a muku ku fita a jikinta lafiya kafin aji kanmu amma baku ji ba."
Turmuje turmuje take sosai tana kokawa dashi amma ina, har saida takai kayan jikinta sun fita saboda bala'i shima kuma ta yaga mishi riga, idonta ne sukayi jawur dasu kamar wuta, cikin muryar shan wahala akace "zamu fita, wallahi zamu fita har abada, ka fad'a mana ta ina kake so mu fita?"
Cikin d'aga murya yace "ta hancinta, kuma bana so ku cutar da ita, sannan kumin alk'awarin ba zaku sake dawowa gareta ba."
"Munyi, munyi wallahi, amma fa zamu...."
Shurin da sukayi yasa yace "amma me, me zakuyi?"
"Gaskiya zamu koma kan masu hannu a turo mu, saboda munsha wahala."
"Karku fara wallahi, ku barni dasu kosu waye ni zanyi maganinsu, in kuma baku ji ba to zaku mutu wallahi, kunji na rantse."
Wata irin bille bille Khairat ta fara ga wata irin majina dake fita ta hancinta kamar an kunna panpo, a cikin haka kuma take had'awa da atshawa kuma idonta rufe, saida tayi atshawa ba adadi kafin ta fad'i kwance amma kuma majinar nan naci gaba da fita daga hancinta ba qaqqautawa, gyara mata kwanciya yayi ya kalli Mamie yace "Alhamdulillah, yanzu sun fita, kuma insha Allah ba zasu sake dawowa ba da yardar Allah, yanzu ku canza mata kaya saiku barta ta samu bacci."
Yana fad'a ya d'auketa ya mayar kan gado sannan ya fita, su Papa ya samu har yanzu suna tsaye cirko cirko, kallonsu yayi yace "karku damu, ta samu lafiya da izinin Allah."
Yana fad'a ya fita su kuma suka shiga d'akin Khairat dan ganin halin da take ciki, saida ya shiga mota ya kula da rigarshi, a haka yaje gida yana fita ya fad'a cikin gidan yana d'an kare rigarshi, kai tsaye d'akin Zuby ya shiga bai kula kowa dake zaune ba, zaune ya sameta tana shan exotic d'in daya wadatata dashi, rigarshi ya cire yana shirin cire wandon Zuby tace.....
_To Hajia Zuby Allah yasa karki sake b'ata ran mazaje._
29/08/2019 à 14:33 - Meerahgee❤: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*JIHADI*
_Umar faruk_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛
_Bismmilahir-rahman-rahim_
6⃣0⃣
"Halan yau mahaukaciyar ta keta maka kaya, dan nasan dai ba fyad'e zaka mata ba, kuma ma ko hakane ai ba kaine farau ba bare ta tashi hankalinta, hasali ma kai *jihadi* kayi."
Da wani irin matsanancin yanayin dashi kanshi baisan ya shiga ba yake kallonta, kasa cire belt d'in yayi ya matso kusanta yace "Zubeida, anya kina da hankali kuwa, kinsan me kika fad'a, Khairat d'ince kike kira da mahaukaciya? to bata haukace ba kamar yanda kuka shirya, kuma da yardar Allah duk abinda kuka shirya kanku zai dinga komawa, tunda har yanzu kun kasa gane itace gaba daku kuma ta muku nisan daba zaku tab'a kamata ba, to bara yau na fad'a miki abinda kullum nake dannar zuciyata da karta fad'a miki haka."
Sake matsowa yayi kusanta yace "kina cewa nayi jihadi ne na auri Khairat, to ki sani Zubeida kema a halin yanzu *jihadi* nake naci gaba da zama dake, kiyi tunani akan abinda na fad'a miki dan babu qarya a maganata, kuma ki sani akwai abubuwa da dama dana sani a game daku Zubeida amma na shanye, badan komai ba sai dan nasan Allah ma baya kama bayinsa da laifi d'aya tak, zaki ga bawa na laifi iya laifi amma sai Allah ya d'aga masa qafa, wala'Allah ya gyara a gaba ko kuma a mishi kamun kazar kuku, to akan me ni ba zan iya yi muku uzuri ba, amma kwata kwata kun kasa gane haka, to wallahi ba zan qara shiru ba, *Khairat ta fiki komai Zubeida, ta fiki zuciya mai kyau, ta fiki halaye masu kyau, ta fiki girma da matsayi ba'a wajena ba har a wajen mutane, kuma da yardar Allah babu abinda zai sake samunta ta sanadiyar jahilai irinku.*"
"Zubeida, ina son Khairat, ina mata son da ban tab'a ma kowa irinshi ba, kuma wallahi zamu zauna da ita muyi rayuwa a tare, ki sani wannan ne na qarshe da zan sake miki uzuri akan banzan quruciya da tab'argazarki, nasan dole zaki ji zafin kalamaina, amma Allah ma yaga zuciyata na kasa jura ne, kuma nayi iya qoqarina na b'oye duk abinda yake damuna."
A fusace ya fice daga d'akin ya nufi d'akin Khairat kamar yanda yake yi duk lokacin da ranshi ya b'ace, saida ya kai tsakiyar gidan ya tuna ko riga babu a jikinshi, bai damu ba haka ya ciro makullanshi ya bud'e d'akin ya shiga ciki, kwance yayi akan gado ya rufe ido yana tuno 'yar rayuwar da sukayi da Khairat da farin cikin daya samu a tare da ita, ya jima d'akin kafin ya shiga douche yayi wanka ya fito ya shirya, fita yayi baibi takan kowa ba bare wata Zuby.
Yana kan hanyarshi ta zuwa ma'aikatarshi yaga motar Salim a gabanshi, wani banzan kallo yama mota kafin ya fara binshi a baya zuciyarshi na raya mishi abubuwa da dama, yana binshi har saida ya shiga wata unguwa da babu mutane sosai, qofar gidan da yayi parking yasa Umar Faruk fitowa shima daga mota, yana kallo ya shiga cikin gidan sai dai bai iya binshi ba saboda yaga irin gidan nanne da an bud'e qofa za'a san wanda ya shigo, yana nan tsaye harya fito tare da mahaifiyarshi Odette, tare suka shiga mota suka d'auki hanya kuma, binsu yayi har suka sauka unguwarsu Khairat amma nesa da gidansu a gidan wani d'an siyasar mai neman kujerar Papa, murmushi yayi ya d'auki glass d'inshi mai baqaqen ido yasa, sake kallon qofar gidan yayi yace,
"Yanzu ainihin maganar zata fito fili, yanzu ne zanyi *jihadin* gaskiya, dan dole saina dawo da farin cikin masoyiyata da iyayenta."
Wani murmushin ya sakeyi saboda ganin Salim ya fito ya shiga mota yayi gaba, cewa yayi "da sannu kai zaka warware min komai."
Binshi yayi ya kira wayar Aliyu, yana d'auka ya fad'a mishi inda yake yace ya sameshi, ba b'ata lokaci Aliyu ya sameshi saboda yana da abin hawa, sauka yayi daga motanshi ya shiga motar Umar Faruk, kallonshi yayi yace "yah Umar lafiya kace na sameka nan?"
Nuna mishi motar Salim yayi yace "kaga wannan motar?"
"Eh na gani."
Nuna mishi Salim yayi dake cin abinci a restaurant d'in yace "kaga mai ita can, ina so ne daga yanzu ka fara bibiyarshi, kuma ina so na dinga sanin duk inda ya kasance."
"Shikenan yah Umar, insha Allah zanyi yanda kace."
Nan ya bar Aliyu shi kuma ya koma unguwar da Odette take, kasancewar yana da kati hakan yasa ya wanke mutanen unguwar ta hanyar tambayarsu wacece Odette, cikin tsoro suke fad'a mishi duk abinda suka sani a kanta, daga nan ma komawa yayi gidan *Alhaji Sani Saley* ya kasa ya tsare har saida yaga fitowar Odette.
Ganin a qasa take tafiya yasa ya d'an jira yaga inda zatayi, yana kallonta kuma sai yaga mota biyu sun fito daga cikin gidan, mai gadi ya gani ya rufe qofar ya zauna qofar gidan akan kujera, saida yaga b'acewarsu sannan ya fita daga motar ya nufi wajen mai gadin, sallama ya mishi suka gaisa kafin ya kalli hanyar da Odette tabi yace,
"Abokina dan Allah tambaya nake, wannan matar data fita ba Odette bace kuwa?"
Ya rik'e sunan ne tun ranar da Papa ya fad'a, kasancewar mai gadin mai hankaline yasa yace "itace, lafiya, ka santa ne?"
Ganin bazai bada matsala ba yasa Umar Faruk gyara tsayuwa yace "sosai ma na santa, tana zuwa harnan kenan?"
"Eh, tana zuwa nan, ai mutuniyar mai gida ce sosai."
"Ok na gane, na gode sosai, amma naga mai gidan ya fita, shin kasan inda yayi?"
"A'a, ban sani ba gaskiya."
"Shikenan na gode."
Hannu ya bashi kafin ya wuce, wani abokinshi ya kira mai sunan *RB* ya nemi sani akan *SS* wato Sani Saley.......
*Yanzu fa Umar Faruk zai fara nashi wasan*
Kwana ma wuya yakewa Umar Faruk yanzu sobada binciken da yasa gaba, kuma cikin ikon ubangiji ya tara hujjoji masu yawan gaske akan Sani Saley da Odette, dan ko rintsawa bayayi sai bincike da tambaya, ya samu masaniya tun daga yanda Odette ta fara harkarta har zuwa yanzu, kuma komai rubutashi yake yana copie d'inshi a wayarshi.
*Yau* ma kamar kullum tafe yake cikin sabuwar motar daya siya izuwa wani gida da wajen bincikenshi a fad'a mishi zai samu masaniya akan duk abinda suke shiryawa game da maganar Salim, yana zuwa daidai kwatancen ya fito daga mota ya nufi gidan, a hankali ya tura qofar sai yajita a rufe, tsaye yayi yana d'an kalle kalle ya hango wani yaro, qarasawa yayi yana fad'in "sannu yan samari, dan Allah masu gidan nan basa nan ne?"
Kallonshi yaron yayi yace "ai duka mazane ba mata."
Da mamaki ya kalli yaron amma saiya share, shafa kan yaron yayi ba tare da yayi magana ba ya koma qofar gidan, d'aga kai yayi ya kalli katangar yaga bata da tsayi sosai, yar dariya yayi a ranshi ya tuna ranar daya ma su Musa kutse a cikin gidansu, kallon unguwar yayi yaga ba hayaniya sosai, tsalle yayi ya rik'e katangar ya haura ciki, yana direwa ya tsaya yana kallon gidan, idonshi ne ya sauka kan takalmin dake qofar d'akin, da sauri ya qarasa jikin bishiya ya b'uya yana jiyo tashin muryoyi, cikin sand'a da dubara ya dinga takawa har ya kai bakin window ya leqa, abinda ya gani shi yasa shi saurin yin qasa yana waro ido waje da tsananin mamaki.....
Da d'an k'arfi ya furta "su Musa, taya hakan zata faru, mutane dake kurkuku me zai kawosu nan, ko dai anyi bellynsu ne?"
Sake leqawa yayi ya tabbatar sune dan haka kawai ya qarasa qofar ya bud'e sakatar qofar a hankali ya fita, da hanzari ya bar unguwar yana tunanin abinda ya gani, Khairat ya kira wacce ke zaune gaban Mamie ta aje mata farfesun kaji tana ci😭(ina ci my Hajiata), koda ta d'auka yace ta taimaka mishi da lambar wannan gendarme d'in daya qwamushe su Mama, yarda da kanta yasa ba tayi tunanin komai ba ta aika mishi da lambar.
Cikin sa'a ya samu lambar Abdul waid, koda ya fad'a mishi wanene shi ya samu tarba ta musamman, tambayarshi ya fara yi ko yasan wanda sukawa Khairat fyad'e? amsar dai itace "eh, lokacin dana dawo nan da aiki ake nuna min su." nan ya tambaye ko zai iya sanin shekara nawa aka yankewa su Musa, nanma fad'a mishi yayi yaji ko shekara basuyi ba a cikin shekarun da aka d'iba musu, d'orawa yayi da "amma kuma taya za'a sakesu bayan basu cika wa'adinsu ba, taya za ayi irin haka?"
Nan Abdul waid ya fad'a mishi basu da laifi a ciki daga samane aka yanke hukuncin a sakesu saboda wani babbane yazo bellynsu, tambayarshi yayi "wa yayi bellynsu?"
"Sani Saley ne." cewar Abdul waid.
Suna gama waya yana ci gaba da tafiya kuma Aliyu ya kirashi, yana dauka nanma ya fad'a mishi yau ma gasu a gidan nan dake unguwar *Lazare*, da mamakin abinda ke kai Salim gidan Umar Faruk yace " kaci gaba da saka masa ido, an jima zaka kawoni gidan."
****************
Tafe suke a mota shi da Aliyu suna yar hira har suka isa wannan gidan, saida suka fito Aliyu ya nuna mishi sannan ya shiga gidan cikin baqaqen kaya, sallama yayi matar dake zaune ita kad'ai ta amsa mishi, sai dai a tsorace take sosai musamman da Umar Faruk yace "sannu Mama, sunana Faruk, kuma ni jami'in bincikene na farin kaya, nazo ne zan miki wasu tambayoyi, fatan zaki bani hadin kai ba saita kaimu ga tafiya dake ba offishinmu."
Cikin saurin kuka matar ta fashe da kuka tace "na shiga uku ni *Salmu*, dama nasan wata rana sai Salim ya jawo min magana, yallab'ai wallahi zan fad'a maka gaskiya, ba saika tafi dani ba."
Kujera Umar Faruk ya janyo ya zauna tare da fad'in "bismillah." a zuciyarshi kuma istigfari yake akan qaryar da yayi yanzun...
_Hummmm, ranar fa ta kusa zuwa._
29/08/2019 à 14:33 - Meerahgee❤: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*JIHADI*
_Umar faruk_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛
_My sweet and lovely Dotana *(Khadija Journaliste)*, ina tayaki murnar fara wannan novel mai sunan *Rayuwata ce*, a gaskiya na jinjina miki sosai musamman yanda kika d'auko yanda ya kamata iyaye su tarbiyanci yaransu, Allah ya baki ladar fad'akarwar daki kayi niyya._
_Bismmilahir-rahman-rahim_
6⃣1⃣
"Ina jinki Mama." ya fad'a yana fito da qaramin littafin ajiye muhimman bayanai a aljihunshi da alqalami.
"Ina so nasan meye tsakaninki da yaron nan Salim da yake yawan zuwa gidan nan?"
Cikin muryar kuka tace "Salim, Salim dai d'ana ne, ni na haifeshi, kuma maraya ne mahaifinshi ya rasu, matsalar Salim rashin jin maganata, a lokacin da yazo min da maganar zaije a matsayin d'an wani babban mutum saida na hanashi, amma sam yaron nan yak'i jin maganata, amma bansan komai ba wallahi."
Shiru tayi haka ma Umar Faruk yana rubutun basaja kamar gaske, jin shiru yasa ta marairaice tace "dan Allah yallabai ka taimakeni kamar yanda Allah ya taimakeka, ka rufa min asiri karka kama yaron nan dan Allah, wallahi shi kad'ai gareni kuma shima ni kad'ai gareshi, idan ka taimaka mana wallahi zanja mishi kunne, kai har garin ma zamu bari na mayar dashi wajen dangin mahaifinshi, dan Allah ka taimaka."
Kallonta Umar Faruk yayi yace "Mama, kinsan girman laifin da d'anki ya aikata kuwa? ya yarda ya zama d'an wanda baiji ba bai gani ba, hakan ya ruguza rayuwar wannan bawan Allah, ya kuma dagula farin cikinshi dana iyalinshi, taya kike tunanin zai samu sassauci?"
"Dan Allah ka taimaka ka min rai, wallahi ba zai sake ba, kuma talauci na daga cikin abinda yasashi aika hakan."
Saboda yanda take kuka yasa yace "shikenan Mama daina kukan, insha Allah zamu duba al'amarin muga yanda za ayi."
"Na gode yaro, na gode sosai, Allah ya saka maka da alkairinsa."
Kiran daya shigo wayarshi ne yasa yaja "ameennn." d'in, fito da wayar yayi ganin lambar babanshi na uku ne ya kira (Bala) yasa ya tashi tsaye tare da d'aukar kiran, abun mamaki muryar macece tace "Hello Umar Faruk ne?"
"Eh nine."
"Dan Allah kayi sauri kazo, Alhaji ne yace a kiraka kazo."
"Ince dai lafiya ko?"
"Ba lafiya, jikinshi ne yayi qamari, kuma ruwan addu'a daka bayar ma ana bashi sam yau yak'i ya karb'a."
"To shikenan, gani nan zuwa."
Yana fad'a ya kashe wayar ya fita ya manta ma da inda yake, da azama ya shiga motar yaja suka d'auki hanya, Khairat ya kira tana d'auka yace "baby, Salim yana gidane?"
"Salim kuma, lafiya?" ta tambaya da mamaki.
"Lafiya lau, ki duba min dan Allah.
Mamie ta kalla dake gefenta ta tambayeta, "yana d'akinshi har yanzu." cewar Mamie.
Maida mishi tayi da "yana d'akinshi bai fita ba, lafiya dai ko?"
"Lafiya lau, dan Allah zaki iya samo min lambarshi?"
"Baby, lafiya, me yake faruwa ne?"
"Babyyyy, kiyi abinda nake fad'a miki mana."
"To naji." Mamie ta sake kalla tace "kina da lambarshi wai?"
"A'a, me zanyi da lambarshi ni kam, sai dai ki tambayi mahaifinki."
"Babu mai lambarshi a gidan nan sai wada yake zaune dominshi, bara na tambayar maka."
"Yawwa 'yar aljannata, ina jiranki."
Cikin mintuna qalilan ta tura mishi lambar bayan ta karb'a daga wajen Papa, yana ganin lambar yasa Aliyu ya d'auketa a wayarshi sannan yace "kasan dubara da za kayi mishi irin taku ta matasa da za tasa ya kai kanshi wannan sabon filin dana siya wanda ke *Yantala*."
Akan titi ya tsaya ya saukeshi Aliyu na mamaki da tunanin yanda zaiyi ya kaishi wajen, da qyar ya samu dubara ya kira lambar, ba jimawa ya d'aga Aliyu ne yace "yane Baabaa, ka fita ko kana gida?"
Fad'uwa kawai gabanshi keyi, cike da qasaita Salim yace "waye kai kuma?"
Cikin murd'awar 'yan ciki Aliyu ya dake yace "kana nufin baka d'auki muryata ba kome?"
Cikin d'an sakin fuska Salim yace " *Rabilou* kaine?"
Cike da dakiya Aliyu ya nuna mishi shima matashin zamani ne yace "shege baabaa, nine mana, dan Allah kazo ka d'aukeni ina nan yantala."
Cike da isa Salim yace "kai ina motar taka take, mema ya kaika can unguwar?"
"Motarce ta bani matsala, yanzu haka ma da wayar makaniken ne na kiraka tawa ba caji, abinda ya kawoni kuma idan kazo na fad'a maka."
A gadarance yace "Ina kan hanyar kita daga gida, ka jirani kawai."
"Sai kazo." ya fad'a ya kashe wayar, wata ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi, dan ba qaramin sauqi bane cika aikin Umar Faruk, da azama ya tari taxi ta kaishi can kafin shi ya isa wajen.
***************
Umar Faruk na barin nan gida ya wuce dan amsar wasu ruwan addu'a a wajen Baba, da karsashi ya shiga gidan da fad'in "assssss..."
Sallamar tashi ce ta maqale a maqoshi saboda ganin hasken fila a kewayen Khairat alamar akwai mutum a wajen, a hankali ya sulala yana takawa danshi gani yake Khairat ce zata masa bazata, leqawa yayi ta katanga sai yaga Zuby ce ke barbad'e a qofar d'akin, mamakinshi bai yawaita ba saboda ba yaune farkon ganinshi ba, dan haka ya qura mata ido yana kallo harta gama zata juyo yayi saurin cewa,
"Sannu da aiki 'yar gidan d'an me ganye."
😂😂😂😂😂😂
Wani irin fad'uwa ne gabanta yayi had'e da kad'awar 'yan cikinta, tsabar tsoro ne yasa ta jefar da ledar maganin da wayar hannunta, kasa kallonshi tayi tunda tasan ko waye, a hankali ya zagayo yana kallonta harya sunkuya ya d'auki kayan data zubar, janyo hannunta yayi ya bata kayan yana ci gaba da kallon fuskarta, ganin dai ta kasa cewa komai yasa yace,
"Wannan itace damarki ta qarshe Zubeida, da ace a abinci nane na samu kina zubawa kamar yanda na tab'a gani, to da zan iya yafe miki kuma na zuba miki ido, danni yanzu ban damu da rayuwata ba kamar yanda na damu data wasu, wasun kuma ba kowa bane face iyalina, ba zan iya miki uzuri ba Zubeida dan kina qoqarin cutar da wacce tafi rayuwata mahimmanci ce, akanta kuma sai inda k'arfina ya qare, Zubeida ki gafarceni, amma dole zan d'auki matakin da nasan ba zai miki dad'i ba, na d'aga miki na miki uzuri duk saboda tunanin zaki shiryu wata rana, amma matsalar tana ga mahaifiyarki ne, ni kuma ban isa na rabaki da ita ba, saboda uwa uwa ce, dan haka zan saukewa kaina nauyin nan, kije *na sakeki saki d'aya*, ban sakeki saboda Khairat ba sai dan na fahimci babu Allah a tare dake, kuma ina neman alfarma da karki fad'awa kowa dalilin rabuwarmu, dan ke zaki fi cutuwa da hakan, Allah ya sadamu da alkairinsa, ki kula min da yarona ko yarinyata."
Juyawa yayi zai fita tayi saurin rik'e qafarshi ta zube qasa tana kuka tana fad'in "yah Umar kamin rai, dan Allah kar kamin haka, wallahi na tuba ba zan sake ba, wal....."
Rufe mata baki yayi ya sunkuya yace "zaifi miki kiyi shiru kar mutane suji, zaifi kyautuwa ki bar gidan nan ba tare da kowa yaji ba."
Fit ya fice ya koma d'akin Baba, sallama yayi shiru dan haka ya tura qofar, jin ta bud'e yasa ya leqa amma Baba baya ciki, da hanzari ya shiga ya nufi wajen ruwan addu'a da yake da tabbacin sune, dauka yayi ya fito ya rufe d'akin, motarshi ya hau kai tsaye ya nufi gidan Bala.
***************
Koda yaje ya samu jikin ya tsananta sosai, tallabo kanshi yayi da niyyar bashi ruwan, yana zuba mishi a baki ruwa suka dinga gangarowa suna fita daga bakinshi, aman da Bala ya fara tare da jini ne yasa Umar Faruk saduda ya kalleshi a matsayin gawa, danya tabbatar wannan karan aljanu sun raina masa hankali, dan lokacin farko daya fara taimakawa Bala sai suka nuna sun tafi, amma ganin hakan a yanzu ya nuna mishi suna cikin jikinshi kuma sun mishi raunin da harya tab'a zuciyarshi, da qyar Bala ya rik'e hannun Umar Faruk ya fara magana cikin rawar jiki yana fad'in "ka ka....ya femin.....ka roqar min..."
Bai qarasa ba ya fara da "Ashhadu an la'ilaha illalah.....tare da taimakon Umar Faruk ya qarasa karlmar shahada.
Koke koke iyalinshi suka fara amma dole dai ayi hak'uri.
😭😭😭😭😭😭 *Zuby anyi rashin uba*
Dare ne dan haka suka d'aukeshi izuwa asibiti dan a ajeshi wajen ajiyar gawa, tun a hanya Aliyu ya kira ya fad'a masa Salim na kan hanyar zuwa wajen, dan haka koda ya ajesu ya taka mota da k'arfi ya isa wajen, kuma zuwanshi yayi daidai da isar Salim wajen yana kiran lamba da Aliyu ya kirashi, Aliyu na ganin motar Umar Faruk ya fito daga wajen daya b'uya danya kalli drama, fitowa yayi daga mota ya tunkari motar Salim, shima yana ganinshi fitowa yayi da niyyar yi mishi magana, da fara'a Umar Faruk ya bashi hannu suka gaisa yana fad'in,
"Petit frère (qanena), yana ganka nan?"
Jin Umar Faruk bai saki hannunshi ba kuma yana nufa dashi wani kango yasa yace "ina jiran wani ne anan."
A lokacin har sun shiga ciki, sakin hannunshi yayi ya tsaya bayanshi, juyowar da zaiyi ya d'aukeshi da mahaukacin marin da yasa ya fad'i kwance kamar sumamme....
_Hhhhhhhhhhh, akwaita fa_
A firgice Salim ya tashi zaune yana dafe da kunci yana ja da baya yana kallon Umar Faruk dake matsowa kusanshi, "kai, meye haka, kana da hankali kuwa, kasan me kayi, ni ka mara? wallahi zaka....." bai qarasa ba Umar Faruk ya matso kanshi ya shaqo wuyan rigashi, jayoshi yayi qiiiii a qasa har saida ya kaishi gaban wani dakali sannan ya zauna ya sashi gaba yana qara had'e rai, kukan da Salim keyi ne yasa daka mishi tsawa yana fad'in "yimin shiru."
Tsaf Salim yayi shirun yana kama baki, a kausashe yace "tambayarka zanyi, kuma ina buqata sanin gaskiyar al'amarin, idan kuma kamin qarya, wallahi saika gwamaci kid'a da karatu."
Kai kawai Salim ke d'agawa alamar toh, cikin daga murya yace "kana jina?"
"Eh, ina jinka, wallahi ba zan maka qarya ba."
"Da kyau." Umar Faruk ya fad'a yana shafar fuskarshi da hannu d'aya, d'aya hannun kuma ya ciro wayarshi ya dannan wajen records d'in murya kafin ya d'ora da "naje har gidanku, kuma na gana da mahaifiyarka ta fad'a min komai, dan haka abinda nake son sani daga gareka shine, ya akayi ka shirya duk abinda aka shirya, sannan su waye masu hannu a ciki?"
Gyara zama yayi yana shafar kuncinshi dake mishi zugin zafin masifa ya fara da "wallahi son kud'ina ne ya jamin nayi duk abinda nayi, mun fara had'uwa da Odette ne a unguwarmu taje gidan wata qawarta 'yar fara, itace ta fara min magana tace wankana ya birgeta, na nuna mata jin dad'ina saita d'auki kud'i ta bani, daga nan duk lokacin da tazo saita nemeni mun gaisa, shine wata biyu daya wuce tazo min da maganar tana so ta sani wani aiki, nan ta fad'a min zanje gidan Mani Bukar a matsayin d'an da suka haifa bata hanyar aure ba, amincewar da nayi yasa ta fara kaini asibiti aka min gwajin da ake so yazo d'aya dana Mani Bukar, cikin ikon Allah sai jininmu yazo d'aya amma sauran qwayoyin hallitarmu sunsha banban, nan ta sanya likitan ya rubuta duk wani gwaji ya zama iri d'aya tsakaninmu ta yanda zan zama kamar d'an cikinshi, kuma bata tsaya nan ba saida ta ziyarci asibiti har hud'u wanda tasan Mani Bukar zai iya tuntub'a idan har bai yarda da abinda muka zo mishi dashi ba, daga cikin likitocin da Papa ke huld'a dasu harda likitanshi na gida daya yarda dashi fiye da kima, hakan yasa ta had'a takardu na qarya da zasu nuna ni d'anta ne kuma jinin Mani Bukar, kuma koda aka kawoni ma muka je asibiti wannan sakamakon qaryar aka fad'a mishi da yasa na zama d'anshi."
Shiru yayi yana zare ido yana kallon Umar Faruk, ganin yana kallonshi yasa yace "ina jinka, baka fad'a min masu hannu a ciki ba."
"Odette, itace alhakin shirya komai, amma dai nasan tana aiki da Sani Saley."
"Bayansu baka san wasu da take mu'amula dasu ba?"
"Gaskiya ban sani ba, amma dai akwai wata mata da suke zuwa tare da 'yar fara, ranar ma dana kai Odette gidan Sani Saley na tarar da wannan matar tare da 'yar fara, sai kuma wasu samari guda hud'u, naji da kunnuwana suna magana akan wani shiri da zasuyi akan Mani Bukar, amma bansan ko menene ba."
"Kenan baka san waya tura maganar kai d'an Mani Bukar bane a social media?" cewar Umar Faruk.
"Na sani, wannan samarin ne, kuma naji suna cewa zasu tattaro sauran matan da Mani Bukar yayi alaqa dasu."
Hararanshi Umar Faruk yayi yace "kar kamin qarya fa."
"Wallahi ba qarya bace, basa doguwar magana idan ina wurin."
"Kenan su sukace ka dingawa iyalenshi iskanci da shaqiyanci?"
"Eh, saboda suna so na baqantawa matarshi rai da Khairat, kuma wannan matarce tace na dinga yin haka, amma duk kud'ad'en da nake amsa nine keyin gaban kaina saboda na samu na fitar da kaina kafin ta kwab'eme mumu."
"Wacece matar?" ya tambaya a daqile.
Shiru yayi alamar tunani kamar kuma an tsokaleshi sai yace "yawwa na tuna, sunan *Asma'u*."
Wani bazawarin murmushi yayi na gefen labb'a, tsayar da d'aukar yayi a wayarshi sannan ya tashi tsaye yana fad'in "bansan ko zan iya taimakonka ba idon doka tazo hawa kanka, dan haka kayi ta kanka."
Ficewa yayi ya samu Aliyu suka d'auki hanyar gida, kiran Khairat ne ya shigo wayarshi ya d'auka,
"Ka kyauta baby, wuni d'aya har ana shirin kwanciya bacci amma ka kasa zuwa gaka matarka da yaronka."
Cike da kasala yace "ayyah baby, kiyi hak'uri ki yafe wa wannan hamagon mijin naki, yanzu haka a hanya nake zanje gida, abubuwa sun faru da dama yau d'in nan, amma dai zuwa gobe da safe nasan zakiji wasu labarai marasa dad'i."
"Subhanallah, meye faru baby?"
"Um um, ba yau ba, saida safe zan fad'a miki insha Allah."
Cikin kukan shagwab'a tace "yanzu kenan ba zaka zo ka ganni ba, nifa ina son ganinka."
Cikin rikitaciyar murya yace "na fiki son na ganki, kin manta yaushe rabon damu had'u ne? aiki shirya kawai, amma idan na kamaki wallahi dole yarona ya samu ingantanccen abincinshi yaci koya samu kuzari."
"Kai baby , wane irin abinci kuma?"
Saida ya d'an cije lips kamar yana gabanta yace "wannan sirri ne, amma idan na daukoki kika dawo gidana, to zaki sani."
Cikin wani kukan shagwab'ar tace "hum hum, wallahi ni har kasa na fara jin tsoron had'uwarmu, dan kasan fa ba 'yar qaramar jarumta nake yi ba wajen d'aukarka, amma yanzu nasan zaka sausauta min saboda abinda ke cikina."
Darayi yayi yace "ashe ana jin maza dauriya kawai akeyi, to karki damu, jarumin mijinki zai dinga sassauta miki, kiji dad'i abinki *maini*."
"Yawwa yaron kirki, ina sonka."
"Nima ina sonki alkairina, saida safe."
Yana kashe wayar ya kalli Aliyun da yake kallonshi kamar wani gunki, maida hankalinshi yayi ga tuqi yana fad'in "yadai Aliyu, da matsala ne?"
Ajiyar zuciya ya sauke yace "gaskiya da matsala."
"Tame?" ya fad'a yana kallonshi.
Gyara zama yayi yace "yanda naji kuna farin ciki kai da aunty Khairat, saiya qara min son aure a zuciyata wallahi."
Murmushi kawai yayi suka ci gaba da tafiya, saida suka kusan kaiwa gida sannan yace "kana son aure kenan?"
"Ina so, amma kasan ba lallai malam yamin ba."
"Me yasa?"
"Saboda nayi qarami."
Daga gira yayi sama yace "a hakan, kana shakara ashirin da d'aya ne za ace kayi qarami, gashi kuma soyayyar wasu ma na birgeka, kaga indai kana so ni zanyiwa malam magana, kuma kaima kasan zai fahimta, fatana kawai Allah ya had'a da mace ta gari mai tsoron Allah, faqat."
"Ameen yah Umar, ai yama had'a insha Allah."
"Toh , wacece wannan?" ya tambaya cikin 'yar dariya.
Shima cikin dariyar yace "wannan yarinyar mana, qanwar aunty Saratu, *Firdaussi*, gaskiya ina sonta, kuma tana da hankali sosai."
Shiru Umar Faruk yayi yana tuna kullum tazo gidan nan to ranar gidansu saiya shaida tazo saboda hidimar da take mishi, bugu da qari inhar zata gaishe dana sama da ita to zata sunkuya har qasa, da haka suka isa gida Aliyu ya nufi makwancinshi sai Umar Faruk daya shiga d'akin Baba ya fad'a mishi rasuwar Bala, fitowa yayi ya baroshi yana jimamin abin, d'akin Zuby ya kalla yaga amma yaga alamun tana ciki, tab'e baki yayi ya wuce d'akin Khairat, dan iba tilastashi za ayi ba ba zai tab'a maido da ita ba cikin sauk'i haka.
*Washe gari* da safe duka mazan gidan malam ya had'a kansu suka tafi wajen jana'izar Bala, Zubeida na d'aki bata san wainar da ake toyawa ba tanata had'a kaya, su kuma basu fad'a mata ba saboda ganin halin da take ciki, sun jima zaune acan kafin suka taso suka dawo gida, sai lokacin Zuby tayi niyyar barin gidan saboda tunanin malam ba zai bari ba, Umar Faruk na shirin shiga d'akin Mama Zubyta fito da kaya da ciki, Mama ce tayi saurin cewa "Ina zuwa haka Zubeida?"
Tana kallon Mama saita fashe da kuka, hankali tashe Mama tayi kanta da sauran matan gidan suna tambayar lafiya, durqushewa tayi a wajen tana ci gaba da kuka, haushi ne yasa Umar Faruk qarasa shiga d'akin ya zauna yasa kwanan abinci gaba yana jiran a kirashi, cikin kuka tace "sakina yayi."
"Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un." shine abinda uwayen suka fad'a a tare.
Baba ne yace "saki fa, Umar Faruk d'in?"
"Kai Umar." cewar Baba cikin d'aga murya.
Da "na'am" ya amsa yana fitowa daga d'akin, yana zuwa gabansu ya durqusa yana sauraronsu, "me yarinyar nan ta maka da zaka saketa a wannan halin, me yake damunka ne?"
Ba tare daya kalli Baban ba yace "Baba ku gafarceni, nasan hakan ba zai muku dad'i ba dama, amma nasan kunsan haka kawai ba zan d'auki wannan matakin ba ba tare da wani dalili ba, a gaskiya zamana da Zubeida ba zaici gaba da yiwuwa ba a haka, shi yasa na kawo qarshen abin."
"Meta maka, wane irin laifi ta maka da zaka yanke wannan hukuncin a kanta, kasan abinda zai iya biyo baya a dalilin abinda kayi?" cewar Mama cikin hushi.
"Babu abinda zai faru Mama, kuma fa Allah ne ya hallata aure ya kuma hallata saki, amma gata nan ku tambayeta idan nayi mata rashin adalci a wannan lamarin."
Maida kallonsu sukayi gareta Mama tace "me kika mishi ke kuma?"
Shiru tayi sai goge hawaye take, Baba ne ya qara "me kika mishi Zubeida?"
Kallon Umar Faruk tayi da tace bata mishi komai ba, amma ganin shima ita yake kallo, dan haka tayi shiru daga abinda taso fad'a, ganin ta kasa magana yasa ya mike yana fad'in "bance ki fita daga d'akinki ba ai, ki zauna anan harki haihu." yana fad'a ya fita daga gidan, hanya ta kama zata fita Mama tace "a'a babu inda zaki je, ki zauna kiyi iddarki kamar yanda yace."
Duk da cikin kuka take saida tace "Allah ya sawaqe, kenan ni gani marar zuciya, ya sakeni kuma yace na zauna nayi idda anan, to ba zai yiwu ba wallahi, ai nima da gidanmu, kuma kunfi kowa sanin inda ya d'aukoni, dan haka banga wanda ya isa ya rik'eni ba wallahi."
Zata wuce Baba yace "kash Zubeida, banji dad'in fitar wannan kalma daga bakinki ba, abinda muka fad'a miki yanzu ba fad'armu bane, wannan fad'ar ubangijinmu ne wanda shi yafi sanin daidai yake kuma tsara mana rayuwarmu, karki bijerewa umarnin Allah da manzonsa, hakan zai iya jefaki cikin hushin ubangiji, amma in kinga hakan bai miki ba to ga hanya nan ki wuce."
Suna kallo itama ta sulalata fita daga gidan tana kuka, Mama kuma haushin Zubeida ne ya kamata sosai, sai taji koba komai d'anta zai iya tsira daga sharrin 'yar uwarta.
***************
Koda taje gida ta fad'awa tanti tashin hankali da masifa kam ta shasu, zagi kuma ba Umar Faruk ba har malam ya samu rabonshi, haka dai ta gaji da masifa Zuby na sauraranta harta d'auki gyalenta ta fita daga gidan.
_Hmmm, yanzu ma kika fara gani._
*****************
Shima koda ya fita daga gidan gidansu habibiyarshi ya nufa, da sallamarshi kuwa suka amsa mishi suna zaune falo, kamar yanda yanzun ya fara zama jiki a wajen Papa zaman gida, zaune yayi suna gaisa har Salim ya fito daga d'aki, kallonshi kawai Umar Faruk keyi wanda Salim kad'ai yasan ma'anarhi, saida ya zo tsakiyar falon ya sunkuya yana kallon Umar Faruk yace "Ina kwananku."
Papa da Mamie basu amsa ba saboda mamaki, sake fad'in "ya tashin asuba?"
"La...fi.....ya lau." cewar Papa yana mamaki.
Murmushi Umar Faruk ya kalli Mammie yace "Hajiata ina d'aya Hajiar tawa?"
Turo baki tayi da kawar da kai tana fad'in "ban sani ba."
Mikewa yayi tsaye ya matsa kusanta yace "ran gimbiya ya huce, kinsan bana son hushinki, fad'a min inda zan ganta ko hankalina ya kwanta?"
D'an dukan damtsenshi tayi tana fad'in "hankalin sarki ya kwanta, sarauniyar tana d'aki."
Da dariya ya nufi d'akin ya bar Salim durqushe anan, yana ganin Umar Faruk ya shige d'akin Khairat ya mik'e tsaye da sauri ya bar gidan gabanshi na fad'uwa yana tunanin ta yanda zai bar gidan nan cikin sauqi, bai zame ko ina ba sai gidansu wajen mahaifiyarshi, da shigarshi ya fad'a d'akin nasu daba kayan kirki, tana kwance ya fara kiran sunan "Ma, Ma, tashi dan Allah zama bai kamamu ba."
Tashi tayi zaune tana kallonshi, "Maa , ki tashi fa."
"Meya faru, ka sake jangwalo wata tsiyar ko? anya Salim kana tuna waye kai?" duk tayi maganar ne tana tashi tsaye.
Kallonta yayi yace "Maa, ba lokacin wannan nasihar taki , yanzu ki had'a mana kayanmu gaba d'aya ki kimtsasu, daga yanzu zuwa ko wane lokaci zanzo mu wuce *Maradi*, tunda can danginmu suke."
Yana fad'a bai tsaya jin ta bakinta ba ya fita a guje, ita kuma da kallo ta bishi har saida ya fita, fashewa tayi da kuka tana fad'in "Salim wace irin rayuwa ka jefa kanka cikinta ka jefani , me zan fad'awa dangin mahaifinka yanzu idan wani abu ya sameka?"
Ganin bata da wani zab'i yasa ta fara had'a musu kayansu, dan ita kanta tayi farin ciki da hakan idan suka bar garin.
**************
Yana shiga ya sameta kwance tana bacci, zaune yayi kusanta yana kallon fuskarta ganin kyawunta harya fara dawowa, ya jima yana kallonta kafin ya tasheta, da taimakonshi ya cire mata kaya ya kaita bayi dan wanka, harya ajeta a cikin bahon wanka yana kallon tanqamemiyar douche d'in, a zuciyarshi kuma yana sake jinjina hak'uri da sadaukarwar da Khairat tayi domin aurenshi, kallon ko ina yake yana ganin tsabagen tsagwaron kud'in da aka narka wa bayan gida kad'ai, wannan idan ka shigo ai awa d'aya ba zata saka ka fita ba *(inaga fa wannan shine dalilin da yakesa Khairat bata fitowa da wuri)*, ganin yanda yake kallon wurin yasa tace "baby ya dai?"
Nunfasawa tayi yace "Ina kallon ikon Allah ne, ashe haka douche d'inki take da kyau da girma, shi yasa ranarki ta farko a gidana kika kasa shiga tawa douche d'in, gaskiya bayan ganin wannan kyakyawar douche d'in taki sai naji kunyar kaina."
Ruwan cikin bahon ta d'iba ta watsa mishi tana fad'in "ka ganka ko, ni kuma yanzu nafi jin dad'in wacce qaramar."
"Hum, wasu shashashu na cewa wai *jihadi* nayi na aureki, amma basu san cewa Khairat ce tayi *jihadi* ba data zauna da Umar Faruk."
Hannu yasa cikin bahon ya fara zuba mata ruwa a jikinta, da kanshi ya mata wanka ta fito daga bahon ya b'oyeta cikin towel sannan ya kaita d'aki, kafin ya gama shiryata ya jima sosai da saida ya rage zafi sannan, a lokacin kuma suka fito falo tare ya fad'a musu rasuwar Baban Zuby, sunyi jimami sosai musamman Khairat sai taji kamar wani babanta ne ya rasu, shiryawa sukayi suma suka tafi wajen rasuwar.
****************
Sai yamma tanti taji rasuwar nan sannan Zubyma taji, uba ubane, saida Zuby tayi kuka sosai tayi jimamin mutuwarshi, tanti ce tace ta shirya taje amma ita ba zata je ba, dan haka Zuby ta nemi rankiyar Zabba'u kuma ta samu.
*Da safe* Zabba'u tazo suka wuce, Zuby taji inama bata je ba, dan matanshi ne suka dinga fad'in ita d'in yarshi ce amma basu san taya ta zama ba, nan aka fara tsurfa iri iri har zuwa ake ganin Zuby, wasu na tambayar wacece mahaifiyarta wasu na tambayar taya ta zama yarshi, saida ta gaji Zabba'u ta janyota suka koma gida.
**************
*Kwana biyu* Umar Faruk ya qarasa had'a duk wasu hojjoji da suke nuna Salim ba dansa bane, kuma shirene na yan adawa tare da hadin gwiwar wasu tsofaffin masu laifi, abinda ya mishi dad'i sosai shine sake binciko mishi wani laifin Musa da Abdul Waid yayi, an sake kama shi da laifin yiwa wata budurwar fyade a wani qauyen *Agadez* da ake kira *Adarbisa* , babban abin farin cikin shine saida Abdul waid yasa wani jami'i dake can garin ya samo mishi cikakkiyar hujja a kan hakan, kuma anyi nasarar samun abinda ake nema, dan haka yau koda ya tashi da kanshi ya ziyarci offishin lawyer Papa.
Bayan gaisuwa ya fad'a mishi abinda ya kawoshi, nan ya nuna mishi jin dad'inshi kuma ya mishi alk'awarin za'a shigar da qara nan bada jimawa ba, amma zaije a nemi amincewar Papa dasa hannunshi, alfarma Umar Faruk ya nema kan baya so asan da hannunshi a ciki, kuma ya amince da duk abinda ya fad'a, a haka suka rabu shi kuma ya kama hanyar auwa gidan Papa.
***************
Koda yaje da maganar ta girgiza Papa sosai, Khairat kuma tace "ai dama na fad'a muku, wannan yaron ba zai tab'a zama danka ba kawai raina maka hankali sukayi."
Da mamaki cikin rud'ewa Papa yace "taya haka zata kasance, docteur *Shehu* fa da kanshi ya mana gwaji kuma ya tabbatar."
Lawyer ne yace "ka kwantar da hankalinka Alhaji, muna da duk wasu hujjoji a hanunmu , koma miye dai zaka ji."
Umarni Papa ya bayar aka shigar da qarar, take aka kai magnar babbar kotu, kamar yanda aka sallama gidan Sani Saley aka bashi takardar sammaci, haka su Musa da sukaga takardar sukayi mamaki, dan a ganinsu babu wanda yasan da fitowasu bare mafakarsu, Odette ma na tsaka da jin dad'in rayuwarta aka kawo mata wannan takarda da tasata gudawa tsawon wannan yinin , tanti na d'aki aka sallama dan haka Zuby ta fita ta karb'o saqon , Zuby ta shiga d'akin ta samu tanti na waya, wayar da tasa cikin Zuby barazanar zubewa.....
_Me kuma taji???_
**Muje zuwa*😘
*Kuyi hak'uri da rashin jina , qanwar mijina ce tayi saukan Qur'ani yau.*
_Wanda suka kira ban d'auka ba kuyi hak'uri, duk kun kirane a lokacin da banawa ba, nasan dai kun fahimta saboda maganar ta manya ce, my Belle *(momyn khadija)*, naga kiranki kema, sorry, i love you all._
***************
6📓2📓
Cike da kwankwanto tanti tace "Malam anya kuwa baka ka kashe Bala ba? danni nasan dai mun baka aiki akanshi."
Jim tayi alamar tana sauraro, ta jima kafin tace "a'a wallahi babu ruwana ni, kai ka kasheshi, nidai kawai nace kasa su gane kurensu amma babu wanda nace ka kashe a ciki."
Nanma shiru tayi alamar tana sauraro sannan tace "yanzu ya kake so nayi in aka ganewa hnnuna a cikin kisanshi? nifa na fad'a maka babu ruwana wallahi." tana fad'a ta kashe wayar ta jefa kan gado, juyowa tayi da nufin fitowa sukayi karo da Zuby dake sauraronta.
Hawaye na zuba a idonta tace "Mama, dama ke kika kashe min mahaifi? lallai Mama kin wuce tunanina, wallahi ke shed'aniya ce ta qarshe, a gaskiya ba zan iya ci gaba da zama dake ba, wallahi gwara na fita ko akan titi ne na dinga kwanciya akan na zauna waje d'aya dake."
"Kinga Zuby ba abinda kike tunani bane, bab.."
"Ya isa haka." ta d'aga mata hannu, takardar sammacin ta jefa mata tana fad'in "ga wannan kad'an daga abinda kika shukane zaki fara girba."
Tana gama fad'a ta shige d'akinta dama kuma bata gama barbaza kayanta ba, dan haka ta tattara ta fito duk da maganar da da Mama ke mata bata saurara ba saida ta fita daga gidan, tunani take inda zata nufa, gidan Uwani ta nufa, amma ina ta samu itama da matsalar data sha mata kai, dan dole ta barnan ta nufi gidan Zulfa'u, itama dai ta samu yanzu ba kamar da ba, dan tana fuskarntar tsangwama ta miji, dan haka bata tafi gidan Zabba'u ba kawai ta wuce gidan mahaifinta kamar yanda Uwani ta bata shawara tun farko, kasancewar anyi sadakar uku hakan yasa bata samu mutane sosai ba, koda ta fad'a musu ta dawo gidan mahaifinta ne tijara wasu suka fara mata, yayin da wasu ke cewa gadone ya kawota, saida ta nuna musu ba shine a gabanta ba kuma ai bata cikin magada kad'ai ta samu lafiyarsu, babbar matar Bala ce tace su barta ta zauna koba komai zasu moreta.
**********
Hankalin SS ya tashi sosai, hakan yasa ya fita ya je ya samu malaminshi amma saiya fad'a mishi sune da nasara, badan komai ba saidan ya samu wani abu a wajenshi, bayan fitarshi kuma lawyern Papa yazo gidan SS amma bai sameshi ba, haka ya koma ba tare daya ganshi ba, yaso dawowa da dare amma bai samu dama ba, hakan yasa washe gari ya dawo ya sameshi, mai gadi ne ya mishi iso har cikin falon SS, kasancewar b'angarenshi daban ne yasa har mata na shigowa wajenshi ba tare da sanin iyalinshi ba, idan ma sun gani babu yanda sukeyi sai dai suyi shiru.
Su Musa ya samu wajen suna tattaunawa, kasancewar su Musa sun sankomai sa game da Papa yasa yanzu haka suke shiri akan yanda zasu had'o duka karuwan da Papa yayi mu'amula dasu dan gabatar dasu a gaban kotu, gaisawa sukayi nan ya fito da duka hujjojin da Umar Faruk ya bashi, da mamaki yasa hannu zai karb'a kawai ya janye takardun da qaramar recorder da aka d'auki muryar Salim, murmushi ya masa yace "yana da daraja, dan haka zaka biya farashinshi."
"Meye wannan d'in?"
"Duk wasu hujjoji da zasu ruguza rayuwar siyasarka, dan da zaran wannan sunje gaban alqali, to babu tamtama cewar za'a yanke maka hukunci ba tare da ansha wahala ba, ni kuma bana son haka ta faru, shi yasa na kawo makasu danka biyani."
Fizge takardun yayi yana fad'in "ka fad'i farashinka ni kuma zan biya."
Yana fad'a mishi kud'in yace ya amince, kallonshi yayi yace "taya ka samu wannan hujjojin?"
Nunfasawa yayi yace "surukinshi mana."
"Wa kenan?"
"Umar Faruk, wanda ke auren Khairat."
Musa ne yace "zaka iya nuna mana shi?"
"Eh to, yanzu bansan ina zan sameshi ba, amma ai gobe zaku had'u dashi a kotu, dan dole zaije duk da ya buqaci karna fad'i shiya samo hujjojin nan."
"Allah ya kaimu goben." cewar Musa yana wata zazzafar qwafa.
**************
Umar Faruk ne ya shigo gidan da sallama, Mama dake bakin panpo ta amsa mishi da fad'in "sannu da zuwa."
"Sannu Mama, ya gida?" ya fad'a yana kallon d'akin Zuby, kallon Mama yayi yace "wai Mama badai yarinyar nan tafiya tayi ba?"
"Um, ta tafi."
Tsaki yayi ya wuce d'akin Khairat ya shirya sannan ya fito, kai tsaye gidansu Khairat d'in ya nufa, falo ya sameta zaune da doguwar riga mai siraran hannaye ta girke plate d'in wainar qwai gabanta da fritte sai yaji da take dangwalawa tana ci, da sauri ya zauna gabanta tare da d'auke robar yajin yana fad'in "kaji min yarinyar nan, yaji ne kike hambad'a haka? gaskiya bana so."
Marairaicewa tayi tace "dan Allah baby ka bani, yafi dad'i da yajin mana."
"Ki shiga hankalinki fa." ya fad'a yana rufe robar yajin.
Turo baki tayi gaba taci gaba da ci tana kallonshi, shima kallonta yake yanda take cin abincin da matuqar birgewa, ganin yana kallonta yasa ta fara saka mishi a baki shima, Mammie ce ta fito cikin shiri zata fita, gaisawa sukayi Mammie tace "ni zan wuce saina dawo."
"Sai kin dawo." cewar Umar Faruk.
Khairat ce ta qara da "qawata ki siyo min abu mai dad'i dan Allah."
"Kamar me?" cewar Mammie.
"Abu mai dad'i fa nace."
"To angama."
Tana fita Khairat ta kalli Umar Faruk tace "baby, docteur fa yace da zaran na fara naquda muje asibiti."
Sanin waye docteur d'in yasa yace "kinga ki rabu da wannan likitan, insha Allah da kanki zaki haihu, karma ki d'aga hankalinki kinji."
"Amma fa baby...."
"Amma me?" ya katseta.
"Na fad'a miki karki damu, da kanki zaki haihu."
Kallonshi tayi tace "a gaskiya ba zan bari nasha wahala ba, tunda yace ga yanda za ayi to kawai ayi yanda yace."
A zafafe ya daka mata tsawa yace "na fad'a miki zaki haihu da kanki, karki qara min maganar banzan likitan nan."
Kallonshi take kamar zata fashe da kuka, d'aga muryar da yayi ne yasa Mamie fitowa daga d'aki, Khairat na ganin Mamie ta tashi da qyar ta juya ta nufi d'akinta yana binta da kallo ganin yanda cikin ya fito sosai har yana mamakin girmanshi, zaune Mamie tayi saman kujera tana kallonshi tace "Umar Faruk, lafiya nake jiyo muryarka haka?"
D'an sosa kai yayi yace "Mama akan maganar da likitan nan ne yayi duk tabi tasa a ranta ta yarda da abinda ya fad'a."
D'an murmushi tayi itama tace "ayya, Umar Faruk ai dole ta yarda, gaskiya fa Shehu ya fad'a maka, dole a gaggauta kaita asibiti data fara naquda."
A sauqaqe yace "Mama, karmu cire rai da rahamar ubangiji, idan muka kai kukanmu ga Allah zata haihu da kanta kuma lafiya qalau."
Ajiyar zuciya Mamie ta sauke tace "abinda baka fahimta ba shine, Khairat na d'aya daga cikin irin matan nan masu matsatsen gaba, kuma nasan kasan haka a matsayinka na mijinta, ba zata iya ba da kanta wahala kawai zata sha in ba'a kaita da wuri ba."
Shiru yayi yana tunani, ashe dama wannan ne dalilin da yasa take matse, ashe halitattar tace haka shi yasa kullum take shan wahala idan zan shigeta, lallai in haka ne kam ba lallai ta iya haihuwa da kanta ba, take ya fahimta ya kuma shiga d'akinta ya bata hak'uri akan tsawar daya mata.
*Washe gari* an shiga kotu, a zaman farko lawyern Papa ya bada wannan qaramin recorder a matsayin hujjar data rage musu ita kad'ai yana fad'in "ya mai girma mai shara wannan itace hujjarmu ta farko kuma ta qarshe da muke da a hannu, da wannan d'aukar ne mai girma mai shari'a zamu samu adalci."
Mik'awa magatakarda yayi, abin mamaki koda aka danna d'aukar sai akaji babu komai a ciki, dan haka lawyern SS ya mik'e ya fad'i ra'ayinshi akan ana so a b'ata sunan SS ne kawai, saida suka gama jawabansu tsaf alqali ya fara magana Umar Faruk ya d'aga hannu ya nemi izinin magana, umarni alqali ya bashi dan haka ya mik'e tsaye ya kalli tanti Odette dasu Musa sannan yace,
"Ya mai girma mai shari'a, ina neman alfarmar kotu data sake bamu wata damar danmu sake kawo wasu hujjojin?"
Saida alqalin yayi yan rubuce rubuce sannan ya kalli Umar Faruk ya kalli lawyensu yace "lawyen mai qara, mai zaka ce akan wannan qorafin?"
Tsaye lawyer ya mik'e yana zufa da in ina yace "muna neman alfarma ya mai girma mai shari'a."
Nanma saida yayi rubutu kafin yace "bayan neman alfarmar kotu da lawyen mai qara yayi, kotu ta karb'i qorafinsu ta basu nan da gobe su kawo hujojjinsu, idan ba haka ba za ayi watsi da wannan qarar, dan ba za'a b'ata lokacin kotu ba, zama ya qare."
Juyawa yayi ya kalli lawyen yana mishi wani banzan kallo, maida kallonshi yayi ga tanti Ma'u, a haka zama ya qare abu ba dad'i.
**************
Da kanshi yaje gidan tanti Ma'u neman Zuby dan yaga lafiyarta data abinda ke cikinta, habaice da zagi da baqar magana ya jisu, amma haka ya toshe kunnenshi har saida ta gama sannan ta fad'a mishi Zuby bata nan, tambaya yayi tana ina amma taqi fad'a dan itama bata san ina take ba, haka ya baro gidan yana kiran wayar Zuby, k'in d'auka tayi dan rayuwarta harta canza cikin qanqanin lokaci.
**************
Bayan yaje gida Khairat ta tambayeshi ina zai samu wasu hujjojin? amma yace ta kwantar da hankalinta ba komai, a raunane ta kalleshi tace "baby, ina jin tsoro fa, dan Allah karka saka mana kanka a matsala, idan wani abu ya ta faru da kai wallahi nima zan shiga wani hali, dan Allah ka fitar da kanka a maganar nan."
Shafa kumatunta yayi yace "karki damu kanki, insha Allah za muyi nasara, kuma mun riga mun fara, kinga bai kamata na cire hannuna ba."
A shagwab'e tace " kenan ba zaka cire hannunka ba?"
Da kai ya ta mata alamar eh, tureshi tayi daga kan gadon ta fashe da kuka tace "shikenan kaje, tunda kana sha'awar ganina ina takaba, mutanen nan ba imani ne dasu ba, kaje kayi abinda kake so."
Juya masa baya tayi yayi rarrashi harya gaji, sai lokacin zai tafi ya ya fad'a mata fa sun rabu da Zuby, ta girgiza sosai ta kuma tambayi laifin me ta mishi, 'kin fad'a mata yayi dan haka ta sake yin wani hushi tace ya tafi itama babu ruwanta dashi, haka ya baro gidan sai dai yasan dole zasu shirya, amma girmanta ya qaru a idonshi.
A hanyarshi ta zuwa gida su Musa suka tareshi, yana ganinsu ya fito yana murmushi yana kallonsu, gaban motar yaja ya tsaya ya rumgume hannaye yana kallonsu suna takowa wajenshi, suna zuwa gabanshi suka tsaya kafin suyi magana yace "Ya dai matasa, kunzo ku gaisheni ne?"
Cikin takaici Bello yace "kai, mune zamu zo gaisheka d'in, kama rainamu wallahi."
Cike da dariyar mugunta da raini Umar Faruk yace "to kenan meya kawoku nan, ko kunzo karbar hujjoji ne?"
"Yawwa d'an gari, abinda ya kawomu kenan, idan ka bamu saimu tafiyarmu salin alin, amma idan ka k'i kuma sai kaji a jikinka." cewar Musa.
Murmushin gefen labb'a yayi yace "da ganina nasan kunsan ni ba matsoraci bane, kamar yanda ni ba ragon namiji bane, dan haka kuyi duk abinda kuke ganin zakuyi, amma fa ba zan baku ba."
"Haka kace?" cewar Musa.
Gira kawai ya d'aga mishi alamar eh, ganin suna tunkarowa wajenshi yasa ya gyara tsayuwarshi yana tattare hannayen rigarshi, Musa ne yasa hannu aljihu ya ciro wata qaramar wuqa yana fad'in "da alama kai jarumi ne, amma fa karka manta mu sojoji ne, kaga kuwa dole ka shafa mana lafiya."
Dariya Umar Faruk yayi yana fad'in "kaji sakarai, jarumi kake so a kiraka kenan? ai jarumta irin taka ba'a fatanta, ka rasa inda zaka nuna jarumtarka sai akan mata wajen yi musu fyad'e, ai jarumta yana nufin shanye duk wani d'aci da qunci harka riski farin ciki."
Dariya Musa yayi yace "to ai ba ragwayen maza ke iya yiwa mace fyad'e ba, musamman ma masu taurin kai da tirjiya irin matarka Khairat."
Yana fad'a suka bushe da dariya dukansu har suna tab'a hannu, lumshe ido yayi dan zafin da zuviyarshi keyi, ji yake kamar ya ciccira namansu a wajen, muryar Bello ce ta dawo dashi yana fad'in "a kan matarka na fara sanin 'ya mace, amma har yanzu ban had'u da wacce ta kaita ba, gaskiya da naji ance tayi aure saida naji ina kishi da wanda ta aura, kullum kowane dare kasa bacci nake saboda tunanin yanzu yana can yana shan romon da muka sha."
Aminou ne ya bashi hannu suka tapa yana fad'in "wallahi kuwa, nima fa har mafarkin wannan ranar nake, gaskiya yarinyar ta had'u."
Cewar Musa "ai zazzafa ce ta qarshe, waiku dan ma baku ne farko ba, aini zan fad'a muku gaskiyar magana nida na fara, a lokacin dana shiga wannan duniyar kai kace a aljanna aka tsundu....."
Bugun daya sauka akan bakinshi ne yasa ya fad'i qasa kwance yana dafe da wuri, kallon Umar Faruk suke da idonshi suka canza kamar ba mutum ba, kafin su ankara ya sake shaqo wuyan rigar Musa ya d'agoshi tsaye yana fad'in " kamar me kake so kace, kamar an tsundumaka a aljanna? banza mahaukaci, kai kana tunanin zaka shiga aljanna bayan ketawa mata haddinsu da kake, aiko a wuta ma zaiyi wuya ka samu mazauni."
Yana fad'a ya sake kai mishi bugu, da azama sukayo kansu suka fara qoqarin rabasu, sosai ya shaqi Musa yake dukanshi, suma dai ganin ya kasa sakinshi yasa suka rufeshi da duka toko ina, amma duk da haka baya jin dukansu dan hango Musa yake akan gado yana kokawa da Khairat har yayi nasarar shiga gonarshi, dan haka yake jin kamar ya cinyeshi d'anye, suna ta dakuwa da bawa hammata iska kawai Umar Faruk yaji wani abu ya sokeshi a ciki, kallon wajen yayi yaga ashe Musa ne yayi nasarar soka mishi wannan qaramar wuqar da wahala ta kai mishi.
A hankali ya fara sakinshi harya sulale qasa, basu barshi haka ba saida suka sake binshi da duka hakan yasa suka canza mishi kamaninshi, duk jini ne ta ko ina, saida suka ga baya motsi sannan suka nufi motarshi suka bincike, ganin basu samu komai ba yasa suka lalaba har jikinshi, nan ma babu komai haka suka tafi babu nasara.
Umar Faruk na kwance baisan inda kanshi yake ba, ya jima a wajen kwance yana zubar da jini, wata mota ce ta nufo wajen da yake, mutanen dake motar ne suka ganshi kwance suka fito, da ikon Allah suka taimaka mishi suka d'aukeshi sukayi asibiti dashi, ta hanyar wayarshi suka kira lambar daya kira qarshe lambar Abbakar, cikin tashin hankali Abbakar ya sanar a gida suka nufi asibiti, ganin halin da yake ciki ga jini ana qara mishi yasa basu kira d'aya daga cikin matanshi ba.
Saida safe ya farfad'o, lokacin Khairat na kiranshi dan tuni sun hallara a kotu rashin ganinshi yasa take kiranshi, Abbakar ne ya d'auki kiran saida suka gaisa take tambayar "yah Abbakar ina Umariri ya shiga ne?"
Sunan data kira saida yasa ya d'an murmusa, dakewa yayi yace "baya kusa, ina asibiti ne."
"Asibiti kuma, meya faru, waye bashi da lafiya?"
Ajiyar zuciya ya sauke yace "ki kwantar da hankalinki Khairat, idan zaki iya zaki iya samunmu a babban asibiti."
Rintse ido tayi saboda fad'uwar da gabanta yayi, a kaurare tace "inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un."
Shiru ne ya ratsa kafin ta sake cewa "yah Abbakar sun mishi wani abu ko? ni nasan dama yasa kanshi a had'ari."
"Karki damu Khairat, jikinshi da sauqi sosai."
"Shikenan yah Abbakar, gani nan zuwa."
Papa ta fad'a ma suka nufi asibitin su Mamie suka jirasu.
**************
Koda ya farka ya tashi zaune ya Fara qoqarin cire qarin ruwan da aka maka mishi, Abbakar ne ya aje wayar ya fara rik'eshi, tureshi yayi da qarfi ya fizge sirinjin hakan yayi sanadiyar fitowar jini daga hannunshi, a tsawace Abbakar yace "wai meye haka, me kake yi ne haka?"
Kallon Abbakar yayi yace "tafiya zanyi, ba zan zauna ba, dole saina qarasa abinda na fara."
Qafafunshi ya zuro da niyyar saukowa, da sauri ya dafe cikinshi inda aka soka mishi wuqar tare da cije lips ya rufe ido, Abbakar ne yace "uhum, ga irinta ai, ina zaka je a wannan halin?"
Bud'e ido yayi ya sauko daga kan gado cike da jarumta da dauriya, rigarshi ya kalla da duk taji jiki itama, Abbakar ya kalla yace "taimakon da zaka min shine, ka kaini gida."
"Umar, baka da lafiya fa, yanzu haka Khairat nakan hanyar zuwanta nan."
Cikin fitar hayyaci ya shaqo wuyan rigar Abbakar cikin d'aga murya yace "me, kana nufin ka fad'a mata, me yasa to zaka fad'a mata? Khairat nada rauni sosai, komai zai iya faruwa da ita idan taga halin da nake ciki."
Shigowar Baba dasu Mama ne yasa saki wuyan rigarshi yana kallon Baba, "lafiya, meya faru?" cewar Baba.
"Ba komai Baba, wai gida yake so ya tafi a wannan halin da yake ciki."
"Gida kuma, me zakayi a gidan?"
A marariraice yace "dan Allah Baba ku barni na tafi, wallahi akwai mahimmanci zuwana yanzun."
Kallonshi Baba yayi sosai kafin yace "shikenan, bara muga ko mun samo maka takardar sallama."
"A'a Baba, ku barsu kawai, ba lallai bane su sallameni."
Haka dai shida Abbakar suka sulale suka bar asibitin, kai tsaye gida suka nufa yana shiga ya canza riga sannan ya had'a sauran hujjojin da suka rage mishi sannan suka tafi kotu.
***************
Koda su Khairat suka zo asibiti su Baba ma na shirin tafiya kotu, da qyar suka fad'a mata jikinshi da sauqi suka lallab'ata suka bar wajen, kai tsaye kotu suka hallara suma, tana ganinshi ta ruga a guje ta rumgumeshi tana kuka, sosai ya rintse ido saboda wani bala'in zafi dake ratsashi saboda dafe wani ciwo da tayi amma ya kasa fad'a mata, yanda take qara cukwikwiyeshi yasa ya saki qara bai shirya ba, da sauri ta d'ago tana kallonshi da mamaki, turo baki yayi gaba tare da dafe wajen data rik'e yana fad'in "kin min famin ciwona."
B'ata rai tayi ta kai mishi duka a wajen tana fad'in "na fama d'in, aiga irinta nan, jiya mena fad'a maka akan maganar nan? amma baka saurareni ba kai mai taurin kai, saina shek'eka da hannuna, hamago kawai kana so mu rasaka gaba d'aya, ya kake so muyi to, me zamu gayama yaranka idan sun tambayemu."
Duk maganar da take tana zubar da hawaye ne, shi kuma hawayen nata yake kallo yanda suke zuba da k'arfi, hannu ya mik'a mata da nufin ta taho, buge hannun tayi da k'arfi tana fad'in "Bana so, bana sonka mugu kawai, saina kasheka da hannuna."
Sake bata hannun yayi ya marairaice kamar zai fashe da kuka yace "dan Allah baby, kizo mana ko naji sauqin ciwon dake damuna, nayi kuskure amma ki yafe min."
Ganin qwalla sun taru a idonshi ne yasa ta fad'a jikinshi da k'arfi har yana shirin fad'uwa tana tsananta kukanta tana fad'in "me yasa Faruk, me yasa zaka sa mana kanka a had'ari, kasan fa muna buqatarka musamman a wannan yanayin."
A hankali ya kai hannunshi kan cikinta ya shafa yana fad'in "ki gafarceni, ina hakane saboda farin cikinki da iyayenki, Khairat na kasa samun sukuni ganin halin da iyayenki ke ciki, dolena ne nayi saboda farin cikinku ya d'ore."
Goge hawayenta tayi tace "Amma ai ina farin cikin kasancewata da kai, kuma su Mamie ma suna farin cikin samun suruki kamarka, farin cikinmu zai gushene idan kasa kanka a had'ari, dan Allah karka sake irin haka, Faruk ba zan juri rasaka ba wallahi, nasan mutuwa zanyi nima idan na rasaka, dan Allah ka zauna tare dani."
Abbakar ne yace "to Roméo da Juliette ku wuce mu shiga ciki kowa ya shiga."
Dariya sukayi suka wuce ciki suka zazzauna, su Musa kam idone ya sake raina fata musamman abubuwan da suke gani a hannun Umar Faruk, lawyer ne ya matso kusan Umar Faruk ya sunkuya yace "kawo hujjojin na fara dubawa kafin alqali ya shigo."
A wulaqance ya kalleshi yace "barshi kawai, aida hannayena nima Allah ya horemin, idan alqalin ya shigo na bayar a bashi."
Yana gama fad'a kuma alqali ya shigo, tsaye suka mi'ke harya zauna, bayan maganganun da alqali yayi ne ya tambayi ko hujjojin sun bayyana gaban kotu kamar yanda Umar Faruk ya nemi alfarma aka mishi, Umar Faruk ne ya mik'e yayi daidai da mik'ewar lawyensu, hararanshi yayi ya rab'ashi ya bawa maga takarda duka hujjojin, saida alqali ya gama dubawa duka sannan ya nisa ya gama ruubuce rubutunshi kafin ya fara magana,
"Bayan hujjojin da aka gabatar a gaban kotu, kotu ta samu Sani Saley Odette Asma'u dasu Musa da laifi dumu dumu, sai dai kuma babu matashi Salim a kotun nan, dan haka kotu ta bada umarnin da a gaggauta gurfanar da Salim a gabanta, dan shima mai laifine, sannan kotu na buqatar a gabatar mata da docteur Shehu, dan shima da nashi laifin abisa cin hanci dan gurb'ata sunan wani."
Tsaye Umar Faruk ya mik'e dan girmamawa yace " ya mai girma mai shari'a, ina so kotu ta sani cewa wad'annan matasan samarin dama fil'azal masu laifi ne, laifinsu kuwa shine fyad'e wa mata, muna da shaida akan hakan idan kotu na buqatara gabatar dasu a gabanta zamu iya, bayan fyad'e kuma ni kaina sun so su kasheni badan komai ba sai dan su karb'i hujjojin dana gabatar, amma da ikon ubangiji kuma Allah bai basu sa'a ba, da wannan nake roqon kotu mai alfarma data yanke ma wad'annan hukunci mai tsaurin gaske wanda ba zai bayar da damar da za'a sake fito dasu ba daga gidan yari, dan a cikin hujjojin dana gabatarwa da kotu akwai bellynsu da akayi ba tare da sun cika wa'adin da aka dib'ar musu ba, abin takaicin ace anci zarafin yar babban mutum kuma shugaba, amma su kasa samun adalci, wannan ne yasa wata matashiyar budurwa da Musa yaci zarafinta yasa iyayenta suka barshi da Allah, dan sun san ba zasu samu adalci ba, na gode ya mai shari'a."
Tsawon lokaci alqali na nazartar lamarin kafin ya fara da "bayan hujjojin da aka gabatarwa da kotu tare da dogon nazari da tayi, kotu ta samu wannan mutane da laifi dumu dumu, dan haka wannan kotu mai alfarma ta yanke wa su Musa hukunci kamar haka, dukansu zasuyi shekara.....a gidan yari, haka ma Odette da Asma'u da Sani Saley da kuma yaro Salim an yanke musu hukuncin d'aurin wata uku uku a gidan yari tare da horo mai tsanani saboda magud'i a cikin siyasa da b'ata sunan wani, sannan kotu na umartar su Musa da subiya tara ta 150 0000cfa ga Umar Faruk saboda rayuwarshi da suka nema, kuma zasuyi hakan ne a cikin sati d'aya tak, sannan kotu ta wanke Mani Bukar cike da girmamawa da mutuntawa, sauran a gurfanar da likita da Salim a gaban kotu, da wannan zaman kotu ya qare."
(Ba lallai hukuncin dana yanke yama kowa dad'i ba, bana da ilimin shari'a, kuma wanda zai bani bayanin haka na rasa lambarshi a d'aya layin da aka min asararshi.)
Kallon tanti yayi yace "kiyi hak'uri tanti, banso haka ta faru ba kuma banji dad'in faruwar hakan ba, amma nasan zaki fahimceni." Yana fad'a yayi gaba abinshi Odette ta bishi da mugayen ashar, tanti kam bakinta ma ya mutu murus bata san me zata ce ba.
A wajen su Bello suka fara tuhumar Musa akan shiya lalata musu rayuwa, gashi yaja musu zasu qarar da rayuwar da basu da tabbacin zasu kaita a gidan yari, suna cike da wannan jimami da zulumi da kuka Umar Faruk dake rik'e da hannun Khairat ya tsaya gabansu yana murmushi, gemunshi ya shafo yana kallonsu yace "gashi a karo na biyu na sake antayaku gidan da kuka fito, amma wannan karan zanyi iya bakin qoqarina naga baku fito ba, kuma na muku alk'awarin ziyartarku kowane qarshen sati dan yin wa'azi wa yan gidan, aci gabza lafiya yan samari."
Wucewa sukayi Musa yayi saurin cewa "dama kai ka tona mana asiri a farko ma?"
Da wani shegen murmushi ya d'aga masa gira kawai suka wuce har saida suka shiga mota Khairat ta kalleshi tace "dama kai ka bayyana masu laifin a waccen lokacin?"
Shiru yayi sai Mamie dake baya ce tace "shine 'yata, haqiqa Umar Faruk ya mana taimakon da ba zamu iya biyanshi ba, sai dai kawai mu bishi da addu'a."
"Ita nafi buqata a wajenku Mama." ya fad'a yana kallon Mamie.
D'ora kanta tayi akan kafad'arshi ta rumgume hannunshi tana fad'in "ashe kaine ka taimakeni a waccen lokacin ma, na gode maka sosai baby, gaskiya kai na daban ne, kuma kasa naji kunya akan abinda na dinga yi maka a baya, da nasan kaine wanda ya taimakeni da banyi abinda nayi ba."
Shafa fuskarta yayi yace "karki damu, komai ai ya wuce, ba gashi kin zama tawa ba."
"Kuma nima ka zama nawa ba." ta fad'a tana qara qamqameshi.
0 comments:
Post a Comment