Saida Umar Faruk yayi jinya sosai kafin ya samu sauqi, a lokacin kuma cikin Zuby yana wata takwas, a lokacin kuma Allah ne yayi ikonsa, yayin da Zuby ke fuskantar rayuwar qansqanci a gidan mahaifinta da wulaqanci iri iri, kyara da zagi ga aiki babu tausayi haka suke sakata duk da tsohon cikinta, amma da zaran Umar Faruk ya shigo gidan da sunan yazo ganinta zasu dinga sakar mata fuska, amma kasancewar shi ba yaro bane yasa ya fahimci canji daga wajen Zuby a take ya fahimci halin da take ciki, amma abin takaici daya umarceta su koma gida sam sai tace gidan ubanta itama zata zauna, dole ya rabu da ita a haka yake d'awainiya da ita da abinda yake cikinta.
Khairat kuma yanzu lafiya ta samu, sam bata cika cin abinci ba sai kayan qwalam da maqulashe, Umar Faruk kuma kullum cikin kashe mata kud'i yake da faranta ranta, yayin da kullum suke maqale da juna bacci kad'ai ke rabasu, tayi nauyi sosai saboda cikinta na watan haihuwa ne, kunburin qafafu kuma shi yafi takurata sosai, sai nauyin jikin da tayi ko qwaqwaran motsi bata iya yi da kyau, hakan yasa har Papa yake tunanin ko za'a fitar da ita ne waje ta haihu a can, amma tace bata so.
Salim kam anyi nema amma shiru babu labarinshi, dama kuma tunda Umar Faruk ya qwamusheshi ya tsorata yasa suka bar garin shi da mahaifiyarshi, basu tsaya ko ina ba sai Maradi, anan suka fara wata sabuwar rayuwar a wani qauyen da ake kira *Madarunfa*.
**************
Wani bala'in ciwo ne ya addabi tanti a gidan yarin da suka rasa gane gabansa, da farko sun d'auka hawan jini ne amma sai suka fahimci abin ya wuce nan, gashi idan aka ce dare yayi to babu mai bacci saboda bala'in haukan da take tsurawa a wajen da hayaniya, a hankali kuma wani qurji ya fito mata a qafa, da sannu sannu saiya dinga girma har yakai matakin da yayi ruwa ya fashe ya fara wari, da qyar aka samu aka canza mata waje ita d'aya.
************
Koda Zuby ta wayi gari ta tashi bata jin dad'i sai rik'ewar da bayanta keyi, sai dai babu wanda zata fad'a ma ya kalleta ma bare ya tausaya mata, tana cikin yanayin nan Hajia babba ta gidan ta fito mata da kayan wanki, duk qoqarin Zuby nasan ta fahimceta amma ina saida ta fara wankin tana kuka, tana gamawa ta d'ora girkin rana, tana idawa ne ta fara qoqarin shara ,amma ina bata kai ko ina ba ta fad'i wajen tana neman taimako, da taimakonsu suka d'auketa suka kaita asibiti sannan suka kira Umar Faruk dan yasan halin da ake ciki.
A lokacin Umar Faruk na zaune bakin gado d'akin Khairat yana kallonta tana kai da kawowa sai sharar gumi take, qafafunta yake kallo da sukayi sumtum dasu kamar zasu fashe, wata qaramar riga ce gareta mai siraren hannuwa, tsaye yayi ya nufi wajenta ya rik'o hannunta yana fad'in "zo ki zauna dan Allah ki huta, yawon ya isa haka."
Fincike hannunta tayi za tayi magana kuma tayi saurin dafe cikinta da qugu tace "washhh, wayyo Allah na, dan Allah ka kira min Mamie, wallahi bana jin dad'i."
Qara rik'eta yayi yace " jikin ne, bara na kirasu To."
Zai fita kenan ta fizgo rigarshi cike da azaba ta durqushe qasa tana kuka tana fad'in "wayyo Allah, Faruk da ciwo wallahi, dan Allah ka min addu'a, wallahi ji nake kamar zan mutu, wayyo Allah na Allah ka taimakeni."
Durqushewa yayi shima yana rik'e da hannunta yana kallon idonta dake rufe sai hawaye ke fitowa, janyo kanta yayi ya manna a qirjinshi ya kara bakinshi a kunnenta yace "kiyi hak'uri Khairat d'ina, ki yawaita anbaton sunan Allah a bakinki, a yanzun kina cikin wani hali ne da babu abinda zan iya yi miki sai dai addu'a, amma mahaliccinki shine ke tare dake a wannan halin, da ace idan nace ciwon nan ya dawo kaina zai dawo, haqiqa da zanyi addu'a a yanzun nan dan na d'auke miki wannan shan wahalar, amma kiyi hak'uri kinji ina tare dake insha Allah."
Sake qamqameshi tayita fashe da kuka, rarrashinta yake yana tofa mata addu'a yana so ya tashi ya kira Mamie amma ina, suna haka ta sake kwamtsa wata qara tare da cakumo rigarshi, a gigice ya d'auketa ya sauko da ita falo inda Mamie suke zauna, nan dai suka nufi asibiti, a hanyar zuwa ne kuma kiran Zuby ya shigo, koda ya d'auka Hajia babba ce, koda ta fad'a mishi sake rud'ewa yayi musamman daya tuna cikin Zuby ba watan haihuwarshi bane yanzun.
D'an magori ya kai Khairat, Zuby kuma asibitin da aka kaita daban itama, koda sukaje aka yi shirin yiwa Khairat aiki dan fito da abinda ke cikinta, cikin nasara kuma akayi sa'ar fito da kyakyawar yarinya sak mahaifiyarta bata bar komai ba dan gane da ita, a lokacin kuma Umar Faruk na wajen Zuby tare da Mama, tasha wahala sosai kafin ta haiho abin cikinta, namiji ne amma sai yazo babu rai saboda yana wata takwas ne, suna cikin wannan jimamin suka tafi ganin Khairat da yarta, nan kuma farin ciki sukayi sosai yayin da asibiti ya cika da mutane ana ta murna.
A hankali Khairat ta bud'a idonta daga baccin da take na hutu, wani irin ciwo taji yana taso mata da ba zata iya misaltashi ba, da qyar ta hango Umar Faruk rik'e da yarinyar yana kallonta sai wasar baki yake, jin abin na qara taso mata yasa ta tara mishi alamar yazo, duk mutanen dake d'akin kallonta suke suna tambayar ya jikinta, bawa Mama yarinyar yayi ya qaraso wajenta, sunkuyawa yayi tare da rik'e hannun nata, bud'a baki tayi tana magana amma baya jin me take fad'a dan haka ya kara kunnanshi wajen bakinta.
Murmushi ta masa tace "baby, ni kad'ai nasan me nake ji, bansan ko zan rayu ba, amma dai saida na tabbatar na baka wata babyn kafin zan barka, ka kula min da ita sannan ka tabbatar ta samu tarbiya wacce ban samu ba a lokacin yarintata, nasan kamin kyautar yarinyar nan tun tana ciki, amma yanzu ta zama taka, dan bata da wani gata daya fika a duniyar nan, alfarma d'aya nake nema a wajenka?"
Kallonta yayi yace "alkairina bana son irin maganganun nan fa, me yasa zaki fad'i haka a irin wannan lokacin, yanzu fad'a min wace alfarma kike nema a wajena?"
Murmushi ta masa tace "ina so ka sawa yarinyar nan suna Islam, ina so ta zama mai tsantsar addini da fahimtar sunna."
Qara matse hannunta yayi yace "zanyi Khairat, dan Allah kiyi shiru kinji."
"Ina....." shiru tayi ta kasa fad'a ta rik'e cikinta, rik'e hannunta yayi yana fad'in "lafiya, me kike jine?"
Numfashi ta fara ja amma ta kasa mayar dashi, ga maganar da take so ta fad'a amma ta maqale mata, nan dai aka kira lokitoci aka koma da ita wani d'akin aka fara dubata, da qyar da sud'in goshi aka ceto Khairat, Umar Faruk yayi farin ciki sosai a lokacin kuma koda akayi sallah la'asar aka kauda yaron da Zuby ta haifa, Zuby tayi kuka sosai gashi yan uwanta ne kad'ai tare da ita babu mahaifiya babu wani babba sai Mama kawai.
6📓4📓
Dukansu sun koma gida, Zuby ta koma gidan mahaifinta Khairat kuma dasu Mama da sauran yan gidan sun tare a sabon gidansu, a ranar Khairat tayi kuka sosai tare da qara godewa Allah da kuma Umar Faruk, dan sak sashin daya mata irin sashinta ne na gida, musamman d'akinta da toilet d'inta, haka ma kayan daya zuba mata irin na d'akinta ne duka, lallai dukiya ta kwanta sosai sai dai ace alhamdulillah, babban abin farin ciki shine, islamiyya daya bud'e dake liqe a gidan, wacce malaman ciki suka kasance, shi, Ruk'ayya, Usman, Aliyu da kuma babban yaya Abbakar, kuma tuni suka fara koyarwa a ciki, mutane na zarya zuwa gidan kuma suna samun kulawa sosai, kasancewar su Uwani na wuni gidan kullum yasa Zuby ke farin ciki dan babu wannan aikin da muzgunawar mutan gidan, bayan kwana biyu sunje su fad'awa Mama Zuby ta haihu, amma sai hankalinsu ya tashi saboda ganin yanda Mama ta koma, a mutanen dake kusa da ita suka samu labarin cewa ko bacci ba tayi yanzu sai surutai da sambatu, sun tsorata sosai musammanma da tayi kamar bata sansu ba, haka suka dawo Zulfa'u dake da tsoro cewa tayi ba zata sake komawa ba sai an sallameta.
Ranar suna anyi bidiri da shagalin da babu wanda yayi tsammanin za ayi, dan Umar Faruk cewa yake walima kawai zaiyi, amma saiya shammaci Khairat ya mata duk abinda tayi burin yi, yarinya kuma taci sunan Islam, sai dai abin mamaki shine Umar Faruk yana kiranta da qaramar Khairat, kullum ya kira sunan sai Khairat ta kalleshi tayi murmushi, a haka aka gama sabga suka fara jego cikin kulawar Mammie da Mama dasu Mama Sa'a, ga kuma tururuwar da har yanzu mutane keyi a gidan, kuma a wannan lokacin ne Khairat ta fahimci kyautatawa nada anfani sosai, a haka suka yi Arba'in cike da qoshin lafiya, sai dai Khairat naci gaba da samun kulawa saboda ita aikine aka mata, kuma jikinta da sauqi sosai.
*BAYAN WATA BIYAR*
A lokacin Khairat ta tayar da rigima sai dai Umar Faruk ya dawo da Zuby, da farko bai amince ba, amma data saka mishi kuka tace zata fad'awa malam dole ya yarda, da kanshi yaje danya dawo da ita, amma saboda tasan ba sonta yake ba yasa tak'i amincewa, ganin irin rayuwar da take yasa yace to su koma can gidansu ta zauna, shima da qyar ta yarda ta bishi suka koma gidan ta fara rayuwar 'yanci.
Sai dai sauyawar rayuwa yasa Zuby yin biyayya wa Khairat tunda itace shugabar gidan, wani abun al'ajabi shine soyayyar Islam da Allah ya sawa Zuby a zuciyarta, kullum ta kalli yarinyar sai taga da yaronta na rayé da yanzu yana kamarta shima, hakan yasa Zuby rainon Islam kullum tana tare da yarinyar, tun tana aika yara su d'aukota mata ita har wani lokacin ta kanje da kanta ta d'aukota musamman in yara na school ko islamiyyar dare, yarinya ce mai shiga rai saboda yar qibartada kyawunta ga kuma gashinta da kullum Zuby ke kan mata gyaranshi duk da uwarta na mata.
Hakan nawa Khairat dad'i sosai danta samu damar zuwa islamiyya hankali kwance ba tare da damuwa ba, kuma kullum cikin kyautatawa Zuby take ko abinci ita ke fidda mata sutura kam ba'a magana, karatu kuma sosai ta mayar da hankalinta kanshi, a islamiyya Umar Faruk malamine, a gida kuma miji, wani lokacin yakan takurata sosai, hakan yasa har bata fata ranar shigarshi ajinsu yayi, tafi son Ruk'ayya kullum dake musu Bulugul Maram.
***********
Tunda al'amarin Mama ya girmama bayan ta fito malam ya duqufa wajen gane meye matsalarta, amma duk qoqarinshi bai gane komai ba, hakan yasa ya tuntub'i malaman da yake ganin sune manyanshi, amma a cewar wasu matsalarta kawai sai dai a tayata da addu'a, amma abun kam ba'a magana kamar wacce bakin uwa ya tab'a, haka itama Umar Faruk ya ware mata d'aki a gidan ta fara rayuwa amma kullum cikin matsalarta suke, qoqarin fita daga gida sambatu iri iri, babu sambatun da suka fi daga hankalinsu kamar idan tana fad'in "eh wallahi, nice nan da kaina nayi sanadiyar mutuwar mijina, domin kuwa baqin cikina ne ya kasheshi saboda ya ganni da cikin Zubeida, uwata kuma, ihihi, ai da hushina ta mutu, wallahi na rantse muku da b'acin raina ta mutu, Bala kuma, hum wai wai wai, ai nice nan nasa aka tura mishi aljanu sukak
kasheshi, wannan yarinyar kuma, matarka ba, matar Umar Faruk, ai tunda ta samu ciki muka bayar da cikin ga aljanu, kuma suka zuba mata cutar da zata kasheta, amma wannan tsinannen yaron ya taimaketa."
Wannan maganganu ne da kullum saita fad'esu, shi yasa Zuby bata zuwa inda take, su Uwani ma basa zuwa gidan, ana haka tsawon wata takwas a gidan wata rana ta fita basu sani ba, ashe kiran ubangijinta ne ta amsa, a titi mota ta kad'eta sai labari mutanen gidan suka samu, sam yayanta babu wacce tayi jimamin hakan, wannan dalilin ne yasa malam ya tarasu ya musu nasiha sosai ya fad'a musu mahimmanci uwa, duk da dai yasan alhakine ke binta, duk da sun bita da addu'a amma dai Zuby kam ita dai ta riga data tsani mahaifiyarta kawai.
Ganin ta daina walwala a gidan yasa Umar Faruk ya tilasta mata komawa islamiyya itama, daga ranar suka fara zuwa tare da Khairat da sauran yara, bayan wani lokaci kuma Umar Faruk da kanshi ya nemawa Ishaq auren Ruk'ayya danshi kunya ta hanashi fad'a, a take malam yasa musu ranar tunda sun amince da junansu dukansu, daga ranar aka fara gudanar da shirye shirye, Khairat kam kai kace itace uwar amarya saboda hidimar da take yi.
Kwanahud'u ya rage bikin Ruk'ayya, yara da Khairat dukansu sunyi roqo akan Umar Faruk ya basu hutu a makaranta amma yace sam bai amince ba, hutun rana d'aya kawai ya basu shima dan a ranar ake biki, Khairat ce ta had'a yaran ta kaisu wajen lalle da kitso duk qoqarinta saida karatun yamma ya sub'uce musu, tana sallah magrib ya shigo bedroom d'in nata, amma tana hangen fuskarshi taga ba annuri sai tak'i sallame sallar ta sake tashi tsaye, gabanta faduwa yake dan sam baya wasa indai b'angaren addini ne, a hankali ta saci kallonshi sai kawai suka had'a ido, da sauri ta liqe idonta take maganganunshi suka dawo kunnenta a lokacin da zasu fita tunda sanyin safiya.
"Alkairina, kinga na lamunce muku kuje yanzu ba tare da kunyi darasin safe ba, amma ina sake jaddada miki, wallahi kiyi iya qoqarinki kiga kun dawo kafin a shiga ajin yamma, idan ba haka ba fa rai zai b'ace, ba kuma na yaran ba kad'ai, harda naki tunda ke kike daurin musu gindi, kin yarda?"
"Na yarda baby, insha Allah ma zamu dawo akan lokaci."
"Hum, Allah yasa."
"Ameen." ta fad'a tana manna mishi sumba a kumatu, shima sumbatarta yayi dan hakan harya zama jikinsu.
A hankali ta aje ajiyar zuciya dan tasan dole sai ranta ya b'ace, zata sake satar kallonshi muryarshi ta daki kunnuwanta "idan kin gama qaryar sallah kije ki had'o min kan yaran ku sameni d'akin karatu."
"Bab...." dole tayi shiru saboda harya fice daga d'akin.
Wani zazzafan iska ta furzar cikin sanyin jiki ta sulala ta nufi b'angarensu Mama, zaune ta samu yaran suna cin abinci Islam na ganinta ta sauko daga qafafun Zuby tana cin abinci ta rarrafo, d'aukarta tayi tana fad'in "yahhh, sarauniyar Papa, ya kike, abinci ake ci?"
Nufa tayi da ita wajen Zuby ta aje mata ita akan qafafu tace "rik'eta ina zuwa, zamuje wajen Papa musha bulala ne."
Mama ce tace "wai badai bai hak'ura ba?"
Cikin sanyin jiki tace "Mama ai kinsan ba zai hak'ura ba dama."
"To kinga tafi da Islam d'in wajenshi."
Da mamaki ta kalli Mama tace "me yasa Mama?"
"Ki tafi da ita kedai."
"To Mama." ta fad'a ta d'auki Islam da rigarta ta fara b'acewa da miya bakinta ma haka.
Had'a yaran tayi suka tafi d'akin karatun, da sallama dukansu suka shiga kuma yana amsa musu, dukansu zaune sukayi akan lumtsumemen carpet d'in dake shinfid'e a wajen, wani littafi ne yake karantawa dan haka yayi banza dasu, aje Islam tayi ta rarrafa wajenshi ta rik'e qafarshi, da murmushi ya d'auketa ya aza saman cinyarshi yana mata wasa, saida ya gama sannan ya kallesu duk kowa jikinshi sai 'bari yake, a kausashe yace "meya hanaku zuwa islamiyya da maraice?"
Duka yaran mayar da kallonsu sukayi ga Khairat, itama kallonsu tayi tace "ya kuma zaku kalleni?"
Kallon Umar Faruk tayi tace "baby wallahi....."
"Waye baby?"
Yanda yayi maganar yasa ta kama jikinta, had'e yawu tayi ta sake cewa "wallahi malam nay...."
A tsawace yace "wai magabar ba zata yiwu ba sai anyi rantsuwa, alamar qarya zaki fad'a kenan."
"A'a malam, dama dan ince ne nayi iya qoqarina naga mun dawo da wuri, amma abin yaci tura, gashi ni kaina ban samu lallan qafafu ba, dole sai dai gobe na koma ayi min."
Wani kallon kin rainani ya bita dashi, wani coffre ya bud'a ya d'auko wata zungureriyar bulala ya taso yayo kansu da ita, ai da sauri kowa ya fara qoqarin gyara zama, cikin muryar kuka suka fara bashi hak'uri, aje Islam yayi akan qatuwar kujerar dake d'akin yace "kiyi kallon yanda mamanki zata sha bulala, bata jin magana."
Daga kan Fateema ya faro yace ta bashi hannunta, tuni Fateema ta b'arke da kuka tana bashi hak'uri, ganin yanda take kuka yasa Khairat cewa "malam, nice babba kuma ni na tafi dasu, dan haka amin bulalarsu na d'auka."
Tabe baki yayi yana kallonta kafin ya kalli yaran yace "to an d'auki kaifinku, amma ku sani idan kuka sake ku zan daka ba wani ba."
Cikin tsawa yace "ku b'ace min da gani."
Duk a sanyaye suka tashi suna kallon Khairat, suna fita ya dawo kanta yace "bani hannunki, kuma kiji da kyau, wallahi idan kika sosa hannunki ko kika janye hannun, to duk sun zube koda kuwa na miki bulala ta kusa data qarshe ne."
Bud'e baki tayi tana kallonshi tana tunanin yanda haka zai yiwu, zaro mata ido yayi yace "kinji dai na rantse miki ko, wallahi nace miki."
"Hannunki." ya sake fad'a.
Had'e wani irin abu tayi mai nauyin gaske daya tokare mata maqoshi, rintse ido tayi ta fara zuro hannun dama a hankali kuma tana d'an janshi da baya, tsawar daya sake mata ce yana fad'in "kefa nake jira." yasa ta zabura ta mik'o hannun.
D'aga bulalar yayi ya sauke mata ita ira a hannu, qara ta saki tare da mayar da hannun cikin hijabi, a kaurare yace mata "kinsan dai ba zaki sani kaffara akan wannan abunba ko, dan haka ki d'auka ban fara ba har yanzu."
Kallonshi tayi sai dai tsagwaron gaskiya kawai ta gani a idonshi, dan haka ta yanke shawarar tsayawa maimakon ta wahalar da kanta a banza, fito da hannayen tayi duka ta mik'a mishi amma idonta rufe, ai kuwa tsuga mata ya dinga yi kai kace qiyayyace tsakaninsu, kamar wasa saida ya mata bulala goma sha biyar ta mutum uku, dan duk d'aya yana da biyar ne, zai zuba mata ta sha shida tayi saurin bud'e idonta ta sauke akanshi, saida gabanshi ya fad'i saboda ganin yanda idonta sukayi jawur dasu, hawayene suka gangaro mata langab'e kai tayi ta marairaice cikin muryar kuka tace "baban Islam, dan Allah."
Shiru tayi daga nan, da sauri ya kawar da kanshi yayi qoqarin mayar da qwallan da yaji na barazanar taho mishi, juyawa yayi ya kalli Islam dake son saukowa daga kan kujerar, maida kallonshi yayi ga Khairat d'in data kasa janye hannayenta, dakewa yayi yace "meye?"
Lumshe ido tayi yayin da gashin idonta yayi sharkaf da hawaye, kasa rik'e kanshi yayi baisan sanda ya jefar da bulalar ba ya durqushe gabanta ya rumgumota a jikinshi, cikin kunne ya rad'a mata "ki gafarceni alkairina."
Kafin tayi magana ya d'agota ya kamo hannayen nata ya rik'e yana kallo, sunyi jawur duk shatin bulala ya fito, sumbatar hannayen yayi ya had'esu wuri d'aya yana kallon fuskarta cike da nadama, a hankali ya sake furta "kiyi hak'uri kinji baby."
Fizge hannayenta tayi ta mik'e tsaye tace " naki nayi hak'urin, kullum nayi laifi baka tab'a min uzuriba saika dakeni, kuma kafin ka dakeni saina baka hak'uri amma baka hak'ura, shine yanzu ni zaka bani danka rainani."
Fita tayi daga d'akin ta koma b'angarenta, bin bayanta yayi da Islam a hannunshi, hak'uri ya fara bata da rarrashinta amma tak'i sauraronsu, saida taga ya damu sosai kad'ai tace "na yarda zan hak'ura, amma da sharad'i?"
"Meye sharad'in to."
"Sai inka amince zaka dawo da Zubeida d'akinta."
Wani tar yayi da ido tare da jan tsaki, shiru ya mata dan haka tace "yanzu baby wannan alfarmar ce ba zaka iya yi min ba? alhalin kana fad'a min zaka iya yin komai saboda ni, kana cewa ranka fansane ga nawa ran, amma ace wannan alfarmar na gagara samunta a wajenka, bafa sab'on Allah nace kayi ba, hasali ma wata sunna ce zaka qara dabb'aqawa mai k'arfin gaske, amma shikenan tunda ba zan samu ba, kaga yanzu saina dinga rik'e kaina wajen tambayarka alfarma dan nasan ba zan samu ba."
Harta juya zata koma d'akinta ya rik'e hannunta, zaunar da ita yayi akan cinyarshi yace " indai wannan ne zaisa kiji a ranki kin wuce komai a wurina, to na amince, ki fad'i ranar da kike so ta dawo gidanta."
Da farin ciki a ranta tace "kawai a sake d'aura muku aure ranar d'aurin aurensu Ruk'ayya."
"An gama alkairina."
Sumbatar kumatunshi tayi sannan ta mik'e ta shiga d'akinta, shi kuma Islam ya d'auka yana fad'in "qaramar alkairina, ina fatan zakiyi koyi da hallayen mahaifiyarki, ita rayuwata ce, ita aljannata ce, ita komai tawa ce, ita dabance a gareni, ba ayi ba kuma ba za'a tab'a yin wacce Umar Faruk zaiso ba kamar mahaifiyarki, ita alkairi ce a wajen Papanki, ina sonta ina qaunarta fiye da komai." ya qarashe da sumbatar bakin yarinyar.
**************
Lokacin da Umar Faruk yaje wa da Zuby da maganar bata amince ba yanzu ma, amma da Mama tasa baki saita amince a sake d'aura musu aure a karo na biyu, nanfa hidima ta qaru yayin da Khairat tayi farin ciki da hakan, washe gari ganin babu wani shiri da Zuby keyi yasa Khairat had'a wani sirri daga cikin sirrin da Mamie ta bata ta aika aka kai mata, da farko taji d'ar a ranta amma data tuna Khairat ba kamar ita bace mai barbad'e saita daure tasha, daga ranar har zuwa kwana ukun daya rage musu ita ta dinga musu gyara, dama kuma ita kema Ruk'ayya d'an abinda zata iya.
Gobe d'aurin aure, anyi sallah magrib gidan ya qara kaurewa da hayaniya, yayin da su Khairat suka kama aiki gadan gadan, duk wanda yasan Khairat ya ganta tana qoqarin d'ora babbar tukunya da ita kanta zata iya shiga ciki a rufeta sai yayi mamaki, tana tsakiyar mutane ta d'ora tukunya Umar Faruk ya shigo da Islam a hannunshi tana kuka, kamar daga sama taji muryarshi yace "alkairina."
Juyowa tayi tana goge zufa da zaninta, takowa tayi ta nufo wajenshi, kallonta yake harta tsaya gabanshi yace "me ki keyi hakane? yaushe kika fara aikin da har zaki fara gwagwarmaya da waccen manyan tukunyan?"
Shagwab'ewa tayi tace "baby, me yake damuna to? yanzu fa Islam watanta tara da haihuwa, kana gani yarinyar dake qoqarin tafiya ma."
"Sai akayi me?"
Shiru tayi tana kallon Islam dake kuka har yanzu tana qpqarin zuwa wajenta, hannu tasa zata karb'eta yace "dan Allah ki daina sakarwa yaran nan ita suna fita da ita waje ana magrib."
Karb'arta tayi tana fad'in "kayi hak'uri ba za'a sake ba, bansan sun fita da ita Ba."
Saida ya d'an saci kallon mutanen dake wajen sannan ya aika mata da sumba, itama mayar masa tayi ba tare da sun tab'a juna ba, juyawa yayi zai fita tace "ango ango, ango Zubeida."
Juyowa yayi yace "ango Khairat da Zubeida dai."
"Kuma baban Islam ba." cewar wata abokiyar wasanshi Chapa'atou.
Hararanta yayi yace "ke kuma wa yasa bakinki?"
Dariya Khairat tayi taja kujera ta zauna zata bawa Islam nono tana fad'in "dama baban qaramar Khairat ki kace da baice miki haka ba."
"Fad'a mata dai, ai kune ke kiranta da Islam, amma ni inkiyar da nake mata itace alkairi."
Kallon Khairat yayi yace "na manta ban fad'a miki ba, Papa yazo fa suna tare da malam."
"Da gaske, amma shine basu fad'a min ba? koda yake ma yanzu sun daina sona sunfi son Islam, amma zasu shigo hannuna, nasan ba zasu bar nan ba dole zasu nemi Islam."
"To ai shi yasa na kawo miki ita danki bata nono tasha, dan da ita zasu tafi gida ta kwana acan."
Waro ido tayi tace "wa, autar tawa zan bayar ta kwana ba kusa dani ba? a'a ma karku fara."
Duk da mutanen dake wajen bai hanashi yowa kanta ba yana fad'in "ina autar take?"
Tashi tayi daga kujerar ta nufi wajen Mama Sa'a ta zauna akan tabarmar tana dariyar mugunta, wani shegen kurmanci ne sukayi daga nan dani kaina ban fahimta ba, naga dai ya kashe mata ido tare da cije lips d'inshi, itama idon ta kanne mishi ta d'aga gira sama ta lashe baki, juyawa yayi zai fita ya nuna mata yatsa yace "zan kamaki."
Gwalo ta bishi dashi harya fita mutanen wajen suna mamakin yanda Umar Faruk ya canza sosai, a da idan ana taro irin haka idan har kayi sa'ar samun ganinshi to da qyar zai tsaya ku gaisa saboda miskilanci da rashin san magana irin nashi, amma yanzu gashi a arha, Chapa'atou dake tare da wata yar uwarsu dattijuwa ce tace "gaskiya idan nice yah Umar, wallahi babu abinda zai sani na maido da Zubeida bayan nasan komai game da ita."
Dattijuwar tace " to ai bashi bane zai maidota gaban kanshi, nida na kwana biyu gidan ai naji meya faru, Khairat ce da kanta tace ya maidota, amma fa harda wani cijewa ita ba zata koma ba, saida Maryam d'in tasa bakinta kad'ai."
"Jar uba, lallai ma ta raina mutane, ita yanzu duk abinda tayi amma har za'a nemi ta dawo tayi tirjiya, wallahi Khairat ta zama yar halak, ta bamu mamaki sosai, farkon zuwanta gidan nan da nazo ganin amarya ko kallon tsiya bata min ba, amma yanzu kaga kamar ba ita ba."
Dariya tsohuwar tayi tace "aike kad'an kika gani, kwana bakwai da nayi a gidan nan naga abubuwa da dama, kinga hidimar da take, yaran nan kowa nata ne kamar yayan cikinta, uwayen kuma kamar su suka haifeta, kai gaskiya yarinyar tayi sai dai fatan Allah ya tsare."
Haka suka dinga tattaunawa akan Khairat harta wuce ta gabansu ta nufi b'angarenta tana amsa wayar Umar Faruk, sake jaddada mata yayi ta shirya Islam yama Papa alk'awarin zasu tafi da ita, cike da jin za'a rabata da yarta tace "amma me yasa babu, yarinyar nan nono take sha, ya zasuyi idan ta hanasu bacci tana buqatar mahaifiyarta?"
"Ba zatayi ba, ni na fad'a miki haka."
"To amma baby..."
"Amma me kuma yar aljanna, kiyi abinda hamagon mijinki yace miki mana."
Murmushi tayi tace "shikenan to zanyi, ka gafarci bahamagiyar matarka da bata jin maganarka sau d'aya."
Dariya yayi da saida taji sautinta yace "aike yar aljanna ce ba kwankwanto, buri da fatana d'aya a duniya shine, Allah yasa nima na shiga aljanna danna rayu dake."
Ajiyar zuciya ta sauke cikin jin dad'in maganganun mijinta tace "idan har na bud'a idona a aljanna ban ganka ba, to na tabbata qamshi da hazon gidanne ya b'oye min mijina."
"Ko kuma matan aljanna sun rik'eni ba." yayi maganar yana qyaqyata dariya.
"Tabdjim, aiba zata sab'ub'a, Allah ko a aljanna dani kad'ai zaka kasance."
Dariya yake kamar yana gabanta kafin yace "kina kishina har haka amma kika sani dole saina raba miki kaina biyu?"
"To ai baka sani ba, zan iya kishi da mata indai ta gidan duniya ce, amma ina jin tsoron kishi da matan aljanna, saboda nasan sunfini da komai, sannan matane da suke burin mazan duniya su riskesu idan sunga basuyi dacen mata ba a duniya."
"Amma ai ban dake, Khairat ke ba kya ciki, wallahi ke yar aljanna ce, na tabbata matan aljanna ma zasu zama hadimankine kawai, amma ba matan mijinki ba."
"Zaka fasa min kai Umariri."
"Toya na iya Khairiri, ke d'ince ta musamman a wajena, idan kika cire farin cikin da nake idan ina cikin masallaci, to nafi farin ciki idan ina tare dake."
Ajiyar zuciya ta sauke tace "idan na biye maka zan kwana a haka, bara na saka mata kaya su tafi, amma ka sani yaufa zan gurzaka sosai."
"A ina?" ya ya fad'a yana d'aga murya.
Kwantar da murya tayi tace "a kan gado mana, tunda yau babu Islam a b'angaren namu, dan haka yau sai kowa na gidan nan yaji ihunka."
"Na shiga tara, dan Allah ki rufa min asiri, wallahi nasan zaki iya, kar kisa mijinki ya haukace mana ko ya zama sakarai a idon Jama'a, ki taimaki wannan bawan Allah mana, kinji babyta." ya qarashe da sigar rarrashi.
"Naqi d'in, saika gane ka shigo hannun mata."
Tana fad'a ta kashe wayar ta aje ta fara sauya mata kayan jikinta, tsaf ta shiryata cikin kyakyawan shiri sai qamshi take kafin ta fito da ita.......
Koda Papa yazo suka shiga falonshi suka gaisa sosai, sun fara tab'a hira kuma Papa yace "malam akwai wani muhimmin abu daya kawoni wajenka."
Gyara zama malam yayi yace "to Alhaji ina sauraranki, Allah yasa muji alkairi."
Murmushi kawai yayi kafin ya fito da wata enveloppe daga aljihunshi ya bawa malam d'in, amsa yayi ya kalli envellope d'in da kyau sannan ya kalli Papa yace "wannan fa."
"Malam a karatun daka mana jiya ka nuna mana mahimmancin yin wasiyya, wannan ne yasa koda naje gida na rubuta kuma na kawo maka, dan kai kad'ai ne kafi cancanta daka adanata wajenka."
"Idan ka duba zaka gani a ciki, na raba dukiyata gida biyar, uku daga ciki, ayi hidimar addini da ita, biyu a kuma a rabawa magada."
Da farin ciki malam yace "a gaskiya naji dad'i sosai da faruwar hakan, ina fatan ubangiji ya saka maka da mafificin alkairinsa, Allah kuma yasa hakan ya zama sanadiyar shigarka aljanna."
"Ameen ameen malam, dama wannan ne ya kawoni, ni zan tafi."
Tare suka fito yayi daidai da fitowar Umar Faruk d'auke da Islam, Papa na ganinta ya saki murmushi tun basu qaraso ba ya tara hannu dan karb'arta, da yake yarinyar ma ta gane Papa sai kawai ta tafi wajenshi tana bud'e baki alamar dariya, amsarta Papa yayi saida ya danna mata sumba kusan guda goma duk suna kallonshi kafin ya rumgumeta yana shaqar qamshin jikinta, ya jima a haka kafin ya dago fuskarta ya kalla, d'an qaramin hijabin da aka saka mata ne yasa Papa ya ganta sak Khairat da tana qarama, murmushi Papa yayi yace "lallai qaramar Khairat."
Umar Faruk dake kallon tsantsar soyayyar da Papa kewa yarinyar ne yayi dariya yace "kuma haka kuke kiranta ne?"
Kallonshi Papa yayi yace "ba kaga tana kama da mahaifiyarta ba?"
"Eh to, da yake ban ganta ba tana qarama." cewar Umar Faruk.
"Hakane kam, bara ka gani." ya fad'a yana fito da wayarshi a aljihu, saida ya nemo photon Khairat sannan ya bashi wayar yace "ka ganta nan tana qarama."
Amsa yayi ya d'ora idonshi akan photon, baisan dariya ta bayyana a fuskarshi ba sanda ya kalli photon Khairat bata wuce shekara d'aya zuwa da wasu watanni, tsaye take da kayanta riga da wando masu kyau farare qal, masha Allah an gyara mata gashinta amma harga wuya, sai chocolate d'in dake hannunta ta turo baki gaba kamar zata fashe da kuka, maida kallonshi yayi ga Islam dake hannun Papa, dan badan yaga Khairat a tsaye ba da sai yace Islam ce kawai saboda matuqar kamar da suke, kallon Papa yayi yace "Papa ko zan iya turawa?"
"Ba komai, amma karka tsokaneta dashi, bata so ana ganin photonta tana yarinya, a qalla akwai photunanta a d'akina sunfi guda d'ari, amma ko d'aya bata da wai bata so."
Turawa yayi a wayarshi harya matsu ya shiga gida ya ganta, Papa ne ya miqo mishi Islam da cewa "gata ko, ni zan tafi, ka gaishe da shalelena ba zan samu damar ganinta ba."
Kafin yasa hannu ya karb'eta saida Papa ya sake sumbatarta kamar karya rabu da ita, murmushi yayi yace "Papa ai kawai ku tafi da ita, idan ma tayi kuka ku bata madara tasha."
Da farin ciki yace "anyi haka Umar Faruk, mahaifiyarta ta sani?"
"Ta sani Papa, kuje Da ita kawai."
"Kai amma gaskiya naji dad'i sosai, saida safe."
Da haka sukayi sallama Papa ya wuce shima ya shiga ciki, amma daya samu Khairat harta koma ga aiki dan haka ya qyaleta kawai ya shiga wani sha'anin shima.
A lokacin daya shigo gidan kuma dare yayi sosai saboda gidan har yanzu akwai wanda basu kwanta ba, ya sameta har tayi bacci ita kuma dan haka yayi wanka shima ya kwanta ba tare daya tasheta ba dan yasan tana tare da gajiya sosai.
***************
Misalin k'arfe 09:00 daidai aka d'aura auren Ruk'ayya da Ishaq, Umar Faruk da kuma Zuby a karo na biyu, hidima ake sosai tare da walima, yayin da Khairat ke juyawa yanda take so saboda babu Islam a gabanta, a haka akayi shagali sai yamma Mamie tazo tare da Islam, koda dare yayi duk kowa ya watse aka tafi rakiyar Ruk'ayya gidanta, Zuby kuma dama daga wani d'akin ne aka wuce da ita wani d'akin.
10:30 na dare Umar Faruk ya sallamo cikin falon, Khairat ya samu zaune da Islam har tayi bacci, aje Islam tayi ta tareshi tare da mishi sannu da zuwa, zai sumbaceta tayi saurin gocewa tana fad'in "a'a, ba yanzu ba baby."
"Me yasa?" ya fad'a yana gyara zaman babbar rigarshi.
Wasa ta d'anyi da idonta kawai taja hannunshi suka nufi d'akin Zuby tana fad'in "muje na rakaka d'akin amaryarka."
Binta kawai yayi saida suka kai qofar d'akin Khairat taja ta tsaya, kallonta yayi kawai tace "kaje kawai, saida safe."
Da saurin ta juya ta dawo ta d'auki Islam ta shiga d'akinta, k'in kallonshi da tayi ya fahimtar dashi tana so ta b'oye yanayinta ne ko kuma hawayeb fuskarta, da sallama ya shiga d'akin Zuby dake kwance ta amsa tare da tashi zaune, sannu da zuwa ta masa ya amsa tare da aje ledojin hannunshi, babbar rigarshi ya cire ya aje sannan ya d'auki d'aya ledar ya fito da ita yace "ina zuwa."
Bud'a d'akin yayi ya shiga ba tare da yayi sallama ba, zaune ya sameta taba Islam baya ta fashe da kuka, tana ganinshi tayi saurin mik'ewa tsaye tana share hawayen, cike da qarfin hali da son nuna ba komai tayi murmushi tace "baby, me kake yi nan kuma?"
Saida ya tsaya gabanta sannan yace "abunfa bashi da sauqi, amma kin kasa gane haka, na fahimci kina son b'oyewa ne kuma na jinjina miki akan hakan, amma karki bari hakan ya cutar dake."
Rufe bakinta tayi ta fashe da kuka ta fad'a jikinshi tace "ina so na taushi zuciyata amma na kasa, kukan nan ne kad'ai zaisa naji sauqi a raina, amma kayi hak'uri banyi dan na b'ata ranka ba."
Shafa bayanta ya dinga yi yana rarrashinta har saida tayi shiru, toilet yajata ya cire mata kaya da kanshi ya mata wanka ya saka mata kayan bacci ya bata maganinta na ciwon kai tasha, dan tana tsoron kanta ya fara ciwo baya kusanta, sannan ya kwantar da ita ya musu addu'a tare da Islam sannan ya fice daga d'akin, yana fita ta sake fashewa da kuka tana jin kamar tayi ihu, ta koma tana kuka amma babu sauqi a al'amarin, dan haka kawai ta d'oro alwala ta kabbara sallah, ba ita ta kwanta ba saida tayi sallah asuba, a lokacin Islam ta farka ta bata nono bacci ya d'auketa, koda ta farka sai taji wani shaqat a zuciyarta ba wata damuwa, hakan ya mata dad'i sosai da farin ciki tayi duk wani abinda ya zame mata jiki tasan tana yi a wannan lokacin.
Tana gamawa ta shiga cuisine (kitchen) tare da abin sauraronta ta maqala a kunne ta fara aikin hankali kwance, saboda Islam tasha wanka ta koma bacci, aikinta take tana rausayawa ita kad'ai tare da bin waqoqin da take sauraro, tana cikin aikin taji kamar motsi a bayanta, da sauri ta jiyo dan ganin waye, tana ganin Umar Faruk tayi saurin cire abin sauraron ta rik'e a hannu tana zazzare ido, danya hanata sauraron waqoqi barkatai musamman idan tana cikin nishad'i, takowa yayi har gabanta ya tsaya ya janyo kunne d'aya yasa a kunnenshi, cirewa yayi yana kallonta yace "yanzu bana hana ba?"
Kamar zatayi kuka tace "kayi hak'uri baby."
"Shikenan na hak'ura, ina Khairat?"
Sakin jikinta tayi tace "ta koma bacci."
Hannu yasa ya bud'e tukunyar data rufe yana fad'in "shalelen Papa kenan, hutu kawai."
"To ai mamanta tabiyo." cewar Khairat.
"Na sani mana, tunda kamarta d'aya ma da mahaifiyarta kamar an tsaga kara."
Kallonshi tayi ta d'auki albasarta taci gaba da yankawa tace "a ina kaga mamanta? da ace ka tsere min da shekaru masu yawa ne sai nace ko ka tab'a ganina."
Kallonta yayi kafin ya d'auki cokali yana juya mata sauce d'in yana fad'in "aiba zaki qara min wayo ba, nasan komai a game dake, kullum na kalli qaramar Khairat saina dinga tunanin ina ta samu wannan tsalelen kyawun na yarinyata, ashe dai mahaifiyarta tayo."
"Wai da gaske ka ganni?"
Kafin ya bata amsa tace "nasan ma aikin Papa ne, dansu keda photona bila adadin."
Rufe tukunyar yayi ya aje cokali ya rumgumeta ta baya yana shaqar qamshinta tare da fad'in "na ganki alkairina, saina kasa banbance a wane matakine ki kafi kyawu, yanzu ko kuma a matakin yarinyata."
"Ai yanzu nafi kyau, kaima ka sani."
"Na gani to." ya fad'a yana juyo da ita gabanshi.
Qura mata ido yayi yana kallon fuskarta a hankali ya kai bakinshi a nata ya fara tsotsa, sunyi nisa a duniyarsu suka ji wani qauri qauri, da sauri suka raba jikinsu suna kallon tukunyar bisa wuta, Umar Faruk ne ya kai hannunshi ya bud'e hayaqi yayi sama, kallon juna sukayi Khairat ce ta turo baki gaba kamar zata fashe da kuka, shima turo bakin yayi yana kallonta ya kama kunnuwanshi alamar ban hak'uri, kawai sai suka tuntsire da dariya kuma har suna rumgume juna, kashe gas d'in tayi tace "tunda wannan ya qone, sai kuyi hak'uri kuci qwai da dankali."
"Ni dama shi nake sha'awar naci." ya fad'a yana satar kallonta.
Qwai ta d'auka yayin da ta had'ashi da dankalin turawa ya ta fara ferewa, zata buga qwan taji yace "ki dai buga a hankali, karki ruguzashi kamar yanda ki kayi a waccen ranar."
Da dariya tasa qugu ta tureshi tana fad'in "ai dane wannan ba yanzu ba, kaima kasan haka yanzu matarka gogaggiyace."
"Uhum, zan gani dai."
Kallonshi tayi tace "baby, amma dai ba zaka fara fara fita aiki da wuri ba ko?"
Hararanta yayi yace "me yasa, yau ma akwai islamiyya, amma kafin na shiga ajin farko zan fita na dawo."
Cikin shagwab'a tace "haba baby, dan Allah ka taimaka ka bamu hutu, ka ganni nan wallahi a matuqar gajiye nake, kawai saboda bana so kaci abinci a wani wurine ba nan ba yasa nake had'a abin karin nan, idan kace mu shiga aji a haka Allah bacci zanyi maka."
"Kiyi baccin mana, ai tsumagiyata nanan."
Aje wuqar hannunta tayi ta matso daf dashi ta rik'e qugu tace "me zakayi, nace me zakayi, dukana wai? to gwada ka gani, wallahi da kayi nadamar da har iya tsawon rayuwarka ba zaka manta da wacece Hajia Khairat ba."
Gimtse dariyarshi yayi shima yace "to ki jaraba ki gani mana, ba Hajia ba ko hajijiya ce Allah zaneki zanyi, kaji min marar kunya kai."
Shaqo wuyan rigarshi tayi ta kara bakinta a hancinshi tace "wacece marar kunya, Ni? yanzu baka ji kunyar fad'a min haka ba, lallai ma yaron nan."
Da sari ya fizge rigarshi ya shaqi kwalar rigarta yana fad'in "waye yaron, Ni, ni kike kira da yaro? karki sake, wallahi kika sake qalubalantar mazantakata zaki gane kurenki."
Itama dai fizge rigarta tayi ta d'auki wuqar dake gefenta ta d'ora mishi a wuya a wajen da babu kaifin tana fad'in "zan zubar da jininka."
Shiru tayi tare da kallon qasan cikinta, da mamaki ta d'ago ta kalleshi dan bataga lokacin daya d'auki cokali mai yatsun daya d'ora mata a ciki ba, aje wuqar tayi tace "hamago, kullum kai ke nasara a kaina, wai me yasa ne haka?"
Aje cokalin yayi shima ya rumgumeta jikinshi yace "ban sani ba nima Khairiri, haka kawai gudanar jinina ke nunkuwa a duk sanda nake kusa dake, kuzarina kuma yana rub'ayya fiye da yanda zan kasance a wani wajen daba kusanki ba, amma duk da haka kuma Khairat ce nasarar Umar Faruk."
D'ago kanta tayi ta kalleshi tace "haka nima, Umar Faruk kaine silar duk wata nasarata da kuma kasantuwata akan hanya madaidaiciya, wannan yasa nake qara sonka a kullum a kowane fitar numfashi."
Laqace mata hanci yayi yana fad'in "ban tab'a tunanin zan mallakeki ba, musamman a lokacin da kike ji da kanki da kuma izza da iko."
Turo baki tayi tace "bana son tuna bayan nan fa, nima ai ban tab'a tunanin zan mallakeka saboda marin daka tab'a kwad'amin, a gaskiya a ranar na tsorata da kai, kuma raina ya b'aci sosai saboda ganin wani ya d'aga min ysata, abinda ba'a tab'a yi ba."
Dariya yayi yace "ashe kinji ba dad'i, amma kuma ba kiyi tunanin ni me zanji ba? aiko yanzu kika qara marina, to zan sambad'eki da marine."
A raunane ta kalleshi tace "kasan kuwa a waccen ranar marin daka min ne yaja na kwanta asibiti saboda b'acin rai."
Ajiyar zuciya ya sauke yace "kiyi hak'uri to."
Maqale kafad'a tayi irin na yara tace "um um."
Dariya yayi ya durqusa gwiwoyinshi biyu ya kalleta yace "ki rama to, idan hakanne zaisa ki hak'ura, ni Umar Faruk zan tsayar da kumatuna har lokacin da kika gaji dan kanki kika dakata."
Maqale mishi tayi a wuya ta sakar mishi nauyinta hakan yasa suka fad'i kwance a tsakiyar cuisine tana fad'in "wace ni na mari mijina, waccen ma ai dan tabbatar da soyayya ne a tsakaninmu."
Da dariya ya kalleta yace "uhum, ashe dai tun a waccen lokacin ma kika kware min, yarinya taga dogon saurayi mai dogon hanci."
Da dariya ta laqace hancinshi tana fad'in "inji wa? ba wani nan malam, kai dama maman Dady tace tsawonka yayi yawa."
Ciccib'awa yayi Da ita sukayi zaune yana rumgume da ita yace "ita maman Dadyn ce tace haka?"
Gira ta d'aga masa shi kuma yace "barni da ita, bansan bata cikin masoyana ba sai yanzu, amma insha Allah d'an da zata haifa zata haifi jarumi ne kamar ni kuma harda tsayin ma da komai."
"Ameen." cewar Khairat.
Da irin wannan shirmen suka qarasa wannan girki da rabinshi surutu ne, saida suka fito falo jera kwanukan abincin suka tuna akwai Zuby fa a b'angaren nasu, tana zaune tana jin hayaniyarsu ita dai tayi shiru tana kallon tv.
************
Haka rayuwar taci gaba da kasance musu cikin farin ciki da jin dad'i da kuma soyayya, har yanzu qalubale na rayuwar aure Khairat bata fara fuskantarshi ba dangane da mijinta, wanda Umar Faruk na ganin Khairat d'in ce silar faruwar hakan, dan duk yanda ranshi zai b'ace ko kuma ta b'ata mishi rai, to a take a wajen take bashi hak'uri tare da rarrashi, dole yake saukowa ko baiyi niyya ba, Zuby kuma yanzu ta kwantar da kai, zaman lafiya da mutunta juna kai kace yan uwane a yanzun, sosai suke zaman lafiya hakan kuma nawa Umar Faruk dad'i sosai.
Yanzu Khairat ta aje fita aiki a ma'aikata yayin da ta damqa ragamar kula da komai a hannun manager, amma daga gefe saita bud'a wani qaton boutique data cikashi da kayan mata komai da komai, shima kuma yana qarqashin kulawar wata mata ce sai dai taje ta dubo ta dawo gida, karatu da kuka da mijinta ne kawai a gabanta da kuma yayanta, arziqi na hab'aka sosai musamman na Umar Faruk kamar yanda wuta kecin busashen ice, ta ko ina bud'i yake gani hakan yasa ya dage sosai wajen taimakawa addininshi da k'arfinshi da kuma dukiyarshi, yayin da ya kwashi suka iyalinshi suka koma sa'udiya yana sake d'aukar karatu.
*SHEKARA TAKWAS* suka d'auka basa qasar, a lokacin idan ka gansu sai kace haihuwar can ne dama, musamman Khairat da Islam da kuma yaran da aka haifa acan, yanzu haka Zuby nada yara hud'u, Imane ce farko sai Ihsan, Kaussar da kuma qaraminsu Marwane, Khairat kuma tana da uku, Islam, Ammar da kuma Usseimine, kuma dukansu saida aka m Khairat aiki ta haifesu, shi yasa ma likitocin garin suka bata shawara akan a juyar da mahaifarta domin lafiya idan tayi haihuwa ta hud'u, Umar Faruk kuma ta amince da hakan, dan haka yanzu take cike da tsoro bata fatan d'aukan wani cikin dan karsu juyar mata da mahaifa, koba komai tana so ta cikawa Umar Faruk gida da yaran da suka fito daga tsatsonta, yaran na d'aukar karatu a masallacin madina kuma hadda kawai ake, hakan yasa iyayen da yaran duka ke jin dad'in zaman acan, amma haka suka dawo suka ci gaba da rayuwarsu da kuma ci gaba da harkokin da suka bari a hannun mutane.
Bayan dawowarsu sun tarar da abubuwa sun faru, a ciki akwai qara aure har biyu da Abbakar yayi, da kuma auren Usman da Aliyu, islamiyya kuma nanan yanda take, amma yanzu daga cikin malamai masu koyar da tahfizin Qur'ani harda Islam da qaninta Ammar, rayuwar Alhamdulillah Zuby da Khairat kai kace ba kishiyoyi bane, zaman lafiya kawai suke, yayin da Umar Faruk ya bawa Zuby jari itama ta fara siye da siyarwa a cikin gida.
***************
Mammie ta dawo gaban yarta da zama saboda tsufa daya kamata tana buqatar mai tamaka mata a yanzun, yayin da Mamie da Papa suka k'i tsufa da soyayya, dan yanzu ne Papa ke nunawa Mamie soyayyar da bai nuna mata ita ba a baya, suma dai suna zaune lafiya cikin farin ciki, Papa ne yama Mamie wata kyauta mai girman gaske data kusan fitar da ita a hayyacinta, kuma ya batane saboda hak'uri da tayi dashi a lokacin da ba kowace mace bace zata iya zama dashi, dan haka Mamie da taji Khairat ta dawo gari tace tana son ganinta idan ta huta, ta fad'awa Umar Faruk kuma yace ta shirya da kanshi zai kaita tare dasu Islam.
***********
Khairat ce zaune akan sallaya ta mik'e qafafu tana azkar na sabah, da sallama Islam ta shigo d'akin tare da zaunawa tana fuskantar mahaifiyarta, amsawa Khairat tayi Islam ta d'ora da "Ina kwana Mamie, antashi lafiya?"
"Lafiya qalau yarinyar da babu kamarta, kin tashi lafiya kema?"
Da murmushi Islam ta amsa da "lafiya lau cher mère (uwa mai tsada), ya gajiya ya kuma hak'uri damu?"
Dariya Khairat tayi tace "ai yara irinku iyayensu basa hak'uri dasu, hasalima kune zakuyi hak'uri da rigimar iyayenku."
Hannayenta tasa ta fara latsawa Khairat qafafunta Khairat d'in ce tace "kamar kinsan kuwa qaramin qannanku yana saka min ciwon qafafu."
Cike da nutsuwa ta kalli mamanta tace "Mamie, zaki sake haifa mana qane ne?"
Kai ta d'aga mata kafin tace "insha Allah ba."
Walwalar fuskarta ce ta d'auke tace "Amma Mamie me yasa ba zaki huta haka ba? kinfi son kullum a dinga fed'eki wajen fito damu duniya."
Dariya Khairat tayi tace "Islam, duk wahalar da nake sha daga d'aukar cikinku har zuwa haihuwarku, ina d'ora idona a kanku saina ji na manta da wahalar dana sha, ina sonku kuma ina sonku fiye da kaina, dole zan juri kowace irin wahala wajen ganin kunsha iskan duniya kuma, bugu da qari bana takaicin haifawa mahaifinku 'ya'ya, da ina da iko Islam saina haifawa mahaifinku yara goma sha biyu, sai dai bansan ko zan iya ba dan ana barazanar rabani da mahaifar gaba d'aya, amma a gaskiya a yanzun haifawa mahaifinku yara ne kad'ai abinda nake ganin zan iya yi na biyashi alkairanshi gareni."
Islam kam da ido kawai ta kafe mamanta tana saqe saqe a ranta, jin shirun yasa Khairat qyasta mata hannu, a d'an zabure ta kalli mahaifiyarta tace "Mamie, ina jin dad'in yanda kike zaunar dani kina fad'a min abinda ya shafi rayuwarki, duk da shekaruna sun kasa amma bakya gudun zaunawa dani kiyi hira, a gaskiya ina jin dad'in hakan."
Da murmushi a fuskarta tace "kefa 'ya macece, dolena na n'a a matsayina na uwa na jaki a jiki, inhar ina so kema idan kin girma karki b'oye min komai daya shafi rayuwarki."
Murmushi kawai Islam tayi yayin da Khairat tace "an jima zamu tafi gida wajensu Mamie saiku shirya da wuri keda qannanki."
"To Mamie, yau zanga mai gidana da 'yar tsohuwa."
Duka Khairat ta kai mata ta goce tana fad'in "uwaki tsohuwar ai."
Sallamar Umar Faruk tare dasu Ammar da Useimine ne yasa suka nutsu suka amsa, qara yaran suka zube suka gaishe da mamansu ta amsa tare da shafa kawunansu tana fad'in "har an dawo daga masallaci kenan?"
"Eh Mamie." cewar Ammar.
"Da fatan dai kun min addu'a ko?"
"Eh Mamie, mun miki."
"To na gode sosai, Allah ya albarkaceku yaran kirki."
"Ameen." duka yaran suka amsa.
Kallon Umar Faruk tayi dake zaune bakin gado yana kallonsu cike da qauna tace "baby ina kwana."
"Lafiya qalau, kin tashi lafiya?"
"Lafiya lau, ya gajiya?"
Islam ce ta kalli babanta tace "ina kwana Papa."
Saida ya shafa kanta yace "Lafiya lau alkairina, kin tashi lafiya?"
Kallonshi tayi tana murmushi shi kuma yace "kullum kina mamakin wannan sunan ko?"
"Eh Papa, ni dai nasan Mamie keda sunan, amma kuma sai kuka kirana dashi."
Kamo hannunta yayi yace "kina ji ko? karki damu kanki da wannan sunan, ina jin dad'in sunan ne saboda soyayyar da nakewa mai sunan, zan iya kira kowace mace da sunan amma kuma mahimmancinshi yasa ke kad'ai nake fad'awa shi saboda girmanki a zuciyar Papanki, sannan a ranar da aka fito dake daga cikin mahaifiyarki, a lokacin mamanki tayi barazanar barina a doron duniya, amma da izinin ubangiji sai Allah yasa kwananta basu qare ba, hakan ma ya qarfafa min gwiwa wajen kiranki da alkairi."
Wata ajiyar zuciya Islam ta sauke tace "Papa, Allah ya bar manaku, Allah ya qara muku lafiya mai anfani, a gaskiya ina alfaharin kasancewa yarku, nasan da za ace iyaye d'aya ne da suka rage a duniya mutanen kirki, to zan iya cewa kune kuma Allah ya mallamaka minku, kunga kenan nafi kowa sa'a."
Rumgumeta Umar Faruk yayi dan sak tana magana kamar mahaifiyarta, Khairat ce tace "ina magana ka min shiru saboda kana magana da 'yarka."
Shiru yayi yana kallon yaran da suka mik'e suna fita daga d'akin, yana ganin ficewarsu ya janyo hannun Khairat ta taso ta fad'a saman qafafunshi yana fad'in "ashe 'yarki ta fini muhimmanci yanzu?"
Da mamaki tace "ban gane ba, meya faru?"
"Tunda har zaki fad'a mata kina da ciki alhalin ni ban sani ba."
Dariya tayi cike da kunya tayi qasa da kanta, binta yayi da kallo yana murmushi, d'agowa tayi tace "kenan lab'e kake mana idan muna sirri nida yarinyata?"
"Eh mana, kuma daga yau zan fara, danna fahimci abinda kike fad'a mata ma ba kya fad'a min."
Kallonshi tayi tace "wai kishi kake da hakan?"
Turo baki yayi gaba yace "eh mana, naga yarinya na neman rabani da babyta ba dole ba."
Danna kanshi tayi tsakiyar qirjinta tana fad'in "babyna sarkin rigima, in banda abin baby ai Islam daban, kuma baban Islam daban."
"Taya zan tabbatar da haka?" cewar Umar Faruk.
Saida tayi wasa da idonta kafin tayi murmushi tace "bara ka gani."
Hijabinta ta bud'a ta zura kanshi a ciki ta fito da nononta tasa mishi a baki tace "har yanzu baban Islam nasha nono, amma Islam ko a mafarki ba zata sha ba saboda ta wuce nan."
Yana jin bakinshi a qamamin nonuwanta kawai saiya narke ya rufe ido ya fara tsotsa yana sauke numfashi da k'arfi, da qyar ya rabu da ita ya ta samu ya kashe wuta ya rufe d'akin, dawowa yayi a hankali ya kwantar da ita kan gado ya ta fara kulawa da ita wata duniyar, da qyar ta samu ta kalleshi tace "baby, ka sarara min mana, jiya fa baka bari nayi bacci ba, gashi ina buqatar nasa wani abu a cikina, idan ka qara yanzu fa zan iya mutuwar maka."
Dariya yayi yace "ba laifina bane baby, laifinki ne da kika zama mafi zak'in zuma da kuma gamsar dani, idan a ra'ayina ne saina shekara tare dake ina abu d'aya, domin kuwa bana gajiya dake ko kad'an, kuma da kike cewa kina buqatar zaki ci wani abu ai wani abun zan baki kici, dan haka ki daina maganar mutuwa ma dan tare zamu mutu."
Yana fad'a ya sake wata addu'ar cike da son kaiwa a bakin gab'a ya zura kanshi, wata irin ajiyar zuciya ya sauke mai kama da kuka, qamqameta yayi yana fafutar sauke numfashi, itama yar siririyar qara ta saki saboda ratsata da yayi, wanda hakan harya zamar mata jiki indai zai shigeta, ya jima a haka kafin ya fara rad'a mata a kunne cikin muryar kuka "Khairat kin had'u, wata rana zaki kasheni da wannan d'and'anon naki, wallahi bana gajiya dake ko kad'an, dan Allah ki taimaka ki rage wahalar dani haka, Khairat na baki kaina da komai dana mallaka, na baki kyautar yayana duka dama gidan nan, Khairat, yawwo Allahna...."
Danna kam kamar karatu ne da kullum saiya biyashi, dan haka ta rufe mishi baki da bata bakin dan karya tona mata asiri yara duk sun farka....
Bayan awa uku suka fito cikin shirin tafiya gidansu Mamie, yaran suka samu zaune sunata hayaniya sai Zuby zaune a kujera tana kallonsu, kallonsu Zuby tayi har cikin zuciyarta taji sun birgeta saboda qyalin da suke fuskokinsu d'auke da tsantsar farin ciki, harga Allah ta sani sarai Khairat ta mata nisan da ba zata iya kamata ba, ta sani ta fita kula da mijinsu yanda ya kamata, da murmushi a fuskarta tace "auntyna barka da fitowa."
Kunyace ta lullub'e Khairat, cike da basarwa tace "barka yer uwa, kina zaune."
"Barka oga." ta fad'a tana kallonshi.
Da murmushi shima yace "barka amaryata, ya yaran?"
Tsaye ta mik'e tace "bismillah ko, abincinku na jiranku."
Dinning suka nufa Khairat na fad'i "yara sun karya?"
"Ai harni na karya, dan naga idan mun tsaya jiranku sai olcer ta kamamu."
Yanda Zuby tayi maganar yasa suka kwashe da dariya suna zaunawa, da kanta ta zuba musu sannan ta zauna suna ci ita kuma tana kallonsu suna hira gaba d'ayansa, saida suka gama Khairat tace "yer uwa zanje gidana amsa kiran Mamie, amma da yaran zamu tafi."
"Dukansu?" cewar Zuby.
"Eh to, ki zab'i wanda kike so na bar miki, saina tafi da wanda suka rage."
Turo baki tayi gaba tace "auntyna ba wayo zaki min ba kuwa, kinsan ba zan kasa cewa ki bar min Islam da Ammar ba, kuma nasan dole kina so ki tafi dasu saboda su Mamie nasan ganinsu."
Cije baki Khairat tayi tace "umm gaskiya kam, to kinga na bar miki Ihsan saboda ta kama miki wasu aiyuka, koya ki kace?"
"Eh to, hakan ma yayi." ta fad'a da fara'a.
D'ora hannayenta tayi akan tebur d'in ta matso da kanta kusan fuskar Zuby tace "toya maganar girki? kinsan fa mijinki acici ne."
Dariya Zuby tayi kafin tace wani abu Umar Faruk ya gimtse hak'ora yana d'aukar makullinshi da waya yana fad'in "idan akayi gulmata Allah yana sama yana kallo, kuma ba zan yafe ba."
Kamar had'in bakin Khairat da Zuby suka kalleshi suna fad'in "zaka yafe ne ai."
Kallon juna sukayi saboda had'a bakin da sukayi, Khairat ce ta d'ora da "zaka yafe idan kaji matsa."
Qasa da sama ya hararesu yace "to saina gani ai idan dole za'a sani."
Zunbur suka mik'e sukayi kanshi da sauri ya bar wajen yana fad'in "kuyi hak'uri dan Allah, wallahi ban shirya canza wannan kayan ba."
Dariya suka saka mishi kafin yace "uwar gida sarautar mata, ke kawai nake jira ki wuce muje idan kun gama kacaccana min yara kamar naman miya, dan ba zan barki kiyi tuqi da kanki ba."
kallon Zuby Khairat tayi ita kuma ta rik'e hannun Khairat tace "baki da matsala auntyna, kije gida kisha zamanki ki huta, girkin rana dana dare yana kaina insha Allah, zan kula da komai kamar kina nan."
Dafa hannunta tayi tace "na gode sosai yer uwa, sai mun dawo."
"Ku tashi mu wuce, Iman kiyi hak'uri ke zaki zauna gida tare da Mamie kinji."
Tashi yarinyar tayi ta rik'e hannun Khairat tace "Mamie ina so naje tare daku nima."
Shafa fuskarta tayi tace "karki damu kinji yata, kiyi hak'uri ki zauna, na miki alk'awari fita ta gaba da zanyi dake kad'ai zan tafi."
"Da gaske Mamie?" ta fad'a da murmushi.
Da ido kawai ta mata alama dan haka ta musu addu'a sai sun dawo suka fice Umar Faruk na fad'in "harda wani fita ta gaba, to waya fad'a miki zaki fita? aike da fita saikin haife abin cikinki insha Allah."
"Ko kuma idan ka haife ba, dan wannan karan kai zaka haihu kaji me muke ji, duk da dai ana cewa waini kamar kyauta nake samun yaran, saboda fasani kawai ake ana fitowa dasu, bansan zafin da ake ji ba n'a a lokacin da yaro yake son fitowa ta gaba ba."
Hakan yayi daidai da zuwansu b'angarensu Mama, da sallama suka shiga nanma sun jima suna gaisawa da tsokanar da yaran ke musu, kafin nan suka fito suka wuce, sai lokacin ya jefeta da tambayar maganar da tayi lokacin da zasu shiga da fad'in,
"Inji wa? ai kinfi kowa wahala." ya fad'a lokacin da yake zaunawa mazauninshi.
Kallonta yayi yace "ai insha Allah kema zaki haihu da kanki, da yardar Allah zaki ji me ake ji kema."
Dukanshi tayi a kafad'a tana fad'in "baby, wacce nake yi ma fa akwai zafi sosai."
"Na sani, amma ina so ya tsaga ya fito ta gaba." yayi maganar qasa qasa yanda yaran ba zasu ji ba.
"Ashe baka sona, amma karka damu zan baka mamaki, wannan karan da kaina zan haihu in Allah yaso ya yarda."
"Haka nake so." ya fad'a da kanne mata ido.
Gida ma koda suka isa gaba d'aya suka shiga ciki, sun samu Papa dan haka suka jima suna tab'a hira kafin Umar Faruk ya barsu a zuwan saiya dawo da dare, duk da Marwane Iman da Kaussar ba daga cikin Khairat suka fito ba, amma sun sake sosai a gidan kuma su Mamie babu wani banbanci da suke nuna musu, haka yaran keta wasarsu har suka fita harabar gidan lokacin ne kad'ai Mamie ta samu ta keb'e da Khairat, anan ta fito da takardu da makullai da kuma check na kud'i ta bata tana fad'in "wannan sune abubuwan da mahaifinki ya bani a matsayin godiyar zama da nayi dashi, takardun gida ne dana compagninshi dake sarrafa kayan roba, sai kuma makullan gidan dana mota, da kuma check ta kud'i har million goma sha biyar."
Da farin ciki Khairat ta rik'e kayan tace "wow Mamie, a gaskiya na tayaki murna, Allah ya qara danqon qauna, ya albarkaci zuri'arku."
"Ameen, amma Khairat ba zan iya rik'e abubuwan nan ba, sunyi yawa, gashi kuma girma yana zuwa mana, ke kad'ai gareni a fad'in duniya, dan haka nima na mallaka mikisu halak malak."
Biro ta fito dashi tayi rubutu akan wata takarda sannan tace "zanyi magana da lawyer, komai zai koma naki."
"A'a Mamie, nima ban amsa ba gaskiya, idan kuma ba kyaso to kawai zai a miki kyauta dashi."
"Na riga da na saka hannu, kiyi abinda ya dace kawai mallakinki ne yanzu."
Ba yanda Khairat ta iya haka ta rik'e wannan kayan, suna nan har zuwa karfe 09:15 na dare sannan Umar Faruk ya iso, saida ya jira ita da yara suka gama harhad'a komantsansu kafin suka wuce, koda suka isa gida kowa wanka yayi babu wanda ya kula ta abinci sai Umar Faruk kad'ai, amma su sun qoshi tun daga can dan haka kowa yabi lafiyar katifa suka kwanta, dare yayi Umar Faruk da Zuby suka tashi daga kallon tarihin annabi Yusuf kowa ya nufi makwancinshi, zai shiga d'akin Khairat yaga haske a d'akin Islam, d'akin ya nufa a hankali ya tura qofar d'akin, zaune take akan sallaya ta d'aga hannaye sama sai kwararo addu'a take a harshen labarci tana kuka sosai, kallon Iman da Ihsan yayi dake kwace akan gadajensu suna bacci, qarasawa yayi wajenta ya sunkuya yana kallonta, tana kallon mahaifinta ta goge hawayen tace "Papa, baka kwanta ba?"
Cike da qaunar yarinyar yace "Qaramar Khairat ya zan kwanta alhalin baki kwanta ba."
D'an murmushi tayi tace "yanzu zan kwanta Papa."
"Amma me yasaki kuka haka?"
Yana tambayarta saita sake fashewa da kuka zuciya a wuya, fad'awa tayi jikinshi tana kuka sosai, da qyar ya rarrasheta yace ta fad'a mishi meya faru, cikin muryar kuka sosai tace "Papa, Mamiena nake wa addu'a, ina tausayinta sosai Papa, d'azu Mamie ta fad'a min bata damu ba dan an fasata an fito damu, ita kawai burinta ta ganmu a raye, Papa Mamie tace zata iya haifa maka yara goma sha biyu kuma duk a fasata amma ba zata damu ba, Papa naji girman mahaifiyata ya qaru a idona kuma ina sonta fiye da yanda nake son kaina, Papa bansan me zamu sakawa mahaifiyarmu dashi ba, Papa shi yasa nake kuka saboda rashin sanin sakamakon da zanyiwa Mamiena."
Shafa bayanta ya dinga yi cikin taushin murya yace "Islam."
Da sauri ta kalli Umar Faruk saboda tunda take bata tab'a jin sunanta daga bakinshi ba, kafeshi tayi da ido tana sauraronme zaice, cikin nutsuwa yace "mahaifiyarki macece da babu irinta nidai a wurina, zuciyar Mamienki zuciya ce da koni dana zama malaminta wallahi bana da irinta, Islam mahaifiyarki tamin alkairi da dama kuma ta nuna min soyayya tare da kulawar da banyi tunanin zan samu ba a rayuwata, ku 'ya'yanta ne dole ta soku fiye da komai, kuma ina fad'a miki da babbar murya kiji da kyau Islam, son da mamanki take miki bana miki ko d'aya daga cikin uku, domin kuwa ni ubane mahaifi, a lokacin data d'auki cikinki an cutar da ita sosai ba ba tare da haqqinta ba, saida takai lokacin da ko ruwa tasha saita amayesu, amma bayan ta samu lafiya ta kuma san ba zata iya haihuwa da kanta ba, wallahi Islam ko sau d'aya bata tab'a nuna min damuwa akan hakan ba, saiya zamana kullum tuna min take akan idan ta fara naquda a kaita asibiti da gaggawa, amma kasancewata ina namiji sai nake ganin kawai zata iya haihuwa da kanta, saina dinga fad'a duk lokacin da tace haka, amma ita burinta kar abinda ke cikinta yasha wahala ba zata so hakan ba, a ranar da aka fito dake daga cikinta sai tayi qoqarin barina a cikin wannan duniyar, bansan tsoroba, amma a ranar na tsorata a lokacin da naga ana fafutukar ceto rayuwarta, maganar Islam a wannan lokacin na fidda da matata, a take a wajen na qudurawa raina zan rad'a miki sunan Islam kamar yanda ta buqata, amma ni zan dinga kiranki da Khairat, amma sai ubangiji yayi ikonshi ta hanyar maido min da farin cikina, wannan yasa kullum nake cikin godewa Allah, maganar da ki kayi kuma ta rashin sanin me zaki sakawa mahaifiyarki dashi, kinsan me zaki yi?"
Kai ta girgiza tana share hawaye, d'orawa yayi da "ki daina kuka idan kina wa mahaifiyarki addu'a, abu d'aya da zakiyi shine, ki dage kullum wajen sakata addu'arki, na biyu kuma shine ki tsaya tsayin daka wajen kyautata mata da kuma yi mata biyayya, na uku kuma ki guji duk wani abu da zai b'ata ran mahaifiyarki, kin fahimta?"
Da murmushi a fuskarta tace "na fahimta Papa, kuma zanyi yanda kace insha Allah."
B'ata rai tayi ta kalleshi sosai tace "amma Papa, waya cutar min da uwa da ina cikinta?"
Kallonta yayi yace "me zakiyi, me yasa kike so ki sani?"
Fuskarta ba alamar wasa ko kad'an tace "zan tsani wanda ya cutar min da uwa, zan sakashi addu'ata Allah ya sakawa mahaifiyata."
Hannunta ya rik'e yace "a'a Islam, wannan ba halin mahaifiyarki bane, burina shine duk wani yaro daya fito ta tsatsona koda ba ita ta haifeshi ba to yayi halinta, tana da yafiya da mantuwa ga alkairin da tayi, ba zan fad'a miki ba dan bana son haddasa gaba a cikin gidana, amma ina umartarki daki yafewa wanda yayi kamar yanda mahaifiyarki ta yafe itama."
"Papa, Mamie ta yafewa mai laifin?" ta fad'a da mamaki.
Murmushi ya mata yace "sosai, aina fad'a miki ita ta dabance, shi yasa nake qara qaunarta kullum."
Itama murmushi tayi tace "shi yasa Mamie bata tab'a yin hushi da kai ba Papa, sai taje islamiyya ka daketa a hannayenta amma ba zata nuna ba a gida."
"Wannan shine karamcin Khairat."
D'aukarta yayi ya dire akan gado ya rufeta da zani yace " kiyi bacci lafiya gimbiyata."
Da murmushi tace "ka kula min da mamana."
Kumatunta yaja yace "wato ni kin wareni ko?"
Da dariya tace "uhhibuka ya Abhi."
Shafa kanta yayi yace "uhhibuki kasiran."
Da haka ya kashe wutar d'akin ya koma d'akin Khairat, tsaye ya sameta tana sallah, amma tana ganinshi saita fara gaggawa dan karta shiga haqqinshi, da hannu yace "kici gaba kawai."
Dan haka bata tsaya ba taci gaba, zaune yayi a tsakiyar gado yana kallonta yayin da yake fad'a a zuciyarshi "haqiqa kyawun zuciyarki ne ya mallamaka miki yarinya kamar Islam, dama Allah yayi alk'awari yana tare da masu hak'uri, kinyi hak'uri kuma gashi kina tare da ubangijinki, da idona ina ganin suffofin yan aljanna a tare dake, kamar yanda nake ganin wacce Allah yake so, a Qur'ani Allah ya fad'a mana wad'anda yake so, kuma kusan duka kin had'a wannan suffofin, Allah yace yana son masu hak'uri, kina da hak'uri alkairina, Allah yace yana son masu tuba da tsarkakewa, kina tuba daga kurarenki na baya da kuma tsarkake zuciyarki a kullum, Allah yace yana son masu tawakkali dashi, kin dogara ga ubangijinki, da kuma sauran suffofi da dama, ina fatan Allah ya qara miki imani da tausayi a zuciyarki, Allah ya baki yaran da zasu ji tausayinki kema."
***************
Kasancewar yau safiyar Alhamis ce yace duka gidan suka tashi da azumi, Khairat kuma ta bawa Umar Faruk wannan kud'in da Mamie ta bata, tambayarta yayi "na miye kuma?"
Cikin fara'a tace "Mamie ta rasa yanda zatayi dasu, shi yasa na baka a matsayinka na mai da'awa, kuyi anfani dasu wajen d'aukaka kalmar Allah, ina so sakamakon ya samu mahaifiyata a duk inda take."
"Khairat, yanzu gaba d'aya kud'ad'en nan kin bayar ayi hidimar addini da ita? Allah kad'ai zai biyaki, kuma insha Allah zanyi iya qoqarina wajen ganin anyi abinda ya dace."
"Haka nake son ji, Allah ya taimaka."
A wunin ranar Ruk'ayya tazo gidan tare da yaranta uku saina biyar dake ciki wanda ba zai wuce wata shida ba, dukansu zaune suke a falonsu Mama, yayin da Aunty Saratu ke d'auke da tsohon ciki matar Usman ma da Aliyu ga kuma Ruk'ayya, hira ake sosai cike da farin ciki da nishad'i, Saratu ce ta kalli Aliyu tace "qaramin miji dan Allah ka taimaka ka siyo mana alala muci."
"Ke fita idona in rufe, da wane kike so naji to, siyan alala ko siyan rago, dubeku fa ku uku zan siyawa ragon suna, wataqila ma cikinku wata ta haifi yan biyu."
Umar Faruk ne ya kalleshi yace "uku kuma, biyar dai ko."
Kallonshi Aliyu yayi ya kalli Khairat da Zuby yace "oho, amma shine baku fad'awa mai siyan ragon ba, to shikenan banda ku a ciki."
Hararanshi Khairat tayi tace "to miye namu a ciki, d'anka za'a goranta ma ace baka siya mishi ragon suna ba."
Zuby kam cewa tayi "nidai ka cireni ma a lissafi, idan akace dukanmu muna d'auke dashi ai sai abun yayi yawa."
"Inji wa, ba wani yawa, suka zamu iya ji daku."
"To nidai ban dani gaskiya." cewar Zubyn.
Umar Faruk ne ya bita da wani kallo yace "in tona?"
"Ka tona mi?" ta fad'a tana kau da kanta.
"Kice eh kawai kiga aiki da cikawa, saina tona tun daga farko."
Da sauri tace "dan Allah rufa min asiri nidai, kar kamin tonon silili."
Dariya aka saka Khairat tace "yer uwa ashe dai gaskiya ya fad'a, to Allah ya raba lafiya baki d'ayanmu."
* To nima nace ameen my lovely and lovely Khairiri*
Allah ya saukeku lafiya Family Ahmad.
Anan nazo qarshe yan uwa, duk da banso abin yazo a haka ba, amma dai nayi qoqari na qarasa muku shi, bansan ko zaku sake jina ba, amma dai ina muku fatan alkairi masoya.
*Mamien Bk*
*Momyn Sultan*
*Momyn Khadija*
*Auntyna Aisha*
*Sis Alawiyya*
*Yar mulki*
*Bilqies*
*KawaTa Hussy*
*Munirah*
*Wassia*
*Ummu Faruk*
*Aisha mahamane*
Da sauransu ina miqa godiyta a gareku, ina alfahari daku.
BISSALAM😘
Sameera Harouna.
0 comments:
Post a Comment